Complete Hausa Novels

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 11

PAGE 3
Daga gidan gona kai tsaye gidan Anty Manfusa Inda ya ajiyw Momy dan tare suka fito. Yayi masu bayanin yanda sukayi da Alhajin dan Anty Manfusan na cikin waÉ—anda zasu saka hannun jari idan Allah yayi buÉ—ewar shopping mall É—in.

"Wato uban nan naku lamarin sa yana matuƙar bani mamaki, yanzu ba'a rufa wata guda ba Yayansu Nihal (Dan Mijinta ne) yake cemun Anyi musu ƙarin kuɗin hayar shaguna a plaza, da aka kawo musu takaddu yaga an canza sunan da yake jiki wai yanzu ta zama ta NAZIRU BECHI, a yanda akace wai siya yayi gurin Alhajin wasu kuma sunce bashi yayi, nima yana faɗa nace wlh ƙaryane bashi yayi saboda rashin tsoron Allah duk girman plazar nan ace ya bawa Naziru shikaɗai shagunan ciki fa sunyi hamsin? nifa da nice a matsayinki wlh da tuni gayyar ta watse dan bazan zauna ana wannnan kutumar ubancin inyi shiru ba"

"To banda abinki Manfusa Naziru ai Ɗansa ne yana da damar mallaka masa duk abinda yayi niyya" Momy ta bata amsa. Manfusa ta harzuƙa tace
"Shi Ahmad ɗin ai Agola kikaje masa dashi shi yasa ze kasa bashi kyaitar fili, tsabar zalunci kuma ya lafta kuɗi har Miliyan ɗari biyu ce masa akayi Ahmad ɗin barawo ne irin sauran Yayansa da ze mallakin waɗannan kuɗin a shekarunsa? Ko kuwa saboda yana rayuwarsa cikin rufin Asiri bai taɓa neman wani abu a hannunsa ba?"

"Hakan ma da yayi nagode Anty dan wlh idan a gurin wani ne darajar filin nan ta zarce haka ko a haya za'a bani a gine dai a shekara Miliyan Hamsin sen bayar da ita wlh kinfa san location kafin ni nasan manyan Organization da suka nema ya hanasu har Gwamnati seda taso ta kwace gurin Baba Alƙali ne ya tsaya masa Allah ya taimaka aka bar masa in sha Allahu in har muka samu abinda muke so shekara biyar tayi yawa zamu mallakeshi ya zama namu kawai dai kuyi ta tayamu da Addu'a" Ahmad ya yayyafawa wutar masifar data fara ruwa, dole tayi shiru tunda uwa da Ɗan da take haƙilo akansu abinma.be damesu ba.

A hanyar komawa gida Momy take ce masa
"Nifa ubana ina tsoron mutanen gidanku akan maganar gurin nan, ban manta ba Yayanku Zakariyya ya taɓa nemar ya bashi ya gina Hotel yaƙi, baka tsoron idan sunji suyi maka lamɓo se ka saka kuɗinka su zugashi ya kwace?"

"Momy, dan Allah ki kyautata zato akan abin nan ki cire duk wani wasi wasi daga ranki. Nida ke duk mun sani Alhaji kaifi É—ayane, idan da beyi niyyar bani ba koda ace duniya zata taru akansa wlh baze bayar ba haka nan yanzu daya ce ze bada bana tsammanin da akwai abinda ze canza masa ra'ayi akan hakan, ki kwantar da hankalinki"
"Ai shikenan, Allah yasa tabbatar da Alkhairi"
"Amin Momy, abinda ya kamata ki faÉ—a kenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin harya sauketa gida ya juya yana so yaje yaga Barr Ansaruddeen Kalam, Childhood friend É—insa ne kuma shiya Aminta dashi da zama Lawyersa, a gidan Barr yayi Magriba da isha suna tattauna yanda za'ayi da takardun daya kamata su haÉ—a kafin su zauna da Lawyer Alhajin.

Cikin hukuncin Allah yarjejeniya ta ƙullu tsakanin Alhaji Audu Bechi da Ahmad Bechi, kowanne bangare ya gamsu da tsarin da akayi har kuma BECHI CONSTRUCTIONS sun aza harsashin gini bisa Jagorancin Mr Lee, Injiniyan da yake shugabantar bangaren gine gine da ƙere ƙere na BECHI GROUP OF COMPANIES kujerar da Hajiya Binta take hari domin kuwa tuni ta matsantawa Faisal tafiya bangaren Engineering ɗin yanzu haka yana shekara ta biyu ne a Civil Engineering, burinta daya gama kuma a tunɓuke Mr Lee ya koma ƙasarsu Faisal Bechi ya maye gurbinsa.

Ubangiji ya sirrinta Al'amarin ta yanda har gini yakai Linta Hajiya da Yayanta basu san abinda ake ciki ba, koda yake Yakubu Bechi ya sani saboda buƙatar fitar da kuɗin da aka kai kan Teburinsa dan tuni ya maye gurbin Aminu Bechi.

Yakubun be fiya shiga sabgar da bata shafeshi ba, a barshi dai da son kansa dan haka muddin Abu ba wai ya shafi personal Interest nasa bane baze ce komai a kai yanzun ma haka ce ta faru yayi shiru ya saka hannu kawai kamar yanda aka buƙata be kuma tattauna maganar da kowa ba.

Yanda akayi Labari ya isarwa Hajiya Binta kuwa hanya ce ta bida ita ta gurin da filin yake zataje gaisuwar Lantana wadda Allah yayiwa Rasuwa, Hajiyar bata yada Lantana ba a wannan bangaren kam tayi Alƙawari dan Lantanar tsautsayi ta gamu dashi a shegen yawonta mota ta kaɗeta shikenan ta gamu da Ƙafa, shekararta goma a zaune kafin Ajali ya sauka Bintan na leƙata lokaci lokaci duk kuma sanda ta wuce seta kalli wannan fili tana wassafa burinta akansa. A Zoo road yake, zuciyar Kasuwanci, kanta takeyiwa tanadi zata gina plaza ta zuba shaguna wanda ko iyakarsu me kadararta tasan ba ƙananan kuɗaɗe zata ringa shaƙa duk shekara ba.

Jiki na rawa ta samu Alhaji Zakariyya da zancen waya tada gini a wannan filin?
"Badai siyar dashi yayi bamu sani ba? Ka nema ya hanaka ina fakonsa shine ze siyar? To duk wanda ya siya ma kuwa ya siyi Asara dan ciniki be yuwu ba" Inji Hajiya Binta. Alhaji Zakariyya da har ya fita shiga ruɗu domin a halin da ake ciki a yanzun ya karɓi kuɗi a hannun Lebanese da suke son gurin zasu gina Hotel dan bashi zeyi ginin ba kuma ya musu Alƙawarin kafin watan da ake ciki ya ƙare zasu fara aikinsu se kuma yake Jin wata magana daban.

Bangaren Land and properties ya tafi ya samu Alhaji Musbahu, basa shiri saboda duk sanda suka tashi cefanar da wani abun muddin basu kai masa takadda ta gaske me ɗauke da signature Chairman ba baya basu Approval, Zakariyyan kuma baya duba Girma ko Shakarun Alhaji Musbahun haka ze zageshi a gabansa yace ai bashida gadon ubansu balle ya ringa hanasu Taɓa dukiyarsu, yau ɗin se gashi harda risinawa ya gaidashi kafin ya tambayeshi suwa aka bawa Filin da har suka fara gini"

"Ban sani ba, kaje ka samu uban naka kaitsaye, ku masu jiran Gado ma kuke É—auka kuyi yanda kuka so da guri balle me abun daya tara da guminsa?" Amsar da Alhaji Musbahu ya bashi kenan shima kuma ita ya mayarwa da Hajiya.

Ranar akayi dacen itace da Girki dukda Alhaji Audu baya gari ya tafi Umara amma a daren ranar ake saka ran dawowarsu shida Hajiya Rabi da Yammatan gidan duka suka tafi Umara wanda Albarkacin Tafiyar da za'ayi da Hajiya ƙarama da Sarah, wanda ze buga musu Visa da karanbaninsa ya haɗa da duka sauran Yara Matan da suke a gidan se kuwa gashi Alhajin bece komai ba akai. Amma fa seda akayi uwarka ubanka da Hajiya Binta kafin tafiyar ta yuwu harda Allah ya isa yanda kasan kuɗinta aka ɗiba akayi tafiyar dasu.

Babu shirin da tayi na cewar yau Megidan ze dawo tunda ya tafi ma sau biyu sukayi waya Albarkacin zata bashi sautin Dogayen Rigunan Gumama wanda take bulalawa a tsakar gida tayita yawo kamar Maroƙiya, idan tacewa Hafsatu ko Sarah su siyo mata cewa zasuyi ta tura da kuɗi shiyasa ta aikawa da Alhajin hotunan kalarsu kamar wani Yaronta tace guda biyar za'a siyo, da taji shiru be duba saƙon ba shine ta kirashi, na biyun ma tinin an siya tayi masa yace Eh Alhalin ko downloading yaga me ta tura beyi bama.

Ƙarfe goma na dare jirginsu ya sauka kafin a gama dakko musu kayansu su tafi gida sha biyu saura shi Alhajin dama VIP lounge na Arrival ya shige abinsa yace idan sun gama a sanar masa dan baze tafi ya barsu su duka mata ba ga dare, Ahmad ne kaɗai ya tsaya Tarbarsu a samarin gidan, a cikin gida kuma Momy ta musu ɗan abin taɓawa dukda dawowar darece amma tasan Alhajin baya cin abincin jirgi ko China zeje sedai yasha ruwa ko shayi shiyasa ta tanadar masa abinda zeci dukda ba girkinta bane sedai ganin Yau Hajiyar ko Hanyar kitchen bata kalla ba yasa tayi, kamar ma dai bata da lafiya ne dan karaɗin da take isarsu dashi a gidan ma yau shiru kunnuwansu sun samu sa'ida.

A Ɗakinsa Momyn ta shirya masa komai ta bari tayi masa sannu da zuwa daga bakin ƙofa ta wuce Ɗakinta da Yammatanta da suka ruƙunƙumeta suna faɗin sunyi kewarta. Dukda darene haka ma'aikatan gidan Maza suka ringa shiga Babban Falo suna masa sannu da zuwa, Hamshaƙai kuwa, Yakubu, Faisal da Salim harda Mu'allim suna Ɗakunansu babu kuma wanda yake bacci a cikinsu daga masu chatting se masu waya da Yammata gara Mu'allim ɗin ya fita ya tarbi uwarsa ya rakata cikin gida kafin ya koma yaci gaba da Chatting, Tashen Balaga yake akayi rashin sa'a kuma Yayyensa da suke kewaye dashi babu wani gwani da ze kwafi abin Arziƙi a gurinsa shiyasa shima yake nema ya tashi da Ɗabi'u irin na gidansu da ya zame musu Gado wato halin ko in kula.

Hajiya Binta bata saurara ko Babbar Riga Alhajin ya cire ba yana sallamar Masu aiki ya hau sama ta dirar masa a Ɗaki, ransa a jagule da rashin ganin sauran Yaran dake cikin gidan tamkar yanda Ahmad yazo ya tsaya kuma yaga motar kowannensu a ajiye dan ya kafa dokar hana yawon dare ƙarfe goma ake rufe masa Get ba shiga sedai fita duk kuma wanda ya kwana a waje shi yasan ta yanda yake hukuntasu kuma sun biyu suna bin dokar.

"Yawwa Alhaji sannunku da sauka, nace ɗazu naje Goron dutse se nabi ta Zoo road zan karbi saƙo, base naga gini tsiriri a filin kaba? Ni na gaza fahimtar ma me ake ginawa yo bulune ta ko ina an tayar da katangu inaga hawa uku ma aka ɗora bene a gurin" Hajiya ta faɗa tana zama idanunta kuma akan kwanukan da Momy ta ajiye. Alhaji ya shiga kacaniyar zare kayan jikinsa, sati biyun nan yaji dadinsu ya samu lokaci da Amaryarsa dan har wani ɗan kumari yayi yanzu ya dawo zata fara ƙwarzabarsa, ita bata tarairayeshi ba sannan ta addabi masu tarairayarsa ta hana musu sukuni.

Seda ya cire rigarsa ta rage singlet da Wandon dakakkiyar Gedzenar jikinsa kafin ya janyo teble ya bude Casserole ɗin da Momyn ta ajiye, Irin dankalin nan na yan gayu da ake soyawa sama sama sannan a gasa yaji Albasa da Koren tattasai da Yellow da zafinsa alamar yanzu aka gama ko akayi Microwaving ƙamshi na tashi. Ya tsiyaya Shayin dake cikin yar buta yayi bismillah ya faraci ba tareda ya bata amsa ba. A daren take son jin yanda ake ciki dan haka tayi shiru ta tuno da tsohuwar kissa ta matsa tana cewa

"Yi haƙuri duk na sha'afa banma ce maka ga abinci ba, Allah sa be huce ba dan na daɗe da gamawa".

"Da dai harshena ya dena tantance É—anÉ—ano sena yarda, sannan yaushe kika fara siyan irin kwanukan nan? Ina cewa kikayi na yara ne sedai a siyawa su Dada ko kuma kin canza shawara kinbi sahun su Aisha tsofai tsofai daku kuna Asarar kuÉ—i a siyan kayan kitchen?" Alhajin ya mayar mata da martani yana murmushin rainin hankali. Tayi tsam, har yar kunya ce ta kamata wato yasan ba ita ta ajiye ba kenan? Amma seta waske tajira harya cinye tas ya shiga banÉ—aki ya kuskuro baki ya zauna a bakin gado yana duba wayarsa.

Maganar ta sakw soka masa hankalinsa naga saƙonnin da yake dubawa yace mata
"Ahmad ne ze bude kanti a gurin".
Ruwa take sha babu shiri ta ƙware nan ta shiga tuttula tari kamar zata amayo kayan cikinta Alhajin na jera mata sannu. Seda ya lafa mata ido da fuska sunyi jajir se sauke numfashi takeyi dan ta shaƙu amma bata daddara ba ta kalli Alhajin tana zaro ido tace

"Ban fahimci Ahmad ne ze buÉ—e kanti ba? Ka gane inda nake maka zance kuwa? Filin Mota fa nake magana bawai wani guri daban ba"

"Nan É—in nima nake miki zance ai, ba kince kinga ana ta gini ba? Shopping Mall ze buÉ—e a gurin" ya sake bata amsa. Yanzun ta tabbatar da ya gane inda take nufin kuma gaskiyar zancen yake gaya mata. A fusace tace
"Ahmad ze buÉ—e shopping Mall ko zaka buÉ—e masa? Ni zaka ninke a baibai wannan filin zakace ka bawa Ahmad ya bude kanti a ciki ina nan da Me sunan Alhaji yace yana son gurin cewa kayi da tanadin da kakeyi akai ashe ÆŠan gidan Aisha kakeyiwa tanadi zaka buÉ—e masa kanti?"

Hankali kwance dan seda ya kishingida kafin ya bata amsa yace
"Ko kaÉ—an yanda dai kikaji nace miki shi ze buÉ—e to hakan ne nidai na bashi fili mun kumayi Agreement harya biyani wani kaso zan gina masa gurin a hankali idan kasuwa ta kafu ze ringa biyana har mu warware"
Data rasa abin ce masa se kawai tace
"Ai shikenan" ta fice daga É—akin.

Da Asubar Allah ta tattago Naziru da Zakariyya ta shaida musu abinda akw ciki, suka ƙule a ɗaki suna ta ƙulleƙullen yanda za'ayi a rusa maganar amma sun gaza samo hanya domin a yanda Alhajin ya iya bata amsa jiya tasan ba wata magana da zata faɗa yanzu ta samu shiga a gurinsa. Idan ya murɗe barinsa takeyi domin a garin tace seta latsa dole se ayi rashin sa'a kwaɓarta tayi ruwa shiyasa yanzun ma kamar zatayi kuka tace

"Kubar komai a hannuna zan barshi dai yanzu tunda naga kansa yana hayaƙi amma zan maidashi hankalinsa ne kuma wlh ba Ɗan Aisha ba ko ubanta ne yayi kaɗan daya mallaki gurin nan se an karɓeshi".

NAZIRU da yayi shiru yana ta tunani ya gyara zama yace
"Wani tunani nayi, tunda kince yace miki ba kyauta ya bashi gurin ba na tabbatar kuma dagaske ba kyautar bane, me ze hana mu bi abin a siyasance? Nasan dai a shekara goma Ahmad indai ba Naman mutane ze ringa siyarwa ba a gurin nan baze haÉ—a kuÉ—in filin nan da ginin da za'ayi masa ba..."

"Kai na rabaka, ka dena ganin yaron nan yana yawo tsalo tsalo dashi wlh neman kuɗine ya hanashi ƙiba, yanda kasan wannan tsohon haka yake babu sana'ar da baya gwadawa" Alhaji Zakariyya ya tare Nazirun. Seya ja tsaki yace
"Ka dakata Malam kaji point ɗina, i know what I'm saying, kai kasan nawa ake taya filin nan Tsohon nan yaƙi siyarwa? Kuma kaidai kasan riba kawai ya sani babu batun faɗuwa ko mu da yake mana Gwanjon kayansa ai saboda uwarmu ta iya ƙasarta ne, ni shirin dana hasaso yanzu as i was saying a shekara goma Ahmad baze biya kuɗin gurin nan ba shi kuma Tsohon nan nasan duk Nacinsa shekara biyar gaba ma yaci ace ya dunguri ƙasa dukda ma naga Sugar nasa da hawan jinin wani sanɗa sukeyi sunƙi su rarakeshi yanda ya kamata ya buɗa mu samu muja kaya.

Yawwa maganata a nan a bar maganar akwace guri ko wani abu, da zarar Alhaji ya sheƙa lokacin kuma Ahmad ya gama wahala da gurin ya rayashi kawai zamu tayar da rigima muce guri na Alhaji ne, babu ruwanmu da ko nawa sukayi yarjejeniya ya biyashi bamu san anyi ba dan haka guri yana cikin lissafinmu".

"Ji banza, kai matsalata dakai wani lokacin se ka ringa magana kamar wani ɗan ƙwaya wlh, da kake cewa idan Alhaji ya wulla semu tada rigima ana maganar yanda za'ayi guri ya zama mallakinmu kana kawo shirme ko kuwa ka manta bamu kaɗai Alhajin ya haifa ba idan anzo rabon kowa se an fitar masa da kasonsa dai dai da namu?"

Naziru yaja hanci irin yanda masu zuƙar hoda sukeyi ya wani karkace yana hararar Zakariyya yace
"Kai ai kanka baya kawo wuta ne kwata kwata, kaji da Kuɗin mutane daka karba nasan sune matsalarka yanzu, zancen Gado kuma ai me sauƙi ne. Karka manta Yaya Tara ne a Ɗakin nan namu mu shida Maza a ciki munfi yan kowanne ɗaki yawa sannan mu muke da ruwa da tsaki a duk wasu sabgogin megidan nan, karka manta Kadarorin da uwar kuɗin kansu se abinda muka ga dama muka fito dashi za'a raba kuma ba wanda ya isa ya ɗaga mana yatsa"

"Wannan gaskiyane" Hajiya da tunda ya fara maganar batace komai ba ta faÉ—a tana gyara zama dakyau dan tafi jin dadin wannan HaÉ—i na Naziru.

"To idan suka haÉ—e mana kai fa? Kasan dai in suka haÉ—u sun nunka mu a yawa Mazansu da Matansu" Alhaji Zakariyya da yake jin shawarar Naziru bata kwanta masa ba ya sake faÉ—a, ta yaya za'ayi a zauna lissafin jiran Alhaji ya mutu? Cewa yayi yau ko gobe ze mutu?

"Kai kana bani ciwon kai wlh, a gidan nan kake zancen haɗin kai? Ko mu da muke Abokanan cin mushe muke cin dunduniyar junanmu ballantana kake maganar waɗanda a cikinsu akwai wanda suka fi shekara basu ga fuskar junansu ba, ni kana haɗuwa da Hussaini kuwa? Kasan zuwana Legos na ƙarshe kawai Mr Oniye ya ambato mun sunansa, wlh na manta a gidan nan munda wani Hussaini se lokacin wai yaron nan lasisin fitar da Mai ya taceshi yake nema bama ya siya a nan ba"

A tare Hajiya da Zakariyya suka zabura suna haÉ—a baki gurin cewa
"Hussainin?"
"Wlh fa, i was shocked irin kamar na faɗa tsakiyar transformer, kai nifa abun nan ma ya fara rikitamun lissafi ta yaya za'ayi ne mu mukeda kuɗi da iko from no where yaran nan su ringa fasowa suna mana over taking?" Nazirun ya sake faɗa, Zakariyya ya dunƙule hannaue yana kaɗa ƙafafu kamar mejin fitsari Hajiya kuwa kasa haɗiye kyashi, hassada da baƙin cikinta tayi kawai ta fashe da kuka tana cewa
"Nidai Binta ina ganin ta kaina a gidannan, na gama da Hadiza dakyar bangama da matsalar Aisha ba gata Zubaida tana neman ɓullo mun niko me nayiwa wani da wannan bala'u suke rikirkitomun haka wani bin wani?"
Haka taro ya watse dalilin wata sabuwa data bullo. (Ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to fa tasa ko É—umi ba zatayi ba).

A bangaren Aminu Bechi tsohon AG kuwa cikin hukunci irin na ubangiji barinsa BECHI GROUPS ba'a ko cike sati ba yana zaune ya fara samun gayyata daga kamfanonin da suke hamayya da BECHI GROUPS din, wasu sun so jansa ne domin su samu damar da zasu karya BECHI GROUPS saboda sunsan dole yasan sirrinsu ciki da waje kuma korar sa da akayi tana iya saka yayi fushi ya nemi ɗaukar fansa a kansu sedai Aminunba haka yake ba, koda cewar beji daɗin abinda ya faru dashi ba kuma yana da wani Rauni daban a zuciyarsa gameda Chairman ɗin BECHI GROUPS wannan bazata saka ya ha'ince su ba domin karya Alhaji Audu daidai yake da karya kansa dan ko babu komai Uba yake a gurinsa shiyayi silar zuwansa duniya wanna ta saka ya karbi aiki a wani ƙaramin Kamfani dan be kai sauran da suke farautarsa ba,

Albashinsa be kai wanda ake biyansa a baya ba amma a hakanma ya godewa Allah tunda ya ishe shi yacigaba da biyan buƙatunsa na yau da kullum dan shi bashida burin ya tara kuɗi daman shiyasa tanadinsa ƙalilan ne, jin daɗi makura yana bawa Iyalansa a duk sanda dama ta zo kuma ya tabbatar ko be mutu ya bar musu komai ba wannan farin cikin da ya sanyasu sanda yana raue zasu ringa tunawa suna masa Add'u, abinda ya rasa daga nasa Mahaifin.

Rayuwa taci gaba da tafiya, wanda yake binta a sannu tazo masa da sauƙi, wanda suka ɗauketa da girma tana cigaba da kwallo dasu bugu ta kowanne bangare har ana rasa na inda za'a tare se fatan ubangiji ya kawo sauƙi. A cikin shekara daya da wasu watanni ginin katafaren Shopping Mall ɗin Ahmad ya kammala. Gini ne akayi shi badai ya gini ba, tsari da taswirar gurin kaɗai ta isa ta sakaka ka shiga kayi siyayya ko badan kana ra'ayin hakan ba. An fitar da komai a tsare, bangare bangare daga na kayan Abinci na dafawa dana kwalama dangin su Alawa su Biscuit, kayan sakawa na manya da yara, kayan amfanin gida daga kan sumunti har zuwa ƙarshen abinda ake buƙata domingida ya amsa sunansa na gida da akwai a gurin, kai babu ce kawai Ahmad ne zuba a gurin ba, kuma wani abin jin dadi yanda ya faɗaɗa komai ya bawa Yan uwa da Abokanan Arziƙi damar shiga su saka hannun jari, bashida kuɗin da ze raya gurin shi kaɗai dan haka yayiwo gayya.

Yan uwansa na gidansu kaf babu wanda be samu akan maganar ba ya kuma tallata masa idan akwai abinda yake so ya zuba ya kawo amma kaɗan daga ciki suka amsa tayin. Takanas yaje har Bechi ya samu Alhaji Babannan wanda seya shekara biyar be taka ƙafarsa a gidansu ba seda babban dalili koda yake waɗanda suke cikin Kanon ma ba zuwa suke ba se su ɗin dai da iyayensu suke cikin gidan su kadai suke dabdalarsu idan kaga wani a cikin sauran tofa ba ƙaramin abu ya faru ba tunda Alhajin yayi musu Aure shikenan kowa ya sallami kansa.

Ahmad ya samu Alhaji Babannan akan zancen Shinkafa wadda yakeyinta sosai kuma yana jin yanda ake yabon irin da yake amfani dashi ana siyan shinkafar sosai dan kamfanunuwa ne suke kwasheta da yayi girbi dan hatta da BECHI RICE suna siyan shinkafar Babannan É—in saboda ingancinta.
"Ina ganin Yaya me ze hana kaima ka samu Alhaji kuyi yarjejeniya kamar yanda mukayi dashi, a maimakon ka ringa siyar da shinkafar daka Noma ya gina mala kamfani ka ringa sarrafata da kanka ana packaging kai tsaye kana siyarwa zakafi ganin ribar abinda kakeyi sosai kaga se a ringa ajiyewa a gurinmu masu siyan É—aÉ—É—aya yan sari kuma suzo kamfani gurinka" shawarar da Ahmad É—in ya bashi kenan.

Alhaji Babannan ya murmusa kawai, shiÉ—in bashida yawan magana tamkar marigayiya Bara'atu amma kuma dafin da yake cikin zuciyarsa yasa maganganun bakinsa basu da daÉ—i sam.

"Kaine mara zuciya da har abin hannunsa ya tsole masa ido ka iya neman Alfarma a gurinsa, yanda beyimun abinda ya zama wajibi na haƙƙina akansa ba bana fatan Allah ya kawo wani abu da ze sakani neman Alfarma a hannunsa komai ƙanƙantarta, abinda nake samu ya isheni rufin Asiri a duniya dan haka ka tashi ka tafi" amsar da Ahmad ya dawo da ita kenan tana masa nauyi a cikin zuciya ya kuma kasa amayar da ita ga kowa domin shi ubangiji ya hore masa ƙarfin zuciyar iya sirri komai girmansa komai ƙanƙantarsa.

Be daddara ba ya samu Ali ɗan uwan Aminu, bayan aikin kamfani yana siyan gyada ya kai kamfani a fitar masa da Mai yayi packaging ya siyar, a cikin waɗanda suke uba daya banda Jafar da baya cikin lissafinsu Alin na da saukin Hali se Hassan su biyun daman yasan da wuya suƙi tayin nasa Alin ya yarda yayi murna sosaima har yake cewa daman ya gaji ya fara tunanin haƙura da harkar saboda yanda yake shan wahala da mutane idan suka karɓi kayan kafin kuɗinsa ya fito. Hassan kuwa Magunguna yace ze zuba a bangaren Pharmacy da aka ware yace kuma ze tuntuɓi Hussaininsa wanda ko Lambar wayarsa Ahmad ɗin yace baya samu zeyi masa magana ko kuɗine se su haɗa su buɗe Pharmacy ɗin.

"Amma Ahmad idan ban shiga abinda be shafeni ba da se nace me yasa kayi register Kamfaninka da BECHI AND SONS sannan kayi Naming Mall É—inka BECHI SHOPPING MALL? why not AHMAD BECHI SHOPPING MALL If you must include the Bechi a cikin sunan? Ni kaina dana buÉ—e Clinic É—ina da BECHI HOSPITAL I'm regretting kuma ina shirye shiryen chanza masa suna soon" Dr Hassan ya faÉ—a, Ahmad ya É—anyi shiru yana mamakin dalilin
wannan maganar lura da hakan yasa Dr Hassan yi masa ƙarin bayani yace

"Magana tazo mun cewar yan gidanku sun cewa duk mu gama wahalarmu a ƙarshe komai da muka tara ya zama nasu mun sauƙaƙa musu ma da mukayi naming property namu da na Alhaji, dukda ni nasan ko sarautar hauka suke taƙama da ita babu wanda ya isa yazo anywhere near my property yayi claiming cewar nasa ne saboda uban nasu ma besan sanda na gina abuna ba balle su" Dr Hassan ya faɗa cikin zafin rai.

"Kayi haƙuri Yaya ka tausasa kalaminka akansa ko babu komai mahaifinmu ne Allah kuma babu ruwansa da wani abu da yake tsakaninka dashi wannan kyautatawa da bayar da girman dole kayi masa" Ahmad ɗin ya tareshi cikin ɗar ɗar domin dama damarsa ya gani akan Alhaji Babannan da har ya iya yi masa togaciyar.
Ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin yace
"Hakane, thaks for reminding me, amma kamar yanda nake gaya maka kai kana tsakiya, you still didn't own the property hundred percent, and you know that Man, he can be cunning, ina tsoron ya maka shigo shigo babu zurfi yayi ta kwace maka kuɗi daga ƙarshe ya barka da rigima da Yayansa ko kuwa ya baka papaers ɗin guri komai is in your name now?"

Ahmad ya girgiza kai a hankali alamar Aa, zuciyarsa naso ta kama zancen Dr Hassan sedai amintacciyar na jaddada masa babu yanda za'ayi Alhaji yayi haka, yama za'ayi hakan ta faru? Ya tabbatar suffar da suke ɗorawa Alhajin bashida ita haba da kuwa ya cika ƙarshen Azzalumi a duniya ace ya rasa wa ze damfara se Ɗan cikinsa kai wannan abin ko a labari be taɓa jin anyi irinsa bama. A sanyaye yace masa

"Bai bani papers ba amma komai da mukayi a rubuce ne akwai copy a gurina da Lawyer na shima haka, sannan Baba Alƙali ya sani, Baba Abdullahi ma ya sani Barr Aminu ma ya sani da Baba Musbahu duk suna cikin shaidu"

"Cikin yaran gidan fa ya sanarwa da wani?" Dr Hassanya sake tambayarsa. Duk se Ahmad ya nemi daya hargitse da tambayoyin Hassan É—in shaiÉ—an ya nemi daya fara rawar disco a zuciyarsa yana kawo masa wasi wasi. Kamar maraya yace
"Aa bansani ba ko ya gaya musu dai Amma Yaya Yakubu ya sani Jafar kuma tare muke shirya komai"

"Jaay, dazun na gama kallon maimaicin wasansu he is really making us proud, kaga a gidan Alhaji Audu, ku biyun nan ne kaɗai abinda zance yamun na kirki daya haifeku ko babu komai My two half brothers are something to write about" Inji Dr Hassan, se Ahmad ya fara tattare takaddunsa cikin alamar haramar tafiya amma Dr ya hanashi yace se yayi Dinner tukunna. Tare sukaje sallar Magriba da Isha'i sukaci abinci sunyi hira sosai sun kuma samu fahimtar juna daya tashi tafiya ya rabawa yaran Dr kuɗi dan yau be fito da Chocolate ba ko a mota bashida sannan ya kama hanyar gida yana tafe yana tunanin irin Daɗin da rayuwar gidansu zatayi da ace guri ɗaya suke zaune gaba ɗaya, se ya ringa ganin kaman samun daidaito a gidansu ze zama abu me sauƙi amma duk sanda ya zauna da wani a cikin yayyensu seya fuskanci abun ya shallakewa tunaninsa, tabbas Allah ya azurta Alhajinsu da zuri'a sedai ya watsata, haɗuwarta kuma se ikon Allah.

A yan ɗakin Hajiya Yakubu ya amsa tayinsa ya zuba zunzurutun kuɗi ba kayaba an kumayi komai a rubuce ta yanda za'a ringa bashi ribar abinda aka samu, shikaɗai ya zuba jari se Jafar wanda daman dashi ake tafiyar, yayi supporting Ahmad ɗin da duk abinda ze iya shima kuma ya zuba kayan ƙwallo da kayan motsa jiki a yanzun shima yana kan tsarin buɗe Academy ta Ball ne under his NGO wanda ze ƙaddamar idan yazo Bikin buɗe shopping Mall ɗin Yaya Ahmad da yace ko za'a bashi query se yazo be kuma sanar da kowa zuwansa ba banda Ahmad ɗin domin muddin Hajiya taji seta hana.

Abinda ya matuƙar bashi takaici duk bayan daya gama zagaya sauran yan uwa ya dawo kan yan cikin ɗakinsu da yake tsammanin bashida matsala dasu se gashi sunyi disappointing nashi. Kaitsaye Sarki yace he should count him out akan duk wani abu me kama da joint business shi kuma Salim da yake yazo ya ringa zama a gurin ranar da bashida lectures a makaranta se cewa yayi sedai idan shi za'ayiwa Manager to ya yarda amma bazeyi yaron shago ba.
"Kai baka san kasuwanci ba, se kaje ka haɗo dame ƙashin tsiya komai ya rushe a barka a ciki bazanyi wannan abunba I'm going to send you something ka ƙara jari ni yanzu hankalina ba'akan Business yake ba because I'm going in to politics" zancen Sarki kenan, Ahmad besan sanda yace

"Saboda shirme kabar Business ka koma siyasa? Ka kwashe kuÉ—inka fa kenan kaje ka zuba a cacar da baka da tabbacin samun nasara who does that? "
"Kai zaka gayamun abunda zanyi kenan?" Sarkin ya faɗa yana tsareshi da ido, Ahmad yayi shiru, basa faɗa irin na sako da sako amma fa basa ga Maciji sam, ba sarki kaɗai ba harda Salim kullum cikin faɗa suke Sarki na ganin Ahmad ya rainashi yana shigar masa rayuwa a son ya nuna masa daidai ko rashin daidai shi kuma Salim yace Ahmad ya takura masa ya tsaneshi komai yayi abin faɗane a gurinsa bayan kuma Ahmad ɗin duk ya fisu gaskiya shi Sarki tunda Abokai suka masa famfo suka ce ya shiga siyasa shikenan lissafinsa ya kwance Salim kuma da Faisal basu da saiti sam shiyasa yake matsanta musu yanzu shi a ɗakinsu Momy da yan uwansa mata ne abokanan hirarsa da shawara Mazan kowa kansa hayaƙi yakeyi.

Cikin nasara akayi bikin buÉ—e BECHI SHOPPING MALL, da yawan mutane kam sun É—auka mallakin Alhaji Audu Bechi ne dukda sunan AHMAD BECHI dake matsayin CEO dayawan mutane ma se sannan sukasanshi a matsayin É—an Alhaji Audun, wani abun mamaki duk tarin Yayan Audu ba kowa ya sansu ba idan ka cire waÉ—anda suke cikin kamfani. Abinda ze baka mamaki shine hatta JAAY da yake sananne kuma shahararre a duniya mutane basu san ÆŠan Audu Bechi bane saboda da yawa suna É—aukar Alhaji Muhammad Babban Yayansu Binta wanda ya tafi dashi UK a matsayin shine mahaifinsa dan yawan ganin hotonsu da akeyi tare acan, ganinsa da akayi a Taron buÉ—e Mall É—in Ahmad da yawa sun bashi expression na cewar Abokin Ahmad ne, ko kuma wani abu na daban ya kawo shi gurin.

Au na manta ban faÉ—a muku bala'in da aka kwasa da Hajiya akan zuwan Jaayy ba, ayi shiru kawai amma Ahmad ya kwashi tsinuwa saboda ta dalilinsa Jaayy ze rasa Miliyoyin da akace mata kullum ana bashi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.