Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 11
PAGE 21
Ya isa gida yana fitowa daga mota ya hango Hajiya daga ƙofar shiga gurinsu tana tsaye kome take a daren se Allah dan goma ta gota tana hangoshi ta nufeshi da sauri.
"Hajiya lafiya? Meya fito dake a daren nan?" Ya faÉ—a sanda suka gamu, tace
"Ina fa lafiya, tun Mangariba nake nemanka a gidannan kowa yace besan inda kake ba na kira wayarka yafi sau shurin masaki baka amsawa".
Se ya zaro wayar daga Aljihu, tunda ze shiga gidansu Afeeyah ya latseta ta shiga silent shiyasa beji kiran Hajiyar ba. Hajiya data gama ƙare masa kallo daga sama zuwa Ƙasa tace
"Daga ina ka fito haka kaci uwar Gizina kamar wanda yaje gaisuwar surukai?"
"Sadik na raka" ya bata amsa yana shafa kai lokaci guda zuciyarsa ta shiga tsalle, tabbas da akwai gagarumar matsala domin dai ya sani ko sama da ƙasa zata haɗe idan shi yace yaji ya gani tofa Hajiya ba zata yarda da wannan haɗin ba, a tsarin zubi na halitta Afeeyah ta dace da Matar da Hajiyar take hakaito masa sedai yasan an saɓa lamba, yar talaka jikar talaka yace ze aureta tofa ya taro gagarumin yaƙi ne ta shiga wanda be zamar mata dole bama tayi kane kane inaga maganarsa? Ta yuwu shi ba a gida zatayi masa nasa taron ba fili zata siya a gidan Radio ko Jarida ta wanke shi tas ta Ahalin daya ke shirin jajibo mata a matsayin surukai.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ya faÉ—a a fili yana dafe kai, Hajiya da tayi magana harta gaji ya zuba mata ido kawai amma alamunsa sun nuna baya tareda ita, cikin hayagaga tace
"Da akayi me kake ja mana Innalillahi? Ina maka magana tuntuni ka tsareni da shegun idanunku na gado ko kuwa kana nufi kaima ba zaka shiga maganar bane?"
"Wace magana kuma Hajiya?" Ya tambaya yana dafe kansa daya shiga sara masa, hasaso Word War III ya tashi a gidan kwai yake da zarar maganar auransa ta fasu. Sati biyun da mahaifin Afeeyah ya bashi sunyi kaÉ—an daya shirya harya saita komai bisa tsari ta yanda koda wani abu ze biyo baya ya zamana bayan cikar burinsa.
"Muje ciki na gaji, rabona da bacci me daɗi har na manta ni kaɗai kamar wadda ta rabawa masifu goron gayyatar biko da wannan ta fita wannan seta shigo" Inji Hajiya ta juya tana jan ƙafafu. Matsalar Hajiya ƙarama ce take neman zautata, Shegen Mijinta da yayi musu lamɓo akayi aure tunda taje gidan nan a kullum sabon Episode yake haska musu na rashin mutunchi. Yanzu wai bata da lafiya sunje Asibiti an ce ciki ne da ita shine yace sedai a zubar ita kuma taƙi yace ta zaɓa ko aurenta ko cikin wai shekararsa Ashirin da takwas be isa ya fara tara yaya su tsufar dashi ba. Tun wancan satin ake jaraba data kirata ta gaya mata tace ta je ta sanarwa Babarsa matar dake bata da mutunchi a faɗar Hajiya Binta wai tacewa Hafsatun ita babu ruwanta bata shiga rayuwar yayanta yanda kowa ya ga dama haka yakeyi tunda yace baya son haihuwar yanzu seta haƙura idan kuma zaman auren ne bata so ga hanya nan yammata da yawa ze samo wata ya aura.
Yau taje gidan Turai suka tattauna shine tace ta samu cikin su Naziru ta saka wani ya kirashi ya masa magana dan tasan Alhaji dai baze shiga wannan batu ba ƙarshe kwancewa kanta zani zatayi a kasuwa kowa yasan halin da ake ciki to ta kira Naziru yace baya Gari, Zakariyyah yace yaron bashida mutunchi baze kirashi ya zageshi a banza ba Yakubu kuwa da tasu a tsakani daman bazata sako shi ba shine take ta neman Jafar wai shi ya shiga ya sasanta dan yanda Hafsatun tace tun jiya ya bar ƙasar ya tafi Dubai bisa rakiyar wata budurwarsa da har gida ta biyo masa suka tafi daman kuma ba baƙon abu bane Ƙawayensa mata sunfi Maza zuwa gidan haka zasu wuni a part ɗinsa idan tayi magana in be dake ta ba se ya gaya mata maganar da zata gwammaci dukan da ita.
"Zan kirashi da safe Hajiya" Jay faÉ—a bayan daya gama sauraronta. Ta muskuta tace
"Gara dai ka kira shi, ta yaya za'ayi banda shi ba ɗan Arziƙi bane yace baza'a haihu ba? Dan uwarsa da ba'a haihuwa shi zezo duniyar ne ko kuwa da ba'a haihuwa da yawa layi zezo na haifa masa yar ya aura ya ringa zuga mata rashin mutunchi? Billahillazi se tayi dozen kuma a ƙalla ciki maza takwas koma goma duk wannan jiji da kan da uwar sa takeyi dan ta haifi Namiji ɗaya tal se mun sauke mata shi Hafsatu zata cika gida musu gida da Yaya ta yanda in ubansu ya mutu aka tashi rabon gado za'a haɗa harda su".
Cike da mamaki yace
"Hajiya, ina kika taɓa ganin jika ya gaki Kakansa?"
"Za'a fara akansu" ta faɗi irin ko a jikinta seya miƙe bayan daya ce "Allah ya rufa asiri bari naje na kwanta"
'Kai wai se yaushe zaka nunamun surukar tawa ne? Kuma yar wace ƙasace? Ya kamata fa azo ayi abinda za'ayi tunda wuri dan auranka so nakeyi nayi biki na kece raini Wanda ba'a taɓa kamarsa a faɗin Najeriya ba" Hajiya ta dakatar dashi seya koma ya zauna ya lalubo wayarsa daga Aljihu, cikin hotunan da yayiwa Afeeyah ranar dayaje gidan Anty Sauda ya buɗe kunno mata ɗaya, ta fito sosai a tsaye dukda fuskarta babu fara'a amma tayi kyau kwarjininta ya fito sosai.
"Kai kai kai zankaɗi zuƙi, Jafaru a ina ka samo wannan ta Gabas ce ko Yamma?" Hajiya ta faɗa tana zooming hoton kafin tayi gaba tana kallon ragowar da sukayi tare, akan wanda ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa kanta na kafaɗarsa dan haka rabin fuskarta ne ya fito Hajiyar ta tsaya, kamar idanunta zasu faɗo haka take kallon wayar tace
"Kyau iya kyau gaskiya kun dace, turamun wannan shi zan nunasu Turai" ya karɓi wayar da take miƙa masa, kunyar kansa ta kamashi da yaga hoton ita kuwa Hajiya kacaniyar nemo wayarta takeyi tana maimaita a tura mata zata aikawa su Turai suga surukarsu
"Wayar ba caji zan tura miki da safe" ya miƙe,
"Ai shikenan Allah ya kaimu, kai zan iya bacci kuwa? Ganin wannan yarinyar ya wankemun haushin shegen Yaron can ma wlh. Kai Allah dai yayi maka Albarka kai kaÉ—ai ko yaushe baka bani kunya kana biye da tsarina yanda ya kamata.
Sanda yaje ɗaki ya tarar Ahmad har yayi bacci, tun daya sahalewa kansa waccen mayyar yake bacci sosai da kuwa seya raba dare yana tsammatar kiranta kuma ba zata kira ba. Ya gama abinda zeyi ya kwanta sedai bacci ya gagara zuwar masa. Tunani kala kala suka addabeshi, laifin da Afeeyah ta masa na boye masa tana da wani bayan shi amma a yanzu damuwar Hajiya ta shafe wannan. Ta yaya ze sanar da saɓanin abinda take hasashe kuma irin abinda yasan zata gwammaci jin komai dashi wato ace shi Jafar data ciwa burin duniya kan matar auransa take zakwaɗin zuwan lokaci se kurum taji akasin abinda take buri wato dai a maimakon taji za'a tafi gidan Tayis Ac sama da ƙasa se a shige Lokon Alfindiki gidan laka shi ya tabbatar yar Bakamiken da Yah Ahmad ya kwaso in ba'ayi wasa ba tafi Afeeyah galihu.
Wannan al'amarin kacokan yana ganin ishara ce Allah ya gwada musu daga shi har Hajiyar, dukda shi bece ya tsani Talaka ba kuma be taɓa inkarin cewar baze auri ɗiyar Talaka ba ta yuwu izgilancin daya ke yiwa Ahmad ne kan zuciyarsa bata san abinda ya kamata dashi ba duk matan Kano ya rasa wadda ze so se yar Bakanike se gashi ubangiji ya masa talala ya jefashi a komar wadda yake ga nata uban ko Tartibiyar Sana'a bashi da ita.
Ya shafa ƙeya jin a garin lissafi ya sake tafka wata ɓaranɓaramar, ya za'ayi kai tsaye ya yanke Babanta bashida sana'a dame yake ciyar dasu sedai in ɓarawo ne ko ɗan Maula irin Babansu Anty Rabi.
"Allah na tuba" ya faÉ—a a fili jin shaiÉ—an na sake ingizashi izgilancin nasa na neman tsallakawa kan Baban Hajiya Rabi kuma.
"Meya faru?" Ahmad da yayi juyi a bacci ya tambayeshi, bashi da nauyin bacci ko yaya akayi magana yanaji.
"Zancen zuci ne ya fito fili, sorry na tasheka" Jay ya faɗa yana gyara kwanciya Ahmad ma baccinsa ya koma ya barshi yana cigaba da saƙa da warwara. Yayi tunanin ya ɓoye wa Hajiya Asalin Afeeyah ayi komai a sirrance tunda dai yasan Baba Alƙali baze kware masa baya ba, shima kuma Alhajin ko ya samu labari baze sake Ƙaiƙayin bakin gayawa Hajiyar ba dan silar na Ahmad har yau be gama komawa daidai maganganun da Yayansa suka sossoka masa ba basu gama sakinsa ba to amma kuma hakan bashida Fa'ida, duk yanda akayi daga baya magana seta fasu kuma abinda Hajiyar zatayi ta yuwu seya zarce wanda zatayi idan tasan komai tun daga mafari. Ko bayan wannan ma shi baze yarda ya gina wata mu'amala tasa da ƙarya ko yaudara ba musamman maganar aure, to shi yaya zeyi yanzu? Yana son Afeeyah so me tsanani cewar ya rabu da ita bama abu ne me yuwuwa ba to ya kuma zeyi da mahaifiyarsa da a duniya babu abinda ta tsana irin Talaka da Talauci??
Bacci ɓarawo ne yayi nasarar sace shi da Asuba kuwa ya farka da ciwon kai dan be daɗe da baccin ba Ahmad ya tashe shi Asuba tayi ga tunani daya raba dare yanayi. Be iya dogon zaman lazumin da Ahmad yake tilasta masa yi ba idan yazo gida ya bi lafiyar gado saboda bacci da ciwon da kansa yake masa, lura da kamar baya jin daɗi dan har idanunsa sun nuna hakan yasaka Ahmad be matsa masa ba shidai yaci gaba da jan carbinsa. Tun jiya yake fama da faɗuwar gaba daya rasa ta mecece ga tunanin Fatima daya masa sauƙi kwana biyu ya juyo dan seda yayi dagaske jiya kafin ya iya dakatar da kansa daga kiranta. Tunda Baba Alƙali ya shaida masa Baffah yace su dakata da zuwa daga nan ya sare daga lamarinta ya tabbata ya rasata kenan tun sannan kuma ya tilasta kansa haƙuri da al'amuranta, ko dar beji sonta ya ragu a ransa ba amma ya taushi zuciyarsa ta karɓi ƙaddarar cewa Fatima ba matarsa bace, yana tsaka da jinyar zuciyarsa kuma sabon abu ya fara bijiro masa daga jiya zuwa yau ɗin tamkar ana masa kiranye haka yakejin so me zafi yana Azalzakar zuciyarsa, kasa dakatar da kansa yayi yabi umarnin zuciyarsa ya cire wayarsa dake jikin chaji ya doka mata kira.
FATIMA
Tana kwance kan abin sallah wand kusan akansa ta kwana, tun bayan da Umma ta gama soka mata maganganu jiya ta shiga ɗaki ta ringa kuka, Allahn daya jarabci zuciyarta da soyayya shi kaɗai yasan halin da take ciki se Baffah da ya tausaya mata yake ƙoƙarin ganin ta samu cikar muradinta badan haka tasa zuciyar taso ba Umma kuwa ta juya zuciyarta baibai taƙi fahimtarta ta yaya zatace ta zare hannunta daga Al'amuranta? Tana fatan ace barazana takeyi mata saboda ta fasa abinda tayi niyya dan in da gaskene ina zata kama tayaya ma koda ace burinta ya cika na zama matar Jay zata samu farin ciki da nutsuwa alhalin Ummanta tana fushi da ita??
Haka ta raba dare tana koke koke daga ƙarshe taci galaba akan shaiɗanin da yake neman nesantata daga neman ɗauki gurin ubangijinta ta fita tayo Alwala ta ringa jera salloli, a baya koda babu yawa takan tashi tayi sallah ta kaiwa Allah kokenta da buƙatunta amma tun da suka fara raba dare suna zuba sharafin soyayya da Jay shaiɗan yayi kinini ya samu abinda yake so. Sanda ya kamata ta tashi tayi sallolin se baccin da batayi da wuri ba da gajiyar data kwasa a yinin su danneta, sallar Asuba ita da take tashin yan ɗakinsu ya zama yanzu ita ake tashi duk free time da take zama ta jaddada kusancinta da mahaliccinta soyayyar Jay ta cinye yau da duniyar ta mata zafi ta ko ina gashi take karɓa dole ta fuskanci mai duka ta kai amsa kukanta.
A baya takan yawaita addu'ar neman zaɓin Allah a cikin lamuran rayuwarta gaba ɗaya, yanda Ahmad ya kasa samun matsuguni a zuciyarta duk kuwa da tarin kyawawan halayensa yasa kawai ta yankewa ranta ba Alkhairinta babe shiyasa ubangiji be haɗa zuciyoyinsu guri guda ba, da Jay ya afko mata yanda ya shiga ranta farat ɗaya nan kuma ta yanke shine cikar burin datake jira Allah ya aiko mata. Bata nemi zaɓin Allah ba kawai ta yanke shiɗinne kamar yanda bata nema akan Ahmad ba ta yanke bashi bane.
Ance ba'ayin aure salin alin amma kuma bata tsammaci auran da ze saka ta samu tangarɗa da iyayenta ba ze zamo Alkhairi a rayuwarta ta yaya ma haka zata faru?? Umma tace ta zare hannu a al'amarinta ta ina zata ga haske a gidan Jay?? Toh amma idan ta haƙura dashi yaya rayuwarta zata kasance? Ta tabbatar babu ita babu farin ciki a gidan auran da ba Jay bane ze kasance Mamallakinta, shi take So, shi zuciyarta ta aminta dashi amma kuma Albarkar iyayenta nada muhimmanci da tasiri a cikin rayuwar da zata gabatar tare dashi.
Ta ringa jera sallah tana kuka wiwi tareda kwashe mintoci masu yawa a sujjadarta tana kaiwa Allah kokenta da neman agajinsa a wannan siraɗi da take kai, seda taji sallar Asuba kafin bacci ya kwasheta bata jima ba cikin baccin ta ringajin ƙarar wayarta data ajiye dabda kanta bayan ta duba lokaci kafin baccin ya kwasheta. Tayi firgigit ta farka, mafarki take wai Jay yazo a fusace ya ɗaga hannu ze kwasa mata mari be kai ga aiwatar da nufinsa ba ta farka tana zare ido, akan me Jay ze mareta a mafarki? Koda yake da fushinta ya tafi jiya ƙila ya huce ne shine ma yake kiranta yanzu da wannan tunanin ta janyo wayar da azama ta duba.
Sunana Ahmad ta gani da manyan baƙi suna yawo a kan wayar, ta ringa maimaita sunan a ranta tamkar ranar ta fara ganin kalmar.
"Allah ka haskamun abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, Allah karkasa aurena ya zama silar gamuwata da mahaifana" Addu'ar data ringa nanatawa a sujjadarta tana bin bayanta da sunayen Allah tsarkaka tare da cikakken yaƙinin samun biyan buƙata. Ahmad da ta manta rabon da suyi magana a waya dashi tun kafin dawowar Jay kamar tun ranar da Anty Sauda ta tilasta mata kiransa ta bashi haƙuri shine yake kiranta yau da farar safiyar nan?
A maimakon ta amsa wayar se kawai ta kifeta ta fashe da kuka kamar wadda aka mara ta ringayi harda shashsheƙa shi kuwa kamar yasan meke faruwa ya ringa kira har seda ta amsa ba tareda ta bar kukan da takeyi ba.
AHMAD
A gigice ya miƙe tsaye bayan da Fatima ta amsa wayarz kira uku ya mata kafin ta amsa ana huɗun ya raya a ransa bacci takeyi amma kuma abinda yakeji a ransa game da ita yasa ya kasa haƙura da kiran har seda ta amsa.
"Lafiya Fatima, meya sameki? Meya faru kike kuka?" Ya jera mata tambayoyi a rikice, daga can gefen ta sake kecewa da kukan daya fi na farko ba tareda ta bashi amsa ba, ya wuce ya buÉ—e wardrobe inda Jallabiyyunsa suke yake dubawa da alamu ya manta da wata a jikinsa saboda ruÉ—ewa
"Dan girman Allah ki faÉ—amun meya faru? Me yasa kike irin wannan kukan?" Ya sake faÉ—i yana zaro riga ya shiga kici kicin sakata akan ta jikinsa.
"Bani da lafiya, ƙirjina ciwo yakeyi" ta faɗa tana jan numfashi kamar zata shiɗe, yaja salati ya dire kafin ya saki rigar hannunsa ya nufi ƙofa se kuma ya dawo da sauri ya shiga jijjiga Jay da tun fara wayar daya ambaci sunanta ya kasa kunne yana jinsa dan baccin nasa beyi nisa ba.
"Meye kuma?" Ya faɗa yana miƙa kamar sannan ya tashi. Ahmad ya latse wayar ya kashe kafin yace masa
"Ka tashi muje, Fatima ce bata da lafiya"
"Alhamdulillahi Allah yasa ta mutu kowa ya huta" Jay ya faɗa kafin ya juya abinda ya kwanta harda jan Duvet ya rufe har kansa. Ahmad yayi kasaƙe yana kallonsa kafin kuma ya tuna abinda yake gabansa ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi ya fice.
Dake safiya ce ko bakwai batayi kuma ana hutun makaranta dan haka babu cinkoso akan titi nan da nan ya isa unguwarsu Fatima. Ko buɗe ɗe ƙofa basuyi ba ko kuma sakayota akayi oho ya niyyata ze buga kenan ya hango Baffah yana tahowa da carbi a hannunsa da alama sannan ya fito daga masallaci.
Mamaki bayyane akan fuskarsa yake kallon Ahmad sanda ya durƙusa yana gaisheshi dan daga nesa be gane shi bane ko kuma be kawo ze ganshi a irin lokacin bane yasa be kawo shiɗin bane.
"Fatima ce na kirata tana kuka tace mun bata da lafiya" Ahmad ya bawa Baffah daya tambayeshi ko lafiya ySa ganshi yanzu amsa. Baffah yayi shiru kafin ya tura ƙofar yayi ciki yana ce masa
"Bismillah"
"Aa Baffah ta fito muje Asibiti kawai kar a ɓata lokaci" ya bashi amsa kai a ƙasa. Baffah ya shige ciki ya tarar da Umma a tsakar gida tana yan kaye kayenta.
"Ina Afeeyah?" Ya tambayeta, ta nuna masa É—akin Afeeyar da hannu dan haushinsa takeji seda suka tafka mahawara jiya kafin sukayi bacci. Wai ya bawa Jafar sati biyu ya turo, data tambayeshi yasan shi ne ko yayi bincike a kansa da zece ya turo maganar aure sati biyu se yace mata
"Banji a jikina yaron nan ze aureta ba koda yana sonta shiyasa nayi musu haka kinga daga ita harshi babu wanda zece an tauye masa haƙƙi. Yace sunan mahaifinsa Abdullahi Tijjani Ɗan kasuwane kuma a unguwar Hotoro suke zaune zan sanarwa Malam Saminu seya bincika shine me mutane a shiyyar dan binciken Ahmad ma kinga shi yayi"
"Lallai Malam, wato bakaji a jikinka auranta zeyi ba? To idan kuma ya ƙaryata jin naka ya turo magabatansa se ayi yaya?" Umman da mamaki ya cikata fal ta faɗa Malam ya sake tamke mata kai daya ce
"Ruƙayya, duk wanda yake shine Alkhairi a gareta Allah ya tabbatar mata, Allah yaga zuciyata, idan son rai na ne Ahmad shi ze zama Mijin Mamana amma tace ba haka ba, bazan mata dole ba zan cigaba da bibiyar lamarinta da addu'a Allah ya zaɓar mata wanda yafi Alkhairi a cikinsu". Tsabar yanda ya kasheta da mamaki yasa ta gagara ce masa komai se kallonsa da ta ringayi, wato baze mata dole ba
"Ai shikenan" ta faɗi ta maida kai ta kwanta ranta fal da mamakin Malam Hafizu. Da sanin yau ta masa se tace kwaɗayin matsayin sabon yaron da Afeeyar ta kawo ne ya jashi to amma idan Arziƙine a Nigeria dai ai ba'a gayawa Audu Bechi uban Ahmad ba. Ta yuwu makauniyar soyayyar Uba da Ya ce tasa ze zama sullutu ya biyewa Afeeyar ta mayar dashi Ƙaramin mutum. Ta raya a ranta zata saka musu ido shi da yar tasa ne taga gudun ruwansu ba zata sake cewa komai akai ba, da wannan haushin ta kwana shi yasa da safiyar da yake tambayarta ina Afeeyar ta masa nuni da ɗakinta kawai taci gaba da sabgar gabanta.
Baffah ya kada baki ya kira Afeeyah dake kwance wurjajan tana kuka jin daɗi, yo jin daɗi mana babu duka babu zagi mutum ya ƙule a ɗaki yana kuka ai se wanda daɗi yaiwa yawa. Ta amsa tana goge hawayenta kafin ta fito tana kare fuskarta da Hijabi. Saboda karma Umma taji abinda ze hasalata yasa ta shigi kitchen ta basu guri, tana jin Malam na tambayar Afeeyah me yake damunta?
"Ahmad na tarar a waje yace kunyi waya yanzu kince masa baki da lafiya meya sameki" inji Baffah. Ta kalleshi da mamaki tana maimaita "Ahmad kuma?" A fili yace
"Eh shi, ko bakuyi waya ba"
"Munyi, amma ai bace masa nayi yazo ba kuma ni lafiya ta Ƙalau" ta faɗa a sanyaye.
"Se kije ai ki sallameshi gashi can duk hankalinsa a tashe, wlh yaron nan tausayi yake bani Jarabta a so babban abu ne me wahalar gaske" Malam ya faÉ—i yana wucewa É—akinsa Umma data fito da tukunya zata tari ruwa a famfo ta koma kitchen ba tareda ta kalli inda take bama ita kuma Afeeyah tsoron abinda Umman zatace ya hanata tashi daga inda take har seda Malam ya sake mata magana.
Ahmad na jingine da ƙofar gidan, daka ganshi kasan yana cikin damuwa duk yayi wani iri yanajin an taɓa ƙofar ya juya da sauri sukayi ido huɗu.
Gabanta ya yanke ya faɗi ba tareda wani dalili ba, kai a ƙasa kamar wata farin shigar munafurci ta gaishe shi,
"Muje Asibiti Fatima me yake damunki?" Ya faɗa yana matsawa gabanta. Ta girgiza masa kai idonta na tara Ƙwalla tace
"Ciwon kai ne daman kuma ya sauka"
"Ciwon kan kikewa kuka haka Fatima? kalli fa yanda fuskarki ta koɗe yanayinki ya nuna ba lafiya ba sannan kice ciwon kaine kuma ya sauka" Ahmad ya faɗa yana ƙare mata kallo.
"Dagaske nakeyi maka ciwon kaina yana da zafi sosai har nakan gwammace nayi zazzaɓi akanshi"
"Kinga kenan kina buƙatar Dr's attention dan haka muje Asibiti kawai"
"Dagaske na warke nasa magananin da aka bani akan duk sanda ya motsa mun nasha Migraine ne" ta sake faÉ—a cikin tabbatarwa. Se tayi murmushi kallonta yace
"Kodai biko na kikeyi shine kika fake da ciwo saboda ki tasoni ko ban shirya ba?"
Tamkar tace masa tayi bikonsa a saboda me se kuma tayi shiru tana wasa da yatsunta murmushi ya kwafsa mata ta hanyar sakin kansa ba tareda ta shiryawa hakan ba. Ahmad yayi murmushi yana gyara tsayuwarsa yace
"Duk sanda nafara fitar da rai da tsammanin samunki se Allahya kawo silar da zata sake maido ni rayuwarki bakya ganin hakan bayinmu bane yin Allah ne? Ta yuwu akwai wani tanadi da yayi mana amma zukatanmu na nesan tamu da riskar wannan tanadin akan lokaci?"
Bata ce komai ba be kuma damu da hakan ba yaci gaba da cewa
"A yanzu na rigada na buɗe zuciyata, na sallamawa Ubangiji komai dukda dama a kullum cikin miƙa lamurana a gareshi nake. Tunda kince lafiyarki Ƙalau bari naje gida, se wani lokaci" be jira komai ba ya wuce ya barta a tsaye. Jiki ba laka ta koma ciki ta dasa jiran tsammanin samun kiran Jay amma har Azahar shiru babu shi babu labari.
Ahmad kuwa bayan ya koma gida ya tarar da Jay na shiri daya tambayeshi ina zeje yace masa Kaduna daga can ze wuce Abuja gidan Hajiya Ƙarama. A taƙaice yayi masa bayanin da Hajiya ta masa jiya, Ahmad ya jinjina Al'amari, Allah kenan me mutane iri iri. A haifi mutum amma tsabar shahara yace shi baze haifi wasu ba to Allah ya rufa asiri. Be ce ze bishi ba kamar yanda shima be nemi rakiyarsa ba za'a iya cewa wannan shine karo na farko da hakan ta faru ace Jay zashi wani guri ba taredaya nemi rakiyar Ahmad ba. Tareda Manager shi suka tafi shi kuma Ahmad bayan ya shiga gida sun gaisa da Momy da sauran mutane ya tafi Shago duk yanajin babu daɗi. Tabbas akwai abinda yake damun Jafar, amma menene wannan da har ya gagara tattauna matsalarsa dashi?
Jiyayaje gidansu wacce yake so basu samu sunyi magana ba balle yaji yaya sukayi tunda kafin ya shigo shi yayi bacci da safe kuma ya fita to kodai shima ya samu matsala irin tasa ance ya dakata ko kuma ma dai iyayenta sun rigada sun mata Miji? Tunanin da Ahmad ya ringayi kenan yana zaune a office ɗinsa. Ya ɗauki wayarsa ze kira Jafar sega kiran Fatima ya sake shigowa wayarsa. Mamaki kamar yayi me, Fatima dai yau meya sameta haka acw a rana da kanta ta kirashi har sau biyu wannan abu kamar Almara. Be sake rushewa da mamaki ba seda ya amsa bayan sun gaisa take tambayar ya yaje gida sannan ta bashi haƙurin tayar masa da hankali da kuma fito dashi da sassafe daga nan sukayi sallama dan ya gagara sakin jiki yayi mata wata Ƙwaƙwarar magana.
Allah sarki zuciya da abinda take so, ɗan wannan kiran yasa duk ya rikice ya cigaba da ɗora lissafin gobensa da Fatima, daya tashi daga Shagon daƙyar ya kanne ya wuce gida dan zuciyarsa nata uzzura masa da ya sake zuwa ya ganta ya kumayi mugun Ƙoƙari da be kirata ba. A daren Jay ya dawo, se yaga kamar sanda ya tafi yafi nutsuwa da kwanciyar hankali akan dawowarsa duk ya wani birkice kuma bece masa komai ba still shima ya kama bakinsa be tambayeshi ba.
A ɓangaren Afeeyah kuwa abu kamar almara haka aka wuni sur tun tana zaton Jay ze kirata harta fitar da rai ta shiga lalube da lissafin yanda rayuwarta zata kasance idan har da gaske Jay ya barta. Ta kirashi sau biyu wayar ta Ƙaraci ringing ba'a amsa ba kuma be biyo baya ba har dare, A ɗaki ta wuni, sunyi Chat da Badar bata ɓoye mata komai ba akan zuwan Jay na jiya, yanda sukayi da kuman zuwan Ahmad da safe harma da Stand ɗin Umma akansu biyu
"Allah na sonki Afeeyah, karki bari ki rasa damar da kike da ita a hannu wlh ba zaki maimaira kamarta ba. Bakoda yaushe abinda muke so a rayuwarmu yake zama Alkhairi ba haka kuma ba duk abinda muke ƙi ne yakan zama sharri tare damu ba. Kiyiwa kanki karatun ta nutsu ki kalli gidajen aurayen da suke a zagaye dake wanda akayisu cikin daɗin rai da sahalewar uwa da uba amma ba'a rabasu da ƙalubale da matsaloli inaga wanda akayi kan doron fushin iyaye? Yanzu ke zaki iya zaman aure da Mijin da mahaifiyarki ta nuna bata sonsa? Bana tsammatar zaki samu cikakkiyar nutsuwa balle kwanciyar hankali nidai irina wlh ko Yan gidanmu ne suka nuna basa son mutum muddin suna da hujja me Ƙarfi zan haƙura dashi saboda su dai dasu zan tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa idan babu goyon bayansu ina zan kai kukana?
Kina gani dai kina zaune Allah ya sake turo miki Ahmad a lokacin da abinda kike ƙulafuci yake ƙoƙar bari hannunki, idan kika sake kikayi wasa da damarki tana iya zama ta ƙarshe dan haka kiyi tunani kuma ki tattaro ki dawo School ki fuskanci karatunki semester ƙarshe muke karki bari kiyiwa kanki sawarwarar da zaki samu matsala a wannan lokacin tun wuri ki saki komai ki sake kama Allah ki kuma bar komi a hannunsa" abinda Badar ta gaya mata kenan da har yasa ta samu ƙwarin guiwar sake kiran Ahmad.
Jay be kirata ba se washe gari, idan kaga yanda ta fita a hayyacinta seka zata ciwo takeyi kwana guda kawai amma ji take kamar ta shekara ba taredashi ba faɗar irin zafin da takeji a zuciyarta kuwa ɓata lokaci ne, ashe haka Ahmad yake ji akanta shima? Tabbas So abune me ciwo da wahalarwa ta yarda yanzu da ta afka masa kuma ta dena ganin baiken masu zaucewa a soyayya domin ita kanta a yini ɗayan nan da takejin kamar tayi bankwana da farin cikin rayuwarta badan tsoron abinda ze je yazo ba ware baki zatayi tayita kwarara ihu a ɗaki harse nauyin da zuciyarta tayi mata ya ragu amma bata isa ba Umma zataci mata uwa da uba ne tabbas a gidan shiyasa sedai ta lafe a ɗaki tayi kuka ta share hawayenta.
Tana tsaka da shirya kayanta dan ta himmatu gobe zata koma makaranta kafin baƙin ciki yayi Ajalinta a gidan babu jimawa sun gama magana da Ahmad dukda ba qata magana me tsayi bace ba shiya kirata yaji ya take idan babu damuwa zezo Anjima da anyi Magrib tace masa Toh shikenan sukayi sallama. Tana zuge akwati wayarta tayi ƙara ta zabura jin Ringing tune data sakawa Jay ne. A tare suka sauke ajiyar zuciya bayan data amsa wayar kafin ya kira sunanta a sanyaye bata amsa ba se kawai ta sakar masa siririn kuka daya saka ya miƙe tsaye daga kwancen da yake babu shiri
"Kuka kuma? So kike ki ƙaramun damuwa akan wadda nake ciki?" Ya faɗi cikin yanayin daya saka Ahmad dake cin abinci kallonsa. Basu jima da dawowa daga gidan Baba Alƙali ba koda yake Jafar ya ɗakko acan besan ma yaje ba seda ya kirashi yace ya biya dan Alkah su taho tare suna shigowa kuma ya wuce gurin Momy ya karɓo abinci shi Jafar yace Azumi yakeyi seda suka gama magana da Fatima kafin ya fara cin abincin.
"To ba kaine ba tun da ka tafi baka waiwayeni ba" ta faÉ—a cikin kuka. Seya koma ya zauna yana cewa
"Kinyi mun laifi, baki kirani kin bani haƙuri ba and you are expecting me to call you kenan baki san girman lafin da kika aikata ba ko?"
"Na kiraka jiya sau biyu baka amsa ba" ta bashi amsa tana tsagaita kukanta se yace
"Jiya, wato baki damu ba na tafi cikin fushi, baki kirani tun a darenba se jiya shima da rana saboda kin lura ina sonki"
"Wlh ba haka bane ba, kai kace na cire layina daga waya na cire se da safe na samu Ƙarama na saka layin a ciki" ta sharfaɗo Ƙaryar da ita kanta se bayan ta dire maganar kunyar kanta ta dabaibayeta.
"Kinci darajar Son da nake miki shiyasa na kasa daurewa amma da wlh nayi niyyar bazan sake kiranki ba har se bayan anzo an tambayan mun auranki but i couldn't, my heart is going crazy about you ji nakeyi kamar nayi hauka just a day banji muryaki ba". Ina ruwa Afeeyah ta buga tsalle ta faɗa dajin ba haƙura Jay yayi da ita ba kuma ba fasa auranta yayi ba ashe punishing nata yakeyi da Ƙin kiranta aiko ta ladabtu.
"Kayi haƙuri" ta faɗa cikin wata lallausar murya, Jay ya saki murmushi yace
"Zan haƙura but let me see ur face first, oh na manta kin cire Sim daga wancan wayan ko? Then zanzo anjima zan taho miki da wani wayan amma ba fa jimawa zanyi ba dan ban gama hucewa ba, zan baki waya ne kawai na tafi"
Cike da zumuÉ—i kamar zata taka rawa tace
"Allah ya kawo ka lafiya"
"Aiit, take care I love you" ya faÉ—a, ta mayar masa da
"I love you more and i miss you" daga nan suka aje waya. Ya kalli Ahmad dake cin abinci yace
"Yau zamuje gurin Afeeyah"
"Wacece haka?" Ahmad ya tambaya, Jafar ya ɓata fuska yace
"Soyayyata"
"Soyayyarka da kake mun boye boye akanta ko? Aje lafiya nima yau gurin Babyta zanje mun shirya".
"Kayi haƙuri, i promise you idan muka dawo zan gaya maka komai ba abinda kake tunani bane"
"Bana so kuma ba zanje ba na gaya maka gurin Babyta zanje nima" Ahmad ya faÉ—a shima yana kumbura fuska kamar gaske Jafar yace
"How about ka rakani nima na rakaka? Amma gurin Soyayyata za'a fara zuwa"
"Then if you mean ita muje amma gurin Fatima zamu fara zuwa nine babba kaga matata tana gaba da taka kuma nasan wayo kake so kayi mu fara zuwa naka daga nan ka zame ka barni" inji Ahmad. Jay ya yamutsa fuska, kamar yasan abinda ya niyyata zeyi kenan, bashida zaɓi tunda yana so Yah Ahmad ya rakashi gurin Afeeyah dole ya yarda da tsarinsa koda yake gara ma yaje face to face ya zazzagewa Wannan Fatiman abubuwan da suke a ransa, wato ta mayar da Ahmad kamar wani Toy tayi wasa dashi sanda taso ta yar sanda taso to yau kuwa ze buɗe mata aiki.
Suka shirya bayan da akayi sallar magriba suka kama hanya. Jay ne yake tuƙi, suna fita Ahmad ya kira Fatima danya shaida mata bashi kaɗai bane kuma sun taho. Ita shaf ta manta ma da zuwan Ahmad tunda Jay yace mata zezo ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta zabari mayafi ta tafi kusadasu aka mata baƙin lalle ranar daya fara zuwa yace mata yana so da yake da wuta nan da nan ta wanke kanta ta busar da Dryer ta tayi styling nasa da adon da ze bayyana sanna ta turara kayan da zata saka Two piece Gown and V Hijab data siya a gurin Ummu-Maheer (07061838488), yadi ne me sauƙin kuɗi amma kyakykyawan ɗinkin daya samu yasa idan ta sakasu ake ɗauka tafiyayyen ne daga Egypt haka Hijabanta.
Umma nata kallon ikon Allah amma bata ce mata komai ba tasan sunyi waya da Ahmad amma bata zaton zuwansa takewa wannan shirin haka.
Tana ganin kiran Ahmad ta tuna da batun zuwansa, ta yi kasaƙe tana tunanin mafita dan Jay ma yace mata yana hanya dukda dai yace ze biya wani guri tukunna. Da sauri ta shiga kiran layin Ahmad bayan data shirya Ƙaryar da zata masa da zata dakatar da zuwansa amma wayar taƙi shiga. Har wani tsirgawa cikinta ya ringayi saboda tashin hankali, ya zatayi idan Jay yazo ya tarar da Ahmad????