Complete Hausa Novels

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 11

PAGE 22
JAY
Suna tafe a mota suna hira gwanin sha'awa irin wadda suka sabayi da alamu yardar zeje gurin Fatima tareda Ahmad ta faranta ran Ahmad ɗin matuƙa dan gashi nan a bayyane. Sun hau kan Gadar ƙofar Nasarawa ya tambayi Ahmad ina zasuyi.
"Miƙewa zakayi Mandawari zamuje" Ahmad ya bashi amsa. Ya taka mota yana cewa
"Ai bansan gurin ba"
"Muje masallacin sarki idan mukayi sallar isha se na karɓi tuƙin" Ahmad ya sake bashi amsa. Jay yayi shiru kamar yacewa Ahmad ai nan ne unguwar su Afeeyah se kuma ya ƙyale. Haka kawai yaki jikinsa ya masa wani iri, gudu yake da mota amma se gashi ya rage speed sosai ya koma tafiya a hankali har suka isa Masallacin, yanajin sanda sukayi waya da Fatiman yaja tsaki bayan da Ahmad yake ce masa wai gidan Yayarta zata tafi

"Kabarta ta tafi kawai se muje gurin my Afee, naga ta kirani ma bana so na amsa kewarta yasa na gudu na barka kace ban kyauta ba"
"Su tsuntsun soyayya, yau dai zanga wannan Afeeyah naga da wane charm ta sace zuciyarka" Ahmad ya faÉ—a yana dariya.

Be manta hanyar daya bi har zuwa bakin titin da ya jira Malam yazo ya tafi dashi ba wannan tasa mamaki ya kamashi sanda yaga bayan sun isa Mandawari Ahmad ya karkata ya shiga titin unguwar su Afeeyah, kasa haƙuri yayi har seda yace masa
"Wai nan ne unguwar su Fatiman?"
"Nan ne, ko kana zaton wata GRA zamuje? To a nan lungun tawa Babyn data sace zuciyata take kuma wlh karka kuskura muje kace zakayi mata izgilanci domin dai ka sani Arziƙi da Talauci duk na Allah ne kuma a aure Tarbiyyar mace ake dubawa bawai girman gidan data fito ba".

Sam bama sauraron Ahmad yake ba illah baza idanu da yayi dakyau yana so ya gane layin da suka shiga da Malam. Akwai wani gida me rumfar langa langa doguwa a daidai kan layin mutane suna zama gurin ya zama kamar masallaci ma dan har butuci ya gani da drum na ruwa a gurin ranar daya zo wannan ya riƙe a ransa matsayin alamar daze ringa gane mashigar lokon nasu dukda idan ya shiga ciki babu tabbacin ya kai kansa saboda zurfin gurin.

Zuciyarsa ta buga Dumm sanda Ahmad yayi parking a daidai spot É—in daya haddace a ransa. Ya ringa kallonsa sanda yake ce masa
"Da yar tafiya daga nan zadai ka iya ko?" Se ya ƙaƙalo murmushin dole yace
"Nida nake zagaye field sau babu adadi kake cewa zan iya wani ɗan trecking kaɗan". Ya fita yanajin wani sanyi na raysa gaɓɓansa dukda cewar zafi akeyi, ya ringa kallon gurin kamar meson yaga ya canza masa daga abinda zuciyarsa take hasaso ma, suka tsallaka yana biye da Ahmad a baya suka shiga cikin lokon

"Ba lallai abinda kake hasashe ya zama gaskiya ba, Ƙaddarah bazatayi muku haka ba, baza ta saka ku Son abu ɗaya wanda baze yuwu ku mallakeshi a tare ba" zuciyarsa ta ringa Ƙarfafa masa guiwa. Ahmad dake masa hira jin baya amsawa ya saka shi kama bakinsa suka ci gaba da tafiya. Jay da yake tunanin idan ya dawo baze iya sake maida kansa gidansu Afeeyah ba se gashi taswirar Lokon na zuwar masa kamar zane a Ƙwaƙwalwarsa, bugun zuciyarsa ya tsananta sanda yaga dagaske sun tasarma layin da gidan Malam Hafizu mahaifin Afeeyah yake ciki, akan kwana yaci burki Ahmad ya kalleshi yace
"Ya akayi naga ka tsaya"
"Nasan Afeeyah tana can tana jirana, so nakeyi na kirata na gaya mata zanyi latti kartaji shiru kayi gaba zan biyo ka" ya rattabo masa ƙaryar da yake ganin ita zata fitar dashi. Ahmad yace

"Ga gidan can ai mu ƙarasa seka kirata ko sarki me Afeeyah" ba tareda ya kalli gidan daya nuna masa ba ya shiga shafa Aljihunsa yana laluben waya amma be jita ba ya saki ajiyar zuciya kafin yace masa

"Wayar na mota"
Dan Allah muje Jafar na sani daman se munyi haka dakai kuma tunda muka zo nan dai ya kamata ka daure kawai mu ƙarasa yau ɗaya kaga Fatima na tabbatar duk wani grudges dake tsakaninku yau zaku warware shi muje please".

"Wannen ne gidan?" Jafar ya tambayeshi a ransa yana fatan ya nuna lungun daya miƙe yace a ciki gidansu Fatiman yake, kai shi da zata yuwu ma Ahmad yace makuwa yayi ba nan unguwar zasu zo ba saboda abubuwan da zuciyarsa take raya masa sunyi muni da yawa baya fatan ace hakan kuma ta zama gaskiya

"Wancan me Ash paint da baƙar Ƙofa daidai inda Solar take" Ahmad ya sake nuna masa gidan da kwatancen da duk yanda yaso da kautar da gaskiya dole ya shige shi. Ya zurawa gidan ido kamar me son gano inda aka haƙo Ƙasar da akayi ginin gidan da ita. Ahmad ya cigaba da tafiya yana ce masa
"Muje mana"
"Zan zo Yah Ahmad Allah bana son rigimar Afeeyah kaga ban gaya mata zan biya wani guri ba kuma na bar wayana a mota kar tayita kira taji shiru kaja mun tayi fushi" ya sake faÉ—i, yanda yayi maganar da ace Ahmad ya mayar da hankali ze fahimci akwai abinda yake dannewa. Ahmad ya girgiza kai yace

"Shikenan, amma wlh idan baka dawo ba Allah ka shirya tarbar rashin mutunchin da zanyi maka" Ahnad ya sake faÉ—a yana jefa masa key É—in mota seya cafe yana murmushin da gara ace kuka ya fasa dashi kafin ya juya yana cewa
"Zan dawo".
Wucewa Ahmad yayi abinsa ya tsaya a Ƙofar gidan kafin ya rangaɗawa Fatima kira a waya, Jay kuwa baya yayi amma be tafi ba, so yakeyi ya tabbatar da gaske wancan gidan Yah Ahmad yake nufi sannan yana so yaga wacece. Fatima a gidan. Indai baya samu makuwar tunani ba wannan shine gidan daya zo shekaran jiya waccen gurin Afeeyah. Irin kallon daya yiwa gidan yasa ko a mafarki baya zaton ze kasa tantance shi balle a zahiri sedai idan kuma gizo idanuwansa sukeyi masa. Bayan fitilar Solar dake kafe a Ƙofar fidan wadda haskenta har tsakar gida yake haska musu da akwai wutar nepa dan haka gurin tarwai yake ta yanda ko abun mutum ne ya faɗi ze iya ganinsa.

Yana jingine jikin katangar daya lafe dan bazeyi gigin tsayuwa akan Ƙafafuwansa kaɗai ba, yaga sanda Ahmad ya saka waya a kunne da alamu ita ya kira kafin ya ajiye mintinu kamar huɗu tsakani ƙofar dake rufe ta buɗe cikin Ƙasa da sakanni biyar Fatima ta bayyana. Tarwai yake hango fuskarta daga inda yake tsaye wadda yake ganin zanen fuskar Afeeyarsa akanta. Irin Doguwar riga Omo blue da farin V hijab da Afeeyah ta tura masa da hotonsu ɗazun a matsayin kayan da zata masa kwalliya dasu ne a jikinta. Daga inda yake tsaya yana iya hango fuskarta da take kicin kicin babu ko ɗigon fara'a inda ta Ahmad ke washe kamar yaron daya tsinci haƙorin makkah.

Bazece ga lokacin daya ɗauka a gurin ba haka kuma baze iya wassafa tunanin da uake zarya a zuciyarsa ba Ƙafafunsa da sukayi sanyi har suka kusan kayar dashi a ƙasane suka ankarar dashi buƙatar ya bar gurin da yake. Tafiya kawai yakeyi bisa jagorancin Ƙafafuwansa ba tareda linzamin idanu ko zuciyarsa ba har Allah ya fitar dashi bakin titin lafiya. Yayi diri diri domin besan ina ze dosa ba. Daga cikin barandar da mutanen nan ke zaune ya hango wasu mutum biyu sun haɗa sahu suna sallah da alama makararrune, shidai baze ce ga yanda akayi ba ya tsinci kansa tsakiyarsu bayan daya saɓule takalmansa, mutanen sukayi raka'a biyu suka sallame Jay ya miƙe ya cigaba da sallah. Tun suna tsammanin ze sallame bayan rama raka'a biyu da be samu tare dasu ba a zatonsu sallar isha'i ce se gashi suna lissafa masa raka'a takwas a jere, ya tashi ze kai ta tara wani dattijo ya riƙe shi yana cewa

"Bawan Allah wace irin sallah ce wannan raka'a goma fa kayi tahiya ɗaya, ai ko sallar Asham ce ba haka akeyinta ba". Be ja ba ya sallame sallar be kuma tanka mutumin ba ya miƙe ya kwashi takalmansa a hannu ya tsallake titi ya tsaya ganin motar Ahmad ya saka ya tuna a mota suka zo harga muƙullin ma a aljihunsa seya zaro shi ya buɗe ya shiga mutanen nan dai suka bishi da idanunu baki harma da hanci wasu na cewa
"Da alamu kan ba ƙalau ba". Wani yace
"Gaskiya babu alamar hauka a tattare dashi idan dai aka ce damuwace ko firgici ya sakashi aikata hakan bazan musa ba"
"Shiko har wace kalar damuwa ko firgici ze sakashi jera raka'a goma har yana shirin ɗorawa ba dan an riƙe shi ba? Wai ba tare suke da yaron nan me zuwa gurin yar gidan Malam Hafizu ba? Su suka tsaya a waccen motar tare kuma suka tsallako yauwa ka gani ma gashi nan ya shiga motar ta yuwu wlh kara zube yake ba ilimin muhammadiyya kasan fa yayan masu kuɗin nan se a hankali da yawansu sallah kawai sukeyi amma basu san me suke yi ba" wani zgudujƙuri ya koro jawabin, oho Jay dai tuni ya bawa mota wuta yai reverse ya fice daga titin ba tare da sanin ina zashi ba.

A can ƙofar gidan Malam Hafizu kuwa bayan fitowar Fatima Ahmad ya kalleta cikin shauƙin So, Allah ne ya jarabce shi da ita dan haka masu ganin baikensa su dena. Fuska a washe kamar kullum yana kallonta bayan daya amsa gaisuwar data masa a daƙile kamar an mata dole yace
"Kinyi kyau" tace
"Uhm" tana wani sake tamke fuska shiko be dameshi ba, ya daÉ—e da sakawa a ransa Fatima tana cikin jerin mutane marasa yawan fara'a shiyasa haÉ—e fuskarta ya dena bashi haushi. Ya gyara tsayuwarsa yana ce mata

"Yasu Baffah da Umma?"
"Lafiya lau suke" ta bashi gajeriyar amaa tana duba wayarta, ya sake mata murmushi yana jingina da bango yace
"Da Sabuwar Fatiman nayi magana a waya kwanakin nan, ina ta zumuÉ—in nazo na tarar da ita se kuma naci sa'ar samun tsohuwar Sarauniya Fatima na nan tana cigaba da zuba mulkinta".

Tayi murmushin nan me kama da taɓe baki bata dai ce komai ba shi kuwa yace
"Tare muke da Jafar yau dai abokanan faÉ—a zasu ga junansu". Da sauri ta kalleshi jin sunan daya ambata tace
"Ashe ya dawo kenan?"
"Gobe satinsa É—aya da dawowa shima soyayyarsa ce ta azalzaloshi ya taho yanda kuma suke buga wasan da zafi ina tsoron karfa suyi mana over taking" ya bata amsa yana kallon fuskarta kamar yanda itama take kallonsa, ta wani yamutsa baki kafin tace
"Allah sarki"
"Dan Allah idan yazo kar kiyi abinda ze sa ku raba hali, gaisawa kawai zakuyi ku maida komai daya wuce ba komai ba already na masa magana nasan shidai baze fara takalarki ba" Ahmad ya faÉ—a cikin sigar lallashi.

Ta harareshi a fakaice kafin tace
"Wato nice ma zan takale shi na janyo abinda zamu raba hali? Kuma da zaka ce abinda ya wuce ya wuce harda zagin mun uba kana zaton yaci banza kenan? Ni bazan iya pretending naso mutumin daya rigada ya furta da bakinsa baya Ƙaunata ba kaima kawai neman tada zaune tsayene ya saka ka taho dashi, ni wlh dana san shine baƙon da kake nufin zaku zo tare bazan ma jiraka ba tafiyata zanyi dan inada abu me muhimmanci a gabana na aje na zauna jiranka" ta Ƙarasa tana sakin ƙaramin tsaki.

Ƙarara fuskarsa ta nuna rashin jin abinda abinda ta faɗa ta gani kuma amma ta ɗauke kai tana cigaba da duba Keypad wayar hannunta tana kallon lokaci kafin ta sake duban hanyar tahowa a ranta tana addu'ar Allah yasa ma yaji haushi ya tafi kafin ya dama mata salalan tsiya.

Ahmad kuwa haka ya haÉ—iye abinda ya taso masa cikin sanyi ya kalli wayar da take ta juyawa a hannunta yace
"Meya samu wayarki na ganki da wannan?"
"Babu komai chaji ne babu na cire Sim É—in" ta bashi amsa ba tareda ta kalle shi ba seya zaro wayarsa daga aljihu ya nuna mata yana cewa
"Ya kamata ma a canza ta tunda anyi lunching sabuwa tuntuni, IPhone É—in kike so ko kina son Samsung irin wannan last week nima na canzata?"

"Waccen ma ta isheni na gode base ka wahalar da kanka ba" ta bashi amsa cikin yanayin irin kamar ya dameta, ya maida wayarsa yana cewa
"Wahala kike kira akan abinda ya shafeki? Idan ban hidimta miki ba neman da nakeyi bashi da amfani kenan. Nifa a rayuwata inajin daÉ—i kawai na kyautatawa mutum koda baze gode mun ba"

Lafazinsa na ƙarshe se taji kamar magana ya faɗa mata ta sake cukulewa bata ce komai ba. Ya waiwaya ya kalli hanya kafin ya ciro wayarsa ya shiga kiran Jay ganin kusan minti nawa shiru babu shi babu labarinsa. A lokacin Jay nata sharara gudu a titi beji kiran ba, sau biyu ya kirashi be amsa ba ya haƙura ya kalleta ganin tana dafe kai ya saka cikin kulawa yace mata
"Ya dai, meya faru kike riƙe kai?"
"Ciwo yakeyi mun yanzu ina tsayen nan naji ya sara" ta bashi amsa tana yatsina kamar gaske nan nan kuwa yace
"Ciwo kuma har yanzu be dena ba amma kika cemun kin warke kin sha magani?"

"Nasha kuma ya dena yanzu ne kawai ya dawo kodan na daɗe a tsaye ne ban sani ba" ta faɗa tana wani sake riƙe kan da hannu biyu. Burinta ya cika dan kuwa sannu ya shiga jero mata yana cewa ko zasuje Asibiti, tace
"Nafa gaya maka an bani magani daman Dr yace na dena yawan tsayuwa da shiga haske sosai su suke tayar mun da ciwon". Ya kalleta kamar me tantamar abinda ta faÉ—a amma yace

"Shikenan ki shiga ciki, bari na sake trying number Jafar idan yazo se ki leƙo ku gaisa ko yayane dan Allah kinga babu daɗi ace yazo kuma baku haɗu ba"
"Tam" ta bashi amsa tana ƙoƙarin juyawa ciki Baffa ya iso gurin, yanda kasan wanda yaga wani da suke wasa ɓuya haka ya sauke ido ƙasa ya kasa kallon Ahmad shi kuma cikin girmamaqar daya saba yi masa ya durƙusa ya shiga gaishe shi ya wuce ciki ya barsu a tsaye.

"Kinga yau kuma Baffah surukuta yakeyi dani daga fara maganar auranmu dukda ma yace a bashi sati huɗu zeyi musu magana" Ahmad ya faɗa bayan da Baffah ya shige ciki, batace masa kamai ba se dafe dafenkai da yamutsar data cigaba da yi hakan ya tuna masa da ciwon da tace yana mata yace ta shiga gida ta wuce har sannan dafe da kai yana binta da sannu. Seda ta shige kafin ya sake ciro waya ya shiga kiran Jay a sannan kuma aka ce masa Call waiting tana dab da tsinkewa ya ɗaga muryarsa tamkar wanda yake maye ko cikin wani shauƙi yace
"I'm sorry Yah Ahmad kuka ta saka mun ni kuma banma san yanda akayi ba kawai na ganni a ƙofar gidansu".

Ahmad ya buÉ—e baki kamar yana gabansa yace
"Tafiya kayi, kuma kake cemun baka san yanda akayi ka ganka a gidansu ba ko saboda ka raina wayo ai shikenan ita kuma motar tana ina toh?"
"I'm coming back to pick you" Jay ya sake faÉ—a da muryar da tafi ta farko zama wata iri, Ahmad yace
"Zan hau Napep, and abinda zance maka kaji tsoron Allah kabar koma menene kake aikatawa a inda kake"
"Thanks" Jay ya amsa shi kafin ya katse wayar ya bar Ahmad da waya a kunne cikin mamaki. Wato saurin da yakeyi kenan so yake yaje ya taɓa yar mutane, kenan Jafar be bar halayyarsa ba har akan macen da yake iƙirarin yana so ze aureta seya gwada mummunar ɗabi'arsa kenan? Tunanin daya ringa masa yawo akai.

Ya aje wayar cikin rashin jin daɗin abin ga ciwon kan daya tasowa Fatima a gefe duk suka dagula masa lissafi suka kore farin cikin daya ke ciki a daren. Titi ya fita ya tare Adaidaita da ze kaishi gida, da ace yasan gidan su Budurwar Jafar ɗin can zeje da ace kuma ya san abinda zeje aikatawa kenan da be barshi ya tafi shi kaɗai ba, dole ma ya kaiwa Baba Alƙali ƙarar Jay akan ire iren abubuwan nan da yake aikatawa, idan aure yake so yayi kawai Ƙila ya shiga hankalinsa ya dena wannan shirmen.

A ɓangaren Jay kuwa tafiya ya ringayi a motar ba tareda yasan inda ya nufa ba, seda yayi tafiya me nisa ya bi titin bypass kamar me shirin tafiya Bechi a daren seda ya wuce guraren cunkoson mutane kafin ya samu gefen titi ya gangara ya tsaya ba tareda ya kashe motar ba yayi parking kawai ya kwantar da kansa akan steery. Ya kasa relating abu, Fatiman Yah Ahmad itace Afeeyarsa, Afeeyarsa ita ce Fatiman Yah Ahmad a garin yaya? Ya akayi haka ta faru? Tunani ya shigayi na haɗuwarsa da Afeeyah har zuwa yau, babu wata kafa ko siga da zata saka ya zargi wani abu akanta, babu abinda be sani akanta ba amma koda wasa zuciyarsa bata taɓa kwatanta cewar zata iya zama ita ce Fatiman Yah Ahmad ba, abinda yake so ya fahimta yanzu shin Coincidence ne ko kuma Set up plan?

Arashine ko ita ta shirya komai ta haɗa soyayyarsa data Ɗan uwansa mafi soyuwa a gareshi guri ɗaya? Idan shiri ne menene ribarta akanyin haka? Me suka mata data zaɓi hukunta zukatansu da hukunci mafi muni irin wannan?
Yana buƙatar sanin amsar waɗannan tambayoyin kafin sanin abin da zeyi a gaba.

Wani abu yakeji a zuciyarsa, ya zarce ya ce zafi yakeji ko ciwo koma menene besan me ze kirashi ba. Ta yaya za'ayi suyi tarayya cikin Son abu ɗaya shida Yah Ahmad? Tilas wannan ya kasan ce shiri dukda ya sani Allah babu yanda baya sanya Al'amura su kasance amma yana da yaƙinin ubangiji baze tagayyara zumunchin da yake tsakaninsa da Yah Ahmad.

Ya saka hannun akan fuskarsa yana goge danshin dayaji yana bin kuncinsa, shi kansa yayi mamakin kansa Hawaye ne wanda fitarsa ke cakuɗe da dalilai da yawa, Allah ya sani be taɓa jin son wata Mace a duniya irin yanda yakeji akan yarinyar nan ba, zuwansa Kaduna gurin Anty Ummu Yayar Hajiya Binta yaje saboda a kaf dangin mahaifiyarsa ita kaɗaice yake da tabbacin zata iya tarar gaban Hajiyar ta feɗe mata gaskiya komai ɗacinta kuma itace yake da yaƙinin zata bashi goyon baya akan auran Afeeyah. Hajiya Ummu ta goyi bayansa dukda ta jinjina Al'amarin domin burin Hajiya sananne ne ga kowa akan sa. Kowa yasan tanadin da take dashi akan Matar auransa. Ita kanta Hajiya Ummun yarta Samiha ta soshi kuma da ace yana da ra'ayin auran Zumunchi daya auri Samiha kodan Anty Ummun amma haka Hajiya ta shafawa idonta kwalli ta manta cewar Ummu ce ta saki Nono ta kama a gaban kowa tace me uban Samiha yake dashi da zata haɗa surukuta da yarsa?

Abinda Anty Ummu ta fara masa bayan daya mata bayanin komai tace "Allah ne ya kama Binta, burin data ci akanka baze zamo gaskiya ba, kanaji ko Jafar idan har kana son wannan yarinyar kar kaji komai kar kuma wani abu ya baka tsoro ka tafi kanka tsaye ka nemi auranta. Karka bi takan Binta ko Mahaifinku domin bakin ganga ne se yanda ta kaɗashi ka tafi kai tsaye ka samu Alƙali nasan in sha Allahu zeyiwa duk wata ɓaraka da ka iya tasowa togaciya tunda wuri, kuskuren da Ahmad yayi kenan amma tunda Alƙali ya karɓi maganar wa ka sake jin yace wani abu akai?"

"Amma Mama Ina tsoron Abinda Hajiya zata yi idan taji maganar nan daga baya shiyasa nake tunanin ki fara sanar mata a lallaɓata harta amince da kanta sannan" Jay ya faɗa, Hajiya Ummu tace
"Jafar kenan, shawara dai kake nema a gurin kuma na baka, wlh tallahi badai Bintar dana sani ce zata amince da maganar nan da kazo da ita ba, tunda dai ba abune daya saɓawa shari'a kake shirin aikatawa ba magana ce ta aure, idan kuma daman ba son yarinyar kakeyi ba to kaitsaye ka janye kawai karma ka janyo wani abin kace nace ka jawowa yarinya suna zaune lafiya da iyayenta Jarabar Binta ta dirar musu, kaje ka samu Alƙali shi ze san duk ta yanda ze biyowa abun" Abinda Hajiya Ummu ta gaya masa kenan, Daya sake nuna mata hoton Afeeyah data buƙata bayan ta gani tace masa

"Niko kamar nasan fuskar nan a wani guri" a lokacin yace mata
"Nafa tura miki hotonta kwanaki can Mama" ya faÉ—a seta jijjiga kai tace
"Tabbas na tuna, gata tabarakalla, Allah yasa yanda take da kyaun fuska haka zuciyarta take" nana suka Ƙarƙare daita bayan ta sake jaddada masa yaje ya samu Baba Alƙali kaitsaye kar yabi ta kan Hajiyarsu, daga can ya wuce Abuja gidan Hafsatu kashe tata wutar, maganganun data zayyana masa na kalar zaman da takeyi da Abban se yaji ashe ko rabi Hajiya bata sani ba, ta bashi tausayi matuƙa duk son zuciyar Hajiya nata suka ja mata, samarin Arziƙi tayi su amma ita da uwarta suka raina musu Ajawali, shi shafaffe da mai da yayi daidai da ra'ayinsu gashi nan tun ba'aje ko ina ba tana kuka da data sanin auransa, gara Hajiya raba baƙin cikin akeyi da ita, ita da take zaune dashi take kwasar kashinta a hannu ita take da abin faɗa. Daya tariyo gidan Naziru, da matarsa ta rufin asiri gashi nan ya tattago matar Jaraba irin wadda Hajiyar take so shi kuma tana gasa masa Aya a hannu, Yakubu ma dai sammakal wata yar gidan da Tarbiyya bata wadata ba ya kwaso yar masu kuɗi yan boko ranar nan yana ji suka kwaso rigima wai bata iya sallah ba daga ya mata magana yace a gidan ba'a sakata Islamiyyah ba ta kira Babanta tana kuka tace ya zage shi tas yace musu kafirai uban yazo yayi tijara a tsakar gidan Alhaji Audu akayi sa'a dai baya nan Hajiyar ce ta fita tana bashi haƙuri duk suna ɗaki suka ƙi fita to irin auran da take so yayi shima kenan.

Bayan ya dawo ya ciza ya busa yaga dai shawarar Hajiya Ummu wadda kuma daman usulun abinda zuciyarsa ta ayyana masa kenan a matsayin mafita tilas ya aiwatar da hakan shine yaje ya samu Baba Alƙali ɗazun ya zayyane masa komai yace kuma ya kwantar da hankaliynsa ya tambayeshi ina ne gidansu yarinyar yace zeje yau ya karɓo full Address da sunan Mahaifinta akan haka suka rabu. Dalilinsa na ɓoyewa Ahmad komai akanta kuma kawai yana jin nauyin abubuwan daya masa akan Fatima, irin izgilancin daya masa na cewar ya rasa Macen da zeso a duniya se yar bakanike, duk matan da suke sonsa isassu bega matar aure ba se ita abin haushin ma tana wahalar dashi se gashi shima ya Ƙare da faɗawa tarkon yar Talaka liƙis da yake ganin kamar ma Mahaifin Fatiman Yah Ahmad ɗin zefi nata wadata, wannan tasa ya yanke hukuncin su tafi tare, yaga komai da idonsa idan yaso daga baya su tattauna domin yasan Yah Ahmad bazeyi judging nasa ba kamar yanda shi ya masa

Ashe shine babban gara a cikin wasan, shi yar bakanike ta ɗanawa mugun tarko ta kamashi kuma yanda ya kamata tayi wasa da hankalinsa. Abubuwa da yawa ne cikin al'amarin, ze tabbatar da Allah ne ya kama Hajiyarsa dashi kansa dumu dumu, rainin arziƙin da yayi musu ubangiji ya tabbatar masa da ba nan take ba, ba rashin wayon Ahmad bane ya saka soyayyarta tayi galaba akansa haka duk izza da jiji da kansa gashi nan ta haushi ta tattakeshi son ranta sannan Tozarcin da Hajiyarsa ta so yiwa Ahmad ne yayi waiwayi ya diro akansa, ina zata tsoma ranta da wannan abin kunyar idan taji labarin yar bakaniken data rainawa Ajawali tayi wasa da Zuciya da Ƙwaƙwalwar Jay da take ganin kaf zuri'ar Audu Bechi babu yashi?.

Daga can gefe gaba kaÉ—an da inda Jay yayi parking Matasa guda uku suna zaune akan Benci suna cin gyaÉ—a. Gida daga cikinsu yace
"Waccen motar tafi minti Ashirin a tsaye anan kuma a kunne", na kusa dashi ya keɓe baki kamar wata mace yace
"Kai da ganin motar ai kasan lalatattun Yayan masu kuÉ—in nan ne baze wuce budurwa ya É—akko yazo nan yana lalubeta ba, yar iskar saboda ma bata da daraja a gunsa baze iya kama mata hotel ba a mota ze latse ta" yanda yake maganar seka rantse da Allah a idonsa yaga ana abinda yake faÉ—ar, na farko daya fara magana ya cafe yana cewa

"Kuma fa haka ne, wlh yanzu haka shegun suke daman indai kaga mota da dare me baƙin gilashi an zuge shi tsaf kuma motar a kunne to wlh Iskanci sukeyi".

Na ƙarshen da tunda suka fara maganar saka musu baki ba se sannan yace
"Haba Lawan, me yasa ba zaku kyautatawa mutane zato ba? Yanzu idan ranar lahira aka tsayar dakai ta yaya zaka kare kanka akan wannan shaidar daka bayar tamkar ya faru a gabanka? Me yasa a koda yaushe zuciyoyinku suke hasaso sharri a maimakon Alkhairi a kusa? Ba ku tunanin lalura ce ta tsayar da me motar nan? Ta yuwu kiran waya ne ya shigo masa shiyasa ya tsaya dan ya amsa domin yafi Alkhairi akan ya ringa tuƙi yana amsa waya.." Wanda ya kira da Lawan ya katse shi yana cewa

"Ji wannan Bashir É—in wace irin wayace sama da minti ashirin kuma ya bar mota a kunne se kace a gidansu ake siyar da mai?"

"Kai kuma me wannan motar ne zaka yi tunanin mai ze zama matsalarsa kalleta fa ni banma san sunanta ba" Wanda ya fara takalo maganar ya bashi amsa, Bashir yayi murmushi yace

"To sa ace ba waya yakeyi ba idan kuma lalurace fa wani abu ne ya same shi a cikin motar?"

"Kamar yaya?" Lawan da Idris suka haÉ—a baki gurin tambayarsa, Bashir yace
"Kwanaki naji labarin wata mata kamar haka tana tafiya a mota ta gangara gefen titi ta tsaya tun mutane basu damu da tsayuwarta ba har dai suka fara tunanin wani abu ana duba motar aka tarar ashe Allah ya mata rasuwa tana kwance kan sitiyari" Lawan ya zabura ya tashi hannu akai yana cewa

"Innalillahi muje mu duba kar gobe mu zama mu zamu bada labarin a radio" ya durfafi motar Jay Idris na take masa baya sannan Bashir. Sau biyu suka Ƙwanƙwasa masa glass, seda ya goge fuskarsa da Tissue idanunsa sun kaɗa sunyi jajir kafin ya zuge glass ɗin gefen da yake gaba ɗaya ta yanda suna iya hangen gefensa zuwa bayan motar. Bashir ya masa sallama kafin yace
"Afuwan ranka ya daÉ—e munga kana tsaye ne tun É—azu shine mukayi zaton ko ba lafiya ba"

Murmushi Jay yayi yace
"Lafiya lau, nagode da kulawa"
"Kai wannan ai Jay ne" Idris ya faɗa cikin ƙaraji tuni kuma Jay yaja motarsa ya bar gurin Idris da Lawan suka haukace suna cizon yatsa, Jay ne a gurin sama da minti ashirin amma basu sani ba
"Kai amma fa naga idonsa sunyi Jaa, kodai shaye shaye yake a motar?" Lawan da be daddaraba ya sake faÉ—a.

Ahmad ya kasa zaune ya kasa tsaye a bakin Gate yana jiran dawowar Jay, baze barshi ba yau se ya masa kaca kaca , yana nan zaune bayan ya kira Fatima tace masa kan da sauƙi sega motar da suka fita da ita ta kunno kai, yanda yake tuƙi ya sake fusata Ahmad dan da gudu ya shiga gidan tamkar me wasan mota. Jay be lura da Ahmad ba dan haka yana kashe motar ya fito yana rangaji ya nufi bangarensu, a daidai barander Alhaji Audu juwa ta kwasheshi kamar wanda iska ta buge se ganinsa sukayi yif ya faɗi a ƙasa Ahmad daya taho a fusace se gashi yayi kansa da gudu cikin tashin hankali, kardai kuma shaye shayen Jay ya fara be sani ba? Tambayar da yakeyiwa kansa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.