Complete Hausa Novels

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 1 of 11

NAGODE
BOOK 2
PAGE 1
"Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!" Taratsi da kwaroroton Binta ya maido shi daga cikin duniyar tunanin daya lula. Ya yunƙura ya zauna da kyau yana cije baki saboda yanda bayansa ya ƙage, baya iya dogon zama tun Hatsarin daya samu shekaru goma da suka wuce a hanyarsa ta zuwa Kaduna Jana'izar Alhaji Zakariyya Mahaifin Binta shikenan yake fama da Baya dukda iyakar bincike ance babu abinda ya samu bayan nasa amma kam yana ji a jikinsa ga kuma shekaru da suka miƙa wannan yana daga abinda yake ƙara ta'azzara masa ciwon.

"Alhaji lafiya kuwa? Nakusa minti goma tsaye akanka ina magana kayi shiru badan idonka a buÉ—e yake bama ai É—auka zanyi ka mutu" Bintan ta sake faÉ—a tana zama a gefensa. Ya tsura mata ido, ya rasa dalilin daya saka ranar Allah ba zata fito ta koma ba tareda Binta ta kawo zancen mutuwarsa ba, ya rasa meya tsare mata a duniya da take cike da burin taga ya kau.

"Kaci abinci ma kuwa? Koda yake la'asar sakaliya yaci ace kaci abincin rana ai" tayi tambaya kuma ta bawa kanta amsa tana tashi tsaye ta nufi firjin dake cikin Makeken Bedroom ɗinsa me kama da Turakar wani sarki. Ruwan gora ta ɗauko da Kofin tangaran da suke jere a saman firjin ta dawo ta zauna tana tsiyaya masa data gama ta miƙa masa babu musu ya karba dan yana buƙatar ruwan.

"Ya kukayi to? An samu kuɗin sun fito?" Ta jefa masa ainihin maganar data shigar da ita gurin nasa. Ya kurɓe ruwan yana gyara zama yace
"Ba'a samu ba, yace besan inda suka shiga ba kuma na yarda Aminu baze yimun sata ba dan haka maganar ta ƙare dukma wanda yayi sama da faɗi dasu shida Allah kuma a sannu wata rana asirinsa ze tonu"

"Kace me? Miliyan dubu dari biyun harda ɗori kake cewa kabar mutum da Allah akanta Lallai ma Alhaji, tsaya ma, yanzu kai har kana da bakinda zaka shaidi Aminu? Yaushe ka zauna dashi da har kasan halinsa da zakace bazeyi maka sata ba?" Binta tayi maganar a zabure. Alhaji Audu ya kalleta sheƙeƙe yace

"Waini nawane kasonki cikin kuÉ—in nan Binta da duk kika bi kika tashi hankalinki kamar ma kin fini damuwa da abinda ya faru?"

"Ni kuwa nake da kaso a ciki, karka manta Yara goma na ƙyanƙyashe maka a gidan nan ga Takwas nan a raye cikinsu kuma Zarata shida duk mazane kaga kuwa ni nake da Kaso a cikin dukiyarka kuma bazan zuba ido ina kallo a ringa damfararmu sannan kayi shiru kace ka bar mutum da Allah ba" ta bashi amsa tana kaɗa jiki tareda juya ido kamar wata ƙaramar yarinya, ya buɗe baki ze bata amsa sallamar Momy ta dakatar dashi seya haɗiye abinda yayi niyyar faɗa ɗin ya amsa sallamar ta ƙaraso ciki hannunta ɗauke da ƙaton Try. Akan Centre table dake tsakiyar ɗakin ba tareda ta nuna tasan da zaman Binta a gurin ba ta kalli Alhajin fuska babu yabo babu fallasa tace

"Ai bansan ka dawo ba seda nake nake cewa shiru kace kuma ba daÉ—ewa zakayi ba sannan Baba Bilki tace ai ko taji shigowarka tunÉ—azun ta zata na sani shiyasa batayi mun magana ba" abincin ta shiga zubawa ta gama jere komai ta sauke kulolin daga kan Teburin sannan ta tura masa shi gabansa yanda zeji dadin cin Abincin. Wani ruwan ta sake dakkowa daga firji ta ajiye masa Binta dai kallonta take tana zare ido a ranta tana tunanin wai ya akayi ta gaza korar wannan sailubar matar har suke dosar shekaru Arba'in tare a matsayin Kishiyoyi?

"Bari nayi sallar La'asar se naci abincin" Alhaji Audu ya faɗa kafin ya yunƙura ya shige banɗakin dake manne da ɗakin barcin nasa. Momy ta zauna kan doguwar kujera kwaya ɗaya dake cikin ɗakin Hajiya kuma har sannna tana zaune kan gado tana ƙarewa Momyn kallo kamae wata farin shigar Maita har Audu ya fito ya tada sallah ya idar ya hau kan abincinsa Binta na zaune ita kuma Momy bata ce mata ta fita ba dukda zaman nata ya ɓata mata rai. Har a yanzu da shekaru suka miƙa tsakanin ita ko Rabi babu wadda ta isa ta shiga Turakar Alhajin a ranakun girkin Hajiya Binta amma ita ko a kwance suke tana iya faɗo musu a yanzu ne kuma Alhaji Audun yake son ya gyara wannan barakar har yake ƙoƙarin taka mata burki wasu lokutan sedai a banza domin ta rigada ta raina shi, bashi da wani kwarjini ko Martaba a idonta da zw ce tayi abu tayi ko ya hanata ta hanu har ila yau kuma zancen tayi laifi ya mata faɗa kamar yanda yake musu fa babu shi, ita lamarin Alhaji da Hajiya Binta ma har rasa matsayin da zata ajiye shi takeyi dan ko a labarai bata taɓa cin karo da Macen da take zuba sharafi a gidan Auranta irin Hakiya Bintan ba.

"Ina kin gaka abinda ya kawoki?" Muryar Audu ta ratsa kunnuwansu, Momy na danna waya ta ɗago so take ta fahimci dawa yake a cikinsu? Ita me girki ko kuwa Binta data zo ta tasasu gaba? Hamshaƙiyar kuwa ƙara gyara zama tayo dan a tsammaninta da Aishar yake seda ya sake maimaita maganar yana kallon idonta kafin ta ankare, ta buɗe baki zata faɗa masa ba dadi se kuma ta gimtse data tuna tanada shirin da take so ta cimma seta miƙe tsaye tana murmushi tace

"Ai to bari naje, duk na shafa'a ne wlh se naga kamar a Ɗakina nake". Tana dafda fita daga ɗakin wayar Momy tayi ƙara alamar shigowar kira, Hajiya ta fice amma ta coge a bakin ƙofa ta kasa kunne, abin ya rigada ya zame mata Ɗabi'a ko ace ciwo, gulma da Laɓe, tsabar yanda ta ɗorawa kanta bala'i ko a hanya take tafe taji wasu na ƙusƙus seta dakata ta kasa kunne ko ba zataji ko ta fahimci abinda suke faɗi ba, ga zargi da tsarguwa ko yayan cikinta taga suna magana seta tsargu da ita suke ko wani abun suke shiryawa.

A cikin É—akin kuwa a speaker Momy ta saka wayar saboda kunnenta dake mata ciwo kwana biyu bata kara wata a kunnen muryar Ahmad ta ratso wayar yana cewa
"Momy, kin masa maganar kuwa?"
"Tukunna dai, wai idan sauri kakeyi haka ka tareshi da kanka kayi masa maganar mana seni zaka mayar yar aikenka" ta bashi amsa. Daga waje Binta ta sake manna kunne a jikin ƙofa tunda taji muryar Ahmad da kuma cewar anyi magana wace maganace? Abinda take so kunnuwanta su zuƙo mata kenan.

Ahmad ya sake marairaicewa Momy yana cewa
"Haba sweet mother, haba rabin raina kinsan dai bazan iya tunkararsa ba kuma na gaya miki Jafar ya masa magana yace he will get back to us yanzun kusan one month kenan bamuji komai daga gareshi ba and time is really against me Momy, idan baze samu ta hanyar sa ba na sani na nemi wani Alternative ɗin kinji Mamana? Ya ƙarasa maganar kamar ze saka mata kuka yana idarwa kuma tari ya sarƙe shi"

"Bakaje Asibitin da nace kaje ba kenan?" Ta jefa masa tambaya ba tareda tabi ta kan maganar da suka fara ba, Ahmad da tarin ya tsagaita masa yace
"Naje wlh Momy an rubutamun magani na ma farasha, kiyi masa maganar yanzu dan Allah kinji"

"Zanyi" ta faɗa a taƙaice daga nan ta kashe wayar. Alh Audu na cin abincinsa kuma yana sauraron duk wayar da sukeyi tuni kuma ya fahimci zancen da tunin da Ahmad ɗin yake magiyar tayi masa. Ruwa yasha yana kallonta yace
"Shi baze iya zuwa ya sameni muyi magana ba se ya ringa turomun yan aike?"

"Wane shi? Wannan ai se Yayan gida Yayan So" ta bashi amsa hankalinta na kan wayarta se yayi shiru yana kallonta, a yan shekarun nan Aishar ta fara canzawa, idan tayi wani abun se yaga kamar ta fara gajiyawa dashi ne kamar me neman wani dalili da ze janyo saɓani a tsakaninsu. Ajiyar rai yayi yace

"Ai shikenan, kice masa gobe ya sameni a gidan Gona na Kwanar Dawaki se mu tattauna maganar kuma yazo da takaddun"

"Baka da lambar wayarsa kaima kenan?" Ta faÉ—a tana tsareshi da ido, tamke fuska yayi be kuma bata amsa ba ya shige banÉ—aki wanko hannu.
Tayi tsaki a ranta wani abu me ɗaci yana taso mata seta miƙe ta shiga tattara kwanukan daya gama dasu ta ɗora akan Try ɗin data kawo su ta fita. A bakin ƙofa sukayi kiciɓus da Hajiya dake dakon jiran a faɗi gundarin abinda take so taji buƙatar da Ahmad ɗin yake nema a gurin Alhajin da har yace ya sameshi a gidan Gona.

Kardai fa tufka take ta baya tana warwarewa tana nan tana haƙilon ganin sun danne komai Aisha ta ringa mata zagon ƙasa suna wawasa ita da Yayanta? Dole ta Ƙara saka idanu kenan akan harkar shige da ficen gidan da duk abinda yake faruwa wannan maganar ma da ba'a ƙarasa ba seta bi diddiginta tunda sunan Jafar ya fito a ciki shi zata tambaya dukda dai shegen Yaro ne ba lallai ya faɗa mata ba tunda sirrin ubansa Ahmad ne. Tana ganin Momyn ta ɗan diririce se kuma ta waske ta tura ƙofar irin dawowa ta sakeyi zata shiga. Momyn ta kaɗa kai kawai ta wuce, ba yau Hajiyar ta sababa Laɓe ya zame mata ɗabi'a.

Hajiya na ganin Momy ta sauka ta juyo itama ta fice dan akwai abinda yake a gabanta yanzu kafin ta juya takan zancen Ahmad ɗin, ɗakinta ta wuce ta tarar da YAKUBU na cin abinci, Hajiya ƙarama na tsaye gaban console mirror dake falon tana gyara ɗaurin kallabinta. Ganinta yasaka Binta sakin fuska ta washe haƙwaranta duka, guda biyu data sakawa Haƙorin Makka na zinari sunata ƙyalli, Umarar Bara da sukaje ta cire Asalin guda daya na bakinta daya cinye aka saka mata biyun.

"Kinyi kyau uwar masu gida, yau zuciyar mahassada sedai ta buga dan baƙin ciki" Hajiyar ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita. Hajiya ƙarama ta saki murmushi kafin ta shiga juyawa dan ta nunawa Hajiyar kwalliyarta dakyau, Fitted gown ce ta wani cotton London Brocade a jikinta dark blue me zanen flower sea green da fari a jiki, kudinsa ya tasamma dubu sittin, Jafar ne ya aikowa da Hajiyar su sun kai guda goma yace a ɗinka mata dogayen riguna saboda laushinsa yasan zeyi dadin sakawa shine Hajiya ƙaramar ta kwashe uku dan tasan ba ɗinkawa Hajiyar zatayi ba ta kai aka mata lalatattun dinkuna a ciki wannan fitted gown din itace me ɗan dama dama dan ta rufe mata jiki gaba daya illarta kawai shape dinta daya bayyana ƙarara.

"Kin fa gama haɗewa Yar nan babu makusa" Hajiyar ta sake faɗa tana bata hannu suka kashe daidai nan wayarta tayi ƙara, sunan Abba Tee ya bayyana akan screen ɗin. Tsanar dadi harda wani maƙale hannaye Hajiya tayi sama kamar Kangaroo bakin nan ko har maƙogaronta ana hangowa, Hajiya ƙarama ta amsa wayar cikin muryar shagwaɓa kamar zata fashe da kuka tace

"Harka iso"
"Yes Babe, ina waje" ya bata amsa daga cikin wayar, ta sake narkewa tana cewa
"Baka shigo ciki ba? Issa baya nan ne? Kayi horn ze buÉ—e maka Get ya shogar dakai palour kafin na fito"

"He isn't here, oh kamar gashi nan wani Buzu ko? ya buÉ—e Get É—in bari na shigo"
" Saurayin ya sake FaÉ—a kafin ya katse wayar.

Hajiya ta sake bata hannu suka kashe tana cewa
"Wai, Allah ya taimakemu, maza kije ki ƙara turare, duba ɗakina akwai wannan Disaina da kike nacin na baki na gurin Yayanki ki ɗauka, bari na duba abincin idan sun kammala"

"An gama kumai har na shirya a Try kaowa kawai za'ayi" Inji Hajiya ƙarama
"Yauwa yar gari, jeki to kar yayita zama Allah ya bada sa'a" cewar Binta. Hajiya ƙarama ta wuce ɗaki ta ƙaro turare kamar yanda Binta tace ta fito tana takun yauƙi Albarkatun jikinta na motsawa danma kayan jikin nata sun matseta kam hakan ya rage musu samun damar rangaji yanda ya kamata.

Yanda Yaran Alhaji Audu Maza suke Dogaye ginannu idan ka cire Ahmad daya ɗauki Jikin Aisha bashida ƙiba sam haka beyi irin tsahonsu ba to Matan ma duk haka suke dogaye masu cikakken jiki, Allah ya taimake su da ƙira mai kyau ta jiki data fuska musamman da dukansu se akayi katari suka ɗauko fuskar Dada, Farare tas ɗin cikinsu Amina, Aslmaiyya da Hajiya ƙarama da yan Biyun Hajiya Rabi Baba Bilki takance kamanninsu kwabo da kwabo da Dadarsu.

"Yauwa, saura kuma ki sake maimaita abinda kikayi wancan karon kika saka yayi fushi, kina kallo dai har dubuta dari Turai ta damfareni, koda yake kwalliya ta biya kuɗin sabulu tunda an janyoshi yazo, soyayyar nan ta zamani ke sekace ba wayayya ba da ita ake kama samarin nan, banda abinki waye ze kwasheki haka siɗan ba tareda ya tabbatar kin iya kalar soyayyar da yake da buƙata ba, yar rungumar nan da kis ne dai Allah na tuba ai ba wani abu bane, ban dai ce kije ki buɗe kafa ba ki saka mu shiga uku kuma kuyi a hankali Alhaji ma sama ze iya saukowa kowan...."

"Hajiya!" YAKUBU da ke cin abincinsa tun shigarta be tanka maganar da sukeyi ba ya kira sunanta cikin ɗaga murya me kama da tsawa dan a firgice daga ita har Hajiya ƙaramar suka kalleta kowacce na tsammanin da ita yake. Farantin gabansa ya ture ya miƙe tsaye fuskar sa tamkar zatayi aman bacin ran daya turnuƙeshi lokaci daya.

Ya nuna Hafsatu da yatsa yana cewa
"Ashe abinda ake faÉ—a akanki gaskiya ne? Iskancin da aka ce kinayi dagaskene saboda kin shahara yanzu har cikin gidan ubanki kika kawo saurayi zakuyi iskanci?" Kai ta shiga girgiza masa tanaja baya domin Yakubu bashida daÉ—i, ba su ba uwar data haifeshi ma shakkarsa takeyi dan Lamarinsa me girma ne. Hajiya Binta ta dake tana hararar sa tace

"Kai bana son ɗiban Albarka, a gidan uwar masu faɗar aka ganta tana iskancin? Koda uban wani tayi a cikinsu da har suke bayar da shaida? Bakaji me nake faɗa bane? Ce mata nake fa ta saki jiki dashi ita ai gida huma ce duk samarin da kake gani suna zuwa suna tafiya ai ƙin basu fuska takeyi shi yake korarsu. Shifa wannan ɗin in gaya maka, Yaron Alhaji Mudi Tanko ne tsohon Senet piresiden kuma yanzu haka takarar gwamna yake a Garinsu, can kwanaki bana muku zancen sa ba har yazo sau ɗaya shine ya tafi be sake dawowa ba? Ai in gaya maka wannan shashashar yarinyar ce ta kusa kwafsa mana, wai fa ɗaukarta yayi sukaje Otal ya kama Ɗaki, daga cewa su shiga ciki shikenan ta gudo wai har da ce masa ita ba yar iska bace se kace yace mata wata tsiyar ze mata idan suka shiga. Shiko yayi fushi ya tafi, dakyar fa yanzu seda na baiwa Turai dubu ɗari ta kaiwa Malaminta akayi aiki akansa shine fa ya zo yanzu, faɗan da nake mata kenan kar a maimaita ta wnacan karon a samu a kamashi a hannu ya fito ayi zancen Auren nan masu yi mun dariya su sha kunya suji da ƙaryar sarauta suzo suga Arziƙi a inda yake dan duk na samu labarim gidansu ba ƙaramar wadaƙa ubansu yakeyi idan ya tashi Aurar da Yara ba".
Yanda take maganar hankali kwance tamkar me faɗar wani abin Arziƙi, Yakubu yayi sakato yana kallonta a ransa kuwa kokwanto yakeyi akan Hajiyar ce ta haifi Hafsatu ko kuwa Riƙonta takeyi?

Anya uwa zata yiwa yarta irin wannan huÉ—ubar kuwa?
"Zatayi mana, mussamman uwa irin taku da take bautawa duniya da abinda yake cikinta" zuciyarsa ta bashi amsa. Seya ja numfashi ya furzar kafin ya zabura ya nufi ƙofa, cikin Hajiya ƙarama ya kaɗa, Hajiya kuwa yatsine fuska tayi tace

"Ke da Allah rabu dashi, ance masa bansan duk abinda sukeyi bane su? Duk fa haka suke lallatse yammatan suma suna basu kuÉ—i balle ke da Aurenki ma zeyi jeki abinki manta dashi kar kuma ko manta uar soyayyar nan da ake nunawa a fim irinta zaki masa kinji ki hargitsa masa tunani yayi maza maza ya turo azo ayi magana kar zancen Auran Aslamiyya ya riga naki tashi".

A saluɓe Hafsan ta fita duk karsashin da take dashi ya barta. A ƙofar fita daga ainahin cikin gidan taci karo da Ali Daya daga cikin Ma'aikatan gidan me kula da shuke shuke, da gudu ya taho badan ta matsa masa ba da tuni yayi tafiyar gari da ita.

"Yawwa Hajiya kiyi sauri, ga Alhaji Yakubu can yana dukan baƙonki" ya faɗa yana haki. Ƙirji ta dafe tana zaro ido daga inda take kuma tana iya jiyo ihun kukan data tabbatar na Abba Tee ne da kuma hargowar Yakubu yana faɗin
"Daga yau ka sake zuwa wani gida ka yi iskanci da ƙanwar wasu". Da gudu ta juya ciki tana kuka tana kiran Hajiya. Binta nacan tana gyara zaman kofunan da za'a kaiwa Baƙon tana kwararaqa me aikinta Ashar akan wai bata goge su dakyau ba so take yace musu ƙazamai sega Hafsa na kuka jage jage, bata ko iya sauraronta gaba daya ba tayi waje cikin tashin hankali tana kiran Yakubu.

Yakubu kuwa dukan Ɗa da Uba yakeyiwa saurayin Hafsatu ya fasa masa baki da hanci ga hauri yana kai masa a ƙafafu yana kiran seya karya su yaga da wanda ze ringa yawon iskancin Hajiya ta iso ta cakumeshi tana zaginsa se kuma ta saka kuka tana cewa

"Shikenan kaima an taɓa ka, nidai yanda naga ka fito ido a jirkice daman kamar wanda iska ta shafa nasan da walakin, ni aka tozarta a gidan nan ko? Anga Asirin da akayiwa Yata yaƙici kullum sababbin Manema take samu shine aka biyo ta wannan hanyar ko? To wlh mu zuba mu gani, bana Boka bana Malam amma ko wanene ya taɓani seyaji a jikinsa" se kuka wiwiwiwi. Ma'aikatan gidan gaba daya sukayi dafifi suna kallon ikon Allah, Drama a gidan dai ba sabon abu bace ta safe daban ta rana daban ba kuma sa gundira da tirka tirkan gidan domin kullum sabon abu suke gani. Audu da hayaniyar ta fito dashi ya isa gurin cikin dakakkiyar murya yake tambayar abinda ya faru se sannan kuma Abba Tee ya samu ya miƙe ya nuna Yakubu yace zasu gamu seya san shiya taɓa, Yakubu ya zabura ze sake damƙarsa ya taka ya gurin motarsa da sauri ya shige yana cigaba da faɗin
"We shall meet in court, zaka san ni ka daka se ka gane baka da wayo".

Cikin tsawa Audu ya bawa ma'aikatan umarnin su watse kowa ya juya gurin aikinsa. Ya kalli Hajiya dake kuka har sannan Hafsatu ta runguketa itama tana kukan kafin ya mayar da hankalinsa kan Yakubu yana tambayarsa meya faru? Waye wancan É—in kuma meya haÉ—a u harta kai ga duka? Kafin ya bashi sa Hajiya tayi zuruf tace

"Me kuwa ya haɗasu? Magautane sukayi masa turen Aljani haka kawai ya rufeshi da duka saurayin Hafsa ne fa, anga Allah ya fito mata da Miji na nunawa Sa'a shine aka bi yanda akayi shima aka koreshi kuma wlh ba'a taɓa banza ba ko wacece a cikin matanka tayi abin nan ta kwana da shirin zubin Adashi tayi ɗauka kuma dole, ka wuce kai kuma ka kwanta kana tsaye kana wa mutane muzurai ko Aljani ƙarƙuzu ne wlh sekaci ubanka sannan ka koma kan wadda ta aiko ka" ta faɗa tana aikawa da Yakubu wata harara me tafe da gargaɗi. Juyawar yayi kamar yanda tace ya fice daga gidan gaba ɗaya ita ma suka koma ciki da Hafsa dake kuka har sannan.

Alhaji Audu ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi yana kallon Ma'aikatan gidan da duk suka maida hankali kamar masuyin wani abun ya tabbatar kuma kunnuwa da hankulansu har sannan yana kansu, an gama na ɗazu ga wata an sakeyi kuma, idan ba'ayi sa'a ba kafin kwanciyar bacci se an kuma kafta wata Drama. A sanyaye ya ringa taku ya fita ya shiga Masallacin dake manne da gidan tunda Magriba ta kawo kai saura mintina kaɗan a kira. Carbi yake ja amma ya lula cikin tunanin daya aureshi, bashi da damar yayi shiru haka nan ko yayi tunanin abu me daɗi kullum se damuwa se ɓacin rai daga wannan se wannan.

Wayar sa dake gaban Aljihu ta ɗauki Ƙara ya zarota, Alƙali Yakubu ne, miƙewa yayi ya fice daga cikin masallacin ya tsaya daga gefe lokacin wayar ta katse dan haka yabi bayan kiran. A taƙaice suka gaisa, Yakubun ya tambayeshi yanda Zaman su ya ƙare da matsaya akan zancen kuɗin.

"Mun rigada mun gama magana yayi rantsuwa akan bashi ya ɗauka ba kuma na yarda amma na sauke shi daga kujerar Takwaranka ze riƙe na lokacin kafin musan abinyi" Audun ya faɗa masa. Daga ɗaya ɓangaren Yakubu yace
"Idan har ka yarda dashi menene dalilin daya saka ka dakatar dashi daga aiki kuma?"

"Haka dokar take a rubuce, duk wanda aka kama da laifin cin hanci ko yiwa Kamfani zamba hukuncinsa korace sannan ze maido da duk abinda aka rasa, bamu baƙaci ya mayar da komai ba amma an dakatar dashi saboda idan banyi haka ba kamar na buɗe Ƙofa ne ga sauran kowa ze iya wasarere da dukiyar Kamfani saboda yasan babu matakin da za'a ɗauka akansa, kuma dalilin daya saka bamu buƙaci ya maido da kuɗin ba saboda Bincike ya tabbatar da basu shiga account ba, a rubuce ne kawai akwai su kuma idan aka tattara lissafi ya kamata ace suna ciki sedai am rasa ta inda suka maƙale".

Dariya jawabin Audun ya bawa Yakubu ya dara kafin yace
"Ai shikenan, tunda har ka gano da kanka inda matsalar take ina ganin babu laifin Aminu kamata yayi ka tattara shuwagabannin kowanne ɓangate su gabatar maka da lissafinsu da kansu sannan ka haɗa dashi wamda suka bashi daga nan za'a tantance me laifi da me gaskiya, most especially guraren da kuke generating kuɗi sosai Oil da sauran Mineral su ya kamata ka tsananta bincike akai na tabbata daga nan matsalar take" Yakubun ya bashi shawara daga nan suka ɗan tattauna wasu batutuwan kafin sukayi sallama dalilin sallah da aka kira.

A cikin gida kuwa a tsakar gida Hakiya ta kafa kujera tana zazzaga bala'i, daga Momy Har Anty babu wadda ta leƙo ballantana ta tanka mata daman da Baba Bilki tana nan ne itace zata kulata to tana gidan Sarki matarsa ta haihu ita take zauna mata. Har aka kira sallar Magriba batayi shiru ba bakinta har kumfa yake yawu na sarƙeta amma taƙi haƙura ita kanta Hajiya ƙaramar datayi iyakar yinta akan Hajiyar tayi shiru taƙi ɗaki ta shige tana cigaba da kukan Asarar da Yaya Yakubu ya janyo mata, ita ai bata ce masa zata biye ta zancen Hajiya ba domin da tana hawa layin data ke ɗorata da tuni ta daɗe da zama riƙaƙƙiyar karuwa a cikin gida domin abinda Hajiyar take nuna mata kullum shine tayi komai ba komai bane muddinba bude ƙafa zatayi ba. Ta rasa irin tunani da son zuciyar Hajiya, bata duba mutunchinta ko zunubin da zasu ɗauka da ita me aikatawar da ita data turata burinta kawai ta cafko musu Dan Attajiri wanda ya kere Mijim Anna dana Khadija da kuma saurayin da yake neman Aslamiyya tunda bata samu yanda take so akan Nazira data janyowa Nakasar data so ta hanata Auruwa daga ƙarshe Audun ya haɗata da wani Yaronsa babu laifi yana da abin hannunsa daidai Misali shima kuma yana sonta.

Ita Anna Ɗan Sarkin Zazzau ta aura Khadija kuma Wani Matashin Ɗan Kasuwa me jida Yayan Banki duk su biyun suna cikin daula da jin daɗin rayuwa ita Khadija ma zamansu rabi da rabi ne a Nigeria sunfi zama a Dubai wannan Daula da Yayan Momy suke ciki ta tsolewa Hajiyar Ido, sannan ga Auren da Sarki yayi ya Auro wata halfcast Ambariyya, Mamarya ce Bahaushiya yar Nigeria Babanta kuma Balaraben Qatar ne Hamshaƙin me Arziƙi Bikin Sarkin da yanda Uban Amaryar yayi wasan kuɗi ya gigita Hajiyar, ada tana hura hanci akan Matar Zakariyya da Matar Naziru yan manyan gidaje ne tana habaicin kaf Yayan gidan babu wanda ya auro Ya daga gida kamar nasu se gashi Sarki ya goge mata hadda ya auro Balarabiya wannan yasa ta sake cin buri akan Hafsa seta auri Mijin daya doke nasu Khadija sannan Jafar shi ze wanke mata takaicin Sarki ya samo wata tsaleliyar Baturiya ko Indiya shida yake sananne a Duniya ma ai Matar da ze Aura se an ganta kawai yanzun hankalinta yafi karkata akan Hafsa tayi Aure se kuma ta mayar da hankali kan Autarta Sarah.
PAGE 2
Kiran sallar Magriba ne ya tasheta badan ta gaji da zazzagar da takeyi ba ba kuma ta gama ba zata cigaba. Ta bubbuga sallarta domin babu nutsuwa tattare da ita ko kaÉ—an tana idarwa ko salati bata iya tsayawa tayiwa Annabi ba taja waya ta shiga kiran Tirau.

"Yaushe zaki dawo? Akwai matsala" ta faÉ—a ba tareda ta tsaya sun gaisa ba.
"Jibi in Allah ya yarda, jirgi muka rasa yau shiyasa ma bamu taho ba se jibin muna Jidd ma, wlh ansha dake, da uwa kuɗinki matar nan ki biya mu tafi abi mu kikaƙi, tafiyar nan tayi daɗi yanda baki zato keni ban taɓa umarah me daɗin wannan ba yanzu ma muka dawo daga kanti munyo siyayya naga wasu riguna har zan kiraki idan kinaso a siyo miki na tuna da dai kyautace zaki karba koda yake ko kyautar ce babu lallai ki saka ma sedai ki Ajiye har su daddage su zama gari" Turai ta bata amsa cikin dariyar shaƙiyanci.

Binta taja tsaki tace
"Ai shikenan se kun dawo É—in, idan kuma naga bazan iya jira ba zanje gurin Hajiya Halima kawai muyi maganar ai tasan gidan Malamin nan naki ko?"

"Daɗina dake rashin saiti wani sa'ilin wlh Binta, ce miki nayi ina haɗen Malami da ƙawaye? To ai ko ke abinda yasa kikaga ina kai matsalarki gurin Malamina saboda nasan ba layinki bane dole tasa kike leƙawa kuma ba zakimun yankan baya ba. Ki kuskura ki kaiwa Halima matsalarki zaki gane baki da wayo wlh ke baki san da yawa neman hanyar ganin bayan mu akeyi bako? To idanbata kaiki inda za'ayi miki magani ba ta kaiki inda za'a ƙara dagula miki lissafi ai. Maganar Hafsatun ce ko yaya? Ba jiya kince mun yau yaron zezo ba? Be zo bane ko yaya? Amma abin da kamar wuya ace be zo ba dan kiranyen da Malam ya masa idan kinga be zo ba to a kabari yake dan wlh aikin da aka masa irinsa akeyiwa Riƙaƙƙun masu laifo kiji ance sun gudu daga Magarƙama to Aljanu ake turawa su ɗauko su, yauwa ya wancan zancen kuɗin komai ya tafi daidai ko? Dan ko ɗazu seda Malam ya mun tunin kasonsa nace masa ban dawo ba bamu zauna naji yanda ake ciki ba tukunna".

"Uhm kedai Turai Allah ya kaimu jibin ku dawo ma zanta, maganganun da yawa ni na rasa ma abinda zanyi wlh" Bintan ta faɗa kamar abar tausayi, Tirai ta sheƙe da dariya tace
"Ai Binta lamuranki kamar me bakin uwa, kiga abu rumi rumi an ƙullashi se yayi kamar yaci komai ya watse gaskiya ki tashi tsaye magauta sunga gadon barcinki lokacin daya kamata ki huta yazo, Yayanki sun kawo ƙarfi amma kuma kwanciyar hankali taƙi samuwa? Allah ya kaimu jibin to mu dawo zuwa gata seki shigo muji yanda ake ciki" daga nan sukayi sallama ta rafka tagumi tana tunani.

Masifar gidan da kullum gaba takeyi ba baya ba ta sakata fara abinda bata da ra'ayi akai kwata kwata wato Bin Malamai, tun Kissar tana ci a sannu ta dena tasiri saboda an kai gaɓar da wata kwarkwasa ko kisisina ta dena tasiri akan Audun, sabgar Kasuwancinsa kawai ya saka a gaba, shekarun baya lokacin da yake ta tiri tiri da ƙoƙarin ganin BECHI GROUP OF COMPANIES ya tsaya da ƙafarsa lokacinsu ma wahala yake masa, ga tafiye tafiye ko yana ƙasar ma se su kwana su wuni basu sakashi a ido ba a wannan lokacin ne kuma tayi Arziƙi domin itace akan komai, Ashana idan babu a gidan gurinta za'a nema cefane se abinda taga dama za'a kawo ta ringa tara kuɗi tana siyar Kadarori, Filaye, gidaje ta zuba yan haya da kuma sarƙoƙin gwal wanda ba sakawa take ba suna nan narke a drawer wani Design dinma wanda suka ƙirkireshi sun manta da Kalarsa.

Da su Zakariyya suka gama makaranta kuma dukda daman tun suna ciki take cusa su akan harkokin Audun kullum tana nuna masa ya kamata ace ya sakasu domin sune magadansa tun yanzu ya kamatu su san komai da yanda ake gudanar dashi ba wai se rana tsaka ne zasu kama abin ba, tun baya sakar musu har yazo dakansa ya yarda yana da buƙatar su horu akan sabgar kasuwancin nasa domin Bare ze iya ha'intarsa wata rana kamar yanda yake gani ga Abokanan kasuwancinsa da suka tashi tare da yawa sun durƙushe kuma idan aka bi kadi daga ƙarshe yakan kasance wasu daga cikin ma'aikatan gurin ne da suka fitar da sirrunsu ga abokanan Hamayya har hakan ya janyo durƙushewar gurin amma se tunanin sa be kawo masa cewar ba su kaɗaine yayansa ba ko kuma ba su kaɗai ne magadan nasa ba kamar yanda take faɗa, burinta ya cika suka samu gurin zama dukda da farko sun fara ne a ƙanana ma'aikata tafi tafi suna haɗa tuggu da manaƙisa irin wadda suka sha a Nono har suka saka aka tunɓuke asalin waɗanda suka da muƙamansu na yanzu suka maye gurbinsu.

Aminu da Alhaji Babannan Alƙali Yakubu ne ya cusa su a gurin da kansa, duk kuma bala'inta haka tayi ta haƙura wannan tasa ta matsa Yakubu ƙarami sukayi yanda sukayi har suka ciccibashi ya kai matsayin mataimakin Accountant General wato mataimakin Aminu a birinsu na ganin a sannu sun tunɓuke Aminun se Yakubun ya maye gurbinsa ta haka suka shirya wannan ƙulla ƙullar suka zabtare lissafi wanda daman aikinsu kenan yawan kuɗaɗen da suka zabtare ne yasaka har ta tashi aka gane aka kuma ɗora laifi kacokan akan Aminu dukda daman kuɗin babu su, lissafi ne kan lissafi tsoho da sabo suka harhaɗa ya bada wannan Adadi amma Asalin abinda suka kwasa Naira Biliyan daya ce kuma tana kwance cikin boyayyen Asusun Crypto wanda Naziru ya buɗe musu, Asusu ne irin wanda ba'a iya tracing koda an tura kuɗi ba za'a iya bibiyar su aga inda suka tafi ba can suke tura duk wata Albarkar office da suka samu kafin su zauna su ukun, ita Hajiyar, Zakariyya da Nazirun ayi kasafi kowa a tura masa nasa dan hatta da su ɗin ba wai ta yarda data bar kuɗinta a hannunsu bane, wani sa'ilin ma Ruwan Cash take karɓowa ta zube a ɗaki abinta tayi ta shafasu tana jin daɗi.

To wani sa'ilin kuma idan Al'amura sun cukurkuɗe mata ta rasa mafita se Turai tace suje gurin Malam, tun akan Muƙamin Yakubun da Audu yaso yayi mata buyagi yaƙi yarda Turai tace ta kawo kuɗi, har yarjejeniya sukayi akan odan aiki beci ba zata maido mata kuɗinta se gashi tana zaune Audun ya kira Yakubun wannan tasa ta fara amanna da sabgar dukda ko buƙatar ta taso ba ita take zuwa ba, Turai take bawa kuɗi aje a mata abinda ya dace tunda sabgarta ce, ta daɗe dayin amannan da Bin Malamai harda Bokaye zuwa gurinsu takeyi shiyasa har kawo yanzu Ta kanainaye Ali, shekaru an tasamma Hamsin amma se yanda tayi dashi ƙarin Aure da yake da burin yi tunda jajayen sahu ta hana haka yake ta gurgura rayuwa ga kuɗi ya tara mata ita da yayanta suna wadaƙa Yau tana waccen ƙasar gobe tana wannan kayan Alatu kuwa kullum cikin siya takeyi dan ita ba irin Binta bace tana cin kuɗinta Binta kuwa har yau har gobe abin naira goma sabo idan ka ganta dashi to Yaranta suka siya mata shi ko ma ace Jafar dan shine duk abinda ya gani na kwalliyar jiki a gurin hamshaƙan mata ze siyawa Hajiyar abin takaici kuma ba zata saka ba musamman idan taji kuɗin kayan, suturu da sauran kayan Ado da kuɗi kam ta tarasu babu Adadi har tsokanarta Faisal yake yana cewa
"Hajiya idan kika mutu zamu ja kaya da yawa dan wlh inaga kason abinda zamu samu na gadonki se yafi na Alhaji" duk ranar da yayi mata wannan maganar kuwa Ashar da tsinuwa babu wadda baya sha tace sedai ubansa ya mutu tamkar ita É—in zata zauna gadin duniya ne.

Bayan sun gama waya da Turai ta miƙe tayi sallar Ishar da aka idar tuni, tana zaune a gurin takaicin duniya ya isheta, jibgin kayan snacks da Kaji da akayiwa Abba Tee take tunawa ya zatayi dasu harda irin shinkafar Larabawan nan da ake dafawa da naman Rago yayi ligib aka masa yanzu duk sun tashi a banza ta saka ran ze cakewa Hafsatu kuɗin da zasu maida wanda aka kashe harda riba se gashi wancan Dan is** yaron ya janyo mata Asara. Tsaki ta rafka yanda kasan wata riƙaƙƙiyar tsaka, ita kaɗai taci gaba da bala'i daga zaunen da take tana dannanwa Yakubu Ashar.

Faisal ya shiga kamar an jefoshi, ya kalli Hajiyar ya kalli cikin falon ganin ita kaÉ—aice zaune kuma tana ta faman sababi yasa ya matsa gabanta yana cewa
"Hajjaju, kinƙi yarda Jayy ya kaiki Asibitin da yace, lamarin nan naki fa kullum ƙara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba"

"Dan ubanka Faisal kaima mahaukaciyar kake so kace mun?" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, Faisal yayi wata dariyar shaƙiyanci yaja ja da baya dan ya san tana iya kai masa duka yace
"Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi kaɗai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a ƙasa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa

"Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga É—aki kafin nayi maka baki"

"Allah huci zuciyarki ni ban faɗa dan kiyi kuka ba, ɗaki kuma sedai kiyi haƙuri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama faɗa mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace. Abincin daya gani a gyare ya ɗebi iyakar abinda ze isheshi ya shaƙo plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da faɗe faɗen maganganu marasa daɗi akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal ɗin daya ɗora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba. Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya ƙure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce ɗaki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje ɗakinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa.

Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta baƙin cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari ƙal.

"Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu haɗin kai idan ya hau kujerar? Jiyan nan fa kar kaga tijarar daya mun a gidan nan ya zubar mun da mutunchi a gaban maƙiya" nan ta bashi labarin yanda sukayi da Yakubu jiya, Zakariyya ya jijjiga kai yace
"Haba kema Hajiya wani sa'ilin se ki ringa abunda be kamata ba, yanzu saboda Allah wannan tarbiyyace? Ko yar wani kikaga zatayi abinda be kamata ba ai hanawa zakiyi amma kike ingiza yarki ta aikata wannan ba daidai bane sam wlh kuma koni da ace na tarar da yaron sena ballashi wlh itaka kuma se naci uwarta dama ana yawan kawo mun zancen bataji na zata hassadace kawai akeyi mata ashe da gaskene to dan ubanta kawai zamu nemo koma waye mu aurar da ita mu huta kafin ta janyo mana abin kunya a gari".

Baki sake Binta ta ringa kallonsa har ya kai aya kamar zatace wani abu kuma seta haÉ—iye ta bar maganar tace
"Ai shikenan, zancen ya wuce, yanzu dai a aikamun da kasona a akawun kai a kawomun kash kawai na ringa ganinsu inajin É—uminsu kusa dani"

"Miliyan dari ukun za'a kawo miki cash Hajiya?" Zakariyya faÉ—a cikin mamaki, ta harareshi tace
"Bangane dari uku ba? Wai nawane kuɗinma da kake kiran wata dari uku za'a bani?" Cikin ɗaga murya tayi maganar yayi saurin yi mata alama da tayi shiru saboda motsin taɓa ƙofa dayaji, Yakubu Bechine ya shiga fuskar nan a turɓune kamar ta Audu, Binta ta lafta tsaki tace

"Dallah rabu dani yaji mana, nama zata wani barene ze shigo"
"Barka da safiya Hajiya, Zakariyya Sannu" ya gaishe su daga tsayen da yake. Hajiyar ta harareshi bata amsa ba dan a cike dashi akan abinda yayi jiya Alhaji Zakariyya kuwa wani banbarakwai yaji daya kirashi Zakariyya gatsal kamar wani sa'ansa, yanzun shigowarsa ya haɗu da Ahmad ze fita shi kuma, seda ya kusa kaiwa ƙasa kafin ya gaishe shi kuma da Yaya ya kirashi ya amsa masa a wani wulaƙance yana shan ƙamshi kamar wanda yazo masa maula kuma yaron ko a jikinsa ya wuce abinsa har yana masa fatan fitowa lafiya daga gidan se yanzu Yakubu ƙaninsa ciki ɗaya ze masa wannan gaisuwar se kace wasu Abokanai? Koda yake ai Yakubun ma ya mutuntashi tunda Faisal da ido kawai ya kalleshi sanda ya shigo ita kanta Hajiyar be tsammaci ya gaisheta ba ya fita dan da ganinsa lokacin ya tashi ma daga barci.

"Tambayarka nake nawane kuÉ—in?" ta sake nanata masa seya sauke ajiyar zuciya yace
"To nidai abinda yace mun kenan kuma baze yuwu a saka kuÉ—in lokaci É—aya ba saboda kinga yanzu EFCC ta tsaurara da binciken shige da ficen kuÉ—aÉ—e a Account É—in mutane kar mu jefa kanmu a matsala gara a ringa sakawa da goma da biyar har ayi balancing"

"Zezo ya sameni kuwa, a gidan ubanwa kasafin ya zama dari uku? Nida nake lissafin kusan dari bakwai shine zaku cemun wata dari uku? Nifa shiyasa naƙi jinin haɗa sabgar kuɗi da Naziru dan macuci ne, tsayin lokaci kullum yace ana juya kuɗin za'a turo ina nan galahanga kenan kuna can kuna sharafinku se yanzu zaku ɗan yafutamun abinda kuka ga dama shiyasa naji ance ka siyawa Matarka motar Miliyan Ashirin shi kuma yana rabon kujerun Umarah ko ni dana hada pulan ɗin ban san komai ba kun ninkeni a baibai" murya a sama take maganar babu ɗar ko shakkar wani ya jita Zakariyya kuwa daga inda yake zaune har zufa ta fara keto masa ta tsoron kar wannan fallasar ta Hajiya ta janyo musu tonon Asiri tun ba'aje ko ina ba, muakutawa yayi cikin rage sauti yace mata

"Yanzu dai kiyi haƙuri na gaya miki yace ze zo kuyi magana tafiyar gaggawa yayi zuwa Legos amma Litinin ze dawo ba jimawa zeyi acan ba"

"Ai ko bezo ba ni zanje har gida na sameshi, yo hauka akeyi mu damfari ubanku sannan ku zagayo nima ku cuceni" ta sake sakin wata maganar

"Dan Allah Hajiya kiyi ƙasa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faɗa,
Yakubu daya haɗo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a manaƙisar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an ɗebi kuɗin ba ya zata lissafi kawai suka ƙara masa. Kwankwaɗe shayinsa yayi ya taso yana cewa

"A fitar dani ko wallahi na fasa ƙwai"
"Dan uwarka ka yanka Kaza ƙarewar fasa ƙwai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haɗe seka gane baka da wayo wlh"

Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace
"Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ƙishin ƙishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa".

Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ƙulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruɗe se kokawa take da waya

"Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta miƙa masa wayarta tana cewa
"Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ƙullata".

"Aikuwa ba zaki same shi a waya yanzu ba dan suna da wasa ƙarfe sha daya, lah lokaci yayima an fara ina tsaye bari kawai na kalla a nan" Yakubun ya bata amsa bayan ya dire mata wayarta a gabanta ya matsa gaban Cinema Tv bango guda wadda Jafar ya sakawa Hajiyar saboda tace wai bata ganinsa dakyau a tsohuwar tata.

Tv na daidaita kuwa kamar me daukar hoton wasan Kwallon da ake yasani ya haskowa Hajiya Binta fuskar JAFAR BECHI tarr kamar ze fito ta cikin gilashin Tv. Zabgegen saurayi irin ƙirar Yayan AUDU BECHI, dogone sosai jikinsa nada ɗan kauri dukda ba za'a sakashi a layin masu ƙiba ba amma a murɗe yake koda gani ba se an gaya maka yana motsa jiki dakyau ba. Fatarsa nada haske sosai dukda ba fari bane sedai hutu da zaman Turai ya bashi wata kala me kyau kuma me wuyar samu a cikin mutane, ba wani shahararren kyan fuska yake dashi ba Aa daidai Misali ne irin na Maza gayu da yanayin muhalli da wankan da yakeyi ne yasa har Mata suke iya sakashi a jerin Maza masu kyau wanda ake gwarama kai akansu , ga duk wanda yasan Hajiya Binta Musamman a zamanin ƙuruciya kai tsaye ze tabbatar da JAFAR din jininta ne dan zubin fuskarsu daya idan ka cire Idanun Gidan BECHI daya samu se labbansa wanda Binta tace irin na Alhajinsune, duk tana jika dai da itan yake kama kenan.

Jafar ɗin na tsaye a coner ya take kwallo da ƙafarsa ta hagu idanunsa kuma na kan saitin inda yake so ya bugata. JC ce a jikinsa Jaa me ratsin fari ta club din Arsenal wadda ke dauke da Number 7, a bayan rigar an Rubuta JAAY, wani murmushi yake saki daidai sanda Referee ya busa whistle gaba ɗaya yan ƙwallo suka shiga tara tara kowa na jiran ya jefo ta inda yake ya kama, baya yaja kaɗan ya buga ball ɗin daga inda yake ta ringa kurɗaɗawa ta tsakakanin ƙafafuwan yan wasan aka rasa wanda ze taketa har seda ta dangana da cikin raga shikansa Goalkeeper kamar an riƙe masa hannu da ƙafafuwa ya kasa tareta har ta shige, ihun yan kallo na cikin Tv tarefa na ZAKARIYYA BECHI da YAKUBU BECHI ya cika falon, Hajiyavkanta da take cikin ruɗu fuska a ɗaure bata san sanda ta saki dariya ba tana cewa

"Ai na sani, sedai idan ba Jafaru na ba be taba kama kwallo ya saka ba tareda ya kaita raga ba, kai Allah dai yacigaba da tuntuɗo maka Albarka ɗan nan Allah ya cigaba da tsole idon maƙiya" Ɗa guda tilo kenan cikin rayayyu tara da take dasu wanda take ɗaga hannu ta roƙar masa nasara a gurin Allah ta kumayi masa addu'ar fatan nasara tareda saka Albarka, yana kuma ganin hasken hakan domin Uwa duk yanda take Uwa ce kuma tasirin harshenta nada girma.

Jafar ɗin me shekaru Ashirin da bakwai a duniya yanzu ya kai matsayi mai girma a duniyar kwallon ƙafa. Matashin Dan wasa ne da ake ji dashi a faɗin duniya wanda kowanne Club suke zawarcinsa, idan ka cire Messi da Ronaldo JAAY shi yake take musu baya a duniyar kwallon ƙafa a yanzun. Ubangiji ya hore masa baiwar sarrafa kwallo, duk rintsi duk tsanani idan JAAY ya karbi kwallo seya kaita ga inda ya hara kafin ya haƙura, juriyarsa da Nacinsa da kuma ƙoƙarinsa na haɗakan Yan Team ɗinsa Abokanan taka ledars shiyake ƙara masa ƙima a idon duniya domin kowa ya shaida wannan jajircewar tasa ce ƙashin bayan cigaba da Nasarorin da duk wani club dayake taka leda a ciki yake samu.

Cikin farin ciki suka haÉ—u suna kallon Wasan, harda Hafsatu da Sarah dake bacci ihun su Yakubun ya taso su ko karyawa basuyi ba suka haÉ—u aka cigana da kallon.

BECHI FARM
Kamar yanda Alhaji Audu yace Ahmad ya sameshi a gidan gona haka ce ta kasance, Alhajin ya riga Ahmad isa saboda baƙi da yayi ze gana dasu acan wanda shine musabbabin daya saka yace Ahmad ya tarar dashi a can ɗin, sanda ya isa Alhajin na tsakiyar tattaunawa dan haka yayiwa kansa masauki a daya daga cikin falukan da suke gidan gonar idan kaga tsaruwarsu zaka ɗauka a cikin gida kake ba wai gidan gona ba. Yana zaune cikin zullumi rungume da takaddun tsarin abinda yake so ya gudanar, zuciyarsa fal wasi wasin yarda ko akasin haka daga gurin Alhaji, idan Alhajin be yarda da buƙatarsa ba a ina ze samu gurin da ze aiwatar da aikinsa tamkar wanda yake nema a gurin Alhajin?

Gajiya yayi da zama da tunani ya tashi ya fita yana zagaya gidan gonar, sashen tsuntsaye ya tafi, acan ya shantake yana kallon Halittun ubangiji, tsuntsaye gasu nan kala kalanda Alhajin yake kiwo danginsu Dawisu, Aku, Kanari da sauran tsuntsaye masu tashi kala kala a keji nan su ga kuma tattabaru nan irin ƙasashe daban daban Jikinsu kaɗai abin sha'awa. Kukan tsuntsayen da surutun masu kula da gurin ne ya ɗebe masa kewa har besan lokacin daya ɗauka ba seda wani daga cikin yaran Alhajin yayi kiransa.

Masaukin daya tarar da Alhajin yafi kowanne haɗuwa a gidan gonar, yana zaune kan Luntsumemiyar Rolar chair two sitter irin zaman da yayi da suturar da take jikinsa kamar wani basarake seya cike kujerar gaba daya kwarjininsa ya cika falon. Tamkar beran da ruwa yayiwa duka haka Ahmad ya raɓe daga gefen kujera yana gaida Alhaji.

"Ka tashi ka zauna a sama, meye haka kakeyi kamar wanda yazo Maula?" Alhajin ya faɗa cikin muryarsa me razana Maza. Ahmad ya sake yin ƙasa dakai cikin tsantsar ladabi yace
"Aa Alhaji nan ma yayi, be kamata kana zaune akan kujera nima na zauna ba"

"Umarni na baka ba shawara ba" ya sake faÉ—a a dake, wani sashi na zuciyarsa kuma yana tsinkewa, Ladabin Ahmad daban ne kaf a cikin Yayansa 28 yayi zarra wanda yake take masa baya kuma Jafar ne wanda zama da Ahmad É—in ya washsheshi shima ya rabautu da kyawawan É—abi'u.

Kamar wanda ya zauna akan wuta haka Ahmad ya ɗosana mazaunansa akan kujerar jininsa yana sake tsinkewa, falon yayi shiru, motsin ƙofa da aka buɗe ya saka Ahmad ɗin zabura kamar mara gaskiya ganin Kuku ne ya shigo yana tura abinda ake ɗoro abinci akai yasa ya maida kansa ya sauke Ajiyar zuciya a hankali. A nan tsakiyar falon kan Ledar da Kukun ya shimfiɗa ya jera abincin daya shigo dasu. Seda ya gama ajiye komai daya kamata kafin ya juya ya fita bayan ya sanarwa da Alhaji komai ya kammala.

Alhajin ya sauka ya zauna a ƙasan ya tokare hannunsa ɗaya da Tum Tum ya shiga serving kansa abincin Ahmad yayi sauri ya sauka ya karɓa. Ganin duk ire iren abincin da Alhajin yake ci yanzun ne dangin Alkama dasu Acca se kayan ganye sakamakon Sugar daya gamu dashi ya saka masa komai madaidaici yanda ze iya ci kafin ya koma ze zauna Kukun ya sake shigowa da madaidaicin Tray ya ajiye a gaban Ahmad ɗin ya sake fita.

"Ga irin naku nan" Alhaji dake cin Funkaso da akayi da garin Alkama da wata miyar tantaƙwashi ga shayin Goruba yana kurɓa ya faɗa.
Ya buɗe baki da niyyar yace ya ƙoshi amma kallon da Alhajin yayi masa ya saka ya buɗe abincin. Soyayyar jollof din Basmati ce se kaza guda gasashshiya da kuma coslow. Favorite ɗin Ahmad kenan shinkafa balle ga Kaza mutuniyarsa a gefe daman be karya ba ya fito dan haka tuni ya manta da surukutarsa da Alhajin ya hau zuba loka. Seda suka ƙoshi ƙat, Kuku ya sake zuwa ya kwashe komai ya dire musu kayan marmari da tataccen ruwan Inibi me sanyi, Alhaji nata satar kallon Ahmad kamar yanda shima yake satar kallon Alhajin.

Dukda wata magana bata shiga tsakaninsu ba har suka gama cin abincin amma duk su biyun yanayin ya musu daɗi domin wannan shine karo na farko da suka taɓa haɗa muhallin cin abinci tun tasowar Ahmad ɗin sedai su hangeshi sunaci da Hajiya tareda Yayanta, sanda suna yara idan ta kira Jafar yazo suci abinci suka tafi tareda Ahmad ɗin haka zatayi ta zaginsa ta koreshi shi kuma Jafar ya saka kuka yabi bayansa wata rana haka da duka zata tisa Jafar ɗin seya zauna dukda bazeci abincin ba domin basa raba kwano da Ahmad da suka fara girma kuma da lokacin cin abincin wanda sukafiyi da dare ya kusa ze ja Ahmad su bar gidan ma doke ta haƙura ta barshi kuma duk abinda akeyi Alhajin be taɓa magana akai ba, ashe haka cin abinci tareda Mahaifi yake da daɗi? Ya raya a ransa.

"Ina sauraronka, menene abinda yake tafe da kai?" Alhajin ya soko ainin abinda ya tarasu. Ahmad ya zaro takaddun daya zo dasu. Filla filla yayi musu a gaban Alhajin zane ne a jiki da guntayen rubutu yayi ta maza ya shiga yi masa bayanin abinda yake shirinyi. Tsarin taswira ne na katafaren Shopping Mall dayake da ƙudirin buɗewa, burinsa ne tun yana yaro provision store yake bashi sha'awa. Sanda suna Goron Dutse kafin su taso har Tireda ya kafa a ƙofar gidansu yake siyar da alawowi harda su Maggi da Omo, sau Biyi Audu yana sakawa a jijjigeta amma idan aka cire Yau in Allah ya yarda kwana biyu yayi yawa zega sabuwa a karo na uku harya niyyata ze cire ranar a kan Idon Ahmad ɗin yace masa

"Dan Allah Alhaji karka ciremun, idan ma kuÉ—in haya kake so na ringa biya zan baka idan na tara kuÉ—i jarina yayi yawa, so nakeyi idan na girma na gina babban Shop da za'a ringa siyar da komai da komai" wannan maganar ta sanyaya masa jiki tasa ya fasa abinda ya niyyata wanda a sannan ma Binta ce tace masa Aisha ta saka Ahmad ya buÉ—e tiredar saboda aga gazawarsa ace ya kasa daukar É—awainiyarsu, maganganun Yaron kuma se suka tuna masa da sanda ya daura É—ambar cika nasa burin sanda yake yaro yanzu da Ahmad É—in yake nuna masa abinda yake so yayi se abinda ya faru kusan shekara Ashirin kenan ya dawo masa.

A nutse ya ringa kallon komai yana kuma sauraron bayaninsa, ya fasalta masa guri da girman filin dayake da buƙata danyin ginin.

"Shin kana da kuÉ—in da zaka gabatar da duk wannan aikin daka É—auko?" Alhajin ya tambayeshi, Ahmad ya haÉ—e yawu kafin yace

"Da akwai tanadin da nakeyi dukda nasan baze isheni nayi koda rabin abinda nake da buri ba a yanzu, amma a hankali ina sha Allah ina saka ran zan samu"

"Ok, to me kake so nayi maka kenan?" Alhajin ya jefa masa tambayar me kama da rainin wayo, jikinsa yayi sanyi dan be hango alamar samun nasara ba amma ya daure yace

"Wannan filin na cikin gari inda ake ajiye manyan Motoci da nake so idan da Hali a bani Aro tunda an dena amfani dashi".

"Aro?" Alhajin ya tambayeshi kamar da mamaki, kansa na ƙasa ya ɗaga masa shi da tabbatarwa seya gyara zama yace
"Se kum me?"
Muryarsa na rawa kamar a tsorace ya sake cewa
"Sannan idan da hali a gina mun, se muyi lissafi a yankemun abinda zan ringa biya duk shekara har na mallakeshi ya zama nawa".

Shiru ya ratsa tsakaninsu fin tsahon minti goma sha biyar har Ahmad ya yanke ƙauna daga samun Amsa me daɗi Alhajin kuwa kallonsa yakeyi yana nanata kalmar Aro da yace ya bashi na guri sannan ya yanka masa abinda ze ringa biya kuɗin hayar daya ambata tun yana yaro kenan ze ringa biyansa, kenan a matsayinsa na Mahaifinsa baze iya roƙarsa ya mallaka masa gurin kyauta ba ko kuma ya gina masa irin yanda sauran Yaransa Yayan Binta sukeyi ko su ɗauki abinsa ma suyi amfani dashi ba tareda saninsa ba?
"Idan ya tambayekan zaka yi masa hakan ne?" Zuciyarsa ta tambayeshi se ya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaja numfashi yace

"Shikenan, ina fatan kana da Lawyer? Ka haÉ—a duk wata takadda data kamata ka kaiwa Barr, kuyi magana dashi daga nan ka samu Mr Lee ku tsara yanda construction É—in ze kasance da abinda za'a kashe daga nan se a tattara lissafin, darajar filin dai shekara goma baya an taya Miliyan dari ban siyar ba, nasan yanzu ya ninka haka sau goma ko fiye da haka tunda kasan inda yake kaima kwaÉ—ayin kyawun location É—in ne yaja hankalinka dan haka zan bar maka shi a Dari biyu, ka gayawa Barr, sannan ka fara haÉ—o kuÉ—in filin tukunna koda rabine sannan zan yarda na fara gina maka".

Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ahmad, ya shiga zuba masa godiya, seda ya gama kuma kwakwalwarsa ta shiga aiki na gaske, Miliyan dari biyu da Alhaji ya ambata kuɗin fili seya biya sannan za'a fara gini a ina ze nemota? Tanadinsa ƙarƙaf idan ya haɗa baze fidda kuɗin filin ba, amma ya yarda a ransa Allah zeyi masa ze kawo masa hanyar da ze samu abinda ze cika burinsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.