Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 11
PAGE 10
Da wata irin kasala ta farka da Asuba sakamakon mafarkin data kwana tana yi. Ta kalli Badar dake masifar tun
É—azu take tashita amma ta mata banza.
"Haba Badar ki barta mana" Maman Minal ta faÉ—a kafin taci gaba da cewa
"Kin san dai Afeeya tana riga kowa tashi ko bata sallah se ta farka ta tashemu tunda kikaga yau ta makara se ki mata uzuri".
Badar tayi tsaki tace
"Idonta biyu fa tsabar iskancine idan ba zatayi sallar ba seta faɗa ai a barta" fuu taci gaba da juye ruwan zafin da take a bokiti. A kasalance Afeeyah ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa
"Zanyi mana", gabanta ya faɗi saboda yanda tajini a jiƙe, mafarkin da tayi ya shiga dawomata seta kalli Badar data zuba mata ido itama, kamar zatayi kuka amma ta kasa cewa komai.
"Kar dai fa Aljanin darene yazo mata? Mutumin data haɗu dashi jiya kwana tayi tana mafarki dashi kuma ta tashi cikin wannan yanayin karfa da gaske Aljanine? kai Innalillahi taga ta kanta ita Afeeya ina ta kwaso Aljanu ta shiga uku" ta raya a zuciyata kafin ta sake yunƙurawa tana tattare rigarta a ranta ta Ƙudurce tana yin sallah zata kira Ummanta ta faɗa mata tun wuri, bata taɓa irin mafarkin ba se yau gara ta faɗa mata koma menene a tareshi tun kafin ya aureta ta shiga uku.
Seda na sauka daga gadon ta kalli shimfiɗar stain ɗin jini da ta gani ya sakata sakin ƙaffaffar ajiyar zuciya saboda ganin wani abu daban ba yanda tayi tunani ba. Towel ta ɗauka ta wuce wanka da Ruwan Badar tana jin tana zaginta amma ban tanka ba. Seda ta kintsa kainta kafin ta cire bedsheet din ta kama inda ya baci ta wanke a baza daman yau zasu haɗa wanki, takwas saura suka fita class bayan sun karya har sannan kuma jikinta a sanyaye yake idan na tuna mafarkin jiyan se taji Zuciyarta ta buga kuma wani abun mamaki sukayi waya da Umma da Baffa amma ta kasa faɗa mata kamar yanda tayi niyya, abin ne da nauyi kawai Anty Sauda zata kira to ta faɗa mata.
A Ajin ma bata da wani kuzari da kuzari Malamin da kansa seda ya tambayeta lafiya take tace kanta ne yake ciwo. Malamin na fita Class Rep É—insu ya tsallaka sit É—in da suke, ta kwantar da kanta a kan Desk suka gaisa da Badar da Yusuf ta harari Sahid dan basa shiri kafin ya kalleta yace
"Whitey (haka yan class É—in suke kiranta ko Afee whitey saboda haskenta) I have been looking for you since yesterday"
Ba tare data É—ago ba tace masa
"Ya akayi?" Dan Sahid akwai dan banzan surutu shima da gulmar tsiya
"Wani mutumi ne, I mean one guy asked me about you yesterday and i told him every detail i know har layinki na bashi, Afee you don do good catch i swear, from his looks gayen nan is Rich, his face looks familiar to me but i couldn't figure out inda na sanshi" Sahid ya fada. Badar ta harareshi tace
"Haka ka iya kai dai ka zama kamar wani kawali kullum cikin haÉ—a yammata da Samari", hausar bata bawai yana jinta dakyau bane Banufe ne dan haka ya kalli Yusuf da suke tare yace
"What is Kalali? Because i know Badariyya, when ever she speak big big Hausa word she is up to no good" dukda yanda nake jina amma seda nayi dariyar maganarsa Yusuf yace
"Tana nufin you are a good match maker"
"Ehen" Sahid din ya sake fada da alamar be yadda da abinda ya fada ba amma se ya maida hankali kaina yana cewa
"He gave 100$"
"Kaji daɗi" Afeeya ta faɗa tana miƙewa saboda cikinta daya hautsina, tsallakesu tayi ta fita da sauri can gurin fanfo tana zuwa ta shiga sheƙa Amai masu wucewa suna binta da sannu. Kamar ta kunno ciwo tana gama aman marata ta riƙe ita da bata Mp se gashi ta gagara tashi tsaye daga gurin seda Badar tazo ta ɗagata.
"Muje Hostel kawai daman baki da lafiya amma kika fito?" ta faɗa suna tafiya a hankali. Yusuf ne ya kaisu har gaban Amina a motarsa kafin suje ta galabaita juye juye kawai take a cikin motar na azaba dakyar ta iya fita ai kuwa nan gurin Security ta kwanta tana kuka shaɓe shaɓe kamar wadda zata haihu, abinda bata sababa, bata taɓa experiencing ciwon Mara ba se lokacin shiyasa take jinsa wani sabon abu kamar zata maɗe.
aka daka saboda ciwo.
"Sannu Afeeya me yake damunta?" Anty Amina daya daga cikin matan security da mmsuke mutunchi dasu ta tambayi Badar,
"Inaga zazzaɓi ne" Badar ta bata amsa Afeeya ta nuna musu mararta da hannu, cikin tausayawa Anty Aminan tace
"Wayyo sannu, daure ku ƙara ciki se kisha ruwan zafi da pain relief, Allah ya kawo Afuwa"
"Kuje kuyi aure yara kun zauna kuna fama da ciwo" Ɗaya matar ta ɓaro maganar, Badar ta Anty Amina suka kamata ganin an fara taruwa akana kallonta wasu na cewa Aljanu takeyi. A common room suka ajiyeta ta kasa zama kan kujera se a ƙasa ta kwanta tana cigaba da murƙususu, ashe haka Matan suke ji amma ta ringa cewa Bafar raguwa idan tana ciwon Mara yau gashi Allah ya kamata itama kamar fa an hura mata wuta takeji a gurin wannan abu da akwai Azaba.
Ta fi awa a gurin kafin ciwon ya lafa mata lokacin har gashin kanta seda ya hargitse kamar wadda tayi naƙuda. A duddƙe ta ringa tafiya har sukaje ɗaki, duk wanda Badar ta gayawa abinda yake damunta se yayi dariya kafin ya mata sannu dan haka take musu. Sururat ta haɗa mata ruwa me zafi takai mun banɗaki kafin ta fito Badar ta haɗa mata shayi me kauri ta gyara mata gado, kamar wata sarauniya haka suke lelenta suna mata iskanci kuma, tasha Paracetamol ta kwanta bacci ya kwasheta wata Jalalar Mutumin ya sake diro mata a mafarki amma ba irin na daren jiya ba.
Na daÉ—e sosai tana bacci har gurin qarfe biyun rana kafin ta farka ta ji daÉ—in jikinta se abinda ba'a rasa ba. Kamar me ciki ta seda ta sakeyin Amai kafin tayi tsarki da ruwa me dumi sosai ta canza pad ta koma É—aki tana tafiya salaf salaf kamar waddata fito daga Labour room.
"Abin nema ya samu" Ummi ta faÉ—a ta harareta kafin ta zauna kan Gadon Maman Minal tana cewa
"Tun jiya Ummi daga zuwa Lecture baki kwana a nan ba?"
"Bayan na fito daga lectures ne na hadu da Surayya shine kawai na bita City tunda yau banida lecture, yanzu ma motar bati na samu shiyasa na taho da wuri" Ummin ta bata amsa kan tabi Cousin É—inta city gidan Antynta.
Afeeya ta kalleta badan ta yarda Zaria City tasan baze wuce yawonta na banza ta tafi ba. Ummi bataji ko kadan, ta santa tare sue a English da zasu shiga Level 3 É—in nan ta bari ta koma Library science saboda rashin mayar da hankali ana nema a koreta, party da clubbing a Zaria babu inda bata sani ba yanzun a hakan ma ta rage ne zama dasu suna matseta dole ta rage wasu abubuwan da wuya ta fita ta kwana a waje duk yawonta zata dawo Hostel.
"Wlh gidan su Surayya naje idan ma baki yarda na kirata yanzu kiji da kunnenki" ta katsewa Afeeya shirun da tayi dason wanke kanta. Wayar Afeeya ta fara ringing akan gado ta É—akkota tana cewa
"To me kikaji nace Ummi? Duk ma abinda mutum yayi ai dan kansa me kyau ko mara kyau zaka tarar da sakamakonka me sonka ne yake damuwa da abinda kakeyi har yake so ka hau hanyar daidai". Ahmad ne yake kiran kafin ta answer ta ktase se lokacin taga missed call daya mata kafin wannan kiran.
Wani kiran ya sake shigowa, ta É—aga yana narke murya dan bata so wayar tayi nisa.
"Fatima kin tashi? Ya jikin?" Ya faÉ—a cikin kulawa, ta kwanta tana cewa
"Da sauƙi, ka kira aka ce ina bacci ne?"
"No, dana kira baki É—aga ba i called Badar ita ta gaya mun bakya jin dadi ta barki kina bacci i hope you are feeling better now? Kodai zakuje hospital ne kira Ilyas ya kaiku?" Ya sake tambayata a tausashe, a maimakon taji daÉ—in kulawar tasa ma haushi yake bata ya fiya sanyi da yawa ta muskuta tana cewa
"Nafa samu sauƙi kuma nasha magani, Ilyas na zata ya bar Zaria ai"
"No yana nan be samu sun canza masa din ba so kuma ma saura two months ya gama shiyasa ya haƙura" (cousin ɗinsa ne yaron sister Momy da yake Internship a Shika Asibiti).
"Ayya Allah ya bada sa'a, ya kake? Abujan? Yaushe zaka dawo?"
"Are you missing me?" Ya faÉ—a yana sakin murmushi najin daÉ—i yau Fatima ta tambayeshi wani abu daya shafeshi, kunya ta kamata tayi murmushin ita ma amma bata ce komai ba yaci gaba da cewa
"Se Thursday In sha Allah, kina zumuÉ—in ki ganni ne?"
"Uhm" kawai tace, cikin tsokana yace mata
"Da gobe fa zan taho, sena haɗu da wata yar farar Yarinya me irin zubinki, ita take so ta riƙeni na kasa tahowa".
Ba wani son sa take ba ba amma se da zuciyarta ta sosu da abinda ya faɗa kishi ya taso mata, a ƙufule tace
"Kace kayi budurwa yar Abuja yar gidan masu kuɗi" yanda tayi maganar ita kantaseda ta idar ta fahimci muryar da tayi amfani da ita tayi kauri da yawa ta kuma bayyana kishin daya taso mata ƙarara. Dariya sosai Ahmad yayi tayi shiru kunya da takaicin kanta suka rufeta, seda yayi me isarsa kafin yace
"Ashe dai Fatima na kishina haka? Gaskiya naji daÉ—i".
Bata sake ce masa komai ba ya gama surutansa tana ji ganin ta ƙi bashi amsa yasa ya canza akalar maganar da cewa
"Haka kawai Tuwo nake sha'awar ci da Miyar Kuka, kamar na tafi Kano yau ma nake ji"
"Ikon Allah Tuwo kuma ka rasa wacce miya seta kuka?" Ta faɗa cikin mamaki dan zata iya cewa a matasa dai shine mutum na farko data taɓajin yana son Miyar kuka, Yah Malam dinsu cewa yayi ganyen bishiyar Aljanu ne tsaɓar hatsabibanci irin na mata suka mayar dashi abinci shiyasa duk me yawan cinsa kwakwalwarsa toshewa take saboda sharri.
"Kuka dai da kika sani, ni ai idan kina so ki burgeni to ki bani abincin gargajiya amma fa with a touch of modernity bawai kuma ayi abu babu sha'awa ba, irinsu dambu, Akubus, Fate, ÆŠanwake babu wanda bana ci kuma a kowanne lokaci zan iya ci be it safe, rana dare duk zan iya cinsu musamman idan an shiryashi ya dace da lokacin".
Kai ta É—aga kamar yana ganinta tace
"Na gane"
"Yawwa idan ma baki iya ba se ki koya dan ni babu ruwana da wasu continental dishes da kika ganni shiyasa ma kikaga nake daidaitan se Umma ta sauke abincin dare nake zuwa gidanku dan ba Ƙaramin daɗin girkinta nake ji ba kuma na ci na Anty Sauda ma naji yayi kalar na Umma Allah yasa kema haka kika iya girki"
"Ina koya" ta bashi amsa a taƙaice tana janye wayar daga kunnenta, minti goma sha daya suna magana zan iya cewa basu taɓa kaiwa haka suna waya ba idan ma sunyi to befi sau a ƙirga ba. Kamar ya shiga ranta taji shima yana cewa
"This is our longest phone call so far, bari na shigar dashi a Diary yau É—in ta shiga tarihi".
Ta yatsina fuska kamar yana ganinta kafin tayi magana cikin sauri taji yace
"Ki huta Fatima, i will call you later Jafar yana kiran É—aya wayana".
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya taso mata dajin sunan wanda ya ambata. Ta tsani Jafar ɗin nan tsana me tsanani da bata san iyakarta ba. Bata ko amsa masa ba ta kashe wayar tqna jan mugun tsaki. Maman Minal da bataji shigowarta ba ta ce
"Lafiya kike tsaki haka?"
"Babu komai" ta bata amsa tana miƙewa saboda yunwa data faraji. Ta zuba taliyar data gani a tukunya ta hau ci ranta duk a dagule, ta kusan cinyewa Badar ta shigo da alama ta kwaso yunwa dan hannu kawai ta wanke ta dirarwa abincin da Afeeyan take ci seta tsame hannu ta bar mata dan daman ta ƙoshi gudun kar su mata masifar da suka saba idan ta rage abinci yasa take turawa daƙyar.
"Jibi tuwo zamuci a É—akin nan" Maman Minal data idar da sallah ta faÉ—a, Afeeya ta kalleta, Badar tace
"Ai kuwa mun kwana biyu bamuyi tuwo ba. Bari rana ta lafa se muje cefane miyar me za'ayi?"
"Kamar Kuka naji kince ko Afee?" Ta jefawa Afeeyah tambayar, zare manyan idonunta tayi tana kallonta da rashin fahimta dan bata gane inda maganarta ta dosa ba, ita yaushe sukayi zancen tuwo?
Maman Minal Ta miƙe tana ninke sallaya tace
"Zancen tuwo naji sunayi da Ahmad shine naji sha'awarsa nima kinga se ta mana Jibi idan zezo"
"Kai Anty Zahra daga jin muna magana bafa cewa yayi yana so ba labari ne kawai ya kawo maganar ba cewa yayi na masa ba" tayi saurin defending kanta kafin su ƙallaba mata abinda bazata iya ba. Badar dake side hannu ta cafe tana cewa
"Aiko yin tuwo Lazim idan ba so yake ba meze saka ya miki zancensa kawai dai be fito kai tsaye bane ke kuma in kinada lissafi ai kinsan me yake nufi Allah ya kaimu jibin dama bamu da Lectures kuma na shinkafa zaki mana Aradu ki tuƙeshi da kyau yasa malmala mu kwashi gara abinmu"
"Aiko zaki ɗige indai ni zan tuƙa miki tuwo, shima ya nemi inda zeci tun dare be masa ba wlh" Cewar Afeeya, Badar ta hayayyaƙo mata tana cewa
"Wlh se kinyi, ko mu ba zaki dafa mana ba se kin wa Ahmad banza wadda bata san Abin kirki ba. Ahmad É—in nan kwanta miki kaÉ—ai ya rage ya farayi amma hakan be saka yaci darajar mutunchi kema ki ringa mutuntashi ba kici gaba ubangiji ya miki ni'ima amma kina nema ki butulce masa in bakiyi wasa ba kika watsar da damarki ba fata na miki ba gaba se kinyi kuka da dana sanin rasa shi dan wlh a zamanin nan samun kamar Ahmad Namiji kyakykyawa, me kuÉ—i ga Ilimi da nutsuwa ga hankali kuma ya soki tsakani da Allah bawai da lalataba se an tona ai mazan dai gasu nan ke zaki bada labari dan babu kalar saurayin da bakiyi ba kowa kuma yazo iskanci yake kawoshi koda wanda ya tsaya bayan Ahmad din" Badar ta faÉ—a a hasale bacin ran ya nuna har kan fuskarta.
Kallonta Afeeya tayi bayan data zauna akan gadonta, bata tanka mata ba ta maida kai kan wayarta tana duba number data kirata yanzu kafinkuma ta answer ta katse, ganin ta waje ce yasa ta ajiye wayar ta yuwu Kamfanine ko sacammer. Tana jin Badar na maganganu tayi mata banza dan idan ta tanka se ran kowa ya ɓaci.
Badar tana yawan faÉ—a mata maganganun da bata jin daÉ—insu akan Ahmad amma tanayi mata uzuri saboda tasan bada wata manufa take faÉ—arsu ba a ganinta damuwa da lamarinta nema har yasa take tada jijiyar wuya akan abinda ya shafeta amma kuma idan aka kalli maganar tata ta wata sigar tana nuna kamr Alfarma Ahmad yayi mata da har yake sonta wanda wannan yana daga cikin abubuwan da yasa bata sonsa.
Bazata auri Mijin da ya zarce matsayinta ba wanda kowa ze ringa mata kallon cusa kanta tayi ko kuma Alfarma yayi mata daya aureta bata kai Ajinsa ba kamar yanda ÆŠan uwansa ya faÉ—a mata.
"Badar na gaya miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba idan kina son Ahmad na bar miki shi kuma zanyi duk iyawata gurin ganin kin same shi. Na sani ba tsarana bane, ire irenki ne m daidai dashi, matsayi da Arziqin iyayenku yayi kamanceceniya kinga babu me ganin cewar Alfarma yayi miki idan yayi tarayya dake" Afeeya ta faɗa zafafe tana barin ɗakin saboda gajiya da maganganun Badar dukda yanda Maman Minal da Ummi suke mata magana akan tayi shiru amma taƙi, dagaske neman fitinarta takeyi yau amma ba zata biye mata ba gara ta fita.
"Saboda ina sonki na damu dake ina miki burin ki auri Mijin da yake sonki kiji daɗi shine kike gaya mun haka ko Afeeya?" Ta faɗa tana Ƙanƙancr ido. Fes Afeeyan ta kalleta tace
"Kinji abinda na faÉ—a ai, Ahmad ne bana sonsa bazan aure shi ba kuma fatan da kike mun baze kamani ba Allah ze kawo mun Miji Talaka daidaini na aura wanda babu me saka mana ido ballantana a ringa fassara duk wani motsina akan sa da sunan na butulcewa ni'imar ubangiji".
"Meye haka Afeeya?" Maman Minal ta dakatar da ita, ta kalleta da idonta da suka fara canza kala tace
"To akan me Anty Zahra? Duk sanda magana zata haɗo akan Ahamd se Badar ta yimun gori a fakaice tace yafi ƙarfi na? ni na janyo shi nace ya soni ko yaya? Da yana da zuciya ma ai da bamu kai haka tare ba saboda na nuna masa bana muradinsa ta duk hanyar data dace amma ya nace ya kafe so takeyi na aureshi Alhalin danginsa basa ƙaunata? Ba'a a kunnenta ƙaninsa yayi mun cin mutunchi ya zagi iyayena sannan ta dage sena cusa kaina inda Allah be kaini ba saboda kwadayin abin duniya?
Toni kudinsa ko wani matsayi nasa ba zasu rufe mun ido ba su sa na jefa rayuwata cikin ƙunci na rayu da mutanen da basa so na, idan tana sonsa gashi nan na bar mata ta aureshi itace daidaishi" ta ƙarasa tana Ƙoƙarin riƙe kukan daya taho mata amma ta kasa dole ta sakeshi ta doshi Ƙofa zata fita amma mutanen da suka tsatstsaya munafunci yasa ta fasa fitar ta shige bayan Ummi da ke zaune ta kasa cewa komai ta kwanta tana kuka.
Maman Minal ta kulle Ƙofar jiki a sanyaye kafin ta zauna tana cewa
"Daga zancen tuwo shikenan se tashin hankali? da alama sheɗan ya shigo ya laɓe a ɗakin nan shiya haɗa komai kuma bazeyi nasara ba in sha Allah".
Badar da jikinta yayi sanyi laƙwas ta zauna daga tsayuwar da tayi ta kasa cigaba da masifar tata. Har ga Allah ita batayi magana da manufar da Afeeya ta ɗauka ba, ta riƙi Afeeyar a matsayin yar uwa shiyasa har take son cigabanta take kuma son ta da Ahmad ganin cewar mutumin kirkine ya na da duk wasu qualities da mace zata so a gurin Namiji gashi yana sonta baya ga haka wlh ita bata da wata manufa ta daban akan maganar.
Dakin ya ɗauki shiru se shasheƙar kukan Afeeya, kowa da tunanin da take a ranta wayarta ta sake ɗaukar ƙara lambar dazun ce bacin ran da take ciki yasa ta kashe wayar gaba ɗaya ba tareda na amsa kiran ba. Ranar har dare dukkansu basu da walwala shiru ɗakin kamar anyi mutuwa, tsakaninta da Badar kuwa se kallo seda Baffa ya kira wayarta akan be samu ta Afeeyan ba sannan nema ta tuna data kashe wayar tata, data miƙa mata bata kar ɓa ba, ta kunna tata ta kirashi.
Sururat ce ta saka su shirin dole cikin daren bayan ta dawo Ummi da Maman Minal suka tsara mata abinda ya faru ta ringa masifa ta kuma É—orawa Afeeya laifi kacokan wannan yasa suma sauran suka buÉ—e baki tare da nuna cewar ita ce bata kyauta ba su da kyakykyawar niyya suke tare da ita kuma wannan tasa har suke son abinda suke ganin ze zamar mata Alkhairi ba wani abu ba.
Bata so aja maganar da tsaho dan haka nace taji ta kuma bawa Badar haƙuri kamar yanda Sururat tayi insisting.
"Wlh Afeeya ina jinki kamar Yah Yusra, idan har zan iya aure ko soyayya da Mijinta to zanyi da Ahmad. Son da yake miki da kamalarsa tasa har nake miki sha'awar auransa dan nasan irinsa basu da yawa a duniyar yanzu amma tunda har zuciyarki tana raya miki wani abu daban akan niyyata in sha Allahu zan kama kaina, bazan sake yi miki wata magana data shafeshi ko ma akan saurayi ba gaba ɗaya. Zanci gaba dayi miki Addu'a Allah ya zaɓa miki abinda yafi Alkhairi" Badar din ta faɗa bayan da Afeeya ta bata haƙurin,
jikinta yayi sanyi ganin yanda idonta ke zubar kwalla sanda take maganar, ta tabbata har ranta gaskiya take faɗa kuma Badar na sonta kamar yanda ita ma take sonta amma abune yazo da rashin fahimta dukkan su kowa tana da dalilanta na so ko Ƙin tarayyata da Ahmad amma ta haɗiye nata za kuma ta cigaba da addu'a Allah ya fiddo mata da Mijinta daidai ita ya fiye mata sauƙi.
Saboda ta tabbatar musu maganar ta wuce yasa washe gari suna gama Lectures tacewa Badar suje kasuwa ayi cefanen, ta kuwa ji daÉ—i sosai dan da sunta share juna amma daga zuwa kasuwar komai ya wuce aka dawo daidai
Harda kayan zoɓo suka siyo, sesaga baya kuma Badar tace su siya Kunun Ayar Shinkafi kawai ba se anyi Zoɓon ba.
"Bari na kira Salima Nasir ta zo manada snacks gobe se a hada masa ko?" Badar ta sake faɗa. Dole Afeeya ta amsa gudun karta ƙara laifi a gurin Badar data saki ranta dalilin za'ayiwa Ƙanin Dadynta girki. Sunyi markaɗen stwe a Kasuwa dan haka suna komawa suka ɗora girki suna hira kamar ba abinda ya faru jiya.
Washe gari haka Afeeya ta tuƙa tuwon rabin kwano tayi miyar kukar da Ƙamshinta ya karaɗe duka block ɗinsu ya buwayi hancin kowa. A Set din food flask da suka ɗakko da safe a gidan Maman Minal ta saka masa tuwon Miyar aka barta a tukunya akan seya zo se a sake dumamawa a zuba a flask din. Kayan da zan saka ko Badar ta turarasu ya kai sau uku, jikinta har rawa yake idan Ahmad zezo musamman wannan karon, sunyi waya da Afeeya ya gaya mata be taso da wuri na ze kai zuwa uku kafin ya sauka dan haka zuwa biyu ta gama komai tayi wanka suka zauna suna ta labarai. Biyu da rabi ya kirata akan ya shigo zaria.
"Na gaji da yawa ni nayi driving zan wuce nayi Lodging hotel idan na huta da Magriba sena shigo kuma bani kaɗai bane tare muke da mutumin Badar" ya faɗa mata. Har zatace masa toh ta tuna da Tuwon data gama shan wahalar tuƙawa hannayenta duk sun sage tafin se radadi yake mata Allah ma yasa kar nayi kanta. Da shagwabar da bata san tayi ba tace masa
"Toh Abincin fa? Shima se da magribar zaka ci?"
"Wane Abinci?" Ya tambayeta cikin rashin fahimta se sannan ta tuna da bata gaya masa tayi masa tuwon ba dan haka tace
"Girki mukayi shine na É—ibar maka ko bazaka ciba?"
"Nidin banza, gani nan yanzu kuwa zanzo na karba kamar kinsan yunwa nakeji ko breakfast banyi dakyau ba saboda dokin son ganinki"
Guntun murmushi tayi kafin suka aje waya. Miyar aka sake É—umamawa Maman Minal tayi masa zubi me kyau duk ta kwashe Albarkatun cikin miyar ta bar musu saura. Hijabi ta É—akko cikin na *UMMU-MAHEER 07061838488)* wankakke gogagge ta É—ora akan doguwar rigar jikinta Badar ta kwaso Ashar ta watsamata ta haÉ—iye dan daman ta san se sunyi.
"Tsabar iskanci in gama shan wahalar turara miki kaya ki wani kwashi Hijabi kamar me takaba ki saka" ta faÉ—a a fusace tana neman fizge hijabin. Maman Minal tace
"Ki barta ai ze dawo anjima se tayi kwalliyar sannan".
"Masifaffiyar banza kawai" Afeeya ta faɗa Ƙasa ƙasa. Sururat ce ta tayata ɗaukan Basket da suka zuba abincin.
Kallon da bata so ya kafeta dashi tun daga corridor harta fita wajen hakan da yayi yasa hankulan mutane da yawa yayiwo kanta har suka Ƙarasa gabansa yana ta sakin murmushi kamar wani wawa.
Kallonsa tayi taga ya sake zama wani dan tsurut musamman daya saka ƙananan kaya se taga ma har tsakiyar kansa tana kallo tsanar sharri, murmushi tayi itama ta shiga gaishe su shida Abokinsa da kana ganinsa kaga Kanuri. Wani Baƙi dashi hausar ma se a hankali se surutu kamar ya ƙone a kai.
"Gaskiya Amaryarmu ba kalar rana bace, dan haka kodai ka nemi inuwa ku zauna ko kuma ka barta ta koma ciki an jima idan gari yayi sanyi seka dawo. Ni ganin basket É—in nan ma gaba É—aya ya sake tadomun da yunwa" Bukar ya faÉ—a ga surutu ga saurin baki.
Kanta na ƙasa tana wasa da zoben hannunta duk kallon da Ahmda ya kafeta dashi ya takurata,
"Bari muje Fatima anjima se na dawo bayan La'asar ko?" Ya faÉ—a cikin sigar tambaya ta É—aga masa kai ta ce
"Toh".
Abokin ne ya karɓi basket ya saka a mota Ahmad ya bishi ya ɗakko wata leda me tambarin super market dinsa BECHI STORES ya miƙa mata ta karɓa ta ɗan rusuna tace
"Nagode"
"Tsarabarki ce, tukuicin girki kuma se naci naji ÆŠanÉ—anon sa tukunna"
Murmushi tayi, ya langwaɓe kai ya jingina da mota yace
"Kamar karna tafi, kinyi kyau sosai Fatima Hijab suna miki kyau" Yaƙe kawai takeyi Abokinsa ya leƙo daga mota yace
"Kodai na zuba na fara ci ne in ba yanzu zamu tafi ba?"
"Kaga kun kwaso gajiya, kodan saboda dashi kuje Anjiman se ku dawo" ta faÉ—a, seya gyara tsayuwarsa yana cewa
"Naga hannunki"
Ƙirjinta ya buga, me ze gani a hannunta kuma? Amma haka ta daure ta miƙa masa hannun da daga wrist zuwa fingers ɗin ne a buɗe,
"Masha Allah ya faÉ—a" kafin ya juya yana É—aga mata hannu da cewar
Se ta dawo ita ma ta É—aga masa. Ta tsallaka ta shige hostel tana ta mamakin dalilin son ganin hannunta da yayi.
Tuwo ta tarar suna ci ta wanke hannu ta zauna, tunda ta gama taso taci jarabar Badar ta hanata wai bakinta zeyi warin daddawa se kace idan ta wanke baze fita ba. Seda suka qoshi Ƙat kafin a zazzage ledar tsarabar.
Wata Arniyar Turkish gown ce Material me sharashara Amma tana da landing Dark blue ce da flowers Yellow da fari da dan yarfin ja kadan. Irin design da ake sakawa roba a waist ta matse ta sama ƙasan kuma ya buɗe ce se mayafai Medium guda biyu plain da kana ganinsu kasan suma daga Turkey suke saboda samfurin jikinsu, takalmi loafers dark blue qafa daya se Wani kwali ƙarami na turarene babu suna a jiki hakan ya tabbatar mata da sabone basu luncher shi ba testing ya kawo mata kamar yanda ya saba tunda suka haɗu, Ahmad yanayin Designer perfumes kuma duk sanda sukayi sabon Turare kafin a fitar dashi seya kawo mata.
Company haÉ—in guiwa ne da wasu Abokanansa da sukayi karatu tare a Paris Asalin kamfanin yake amma a Dubai suke operating.
Tarkacen Chocolate na yan gayu birjik su su Badar suka ɗiba ragowar kayan ta watsa su a kan gado. Ahnad baya gajiyawa kullum cikin hidimta mata yake. Idan ya tashi siya mata kaya tamkar besan zafin kuɗi ba daidai da Slippers yanda yake saka Designer haka yake siya mata tun Baffa da Umma na faɗa har suka haƙura suka zuba masa ido kyautar Kuɗi ce dai Baffa ya dakatar shine yace idan an hanata karɓan kuɗi ai ba za'a hanata kaya ba dukda haka kuma idan zata koma school seya tura mata kuɗi masu nauyi sedai taji dirim.
Shida saura Ahmad ya kirata akan sun fito suna hanyar Samaru, bisa takurawar Badar Ummi tayi mata light make up ta cakare cikin Atamfa dinkin fitted straight Bubu, bata kamata tsam ba haka bata yi buhu ba tabi shape dinta ko ina ya fita masha Allah abinka da dogowar Mace na ta juya Anty Zahra tace
"Afee kinyi kyau, komai kika saka kyau yake miki".
Badar ce tayi mata É—auri me kyau daya dace da kwalliyarta
Seda aka idar da sallar magriba kafin ta fita dan bayan ya isa kirata yace ze shiga central mosque yayi sallah tukunna. Bata cika fita babu Hijabi ba infai ba Abaya ta saka ko irin Bubu plain Gown ba a hakan babu kwalliya gajiya takeyi da idanun mutane balle yau datayi shigar Atamfa harda kwalliya a fuskarta ga ɗaurin gaban goshi wani irin kyau tayi me sanyi da ƙayatarwa ba Maza ba hatta matan dake kaikawo a waje Hostel binta suka ringayi da kallo duk seta jita a takure shoyasa tafi gane ta suturta kanta da Hijabi Ko Abaya.
Yanda Ahmad ya saki baki yana yabon kyan da tayi ko har seda abin ya bata kunya ta sunkuyar dakai tana murmushi. Shi kaɗai ya dawo Abokin nasa wai ya shiga City, a nan Basket ball court suka zauna suna hirar duniya dan a itane take sakewa dashi suyi magana ko zancen Business dan tanada sha'awar kasuwanci sosai abinda ma zata ce ya a birgeta da Ahmad kenan Business mind set, a tsaye yake da ƙafafunsa kuma kullum cikin nuna mata amfanin neman na kai yakeyi. Yakan ce mata
"Ina so naga matata tana sana'a badan bazan wadata ta da komai na rayuwa ba Aa sedan ni na yarda da ko wani zeyi mun abu ya zamana nima inada abuna wanda zan kalla nace da gumi na na sameshi".
Seda aka kira yace ta kira su Badar su fita wannan daman constant ne duk sanda yazo seya fita dams yawo sun sha iska sunyi ciye ciye, tana kiranta minti goma suka fito duk a shirye harda Ruth suka zauna su huÉ—u a baya ita a gaba banda Maman Minal suka tafi Zaria Suya kamar yanda Badar tace can za'aje sunata hira da Ahmad har suka isa.
Sunci kifi sun sha shayi sunyi take away kaza da Suya amma banda Afeeya da idanun da Ahmad ya kafeta dasu suka hanata sakat. Yau se take ganin kamar tasan wani bayan shi me irin idon, amma ta gaza tuna waye.
PAGE 11
"Saura sati nawa kuyi hutu?" Ya tambayeta yana sake narkar da idanunsa a kanta. Ta lissafa a zuciyarta kafin tace
"Four weeks i think"
"Fatima" ya kira sunanta da sautin dake nuna muhimmancin maganar da zasuyi, ta gyara zamanta ta saci kallonsa yaci gaba da cewa
"Shekara biyu kenan since i meat you. Banyi zaton zan ƙara wata shida ba daga ranar dana haɗu dake ba tare da kin zama matata ba amma se gashi har an tafi shekaru which kece kika jawo hakan, please Fatima, i will ask you again ki aureni, last week na je na samu Baffa akan ina so na turo magabatana yace na nemi Amincewarki tukunna, idan kin yarda ko yaushe na shirya na tura ayi magana.
Bansan me kike jira ba, Fatima Aure baze hanaki ƙarasa karatunki ba tunda shine maganarki kullum ke kinfi so ki gama makaranta ni bazan hanaki karatu ba idan kin gama wannan kina so kici gaba wallahi ko a Nigera ko wata ƙasa ni zan tsaya miki har se ke da kanki kince karatun ya ishe ki tukunna kawai ki Amince mun ki bani dama na tura Iyayena ayi maganar auran mu saboda wlh Haƙuri na ya fara ƙarewa Aure nake so Fatima"
Shiru tayi masa kuma kunyar kalamansa na ƙarshe ne ya assasa shirun wai Aure yake so, matso da kujerar sa yayi kusa da tata kamar ze haɗe su yana cewa
"Talk to me Fatima bana son shirun nan naki menene matsalarki bayan maganar karatu? Idan da akwai wani abu daban let me know please"
Kamar tace masa "shi ɗin ne bata ra'ayin aure se kuma ta canza maganar dan ko babu komai kirkin Ahmad ya wuce tayi masa irin wannan cin fuskar. Kora da hali dai ba wadda bata masa baa baya amma ya ƙifahimta to ya yake so tayi dan Allah? Gyara zama tayi ta dan ja baya saboda kusancin nasu yayi yawa kafin tace.
"Nidai Ahmad nafi so na kammala karatuna tukunna in so samu harma nayi NYSC kafin nayi aure, sannan kana cewa muyi aure naci gaba da karatu na tayaya hakan zata faru bayan Matan gidanku bas karatu?"
BuÉ—e ido yayi irin na mamaki ya kalleta kafin yace"Waya gaya miki haka?"
"Haka naji a gari" ta bashi amsa tana sauke ido ta saboda yanda ya saka mata nasa, cikin taushi yace
"Fatima abin harda sharri? A wane gatin kikaji? Waya ce miki matan gidanmu basa karatu?
Matan Yayyena harda me Phd Matar Dr Hassan tana aiki Lecturer ce, inaga a cikin sauran babu wadda batada Degree, idan kuka Ƙannena kike nufi Aslamiyya da Hajiya Ƙarama Level 2 suke kowacce kuma Next two month aka saka ranar Auransu kowacce zata gama Karatun a gidan Mijinta ya za'ayi kice ba'a karatu a gidanmu kodan kinga Alhajin mu ba Ɗan Boko bane?"
"Ni bance haka ba, to inaga qadda ta gaya munce bata ji daidai ba" ta faÉ—a cikin kare kai shaci faÉ—i kawai tayi seta daki garwa. Ya saki murmushi yace
"You know nothing about my family kar kuma kice zakiyi judging da abinda kike ji a bakin mutane. Babu wata mace da aka taɓa aurowa a gidanmu akace ba zatayi karatu ko aiki ba, duk wadda kikaga bata aiki bata da ra'ayi ne, amma dai ni in particular bazan yi miki ƙarya ba tun yanzu ki sani idan har Allah ya sa ka munyi aure babu maganar aiki ba zakiyi ba. Ba zan yarda Matata ta ringa yawo a gari da sunan aiki a Ƙarƙashin wasu ƙatti ba. Business dai wannan idan zakiyi zan baki jari daga naira ɗya har zuwa Miliyan ɗari ya danganta da abinda zaki siyar amma ban miki ƙaryar zakiyi aiki ba" ya faɗa da iyakar gaskiyarsa.
Duk yanda yaso ya sha kanta akan ta bashi dama ya tura, ya yarda aje ayi magana idan yaso a saka rana sanda zata gama Makarantar idan haka ne burinta amma ta tubure ita ba haka ba. Cikin yanayin dayake nuna ransa ya ɓaci da rashin samun amincewar tata ya maidasu Makaranta, be tsaya ba yace mata Bukar ze maido mata da Flask gobe be taho dasu ba shi Asubanci zeyi ya wuce Kano.
"Idan yazo Badar ce zata karɓo ba keba" ya faɗa da sigar umarni. Cikin wasa Badar ta ɓata fuska tace
"Wato ni mara galihu tunda bani da tsayaye ko"
"Kika sani ko ya zama tsayayyen?" Ya tsokaneta. Bundle É—in 1k ya bawa Badar yace
"Tukuicin Tuwo, yayi daÉ—i da alama ke kikayi"
"Afeeya ce wlh" ta faÉ—a bayan data dafe kuÉ—in, ya juya mota yana cewa
"Idan ta amine da muradi ma zan haÉ—a na bata tukuicin a tare" yaja ya tafi babu wata profer sallama da suka sabayi.
"Alamu sun nuna kin kwafsa Afeeyah,wai dan girman Allah se yaushe Ahnad zezo Zaria ya koma da farin cikinki ne?" Badar ta faÉ—a suna shiga Hostel.
"Hmmm" ta bata amsa dan ita da kanta taji rashin daÉ—in yanayin daya tafi, duk shanye fushinsa yau seda fuskarsa ta nuna, amma ya zatayi toh?
A rabon Maman Minal ta yafita mata Kaza taci dan da Badar rantsewa tayi ba zataci ba tunda bata da mutunchi.
Harta kwanta wayarta ta fara Ƙara, International number ce, kwana uku kenan ana kiranta da ita kullum kuma ko ta tsinke kafin ta ansa ko kuma taga miss call ita kuma ta san bata da wani a Ƙasar waje da ze kirata shi yasa bata taɓa bin baya ba ta yuwu ma scammers ne.
Ta amsa wayar ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba, kusan minti guda ita shiru haka wanda ya kira shima beyi magana ba daga can ƙasa dai tana jiyo maganganu alamar yana kusada inda ake hayaniya. Suka ci minti uku, harta yanke shawarar kashe qayar dan ba zata fara magana ba ta yuwu wand aaka ce suna tsotse jinin mutane ta waya ne suna jira tayi magana su gama da ita, harta zareta daga kunne taji wani sauti daya saka zuciyarta tsayaqa na wasu seconds kafin taci gaba da aiki
"AFEEEYAAAAHHH!" Yaja sunanta, bata iya amsawa ba se sunayen Allah da take maimaitawa a ranta Ƙirjinta na lugude.
"Afeeya!" Me kiran ya sake maimaitawa, bugun Ƙirjinta ya tsananta zufa ta fara tsassafo mata haka numfashinta ya shiga yi kamar ze tsaya tamkar wadda take cikin matsanancin tsoro kuma kamar wadda aka kafe ta kasa cire wayar daga kunnenta se kokawa take da numfashinta dake barazanar tafiya hutu saboda tasirin da muryar wanda batasan ko waye ba yayi a kanta.
Bata taɓa katari da Bakin daya iya furta sunanta, ya bawa kowanne harafi haƙƙinsa kamar me waƙa.
"Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa cikin wani sauti me haɗe da irin ƙaramar dariyar nan, take ta kware da yawun bakinta ta shiga tari tul tul Ummi data fi kusa da ita ta miƙa mata ruwa tasha tana maida numfashi har sannan kuma be kashe wayar ba, kwakwalwata ta ayyano mata me wannan muryar, sallamar da yanayin da yayinta ya tuna mata da jinjirin Samudawan da tayi gamo dashi ranar Monday.
"Sannu, badai loman abinci kikeyi ya Ƙwarar dake ba?" Ya sake tambayeta se kawai taji bakinta ya saki tsaki kafin ta zare wayar ta kasheta tareda ajiwa batama lura da yanda yan ɗakin sukayi shiru tareda zuba mata ido ba se sannan.
"Afeeya meya faru? Kinga fuskarki kuwa se kace wadda Fulanin Daji suka kira?" Maman Minal ta faÉ—a, ta shafa fuskar da hannu, Badar tace
"Meya tsorataki? Kin kara waya a kunne kusan minti goma bamuji kince komai ba lafiya ko wani abun ne ya faru?"
"Uhm" kawai tace ta miƙe tareda ɗaukar ɗankwalinta ta fita ba tareda ta amsa tambayar ba har sannan kuma zuciyarta bata bar bugawa ba kamar yanda jikinta yake rawa. Last floor ta haye ta tsaya tana kallon 90s mutane nata karaina surutu duk ya cika gurin, tunani takeyi shi ɗin ne ko ba shi ba? Idan shine a ina ya samu number ta sannan kiran me yake mata?
Zancen Sahid dayace ya bawa wani number ta ya faÉ—o mata to ko shi yake nufi a gurinsa ya samu number wayata tunda ta faÉ—a mata sunanta daman?
"Afeee" aka Ƙwala mata kira daga Ƙasa, tayi firgigit daga tunanin da take ta kalli inda taji sautin na tasowa tsabar wulaƙanci Nurain ne yake kwala mata kira daga cikin 90s, bata amsa ba ta harareshi ya ɗago mata Kwalin popcorn yana cewa
"Kinyi kyau, zaki ci popcorn?" Still da Ƙarfi yayi maganar abinda ya janyo hankulan waɗanda ke kusa dashi suka kalli gurin dan ganin dawa yake tana ganin haka tayi saurin sauka ta koma Floor ɗinsu dukda haka tana hango su se shegiyar dariyarsa yakeyi tana shiga Badar tace
"Cin kan Bestin naki ya motsa yau"
"Ke kuma sweetynki ba" tabata amsa tana Ƙoƙarin cire rigar jikinta wayarta ta shiga ringing, data Badar a tare ta ɗaga ganin Ahmad ke kira bayan ta haye kan gado, hira suka shigayi ya saki kamar bashi ya tafi fuska babu walwala ba, Bashi da ruƙo, yana daga cikin kyawawan halayensa se santin kwalliyarta yakeyi har yana cewa saura ƙiris yayi abin kunya next time karta sake saka Red Lipstick idan zata masa kwalliya har se ta zama matarsa.
Sedata kashe wayar ta kura Badar ta fita Ruth tace mata sun fita da Ummi Nurain ne ya kirata
"Gulma, ana so ana kaiwa kasuwa" ta faÉ—a,daga nan ta gyara kwanciyarta ta bhau WhatsApp.
Lambar Basamude ta gani a farko yayi mata magana
"Why did you hang my call and you hissed at me? Not even in your dream you try that again" Ta maimaita saƙonbabu Adadi Mamaki ya kasheta, a fili tace
"Ikon Allah, ji wata magana kamar wani uban mutane, wannan yana da lafiya kuwa?" a maimakon ta amsa se ta shiga profile É—insa, Hoton Jessy ne akai ta Yan Ball kalar Red da white no 9 an rubuta *JAY* a jiki, batasan ko ta wanne club bace ba abinda ta sani dangane da yan Ball.
Tayi tsaki na fita daga chat ɗin tana jinjina Ƙarfin halinsa, status ta fara kallo kira ya shigo video call tayi rejecting wannan mutum ko maye ne ai se haka wannan Naci har ina?
Be haƙura ba ya sake kiranta voice call ta sake rejecting, seda ya kira sau uku ana huɗun ta amsa tun kafin tayi magana yace
"Wallahi Afeeya, if reject my call again I'm going to deal with you"
"Malam kanka guda kuwa? Who are you? Are you suppose to tell me what to do or what?" Ta bashi amsa a haslae jin abin nasa ze zarce ganga da makaÉ—i.
Tana ji yaja numfashi kafin ya sassauta murya yace
"Baki san abinda nake ji a zuciyana bane, 3 days i have been calling but you are not answering, na sameki yau and you hanged on me haba Afee bakida tausayi ne?"
"Don't call me that again" ta faÉ—a jinyanda Afee daya kirata ya saka tsikar jikinta zuba,
Tanaji yayi wani mayaudarin murmushi yace
"*AFEEYAH* God i love the name, gaskiya Dadynki ya kyauta daya saka miki suna me daÉ—i da Ma'ana, idan munyi aure nima zaki haifarmun tawa Little Cute Afeeya like you ko?"
"Qit" takashe wayar,, koda wanda ta sani bata wannan zancen shirmen ballantana da stranger wanda bata san mutum bane ko Aljan. Seda ta kashe Data ta saka wayar a Silent kamar yanda takeyi idan zata kwanta kafin tayi addu'a ta rufe idonta amma bacci yace be san zance ba, dakyar da taimakon Allah ya saceata. Kwana tayi tana mafarkin mutumin wai suna tafiya akan Gajimaren suna tsinkar furen soyayya.
Da Asuba ta samu tsarki tayi wanka tana Azkar Ahmad ya kirata suka gaisa ya gaya mata yanzu ze tafi Kano.
"Da wurwuri haka?" Ta tambayeshi, tana ji yana warming mota yace
"Alhaji ne ya kirani zan takashi Hadeja Ɗaurin Aure kinga dole na tafi da wurwuri karna ɓata masa lokaci"
"Haka ne, Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya" tayi masa Addu'a ya amsa da "Amin" kafin sukayi sallama ta kashe wayar ta juya da niyyar maida kai taui bacci aka sake kiranta.
"Jarabar duniya" ta furta a fili ganin me kiran da farar Asubar nan se kace wanda yake binta bashi ze fara kira wannan wane irin mutum ne mara lissafi ta shiga mita a ranta amma hakan besa taƙi amsa wayar ba dan harga Allah can ƙasan ranta har wani daɗi taji daya kira.
Cikin dakakkiyar muryarsa ta Maza irin wadda zakaji kamar har echo tke yi yayi mata sallama ta amsa tana jin wani sabon yanayi yana mamayarta.
"Jiya kika kashe waya kuma bayan nace bana so, kuma nayita kira baki amsa ba why?" ya faÉ—a a tausashe kamar bacci be gama sakin muryarsa ba hakan ya sa muryar tayi wani amo na daban me tsinka jini, numfashi taja ta fesar amma batace komai ba yaci gaba da magana yana cewa
"Bana so, don't you ever hang on me again gara ki gayamun ni na kashe wayana da kaina if you don't want to talk to me, raini ne wannan kuma bana so".
Ta shagala da sauraron Muryarsa se kuna ta zabura tace
"Wai kai a matsayinka nawa ne da zaka ringa kafa mun sharaÉ—i?"
"Ina son tsiwa, amma bana son rashin kunya, idan kika ci gaba sena fasa miki baki, then i will keep kissing it har se ciwon ya warke" ya bata amsa seta hangame baki ta kasa cewa komai, baccin da take tattalawa ya kama gabansa.
"Afeeyah, i hate it when someone hisses at me, karki sake" ya sake cewa
"Waye kai?" Ta samu kanta da tambaya dan wannan gadarar tasa ta shallake ta masu hankali kuma,
"I will call you by 10am, kina free?" Be bata amsar tata tambayar ba ya jefa mata tasa
Ta wurga ido kamar yana gabanta kafin tace
"No, i have class by that time"
"2pm?" Ya sake faÉ—a se ta karkace tace
"That will be my resting time"
"In the evening?" Be haƙura ba ya sake tambaya ba kai tsaye tace masa
"Kasan me, ina da lokaci amma ba naka bane so you better respect your self and stop calling me talk less of Bossing around kana wani gayawa mutum abunda zeyi da wanda ba zeyi ba"
"Idan na kira karki daga kinji" ya faÉ—a yanda kasan wani Baffanta kafin kuma tace wani abu ya kashe wayarsa ya barta da baki a gantale.
"Afee don do new catch" Sururat ta faÉ—a teasingly, takaicin daya cikata ya sa bata tanka mata ba tana jin Badar na cewa
"Tun jiya take wata waya kamar ta munafukai koma wanene yayi ta kansa wlh dan ina gani babu wanda ya isa yayiwa Ahmad over taking".
Kwanciya tayi cike da jin haushin kanta da biyewa mutumin har ya samu damar raina mata hankali.
"Amma ya haɗu, haka take son tsayayyen namiji, ta tabbayar da Ahmad ne sedai yayita lallaɓata yana cewa tayi haƙuri".
AHMAD
Ƙrfe Tara da mintina ya isa Kano dalilin Hold up daya samu a Kwanar Ɗangora wata babbar Mota ta faɗi a tsakiyar Titi wannan ya kawo cin koson ababen hawa a titin dan se zagaye suka ringayi suka kaucewa inda hanyar ta rufe ma. A Ƙofar Katafaren Get ɗin gidan Alhaji Audu Bechi ya tsaya yana danna Horn, Issa ya tsallako da gudu daga gidan dake kallon nasu inda suke zaune da sauran masu gadin gidajen layin ciki. girmamawa yake masa sannu da zuwa
"Yi sauri Issa, na makara Alhaji yana jirana" ya faɗa ganin Issan ya tsaya ɓata masa lokaci da gaisuwa da sannu da zuwa hakan yasa ya wangale masa Get ya shiga.
Cikin Rumfunan da aka tanada domin Ajiye mota yayi parking, motoci ne birjik a gurin yanda kasan kamfanin saidasu, cike da murna ma'aikatan dake kaikawo a Kantamemen compound ɗin suka nufeshi suna masa maraba, duk saurin da yake haka ya tsaya yana basu hannu, babu kyama balle nuna banbancin kasancewar Barorin gidansu ne su yake mu'amalantarsu wannan Ɗabi'a tasa ta karrama Ɗan Adam yasa yake da farin jini matuƙa gurin mutane.
Junaidu daya daga cikin masu kula da shara ya ɗaukar masa Ƙaramar Akwatin da kayansa suke ciki, har ya nufi bangarensu na Mazan gidan yayi burki ya juya zuwa ainihin cikin gidan.
Da sallama ya shiga tsakar gidan shiru babu kowa kai tsaye ya doshi Falon Momy, ya kai tsakiya ya tsinkayi muryar Hajiya a bayansa tana cewa
"Aa, su uban Bilki an dawo kenan?" (Baba Bilki tana kiransa Babanta saboda Tace Asalin sunan Tijjani Amadu ne dan haka da Babangida da Ahmad duk sunan Malam Babansu sukaci shine Hajiya ta samu idan iskancinta ya tashi take ce masa Uban Bilki) Jiya ÆŠan uwanka yake cewa kace masa zaka daÉ—e a Habujan se gaka kuma da Sassafe lafiya dai ko?"
Birki yaci yana cije lebensa, ya tsani sunan nan data ke kiransa kuma a duk sanda tayi hakan tana nufin zagin Baba Bilki ne ta yuwu sunyi hatsaniya shine zata fake da haka ta zageta da alama kuma yau da ɓurɓushin mutunchi tunda har ta kira Jafar da Ɗan uwansa
Seda ya daidaita fuskarsa kafin ya waiwaya ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya durƙusahar ƙasa kamar yanda yake gaida Mahaifiyarsa yace
"Hajiya Ina kwana?"
Tana ƙara matsowa ta amsa masa da lafiya tana sake maimaita tambayar dalilin dawowarsa da safiyar nan da be bata amsa ba. Ƙatuwar Robar hannunta ya kalla ya girgiza kai, Nama ne shaƙe a ciki yau Juma'a da alama tayi halin, zuwa take ta zaftare naman Abincin sadaka da akeyi duk ranar Juma'ar, tun suna yara haka Hajiyan takeyi ko ran girkinta ko ba nata ba se taje ta kwashe Naman kuma babu wanda ya isa yace dan me hatta kuwa da me bada kuɗin Naman wato Alhajin gidan.
Gaba yayi yana ce mata
"Wlh Alhaji ne yayi mun kiran gaggawa zan rakashi Hadeja, yanzu ma sauri nakeyi nasan ya shirya ni yake jira". Ya lura da yanda murmushin kan fuskarta ya ɓace ɓat kamar ɗaukewar wutar Nepa hakan kuma nada nasabada jin cewar Alhaji ne ya kirashi.
Wucewa yayi ya barta nan a tsaye,
Da sallama ya shiga falon Mony wanda ya tarar da Ƙofar a buɗe, Momy na zaune a ƙasa tareda ƙanwarta Anty Maimuna da bata fi minti Goma sha biyar itama da shigowa Kanon ba daga Katsina inda take aure suna karyawa Ahmad ya shiga. Seda ya cire takalminsa sau ciki a baqin wajen kafin ya shiga yana sake nanata sallamarsa Momy da Anty Maimuna suka ɗago a tare kowacce fuskarta washe suna amsa masa ya zube a gabansu yana kallon Antyn nasa dake masa oyoyo kamar wani ɗan yaro yayi dariya yace
"Anty saukar yanzu ko nan kika kwana? Koda yake munyi waya da Momy dazun bata ce mun kina nan ba kenan yanzu kika zo".
"Zuwana " kenan Amadi ban daɗe ba, kayan lefe nazo haɗawa ƙnin Baban Sayyid nayi waya da shagon da zan siyi kayan basu fito ba shiyasa nayo nan na karya tukunna" ta bashi amsa seya ƙara washe baki yana gaisheta tareda tambayar Yaranta tace duk suna gida suna gaishesu kafin ya juya ya fuskanci Momy da murmushin kan fuskarta ya gagara gushewa saboda farin cikin ganinsa. Cikeda tsantsar ladabi ya gaisheta ta amsa tana tura masa plate din gabanta tace
"Nasan baka karya ba"
"Kai Momy, so kike Alhaji yamun faɗa kenan ƙarfe tara fa yace zamu tafi gashi yanzu goma ake magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy ta goge hannunta da tissue tana cewa
"Dana ji shiru ma na zata har ka shigo kun tafi dan tun ɗazun dana kai masa abin kari naji kuna waya yace ka kusa gida da ai da Takwaran Alƙali zasu je ban san ya akayi tafiyar ta juyo kanka ba"
"Haba dai, kina da rai na taho daga wani gari na shigo har cikin gidan nan na fita ba tareda nazo na ganki kin saka mun Albarka ba ai ko bakida rai na shigo na kalli ɗakinki nayi miki Addu'a Momy" Ahmad ya faɗa, wani murmushi me nuna irin Alfaharin da Momyn keyi da kasancewar sa ɗanta tayi kafin ta miƙe tana cewa
"Ka hanzarta dan nasan yaji shigowarka karka ja yayi maka suruti" seya rusuna a gabanta yana cewa
"Zan fita"
"To Ɗan Albarka, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya Allah kuma ya tsare ku daga sharrin ƙarfe" Momyn ta faɗa tana dafa kansa kamar ƙaramin yaro ya miƙe yana murmushi yacewa Anty Maimunan ya tafi itama tayi masa Addu'a kafin ya zura takalmin sa rabi ya fita da sauri jin agogo yana buga goma.
Anty Maimuna ta rakashi da murmushi kafin ta kalli Momy tace
"Allah kenan, idan ya baka dubu masu bata maka se ya baka ɗaya da ze wanke maka takaicin duka dubun nan. Yanzu ki gani har qofar dakin nan Salim yazo keda kika haifeshi baki isa ya leƙo yace ya kika tashi ba balleni baƙuwa zuwan yanzu kuma ba kunya ya karɓi abinci yayi tafiyarsa.
Momy ta kai zaune tana cewa
"Ai Maimuna Al'amarin Salim a kullum maimakon yayi sauƙi ƙara ta'azzara yakeyi. Ba Salim kadai ba ni yanzu Yayansu shi yafi damuna, ace mutum beyi shashanci ba da ƙuruciya se yanzu daya fara tara iyali? Kuma wannan ƙallababbiyar sabgar siyasar da ya shiga ita take neman canza masa alƙibla, daman ni sam abin be kwanta mun ba. Tunda ya fara yake sakani magana, kullum matarsa na hanyar kawo ƙararsa.
Yanzu shekaran Jiya seda sukazo sulhu da saboda tsabar wulaƙanci Yaron nan wai wancan satin ya kawo mata wasu ɗirka ɗirkan yayan Ƙabilu gida wai Yawon Campaign suka zo basu da masauki duk Hotel da suke Kano bega inda ze kama musu ba se gidansa yace ahine ta zo nan take gaya mun na kirashi nayi masa tatas ya sallamesu be daddaraba shekaran jiyan sega wata ya sake kaiwa wai sati ma zatayi a gidan shi zasu tafi Abuja dan haka zata zauna a gidan har ya dawo data kira waya ta gaya mun na sanarwa ubansa bece komai ba, se Alƙali na kira na gaya masa shi kuma ya kirashi sukaje can aka kashe maganar to Allah yasa dai yaji, Haba Yanda kika san su kaɗai ne Yaya a gidan nan kullum cikin sakani magana da ɗakko mun zance suke Salim da Babana na rasa yanda zanyi dasu".
"Hmmm, Anty Aisha kenan, ai bazangaji da gaya miki ba kin tafka kuskure a baya kuma sakamakon sa kike girba a yanzu. Sufa Yaya kiwo ne Allah ya bamu, ba kuma iyakar wanda ka haifa daga cikinka sune naka ba, Malamai fa suna cewa ranar Lahira hatta akan gidan auranmu da zamantakewar mu se anyi mana Hisabi kinga kenan dole mu yi iyakar iyawarmu gurin ganin mun sauke duk wasu nauyi daya rataya akanmu shine kuma ya haɗa da kula da tarbiyyar yayanmu da duk wand suke zagaye damu. Kinga waɗannan yaran da kika ringa zuba ido ana cutarwa? Rayuwarsu ta ringa gantafalfala alhalin kinada halin taimaka musu ki kwatar musu yancinsu ta yanda koda basu samu dukkan gata ba zasu samu rangwamen halin da suke ciki amma kika naɗe hannu da sunan ba ruwanki baki shiga abinda ba'a sanyaki ba wlh ko kaffara bazanyi ba harda haƙƙinsu cikin abinda ya saka kika gaza ganin daidai a cikin taki zuri'ar.
Kuma irin tarbiyyar da kika bari aka ginasu akanta ita naki yayan da suka tashi suka ɗauka, abinda da yawa muke kasa ganewa kenan a duk sanda kaga Ɗan wani musamman na kishiya yana abinda be kamata ba kar kace babu ruwanka ko bazaka tsawatar masa ba domin ze cuɗanya da naki Yayan, duk bakin tarbiyyar da kika haƙiƙance kina yi musu kuwa kina can ba zaki san lokacin da zasu ɗauki halaye marasa kyau ɗin da kika bari suka ci gaba ba.
Kinzo gidan nan kin tarar da yara da yawa, da ace ke me dabara ce a sannan jan su zakiyi a jiki kiyi musu irin tarbiyyar da Kike fatan yayanki su tashi akanta, haka mata masu wayo sukeyi suja yayan kishiya a jiki su kula dasu da tarbiyyarsu karki taɓa duba halin uwarsu ko abinda zata miki domin taki gaban kike gyarawa, yanzu wa gari ya waya? Banda Ahmad da Matan da kika samu Allah ya duba miki ya sassauta abin akansu dukda suma ɗin da nasu, gaba ɗaya yayan gidan nan babu wata shaƙuwa ko soyayya a tsakaninsu, kowa kansa ya sani wlh ina jiye muku ranar da mutuwa zata fara ɗauki ɗai ɗai tsakanin Iyaye ko yayayen, kar a wayi gari a ce cikin Rayayyun yan uwa a rasa masu duba bayan abinda Ɗan uwansu ya bari.
Wlh ki farka ki dage da Addu'a ki kuma sa a miki Allah ya haÉ—a miki kan zuri'arki dan wlh cikin waÉ—annan Yayan naki Ahmad kaÉ—ai nake da tabbacin yau idan wani cikin sauran ya faÉ—i ya mutu baze bar zuri'arsa tayi kukan maraici ba, amma kinga wannan Uban namu da Salim? Allah ya rufa asiri kawai kawunansu kawai suka sani sedai Allah ya duba ya shiga cikin Lamarin".
Jikin Momy yayi laƙwas kamar an zubawa Salak gishiri, maganganin Maimuna sun shigeta kuma ta sani gaskiya ta faɗa a yanzu ne take nadamar rayuwar baya data zama kamar hoto bata taɓuka komai gurin gyaranmakauniyar tafiyar da akeyi a cikin gidan ba, a lissafinta idan taja nata yayan sun isa suyi rayuwarsu sedai kuma ta tafka kuskure gashi kuma yanzu tana girbar abinta saboda wannan hanyar da Yayayen nata suka ɗauka ta kowa kansa ya sani ta samo Asali daga abinda suka tashi suka gani anayi a gidan nasu ne.
Maimuna na kurbar shayi tace
"Gara dai ki yi ta kanki kina kallo ita Harbutsatstsiyar gidan naku duk da rashin kan gadonta batayi saken da kan yayanta ya rabu ba kuma komai da ita suke shawara bakinsu ɗaya ke kuwa fa? Banda Ahmad wa yake zuwa ya durƙusa gabanki ya faɗa miki halin da yake ciki ko ga wani abu da zeyi?"
"Allah ya rufa asiri dai Maimuna, gama cin abincin mu fita rana ta farayi kuma yai Juma'a ki samu ki gama da wuri" da haka suka bar zancen.
Ahmad kuwa bayan fitarsa Kusan karo sukaci da Hajiya dake fitowa daga É—akinta da tabarma a hannunta da alama shimfiÉ—a zatayi ta zaunasana'ar tata ta sakawa masu shiga da fice idanu.
"Aa, Amadu har ka fito kenan" ta faÉ—a fuska a washe ba kamar É—azu dayace .ata Zasuyi tafiya tareda Alhaji ba.
Cikeda gajiya da tambayoyinta yace
"Na fito Hajiya, na gaya miki Alhaji yana jirana tafiya zamuyi"
"Ayyo to, da ai da Yakubu zasuje,sedaga baya Yakubun yace yana da aiki nace ma suje da Faisal shi kuma wai tes zeyi a makaranta ashe kai ya kira banda Alhaji seya tattagoka tun daga Abuja base ya ɗauki Direba yayi tafiyarsa ba? Shikenan dai, ya akayi yau naga ka shigo mana gida hannu na dukan cinya babu yar tsarabar daka saba riƙowa ne?"
Ahmad yai zuguÉ—i yana kallonta se kuma ya zabura daya tuna abi da yake gabansa ya tafi yana cewa
"Idan mun dawo zan kawo muku" ya wuce da mamakin Hajiyar, tsarabar da kullum ya kawo haka zata amshe tana aibata shi tana masa shaguben Allah sa da kuÉ—in Halal ya siyo shine yau tambayar bata gani ba?.
Hajiya ta bishi da kallon tsana ƙarara tana jan ƙwafa, ta tsani Yaron ya kuma zamar mata ciwon ido dan ta rasa ya zatayi dashi. Yanzu da Alaƙa take ƙara Ƙarfi tsakaninsa da Alhajin ya sake dagula mata lissafi ba kuna zata lamunta ba duk yanda zatayi setabi gurin datseta tun kafin tayi ƙarfi. Ko yanzu da gayya take ta jansa da magana saboda ya ɓata lokaci har Alhajin ya fito yayi masa tijara burinta kenan ba wani abu ba.
A gurguje ya shirya, wata dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya ya saka ta haska Fatarsa dake da duhu bacan ba ɗinkin babbar riga ne, be sakata ba ya riƙe a hannu da hular da ze saka da Agogo, Takalmi da Azurfa, cikin sauri ya fesa turare ya fita da silifas a Ƙafarsa. Alhaji na tsaye bakin motar da zasu tafi a ciki an kawo masa ita daidai Barabder yana waya da alama Ahmad alamu sun nuna Ahmad kawai yake jira kenan.
Cikin tsantsar ladabi jikinsa har rawa yake ya durƙusa yana gaida Alhajin, wata Kafirar Shaddace data sha aiki na Alfarma a jikin Alhajin, yanayin ƙirarsa ga shigar da yayi ta ƙasaita yasa kwarjininsa nunkuwa tamkar wani Basarake. Ba yabi ba fallasa ya amsawa Ahmad gaisuwar kafin yace masa
"Ya haka zaka fito kamar wanda aka koro?"
"Babu komai Alhaji, daman so nake sena shiga mota sena ida shiryawa".
Harara Alhajin ya maka masa, yasan abinda yake nufi dan haka sum sum ya shige falon ya shiga ƙarasa shirinsa. Tsaf ya fito bayan ya kafa hula Babbar rigar ce dai be saka ba saboda karta yamutse kuma takura masa ma zatayi, data son ransa ne ma Normal Kaftan ze saka na yadi ba shadda ba sedai sanin halin Alhajin tsaf idan yayi shigar da bata gamsheshi ba dizgashi zeyi gaban jama'a babu ruwansa. Shi Mamaki yayi ma da Alhajin ya nemi ya rakashi wata unguwa me muhimmanci irin wannan domin be taɓa ba, Yanzu da sabgogi sukawa Su Zakariyya yawa Yakubu ne abokin rakiyarsa ko Faisal, wani Sa'ilin har Lawan ɗauka yakeyi ya rakashi be san dalilin daya saka Alhajin nemansa ba.
A kunne motar take dan haka yayi bismillah ya shiga, Alhaji ya gama sallamar Balarabe me ban ruwan Fulawa kafin ya buɗr gidan gaba kusada Ahmad ya zauna yana hailala, wannan kuma haline klda su Naziru ze fita a gaba yake zama. A ɗarare Ahmad daya gama karanto Addu'ar hawa abin hawa ya taka motar suka tafi, a tare suka ringa ɗagawa masu aiki dake musu Allah ya tsare hannu, Alhajin me halin tsiya dana kirki kenan, a ɓangaren mu'amala da mutanen waje bashida matsala. Duk qanqantar mutum in har musulmi ne yazo giftashi zeyi masa sallama har ya bashi hannu suyi musabiha barshi dai da halinsa idan ya motsa wannan kam kowa ma yi masa yakeyi.
Tafiya sukeyi babu me cewa komai in banda karatun Alƙur'ani da Ahmad ya kunna can ƙasa yana bi a hankali. Jefi jefi Alhajin yake amsa waya, wata ta kasuwanci wata kuma Abokanansa ne masu tambayar ko ze samu halartar ɗaurin auran bikin ɗan Abokinsa ne da sukayi makarantar sakandire tare. Sun miƙe hanya sosai kamar daga sama Ahmad yaji Alhajin yace
PAGE 12
"Rayuwa kenan, duk waɗannan da kaji muna magana dasu a sanda mukayi makaranta ƙyamatarmu sukeyi saboda su lokacin a gaban Iyayensu suke mu kuwa Almajiranci aka kawo mu Kano, naci da dagiya tasa muka Shiga Bokon amma yanzu dubi ka gani kowanne cikinsu so yakeyi yayi alaƙa damu, bakaga roƙon da Alhaji Mustapha ya ringayiwa Babanku Alƙali akan ya ɗaga tafiyarsa Umarah yaje masa ɗaurin aurannan ba, Allah kenan wato shiyasa duk yanda mutum yake karka rainashi dan baka san me ze zama a gaba ba, a lokacin suna ganin su yan gatane se gashi a yanzu da Yan Bokon cikin su da Yan Kasuwar babu wanda ya zarce nida Ɗan uwana" Alhajin ya faɗa cikin Alfaharin abun.
Murmushi Ahmad yayi, be tanka ba dan Alhajin yakanyi magana shi kaÉ—ai wani sa'ilin, ya tabbatar idan so yakeyi ya bashi amsa kai tsaye ze ambato sunansa a cikin maganar, to mema zece masa shi?
Yana wannan tunani kuwa yaji Alhajin ya sake cewa
"Ya aikin Super market É—in kuwa? Jiya Asiwaju ya kirani yana ta zuzuta gurin yace har yafi na Kano girma da tsari ko?"
"Ina ga dai kallon tsoro yayiwa gurin gaskiya amma befi rabin na nan Kano ba, kawai dai yanda aka fitar da taswirar ginin ne yasa ya ɗauki hankalinsa, an kusan kammala komai dan har an fara zuba kaya ma, yace so yakeyi a buɗe ranar Bikin haihuwar Yarsa, daman na bari sena dawo ne se muyi maganar" Ahmad din ya bashi amsa yana shafa kai domin ko Legos ɗin baje baniyyarsa daga Zariya idan ya dawo Kano seya bi jirgi. Ginin sabon Shopping Mall sukeyi wanda wani Aminin Alhajin Asiwaju Bayerabe Attajirine a birnin Ikkoh ganin yanda Bechi Mall ya samu karɓuwa a Kano yasa yace Ahmad yaje ze bada fili suyi haɗin guiwa ya sake gina Bechi Mall a Lagos ɗin gashi har an kusa kammala komai se abinda baza'a rasa bane ya rahe a gurin.
"Ai tun daga plan daman da gani kasan ginin ze bada ma'ana, Allah ya sanya Albarka yasa a buÉ—e a sa'a. Maganar kayayyakin mu kuma idan kuna ka samu Idi kuyi yanda kuka saba".
"In sha Allah" Ahmad ya faÉ—a daga wannan seda suka sake shafe kusan minti talatin suna sharara gudu a titi kafin Alhajin ya sake cewa
"ÆŠan uwanka fa? ya tafi ne ko yana nan har yanzu?"
"Aa ya wuce tun ranar Litinin, be kira waya bane?" ya faÉ—a yana satar kallon Alhajin. Shiru yayi harya fitar da ran ze amsa masa kafin yaji yace
"Kai kafi kowa kusanci dashi ka ringa masa faÉ—a kana nuna masa rayuwa shi yaro ne har yanzu baze gane abinda ake son nuna masa ba. Saboda nayi masa faÉ—a nasan uwarsa ce ta zugashi tace ya dena kirana ko? To ka jaddada masa wallahi, muddin na sake samun labari makamancin wanda ya faru sena a nan ze gane ni ba abokin wasansa bane, kuma daga ranar ya bar buga Ball".
"In sha Allah zan sanar masa, hakan ba zata sake faruwa ba" Ahmad ya amsa masa dan a yanda Alhajin yake magana ya hasala in kuma yace ze fahimtar da shi ya wanke Jafar daga laifin dayake zargin ya aikata yasan rufta kansa zeyi duk su hadu suyi laifi a gurinsa amma banda haka a bune a buɗe kawai dan shi Alhaji besan me duniya take ciki ba shiyasa ya ɗauki abin da zafi. Rape Allegation ai ya rigada ya zama ruwan dare akan Celebrities, Matan sun maida wannan harkar samun kuɗi a shekara Ɗaiɗaidaikun Manyan Celebrities ne suke tsallake sharrin Mata ba tareda kaji ance anyi ƙararsu akan sunyi Molesting wata ba abinda ya faru da Jafar kenan wata yarinya tayi Ƙoƙarin ɓata masa suna akan yayi Raping nata shi Alhaji har se bayan ma anyi case an gama yarinyar ta Ƙaryata kanta har kotu ta yanke mata hukunci kafin can ya gano tsohon labarin a Jarida.
Shine dalilin tattago Jafar yazo gida babu shiri, sunga Tijara daidai gwargwado wanda hakan yayiwa da yawa daga cikin Ahalin gidan daɗi dan Alhaji kulle ido yayi ya wanke Hajiya tass ita da ɗan gaban goshinta. Cewa tayi ita bataga laifi ba idan ma Jafar ya aikata abinda kace yayi, ubanwa ya kai yarinyar gurinsa?/ ko janta yayi ta ƙarfi? Basu suke bibiyarsa kamar jela yana yakice su ba banda ma rainin hankali Maza nawa ta buɗewa ƙafa se shi data raina take bibiya da sharri zatace ya mata Fyaɗe shine fa Alhaji ya zazzage mata tijara a tsakar gida yace ba zata saka yaje ya zubar masa da mutunchi a duniya ba. Abu ɗaya yasaka ya sassauta masa be tsaurara mataki akansa ba saboda sunan Bechi da be jona a sabgar ƙwallonsa ba, ba kowa nema ya san Ɗansa bane banda Close Family and Friends da yawa Muhammad Yayanta sukewa kallon Babansa dan dashi ake ganinsa ko Biography ɗinsa kayi searching it only shows Abdullahi Tijjani As his Father's name Nationality kuma Nigerian from Kano shikenan. Daƙyar Alƙali ya kashe maganar Jafar ya koma ashe Alhajin be haƙura ba.
Sun isa Haɗeja Lafiya kai tsaye fadar sarkin Haɗeja sukayiwa tsinke inda a can za'a ɗaura auran. Alhaji Mustapha Babandede yayi matuƙar jin daɗin ganin Alhaji Alhaji Audu Bechi, suka riƙe hannun juna ana gaisawa yanda Alhajin ya sake da tsofaffin Abokanansa ana gaisawa cikin barkwanci ya bawa Ahmad mamaki, koda yake daman hakane, duk girma da wani matsayi da mutum ya kai a rayuqa idan ya shiga cikin waɗanda sukayi gwagwarmayar Karatu tare se kaga duk an koma yara ana tuna baya. To tare akaci daɗi aka sha wuya, lokacin da kowa be gama fahimtar tanadin da ubangiji ya masa a rayuwa ba.
Yakubu ya taɓasu labarin daya kai Alhajin taron Tsofaffin ɗalibai a ranar har rawa yayi, wai hana yin video akayi shiyasa be ɗakko musu ba abun ya basu mamaki suka ringa hakaito Alhaji yana rawa wane irin farin ciki ne haka ze sakashi ya taka se gashi yau Ahmad yaga makamancinsa a fuskarsa dan Dariyar da Alhajin yakeyi harda ƙyaƙyatawa abin ya tashin kansa ya kuma sake tabbatar da Abotar makaranta tana da wani ƙarfi da tasiri na daban sama da sauran Abota, an girma shekaru sun taru amma idan aka haɗu se a ringa ji kamar an koma bayane.
Se bayan da aka ɗaura auren a gurin Reception ya haɗu da yayayen Abokanan Alhajin waɗanda suka kawo iyayensu. Wasu ya sansu suna hulɗa wasu kuma ranar ya fara ganinsu, Basu bar Haɗeja ba se ƙarfe huɗu bayan sunyi sallar La'asar kafin kowa ya kama gabansa. A hanyar dawowa Alhaji ya ware yana masa labari irinsu "kaga wane? Lokacin da muna makaranta fa kaza da kaza amma yanzu kalli kaza ya faru" Ahmad ya lura Alhajin na cike da shauƙin ganin tsofaffin Abokanai shiyasa yau harya maidashi abokin hira.
"Ya kamata ku motsa ku fito da mata kuma tunda ƙannenku mata sun tsaya shiririta. Kasan ban fiya mayar da hankali gurin gayyato tsofaffin Abokanai na na ƙuruciya sabgar auren yayana ba amma ina ganin wannan karon har Gala Nigh zan shirya mana ta yanda zasu zo su kwana musha hira kafin ranar ɗaurin aure" Alhaji ya fada.
Ahmad ya shafa ƙeya da hannu ɗaya yana murmushi me kama da dariya, wato su Alhaji har Gala Night za'ayi lallai abin nayi ne, shi kuwa Alhaji yanayin nasa se yasa yayi zaton kunya yaji da yace su fito da Mata tunda yau a giya tara yake yan mutunchin na kusa se yace masa
"Toakwai ta a ƙasa kenan irin wannan murmushi da kake bugawa, Yar gidan wacece?"
"Ƙuuu" cikin Ahmad ya kaɗa, maganar tazo masa a bazata, ba tanan ya shirya tasota ba. Ya rigada ya gama tsara takan Baba Alƙali zebi shi ze kaiwa maganar auransa kai tsaye tunda dai shima Alhajin idan maganar ta tashi shi ze wakilta amma yanayin nasa neman auran yasa gara ya fara samunsa dan ya tayashi gyarota idanma matsala ta shirya afkuwa yanzu kuma Alhaji na nema ya titsiyeshi, be kuma san ya ze ɗauki maganar ba idan ya sanar masa da wadda yake nema musamman da yaji ya tambayeshi Yar wacece kenan yana tsammanin ze samo yar wani Attajiri ko ƙusar gomnati wanda yana faɗar sunansa ze gano wanenene?
"Kayi shiru, ko babu ne?" Alhaji ya sake faÉ—a yana kallonsa. Harda rage gudu Ahmad yayi kafin ya saci kallon Alhajin yaga shi yake kallo shima sannan ya haÉ—iye yawu yace
"Wata yarinya ce Fatima, a Marmara gidansu yake amma cikin lungune se anyi tafiya kamar za'a shiga Alfindiki, Mahaifinta Bakanikene yana gyaran mota da babur Amma kafin ma na fara zuwa gurinta seda nayi bincike wlh mutumin kirki ne kwarai da gaske haka ma ita yarinyar tana...."
"Ban tambayeka halinta kona mahaifinta ba ko kuwa kai ne zaka mun binciken halin waÉ—anda zan haÉ—a surukuta dasu?" Alhajin ya dakatar dashi muryarsa dai kadaran kada han babu farin cikin da yake ciki dazu haka babu zafin da kai tsaye Ahmad ze zarce cewa be aminta da abinda yazo dashi ba.
Tamkar Ahnad yace
"Ai naga kamar su Yaya Naziru su sukayi binciken Matan da zasu aura shiyasa baka hanasu ba" se kuma yayi azamar kwabar zuciyar dake neman kwanto masa ruwa ya shiga taitayinsa, Ya sauke ajiyar zuciya tareda yin shiru Alhajin ya sake jefa masa wata tambayar yace
"A ina kuka hadu da ita?"
"A Shago, sunzo siyayya tare da Yayarta" ya bashi amsa a sanyaye Alhaji ya sakeyin shiru kafin ya kuma cewa
"Ita yayar tata budurwa ce ko matar aure?" Se Ahmad yayi saurin cewa
"Matar aurece, Dan gidan Balarabe Faranshi take aure ma yaranta uku yanzu" ya shaidawa Alhajin harda sunan uban Mijin Anty Sauda domin ya sanshi, dukda ya rasu amma har yanzu akwai manyan Yayansa da suke huldar kasuwanci dasu, dabararsa hakan zesa Alhaji ya fahimci ba a gidan banza ya nemo mata ba.
Alhaji ya muskuta yace
"Marmara? Ina ganin Musbahu ne kamar naje Ɗaurin auransa a nan masallacin sarki idan ban manta ba shekaru bakwai kenan yanzu dan tsiran auran da shekara ɗaya Alhaji Balaraben ya rasu. Amma yarinyar daya aura shi ai kamar Baƙar buzuwa ce dan ban manta ba na halaci Dinner da Alhaji Balaraben ya haɗa musu"
Rai fes Ahmad yace
"Itace, mahaifiyarsu ce Buzuwa amma mahaifinsu haifaffen nan Marmaran ne duk yan uwansa anan tsukun suke yaran ne dai sukayi kama da Mahaifiyar tasu shi yasa idan aka gansu se a dauka Buzaye ne"
"Wato farar fatar ce da dogon gashi suka ruÉ—eka ko?" Alhajin ya faÉ—a fuska babu wasa yana tsare Ahmad da ido nan ya diririce murnar da yake ta koma ciki, cikin in ina yace
"Aa wlh Alhaji kawai dai.."
"Kawai dai me? Da ba Suhaima yar gurin Alhaji Lamin kake nema ba?" Alhajin ya dakatar dashi. Tamkar ze fasa masa kuka yace
"Ni daman ita ta ke sona, kuma daga baya tace ita ba zata zauna a Nigeria ba tunda yan gidansu sun koma US sedai na bita can nima abinda ya rabamu kenan"
"Eh anyi haka, naji yayyenta biyu ma duk auransu ya mutu da sukace zasu bi uban su koma can da zama, Lamin,Lamin ban san kalar kwayar da yake sha ba. Haka kawai ya tattara wai shi ya bar Nigeria banda shirme waÉ—anda suke a wajenma idan girma ya riskesu dawowa gida suke su mutu cikin Ahalinsu se shi ze tattara ya koma can, to ita kuma Safiyyah yar wajen Goggonka Salaha fa?" Alhajin yayi kiÉ—ansa ya taka rawarsa lokaci É—aya.
Ahmad da gaba ɗaya ya gama shigewa ruɗani, da fari abu kamar ze zo a sauƙaƙe amma kuma yana neman yayi wahala Alhajin se wani kale kalen magana yakeyi, ta maza yayi dan duk ji yake kamar ya fashe da kuka ko Alhajin ze barshi da zaɓinsa yace
"Ai ita Abbanta yace yayi mata Miji, Momy bata gaya maka ba auran ma saura wata biyu yanzun ma Anty Maimuna tazo siyan kayan Lefe ÆŠan Mijinta ne wanda Safiyyan zata aura"
"Wato sun hanaka zasu bawa ÆŠan Mijin Maimuna, kai dashi waya fi kusanci dasu?" Alhaji yayi maganar cikin faÉ—a Ahmad besan sanda ya É—age kai da hannu biyu ya saki sitiyari ba yana cewa
"Wallahi tallahi ba hanani sukayi ba, gajiya Abban yayi da jiran kuje ayi magana kuma daman ya rigani fara nemanta seda ma Anty Salahan tace a fasa dashi Mony ce tace Aa ba za'ayi haka ba tunda dai ya riga a bashi"
"Baka da hankali zaka saki mota?" Alhajin ya buga masa tsawa se ya nemi gefw ya faka, Allah yasa babu mota dake biye dasu gab kuma ba gudu yake sosai ba shiyasa daya sakwta bata watsasu wani gurin ba. To fisabilillahi kamar wanda aka ritsa a Kotu Alhaji se zabga masa tambayoyi yakeyi yana muzurai ba dole ya manta abinda yakeyi ba?
Shiru ne ya biyo baya, babu kalar addu'ar da Ahmad beyi a ransa ba akan Allah ya sassauto zuciyar Alhaji ya amince da buƙatarsa babu ja in ja.
"Tada motar muje gida, zamu ƙarasa maganar a can" Alhajin ya faɗa bayan daya mula. Jiki ba laka Ahmad yaci gaba da tuƙi, har wani zazzaɓi yake ji yana shirin saukar masa domin yanayin Alhajin ya nuna koda ace ze yarda da batunsa tofa se an kai ruwa rana.
Sun shiga Kano anyi magriba, a kusada wata Majalisa yace ya tsaya ganin suna hada jam'i da alama makararru ne nan suka yi alwala suka bisu. Bayan sun idar ganin Alhaji na lazumi Ahmad ya tsallaka inda yaga wani me gasa Nama yayi sa'a akwai wanda sukayi nan da nan yasa aka shiga yanka masa kashi kashi aka gama tsaf ya basu kuɗinsu yara suka kai masa mota ya sake jido fruits ya ƙara daidai nan Alhaji ya shafa Addu'arsa ya taso suka cigaba da tafiya.
Har bakin falonsa inda ya ɗauke shi ya tsaya da motar Alhajin ya sauka yana Hamdala, filin gidan tarwai da haske tamkar idan allurarka ta fadi zaka ganta. Sarah ce ta fito da Dogon Hijabi da alama aikenta akayi tana ganin Ahmad ta fasa ihun murna ta ɗaleshi, Alhaji ya zabga mata harara kafin ta sauka da gudu ta koma cikin gida se ga gayyar Maimuna da Yan biyun Anty da Mariya tareda Zayyad ta kirasu suka dabaibayeshi suna sowa da murna ga Yah Ahmad ga Yah Ahmad bakinsa ya gaza rufuwa ya ringa ɗaga wadanda ze iya yana saukewa kafin ya buɗe Boot ya shiga fito da ledojin ciki tun a gurin yasa aka ware dan haka ya danƙawa kowa ta ɗakinsu Hatta su Issa dake nan tsaye yayo musu kashinsu suka karba suna murna dayi masa Addu'a, ya gama rabon tsaf ya rage ledoji biyu a hannunsa, Alhaji na tsaye har sannan be shiga ciki ba yana kallon Ahmad.
A cikin Yaransa Ashirin da takwas ya fita daban kyautatawarsa ba kadan bace baga su iyayensa ba ga kowa daya rabeshi se yayi sambarka da halinsa, se yake ganinsa kamar shi a zamanin ƙuruciyarsa.
"Ina nawa Naman toh? Tun ɗazu nake haɗiyar yawu a mota" Alhajin ya tambaya fuska a tamke kuma, Ahmad ya ƙarasa gabansa ya rusuna yana miƙa masa Leda yace
"Fruits É—in idan an gyara se a kawo tunda kafi so a matse"
"Allah yayi Albarka" Alhajin ya faɗa bayan daya karɓi ledar, cikeda farinciki Ahmad ya amsa da "Amin" domin yasan alfanun Addu'ar iyaye, ita take dabaibaye dashi yake ganin haske a rayuwarsa. Tasowarda yayi kamar hadari yayiwa jama'a da yawa rumfa a matsayinsa na matashin Ɗan kasuwa, buɗe shopping mall ɗinsa ya saka kasuwar wasu da yawa tayi ƙasa badan tasirin addu'ar iyayen ba ai da yanzu maƙiya sun kaishi ƙasa.
Da kansa ya kaiwa Momy tata ledar kafin ya wuce ɗaki yayi wanka yayi sallar Isha'a dan an rigada anyi a masallaci. Ya ɗan jima a zaune yana azkar da be samu yayi ba a hanya kafin ya sake shiga cikin gidan yana tafe yana kiran layin Fatima wadda tun suna Haɗeja ya kirata basu wani yi magana me tsayi ba se yanzun yake sake so yaji ya take ya kuma ce ta tura masa da Kwalliyar Juma'ar da duk sati seya roƙa kafin ta bashi.
Busy yaji layin nata a ransa yayi tunani ƙila da yan gidansu take waya shi kansa badan tafiyar da yayi ba yau ya kamata ya leƙa ya gaida Baffa dan kusan duk sati indai yana Kano ko Fatima bata nan se yaje ya gaishe su, yanzun babban abinda yake a ransa jiran jin amincewar Alhaji game da maganar auransu wanda kuma a jikinsa yana ji in Allah ya yarda ba za'a samu matsala ba fatansa daya Allah yasa kar Alhajin yayi zancen da Hajiya har ya gaya mata yar wa yake nema ita kaɗaice a cikin gidan yake da tabbacin zatayi Adawa da auransa da Fatima domin ta tsani TALAUCI da TALAKA, ya tabbatar kuwa muddin ta sani se inda ƙarfinta ya ƙare gurin ganin haƙansa be cimma ruwa ba na auran Fatima, ko ba dan komai ba ta samu hanyar rama tsaya mata a maƙwogwaro da yayi ya hanata rawar gaban hantsi, ya tabbatar zata shiga ta fita gurin ganin be samu abin da yake so ba amma Allah ya fita.
A haka ya shiga cikin gidan Hajiya Rabi na tsakar gidan tana bawa Baba Mairo sallahun abinda zata taho mata dashi wani satin idan zata zo, Baba Mairo dai me girkin gidan tun zamanin Hajiya na Amarya duk haifarsu akayi suka ganta a gidan bayan sun dawo nan Hotoro GRA kusan shekaru Ashirin kenan, wannan tazarar tasa bata biyo su ba saboda har yanzun Mijinta yana raye yana kwance yana Jinya se ya zama se sati sati take zuwa tana girkin Sadaka ana biyanta dukda girma ya kamata yanzun amma macece me lafiya da kazar kazar sannan aikin na rufa mata asiri shiyasa bata saki duka ta daina ba.
"Yaya Ahmad, an dawo" Antyn ta faÉ—a kamar yanda yaran gidan suke kiransa tana murmushi, ya sunkuyar da kansa shima yana murmushin yace
"Tun dazu Anty, har nayi wanka naje sallah ina wuni" ya gaisheta bayan daya idasa kaiwa tsugunne ya sake kallon Baba Mairo da bakinta yaƙi rufuwa da ganinsa yace
"Iya, ina wuni? Ya jikin Baba?"
"Lafiya lau Alhaji, Malam jiki da sauƙi Alhamdulillahi ko da zan fito seda yace na gaishe ka na kuma ƙarayi maka godiya. Na dai barwa Hajiyar tsakiya sallahu da aka ce baka nan amma naji daɗisosai dana ganka mun gode Alhaji Allah ya saka da Alkhairi yaci gaba da yalwata arziƙi ya kuma rabaka da Alhaji Babba da Hajiya lafiya".
Anty ce ta amsa da Amin fuskarta a washe ta tabbata halin nasa yayi musu na Alkhairi, kyautar Ahmad irin wadda Annabi yace ayi ce, ka bayar da hannun dama ba tareda Hagunka ma ta gani ba, ya miƙe yana sake cewa Anty
"Ina Aboki? Dana dawo da safe banshi ba ina sauri shiyasa ban shigi na dubashi ba"
"Ai bama nan ma da wuri na fita ma kaishi Allura seda muka dawo Momy tace ka shigo amma kun fita da Alhaji, yana ciki rigima yake tayi tunda akayi allurar bari Hasna ta kawo maka shi ko zaka shiga?"
"Bari na leƙashi to ance idan anyi allurar ba'aso ana jagwalgwalasu ko ƙila zafi take masa" ya faɗa yana nufar ɗakinta. Tun daga wajen falon kuwa yake jiyo kukan Abdallah Autan gidan a yanzu me watanni uku kuma shine Ɗa na shida da Antyn ta haifa. Babban Ɗanta Musa da suke kira Mu'allim nada shekara goma sha takwas yanzu, se yan biyu mata Husna da Hasna masu shekaru sha biyar sannan Mariya me goma Zayyad me shekaru takwas sai kuma Abdallah data haifa watanni uku baya.
Fadar tashin hankalin da akasha da Hajiya akan cikin nan bata baki ne dan tabbas Allah ya hakunta zuwan sa badan haka ba iyakar baƙin cikin da takaicin da Anty ta ringa sha na Hajiya da gori da cin mutunci akan tazo tana ta zuba yaya saboda taci gado yar matsiyata yaci ace cikin ya bare kota haifi yaron da lalura se gashi Allah ya bata lafiyayyan Ɗa kuma Namiji abinda ya sake gigita Hajiyar ta ringa abu kamar wadda ta zauce, Allah kaɗai yasan da yanda tasha kan Alhaji haka ya saka Antyn a gaba taje Asibiti aka juyar mata da mahaifa wai da shekarunsa rututu ga manyan yaya abin kunya ne ace har yanzu ana haihuwa a gidansa yana haifar Ƙannen Jikokinsa badan Manyan Yayan Alhaji Babannan da Babangida duk Mazane ba da yanzu ma ya fara aurar da jikoki itama Antyn tace daman ko bece ba ta gama haihuwar.
Karɓan Abdallan yayi daga hannun Mariya dake jijjigashi yana cewa
"Ya haka, me yasa yake kuka kuma?"
"Wlh Yaya Hasna ce ta ja masa ƙafar da akayi masa allura wai zata fi saurin saki shine fa yake ta kukan nan". Ahmad ya harari wadda aka kira da Hasna ta sunkuyar dakai kafin yace
"Banda cin zali ya za'ayi kija masa ƙafa? idan ke kikaji ciwo aka taɓa miki ya kikeji hum?"
"Kayi haƙuri Yaya" ta faɗa tana sadda kai ƙasa, yayi tsaki kafin ya juya da yaron ya fita Husna Usainarta tace
"Wlh Naso Yah Faisal ne ko Yah Salim da kinji a jikinki banza muguwa kawai.
A falon Momy da Ahmad ya shiga ta karɓi Abdallah tana cewa
"Meya samu babana tun É—azu nake jiyo kukansa kuma dai shi baya kukan banza?"
"Wai Allura akayi masa" ya bata amsa bayan daya sake gaiaheta.
"Wayyo, Babana yau ansha ƙarfe, yi shiru kaji kar suyi mana dariya ace tsohona rago ne, Allah ya taimaka bata saukar masa da zazzabi bama zuwa safiya in sha Allahu ze ware" ta faɗa tana zare masa dogon wandon dake jikinsa ta cire masa Diaper da aka matse masa cinya tana sake cewa
"Da gani wannan aikin Hasna ne uwar raino yau kam ai a ɗaga masa ƙafa da wata Diaper a barshi yaji da sagaggiyar cinya" tana cirewa kuwa ya dena kukan ya shiga wulla ƙafa, Ahmad yayi murmushi yace
"Babu baki, ƙila ma duk abinda ya takurashi kenan yake ta kukan haka su kuma basu sani ba, ina Anty Muna badai ta wuce ba?"
"Ka ganni Amadi sallah nayi kai nake jira ka shigo musha hirar yaushe gamo" Anty Maimunan ta faÉ—a tana fitowa saga Bedroom É—in Momy. A nan yaci abincin dare tareda Salim da tunda garin Allah ya waye se sannan ya shiga falon ya zauna da Momyn suka gaisa kuma yana gidan wuni sur sallar Juma'a kawai ya fita ya dawo wai bashida lecture a makaranta shine ya wuni bacci. Har gurin sha daya kafin Ahmad yayi musu sallama ya tafi makwanci ransa cike da mamakin abinda ya samu wayar Fatima yana zaunen ya kira yafi sau goma amma still busy ake gaya masa, abin ya bashi mamaki dan layinta akan tsarin call waiting yake in dai wayace da zasu gaya masa sedai idan a DND ta saka wayar ko kuma a kashe take sharrin Network yake ce masa busy, haka ya kwanta duk yanajin babu daÉ—i ga kewar muryarta duk ta cikashi danya saba koda ba wata hirar soyayya suke ba amma yana jin daÉ—in magana da ita a haka bacci yayi awon gaba dashi.
FATIMA
Ƙarfe ɗaya harda mintuna suka gama Ajin ranar dan Lecturan nacewa yayi akan se yayi covering abinda ya rage mana sannan yayi fixing musu test ranar Monday saboda Next week ake saka ran fara First Semester exam. Sanda suka fita har an fara tafiya Masallaci, tayi murmushi tana kallon yanda Mazan Makarantar suke tafiya a sahu cikin shiga me kyau a fili tace
"Allah mun gode maka da kayi mu musulmai, dan Allah Badar kalle su, ina son Juma'a a school É—in nan ranar ne wanda ma baka taba zaton musulmi bane zaki ganshi da Kaftan ya tafi masallaci".
Haka suka ringa hira suna ratsa mutane har suka isa Hostel. A gurguje suka yi Alwala, cikim postgraduate Hostel suka fita zuwa masallacin yau basu samu ciki ba saboda sun makara dan haka a waje sukayi sallar kafin suka koma É—aki.
Ta kira yan gidansu suka gaisa a wayar Baffa dan har sannan ba'a gyara wayar Ummansu ba, yaran Anty Sauda na gidan ta ɓata lokaci sosai suna magana dasu harda Autar Goggonsu Faɗima da taje gidan hutun makaranta. Tana gama wayar kiran JAY ya shiga, tayi ƙaramin tsaki kafin ta sauka daga kan gado saboda hayaniyar mutanen ɗakin sunyi baƙi Jama'ar Sururat kunsan mutanen Yarabawa badai ɗaga murya ba idan suna magana.
Guri ta samu me kyau ta zauna kafin ta duba wayar yayi mata two missed calls, kusan Minti goma tana jira ya sake kira dan tace ita ba Asararriya bace da zata kira layin waje da Katin Ahmad, harta fidda ran ze kira se ga wayar ta shiga Ringing bata ko tsaya dubawa ba saboda yanda zuciyarta take azalzalarta da son jin wannan muryar tasa ta kai wayar kunnenta sedai Muryar Ahmad tayi mata sallama ba wadda tayi tsammanin ji ba.
A taƙaice sukayi magana dan rabta babu daɗi dalilin ta tsammaci JAY ne, ya gaya mata yana Haɗeja ya kai Alhajinsu Biki dalilin tafiyarsa da sassafe kenan maganar batayi tsaho ba sukayi sallama yana kashewa kiran da take ta zaman jira ya sake shigowa.
Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi har ranta taji daɗin da ta kasa tantance na menene amma dukda haka seda taja aji wayar na dabda katsewa kafin ta daga
"Hello Baby" ya faÉ—a da muryarsa me tsinka daskararren jini kota daskarar da tsinkakken to itama dai daskarar da nata jinin yayi dan hatta bakinta ji tayi ya mata nauyi ta gaza furta komai seda ya sake cewa
"I'm sorry, Assalamu alaikum".
A hankali taja numfashi kafin ta amsa masa daga nan ta sakeyin shiru.
Jay dake tsaye gaban Mirror cikin katafaren Bedroom ɗinsa yana taje Quater Million Sajen dake kan fuskarsa yayi ƙaramin murmushi kafin yace
"How are you my love?", zare ido tayi kamar tana gabanshi kafin cikin tsiwa nace
"when did i become your love? Don't call me that again"
"The first time i set my eyes on you, i know you are my lost but found true love" Jay ya faÉ—a yana É—aura agogo, fita zeyi, kiran da ya mata bata É—auka ba shine ya shiga wanka yanzu ya fito yana shiryawa ya sake kiranta.
Baki ta tura amma kalamansa sun mata daÉ—i, wato da confidence yake komai nasa babu wani É—ari É—arin irin na Ahmad shi gaba gaÉ—i yake faÉ—ar abinda yake a zuciyarsa.
"Hey sweet, are you there?"
"Uhm" ta iya furtawa kawai dan ta rasa bakin magana. Ta kasa gane kanta da wannan stranger É—in, bala'in jin daÉ—in magana dashi take kusan zata iyacewa a class hankalinta duk yana kan wayar da sukayi da Asuba, bata sanshi ba bata san waye shiba ba amma har cikin ranta ji take kamar sun shekara dubu tare.
"I'm going out, dama na kira ne naji muryarki nayi miki barka da Juma'a, i might be late out though, will you wait for me ba zakiyi bacci ba har na dawo muyi magana?" Jay ya faɗa tamkar me barwa matarsa sallahun ze fita wani guri, mamaki ya sake kasheta amma cikin tsiwa kuma ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta tace
"To ni meye haɗina dakai kuma da zanƙi bacci na jiraka?"
"Abinda nake so muyi magana akai kenan, ina so kisan meya haÉ—aki dani yau" ya bata amsa a tsume jin zata fara masa rashin kunya, wai kuma se shakkarsa ta shigeta harta gyara harshenta tace
"Karma ka kirani dan bacci na zanyi koma zan kashe wayar kawai tunda kai idan ka fara kiran mutane se kace sunci bashinka baka haƙura se an amsa"
"Wait for me please" ya faɗa da taushin daya saka ta ɗaukewa na sakanni, yayi miskilin murmushi, ya gama gane lagonta ba ita kaɗai ba yammata da yawa muryarsa na cikin abinda yake saurin kassarasu shiyasa ya laƙanci salo salo da yake amfani dasu gurin ladaftar da masu kunnen Ƙashi irinta.
"Will you?" Ya sake faɗa da sautin dayafi na farko taushi, tsikar jikinta ta hau zuba, kai ta ringa ɗagawa kamar Ƙadangaruwa kawai kafin dakyar tace masa
"Toh, amma kar yayi dare da yawa"
"Till i call, bye, I love you" ya sakar mata maganganun kafin ya kashe wayarsa. Taji I lobiyu tabi kashi Miliyan amma bata taba jin wadda ta gamsar da ita irin wannna da bata da tabbacin da gaske yake ko ƙarya ya sharara ba.
Da yamma ta suka fita karatu sai bayan Magriba suka dawo rabi da rabin hankalinta nakan Jay dayace ze kirata, dukda yace se dare amma fata take ya sake kira da yammar. Suna hanya Nurain ya kirata akan ya shigo Makarantar.
"Ina my Badar? Wayarta baya shiga?" Ya tambayeta. Ta saci kallon Badar data ƙurawa hanya ido kamar me neman wani abu kafin tace
"Gata muna tare, ka jiramu a white sit mun kusa isowa"
"Alright Bestie" ya kashe wayar.
A nan gurinsa suka lalace suna hira har gurin tara dukda hankalin Afeeya rabi da rabi ne a gurin Badar ce suke kurɓar madarar soyayya da Habibin nata ayi faɗi. Tara da rabi tace ita zata shige ciki yunwa takeji Nurain yace suje su siya abinci a Baescope.
"Wlh ba zamuje ka sake yarfamu irin na ranar nan yau ban fito da kuÉ—i ba" Afeeyah ta faÉ—a yayi dariya yace
"Haba da kenan, yanzu ko wani na gani ze yanƙwana Baby na Badar ai se inda ƙarfi na ya ƙare balle nida kaina.
Suka tafi a motarsa, a can sukaci ya siya musu Ice cream suka dawo.
"Bestie meya faru ne? Fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa?" Nurain ya tambayi Afeeyah ganin duk walwalarta ta gushe. Tunda suka je gurin yake lura da yanda ta tsume abincinma tsakurarsa tayi bayan ita tace tana jin yunwa jefi jefi kuma tana duba waya tana tsaki.
"Babu komai Bestie I'm just too tired, bari na baku guri dan nasan Badar tsuntsun soyayya baze barta ta gaji ba" ta wuce Badar na zaginta.
Harta gama shiri ta hau gado badan tana jin bacci ba sedan ranta babu daÉ—i Jay be kira ba kamar yanda yace. Ta rufe idonta tana jin kamar ta fasa kuka, su Ummi suka tambayeta lafiya tace kanta ne yake ciwo kowa ya mata sannu suka barta.
A zabure ta miƙe jin wayarta ta fara ringing, a jikinta taji cewar shine, ta dire daga kan gado tana neman hular da zata saka takalmi ma wari da wari ta zura ta fita har suna karo da Badariyyah.
"Wai Afeeya wane salon munafunci kika samu na ba zakiyi waya a ɗaki ba?" Badar ta faɗa tana riƙe Ƙugu, Afeeyan ta harareta tace
"Yo aike ke tashen munafunci yanzu, ki gama cika baki Allah ya sawwaƙa me zaki ci da Bestie na ashe mu kika mayar shashashu kuna can kuna tsinke furen ƙauna"
"Ya ranki?" Cewar Badar tana fari da ido, Afeeya ta girgiza kai kawai ta fice. Dukda dare ga uban sauro haka ta samu wani saƙo ta lafe ta bi kiran Jay daya katse, be amsa ba ya kashe ya kirata back
"Irin Ahmad ta raya a ranta" muryarta na amsa kuwwa a kunnenta ta manta da wani batun Amadi bawan Allah ta fuskanci Jafaru.
PAGE 13
"Assalamu alaiki" ya faɗa cikin murya me sauƙi kamar wanda yake cikin nishaɗi sosai. Ta amsa can ƙasa, yayi murmushin daya saka kunnenta fara Ƙaiƙayi kafin yace
"Na kiraki morethan ten times baki amsa ba, you are lucky ina cikin farin ciki yau amma da sena hukuntaki"
"Toh" tace masa,
"Oh toh ma zakice kawai? U are not apologing, Any way how is my sweet baby doing? Ya Juma'a?"
Ta karkace ta gyara zama kafin tace
"Komi lafiya"
"That's great" ya bata amsa se sukayi shiru na kusan minti biyu kafin ya sake cewa
"Afeeya, i hope you remeber me?"
"Nidai idan zakayi magana ka dena kiran sunana and i don't remember you i don't think we have ever met" ta faÉ—a da shagwabar da batasan tayi ba saboda yanda yake kiran Afeeyan gaba É—aya wani yanayi yake sakata.
"Babe karki Kashewa Hajiya ni da wannan shagwaɓar taki" ya faɗa, yanda yaja Babe ɗin ya sakata jin wani sanyi yana ratsa mata ɓargo har seda ta haɗe jikinta tanayin kamar kanta na hayaƙin shauƙi. Allah ya sani Ahmad na iyakar yinsa gurin riritata yana faɗa mata kalaman soyayya amma batajinsu kamar na wannan mutumin.
"We met on Monday, kina sauri zaki tafi class i followed you to your department a gurin Class Rep naku na samu number ki so you are this popular ina cewa Afeeyah yace ya sanki, i hope you are known for the good not for the other way?".
Shiru tayi masa dan idan yana magana bata so ya dena, sautin muryarsa is killing her,
"Afeeyah" ya kira sunanta ta amsa da
"Uhm".
Shiru yayi kafin yaja numfashi yace
"Kafin muyi nisa Afeeya let me make this clear to you, ina da saurin fushi like the smallest thing you couldn't imagine can trigger my temper. Na tsani na yiwa mutum magana yayi shiru ko ya amsa mun da uhm ko body language, I prefer kayi mun magana ko zagina zakayi and bana son nuƙu nuƙu da boye boye na tsani ƙarya da munafunci, i love bold and straight forward person in dai kika kiyaye wannan zamu zauna lafiya, lastly I'm a lover boy, i love to be loved and be pampered, kinga idan kina riritani kina shayar dani madarar love na rantse har Ƙafarki zan ringa lasa tsabar biyayya".
Bata san sanda ta tuntsure da dariya ba saboda maganarsa ta ƙarshe wai lashe ƙafa kamar wani maye kai wannan mutum da abin dariya yake ma wlh. Tayi dariya sosai shi kuma yayi shiru yana sauraronta seda ta gama dan kanta tace
"You are so funny wlh"
"Some times" ya bata amsa kafin ya sake cewa
"I should make a proper introduction of my self now. Sunana JAFAR but the world knows me as JAY, Bahaushe ne ni haifaffen Kano amma rainon Turai, na bar Nigeria when i was 13 na tafi Manchester nayi joining Football Academy. I'm a professional footballer, shekarana 11 ina taka leda yanzu professionally, I'm currently playing with Arsenal, ina buga number 7 or 9".
I'm from a polygamous family, inada siblings da yawa sosai i think that's all that you might want to know now about me for now, may be with time zaki ƙarasa sanin komai a kaina".
A duk bayanin nasa babu abinda yayi catching attention É—inta kamar sunansa da kuma profession dinsa, JAFAR kuma FOOTBALLER? Samun kanta tayi dace masa
"Kai kaÉ—aine Jafar musulmi kuma dan Nigeria da yake buga kwallo a Turai?"
"No bani kaɗai bane, akwai Jaybee a Tottenham se Jay Jay a Leinster, but they are all half Nigerians me yasa kika tambaya?" Ya maido mata seta sauke wata ƙarfaffar ajiyar zuciya yanda kasan wadda aka ritsa da bindiga ta samu ceto koda yake da tunanin da yake zuciyarta ai har gara ace bindigar ce, indai ba mantawa tayi ba Jafar ƙanin Ahmad ma ƙwallo yake yi a turai idan ya zama shine Jay da take magana dashi ai sheƙe kanta kawai zatayi ta mutu, zuciyarta ta aminta da cewar Jafar ɗin Ahmad yana cikin ɗayan biyun waɗancan daya faɗa ko Jaybee ko Jay Jay tunda bata san mamanshi ba, ta yuwu halfcast ce kamar yanda yace suɗin half Nigerians ne amma ba wannan JAY ɗin bane ba, babu yanda za'ayi ya zama JAY ma.
A yanzun haka suna da aikin da sukayi sharing da Jafar ɗin yasa kaso Arba'in na zumuɗin da takeji akansa ya disashe, zuciyarta har wani harziƙowa tayi da tunanin abokin faɗan nata, Jay da yaji shirunta yayi yawa yayi gyaran murya yace a sanyaye kamar bashi ba yace
"Afeeya lafiya kikayi shiru ko da akwai wani abu ne"
"Babu komai, kawai sunanka da profession dinka sunyi kama da na wani abokin rigimata" ta bashi amsa, muryarsa har ƙara sauti tayi kamar a fusace yake tambayarta
"Wanene shi? Meye ya haÉ—aki rigima da Namiji?"
"Cousin ɗina ne" ta samu kanta da yanko wannan Jibgegiyar ƙarya da seda ta faɗa sannan takaicin kanta ya kamata to saboda me zatayi masa ƙarya? Haka kawai taji bazata iya ce masa ƙanin saurayinta bane ba, daga can Jay ya sauke numfashi yana cewa
"Your cousin is a footballer too, wane club yake?"
"Nima ban sani ba, amma kamar a Arab countries ɗin nan yake" ta faɗa saboda last tima kamar daga Qatar taji Ahmad yace yazo shiyasa ta bayar kawai tacan Arab countries yake ƙwallon. Bata taɓa ganinsa a fili ko a hoto ba balle ta kwatanta masa shi, a waya suka taɓa magana sau ɗaya wadda yaci mata mutunchi se jefi jefi idan yana gari ta kan jiyoshi tareda Ahmad har ya gasa maganganu itana ta rama. Har sannan murya babu walwala Jay ya sake ce mata
"Oh i see, i hope there is nothing between you two? Bama shi ba da farko if you know you are committed to relationship wanda iyayenki suka shiga tell me?"
"Babu" ta bashi amsa a sanyaye kamar me tsoron yace ya fasa kulata.
"Amma dai Mace kamarki ba zata taɓa rasa suitors ba, ina da kishi beyond your imagination. Bana so nayi sharing abinda nake so da wani, that is why i hate someone saboda the person stole the most precious thing to me" ya faɗa cikin jin haushin Fatiman Yah Ahmad kafin yaci gaba da cewa
If you know you are in to any relationship just call it to end saboda me guri yazo kowa ya tafi kawai"
"Late comer ya kwace maka budurwa ko?" Ta tambayeshi kishi na neman kamata itama.
"Forget it, kawai kiji abinda na gaya miki. Allah i will not accept sharing you with anyone. I love you fisabilillah and i want Marry you Afeeyah. I want to settle down hopely by the end of this year kuma dake nake so nayi aure will you do me the honor and be my beloved wife?"
Ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi, kalamansa sun shigeta har tsajiyar zuciyarta wani yamm takeji a jikinta. Cikin nutsuwa irinta wanda ya san kan soyayya da yanda ze farauci zuciyar mace a karon farko ya ringa tsarata. Tayi shiru tana sauraronsa, tayi nisa cikin hakaito kamanninsa, se ta ringa ji kamar kafin haɗuwarsu a makaranta. Sana'arsa data sani a yanzu ta bata satar amsa tabbas tana ganin fuskarsa a wasu guraren kamar posters, jikin Baburan Adaidaita sahu da sauran gurare. Ta tuna Sani Abokin Yayanta Jay ake masa dalilin son da yakeyiwa Ɗan ƙwallo Jay, amma ya akayi bata ganeshi ba? Koda yake ba wai kallon Ball takeyi ba shima shahararsa ce da kuma yanda su Yah Malam kullum basu da aikinyi se magana akansa tasa ta riƙe sunansa da fuskarsa amma kuma data ganshi a fili ya canza mata.
Be rabu da ita ba seda ya tabbatar ya isa duk inda ya kamata a cikin zuciyarta kafin yace taje ta kwanta dare yayi. Be tambayeta komai akanta ba, ta ringa jin wani iri, ta sani surah da kyan fuskar da Allah yayi mata ne ya ruÉ—i Jay zuwa gareta idan har yasan ainihin ita wacece tabbas ze gujeta, Sanannen mutum a duniya kamarshi bazeyi tarayya da yar Talaka kamarta ba balle har suje ga batun aure.
Yanda ya ringa nanata mata Hajiyarsa tana sonsa ya tabbatar mata da Mama's boy ne, yace a gidansu sunfi su Talatin, daga kuma few things daya faɗa mata akan familynsa ta fahimci suma suna da ire iren matsalolin da da yawan Manyan gidajen masu hannu da shuni wanda suka tara Iyalai da yawa suke fuskanta, wasu har a social media zakaga suna raba hali. Yanda ta fahimta suna da matsala irin ta yan ubanci a gidansu, ta tuna Ahmad shima gidansu suna da yawa amma kuma bata taɓajin ya gaya mata wata ɓaraka a tsakaninsa da yan uwansa ba, sudai Allah ya taimakesu toh.
Kwana tayi tana juya maganarsa da yake ce mata
"Amma kinsan san dana ganki banyi zaton zanji kinyi hausa ba because you look Asian, da akwai wata girlfriend da nayi Zoya she is from Korea amma Dad É—inta ne Korean mum É—inta is Arab from Iran so she has that Iranian look and Korean skin, oh my God you need to see her, i have never seen someone as beautiful as she is se ke dana ganinki kunyi kama sosai wlh tsayi kawai zata fiki".
"Ikon Allah" ta fada a zuciyata bangare daya kuma haushin wai girlfriend É—insa da taji ya ce ya kamata har bata san sanda bakinta ya furta
"Oh saboda nayi kama da Ex Girlfriend É—inka yasa ka kulani kenan?"
"Ko ɗaya, sanda nake tare da ita ma she was the one pushing the relationship and i supported her just because she was nice, Zoya was the most beautiful soul i have ever met in my life tana da kirki na ƙarshe ta so ni she really wanted to marry me kuma ko ni i lokacin idan da zanyi aure it will be her but unfortunately she lost her life in a plane crash ta tafi ganin Mamanta a Iran from London bata da lafiya tafiyan da bata dawo na kenan sukayi hatsari shekara biyu kenan and since then i remain single".
Ita da kanta ta yarda akwai mutanen da kirkinsu yake sakawa dole kayi mu'amala dasu kamar Ahmad, ta kwatanta a ranta ace shi ya mutu, irin yanda taji yasa tayi saurin kawar da tunanin daga raita
Washe gari dakyar ta iya tashi baccin da bata samu isashshe ba, sun daÉ—e suna magana da Jay a waya sannan data kwanta ta kasa bacci tayita bitar hirar da sukayi. Shida da rabi ta idar da sallah tana Azkar ya sake kiranta ta É—aga fuskarta da murmushin da batasan ma tanayi ba suka gaisa.
"Zan fita ne nace bari na fara kiran Baby na naji ya ta tashi, or you are still in bed?" Ya faɗa salonsa dake kassarata. A shagwaɓe tace
"Aa na tashi nayi sallah Azkar nakeyi yanzu".
"Kinyi mana addu'a ko?" Ya tambayeta ta É—aga kai kamar tana gabansa se ya sake cewa
"Zan fita Training ki kula da kanki i will call you when I'm back ok?"
"Allah ya kaimu" ta bashi amsa a sanyaye dan se taji bata so ya ajiye wayar. Be sake magana ba ya kashe tana ajiyeta kiran Ahmad ya shigo seda ta harari wayar kafin ta ansa.
AHMAD
Yana zaune a gefen gadonsa, shigowarsa kenan daga masallaci tun Asuba kwana yayi da tunaninta, tunda ya farka da Asubar yaso ya kirata amma ya daure ya bari gari yayi haske.
"Fatima, meya samu wayarki jiya taƙi shiga na kira yafi sau goma?" Ya faɗa bayan data ɗaga wayar. Muryarta a kumbure kamar me bacci alhalin haushine ya cikata tace
"Bacci nayi da wuri, kuma ban sani ba ta shiga DND se yanzun dana tashi na cire".
"Haba nayi mamaki duk hankali na kuma ya tashi amma yanzu na samu nutsuwa tunda lafiya kike, ya school É—in toh?" Ya faÉ—a har yana sauke ajiyar zuciya se kuma tausayinsa ya kamata wato So Jarabtace wanda Allah ya dorawa kaÉ—ai yasan wahalarsa gashi itama idan batayi da gaske ba tana neman afkawa komar wanda ze wahalar da ita.
Ta miƙe tana ninke sallaya tace masa
"Lafiya lau nake, ya hanya? Kun koma Kano ko can kuka kwana?"
"A cikin Kano mukayi sallar Magriba ma" ya bata amsa ta haye gadonta tana cewa
"Masha Allah kunyi sauri gaskiya toh sannunka"
"Yawwa kema sannunki" daga nan suka É—anyi shiru se ya sake cewa
"Bari na barki zaki koma bacci ko yau weekend nima cikin gidan zan shiga na gaida Momy se na dawo na kwanta an jima idan Allah ya kaimu zanje gurin Baffa kina da saƙo ne?"
"Aa, babu" ta bashi amsa se yace
"Toh shikenan ki kwanta we talk later"
"Bye" daga haka ta kashe wayar taja bargo dan bacci be isheta ba Badar ta fincike tana cewa
"Gidan uwar wa kika tafi jiya har sha biyu wayarki kuma bata shiga?"
"Not this early Badar bacci nakeji" Afeeyah ta faɗa tana sake jan bargon da taga zata takurata ta sakar mata ta janyo Hijabin data cire ta ƙudunduna duk kuma tsiyar Badar bata kula taba dan ita idan taso bacci babu abinda yake hanatayi dan mutum yaga dama ya dakko police band ya kaɗa baccinta zatayi sanin haka itama yasa ta barnta ta koma nata gadon tana cigaba da mita kafin tayi shiru tayi bacci. Se bayan Azahar da tayi wanka tana shiryawa ta lura da aika aikar da sauro yayi mata zaman da tayi a waje jiya jikinta yayi Jaa duk inda ya ciza ya tashi, Maman Minal tace
"Yauma cikin flowers kika je yin waya ko? Waini Afeeya wa kika samu da ba zakiyi magana dashi a É—akin nan ba se kinje cikin sauro?"
"Bari na dawo ke kaɗai zan bawa labari Anty Zahra tunda mutane yanzu kowa boye sirrinsa yake" ta faɗa tana hararar Badar ta gefen ido, ta aje turaren hannunta da take fesawa ta kwaɓe
fuska tace
"Nasan idan kuka sani sena tsani kaina saboda tsokanarku duk na gama cika baki wlh So be kyauta mun ba wlh".
Suna class Jay ya kirata lokacin wayar na hannun Badar ta shiga Ig tana duba styles na É—inkin da zasuyi da bikin Anty Yusra.
Ta miƙa mata wayar ta ɗaga ƙasa ƙasa tace masa
"I'm in class zan kiraka in mun fita" ta kashe.
"Waye kuma Jay kika samu?" Badar ta tambayeta bayan ta maida mata wayar, tayi fari da ido nace
"New catch, a big fish"
"Yaushe kika zama Money monger Afee?" Ta faÉ—a tana kallonta, Afeeyah ta zare ido tace
"Daga cewa Big Fish? To na janye ni ba abinda nake nufi kenan ba matsayinsa nake kwatanta miki, Professional footballer ne a Arsenal yake wasa ma"
Seta kalleta da sauri tace
"You mean JAY? No you must be kidding, Afeeyaj a ina ma ze ganki yana UK kina Nigeria? bama wannan ba JAY fa Afee, yes i know you are Beautiful, kin kai a soki but JAY noooo. A yanda nake jin labarinsa he can't date Nigerian girl Hausa for that matter. Shifa ko yammatan da ake ganinsa dasu se kin kallesu kin sake, irin models din nan ne da zakiga kamar su suka yi kansu sedai idan wani ne yake so ya yaudareki da sunansa dan ko a IG kika duba accounts masu sunansa sunfi dubu ma".
Kasaƙe tayi tana kallonta, koda ba laifinta bane gaskiya duk wanda tacewa JAY dai na Arsenal take waya dashi kallon batasan me take cewa ba zeyi mata amma dukda haka se tace mata
"Toh Badar ina shi Bahaushene me yasa za'ayi mamaki idan yaso Bahaushiya kuma lower class irina?"
"Yes Bahaushene Dan Kano nema aka ce amma abinda nake so ki duba shifa babban Celebrity ne, koda yake ke ba sabgar Ball kika sani ba amma da keda kanki idan aka ce miki shine sekin ƙaryata. Kamar fa kice min Messi ya kiraki ne ko Ronaldo".
Maganar Badar ɗin ta sakata tunani domin abinda ta faɗi yakan iya zama gaskiya tunda dai ita ba sanin wancan Jay na gaskiya tayi ba haka kuma wannan sau ɗaya ta ganshi sedai tabbas akwai kamanceceniya a tsakaninsu to amma menene ribarsa idan yayi mata ƙarya da sunan wanda ba shine ba?
"Dubo mun picture É—insa na gani indai shine zan gane" ta faÉ—awa Badar, seta kalleta kafin tayi dariya da alama cewar da tayi idan ta ganshi zata gane ne ya saka Badar dariyar.i
"Ashe kun haÉ—u face to face ma? ko hoto ya turo miki?" Tayi mata tambayar da sigar rainin hankaki ita kuma Innocently tace mata
"A school É—in nan fa muka haÉ—u Badar ranar Monday da ace kina nan kema da kin ganshi na fito zan tafi class da safe ya tareni kuma shine wanda Sahid yace ya bawa number ranar da muna tare dake".
Data fara dariya har seda hankalin Lecturer ya dawo kansu duk aka juya ana kallonsu babu ɓata lokaci kuwa ya korasu waje kuma har sannan ba wai ta bar dariyar bane guri ma ta samu ta zauna tana ci gaba da abarta dan harga Allah abin na Afeeyah mugun bata dariya yayi, Jay Afeeyah zatace ta gani a cikin ABU Zaria? Jay ne ze shigo Zaria ba tareda garin ya girgiza ba? Da ace Afeeyah na kallon Ball ko ta taɓa nuna ra'ayi akan Jay Footballer da se tace tsabar yanda ta kwallafa rai akansa ne har yasa ya fara mata gizo amma yanzu ta tabbatar wani ne yake so yayi mata wasa da hankali amma ya akayi har Afeeyah tayi falling wa cheap trick kamar wannan da sauri haka?
"Bana son iskanci Badar me kika daukeni ne?" Afeeyah ta faÉ—a a fusace se Badar ta nuna ta tace
"Da alama zaman da kikayi a waje kwana biyu kinyi gamo dan wannan maganar da kike batayi kama data me cikakken hankali ba". Ran Afeeyah ya ɓaci ta hayayyaƙo mata tace
"Wato kin gama akan Ahmad yanzu kuma kin samu sabo ko? Wani Badar me kika É—aukeni ne? Alfarma maza sukeyi mun su soni ko kuwa ban kai macen da za'a ce ana so ba?".
Kafin ta bata amsa Sahid ya kwaso da gudu kamar wani ƙaramin yaro har yana ture waɗanda suke fitowa daga class ɗin alamar an gama lecture ya tsaya a gabansu yana haki yace
"Afeeya i have been looking for you all round the school, na yesterday i remember where i know that Guy's face from, he is JAY Afeeya the great JAY of Gunners was in front of me but i couldn't recognised him God i was so stupid, definetly my village people are behind this misfortune but still I'm lucky and I'm happy that i gave him your number i hope he called? If yes please Afeeya do me this favour of introducing me to him as his ride or die fan wallahi....."
"Sahid haba mana ya isa" ta dakatar gashi ganin maganar bata da alamar ƙarewa s zuba yake kamar wanda kanda ya ƙone, a fusace ta sake maida kallonta kan Badar dan ta ƙarasa zazzaga mata abinda ke ranta rungunar da tayi mata tareda fasa ihu kamar zata toshe mata kunne bata ko damu da a waje suke ba ta shiga tsalle tama kasa magana kamar wata wawiya se ihu takeyi.
"Innalillahi Badar kinyi haukane ko yaya sakeni dan Allah karki kayar dani" Afeeyah ta faɗa tana Ƙoƙarin yakice Badar amma taƙi sakinta cewa takeyi
"Da gaske JAY ne yake son Afeeta innalillahi daÉ—i kasheni" ta sake fasa wani ihu Sahid na tayata yana mata rantse rantsen wlh shine, yau da safe ya kalli Recap na wasansu kawai ya ganshi shine ya tuna
"Amma taya akayi ya shigo harya fita babu wanda ya ganeshi se ku biyu?" Badar data tsagaita da ihub ta tambayeta, Afeetah tayi tsaki tana tafiya tace
"Seki nemo shi ai ki tambayesa, ni taya zanyi na sani?" a gurin ta barta saboda haushi ta tafi Hostel tana tafe ranta na suya akan abinda Badar tayi mata so takeyi dagaske ta yarda izgilanci yasa take mata irin waÉ—annan abubuwan amma zuciyata ta gaza karbar hakan.
Da gudu ta bi bayanta dan tayi nisa sosai, ta rungumeta har suna shirin faduwa tace
"Haba mana Afee wai fushi kuma kimayi?" wai dan Allah dagaske kin hadu da JAY? Kedai kina da sa'a Afeeyah ga Ahmad yanzu kuma ga Jay kin samu, na daɗe ina crushing akan JAY amma nasan nisan dake tsakanina dashi kamar nisan sama da ƙasa ne shiyasa na sahalewa kaina Afeeya ke me sa'a ce kina zaune yazo har inda kike ya tarar dake na miki murna Allah ya sakamu a danshinku Miji kam se kin zaɓa kin darje" ta faɗa idonta suna kawo hawayen da batasan na menene ba. Wani iri taji, can kuma haushin cewar da tayi Jay crush ɗinta ne shi yasa ta tureta tana cewa
"Ni dalla cikani, me kika gama cewa? ban kai kalar matan da yake kulawa ba wani ne yake mun ƙarya dashi"
"Afee ki fahimce ni, wlh ruÉ—ewa nayi. Kamar fa nace miki Shahrukhan ya kirani yana sona dan Allah zaki yarda kai tsaye?" ta faÉ—a da iyakar gaskiyarta, Afeeyah ta fincike hannunta tana cewa
"Ai ni ba shahrukhan nace miki ba, Jafar nace Bahaushe kamata dan Kano kinga kuwa ko sarkin ingila ya zama ba abun mamaki bane dan ya so wadda suke da tushe daya. Sannan naji kamar kince crush É—inki ne ko? Gara da kika faÉ—amun tunda wuri ba se anyi nisa kizo kina mun ihu da hayaniya a gaban mutane a kansa ba saboda kishi. Zan gaya masa kina sonsa Allah yasa ki masa tunda yanzu na gane ko Nurain da kike mun masifa kina hanani haÉ—uwa dashi ashe son sa kikeyi".
"Karki gaya mun maganar banza Afeeya saboda ma kinga ina lallabaki shine zaki ringa botsarewa bafa ke kadai kika iya tijara ba" Badar ta faɗa tana ja baya yanda fuskarta ta nuna lallai taji zafin abunda Afeeyah ta faɗa mata. Itama seta riƙe ƙugu tana kallonta ta sake cewa
"Na faɗa ɗin ko ba haka bane? Duk sanda Nurain ze kirani kin ringa baƙin rai kenan kina bin bini se kinji me muke cewa ba zaki taɓa barina na fita gurinsa ni kaɗai ba haka Ahmad a koda yaushe cikin gasa mun magana kike kina nuna ban kai ba Alfarma yamun daya soni haka kullum cikin yaba kirkinsa kike da nuna da zaki samu kamarsa ba zaki tsaya sokonci iri na ba and now Jafar kai tsaye kin gaya mun he is your crush duk hakan me yake nufi Badariyya?"
"Meye haka Afeeyah lafiya kuke taaye kuna hayaniya akan hanya? Abdurrazaƙ course mate ɗinsu daya ƙaraso gurin ya faɗa. Badar data kasa cewa komai tunda Afeeyah ta fara magana ta tsaya kawai tana kallonta ta sauke ajiyar zuciya kafin jiki babu kwari ta fara tafiya ta barsu a tsaye.
"Yanzu Afeeya saboda abun kunya keda Badar za'a gani kuna faɗa a kan hanya? Ai koma me ya haɗaku kamata yayi kuje ɗaki ku sasanta amma ba anan ba gaskiya kun bani kunya kuma da alama kece bakida gaskiya dan naji wasu daga cikin maganganun da kikeyi" Abdurrazaƙ ɗin ya sake faɗa. Ajiyar zuciya ita ma ta sauke, bata ce masa komai ba ta juya itama ta tafi, Ribadu Hall ta shiga gurin Islam, ƙawartace tsohuwar Roommate dinsu kuma. Ta kwanta akan gadonta duk tana jin babu daɗ kuma akan abinda ya faru amma ta rasa abinda yasa ta kasa controlling kanta duk abinda ya tunzurata kuma cewar da Badar tayi Jay crush ɗinta ne sosai takejin zafin abin a ranta har sannan akan me zata faɗi haka bayan da tasan suna waya kuma hakan yana nufin maganar So ta shiga tsakaninsu?
Islam ta dafa Indomie ta juye a plate kafin ta hau gadon tana cewa
"Tashi muci, in Badariyyah na ganki ke kaÉ—ai? Koda yake nasan faÉ—a kukayi.
"Naqoshi, kuma wayace miki faÉ—a mukayi?"
"Ai tunda na ganki ke kaÉ—ai kinzo kin kwanta kamar Manja daman nasan da walakin indai ba bata school ba to faÉ—a ne kawai zesa ba'a ganku tare ba kuma kece da laifi wato har yanzu dai ba zaku canza hali ba kamar kaji kullum se kun raba hali? Da ana ganin kamar kece abar tausayi Badar ce rigimammiya se wanda ya zauna daku ne ze gane halinki tsaf Afeeyah baki da daÉ—in sha'ani idan baki so ba"
Ƙaramin tsaki tayi tace "You know how Badar can be annoying, rainin wayonta ya fara yawa wlh shiyasa nake kasa yin shiru yanzu"
"Yes i know, amma Afeeya kin fita zafin kai maganar ta gaskiya. Na san Badar da faɗa amma da wuya tayi akan rashin gaskiya ke kuwa kina sane kike fitittikewa kiyi abu duk kuma yanda mutum ze nuna miki kuskurenki se kinga dama zaki yarda" Islam ta faɗa calmly. Afeeyah tayi shiru dan tasan gaskiya ta faɗa ko a gida haka Ummansu take cewa tanada rikicin gangan kamar yanzun dai in dai gaskiya ne be kamata maganar Badar ta batamata rai ba amma bata san me yasa take hasala ba duk sanda irin hakan ta hado su dukda cewar koda da gaske tana goranta matan ne batayi ƙrya ba, bata kai matsayin da Maza masu Aji kamar Ahmad da Jafar zasu ringa karakaina akanta ba. Ko a layin ƙawance tsakaninta da Badar ɗin kanta akwai tazara matsayinta na yar Ex Sanetor ita kuma ɗiyar me gyaran mota.
"Ke kika takaleta ko?" Islam ta sake tambayarta, a taƙaice ta faɗa mata yanda sukayi da abinda ya haddasa faɗan,
"Ke É—ince ai baki iya magana ba Afeeyah ga rashin fahimta kuma da gangan kikeyi"
"Yanzu ko wani ne yace miki Badar zata so saurayinki Afeeyah seki yarda balle harke da kanki ki ringa wannan tunanin? Gaskiya kin bani kunya lamarinki kuma ya fara shallake hankali. Tabyaya kina zaune da ita for good three years amma ace babu trust a tsakaninku? kin taɓa kamata da laifin cin Amanarki ko me da zaki ringa wannan tunanin akanta?" Islam ta faɗa cikin fushi kamar wata Mamanta. Ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace
"To amma Islam aikin san yanda kullum take mun akan Ahmad, ke kanki shaida ce tasha faÉ—ar da ita ta sameshi da tuni wata maganar akeyi yanzu ba wannan ba"
"To ai ko ni zan faÉ—a miki wlh dani Ahmad yake so Afeeyah da yanzu na haihu ma a gidansa, dan bazamu rufa six months da haÉ—uwa ba zamuyi aure. Ke kinsan yanda samun Nagartaccen Mijin aure yayi wuya kuwa? Ki ajiye maganar wasata samun me nutsuwa wanda idan ya aureka ze mutuntaka ya mutunta iyayenka ma kaÉ—ai sunyi wuya balle harda Bonus na Tsabar dukiya ga kyau ke kuwa me kike nema a duniyar nna da baki samu ba kike ta bulayi?
Let me be prank with you Afeeyah, ki ga wannan Jay kikace ko waye da kika samo yes babban mutum ne world class Celebrity, you can flight with him and get popularity amma zancen aure tsakaninku Afeeyah karki fara saka shi a ranki. Tabbas Allah yakan haɗa soyayya tsakanin duk mutanen da yaso matsayi ko wata nasaba ba zata zama togaciya ba amma kece kike yawan faɗin kin fi so ki auri Miji daidai ke wanda babu me miki kallon kwaɗayi ya saka kika aureshi ko kuma a ringa ganin yafi ƙarfinki, idan ban manta ba kince mun dalilin daya saka baki bawa Ahnad dama ba saboda kina ganin tazarar dake tsakanin Families ɗinku kamar idan maganar aurenku ta tashi za'a iya samun matsala shine yanzu kike so ki saka kanki a soyayyar wanda criticism na fan kaɗai ya isheki kafin aje ga nasa Familyn da baki san waɗanne iri bane ba? Think twice, Afeeyah, kiyiwa kanki Hisabi kafin ki fara abinda zakizo daga baya kina dakin sani.
Samun Ahmad da yardar Ahalinsa seya fi miki sauƙi akan wannan sabon mutumin da naga alamun kinyi nisa a cikin soyayyarsa. Kinsan Ahmad kin San duk abinda yakeyi, yana mutuwar sonki idan kika aureshi wlh kin gama dacewa dan kin samu mijin kerewa sa'a amma wannan ɗan ball da kike hasashe kinsan yaya ɗabi'unsa suke? Shin yana da hali me kyau ko kuwa? ace duk kin tabbatar da wannan kin ma kin aureshi wlh yanda kike da bala'in kishin nan iyakar matan da zasu ringa bibiyarsa kaɗai se sunsa kinyi mutuwar tsaye. Soyayyar da kike kwaɗayi ba zaki sameta ba kuma baki isa kiyi ƙorafi ba yana da damar yin duk abinda yaga dama.
Ya rage naki kiwa kanki karatun ta nutsu tunda wuri, sannan tun wuri idan kin tabbatar ba auran Ahmad zakiyi ba to ki bar mana filin mu gwada sa'armu tunda ke kanki baya kawo wuta dakyau, lissafinki a gaba a baya kikeyinsa".
Ido Afeeya ta zubawa Islam tana auna duk wata magana da take fada amma da kyakykyawan ma'auni bata bari zuciyarta ta kawo mata shirmen data saba ba dan idan haka kawai ne tsaf zata fassarata akan kawai tana so ta rabata da Jafar ne maganar ta ta ƙarshe ta saka ta zabura jin wai ta barsu su gwada sa'arsu akan Ahmad. Tayi rau rau kamar zata saka kuka tace
"Duk ku ba zaku gane ba"
"Daman ba zamu gane ba mana se ke da kika sakawa kanki abinda yafi ƙarfinki kece zaki gane ai" Islam ta faɗa. Afeeyah tayi shiru me tsayi tana saƙa da warwara. Tabbas auran Ahmad ze fi zama abu me sauƙi fiye dana sabon masoyinta. Amma Jafar take so, ta yarda zuciyarta ta mace akansa Ahmad kuwa koda ta aureshi sedai ta zauna dashi tukuicin kyautatawarsa gareta da iyayenta. Cikin rauni tacewa Islam
"Amma yana sona, shifa ya tareni kuma ya nemi number na ya kirani yace yana sona aurena zeyi"
"Shi wa?"
"Jafar"
"Afeeyah kenan, daman zece yana sonki mana, kuma zata yuwu da gaske yakeyi amma kuma ba iyakar son ba kiyi tunanin me soyayyar zata haifar miki? Amma tayaya za'ayi mutumin daga haÉ—uwa lessthan sati guda ki kamu da soyayyarsa har haka? Ko daman kin sanshi ne?" Islam ta tambayeta. Ta rintse ido fuskar Jafar nayi mata gizo kafin ta buÉ—e tace
PAGE 14
"Ban san shi ba ban kuma taɓa ganinsa ba se ranar. Ni kaina Islam bansan ya akayi ba na kamu da sonsa har haka ba. Ta yuwu kodan yayi daidai da tsari da kuma mafarki na akan Abokin rayuwa shiyasa"
"Kiyi addu'a idan da Alkhairi a tsakaninku Allahya tabbatar amma ki cire son rai a yayin da zaki nemi zaɓi a gurin Allah kuma ki dena wannan halin na zargin wata zata kwace miki abinda kike so sannan ki lallaɓa Badar wlh Afeeyah samun mutum da ze soki tsakani da Allah kamar ita a yanzu yana da wahala"
"To ni yanzu taya zan bata haƙuri kinsan dai Badar sanda kake lallaɓata sannan zata botsare ta fara rashin mutunchi ni kuma ba zan jure ba sena tanka mata"
"Tunda kece baki da gaskiya kuwa haka zaki yi shiru ko zaginki zatayi, yanzu ki kirata tazo nan ku sasanta tun wuri ma ba se kun koma ɗaki ku sake raba hali ba a ringa yawo daku a baki" Islam ta sake faɗa ta kalleta da son jin ƙarin bayani ta yamutsa fuska tace
"Eh mana, ce miki akayi duk wanda kake dariya dashi me sonka ne tsakani da Allah? A aji ranar ina jin Ummi na hirar kuna ce mata tana yawo bayan kuma abinda kukeyi kenan ko kuwa samarin da suke kashe muku kuɗi ƙannen babanki ne da zasu ringa muku bauta ba tareda suna benefiting komai a gurinku ba"
Take ta sake hasala tace
"Ita Ummin take cewa haka?"
"Bana faÉ—a miki bane saboda kije kiyi tashin hankali, ke matsalarki kenan bakya cin ribar zance da an faÉ—i abu kamar wuta fuu zaki tashi se daga baya kizo kina regretting action naki I'm only telling you so that kusan zaman da kukeyi da kowa kuma ba komai zakuci gaba da sakin baki duk sirrinku kuyi ta faÉ—a a É—aki ba, ai dai tun muna tare nake muku wannan faÉ—an daga ke har Badar kun fiya saurin yarda da mutane baku da sirri".
Tilas ta kira Badar dan ta yarda da gaske bata kyauta ba ta ringa bata haƙuri bayan tazo, Badar bata da ruƙo, sha yanzu magani yanzu ce dan haka take ta zazzage mata abinda yaje ranta maganar ta wuce. Ta dai gaya mata wlh koda wasa ta sake maimaita mata abinda tayi zata nuna mata bawai bata da zuciya bane ko kuma ita kaɗaice me baƙin rai, zata fita a harkarta dan bazata cigaba da zama da ita Alhalin zuciyarta bata aminta da ita ba. Gurin Islam suka wuni, Badar bata iya boye abinda yake a ranta tayiwa Afeeyah murna akan Soyayyarta da Jay amma tace
"Afee karki sakashi a ranki sosai saboda gudun abinda zeje ya dawo. Muyita addu'a idan shine Alkhairinki Allah ya tabbatar amma magana ta Allah nafi sonki da Ahmad sedai idan kuma za'abi ta suna Jay ɗin nan fa ze ɗaga mana aji, ganinmu za'a ringayi muna cafkewa da world class Celebrities, Allah kenan sega Badar zata haɗu da JAY a ɓagas, kinga su MESSI duk zasu zama Abokanmu wayyo Allah na" suka ringa dariya, Afeeyah jinsu takeyi ta tabbatar gaskiya suke faɗa mata amma kuma zuciyarta ta rigada ta afka ga koginda fitowarta se anyi da gaske.
******************
"Naziru kalleni dakyau nayi kama kama da wawiya da zaka zauna kana tsarawa wannan zancen na kama? Ni ba surutun banza da iska nake so naji ba, kuɗina zaka bani maza ka zuba munsu anan" ta warware ƙaramar Ghana Must Go dataje da ita kafin taci gaba da cewa
"Maza maza kana ɓatamun lokaci daga nan janguza zanje an yanka wasu filaye zanje na siye na ajiye abuna tunda lamarin ƙannenku babu Allah yan iskan yaya sun zama ɓarayi, yaron nan Faisal da Jafaru yaƙi bashi kuɗin shine yabi dare yayi mun sata, ni banma san nawa ya ɗauka ba dan lissafi ya kwace mun tunda naga haka nace toh ba yanzu ya saba ba, daman na daɗe ina ganin kuɗin nayin ƙasa se in ɗauka ajiya ce ta saka sikayi laushi. Kuma fa kwana suke cikin sanyi yanda kace, kaji ɗakin kuwa kamar dusar Ƙanƙara zata zubo....."
"Haba Hajiya, ki tsahirta mana karki ƙware" Naziru ya dakatar da hajiyar dake ta zuba kamar nunanniyar kanya kafin yaci gaba da cewa
"Na gaya miki Hajiya yawan shige da ficen da kuɗi sukeyi a personal account ɗina yana neman ya jawo mun matsala. Kinsan dai yanda EFCC yanzu suke saka idanu kan duk wani motsin manyan kuɗi a ƙasar nan, na gaya miki ba'a account ɗin company suke ba kuma ko a nan ne ke account ɗinki idan aka tura kuɗaɗen nan wlh suna iya rufeshi azo bincike ki saka kanki a matsala. Haƙuri zakiyi kamar yanda nace zan ringa ciresu a hankali ana juyawa se a ringa tura miki da kaɗan ko Miliyan ɗaya ce duk wata".
"Ai shiyasa nazo da jaka tashi zakayi mu tafi bankin ka ciremun kuɗina na gaji da wannan ƙarairayin naka kullum bayan Alhaji Zakariyya ya gaya mun ya karɓi nasa ni kake so ka cuta kenan ka cinye mun kuɗi to baka isa ba" Hajiyar ta faɗa cikin ɗaga murya. Naziru ya dafe kai, ya rasa bayanin da zeyiwa Hajiya ta fahimceshi, saboda Allah tayaya ze tura mata Miliyan ɗari uku ko kuma ya cirosu ya zuba mata a Ghana Must Go a wannan halin da EFCC ta matsa ko da account ɗin kamfani cikin takatsan tsan suke abubuwa balle aga kuɗi irin haka suka fita daga personal account ɗinsa ai tona masa asiri zatayi.
"Hajiya shima kayan kuɗi ya karɓa ba zallarsu ba kuma kiyi haƙuri ki dena ɗaga murya mutanen gidan sunajinki" ya faɗa a tausashe. Ta zabga masa harara tace
"Ni kuɗi na nake so, waima kayan uban wane kuɗi kuke magana akai kamar wasu marasa gaskiya haka yace mun wai kaya ya karɓa su kayan basu da suna ne bayan Mai akwai abinda ka fara siyarwa ban sani bane da ake samun kuɗi saboda mugunta baka gaya mun ba balle na gwada nima?"
"Zinare ya karɓa na gaya miki na fara haƙar zinare a Zamfara ai"
"Dan ubanka da akace dutse yana ruftowa mutane so kake ka mutu saboda rashin godiyar Allah zaka zurƙuma cikin rami wai haƙar zinare Naziru?" Hajiya ta faɗa tana zare ido kamar ance mata dutsen ya rufta dashi. Ya kalleta, da ace watace daban daya tambayeta a duniya waya kaita son zuciya amma uwarsa ce duk iskancinsa baze kwatanta haka ba se yayi murmushi yace
"Bafa da kaina nake shiga ba Hajiya kamfani ne suke haƙan da injina kuma jari kawai na saka ina karɓan ɗanyan gold se na fitar a sarrafashi"
"To nima ina so a saka kuɗin, amma ni idan an haƙo gida za'a kawomun abuna in ajiye se yayi tsada sannan na fitar na siyar sarƙoƙina ma zan kwashe su idan zan tafi Umarah Turai tace sunfi daraja yanzu acan zan siyar se in baka kuɗin a ƙara jarin yanda za'a ringa samu da yawa. Wallahi fa ance kuɗi akeyi sosai da harkar nan, kaga yaro bashi da ko taro amma dayaje ya shiga rami ya dawo kaga ya zama Miloniya wannan tubda da Inji nema za'a haƙo sedai muna zaune muyita karɓar kaya toh haka za'ayi, amma bani ko Goma ce yanzu na tafi da ita dan na saka rai zan siyi filayen nan har nace a dubamun na bakin Titi zasu fi daraja idan an kwana biyu".
Naziru ya sauke ajiyar zuciya jin ya tsarata kuma ta hau kafin ta sake botsarewa ze san abinyi. Dole ya shirya suka fita Banki ya cire 10M aka saka mata a Ghanarta ko tsoro bataji ta haye Napep wai ta tafi Janguza, dayace ze kaita cewa tayi Aa, a dabararta karyaje yaga inda Filayen suke. Yakubu sau biyu yana sace mata Takardun Manyab Fikaye yaje ya siyar, dake bata mantawa da komai nata har gewaya take zuwa taga lafiyar kadarorinta ɗaya taje taga an yi gini har An saka Amarya ɗayan kuma Plaza akayi tayi masifar tayi bala'in ƙarshe tayi Allah ya isa dan Yakubun taurin kaine dashi kamar me kuma hauragiyarta ba tsorata shi take ba, sa'idar data samu yanzu matsayinsa daya ƙaru a Kamfani, sedai shegen Yaron kamar yanda take faɗa kansa kawai yake Azurtawa. Ko sun so ayi cuwa cuwar da aka saba ya kankane komai ya hana ta tabbatar idan suka matsa kuma kamar yanda yake cewa tsaf ze fasa ƙwai, rabuwa dashi tayi yanzu amma tana nan zatayi maganinsa yanzu maganar auran Hajiya ƙarama data taso ce a gabanta daia Abba Tee har iyayensa sunzo anyi tambaya shima Yakubun Aure zeyi.
AFEEYAH
Sannu a hankali soyayya da shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakaninta da Jay, wani irin so take masa da bata san iyakarsa ba, kodan ya dace da duk wani mafarki nata akan Mijin da take so t aura ne oho?
Ahmad da kansa ya gane cewar akwai wani al'amari a gabanta wanda ya sake karkatar da hankalinta daga kansa saboda yar hirar da yake samun dama sunayi ma yanzu gagara takeyi, duk sanda ze kirata uzuri zata bashi na tana wani abun musamman da suka fara Second semester exam daga tace masa karatu takeyu se ta gaji zata huta alhalin lokacinta karankaf yanzun na Jay ne, karatun kansa ba wani mayar da hankali takeyi kamar da ba da idan akace zasu fara exam da sati ɗaya ma ta dena hawa Social media tattara hankalinta take tsaf har se sun gama sannan to wannan karon kuwa se a hankali, idan tana waya da Jay manta kowa da komai takeyi bata ma son abinda ze katseta se su raba dare suna magana har se da kansa yace ta kwanta tayi bacci dan bata faɗa masa ma mun fara exam ba seda sukayi guda huɗu ya rage uku su gama sannan ranar kuwa tasha fada ta kuma ƙara tabbatar da Jay baya ɗaukar nonsense dagaske kamar yanda yake cewa.
Har yajin kiranta yayi na wuni guda aikuwa taji a jikinta dan ya mata mugun sabo da soyayyarsa me tsayawa a rai. Jay ya iya soyayya, ya iya saka mace ta manta kanta duk taurin zuciyar Mace idan ta shiga hannun Jay tilas ta sallama dan yasan duk wani lago na mace da ze karya ta dashi, ita da kanta ta kance salon Jay da Ahmad yana kama. Tabbas da ta bawa Ahmad dama ta buÉ—e masa zuciyarta ze mallaketa tsaf ta yanda wani baze samu matsuguni ba amma ta rasa abinda ya hanata yin hakan, ta yuwu dalilin zuwan Jay ne, wani lokacin se taji muryoyinsu har kamanceceniya yake mata kawai dai ta Jay tafi ta Ahmad tashi, haka idanunsu iri É—ayane, seda tayiwa hoton Jay kallo na tsanaki ta fahimci haka idanunsu iri É—ayane, shape É—insu, kalar kwayar idon da komai Badar tace mata wai Sexy Eyes kenan masu irin idanun sun iya soyayya kuma dasu suke cafke zukatan Yammata ta yarda da hakan dan bata iya haÉ—a ido da Ahmad se taji gabanta na faÉ—uwa duk sanda ta kalli idonsa ji take kamar ta sallama masa amma taurin kai irin nata ya sa har aka kawo i yanzu.
Saura kwana biyu su gama Exam ranar Ahmad ya kirata, kwana biyu ya bata space tunda tace masa Exam sukeyi idan ya kira bata ɗaga ba kota amsa ta bashi uzuri sosai ransa yake sosuwa shiyasa ya zaɓi daya barta ta gama exam ɗin idan har da gaske itace uzurin daya saka baya samun lokacinta. Tana kwance duk batajin daɗin dalilin yajin kiran wayar da Jay ta daka mata, tunda ya fahimci Exam suke kuma take wasa da karatunta tana biye masa shine yayi fushi. Ya gaya mata baya son mutumin da bashida focus, yana sonta amma baze taɓa haɗa lokacinta da Aikinsa ba me yasa ita zatayi wasa da Karatunta saboda shi?
Yace baze sake kiranta ba se sun gama kuma ta tura masa da Time table sannan idan ma ta kirashi baze amsa baz kullum da safe ze mata text haka da rana da dare amma babu phone call saboda magana dashi yasa takeji kamar wata mashashshara ce ta kamata duk ta rasa gane kanta. Tana ganin wayarta na ringing ganin Ahmad ne kamar ba zata amsa ba se kuma ta É—aga dalilin tunanin da tayi a ranta, tabbas Alhakin Ahmad ne tun ba'a je ko ina ba Allah ya jarabceta da Jay.
A sanyaye suka gaisa daga ita harshi babu wani me karsashi,
"Yaya Exam ɗin? Saura guda nawa ku gama?" Ya kauda shirun da sukayi bayan gaisuwa ta bashi amsa a taƙaice da
"Lafiya lau, saura biyu"
"Masha Allah, Allah ya bada sa'a" daga nan suka sakeyin wani shirun. Ya sani idan zasu kwana a haka ba lallai ta sake cewa komai, wlh daze iya da ya rabu da yarinyar nan dan duk wata hanya da mace zata nuna bata ra'ayin mutum ta nuna masa amma zuciyarsa ta kasa haƙura da ita. A kullum cikin Addu'a yake akan idan babu Alkhairi a tarayyarsu Allah ya cire masa ita daga zuciyarsa ya musanya masa da wadda ta fita amma abun kamar ana rura wuta ƙaruwa yakeyi.
Idan Jafar yana bashi labarin sabuwar soyayyar daya gamu da ita se yace shi kam bashida sa'a ne a soyayya da Alama. Bega Yarinyar da Jay yake so ba, amma yanda har Jay yake labarinta ya sani ba ƙaramin sonta yakeyi ba itama kuma tana riritashi, ze iya cewa be taɓa ganin Jafar a yanayi na soyayyar gaskiya irin wannan ba, yace masa auran yarinyar zeyi, Bahaushiyace yar Nigeria a Zaria suka haɗu. Yaƙi ko gaya masa sunanta dayace ya tura masa hotonta ya nunawa Fatima ko ta santa nan ya fitittike ya ringa zuba masa Tijara yace kuma baze tura ba se ya dawo zasuje ya ganta face to face ko sunanta baze gaya masa ba balle ya faɗawa Fatiman.
"Tana da Friends haÉ—aÉ—É—u irinta zan samo maka guda É—aya ka fita daga sabgar waccen Ajawon Fatiman da take wahalar da kai Yaya Ahmad" abinda Jay ya gaya masa.
Ahmad yaja numfashi, kusan minti bakwai daga shi har Fatima babu wanda yace wani abu. A sanyaye yace
"Fatima, idan wani laifi nayi miki kiyiwa girman Allah ki sanar mun na baki haƙuri, na gaji da azabatar da zuciyata da kikeyi kusan sati uku kenan kin hanani zaman lafiya nace zanzo kince Aa, idanna kiraki a waya koda yaushe cikin bani Excuse kike me nayi miki? Idan maganar kai gaisuwa da nayi ce kince Aa kuma na haƙura bayan wannan wane laifi nayi miki da kike hukuntani ta hanyar azabtar da zuciyata haka?"
A maimakon ta sassauta se maganganunsa suka sake ƙukar da ita, ta tsani Namiji da bashida ra'ayin kansa se abinda mace tace yayi wannan yana daga abinda bata so da Ahmad yanda yake mata wani lako lako kamar ita ce Namijin shine macen, to tun yanzu baya iya taɓuka komai daga abu ya haɗa m
Su ya fara kamar zeyi kuka yana lallaɓata idan sunyi auren kenan baze ringa tsawatar mata ba idan tayi masa laifi. Haɗuwarta da Jay tasa ta ƙara fahimtar banbancin Namiji da muna Maza, duk yanda yake nuna So ta yake riritata idan tayi masa abinda be gamshe shi ba murɗewa yakeyi ita ce zatayi ta lallashinsa da ban baki kafin ya sakko kamar dai yanzu daya yi fushi saboda bata maida hankali akan Exam ɗinta ba ta tabbata da Ahmad ne tsayawa zeyi yana lallashinta akan tayi kaza ko kartayi.
"Dan Allah Fatima ki tausaya mun. Na sani bakya sona Alfarma kike mun ina roƙon da ki daure kici gaba, ki dubi kalar jarabawar da nake ciki ta Sonki ki tausaya mun. Wlh Fatima da zan iya da tuni na cireki daga raina na rabu dake, koda baki taba buɗe baki kin gaya mun ba nida kaina nasan bakya sona kina kulani ne kawai saboda wulaƙnta ɗan Adam ba tarbiyyarki bace kuma na gode da hakan. Bazan gaji da roƙonki na akan ki bani dama, ki bude mun zuciyarki ko yaya ne in Allah ya yarda ba zakiyi nadamar tarayya dani ba" Ahmad ya sake faɗa a sanyaye.
Zuciyarta tayi rauni da jin abinda ya ke cewa, wato shi da kansa yasan bata sonsa amma ya gaza haƙura da ita tashi jarabawar Sonta ita kuma tata Son Jay Allah kenan.
Ajiyar zuciya ta sauke na shaking tace
"Nifa Ahmad ba haka bane ba, na gaya maka exam mukeyi ina buƙatar isashshen lokaci saboda nayi karatu shiyasa duk wani waya da wani chat na ajiye su amma mun kusa gamawa nan da Three days In sha Allah".
Yayi murmushi da jin abinda tace shima yace
"Ranar Thursday kenan zaku gama?" Ta yatsina fuska kamar yana kallonta tace eh, se ya sake cewa a sanyaye
"To yaushe zaki dawo Kano?"
"Paper safe ce, in har na gama komai kafin 12 ma zan taho a ranar in Allah ya yarda"
"To nazo na ɗakko ki?" Ya faɗa da sigar roƙo kamar wani me magana da ogarsa a gurin aiki, bata san sanda tsaki ya subuce mata ba tace
"Zan dawo da kaina, kasan Baffa ya hana ai ka ringa barin aikinka kana tahowa hidimata".
"Dan Allah Fatima karkice Aa kar kuma ki jingina maganar nan da Baffa sedai idan bakya sone kawai sena haƙura" ya sake faɗa gwanin ban haushi kuma ban tausayi kamar ze mata kuka, babu yanda ta iya haka ta yarda akan yazo ya ɗauketa, ita kanta zata ji daɗin hakan saboda hutun Session ne zata tafi da duka kayanta.
Ya ringa zabga mata godiya kamar wanda tayiwa kyauta daga ƙarshe sukayi sallama bayan ya sake roƙarta akan dan Allah ko sau ɗaya ne a rana idan ya kirani ta ringa amsawa gaisawa kaiwai zasuyi baze ja mata lokaci ba tace Toh.
"Allah sarki Ahmad, wlh yana bani tausayi na daÉ—e banga soyayya me zafi irin wadda yakeyi miki ba Afeeyah,dan Allah ki tausayawa mutumin nan yaci Albarkacin so wlh na tabbatar ba zaki yi nadamar auransa ba saboda yana sonki" Badar ta faÉ—a, Afeeyah ta hararaeta tace
"Kyaji da fuska biyunki anjima idan Jay ya kira waya jikinki na rawa zakiyita karaÉ—i kina bashi assurance na ze sameni ke ga campaign coordinator kuma se na gaya masa abinda kike cewa yanzu"
"Amma Thruth to be told Afeeya wlh Ahmad yafi sonki, ki gani fa shekara biyu yana binki kina jansa a ƙasa na tabbata Jay baze ɗauki haka ba Mace ta ringa wasa dashi kamar wani Toy, da yanzu ya daɗe da sallama ki" Badar ta sake faɗa. Afeeyah ta tashi zaune daga kwanciyar da take tace
"To ai banbancinsu kenan shi yasan mutunchin kansa baze zauna a ringa wulaƙantashi akan abinda yafi ƙarfi ba shi kuwa Ahmad kamar mara zuciya ke nifa ba zan auri Mijin da zan ringa juyawa ba ga yan uwansa basa sona naje ana wulaƙantani baze iya tsayawa ya kwatar mun yanci ba".
Badar tayi kasaƙe tana kallonta amma ta haɗiye abinda tayi niyyar cewa ta canza maganar da wata tace
"Yawwa, nikam kinsan Familyn Jay ne?" kai ta girgiza mata tana cewa
"Aa, me yasa kika tambayeni?"
Tayi ajiyar zuciya zata yi magana kenan Ummi tayi sallama ta shigo, ciki ciki ta amsa fuska a É—aure Badar ce ta tambayeta ya Exam ita kuwa ta zari Bucket ta fita dan tun daga ranar da Islam tace mata tana faÉ—ar maganganu akansu ta washsheta, bata son munafukin mutum, idan ta yarda dakai kayi breaking trust É—inta shikenan kuma.
A gurguje tayi wanka ta shirya dan har Badar ta shirya zata fita Library tace ta jirata suje tare. Maganar da suka fara ɗazu na rantaso take taji dalilin daya saka Badar ta tambayeta ko tasan Familyn Jay dan yanayin da tayi maganar ya nuna akwai wata a ƙasa. A Frizlers sukayi Lunch, tana kallon Badar dake ƙarasa cin abinta tace
"ÆŠazu kina tambayata akan Familyn Jay?" tasha ruwa ta goge bakinta kafin tace
"Oh yah nace kin san wani abu akansu kuwa?"
"Nace miki ai ban sani ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ta tambayeta tana yatsina fuska, Badar ta gyara zama tace
Ranar Monday da naje office din Yah Sani (Abokin Yayantane ta ne da yake Lecturing anan) kinsan na gaya miki na taɓa ganinsa sunyi hoto da Jay sanda yaje Masters Uk hoton na office ɗinsa shine ina zuwa da na gani maganarku ta faɗo mun a rai nave masa two weeks ago Jay yazo school ɗin nan, he was suprised yace mun wai ya akayi na sani, then i told him about your encounter kinga mamakin da yayi kuwa? Ashe Mamansa da Maman Jay cousins ne shima suna bala'in shiri sosai gurinsa ma yazo nan Zaria kwanan sa ɗaya ya wuce babu wanda ya san yazo dan da daddare ya shigo kuma a gidansa ya sauka da safen daya fito ma be san inda yaje ba kuma harya tafi babu wanda yace masa ya ganshi then he asked me wai waye Dad dinki a Nigeria da har Jay yace yana sonki?"
"Ban gane ba?" Afeeyah ta katseta fuskar ta na nuna alamar confusion, Badar taci gaba da cewa
"Nima abinda nace masa kenan, to cut the story short Afeeyah abinda na fahimta Mamarsa yar Jari hujja ce, Yah Sani ya gaya mun Jay personally bashi da matsala, and tunda yace yana sonki dagaske yake yi amma inda matslar take mawuyacin abune Mahaifiyarsa ta yarda ya aureki saboda a duniya idan da akwai abinda ta tsana be wuce Talaka ba. Yaranta auran Jari take musu kuma babu wanda ta É—ora buri akansa Irin Jay saboda tafi sonsa duk cikinsu matsayin da yakai yasa ta tattara duk wani burinta na duniya akan matar da ze auro, ita a sonta cikin turawa ko larabawa zeyi aure ai kinsan Shahida Anchau ko?" Ta jefo mata tambaya, ruÉ—u da tashin hankalin da ta shiga yasa dakyar ta É—aga mata kanta da yayi nauyi Badar taci gaba da cewa
"To Mamansu babu yanda batayi akan a haɗa auransu da Shahida ba kinga dai Abbansu kafin ya rasu yayi kuɗi kamar me kuma har yanzu Mamansu kanta tana da kuɗi amma wai Maman Jay taƙi, ba Shahida kaɗai ba yace a Familynsu babu daga gidan da ba'ayi masa tayin aure ba amma taƙi bari ya karɓa. Ki ga dai Familyn ANCHAU duk Kaduna babu wanda be sansu ba saboda tsofaffin kuɗine, arziƙinsu tun duniya na kwance har jikokinsu ba lallai suyi talauchi ba amma Mahaifiyar Jay ta raina su tace bataga yar da ta dace da shi a ciki ba. Ni wlh mantawa nayi ma tunranar ban gaya miki ba se yau abin ya faɗo mun a rai nace masa ma zamuje tare ya faɗa miki da kansa kafin ki ce hassada nake miki ko ƙarya na shirya saboda na rabaki dashi".
Ƙasa Afeeyah tayi da kanta tanajin wani abu nayi mata yawo tsakanin ƙirjinta da maƙoshi yaƙi wucewa yayi ƙasa kuma yaƙi haurowa ya fito. Wato kallon yar masu ƙumbar susa Jay yayi mata saboda ya ganta fara ƙal kalar madara ya shaƙi ƙamshin designer turare a jikinta ga Hijabin Crep yard da Ummu-Maheer tayi mata ze tsammaci irin yan Turkey ɗinnan ne ko Egyptian shiyasa yake sonta?
Kenan wannan ne dalilin da ya saka yake yawan kawo mata labaran ƙasashen duniya idan ta nuna bata sani ba yace wasa takeyi masa? Bata manta ba ranar nan suna maganar kallon Ball da tace masa Badar na kalla a waya yace me yasa ita bazata kalla ba tace masa kawai, se yace ta roƙi Dadynta wannan Holiday ɗin suje Muje London ta kalli wasan sa Live har take ce masa ita Baffa ne da ita ba Dady ba kuma wace London ita da ko Aiport bata taɓa zuwa ba ya ringa dariya yana cewa ta raina masa hankali kenan kallon yar Masu kuɗi yake mata irin wadda Mahaifiyarsa take da burin ya aura lallai kuwa an yanka ta tashi.
"Afeeya your body is shaking, ki nutsu dan Allah ba fa na faÉ—a miki maganar nan saboda ki saka kanki a damuwa bane ba...."
"Na fahimta Badar na gane wlh dama kuma nima ina yawan wannan tunanin a raina, Ahmad da be kaishi matsayi da suna a duniya ba Yan uwansa suna ganin ban dace dashi ba ina ga JAY wanda ba yan uwa ba na tabbata mutanen duniya kansu se sunyi mocking ɗinsa idan suka san yar wa ya aura, damuwata kawai Badar me yasa yasan da wannan tsarin na mahaifiyarsa ze zo gurina? Tun haɗuwata dashi ban boye masa komai a kaina ba, na gaya masa Mahaifina ba kowa bane me neman na kansa ne amma se yayi dariya kawai yaga kamar wasa nakeyi, kuma banyi wani abu na ƙarya da ze saka yayi tunanin na fito daga wani babban Ahali ba ko kawai kenan Surata ce ta rudeshi yayi mun kallon daidai da matsayinsa? Kenan a gidan Masu kudi kadai ake samun Yara masu Kyau da sura irina ba'a haifarsu a gidajen Talakawa?" se tayi shiru tana jin kuka yana taso mata, bata iya riƙe shi ba kuwa ta fara Badar ta miƙe hankali a tashe ta dawo kusada ita ta riƙe hannuna tana cewa
"Dan Allah ki dena kuka kinga ana kallonmu"
"Badar ina son Jay, idan na rasa shi bansan ya rayuwata zata kaya ba. Na sani ban kai koda matsayin me aikinsa ba amma zuciyata ta yi ɗage ta kai kanta inda be kamata taje ba kuma shine sila, shi ya kwaɗaitamun soyayyarsa irin wadda na daɗe ina nema me yasa be dubi matsayi da tazarar dake tsakani mu ba ya shiga rayuwata da alƙawarurrukan ƙarya da ya san baze cikamun su ba ya san mahaifiyarsa nada zaɓi kullum yake cemun duk abinda yake so shi take so ba zata taɓa hanashi auran wata mace ba muddin yace ita yake da muradi?"
"To ai Afeeyah kinga shima Yah Sani ya faɗi abinda ya sani ne kawai akan Mamanshi, zata yuwu ta canza ko kuma kamar yanda ya gaya miki ba zata hanashi auran duk macen da yace yana so ba tunda ta fi sonshi cikin yayanta doke taso farin cikinsa. Ni dalilina na faɗa miki maganar nan saboda karki sake jiki kuma daga ƙarshe ba fata ba ki zama disappointed, amma kamar yanda kika ce shi yasan wacece ke kuma a hakan yace yaji ya gani yana sonki ki kwantar da hankali all shall be well in sha Allah" Badar ta faɗa cikin lallashi.
Afeeyah ta kife kai kan Table taci gaba da rera kuka tamkar har ranar rabuwarsu da Jay tazo, she can't imagine loosing Jay, is like loosing her whole life dan bata tsammanin zata sake moruwa, soyayyar sati uku jinta takeyi tamkar ta shekara ɗari uku, daƙyar ta haƙurtar da kanta ta kuma ɗauki shawarar Badar da tace tayi confronting Jay domin tasan makomar relationship ɗinsu tunda wuri tunda dai shi zuciyarta tayi amannan da. Tabbas tana da buƙatar hakan, zata so ya furta mata da bakinsa tunanin da yakeyi akan Ahalin da ta fito sannan zata kawo maaa maganar Mahaifiyarsa taji view ɗinsa akai.
PAGE 15
A daddafe suka ƙarasa exams idan kaga Afeeyah se ka ɗauka jinya takeyi saboda yanda ta fita a hayyacin ta. Tun daga ranar da Badar ta bata taƙaitaccen labarin Mahaifiyar Jay ta shiga wani yanayi na tunani da lissafin yanda makomarta zata kasance. Ƙarin tashin hankalinta kwanki huɗu kenan basuyi waya da Jay ba, zeyi mata text safe rana dare ya tambayeta ya take amma a ƙarshe ze sake jaddada mata karta kuskura tace zata kirashi har se ta kammala Exam ta san koda ta kira kuma baze amsa ba ita kuma taso suyi magana, ya warware mata abinda ya addabeta a zuciyarta ko ta samu nutsuwa.
Ranar Thursday suka kammala, ƙarfe bakwai da rabi suna shirin fita Ahmad ya kirata wai ya shigo Zaria yana Dogarawa lokacin, tayi kasaƙe da waya tana mamaki dan gaba ɗaya ma ta manta da batun ze zo ɗaukarta yau, ita bata ma shirya kayanta ba dan lissafinta kawai se gobe Juma'a zata wuce gidan amma tunda yazo babu damar tace ya koma hakan dai dole zata shirya ta bishi su tafi dan haka suna fitowa daga Exam basu tsaya komai ba suka wuce Hostel. Ahmad ya sake kiranta akan idan babu damuwa zeje Kd yanzu ya amso wani saƙo kafin ta gama shiryawa ya dawo
"Idan ba sauri kakeyi ba ka jira kawai mu tafi tare se mu kai Badar gida" ta faɗa masa, Badar ta ƙwalalo ido tana kallonta tace
"Ni nace miki yau zan tafi?"
"Nima ai ba yau nayi niyyar tafiyar ba saboda ya rigada yazo yasa dole zan tafi, ki tashi dan Allah karmu tsayar dashi" Afeeyah ta gaya mata. Dole Suka kashi kaya dan shirin da basu ƙarasa ba kaɗan ne, Badar nata mitar batayi sallama da Sweetynta Nurain ba kuma sunyi yau ze kaita yawo yanzu tasakata tafiya gida ita dai ta toshe kunne har suka kama hanya.
Badar da Ahmad keta hirar su ba tareda sun damu da Afeeyah ba dan daman sun saba muddin tafiya ztacehaɗa irin haka shiru takeyi tabarsu idan ma daga shi se itane sedai ya gaji da magana ya kunna Radio. A gidan Hajiya Ummu Yayar Hajiya Binta ya karɓi saƙon Laces ne ya siyawa Momy, a mota ya barsu ya shiga shi kaɗai da ze fito Hajiya Ummu da itama zata fita daman shi take jira ta biyo shi suka fito tare.
"Au daman tare kake sa baƙi shine ka barsu a Mota Ahmad? Rowar yar tawa kakeyi mun ko kuma baka riƙeni uwa ba shiyasa ka hanasu shigowa?" Hajiya Ummu ta faɗa. Ahmad ya duburburce, sam be kawo zata fito ba kuma shi be ƙiyi musu tayin shiga ba sedan baya so su ɓata lokaci dan yasan Antyn Ummun cewa zatayi se sun zauna sunci abinci dan shi kansa daƙyar ta barshi ya fito shaf shaf ɗin gashi kuma yanzu yayi complicating abun.
"Wlh Mama ba haka bane, ita wannan gida zamu sauketa Fatima kuma mu wuce Kano tare. Naga rana tayine bana so mu ɓata lokaci amma kiyi haƙuri bari su shigo". Yanda duk ya rikice yana mata bayani yasa tayi murmushi tace
"Karkayi kuka na yarda ba da niyya kayi ba". Ahmad yayi dariya, Badar da Fatima suka fito suka gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa wacece Surukar tata a cikinsu.
"Ki zaɓa Mama" ya faɗa yana shafa kai, tace
"Kowaccece a ciki Allah ya tabbatar da Alkhairi, saura ɗan uwanka ya kamata shima ya bar ruwan ido haka ya fitarda mata" ta koma cikin gida bayan tace su jira tana zuwa. Hijabai ta ɗebo ta basu sukayita godiya. Badar data karɓi ledar bayan sun shiga mota kafin Ahmad ya shiga tacewa Fatima
"Ke Hijaban Ummu-Maheer (07061838488) ne, kinga ledarta".
"Ai sun zaga duk inda bakya zato Kyau iya kyau, kasha gayunka da kuɗi ƙalilan a ringa zaton tafiyayye kika saka dole ki ganshi a gurin manyan mata irinsu Hajiyar nan".
Suna yan hirarrakin Ahmad ya dawo suka kama hanya. Tilas seda sukaci abinci sukayi Azahar kafin Momynsu Badar ta barsu suka tafi. A hanya Ahmad nata mata santin kirkin Maman Badar. "Ai Momy badaga nan ba gurin kirki, ita Badar ta gado" amsar data bashi kenan ta kame baki ya gaji da jan maganar shima ya kunna musu karatun Alƙur'ani ƙasa ƙasa suka cigaba da tafiya.
Lokaci lokaci yake kallonta yana ganin yanda ta mayar da hankali kan wayarta kome takeyi se Allah idan ta nisa kuma taja tsaki ita kaÉ—ai tayi tagumi ta kalli window. Yana so ya tambayeta me yake damunta amma ya kanne, so yake ya fara jurewa yana danne sonta ko ze samu ta fara dubansa da kimar da yake so. Bukar ya gaya masa ya bata iska, bawai barta ba tunda yana sonta amma ya koyi kamewa shima ya dena nuna mata cewar idan babu ita baze iya rayuwa ba.
Wayarta tayi ƙara, yana ganin yanda ta zabura ta duba in beyi ƙarya ba har sautin ajiyar zuciyar da tayi ya jiyo. Suka haɗa ido sanda ta saci kallonsa kafin ta ɗaga wayar. Zuciyarsa ta harba, daga yanayinta da yanda take magana a wayar dukda bajin me take cewa yakeyi ba tsabar yanda tayi ƙasa da murya ya gane da Namiji take maganar. Kansa ya ɗauki zafi, har wani sara masa yakeyi idanuwansa sukayi jajir lokaci ɗaya saboda wutar kishin data tashi ta fara ci balbal a zuciyarsa. Be san ta gama wayar ba seda yaga tana Ƙoƙarin saka cajin wayar ta ajikin cajar motar. Murya a kausashe da irin sautin da bata taɓa jinsa dashi ba ya kira sunanta kafinyace
"Ni ba shashashan Namiji bane da kina zaune tareda ni wani ze kiraki a waya ki É—auka, this should be the last time da zaki kwatanta wani abu kamar haka. Wlh kika sake sena fasa wayar idan yaso naga da abinda zaki cimun fuska kiyi magana da wani Namiji".
Tsabar yanda maganarsa ta shigeta har karkarwa jikinta ya ɗauka, tunani takeyi daman Ahmad ya iya faɗa irin haka? Yanda ya juye mata lokaci ɗaya ya firgitata ga speed daya ƙarawa motar yanda kasan zasu tashi sama.
"Kayi haƙuri" ta faɗa bakinta na rawa. Har suka isa Kano kuma be sake ce mata komai ba, a bakin layinsu da suka isa ya faka be kulata ba ya fita ya samu yara ya buɗe booth suka kwashe mata kayanta. Be bata fuskar da zata sake masa wata magana ba, a wajen motar ma ya tsaya har seda ta sauka kafin yaja yayi tafiyarsa ya barta da bin bayansa da kallo.
A sanyaye ta isa gida kafin ta shiga dai tayi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta saboda gudun tambayar meya sameta. Ta tarar da Anty Sauda da yaranta, ganinsu yasa ta sake sakin ranta musamman kuma da sahibul Ƙalbinta ya kirata ya mata fatan sa'a akan Jarabawar da suka gama yace zasuyi magana idan ta isa gida. Wannan birkicewar ta Ahmad ce ta jirkitata amma tana shiga gida ta manta da babinsa ta shiga sabogogi sedai lokaci lokaci yakan faɗo mata, yanda ya fututtuke se taji kamar Jay yana sababi, daman ance masu haƙuri basu iya fushi ba yau kuwa gashi ta tabbatar.
Ahmad kuwa seda yayi dagaske kafin ya danne abinda ya ringa cin zuciyarsa, yana da kishi matuƙa musamman akan abinda yake so kamar Fatima. Koda yake binta yana lallaɓata dan yasan kawai ra'ayinsa ne batayi bawai wani saurayi ne da ita daban da yasa take ƙinsa saboda shi ba. Yasan bata double dating, shiyasa ya nace yake ta roƙon Allah yana kuma ƙara cusa kansa gurinta amma yanzu ya fahinci ta samu wani saurayin da take ra'ayi shiyasa harta iya ci masa fuska ta ringa waya dashi a gabansa shi ga sakarai wato bazeji komai a ransa ba.
Seda aka kwana biyu da ɗakkota da yayi be sake kiranta ba, dan ya yanke dole ya koyawa zuciyarsa haƙuri da ita tunda har ya fahimci da wani bayan shi yanzu komai yana iya faruwa kenan. Da safe ranar Asabar kwana biyu kenan da dawowar tata yana kwance a ɗakinsa se gashi ta kirashi. Ya ringa kallon wayar kamar wanda yayi loosing memory saboda ya kasa yarda Fatima ce take kiransa da karan kanta yau. Rejecting yayi kafin yabi bayan kiran duk da zuciyarsa nace masa karya amsa ya bar wayar tayi ringing ta gama harta sake kira dan ya tabbatar da gaske shi take kira ba tuntuɓen number tayi ba.
"Ina kwana?" Ta faÉ—a a sanyaye bayan da yayi mata sallama ta amsa. Ya amsa gaisuwar yana jin tamkar ya taka rawar murna, dahgaske kenan idan mutum yaja aji za'a mutuntashi tunda gashi fushin kwana biyu ya juyo masa da hankalin Fatima.
"Kayi haƙuri akan abinda ya faru ranar nan banyi da wata niyya ba" ta sake faɗa a sanyaye. Daɗi ya sake kamashi, har tasan ta kirashi kenan ta bashi haƙuri ai kuwa akwai haske a cikin tafiyar. Ya wani mula yace
"Babu komai kawai dai na gaya miki idan kika sake sena fasa wayar tunda bazan iya fasa miki baki ba"
"Ai dai nace kayi haƙuri" ta sake nanatawa yace
"Na haƙura na kuma yafe miki Alhakina da kika ɗauka kika sa nayi fushi dake".
"Uhm" kawai tace, suka ɗan taɓa hira kafin sukayi sallama bayan yace mata zeje da yamma tace tana gidan Anty Sauda ya sameta a can dan kwana zatayi.
"Toh ko kefa? Nifa harga Allah zancen wani Ɗan Ball be kwantamun a rai ba. Haka kawai zaki kwasarwa kanki abinda ze saka miki ciwon rai idan ya aureki ɗin ma kenan. A matsayinki nawa Afeeyah zakice zaki auri world class Celebrity? Ai ɗagen yayi yawa, irin waɗannan ai ba kowacce mace ba, kuma duk ma ba wannan ba na tabbatar wlh fuskarki ce kawai ta ruɗeshi, babu tabbacin idan yasan wacece ke ya yarda ya aureki a haka gara miki Ahmad ɗin. Mutumin nan ga Hankali, nutsuwa, mutunchi, karamchi uwa uba yana matuƙar sonki kuma ya sanki ciki da bai yasan Mahaifanki a hakan kuma yace yaji ya gani yana sonki ze aureki na rasa wace masifa ce tasa bakya son Bawan Allahn nan Afeeyah wlh in guje miki kiyi nadanar da ba zata amfana miki komai ba a gaba" Anty Sauda wadda ita ta tursasata kiran Ahmad bayan data shaida mata abinda ya faru tsakaninsu ta faɗa.
Afeeyah ta zumɓura baki, kafin tayi magana wayarta ta shiga ƙara, ringing tune data sakawa Jay ne dan haka ta miƙe da sauri da wayar a hannunta ta shige ɗaki Anty Sauda ta rakata da ido tana cewa
"Idan kina da rabo Allah ya ganar dake amma wlh nasan wannan Jay yake kowa yaudararki yakeyi ba auranki zeyi ba gara tun kina da sauran dama kiyi amfani da ita amma ba takanki zanbi ba, Baffa zan samu tun wuri asan abinyi baze yuwu shekara biyu ki gama yaudare bawan Allah kizo kice ba zaki aure shi ba" taja wayarta ta shiga kiran Baffansu sedai wayarsa a kashe. Tayi ƙwafa a fili ta sake cewa
"Har gidan zanje, gara ko auran dole ne miki tunda baki da hankali" ita dai Afeeyah na kan gado tana malele kuwa Jay na kasheta da kalaman Love, tunda suka shirya ta manta komai. Hatta maganar dake ta azalzalar zuciyarta ta mahaifiyarsa bata tayar ba tama manta da batun ta sake zama daram akan Alƙawarurrukan madarar ƙaunar da yace ze shayar da ita idan sukayi aure. Ya mata Alƙawari nan da watanni shida zezo Nigeria musamman saboda ita, ya kuma ce mata zuwan da zeyi zeje ya gaida Mahaifinta daga nan iyayensa suzo dan ya rigada ma harya gayawa Yayansa maganarta shima shirin Aure yakeyi tare za'a haɗa da nashi dan haka ta fara duk wani shirinta da idan yazo tana iya yuwuwa daga tambaya taji an ɗaura musu aure kawai sedai taji ana fito kibi Mijinki.
Ranar tayi dariyar maganarsa yace tasaka wasa zata gani da gaske yakeyi, Alhajinsu bashida wasa ko yau yace masa zeyi aure muddin ya yarda da inda ya nemo auran magana ta ƙare tambaya kawai za'aje ayo. Wannan tasa ta yanke shawarar sanar da maganarsa a gida tunda wuri ba wai se rana tsaka ba, ta fara takan Anty Sauda domin itace tsanin da ze kaita gasu Baffa. Muddin tayi na'am da abin tasan komai ze zo da sauƙi sedai daga yanda ta karɓi maganar tasan ko zata yarda se an yi ƙwaibai da ita dan tamkar Badar itama Ahmad ya lashe mata zuciya sonsa suke nasa son abinda ze taɓa shi. Daga ce mata sunyi faɗa tace seta kirashi ta bashi haƙuri idan ba haka ba ta gayawa Baffa ta samu wani saurayi yana hure mata kunne harta kori Ahmad ta masa wulaƙanci shiyasa ta kirashi.
****************
Hajiya Binta zaune kan carpet tana zubawa Alhaji Audu faten Accar da tayi masa saboda tana da buƙatu yau da kanta ta tsaya ta masa girki me kyau ta kashe gayu da wata kamfalarta shadda ta saka daham, lallen bikin da aka mata tun yau litinin yayi raɗau a hannayenta da Ƙafa dukda na Salatif ne me yankan Siga amma da yake fatar da sauran Armashinta ya mata kyau. Humrar da akayiwa Amarya Hafsatu ta bulbula abinta ƙamshin har hawa kai yakeyi dan seda Alhajinya kunna fanka bayan Ac dake falon saboda Atishawar da turaren nata ya saka ya fara jerawa.
Hira take masa wadda duk labarin irin tsaruwar gidan Hajiya ƙaramar take zayyana masa. Jiya su Turai suka dawo daga jere, dakyar da roƙon Allah ma ta yarda ta zauna dan cewa tayi da da ita za'aje.
"Wannan wane irin abune babu kunya kawai Binta ki bimu se a ganki tsalam ace ga uwar Amarya a ina kima taɓa ganin anyi haka? Ita Aisha data aurar da Yaya biyu gata uku wanne kika gani a ciki tajewa jere baku ne kuke zuwa ba se kece zakice se kinje salon ki zubarwa da yarinya ƙima tun bata kai ga shiga cikinsu ba? Abujar ce baki taɓa zuwa ba ko kuwa ance za'a rufe shigarta ne idan bakije yanzu ba?" Turai ta ringa zazzaga mata bala'i dan lamarin Ƙawar tata ya fara kaita bango.
Fafur tace Anty Rabi da Momy ba zasuje mata jere ba, Baba Bilki ma da tace ba za'a da ita ba dake har yau na sanyi tayi ba tace ai uban Binta ma yayi kaɗan balle ita ta hanata zuwa gano gidan Yar Audu. Saboda neman suna tace wai Hajiya Balaraba tazo aje da ita tace Aa saje kai Amarya daga ƙarshe dai bisa tursasawar Turai suka tafi da ita da Momy wadda bata so zuwa ba se Hajiya Zainab da Munirah ƙanwar Binta wadda har yau sama da shekaru hamsin kenan tana zaune bata samu Mijin aure ba bayan rasuwar Mamansu ne ta dawo nan Kano da ta fara zama gidan Binta zama yaƙi daɗi se kawai ta siyi gida take zaune abunta tana kasuwancinta tana cigaba da roƙon Allah daya yanke mata dukda ta san cewar ba komai ya janyo mata shiga halin da take ciki ba se haƙƙin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba suka laƙa mata sharrin da harta mutu wasu na kallonta dashi. Suka hanata zaman lafiya a gidan auranta harta koma ga Allah.
A can Kaduna suka haɗe da sauran yan uwan Binta akaje akayi jeren wanda babu wani abin arziƙi data siya. Kayan Gado dai a BECHI FURNITURES yace aje a ɗaukar mata duk abinda uba yakeyi saɓanin su Khadija dayake ƙayyade Adadin kuɗi yace a ɗauki kaya na kaza. Su Turai ne sukaje suka zaɓa suka darje kaya na ƙarshen mutunchi a shagon, da Alhaji yaga Invoice ya ringa surfa masifar da bata da Amfani domin dai shiya nada dama kuma sun rigada sun ɗauka har an jera dan a Branch ɗinsa na Abuja suka kwasa ƙarshe abin ya ƙare akan Aslamiyyah yace Gado biyu kujera biyu za'a ɗaukar mata saɓanin Hajiya ƙarama da aka sakawa huɗu, ɗaki biyar ne a gidan da faluka biyu manya se ƙarami ɗaya wanda yake haɗe da Master Bedroom a sama shine na Megidan iyayensa sun gyara masa dan haka hatta ɗakin da me aiki zata zauna Royal aka saka saboda samun guri da nuna akwai.
Kayan Kitchen dai daman yace musu a Al'adar Hausawa uwa ce takeyi to yana kan wannan magana har akan Hajiya be saketa ba dan haka ita tayi kayan kitchen tarkacen banza da wofi wasu matsiyatan kuloli da fulasai ta bakin Turai. Yanda ta ringa zuzuta ta gama siyan komai dan ƙin yarda suje siyayyar tare tayi, haka ta nuna mata kayan taƙi se randa zasu tafi Jere da za'a ɗiba aka tattara kaya ko cika buhu biyu basuyi ba amma faɗi take
"Kinga kaya ko Turai? Dama na gaya miki sena baki mamaki ai bikin Nazira shammatata akayi amma wannan na shirya"
"Billahillazi Binta idan baki fitar da kuɗinki kinci kin morawa kanki ba se kin mutu kina kwance a ƙasa zakiga yayanki na wadaƙa dasu, yanzu wannan kayan kike zuzutu akai? Abinda ko Talaka me zuciya se yayi ninkin abinda kikayi wannan abin kike so akai ace daga gidan Bechi suka fito? Turai ta ringa masifa kamar zata ari baki tana kafa mata hujja da kanta yanda takeyi idan zata aurar da Yayanta da sauran ƙawayensu, ta kawo mata Misalin Momy, auran Khadija da Annah ita da kanta tace har seda suka maido da wasu abubuwan gida dan seda aka kai sukaga an siya an ƙara siya tasan kuma yanzu ma na Aslamiyyah haka zata fitar da kanta kunay.
Duk wanda yaga kayan gadonta da kujeru yasan ubanta ne yayi mata ke za'a zaga ace uwarta bata da zuciya dan wlh ko yar riƙo a gidan nanta wuci akaita da wannan tarkacen. Ƙarshe se Alhaji Zakariyya da Alhaji Naziru harda Yakubu Turan ta kira tace kowa yazo ya bada abinda ya samu, ta tattara ta bazama kasuwa tayo mata siyayyar kayan kichen na fita kunya suka kai ta barwa Binta tsiyarta da tace ta ajiyewa Auta Saratu ta huta ita tasan ba zata raina wannan ɗin ba toh fa tunda suka dawo aka kawo mata Video shikenan ta kasa nutsuwa labari data kai aya zata maimaito tun Alhajin yana ji harya gaji yace mata
"Binta yanda kike nanata mun labarin gidan nan ko zuwa nayi yanzu bazan ɓata ba danna gama gane kowanne lungu da saƙo na gidan, ki bani abincin naci kafin ya huce dan Allah do nakeyi na fita zamu haɗu da Alƙali mu tattauna yanda taro ze kasance kinga lokaci yana ƙaratowa yau Litinin saura kwana huɗu ɗaurin aure".
"Ai toh yi haƙuri wlh santin gidan ne yaƙi ya barni, ai Hajiya dai tayi gida Allah ya tsole idon maƙiya yasa mutu ka raba" ta faɗa tana bashi. Shida ya shiga cin abincin yana jinta dan batayi shiru ba. Ta gyara zama tace
"Dama Alhaji zancen gurin Kamu ne an gama magana da mutanen nan yanzu sun dawo sunce wai kuɗi yayi kaɗan se an ƙara kuma ni nayi ƙarƙaf dubu Ashirin yanzu se nayi da gaske zan fito da ita ai bikin nan dai ya talautani da gaske".
Ya kalleta ta gefen ido a ransa yana mamakinta, wai ta kashe kuɗi kome ta yi se Allah bayan duk abinda ake ciki yana da labari. Zakariyya ya gaya masa su suka bada kuɗin kayan kitchen bayan ta ɗiora musu Alhakin abinda za'aci a gurin Mother's eve data shirya shi kuma nan be san Buhu nawa da galan na mai nawa da sauran kayan abinci data kwashe masa a Store tace za'ayi abincin biki ba. Kaji ɗari biyu ya saka aka bata ita kaɗai banda Sa da za'a yanka na abincin yini. Tunda aka fara zancen bikin nan Aisha bata ce ma ya bata sisin kobo ba, Bilki ce ta nusashsheshi har ya batan dukda be kai ko kwatan abinda Binta ta Ƙwamusa a hannunsa ba. Kayan gado kansu ya banbanta Hajiya Ƙarama cewa yayi su ɗauki wanda ya musu Aslamiyya kuwa dalilin ɓarnar da su Turai suka masa shiya faɗi kalar wanda za'a ɗaukar masa an gaya masa Ahmad da Sarki ne sukayi cikon Kuɗaɗe masu nauyi suka ɗaukar mata irin na Hafsatun kuma duk abinda ya kamata ace yayi wanda Aisha bata tambayeshi ba su sukayi yana kallo aka ringa sauke ruwa da lemo besan katan nawa bane inji Ahmad Jafar kuma shi ya siya Musu Cinema Tv su biyun nan cikin Yaya bila'adadin daya haifa ne suke da zuciyar bashi gudummawar auran ƙannensu dukda sun san yana dashi ba babu ba amma yaji abinhar cikin zuciyarsa.
"Alhaji kayi shiru" Hamshaƙiyar ta girgizashi. Ya aje farantin hannunsa ya miƙe tsaye yana cewa
"Ki karɓo kuɗinki kizo kuyi a nan cikin gidan kamar yanda su Aisha zasuyi ni banida wasu kuɗi da zan sake baki kuma a yanzu nayi iya abinda zan iya"
"Ai shikenan, kana ji Jafaru wai baze zo bikin bako? Gaskiya ka kirashi kayi masa magana ta yaya za'ayi ace baze halarci ɗaurin auran ba? Ta ya mutane wai zasu san Ɗanka ne yafi so ayi ta kallonsa a ba kowa ba ai idanya fito kowa ya san Ɗanka ne darajar sa seta sake linkuwa a ƙasar nan ko ya kace?" Ta sake soko masa wata maganar, ya miƙe yana shiga ɗaki yace
"Duk yanda kika ce Binta, bari na shirya na fita dai na baki guri" ya barta tana cizon yatsa. Daman ba Even centre data kama, tunda taji a gida Momy zatayi Kamunta zata kira masu Decoration taje kakarta ta yanke saƙa bari zatayi ta gama shirya komai se ranar tayi ta kankane ita da mutanenta dan ba zata iya zare Miliyan nawa ta kaiwa masu gurin biki ba, abinci ma da Turai tasa ta kashi kuɗaɗe ta bayar ciwon rai takeyi, so tayi ta bawa masu aikinsu ayi shi nan a cikin gida amma tace gun yan gayu zasu kai, so tayi ya bata kuɗin ta rage asarar wanda tabayar shine yace bashida su yanzu duk kwalliyar nan da tayi ta tashi a banza kenan ai shikenan.
Alhaji ya fito a shirye yana waya, bata san da waye ba abinda taji kawai ya fizgi hankalinta shine
"Babu damuwa nagode, bari mu gama da hayaniyar wannan bikin zanyi magana dashi. Idan son samune ya haƙura da yarinyar ya nemi wata dan sam banji abin ya kwanta mun a rai ba amma bama so na hanashi abinda yake so saboda yaron nada biyayya nasan muddin nace Aa tilas ze haƙura koda ace hakan ze cutar dashi amma yanzu zan samu Alƙali shima da maganar yanda mukayi zakaji".
"Toh fa wane yaro kuma ake magana akai?" Tayi tsalam ta tambaya bayanya kashe wayar. Yana tafiya ze sauka ƙasa tabi bayansa yace
"Ahmad ne, ya samu yarinyar da ze aura. Kiyiwa wancan yaron magana shima ya dakata da shashancin da yakeyi ya fitar da mata dan tare zan haÉ—u bana son Biki a rarraben nan"
"Yo naji kana cewa yarinyar bata maka ba? Halan kwashe kwashe yayo ko? Ni daman nasan za'a rina Allah yasa dai ba gidan matsiyata ya kwaso auran ba mu shiga uku su ƙara yawa bamu gama data gidan nan ba ya kwaso mana wata" Hajiya ta faɗa shidai be bata amsa ba ya fice daga falon dan Malam Sadi Driver sa yana tsaye harya kunna mota.
Ta wuce ciki inda ta baro ƙawayenta da sukazo ana ta tsara yanda biki ze kasance, Kamu dai rigar na Momy zasu shiga dukda ba haka su Hajiya Zainab suka so ba Turai kuma tace haka ne daidai tunda dai Yaran nan ubansu ɗaya toh ayi Kamun nan a tare idan yaso tunda kowacce gidan Mijinta sun shirya Dinner se suyi abarsu daban ga sauran events da kowacce Amarya zatayi da Ƙawayenta.
"Yanzu kawai sedai mu zama yan kallo mun raɓe raɓe kenan?" Hajiya Sha'awa ta faɗa, Binta ta karkace tace
"Inji wa? Ai biki namune wahala kawai zasu mana su shirya komai. Da kunji ance ina uwar Amarya ku rufa mun baya mu shige, duk wani kira da za'ayi ku shike kuyi kinini karku basu wata ƙofa a gurin" akayi shewa aka tafa.
Se ranar Laraba Ahmad ya kaiwa Fatima Ɗinkakkun kaya, Atamfa me kyau da akayiwa ɗinkin zamani amma Modest ɗinki se wani shegen Lace da Anty Sauda tace ya haura dubu ɗari biyu. Kowanne kaya da mahaɗinsa, Takalmi, mayafi, jaka harda Sarƙa da agogo. Zobunan gold guda biyu ya saka mata a ciki ganinsu ya tuna mata da ranar da yace ta nuna masa hannunta kenan measurement ɗin hannun ya ɗauka. Yace mata Atamfar ta Ankon Kamun ce dan ya gaya mata zasuyi biki har Iv ya tura mata Lace kuma kawai ɗinka mata yayi na Dinner.
Tace ba zataje ba Umma ta goya mata baya a cewarta babu tsayayyar magana a tsakaninsu da har zata saka taje musu biki, idan kuma zuwan nata ya janyo wani abu da ba za'a so ba fa? Gara dai da ace anyi magana yan uwansa sun san da zamanta da sauƙi ko cikin yan uwa tana iya samun wata suje tare su dawo. Baffa ma da aka gaya masa cewa yayi Aa. Da kansa ya kira Ahmad yace ba zataje ba, yayi kuma faɗan zobuna har biyu da Umma tace masa zinare ne yace in yazo ya karɓe su ya ajiye idanAllahyasa taje gidansa ya bata ya dai amsa da Toh amma koshi Baffan yasan baze karɓa ba dan yasha ya kawo mata abu yace a mayar yaƙi karɓa sedai ya kalallameshi da magana yace ko babu soyayya tsakaninsu Baffa Babansa ne zeyi mata komai saboda shi. Wannan ya rushe batun zuwanta Biki wanda daman ko da an barta a karan kanta ba zata so taje ba, to wai se taje a matsayinta nawa???
An dai yi biki a gidan Alhajin Bechi lafiya duk kalen bala'in Hajia da yan korarta dole suka kama kansu domin Yan uwan Momy da ƙawayenta wannan karon basu zo da wasa ba. Yanda Hajiyar ta saba musu idan ana biki ba yarta ba amma komai yana hannu ta se abinda tace se yanda ta tsara za'ayi wannan karon basu bari ba. Basu saurari Alhajin ba kansa Ahmad da Sarki sun share mata hawayen komai domin duk halinsa shima wannan karon Ahmad ya shawo kansa sun fitarda mahaifiyarsu kunya ba tareda sunyi jiran kowa ba. Anyi biki lafiya Amare sun tare Hafsatu an tafi Abuja Aslamiyyah na nan Kano se Amaryar Yakubu shima da Allah yayi bana yayi auran tsalle tsalle ya ƙare dukda seda Alhajin yayi masa barazana da ze saukeshi daga Acting Account General dan har yanzu ba'ayi confirming nasa ba kafin ya kawo matar akayi Bikin.
Afeeyah kuwa Rikicewa ta ringayi harta fara zaton WhatsApp ɗinta ya samu matsala saboda status ɗin Ahmad da Jay da suka zama iri ɗaya tunda aka fara bikin har aka gama seta yi tunanin repeating sukeyi taga kamar ana Jay dan komai ma gizon sunansa yake mata yanzu. Ko kusa bata kawo cewar Jay ze iya haɗa wata alaƙa da Ahamd ba shiyasa ma bata tsawaita tunani ko bincike ba ganin kuma komai ya koma normal shikenan ta manta. Ada bata fiya wani duba status ba amma haɗuwarta da Jay kusan kullum seta duba update ɗinsa wanda duk akanta yakeyi. Yace mata yaso yazo Nigeria abinda ya hanashi zuwa contract ɗinsa da Arsenal taje ƙarshe, Clubs da yawa suna zawarcinsa har yanzu kuma beyi finalizing inda ze koma ba yana so se yayi sealing deal ɗin kafin yaje wani guri. Ya tura maata da sabon Field name ɗinsa, a maimakon JAY its going to be AJAY. Yace A for AFEEYAH and JAY remain for the JAFAR bata yarda da gaske yake ba har se ranar da yayi sealing deal da PSG sabuwar rigarsa da AJAY aka bugata.
Ta ringa murmushi kamar wawiya sanda take kallon Interview ɗinsa, an tambayeshi me yasa ya canza suna kuma me A take nufi yace it remains secret lokacin da ze bayyana yana zuwa. Tana jin Yah Malam ɗinsu da Abokinsa Sani da tsabar yanda yake son Jay sunansa ya koma Jay ranar sunata magana. Ance Initial ɗin budurwarsa ne, wasu sunce Initial ɗin Yayansa ne da yake bala'in so kowa dai da abinda yake faɗi. Kamar taje ta gaya musu gaskiya se kuma ta kama bakinta. Anty Sauda tayiwa Umma zancen itama bata bada goyon baya na cewa ma tayi karsu bari Baffa yaji dan ranta ne ze ɓaci. Ya za'ayi tsayin lokacin nan ta dawo tace wani daban ba Ahmad ba itama tasan wasa takeyi. A ranta ko babu gudu babu ja da baya tasan kuma Baffa baze taɓa bin ta tasu ba ya aura mata abinda bata so. Ai da bakinta bata taɓa cewa wani tana son Ahmad ba ko zata aureshi su suke kiɗansu suna rawarsu dan haka babu wata hujja da za'a kafa da zata rabata da wanda take so, badai yace ya kusa zuwa Nigeria ba yana zuwa zata kaishi gidan ayita ta ƙare da haka suka cinye hutun session daya ritsa da Strike kusan watansu uku a gidan kafin suka koma School First semester Four hundred level.
PAGE 16
Rayuwa ta shuɗa, soyayyar Afeeyah da Jay tana ƙara ƙarfi inda al'amarinta tsakaninta da Ahmad yake sake taɓaɓarewa. Zywa yanzu ya gama tabbatarwa Fatima bata ta tashi da gaske wani ya masa shigar sauri kuma ya sure Imaninta. Ya sake tsananta Addu'a akan Al'amarin amma mainakon rangwame se sake jinta yakeyi a zuciyarsa kamar ture. Damuwar da yake ciki da ayyuka da suka masa yawa yasa duk ya sake figewa ya fita a hayyacinsa. Kowa a gidan yaro da babba ya shaida Ahmad yana da damuwa hatta Hajiya kuwa seda ranar ta tsare shi tace
"Kai Amadu anya magauta basu danneka ba? Wannan uwar rama haka kamar wanda ake ɗiba ayi miya kullum? Koda yake jarabar neman kuɗi daka saka a ranka ai dole kaƙi abin kirki, ni na rasa ma me kake nema ko kuwa so kake se ka yi gasa da ƙaninka ne? Shidai kasan yan guje guje kawai zeyi a fili ya dirim Miliyoyi sun shiga akawun, shiyasa yake mulla ƙibarsa kai kuwa kana ta fama da dogon wuya kamar tsohon raƙumi takwaran ubanka". A Ƙofar ɗakinta take maganar ga Hajiya bata rage Volume dan haka hatta Momy dake cikin falonta suna magana da Baba Bilki sun jiyota. Baba Bilki ta girgiza kai tace
"Yau rashin mutunchin Binta ya motsa kenan, daɗina da ita bata bar kowa ba, kinji Mijinku ne takwaran tsohon raƙumi. Amma fa maganar gaskiya ki matsa Babana ya gaya miki me yake damunsa da gaske wannan ramar tasa tayi yawa, ni dana tambayesa yace wai aiki ne amma kuma wane aiki ne haka damuwarsa zata nuna har a fuskar mutum? Amadi da ko yaushe fuskarsa take a washe ga barkwanci amma yanzu se a wuni baka ga murmushinsa ba gaskiya ya kamata kiji damuwar yaron nan idan kuma naje Bechi daman zan karɓo masa taimako dan dole mahassada suyi masa caaa irin wannan buɗi da ubangiji yayi masa kiga komai yaro ya taɓa se ya zama kuɗi".
Tana rufe baki ya shiga falon da sallama ƙasa ƙasa, suka bishi da kallo harya zauna kusada ƙafafun Momyn. Murmushin yaƙe yayi ganin yanda suka zuba masa ido yace
"Lafiya dai Innata da Momy kuke kallona haka kamar kunga baƙo?" Inna yake kiran Baba Bilkin Jafar ma ya kama saɓanin sauran da Manyan suce mata Hajiya ragowar Baba.
"Ai dole mu kalleka Ahmad, kana duban kanka a Mirror kuwa? Wannan ƙasumbar da gashin daka tara a kanka na magani da menene?" Momy ta tambaya tana dafa kan nasa. Ya shafa gashin shima yace
"Lokaci ne ban samu naje aski ba amma yanzu idan na fita zanyi"
"Gara dai kayi ko ka koma hayyacinka amma fuska gashi biya biya kuma ba'a kintse ba ai babu kyau" Baba Bilki data miƙe ta sake faɗa yayi murmushi yana tambayarta fita zatayi tace masa Bechi zata tafi kwana biyu bataje ba sati zatayi kafin ta dawo.
"Da bana komai ai da na kaiki"
"Aa yi zamanka, tare zamu tafi da Yaya Yakubu ai can gidan nasa ma zan tafi yanzu"
"Toh Allah ya kiyaye hanya ki gaidasu" sukayi mata bankwana. Bayan fitarta Momy ta fuskance shi dakyau tace
"Karka boyemun komai ka faÉ—amun gaskiyar abinda yake damunka Ahmad".
Ya nisa kamar bazeyi magana ba se kuma yace
"Momy Fatima ce na kasa gane kanta"
"Matsala kuka samu?" Ta tambayeshi tana nazartarsa. Ya karkace kamar zeyi mata kuka yace
"Ni dai babu abinda nayi mata Momy itace dai bansan ko na mata wani abu ba. Gaba É—aya ta canza duk na kasa gane kanta".
"Ahmad kama Addu'a kuwa akan lamarin yarinyar nan?" Ta tambayeshi, yaja rantsuwa yace
"Wlh ina yi Momy, ko jiya kwana nayi ina sallah ina addu'ar neman zaɓin Allah amma wlh kamar an ƙaramun sonta a maimakon ya ragu a zuciyata"
"Kuma ba addu'ar son rai kakeyi ba? Kana cewa kana neman zaɓin Allah amma kuma ranka ba haka bane ka rigada ka zaɓarwa kanka abinda kake so?" Momy ta sake faɗa tana dubansa yace
"Momy shekara uku fa kenan, na san ba nacina ko dagiyata ce zata bani abinda nale so ba amma kuma Allah na barwa zaɓina ina ganin da inada wani haske daban bayan ita da yanzu na ganshi amma Momy ita ɗin dai ita na gani nake kuma ji a jikina itace matata".
"Toh addu'ar dai ita zamu cigaba dayi akan koma menene Allah ya warware sannan damuwar daka saka a ranka ba zata amfana maka komai ba kayi Ƙoƙari ka cireta, duk abinda Allahya saka cewar rabon bawa ne a duniya seya same shi idan kuma ba rabonka bane duk wuya haka zaka haƙura domin ba zaka sameshi ba. Sannan kuma ni ina ganin cewar harda halinka yasa yarinyar nan take maka koma menene"
Ya zabura yace
"Halina kuma Momy? Me nakeyi?" Momy tace
"Shekara uku kace da bakinka yanzu, wace irin soyayya ce haka har yanzu da za'ace ba za'ayi aure ba? Kaida bakinka kace mun mahaifinta yace maka ko tana cikin makaranta idan ka shirya aurar da ita zeyi to me kake jira har yanzu? Kana tsammanin zata cigaba da zaunawa tana ɓata lokaci dakai ne Alhalin ƙila tana da wasu masoyan da suka fika himma?"
Yayi shiru dan besan bayanin da zeyiwa Momy ta fahimta ba. Baya so ya ɓata Fatima a idonta ta hanyar sanar mata cewar itace har yanzu batayi na'am dashi ba kuma ita taƙi bashi damar ya tura ayi maganar auransu idan kuma yayi shiru Momy zata cigaba da bashi laifi na cewa shi yake ɓatawa Fatiman lokaci wannan yasa ta karkata hankalinta ga wani daya fishi himma kamar yanda tace.
"To ai Momy yanzu tana Level 4 har sun gama First semester da bari nayi tunda son zo ƙarshe kawai ta ƙarasa daganan se aje ayi magana"
"Oh so kakeyi harta gama makarantar tazo ta zauna sa'annan ka gama shiriritarka se aje ayi maganar aure ko? Lallai kuwa kana zaune nan zakaji wani ya aureta. Waima sanyar me kakeyi ne? Ina kace tun tuni ka sanar da Alhaji maganar nan me kake jira da ba zaka sake tayar masa da ita ba tunda ka nace lallai se shi zaka kaiwa maganar auranka?"
"Aa Momy ba haka bane ba, naga ai Alhaji ne Ahaƙƙu da na sanarwa da zancen aurena idan yaso shi kuma ya iya saka wakili ya shige mun gaba" ya bata amsa kai a ƙasa. Momy ta harareshi tace
"Sannu uban fitar da Ƙoƙon Asali, dama dai yanda kake da ƙulafucin uban nan shima haka yake ta taka amma na tabbata yanzu ya manta ma da kunyi wata magana data shafi zancen auranka dashi. Se kaje ka sake samunsa ai ka tuna masa, idan kuma yace Aa kaga aiseka fara sabon lissafi tunda ga tudun dafawar da duk yanda aka ciza ze tsaya maka kace baka san zance ba ba zakaje ta wurinsa ba".
"Ni Momy bana so a sakeyin irinta Yaya Sarki kina kallo dai Alhaji swda yayi ta faɗa akan ya zameshi daga maganar auransa shiyasa amma ba wani abu ba kuma nasan ai dai ko shi na gayawa dole dai Baba Alƙalin ze wakilta" ya sake faɗa Momy tace
"Ai shikenan, amma dai mafita guda ce in har da gaske kake son yarinyar nan manya su shiga maganarku, kaje ka samu ubanka ka fayyace masa komai ya tura a nema maka auranta in kuma zaka zauna nuƙu nuƙun ne kuma shikenan"
"Toh Momy zanje" daga nan suka bar maganar suka shiga wata. Bayan fitarsa ya ringa shiryawa yana warware ta yanda ze sake tunkarar Alhaji da zancen aurensa da Fatima. Amma ta yaya ma ze taso magana alhalin ita wadda za'a aura É—in bata yarje masa ba?
Ya samu jikin katanga ya lafe ya shiga kiran layinta, yanzu abin ya sake ta'azzara har rejecting take in bata ga damar amsawa ba kuma ya dameta, So hana ganin laifi haka yake jurewa domin ya yarda ƙaddarar sa ce Son Fatima. A kira na biyu ta amsa muryarta ta shaida masa bacci takeyi dan haka yace
"Kiyi haƙuri na tasheki a bacci"
"Babu komai ina zaune ne nima ban san baccin ya kwasheni ba, ina wuni?" Ta gaidashi. Tana da kirki, tana da tarbiyya, Mahaifanta mutane ne kai tana da duk wani quality da yake nema a gurin matar auransa baya zaton idan ya barta ze damu full option abinda yake nema a gurin mace tamkar nata ya ayyana a ransa.
"Kina free yau da dare zanzo?"
"Eh" ta bashi amsa a taƙaice, shikenan ya mata sallama akan se bayan Magriba zeje haka kuwa akayi yaje yayi aski ya ɗan shiga saiti ana sallar Magriba ya sha kwalliya ya tafi gidansu. A can yayi sallar Isha a masallacinsu Baffa kafin suka ƙarasa gidan tare. A ƙofar gida Baffa ya dubeshi yace
"Malam Ahmad na bawa Mamana Saƙo kusan sati nawa amma banji amsa ba".
Da rashin fahimta ya dubi Baffan kafin cikin girmamawa yace
"Ina ganin ta sha'afa ne Baffa ko kuma nine na manta da ta gayamun amma wace magana ce?"
Baffa yayi murmushi yace
"Dama maganar zuwan magabatanka ne nace lokaci yayi daya kamata ace manya sun shiga cikin maganar nan, ni badan ka buye ta tata ba kace a barta ta gama karatun kamar yanda take so ai da tuni kuma ka huta da biyo dare kana maƙalewa jikin katanga" Baffa yayi masa barkwanci. Yayi yar dariya yana sosa Ƙeya, Baffa ya sake cewa
"To ina sake maimaita maka tunda da alama ta sha'afa kamar yanda kace, a sanar musu saboda a san abinda ake ciki"
"In sha Allahu Baffa zan sanar musu" ya faɗa kai a ƙasa, Baffa ya wuce ciki yana masa Addu'a da fatan Alkhairi. Shiya turo masa Fatima wadda ta manta da batun zuwan Ahmad ɗinma seda Baffa yace mata yana waje. Dogon Hijab ta saka, bata shafa ko hoda ba ta fito tana bulbula ƙamshin designer perfumes ɗin da yake kai mata akai akai. Ta gaishe shi ya ringa kallonta kullum ya ganta ƙara sonta yakeyi, jinta yakeyi har tsakiyar ransa shi be taɓa sanin haka So yake ba seda ya afkawa kogin ƙaunar Fatima.
"Yanzu Baffa yake cemun ya baki saƙo amma baki gaya mun ba" ya faɗa yana kallonta. Ta juya ido abinda ya sake kashe shi kafin tace
"Wane saƙo kenan?"
"Ya wuce ai tunda ya faÉ—a mun da kansa. Magana ce akan turo magabata na ayi maganar auranmu, na so na gaya masa har yanzu bamu samu fahimtar juna nida ke ba amma kuma na kasa".
Ta ringa kallonsa babu ƙyaftawa harya kai aya kafin ta sauke kanta jikinta nayin sanyi kamar wadda rana ta daka, Ahmad ya harɗe hannu a ƙirji yana kallo ta ya sake cewa
"Baffa da kansa ya mun magana na turo neman auranki, kar kisa ya ɗaukeni a mutumin banza idan na gaza cika umarninsa. Fatima me kike da buƙata? Ki gaya mun dan Allah me nene dalilin daya saka ba zaki bani dama na shiga rayuwarki ba?"
A maimakon tayi masa magana kawai se gani yayi hawaye ya fara mata tsere dan da hasken Nepa tar a ƙofar gidan, ya buɗe baki yana kallonta da mamaki kafin yayi magana ta juya da sauri ta shige gida tana cigaba da kukan. Yayi kasaƙe a gurin, shi ba abin ya bita ciki ba mamakin dalilin kukanta ya rufeshi. Yana tsaye Baffa ya fito be ankate ba seda ya kira sunansa.
"Malam Ahmad lafiya kuwa naga ta shiga gida tana kuka ko wani abu ne ya faru?" Baffan ya tambayeshi. To shi me zece masa yanzu? Gaskiya ze faÉ—a masa ko kuwa yayi shiru Baffan ya zargi wani abun yayiwa yarsa?
"Wlh Baffa babu abinda ya faru, tambayarta kawai nayi ta amince na turo iyayena shine ta fara kuka ko magana batayi bama ta wuce ciki" ya faÉ—a cikin rawar murya. Baffa yayi ajiyar zuciya yace
"Kayi tafiyarka kayi abinda nace maka in har da gaske kake son aurenta ka turo magabatanka"
"Nagode Baffa in sha Allahu zaka jini bada daɗewa ba" daga nan yayiwa Baffa Sallama ya wuce, farin cikin daya samu dalilin ganinta ya gushe, har wani ciwon kai yaji yana neman kamashi kukan Fatima ya tabbatar masa da gaske bata sonsa tilas ya haƙura da wannan yarinyar muddin ba rabuwa da ita ne Ajalinta ba.
A can gidansu Fatima kuwa bayan Baffa ya koma ciki tarar da ita yayi tana sharɓar kuka Umma na tsaye kanta tana faɗa kamar zata rufeta da duka.
"Ya isa Zara'u rabu da ita" Baffa ya faÉ—awa Umman, ta zauna tana tsaki, ji take kamar ta rufe Afeeyar da duka ko zata maidata cikin hayyacinta.
"Duk menene dalilin wannan abun? Me ya sakaki kuka daga yace ze turo magabatansa dama bakya sonsa ne ko kuwa ra'ayi kika canza?" Baffa ya tambayeta. Bata amsashi ba se kuka da takeyi ƙasa ƙasa. Umma ta jefeta da takalmi tana cewa
"Ba magana ake miki ba kinaji kinyi shiru?"
"Nace ki barta Zara'u ko?" Baffa ya faɗa a ɗan fusace. Umma tayi ƙwafa ta wuce ɗakinta. Baffa ya sake duban Afeeyah, yanda taji muryarsa ta tabbata ransa a ɓace yake ta san kuma fushi ba ɗabi'arsa bace tabbas ta kaishi bango ne dan haka yana sake maimaita mata tambayar jiki na rawa taja baya daga kusa dashi kafin tace
"Ni daman Baffa ban taɓa cewa ina sonsa ba kawai bazan iya wulaƙantashi bane amma duk wata alama da ya kamata na nuna masa nayi amma yaƙi ya haƙura".
Baffa ya ringa kallonta har tayi shiru, yafi minti goma kafin ya iya cewa
"Kina nufin tsayin shekara uku da yaron nan yake bibiyarki yana wahalta miki duk ya tashi a banza yanzu zakice ba sonsa kikeyi ba?"
"Wlh Baffa ni ban taɓa cewa yayi mun abu ba, kuma ai ko kai kana hanashi amma se ya dage se yayi kuma ni ina gaya masa ya dena kawai shine baya ji"
Umma ta leƙo a fusace tace
"Dan ubanko dole yanzu kice bakya sonsa mana kuma bake kika saka ya ringa miki wahala ba, Kare ne shi da ze shekara uku saboda rashin zuciya yana tare dake kina nuna masa rashin So kuma yaci gaba da zama dake? Kin gama yaudarar sa kin ɓata masa lokaci saboda baki da mutunchi yanzu zakice bakya Son sa me yasa tun farko baki faɗawa Malam ɗin ba shi da kansa ya kirashi ya sallame shi se yanzu da koɗaɗɗiyar fuskarki zakicewa mutane ke daman bakya son sa to wlh baki isa ba" Umma ta shiga sababi harta manta darene ta muryarta a sama.
Baffa daya kasa magana tuntuni ya kalli Fatima yace ta wuce ɗaki, sum sum ta shige tana jin kamar an sauke mata wani nauyi daga kanta tunda har ta iya furtawa Baffa bata ra'ayin Ahmad tasan magana ta ƙare. A ɗaki Umma ta warwarewa Baffa komai game da zancen Yaron da Afeeyah take so wato Jay ɗan Ƙwallo.
"A ina suka haÉ—u?" Ya tambayi Umman, ta watsa hannu kafin tace
"Wai acan makarantarsu, Malam ka sanarwa Yaron nan kawai ya turo Iyayensa suzo a ɗaura musu aure kawai idan yaso ta mutu ƙarshen rashin Son Sa".
"Ba za'ayi haka ba, za'a bi komai a hankali, magita zata samu da yardar Allah" inji Baffa. Daren raba shi yayi yana sallah da addu'oi, ya kasance me yawan tsayuwar dare amma yau Umma tasan sallar tasa harda ta neman ɗauki gurin Allah kan wannan abin daya tunkaro shi. Baffa na Son Afeeyah, amma abu ɗaya da tayi imani dashi shine baze bi Son rai ya zubar da ƙimar sa ba shiyasa ya maida lamarin ga buwayin sarki gagara Misali wanda duk hukuncin daya yanke babu wanda ya isa yayi inkari akai.
Kwanaki uku Baffa ya jera yana Istikara cikin tareda tsananta Addu'a da roƙon ubangiji akan Al'amarin, Afeeyah kuwa rai fes dan Ahmad be sake kiranta ba tunda ya tafi kuma ta furta abinda yake ranta dan tasan Umma ta gayawa Baffa zancen Jay babban abinda ya sakat nishaɗi da farin ciki kuma shaida mata da Jay yayi yana tafe Nigeria nan da sati biyu masu zuwa. Saura kwana biyar su koma makaranta semester ƙarshe ce babu Lectures da yawa se aikin project da abinda baza'a rasa ba dan haka ta yanke ba zata koma bahar se yazo tukunna abinda bata taɓayi ba ƙarin hutu tunda ta fara University.
Ta gayawa Badar Jay yana tafe, Badar nason Jay da Afeeyah amma ba kamar yanda take sonta da Ahmad ba kamar yanda take ce mata Ahmad Mijin Aurene Jay kuma na rage lokaci da neman suna domin ita dai bataji a jikinta Jay auran Afeeyah zeyi har yanzu ba duk kuwa da tarin ƙaunar da yake nuna mata akan haka har faɗa suka sakeyi ta dai rabu da ita tana kuma yi mata addu'a a matsayinta na ƙawarta.
Takanas taje gidan Anty Sauda tace mata nan zata fara kawo Jay kafin Umma ta sauka daga fushin da takeyi da ita tukunna se ta kaishi gidan.
"Yanzu kina ganin abinda kika zaɓawa kanki daidai ne Afeeyah?" Anty Sauda wadda Umma ta gaya mata duk abinda ya faru ta tambayeta.
"Haba Anty dan Allah wai ana aure dole ne? Naga kema zaɓi aka baki kika kawo wanda kike so me yasa ni ake nema a tauye mun haƙƙi?" Ta jefawa Anty Saudan tambaya. Seta girgiza kai kawai tace mata Allah ya kawo Jafar ɗin lafiya, bata wani jima ba ta koma gida dukda zaman gidan ba wani daɗi yake mata ba yanzu saboda yanda Umma ta canza mata. Daga ita har Baffa babu wanda ya mata zancen ganinbata koma makaranta bama se Yah Malam daya zo hutu ne yace ya ya ganta a gida tace se wani satin zata koma. Baffabe canza mata kamar Umma ba dan ze amsa gaisuwarta har ya sakata aikace aikace kamar yanda ya saba amma Umma ko gaiseta tayi da harara take amsa mata tti duk yanda zatayi Umman ta sakko amma abu yaci tura tasan dai fushin Umma akan Ahmad ne addu'a takeyi Allahya kawo Jafar wanda yace zuwa ɗaya zeyi kafin yayi na biyu za'a tambaya masa auranta dan ya matsu.
"Yah Ahmad ka dena sona wlh, yanzu ace zanzo gida amma babu wani murna ko ɗokin gani na daka sabayi kawai Allah ya kaimu shikenan abinda zaka ce?" Jafar ya dasawa Ahmad mita akan beyi murna daya ce masa zezo gida ba. Ahmad daya kwanta zazzaɓin malaria kamar yanda yayiwa Momy ƙarya amma gaskiyar abinda yake damunsa Love sickness ne. Tun ranar daya baro gidansu Fatiman damuwa ta saukar masa da ciwon kai da zazzaɓi me zafi amma haka yake bankar Anti Malaria da Momy tasa dole yaje asibiti aka rubuto masa.
"I told you bani da lafiya Jafar amma kana ta so se ka sakani magana"
"Ni ai bazanyi maka sannu ba saboda wannan ciwon kai ka É—orawa kanka, let me ask you please, is this Fatima made of Gold or some sort of precious stone da tayi deserving wannan soyayyar da kakeyi mata?
Yah Ahmad me yake damunka? For heaven sake kana nema ka kashe kanka akan wata banzar mace? Is she the only living woman on earth? Ko dai asiri tayi maka? Oh na manta mayyace believe me ta cinye maka zuciya kuma wlh bata isa ba. Ko waye ubanta she must leave you, seta fita a rayuwanka let me come back first I'm going to deal with her personally, se ta gane bata da hankali wlh" ya ringa sababi kamar ze aro baki daman kuskure Ahmad yayi daya taso masa da maganar gashi yana neman ya sake ƙara masa ciwo.
"I love her, kuma banajin zan iya dena sonta idan da abinda zakayi kasa ta soni i will appreciate it more zaginta da kakeyi dan baka san abinda nake ji bane ba nidai idan kana sona da gaske just help me fight na samu Fatima" Ahmad ya faɗa. Jafar yayi shiruj irin wanda takaici ya gama tiƙewa kafin yace
"Indai haka ne ze sa ka yarda Ina sonka then I don't love you Yah Ahmad and i will never love you indai se naso wannan yarinyar ne ka cireni a jerin ƙannenka, i hate her, i hate her with all my life kuma ko Allah yasa ka aureta bazan taɓa shiga gidanka ba" yana gama magana ya kashe wayansa yanda Ahmad ya jishi yasan ba ƙaramin zafi ya ɗauka ba. Yayi murmushi, yasan rigimar Jafar na lokaci ne zuwa anjima ze sake kiransa kawai dai wannan ƙiyayyar da yakeyi mata me zafi ce ya rasa dalilinta, saboda shine kuma yanzu so yakeyi ya haƙura da ita ba shikenan ba.
****************
"Alhaji, ni tun kwanaki naji kana zancen Amadu ya samu mata ko? Ashe ma ya taɓa kaiwa Ummu ita, se jiya da muke magana Jafaru yace daya zo za'aje masa neman aure shine tace mun zancen ai taga budurwar Amadun ma ya ɗaukota daga makaranta suka biya gidanta wai ya karɓowa Aisha Leshi, wai a Zaria take makaranta, nace Yayan masu kuɗi suna zuwa wannan makarantar kuwa?"
Alhaji Audu na kurɓar baƙin shayi daya sha spices, Girkin Hajiya Rabi ne ita ta dafa masa tana kawowa Hajiya Bintan tazo ta kankane gurin dole ta fita ta bata guri dan har ta fara sakar mata maganganu tana ci mata zarafi shi kuma Gwankin na zaune shirim bece komai ba. Ya gama sauraron Hajiyar kafin yace
"Oh ya samu mata kenan da yake ke zaki nemo masa auran shiyasa ya fara sanar dake?"
"Shi wa? Ummu nace maka ni a suwa Amadu ze faɗamun ya samu Matar Aure Aisha ce ni kowa?" Ta faɗa tana wani taɓe baki. Alhaji ya sake zuba shayinsa yana sha yace
"Shi ÆŠan naki nake magana"
"Wai Jafaru? Dama idan be gaya mun ba toh wa kake so yaje ya fara sanarwa ko yana da wata uwar ne bayan ni a duniya?"
"Aa bance ba, shi Ahmad É—in dake ya É—aukeni uba ai tun fara neman yarinyar da yakeyi ya sanar dani, kawai inda ya nemo auran ne be gama kwanta mun a rai ba shiyasa ma kika ga an kawo yanzu maganar bata tashi ba amma yafi shekara da sanar dani".
Har wani zullo tayi kamar zata kwanta a gabansa tace
"Ashe maganar ta daÉ—e? Daman Ummu tace anfi wata shida da zuwan nasu tun kafin lokacin bikin su Hafsatu to ashema ka sani toh naji kace gidan daya nemo auran ne beyi maka ba, da akwai matsala kenan?"
Da zuciya É—aya yace mata
"Yar wani Bakanike ce yarinyar Malam Hafizu akace sunansa a Alfindiki yake, a binciken da na saka akayimun dai Mahaifin yarinyar nace bashi da matsala mutumin kirki ne toh amma ita yarinyarce surutu yayi yawa akan yanda Samari suke zuwa gurinta wannan yazo wannan ya tafi gashi a matsayin mahaifinta irin rayuwar da akace tanayi ta wadata ya zarce ace shi yakeyi mata, kinsan yaran yanzu, zakiga Iyaye suna iyakacin ƙoƙarinsu gurin tarbiyya amma idan sun fita se abinda hali yayi musamman masu tafiya karatu wasu garuruwan ba gaban Iyayen nasu ba to wannan yasa na dakata kuma shima Ahmad ɗin tun maganar farko da mukayi be sake tayar mun da zancen ba dukda dai ina da labarin suna tare haryanzu kuma ita kaɗai yake kulawa ta yuwu yana jira ta kammala makaranta ne tunda ance shekarar ƙarshe take".
Tamkar me É—aukar karatu haka Hajiya ta naba'a tana sauraron Alhaji se gyaÉ—a kai takeyi har ya kai aya kafin cikin Jimami tace
"Ikon Allah, shi kuma Amadu inda ya tafi kenan? Nida nake ta sauraro naji ya samo yar gidan Ɗangwate ko BUA tunda suke abokanan goga kafaɗarka a ƙasar nan seya ɓige da yar gidan Bakanike? Toh Allah ya rufa asiri, ita dai ta Jafaru ance Balarabiya ce dan ya turawa da Munirah hotonta wai irin wanda ake kalla sau ɗaya ne shiyasa bata kwafa ba ta ajiye mana. Todai daya zo koma ya ake ciki zamuji, seka fara shirya wa'inda zasu nemo masa auran inajin dai baze wuce a Saudi Arebia ba ko Dubai"
Alhaji yace mata
"Toh, Allah ya kawo shi lafiya"
"Toh amma Alhaji ina da wata magana idan babu damuwa kuma ka bani dama in faɗa" yanda tayi maganar yasa ya tattara hankalinsa akanta dan yaji me zatace. Hajiya ta gyara zama kamar gaske kai a ƙasa tace
"Dama Alhaji akan mu'amalarka da yaran gidan nan ne naga ya kamata a gyara wasu abubuwan, ina nufin su Alhaji Babangida da sauran yaran da basa cikin gidan nan. Bana jin daÉ—in yanda kowa idan ya tashi yake É—ora mun laifi a ringa cewa ni ce na rabaka da yayanka.
Kaga girma ya cin maka, ya kamata ace zuwa yanzu ka fara sakin wasu abubuwan ka bari Manyan yayanka suyi maka".
Alhaji yayi tagumi yana kallon Hajiya Binta data sake gyara zama tana cewa
"Ba harkar kasuwancinka nake nufi ba, wannan ai kana da magada daka rigada ka koya musu komai kuma suka goge akai ina nufin kamar harkokin aure, kaga daga kai har Yakubu kun manyanta ya kamata ku zauna ku huta ku fara sakarwa Yayanku suna jan ragamar abubuwa".
"Wato ba zaki ringa karanta sunan Yakubu ba, Idan beci darajar girmata da yayi kin kirasa da Yaya ba ai kya bashi sunan da kowa yake kiransa dashi Alƙali" Alhajin ya tareta. Ta lanƙwashe kamar yarinya tace
"Allah baka haƙuri saboda faɗa ne uffararan Baba Alƙali nake so nace, to da kai dashi duk ku huta ka kirawo Yayanka gaba ɗaya ka zaunar dasu kuyi maganar nan, ka ware wanda zasu ringa zuwa tambayowa Maza aure da kuma wanda zasu ringa karɓan na mata idan an zo. Amma kafin nan ya kamata duk wani abu daya taso ka ringa tarasu kana shawara dasu, ta hakane zaka jasu a jiki suma su sake dakai a hankali se kaga duk sun dawo gida a dena zagina a gari ana cewa na raba yaya da ubansu".
Alhaji ya sakeyin shiru yana nazarin maganarta, Alƙali Yakubu ya taɓa yi masa makamanciyar magana irin wannan, yace ya kamata ace ya ringa janyo Yaransa a jiki domin ya gyara kuskurensa na baya. Rayuwarsa ta fara zuwa gangara, be kamatu ace ya mutu ya bar kan iyalansa a rarrabe kamar yanda suke a yanzu ba. Maganar Bintan se ta sakashi Nazari, tabbas abinda ta faɗa gaskiya ne domin Abokanansa masu Manyan Yaya kamar nasa da yawa yanzu a kwance suke suna hutawa komai da masuyi musu, ze gwada shawarar tata koda akan zuwa batun Neman aure ne da karɓar ze saka su yasan babu wanda zece bazeyi ba a cikinsu.
"Kamar yanzu da zancen auran Ahmad dana Jafarun nan musamman na Ahmad da kake da kokwanto akan yarda ko akasin haka, ka tarasu, ka nemi shawararsu kaga zasuji daÉ—i suga ka mutuntasu kuma su sun fika sanin kan duniya yanzu se kaga an samu maslaha ai ko?" Ta sake faÉ—a. Alhaji ya jijjiga kai da alamar gamsuwa, tayi murmushin cin nasara sannan tace
"Toh amma fa karka gayawa matanka ko Yan uwanka shawarata ce dan ka san cewa za'ayi da wata manufa nayi ni kuma Allah yaga zuciyata babu komai face Alkhairi so nakeyi ka shirya da yayanka ka haɗa kan zuri'arka", bata tashi daga gurin ba seda ta gamsar da Alhaji Alfanun abinda tace yayin ya kuma yarda da hakan. Babu ɓata lokaci a daren ya kira Alhaji Babangida, umarni ya bashi akan ya haɗo masa kan Yan uwansa daga Babannan zuwa Mu'allim, banda Matan da kuma Zayyad da Abdallah da basu isa ayi wannan shawarar dasu ba. Alhaji Babangida ya shiga mamakin ko lafiya wannan kira haka da Alhaji yayi musu amma babu damar tambaya. A washe gari ya sanarwa da waɗanda yake da numbers ɗinsu a waya ta hanyar Text message yace su sanar da sauran. Ya sake kiran Alhaji domin ya manta be tambayi ranar da yake da buƙatar ganinsu ba.
"Ranar Asabar É—in nan" Alhaji ya bashi amsa. Alhaji Babangida yace
Zan sanar dasu ranar, amma naji Jafar yana tafe ranar Talata, ba za'a iya É—age taron a jirayi zuwan saba?"
"Aa, duk abinda aka tattauna idan ya dawo zaku sanar dashi" da haka sukayi sallama. Ya gayawa Alƙali ze zauna da yaransa duka ya kumayi murna da hakan domin an samu cigaba kenan Alhaji Audun ya shiryi samun daidaito tsakaninsa da Iyalansa.
PAGE 17
A bisa dole Iyalan Alhaji Audu suka amsa goron gayyatar daya aika musu dashi. Ba kalar mitar da basuyi ba amma haka suka zo domin koda basa ga maciji da mahaifin nasu sun sanshi sarai baya É—aukar wargi, farillan rashin mutumchi kuwa sala sala yanadasu wanda yake amfani dasu gurin ladabtar da duk wanda yace zeyi masa giggiwa.
A cikin su daman wanda yafi kowa taurin kai Alhaji Hussaini ne, da Dr Hassan ya sanar masa da kiran Mahaifin nasu take yace masa
"Bazanzo ba, inada abubuwan da suka fi muhimmaci da sauraron kalaman son rai da wannan tsohon ze faɗa mun in kuma ya fara tafiya gargara ne yake so ya bada wasiyya ka karɓa harda tawa ka riƙe na bar maka in ma mutuwa yayi ni wlh na yafe gadonsa tuni". Seda Hajiya Zubaida Mahaifiyarsu tayi masa kaca kaca bayan da Dr Hassan ya sanar mata da abinda yace tace kuma tilas yaje idan kuma ya isa ya tsallake umarninta daman ita kaɗai take maganin Iya shegensa, yana son mahaifiyarsu yana tausaya mata yana kuma riƙe da abinda aka labarta musu cewar Alhaji Audun yayi mata tun kafin haihuwarsu da bayan zuwansu duniya.
Ƙwato su da yayi ya maidasu gidan ya zube su a tsakar gida shine abun daya ƙara ta'azzara tsamar dake tsakaninsu. Yanda Hajiya Binta ta ringa yi musu, kalar azabatarwar da tayi musu har gobe yana addu'ar kafin ta mutu in sha Allahu seta ɗanɗani sama da baƙin cikin data shayar dasu. Matan da akace banda su dalilin irin wannan taro da ba'a taɓa yin irinsa ba suka san lallai da akwai wani babban Al'amari a ƙasa wannan tasa kowacce ta wanko ƙafarta ta taho ranar taron. Momy da Hajiya Rabi basu san wainar da ake toyawa ba har s ana i gobe taron da suka tsinkayi muryar Hajiya Binta na bada umarnin abinda za'a girka gobe da yawan wanda za'ayi. Lokacin Salim na falon Momyn yana cin abinci yayi tsaki yace
"Wai me matar nan take shiryawa ne? Dan dai Alhaji bashida wata shawara tasa ta kansa se abinda tace masa"
"Wani abu ya faru ne?" Momy ta tambayeshi shine ya faÉ—a mata kiran da Alhajin yayi musu. Tayi shiru, ita tayi girki jiya yauma itace amma ace Alhajin bega ya kamata ya sanar mata da komai ba ai shikkenan. Bata masa zancen ba har washe gari da Asuba kafin ta baro bangaren nasa taji yana waya da wani abokinsa yana sanar masa baze samu zuwa wani É—aurin aure ba shine bayan ya gama yake ce mata wai ze gana da Yayansa duka akan maganar aurab Ahmad.
Cikin mamaki tace "maganar auran Ahmad kuma? Yaushe zancen ya taso da ni ban sani ba? Sannan naji kace zaka tattauna da Yayanka akan maganar daman haka kakeyi idan auran yayan naka ya tashi ko kuwa wani sabon salo ne ka tsiro dashi da za'a fara akan Ahmad?"
"Ya zaki ringa min wasu tambayoyi se kace wani ɗanki? Tsakanin nida ke waye yafi zamarwa dole daya san maganar auran Ahmad ko kuwa ke zakije ki tambayo masa auran?" Alhajin ya faɗa yana wani zare mata ido irin ta zo masa da raini. Zuciyarta ta harzuƙa domin ta tabbatar wata maƙarƙashiyar ce aka shiryota kuma Binta ce idan ba haka ba ita dashi basu taɓa zancen auran Ahmad ba, tabbas Ahmad ya gaya mata iyayen yarinyar sun bashi izinin ya turo magabatansa har yace tayiwa Alhajin magana tace ba zatayi ba ya same shi da kansa bayan nan kuma ya fara rashin lafiya ta tabbatar da ace sunyi magana da Alhajin tilas seya gaya mata yanda sukayi domin a ko ina zata shaideshi baya abu gaban kansa ba tareda yayi shawara da ita ba kuma duk yanda ake ciki seya koma ya gaya mata ta sake bashi haske akan abinda ya kamata yayi.
To ace ma Ahmad ya masa magana sun tattauna shiya manta be koma ya gaya mata ba ai shi Alhajin a matsayinta na uwar Ahmad tana da haƙƙin ya sanar mata da zancen auransa ba wai taji a sama yaje ya shawarta da wadda a kullum bata da burin da taga kasawarsu. Ta sani ya fayyacewa Binta inda Ahmad ya nemo aure shine zatayi amfani da hakan dan ta tozarta yarinyar da iyayenta toh kuwa Allah ya fita ba zata taɓa cin galaba ba.
"Ai ko riƙon Ahmad nakeyi ba wai ni na haifeshi ba ya kamata a fitar mun da ladan wahalata a sanar mun da zeyi aure, kuma a gidan nan baka taɓa haɗa taro dan wani Ɗa zeyi aure ba akan me za'a farashi akan Ahmad? Saboda shi me biyayya ne duk yanda aka bi dashi zece toh shi yasa kake so ka tauye masa haƙƙi ko yaya?"
"Ki fita kuma ƙarfe goma ne taron, umarni ne na baki ba wai shawara ba ki kasance a gurin" ya bata amsa cikin halin ko in kula ba tareda ya bi ta kan maganganunta ba. Hawayen takaici suka zubo mata ta share ta fice daga ɗakin, tana can ƙuryar ɗakinta ta kira Yar uwarta Maimuna ta gaya mata abinda ake ciki.
"Kije ki zauna a gurin saura kuma ki zama hoto kiyi shirun da kika saba a zartar da abinda ba haka ba dan nasan munafunci yasa aka shiryi wannan zaman ba wai dan Allah bane" Maimuna ta gaya mata. Tana shirya masa abin kari Hajiya Rabi ta shiga Falonta. Suka gaisa take tambayarta zaman da Alhaji ya kirata a waya yanzu yace mata wai ƙarfe goma.
"Nima da Asubar nan ya gaya mun wai akan Ahmad ne, amma ita hamshaƙiyar ai tasan da komai tunda tun jiya naga tana bada umarnin abincin da za'a dafa" Momy ta bata amsa tana murmushin takaici. Hajiya Rabi cikin jimami tace
"Ahmad kuma? Nasan dai ba laifi yayi ba koma menene Allah yasa Alkhairi ne, bari naje na shirya toh" daga haka ta wuce tana ta lissafin to wane irin abu kuma Ahmad yayi ko zeyi da har se an masa taron dangi haka?
Tun tara Iyalan Alhaji Audu suka fara hallara a gidan. Wasu su kaɗai suka zo wasu tareda yayayensu da matansu dan haka gidan ya cika hayaniyar jikoki kota ina tashi takeyi suna ta guje guje. Ƙarfe goma Mazan suka hallara cikin babban falon da ke bangarensa a ƙasa gaba ɗayansu Jafar ne kawai babu a gurin.
Bayan an buɗe taro da Addu'a tareda jawabin maraba daga uban garken, babu ɓata lokaci ya shiga zayyano musu maƙasudin kiransu wannan taro.
Shiru falon ya ɗauka banda ƙarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare ɗaya, yanda takeyi seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar, tamkar bada ita ta tsarawa Alhajin daya tara su ba domin ta ƙaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miƙe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai ƙasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taɓa haka? Shi yaushe ya cewa Alhajin maganar aurensa ta tashi? Auran da yake ƙoƙarin yakicewa ya haƙura da yarinyar shine aka zo ana masa wannan taron dangin akansa?
"Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kuÉ—i kamar Æarawo?" Hajiya Bintan ta faÉ—a, Momy ta É—ago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jiÉ“anci gudan jinin nata da ita wai Æarawo ita kuwa Hajiya bata dakata ba a fusace taci gaba da cewa
"Wallahi tallahi ko sama da ƙasa zata haɗe banga uban daya isa ya ƙulla auran nan ba, yar Bakanike Amadu? Mu zamu haɗa surukuta da Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba. Iyakar irin tsiyar da aka ɗakko mana sun isa ba se an haɗo mana da wanda zasu zo suna mana ɗauki ɗaiɗai suna ciyayya ba" Hajiyar ta kai aya tsabar masifa numfashinta har neman sarƙewa yakeyi.
Alhaji Audu dake kishingiɗe akan kujera ya nisa yace "Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun ƙi da ze saka a hana shi auranta ba, ni kiram da nayi muku na taraku ne dan muyi shawara akan yanda za'abi gurin neman auran, suwa za'a wakilta suje".
Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani É—anta tace
"Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman"
Mamaki kamar ya shaƙesu jin abinda Hajiyar ta faɗa masa, kunne, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze ɗauka amma sukaji muƙus ko tari Alhajin beyi ba sema Hajiya data ci gaba da sababinta tana cewa
"Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka jikar talaka kuma Mayya".
"Amma Hajiya talauci fa ba fasiƙanci bane, sannan baya cikin sharuɗɗan da suke hana aure. Kuma maita da kike jifanta da ita kin san cewar fa ba ƙaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin ƙararki akan hakan tunda baki da wata tartibiyar hujja data tabbatar da abinda kike jifansu dashi" tsautsayi ya saka Hajiya Rabi magana tamkar kuwa Hajiya Binta na jiranta daman tace
"Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu ƙarin yar uwa ko Ahalul fuƙara'u za'a ƙara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tsayayyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba da se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa ƙaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta faɗi, daka fita ka bashi kuɗin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya ƙare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi ɗan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar nan da yakeyi ina ganin har sun fara lasar sane wlh sun zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta faɗa tana tsaida idonta akan Alhajin.
Baƙin cikin maganganunta suka sanya Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru kusan Ashirin kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake ƙara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar Ƙoƙari yanayi cikin su ukun ita kaɗaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kuɗin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar ɗabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kuɗi, ya dai rage amma fa kullum yana tafe gidan Alhaji Audu, sabulun wanka omon wanke wanke ko yana da kuɗin da ze siya se yazo ya roqa an bashi.
Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu'allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara ƙwallar baƙin ciki
"Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin faÉ—i" Hajiyar ta faÉ—a tana buga cinya kamar wata yarinya.
Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace
"Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba tun da dai ba ɗanki bane. Ita mahaifiyarsa batayi ƙorafi ko nuna rashin amincewarta akan abun ba se ke meye naki a ciki? Sannan koda ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za'a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane"
"Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taɓa titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yaranmu shaiɗanci amma waya ɗaga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba'aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze haƙ
Lura ai biyayya kuma ba hauka bace" Dr Hassan ya faɗa cikin ƙunar rai.
Hajiya ta harari Alhaji Babangida, koda ta girme shi amma shakkarsa takeyi ta san ko shi Alhajin yana bashi darajar kasancewarsa Ɗa na fari a gidan, maganar Hassan ce tasa tayi kasaƙe tana kallonsa. Naziru ya zaburo masa yana cewa
"Ka kira sunana kai tsaye ka dena wani kwane kwane, kuma na auri yar Tiktok É—in koda abinda zakayi akai?"
"Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi" Hajiya ta gyara zamanta taci gaba da cewa
"Yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al'amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa ai dole kace wannan ma ba......"
Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama da saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta maƙalewa. Cikin yanayin da yake nuna ƙololuwar ɓacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fito ruɗu ruɗu haka idonsa ya rikiɗa yayi jajir ya nuna ta yana cewa
"Akul Binta, duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan waÉ—anda kika raina karki yi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki domin yanzu ba da bace idan kuma ba haka ba...."
"Idan ba haka ba me zakayi?" Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata jikinta har ɓari yake ta ja hannunsa Zakariyyah tana cewa
"Barshi Ubana kasan É—an hau ne"
"Ki ƙyaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da ƙwaya yake ji dasu shi ƙaramin ƙwarone kansa baze ɗauki ko rabin chajin da nakeyi ba an faɗa ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak...."
Marin da Hussanin ya ɗaukeshi da shi irin me jirkita ƙwaƙwalwar nan ya sakashi wuntsilawa gefe dafe da fuska yana raba idon, Hajiya Binta ta fasa ihu tayi kansa ganin yanda yake zare ido kamar tunaninsa ya kauce, a fusace shi kuma Naziru ya cakumi kwalar Hussanin ya kai masa naushi a fuska yana cewa
"Wlh baka mari banza ba sena rama masa" kafin kace me dambe ya sarƙe a tsakaninsu kowanne ya shiga kaiwa ɗan uwansa mugun hari da yake jikinsu iri ɗaya ne, dukkaninsu sangangan suke irin jikin Audu Bechi wannan ya ƙarawa Damben nasu armashi dan kowa ya gagara kai ɗan uwansa ƙasa amma dai Hussainin yafi kai hari a zuciye.
Ahmad, Momy da Dr Hassan ne suka shiga ƙoƙarin raba su sauran jama'ar falon kuwa seka rantse a Tv suke kallon wannan Al'amari babu wanda ma ya motsa balle ya kai agaji sema tattare ƙafafunsu da sukayi dan kar a faɗo musu. Hajiya na gefen Alhaji Zakariyyah dake kururuwa kamar mace sakamakon yanda Marin ya shammaceshi ya shige shi dagaske ga haƙorinsa ɗaya daya turguɗe a ƙasa, ihu Hajiyar take itama tana Zagin Hussaini, jafa'in duniya babu wanda bata janyo masa ba dashi da Hassan ɗinsa harda uwarsu dake can gida bata san wainar da ake toyawa ba ta karɓi rabonta se abi da Hajiyar ta manta ne bata ambata ba.
Momy ta kalli Alhaji Audu dake zaune akan kujera tamkar gunki cikin kuka tace
"Kana kallo Alhaji, jira kake se ɗaya ya kashe ɗaya kafin ka tsawatar musu? Wannan shine daidaiton da kake fatan samuwarsa cikin zuri'arka? Anya kuwa Alhaji ka shiryi tarar da ubangijinka cikin salama kamar yanda kowanne musulmi yake fata?" Tana gama faɗar haka cikin kuka ta fice daga falon, a bakin ƙofa taci karo da yayansu Mata a tsaitsaye cikin tashin hankali. Hajiya ƙarama datafi kusa da ita tacewa
"Kira Babanku Alƙali ki gaya masa yazo babu lafiya a gidan nan" ta shige cikin gida tabar Hajiya ƙarama na ƙoƙarin kiran Baba Alƙali amma sau biyu wayar na suɓuce mata saboda yanda jikinta yake rawa daƙyar ta iya danna kiran.
Momy kuwa harta isa ɗakinta hawaye be tsaya mata ba, ba kuma tasan ranar da zata dena zubar dasu ba hawayen baƙin ciki, takaici da dana sanin auran wannan mutumin da sam bata san me zata kirashi ba. Son zuciyane ko kuwa tsabar ƙin Allah ya saka Alhajin yin abubuwan da yakeyi bata sani ba amma koma menene ta tabbata muddin be tuba ya gyara alaƙarsa da Ahalinsa ba ya mutu a haka tabbas baze kwanta cikin salama a Kabarinsa ba.
A can falon kuwa Hussaini ya mazge Hassan ɗinsa daya cukumi cikinsa yana ƙoƙarin janyeshi kafin ya kaiwa Ahmad ƙafa amma ya goce ba shiri suka matsa daga rabon damben suka barsu zuwa sannan Hussainin keda nasara dan ya kai Naziru ƙasa ya masa lilis har ya kai baya iya maida martani se Ƙoƙarin kare kansa kawai yake amma Hussaini be haƙura ba yaci gaba da jibgarsa kamar Allah ya aiko shi. Dama ce irin wadda ya daɗe yana fatan samu da ze huce kaɗan daga irin takaicin da Hajiya Binta da Yayanta suka ƙunsa musu a rayuwa. Lokacin yarinta tsoron hukuncin da Alhaji zeyi musu da izayar da zasu sha a hannun Hajiyar tasa yake haƙura idan zuciyarsa ta raya masa daya jibgi yayanta in suka musu abu, yasha ya kwatanta ya dake sun in yaso ya gudu ya bar gidan amma yasan Hassanbaze yarda ya bishi ba, saboda shi ya shanye duk wani wulaƙanci a gidan yanzu kuwa Allah ya bashi damar da duk wanda yace ze shigarwa Nazirun seya haɗa dashi ya zane.
Seda Hussani gama yayiwa Nazirun casar gero kafin Allah ya bawa Alhaji Audu ikon yunƙurawa daga zaunen da yake tamkar wanda ya tafi hutu wata duniyar na wucin gadi ya dawo haka ya shiga jan numfashi kamar me Asthma. Ahmad yayi kansa yana cewa
"kun gani ko ku bari idan ba kashe shi kuke so kuyi ba".
Hussaini daya gama aikin Allah ya tsugunna ya É—auki Agogon Azurfarsa daya tsinke a garin dambe bayan daya gaji da jibgar Naziru ya kalli Ahmad yace
"Toh ya mutu mana, dama wa rayuwarsa ta dama bare idan ya mutu yayi baƙin ciki? Ƙilan ku da su daya ɗauka Yaya ya fifitasu akan kowa sune zasu shiga uku duk ranar da aka ce babu shi" sannan ya kalli Hajiya Binta da idanunsa da suka koma abin tsoro yace
"Nan gaba idan wani daga cikin marasa kunyar Yayanki yayi niyyar tsoma baki a sabgata ki gargaÉ—eshi, idan ba haka ba zanci gaba da nuna muku abun da ÆŠan Tubabbiyar karuwa ze iya aikatawa" yana gama faÉ—ar haka ya fice daga falon a fusace fuuuu kamar kububuwa.
Maganganun Hussaini sun daki ƙirjin Alhajin kamar shigar bullet, ya yunƙura cikin wani yanayi ya tashi tsaye dan bakinsa kamar an liƙe masa shi da glue yake ji yana tsayuwa akan ƙafafunsa jiri ya kwasheshi ya koma kan kujerar Yaraf kamar wata gingimemiyar giwa ta faɗi. Ahmad da Hassan suka rufu akansa, Hassan ɗin ya kalli Ahmad yace
"Riƙeshi, bari na ɗakko Kit ɗina a mota mu gani idan kuma babu hali mu wuce Asibiti dashi kawai" yana gama faɗar haka ya fice da gudu kamar yaro ya nufi motarsa.
Da wani irin yanayi Alhajin ya ringa kallon Yayansa Maza da suka fara miƙewa da ɗaɗɗaya suna barin falon harda masu sakin ƙananun tsuka dalilin ɓata musu lokaci da akayi da wannan wasan kwaikwayo da suka rigada suka saba dashi babu Wanda ya nuna damuwar cewa wai Mahaifinsa ne a wani yanayi da ko ba'a faɗa ba sunsan Hawan Jininsa ne ya tashi Allah ma ya taƙaita ba Paralysis ya samu ba irin wannan komawa da yayi ya faɗi akan kujera, wani abu ya tokarewa Alhaji Audu maƙoshi, hawaye ya ziraro a idanunsa abinda ya sake rikita Ahmad kenan a shekarunsa Talatin a Duniya sau ɗaya ya taɓa ganin ƙwalla a idon Mahaifinsa lokacin da aka kawo gawar Brigadier General Baballiya se yanzu kuma hawaye yake dagaske tabbas Al'amarin dake zuciyarsa ba ƙarami bane.
Yanda Dr Hassan ya dawo yaga Alhajin yasa yace kawai su kamashi a tafi Asibiti. Seda ya É—ura Ashar kafin su Salim suka saka hannu aka fita da Alhajin dan Manyan daman tun yana wajen yaga suna ta shigewa motocinsu suna jiran Iyalansu su fito su tafi, da alama Abincin da Hajiya tasa akayi zeyi bandaro dan zama beyi daÉ—in da har za'a jira cin abinci ba.
Hajiya ta ringa ihu kamar wadda ta shiga ƙaramin hauka, Ga Zakariyyah fuska harta suntume saboda haƙorin daya fita ba bisa ƙa'ida ba Naziru kuma na kwance numfashi ne kawai ya banbantashi da matacce Hussaini ya sauke masa duk wata giggiwa da yake fama da ita suma ɗin Dr Hassan ne yasa aka watsa su a mota duk suka rankaya a Asibitinsa. A hanya Ahmad ya kira Baba Alƙali yace masa yana tafe ya kusa isowa gidan Hajiya ƙarama ta kirashi se yace masa ai suna hanyar Asibiti be jira jin ba'asi ba yace ze same su acan domin yasan a runa.
Haka nan rana tsaka Audu ya tattaro irin wannan haɗuwar ba tareda yabi matakan da suka dace ba, zuri'ar da kowanne yake da wani fushi ko miki a zuciyarsa ta yaya zaka ce a lokaci gida zaka sasanta komai ka samu yanda kake so? Ya tabbatar wani abun akayi ko aka faɗa masa da ze saka jininsa ya hau tilas Allah dai ya taƙaita.
Emergency aka karɓi Alhaji Audu su Naziru ma aka watsa su inda ya kamata. Seda akayi stabilizing kowannensu kafin suka samu nutsuwar zuciya. Baba Alƙali ya ringa sababi kamar ya ari baki sanda Dr Hassan ya bashi taƙaitaccen labarin abinda ya faru.
"Ka kira Hussainin ka mai komai dare ya sameni a gida yau wane irin abu ne yake damunsa duk me ubanku ya muku ai baze canza masa suna ba ya za'ayi ya faɗa masa irin wannan maganar? Kai bama shi kaɗai ba gaba ɗayanku ku hallara ina son ganinku tunda naga alamar so kukeyi ku janyo mana abinda ze fi ƙarfin mu".
"
"Nima dai haka na gani Alƙali, ni daga yin abu dan Allah da zuciya ɗaya nace a shirya taron nan ya janyo yayansa a jiki su samu daidaito amma kaga yanda abu ya ƙare dana sani bance ayi ba haka kawai wannan la'anannen yaron ya cutar mun da yaya ya barsu da jinya" Hajiya Binta ta faɗa. Alƙali ya kalleta, cikin tsanin fushi yace
"Har akwai wani la'ananne bayan ke ne Binta? Ke ce saboda rashin tsoron Allah zaki ce kin shirya abu da zuciya ɗaya saboda Audu ya samu daidaito da Yayansa ko ki sake farraƙasu? Kinyi ne da niyyar ki tozarta Ahmad da matar da yake son aure tun gabanin ta shigo cikin mu kina so kuma ki lalata kyakykyawar Alaƙar da kikaga ta fara ginuwa tsakaninsa da Mahaifinsa ta hanyar saka Audu ya hanashi abinda yake so daga nan ki saƙa mumummunan zare a zuciyarsa ko? To ba zakiyi nasara ba da yardar Allah duk wani sharri da kike yi bazeyi tasiri ba, duk wani sharri da kika niyyaci ƙullawa akanki ze ƙare.
Kin bawa shekaru hamsin baya, ubangiki yayi miki Arziƙin tsahon rai ya baki dama da zaki gyara kurakurenki na baya amma saboda kin rigada kin auri duniya shaiɗan ya gama samun isahshen guri a zuciyarki baze barki ki hango gaba ki tubarwa Allah ki gyara laifukanki na baya ba a kullum zuciyarki sharri ce a ciki shi kike ƙoƙarin aiwatarwa. Ni naji daɗin daya dake su, kuma da kaina zan bashi goyin bayan duk mara tarbiyyar daya sake taɓa martabar Mahaifiyarsa idan ya samu dama ya tsinke masa harshe, abu guda ne bazan lamunta ba rashin Ɗa'a ga ubanku, kome yayi muku tilas yaci arziƙin yin silar zuwanku duniya, in har da gaske yakeyi ya shirya neman sasanci daku ku bashi dama domin ubangiji ma muna saɓa masa kuma mu nemi afuwarsa ya yafe mana wannan shaiɗaniyar ita ce silar faruwar komai a rayuwar Abdulwahabu ku taru ku taimaka masa ku kaita ƙasa ku bata kunya tunda dai ita babu gyara a rayuwarta tamkar dabbar Daji take kullum ƙara nausawa dawa takeyi".
Alƙali Yakubu be damu da cewar a Reception ɗin Asibiti suke ba kuma da mutane suna ta kai kawo a gurin duk anyi cirko cirko ana sauraronsa ya wanke Hajiya Binta tas da soson kaba haɗi da klin da hypo, yanda yake maganar murya a sama zaka tabbatar da cewar yau zuciyar Mazan ta harzuƙa dab kuma yake daya kwasa mata mari muddin tace zatayi inkari akan abinda yake faɗa. Hajiya kuwa hannaye biyu ta aza akai tana kuka tana cewa
"Daman na sani kaf dangin Audu babu wanda ya tsaneni ya tsani zuri'ata irinka Yakubu, ni kake kira La'ananniya? Nice shaiɗaniya? To bari naje seya tashi ya Zaɓa koni ko kai. Idan kai ya zaɓa daga nan gidanmu zanyi dan babu abinda ze sake zaunar dani a inda ba'a san mutunchina dana Zuri'ata ba idan kuma ya zaɓeni wlh se dai ya rabu dakai ya zareka daga Al'amuransa tsaf babu mu babu kai. Shikenan kawai saboda kai matarka bata da zuciyar haifar Yaya Maza seka ringa baƙin ciki da ɗaukakar da Allah ya bawa nawa dana haifa? Ai nasan duk ba komai bane baƙin cikinka saboda Audu nada Magada kuma Yayana nane akan Dukiyar Audu yau idan ya faɗi ya mutu ko sillin gashi baka da gado a cikin tarin Arziƙinsa. Takaicinka kuma yanda kullum Yaya nane a gaba sunfi duk sauran yayan da aka haifa a gidan Ƙashin Arziƙi".
Alƙali Yakubu yayi wata dariya, da alamu ya mance da inda suke shiyasa yake zaro maganganu duk yanda sukayi masa. Kallonta yayi sama da ƙasa yace mata
"Ina Alfahari da Yayan da ubangiji ya bani Mata, Namiji gudan daya bani ya fiye mini taron Yuyuyu irin wanda ke kike iƙirarin kin haifa. Ke har kinyi haihuwar da zaki bigi ƙirji kiyi Alfahari da ita Binta? Arziƙin yayan da yake cuɗanye da na sata da na ƙazantacciyar harƙallah? Bari kiji, wlh idan naso jirkita rayuwarki a cikin taƙaitattun sa'oi se kin bazama neman inda zaki boye a cikin ƙasar nan, kije ki fara gyara tarbiyyar Yayan da kike tinƙaho dasu kafin su zama abin Alfaharin, ina mai tabbatar miki Binta da raina ko na mutu akwai ranar da baƙin cikin waɗannan yayan da kika cuta kika gurbata musu rayuwa kika koya musu zalama da rashin wadatar zuci irin naki se sun saukar miki da Ciwon da in bakiyi wasa ba shi zeyi Ajalinki"
"Dan girman Allah Baba kayi haƙuri, ba anan ya kamata ayi maganar nan ba, Ahalinmu sanannu ne yanzu se kaji zanje yana tashi a Kafafen sada zumunta daga nan Allura seta tono garma" Dr Hassan daya matsa kusada Baba Alƙali ya faɗa yana kama hannunsa, shiyasan me Alƙalin yake magana akai.
PAGE 18
"Gara Allurar ta tono garmar ai ko wannan Mahaukaciyar da ubanku yake zaune da ita shekara da shekaru zata nutsu tasan Annabi ya faku" Alƙali Yakubu ya sake faɗa, Ahnad da Dr Hassan suka rufu suna bashi baki yayinda Binta take kuka tana kiran ita yake cewa mahaukaciya yau tilas Audu ya zaɓa ko ita ko shi.
"Hajiya Dan Allah kije waje kina damun marasa lafiya da suke kwance" Wata Nurse ta faɗawa Binta, a maimakon ta fita kamar yanda aka bata umarni seta doshi Amenity ward inda Alhaji Audu yake tana kururuwa da hayagagar zata taso shi ya zaɓa ko ita ko Yakubu securities suka mata burki, Alƙali yace
"Ku barta ta shiga, kai Hassan kira É—an uwanka kace ya maza yazo Asibitin nan ga wani Aikin Allah ya samu".
Abin dariya abin takaici sega Hajiya ta taka da gudu ta fice daga reception shi kansa Alƙali Yakubun dukda yanda ransa ya ke a ɓace seda ya dara suka wuce office ɗin Dr Hassan suka cigaba da tattaunawa. Hajiya kuwa Adaidaita ta tara ta koma gida, tana sauka Hajiya Rabi suna fita da Direba bayan ta gama haɗa abubuwan da Alhajin ze iya buƙata a Asibiti dan Momy cewa tayi ba zataje ba.
Kamar yanda Baba Alƙali ya bada umarni haka zuri'ar Audu Bechi maza suka sake taruwa a gidansa da daddare banda Naziru wanda yake can kwance gadon Asibiti da Zakariyyah shi an sallameshi bayan da aka bashi magunguna seya wuce gida ya kwanta dan ba wai ya gama komawa hayyacinsa bane ga bakinsa daya suntume an tabbatar dai babu komai a sannu kumburin ze saɓe. Kaca kaca Baba Alƙali yayi musu inda ya fi dora laifi akan Alhaji Babangida da yace shine babba.
"Yau idan Abdulwahabu ya faɗi ya mutu kaine madadinsa kuma duk lalacewarsa sunansa baze taɓa canzuwa daga ubanku ba kuma har a gaban Allah baku da wata hujja ta saɓa masa ko muzantashi, idan kuna riƙe da abinda yayi muku ko yayiwa iyayenku a baya tambayarku zanyi ta ina abinda ya faru ya rageku koya tauye rayuwarku? Shin luɗufin da ubangiji yayi muku a yanzu ba sakayyar wahalar da kuka sha a baya bace ba? Waye a tagayyare duk a cikin ku? Kafataninku kuna zaune lafiya kuna rayuwa cikin wadata me kuke nema? Ta ina rashin kulawar da ubanku ya nuna muku ta rage ku a yanzu?"
Kallonsa sukayi kowanne da magana a bakinsa, shi ɗin ba wani sakakan mutum ne da zasu iya mayarwa da martani shiyasa sukayi shiru. Ya gama musu faɗa kafin ya koma nasiha yana janyo musu Ayoyi da hadisai da suka tilasta musu yin biyayya ga mahaifansu ba wai ganin dama ba, Umarnin Allah da Manzonsa ne kuma kaucewa hakan babban laifine, yace suyi iyakar iyawarsu su rabu da mahaifinsu lafiya, baya musu fatan daga su harshi su tashi gaban Allah rataye da haƙƙoƙin juna da suka kasa saukewa a duniya. Ya roƙe su da suyiwa Mahaifinsu uzuri, ko babu komai albarkacin silar su duniya da yayi har suka taka matsayin da sukejin sun isa ja dashi a yanzu ya isa yasa su Yafe masa kura kuren da yayi musu.
"Kayi haƙuri Baba, amma wata shari'ar se a lahira, banajin zan iya manta abinda Alhaji yayiwa mahaifiyarmu, harta koma ga mahaliccinta da ciwonsa a zuciyarta. Duk sanda na ganshi hotunan yarintarku ne suke yawo a idanuna shi yasa na zaɓi dana zauna a Bechi nayo nesa dashi, idan ka tursasamun kace na yafe masa ko na faɗa iyakar fatar baki ne be zama lallai har zuciyata ina nufin abinda na furta ba" Alhaji Babannan ya faɗi kansa a ƙasa yana direwa Hussain ya cafe cikin ƙunar rai yace
"Mufa shegantamu yayi, ƙila da bamuyi kama dashi ba da har yanzu muna watangaririya a duniya baze karɓe mu ba".
Se Alƙali Yakubu ya rasa abin sake cewa kuma, a sanyaye yace
"Kuyi haƙuri, ku yafewa Ɗan uwana. Na sani yana cike da nadama da dana sanin wani bari na daga rayuwarsa ta baya kuma nasan a shirye yake daya gyara kuskurensa ku bashi damar haka muddin ya nema karkuce zakuyi masa bore".
Taro ya tashi jikin wasu ya sanyaya yayin da na wasu ya zama kamar Baba Alƙalin ya tado musu da tsohon tsumi ne. Hussain sarkin ɓarota cewa yayi
"Dama duk kaika haife mu bashi ba"
"Dani dashi duk abu guda ne, jarabawa ya gamu da ita wadda ba kowanne mutum yake iya tsallaketa ba itace ta rashin dace da Macen ƙwarai, shi yasa a koda yau nake muku nuni da ku ajiye komai idan aka zo gaɓar neman abokiyar zama ku dubi tarbiyya, Addini da nagarta tareda Asali ku bar duk wani ƙyale ƙyale da kwaɗayi domin gujewa maimaita irin kuskuren da mahaifinku ya tafka" Baba Alƙali ya sake tunasar dasu nan ne Faisal yaso ya gwada halin daya tsotso a Nono ya karkace zeyi fitsara yana cewa
"Auran mahaifiyarmu ne kuskuren da yayi kenan Baba ko wa?" Kafin ma Baban yace wani abu Yakubu ya bige masa baki har seda leɓensa ya fashe. Haka dai aka tashi taro kowa ya kama gabansa.
Kwanan Alhaji Audu uku a gadon Asibiti, jininsa ne ya hau ƙololuwa, yanda bincike ya tabbatar da ace faɗuwar da yayi a ƙasa ne tabbas babu abinda ze hanashi gamuwa da cutar shanyewar rabin jiki. A kwanaki ukun nan da yayi a gadon Asibiti idan kaji sautin muryarsa toh da Alƙali Yakubu yake magana se ko Dr da Hajiya Rabi dake jinyarsa wadda itama jefi jefi yake mata maganar. A ɗan taƙin yayi rama, tsufansa da jindaɗi yayiwa kwaskwarima jinyar kwana uku ta fito masa da ita. Kana kallonsa zaka fahimci cewar yana cikin wani yanayi mara daɗi, yawan shirunsa ya tabbatar sa tunani yakeyi wand kuma hakan yasa jikinsa yaƙiyin yanda ake so.
Tun daren da aka kwantar dashi Likitansa me kula da lafiyarsa yaje akan ze maidashi can Asibitinsa kafin ya shirya masa su fita can UK inda ya saba zuwa a duba lafiyar tasa amma yace Aa ze zauna a Asibitin Ɗansa, Asibitin da tun da aka assashi sau ɗaya ya taɓa taka ƙafarsa ranar da aka buɗe se wannan karon da jinyar bagatatan ta kawoshi ya kuma ga gata, shi da kansa ya yarda da Ƙwarewar Dr Hassan tareda ingancin Ma'aikata da kayan aikinsa. Idan Dr Hassan ɗin na Assessing ɗinsa ya ringa binsa da kallo kenan duk inda yayi, a zuciyarsa yanajin wani irin nauyi tareda kunyarsa, wai fa Ɗan Zubaida ne, Ɗan daya kusa shegantawa wanda a silar samuwarsu ya rabu da mahaifiyarsu yau gashi shine yake tsaye akan ganin lafiyarsa ta daidaita.
Har wayau shida Ahmad ne tare dashi, su suke kula dashi da jikinsu da dukiyarsu domin dai sile biyar ba'ace ya kawo ba, bayaga Yayansa mata Mazan babu ƙeyar wanda ya gani a Asibitin har ya kwana huɗu aka sallameshi ya koma gida. Tunda Hajiya ta bar Asibitin dama bata koma ba, tana gida tana saƙa da warwarar yanda zatayi, ta dai turawa Turai kuɗaɗe masu nauyi wanda tace zataje mata gurin Malamin da ze mata maganin Yakubu take yanke, baze wulaƙan tata a bainar nasi yaci banza ba, dole su tashi tsaye akansa domin akwai gagaruwar matsala idan akace Alhaji Audu ya riga Yakubu mutuwa, tabbas yanda baya ƙaunarta se yayi duk yanda ya iya ya cuceta ita kuma ba zata lamunchi wannan abu ba.
Ta manta ma da wani Alhaji na Asibiti seda taji ance ya dawo. Ta zurma Hijabi a baibai ta fita tana casgaɗa ƙafa yanda kasan wata sabuwar cogal a haka ta isa Falon Alhaji na ƙasa. Yana zaune tareda baƙi, gama sallamar ma'aikatan gidan kenan da suka bishi suna sake masa sannu da zuwa dan duk sunje Asibiti sun dubashi suna fita wasu mutanensa suka zo dubashi sunje can Asibiti aka ce an sallameshi shine suka bishi gida. Manyan mutane ne sosai, suna tsaka da tattaunawa se ganin Hajiya sukayi kamar an jehota tana cangala ƙafa tareda numfarfashi yanda kasan wadda ta tashi daga wani ciwo.
"Alhaji ashe ka dawo? Da rabon fuskokinmu zasu gamu ka ganni nima tun ranar nake a kwance, sabili kawai da nace zan shiga na dubaka a Asibiti Alƙali ya koreni na dawo gida duk ba'a hayyacina ba na zame na faɗi a bakin ƙofa tun ranar se yanzu na iya yunƙurawa na fito da naji ance kun dawo nace gara na zo mu haɗu karna mutu a ɗaki har se nayi wari sannan aji a dubani tunda kowa ya tsaneni Matanka babu wadda tako leƙa taga ya nake ace dai kwanaki huɗu ba'a ga giftawata ba ai yaci a tuhumi lafiya dai amma babu wadda tayi" Hajiya Binta ta ringa rattaba zancen da seda ta kai ayarsa kafin ta lura da cewa ba Alhajin ne kaɗai a gurin ba, tayi sak kafin ta shiga rirriƙe hijabi duk ta diririce da gani base an faɗa ba kunya ce tayi mata rubdugu.
Alhaji ya nunata da hannu yana kallon wanda yafi sauran kalar jiƙuwa da kuɗi yace
"Gata nan, ita ce Surukar Ɗan naka". Wanda aka nunawa Hajita ya kalleta babu yabo babu fallasa kakar yanda sauran baƙin suke kallonta kowanne da yanayin da yake kan fuskarta yace
"Sannu Hajiya, ya me jiki? Ya kuma naki jikin?"
Babban abun ma shine bata san uban waye cikin surukan nata ba amma dai iyakar zubar da kai yau tayi ta tafka abin kunyar da ita da kanta yau ta gagara naɗe tabarmar kunya da haukan data saba ae jan Hijabi takeyi ita ba abin ta cire ta maidashi daidai ba duk ta rasa abinda zatayi. Momy tayi sallama cikin kyakykyawar shiga ta Abaya ta yafa yalwataccen Mayafi akai bayanta Maimuna ce da me aikinta Amirah kowacce da dogon Hijabi sun ɗauko manyan Trays. Har ta kalli Binta ta wuce ta samu gurin zama kan kujerun da suke daga gefe kaɗan, su Maimuna suka ajiue kayan hannunsu suka gaida baƙin kafin suka fita sa'annan suka shiga gaisawa da Momy cikin dattako da mutuntaka.
"Itace Matata ta biyu Mahaifiyar Ahmad" Alhaji ya gabatar da ita. Baban Sirikin Binta yayi murmushi yace
"Ga kama nan kuwa har jikin ma irin nata yayi baza'ace ita ta haifesu ba" Alhaji Audu ya É—anyi murmushi sega Hajiya Rabi nan itama ta shigo a kamalance da sallamarta ta zauna suka gaisa.
"Ga kuma Amaryata" Alhaji ya gabatar da ita". Hajiya Binta ta muzanta iya muzanta, wannan abu da Audu ya mata ya kaita wuya amma kamar wadda aka zubawa glue aka liƙe a gurin da take ta kasa gaba ta kasa baya haka ta gagara magana.
Momy da Hajiya Rabi suka miƙe a tare suka musu sallama suka fice, tun a hanya da suna dawowa daga Asibiti ya sanar da Hajiya Rabi, Alhaji Tamim Uban Mijin Hajiya Ƙarama yace yana tafe ze shigo dubashi dan yana Kano, ya sanar masa sun wuce gida basa Asibiti ya sameshi a can, shi yace ta gayawa Momy wadda take fushi dashi kan abinda ya faru. Sau ɗaya taje dubashi Asibiti amma kullum zatayi girki safe rana dare akai masa ita kuma Hajiya Rabi can zata wuni da dare ta dawo Ahmad ya Kwana dashi.
Abinda yasa yace a gaya mata zuwan baƙin yasab ba zata rasa abinda zata fitar dashi kunyarsu ba dan bata rabo da abubuwan motsa baki tunda yamma ce ba lokacin cin abinci bane ba gashi kuwa data tashi zuwa tazo musu da abubuwan taɓawar da ruwa da Lemo. Shi ya manta ma da Hajjajun seda ta shigo, yanda yaji kunya kuwa dai ba'a cewa komai amma ya godewa Allah da ba ita kaɗai yake aure ba, sedai a tafi da ita kaɗai a baki domin sauran matansa sun fitar dashi kunya.
Kamar sun manta da tsayuwar Hajiyar a gurin Alhajin ya musu Bismillah suka ɗan taɓa abinda aka kawo musu. Alhaji Tamim da Abokanan tafiyar tasa wayayyun mutanene suka shiga hirar kasuwanci inda ko wannensu yafi kauri. Hajiya ta gama tsayuwarta kafin ta miƙe ƙafafun da da yake cangalawa ta fice kamar kazar da Ƙwai ua fashewa a ciki. Tana fita ta haɗu da Faisal ta tsareshi da tambayar suwaye a Falon Alhaji.
"Baban Abba T ne" ya bata amsa, seta ɗora hannu biyu aka kafin kuma ta sauke da sauri har tana neman harɗewa ta wuce cikin gidan da saurin bala'i. Jikinta har rawa yake ta kira Hajiya Ƙarama, bata bari sun gaisa ba ta shiga surfa mata bala'i harda Allah ya isa akan.
"Kin huta yanzu ai se su dawo suyita bada labarin sunzo sun tarar da uwarki kamar mahaukaciya" ta faɗa tana rushewa da kuka kafin tayi cilli da wayar. Audu ya cuceta da be gaya mata su waye zasu zo ba yanzu yaja taje ta zubarda mutunchinta, surukin Hajiya ƙaramar ne kawai ya gaisheta amma tana gani da Aisha da Rabi suka ahiga duka harda sauran Abokanansa suka gaisa a mutunce ba irin tata gaisuqar daya mata ta jeka nayi ka ba. Ta sake zuge tazugen rashin mutunchi ta ayyana yanda zataci kan uban kowa a gidan tunda taga alamar raini ya fara shiga tsakaninta dasu kuma ba zata lamunta ba amma yanzu bari ta fara gamawa da zancen Yakubu tukunna shine Ƙayar da ya tsaya mata a wuya. Ta Alhaji Audu me sauƙi ce saboda tana da maganinsa a hannu, wurudin da Turai ta bata zata cigaba dayi tana banka masa yana sha ya dawo hayyacinsa dan taga alamar yana neman yafi ƙarfinta.
FATIMA
Ko a jikinta lissafin kwanakin zuwan Jay kawai takeyi wanda ita dashi sukeji kamar su janyo kwanakin su rage musu tsaho. Wani irin so da shaƙuwane a tsakaninsu, yanda suka damu da junansu suke tarairayar juna seya baka mamaki ba zaka ce soyayyar gani ɗaya bace kuma a waya akeyinta. Hatsaniyar da kayi a gidansu Jafar ɗin ce ta kawo tsaiko a zuwan nasa ya ƙara kwanakin zuwansa Nigeria da sati ɗaya akan yanda ya tsara dan abin ya faru yaɓa shi ya kuma ɓata masa rai matuƙa, idan yace zezo a lokacin da abun be idasa lafawa ba rigima zata dawo sabuwa ne domin dukda cewar baya son Fatima baya son auranta da Ahmad amma hakan bashi yake nufin ze zuba ido a Tozarta Ahmad ba, shi laifin Fatiman nema ya sake ninkuwa a zuciyarsa domin ta dalilinta ne aka yiwa Ahmad ɗin haka kuma ta zama silar da take neman sake janyo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu saboda abinda ya faru dole ze sake tsanata gaba tsakanin Yayan Hajiyarsu da Su Hassan sannan a silar auranta Alhajinsu ya kwanta a Asibiti.
A ƙa'ida saura kwana uku yazo ranar yace mata an samu matsala se wani satin ze zo. Be gaya mata dalili ba, yanayin muryarsa da taji ta sakata tsurewa kodai wani abu tayi masa saya saka ya ɗaga zuwan? Cikin rawar murya kamar me son fashe masa da kuka ta tambayeshi dalili. Ya sassauto daga tunzurin da zuciyarsa take kai yace mata
"Babu komai, gidanmu ne babu lafiya an samu yar hatsaniya shiyasa kawai na ɗaga zuwan nawa saboda ze iya maido da ƙurar data lafa".
Bata fahimce shi ba amma tunda dai ba ita ta masa laifi ba ai da sauƙi. Ta ringa masa shagwaɓa da sangarta harda kukanta akan ya fasa zuwa jibi bayan ta fara shirin tarbarsa, wannan ya sanyaya masa zuciya ya shiga rarrashinta da mata Alƙawarurruka idan yazo kafin sukayi sallama ya ajiye waya.
'Ga mata nan irin su Afeeyah birjik a duniya akan Me Yah Ahmad ze nacewa waccen yari yar da babu komai tattare da ita se baƙin talauchi da sharri, daga maganar auranta ji abinda ya faru to inaga kuma ya aurota ya ajiyeta a gidansa ai se abinda Allah yayi kawai. Abin haushi da takaici kuma wai duk badaƙalar nan da akayi yanda Ahmad yace ko gezau beji soyayyarta tayi rawa a zuciyarsa ba tana nan daram dam shi dai yayi Allah wadai da So Ɗaya tak irin na Yah Ahmad' Tunanin Jay.
AHMAD
Yana tsugunne gaban Alhaji bayan daya gama ɓalla masa magungunansa yasha ya kuma gwada masa Bp da abinda Dr Hassan ya kawo ya kuma koya masa yanda ze ringa masa kullum da safe shi kuma da yamma yake zuwa ya sake dubashi, Sati guda kenan da dawowar Alhajin babu inda yake fita saboda jikin yaƙiyi masa yanda yake so, zuciyarsa a ƙuntace take, duk sanda yayi shiru abinda ya faru waccen ranar ne yake dawo masa dallah dallah. Wani irin abu yakeji a zuciyarsa da baze iya fasaltawa ba, Ɗansa na cikinsa a gabansa ya faɗi cewa mutuwarsa da rayuwarsa bata da banbanci a gurinsa shi kuwa wane irin bigire ya ɗora rayuwarsa akai? Anya idan ya mutu ze ringa samun kyawawan Addu'oi daga zuri'ar daya tara kuwa?
"Alhaji da akwai wani abun ne?" Ahmad ya sake tambayarsa karo na uku, yana ta masa magana amma ya zubawa guri guda ido yayi shiru. Yayi firgigit irin na wanda ya farga daga wani tunani kafin ya gyara zama yace
"Babu komai, fita zakayi ne?"
"Eh Alhaji, yau Jafar ze taso da daddare zasu sauka Abuja, ina tunanin na tafi can na jirashi da safe se mu juyo tare"
"Toh Madallah hakan yayi Allah ya kawo shi lafiya, nima dai inaga Abujar zan bika muje can na zauna na lokaci ko na samu jikina ya daidaita dan a nan mutane ba zasu barni da hayaniya na warke yanda ya kamata ba" Alhaji ya faÉ—a, Ahmad yayi murmushi, yasan da Hajjaju yake dan itace kamfanin hayaniya a gidan. Ba Alhaji ba hatta shi da yake yawan zama tare dashi idan tazo gajiya yake da sauraron maganarta kansa har ciwo yake É—auka inaga Alhajin da ba lafiya ce ta ishe shi ba?
"Ƙarfe nawa zaka tafi?" Ya sake tambayarsa. Ahmad ya duba Agogo yace
"Da jirgin shida kona tara nake tunani dan yanzu zanje gidan Baba Alƙali yace yana son ganina".
"Akan maganar neman auranka ne, kayi haƙuri da abinda ya faru ban shawarce ka tarko aka kafamun na shiga da kyakykyawar niyya bansan cewar wanda yayi shi da wata manufarsa ta daban ba. Mun tattauna da shi yace ze kiraka ku sake yin magana daga nan ze yanke rana da lokaci da za'aje masa neman Auran. Dama ina so naji zancen Muhalli ka tanada ne ko kuwa baka fara shirin komai ba game da auran?"
Ahmad yayi kasaƙe yana sauraron Alhaji, kalmar haƙuri da Alhaji ya fara da ita ta saka jikinsa sanyi laƙwas. Ya ringa tisa maganar Alhajin harya gama kafin ya fara tattaro amsar da ze bashi a zuciyarsa.
Shifa Fatiman nan sun kusa sati biyu rabon da suyi magana da ita tun ranar da Baffanta yace ya turo iyayensa be sake komawa ba haka be kirata ba itama bata neme shi ba ya kwanta jinya daga nan kuma wannan lamarin ya faru ya maida hankali ga jinyar Alhajinsu. Daman shi bashi ya tado da zancen aure yanzu ba Alhaji ne gashi yanzu har magana taja ana batun za'aje tambaya dukda cewar Mahaifinta ya bashi dama amma ai itama yana buƙatar amincewarta tunda dai da ita ze zauna idan bata sonsa baze samu farin cikin da yake fata a zamantakewarsu ba.
"Kayi shiru baka ce komai ba" Alhaji ya faÉ—a yana kallonsa, ya shafa kai yace
"Dama Jafar nake jira yazo tunda shima da tasa maganar se mu shawarta inda zamuyi gidan"
"Toh yayi, da akwai filaye dana siya nan bayan Sufi Mart, kuje kuga gurin idan yayi muku se ku zaɓi biyu a gina" Alhaji ya sake faɗa.
"Mungode, Allah ya ƙara girma" Ahmad yayi godiya kafin ya tashi ya fita. Gidan Baba Alƙali yaje, har number Baffansu Fatima Alƙalin ya karɓa a hannunsa da zummar ze kirashi ya basu lokacin da zasuje haka ya bashi dan bakinsa ya kasa buɗuwa ya fayyace wa kowa halin da suke ciki da Fatima. Idan yana da rabon auranta ya sani ze samu, idan ba rabonsa bace in sunje Mahaifinta ze musu bayanin komai, baya so ya faɗi har yanzu basu samu daidaito da ita ba saboda kar daga baya Allah yayi faruwar auransu ya zama yan uwansa su ƙi karɓarta yanda ya kamata.
Ya faɗawa Alƙali Yakubu filayen da Alhaji yace suje su gani in ya musu shida Jafar.
"Lallai kun gode, toh amma idan akace gini za'a tado zeja lokaci fa ta yuwu sama da shekara kafin ace anyi Auran nan dan nidai kunsan bana son wannan ginin burbur na zamani da akeyi wata shida ace ko ƙasa da haka kaga anyi gini har an tare ruwa be daki bulo da ciko sun zauna da kyau ba, in dai ba kuna so a saka auran da nisa ba shekara zuwa da rabi ba kamata yayi ace an nemi ginannen gida ko kuma cikin waɗanda aka fara ba'a kammala ba in ma tsarin ginin akwai abinda be muku ba kwaskwarima zatafi sauƙi akan ace a tada sabon gini".
Ahmad ya jijjiga kai dan yayi na'am da maganar tasa Alƙali Yakubu ya sake cewa
"Zan same shi zamuyi maganar" daga nan suka sake tattaunawa har bayan la'asar sannan ya koma gida. Ya zata da wasa Alhaji yake da yace zashi Abuja seda ya koma ya tarar dashi da Hajiya Rabi a shirye wai tare zasu tafi. Jirgin ƙarfe shida suka bi, A katafaren gidan sa na Abuja sukaji zango, gidane da bayyana tsaruwarsa ma ɓata lokacine. Bayan shi yana da gidaje da bazasu irgu ba a Abuja Manya da ƙanana banda Estate da Plazas da sauran Kadarori da iyalansa ma basu san da wanzuwar wasu daga ciki ba.
Manya Manyab Mansions ɗin da barin su da akeyi babu kowa ciki se masu aiki da suke kula da gidajen tasa yayi shawarar bayar dasu haya suka zama Masaukan Manyan baƙi tunda da komai na more rayuwa a ciki mutum sedai ya shiga yayi iyakar zamansa ya fita. Wannan gidan kaɗai ya ajiye yake sauka a jiki idan yaje Abujan, duk zalama da son duniyar Hajiya Binta ya rasa yanda akayi bata taɓa nuna sha'awar tana so ta koma Abujan da zama ba, a Shekarun baya dai Aisha ce ma ta ringa nacin daya raba musu gida, kodai ya maida Hajiyar wani guri daban ko su ya fitar dasu amma daya shawarta da Abokanansa akan hakan suka ce masa Aa, a girmansa da shekarunsa be kamata ace ya rarraba kan iyalansa ba, ai duniya ma se tace be isa da gidansa bane shi yasa ya kasa haɗe su a inuwa guda wannan ne ya daƙile maganar.
Ahmad yafi gane sauka a Hotel idan yazo Abuja amma yanzu saboda Alhaji tilas ya shiga É—aki ya kwanta yanajin duk babu daÉ—i, Sha biyu da rabi na dare su Jafar zasu sauka amma Alhaji yace yayi kwanciyarsa in ya dawo ya kwana a Aiport da safe ya taho gida babu wanda ze fita É—auko shi a daren nan baze yi masa musu ba ya kwanta yana ta jiran kiran Jay aikuwa ÆŠaya saura se gashi ya kirashi ta WhatsApp wai ya fito yana ina?
"Alhaji yace ka kwana a Aiport seda safe ka wuto gida" Ahmad ya bashi amsa yana dariya dan ya san abin seya zafafi Jafar aikuwa ya shaƙa yayi tam yace
"Amma fa ce mun kayi zaka zo ka jirani a Abuja yanzu kuma kana cewa Alhaji yace menene Allah Yah Ahmad ko"
"Toh ai ina Abujan, tare muka zo da Alhajin shima ze tareka"
"Ya samu sauƙi kenan? To nidai gaskiya ka saci hanya ka fito ina jiranka" cewar Jafar, Ahmad ya girgiza kai yace
"Kayi haƙuri ka zauna zuwa Asuba zan fito kasan yanayin gari yanzu yan one chance fa sun takura shiyasa naso na zauna nan na kama mana ɗaki amma da muka iso yace dole mu wuto gida tare". Saboda Haushi Jafar kashe waya yayi be cewa Ahmad komai ba ya ringa kiransa kuma yaƙi ya ɗauka duk ya damu ya kasa bacci.
Can jimawa seji yayi ana buɗe Get, ta window ya leƙa yaga Jafar na fitowa daga mota filin gidan tarwai yake da haske dan haka yana iya hango yanda ya cukule fuska. Masu gadi ne suka biyoshi da Back pack ɗinsa wadda daman ita kaɗai yake ruƙowa idan ze yau kuma ya ganshi da saitin Akwati me biyu da Kit, daga sama yake hangosu kuma dare ne amma a hakan yaga kyansu, bakinsa har kunne dan ya san wannan tsabar Masoyiyar da ake wa kowa rowarta ce, lallai Jafar da gaske yakeyi, a saninsa be taɓa ruƙowa wata Mace tsaraba.
Falon ƙasa ya sakko tarbar sa nan ya tarar da Alhaji da alama motsin buɗe ƙofa ne ya fito dashi shima. Jafar ya gaida Alhaji yana hararar Ahmad wanda ya gumtse dariyarsa jin Alhaji na cewa
"Ka karya mun dokar gida kana sane ko?" Shiru yayi Alhaji ya juya ya koma ciki se sannan Jafar ya farawa Ahmad mita suka wuce sama tare.
"Kai baka san dare bane wai ka bari da safe se kayi surutun naka mana" Ahmad ya faÉ—a yana zama a gefen gado. Jafar ya shiga cire kayan jikinsa wayarsa daya ajiye kusada Ahmad ya shiga ringing.
"Toh fa, ruhi na kira" Ahmad ya faɗa cikin sigar tsokana yana miƙa masa wayar ya karɓa yana wani tura masa baki kamar yaro. A speaker ya saka wayar, muryar Afeeyah dake cakuɗe da bacci ya ziyarci kunnuwansu a lokaci guda.
"Love, ka isa gida?" Ta faɗa, Jay ya wani langwaɓe kafin yace mata
"Yes Bae na iso gida, waifa Alhaji cewa yayi na kwana a Aiport ba za'azo a É—auke ba"
"Kai! haba dai" ta faÉ—a" tana ware ido, yace
"Wlh fa, but na dawo, na gaji da yawa wanka nake so nayi yanzu, I'm sorry for keeping you late na hana kiyi bacci"
"Haba mana, kana zaton zan iya bacci Alhalin kana hanya ban san ka isa gida ko Aa ba?"
"Awwwnn I'm blushing" ya faɗa yana shafa kai tareda satar kallon Ahmad dake kallon wayar babu kyaftawa yana auna kalaman me magana a cikin wayar ɗaya da ɗaya. Be sani ba ko kewar Fatima ce tasa yakejin muryar Budurwar Jafar tamkar tata ko kuma irin shauƙi me nuna tsantsar soyayyar da take yiwa wanda take magana dashi wanda ya daɗe yana fatan yaji daga Fatima ne yasa har yake hakaito ita take maganar ko yaya? Besan Jafar ya kashe wayar ba seda ya taɓa shi yana cewa
"Da akwai abinci a gidan nan kuma? Yunwa nakeji wlh"
"This is past 1 fa Jafar kai kake neman abinci irin wannan lokacin?"
"Bazaka gane ba, zumuÉ—in ganin Afeeyah yasa na kasacin komai, naji haushi sosai da ba zan ganta yau ba, Allah badan Alhaji ze hana ba yanzu zan tafi Kano irin 6 na isa na wuce gidansu kawai"
"Ka ɗauka a Turai kake kenan ko Yaya? To a Naija Ƙwamushe mutane akeyi a Abuja-Kaduna Road yanzun da tsakiyan rana ma balle ka kai musu kanka da daren nan, Allah ya tsare hanya kaga Ransom ɗin da zasu saka akanka nasan sedai FIFA ta biya badai Alhaji ba".
Da Jafar yayi wanka ya haÉ—o Tea nan ya hana Ahmad sakat da zancen Afeeyah, idan ya buÉ—e wayarsa ze nuna masa hotonta se kuma yace
"Aa ma, gobe zamuje kawai ka ganta face to face kaga Mace ba muna mata ba irin wadda kake wahalar da kanka akanta bata san kanayi ba"
"Uhm, Allah ya nuna mana" Ahmad ya faɗa yana kwanciya, gaskiya Jafar ya faɗa Son maso wani yakeyi da hausawa sukace ƙoshin wahala to amma yaya zeyi? So halittace ce wadda baka iya sanin sanda zata shigeka sannan baka da zaɓin kan wa zata faɗa, masu ganin laifinsa akan yaso Fatima suna bashi mamaki domin jarabtar data same shi tana iya faɗawa akansu suma. Tsananta soyayya tamkar gado ne a gurinsu, abin a jininsu yake, suna da matuƙar zafafawa akan abinda suke so hakan nan in suka ƙi abu toh fa ya shiga uku. Yanzu irin yanda yaga son Afeeyah a idanun Jafar ya tabbatar da ace shima tasa jarabawar ta zamto irin tasa ma'ana yana sonta ita kuma wani daban take so ta yuwu wawancin da zeyi a soyayya se yafi wanda shi Ahmad yakeyi.
Bacci be ishe su ba amma saboda yanda Jafar ya azazzaleshi tilas suka tafi Kano a Mota dan sunyi missing Jirgin Safe da already sukayi booking, na rana da probabilityn ayi postponing ɗinsa ya haɗe da na dare kamar yanda wanda ya kira ya sake musu booking ya sanar masa shi kuwa Jafar baya iya jiran har Bayan Magrib kafin ya isa Kano shiyasa yace su tafi a Mota. Sun shiga Kaduna ya kunna layinsa na Nigeria dan ta WhatsApp yake waya da Afeeyah tun jiyan saboda Hajiya kuma yaƙi kunna wayar ilahi kuwa yana kunnata sega kiranta kamar tana jira ta fara masa masifa da bala'in da suka zame mata kalaman barka da zuwa ya ringa bata haƙuri dan faɗan akan meye ze kira Ahmad ya ɗakko shi bayan ta hana?
Ita bata ce zata sake haɗa masa taro ba amma ai ta gaya masa muddin ze zo ya sanar da Faisal ko Lawan suje su taro shi daga koma ina ne ba Ahmad ba amma seji tayi ance ya tafi Abujar ƙarin baƙin cikinra tafiyarsu tareda Alhaji harda Hajiya Rabi, ko sallama be mata ba Yakubu daya kawo masa takaddu ya saka hannu kafin suka tafi ne ya gaya mata, kwana tayi tana tijara, ita da taso abinda ya faru ya haifar da Ƙiyayya mai tsanani tsakanin Ahmad da Alhajin amma tun daga Jinyar sa da yakeyi taga alamun shaƙuwa ce take sake shiga tsakaninsu ba wai barakar da tayi fatan a samu ba.
Ta ringa kiran layin Jafar kuma a kashe alamar be kunna ba bayan an tabbatar mata daya sauka shine tun farar Asuba take sake gwadawa har Allah yasa yanzu ta shiga ta rusa masa budget É—insa na biyawa gidansu Afeeyah tilas suka wuce gida Ahmad na masa dariya domin yasan dama za'a runa ya tabbatar kuma nasa kason yana nan yana jiransa abu guda dai shidai baze bari wani hargagi ko cin mutunchin Hajiya ya shiga tsakanin zumunchinsa da É—an uwansa ba.
Aiko yasa zagi da tijara kamar ko yaushe yayi murmushi ya fice daga gidan, ya rasa me yasa wayar da Jafar yayi da Afeeyah jiya ta tsaya masa a rai ta kuma tado masa da kewar Fatima dan muryarta keyi masa gewaye a ƙwaƙwalwa, da daddare Baba Alƙali ya kirashi yake shaida masa ya kira mahaifin Fatima sunyi magana a waya ya sanar masa da zasuje nema masa auranta yayi murna sedai yace yana neman Alfarma da su bashi lokaci domin akwai shirye shiryen da yake so ya kammala kafin tasowar maganar auran.
"Yace daga nan zuwa sati huɗu zamu ji shi duk yanda ake ciki, amma Ahmad anya kuwa iyayen yarinyar nan da kansu suka ce ka turo maganar aure?" Baba Alƙalin ya tambayeshi. Ya sosa kai kamar yana gabansa zuciyarsa na dukan uku uku, Baffa yace a dakata da zuwa nema masa aure bayan shi da kansa yace ya bashi dama daya turo to me hakan yake nufi?? A sanyaye yace masa
"Wlh shi da kansa yace mun na turo"
"Toh inaga ko wani abun ne ya taso da yake buƙatar ƙarin lokaci, to babu laifi ai sati huɗun daya ambata kamar yauce. Kafin nan shima Jafaru idan inda yake neman sun shirya se aje muku gaba ɗaya a huta" da haka sukayi sallama jikin Ahmad yayi wani laƙwas kamar an zubawa Salak gishiri, ta tabbata dai ya rasa Fatima tunda har Baffa da kansa yace su dakata to tabbas nauyin Baba Alƙali yaji kai tsaye ba ze iya ce musu baze bashi yarsa ba. Amma me yasa Baffa zeyi masa haka? Koda yake ba laufin Baffa bane tunda dai bashi ze aura ba ita kuma Fatiman tace bata ra'ayinsa ai ba za'ayi mata dole ba.
Zazzaɓi ne ya dawo masa haɗe da ciwon kai me zafi dan kasa maida kansa gida yayi se Salim ya kira dan Hajiya ta saka Jafar a Ɗaki kamar sabuwar Amarya tunda suka dawo ta hanashi motsawa ko nan da can.