Complete Hausa Novels

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 11

PAGE 19
FATIMA
Duk irin ɗaure fuskar da Umma take mata tareda maganganu be saka taji ko ɗar a zuciyarta dangane da zaɓinta ba musamman da ta samu lako lako a gurin Baffa, shine me bayar da auranta tasan kuma bazeyi mata dole ba. Idan gidan ya isheta ta gaji da faɗan Umma sta tattara ta tafi gidan Anty Sauda can idan ta nemi ta takura mata da zancen Ahmad buɗe baki take ta mayar mata da martani saɓanin Umma da sedai ta sunkuyar da kai tayi hawaye.

"Dan Allah ku barni na auri abinda nake so, yanzu da dole aka miki zaki samu wannan walwakar da kik ciki harki ringa ƙiba kina walwali? Ni ban taɓa cewa ina son Ahmad da aure ba ko shima yasanda haka, to akan me kuma za'a kafa mun ƙahon zuƙa dan nace ga wanda nake so yanzu?" Ta faɗa tana turawa Anty Sauda dake mata mitar zancen Ahmad ƙeya.

"Ai shikenan daman mu yan mu baki shawara ne kamar yanda kika ce kece me zaman auren ba wani ba, amma ki sani hausawa sukace Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, ko Ahmad kika aura na tabbatar se kin haɗa da haƙuri da ɗauke kai saboda matashine da uwar kuɗinsa a hannunsa abinda kika raina ɗin wasu na can suna haƙilon yanda zasuyi su same shi balle kuma kuma wannan da kike So ai wlh faɗuwar gaba da tunanin ina yake su waye tare dashi kaɗai ya isheki, baki kuma isa kice zaki raba shi da mata ba dan dasu kika ganshi. Mutumin dake karakaina cikin masu jajayen kunnuwa Mata masu kyau ba irin wacce be gani ba, Allah kaɗai yasan nawa yake tare dasu a yanzu dan ko be nemi Mace ba su zasu kai masa kansu, to dan Allah meye ribar auran soyayyar da zuciyarka kullum zata zama a tsaye? Ai wlh ka auri Mijin da son sa yafi naka shine ka morewa aure, koda kika ce ina ƙiba saboda Mijina na so na ne, ina juyashi son raina idan nace ina son abu jiki na rawa zeyi mun in ko nace bana so haka ze bari wannan shine burin kowacce me hankali data san me takeyi ba irinki ba da kike nemarwa kanki Jafa'i Mijin da ze ringa ɗaure miki fuska yana fafara miki tsawa" Anty Sauda take sababi.

Afeeyah tace "nawa zaɓin kenan, se a tayani da addu'a yanda akeyiwa kowa". Saboda takaici Anty Sauda bata sake ce mata komai ba, daman wai taje ne ta sanar mata Jay ya ɗaga ranar zuwansa. Ita saboda yanda abin yake ɓata mata rai ko Mijinta bata gayawa shegantakar da Afeeyar tazo da ita ba, randa ya tsinci tana mata faɗa ne tayi briefing nasa akan wani ta samo kuma wai yanzu ba Ahmad ba, dake ya iya ɗaurewa ƙarya ƙugu shima yace wai a bita a hankali, Aure da mutuwa babu me tsara su tafe suke da lokacinsu da kuma wanda zasu riska babu kuma wansa ya isa ya canza haka.

A ranar bayan Afeeyah ta koma gida da daddare Baffah ya kirata, suna zaune a Baranda saboda garin akwai zafi kuma babu wutar Nepa har Umma tayi masa shimfiÉ—a a gurin da yace indai ba an maido wuta ba ko kuma ruwan sama ya sauka a nan ze kwana. Ita kanta zafin ya addabeta amma dole ta zauna a É—aki saboda gujewa maganganun Umma ga Yah Malam ya koma makaranta sun fara Final Exam daman dayana nan ne take samun yancin zaman tsakar gida ko Baffah baya nan tunda yana tare mata faÉ—an da Umma ta ara ta yafa ya zama halinta yanzu dukda dai shima bawai ya goyi bayan abinda take so tayi bane dan abinda ya gaya mata shima É—in dai kamar sauran ne

"Indai nagarta kike nema a aure to tana gurin Ahmad, idan kuma soyayya da ƙyaleƙyalen rayuwa ce ki auri Jay kuma na tabbatar duk abinda kike hasashen samunsa a gurinsa idan kin bawa Ahmad dama se yayi miki fiye da haka".

Ta isa gaban Baffa tana sunkuyar da kai daga gefe ta tsugunna dan tana hangen hararar da Umma ke aika mata ta hasken farin wata da fitilar data kunna musu a tsakar gidan.

"Mamana na kiraki ne saboda ina so na ji abinda yake a ranki, dukda kwanaki munyi magana amma yanzu ina so ki sake faÉ—amun gaskiyar abinda kikeji game da Ahmad" Baffa ya faÉ—a yana gyara zama. Ta kalli Umma ta sunkuyar da kai, Baffah yace
"Ruƙayya ɗan bamu guri mana"
"Aiko ina nan Malam bazan shiga cikin zafi saboda maganarku ba" Umma ta bashi amsa, yayi murmushi yace
"To ki dena kallonta kar shakkarki tasa ta faÉ—i ba abinda yake cikin zuciyarta ba"
"Uhm" kawai Umma tace ta juya kai. Seda ya sake maimaitawa Fatima tambayar kafin cikin rawar murya tace

"Tsakani da Allah ni Baffah ina kallon Ahmad ne kawai a matsayin Yaya, tsayin lokacin nan nayi masa hannunka me sanda saboda kirkinsa ya wuce na buÉ—e baki nace masa bana sonsa, shi da kansa ya sani tunda yana faÉ—ar haka..."

"Tambayarki kawai nayi me kikeji game dashi a zuciyarki ba wai dogon bayani ba" Baffah ya katseta. Ta duƙar da kai cikin ƙaramin sauti tace
"Banajin komai game dashi Baffah"
"Bakya sonsa so irin na aure kenan?" Baffah ya tambayeta yana tsareta da ido kanta na ƙasa amma taji tasirunsu a jikinta, zuciyarta taki ta tsinke hawaye ya taho mata, daga can ƙasan ranta tana jin tamkar tamkar bata kyauta ba, to amma ya zatayi da muradin tata zuciyar? Idan ta haƙura ta karɓi Ahmad tasan dashi da ita zasu ƙare rayuwarsu ne cikin ƙunci saɓanin haka gara tayi musu gata kowa ya nemi rayuwar da zata dace da muradinsa.

"Banajin sonsa a zuciyata Baffah" ta faɗa cikin rawar murya kafin kuka ya ƙwace mata. Umma ta saki ƙwafa tace
"Munafuka, ai bakiyi kuka ba tukunna, ranar kuka tana tafe"
"Haba Ruƙayya, wannan wace irin magana ce haka? Ya zaki ce mata ranar kuka tana tafe baki fa kikeyi mata?"

"To Malam ina kukan daɗi takeyi yanzu ta yaudari bawan Allah ta ɓata masa lokaci shekara uku yana hidima damu da ita sannan rana tsaka tazo tace bata sonsa wani can daban take so? Ai wlh ko ban faɗa ba haƙƙin Ahmad seya bibiyeta, akan me bata sonsa tsayin lokacin nan bata fito ta faɗa ba? Idan da shegiyar ƙaryarta tace nauyinsa takeji mu ta faɗa mana kota faɗawa yan uwanta ko ƙawayenta mana? Ba zata aureshi ba shekara uku ta barshi yana mana bauta har idan ka hana ya zagaye yaje ya kai mata makaranta ta karɓe suturu da manyan wayar da take riƙewa da ya ruɗo mata wanda take Ƙulafucin Son duk waya ke yi mata su ba Ahmad ɗin bane? Sannan yanzu tazo tace bata sonsa to nidai babu hannuna a ciki ba za'ayi wannan abin kunyar dani ba wlh kuma tunda biye mata zakayi kuje can ku ƙarata Allah ya taimaka" Umma ta tattari kayanta ta shige ɗakin da tace da bazata shiga ba saboda zafi.

Afeeyah na durƙushe gaban Baffah tana kuka kamar ranta ze fita, yayi shiru ya rasa abin faɗi. A sanyaye yace mata
"Kiyi shiru ki saurareni". Ta tsagaita da kukan amma ba gaba É—aya ba. Baffa yace

"A matsayina na Mahaifinki ina da ikon da zanyi miki zaɓin Mijin aure na kuma tursasaki koda bakya so domin Addini ne ya bani damar hakan se dai kuma kema a matsayinki na Ya ba baiwa ba kina da damar da ki kawo naki zaɓin idan har beci karo da Addini ko shari'a ba za'a barki dashi. Auren dole bashi da fa'ida Fatima, yanda na baiwa yar uwarki dama ta kawo zaɓin aurenta kema na baki. Nayi tsammanin lokacin da kika ɗauka tareda Ahmad alamune na cewar kun Aminta da juna, Karatunki da kike da ƙulafuci a tsammatata shine abinda yasa kuka tsahirta tado da zancen aure har se zuwa kin gama.

Baki taɓa nuna wata alama ko faɗi da baki cewar bakya sonsa ba dukda Mahaifiyarku da Yayarki suna yawan kawo mun ƙorafin yanda kike mu'amalantarsa basa jin daɗin hakan, nakanyi miki uzurin yanayin halayyarki ta kasancewarki mutum mara sakewa da mutane sosai ban taɓa tsammatar rashin So ko gamsuwa dashi ne yasa kikeyin hakan ba me yasa kikayi ƙwaron baki ki barshi tsayin wannan lokacin se yanzu da Aski yazo gaban goshi zakice kin fasa baki ganin hakana matsayin cutarwa?" Baffah ya ƙarasa yana tsareta da ido.

Taja hanci, fuskar nan har tayi Jaa kafin tace
"Wlh Baffah nauyi da kunyarsa nakeji shi yasa na kasa faÉ—a masa da baki amma na nuna masa duk wata alama data kamata ace ya gane"

"Da kika ga alamar be gane ba, ko kuma ya gane amma ya cigaba da dagewa domin ya gwada sa'arsa tunda har kika tabbatar bakya ra'ayinsa seki cire wani nauyi ko kunya a gefe ki sanar masa ko ki sanarwa wani ya gaya masa" Baffah ya faÉ—a a É—an fusace. Ta sake rushewa da kuka yayi tsaki yace

"Yanzu da wace fuska kike so na kalli yaron nan? Ni kike so na gaya masa bakyason sa kenan ko wa?"

"Ni Baffah.. Ni wlh ban..." Ta shiga in ina tana kuka ta kasa haÉ—a maganar. Baffah ya ajiye numfashi, gaba É—aya ta jefashi a tsaka mai wuya ya rasa abinda zeyi seya nisa yace mata

"Shi wanda kike so É—in wanene? Kuma É—an gidan wanene?"
"Sunansa Jafar, Ɗan ƙwallo ne, Mahaifansa duka yan Kano ne amma shi a Turai yake can yake sana'arsa" ta bashi amsa cikin sauri ya kalleta kafin ya sake tambayar s ina suka haɗu nan ma ta gaya masa. Yayi shiru na tsayin lokaci, zuciyarta ta shiga tsinkewa dalilin shirun nasa. Shidai shine me bayar da auranta, idan be amince da wannan batu ba to fa ko zata mutu tilas ta haƙura da Jafar.

Ba kalar Addu'ar da batayi a zuciyarta ba a lokacin can Baffah ya nisa yace
"Ahmad yaron kirki ne Afeeyah, babu uban da zeso ya rasa nagartaccen siriki irinsa" batasan sanda santsin bakinta ya jata tace masa
"Wlh shima Jafar É—in yanada nagarta dan baka sanshi bane" takaici ya saka Baffah yin murmushi kafin yace
"Ki gaya masa yazo ina son ganinsa gobe".

Cikin tsananin murna da zumuÉ—in hango nasara muraran tace
"Bayanan Baffah, ranar Lahadin nan ze dawo kuma daman yace da ya dawo zezo ya gaisheku".

"Fatima!" Baffah ya ambaci Asalin sunanta da kakkausar murya, murnar data fara ta datse, tsoro da fargaba suka maye gurbinta dalilin tun tashinta ba zata ce ga rana É—aya da Baffah ya kirata da Fatima ba kuma da kakkausan sauti irin wannan. Baffan yaci gaba da magana cikin muryar gargaÉ—i da nuna tabbacin abinda yake magana akai.

"Ranar Lahadi kikace ze dawo ƙasar nan, tsakanin Lahadi zuwa Juma'a ki tabbatar ki fitar da ranar daze zo ni dashi mu gana. Ba zan tursasaki ki auri abinda bashi ne muradin zuciyarki ba, zan binciki ko wanene wanda kike so ɗin amma ki sani muddin naci karo da wani abu dangane dashi da beyi mun ba ba zan sake zama dake ko neman shawararki ba, Ahmad shine zaɓin da zuciyata ta aminta dashi kuma shi zanaura miki".

Kwana tayi tana juyayin maganar Baffah a zuciyarta. Tana jiyo sababin da Umma ta ringayi bayan tashinta daga gurinsa tana tambayarsa kenan ya goya mata baya? Me ze cewa Ahmad?
"Na sani Ahmad yaro ne hankali da nutsuwa, shi rabon aure dana haihuwa basa canzuwa, wani baya auranmatar wani kamar yanda hausawa sukace MATAR MUTUM Kabarinsa, hikimar zancen shine ba'a binne wani mutum cikin kabarin wani kamar yanda wani baze zarga igiyar auransa kan macen dake ɗauke da igiyoyin wani kafin shi ba. Muyi mata addu'a, wannan gaɓar itace gaɓa mafi muhimmanci a rayuwar Mace, idan tayi dacen abokin zama na gari rayuwarta ta inganta haka zalika idan akayi rashin dace rayuwa ta shiga wani hali ina roƙonki da ki tattare duk wani fushi naki ki ajiye shi a gefe kiyi mata addu'a itace abinda tafi buƙata yanzu dama da zagi da hantarar da kikeyi mata.

Tun a daren ta sanar da Jay,
"Wannan shine first Agenda na, neman auranki is number one on my to do list dana sauka a Nigeria, ina fatan Allah yasa nayiwa Baffanki, karyace baze bawa mutum irina auranki ba kinsan fa akwai mutane da yawa da suka ce Ball ba sana'a bace ba, da akwai Friend ɗina da aka hana aure Baban yarinyar da yake so yace bashida sa'a and haka ya haƙura ya auri wata" inji Jay daga nan suka cigaba da shirye shiryen yanda abubuwa zasu kasance musu.

Da sukayi waya da Badar ma ta gaya mata abinda Baffa yace,
"Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi Afeeyah" Badar ta faɗata amsa mata da cewar
"Amin idan da gaske kikeyi"
"Uhm Afeeyah kenan, a bazanji tsoronki in fasa cewa mi dai nafi sonki da Ahmad ba kuma ko Baffan har ransa yafi son Ahmad kawai ya baki damarki ne kuma da kina da tunani seki haƙura kawai ki bi abinda yake so" Badar ta sake faɗi ƙit kuwa ta kashe wayarta dan bata son abinda ze canza mata mood ɗinta na farin cikin dawowar Jay.

A gidan Anty Sauda ta shirya tarbarsa, ya sanar mata ya sauka Kano da ranar Litinin zuwa Yamma zeje ya ganta dan baze iya sake kwana guda a Naija ba tare da yaga fuskarta ba. Tsabar takaicin rawar jikin da takeyi Anty Sauda ficewa tayi daga gidan ta barta da masu aiki suna tayata, sanda ta dawo kuwa gani tayi kamar an canza gidan, tana tsammanin har bango Afeeyah ta wanke mata yau ko ina yayi haske ga ƙamshi kamar gidan sabuwar Amaryar Kanuri.

Tana idar da Sallar La'asar ta zauna kwalliya dukda ba wani shafe shafe tayi ba powder ce kawai ta lailaye fuskarta da ita se kwalli ta taje gira ta shaf Lip balm me maiƙo da ƙyalli kafin ta taje gashinta da taje tayi steaming tun jiya. Shi kaɗai ne abinda zata iya cewa be gama cika a halittarta ba. Gashi ta nada cika yana kuma da laushi sosai gashi baƙi tsayinsa ne dai da kaɗan ya wuce kafaɗarta ba kamar na Anty Sauda da Ummansu da yake ya wuce tsakiyar baya ba. Jay ya gaya mata yana son gashi, yana son mace me gashi, har hoton gashin nata ta tura masa abinda bata taɓayi ba, yace mata cikarsa yayi masa tsayin ma babu laifi tunda Natural ne idan ta saka Relaxer zefi haka sauka kuma ze taho mata da Mayukan gashi wanda zata gwada amfani dasu dan dagaske fa shi son gashi yake kamar me Iskokan gashi.

Ta gyara gashin tsaf ta ɗaure bayan ta shafa White gel kaɗan a gaban yanda ze sake kwanciya dukda daman a kwance yake kamar na jariri sabuwar haihuwa. Ta fesa body spray da body mist kafin ta saka Undies, kaya kala uku ta ajiye a kan Gado, ga Atamfa ga Lace ga Wata Chiffon gown ta rasa wanne zata zaɓa ƙarshe Salaha me aikin Anty Sauda tacewa ta tayata zaɓi.

"Ki saka wannan, Abaya na Matuƙar yi miki kyau" Salahar ta nuna Doguwar rigar Kanti. Ta sallameta ta ɗaga rigar tana dubata, wadda Ahmad ya kai mata ce zuwansa Zaria na ƙarshe kafin ranar daya maidota gida hutun First Semester. Se sannan ta tuna da rabonda suyi waya tun ranar da Baffah yace masa ya turo tambaya kusan sati uku kenan. Wani iri taji a ranta, ta saka rigar tayi mata kyau har ya zarce a misalta. Hula ta saka akanta kafi ta yafa medium plain veil daya dace da rigar shima Ahmad ne ya kawo mata ta shafa latest designer oil perfume na kamfanin Ahmad ƙamshin ya ratsata, bata taɓa amfani dashi na se yau.

Tayiwa kanta kyau balle kuma Jay ya ganta. Tana tsaka da jujjuyawa a gaban Mirror Anty Sauda ta shiga ɗakin, ga baƙonki can ya iso" ta faɗa tana kallonta.
"Nayi kyau" ta tambayeta, ta juya tana cewa
"Ban sani ba ina mudubi ne a gabanki ko idanunki basa gani ne da kyau?"
Ta rungume Anty Saudan ta baya kamar zatayi kuka tace
"Haba yar uwata rabin jikina wai har se yaushe zaku dena fushi dani? Na zata ku masu farin ciki da zaɓi nake tunda ba wani abu na kawo wanda ya take shari'a ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. Anty Sauda ta juya ta kalleta ganinhar idonta ya tara kwalla tace
"Karki ɓata kwalliyarki kinyi kyau kije anjima in ya tafi zamuyi magana ai yau zanga zaɓin naki".

Tamkar wahainiya haka take taku zuciyarta cike da tunani kala biyu, farin cikin ganin rabin ranta da kuma taraddadin yanda makomar soyayyarsu zata kasance yanzu da take kan siratsi. Tayi Sallama, yana zaune akan Three sitter a falon Mijin Anty Sauda, idanuwansa akan hanyar shigowa yanayin zamansa yafi kama dana wanda ya ƙosa da zaman jira dan har zamowa yayi kaɗan daga kan kujerar.

JAFAR
Toshe kunne kawai yayi yana sauraron hargagin Hajiyar daya zame masa jiki, daƙyar ta barshi ya fita sallar Azahar Masallaci ya gaisa da mutanen da sukayi cincirundo a ƙofar gidansu suna jiransa. Bega Ahmad a masallaci ba seya kirashi a waya yace masa ya fita duba wasu kaya da suka sauka ya huta da yamma idan ya dawo zasu haɗu.
"Bayan La'asar fa zanje gidansu Afeeyah dan Allah ka dawo da wuri" ya faÉ—awa Ahmad.
Daga can ɓangaren Ahmad yayi murmushi yace
"Na Afeeyah, to ka gaida mun da ƙanwata"
"Tare zamuje ai" Jafar ya bashi amsa da sauri Ahmad ya buÉ—e kamar yana gabansa yace
"Kawai goÉ—ai goÉ—ai dani sena rakaka zance? To ba dani za'ayi wannan abun kunyar ba".

"Haba Yah Ahmad idan baka rakani ba dawa zanje? You are my only bestfriend fa ka sani. Magana akeyita Jafar zeje hirar gaske bata yaudara ba" Jay ya faÉ—a yana marairaicewa. Ahmad ya yi datiya yana cewa
"Ashe dai kasan kai mayaudari ne"
"Ai na tuba, dan Allah ka dawo muje tare" ya sake pleading.
"I will come but on one condition, nima zaka rakani gidansu Fatima biko" Ahmad ya faÉ—a masa. Yayi shiru kafin yace
"Deal" ya faÉ—a ne kawai dan Ahmad ya rakashi nasa uzurin amma ba har zuciyarsa ba.

"Idan ka gama shiryawa ka kirani se mu haÉ—u a hanya saboda bana zaton zan gama abinda nakeyi da wuri na dawo gida ba, ka fito mun da hula" cewar Ahmad daga nan sukayi sallama take kuma ya kashe wayarsa gaba É—aya, shi kamsa baze ce ga dalilin daya sakashi kashe wayar ba, kawai baya jin daÉ—in komai kansa ciwo yake masa bama yajin daÉ—in jikinsa gaba É—ayasan kuma duk bayanin da zeyi masa ba saurara zeyi na gara yayi masa mita da daddare idan sun dawo wani lokacin idan ze koma ya rakashi.

Jay ya shirya tsaf ze tafi gurin Afeeyah. Wani Yadi ya saka Dark Ash ɗinkin half Jumper, plain ne yadin haka dinkin babu komai a jiki se links daya saka a hannu shi kansa daya kalli kansa murmushi ya saki. Ya daɗe be saka manyan kaya ba se yaga yau kwalliyar tasa hartafi ta kullum kamar wani sabon Ango in ba idonsa bane ma har ƙyallin goshi yaga yanayi. Ya kafa hula ya ɗaura Agogo sannan ya saka Takalmi. Signature Perfume ɗinsa ya saka wanda Yah Ahmad yakeyi masa, shi kaɗai yake amfani da turaren saboda yakai ya kawo ko suna ba'a yiwa turaren ba amma yanzu Ajay zeyi naming nasa. A safe locker Ahmad yaga wasu kwalabe masu kyau da ko be dubaba yasan Oil ne, ya ɗauki wanda kwalbarsa tafi burgeshi ya shanshana, Ƙamshi me sanyi da kwantar da hankali ya ziyarci hancinsa ya lumshe ido kafinya jefa kwalbar a Aljihu, namatane tunda ya ganshi a gurin kuma ya tabbatar waccen yarinyar da bata san darajarsu ba ze kaiwa gara ma ya bawa Afeeyarsa atleast ta isa tayi amfani da irinsa.

Motar da Ahmad ya zuba masa akwatin tsarabar Afeeyah ya fita da ita, Tinted glass ce motar dukda haka ya saka face mask da dark shades yayi badda kamar daya saba. Tun da safe ta tura masa da Address ɗin gidan sisternta, yasan Arean dan haka hankali kwance ya ringa tuƙi yana sake gwada number Ahmad da tunda ya fito daga wanka yake kira amma a kashe. Yaja tsaki sanda ya isa layin data rubuta masa a Address, Yaja da wani Aboki Asharb Bala a arean shiya kira, bayan gaishe gaishen yaushe gamo ya tambayeshi ko yana gida gashi a unguwarsu.

"Ina Kaduna Jay, can nake zama yanzu ai baka sani ba? Nasan dai ba takanas gurina kaje ba Wani abu kake nema a unguwar ko wani Address aka baka?" Asharb ya faɗa. Jay ya shafa kai kafin ya gaya masa wani gida yazo shine yake kiransa ya rakashi, daya faɗa masa number gidan kaitsaye ya directing nasa katangarsu ɗaya da gidan ta baya nan sukayi sallama da Alƙawarin zasu haɗu kafin ya koma. Yana faɗawa me gadin gidan sunansa ya buɗe masa Get dan an sanar masa za'ayi Baƙo. Bayan ya ajiye motarsa ya fito ya tsaya a fakaice yana ƙarewa gidan Kallon, gini me kyau na zamani daga gani me gidan Ɗan gayune daga yanda ya ƙalƙale ko ina da kwalliya ta zamani. Mu'az Babban Yaron Anty Sauda ya fito sanue da Jacee me sunan AJAY a jiki da Ball a hannunsa shi ya kira bayan ya gaisheshi yace ya shiga ya sanarwa da Afeeyah yazo yaron ya wuce ciki da gudu se gashi babu daɗewa ya dawo yace masa ya shiga ciki, seda ya rakashi har falon da akace ya kaishi kafin ya juya ze tafi.

"Ka sanni?" Jay ya faɗa, se yaron ya tsaya yana kallonsa, fuskarsa rufe da Face mask ta ina ze sanshi? Kamar Jay yasan tunanin da yakeyi ya zare Shade ɗin idonsa tareda face mask. Yaron ya buga tsalle kamar wanda aka baiwa abinda yafi so a rayuwarsa tsabar murna be san sanda ya faɗa jikin Jay ba yana kiran sunansa da ƙarfi.
"Shiiii, karka tara mutane mana" Jay ya kwaɓe shi, Mu'az ya riƙe bakinsa da hannu biyu yana dariya kamar sakarai dan ya kasa magana kafin kuma ya falla da gudu ya fice daga falon Jay ya rakasho da kallo yana murmushi.

Kacokam ya maida hankalinsa kan ƙofar da yake tunanin tanan ake shiga falon daga cikin gida. Tun kafin ta iso yaji a jikinsa tana tafe, ya zame daga kujerar da yake zaune hannaye da Ƙafafunsa har tsuko suke masa tsabar Zaƙuwar daya ganta se gata kuwa ta shigo falon, kallon da yake mata tamkar ze hango jijiyoyin da suke gudanar da jini a cikin jikinta. Idanunsa suka saka ta sake rage saurin tafiyarta kamar ma ƙafafun sun mata nauyi ne, yanda take tafiyar ne yaga tamkar ɓata masa lokaci takeyi, ya miƙe, taku ɗaya, biyu Afeeyah batayi aune ba se jinta tayi gaba ɗaya a kan ƙirjinta ya zagaye bayanta da hannaye biyu kafin taji kamar ƙafafunta sunbar kan Ƙasa.

Cikin Azama ta shiga Ƙoƙarin kwace kanta zuciyarta ma wani irin bugu kamar zata tsaga ƙirjinta ta fito fahimtar abinda take niyyarti yasa ya direta amma be saketa daga jikinsa ba swda tayi yunƙuri da gaske kafin ta janye tayi gefe tana sauke numfashi tareda zare idanu kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.
"Subhanallahi, I'm sorry, I'm so sorry Afeeyah i don't know what come over me i missed you so badly shiyasa na kasa riƙe kaina. I'm sorry for not seeking your permission before i touched you" Jay ya faɗa yana matsawa kusa da ita, taja da baya da sauri yanda tayi yasa ya fashe da dariya babu shiri. Kamar taga dodo ko wani Aljani.

Komawa yayi kan kujerar daya tashi yana kallon yanda take kokawa da numfashinta tana zare ido.
"Kizo ki zauna" ya faɗa yana nuna mata kusa dashi, ta maƙale masa kafaɗa. Da wani mayaudarin sauti bayan daya saka idonsa cikin nata yace
"Please Afeenah". Yanda kasan ya jata da magnet haka ta fara takawa dukda can ƙasan ranta wani irin tsoro da kokontonsa ne ya shigeta, karo na farko kenan a rayuwarta da makamancin haka ya faru da ita. Namiji Baligi ya runguneta harya ɗaga ta sama tayi tantiran Samari kala kala amma babu Wanda Allah ya bawa sa'ar kwatanta mata irin wannan abun sw Jay. Bawan Allah Ahmad ya faɗo mata a rai, a shekara uku sau ɗaya fatar hannunsa ta taɓa haɗuwa da tata shima bada niyya ba, ko hoto zasuyi basa tsayuwar da jikinsu ze gogi juna...

"I said I'm sorry fa, menene kum duk fuskarki ta canza or you are mot happy to see me?" Jay ya sake marairaicewa yana faÉ—a yatsunta guda goma cikin nasa yana murzawa, bata san sanda harya kama hannun ba seda ya fara magana ta ankare.

"Jayyy, babu kyau, don't touch me again" ta faɗa kamar zata rusa masa kuka bayan data zame hannayenta daga nasa. Yayi wani mayaudarin murmushi kafin yaja baya ya zauna dakyau seya tallafe fuskarsa da hannu biyu ya zuba mata iso, irin kallon ƙurillar. Ƙasa tayi da kanta dan bazata jure wannan kallon ba bayan abubuwan daya yi mata,
"Kinfi kyau a fili, kinfi kyau a kusa" ya faÉ—a yana kai hannunsa ya shafa fuskarta, ta tura baki da sauri yace
"Don't do that again ki bari ba yanzu ba se kin zama halalina don't make me loose my self Afeeyah you won't like me".

Da sauri ta miƙe daga inda take zaune saboda yanda yayi maganar daidai nan Salaha ta turo ƙofa janye da Food Trolley. Akan kantamemen centre table da yake tsakiyar falon ta shiga jere abubuwan data kawo bayan data gaida Jafar. Seda ta gama tas ta fita har sannan Afeeyah na tsaye dan gaba ɗaya Jafar ɗin ya tsoratata.

"Ki zauna wlh bazan sake taɓa ki ba" yayi magana yana mata murmushi, gabanta ya yanke ya faɗi, sautin muryarsa da murmushin da yayi taga sun rikiɗe mata ya koma kamar Ahmad. A sanyaye ta zauna kan kujerar da ke can nesa dashi. Yan kallonta yace

"Ko gaisawa bamuyi ba duk na tsorataki, anya ma kuwa zaki iya dani yarinyar nan naga alama tsoro ne dake sosai".

"Ina wuni" ta faɗa a sanyaye tana ƙoƙarim kauda tunanin Ahmad daya ziyarceta. Seda Jay yayi dagaske kafin ta sake ba duka ba dan salon daya zo mata dashi yasa ta ɗarare ga Ahmad dake ta mata yawo a zuciya. Shiya ringa janta da hira tana amsawa se yayi shiru fuskarsa ta canza nan da nan hankalinta ya tashi ta shiga tambayarsa meya faru.

"I said I'm sorry amma from the way you are behaving kamar bakiyi mun uzuri ba. Kasa riƙe kaina nayi nace bazan sake ba in sha Allah amma kalla ko magana ma ni kaɗai nakeyi daman saboda ki ɓata mun rai kika damu nazo" ya wani haɗe fuska kamar gaske aiko ya tayar mata da hankali yanda ya tsammata se gashi ta buɗe baki tana bashi haƙuri yana shan ƙamshi daga nan kuma suka koma normal suka fara hira irin yanda suka saba a waya. Duk abinda tace ita ta girka da kanta ya taɓa kaɗan Chinese rice da tayi da wani Chicken wings yace ta masa packaging zeje gida da shi. Seda aka kira Magriba kafin suka rabu yace zeje masallacin daya gani a farkom dake layin yana fita ya tarar da taron jama'ar da Mu'az ya haɗa a wajen gidan dan megadi ya hanasu shiga.

Yaran unguwa Abokanansa ya ringa bi gida gida yana ce musu ga Jay a gidansu suka taho harda manya marasa abinyi za'ace ko kuwa tsabar sonJay yasa suka yarda da maganar Mu'az É—in shi kuma Malam Sa'idu ya hanasu shiga dan daman ba kirki ya cika ba. A falonya koma yayi sallar dan baze fita ba,bayanya idar ya kirata tace gata nan tareda Anty Sauda zasu gaisa.

A mutunce tamkar tanayi dashi Anty Saudan suka gaisa yana jan Amani data liƙe mata suka fito tare bayan sun ƙare gaisuwar ta barshi da Afeeyah suka ƙarasa magana. Jikinsa ya sake janta ya shiga ɗaukansu pictures wanda duk ta kare fuskarta da hannu ba'a ganinta. Tana ƙunƙuni suka fita ta rakashi jikin motarsa ya fitar mata da tsarabar daya kawo mata.

"Bangaji da ganinki ba, kamar karna tafi" ya faɗa yana binta da kallo daga sama zuwa ƙasa kamar Maye. Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta, yayi murmushi ya sake cewa
"Se yaushe, yaushe zanje na gaida su Baffah?"
"Yace from today to friday" ta bashi amsa a sanyaye tana tuna kalaman Baffa. Yanzu ace ya san Jafar ya kakkamata haka ai babu ma zancenya bashi auranta tasan cewa zeyi bashi da tarbiyya, ta dai yi masa uzurin kasancewarsa Rainon turai a gurinsu wannan ba wani abu bane su.

"Ok, wednesday yayi?" Ya tambaya yana É—age mata gira, ta gyaÉ—a kai, ya yashi daga kishingiÉ—ar da yayi jikin mota yace
"Gobe anan zan sameki ko gidanku?"
"Gobe ma zaka dawo?" Ta tambaya tana ware ido,
"Ko kar nazo kin gaji dani?" Ya mayar mata tambayar yana buɗe ido yanda tayi se tayi ƙasa da nata tana murmushi tace
"Aa"
"Don't worry, I'm not going to touch you again tunda naga raguwa ce ke".

Yanda yayi maganar yasa taji kamar ta nitse a gurin da take tsaye, Ƙarara zaka fahimci da biyu yayi maganar musamman murmushin da yakeyi da irin kallon dayake binta dashi seta juya da sauri ta shige gida. Me gadi ya bawa Boxes ɗin ya shigar mata dasu bayan ya masa ihisani ya wuce gida cikin nishaɗi jama'ar da Mu'az ya tara kuwa hannu kawai ya ɗaga musu suka ringa ihu har seda matan cikin gida suka fara zaburowa sunayin waje suga meya faru shidai tuni ma yabar layin ya kama hanyar gida. A traffic ya shafa Aljihunsa yaji kwalbar turaren daya ɗauka a safe ɗin Yah Ahmad, ya zaroshi ya kai hancinsa ya shaƙi ƙamshin, hannunaa na hagu ya shanshana wanda ya fi amfani dashi gurin riƙe Afeeyah ba hannun kaɗai ba duk jikinsa har motar ma ta kama ƙamshin turaren da yake da yaƙinin na jikinta ne dan ya shaƙe shi yanda ya kamata lokacin daya ɗagata sama.

Daya kasa gane abinda yake so ya tantance se kawai ya ajiye turaren a gefenshi, ta yuwu yanda ya shaƙeshi a gida da daɗin daya masa yasa yaji kamar shine a jikinta. Da wannan tunanin ya aminta yaci gaba da tuƙi yan tuno ta harya isa gida ganin motar Ahmad yasa ya wuce ɗakinsu ba tareda ya shiga cikin gida ba dukda tun yana gurin Afeeyah yaga kiran Hajiya, yanzu a hanya ma ta sake kira.
PAGE 20
Ranar laraba kamar yanda sukayi da Afeeyah tun safe yake shirin zuwa gaida Mahaifita. Ya jawa Ahmad kunne akan kar a maimaita ta wancan ranar, dawowa da yayi ya tarar dashi ba lafiya nema ya rage kaifin Mitar da yayi niyyar dasa masa.

"Zaka rakani gidansu Fatima biko nima" Ahmad ya faɗa masa. Jay ya taɓe baki, ya lura kamar sun samu matsala da Fatiman dan beji ya kirata ba kuma sukukun da ya ganshi yasan baya rasa nasaba da rashin shirunsu Allah yasa dai abinda ya faru ya saka ya haƙura da auranta kowa ya huta.

BayanSallar Magrib suka shiryi tafiyar dan Jafar baya ditar rana muddinba hayaniya da cunkoso yake so ya haɗa ba. Tsaf suka shirya kamar tagwaye, kaya iri ɗaya suka saka Shadda Cream Color ta karɓi jikin kowanne duk iya hassadar mutum sedai ya kallesu yace Tabarakallah badai ya kushe shigar wani daga ciki ba. Jafar ya sake jefa turaren jiya a Aljihu dan karya manta. Suka jero suna tafiya Ahmad na tsokanarsa har suka zo daidai part ɗin Alhaji.

"Ba zaka shiga kayiwa Hajiya Sallama ba?" Ahmad ya tambayeshi se yayi saurin cewa
"Kai Aa muje kawai, tun fa dana dawo maganar da take tayi mun kenan wacece nake so a ina nake neman Aure, kasan matsaltsalun Hajiya yanzu setace ba haka ba shiyasa nake so ayi komai a sirrince se an kai kuÉ—i idan Allah yasa an É—aura auran kawai se taji labari".

Ahmad ya ringa dariya yana cewa
"Lallai ka shahara, to wlh na barka da Allah idan ka janyo mun magana dan cewa zatayi ni na zugaka ka ɓoye mata"

"Ina zakuje haka?" Muryar Alhaji Audu daya fito da shirin fita masallaci ta dakatar dasu. Ko wanne ya tsume kafin suka shiga gaishe shi.
"Se ina haka kuka kafa huluna kamar sababbin Angwaye?" Alhaji ya tambaya. Ahmad ne ya bashi amsa yana shaf kai yace

"Gaisuwar surukan Jafar zamuje". Kamar Alhajin zece wani abu daga yanayin kallon daya bisu dashi se kuma ya canza da cewa
"Amma da kun jira kunyi sallar Isha'i a Jam'i ba lallai inda zakuje ku tarar basu idar ba" ya wuce is suka bishi a baya. Bayan an idar da sallah suka sake rankayowa tareda Alhajin suka shiga gida. Har Ahmad ya tada mota Balarabe guda daga ma'aikatan yaje da sauri yace masa Alhaji na magana seya bar motar a kunne ya wuce yanajin JafdaƘƙƊƘananun tsaki, har mamakin irin zumuɗin da yakeyi akan yarinyar yake kamar ba Jafar da Mata ne suke zigilli akansa ba se gashi wata ta zargeshi tsaf tana ja a ƙasa.

"Yanzu na samu waya Alhaji Munzali yayi hatsarin mota kuma jikin babu daÉ—i ina so naje na ganshi" Alhaji ya faÉ—a bayan da Ahmad yaje. Cikin jimami yayiwa Abokin Alhajin jaje da fatan samun lafiya. Alhaji ya sake cewa

"Bari na shiryo seka rakani mu duba shi" ya wuce sama ba tareda ya jira amsarsa ba. A waya Ahmad ya kira Jafar ya shaida masa, ya fara balbalin bala'i,
"Ai se kazo ka sameshi da kanka ka tuna masa fita zamuyi, nasan ba mantawa yayi ba yana sane tunda ya buƙaci na kaishi kayi haƙuri kawai kaje ma koma tare wani lokacin" Ahmad ya faɗa da Jafar yace wai ya gayawa Alhaji fita fa zasuyi.

"Amma ni kaÉ—ai zanje gaida mahaifin nata kamar wani mara galihu?" Ya faÉ—i kamar ze masa kuka, Ahmad ya sake cewa
"Duk ni sanda nake zuwa nawa gaisuwar dawa mukaje? In baka iya zuwa kai kai kaÉ—ai ka kira ko Sadik ko Anwar su rakaka"

"Ni dakai nake so muje"
"Shikenan seka jira na kai Alhajinmu dawo se mu tafi"
"Salon Babanta yace I'm not serious ba? Allah kawai dan ta riga da ta gaya masa ina zuwa da fasawa zanyi kawai naje muyi hira idan yaso daga baya se muje gurin Popsyn nata da kai" Jafar ya dira mita daga ƙarshe ya kama hanya ya tafi shi kaɗai Ahmad kuma ya kai Alhaji AKTH duba Abokinsa. A hanya Alhajin yake cewa Ahmad

"Babanku ya gaya mun iyayen yarinyar sun dakatar da zuwa tambaya sunce a basu sati huÉ—u ko?"
"Eh haka yace Alhaji" ya bashi amsa ba dan yaso ya tado masa da maganar ba. Alhaji ya sake cewa
"Ka bincika kaji dalilin daya saka suka ce hakan ne?"
"Eh, kawunta wanda ze bayar da auran ne baya nan yayi tafiya shine dalili" Ahmad ya yanko ƙarya ya lafta masa.

"Uhm kodai basu shirya ba dai kuma suna jin nauyin su gaya maka ka saka musu hannu a cikin shirin nasu?" Alhaji ya sake faÉ—i yana kallon Ahmad da yanayinsa ya nuna he is not comfortable da maganar da maganar da Alhajin ya tayar. A sanyaye yace kawai yayi shiru be bashi amsa ba hakan tasa shima Alhaji ya kama kansa can kuma ya sake soko wata maganar yace

"Wato shi gaban kansa yakeyi babu wanda ya saka cikin lamarin auransa daga kai se Uwarsa ko?"
Yasan da Jafar yake dan haka yace
"Jiya ya fara zuwa gidansu Alhaji, tsarin Babansu ne kuma se yaga mutum kafinya bashi damar neman auran yarsa shiyasa zeje yau ya gaishe shi amma ba wai maganar auran ce ta taso ba".

"Dama aiba zaka taɓa faɗar laifinsa ba, shi kuma yar waye yake nema?"
"Nima ban sani ba yanzun zamuje daman kuma ya tafi shi kaɗai" cikin yanayin Ƙosawa da tambayoyin ya bashi amsa se Alhaji ya Ƙaro radion Mota yayi shiru.

Jay kuwa be fahimci kwatancen da Afeeyah ta turo masa ba dan haka tace tayi sharing masa live location ɗinta haka kuwa akayi yana biye da Map tiryen tiryen se gashi a cikin gari tsukin unguwar Marmara. A bakin titi yayi parking mota yana ƙarewa gurin daya zo kallo, dukda darene amma Jama'a nata kai kawo yanda kasan kasuwa ga surutu kaya kaya banda ƙarar ababen hawa da suke karakaina akan titi.

He couldn't believe it a wannan unguwar suke zaune. Ya ringa zungura kai yana leƙa yan hanyoyin da yake gani, gurin da Map ɗinza yake pointing lungune da babu alamar Mota tana iya shiga.
"Ta yuwu Babansu irin mutanen nan ne da basa son canza muhalli shiyasa ya ke zaune a nan ƙila da akwai wata hanya kota can baya da suke bi da mota har ƙofar gida" ya shiga baiwa kansa Ƙwarin guiwa. A waya ya kirata ya gaya mata yana bakin titi besan ta inda ze shigo ba tace masa zata bawa Yayanta wayarta seya zo ya tafi dashi haka kuwa akayi ta bawa Yaya Malam wayar sukayi magana harya gano inda yake.

Seda ya rufe fuskarsa da Facemask kafin ya fita daga motar, sukayi musabiha sannan suka tsallaka Titi, suka ringa bin lunguna suna tafiya shidai bin Malam kawai yakeyi a baya a ransa yana mamakin wannan unguwa daya zo yau, a rayuwarsa be taɓa shiga makamancin lungun ba, iyakarsa da nan haka gidan Sarki dan kafin ya tafi Turai yayi nacin son Doki da sallah ko idan an gayyaci Alhajinsu wani taro yakan biyo shi saboda yaga Doki shi be san akwai irin lokunan nan bama a Kano.

Tun yana hasashen ganin gida me Gate harya saduda domin dai gidajen jar laka yake tacin karo dasu wanda Hasken Nepa da Sololin da gwamnati ta ƙawata lokunan dasu suka taimaka masa gurin ganinsu tsaf kamar da rana. Seya saki tunanin gidan Gate ya kama na kodai Babansu Basarake ne? Tunda akan samu gidan Sarakai cikin lungu. Bashi da me bashi amsa haka ya ringa jefa ƙafafu har suka isa inda yaga Malam ya dakata da alamu nan ne gidansu Afeeyah.

Ya ƙarewa gidan kallo cikin abinda befi sakan biyar ba, da fulasta lulluɓe dan haka bayace ginin ƙasa bane kona sumunti. Filin dai dukansa baze wuce taku Ashirin da biyar a kwance ba idan ma ya kai, be san ya zurfinsa yake ta ciki ba. Zuciya da saƙe saƙe take ta ayyano masa ai Akurkin da Alhaji Audu ya watsasu a gidansa ma yafi wannan gidan girma da yalwa.

Muryar Malam ta dawo dashi daga tunanin daya tafi yana cewa
"Bari na sanar mata ka iso" ya wuce cikin siririn soron gidan Jay harda tura wuya yana leƙawa. Ya saki ajiyar zuciya me ƙarfi bayan da Malam ya dawo yace masa Baffah yace ya shiga. A baya ya bishi cikin taka tsan tsan dan kar Ƙofar gidan ta rafke masa goshi dan ya lura shima Malam ɗin da yake dogo ne sosai seya ranƙwafa yake shiga.

Tilas ya yabawa tsaftar matar gidan domin dukda darene ko ina tsaf yake babu tarkace, a fakaice ya kalli ƙofofi guda huɗu da suke cikin gidan wanda yake tsammanin ɗakuna ne, ya hango kitchen da kuma inda yake zaton makewayine saboda ga famfo nan se siririn lungu ya shiga ciki. A cikin barandar dake gaban ɗakuna biyu suna kuma kallon ragowan biyun ya zauna kan shimfiɗar babbar darduma da akayi. Harda standing fan a ajiye a gurin. Malam ya shige ɗakin Baffah ya sanar masa ga Baƙon wanda tuni Ƙamshin turarensa ya sanar musu da shigowarsa.

Dattijon daya tabbatar shine mahaifin Fatima ya fito, fuskarsa a sake yake yiwa Jafar da duk yaji ya rikice kamar wanda yaje gaban Sarki Maraba. Ya zauna daura dashi, Jafar ya duƙe yana gaida shi amma Baffan ya bashi hannu sukayi musabaha. Tattaunawar tasu batayi tsayi ba, ya tambayeshi waye shi sana'arsa data mahaifinsa. Daga yanayi na kamala da kuma tambayoyin da Baffah yayi masa be ga wata matsala a tattare dashi ba. Baffan yace masa

"Da akwai wanda yake neman Afeeyah kafin zuwanka sun jima dashi amma ta tabbatar mun da kai take so, ina fatan a shirye kake domin bana so maganar auran taja lokaci, zan baka daga nan zuwa sati biyu ka turo magabatanka domin muyi magana, da zarar ta kammala karatu a É—aura muku aure"

"In sha Allahu Baffah" Jay ya faÉ—i yana goge zufar data tsatstsafo masa daga goshi. Baffah ya karkato masa da fanka saitinsa yana cewa
"Garin da akwai zafi sosai dan ma an samu wuta kasha ruwan ko zaka samu sauƙin zafin" ya nuna masa ruwan pure water da Zoɓon gora wanda Umma take siyarwa Malam ya ajiye masa tun zamansu. Umma ce tace pure water za'a bashi domin su na famfo ma suke sha ai kuwa har kuka Afeeyah tayi akan hakan.

Jay ya kalli farantin ruwan yayi murmushi kawai ba tareda ya sha ba, Baffah ya miƙe yana cewa
"Bari naje, an gayyaceni Mauludi anan Ƙasanmu zuwan kane ya dakayar dani da tuni naje dan bana so nayi dare a waje" se shima Jay ya miƙe tsaye yana laluba Aljihunsa. Bandir na dubu ɗaya ya zaro ya rage tsayi kafin ya miƙawa Baffan yana cewa
"Gashi babu yawa a siyi goro". Baffah ya kalli kuɗin yayi ƙaramin murmushi kafin yace
"Nagode Allah yayi Albarka" ya wuce ba tareda ya karɓa ba yana cewa Umma ta leƙo su gaisa. Malam ne ya fito daga falo yace ya shiga can kawai, yayi masa jagora Umma na zaune kan kujera tana kallon Arewa 24 a yar Plasmarta da Baffah ya saka mata kwanannan da Hijabinta har ƙasa Jay ya kai ya gaisheta ta amsa a mutunce tana cewa ya hau kujera sw ya sake kalmashe ƙafa ya zauna sosai akan Centre carpet kansa a ƙasa.

"Kira masa ita" Umma ta faɗa tana miƙewa ta fice daga falon sega Malam da Afeeyah, ya baje a gabansa daman Baffa yake jira ya fita dan ta Umma me sauƙi ne. Kamar wanda za'ayi wa Ƙarin karatu haka ya zauna bakin nan har kunne yau gashi ga Jay a gidansu.

"Wai meye haka Yah Malam?" Afeeyah ta faÉ—a tana tura baki. Jay ya kalleta bbau yabo babu fallasa yace
"Ina ruwanki? Yayanmu ne kuma Fan"
"Loyal Fan ma kuwa, dan Allah ina zuwa be kamata naci amanar Jay ba gara na fara sanar masa ya zo ya ganka inaga har suma zeyi yau saboda ÆŠaÉ—i" Yah Malam ya faÉ—i kafin ya sake ficewa da sauri kiran Amininsa Sani. Tsabar yanda yake Son Jay ne sunansa ya koma haka, babarsa kanta ta tashi daga Mamansu Sani ta koma Mamansu Jay dako ka zagi Jay a gaban Sani gara ka ambato Babansa Malam Hamza ka zaga.

Bayan fitar Malam Afeeyah ta zauna yanda Jay yake binta da kallo kamar me neman wani abu a jikinta ne duk yasa ta tsargu. Atamfa ta saka yau A line gown Dark blue ce da fari se dan jaja kaɗan a jiki kalar ta haska ta sosai ta mata kyau. Cikin sanyin murya ta gaishe shi, ya amsa bataji sautin muryarsa ba laɓɓansa taga sun motsa shine ta fahimci ya amsa mata. Jikinta yayi sanyi, murnar dake ranta ta yau Jafar yazo gurin Baffah alamar maganar auransu na dab da Ƙulluwa ta disashe. Ta tsammaci ganin fuskarsa a washe kamar jiya koma tafi hakan amma se taga saɓanin zatonta, ba yabo ba fallasa, ba wannan Fara'ar da ya ringayi jiya balle zumuɗin taɓata se binta yakeyi da kallon data rasa dalilin sa.

Sukayi shiru for almost 10 mins shi yana kallonta ita kuma tana wasa da zoben hannunta zuciyarta na dakan lugude. Meya kawo canji a fuskar Jay? Abinda take tambayar kanta kenan.
"Afeeyah" taji ya kira sunanta ta ɗago a hanzarce kamar tana jira, idanunta da suka fara tara saboda tunane tunanen da takeyi ta sauke a cikin nasa daya zuba mata. Tana kallo ya taune Lips ɗinsa na ƙasa kafin ya kalli gefe alamu sun nuna maganganu ne a bakinsa bama magana ba amna ya haɗiye su se ya miƙe yana ƙaƙalo murmushin data tabbatar na yaƙene yace mata

"Muje ki rakani, kar Umma tace bani da kunya na shige mata falo nayi zamana". Yanda yayi maganar yasa dole ta murmusa lokaci ɗauke ƙwallar data ziraro mata duk akan idonsa. Ya cire rafar Kuɗin ɗazu ya ajiye a inda ya tashi kafin ya juya ya fara tafiya tabi bayansa tana cewa
"Ka ɗauki kuɗinka indai ba faɗa kake so ka janyo mun ba" be amsata ba ya sa kai ya fice. Umma na tsaye gaban ƙatoton Fridge ɗinta tana jera Gororin Zoɓo, dama yanzu take shiri a ranta ta leƙa falon se gasu sun fito. Jafar yayi mata sallama tace ya gaida mutanen gida ta juya taci gaba da aikinta Afeeyah tabi bayansa zalo zalo jiki a saluɓe.

A soro ya tsaya bayan ya tura ƙofar gidan ya jingina bayansa da ita ya harɗe hannu a ƙirji yana mata kallon da yake sakata faɗuwar gaba. Ko a mafarki be taɓa hasashen Afeeyan ta fito daga irin wannan gidan ba, ƙirarta, fatar jikinta, kwalliyarta basuyi kama dana wadda take rayuwa cikin wanna lokon ba. Abubuwa da yawa suke masa yawo a rai amma yayi ƙoƙarin furzo wanda yafi tsaya masa a rai da Baffanta yace masa akwai wanda ta daɗe tare dashi amma tace shi take so. Kamar saukar Aradu haka taji tambayar
"Wanene wanda Baffa yace kun daÉ—e tare dashi?".

Seda tayi dagaske kafin ta iya danne firgicinta ta saita kanta ta hanyar marairaice fuska, yanayin da tayin ransa a ɓace yake amma abin ya bigeshi se kawai ya ɗage kai sama yana shaƙa tareda furzar da iska me cakuɗe da Ƙamshin turaren da a yanzu ya tabbatar a jikinta yake jinsa.

"Kai da kanka kana cewa baze yuwu ace mace kamata na rasa saurayi ba, haka ne amma kuma babu wanda nake so cikinsu" ta faÉ—a cikin rawar murya
Idanunta akan fuskarsa, so takeyi ta fahimci abinda yake zuciyarsa amma yaƙi bayyanar da hakan. Zuciyarta ta sake tsinkewa sanda taji yace

"Bana son ƙarya Afeeyah na kuma tsani me yinta. I asked you everything that concerns you me yasa zaki ɓoye mun wannan? Kuma har Baffahnki yasan da zamansa tsakanin ni dashi wa kike shirin ki yaudara?"

"Amma kasan babu batun yaudara tunda har na kawoka gaban Mahaifina, idan ƙarya nakeyi maka bazan taɓa bari kaga tushe na ba zamu ƙare soyayyar mune kawai a waya ba zaka taɓa sanin inda zaka saneni ba idan na gama na sallameka"

"Shi da k ika fara kawowa shi kika yaudara kenan?" Ya tsareta da idanunsa da suka canza kala saboda abinda shi yaɗai yasan menene. Tayi shiru dan gani tayi kamar ze iya kwasa mata mari idan ta sakw faɗin wani abu. Ya dafa ƙofa yana nunata da yatsa yace

"Ki tabbatar da kin sallameshi, karna sake ganinki da duk wani abu daya dangance shi, i mean daga kan sutura, cosmetics har wayar hannunki ki cire Sim yanzu I'm going to send you another one. Ki nemi izini gobe or the next day I'm taking you out to shop, bana so na sake ganin duk wani abu daya siya miki a jikinki har wannan turaren da kike sakawa bana so na sake jinsa a jikinki".

Yanda kasan Ya da Uba haka yake nunata yana zazzaga mata maganganu, tunda take a rayuwarta bata tabajin ta tozarta irin na wannan lokacin ba, a tsaye take amma ji tayi inama ƙasa ta buɗe ta shige ciki ko kuma ta rufe idonta ta ɓace ɓat daga gurin. Maganganun Jafar suna nufin ita ko iyayenta basu isa su mallaka mata ire iren suturu da sauran kayayyakin da take ta'ammali dasu ba, yazo yaga gidansu dole ya samu bakin faɗa mata maganganu ai. Yanda yake magana fushin dake cikin muryarsa ya zarta ace iyakar na disappointment ne, ya wuce ace na ƙaryar da yake iƙirarin tayi masa ne tabbas da akwai wani abu daya tunzurashi bayan wannan.

Jiki a saluɓe ta shiga gida bayan daya sallameta ya tafi ta shige ɗaki ta faɗa kan katifarta tana sakin kuka me sautin da ta kasayi a gabansa se hawaye. Muryar Umma dake kwarara mata kira da hayaniyarsu Yaya Malam ta sakata dole ta tashi, seda ta wanko fuska a bakin famfo kafin ta shiga falon da suke.
"Wannan kuÉ—in fa na menene?" Umma ta tambayeta tana kallonta kafin ta Amsa Sanin Jay ya zaburo yana cewa

"Yana ina Afeeyah? Ni daman nasan ƙarya kakeyi haka kawai ina gurin Babyta ka tasoni yanzu kasa na faɗa mata magana yanzu nayi two zero, ni banyi hira da ita naji daɗi ka yaudareni da sunan Hero".
Malam daya sha wahalar nemo Sani ya galla masa harara yace
"Minti nawa nayi ina gararanba a lokon nan kowa yace besan inda kake ba? Amma dai ko ƙamshin da gidan nan yakeyi ai ya isa kasan yau anyi babban baƙo"

"Ji banza, wane kalar turarene Ahmad be baza mana a Lokon nan ba? Shifa idan yazo tun daga titi ake sanin ya iso gidan nan kuwa a Ƙalla yana kwana uku kafin ƙamshin ya gama bajewa" inji Sani Malam yace
"Zubairu" Umma ta daka musu tsawa jin zasu kaure da musun da suka saba tace au fita su bata guri tunda basu san sun girma ba.

Afeeyah na tsaye har sannan ta sake nuna mata kuÉ—in tana tambayar na menene
"Shine ya ajiye kuma seda nace masa ya É—auke zakiyi faÉ—a amma be jiba" ta bawa Umman amsa. Murmushin takaici Umma tayi tace

"Ba laifi ai tunda shi naga harya harbo jirginki da wurwuri ya fahimci mayadariya ce ke kuma makwaɗaiciya. Shi dayake free ne gashi nan ya buɗe miki ai ya nuna miki kar yake kallonki tunda dai yaga ubanki ya san bashi yake miki hidimar da tasa kike jin kanki kina goga kafaɗa da waɗanda suka tsere miki ba kinga ko auransa kikayi yasan ba dan Allah bane kin aureshi ne saboda abin hannunsa. Ko da dai banga wata sufa ta rashin da'a a tattare dashi ba amma ki sani inda kaso dari ya yarda dake daga kalamansa kin rasa kaso hamsin na ƙima da darajar da yake kallonki dasu ada in ma be zarce hakan ba.

Ga wanda kika daɗe tare dashi yana bauta miki yanzu da kika hango kazar data fishi maiƙo shine kika tubure akan kw baki taɓa cewa kina sonsa ba ai shikenan ni babu abinda zance miki tunda ubaki ya tsaya miki, Allah ya shige gaba" Umma ta faɗa kafin ta maida hankalinta kan Film ɗin Hausan da aka fara a Arewa. Afeeyah na tsaye tana hawaye, jin Umman tayi shiru ta fahimci ta gama maganarta. Wai dan Allah da wane yare zata fahimtar da Umma? Abinda take tambayar kanta bata da amsa dan haka cikin muryar kuka tace

"Kiyi haƙuri Umma"
"Da kika mun me ni kuma? Ai ke ya kamata na bawa haƙurin shiga rayuwarki da nakeyi, ni ai babu abinda zan sake cewa kuma Afeeyah ai magana ta ƙare tunda har kin turoshi kenan ba gudu ba jada baya kina kan bakanki shima kuma Malam naji ya bashi sati biyu ya turo, to dai ku tsananta bincike kar azo ayi abinda daga baya za'a ringa wlh tallahi" Umman ta sake magana, yanda tayi seka rantse da wata Ƙawa ko yar uwarta suke shawara akan auran wata, tamkar ba auran yar cikinta ake magana ba wai su tsananta bincike ita da Baffa kenan ta zame hannunta a ciki kai se a bar Umma dai.

Kuka Afeeyah ta fashe mata dashi tana zama a gurin
"Umma magana kikeyi fa tamkar kin zare hannunki daga cikin sabgata kina nufin nayi gaban kaina?" Ta faÉ—a cikin kuka, Umma tace
"Au wai baki sani ba tuntuni? Ai ni tun daga randa kika nuna mun kin girma, kin isa ki yankewa kanki hukunci na zare hannuna daga sabgarki Afeeya ai yanzu kece uwar kanki, abinda kike so ne kuma na barki da zaɓinki
Ke bakiyi ko rabin tashen da nayi a zamanin ƙuruciyata ba, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba soyayyar da kike iƙirarin kinawa wancan yaron batavkai zafin wadda nayiwa nawa muradin ran ba, da ace na zamo me kafiya da taurin kai irinki da ban auri ubanki ba har nazo na haifeki kika tsaya gabana kina faɗin ke ga wanda ranki yake so.

Ban fara son ubanki ba seda na zauna dashi domin daya ganni yace yana sona ya samu Mahaifina uffan ban tofa ba nabi abinda nawa uban ya zaɓar mun gashi naga ribar biyayyar danayi masa saboda shekara talatin da biyar Alhamdulillahi babu abinda zancewa ubangiji se godiya domin matsalolin aure sedai naji su gurin mutane badai a cikin gidana ba, ƙila dana bijire nabi zaɓin raina kamar yanda kike shirin aikatawa Allah kaɗai yasan takaicin da zan kwasa a tsayin shekarun nan" Umma tayi maganar cikin zafin rai. Afeeyah dai se kuka take Umman ta miƙe ta nufi Ƙofa tana cewa

"Kukan daɗi kikeyi, Allah ya gani iyakar yi mun kare mutunchinmu, se ki zuba ruwa a ƙasa kisha kin jawo mana abinda za'a yi damu, ba unguwar nan ba na tabbatar duk wanda yaji labarinmu seya zagemu shekara uku kina cinyewa yaro kuɗi yana miki hidima rana tsaka kice baki san zance ba Allah yasa yazo yace a biya shi se ki san ta inda zaki fara tattaro masa kaya da kuɗaɗen daya kashe miki"

"Haba Ruƙayya shin wai maganar nan ba zata mutu haka ba?" Baffa da tun daga soro ya tsinkayi mitar Umman ya faɗa bayan dayayi sallama. Ta kalleshi kafin tayi murmushi irin na zallar takaici tace
"Malam kenan, ai ba'a ma haifi maganar ba balle ta mutu, yanda mutanen unguwar nan basa raina abin magana idan bamuyi wasa ba ai fita seta gagaremu na wani lokaci saboda yanda za'a ringa zunÉ—en mu. A haka ma meye ba'a cewa duk akanta balle kuma aji wannan shegantakar Allah dai ya rufa asiri" ta fice daga falon ta barsu shida Afeeyah dake aikin kuka har sannan.

"Tashi kije ki kwanta" ya faɗa mata a sanyaye, tabbas Umman batayi ƙarya ba, tarayyar Afeeyah da Ahmad ba abinda mutanen unguwa basa faɗi wasu ma cewa suke lalatarsu kawai sukeyi amma idan ba haka ba Ƙanin uwarta ne kona ubanta ze ringa mata hidima haka?.

Jay kuwa da tunani kala kala fal kansa ya bar gidansu Afeeyah, ya ringa bulayi a loko dan ya manta ta inda suka shiga kuma shi kaÉ—ai ya fito, daidai Allah yasa ya ganshi a titi sedai ya banbanta da inda ya ajiye motarsa dakyar da tambaya ya koma kan Titin daya ajiyeta ya figi motar a tsiyace ya bar unguwar.
Abu goma da ashirin haka ya ringa saƙa da warwara. Be taɓa koda a hasashe hango Afeeyah ta fito daga irin low class family haka ba. Dukda bata yi masa ƙaryar ita yar masu Arziƙi bace dan ko magana sukeyi takan nuna masa batasan abubuwa da yawa da yake maganarsu ba seya ɗauka wasa takeyi seyau ya tabbatar ya kuma ganewa idanuwansa.

Asalinta ko matsayin mahaifinta be girgiza komai daga Son da yakeyi mata ba amma ƙaryar daya kamata dumu tayi masa ita ta hasalashi, seda ya tambayeta idan da wanda yake nemanta har iyayenta sun sani ta gaya masa tace babu. A duniya idan akwai abinda ya tsana be wuci wulaƙanci da ƙarya ba gashi ya kama wadda yake mutuwar so da dukka laifukan saboda shi ta masa ƙarya ta kuma wulaƙanta koma wanene take tare dashi bayan tsayin lokaci daya ɗauka lokaci yana hidima da ita, daga irin suturun da take sakawa kai ko fatarta ka kalla kasanba ƙaramar kulawa take samu ba ta mayuka masu inganci tabbacin koma wanene yana da buruka masu yawa akanta shiyasa baya ƙyashin kashe mata ko nawa ne amma ace lokaci ɗaya ta sutaleshi.

Tabbacin da yake dashi shine tana sonsa tunda gashi har mahaifinta ya faɗa shima kuma ya yarda da hakan domin ya gani a idonta ya kuma fahimci hakan daga ayyukanta badan haka ba shima ze ce tana da target akansa idan ta samu wanda ya fishi watsar dashi zatayi. Allah kenan, wato tasu ƙaddarar kenan shida Yah Ahmad soyayya da irin waɗannan yaran. Dalilin abinda yakeji akan Afeeyah yasa yaji ya farayiwa Ahmad uzuri bisa jure cin kashin da Fatima takeyi masa domin yanda yakejin Afeeyah a ransa ya tabbatar shidai baze zama sullutu irin Ahmad ba amma fa ko taƙi Allah ko bata sonsa se ya aureta a hakan sedai ta mutu tunda dai ya samu cikar burinsa amma shi ya zauna yana lallaɓata tana wulaƙantashi bayan yana da makaman da ze iya juya komai dasu se yanda ya tsara za'ayi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.