Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 11
PAGE 24
Comment section ta shiga, hawayen da suka lulluɓe mata ido suka saka bata iya ganin abinda aka rubuta. Tana kuka tana typing
"Unblock me and answer my calls Jay dan girman Allah I'm going to explain ba abinda kake tunani bane" Tana turawa ta fita ta shiga gurin message nan ma ta fara jera masa maganganganu amma harta haƙura cire tsammani be amsa ba, kuma official account ɗinsa ne babu batun ace be gani ba. Wacece wannan yarinyar? Menene haɗinsa da ita? Ta ringa tambayar kanta. Kuka tasha har seda taji tana neman shiɗewa sannan tayi shiru amma hawaye basu dena zubar mata ba.
JAY
Abuja yayi zango bayan ya bar Kano, sati huɗu yayi niyyaryi tareda Afeeyarsa kafin ya koma, abinda yake ji a ransa yasa baze iya cigaba da zama a Kano ba kuma baze koma France ba dan ya san kewa ce zatayi masa yawa, damuwar da yake ciki nunkuwa zatayi. Ahmad ne ya rakashi Abuja as usual a Ƙoƙarinsa na son nuna komai lafiya lau sedai Ahmad ɗin ya masa shiru ne kawai yana binsa a yanda yake so amma ya gano tabbas akwai abinda Jafar ya ke ɓoyewa, sanin menene kuma ya barwa Allah yana dai da yaƙinin ko meye idan lokacin daya kamata ya sani yayi base ya tambayeshi ba ze gaya masa. Ya masa magana dai akan Afeeyah saboda sun fita da Alhaji yace masa Baba Alƙali ya masa zancen an fasa zuwarwa Jay tambayar aure kamar yanda aka shirya a farko, daya tambayeshi dalili yace masa
"Mayaudariya ce Azzaluma, tana da wanda iyayenta suka fi so yake wahalta mata for ages so tayi ta yaidareni Allah yasa na ganota da wuri" ya bashi sa. Ahmad yace
"Kuma da gaske kakeyi ka haƙura da ita? Daman duk kurarin soyayyar nan a bakine ba gaskiya ba? Ai na zata se in har kaji an ɗaura mata aure da wani ne zaka sare ashe ma bada gaske kakeyi ba"
"Yah Ahmad kenan" abinda ya sake ce masa kenan daga nan suka bar maganar dan shima be jata ba. Daya kaishi Abuja a ranar ya juyo dan da sassafe suka tafi be kuma zauna ba ya masa sallama ya juyo dan akwai ayyuka a gabansa sosai da yake so yayi. Wannan tasa Jay ya kashe wayarsa dan baya so wani a gida ma yasan be tafi ba, seda ya shafe kwanaki biyu a Hotel room sedai yayi wanka yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana tunani. Duk ta yanda ya ke lissafa ze warwarewa Afeeyah se yaga daga ƙarshe abin akan Yah Ahmad ze ƙare. Ranar daya kwana uku ya gaji da kwanciya da dare ya shirya ya fita, mota ya ɗauka a Hotel ɗin ya fita ya ringa yawo a titin Abuja harya gaji, haka nan yaji yana kwaɗayin Shawarma dan haka ya tsaya wani guri dake kan titin daya biyo.
Yana tsaye gurin cashier kamar daga sama yaji an kira sunansa
"Jayyy" yanda taja sunan ya sanar masa da wacece, ita kaɗai take kiransa haka mamakinsa ya akayi ta ganeshi? Ya juya baya kuma kota gaba ta kalleshi fuskarsa lulluɓe take da facemasks saboda tsaro. Ya juya sosai yana kallonta, FATIYYAH MU'AZ ce, fuskarta ɗauke da murmushi me kyau take kallomsa itama, kafin yayi wani abu ta isa gareshi ta rungumeshi and he couldn't help it but to hug her back.
"When did you come back to Naija?" Ya tambayeta bayan daya raba jikinsu, hannunta sarƙe cikin nasa tana binsa da kallo kamar mayya tace
"Since last month, mun ma dawo duka nan ai"
"Wow, at long last" ya faɗa da wide smile. Ta kai hannu zata zare masa facemask ya riƙe yana girgiza mata kai ta ɓata fuska,
"Excuse me sir, your order is ready" muryar wata waiter ta katse shi tana miƙa masa ledar kayansa ya amsa har sannan Fatiyyah na manne rabi a gefensa ya kalleta yace
"Let's go". A tare suka fito daga gurin, motar daya zo da ita suka shiga suka zauna Fatiyyah ta shiga É—aukansu hoto bayan daya zare facemask É—in.
"Ki bari muyi magana mana" ya faÉ—a yana kwace wayar ta sakar masa tareda maida hankali tana kallonsa harda yin tagumi da hannu biyu.
"Idanunta irin na Afeeyah" ya raya a ransa, ya san Fatiyyah tun kafin yasan ze haɗu da wata Afeeyah a duniya. Yarinyar CBN governor ce, a London suka haɗu, friend ɗinta ce Asali budurwarsa Maryam se kuma suka fara Ƙawance da Fatiyyan sosai daga ƙarshe ma Maryam ɗin tayi aure wannan yasa alaƙarsu ta fara canzawa da Fatiyyan saboda tana nuna so takeyi suyi soyayya. Yes tana da komai da ze saka Namiji ya sota amma beji yana ra'ayinta a lokacin ba, abinda ya burgeshi da ita har yasa ya kasa man tata yanda ta kama kanta taja ajinta ta rabu dashi tunda ya nuna baya ra'ayinta saɓanin sauran yammata da suke naci suna binsa yana wulaƙantasu kamar mayu. Kusan three years kenan basu haɗu ba suna dai chat jefi jefi se yau Allah ya sake haɗasu.
Sunata labari a mota har seda Maman Fatiyyah ta kirata dan tace zata siyo shawarma ne yanzu ta dawo kuma tajita shiru wannan ya ankarar da ita daÉ—ewan da tayi a wajen sukayi sallama ya rakata motarta, Shawarman daya siya ma bata yayi suka rabu akan zeje gidansu da safe kafin ya wuce saboda yace mata probably ya wuce France zuwa jibi.
Bayan ya gama abinda yakeyi ya hau gado ya kunna Wifi ya shiga WhatsApp, status É—insa yayi updating da 'found a new love'. Badan yayi blocking Afeeyah ba tun a ranar zata gani, Ahmad ne ya fara buÉ—ewa ya masa replay da
"Who is the new catch"
"Some one that i deserve, and she deserves me" ya maida masa. Se Ahmad ya kirashi ta WhatsApp ɗin dan tunda ya tafi kamar yanda sukayi zato ta nan suke magana yaƙi kunna wayarsa.
"Jay dagaske kake ka haƙura da yarinyar nan wai?"
"Dagaske mana Yah Ahmad kasan dai sau É—aya nake so kuma if i hate something and turned my back against it i never go back to it" ya bashi amsa. Ahmad yayi murmushi yace
"Amma ko, da zan baka shawara da nace kayi haƙuri indai abinda ze iya gyaruwa ne tsakaninku ka gyara saboda i can tell you truly love that girl Afeeyah dan ban taɓa ganinka a irin yanayin da soyayyarta ta sakaka ba, kaga koda kake ganin kamar bani da zuciya akan Fatima ba haka bane ba, Ina sonta ne jikina da zuciyata ba zasu taɓa samun nutsuwa da wata mace ba bayan ita shiyasa nake jure komai saboda na sameta"
"Yanzu a baka zaɓi ni ko ita wanne zakayi choosing?" Jay ya tambayeshi, yayi murmushi yace
"Kai jinina ne ita kuma rayuwata ce"
"Ita zaka zaɓa kenan?" Jay ya sake tambaya Ahmad yace
"Aa, rayuwa ba zatayuwu ba seda jini yana kwaranya a jikin mutum kaga kenan ku É—in dafe kuke da rayuwata, rasa É—aya daga cikinku tamkar rasa nine"
"Yanzu kenan ba zaka iya sadaukar mun da soyayyarta ba idan na buƙata?" Jay ya sakeyi masa tambayar da se bayan ta fito yayi nadamar yinta. Ahmad yayi shiru har ya fara zaton ko wayar ta katsene kafin kuma yaji yace
"Zan kwanta cikin salama bayan na mutu idan har ka kasance kaine zaka maye gurbina ka tarairayi iyalina, amma fa dukda haka nasan se nayi kishi, amma karka sake faÉ—ar haka Alhalin ina raye amma da gaske kakeyi ko wasa wannan maganar?" Ahmad ya tambayeshi. Kamar wanda ake ingizawa Jay ya sake cewa
"Idan da gaske nakeyi zaka iya barmun ita?"
"Ta yaya wannan zazzafar Ƙiyayyar zata rikiɗa ta koma soyayya har ta samar da kyakykyawan yanayi na kwanciyar hankali a zaman aure? Kaifa kace ka tsaneta kamar mutuwarka" Ahmad ya sake bauɗewa daga daga barin bashi amsar abinda ya buƙata, cikin yanayi kamar na ƙufula Jay yace
"Toh ai baka amsa mun tawa tambayarba" se Ahmad ya saki sanyayyan murmushi yace
"Babu abinda bazan iya sadaukar maka ba Ƙanina amma ina son Fatima sedai son da nakeyi mata be kai wanda nake maka ba dan haka indai ita ce burinka zan bar maka ita". Da saurin gaske Jay yace
"Wasa nakeyi, kawai so nakeyi na gwada tsakanin nida ita wa kafi so amma Allah ya kiyaye me zanyi da wannan yarinyar? Ya za'ayi ma naso abinda kake so? Ai ko ina sonta na gane tilas na haƙura bazan taɓa takarar wani abu a rayuwar duniya da kai ba ko menene koda rayuwata zata salwanta a dalilinsa zan haƙura na bar maka shi".
Sukayi shiru na wani lokaci, a zuciyar Ahmad lissafi yake dalilin daya kawo Jay ya soko wannan maganar? Zancen Afeeyarsa sukeyi me yasa ze kawo maganar ya bar masa Fatima kuma? Shi ya kasa tattara abubuwan ma ya gane me suke nufi. Jay kuwa sake auna nauyin soyayyar da Ahmad yakeyiwa Fatiman yake a zuciyarsa, idan har ya zama silar rabashi da ita beyi masa Adalci ba amma be cancanci Azzalumar mace irinta ba mara tsoron Allah muguwa, Allah kaÉ—ai yasan dalilin wannan haÉ—i.
"Yau na haÉ—u da matata" Jay ya katse musu shirun, Ahmad yace
"Uhm, da wurwuri haka?"
"Dama ya kamata ace ita ce, rabon na sja wahala ne yasa na barta kuma yanzu Allah ya sake dawomun da ita cikin rayuwata bazan bari kuma ta kufcemun ba"
"Ikon Allah, ita kuma wacece ita?"
"Fatiyyah Mu'az" ya bashi amsa, Ahmad ya maimaita sunan da alama so take ya tuna koya santa can kuwa yace
"Fatiyyah Fatiyyah dai? Daman kuna tare har yanzu? I thought ma tayi aure itama kamar Maryam?"
"Nop batayi ba, we met not so long ago"
"Ayyah tana France kenan?" Ahmad ya tambayeshi, se yayi jumm daya tuna ashe ya kusa ya kwafsa kafin yace
"Eh, Aa, a Abuja muka haÉ—u kafin na wuce ai ta koma Nigeria ta gama karatunta"
"Allah ya tabbatar da Alkhairi" inji Ahmad da sam be gane kan Jay ba.
Washe gari yaje gidansu Fatiyyah kamar yanda yayi mata Alƙawari, Mamanta, Babanta da duka siblings nata sun sanshi sun kuma saba tun a lokacin da suke tare dan haka da yaje normal suka gaisa sukayi hira da Mamanta kafin ta basu guri. Sister ta ce ta ɗaukesu video a wayarsa da Fatiyyan ta karɓa ta bata sanda suka fito rakashi. Fatiyyan da kanta ta shiga tiktok tayi uploading video da Caption ɗin ~FATIYYAHJAY~, shi bema san dashi ba se bayan daya koma Hotel ya kunna router yaga messages ɗin friends ɗinsa da suka sanshi da Fatiyyan a da, kowa tambayar da yake masa "sun dawo tare ne?" Wasu suce they will make a perfect couple. Daman be bi takan comments na tiktok ɗin ba shiyasa ma bega saƙon Afeeyah ba dan normally idan yayi posting turning off comments yakeyi saboda bashida lokacin dubawa, washe gari ya koma France yayi resuming field har sannan kuma zuciyarsa ba'a sake take ba.
Mixed feeling yake dashi akan Afeeyah, Soyayyar da yake mata na neman ta hana tsanarta daya fara tun usuli cigaba dayin tasiri a ransa. Sabon babin da suka buɗe na Ƙauna da Fayiyyah ne yake ɗebe masa kewa. Fatiyyah na sonsa, so na gaske, a gefensa zece yana sonta amam ko rabin yanda yakejin Afeeyah har a yanzu cikin zuciyarsa bata kamo ba amma kuma yana jin a ransa ze iya auranta yanzu musamman da yake neman ruwan kashe gobara shiyasa yake iyakar ƙoƙari gurin ganin ya maida mata da kwatankwacin soyayyar da take gwada masa. Abu guda da yake haɗa shi da Fatiyyah rawar kanta kuma tun asali abinda yayiwa tarayyarsu tasgaɗo kenan yar gata ce da bata san komai ba se a tattalata a jiyar da ita daɗi, irin soyayyar da sukayi da Afeeyah wadda da acw a baya ne ko wani ya gani yana kalarta cewa zeyi baƙauye ne a yanzu ita yake muradi a gurin Fatiyyan sedau wayewarta tayi yawa nata salon soyayyar na manyan yara ne masu buɗaɗɗun ido irin wadda take burgeshi a da kenan yanzu kuma soyayya me tafe da sirkin kunya data ɗanɗana a baya ita yake muradin sake samu amma Yah Ahmad ya yi masa tsakani da ita.
A ta gefen gidan Alhaji Audun Bechi kuwa rayuwa ce take ta gurgurawa yau fari gobe baƙi, Malam Hafizu ya cika maganarsa kamar yanda yace a bashi sati huɗu shida kansa ya kira Baba Alƙali ya shaida amsa ya shirya suna iya zuwa sannan. Da Alƙalin ya gayawa Alhaji Audu se cewa yayi ba za'aje ba, wai yar ta gwal ce da har se ya bawa mutane lokaci sanda yaga dama sannan za'aje neman auranta?
"Kota zubardaji ce ba Gwal ba wannan ba matsalarka vace ba, ma'aurin yace yaji ya gani seka kawo idanu ka zuba yanda ka sabayi a lamarin auran sauran yarorinka, karka cusa bakinka ciki muddin ba Alkhairi zaka saka musu ba" Alƙali ya dakatar dashi. Alhaji Audu yace
"Nifa kawai auran yarinyar be kwantamun a zuciya ba, tunda yana jin maganarka ka bashi baki ya nemi wata ga yayan manyan mutane nan yan Asali ko yaushe ne seda Alhaji Madari yamun maganar yarsa yace ko shi ko Jafaru..."
"Ai kasan shi Jafaru uwarsa ma ta isheka shiyasa ba zaka somo dashi ba wannan kuma daya zama karkatacciyar kukar kowa me daɗin hawa dole ka nemi hanashi abinda yake so. Ni daman na daɗe da sanin bawai Binta ce kaɗai shaiɗaniya ba, hali ne ya tarar da hali kaida itan shiyasa zamanku yayi tsayi.. To ni duk ba wannan ba, zancen muhalli a ina zauna?" Cewar Baba Alƙali.
Alhajin Bechi ya karkace yace
"Yanzu Ahmad kake tambayar i
FATIMA
Kafin cikar wa'adin da Baffah ya yanka ta tattara ta koma makaranta kowa ya ganta seya tambayi me yake damunta se tace musu rashin lafiya tayi saboda yanda ta fita a hayyacinta kana ganinta kasan bata da nutsuwa sam. A bakin Anty Sauda taji cewar Baffah ya kira Kawun Ahmad kamar yanda ya roƙi su bashi sati huɗu lokaci ya cika kuma ya gama uzurin da yake a gabansa yanzu dan haka duk sanda suka shirya suna iya suje.
Anty Saudan dai ta sake shaida mata Ranar Juma'a yan gidansu Ahmad zasu zo, Ranar kwana tayi tana kuka har wani zazzaɓine ya sake saukar mata ta ringa sake gwada kiran Jay da tura masa saƙonni ta kowacce kafa da ta san tana samunsa a baya amma a banza kamar me aikawa lahira. Sanda ta samu saƙon sunje har an tsayar da maganar auransu watanni shida masu zuwa kusan suma tayi dan a tsaye take ta sulale ta zauna seda aka jijjigata kafin ta farka daga suman zaunen ta kuma fasa musu kukan da tun suna bata baki da tambayar meya faru har kowa ya gaji ya rabu da ita, Maman Minal ce ta kira Anty Sauda dan taji ko mutuwa akayi a gida akan sanar mata, bata fiya zafi ba amma ranar seda ta warwarwa Afeeyah tayi mata tatas wai dan ma Badar bata nan ta tafi Kd dan har sannan Jikin Babansu se a hankali an dawo dashi dai amma duk weekend a gida takeyi Friday basa komai ranar take tafiya ta dawo Sunday bata ma san da zancen kawo kuɗin ba yanda Afeeyar bata gaya mata ba itama yanzu ta dena damun kanta da matsalarta, ta dai gaya mata yanda suke ciki da Jay ta kuma jimanta mata ta sake nusashsheta abinda ake mata hasashe kenan sanda suke ce mata karta saki jiki dashi shikenan ta kama kanta ta rabu da ita tunda bata ga alamun zata hankalta ta gane Allah guda bane domin har sannan cewa take Ahmad ne ya janyo mata zuwansa ne ranar ya ruguza komai.
Sati tsakanin zuwarwa Ahmad tambaya akaje na Jay, a bazata batun ya zowa kowa harda Ahmad da ita kanta Hajiyar seda aka saka ranar zuwa taji labari a bakin Alhaji Zakariyyah, data zabura zatayi bala'i se kuma tayi laƙwas kamar Tarwaɗa taji gishiri ta shiga zare idi dajin Yar wacce za'aje tambayowa Jay auranta. Se gani kawai Alhaji Zakariyyah yayi ta fashe da kuka, a zatonsa kukan bata sani bane kamar yanda ta tasammayin tijara a farko seda yaji tana cewa
"Ashe dai burina ze cika, Jafaru ze farantamun ya wanke mun takaicina Allah na gode maka kace dai ya gidan gwaunan bankin Najeriya ce ko ubana?" Zakariyyah murmushi kawai yayi dan yanda Hajiyar ta keyi kamar wata yarinya, daya tana neman ta ishe shi da tambayoyi ya fice ya barta ta shiga bige bigen waya tana sanarwa su Turai abin Arziƙin daya samesu. Ahmad kuwa Baba Alƙali ne ya kirashi yace ya shirya zasuje Abuja neman auran Jay, yayi mamaki, ko awa guda basu cika da gama magana da Jay ba amma beyi mentioning masa zancen auran ba koda yake duk Jay ɗin ya canza ya kuma kasa gane kansa balle abinda yake damunsa. Daya samu labarin shiru yayi be ce masa komai ba, a ransa yayi murna zasuyi aure lokaci ɗaya kamar yanda birinsu yake tun suna yara.
Juma'a Baba Alƙalin yace zasu tafi su kwana a can Asabar idan sun gama abinda ya kaisu su juyo a ranar shi kuma yayi niyyar tafiya Zaria gurin Fatima wadda tun bayan Baikonsu Al'amura suka fara sauyawa a tsakaninsu, a yanzu base ya kirata ba takan kirashi da kanta dukda dai babu sakewa ko soyayyar da yake fatan samu daga gareta amma a hakan shi ji yake kamar yafi kowa farin ciki ba kuma shi da wata damuwa dan haka ya kirata ya sanar mata da baze samu damar zuwa ba zasuje Abuja neman ma Jafar Aure, bata nuna taji ba balle ya saka ran zata sakawa lamarin Albarka. Ita kuwa sunan Jafar daya ambata mata tamkar fami ya zamar mata kan nata Jafar ɗin da har yau bata dena kukan rasa shi ba, dangana tayi ta ta kuma buɗe zuciyarta ta fahimci abinda aka daɗe ana nusashsheta amma ta doɗe zuciyarta da idanunta taƙi fahimta a yanzu ne ta ke godewa Allah domin nacin Ahmad ya mata rana domin da ace ya barta tamkar Jafar bata san wa zata kama ba.
Ita da kanta ta yarda haɗuwarta da Jafar da soyayyarsu har zuwa rabuwarsu haƙƙin Ahmad ne, ta godewa Allah daya bata damar gane kurenta harya yasa tana da sauran lokacin da zata iya gyarawa, sedai aka ce So ɗayane, har yau har gobe tana son Jay, bata sani ba ko se ranar data tabbatar da ta zama mallakin waninsa sannan zatayi jana'izar soyayyarsa ta binneta badan ta mutu ba.
Baba Alƙali, Alhaji Babangida, Alhaji Abdullahi, Zakariyyah Bechi, Naziru Bechi, da Ahmad Bechi da se Aminan Alhaji Audu na ƙut da ƙut Alhaji Mu'azzamu da Alhaji Aliko sukaje neman auran saɓanin na Ahmad da Baba Alƙalin ne tareda Alhaji Abdullahi sukaje, ya sanarwa Alhaji Babangida lokacin ya bashi uzurin ranar ze tafi Umarah dalilin daya saka ba'aje dashi ba. Harka akayita girma, aure ake shirin yi irin wanda ake kira ƙwarya tabi ƙwarya. Shima kamar Ahmad watanni shida aka saka, suka dawo Kano niƙi niƙi da kayan arziƙin da aka haɗo su dashi. Hajiya bata iya bacci ba, tun daren Juma'a take dokawa Naziru kira daya gaji da amsa ma yayi restricting number, yanda kasan zatayi tsuntsuwa ta tafi can haka tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye har seda suka dawo abubuwan da suka zo dasu suka gigitata haka ta fita tsakar gida tana taka rawar murna tareda sakin habaici wa Momy da ko biskit ba'a kawo mata daga gidan Surukan Ahmad ba sanda akaje neman aure sun dai kawo tukucin naira dubu hamsin wadda aka cire musu daga dubu ɗari biyar da suka kai kuɗin aure da saka rana. Shima Jay ɗari biyar ɗin aka kai dukda Hajiya tace tayi kaɗan Baba Alƙali dashi ya bada kuɗin daman yace haka yayi niyya kuma baya isa ta saka a ƙara ba ko Zinariya ze auro.
Bayan sun dawo Ahmad ya kirashi murya a sake sam be riƙi cewar Jay ya zame shi daga abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarsa a yanzu ba ya shiga tsokanarsa da Ango Ango. Seda suka gama barkwanci kafin yace masa
"Amma fa na É—anji babu daÉ—i, ni ya kamata nayi breaking news na auranka bawai naji labari daga sama ba, amma ya wuce ,I'm happy for you, I'm happy for us, at long last mun kusa mallakar muradan zuciyarmu"
"Ka kusa mallakar muradin zuciyoyinmu nida kai dai" Jaya ya raya a ransa a fili kuma ya marairaice yace masa
"Kunya nakeji, bansan taya zan gaya maka ba". Dariyar da Ahmad ya ringayi har seda ya sauka daga kan kujerar Momy da yake zaune, seda yayi me isarsa kafin yace
"Amma bakaji kunyar kanka ba da kake faÉ—ar wannan maganar? Ni zakace kana jin kunya ba zaka iya gaya mun za'aje neman maka aure ba? Ai shikenan amma ko na ji tausayin Afeeyah ne sunanta ko? Allah kaÉ—ai yasan yanda zataji idan labarin nan ya iske ta".
A fusace Jay yace
"Allah yasa ya zama silar Ajalinta ma kowa ya huta Annamimiya me fuska biyu munafuka kawai"
"Jafar me yake damunka? Me yasa baka da magana seta fatanma wani mutuwa haka kawai san kana da matsala dashi? Babu kyau tsananta Ƙiyayya, ina jiye maka tsoron kar a jarabceka da abinda kafi ƙi a rayuwarka wlh seka gwammaci kida da karatu" Ahmad ya faɗa in a serious tune se Jay yace
"Na nawa kuma? Jarabta ai an mun sedai nayi addu'ar Allah ya bani ikon cinyeta kawai amma batun wai wani waye tuni an wuce gurin"
"To karkayi saɓo Malam nikam se anjima, daga kira muyi farin ciki kar ka jawo abinda rayukanmu zasu ɓaci, haba, kanka aka fara kasa Namiji a neman aure da zaka ɗauki abu da zafi ka hana rayuwarka sakat? Duk ka canza daga Happy Jay ka koma wani Aggressive person akan me? Ita rayuwa daman ai tilas akwai samu akwai rashi ba kuma dole duk abinda mutum yaso ace ya same shi ba. Nasan zafin So amma idan ka kasance me neman zaɓi da yardar Ubangiji cikin dukkan lamuranka koda zakayi fushi da wani abu daya sameka a rayuwa ya zama na ɗan lokaci, Allah ya fika sanin dalilin daya saka ya hakana samun wannan abun naci da dagiyarka se ta janyo maka abinda zaka zo kana dana sani da nadama mara amfani a rayuwarka se Allah ya barka da abin yaga iyakar gudun ruwanka. Ga rabonka nan ka dace da ita, kayi addu'a Allah yasa ta zamo maka sanyin idaniya macen da kowanne Namiji yake fatan samu"
Da "In sha Allah" Jay ya amsa masa shikenan aka gama wayar saboda ya sake goga masa gishiri akan rauni. Tun haɗuwarsa da Afeeyah yake hasaso yanda wannan ranar zata kasance musu, ranar da za'ace yarjejeniyar aure ta Ƙullu tsakaninsu, yaci burin zuwan lokacin har party yace ze shirya se gashi tazo masa da wacce be taɓa koda hasaso zata zama matarsa ba. Gaba ɗaya ma yanda abubuwa suke faruwa shi baze ce ga shi ba kawai dai komai yana faruwa ne tamkar shirin film kamar wasa yanzu an tasarma zuwa No going back stage
"Ya rayuwarsa zata kasance da watan Afeeyah???" Tambayar da ke kara kaina cikin zuciyarsa.
Shirin biki ya kankama a gidan Alhaji Audu Bechi. Shiri akeyi tamkar a wannan karon ne za'a fara aurar da ÆŠa a cikin gidan dukda shirin tsakanin Yayan cikin gida ne na waje dai nasu ido. Hajiya Binta tamkar zata haukacw saboda yanda ta azawa kanta tashin hankali akan wannan aure da Jay zeyi, Turai da Hajiya Zainab ne kan gaba akan shirin Komai, su suke haÉ—a Lefe, kuÉ—aÉ—e masu nauyin gaske ya aika musu na haÉ—a lefen. Me hali baya fasa abinsa, duk irin zumuÉ—i da zirgillin da Hajiya takeyi akan shirin Bikin da aka zo batun haÉ—a lefe taga uban kuÉ—aÉ—en da ake narkawa domin Turai tsakani da Allah ta tsaya take abun nan Hajiya ta rikice tace bata san zance ba ta yaya za'aje ana siyan Lesuna na dubu dari biyar zuwa sama ai Almubazzaranci ne.