Maradams Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 2 by Aysha A Bagudo.txt
Chapter 13 of 14
Page 24
yadda yake fari tas tmkr balarabe da yadda idanusa suke da d'an girma da dogon hancisa yanayin tsayinsa fuskarsa sai gashin bakinshi dake zagaye da gemunshi komai shine hatta yanayin fuskarsa da take a d'aure ba'a bari ba."muryarsa a kasalance "very nice !ya fad'a yana sauke numfashi had'e da gyara tsayuwarsa yana kallon zanen kansa ."cike da tsinkewar zuciya yace "a kira number wayar wanda yayi zanen nan kasancewar yaga kowani creations dake ajiye ajikinsa akwai farar takarda makale mai dauke da number waya da address sai dai ita maryama iya number wayarta kawai tasa "okay sir cewar James cikin abinda bai wuce one second ba ya juya har ya kai bakin kofa ya tsaya batare daya juyo ba "ka biyoni da creations din "James ya sake cewa "okay sir!"Cikin abun da bai wuce minti goma ba James ya shiga neman layin maryama da number compaing dinsu amman number a kashe ya jaraba kiran yafi sau goma still dai swcth off ake maimaita masa dan haka ya shiga office din ATA cike da girmamawa ya rusuna yana cewa "sir nayita qoqarin neman layin amman swcth off ake cewa "okay keep trying !ya fad'a yana cigaba da operating system." wuni ranar James duk akan kiran layin maryama ya qare amman still the same thing ake fad'a masa ."
Washegari ATA na zaune akan kujera yana kallon screen din system dinsa gefe guda kuma yana jin bayanin James bai ce uhm ba bare uhm umm har sanda ya dasa aya inda a karshen maganarsa ya dan nemi ya rikitashi a natse ya ture system din gabansa ya mike tsaye ya zagayo ya zauna akan table yana dubansa "okay itace girl din jiya kenan ?cike da tashin hankali yayi shiru ya kasa bashi amsa "da kai nake magana fa cike da matsanancin tsoro yace"Yes sir itace !shiru yayi yana sake jin bugun zuciyarsa na qaruwa akan na jiya ya kai idanunshi kan tangamemen zanen dake ajiye a office dinsa yana kallo yana jin wani irin sanyi ajikinsa tunda yake bai ta'ba jin abinda ya tsaya masa arai ba Kmr princess dinsa sai yarinyar jiya da kuma wannan zanen "wanna duk kuskuren ku ne mutun yazo da irin abu haka mai matukar mahimanci ai ko dan darajan kokarin da mai shi yayi wurin zanani ya kamata ku bashi kulawa ta musaman sannan kafin ku aiwatar da komai ku nemeni but wannan laifi stupid sectary ce bani da time dinta yanzu zanji daita later gabdaya zanenta yafi na kowa kyau ina son ganinta eyes to eyes ina son nasan yadda akayi ta zanani haka
bansan me yasa kuke wa masu zuwa ma'aikatan da wata bukata haka ba ?yayi maganar a matuqar fusace “we are sorry sir “ shiru ATA yayi yana ciza lip’s dinsa da karfi ."
Maryama suna zaune a parlour’nsu tare da yaya sadam suna hira kira ya shigo wayarsa kamar koda yaushe shiru yayi gabansa na faduwa ya rasa dalili yasa bata kiransa sai lokacin da yake tare da maryama daga maryama har yaya sadam shiru sukai suna kallon juna muryarta a matukar sanyaye tace “yaya sadam ko akwai damuwa ne ? ya girgiza mata kai alamun babu komai “no yaya sadam karka boye min idan akwai damuwa ka fad'a min zan fahimceka “nace babu wata damuwa still kira ne ya sake shigowa wannan shine karo na biyar ana kiranka baka dauka kuma kace babu komai kuma duk sanda zamu kasance tare zayita kiranka bazaka d’auka ba amman shikenan tunda ni ban kai matsayin da zaka sharing problem’s dinka dani ba gara kawai a fasa auren nan dan ina ganin Kmr akwai damuwar da kake boyewa “ta fad'a tana mikewa tsaye zata shiga da sauri ya rike hannuta yana cewa " haba sauraniyata Kiyi hakuri babu wani damuwa kema kinsan idan akwai zan fada miki idan kika fasa auren nan ai sai dai kisan yadda zakiyi dani da ummah nah dan mutuwa zamuyi ya qarasa mgnr a marairaice.”
murmushi tayi wanda ya bayyana wushiyarta sama da kasa sannan ta koma ta zauna tana cewa “haba yaya sadam wasa nake maka amman bani wayar naga su wa ke kiranka haka “ ta kai hannunta zata d’auki wayar ya dauke wayar da sauri yana cewa “no no!!” oh am sorry shikenan kayi hakuri na shiga rayuwarka ,no karki damu kace kana sona yanzu ?
”sosai kuwa dan zan iya rasa raina idan kika barni amman me yasa baka son fad'a min damuwarka matsalarka sannan ni ina son ka dinga tmbyta wasu abubuwa da suka shafi rayuwata sirrikana me nayi da sauransu "yanzu duk abinda nake miki bakya gani ? Ta gyada masa kai alamun a’a “zan fashe miki da kuka fa maryama yana rufe bakinsa kira ya sake shigowa wannan karon yace “ excuse me tare da mikewa tsaye “ am very sorry yaya sadam saboda ni ka kasa daukar kiran daake maka ,babu komai kaje daga waje ka amsa kiran ya gyad’a mata kai ya fito waje yana amsa kiran muryarsa can qasa qasa.”
Mikewa tayi cike da sanyin jiki ta fito haraban gidan tana tafiya a hankali tana tunanin yanayin yaya sadam wayarta ce ta dauki qara ta duba taga number compaing din da taje neman aiki ne suka mata wulakanci "taja dogon tsaki ta katse kiran wani kiran ya shigo still tayi discounting kira na uku ya sake shigowa " ta sake jan tsaki "ina ganin sai na kashe wayata gabad’aya zasu daina kirana ta kashe wayar tana cewa “marasa mutunci bayan kun gama wulakantani sannan ku dawo kuna kirana kiran me kuke min? .dan girman Allah nadia ki daina damun kanki da yawon kuka ,nima ina sonki amman maganar da nake miki yanzu aurena ma ya kusa ana daf da daura min aure da yaruwata , ki manta dani kawai komai ya rigada yazo karshe a tsakaninmu Allah ya baki wanda ya fini , look nadiya dan allah karki sake kirana ..” yana juyowa yaga maryama tsaye a bayansa “kai dawa kuke waya har kake cewa karta kara kiranka aurenka ya kusa ?”shiru yayi ya rasa amsar da zai bata dan haka ta juya zata bar masa wurin ya riko tsintsiyar hannunta "please maryama! ta juyo tare da tsura masa narkakkun idanunta wad’an da ‘bacin rai ya qara narkar dasu “ka tsaya kana kallona tambaya ce mai sauki nayi maka.”
“ shikenan wata yarinya ce dake sona tare mukai karatu daita amman na rigada na fad'a mata bazai yuwu muyi aure daita ba dan na kusa aure nan bada jima ba ,amman gbdy ta kasa fahimtata numfashi ta sauke tare da cewa “ maza Kenan " allah ki yarda dani Kiyi hakuri idan kinji babu dadi aranki yaya sadam mai yasa zaka wani damu kanka haka ai babu komai? “ tayi shiru tare da kamo lip’s dinta tana jin zafi a zuciyarta , yanzu taji da kunnenta yana furta mata yana sonta amman kuma wai ita Ke sonshi tô su maza zuciya nawa garesu ?”numfashi ta sauke tace “amman duk lokacin da zamu kasance tare tana kiranka amman idan na tmbyarka sai ka boye min why yaya sadam alhalin zuciyarka na sonta ?” shiru yayi ya kasa furta komai yana kallonta gabad’aya yanayinta ya canza har kwayar idanunta ? ni kinji na fad’a miki ina sonta ?da mamaki take kallonsa lallai halin maza sai su idan suna da mata biyu soyayyarsu biyu ce fa byn ta gama kallonsa tace “yaya sadam ban san me yasa ba zuciyata ta kasa yarda da baka son yarinyar nan domin gbdy yanayinka ya nuna akwai soyayyarta mai karfi a zuciyarka ,do you know something yaya sadam ?cigaba da kallonta yayi ya kasa cewa komai “idan kasan tsakani da Allah kana sonta ka aureta dan ni bana son boye boye arayuwata komai nafi son gsky da gsky amman kai gbdy baka son mu gina soyayyar mu akan hakan“.
“no karki yi wannan tunani “ ni dai idan kasan zuciyarka ta rabu gida biyu dan allah ka hakura dani ka tsaida zuciyarka wuri daya” tana gama mgnr ta zare hannuwanta zata juya ya riko tsintsiyar hannunta bata juyo ba ya zagayo ya tsaya gabanta yana kallonta tare da kamo d’ayan hannunta ya kai bakinsa yayi kissing sannan ya cigaba da mgn “ina sonta amman nafi sonki maryama akanta ki yarda dani tunda har zan iya hakura daita na aureki ya kamata ki gane sonki yafi nata ,amman wannan ba adalci bane yaya sadam ya kake son tayi da sonka ?ka kuwa san yadda mace take ji acikin zuciyarta idan an kayi breaking heart dinta ?kasan halin damuwar da take ciki a yanzu ?ya zanyi maryam kafin na shigo da maganarta ummah ta zarta da hukunci akaina kin fi kowa sanin komai ya kamata ki fahimceni ki min adalci . magana ta gskiya ni yanzu Ke nake so shiyasa nake bata hakuri ,kiyi hakuri karki yi fushi dashi ahankali ya dinga kwantar mata da hankali . hankalin maryama ya kwanta “kin hakura ? na hakura tana gama fad’ar haka ta zare hannuwanta cikin nashi shige part dinsu shiru yayi kafin a hankali ya juya ya bar wajen ."
***
ATA na zaune a office haka nan zuciyarsa ta kasa samun natsuwa James ya shigo hannusa rike da cup din coffee ,sir ga coffee ATA ya karba ya curbi kadan ya ajiye "dan allah sir ko zan iya cewa wani abu yace “uhm !”me yasa ka damu kanka sosai dan an kira yarinyar nan taki dauka ? sai akayi ya kenan ? ya fad'a yana d’ago kansa” wannan shine abinda ya shigo da kai ?”no sir kawai dai bana son ganinka cikin damuwa ne ya numfasa kana ya cigaba da motsa lip’s finds “ni ba damuwa nayi daita ba yadda aka wulakantata ne ya dameni ,amman sir babu abinda aka mata na wulakanci kawai bayani aka mata akan lokacin da zata samu amsarmu, ni ina ganin damar kamar ranta a bace yake. “enough James ka dameni zaka iya fita please “james ya daga kafafunsa ya bar office din bayan kamar minti goma ya sake neman izinin shigowa cike da girmamawa ya tsaya gabansa “sir akwai wani dayazo yana son ganinka "babu wanda zan gani yanzu sai dai gobe ya fad’a tsawace .”
James ya juya da sauri zai bar office din yajiyo sautin muryarsa cikin fushi idan ka fita kace wa umar da sauransu suzo ina son ganinsu a conference room “okay sir ya qarasa fita da sauri "ATA ya mike yana zariya a office can kuma ya tsaya cak gaban zanensa yana kallo ya kai hannu yana shafa fuskarsa dake cikin zanen”hakika zuciyata na matuqar qaunar son ganin yarinyar nan zan so ta zana min zanen princess dina a qarshe na ajiyeta a qarqashin ikon AGC domin zatayi mata amfani .ya kai hannunsa ya shafa sumar kanshi yana furzar da iska mai zafi sannan ya d’auki zanen ya nufi wani d’aki dake cikin office dinsa “ kafin kace me manyan ma’aikatansa sun hadu conference hall a natse ya soma magan fuskarsa a hade “abinda zan fad'a maku shine ina bukatar ganin yarinyar data zana zanena acikin kwanaki biyu kacal a nemota a duk inda take acikin garin nan idan ba haka duk zaku rasa aikinku . a lokacin da yakewa maaikatansa magana system ne a hannunsa yana operating yana masu bayani “fatan kun fahimceni .”
“yes sir ."! suka furta gabadayansu ya juya a natse
ya koma office dinsa "ya zamuyi kenan ?suka furta atare cikin tsananin tashin hankali “ya kuwa zamuyi kawai mu dudduba muce masa bamu ganta ba ko kuma mu zakalu d’aya daga cikin wadan da suka kawo nasu muce itace .falalu ya kallesu gbdy yace” wai me yarinyar zata masa ?wata yarinyar mafarkinsa yake nema, ya zanata da kansa yau tsawon shekaru sama da goma sha kenan yana nemanta shine yayi tunanin may be bai zanata yadda ya ka mata bane yasa bai ganta a duniyasa ba shine fa yace a nemo masa kwararrun masu zane zai fad'a masu yadda take su zana masa ya gani tô cikin wad’an da suka kawo gwajin su aka samu mutun d’aya wacce ta zana shi kuma itace zanenta yafi d’aukar hankalisa “falalu yayi masu bayani atakaice “gbdy suka sauke ajiyar zuciya suna jinjina girman lamarin mai gidansu sun dade suna tautaunawa akan yadda zasu bullowa lamarin kafin daga baya duk suka watse ."
Tsaye James yake a gaban ATA a office dinsa cike da girmamawa yana masa bayani “sir yarinyar nan dana baka labari kwanakin baya akan tana da kwarewa sosai akan ilimin lissafi duk wani calculations na Z&A itace take yi wanda yasa ta samu gurbi aiki a karkashin Z&A amman taki, itace the same yarinyar da tayi zanenka ,kaf a garin nan itace ta iya zane mai matuqar daukar hankali ,intakaice maka sir yarinyar ta had’a komai na samu nayi waya daita amman tace bata bukatar yi mana zane “da mugun sauri ATA ya d’ago yana dubansa cikin tsananin fad’uwar gaba yace “ what ? She rejected our job again duk yadda masu zane suke shan wahala a kasar nan kafin a karbi zanensu .”wallahi sir nima nayi matuqar mamakinta babu yadda banyi daita ba amman ta kafe bata son aiki damu .”ATA yayi murmushin ciki sannan ya koma ya zauna sosai akan kujera yana jan numfashi da kyar “wannan shine karo na biyu da aka fad’a masa baa son yin aiki a masikatarsa, yaji abun ya damesa matuqar . “
a hankali ya cigaba da murmushin gefen baki wanda da gani kasan na bakinciki ne “ina ganin wannan yarinyar tana da damuwa a rayuwarta amman me yasa ka kawo min wannan dogon bayanin akanta tun kasan bazatayi aiki damu ba ?”kawai dai wai dan ..” dogon tsakin daya ja tare da furta “noncess.”yasa james yayi saurin cewa“Am very sorry sir ,amman tace zuwa nan gaba zata iya kasancewa damu tunda ATA yayi shiru bai sake yin mgn ba kawai bakinciki ne ke cin zuciyarsa sai faman tsaki yake ja yayinda kwakwaluwarsa na shirya masa yadda zai yi tazo hannu cikin sauki “lallai tunda zuciyarta ta zabeta dan dole sai ta kasance a qarqashin ikonsa kuma kome zaiyi zaiyi kuma yasan shi né da nasara “leave !ya furta wanda tuni james ya isa bakin kofar fita nan da nan ya kira layin wani yaronsa segun dake ogun tsate bayan ya d’aga kiran ya shiga fad’a masa abinda yake son yayi masa tare da number fad’a masa number wayar maryama kai tsaye batare da ‘bata lokaci ba ya soma aiwatar da aikin mai gidansa ta hanyar tura mata sako .”
***
“Heartbeat! firgigib maryama ta farka daga baccinta tana cewa “after dad ta kirasa tana hamma hade da mika tana dubansa” a ina ka kwana habib anan na kwana ina jiran shigowar ka ? “yanzu ka shigo ? shiru yayi yana dubanta “ kasan bana son kana kwana a waje habib mai yasa baka jin magana na kiraka yafi sau babu adadi wayarka akashe ,mai yasa baka jin magana “kiyi hakuri heartbeat wani abokina bello ne bashi da lafiya shine gabday nida sauran abokanmu mukaje dubasa to kuma babu wanda zai kwana awurinsa shine nida atiku muka tsaya” okay ! ta fad’a tana sakin fuska “gsky wannan abu ne mai kyau nasan dole zaka rama bacci da ganin idanunka bacci bai isheka ba, dan allah ka dinga kiyayewa karka daukowa mahaifiyarmu magana ka dai ga yanayinmu dan Allah ka rufa mana asiri karka bari abokai su koya maka shaye shaye ,domin shaye shaye shine abinda mutun zai yi ya gurbata rayuwarsa dan shi da samun kwanciyar hankali har abada “in sha allahu zan dinga kiyayewa amman fa yau ma acan zan kwana babu damuwa ai taimako ne amman ka kiyaye dan Allah ,ya shiga dakin mahaifiyarsu ta sake yin mika ta shiga dakinta .
Bai samu aunty a daki ba dan haka ya fito ya nufi kitchen adaidai bakin kofa suka hadu ya gaisheta male ki dafa min indomi amman a soya” kai kuma daga ina haka amman ba gidan nan ka kwana ba ?ta fad’a tare da bin gefensa ta wuce tana rike da kular shiru yayi “a ina ka kwana ? uhmm aunty laifina ne da ban fad’a miki ba dan ya fad’a min bazai samu damar kwana a gida ba “wai a wurin abokinsa bello zai kwana a hospital maryama ta bawa mahaifiyarsu amsa tana karba kular hannunta “wai mai yasa aunty bakya bari na miki aikin komai ne byn na iya ?ai sai na sangarce naje gidan mijin na kasa yiwa mijina komai “ ai kina aiki kuma ma girki ai na safe kawai nake “babu wata matsala da zaki samu dan kin kware in dai wurin girki ne maryama tayi murmushi farinciki samu nasarar kare danuwanta da tayi “kai aunty banda yabo fa kar azo aji kunya ta fad’a tana ware idanunta “.
babu wani yabon kai ai gsky na fad’a bazanji kunya ba matukar akan girki ne kai dama komai ma “wannan gsky ne male muna alfahari dake ,nima ina alfahari daku yarana shiru sukai gbdy har habib suna tunani maryama ta dubesu yau fa a lissafina sauran sati day’a a daura min aure gashi har yanzu aunty bakiyi maganar zuwa wajen yanuwanki damu ba “kai heartbeat kina son damun kanki akan wad’an nan mutanen idan mu bamuje ba su me yasa bazasu zo nememu ba ?”kawai ki sharesu mu cigaba da rayuwarmu cikin qaddarar rayuwar iyayenmu tare da yiwa mahaifinmu addua ,muje muyi breakfast suka zauna kusan atare suka saka aunty a tsakiya sannan suka fara breakfast maryama na cin abinci taji shigowar sako wayarta ta dauka ta duba tare da yin shiru ta dafe goshinta da hannu daya ta shiga dogon tunani “ya’akayi naga kinyi shiru ina tunanin yadda zan bar gida ne na rigada na saba da danuwana ,muyi hira tare muci abinci tare muyi kuka tare muyi dariya tare in fact komai ma “gara dai kiyi aurenki shine kwanciyar hankalinmu gbdy inji cewar habib maryam ta dungure masa kai” tana cewa “kenan bazakayi missing dina ba ?” zanyi mana ni ne ma zan fi kowa kewarki amman ya zanyi tunda aure zakiyi kuma zamu dinga ganin juna a duk lokacin da muka so kinga ai banga abun damuwa ba zamuyi komai Kmr yadda muka saba ya fad’a yana kallonta komai dai menene zan fi jin kewarka sosai .”
“ karki damu heartbeat idan ma kikace mu tattara kayanmu mu dawo gidanki mu zauna tare zamuyi tunda nasan yaya sadam ba mai damuwa bane inji cewar habib wani sako ne ya sake shigowa wayarta ta duba tana gama dubawa taja tsaki” yakayi princess ya kikayi tsaki “ wani kafanin ke son nayi aiki dasu na tura masu yanayin zane na tun da dadewa to basu tashi bukatata ba sai yanzu , at the same time ga wani sako daga ogun state wai suna son naje har kamfaninsu dake ogun state nayi masu zane , ni bama zanen bane damuwata ba yadda kmr yadda date din da zaa masu zanen ya zamo date din daurin aurena bari kawai na tura masu bazan samu dama ba su kuma wad’an can zan tura masu sako nan da qarshen wata zan zo na fara aiki dasu .“ fine daidai kenan amman zuwa ogun state din ma ai ba damuwa bane ta dubi habib taya zakace ba damuwa bane ?Ko nace zanyi hankalina bazai kwanta ba ,”zaki iya zuwa Kiyi bayan an daura aure idan kin dawo sai ki cigaba da hidimar bikinki tunda abun kwana daya ne “ ni dai gsky ban yarda kije har ogun state ba aunty ta fad’a gara ki hakura idan ba haka ba bazaki samu natsuwar hidamar yin biki ba daga yau hankalinki zai rabu gida biyu shiru sukai gbdy can maryama tace “ gsky kika fad’a “ni dai ina son kike ki fad’awa yaya sadam sai ya rakaki kuje tare “okay bari zan yi masa mgn muji meye raayinsa Kiyi masa mgn idan ya amince sai kuje tare .”
Bayan kwanaki uku
Tsaye yaya sadam yake a d’akinsa muryarsa can qasa qasa yana waya da nadiya “haba nadiya nasani nasan ban miki adalci ba amman kema Kinsan yadda nake mutuwar sonki ,soyayyar shekaru biyar fa ni kad’ai nasan me nake ji ajikina tabbas nasan laifina ne da ban shigo da maganarki da wuri ba har aka zartar da wannan hukunci ,No bazan iya cewa mahaifiyata haka ba . zan dai san abun yi ki kwantar min da hankalinki ki saurareni at anytime .a natse ya fito cikin jallabiya ruwan qasa kawai yaga maryama zaune ita kad’ai a falon .”sai daya zauna sannan suka kalli juna shi da maryam gano yanayin maryama kamar tana cikin damuwa ya matsota sosai har suna iya shakar numfashi juna dan a tunaninsa ko taji wayarsa ne ahankali ya kamo yatsun hannunta wanda yasa taji wani irin zirrr a sansar jikinta nan da nan tayi qoqarin zare hannunta bai damu ba yace “lafiya na ganki haka ?daman magana nake son muyi “ina jikin me zaki fad’a min ?”amm amm daman akan wani aiki ne daaka kirani nace na fad’a maka nan dai tayi masa bayanin komai ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta “kinji abinda naji kuwa ?wani irin aiki ne har ogun state kuma a ranar daurin aurenmu ?nan da nan jikin maryama ya kama rawa “kayi hakuri bansan mgr zata bata maka rai ba na hakura ba sai naje ba na cigaba da aikina anan daman ba wai zasu d’auke bane aiki ne na lokaci zuwa lokaci kuma ba aikin kwana bane amman kayi hakuri karkayi fushi dani ta qarasa mgnr muryarta cike da rauni .”
ya kalleta cike da tausayinta sakamakon yadda take magana cikin sanyin murya da tsoro ,ita kanta a yadda take maganar tana jin babu dadi har cikin ranta “shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu me kike ganin zamuyi ?”ya tambayeta cikin sanyin rai “tô wai idan ka amince sai muje tare da kai ,idan kuma baka amince ba wallahi babu komai na hakura allah ya zaba min abinda yafi zama alkhairi murmushi ya sakar mata yace “shikenan karki damu amaryata zamuje tare ai ni yanzu duk abinda kike so ina so ko bangon duniya kika ce zamuje tare allah ya nuna mana ranar nan da nan murmushi ya bayyana a fuskarta “amman naji dadin amincewarka wallahi baka ta’ba sakani farinciki irin na yau ba na gode sosai allah ya jikan iyayenmu Allah yasa suna aljanna Allah ya saka maka da alkhairi Allah yaja da kwanan ummah ,Allah ya bamu zaman lafiya a arayuwar aurenmu “Ameen Ameen ya Allah Allah ya nuna min kin haifa min yara masu yawa tasa hannu tana rufe fuskarta nan suka cigaba hirarsu.”
Ranar lahadi 14 ga watan October shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auren maryama da yayanta sadam .ana gama daurin aure suka fara shirin tafiya ogun state wanda kusan yaya sadam ne yayita matsa mata ta d’auko kayan aikinta tare suka shiga wajen ummah lokacin tana tare da yan’uwanta dana mijinta tayi masu fatan alkhairi fuskarta dauke da farinciki maryama ta zama mallakinta gabdaya lokacin da zasu wuce aunty hassna tace “yanzu dan lalacewa aunty har da murna kike tun baaje koina ba an mallake miki d’a “cak maryama ta tsaya cike da sanyin jiki “me zanyi hassana matarsa ce kuma ya amince tunda ya amince meye nawa aciki ?kunga kuyi maza ku kama hanya Allah ya tsare min ku suka sa kai zasu fice har sun kai bakin kofa umma tace “sadam ya juyo daga inda yake “ka kular min da maryama da kyau ,Allah ya tsare hanya “to ni ummah bazakice ta kular miki dani ba ?tayi murmushi shikenan “maryama ki kular min dashi Allah yayi maku albarka suka ce “ameen suka fito suka shiga mota suka d’auki hanyar ogun .”
Cikin sauri sauri ATA ya fito daga dayan bedroom dinsa cikin wasu had’ad’den kanana kaya bakake ajikinsa ,ya shiga dayan dakinsa wanda kusan abubuwansa masu mahimanci anan suke, yadda jikinsa ke fitar da kashin turarensa reed akoda yaushe haka dakin Ke dauke da kamshin turensa, cikin sauri ya dauki farin glass dinsa ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya dauki agogo baki ya daura a tsintsiyar hannunsa ya bude bedside ya dauki wallet dinsa ya tura cikin ajihunsa ya daura facing cup yayi mugun kyua ya fito sanyayyen kamshin turarensa na binsa cikin sauri yake taka step cikin . a zaune ya iske mami tana waya ya d’an tsaya yana kallonta dan ga dukkanin alamun da wannan yarinyar take waya gyaran murya yayi yana sham kamshi ta waigo tana dubansa “ina zuwa kuma ? wani aiki !ya bata amsa atakaice yana had’e gira sama data kasa dan kar ma tayi masa mgnr mrym “naga yau weekend ce ?eh ogun state zani zan iya dawowa a yau watakilla kuma sai gobe dan aikin nada matukar mahimanci .”yana gama fad’ar haka ya nufi kofar fita .”
To adamcy mami fatan nasara
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 25
Tafiyar awanni hud'u ta kawosu maryama ma'aikatan ATA dake jahar ogun state yaya sadam yayi parking din motarsa acikin haraban ma'aikatan sannan suka fito atare yana gyara zaman farar shaddar jikinsa yayinda maryama ke qoqarin neman layin mr segun kira d'aya mr segun ya d'aga sukai magana na second biyu sannan ta fuskanci yaya sadam fuskarta kwance da annurin farinciki mara iyaka tace "kad'an yi hakuri yanzu za'a yi mana iso zuwa ciki " yaya sadam ya gyad'a mata kai kawai alamun babu komai yana sakar mata tsadaddaden murmushinsa ,suka tsaya suna magana kasa kasa kafin ayi masu iso .wani matashin saurayi ne ya sauko sanye da bakaken kaya ya shigar dasu ciki .
a wani dogo office aka shigar dasu wanda gabad'aya nsa glass ne dan ana iya hango duk wanda yake ciki ,basu d'auki cikakken mintuna goma ba mr segun ya shigo yana tmbyr saurayin daya shigo da
su maryama "niyi ina bakuwar daka shigo daita ?
"sir itace a gabanka zaune” mr segun ya d'an ware idanunshi akan maryama dake zaune yana mata barka da zuwa yana mai sake masu iso zuwa wani office din dabam wanda daga shi sai wanda ATA yake cikin zaune zaman jiran qarasowarta .
"kusa da maryama yaya sadam ya samu waje ya zauna kamar zai mata numfashi "madam ya hanya ?"
mr segun ya tambayeta cike da kulawa yana kallonta "alhamd sir tunda gamu mun samu mun qaraso lfy amman fa da kyar dan hanyar nan taku bata da kyau tafiyar da ya kamata ace one to two hour's ne ya kawomu shine ya d'aukemu har four hours amman alhamdulillah "wannan gsky ne mutane na yawon complain akan hanyar nan tamu amman dai alhamd tunda kun qaraso lafiya tun mai gida bai gaji da zaman jiranki ba dan awaninsa biyu da qarasowa bari nasa akawo maku abun sha, idan kin gama wancan office din dake kallonki zaki shiga kafin nan ma zaki same aciki "yana gama fad'ar haka ya fita da d'an sauri ya barsu zaune maryama ta zuba ma yaya sadam ido har sanda aka kawo masu abun sha ta d'auka ta tsiyaya masa a glass cup ta mika masa ."
ahankali yasa hannu ya amsa cup din hannunta ya kur'bi kad'an yana mai lumshe idanunshi sannan ya ajiye cup din hannunsa yana dubanta a tsanake "ya naga duk kinyi wani iri ?"naji yace idan na gama na shiga ni kuma nafi son mu shiga tare da kai banason na barka kai kad'ai zaman jirana "
Gajiyayyun idanunshi ya ware sosai akanta kafin ahankali ya hadiye wani abu daya tsaya masa a makoshi sannan yace "karki manta aikinki kika zo ,kuma kema Kinsan ke kad'ai zasu bukaci gani banda ni ?" duk da haka idan a son raina ne mu shiga tare "ta fad'a tana mai tsareshi da narkakkun idanunta ." suna zaune wnn saurayin da yayi masu iso ya shigo yana cewa "madam ki shiga ke kad'ai mai gida yake jira "ok but dan allah ko zamu iya shiga mu biyu ?cike da jin haushin maganarta yace "tare zakuyi aikin ne ?no ni kad'ai ce !to ke kad'ai ake buqatar gani aciki dan mai gida baya son hayaniya "ya qarasa maganar tare da ta'be baki sannan ya fice ya shige wani office ."
hankalin maryama ya tashi matuka dan har ga allah haka nan taji bata son shiga ita kad'ai qarara damuw ta bayyana acikin kwayar idanunta da shi kad'ai yaya sadam yake iya gani har ya fahimci halin da take ciki ,ahankali yaya sadam ya tsiyaya mata drik ya miko mata ta girgiza masa kai alamun bazata sha ba ,"why ?! ya tmbyeta yana sake tsareta da idanunshi dafe goshinta tayi tana cewa "bana jin shan komai a yanzu ,tun daya ga haka yasan ko me zai yi 'bata lokacinsa kawai zai yi dan bazata kar'ba ba, dan haka ya mike tsaye suka fito tare tana gabansa yana take mata baya har suka fito dogon hanyar da zata kai su office din ATA wanda alokacin yana tsaye acikin tangamemen office dinsa ya hard'e hannuwansa duka a faffad'an qirjinsa idanunsa kyam akan maryama da yaya sadam ta cikin glass door ,har ta fara taku domin qarasowa zuwa inda office dinsa yake yaga ta tsaya ta koma baya kad'an tana magana da wani da bai san ko waye ba ,sai dai idanuwanta yana kansa ,kwakwa luwarta na hasko mata fuskarsa daga nesa kamar tasan fuskar yayinda shi din ma kallonta yake cikin shigarta ta mutunci kamar ranar farko daya fara d'aura kwayar idanunshi akanta ."doguwar riga ce sanye ajikinta har qasa mai dogon hannu da qaramin hijab dinta mai zip a gaba,sai nikaf kalar hijab din da take sanye dashi wanda iya kwayar idanunta kad'ai ake iya gani ,tsaki yaja da karfi fuskar nan tashi babu wani annurin kirki dan babu abinda ya tsana arayuwarsa kamar 'bata lokaci ,yana wasa da komai arayuwarsa amman baya ta'ba wasa da lokacinsa ,ita kuma abinda ya fahimta kenan daga gareta tana da matukar wasa da lokacinta da kuma damarta ".
"ya kuma kika tsaya madam bayan an fad'a miki ke kad'ai mai gida yake jira ?"ta jiyo sautin muryar segun daga bayansu ta juyo a natse idanunta kyam akan yaya sadam sannan tace "yanzu zan shiga na d'an tsaya muna magana da mijina ne "miji kuma alokacin aiki ? yayi mata tambayar da mamaki akan fuskarsa dan shi a tunaninsa bata da aure tunda ta amsa gayyatarsu a weekend mutumin daya gansu tare kuwa ya d'auka d'an rakiya ne ko kuma saurayinta ."a natse ta gyad'a masa kai tana cewa "Eh mijina ne kuma yayana ne ". ATA wanda yake tsaye yana ciza lip's dinsa da karfi cikin zafin rai bai san wainar da'ake toyawa ba amman haka nan yake jin matsanancin bugun zuciya da kuma 'bacin rai mara misaltuwa "any way kiyi sauri ki shiga kiyi abinda ya kawoki dan mai gida baya wasa da lokacinsa ,akan lokacinsa zai iya aikata komai kafin ta bashi amsa yaya sadam yayi murmushi ya matso kusa daita sosai tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihu wondonsa fuskarsa a sake "karka damu yanzu zata shiga kuma zata maku abinda kuke so "ya fad'a masa haka sannan ya maida hankalinsa kan maryama kamar zai mata numfashi"k'anwata kuma amaryata karki wani damu da jiran da zan miki ni kad'ai abinda nake so dake ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina "nan take idanuwanta suka cicciko da ruwan hawaye "yaya sadam na gode sosai ,na gode da yarda daka min ya allah ka yarda dani kamar yadda mijina ya yarda dani "ameen ya hayyu ya qayyum "ya fad'a tare da ciro handkey fari daga gaban aljihun rigarsa ya goge mata hawaye then ya kai bakinsa yayi kissing foring head dinta yana mai karfafa mata gwiwa murmushin gamsarwa ta sakar masa sannan tayi gaba tana d'aga masa hannu ."
bayanta yabi da kallo cike da tausayawa take taka kasa kamar bata son takawa yana tsaye har sai daya ga ta tura kofar office din ahankali ta shiga kusan second biyar ya d'auka tsaye yana kallonta ya kasa d'auke idanunshi akanta ,ATA wanda yake rike da waya a daidai bakinsa da hananu d'aya yayinda d'ayan hannunsa ke rike da wata farar takarda yana magana yana kai kawo acikin office din hakazalika segun na tsaye a gefe guda cike da girmamawa bai kalli inda take ba .”
ahankali yaya sadam ya juya ya fara taku zuwa kasa jikinsa a matukar sanyaye ya bud'e mazauninsa na direba ya shiga ya zauna yana sauke wani irin naunayen ajiyar zuciya sannan ya d'auki wayarsa ya rike yana dubawa missed call's din nadiya ya gani rututu ya sauke numfashi sannan ya kirata tana d'auka ta fashe masa da kuka "menene kuma abun kuka ?"na fad’a miki zan cika miki alkwarin da nayi miki bazan ta’ba cin amanarki ba nan da wasu watanni masu zuwa zamu kasance tare amatsayin ma’aurata ,oh my god dan an d'aura aurena shi yake nufi me ?kinga nadiya banason abinda kike min wallahi kukanki yana mugun 'bata min rai ."
"a natse ATA ya juyo mata fuskarsa sosai tare da tsayawa ya tokare hannunsa dake rike da farar takardar a makeken table din gabansa yana cigaba da wayarsa ."idanun maryama suka sauka kan kyakkyawar fuskar ATA wanda zuwa lokacin ya runtse idanunsa gam zuciyarshi da bakinsa ne kawai ke aiki ,ta tsura masa idanuwanta sosai tana cigaba da kallonsa " tabbas ba gezo idanuwanta suke mata ba shine shararren d'an kasuwan nan data d'auki tsawon lokaci wajen zanashi wanda a qarshe ta kai zanensa ma'aikatansa babu wata gamsashiyar magana mai dadi daga ma'aikatansa ."tayi shiru tana dubansa a tsanake tana shakar kamshn turarensa mai sanyi da ratsa zuciya "tun daga ranar data kai masu zanensa suke nemanta a waya "to mai yasa suke bibiyarta ?"mai yasa suka jawota zuwa nan ?"
ta yiwa kwakwaluwarta tambyr da bata da mai bata amsa wani irin mummunar fad'uwar gaba take ji babu abinda kwakwaluwarta bata hasko mata akansu ba amman tai qoqarin sharewa ta cigaba da tsayuwar jiransa ."bakinta na furta hasbiyallahu la ila a illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim sakamakon wani sabon tsoro da ya shigeta ."
maryama na tsaye har kusan mintuna shabiyar ATA bai gama wayar da yake ba haka zalika bai bud'e kwayar idanunshi ya bata umarnin zama ba haka ma segun na tsaye bai zauna ba adaidai lokacin da qarfe d'aya na rana ta buga wanda a daidai lokacin wasu masallatan sun tada sallarsu dan haka ranta ya soma 'baci ta soma tunanin an janyota ne kawai dan a sake wulakantata a karo na biyu ji tayi kamar ta juya ta wuce shi da segun ta kama gabanta ,ta kalli inda segun yake tsaye shima ya kalleta haka nan ya tsinci kansa da shafa mata qirjinsa alamun tayi hakuri "segun !yes sir ya fad’a cike da girmamawa ya mika masa farar takardar dake rike a hannunsa batare daya bud'e idanunshi ba "ina bukatar copy's dinsu "okay sir ya amsa ya fita da sauri ."ko bayan fitar segun ata bai bud'e idanunshi ba bare yayi mata magana sai kuma taga bai kamata ace tana jiran sai shi ne zai fara mata magana ba dole dai sai itace zata fara masa magana kafin ya saurareta ,dan haka ta qara taku d'aya ta tsaya daidai saitin kunnensa cikin muryar dake nuna alamun gajiya "ta gaishesa bai amsa ba sai ma ya matsa baya ransa a 'bace yayinda zuciyarsa na tafasa dan ya tsani yazo jira duk abinda zaayi masa dole shi zaa jira karo na farko kenan daya zauna jira jiran ma akan itace zata qaru dashi .”
wulakanci da yayi mata yayi mata ciwo, dan ta tsani disgi da wulakanci kamar taja masa tsaki ta fice daga office din sai kuma tayi wani tunani su manyan nan haka halinsu yake kafin kayi nasara akansu dole sai ka kwantar da kai dan haka ta sanyawa zuciyarta hakuri tayi kasa da muryarta da kanta tana wasa da yatsun hannunta "ranka shi dade lokaci na tafiya yana da kyau abani aikin daya kawoni nayi ga kuma lokacin sallah yayi ina buqatar nayi sallah "sake jin sautin zazzakar muryarta ya sanyashi bude idanunshi ahankali tamkar mai tsoron ganin wani abun agabansa ,ya zuba mata tsumammun idanunshi masu mugun rikitarwa yana kallon cikin qwayar idanunta dake d'auke da zara zaran gashi ido itama shi take kallo tana jira daga garesa ".
shiru yayi yana cigaba da kallon cikin kwayar idanunta gabansa na wani irin luguden bugu da karfin gaske,kallon da yake wa kwayar idanunta kallon né na sani "jiki a sanyaye ya nuna mata wata kofa dake manne da office din "ki shiga kiyi alwala "yana gama fad'ar haka ya juya mata baya .”
shiru tayi kafin ahankali cikin sanyin jiki ta juya ta shige toilet ta d'auro alwala ta fito ta tada sallah a natse yana zaune yana kallonta yana waya ,ganin har ta idar da sallah bai tashi ba bare shima yayi tunanin ya tashi yayi sallar yasa tayi zaton ko ya manta daita acikin office din ne hakan yasa ahankali ta matso kusa dashi ta motsa labbanta"sir abani aikin da zanyi bani da ishashen lokaci da gefen idanunsa ya kalleta a d'age sannan muryarsa ta biyo baya a dake "kece kika zana ni? muryarta a sanyaye tace "eh nice sir !kinsan ko ni waye ?"shiru tayi har kusan mintuna goma tana nazarin maganarsa sannan cike da girmamawa tace "eh sir !
"Waye ni ?ya sake tmbyrta a dake tamkar bashi yayi maganar ba "kai ne shararren dan kasuwan nan da kasar nan dama duniya gabad'aya take ji dashi "tana gama fad'ar ya juyo a matuqar fusace ya fuskaanceta yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "shine dan iskanci kamfanina ya buqaci yin aiki dake amman kikayi rejecting?ya qarasa maganar a matukar tsawace yana zare mata idanunshi .”
nan da nan hankalinta yayi matseefar tashi tayi saurin matsawa baya jikinta na kyarma "aikin banza kawai yanzu haka ke din ba diyar kowa bace amman kin d'auki girman kan tsiya kin d'aura wa kanki nonsense" yana gama fad'ar haka ya mike ya barta tsaye sake da baki "nice nonsense? ta tambayi kanta cike da mamaki jin abinda ya fad'a mata “nonsense!ta sake maimaitawa a fili tana mai jin d’acin kalmar domin tunda take ba’a ta’ba dangantata da kalmar ba .tana kallonsa ya nufi wani d'aki tana mai jin wani irin tuttukin bakinciki tare da damuwa mai tarin yawa har ya tura kofar zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana jan tsaki "give me ten minutes "
yana gama fad'ar haka ya qarasa shigewa .”
runtse idanunta tayi "wannan kuma wani irin sabon salon wulakanci da 'bata lokaci né ? ya kuwa san me ake kira da zane ?"abu ne da yake bukatar isashen lokaci "ita bama kanta take ji ba kamar yaya sadam mutumin daya sadaukar da farincikinsa ya biyota cike da zafin zuciya ta juya zata fita daga office din sai ga mr segun , ya tsaidaita yana cewa "ina zuwa kuma ?zan wuce ne dan bana tunanin aikin nan zai yuwu "calm down madam ki samu natsuwa kiyi abinda ya kawoki baqaramin sa'a kika taka ba da mai gida ya bukaci yin aiki dake "yana 'bata min lokaci gashi tare da mijina muke "nasani yanzu me yace ko tunda na fita bai yi magana dake ba ?"Yayi a qarshe wai na bashi ten minutes ."tayi mgnr kamar zatayi kuka "ok kiyi hakuri ki bashi lokacin dayace kin 'bata sama da awa acikin office din nan sai mintuna goma né kawai zai gagara watakilla ma bazaki yi aikin a yau ba ,zai baki ne kije gida kiyi idan kin gama sai ki kawo cike da jan hankali ya dinga karfafa mata zuciyarta dan haka ta cigaba da tsayuwar jiran ATA ."
kusan mintuna goma sha ya d'auka sai gashi ya fito tare da furta "kika ce kice kika zana ni? Kamar tace masa a'a dan taga abun nasa akwai rainin hankali ciki .amman sai ta tsinci kanta da jin tsoro dan haka ta maida kwayar idanunta ta lumshe masa tana wasa da agogon tsarka hannunta wanda ya qara wa zanen lallenta kyau ,lallen yabi da wani shu'umin kallo tun da yake bai ta'ba ganin zanen lallen da yayi masa kyau har ya d'auki hankalinsa ba sai nata yaji kamar ya kamo yatsun hannunta ,ya d'ago idanunshi a natse ya kalli fuskarta nan da nan idanunsu ya tsarke cikin juna wannan karon sauri cire kwayar idanunta cikin nashi tayi tana mai kawar da fuskarta gefe tare da danne bugun zuciyarta "shi kuwa wani yanayi ya tsinci kanshi ciki mai sarkakkiya da wuyar misaltuwa sakamakon idanunsu da suka sake tsarkewa cikin juna abinda ya lura atattare daita itama tana da jin kai da miskilanci"a natse ya sake bin zanen lallenta da kallo wani irin kallo ta watsa masa gabanta na fad'uwa wanda ta rasa dalilin jin haka ."
Ahankali ya samu waje akan kujerun kushin dake office din ya zauna batare daya bata umarnin zama ba "bata zauna ba sai ma idanunta data tsura masa tana kallonsa tana sauke numfashi dan itama taci alwashin bazata yi mgn ba har sai yagaji dan kansa yayi . abinda batasani ba shi ko ajikin ATA da zasu kwana a haka ma bazai damu ba abinda yasani ne ba zai barta taje koina ba har sai tayi masa abinda yake buqata daga gareta ."ya lumshe tsumammun idanunshi yana jijiga kafarsa d'aya yana jira daga gareta ."a qalla sun kusan minti talatin yana zaune ita da segun suna tsaye ta kalli agogon dake d'aure a hannunta a karo na kusan biyar a kasan ranta taja qaramin tsaki bata san me ya janyota zuwa wannan aiki ba nan take kwakwaluwarta ta shiga aikin neman mata mafuta ."kafin ahankali ta samo zance zuci"maryama dole ki ajiye komai ki qarasa gabansa Kiyi masa magana idan aikin nan zai yuwu ayi idan bazai yuwu ba ya sallameki ki kama gabanki tun kafin hakurin mijinki ya qare"da sanyi jiki take qarasowa zuwa inda yake ahankali ahankali har ta iso ta zauna a kujerar dake facing dinsa "wani irin zane zanyi "? tayi tmbyr cike da sanyi murya "ahankali ya motsa lip's dinsa "ina kayan aikinki ?da hanzari ta bud'e jakar kayan aikinta ta fito da kayan aikinta tare da janyo kujerar gabanta zata ajiye ta jiyo sautin muryarsa "ba'a nan zakiyi ba” ya fad'a tare da mikewa tsaye "biyoni ! "
fitowa sukai daga office din yana gaba tana biye dashi haka ma segun yayinda gbdy hankalinta ya rabu gida biyu wani yana gurin mijinta wani yana gurin ATA ."wani office ya shiga daita kai tsaye gaban wani farin baod yaja ya tsaya tare da jingina jikinsa da bango segun yayi saurin janyo kujeru guda biyu daya a gaban baod din dazaayi zane d'aya kuma a inda ATA zai zauna "sir ka zauna ! ya zauna tare da daura kafarsa d'aya akan d'aya jiki a sanyaye maryama ta zauna tana jiransa sai daya gama shan kamshinsa sannna ya sallami segu ya fara mata bayani tana jin ya fara magana ta d'aura hannunta akan boad ta fara fidda kyakkyawar shep din jikin zanen da yake buqata , yana mata bayani tana zanawa lokacin data zana karan hancinta taji wani mummunar tsoro ya shigeta cak ta tsaya ta kasa cigaba da zanen da take ta tsurawa baod din gabanta ido kwaayr idanunta ta zana da hancinta har ma da yanayin jikinta babu abinda yazo zuciyarta kamar zanenta data gani a office din m . malik “ nan da nan gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta.shi kuwa gyara zamansa yayi sosai yana kallon zanen lallen hannunta da yadda take tafiyar da aikinta bai san ya'akayi ba yaji saukar hannunsa akan hannunta yana shafawa ."
Cikin gigita gangan jikinta ya kama rawa wanda yasa ATA ya dawo haiyacinsa sai dai ya kasa d'auke hannunsa ajikinta da kwayar idanunshi wani irin tsoro da matsanancin firgici ATA yaga ya bayyana afuskar maryama ,yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, cikin sanyin jiki ta sabule hannunta cikin bacin rai tace "meye haka ?"dan allah aiki nazo yi banason irin
wannan wasan iskanci mai barazana ga rayuwata wannan ya zamo karo na farko da qarshe karka sake kuskuren sake kai hannunka jikinta "ta fad’a tana jan tsaki" ajiyar zuciya ya sauke tare da kafa mata tsumammun idanunsa cikin sayin murya yace "look at me “ta kallesa Kmr yadda ya buqata babu wasa acikin kwayar idanunshi "Kinga nayi miki kama da dan iska ?sosai kuwa dan gashi naga alama daga zuwa aiki sai ka bige da kai hannunka jikina batare da kayi laakari da ni din matar aure bace ko kuwa budurwa bace ".hakan nan yaji ya tsinci kanshi da adduar allah yasa single ce ba matar aure ba ya sake kai hannunsa tsintsiyar hannunta tayi saurin zare hannunta har agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ya zame cikin nashi “wai meye haka dan allah nifa matar aure ce kuma tare da mijina nazo aikin nan “ta fad'a hankalinta a matukar tashe shiru yayi yana qare mata kallo qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi wanda baya jin haka akan kowace mace sai akan mafarkinsa.”
ahankali ya motsa labbansa "ko zan iya ganin fuskarki ?"ya tmbyeta yana qara gyara zamansa
"no !ta bashi amsa a matukar tsorace ya sauke numfashi tare da mikewa tsaye ta sake ja baya tana cewa "karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba ganin tana nema ta fice daga hayyacinta ya sanyashi kamota hadi da zaunar da ita "lokacin daya kamota wani irin socking ne ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa nan take bugawar da zuciyarsa take ta qaru fiyye da kaida sai dai ya kasa magana a fili sai a zuci "ki natsu wallahi babu abinda zan miki ni kaina bansan meke damuna ba yau , tun da kika kasance tare dani naji komai nawa ya sauya .”
Yayi shiru tare da tsura mata ido ita kuwa banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, neman hanyar guduwa take daga garesa ."yayinda wasu irin hawayene masu azabar zafi suka taru a kurmin idanunta "wallahi ka cuceni tun da nake babu wani nmj daya ta'ba kai hannunsa jikina tun ina matsayin budurwa sai yau dana kasance mallakin wani tana gama fad’ar haka ta fashe da wani irin kuka "okay ki zauna ki qarasa min aikina na sallameki and ki yafe min bisa kuskurena kafin ya gama mgnrsa har ta soma tattara kayan aikinta ta zuba cikin jaka ta fice da sauri ."da sauri ya fito ya biyota yana kiranta "ke!!!
"ita kuwa da sauri sauri gudu gudu ta shiga lift ta danna grand segun ne ya fito da sauri sakamakon jin sautin muryar mai gidansa , cikin gigita segun yace sir meke faruwa ne ?"karka bari yarinyar nan ta wuce ka tsayar min daita !ka tsayarda ita segun amman ina cikin kankani lokaci maryama ta sauka kasa tana goge hawayen fuskarta cike da tashin hankali ta nufi inda motar yaya sadam yake a pake jikinta na wani irin kyarma ta bud'e ta shiga ta zauna kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana tattare da damuwa nan da nan ya rud'e ya shiga jera mata tambayoyi "ka taimakeni yaya sadam ka bar garin nan dani akwai matsala "wacce irin matsala ?zan maka bayanin komai idan mun isa gida daga haka bai sake cewa komai ba yaja motarsa a guje suka fara qoqarin ficewa koda segun ya fito har motarsu ta fice daga ma'aikatan ."
Wani irin gudu yaya sadam ke falfalawa akan titi yana cikin gudu ya hango wasu motoci gudu uku abayansu suna biye dashi idan ya rage gudu suma sai su rage gudu haka idan ya qara gudun motar zasu qara "maryama kamar ana binmu ki fad’a min meke faruwa ? ta kasa magana kawai ta fashe masa da kuka dan bazata iya fad'a masa abinda mai kamfanin creation yayi mata ba ,ya zama abun kunya gareta ace ta fad'a masa wani kato ya ta'ba mata jiki ya zai dauketa ina yarda da yayi mata ?"kuka ta cigaba da yi shi kuma yana falfala gudu akan titi shi kansa kana kallonsa kasan a matukar tsorace yake sun yi tafiya mai dan nesa sannan suka nemi motocin uku dake biye dasu suka rasa sai daf daa zasu fita daga ogun state kawai sai ga motocin guda uku sun sha gabansu."cak yaya sadam yaja burki ya tsaya cikin tsananin fargaba wasu tika tikan murd'ad'd'un mutane suka shiga firfitowa daga cikin motar d'aya bayan d'aya har suka fito gaba d'ayansu sanye da kaki wanda ke nuna alamun sojojin nigeria ne wani irin matsanancin tsoro da firgici ne ya kama marayam tayi saurin riko hannun yaya sadam gam cikin nata jikinta na kyarma shima ya riketa gam bai yi tunanin ko yan fashi da makami bane sakamakon kakin dake sanye ajikinsu zuciyarsa tafi bashi wani abu dabam ,mutun uku daga cikin sojojin suka qaraso da sauri suka bugi kofar motar da karfi batare da 'bata lokaci ba kofar ta bude basu tsaya wata wata ba suka fito da yaya sadam tare da buga masa bakin bindiga nan take ya zube kasa .”
maryama ta saki qara mai sauti ta fito ta durkushe gabansa cike da matsanancin tsoro yaya sadam ya janyota zuwa jikinsa ai kuwa ta kamkamesa dan gabad'aya a tsorace take hawaye né ya soma bin kuncin maryama cikin sheshekar kuka maryama ta soma magana "bayin Allah laifin me mukayi maku ?dan Allah karku cutar da ni da mijina ,dan allah ku barmu mu wuce tunda nasan bamuyi maku laifin komai ba "ke ce bakiyi mana laifin komai ba amman shi wannan bakin munafikin yasan abinda yayi mana "inji cewar daya daga cikinsu da sauri maryama ta tsurawa yaya sadam idanunta tana kallonsa "wai kai dan rainin wayo ko ?mu zaka rainawa hankali ?".a d'an rud'e yaya sadam yace "Nifa duk ban fahimceku ba hasalima ban san laifin da nayi maku ba ,su waye ku ?meye hadina daku ?laifin me nayi maku ?ya jera masu tambayoyin yana sake riko maryama jikinsa "kai karka nemi ka rainawa kanka hankali dan ubanka kayi tunani laifin daka aikata acikin satin nan wanda kai kanka kasan dole zaa iya bibiyarka?".
yaya sadam yayi shiru yana nazarin maganr shi dai asaninsa bai aikatawa kowa laifin komai ba baya ga auren maryama da yayi "har kusan minti biyar yaya sadam bai ce uffan ba yasa suka cigaba da magana "me taurin kan tsiya kawai amman tunda baka tuna ba idan kaje lahira zaa maka bayani dalla dalla akan taurin kan da kayi ,kai jojo ku daukosa mu aikasa lahira yadda yayi taurin kai dan son more duniya bazai zauna a duniyar ba "nan da nan suka rufe masa ido da bak'in kyalle ,suka d'aure masa hannayensa duka abayansa kafafunsa ma a d'aure ,suka rufe masa baki suka ciccibosa suka watsa shi acikin mota "itama yarinyar kuyi mata kamar yadda kuka masa ku sata acikin mota ku had'a daita batare da 'bata lokaci ba aka rufe fuskarta aka tasa keyarta cikin mota tunda tashiga motar take rutsa kuka mai ta'ba zuciya tare da kiran sunan Allah yayinda yaya sadam yasa hannuwansa duka ya dafe goshinsa yana zurfafa tunaninsa alokacin da motocin suka karya kwana cikin wani kungurmin daji mai cike da duhu da ban tsoro suna sharara gudu."
tunanin duniya yaya sadam yayi amamn iya tunaninsa bai ga wanda zai iya masa haka ba idan safiya ce yasan baa akansa zata huce ba sai dai akan maryama tunda tasha fad'a masa muddin taganta sai ta aikata lahira ."nadiya kuwa yasan kwata kwata bazata masa haka ba shi kuwa wa yayiwa laifi ?"idan ma laifi ne to sai dai akan auren maryama da yayi ne to waye wanda zai masa hk ?bai samu amsar tambayarsa ba yaji motocin sun ja wani irin burki sun tsaya a daidai karshen dajin tare da bubbud'e kofofin motocinsu a zuciye, na karshen ne ya fito rike da kwalar rigar yaya sadam wanda babu halin yin kwakwaran motsi ballantana yasamu damar yin ihun ceton ransa da'ake barazanar raba shi dashi, ahankali suka shiga jansa a k'asa suna tafiya dashi cike da tsansar rashin imani , wanda kallo daya zaka masa kasan a rikice yake d'aya daga cikinsu ya rike hannun maryama ."
Basu tsaya akoina ba sai a bakin wani katon rami suna huci "ku binnesa da ransa jin haka yasa maryama ta rikice ta gigice tashiga wage wage tana kiran sunan yaya sadam "dan girman allah karku kashesa karku binnesa da ransa gara ku kasheni wallahi banason na rasashi yana da matukar mahimanci arayuwata na bada rayuwata fansa, gara ku dauki raina ku barshi dan Allah karku kashesa duk wani abu da zaku masa kuyi min ni daman nafi bukatar mutuwa da rayuwata dan bana jin dadin rayuwar nan na rasa komai karku bari na rasa mijina tausayinta ya kamasu "d'aya daga cikinsu ya jawosu gefe yace "me kuka ga zaa yi ?"ya tambayesu "kar mu batawa kanmu lokaci wajen tausayi mu cika aikin daaka ba mu "shikenan a wuce gurin .”
aiko suka dauki yaya sadam suka jefa cikin rami suna shirin jefa maryama mutun daya acikinsu wanda shine yafi jin tausayin maryama yace mu barta tunda daman shi kadai aka bamu aiki "okay! suka amsa. a matukar gigice take batasan ya’akayi ba ta zare kyalen da suka rufe mata ido dashi tana gama bude idanunta yaya sadam dinta ta gani acikin rami suna zuba masa kasa zuciyarta ce ta tsaya cak ta daina aiki a lokaci har suka rufesa da ransa ."
Bayan sun gama suka hau jijigata a gigice ta dawo haiyacinta idanunta na zubar da hawaye wani razananniyar qara ta saki da karfi tana kiran "ina mijina yake ?idan har kun kashesa ku had'a dani ku kashe dan allah karku barni a raye dan bazan iya rayuwa babu shi ba haka ma mahaifiyarsa ." numfashi suka sauke atare "aikin gama ya gama yarinya tuni mijinki mai taurin kai yana cikin nan suka nuna mata inda suka binnesa, an gama da labarinsa sai dai uwarsa ta haifi wani idan an sake haifosa a duniya bazai sake kinjin magana ba "ai tana gama jin maganarsu numfashinta ya soma barazanar d’aukewa "me yasa ?me yasa zaku masa irin wannan hukuncin inna lillahi wa inna ilaihi rajiun me yasa zaku kashesa tayi taku biyu zata isa inda suka binne mata miji kafafuwanta suka gagara daukarta ga wani irin nauyi da kanta yayi idanunta suka fara rufewa jiri take gani nan take ta zube kasa sumammiya ."
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 26
Ran ATA a matukar 'bace yake zaune acikin jirginsa yana tunanin maryama ,wani irin ciwo yake ji a zuciyarsa dan bazai iya misalta yanayin bugun zuciyarsa ba ,ga wani sara da kanshi ke masa har baya iya bud'e idanunshi sosai yayinda kowani second 'bacin ransa na sake nunkuwa wanda baya raba d'ayan biyu damuwar maryama ce bai san dalilinsa na kai hannunsa jikinta ba ."mai yasa yaji sauyi ajikinsa adalilin sake d'aura kwayar idanunshi akanta ?"mai yasa yaji yana buqatar ganin fuskarta a zahiri ?
yana jin wani irin sauyi akanta lallai yana buqatar ganin halittarta a zahiri zuciyarsa ta amsa masa kuwan haka ." da wannan tunanin ya isa gida alokacin da magariba ta kawo kai .jirginsa mai saukar ungulu na gama tsayawa a haraban gidansu rai a 'bace yake tattaka matattakala yana qoqarin saukowa , kai tsaye ya shiga bangaren mami sosai yake jin damuwa acikin zuciyarsa qoqarin danne damuwarsa yayi dan kar hankalin mami ya tashi sai dai kallo d'aya tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ."
"muryarsa a kasalance ya gaishe da mami ."kamar ko yaushe ta amsa masa tana mai tsura masa kwayar idanunta kamar wacce taga wani sabon halitta ,cike da kulawa tace "sannu da zuwa adamcy ya hanya ka dawo lafiya ?da sauri ya amsa mata da "lafiya !"yana qoqarin hayewa samansa hannunsa d'aya soke acikin aljihun wandonsa .bayansa tabi da kallo "shigowarsa cikin wannan yanayin yasa duk mami ta d'an rikice kasa samun kwanciyar hankali tayi ,cike da tashin hankali ta mike tsaye tabi bayansa .
ahankali ta tura kofar parlour'nsa ta shiga duhu falon dan haka ta kunna wuta nan da nan haske ya haskaka koina a parlour'n sai dai bata gansa ba dan haka ta nufi hanyar bedroom dinsa ta shiga nan ta iskeshi tsaye ya jingina jikinsa da bango d'akin yayi sama da kanshi hawaye ne kwance acikin idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa meke masa dadi arayuwarsa bai san ta ina zai fara ba ,komai ya rigada ya tsaya masa gabad'aya baya jin dadin rayuwarsa ,ya kasa fahimtar kansa ko kuma yace yau tazo masa da abubuwa da yawa wanda duk tarin damuwa ne akan wanda yake ciki ya dinga jin kamar ya kashe kansa ya huta da rayuwar da yake ."
lumshe tsumammun idanunshi yayi sai ga hawaye sharrr na bin kuncinsa "adamcy nah ! ".mami ta kira sunansa cikin tsananin tashin hankali har jikinta na rawa . amatukar firgice ya tsaida kwayar idanunshi dake cike da ruwan hawaye akanta qirjinsa na wani irin dokawa da sauri dan bai ji motsin shigowarta ba sai sautin muryarta wani irin zazzafan numfashi ya sauke yana sake maida kanshi sama tare da ciro hanky ya shiga d'auke hawayensa"lafiyarka kake zubar da hawaye adamcy ?ta tambayesa cikin tsananin tashin hankali dan duk abinda zai sashi zubar da hawaye baqaramin abu bane da muninsa ya wuce misali. shiru yayi ya kasa magana dan bai san me zai fad'a mata ba "kayi min magana mana adamcy dan kasa har zuciyata ta fara tsinkewa."
da yatsan hannunsa ya nuna mata daidai saitin zuciyarsa dake bugawa fiyye da kaida ."sake matsoshi tayi sosai tana cewa "meke damunka "?"zuciyata sweet.." yana kai wa nan yayi shiru ya kasa cigaba da maganar idanunshi na sake cikowa da ruwan hawaye"me ya samu zuciyarka ?" ta sake tambayarsa hankalinta na qara tashi "I don't know what's wrong with me sweetheart amman dai nasan zuciyata kullum ciwo take min"."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta "abinda mami ta shiga furtawa kenan tana sake maimaitawa " i know something is wrong with my heart wallahi sweetheart akwai ciwo mai zafi acikin zuciyata wanda zai iya kasheni nan kusa .."
nan da nan fuskar mami ta qara sauyawa hankalinta a matukar tashe tace "ka dinga sausautawa kanka adamcy da yawon tunani ,ka dinga addua akan duk abinda ya dameka addua tana canzawa bawa qaddararsa kuma tana saka natsuwa acikin zuciyar bawa "numfashi ya sauke da karfi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ,magana yake son yi amman zafin da zuciyarsa keyi ya hana shi cewa uffan "kasamu natsuwa adamcy ka dinga furta wannan adduar zaka samu natsuwa da sausauci a wajen Allah zai yaye maka dukkanin damuwarka "allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta ahankali ya sauke idanuwanshi ya tsura ma mami kawai yana kallonta cikin yanayi na tsanani damuwa "ka sani idan wani abu ya sameka nice farkon wacce zata fara shiga damuwa ga kuma d'an cikin jikin maryam wanda bamu san abinda zata haifa ba karka bari muyi maraicinka. adamcy kasan yadda nake sonka idan na rasaka zan shiga damuwa a kullum adduata na mutu na barka a duniya ba ka mutu ka barni ba tunda ta fara magana bai ce mata uffan ba sai ma ciro wayarsa da yayi ya soma neman layin likitansa muryarsa ce ta katse mami daga maganar da take masa ahankali yake magana tamkar mara lafiya "doctor kazo ka dubani please ".daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran d'akin yayi tsit tamkar babu mutane acikinsa ."
Ahankali ya soma d'aga kafafunsa zuwa Kan gado ya fad'a ya kwanta flat ransa duk babu dadi yayinda idanunshi na kallon saman d'akin babu abinda yake gani sai kwayar idanun maryama da yatsun hannun ta da sautin zazzakar muryarta mami tazo ta zauna kusa dashi tana daura hannunta saman kansa tana masa sannu "bayan mintuna shabiyar sai ga doctor ya shigo tare da sallama tashi yayi ya zauna ya jingina bayansa da abun gado yana sauke numfashi da kyar tare da yiwa doctor bayanin yadda yake ji batare da 'bata lokaci ba doctor ya fara masa gwaje gwaje bayan doctor ya gama yayi masa allura sannan yace "ranka ya dade jininka ne ya hau kad'an yana da kyau ka dinga saukakawa kanka wasu abubuwa dan zuciyarka na bukatar hud'u yanzu dai nayi maka allurar bacci in sha allahu kana tashi zakaji daidai Allah ya baka lafiya ya ajiye masa magunguna yace zai wuce ."mami tayi masa godiya adaidai lokacin da doctor ke had'a kayansa yayi mata sallama ya wuce ."
"Ka tashi kayi sallah magriba kafin bacci ya d'aukeka sannan me za'a kawo maka coffe ko tea "any one sweetheart." ya furta tare da mikewa da kyar ya shiga bathroom ita kuma mami ta fita kawo masa coffe dan tasan shi yafi bukata wanka ya fara sannan yayi alwala ya fito ya cire kayan jikinsa ya canza zuwa jallabiya brown colour mai ratsin baki ya isa inda abun sallarsa yake ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma Kan gado ya kwanta lamo tare da janyo bargo ya rufe jikinsa koda mami ta dawo d'akin ATA na bacci ta zauna gefensa tare da zuba masa idanunta tana jin wani irin qaunar d'anta na ratsata bata iya dogon fushi dashi hakazalika bata son ta rasa shi. hawaye ne ya fara bin kuncinta ji take a duniya data rasashi gara ta rasa komai dan idan ta rasashi ta ina zata cigaba da rayuwa?" ina bazata iya ba bazata iya jurar rasashi ba gara ita ta bar duniyar tun kafin taga mutuwarsa ahankali ta mike tana goge hawayen idanunta ta qarasa ta rage masa karfin ac sannan ta canza masa wutar d'akin zuwa mara haske ta duka daidai fuskarsa tayi masa addua sannan ta fita daga d'akin ."
Washgari tun da yayi sallah ya koma bacci har karfe goma bai tashi ba yana kwnace yana sharar bacci shigowar mami yafi sau uku dubashi yana bacci sai dai ta kalli fuskarsa ta fita sai wajen shadaya da wasu mintuna ya tashi hanyar bathroom ya nufa ya fad'a yayi wanka ya fito yana goge sansar jikinsa ya sanya kananan kaya masu matukar kyau he look very attractive kullum ka kallesa qara kyau yake ya d'auki kwalbar turare yana feshe jikinsa yana fesa turare kwakwaluwarsa na tunanin maryama da sauri ya ajiye kwalban turaren hannunsa ya qarasa inda ya ajiye kayansa na jiya daya cire ya dauki dogon wondonsa ya shiga laluba wondon cikin kankanin lokaci ya ciro agogon sarkarta .yayi shiru yana kallon agogon yana ganin tsinysiyar hannunta aciki "mai yasa zuciyata ta damu akanki ? zuciyarsa tace "kasani ko ubangiji ne ya turo maka ita cikin rayuwarka da wata manufa a boye kayi duk yadda zakayi tayi aiki akarkashinka sosai ya dinga jin damuwa akan abinda yayi mata abu ne da bai tabayi ba .wai ya kai hanunsa jikin wata mace da sunan ta burgeshi ya dauki kusan mintuna goma yana kallon agogon tsarkar sannan ya bud'e durowarsa ya jefa ciki ya fito yana taku . "
cike da isa yake taka step, tun daga kan step yake jiyo sautin muryar baba qarami yana tafiya da kyar har ya sauko kasa ya tarar da mami zaune a inda ta saba zaman a parlour'n gabanta kuma baba qarami ne zaune yana magana cikin tsananin fushi tunda yayi masa kallo d'aya ya dauke kanshi bai sake kallon inda suke ba ya wuce dining ya dibi abinci da kanshi ya a zauna akan kujerar dake kallon step bayansa kawai zasu iya hangowa haka zalika duk abinda suke fad'a yana jinsu bayan ya gama cin abinci ya d'aga kanshi yana kallon agogon dake manne a parlour'n dake walwalin haske karfe 12:00 na safe ne yanzu mikewa yayi ya qarasa gurin mami yace "sweetheart ni zan fita mami tace "kai da baka da lafiya ina kuma zaka ka dinga hutawa dan Allah ?" numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "ka zauna akwai maganar da babanka yazo dashi shiru yayi yaki zama "banason musu kayi abinda nace "a natse ya samu waje ta zauna still bai kalli inda baba qarami yake ba bare ya gaishesa "magana ce yazo daita akan hindu me kasani akai ?zuciyar ata a dake ya fad'a mata komai game da abinda ta aikata ."
baba qarami ya kalli ata yana jin haushi irin haushin da mutun zai iya kashe mutun "na dauka ko wani ka ga yayiwa hindu haka sai inda karfinka ya qare kuma zaka taimaki rayuwarta amman wulakanci ka bar min 'ya a tsare har tsawon watani sannan aka wuce daita gidan yari bancin na tashi tsaye da haka rayuwarta zata qare . tsakanina da kai adamu allah Ya isa ban yafe maka ba duniya da lahira "kayi hakuri baba qarami duk abun bai kai haka ba zai sa a sakota in sha allahu "wani irin kallo ata yayiwa mami ta juyo ta kallesa a tsanake tace "me yasa kayi haka adamcy ?dokarki nabi kikace a dauki mataki akan duk wanda yayi yunkurin kashe miki maryam ko ba haka ba ?mami tayi shiru tana dubansa sam bashi da tsoro akan komai "naji amman kasa a sakota bana jin ma itace zata aikata haka "kiyi hakuri sweetheart babu ta yadda zaayi na saka baki saboda abinda ta aikata mummunar laifi ne kuma ta amsa da bakinta ta aikata "a gidan ubanka ta amsa haka ?"
"mugun kawai mai mugun hali ni nasan hindu bazata aikata hakan ba sai dai idan azabtar daita akayi yasa ta amsa laifin da ba nata ba gefen bakinsa ya ciza da karfi "nifa duk abinda zaa fad'a akaina ba damuwata bace idan kuna da hujjar da zata wanke kanta tayi ,ku kuma ku sake shigar da qara kotu amman ni Adam bazan saka baki a fito da tantiriya yar tasha irinta ba." tayi laifi kuma ta amsa laifinta dole hukuma ta hukuntata ni na gama magana sweetheart ko zan iya tashi ?"daga baba qarami har mami suka zuba masa ido suna kallonsa ranshi fess ya mike yayiwa mami sallama ya wuce yana fita ya iske masu tsaronsa a inda suka saba tsayawa suna ganinsa suka qaraso da sauri cike da girmamawa suna gaishesa atakaice ya dinga amsa masu batare da bata lokaci ba aka bude masa bayan mota ya shiga suka bar gidan a can parlour'n mami kuwa hakuri kawai take bawa baba qarami tana tabbatar masa lallai hindu zata fito ya bar komai a hannunta da kyar ta samu ya wuce sai dai kallo daya zaka masa kasan ransa a bace yake kuma zai iya aikata komai akan adam ."
*****
Bangaren maryama kuwa har karfe goma na dare babu su babu labarinsu, aunty da umma da habib da sauran yanuwan ummah wadan da suka zo biki da dangin mahaifinsu da basu wuce gida ba duk suka damu sukai ta neman layinsu amman shiru ga dai wayoyinsu yana ringin amman ba d'agawa nan fa hankalinsu ya tashi matuka zuciyarsu ta fará tsinkewa gabad'aya suka taru acikin parlour'n umma cikin jimami da tashin hankali ."Allah sarki umma duk yadda take jin mummunar faduwar gaba da tsinkewar zuciya amman sai ta dake ta kasa nunawa kowa damuwarta da yanayin da take ji sai ma ta dinga kwantar masu da hankali tana cewa "babu komai wata killa yanayin aikin ne ko kuma ababen hawa né sukai yawa a hanya "haka suka kwana zaune cikin tashin hankali da zullumi ."
washegari kuwa tun da asuba fari habib da a bokinsa faisal suka d'auki hanyar ogun state kasamcewar duk inda maryama zata aiki tana tura masa address gabad'aya habib baya cikin natsuwarsa ji yake kamar zuciyarsa zata buga hakan ne ma yasa sam baya ganin gudun da motar tasu take akan titi har ma yaji kamar su fita su canza wata motar kamar bazasu kai ba sai gashi sun karaso jikinsa na tsuma kamar wanda ake zubawa ruwan zafi suka dauki hanyar ma'aikatan isarsu ke da wuya aka sheida masu sunzo amamn tun a yammacin jiya suka wuce
cikin tsananin tashin hankali habib ya shiga kiran number aunty kira d'aya ta dauka tana kiran sunansa nan dai habib ya sheida mata komai
tunda aunty ta kira sunan habib idanun ummah ke kanta tana jiran ta gama wayar taji mai zata fad'a ganin yadda ta fashe da kuka tana salati yasa ummah ta dawo kusa daita jikinta na wani irin rawa "balkisu meke faruwa mutuwa sukai ko me ?
"Cikin muryar kuka aunty tace "ummah wai tun da yammacin jiya suka baro kamfanin salati ta saka tana addua tare da karfafa zuciyarta data aunty "karki damu balkisu babu abinda zai samesu koma menene in sha allahu Allah zai kawo masu mafuta ta fad'a tana share hawaye "gsky ummah ina ji ajikina akwai wani abu dake faruwa dasu." numfashi ummah ta sauke cikin karfafa ma aunty zuciya "haba bilkisu ki daina wannan tunani kisa aranki babu abinda zai samesu "Allah yasa amman tun jiya da yammaci suka baro kamfani amman har zuwa wannan lokacin babu su babu alamunsu "ke dai kiyi masu addua kawai ta fad'a cike da tausayawa kanta dan ita kanta tana ji ajikinta akwai wani abu dake faruwa dasu sai dai tana fatan ya zama alkhairi arayuwarsu gabad'aya."ta mike ta shiga dakinta ta zauna cikin tsananin tashin hankali hawaye ne ya dinga zuba daga idanunta ahankali idanunta ya sauka akan frem din hoton sadam dake ajiye akan qaramar durowarta yana sanye da kananan kaya ya daura rigar sanyi akan kayan idanunshi manne da bakin glass ,tayi shiru kawai tana kallonsa kallonsa take saboda shi kadai ne ya rage mata a duniya bata da uwa bata da uba bata da miji yanzu idan wani abu ya samesa dole zata shiga damuwa ta qarasa zancen zuci tana fashewa da kuka mai ban tausayi "in sha allahu bazan rasaku ba sadam da maryama ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke Allah ya dawo mun daku cikin koshin lafiya ."
suna nan zaune cikin tsananin jimami da tashin hankali har yamma sai ga habib da abokinsa ajigace suka karaso gida sakamakon yanayin damuwar da suke ciki cikin tashin hankali aka kira baba gali da sauran yan'uwan dangin mahaifinsu cikin kankani lokacin suka hallara dan daman suna bangaren aunty hassana .bayan sun gama jin komai suka fara zuba ruwan maseefa hajiya fatima tace "ai duk abinda ya faru laifin umman sadam ne dan itace ta basu gudunmuwa tafiya , inda take shiga batan take fita ba nan da nan sauran yan'uwa suka kama ita dai ummah shiru tayi kawai tana karanto duk adduar datazo bakinta ita yanzu batasu take ba yadda ya'yanta zasu dawo gareta take ."yadda suka wuni jiya cikin tashin hankali haka suka wuni yau din ma dan har karfe 12:00 na dare ba labarinsu ummah tace kowa yaje ya kwanta aga zuwa gobe ."washgari baba gali da habib da sauran yanuwa maza suka bazama nemansu har ogun state din aka sake komawa sai dai babu wani labari duk hankulansu a tashe yake aunty kuka kawai take ummah kam tayi dauriya habib ma kuka yake yana kiran sunan maryama da yaya sadam abun gwanin ban tausayi ."
bangaren aunty salma kam abun yayi mata dadi fiyye da tunanin mai karatu ,dan adduar mutuwa ma ta dinga masu ,allah yasa mummunar hatsari suka samu a hanya "burinta daman maryama ta bar duniya ko kuma tayi rayuwar kaskanci ko zama babu aure. sai gashi burinta ya cika batare da ta 'bata kudinta ba ,tana zaune baba gali ya shigo ya tsaya akanta "salma ina fatan dai babu hannunki cikin rasa sadam da maryama ?wani irin kallo ta watsa masa "idan da hannuna me zai faru ?Aa to gsky ni dai babu ruwana kuma muddin da hannunki Kiyi maza kisa a dawo dasu "gsky a wasu lokutan sai naga kamar kana bin bayana amman kuma wani lokacin sai naga kana nuna min wariyar launi ,kai yanzu meye damuwarka dan an nemesu an rasa kai daya kamata kaji dadi kayi farinciki an nemesu an rasa maryama bazata yi rayuwar jin dadi a gidan ba zata bar ya'yanmu suyi rayuwarsu cikin jin dadi ko da yake shi kanshi yusif din yanzu mun rasa gane kanshi ko shekaranjiya da suka zo daurin aure da abbansa bai leko inda muke ba da alamun aikin daakayi masa ya fara barin jikinsa sai an sabanta wani sabo ".
"ni yanzu ba wannan bane damuwata ki fad'a min gsky da hannunki a rashin dawowar su gida ko babu hannunki ciki ?"ta sosa idanunta da hannunwanta duka tace "babu hanuna !"to amman ai shekarajiya naji kina waya da malaminki kina cewa ayi duk yadda zaayi a salwantar da .."kaga dakata daka ji ina magana cewa nayi a salwantar dasu duka ko maryama ?to ai ni ko maryama ma bana son ta rasa rayuwarta bare kuma sadam "tsaki taja tana turo masa baki "ai daidai ne ma idan sadam ya mutu idan bakasani ba bari na fahimtar da kai, idan sadam ya mutu kai ne zakaji dadin rayuwarka dan duk wani abu daya mallaka zai zama naka halak malak kai da sauran yanuwanka hassalima naka ne zai fi na kowa yawa tunda bashi da magaji ,mahaifiyarsa ce kawai ita kadai ranta kuma bazata gajesa ba "kinji zaki sake lalata komai ni dai bana son ran kowa ya salwanta a hannuna ".yana gama fad'ar hk ya fice tabi shi da kallon kaskanci tana ta'be baki "ina ganin shima wannan sokon sai nasa an gama min dashi gabad'aya na huta tai murmushi "wallahi ina farinciki da rashin dawowarsu allah yasa ko gawar su kar agani ."
Maryama kam cikin wani jahili gida su jojo suka nufa daita a sume can wajen gari a tsakanin lagos to ile ife , gida ne na sirri wanda ba kowa yasan dashi ba gida ne da mai gidan ya gidana domin taronsa na sirri ko kuma duk sanda zai holewarsa ko kuma wani meeting sannan yana ajiye mahimman abubuwansa agidan ,gida ne mai hawa daya kuma agyare yake babu abinda babu acikinsa najin dadin rayuwa gida ne wanda babu wanda zai san an shigar da mutun sai su da kansu idan sunyi raayin asani ." a babban parlour'n sukai masauki tare da wanda ya basu aiki shima kuma ba gidansa bane gidan abokinsa ne ya amshi key a hannunsa kai tsaye ya nufi bedroom suka biyosa da maryama kan wani makeken bed din dake dakin ya nuna masu suka shimfideta "aikin
ku yayi kyau sosai fa .gabad'aya suka kwashe da dariya shikenan an kashe boss kowa ya huta sosai kuwa suka amsa masa atare tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi yana lashe lip's dinsa "kusan wani abu ?gabadaya suka girgiza masa kai "da alamun yarinyar nan ta shiga comer?nima abinda na fahimta kenan "idan dare yayi ku dawo ku dauketa ku bar nan daita domin bata da wani sauran amfani agareni , ku dauketa ku kaita duk hospital din da kuka ci karo dashi amatsayinku na sojoji bazaayi wani bincike akanku ba, kuce kun tsinceta ne a hanya cikin wannan yanayin ."an gama!" zuwa gobe zakuji alert dina "okay babu matsala ."
Da misalin karfe goma ba daren ranar mutun biyu acikinsu suka fitar da maryama wacce bata san halin da'ake ciki ba suka nufi wani hospital daita yadda akace suyi haka sukai suka ajiyeta da wayarta da jakarta suka qara haba taimakon gaugauwa aka fara bata sai dai har zuwa washegari bata farfado ba har sanda aka kira number number wayarta suka dauka tare da sheidawa wanda ya kira halin da'ake ciki ."
Kallo daya zaka yiwa su ummah ka tabbatar da cewa baa cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali suke ba, tunda suka duro hospital bayan wayar da sukai da ma'aikatan hospital din ,daman kuma tun ranar farko da tafiyarsu sadam din basu sake samun isashen bacci da nutsuwa ba har sai da suka daura kwayar idanunsu akan maryama "me ya sameta haka da har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti "ina sadam da suka ganta ita kadai kwance rai hannun allah? kamar kar su zo ta fara sambatu tana kuka tana kiran sunan yaya sadam tana fad'ar irin abinda akayi masa aunty Kuka ta fashe dashi cikin tsananin tashin hankali tana bubbu qasa tana fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "dan allah karku kashesa dan Allah ku fito min dashi daga cikin rami ,su waye suka sakaku wannan aikin ku fad'amin wanda ya sakaku zan mika masu rayuwata dan bana son na rasa yaya sadam .wannan mummunar kissar dani yafi dacewa bada bawan Allah kamar shi ba dan Allah ku fito min dashi "tana ihun fad'ar haka sai taji anfasa wani razanannen kuka akanta mai kukan tana fad'ar "lahaula wala kuwwata " me ya samu sadam shikenan kin kaishi an kashe mana shi"inji cewar aunty hassana ummah kam kalmar innalillahi wanna ilaihi raji'un kawai take furtawa "wannan yarinya me yayi miki da zaki sakamasa da wanna muguwar sakayya."?
farkawa maryama tayi ta ganta akan gadon hospital cikin yan'uwanta dana ummah ,ummah ta riko hannunta cikin nata tana mata sannu aunty kam kuka kawai take tana furta adduaoi, cikin haka doctor ya shigo ya sallamesu gabdaya domin duba jikin maryama sai bayan daya fita suka dawo dakin suka cigaba da zage zage har sai da ummah ta dinga taka masu burki , duk wanda zai yi magana sai ummah ta hana tare da cewa yaje waje maryama na bukatar hutu a qarshe dai daya bayan daya suka fice sai daga baya suka dawo har dare babu wanda ya sake cewa komai sai da irin kallon da suke binta dashi babu sausauci ."maryama dake kwance cikin tsananin tashin hankali ta zuba ma ummah dake zaune a gefenta ido tana dubanta ,itama umma ita din take kallo duk ta fita haiyacinta yadda idanunta suka kunbura sukai wani irin girma sun bata tsoro matuka yayinda gabad'aya fuskarta tayi jajur saboda kuka ahankali ummah ke mata nasiha tana tofa mata addua wani irin yanayi maryama ta shiga alokacin da idanunta da kwakwaluwarta suke sake hasko mata komai daya faru ."
a natse ta dinga bin kowa dake gurin da ido sai dai taga wani irin mugun kallo suke mata zuwa can taji aunty hasana na cewa "ji yadda take bin mutane da kallo wannan yarinyar fa muguwar munafuka ce dan allah tashi ki fad'awa mutane inda kika kai mana d'anmu daga rakiya ai wallahi baki isa ba sai kin fito mana dashi dan shi kadai muke kallo a matsayin mahaifinsa ."mikewa maryama tayi jikinta a sanyaye har ga allah tafisu bukatar yaya sadam arayuwarta sannan yadda suke nuna mata baya mata dadi duk da tasan basa qaunarta amman batayi tunanin zasu zargeta ba kanta ta daura akan cinyar ummah tasa kuka tare da jin wani kullin abu ya tsaya mata yaki gaba yaki baya "ummah ce ta dinga rarrashinta tana yiwa aunty Hasana fad'a "wallahi ummah bansan mutane nan ba bazan iya cutar da mijina kuma danuwana ba wallahi ina son yaya sadam ."
"nasani maryama bazaki ta'ba iya aikata hk ba cikin jin dadin kalaman ummah maryama tasa kuka tana cewa "ku taimakeni ku nemo min yaya sadam domin ban san inda zan saka rayuwata ba tana kuka ummah na share mata hawaye duk da itama hawayen take sosai hankalin mutane ya tashi kowa kuka yake a wajen ".
"ummah Kiyi hakuri ki yafe min nayi nadamar fita wannan aiki ban san me ya jani na aikata haka ba kuma wallahi na daina farinciki da iya wannan aiki da nayi arayuwata ummah kuzo muje inda aka binne yaya sadam da ransa zaa iya samunsa a raye ina ji ajikina bai mutu ba hawaye umma ta share amman maryama kwanaki biyar kenan da faruwar wannan alamarin kina ganin zai rayu "?numfashi ta furza mai zafi "ummah !"sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka tana tuna kalamansa na qarshe gareta "abinda nake so dake maryama ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina wani sabon kuka ta fashe dashi "ummah ta riko hannunta gam cikin nata itama kuka ta fashe mata dashi sosai cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan allah tana cewa "laifin me d'ana yayi masu wannan hukuncin yayi tsauri ga rayuwar sadam babu wanda zuciyarsa batai rauni ba aunty da wasu daga cikin yanuwa hawaye suke dan tausayawa ga umma d'aya bayan suka dinga barin dakin inda dakin ya saura daga aunty sai ummah da maryama "umma muje inda aka binne yaya sadam a fito dashi jikina na bani yana nan a raye ummah ki tausaya min wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba "ki samu natsuwa maryama in sha allahu zamu je gobe"iya abinda ummah ta iya fad'a kenan bata sake cewa komai ba dan bazata iya magana mai tsawo ba ."
washegari aka kai maganar gurin hukuma aka shigar da qara tare da nuna hoton yaya sadam daga nan aka yiwa maryama tambayoyin daya dace sannan aka saka maryama gaba sai hanyar ogun state tafiya suke tana share hawaye tana addua duk kwanar data gani sai ta rikice tace nan ne . sai an tsaya tace a’a ba nan bane ahaka suka kusan kaiwa cikin ogun state dan daga inda suke suna iya hango sambaod din wel come to ogun state tayi sauri tace “ kamar kafin mu kawo wannna sambaod din ne .”cak direba dake tukasu ya tsaya tare da juya Kan motar suka koma dayan hannun sun sha wahala sosai a qarshe dai ta gane daidai inda sojojin suka sha gabansu saka makon warin takalminta data gani yashe a gefen titi .” jikinta na rawa ta soma kuka tana cewa "ku tsaya nan ne !"batare da bata lokaci ba suka firfito “tabbas anan ne suka sha gabanku “ta fad’a tana kuka .daya daga cikin jami’in tsoro yace a ina aka binnesa nan maryama ta hau zazzare ido “tabbas daga nan suka rufe mana ido amman duk da haka jikina na bani wannan kwayar suka shiga damu basu mutsa mata ba suka shiga mota suka bi hanyar tafiya suke amman jikin maryama rawa yake dan bata son tayi kuskure wajen gano wajen .”
gabad’aya babu inda baa duba ba ko zaa ga alamar tudun kasa amman babu ,jami'an tsoro suka tsaya suna kallonta "kin tabbatar nan ne?tayi shiru tana share hawaye dan gbdy ta rikice ummah Ummah duk ta rude sai zufa take fitarwa ta matso kusa daita tace “maryama ki natsu da kyau a samu a gano inda suka binnesa” tayi mgnr cikin rawar murya maryama ta fashe da kuka tare da zubewa kasa sakamakon ta rasa mafuta.”dan kwakwaluwarta ta cunkushe waje d’aya yadda maryama take kuka haka umma take kuka tana janyota jikinta gabdaya jikknta ya d’auki zafi kamar garwashin wuta yayind jami’an tsaro suka cigaba da dudduba wajen ko zasu ci karo da tudun kasa amman still dai babu wata alama inda aka binnesa ganin suna bata alokacin su ne yasa suka ce su wuce zaa zaa sanar a gidan radio da tv maryama kam duk ta gama rikice masu sai sunan yaya sadam dina kawai take kira “ku nemo min shi dan Allah karku barni haka da kyar aka samu aka saka acikin mota suka kama hanyar gida .”
******
Shabiyu ne na rana yana tsaye acikin office dinsa sanye da t shirt long sleeve light puppy da wondo baki sai tie baki zagaye da wuyansa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa wani irin kamshi jikinsa ke fitarwa mai sanya natsuwa da kwantar da hankali fuskar nan tashi a murtuke zariya ya soma yi acikin office din yana tunanin maryama wanda bai san dalili ba tunaninta yaki barinsa babu abinda zuciyarsa yake kwadayin sake gani kamarta kafin ahankali yayi burki a daidai mazauninsa turo kofar office din akayi batare da an nemi izinin shigowa ba ya kalli kofar ammar ya gani yanayin yadda yaga fuskarsa ya dan fahimci akwai wani abu yana gama shigowa ya soma magana cikin tsananin fushi "burinka ya cika maryama tayi aure “
“so what idan tayi aure what’s my business with her ?wai menene matsalarka adam ?"da nayi me kenan ?wallahi ban san baka da sa'a arayuwarka ba sai da maryama tayi aure "tô ni menene damuwa ta da aurenta ?kaga dan Allah karka sake min maganar ta karka qara min damuwa akan wanda nake ciki "kai ne kuwa kake da damuwa daita ."hade rai ata yayi sosai yana yiwa amar wani irin mugun kallo mai bugar da zuciya "kasani inada dalilina na son ku hadu daita tun kafin tayi aure.ata yayi taku daya biyu yana mai juya masa baya wallahi da ka daure kaga maryama da zaka fahimci abinda na gani har yasa nake son ku hadu daita."
juyowa ata yayi ya fuskancesa yana hura masa hanci tare da kai hannu yana sunce tie din wuyansa "kai ma tunda kaga na na nace ai ya kamata kayi amfani da sense dinka ,bazaka ta'ba jin dadin wata mace a duniya ba sama daita" look ammar bana son damuwa ,"my friend you have to use your common sense and think akwai dalili mai karfi dayasa naso ku hadu "ata ya sauke hanunsa daga wuyansa ya maida cikin ajihunsa yana nazarin maganar ammar "ba dai ka rasa maryama ba kasani zuciyarka zatayi nadama fiyye da kowani nadama da d'an adam keyi a rayuwarsa "ya d'ago ya tsurawa ammar idanunshi tare da cire hannunsa d'aya cikin aljihunsa ya rike kugunsa," wasu ma suna janyota jikinsu domin su amfana daita bare kai da ..."wai meye haka ammar ?ka dameni ka cika min kunne da surutun banza da wofi dole ne sai na aureta ko dole sai na janyota jikinta ?"kaga enough please ka rabani da maganar wata maryama din banza bana son jin ko sunanta bare na aureta "yayi maganar a tsawace yana furzar da iska mai zafi "ai kuwa ka shiryawa shiga tashin hankali da damuwa domin duk ranar da zaka ganta kuma amatsayin matar aure sai kayi nadamar rashin haduwarku akan lokaci ,kuma lallai bazan daina fad'a maka rashin haduwa daita damuwa ne akan damuwa kuma har qarshen rayuwarka bazaka daina da kasani ba kai in takaice maka zaka iya rasa ranka ". ata ya dafe goshinsa da hannunsa daya "ammar kana rikita min kwakwaluwa zuciyata tana tsinkewa magangunka gabad'aya suna nema tarwatsa min zuciya gabad'aya na kasa fahimtar abinda kake nufi yayi maganar kamar zai yi kuka tare da zama akan kujera yana kallonsu "you are mad adam yanzu abinda ya rage maka ka zauna kayi tunani akan maganganuna " yana gama fad'ar haka ya buga masa table din gabansa ya juya ya fita a fusace ."
ata ya kai hannu goshinsa kafin daga baya ya soma jujjuya jikinsa akan kujera wani irin ihu yayi yana kai hannusa ya ture tarin file din dake Kan table sannan ya mike tsaye zambur Kmr zaki ya dafe kanshi gabad'aya ya rasa meke masa dadi dan wani irin abu yaji yana yawo acikin ilahirin jikinsa mai kama da abinda yake ji akan mafarkinsa yau shine karo na biyu da yaji wani abu wanda ya shafi mafarkinsa akan wata mace "wacece mai zanen creation wacece maryama datai aure coz the same abu yake ji akansu wanda yake da kusanci da abinda yake ji akan mafarkinsa “karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba itama matar aure ce “ya rabbi what’s wrong with me ?yana cikin wannan halin james yayi knocking yana neman izinin shiga sai da ata ya dauki lokaci sannan yace "coming !" ya shiga cikin taka tsantsa "mai gida ina son nayi magana da kai ko zan iya magana ?" leave!" mai gida magana ce mai mahimanci "I said leave bana bukatar jin komai yanzu."da sauri ya juya ya fice .cikin company ranar kam kowa ya kama kanshi dan dukkanin alamun sun nuna an tabosa, duk kuma wanda yayi kuskuren shiga track dinsa zai sha bala'i idan ma bai ce ya kori mutun ba har ya dawo gida maganar ammar na damunsa cikin rai sai yayi kamar ya kirasa ya sake masa karin bayani sai muguwar zuciyarsa ta gargadesa "
Bayan sati d’aya wanda yayi daidai da kwanaki shabiyu da daura auren maryama da yaya sadam sultana ta dirá a kasar kuma kai tsaye abdullahi estate aka nufo daita murna wajen aunty abida abun baa magana ,tun daga lokacin da sultana ta shigo estate din aunty abida ta fara aiwatar da shirinta kullum suna bangaren mami sai dai basa samun ganin ata suna samun sa’banin shiyasa yau sukai sakamakon yau .ahankali yake ssukowa daga Kan step cikin shigarsa na kullum sai kamshi yake idanunsa bai sauka akan kowa ba sai akan aunty abida da sultana kallo daya yayi masu ya dauke idanunshi ya cigaba da taku har ya wucesu ta mike ta sha gabansa tana kiran sunansa “adamcy barka da saukowa.” ya tsaya kawai yana kallonta batare da yace mata komai ba “ga sister ta kawo mana ziyara Ya ganta ta hadu ko ?still dai bai tanka mata ba tayi murmushin yake tana cewa “daman nace bari na kawota ku gaisa sultana ga cup din tea dinsa can dauko ki bashi .” jikinta na rawa ta juya ta dauko Orenge cup din dake ajiye wanda daman dan shi aka tanada ta mika masa ,sai dai bai kar’ba ba yace "am okay coz am oready late” zai wuce ta sake tsaidashi Ya tsaya cak yana duba agogon dake daure da tsintsi yar hannunsa kamr yadda kasani sultana kanwarmu ce kuma ta kware a harkar zane dan naji ance kana bukatar kwararun masu zane shiyasa nace tazo dan tasan Kan aikinta sosai idan bazaka damu ba ko zaka bata dama kaga irin nata kwarewar ?shiru yayi bai ce uffan ba “.
“nasan bazaka ta'ba zuba ma yaruwarka kasa a ido ba zaka gwada yaruwarka kaga irin nata baiwar bayan shi ma ina son ka taimaka ka bata aiki a maakatarku Z&A idan ma da hali ka barta a kusa kusa da kai wato P.A dinka dan na yi imani zaka ji dadin aiki daita dan ....”duk naji bayaninki.” ya katseta ta hanyar fad’ar haka kafin ya cigaba tayi saurin cewa “ zata joining compaing kenan ? kai amman na gode sosai sultana bana fada miki ba bashi da matsala gashi da sauki kai ga kirki da son yanuwa gyaran murya yayi yace " ammm karki yi Godiya tukun dan bani zan bata aikin ba kiyiwa mijinki magana I know he can do more that for her “mijina kuma ?tai masa tmbyr tana kallonsa tare da nazarin maganarsa tana kallonsa ya zagayesu ya kama gabansa “nifa Aunty duk ba wannan bane matsalata ni dai kawai kisan yadda zakiyi na kasance a kusa dashi nasan komai zai zo da sauki “amman yanzu a gabanki kikaji ina masa magana zaki ce bakiji abinda yace ba, wai nayiwa Ibrahim mgn Ibrahim din da ba wuri daya suke ba .”
Dan allah ayi min afuwa posting zai koma a sati sau daya sakamakon bana samu lokaci ga hidima da mai gidana ga business ga typing sannan ina bukatar hutu Kunga abun yayi min yawa ina maku fatan alkhairi sai Saturday ko sunday in sha allahu.”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 27
Jiki a sanyaye ATA ya fito cikin 'bacin rai daga d'ayan bedroom dinsa wanda ya rasa dalilin 'bacin ransa , a yanzu kusan kullum ransa a 'bace yake azaba yake ji sosai a cikin zuciyarsa so yake ya rabu da damuwar dake damunsa amman ya rasa yadda zai yi ,cike da natsuwa yake taku acikin d'akin yadda jikinsa ke fitar da kamshi mai sanyaya zuciya haka d'akinsa ke d'auke da kamshin dad'ad'an turarukan sa .a natse ya d'auki farin glass dinsa ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya d'auki agogon fata mai tsada ya d'aura a tsintsiyar hannunsa, ya bud'e bedside domin ya d'auki wallet dinsa." ya kai hannu ya d'auka ya tura a bayan aljihun wondonsa yana qoqarin rufe bedside din ne idanuwanshi suka sauka akan agogon sarka hannun maryama daya zamo cikin hannunsa a wancan ranar ,yayi shiru yana kallon agogon yana jin wani iri a gaba d'aya ilahirin jikinsa, ya kusan minti goma tsaye yana cigaba da kallon agogon gabansa na wani irin bugawa da sauri sauri tunowa da yayi matar aure ce yarinyar yasashi jan dogon tsaki yana ciza lip's dinsa."
a natse ya maida agogon ya ajiye ya qarasa inda wayoyinsa suke business phone dinsa ya fara kunnawa nan take kira James ya shigo lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya d'aga kiran ba, kiran na qoqarin tsinkewa ne ya d'aga "hello sir! good morning sir ya fad'a a tare ?"morning !ya fad'a atakaice yana hura hanci "akwai wasu mutane da suka zo da buqatar ganin sabon creation shine nake neman izini a wajenka ko zamu nemi d'aya daga cikin kwararrun da suka kawo zanensu ko zaa dace ?"lumshe idanunsa yayi yana jin wani irin d'acin maganarsa dan a yanzu bai buqatar ganin zanen kowa sai na wannan yarinyar amman kuma sai ya tsinci kanshi da cewa "okay ! yayi maganar a can kasan makoshi kamar mara lafiya sannan katse kiran ya fito daga d'akin zuwa kasa ya nufi hanyar da zata kai shi bangaren mami bai wani jima ba ya fito kai tsaye AGC aka nufa dashi "
Bayan kamar awa uku da zuwansa office james ya shigo tare da some cike da girmamawa James yace "sir bayan munyi waya da kai d’azu da safe sai kuma muka canza shawarar mu sake neman wannan yarinyar data zanaka dan gsky gabad'aya zanenta yafi kyau amman anyi rashin sa'a layinta baya zuwa " take ya fahimci kowace yarinya yake magana akai, bai ce masa komai ba ya cigaba da mgn "kayi hakuri sir nasan zakaji babu dadi aranka amman ni ina ji ajikina zata zo mana da sabon design masu ... "enough james you can leave ."sorry sir ! tamkar wanda akayi wa duka ko wanka da ruwan sanyi ya simi simi nufi hanyar fita ."some ta sauke numfashi tana mai gyara tsayuwarta tare da fara magana "sir masu supply din kaya daga kafaninmu wasunsu sunki kar'bar kayanmu in group wanda ban san dalilin faruwar hakan ba "one second! ya furta yana cigaba da operating system din gabansa shiru tayi cike da girmamawa ,yayinda office din ya d'auki shiru baka jin motsin komai sai na qarar ac da system din gabansa sai kuma saukar numfashinsu "kuma kun tabbatar babu wata matsala a kayayyakin mu ?"no sir babu wata matsala ectually ma wasu sun kar'ba wasu ne dai basu kar'ba ba" amman ai gashi ina ganin sakoninsu cewar basa bukatar design din da akayi masu ne yanzu ke wannan ba wata matsalar bace a ganinki ? eh nayi magana da oga Ibrahim sir amman har yanzu bai ce komai ba ina tunanin yana son sai kuyi magana dashi ne "shikenan zan san yadda zaa gyara komai ya mike ya zagayo daga wurin zamansa yana kokarin fita yayi taku d'aya biyu ya tsaya batare daya juyo ba "kisa a binciko min inda yarinyar nan take da zama sannan kice james ya kira chef adisa ina son ganinsa gobe goben nan bai tsaya jin abinda some zata fad'a ba ya soma qoqarin ficewa "okay sir ."
A dogon koridoor suka hadu da sultan bai kallesa ba bare ya tsaya duk da yasan wurinsa yazo ya ra'ba ta gefensa ya wuce ,har yayi taku biyu ya jiyo sautin muryarsa " Adam...! ya kira sunansa a gadarance har yanzu kai muke jira da mahaifinmu domin muna da bukatar wani kaso daga cikin kafanuni araba abamu namu kowa yaci gashin kansa, cak ATA ya tsaya daga tafiyar da yake ya zura hannunsa daya cikin ajihun wandonsa "idan naki fa ?yayi mgnr batare daya juyo ba " dole kabi umarnin mahaifinmu dan bazamu cigaba da aiki akarkashinka ba alhalin dukiyar nan gabadaya tamu ce dan dole kayi wani abu akai .”a fusace ATA ya juyo gabadaya ya fuskancesa "kasani wannan dukiyar gabadayanta ta mahaifina ce kamar yadda na fad'awa mahaifinka yau da rokona kukayi zan iya daukar wani bangare na bawa mahaifinku amman tunda zalinci ne abun bazan bada ba kamar yadda na fad'a kuma zan iya dakatar da duk wani mai numfashi dake d’akinku wanda yake karkashin ma'aikatar nan idan kace karya ne ka cigaba da shiga track dina "shiru ne ya biyo baya"kafin ahankali ata ya wucesa yana jan tsaki tare da furta "nonsense."
*****
Zaune ata yake akan kujera sanye da suit baki yana jujjuya jikinsa bayan ya watsawa chief adisa tambayoyi cikin 'bacin rai ,cheif adisa yayi shiru yana nazarin abinda zai fad'a masa "answer me !ya furta cikin tsananin bacin rai mara misaltuwa "komai zance yanzu bashi da wani amfani sir tunda na rigada nayiwa sectary dinka bayani komai "Eh nasani but ina son naji daga bakinka ,yayi maganr yana gyara zama tare da daddana system din gabansa batare daya dago kanshi ba , dalilin dayasa muka daina amsar produc din design dinku sunyi matukar tsaida ne,dan alal hakikanin gsky kudin daaka sa sunyi yawa yayinda muke samun exactly irin design din a wasu wurare akan farashi mai sauki atakaice dai wannan shine dalili."
shiru ata yayi byn ya gama sauraronsa ya cigaba da tura sakonni kafin daga baya ya dago kanshi a hankali ya kafe cheif adisa dake zaune a gabansa da ido yana qare masa kallo ta cikin farin glass dinsa sai daya furzar da iska mai zafi sannan ya bude bakinsa da kyar yace "kasan abinda abu original yake nufi ? cheif adisa yayi shiru ,"wadan da kuke siya a sauran compaing's copy din namu ne, namu kuma asalin masu kyau ne ". ba maganr quality ake yi ba sir maganar contitie akeyi kafa san dan kasuwa duk wani dan kasuwa yana bukatar farashi mai sauki wanda shine business, da dai zaa cigaba da bamu farashin daaka saba ne sir da komai zai tafi normal ".ATA ya sauke numfashi yana jan tsaki " ko ku siya a haka ko kuma ku barshi domin bazan rage naira daya daga farashin dana saka ba yana gama fadar haka yace "get out .cheif adisa ya mike tsaye tare da cewa "okay sir ya dauki system dinsa ya qara gaba tsaki yayi ta ja babu kaukautawa ,ya mike tsaye ya shiga zariya acikin office dinsa yana shafa sumar kanshi.”
ATA na tsaye a parlour'n mami ya zuba hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa dawowarsa kenan daga office ko cikakken minti biyar bai yi da shigowa ba sai ga fahad ya shigo a matukar fusace kamar an jehoshi yana cewa "wai kai dame kake takama ne ?yayi mgnr yana nunasa da d’an yatsantsa .""what do you mean ?ATA ya tmbyesa a tsawace yana watsa masa harara a lokacin da hjy zulai ke qoqarin saukowa daga saman ata "bani zaka tmby ba kamata yayi ka tmbyi dakikiyar kwakwaluwarka , taya ma zaka yanke wannan banza hukunci haka?"lafiya fahad ! ? " mami ta tambayesa cikin rawar jiki “wannan yaron ne mana yake son jawowa mutane asara ,yana yin abu tamkar shi kadai yafi kowa waye wa da ilimi
yau ko kamfanin ba group bane ai bai cancanta yayi haka ba bare yasan wannan kafanin ba nasa bane shi kadai .ya qarasa mgnr yana kallon ATA a fusace .
Suna cikin haka sai ga yaya Ibrahim shima cikin tashin hankali ya rufesa da fad'a nan mami ta koma kansa "ki duba ki gani mami yadda farashin komai na kaya ya sauko daga sauran kamfanoni amman shi tashi daya ya qara farashi nikin baninkin gashi costumers sunki karba kaya daga hannun kowa "very good ."ata ya furta yana hura hanci “What ?
" I said very good ,"ya sake maimaitawa a natse tmkr maganar ba daga bakinsa ta fito ba “very good ma zaka fad'a saboda baka da hankali da tunani "yes of course it good and to be your last warning da zaka kirani da mara hankali ."yaya Ibrahim bai damu da abinda ya fad’a ba yace “me yasa zakayi haka adamcy ?” me yasa zaka bata kasuwancinmu maganar gsky muddin haka zaa cigaba da tafiyar da kamfanin gara kowa ya watse a rufe kamfani kowa ya kama gabansa "okay wannan shine daman shirina ai a rufe kowa ya kama gabansa "Ibrahim da fahad suka kallesa a rude suna mai mamakin jin abinda ya fad'a " yes haka nake so "okay saboda kasan kana da wasu compaines masu zaman kanka shiyasa kake son a rufe wannan ?"yayi kyau yayi kyau gara daka fad'a mana muka sani ."ai daman mugunta ne acikin cikin wannan mugun mai girman kan , kai ne dai ka kasa ganewa kake daukarsa amatsayin mutumin kirki ai ga irinta nan zai janyo kowa ya rasa saboda tsabar bakinciki irin nasa da dai a rufe gara a siyar a bawa kowa hakinsa "inji cewar fahad .
Dan allah fahad ka samu natsuwa kai ma Ibrahim ka natsu kar wannan abu ya zama damuwa " karki damu mami ba wani abu bane ai bazamu biye masa ba zanyi komai domin naga business din ya tsaya da kafafunsa "ko kuma a siyar ba nifa gara a siyar dashi inji cewar fahad "wannan kuma karya ka fad'a dan matsawar ina raye babu wanda ya isa ya siyar da AGC "mu zuba mu da kai dan halak ka fasa yadda kake ji da taurin kai muma muna ji dashi a qarshe zan maka gargadi ka rage wannan zakewar da jijji da kai idan ba haka ba wallahi zaka rasa rayuwarka a banza kuma babu abinda zaayi "yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuu ya fice har zai bi bayansa mami ta sha gabansa da sauri tare da ware hannuwanta “karka kuskura kabi bayansa ,kana jin mutun yana ikirarin zai kasheka ya kashe banza shine zaka bi bayansa “sweetheart ki barni babu abinda zai iya yi “wallahi bazan barka ba idan kai baka son rayuwarka ni ina da buqatar ka a raye ,oya koma can ka tsaya ko ka wuce d’akinka, tsayawa ya kasa furta komai yana cin ransa .”
yaya Ibrahim yace" idan har baka bari an sauko da komai ba ina tabbatar maka gobe goben nan zan bar aiki a kamfanin ."so what idan ka bar aiki ? ya kallosa a fusace yana huci ,ka sani ni kasuwancina ba kamar na kowa bane kuma nasan kan business dina kuma babu wanda ya isa acikinku ya janye daga hukuncina "enough adam ya fad'a a tsawa ce shima tmkr zai maresa shima AD yayi kusa dashi sosai yana zaro masa idanuwanshi da suka gama canza kala tsabar bacin rai "ka sausauta muryarka akaina Ibrahim " idan ba haka ba me zakayi ? "Zan... zan canza maka kamani yanzu ya fad'a yana huci kamar zaki .shima sai da mami ta shiga tsakaninsu "wallahi adam ka raina ne kana magana dani kamr bakasan tazzrar dake tsakaninmu ba, kai duk abinda yazo bakinka kake fad'awa mutane da wadan da suka girme maka da saaninka "adam ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana hura masa hancin "dan allah ku daina fad'a akan dan wannan matsalar duk ku kwantar da hankalinku komai zai daidaita kai adamcy wuce d'aki .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana furzar da iska acikinsa sannan yayi wani juyi ya hau step da sauri sauri yake taka step yana cewa "babu wanda ya isa ya canza tsarina shi kuma wancan d'an iskan zai gane kurensa har ni zai yiwa barazana da mutuwa ? bayansa suka bi da kallo har da suka daina hangosa sannan yaya Ibrahim ya kalli mami "dan allah mami kiyi masa magana nasan ke kadai zaki fad'a masa yaji mutane bila adadin ne suka dogara da wannan kamfanin me yasa zai yi qari ? ban san me yasa zuciyar adam bata da tausayi ba wallahi idan bai sauke raayinsa ba akan wannan matsalar am sorry to say mami zamu samu babbar matsala dashi ."
Mami ta riko hannusa ta qarasa dashi kan kujera ta zaunar dashi taje ta dibo ruwa mai sanyi a glas cup ta dawo ta mika masa " sha ruwa Ibrahim ka samu natsuwa " bai yi mata mutsu ba dan yana bukatar ruwan ya karba ya sha kadan ya mika mata cup yana sauke numfashi "kayi hakuri kaji ibrahim ka bar komai a hannuna kamar yadda kace maganata kawai yake ji ,zai ji da izinin allah duk yadda kuke so zaayi ya sauke numfashi yana cewa "na gode sosai mami allah saka miki da alkhairi dan allah kiyi kokari ki sauko da adam nasan yayi haka ne da wata manufa amman ya duba mutane dake amfana da ma'aikatan ba wadan da suka bata masa rai ba in sha allahu zai ji kuma zaka ga canji " allah yasa ya fad'a tare da mikewa ya rusunawa yayi mata sallama ."
tsaye yake a d'akinsa yana faman zariya yana cika yana batsewa "har ni fahad zai wa barazana da mutuwa ?daga yanzu bazan cigaba da daukar wulakancinsu ba a hankali yake magana yana balbale botiran gaban rigarsa ya cilla rigar a saman gado ya saki numfashi da karfi tare da kwance agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yayi taku biyu ya ajiye a inda ya saba ajiyewa.jkinsa na tsuma ya tsura wa mirrow idanunshi yana kallon kansa gabadaya sai yake jin rashin dadin abinda yayi sam sam bai kyauta ba kuma ya tabbatar da maganar Ibrahim gaskiya ne mutanen da zasu shiga damuwa idan mummunar abu ya samu da kanfani suna dayawa amman bazai ta'ba daga wa kowa kafa ba ya furta a fili yana jan tsaki ya juyo ya fad'a kan katifa "
Mami ta hada abinci a qaramin tire kamar yadda ta saba dan abinci idan ba daga hannunta bane baya ci saboda tsoro abinda zai cutar da rayuwarsa a natse ta nufi kofar parlour'nsa ta wuce bedroom dinsa ta shiga yana kwance flat akan gado ya daura hannuwansa duka à faffadan qirjinsa ."
Ta ajiye tiren abincin akan wani qaramin table wanda daman dan cin abinci aka tanadeshi ya mike a hankali daga kwanciyar da yayi ya zauna ya hade hannunwansa wuri daya bata tace masa komai ba kamar yadda shima bai ce mata komai ba ta dauki plet da spoon din abinci data shigo dashi ta kai bakinsa ahankali ya dinga amsa yana ci har sai data fahimci ya koshi ta ajiye sauran ta sakar masa murmushin farinciki tare da kamo hannunsa cikin nata kafin tayi magana ya motsa labbansa ahankali "na gode sosai sweetheart allah ya bar min ke "ameen adamcy nah kai ma allah ya bar min kai bata nemi tayi masa mgn akan lamarinsa dasu Ibrahim ba ta barshi har ya dan sauko hira ta soma janshi ."Ahankali ahankali ya dinga biye mata suka shiga hira ta tsakanin uwa da d'a a qarshe ta shigo masa da maganar .”ka zama mai hakuri da yanuwanka adamcy dan baka da kamarsu sannan ka zama mai tausayi domin kai ma kana buqatar tausayawar ubangijinka , akwai mutanen da kamfaninku suke ci suke sha suke komai na rayuwarsu ka duba allah da ire iren su ka sauko da komai sai kayi tawassali da aikin alkhairin da kayi ka roki Allah wata buqata kaga yadda Allah bazai maka ba “babu abinda nake buqata sweetheart kamar mafarkina ina tsananin son kasancewa daita “ya fad’a acikin ransa.”mami ta dade tare dashi har sai data ga bacci na qoqarin daukarsa sannan ta barshi ta shafa sumar kansa.”
tana tsananin son danta bata qaunar abinda zai kawo masa damuwa arayuwarsa yanzu shiyasa ma tayi qoqarin danne damuwarta akan matsalarsa da maryam tunda yace bai so ta hakura har abada Allah ya raya abinda zasu samu blanket ta janyo ta lullube masa rabin jikinsa ta fito daga dakin ." bacci mai dadi ata yake yana rungume da hannunwansa cikin baccinsa ya fara mafarkinsa wanda a qalla ya kusan wata uku bai yi ba koma yace fiyye da haka ,yarinyar daya saba gani ita ya gani sai dai wannan karon cikin mawuyacin hali ya ganta acikin wani kungurmin daji gashin kanta duk ya hargitse ya zubo gadon bayanta tana gudu tana ihun kiran sunansa da iyakacin karfinta cikin haka wasu mutune guda uku maza suka biyota tana gudu suna binta har sai dai ta bace masu amman ita bata daina gudu acikin dajin ba juya ne ya soma dibanta kanta ya soma juyawa tana kokarin zubewa kasa sai gashi ya qaraso gareta ya tarota da hannuwansa duka sukai zube kasa tare ." lumtsatsun idanunshi ya tsura mata yana kallonta yana kiranta da sunan da yake kiranta dashi dan tuni numfashinta ya dauke ganin halin da take ciki yasa hankalinsa yayi mugun tashi ya kamo hannunta yana murza tafin hannunta cikin sauri amman still bata tashi ba hakan yasa ya hade bakinsu waje d’aya ya fara tsotsa yana sake hade hannuwansu ya cigaba da murzawa ."
Yana shan bakinta hankalinsa na tashi dan jijiyarsa tuni ya tashi, ahankali numfashi ta ya dawo ta soma bude idanunta har ta budesu akanshi still bakinsu na hade ya kasa cire bakinsa cikin nata ,hannuta ta kai ta shafa gashin dake kwance a fuskarsa wanda hakan yasa ya zare bakinsa a nata yana dubanta .ahankali idanunshi suka sauka akan tudun brest dinta nan take yaji shaawarta ta kamashi ya rungumeta ajikinsa tsam ajikinsa yana shafa bayanta naunayen ajiyar zuciya ya sauke Jin yadda jikinta ya dauki zafi gbdy jikinta yayi sanyi ya sake "su waye wadan nan mutanen dake binki ?shiru tayi babu amsa "me kika yi masu suke binki ?shima shiru tayi masa ya zareta ajikinsa ya tsura mata ido ina ne gidanku ?sai lokacin ta motsa jikinta ta nuna masa wani doguwar hanya ya mike daita rungume ajikinsa da hannunta ta dinga nuna masa hanya har suka qaraso wani gida mai get kai tsaye suka shiga da gudu yaga wata mata tayo kansu tana kuka , tasa hannu ta karbeta a hannunsa ta kwantar daita ajikinta yana qoqarin bude bakinsa yaji "allahu akbar !! Kiran sallahr daaka kwalla daga masalacin gidansu ne ya farkar dashi agigice ya mike ya zauna a tsakiyar gadonsa gbdy zufa ne ke tsiyaya ajikinsa gabansa sai faman bugawa yake ,jijiyarsa yaji ya harba da sauri yabi jikinsa da kallo yadda gabansa ya tashi sosai gbdy ruwan shaawa ya jika masa qaramin wondonsa nan take ya dauke idanushi dan ba wannan bane damuwarsa halin daya ga princess dinsa ne ya damesa ko a wani hali take ciki "oh my god a ina zangaki princess ?ya jima zaune yana tunani har lokacin sallah yyi ya sauko ya shiga bayi ."
Da misalin karfe goma na safiya yana zaune ya dan jingina jikinsa akan wani karamin table a dakinsa yana tunani mafarkinsa na jiya bai ta'ba mafarki mara dadi akanta ba sai jiya "ina jin sonki sosai princess ko a wani hali kike "wacece wannan? yaji sautin muryar mahaifiyarsa da sauri ya dawo haiyacinsa yace "ba kowa ! ya bata amsa Kmr zaiyi kuka "karka ce haka adamcy na shigo dakin nan kayi zurfi cikin tunani ta qarasa mgnr tare nufar inda wordrobe dinsa yake ta ajiye masa kayansa ta dawo kusa dashi" kana damun rayuwarka dayawa adam numfashi ya sauke yace " sweetheart bazaki fahimci halin da nake ciki ba ta sauke numfashi tare da dafa kafafansa" fad'a min naji zan fahimceka shiru yayi yana tunanin abinda zaice mata , ganinsa ko ya fad'a mata shirme zata dauki maganarsa kamar yadda ta saba kawai gara yace mata babu komai ya hutar da rayuwarsa muryarsa a sanyaye yace babu abinda ke damuna numfashi ta sauke "bazaka iya boyewa mahaifiyar komai dake damunka ba fad'a min me kake tunani ?shiru yayi yayinda abinda ya gani a mafarkinsa yana sake dawo masa kamar a zahiri ."
"sweetheart !
Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai kana kallonsa kasan yana cikin damuwa "ya kayi shiru ina jinka ka fad'a min abinda ke damunka adamcy fuskar yarinyar ya soma gani acikin kwayar idanunshi cikin muwuyacin hali " tell me what's the matter ".dan allah sweetheart ki fahimceni akan abinda zan fad'a miki "uhm ina jinka gskiya akwai abinda yake damuna amman akan mafarkina daman har yanzu kana mafarkinta ne “?ya d’aga idanunshi sama alamun tunani sannan ya saukesu akanta “na dan jima ban ganta ba sai jiya na ganta cikin mawuyacin hali wanda yasani shiga damuwa sosai nan ya shiga fada mata irin abinda ya gani duk sanda nayi mafarkinta tana min murmushi tana min magana cikin sanyin murya sweetheart intakaice miki tana min komai amman jiya duk babu sai tarin tashin hankali.”
shiru sukai gbdy byn second biyar ya motsa labbansa " sweetheart zan dage da yi mata addua allah yasa ba wani abu ne ya faru daita ba "Ameen !"ya tsinci muryar mami ta amsa da sauri ya kalleta "ina ma wannan yarinyar gasky ce adamcy ?amman na sha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane ."walalhi yarinyar nan da gsky ce da ina tabbatar maka ko ina take zan nemo maka ita ka aurenta saboda na fahimci kana tsananin sonta "."so much sweetheart ya furta yana dafe daidai saitin zuciyarsa shiru hjy zulai tayi tana dubansa Kmr zatai masa kuka "ya allah kasa wannan yarinyar gsky ce a duniya idan ba hk ba rayuwata zata qare cikin cakwakiya "Ameen Ameen in sha allahu zata kasance gsky ta fad'a cike da tausayawa hawaye na kokarin zubo mata .”ya mike ganin halin da mahaifiyar sa ta shiga sai dai saukowarta akan mafarkinsa ya bashi gwarin gwiwa sosai da kuma tabbacin zai sameta” na gode sweetheart bari naje na shirya naje office I have some work" bazakaci komai bane ? "No !kawai ya furta ya nufi kofar bathroom yana layi .”tabishi da kallo ina ma tana da halin ciremasa damuwarsa ina ma da yadda zatayi amman babu sai dai tayi imani babu abinda yafi karfin allah zan tayaka da addua adamcy Allah ya sausauta maka ."Idan kuma daga nice ya Allah ka sheida na yafe masa duniya da lahira ka yaye masa wannan danuwar .”
****
bayan ya dawo daga d'aya cikin ma'aikatansa yana sauka idonsa da abida sukaci karo dauke kanshi yayi ya cigaba da taku "AD !!!! ta biyosa tana kiran sunansa sai dai bai tsaya akoina ba sai parlour'n mahaifiyarsa "ka tsaya kaji me zance mana cak ya tsaya "uhm ina jinki ya fad'a yana duba file din dake rike ahannunsa "dan allah ka bawa sister dina sultana dama just give her a chance wallahi zata maka abinda kake so she can’t disappoint you zata maka zane kamar yadda zaka mata discreb din abinda take so wallahi ta kware sosai kalli yanayin zanenta ka gani ."
Yayi shiru yana dubanta tare da dage girasa daya domin dai duk ya fahimcesu so take ta karfi da yaji ta tura masa kanwarta batasan shi din kwararren mai basira bane ta miko masa takadar zanen da take rike dashi "just one chance AD." ke kikasan takware sosai amman ni babu abinda zanyi da zanenta "ni dai kayi hakuri dan allah to idan bazaka amince ba ka bata aiki akarkaahinka kamar yadda na nemi alfarma a tun farko do it sake of me please tayi kusa dashi sosai tana magana kamar zata shige jikinsa yayi saurin ja da baya yana mata wani irin mugun kallo "kace ka amince dan allah "nifa bazan kawota kanfani da sunana ba amman duk wanda zai kaita banida matsla da hakan "ya fad'a yana barin wurin gabadaya ya haye sama ta juyo a hankali ta bar parlour'n ."
Umma zaune a gefen gadonta cikin tsananin tashin hankali da alhinin rashin d'anta a lissafinta Kwanaki 90 kenan wanda yayi daidai da wata uku da rasa sadam dinta hawaye ne masu zafi Ke fitowa daga idanunta yayinda kwakwaluwarta ke hasko mata fuskar tilon d'anta "ta yaya zan iya jure rashin sadam arayuwata ?zuciyarta tai mata tambayar "duk runtsi duk wuya zan jure domin na barwa allah komai zan cigaba dayi masa addua kamar yadda na kewa mahaifinsa,shikenan sadam ya tafi ya barni ni kadai a duniya alhalin bani da kowa bani da komai sai shi kad'ai." ta qarasa mgnr wasu sabbin hawaye masu ciwo da radadi suna sauka akan kuncinta .”ahankali ta mike tsaye ta qarasa Inda tangamemen hotonsa yake manne da bangon d'akinta ta tsurawa hoton ido tana kallonsa "allah na gode maka akan wannan jarabawa da kamin kasan ina tsananin son sadam arayuwata amman ka rabani shi domin ka gwada imanina “allah nayi imani da qaddara da hukuncinka gareni ,na dai shiga damuwa ne saboda tsananin kewa da sabon da nayi dashi amman zan gargadi zuciyata zan sata tayi hakuri da rashin sadam domin nayi imani rayuwa da mutuwa duk naka ne zan daina kuka ..." a hankali ta dinga furta kalmar zan daina kuka amman still bata daina zubar da hawaye ba ."
tana cikin wannan halin maryama ta shigo d'akin cikin yanayi na sanyi jiki dan zaune take a falo kananan maganganun su aunty salma ne yasa ta baro falon dan bazata juri jinsu ba .kowa ya ganta yasan ta zube sosai akan yadda take daman kuma ba wata mai kiba kirki bace sosai ta d'ashe tamkar mara jini dan haka ramarta ta sake bayyana .”ahankali ahankali take d’aga qafafuwanta har ta qaraso ta durkusa a daidai kafafun umma "umma ki daina kuka ."ta furta mata idanunta na kawo ruwan hawaye "umma ta d'ago idanuwanta ta kalleta da tarin damuwa sannan ta d'auke idanuwanta "umma nasan da wuya ki iya mantawa sadam koni bazan iya mantawa da yaya sadam a rayuwata ba bare ke da kikayi silar zuwansa duniya amman dan girman allah umma kuka nan ya isa haka kar wani mummunar ciwo ya kamaki na shiga uku ,".
“ wallahi ummah ban san ina matukar son yaya sadam zuciyata ba sai dana rasa shi zuciyata na cike da matsanancin soyayyarsa "nasani maryama allah ya jikan sadam ke kuma Allah ya baki hakurin rashinsa "ki daina furta hakan umma jikina na bani yaya sadam bai mutu ba tunda na ji ajikina bai mutu ba tabbas bai mutu ba zai dawo garemu ."umma tayi shiru tana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya a duk lokacin da taji maryam ta furta hakan ta Kan samu saukin zugin da zuciyarta keyi cike da matsanancin soyayya ta kamo kafad'an maryama ta d'agata tsaye bisa kafafunta ta rungumeta tsam ajikinta"maryama maganarki tana kwanatar min da hankali duk da nasan da wahala ace sadam dina yana raye ."kusan minti goma suna rungume da juna kafin daga baya maryama ta zare jikinta ta tsurawa hoton yaya sadam ido ."
A hankali ta kai hannu ta d'auki hoton ta koma kan gadon umma ta zauna tana cigaba da kallon hoton tana shafa fuskarshi yayi matukar kyau sosai fuskarsa kwance da murmushi "umman kin tuna ranar daya d'auki hoton nan ?cewar maryama" na tuna ranar daurin auren mashkur abokinsa ne ta fad'a tana zama kusa da maryama"yaya sadam ka dawo garemu karka barmu zuciyar ni da umma na matukar qaunarka bazamu iya jurar rashinka ba dan allah ka dawo garemu ." shiru sukai gabadaya zuciyarsu cike da tunani umma ta janyo akwatin kayansa ta fito da kayan sawarsa tana nikewa tana maidawa cikin akwatin ,maryama ta d'auki jeans dinsa ta rike tana kallo kafin ahankali ta motsa bakinta "karki damu umma zai dawo fa ".umma ta kalleta kawai dan ita tasan bazai dawo ba har abada mutumin da'aka binne da ransa ta yaya zaayi tunanin zai rayu har ya dawo ?"cike da sheshekar kuka tace "ya allah kabamu hakuri rashin sadam domin zuciyoyinmu sun gaza hakuri akansa maryama ta matso sosai ta kwanta ajikin umma cike da tsananin qauna "d'ana sadam mutumin kirki ne, d'ana sadam mai kyakkyawan zuciya ne ,d'ana sadam mai hakuri ne gashi ya tafi ya barni batare da kowa nasa da zan kalla naji sanyi araina ba."
“shikenan na rasa mai sakani dariya na rasa mai kawar min da damuwa na rasa mai dibe min kewa."
ta qarasa maganar tana zubar da hawaye."maryam ta kai hannunta ta shiga gogewa umma hawaye tana cewa “ karki damu umma zanyi miki duk abinda yaya sadam yake miki sannan kuma kisa aranki zai dawo garemu mu cigaba da yi miki komai tare "
"Zo zo!! ku ga wani abun mamaki Aunty salma ta jawo hannun baba gali da aunty hasanaa zuwa bakin kofar d'akin umma, kalli ku gansu "wannan matar anyi shasha an kashe mata d'a amman dan shashanci ku kalli shirmen da take "ke yanzu wannan ne ya dameki ? baba gali ya fad'a tare da juyawa ya samu waje ya tsaya suka biyosa suka tsya kusa dashi suna dubansa bakinsu na son furta wani abu "salma ki rabu dasu kawai mu dai muyi yadda zata dawo daidai kafin wannan yarinyar ta gama takaba araba gado ,aunty salma ta saki murmushin jin dadi burinta zai cika "kai wallahi ina cikin farinciki saboda kaso mai yawa zaka samu “sosai kuwa dan kaso biyu zanci tunda ni nmj ne "ya qarasa maganar cikin tsananin farinciki wannan kuma haka ne bari kama gabanmu su kuma suje su qarata da kukansu hawaye ne yayi masu yawa" wallahi nima allah allah nake lokaci yayi araba abani kasona inji cewar aunty hasana baba gali ya saki murmushi "ni Allah yasa a mallaka min kamfanin burodi gbdy aunty salma tasa dariya murna kmr su rungume juna a wajen ."baba gali da aunty salma suka fice suna dariya aunty Hasana ta shiga kitchen domin daurawa umma abinci dan tun daaka nemi sadam aka rasa kusan rabin yininta anan take yi ."
Umma ta kai hannu ta shafa sumar kan maryama "allah yayiwa rayuwarki albarka ,allah ya qara mana hakuri, muyita hakuri da sannu allah zai mana sakayy.. “qarar wayar umma ce ta katseta maryama ta mike da sauri ta shiga duba inda wayar take "gashi can a karkashin pillow ta fad'a tare da d'auko wayar ta mika mata cike da ladabi ta d'auka "assalamu alaikum, wallahi alhamdulillah mun godewa allah ya kunfan jiki Aa da kanki ai da kinyi zamanki hjy ba sai kin wahalar da kanki ba to shikenan allah ya kawoki lafiya sukai sallama " umma waye zai zo ?granny ce "shiru tayi tana tunani , tashi muje parlour'n tare suka fito zuwa parlour umma na kiran sunan "hassana "kanwar hajiyata na nan zuwa in sha allahu gobe ,hasana ta fito daga kitchen tana goge hannunta tana cewa "kai allah ya kawo mana ita lfy ta kalli maryama ta galla mata katuwar harara "maza ki d'auke wad'an mugayen idanunki akaina aí mu dai wannan yarinyar ki zame mana balai a danginmu wai aunty yaushe zata bar bangaren nan ne ta koma can gurin uwarta kar muma ta lashe mana kurwa ?wallah duk san dana daura idanuna akanta ina jin kamar na kasheta ta mutu kamar yadda ta zama silar kashe min dan danuwana dan girman allah ki sallema ta bar bangaren nan mu huta da jaraba "ke dan Allah ya isa haka ina zata alhalin tana cikin takaba? wallahi hassana banason abinda kike wa yarinyar nan yana matukar kona min rai dame kike son yarinyar nan taji ?Ko ance miki ita ta kashesa né ?Kiyi hakuri aunty in sha allahu na daina umma ta juya mata baya tana danne hawayenta ".amman Aunty ya kamata ki fito da kayan sadam tunda yanzu ya zama na magada sai bawa yara su yi amfani dashi tunda ya mutu kafin wannan mayar ta gama takaba araba gadonsa .."
"sadam bai mutu ba"maryama ta fada da iyakacin karfinta tana juyowa ta fuskanceta tare da dafe qirjinta "tabbas sadam bai mutu ba ta qarasa mgnr tana kuka "yanzu ke hasana har kina tunanin abinda ya mutu ya bari sun zama na magada ku kenan ?dan kune magadansa sai ni da matarsa maryama nan da nan idanun umma suka cika da kwalla ta shiga girgiza kai "wallahi hasana ki bani mamaki sam banyi tunanin haka daga gareki ba "idan ma kiyi hakuri ni da kaina zan nemi araba duk abinda ya bari domin allah ne yace araba gado ni ban isa nayi jayayya da hukuncinsa ba amman at least kunyi hakuri ku daina daga hankalinku ,baku barni na huta ba baku bar yarinyar mutane ta huta ba wai me yasa haka né ?karki manta maryama jininki ce domin kinfini kusanci daita dan diyar yayankice uwa daya uba daya wallahi naso sadam ya rayu kodan ya kula min daita ya gatanta min ita ya bata kulawar da duk wani miji yake bawa matarsa ."ta qarashe mgnr tana kuka ".
maryam ma ta fashe da kuka ."Umma ko zaa raba abinda sadam ya bari dan Allah a d'an jirkinta tukun har zuwa wani lokaci saboda har yanzu police suna Kan invesgetion idan ya zamo yana raye fa bai mutu ba kuma an rigada an raba komai nashi ni dai a nawa shawarar kar a ta'ba komai nashi hatta suturarsa abarshi tukun nan." da wani irin mugun kallo ta d'auketa dashi " yanzu ke maryama kina tunanin yana raye ? " bai raye yana raye ya kamata abari hukuma ta gama bincikenta alabashi komai zaa yi sai ayi amman for now abar komai gsky
Tunda tasoma magna Aunty hasana tayi shiru tsaye tana mka maka mugun kallo, da ashariya daga cikin zuciyarta "kaji min tsinanniyar shegiyar yarinya suka jiyo muryar aunty salma gabadaya suka juya bayansu suna kallonta ahankali ta dinga taku har ta qaraso inda suke "lafiyarki ma kuwa maryama ?gsky akwai alamun kin zauce ayi hanzari akaiki asibitin mahaukata a duba lafiyar kwakwa kuwarki,"kece fa da kanki kika tabbatar mana yaro nan ya mutu tunda a gabanki kika ce an binnesa da ransa amman ki kekashe kasa akan bai mutu ba " wallahi aunty bai mutu ba dan ina ..."ke jaira kiyi mana shiru anan kafin na zuciya na soma yar yar fa miki mari sadam ya mutu kuma bazai dawo ba har abada idan ma zaki cire hkn aranki ki cire ki fara tunanin wata rayuwa."
ta fad'a tana huci “wallahi bai mutu ,kuma babu mai raba gadonsa hasalima babu takabarsa akaina ina nan ma tsayin matarsa har tsawon shekaru hudu “lallai hasashena ya tabbata yarinyar nan ta samu tabin hankali “to tsaya kiji da kyau duk macen da mijinta ya bata ne zatayi dakon aurensa na tsawon shekaru hudu sannan bayan haka tayi idda idan kin haukace ne gara tun wuri musani amman rabon gado tabbas zaayisa acikin gidan nan inji cewar aunty salma .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 28
Kwanciya maryama tayi a kasa tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya da ban tausayi sai dai duk wannan kukan da take sautin muryarta bata fita sosai ,tana jin ina ma sautin kukanta ya fito fili da hakan zai fiye mata sauki fiyye da rashin fitowarsa bugu da qari ko yasa yan'uwan mahaifinta sun sauko daga tsatsauran raayinsu su tausayawa rayuwarta ta jurewa kowance irin jarabawar da Allah yayi mata amman ta kasa jurewa wannan jarabawar, ta kasa jurewa jarabawar rashin miji da kuma d'anuwa gareta."meye tarin zunubina?tayiwa kanta tambayar hawaye na sake gangarowa akan kuncinta "ya Allah ka sausautawa rayuwata domin idan abubuwan dake faruwa akaina suka cigaba da faruwa zuciyata zata buga ."idanun umma dake cike da ruwan hawaye ta zubawa aunty salma tana kallonta cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da bakincikin mummunan kalamanta ga maryama ."cike da tsananin tausayawa maryama umma ta qaraso gareta ta durkusa ta riko tafin hannunta cikin nata cikin yanayin tashin hankali tace "kukan ya isa haka maryama kada kanki yayi ciwo ."
"mai yasa abubuwa suke zuwa min haka umma ?"ya zanyi da wannan rayuwar ? ya Allah ka d'auki rayuwata na mutu na huta da wannan duniyar da babu komai acikinta sai tarin bakinciki ya Allah ka d'auki rayuwata tunda haka rayuwar duniya take "daga wannan tashin hankali sai wannan tashin hankali meye laifina ?nan take tausayin maryama ya sake ninkuwa acikin zuciyar umma tare da jin wani irin tarin qaunarta mara misaltuwa "kiyi hakuri maryama ki daina furta wad'an nan kalaman haka rayuwa take cike da kudirorin ubangiji ,sannan dukkan rayuwa d'an adam rubutaccen al'amarin ne daga Allah,na shafa fad'a miki duk mutumin da Allah yake so shi yake yiwa jarabawa." wani sabon kuka ta fashe dashi tana jin kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta aunty salma ta kwa'be baki tana duban umma da maryama a kaskance kafin ahankali ta cigaba da cewa "da dai kin daina wannan kukan munafurci da kike yi da bazai ta'ba miki maganin halin da kike ciki ba, mutuwa ce da bakinki kika ce agabanki aka binne sadam da ransa to me kuma yayi saura ?Jin haka ya qara sa ran umma yayi matukar 'baci ta d'ago idanunta cikin zafin rai ta kira sunan aunty salma "salma !"
Yanayin yadda ta kira sunan cikin tsawa ya d'aga masu hankali gabad'aya sukai tsuru suna kallonta domin wannan shine karo na farko da suka ga tarin damuwa da 'bacin rai acikin kwayar idanunta,"salma karki bari 'bacin raina ya sake ninkuwa akan wanda nake ciki ,nayi ta qoqarin na danne zuciyata akanku amman naga alamun so kuke sai na nuna muku fushina da 'bacin raina"me maryama ta tsare maku ?wani irin numfashi mai zafi umma ta fesar kamar an tsikareta haka umma ta tashi daga gaban maryama "wallahi wallahi !!kunji na rantse akan maryama zan iya 'batawa da kowa dan haka ku shiga hankalinku ku san irin magangun da zasu dinga fitowa daga bakinku saboda kuma kuna da naku ya'ya,allah yasa mata kuka haifa dayawa kusani duk mugun nufinku ga maryama kanku ko kan ya'yanku zai dawo domin allah baya zalinci kuma baya son mai zalinci amman nasan rashin ilimi ke damun rayuwarku domin da kusan dukkan rayuwar rubutaccen
lamari ne daga rabbi, kilan da baku tsaya ' batawa kanku lokaci ba gurin matsawa kanku da hassada da hankoron neman duniyar da wani ba ."
aunty salma ta kalli umma wacce har lokacin kwayar idanunta na kanta cike da tarin 'bacin rai sannan ta waiga inda baba gali da aunty hasana suke tsaye suma cike da mamakin umma .aunty salma ta daure zuciyarta da maganar umma tace "irin fatan da zaki mana kenan ?"irin fatan dai da kukewa kanku kenan." da sauri umma ta bata amsa da haka sannan tana cigaba da cewa " maza ku fice min daga parlour bana son ganinku kuma wannan ya zamo karo na farko dana qarshe da zaku shigo inda nike kuyi lamarinku nayi nawa bana son ganin gaba d'ayanku a inda nake kowa ya zauna inda allah ya ajiyesa ."saboda an ta'ba miki yar so zaki fad'a mana haka ? Inji cewar aunty hasana "kwarai kuwa zan ma iya yin abinda yafi haka matuqar akan maryama ne aunty hasana ta numfasa kana tace "idan bake ba aunty ai murna zakiyi da abinda ake wa yarinyar nan yarinyar da ta zama silar rasa tilon d'anki "sadam dai d'ana ne dana haifa da cikina duk kuma wanda rashinsa zai wa ciwo a bayana yake to na barwa Allah kada wanda ya sake dawo min da hannun agogo baya kuje na sallameku bana son ganinku, yadda baku qaunar maryama nima wallahi a yanzu bana qaunarku daga yau na yanke duk wata halaka daku ." da sauri aunty salma ta qaraso ta durkushe gaban ummah ta rike qafafuwan umma da duka hannuwanta ta soma girgiza mata kai kamar wata kadangariya tana kuka tana bata hakuri "dan girman allah aunty kiyi hakuri bazamu sake cewa komai akan lamarin mutuwar sadam da gadonsa ba ki yafe mu dan Allah wallahi sai yanzu nake jin nadamar abinda nayi in sha allahu bazan sake ba tabbas maryama tamkar diyarmu ce Allah ya huci zuciyarki wallahi bazamu sake ba ."
gwalalo idanu aunty hasana da baba gali sukai suna kallon makirci irin na aunty salma ,sam basu ta'ba tunanin zata aikata haka ba "lallai ta cika babba makira ta qarshe "kiyi hakuri dan Allah aunty ta sake fad'a tana mai sakar ma umma qafafun ta kamo hannunta numfashi umma ta sauke da karfi sannan ta samu waje ta zauna akan kujera tana runtse idanunta tare da dafe goshinta" sigina aunty salma tayiwa baba gali da aunty hassana alamun suma suce wani abu ai kuwa nan da nan suka matso kusa da umma suna mata magiya da ban hakuri "shikenan komai ya wuce allah ya yafe muna gabadaya amman dai kusani maryama bata cancanci haka daga gareku ba ,maryama a yanzu tafi bukatar kulawa da tausayawa da soyayya tattare da rarrashi daga gareku tun daga farkon rayuwarta baku qaunaceta ba wallahi kuji tsoron allah na rashin rike zumunci tsakani da Allah da kukayi ,wani abun mutane sunayi ne dan ganin ido wani dan zumunci zasu fake suci amana mussaman zumuncin wannan zamani amman ku babu wanda kukayi aciki kona ganin idon ma bakuyi ba bare bayan ido amman wallahi kusani zumunci a duniya wajibi ne duk kuma wanda bai yisa a duniya ba zai yisa a lahira alahirar ma acikin wutan jahannama ta fad'a tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta ".
"wannan tabbas haka ne allah ya shireyar damu gaba daya allah kuma ya bamu ikon sadar da zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba "baba gali ya fad'a yana mai cike da nuna tausayawa ga maryama wacce hawaye biyu biyu ke bin kuncinta yace "diyata maryama Kiyi hakuri kinji in sha allahu kuka da damuwarki sunzo qarshe domin a yanzu a shirye nike dana baki duk wata kulawa da uba zai bawa diyar cikinsa ."da sauri maryama ta d'ago kwayar idanunta da suka jeme ta tsurawa baba gali cike da mamakin jin furucinsa aunty salma tayi tsigil tace "ki daina mamaki jin abinda babanki ya fad'a ,daa na shiga zuciyar mutun a ga abinda yake ciki da mun bude miki zukatanmu a yau kinga irin tarin nadamar da mukayi a yanzu babu wacce muke son gani cikin farinciki kamarki ki yafe mana duk da bamu dace da a yafe mana ba saboda abubuwan da muka dauki tsawon shekaru muna yi miki "in a slow voice maryama tace "babu aunty salma komai na wuce na yafe maku ." murmushin bakinciki suka sakar mata kafin ahankali suka shiga wata hirar allah sarki umma har ga allah ta hakura domin ta d'auka nadamar gasky sukai ,ta sake dasu sosai tayita masu nasiha kuma duk akan zumunci ne bayan kamar mintuna shabiyar d'aya byn d'aya sukai wa umma sallama suka fice suka bar umma da maryama .
"Umma nah !"
maryama ta kira sunanta cikin sanyin murya "na'am maryama kina bukatar wani abu ne ?bana bukatar komai umma ,ina dai jin dadi ne tare da godewa allah daya bani ke amatsayin uwata kuma uwar mijina , ya allah ka bani ikon kyautata ma umma nah ,ya Allah ka bani ikon yi mata biyayya, ya Allah ka dawo mana da yaya sadam cikin koshin lafiya ka azurtamu da samun zuria masu albarka dashi ,ya Allah kasa mu kasance har a aljannatul firdausi atare "ameen maryama ina alfahari dake, nima haka umma ina sonki "baki kai wa ni ba maryama sonki ajinina yake maryama, allah ya za'ba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki,Allah ya bamu ikon cinye jarabawar mu ,ahankali suka dinga kwantarwa da zukantansu hankali har suka samu natsuwa sai dai da zarar ka d'aura idanunka akansu zaka fahimci zallar tashin hankali da damuwar da suke "ummah ina jin kauri "bari naje na duba ina ganin abincin da auntynki hasana ta daura ne yake kauri ."a'a umma Kiyi zamanki bari naje"uhm uhm maryama bana son kina damun kanki "a'a ummah nah sai dai muje tare ta fad'a tare da mikewa ta tsaya kusa da ummah, umma tayi murmushi a tare suka nufi hanyar kitchen."
*******
tsaye nuzlah take ajikin wondo d'akinta tana zubar da hawayen nadama a yanzu damuwa tayiwa zuciyarta mummunar kamu dan ko abinci bata ci tunaninta kaf ya tafi ne akan son sanin matsayinta a wajen yaya hisham ,shin zai aureta ne ko kuma zai zillewa aurenta ne ?kanta yayi mugun kullewa mafuta kawai take nema "idan har bai aureta ba tayi biyu babu kenan bata ga auren ata bata ga nashi auren idan kuwa haka ne ta cuci kanta da kanta tana cikin wannan halin ta hango shigowar motar yaya hisham din cikin haraban estate dinsu da sauri ta saki labalen ta qarasa gaban mirrow ta soma gyara fuskarta ta d'auki bakin mayafin abayar da take sanye dashi tayi rolling kanta ta feshe ilahirin jikinta da turare ta fito cikin sauri wanda alokacin har sun samu waje sunyi parking din motarsu sun fito suna taku yaya hisham na rike da jakar nana hauwa'u yayinda nana hauwa'u take takawa da kyar saboda cikinta ya tsufa ."da sauri nuzla take daga kafafunwanta lokacin data qaraso daf dasu ta kira sunansa "yaya hisham!" cak suka tsaya a tare shi da nana hauwa'u sai dai ita bata juyo ba dan tasan muryar wacce ,muryar nuzla a raunane tace "yaya hisham ina son muyi magana da kai "jin haka yasa nana hauwa'u ta daidaita natsuwarta tare da danne zuciyarta da kishin mijinta ba dan komai ba sai dan ta qara kankaro wa kanta mutunci a idanunsa domin ba komai ake magana akai ba hakan yana zubar da martabar mace a idanun mijinta sai dai wani irin bugawa zuciyarta keyi da karfin gaske saboda tsananin kishin mijinta ."
ahankali ta cigaba da d'aka qafafuwanta domin basu dama hakan yasa yaya hisham ya juya bayansa tare da zubawa nuzla ido yana kallonta a tsanake " duk ta rame ta d'ashe kamar wacce tayi shekara babu lafiya ko wacce babu jini ajikinta "idan na kiraka baka d'aga kirana yaya hisham laifin me nayi maka ?tayi maganar cike da rauni ,yayinda hawaye suka cika kwarnin idanunta" ban ta'ba expecting haka daga gareka ba well duk a ajiye wannan maganar ya batun aurenmu dan naga kamar yanzu ka fara canza raayinka akaina ?"Eh tô nuzla kamar haka ne dan a yanzu dai gsky bana jin wannan abu zai kasance a tsakaninmu "me yasa yaya hisham ?ta tambayesa tana mai kamo hannunsa cikin tsananin tashin hankali "babu wani dalili kawai matata ta isheni daman can giyar soyayyarki ce ta hanani gane quality's dinta a yanzu kuma idanuna sun bud'e na fahimci duk duniya babu salahar mace kamar nana hauwa'u mace ce mai hakuri mai biyayya mai kyautatawa mai kawaici bazan iya had'ata da wata mace ba ita kad'ai ta isheni na qarasa rayuwata ,na godewa allah na godewa mahaifiyata da tayi silar da nana hauwa'u ta zamo mata agareni "dan girman allah yaya hisham kayi hakuri ka aureni nima zanyi maka duk abinda ka lissafa "bazaki iya ba nuzla bazaki iya hakurin da nana hauwa'u take dani ba "saboda me ?murmshin takaici yaya hisham yayi yana girgiza mata kai "kayi tunani akaina yaya hisham karka hukuntani akan laifin da nayi maka wallahi sharrin sheidan ne ,ita soyayya fahimtar juna ne kuma tun farko bamu fahimci junanmu dake ba shiyasa muka samu matsala,ina sonki baki sona zuciyarki na kan wanina wanda ke a karon kanki Kinsan bazaki ta'ba samunsa ba "yanzu nake qara jin wannan nadamar da dana sanin abubuwan da nayi maka dan girman allah kayi hakuri wallahi har da sharrin sheidan ".
" babu wani sharrin sheidan nuzla kisa aranki babu qaddarar aure a tsakaninmu ne ana gobe fa daurin aurenmu kika gudu kika barni da tarin damuwa Kiyi hakuri kawai haka Allah ya qaddaro miki sheidan bai isa ya raba abinda allah ya hada ba saboda shi Allah daya hadani da nana hauwa'u yasan abinda yasa ya rabamu ya hadani daita ,a yanzu soyayyar dake tsakanina da nana hauwa'u babu dalilin da zai sa na ita had'ata da wata ina sonta da dukanin rayuwata kasa cewa komai nuzla tayi dan gabad'aya ta lura hankalinsa naga matarsa wacce take can ta rasa yadda zatayi ta shiga cikin parlour'n mami dan zuciyarta wani irin dokawa take da karfin gaske wanda hakan ya haifarwa d'an cikin hantsilawa."
da nana hauwa'u tayi niyyar tura kofar parlour'n mami sai taji ta kasa tsoro take ji zuciyarta na cike da tsoron bari mijinta a hannun nuzla da tayi shi kansa yaya hisham din bai mata adalci ba daya cigaba da tsayuwa da nuzla ai ko babu komai ya kamata yaji kunyarta sannan ya nunawa nuzla tana da matsayi ko yaya ne agurinsa amman saboda bai dauketa da daraja ba yana kallonta ta wuce ya cigaba da tsayuwa daita runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharrr sun biyo kuncinta ."
da kyar dafe da qirjinta dake faman luguden bugu dum dum ta tura kofar ta shiga allah ya taimaketa bata iske kowa acikin parlour'n ba numfashi ta sauke wani zufa na karyo mata a saman goshinta da karan hancinta zagaye parlour'n ta shiga yi zuciyarta na tafarfasa tana cikin wannan halin taji sautin sanyayyiyar muryarsa kasa juyowa tayi ta kallesa dan zuwa lokaci hawaye sun qara cika idanuwanta "baby nah!"tana jinsa amman ta kasa juyowa ta kallesa dan bata son yaga rauninta "baby nah kukan me kikeyi diriricewa tayi tana qoqarin maida hawayenta "zo gareni !qoqarin juyowa take amman kukan da take yasa ta kasa sai numfashi da take fixgowa tana fitarwa da kyar "please baby nah maman abar qaunata ."still bata juyo ba ta cigaba da tsayuwa tana jan numfashi ahankali ya qarasa ya tsaya abayanta ya had'eta da qirjinsa ya daura hannunsa daya akan cikinta yana shafawa yana shakar kamshin turaren jikinta kusan second goma suna tsaye haka tunani tayi kar wani yazo ya samesu haka yasa ta zare jikinta kwayar idanunsa ya tsura mata yana jin yadda soayyarta ke sake huda zuciyarsa ."
Ahankali ya riko tafin hannunta yayi taku biyu ya zaunar daita akan kujera mai zaman mutun daya ya dawo gabanta ya durkusa a gabanta tamkar mai neman gafara tare da kafeta da kwayar idanunshi yana kallonta yana nazarin yanayinta ahankali ta kawar da fuskarta gefe tana qoqarin sake danne damuwarta numfashi ya sauke da karfi tare da tsarke hannunshi cikin nata ya dawo da fuskarta garesa "am sorry baby !ya fad'a yana murza tafin hannuta cikin nashi" me kayi ?naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana sake damke hannunta cikin nashi sannan ya motsa labbansa "na haifar miki da damuwa "wani irin damuwa kuma ?ni babu wata damuwa daka haifar min?na haifar miki da damuwa mana nayi silar saka zuciyarki shiga qunci na tsaya na saurari nuzla alhalin ban nemi izini daga gareki ba nasan dole zakiji babu dadi aranki dan Allah kiyi hakuri ki yafe min ."murmushin tayi wanda yafi kuka ciwo "dan Allah ka daina fad'ar haka banaso meye aciki dan ka kula nuzla ?karfa ka manta ni matarka ce nuzla kuma yaruwarmu ce gabad'aya kana da damar aurenta ma ba kulata ba ,karka manta na baka wannan damar idan har yanzu kana raayin aurenta kofa a bud'e take bazan haramta halal din da Allah ya halallta ba sai ma nayi maku fatan alkhairi ta fad'a tana kallonsa shima ita yake kallo yana sake hango damuwa daga gareta ,"
gabad'aya fuskarta ta sauya hankalinta a matukar tashe take maganar da take amman kaji abinda ta fad'a dan karta haifar da damuwa atsakaninsu "ni dai Kiyi hakuri bazan sake kulata ba yau ma na tsaya na kawo qarshen komai ne a tsakaninmu sautin muryarta ne ya katse masa magana "tashi ka zauna please kar qafafuwanka sunyi ciwo ka daina damun kanka dan baka min laifin kome ba tana gama fadar haka ta mike da kyar tana cewa "bari na shiga dakin mami yanzu zan fito ta soma daga kafarta da kyar bayanta yabi da kallo yana mamakin hali irin nata da duka matan duniya haka suke kamar matarsa da baa samu wata damuwa a gidan aure ba komai nata dabam ne yasan tana da tsananin kishi akansa amman yanayin kishinta na daban ne kuma yana burgesa dan sau tari idan ya kira tana d'auka zata ce "an gaishe da mijin nuzla da nana hauwa'u tun abun na masa dadi har yazo ya fara jin zafin abun dan tun yana amsawa yazo baya amsawa sai dai kawar da maganar ya shigo da wata ,mata mu sani wannan d'abia ta nana hauwa'u d'abia ce mai kyau mu dinga kawar da idanunmu da hankulanmu akan mazajen mu ,mu basu dama kada mu saka ido dayawa akan lamuran su most especially akan mata domin Allah ya halatta zuciyar maza da son mata dayawa yayinda zuciyar mata take son nmj kawai mu san irin salon kishin da zamuyi idan kayi mijinka kawaici tabbas zai dinga jin kunyar aikata wasu abubuwan."
"Tun dazu nake binka akan maganar sultana Adamcy fa sam sam yaki yarda ya dauketa aiki akarkashinsa amman kaki kayi komai akai aunty abida ta cigaba da bin yaya ibrahim abaya tana masa magna amman bai ce mata komai ba "yanzu shikenan babu abinda zaka iya yi akai ?ta fad'a adaidai lokacin da suka tsaya suna fuskantar juna "na rasa meke damun taunainki kina yi kamar baki san halinsa ba tsawon shekaru kina cikin gidan nan kuma babu abinda baki sani akansa ba , kinsan yadda halinsa yake "haka ne nasan komai amman ni nasan yadda zanyi wanda shi kansa bazai ta'ba tunanin zan iya aikatawa ba ai tunda har nayi niyyar sultana ta auri adamcy kamr anyi auren nan an gama muddin ina raye "wannan shine dalilinki naso ta kasance kusa dashi ?ta gyada masa kai alamun "eh! "kina tunanin Adam zai amince da wannan hadin naki ?" ka tsaya kasa ido kaga ikon allah muddin ina raye sai ya aureta "numfashi ya sauke "gsky da kin canza shawara kina kallon yarinyar da mahaifiyarsa ma tayi masa umarni ya aura da kyar ya yarda yayi mata biyayya a qarshe ma sai daya saketa bare wata sultana can ,dama baa acikin family's dinmu take ba ".
"kai dai ka tsaya kasa ido kayi kallon abinda zanyi tunda shi har yanzu bai fahimci menene dalilin da yasa nake son sultana ta kasance a kusa dashi ba dan haka zanyi komai akai tunda kaima har yanzu kana bada umarni a kafani kamar yadda yake bayarwa ko..."dan allah malama ki bar wannan shirmen naki tun wuri ki dawo hankalinki idan ba haka ba zaki aikata katoton kuskuren da zai jawo miki matsala tabbas ina da iko akan kafanin adalili mahaifina kuma shima mahaifina nawa a koda yaushe cikin bin bayan adamcy yake akan komai he always supporting Adam nayi imani ko wannan tsarin daya kawo baba babba yasan da komai dan haka a matsayina na mijinki zan baki umarnin ki cire hannunki ki fita cikin lamarinsa idan ba hk ba duk abinda yabi yo baya babu ruwana ya qarasa mgnr yana nunata da dan yatsansa sannan ya kama gabansa shiru tayi tana kallon bayansa tana ystsina fuska ."
Maryama zaune a kusa da mahaifiyarta cikin halin damuwar data tsinci kanta, kullum qoqarin raba kanta da tunani take amman ta kasa domin da zarar ta runtsa idanunta yaya sadam dinta take ganin cikin tashi hankali yanzu hk ma jan hankali mahaifiyarta take mata "ki fahimceni princess wannan matsalar gabadaya ta shafemu ko nace na fiki shiga cikin damuwa da tashin hankali mai tsananin akan mutuwar sadam amman me zamuyi daya wuce hakuri mu barwa allah komai hatta mahaifiyarsa ta hakura ta barwa allah mai yasa Ke bazaki hakura ba "nasan akwai ciwo sosai amman ki dauka haka taki qaddarar take bawa kuma bai isa ya canzawa kansa qaddararsa ba ,bamu sani ba ko wani mijin Allah zai kawo cikin kankanin lokaci yasa wannna lamarin ya faru "numfashi maryama ta sauke mai hade da saitin kuka" dan allah kiyi hakuri ki daina fad'a min haka babu wani aure da zanyi na gama aure har abada ."ta jingina bayanta da abun gado ta daga idanunta sama hawaye na zubo mata "you better eat enough with all this cry cry ..."bazan iya cin komai ba aunty ."
"Common bude baki na baki abinci kinji my princess wasu sabbin hawaye ne ya zubo akan kuncin maryam ta dube mahaifiyarta gabadaya ta fita haiyacinta adalilin damuwar data sameta " aunty kin cikin abinci ne ?banci ba ina son sai naga kinci ne taya zan iya cin abinci alhalin princess dina tana kwance kwana uku kenan bata sakawa cikinta komai ba ,maryama ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta dauki karbi spoon din hannun mumcy ta dibi abinci ta kai bakinta "kici abinci sannan naci batai mutsu ba ta bude mata baki ta kai lomar abinci bakin mahaifiyarta, bata kai ga cire spoon din ba aunty ta dibo abinci da hannu ta kai bakin maryama."
Maryama na hawaye mahaifiyarta hawaye aunty tana matukar tausayawa kanta da rayuwar yayanta "ina rokon allah yayi min sausauci domin zunubina yake shafar yayata da basu baji basu gani ba wasu hawaye masu ciwo ne masu zafi sukai zuba a idanunta "in sha allahu zan koma ga dangina zan rokesu gafara "dan allah Allah ki daina damun kanki nima na daina damuwa na yarda da qaddarata "aunty ta rungume maryam " yauwa princess ki kula da kanki kinji ,karki ji komai aunty in sha allahu zan kula miki da kaina ."
"Me zaki ce da rana ?kinga aunty ba sai kin wahalar da kanki ba wannan abincin da naci ma ya isheni har gobe aunty ta dan ware idanunta waje "a'a ki fad'a min kawai duk wahalarsa zan girka miki maryam tai murmushi bata ce uhm ba bare umh uhm sai ma ta daura kanta akan cinyar aunty yayinda ta saita idanunta akan takardun zanen jamaa dana kayan sawa a hankali tayi zurfi cikin tunanin makomar rayuwarta ta rasa komai ta rasa aikin yi duk inda ake bukata zanenta yanzu an daina nemanta ko tayi ta kai masu ma basanuna alamun ma yayi masu bare su karba dan mijin datasa mu ya tafi ya barta me kuma ya rage mata yanzu ?mutuwa !zuciyarta ta bata amsa da haka ta runtse idanunta gam saboda batason mahaifiyarta ta fahimci damuwarta aunty ta daura hannunta akanta hular kanta ya zame nan kwantaccen gashin kanta ya bayyana "princess dan Allah ki barwa allah komai kinji da sannu allah zai yaye mana komai numfashi ta sauke tana riko hannun aunty cikin nata "na gode sosai mamana allah ya tabbatar mana da alkhairi ."
Zaune suke a babban parlour'n hajiya zulaihert baba babba da babba qarami da uncle jay sai fahad gabansu kayan motsa baki ne aka kawo masu kowannensu cikin shiga ta alfarma acikinsu babu wanda bai taba abinda aka kawo masu sai baba qarami wanda yake cika yake batsewa sannan yake allah allah Adam ya sauko ."ahankali ATA Ke saukowa daga matattakala jikinsa sanye da kaya light blue kansa sanye da facing cap fari sol haka ma kafafuwansa wasu hadaddun silifas farare ne sanye dasu sai kamshi turaren REED ne Ke tashi ajikinsa a natse ya qarasa saukowa ya qaraso inda suke ya gaishesu gabadaya yana tsaye bai kai ga zama ba babba qarami ya zabura ya mike a matukar fusace ya soma magana "kai wani irin yaro ne ?"kawai kana son batawa yara kasuwanci dan kawai kayi certified din kanka ,dama ubanwa ka zauna kayi shawara ko kuwa kafanin naka ne kai kadai da zaka zarta da hukunci akaron kanka "?"akan ma wani dalili zaka qara farashin kaya ."
Ganin baba babba da uncle jay yasa bai dauki zafi ba ya kwantar da murya yace "nayi haka ne saboda ingancin kayanmu bawai da wata man.."karka fad'a min haka domin wannan maganar banza ce ai sai da yaya Ibrhim ya fad'a masa kar yayi haka amman yaki inji cewar fahaf " wani mugun kallo ATA ya daukesa dashi wanda yasa babu shiri yaja bakinsa yayi shiru "duk wasu yan kasuwa ku barsu suje wasu compaing su dauki kaya daga ingancinsu zasu rasa abokan kasuwancinsu ni nasan abinda nake ba yau na fara kasuwanci ba koma nace kasuwanci ajinina ya....."enough Adam karka wuce gona da iri yadda kake taimaka da kasuwanci muma itace silar zuwanmu duniya ba kuma zamu yarda ka batawa yayanmu kasuwancinsu dan muma munyi business sama da shekara talatin , so munsan kasuwanci dan haka bamu amince da wannan tsarin naka ba domin tsari ne da zai korewa kanfani kasuwa daga yanzu da nake maka wannan maganar ka janye kudirinka akai "wannan shine magana ta gasky baba abinda yaya Ibrahim yayita fama dashi kenan Faaha ya fada yana hura hanci abinda ma ya kamata da zai dauki wannan mataki ya zaunar daku gabadaya ya tautauna daku ba wai ya yanke hukunci a qaron kansa ba nan fa baba qarami ya dinga zuba ruwan bala'i ta inda yake shiga bata nan yake fita ba ,sauran yan'uwansa na bashi hakuri da kokarin kwantar da fushinsa dan bai iya fushi ba mutun ne mai tsananin zafin rai zuciya ".
"Ku daina bashi hakuri yayi duk abinda zai yi ".ATA ya fad'a a fusace sannan ya tsaida kwayar idanunshi akan baba qaramin "baka da wannan cikakken iko akan wannan kafanin magana ta karshe ka janye jikinka akan wannan kafanin ka maida idanunka akan wanda yake naka ne kai kadai "ni kake fadawa haka saboda baka da mutunci ?" Ata yayi shiru yana hura hanci tare da soke hannuwansa cikin ajihu "dan banza yaron kawai mai banza zuciya ni wallahi bansan inda uwarka tasamoka ba dan ubanka bashi da mugun hali da mugunta ,yaro kamar sheidan idan anyi nan yayi can dan iskan yaro kawai wallahi maza maza ka tattara ka kama gabanka kabar masu kamfani su cigaba da kula dashi ka tsaya iya mallakinka dan kai ne zaka hakura ka bar mana ."
shiru ata yayi yana kallon baba qarami zuciyarsa na tuttukin bakinciki wani irin tsanarsa yaji ya darsu acikin zuciyarsa ransa idan yayi dubu ya baci wallahi yaci darajan babba babba dake zaune da girman mahaifinsa da kuma uncle jay da yau ya gane kurensa domin kuwa da ya nuna masa ya zarta dan iskan daya kirasa dashi cike da fushin zuciya ya juya zai wuce baba babba ya kira sunansa "Adam ..!
Cak ya tsaya sakamakon jin sautin muryar baba babba "dawo nan Adam a gama magana gabadaya ya juyo a sukwane fuskar nan tashi ta sake rikicewa ta hade kwata kwata babu wani alamun annuri "me zance tunda ya zarta da hukuncin da yake so kuma ga dukkanin alamun yayi maku daidai ,"baba qarami ya kallesa ya watsar"ba haka bane adam !" baba babba ya fad'a tare da mikewa tsaye yayi taku zuwa inda yake tare da yin kasa da muryarsa "kafi karfin duk wannan adam ka janye hannunka tunda sun kasa fahimtar dalili dayasa kayi haka "kenan ka yarda da tsarinsu ?yes saboda zaman lafiya ne domin bazasu ta'ba fahimtarka ba idan ma da hali ka cire hannunka gbdy dan bana son na rasaka ,rayuwarka nada matukar amfani a gareni ."ata bai sake cewa komai ba ya juya a matukar fusace ya haye sama yana taka step cikin sauri sauri."
Mmn sudai
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 29
Zuciyar ATA cunkushe da haushi tare da takaicin baba qarami ya tura kofar parlour'nsa ya shiga yana shiga kai tsaye bedroom dinsa ya shige ya rike kugunsa da hannu d'aya yayinda yasa d'ayan hannunsa ya dafe goshinsa da yaji yana masa wani irin mugun sara sakamakon'bacin ran daya shigo dashi ,babu abinda yake gani sai fuskar baba qarami ita ke masa gizo cikin tsananin 'bacin rai saurin runtse idanuwansa yayi yana mai sake jin bakincikinsa na nunkuwa wani irin zafi da suya zuciyarsa keyi,duk da ya murje idanunshi ya fad'a magana son ransa amman hakan bai masa ba yaso ya zage kunjinsa ne ya zabga masa rashin mutuncin da har ya mutu bazai manta dashi ba .kusan mintuna shabiyar yana tsaye yana zariya acikin d'akin tamkar wanda yayiwa sarki karya ."a can parlour'n kuwa baba babba ne a gaban baba qarami , bai damu da cewar shine babba ba ya kwantar da kai cike da tausasawa yake masa magana "dan girman allah baba qarami kayi hakuri karkayi fushi da adamu tunda ka rigada kasan halinsa kuma ... "ba maganar hakuri bane yayi saurin dakatar dashi ta hanyar fad'ar haka "kawai kasashi yayi abinda ya dace shine zaman lafiyar kowa idan ba haka ba zaayi wacce za'ayi "in sha allahu zai yi biyayya a gareka "dole ya sauke ra'ayinsa yabi naka domin kai uba ne agaresa "wannan haka ne dole yabi umarninsa "inji cewar uncle jay "kayi hakuri da duk ma abinda adamu yayi maka d'anka ne babu yadda zakayi dashi sai ma fatan alkhairi daka masa arayuwarsa .""baba qarami ya katse uncle jay ta hanyar d'aga masa hannu "dakata jamilu ya isa haka karka cika ni da surutu "adamu ba d'ana bane kune dai kuka d'aukesa amatsayin d'a dan d'an cikina bazai ta'ba maida min magana ba kamar yadda yayi a yanzu a gabanku adamu yasan ubansa ni kuma nasan ya'yan dana haifa ,sai abu na qarshe wallahi wallahi kunji na rantse ku gaya ma wannan gantalallen d'an naku ya kiyayaeni kar ya kuma yin gigin shiga hurumina dana ya'yana yayi lamarinsa muyi namu yayi na farko yayi na biyu kar yayi kuskuren aikata na uku domin idan yayi na uku bazai ji dadina ba "baba babba yace "shikenan in sha allahu bazai sake ba "baba qarami yace "da dai ya fiyye masa dan wallahi idan ya kuma yunkurin shuka min rashin mutunci ba wannan mgnr zaayi ba dan zan shuka masa wanda yafi nasa ."
" da kyar uncle jay da baba babba suka rarrashesa suka samu ya d'an sauko sai dai duk da haka ya fita yana zage zage tare da tsinewa ata din wanda shine abinda yafi komai konawa mami rai dan har sai data ta zubar da hawaye dan bakinciki ."
Ahankali baba babba ya numfasa ya cewa uncle jay " tashi muje mu samu adamu shima mu kwantar masa da hankali dan a samu komai ya wuce atare suka mike suka haura saman d'akinsa alokacin ata ya samu waje ya zauna a gafen gadonsa ya had'e fuska tamkar hadari duk wanda ya kalli fuskarsa alokacin sai tsoro da firgici ya kamashi ,suka tsaya a gabansa suna kallonsa na tsawon lokaci kafin su fara magana .ahankali baba babba ya fara da nasiha mai ratsa zuciya da shiga jiki akan yayi hakuri da yan' uwansa "shiyasa a kullum yake qara ganin kimar dattinjon domin dattijo ne da yasan yakamata bayan baba babba yayi shiru shima uncle jay ya soma nashi "kayi hakuri ata hakika mun san komai mun san kamfani na mahaifinka ne alfarma kawai yayi wa yan'uwa alokacin da yake raye hasalima babu wanda yasan cewar nashi ne sai mu shakikansa dan tun kafin rusuwarsa kamar yadda kasani ya fitarwa kowa da hakinsa amman kasan halin kawunka sam baya kyautawa kanshi kuma baa isa a fad'a masa gaskiya yaji ba duk da yasan gskyr aka fad'a masa kai dai abinda nake so da kai ka cigaba da hakuri dashi, kasa aranka duk abinda ya aikata agareka tamkar mahaifinka ne yayi maka ,kayi hakuri ka zauna lafiya da kowa wannan shine muradinmu da kuma kwanciyar hankalinmu dana mahaifinyarka" jiki a sanyaye ata yace "naji kuma a gode sosai da kulawarku "Allah yayi maka albarka sukai masa sallama suka fice daga gidan gabdaya."
Bayan fitarsu da kamar mintuna talatin sai ga mami ta shigo inda ta iskeshi a zaune a parlour'n akan one siter hannusa rike da waya yana daddanawa a yadda yake operating din wayarsa zaka d'auka kwata kwata baya tattare da wata damuwa ne ballanatana wani abu makamancin matsala amman ala hakikanin gaksy kallo daya zaka masa ka fahimci yana tattare da zallar damuwa masu tarin yawa cike da tausayawa mami take kallonsa .
ahankali ata ya d'ago tsumammun idanunshi da suka gama canza kala tsabar tashin hankali da yake ciki ya tsurawa mahaifiyarsa ido yana kallonta cike tsananin qauna ,waje ta samu ta zauna a gefensa murya a raunane ta kira sunansa"adamcy !gabadaya ya juyo bangaren da take zaune ya natsu sosai domin yaji abinda zata fad'a itama dan ya rigada yasan taji komai daya faru kawai fitowarce taki yi shima yasan dan gudun abinda zai biyo baya ne yanzu ma yasan fad'a ne da nasiha ya shigo daita "yayi maka kyau adamcy da duk abinda ka janyowa kanka ."shiru yayi kawai yana sauraranta kafin ahankali ya runtse idanunshi ya kasa cewa komai ,mami ta cigaba da magana "wallahi adamcy ka rage wannnan zafin zuciyar karta jawo na rasaka . ina umartaka ka janye hannunka bazan so wani mummunar abu ya sameka ba domin duk abinda ya sameka ya sameni dan sai yafi min ciwo akanka bazaka san yadda iyaye suke ji akan ya'yansu ba sai randa ka mallaki naka wallahi bana son nayi kukan rashinka dan allah ka hakura ."
"yanzu sweetheart kina ganin akwai abinda zasu iya min ?ya fad'a ransa a 'bace ta gyada masa kai alamun "eh !"kinyi imani da allah sweetheart ?"sosai kuwa nayi imani da allah "to kisa aranki babu abinda zasu iya min ni ban ma yarda akwai wani dan Adam din da zai iya cutar da wani ba fashe da izinin allah ya qaras maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "tabbas nasan da haka amman dai fita hanyarsu "shiru yayi mata "kenan bazakayi abinda nace ba ?tayi maganar cikin zafin rai "wallahi da ana canza mutun adamcy da tunin na dade da canzaka kowa ya huta acikin danginka dan kwata kwata baka da kirki "ata dake zaune yayi shiru tare da cigaba da duban mami batare da yace mata komai ba dan ya ma rasa abinda zai ce mata ne yasashi yin shirun
sai dai cikin zafin rai ya kamo lips dinsa na kasa ya soma cizawa da karfi "ina sake umartarka da ka sausauta komai idan ba haka ba zaka ruguza gida d'ayan da amafinka ya had'a "
" kada kayi Kuskuren ruguza ahli dangin mahaifinka adamcy domin cikar muradinka idan ka aikata haka mahaifinka bazai ji dadi ba dan girman allah ka bar ruhinsa ya samu salama "ta qarasa maganar muryarta na rawa alamun tana son yin kuka "sweetheart zaki fara ko ?ya fad'a yana riko tafukan hannunta cikin nashi "kai din ne adamcy baka da kirki wallahi ban san wani irin zuciya gareka ba sam sam baka da tausayi "sweetheart ba haka bane kema kinsan adamcy dinki na iyakar kokarinsa akan ahlin mahaifinsa yana yin komai dan jin dadinsu ne ,babu abinda bana masu suna jin dadi ta koina tare da qoqarin sanyasu farinciki burina mu amafana da wannan kamafanin gabdayanmu nayi qarin kudi ne domin suji dadi ba dan mugunta ko dan jin dadina ba amman sweetheart ki duba kiga abinda baba qarami yayi ,wallahi banyi haka dan zalinci ko son rai ba kayanmu suna da ingancin da ko nawa muka saka farashinsu zaa siya idan baa siya ba wallahi tabbas zaa dawo daga baya saboda ingancinsu ."ya qarasa maganar zuciyarsa cike da rauni ."
jikin mami yayi mugu mugun sanyi da gane da jin abinda ya fad'a ta matso sosai kusa dashi tare da d'aura hannuwanta duka ta riko fuskarsa dashi tana kallonsa wani irin matsanancin tausayi ne mai tattare da qaunar d'an nata taji ya sake nunkuwa acikin zuciyarta yayinda taji kuka from no where ya kufce mata, kawai ta rungumesa ajikinta tana wani irin kuka mai ban tausayi "wallahi nasani adamcy duk abinda zakayi akan agc babu mugunta acikinsa amman bana jin dadin furuncin babanka akanka haka zalika bana jin dadin yadda kake masa ko babu komai uba ne agareka kanin mahaifi ne albarkarsa albarka mahaifinka ne haka zalika tsinuwarsa tsinuwar mahaifinka ce ,ina neman alfarma agareka ,na rokeka dan allah kada ka sake fad'a masa bakar magna akan komai shi din ubanka ne halak malak duk duniya baka da kamrsa ka cigaba da hakuri da yanayinsa haka halinsa yake tmkr naka duk da dai yace bai san inda na samoka ba bayan ya manta cewar duk wannna halin naka shi ka d'auko amman in sha allahu zaka canza ,zaka canza da izinin Allah,allah yayi maka albarka ina maka addua allah ya baka abinda kake so duniya da lahira wannan yarinyar mafarkinka da kake so ina maka addua Allah yasa gaskiya ce.
wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa wanda bai ta'ba jin irinsa ba babu alokaci d'aya zuciyarsa ta tsunduma cikin tunanin princess dinsa nan da nan kuma yarinyar data zanashi ta fad'o masa tun daga ranar farko daya soma ganinta har zuwa had'uwarsu a ogun, shiru yayi zaune tare da rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana tunaninta, muryarta sak irin muryar yarinyar da yake mafarki, yaso kwarai yaga fuskarta a wancan ranar sai dai cewar ita din matar aure ce yasa ya hakura amman wasu wurare ajikinta duk irin na princess dinsa ne hatta yatsun hannunta irin na princess ne haka ma yatsun kafafunta kawai fuskarta ce ta rage masa ya gani ya tabbatar da ko ita ce. oh my godness god ! allah karka sa yarinyar nan tazo min amatsayin matar aure dan ban san yadda zanyi da rayuwata ba"kayi shiru ." bai motsa ba dan bai ji abinda ta fad'a ba "ka daina zurfafa tunani ni dai a kullum ina maka adduar idan mutunce kuma alkhairi ce arayuwarka Allah ya gaugauta had'aku idan ba gaskiya bace Allah ya kawar maka da tunaninta ka huta "
Agogon tsarka hannuta daya zamo hannusa lokacin daya matso kusa daita yana shafa zanen lallen hannunta tayi baya da sauri sauran kadan ta kai kasa yayi sauri riko tsintsiyar hannuta sosai alokacin suke kallon juna ido cikin ido suke kallon cikin kwayar idanun juna nan ma sai da yayi kokarin bude nikaf din tayi saurin kawar da fuskarta ."ahankali ya mike tsaye ya shiga bedroom dinsa ya d'auko agogon tsarka ya fito ya tsaya yana qarewa agogon tsarkan kallo mai cike tsananin sheki yana jin kamar suna tare daita ne a lokacin a hankali ya shiga kai kawo acikin dakin yana cikin wannan halin mami ta mike ganin kamar ma ya manta da zamanta acikin parlour'n "Adamcy ta kira sunansa ya dan gigice ya waigo yana dubanta "meye damuwarka ?daga magana ka fita haiyacinka "ya girgiza mata kai alamun babu komai "ta sauke numfashi tace "ya babu komai daga magana ka shiga tunani daga tunani ka bazama ka d'auko agogo kana kallo agogon waye kamar na mata ?"bai ce mata uffan ba illa ya samu waje akan three siter ya kwanta tare da lumshe tsumammun idanunshi "ka fad'a min agogon wacece a hannunka ?kwanciya sosai yayi ya mike akan kujera batare daya bata amsar tambayar data masa ba ya damke agogon sosai ahankali ahankali ya qara runtse idanunshi yayi pretending like kamar yana jin bacci "adamcy me ya kawo agogon mace hannunka neman mata ka fara ko me ?" "sweetheart I'm feeling sleepy ""Feeling sleeping?"ta maimaita abinda ya fad'a "yes sweetheart bacci ".mami taja numfashi ta sauke ahankali sannan tace "alright !amman karkayi dogon bacci dan laasar ta kusa idanunta akanshi ta fice daga parlour'n sai dai zuciyarta cike take fal da mamaki da zarginsa ."
********
"Maryama taso kizo gareni maryama ta mike da kyar dan gbdy jikinta babu laka ta dawo kusa da granny wacce ta kawo masu ziyara a safiyar yau din ta zauna granny ta kamo hannunta daya ta rike gam cikin nata cike da matsanancin tashin hankali ta soma magana "wai meke faruwa da rayuwar yarinyar nan ne ?gabadaya na kasa fahimtar abinda ke faruwa daita duk lokacin da zaayi mgnr aureta ko tayi saurayi sai wani mummunar abu ya samesa? yanzu kuma gashi wanda ya aureta shima ya mutu ya barta , maryama tai saurin girgiza mata kai " granny bai mutu ya barni ba fa an dai binnesa amman nayi imani bai mutu ba zai dawo domin ina cikin son yaya sadam dan duk cikin wad'an da suka nemi aurena babu wanda zuciyata ta yarda ta kuma amince dashi kamar yaya sadam ni kaina na kan zauna nayiwa kaina wannan tunani granny "why abubuwa suke faruwa dani haka ? daga wannan sai wannan tayiwa kakar sadam tambayar tana sheshekar kuka “ya allah laifin me nayi haka da wannan jarabawa tamin yawa ?yanzu ni nasan haka zan qare rayuwata matukar na rasa yaya sadam babu mai kuma Kuskuren sake zuwa neman aurena ". tayi shiru hawaye na zuba daga cikin idanunta "me yasa kuka min haka ? me yasa kuka nisanta da mijina wallahi zuciyata bazata iya d'aukar wannan tashin hankalin ba?me yasa ? Why why !!! ta qarasa mgnr tana wani irin kuka nan take suka rufa akanta har mahaifiyarta suna bata hakuri ".
ahankali zuciyarta ta tsaidaita daga kukan da take tare da bata kwarin gwiwa "sadam dinki bai mutu ba sannan bai barki ba zai dawo gareki ki bawa zuciyarki kwarin gwiwa ki kwantar da hankalinki domin kwanciyar hankalinki shine kwanciyar hankalin duk wani masoyinki Kiyi masa addua da yarda allah zai dawo gareki ."tun lokacin da granny ta kirata zuwa gareta ya qaraso bakin kofar shigowa parlour'n da fuskarta ya sama cin qaro tana zubar da hawaye wanda ke fita daga kasan zuciyarta kamar ance ta d'aga idanunta dan daman tana fuskatar kofar shigowa ne idanunta ya sauka akanshi ."shiru tayi tana dubansa tana ganin tamkar a mafarki ne kallon juna suke ido cikin ido kafin a hankali ta motsa bakinta ahankali tace "kai ne a gidanmu sir !?bai ce komai ba haka zalika bai shigo ba ya cigaba da tsayuwa "maryama! umma ta kira sunanta ta sauke numfashi tana duban umma "Kina bukatar wani abu ne ?batace komai ba ta sake yunkurin maida idanunta inda ta gansa sai dai wayam tagani babu shi babu alamun sa byn kmr minti goma ta sake ganinsa wannan karon mikewa tayi da sauri ta nufi kofar d'akin wanda hakan ya maida hankalinsu gurin cike da tsananin tashin hankali aunty hassana da aunty suka biyo bayanata haka umma tayi kokarin danne damuwarta ta biyosu "sannu da zuwa oga ammar ka shigo daga ciki mana ." yayi shiru yana kallonta dan gabadaya bata haiyacinta yaso ya wuce a tun ganin farko da yayi mata amman ya kasa "waye shi maryama ?umma ta tmbyeta "shine wanda ya taimaka ya bani aikin dana barwa subaia a Z&A .”
nan take murmushi ya dan bayyana akan fuskar umma "Ke ki rufewa mutane baki da shegen karyar tsiyar "wannna ai mai gidan sadam ne " umma ta dubi aunty hassana cike sa mamaki a ina tasan ogan sadam ?amman dai tayi mata alamun tai shiru sai dai aunty hasana taki shiru ta cigaba da zuba magana " mai gidansa ne dan haka naji anata fada ranar sadakar bakwai hatta kayayyakin daakaita amfani dashi shine ya kawo yanzu nasan da wani abun arzikin yazo ,fuskar maryama bayyane da murmushi tun bayan rashin sadam datai sai yau annuri ya bayyana akan fuskarta kuma tayi imani na ganin oga ammar ne dan bata ta'ba expecting zai zo gareta ba to me ma ya kawosa ?ta jefawa wankakki yar kwakwaluwarta kafin ahankali ta mayar da kanta Ta sunkuyar a kasa "yallabai amar sannu da zuwa dan allah ka shigo daga ciki bai dace ka tsaya a bakin kofa ba cewar umma da kyar ya ra'ba ta gefen maryama ya shigo still tsayawa yayi kamar yadda maryama tayi ya tsura mata idanunshi masu shigar da mutun cikin wani halin " .
“ka tsaya yallabai dan allah ka zauna ga guri “
numfashi ya fezgo da kyar ya fesar saboda ba zaman bane abinda ya damesa tashin hankalinsa yadda yaga yanayin maryama yafi komai damunsa ta rame sosai sai dogon hanci da dogon wuya tsawon second goma ya dauka yana tsaye yana kallonta ya jiyo sautin muryar umma " ga guri ka zauna babu yadda ya iya ya dan dosana jikinsa ya zauna yana sauke numfashi "yallabai mun fa gode sosai da kulawarka allah ya saka maka da alkhairi idanunshi kawai ya lumshe batare da ya amsa ba duk da yaso yayi magana koda gaisuwa ce amamn hakan ya gagara sai dai ya balai tsurawa maryama idanunshi ta cikin glass yana kallonta kallo mai tattare da abubuwa dayawa ya shiga wani yanayi da bai ta'ba shiga ba adalilin ramarta tausayi ne menene shi dai bai sani ba amman yasan zuciyarsa bata son ganinta cikin damuwa .”a natse maryama ta dauke idanunta akanshi ta maida Kan hoton mijinta dake manne da bangon parlour'n "yallabai ga ruwa aunty hasaana ta ajiye masa tire mai dauke da glass cup da roban ruwa kwaya daya akan qaramin table ."naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana mai dawowa haiyacinsa sai dai still idanunshi na kan maryama sai dai ya lura idanunta ba akansa suke ba hasalima wani guri take kallo fuskarta dauke da murmushi da
iya wannan murmushin kawai zata gama da duk zuciyar wanda ya daura idanunshi akanta ."
Ahankali ya kai dubansa inda take kallo nan yaga tangamemen hoton mijinta sadam take kallo tana murmushi hankalinsa yayi matukar tashi nan take daidai zuciyarsa ya dinga bugawa da karfi tamkar ana buga masa guduma hankalinsa ya sake tashi macen da abokinsa kuma danuwansa ya dauki tsawon lokaci sama da shakaeu shabiyar yana renon soyayyarta amman yau ga abinda sakacinsa ya janyo masa yasani idan ata yasan itace yake ta qoqarin ganin sun had’u to zai yi nadamar har qarshen rayuwarsa .ya furzar da numfashi yana jin wani irin zafi acikin zuciyarsa dan ya san da ata ya yarda ya ganta a tun farko a lokacin da ita din ba matar aure bace da ko sama da kasa zasu hade babu mai aurenta sai shi .waigawa yayi yaga babu kowa a parlour'n alamu sun basu wuri "dukkanin alamun sun nuna kina tsanin son mijin nan naki da sauri ta juyo ta tsura masa ido jin abinda ya fad'a ahankali ta lumshe masa idanunta tana tuno yaya sadam dinta byn kmr minti goma sai kuma ta fashe masa da kuka "yaya sadam his very special to me ya fiyye min komai dake cikin duniyar nan zuciyata zata rayu da qaunarsa ne kawai .”yayi shiru kawai yana kallon qaramin bakinta da take motsawa a natse a ransa yace “idan ata ya sameta sai yayiwa wannan bakin kaca kaca kai bama iya bakinta ba ita karon kanta sai ta gane kurenta sai ta gane tashiga hannu .”oga ammar ka kuwa san abinda ake kira da soyayyar gasky ? karkace kai yayi kawai yana sake tsura mata ido dan da alamun soyayya ta zautar daita abokinsa zai sha aiki ba qarami ba “tô yaya sadam yana mun fiyye da soyayyar gsk ...."sorry allah ya jikansa allah yayi masa rahma naso na qara dawowa tun bayan sadakar uku amman sai wata tafiyar gaugauwa ta sameni yau kwanaki goma kenan da dawowata nace nazo naga lafiyarki fatan dai kina lafiya baki da wata damuwa ?”
“bani da wata damuwa sai ta rashin mijina” miji miji !! ya fad’a acikin kasan ransa gbdy sukai shiru a tun bayan data furta haka bai sake cewa komai ba dan yana taya abokinsa jin haushin yadda take nuna son mijinta a fili parlour'n ya dauki shiru kafin ahankali maryama ta dago ta tsura masa idanunta "nasan subaia ce ta fada maka abinda ya faru ko ?yes itace zuciyata ta kadu sosai ban san sanda na janye fushin da nayi dake ba "na gode sosai allah ya jikan iyaye "ameen !”ya furta a fili wannan kalmar nata na cikin abinda take qara burgesa dashi ya dauki kamar awa daya tare daita sannan yace ni zan wuce daman nazo naga yanayin jikinki dan lokacin danazo ance bakya cikin haiyacinki shiru tai tana kallonsa kafin tayi wani hanzari har ya mike tsaye tare cewa " idan kina bukatar wani abu ki bari nasani yana gama fadar haka ya juya har ya kai bakin kofar fita ya juyo ya tsaya yana kallonta yana sake jin tausayinta na mamaye zuciyarsa ta yunkura ta mike da kyar tayi taku biyu ta tsaya tana watsa da yatsun hannunta "take care !"taji ya furta ahankali daga saman lip's dinsa kai kawai ta gyada masa bayan fitarsa da wasu yan mintuna sai ga yara suna ta shigowa da kayan abinci aunty hasana tayi tsalle cike da murna tace "kai gsky wannan mutumin ba qaramin mai kudi bane kaga abun arziki tunda akayi mutuwar nan yake aiko da kayan abinci bata rufe bakinta ba sai ga yaronsa ya shigo da bandir din yan dubu dubu guda biyar ya mikawa aunty hasana kasancewar itace a kusa dashi "gashi inji yallabai "da sauri ta kar'be tana zuba uban godiya aunty kinga wani sabon abun arziki ? gsky mutumin nan yana da matukar kirki sosai ai da gobe nayi niyyar zuwa gidan aunty fatima nayi kwana biyi amman yanzu gsky babu inda zani wannan abun arziki haka ai sai an gama lashewa dani tasss sannan zan..."haba hasana ke mutuwar nan ma kamar dadi kikaji daakayita karki manta duk wannan abun bazasu taba kwantar min da hankali ba d'a fa na rasa sukunta guda dan ma kwaya daya amman kike murna dan an kawo abun duniya gsky idan haka zaki cigaba ni da kaina zan sallameki ki koma bangarenki dan zuciyata bazata iya d'aukar wannan cin fuskar ba.”
“ baki yiwa wannan yar iskar fada ba ko ki koreta a gidanki alhalin itace silar jefa rayuwar d'akin ciki halin mutuwa sai ni ?ai idan kora ne ga wacce ta fini cancatar ki kora bani ba, kai ni me ma nayi tukun ?tayi mata tmbyr tana dubanta a dage babu abinda tayi ita din yarinyar kirki ce datasan mutunci kuma har yanzu dana rasa d'ana bana jin komai akanta sai tsananin soyayya yadda nake matukar qaunar sadam haka nake matukar qaunar maryama domin ita din tamkar diyar cikina take." bata da wani bambamci da sadam a wajena hawaye ya zubo akan kuncinta "fatan kin fahimceni wannan family na bukatar kwanciyar hankali idan kuma kikayi kokarin kawo min tashin hankali wallahi zan ajiye duk wani zumunci agefe fatan kin fahimta,ina bukatar zaman lfy acikin gidan nan tana gama fadar haka ta nufi kofar d'akinta bata kai ga shiga d'akin ba ta jiyo sautin muryar maryama "tunda dai har zamana a gidan nan yana kawo tashin hankali atsakaninku ina ganin lokacin barina gidan yayi ."granny ta girgiza mata kai haka ma aunty wacce jikinta har rawa yake tsabar tashin hankalin maganr maryama .”
Yayinda gaban umma yayi wani irin buga
da mugun sauri ta juyo lokacin har maryama ta soma tafiya "tsaya !maryama ta tsaya cak tmkr yadda umma ta bata umarnin tana ko kuwa da numfashinta har sanda umma ta qaraso ta dafata "babu inda zaki kina nan har sai kin kammala takabarki idan kin yi raayin tafiya sai ki koma gurin mahaifiyarki idan kuma kinga zaki cigaba da zama dani duk daidai ne awurina amman a yanzu babu inda zaki kina tare dani ko kina son ki tafi ki barni Kmr yadda sadam yayi ?ta girgiza mata kai tana kuka "banason na barki umma amman ki duba ki gani kullum kuna samun matsala akaina da aunty hasana gani take nice silar komai alhalin bansan komai ba bansan meke faruwa da rayuwata ba umma da dai kin bari na tafi kawai ni yanzu bama zan cigaba da zama da kowa ba zan tafi inda babu wanda ya sanni na cigaba da rayuwata .”bazaki iya canza qaddararki ba maryama abinda zai faru ya rigada ya faru babu kuma wanda ya isa ya hana ko yasa "umma ina matukar qaunarki araina numfashi ummah ta sauke tace "muje ki zauna ki huta kinji maryama "kai ni ban ta'ba ganin mahaukaciyar mata kamarki ba "taya zaki maida wacce tayi silar barin danki duniya tamkar diyar cikinki kin sani nasani kowa na yasani maryama ba diyarki bace diyar yayar mijinki ce km dan wani baya ta'ba zama tamkar d'anka kina ganin zata zama kamar sadam ne?"
“kowa da yanayin rayuwarsa hasana ni haka tawa rayuwata take da d'ana da ba nawa ba duk abu d'aya ne agurina qaunar da nake ma maryama yasa na hadata aure da dana duk da na fahimci yanayinta a tun farko na nakin auren amman daga baya ta amince saboda qaunar da take min kuma da ina da wani dan a duniya bayan sadam wallahi zan sake aurawa maryama shi kuma ina da tabbacin ko itace ta mutu bilkisu zata sake daukar diyarta ta bawa sadam ya aura "dan hka kije kiyi abinda ke gabanki ko ki bar min gidana na rasa me yasa hasana kike yin haka shin maryama ba diyarki bace ba ,idan ma baki dauketa matsayin diya ba wannna qaddarar da ta sameta idan ta samu diyarki ya zaki ji ? "wannan shine karo na biyu da kika ce na bar miki bangarenki to zan bar miki bangarenki amman karki sake hada yayana da maryama domin diyata bazata ta'ba tursasa mijinta lallai sai ya kaita har wani gari kawai saboda wani zanen banza da wofi ba kar ma ki sake hada maganrki da diyata banaso amman ki rubuta ki ajiye dai maryama zata juya miki baya tunda dai bakece kikawota duniya ba ."naji komai zakice allah ya raka taki gona “a’a abun bai kai ga haka ba duk kuyi hakuri Ke hassana kiyi zamanki amman fur tace tafiya zatayi da kyar granny ta shawo kanta ta hakura sai dai duk sanda zasu hada ido da maryama harara ne ke biyowa baya “
*****
Maryama zaune shiru duk da zuwa yanzu hankalinta ya dan kwanta amman bata wani cin abinci yadda ya kamata haka ne ma yasa jikinta yaki dawowa daidai umma da granny suka zo suka sakata a tsakiya "maryam taso muje kici abinci ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana girgiza kai "bana jin yunwa "haba maryama ina lura dake tun jiya baki sakawa cikin komai ba karki cutar da kanki domin rayuwa babu ci babu sha akwai matsala idan wani ciwo ya kamaki yaya kike son muyi da rayuwarmu “. tayi murmushi kawai tana duban umma “idan ma bazaki tausayawa kowa ba ki tausayawa ummanki cewar granny umma bata ce komai ba ta koma hannunta daya fuskarta dauke da murmushi granny ta riko dayan hannunta suka nufi kan kujera mai zaman mutun uku daita atare suka zaunar daita "umma da kun barni wallahi bana jin cin komai Aa bazai fa yuwu ba ko bakya jin cin komai ya zama dole ki sakawa cikinki wani abu kafin ta sake yin magan granny ta kai spoon din abinci bakinta murmushi kawai maryama tayi ta karba ta soma ci granny na bata umma na bata ."ta kai hannu ta karbi spoon din hannun umma” nasan kema baki ciki komai ba ta dibi abinci ta kai bakinta "umma nah kici abinci “ta girgiza kai tana shafa fuskar maryama sannna ta bud'e bakinta fuskarta dauke da murmushi.”
****
Maryama zaune a parlour'n ummah sanye take cikin wondo da riga yan kanti kanta babu dankwali yayinda gashin kanta ya zubo gadon bayanta gabanta qaramin table ne wanda ta daura farar takardar zane kasancewar ta samu aiki ta hanyar wata abokiyar aikinta yusira ,gefenta kuma tarin fararen takardu ne datai zane bata samu abinda take so ba ,sosai ta dukufa gurin ganin ta zana abinda ake bukata ,tana nan zaune umma tazo ta wuceta ta shiga kitchen byn wani lokaci ta fito ta dan tsaya tana dubanta kafin daga bisani ta koma ta cigaba da abinda take duk maryama bata dago ba dan sosai tayi nisa sai dai har zuwa wanna lokacin bata samu nasara ba ."har yanzu banga kinyi abun arziki ba keda zane baya baki wuya “ta dago a galabaice tamkar zatai kuka "wallahi umma bansan dalili ba na kasa samun abinda nake so ni ma rasa abinda Ke damuna gabadaya na manta komai umma ta qaraso ta dafa kafadarta” karki damu yarinyarta ki ajiye ki huta zuwa wani lokaci zaki samu abinda kike so
Suna Cikin haka kawarta yusira ta shigo bakinta dauke da sallama sam maryama bata dago ba , ta dai amsa sallamar ta cigaba da abinda take umm ta fito daga kitchen tana murmushi "yusira ce agidanmu ? .
"Nice umma ina yini ?Lafiya lau yusira ya mamanki ? tana lafiya ta fad'a tana zama kusa da maryama maryama kardai har yanzun baki qarasa ba gashi dashi nake son na wuce ?ta fad'a tana leka zane jirgin sama ne " uhm wallahi gashin nan fa yusura har yanzu ta kusan awa daya kenan banga alamun zata gamasa ba, kai tunda nake daita ma ban taba ganin zane data bata lokaci irin wannan ba”. cewar umma tana gama fada ta nufi hanyar kitchen .”
Yusira ta biyota abaya "umma me zai hana da zaman nan da maryama take ta nemi aiki tunda ta gama tabarta,banki maganrki ba yusura amman maryama ce wani lokacin akwai taurin kai cewar umma “da kuwa datayi kokari ta sake applied din aiki daya fi, kinga akwai wani compaing AGC dake bukatar ma'aikata nima zanyi applied kinga da sai munje tare abinda ma ya kawo kenan amman sanin yanzu bata bukatar yin aiki yasa nace na fara miki magana dan kinsan yadda zaki shawo kanta ciki sauki ta amince” da zata amince hakika da naji dadi tunda zaman hk bashi da wani amfani banda tunani dake sa mutun amman Kinsan halinta idan tace bazatai abu ba to fa sai ahankali "Allah ya kyauta cewar yusura "amman Kinsan wani abu zan tura masu applications batare da saninta ba sai dai taji ankirata idan sun dauketa shikenan .” gaskiya umma hakan yayi kuma naji dadi sosai ina son duk inda zan kasance muje mu kasance tare ai kwanaki yayi min ciwo data bawa subai,a aikinta wallahi umma da ina gari bazai yiwu ba "to Ke kuma banda abunki ai taimako tayi kinga tafi maryama bukatar aikin duk halin tsananin dasu maryama suke ciki sunfi subaia tunda su ko babu komai muna nan kuma bazamu bari su rayu cikin kunci ba amman subaia da abinda zasu ci ma wahala yake masu ?."
"Haka ne kuma allah yasa mu dace mu samu aikin nan dan aikin a kafanin AGC ba karamin albashi ake samu ba ,samun aiki ma awurin yana daga darajan mutun shiyasa kullum cikin addaua nake akan na samu aiki a wajen ,” bari na baki mail dinsu da zaki tura masu sako tayi maganar tana kokarin ciro wayarta "to shikenan yusira na gode amman me zai hana ki tura min ta Kan waya kawai kamar zai fi sauki ? .""Eh ! Haka ne kuma bari idan na koma gida sai na turo miki duk wannna maganar da suke babu wanda maryama taji domin tayi busy akan zane
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book 2 end
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.