Complete Hausa Novels

Matar Mutum Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Mutum_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 11

PAGE 23
"I'm fine, i just missed a step" Jafar daya yunƙura ya tashi da taimakon Ahmad ya faɗa. Ko kusa Ahmad be kama zancen wai lafiya yake ba domin idanunsa sun ƙaryata hakan sannan damuwa ta nuna ɓaro ɓaro akan fuskarsa dukda a lokacin be karanci yanayin nasa a matsayin damuwa ba, to wace damuwa ce haka zata samu Jafar. Yana riƙe da hannunsa kamar yaro gudun karya sake faɗuwa su ka kai ɗaki duk yanda Jafar ke ce masa ya barshi ze iya tafiya be saurara ba. Ahmad yayi mamakin da Alhaji be leƙo ba duk salatin da ma'aikatan gidan suka ringayi kuma yana zaune a falo ya tabbatar ma ya hango me yake faruwa dan a buɗe Ƙofar take, Jay ya kwanta akan gado tareda juyawa Ahmad baya, gani yake idan suka cigaba da haɗa ido ze karanto abinda yake ƙoƙarin dannewa ba kuma ya so ya fahimta.

"Meya sameka Jafar? What did you take?" Ahmad dake tsaye akansa ya tambayeshi, Jay ya juyo, kafin ya kai ga bashi amsa aka banko ƙofa, tashin muryar da sukajiyo gabanin buɗe ƙofar yasa suka gane wacece
"La'ilaha illallahu shikenan magauta sunyi nasara akaina na shiga uku ni Binta na lalace jifa ya tarar da Jafaru" ta faÉ—a hannaye biyu dafe da kai tana jijjiga. Jay ya tashi zaune Ahmad kuma ya matsa gefe can ya jingina da bango yana kallon Hajiya seta kuma juya a fusace kansa tana cewa

"Aniyarka ta bika wallahi tallahi duk wani mugun abu ya ƙare akanka, wato ka ƙunsheshi a ɗaki kana jira ya mutu seka fito dashi ko?"

"Haba Hajiya wai meye haka kikeyi? Wace irin magana kike haka dan Allah?" Jafar ya katseta cikin ɗacin rai, ko wane munafuki ne yaje ya gaya mata se Allah, salon tazo ta Ƙara masa damuwa kan wadda yake ciki. Hajiya ta juya kansa tana cewa

"Banza sallamamme dabe san ciwon kansa ba, wato ya tattareka ya kaika ta yuwu ma tuni ya sadaukar da kurwarka shine yau ya kai musu kai su lashe, to billahillazi kurwarka ɗaci ne da ita ba zata ciwo ba sedai ya musanya musu data tsohon ubanku da dama yaci yanzu ya matsa ya bar mutane su sarara, taso muje ai inada sauran Tazargade da tsakin kuka yanzu zan turara maka su koma wane shegen maye yayi gigin taɓaka sedai ya cinye kurwarsa wlh" ta matsa ta shiga janyo ƙafafunsa kamar wani yaro ƙarami. Da iyakar ƙarfinta take jansa hakan yasa ya miƙe dan dole yana mata mitar abinda takeyi. Ko a jikinta ta tasashi gaba, ta waiwaya ta gallawa Ahmad dake nan tsaye yana kallon ikon Allah harara kafin tace

"Waya sani ma ko kaima har sun lasa maka, to wlh nafi ƙarfin ƙaramin maye irinka manyan ma nan zasu ganni su barni". Dariya ta bashi dan har seda ya murmusa kafin ya zauna akan gado bayan da suka fice ta tasa Jay a gaba. Kwanciya yayi rabin jikinsa na kan gadon Ƙafafuwansa na ƙasa ya tallafe kansa da hannu biyu ya zubawa POP dake ɗakin ido. Meya samu Jay? Wane abu ya fara ko kuma yake aikatawa daman can dabe sani ba? Meya janyo sauyawarsa tun bayan daya dawo yake abubuwa ba tareda ya sakashi a ciki ba? Shi damuwarsa ba rashin including nasa da Jay bayayi a sabgoginsa bane ba Aa yanda yake abubuwan a Ƙudundune ne kamar mara gaskiya. Jay da ko Ƙofar gida muddin yana nan baze fita shi kaɗai ba seya rakashi amma shine ya iya tafiya har Abuja ba tareda rakiyar Ahmad ɗin ba, wannan be bashi mamaki sosai bama akan zuwa gidan Baba Alƙali da yayi nan ma shi kaɗai. Yanzu sun fita lafiya ya dawo cikin wani yanayi daya kasa fassarashi. Babu wata alama a tattare dashi da zata nuna maye ko wani abu makamancin haka sannan daka kalle shi kasan baya cikin hayyacinsa, Fargabarsa da damuwarsa yasan menene yake damun Ɗan uwansa a yanzu.

Fatima ta faÉ—o masa a rai ya zaro wayarsa daga Aljihu ya kirata dan yaji ya anta ciwon kan amma bata amsa ba se ya soka wayar a chaji ya tashi, seda ya cire T shirt É—in jikinsa ya mayeta da Jallabiyya kafin ya fita dukda goma ta gota ya shiga cikin gida. Momy da Maimuna tareda Sarah autar Hajiya Binta suna zaune a falo, Momyn na kallo su kuma suna aikin filling Samosa.

"Manyan yan kasuwa" ya zolayesu bayan daya zauna suka gaishe shi. Sarah tace
"Dan ma Yaya kaƙi ka bari mu fara kaiwa Mall ɗinka ai da wlh da yanzu munfi haka"

"Wannan jagwalgwalon ze bari ku kai musu?" Momy ta faÉ—a se yayi saurin cewa
"Haba ba jagwalgwalo bane Momy gyare gyare mukeyi shiyasa ma ban amsa musu ba amma da mun gama bayan frozen har soyayye zasu ringa kaiwa ai naci naji da daÉ—i kuma na yarda da tsaftarsu".
Sarah da Maimuna suka tafa cike da jin daÉ—i kafin suka shiga tattare kayan aikinsu dan daman sun gama suka wuce kitchen. Bayan shigewarsu Momy ta kalli Ahmad tace

"Ina kukaje da Jafar ne uwarsa ta shigo ɗazu tana ta hayagaga da faɗar maganganu?" A taƙaice ya bata labarin fitarsu zuwa dawowarsu da kuma abinda ya faru yanzu a waje. Momy tace
"Allah ya rufa asiri toh, ta yuwu ko bashida lafiya musamman tunda ya dawo be zauna guri guda ba yana ta stressing kansa ga Ranar kwanakin nan da zafi ba irin wadda ya saba da ita bace, daman É—azu ina falon Alhaji Babanku ya kirashi yake gaya masa Jafar yaje gurinsa akan maganar zuwa tambayo masa aure ko?"

"Eh haka ne" ya bata amsa ta sake cewa
"A ina ne?"
"Wlh ban sani ba, yau mukayi zamuje kuma ya tafi ya barni"
"Au kaima baka sani ba? Koda yake ai na fuskanci kwanakin nan uwarsa ta matsa masa ni tunda ya dawo ma sau biyu ya shigo falon nan
"Uhm" kawai yace mata jin haka yasa itama tayi shiru da maganar can ta sake cewa

"Toh ya kukayi da ita Fatiman? Babanta yace a bashi sati huÉ—u me tace maka akan hakan?"
"Bamuyi maganar ba Momy amma daman Baban nata yace ai wanda zasu karɓi auran ne basa nan shiyasa yace a basu lokaci amma ko ɗazu ma mun haɗu yace yana gaishe ku"

"Toh muna amsawa, ya kamata dai a fara abinda ya kamata dai toh, bari kaga wasu Atamfofi ɗazu *UMMU-MAHEER 07061838488* ta turasu a group ɗinta *BUYERS BATIK/ALIZA BATIK* ne kyau garesu quality kuwa ba'a magana gasu unique designs babban abin da yake burgeni dasu seka gama yayin Atamfar nan baka ci karo da me irinta a gari ba gasu basa koɗewa sedai ka gaji ka bayar kai *BUYERS BATIK* fa ta haɗu" ta ƙarasa tana miƙa masa wayar.

Ba wani sanin kan Atamfa yayi ba dan yafi ganin kyan Lace shi a jikin Fatima nema Atamfar take burgeshi amma yana ganin *BUYERS BATIK* ɗin ta tafi da imaninsa. Ya ringa scrolling yana duba designs ɗin da duk babu na banza a ciki, harya hasaso su jikin Fatima dan kalolin duka zasu karɓeta. Ya maida wayar yana cewa

"Amma sunyi kyau Momy"
"Ƙwarai ma kuwa, guda nawa za'a ɗauka?" Momy ta tambayeshi se yace

"Ki zaɓi wanda kike so se ki ɗaukarwa Maimuna ma nawace?" Ya mayar mata cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa. Ta harareshi tace
"Tun yaushe muka zaɓi tamu, maganar lefenka nakeyi guda nawa za'a saka ko kuwa seta ƙare sannan?" Se ya hau shafa kai irin na yaji kunya kafin yace

"Ai duk sunyi kyau ma"
"Se a saka duka design goma ce" daga nan suka cigaba da tattaunawa wanda duk maganar auransa Momyn take sako masa.

Jay kuwa bayan sun isa falon Hajiya kwanciya yayi akan kujera tana ta aikin mita ta tafi can kitchen ɗinsu na baya inda suke hura Itacen da ita ta saka dole ake amfani dashi ta samo garwashi a cikin kasko. Tsabar magana tana zuba maganin a wutar seda hayaƙi ya turniƙeta ta fara tuttula tari har bata san sanda ta ture kaskon nata ba gaushin ya zube Allah ya rufa asiri akan Tiles ne carpet ba. Kansa kamar ze tsage masa haka ya tashi ya ɗakko ruwa ya kashe garwashin ya bawa Hajiyar tashi bata daddara ba faɗi tajeyi
"Shikenan ashe ba kai kaÉ—ai sukayi galaba akanka ba harda ni"

"Dan girman Allah Hajiya ki bari, ni lafiyata ƙalau na gaya miki gajiya nayi kawai bacci bake da buƙatar nayi yanzu" yanda yayi maganar ya saka Hajiya binsa da kallo shi kuma jin bata ce komai ya juya yana tafiya daƙyar saboda yanda zuciyarsa tayi masa nauyi Hajiyar kuma bata dakatar dashi ba. Kan gado ya kwanta ya rufe idonsa, wayarsa ta shiga ƙara a Jikinsa yaji cewar itace. Wani ɓari na zuciyarsa na rasa masa ya amsa ya tambayeta dalilinta na aikata musu abinda tayi inda ɗayan yayi galaba ta hanyar hanshi amsa wayar. Jin muryarta a yanzu babu abinda ze ƙara masa se baƙin ciki da damuwa. Har yanzu gani yakeyi kamar bada gaske bane, dukda a zahiri yaga komai ba gaya masa akayi ba amma so yakeyi ya ƙaryata hakan ya cewa zuciyarsa ba gaskiya bane ko kuma komai be faru ba.

Idanunsa suka sauka kan wayar Ahmad da yake chaji ya yunƙura daƙyar ya ɗaukota kansa na sara masa kamar ze tsage biyu. Number wayarta ya shiga dialing yana fatan ya zaman babu ita a wayar sedaj yana saka 0803 numbarta ce ta farko data zo a suggested contacts ga sunan da Ahmad ya mata saving dashi FATIMA da manyan baƙi se Jan Emoji me alamar zuciya a gaba. Ya runtse idonsa da ƙafin ya buɗe WhatsApp a hankali ya ringa bin chats ɗinsu kamar mr bitar karatu yana cike guraben maganganunta da ire iren daɗaɗan kalaman da take amfani dasu gurin magana dashi wanda saɓanin haka chat ɗin nata da Ahmad babu wani armashi balle soyayya a ciki. Ya ga hotunanta da basu da yawa idan aka haɗa da wanda ta tura masa shi daga haɗuwarsu zuwa yau ɗin, wato yarinyar first class maƙaryaciya ce, ma ha'inciya kuma Azzaluma.

Ya tuna wayarsu ta farko data tambayeshi ko shikaɗai Jay ɗan Nigeria dayake ƙwallo, me yasa tun a sannan be taɓa hasaso cewar ita ce ba?

Maida masa da wayar yayi jikin chaji ya kwanta rubda ciki ya danne kansa da pillow. So be kyauta musu ba daga shi har Yah Ahmad su rasa wadda zasu so se wannan Azzalumar mara tsoron Allah. Shi ya gama tabbatarwa ma da tasan su, tasan gidansu ɗaya shirya komai tayi ya kuma godewa Allah daya saka ya ganota tunda wuri kafin tayi nasarar karya zuciyar ɗan uwansa da babu komai cikinta face tarin Alkhairi da son kyautata mata. Yana jin Ahmad ya shigo lokacin kuma wayarsa ta sake ɗaukan ƙara a karo na babu Adadi amma be amsa ba se Ahmad ne daya shigo ya janyo wayar daga gefen kansa inda ya ajiyeta yana cewa

"Na gaya maka ka dena aje waya kusada kanka idan zakayi bacci bakaji kuma duk wannan ƙarar yanzu se kace baka ji ba toh Afeeyah ce kar gobe kazo kana mun kukan ta ƙi amsa wayarka".

Da hannu yaja wayar ya latseta gaba ɗaya ta mutu ba tareda ya amsa ba, Ahkad yayi sororo yana kallonsa, da kuma ya tuna ba matsalarsa bace se yaci gaba da abinda yakeyi ya gama yayi shirin kwanciya yabi lafiyar Gado. Zafin jikin Jay daya matseshi ne ya farkar dashi daga bacci dan shi bashida nauyin bacci ko kaɗan, ya taɓa Jay ɗin, zazzaɓi ne rau a jikinsa har numfashinsa hucin zafi yake fitarwa amma bacci yake wanda da gani bana daɗi bane. Ruwa ya samo me madaidaicin sanyi da ƙaramin Towel ya jiƙashi ya fara shafa masa a fusak, Jay ya saki ajiyar zuciya ya buɗe ido daƙyar ya kalli Ahmad ɗin kafin ya lumshe su. Da taimakon ruwan daya shafa masa da Maganin daya saka ya tashi yasha a lokacin zafin jikin ya ragur masa se Azababben ciwon kai da yakeji kamar ƙwayoyin idonsa zasu fito, kafin safiya ya fita hayyacinsa Idonsa yayi Jajir ga jijiyoyi a goshinsa kamar zasu faso su fito, yanda jikinsa ke karkarwar sanyi bayan yayiwo Alwala ya saka Ahmad dakatawa sukayi sallah a ɗakin sannan ya kamashi suka fita a duku dukun suka tafi Asibiti.

"Wai me ya same ka? Lafiya kau muka rabu jiya meya sameka a can in da kaje kuma?" Ahmad ya tambayeshi. Cikin dauriya yace masa
"Inaga Malaria ce, kwana biyu sauro ya cije ni"
"Sedai a gidansu Afeeyan ka kwaso Malaria dan mudai gidanmu babu sauro, kafin kazo seda akayi fumigation kuma still kullum se an saka magani, kuma Malaria ce zata kwantar da mutum haka lokaci ɗaya? Zamuje Asibiti dai koma menene yake damunka da baka so na sani zasu gayamun" Ahmad ya faɗa, shidai Jay be sake ce masa komai ba fama yake da jinyar fili data zuciya, abune goma da Ashirin yayi masa rubdugu lokaci ɗaya. Yarinyar daya ɗora dukkan buri da tanadinsa akanta, Macen da yake So tamkar ransa, da ita yake fatan ƙare rayuwarsa lokaci daya ta rikiɗa ta dawo Macen daya fi tsana a duniya, tun saninsa da ita yake jin ƙinta tun kafin ya ganta yasan wacece ita, abinda tayi musu a yanzu ya sake linka tsana da ƙiyayyarta me tsanani a zuciyarsa. Ya gane dalilin daya saka jininsa da ita a matsayin budurwar Ahmad ya ƙi haɗuwa, Soyayyar da sukayi a rashin sani wannan ya karɓeta a matsayin sakayyar abinda yake gayawa Ahmad dalilin soyayya da ita, Ubangiji ne ya nuna masa isharar cewa shi yake ƙunsa So a zuciyar bayinsa bawai yin kan mutum bane ba amma ya tsinewa dalilin zuwansa Zariya da har yayi silar haɗuwarsa da wannan Annamimiyar yarinyar me suffar salihai.

Asibitin Dr Hassan ya kaishi, basu tarar dashi ba se Dr Michel da yayi night duty shine ya dubashi. Ahmad yana waje yana jiransu dan daya shigar dashi fitowa yayi ya basu privacy. A ciki bayan Dr ya gama auna Bp sa saboda ciwon kai da yake shi yake damunsa kuma ido da fuskarsa ma sun nuna hakan. Cikin tsanaki ya kalleshi yace
"Bp ka yayi high sosai also rate na heart beat naka ya zarce misali me yake damuka?"

"Forget about it Dr, kawai ka bani necessary assistance and please don't tell anyone about it ka cewa Yah Ahmad Malaria ne yake damuna" Jay ya faɗawa Dr Michel, Dr ya zura masa ido ya buɗe baki da niyyar sake masa magana Jay ya haɗa hannaye biyu alamar roƙo yace
"Please, do me this favor"
"Fine amma dole koma menene ka cireshi daga ranka saboda lafiyarka ta daidaita ka sani this will not be good for your career and..."

"I know Dr i will try my best" ya sake katse shi. Dr ya girgiza kai kafin ya danna Ƙararrawar kiran Nurse se gata ta shigo. Paper daya rubuta prescription wa Jay ya bata ta tafi ta haɗa komai ta kai ɗakin da zasuyi admitting nasa zuwa Bp ya daidaita sannan ta koma ta gaya masa. Da kansa ya kamashi suna fita Ahmad ya tayashi har zuwa ɗakin, ruwa ya saka masa wanda ya zuba Allurai a ciki harda ta bacci babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba dashi. Cikin damuwa Ahmad ya shiga tambayar Dr me ya samu Ƙaninsa yace masa Malaria ce. Ganin ya samu bacci yasa ya koma gida, Alhaji ya fara sanarwa Jay bashida lafiya yana Asibiti

"Toh Allah ya bashi lafiya, se a sanarwa uwarsa ai" Alhajin ya bashi amsa, se yaji abin wani banbara kwai ba yanda Alhajin ya saba ruwa da tsaki a lamarin Yayan Hajiya ba, koda yake daman ko a cikinsu basu fiya jituwa da Jafar ɗinba saboda rikici da taurin kansa sak irin na Alhajin ne dukda yanda Hajiya take so ya zama yafi kowa shiga jikinsa amma abin yaci tura shiyasa take baƙin ciki da shirin da sukeyi da Ahmad a yanzu. Daya gayawa Hajiya kuka ta ringa zundumawa harda tumami a Ƙasa tana kiran ta shiga uku ta lalace shike nan magauta sunci galaba akanta. Ta tattara ta tafi Asibiti can ta tare ita da jama'arta da surukanta data ringa wa waya tana gaya musu suzo an jefe Jay gashi kwnace magashiyyan a gadon Asibiti, Turai ta tafi mata tambaya dan su binciko wanda ya taɓa Jafar ɗin, Momy da Anty sunje sun dubashi da daddare se sannan Ahmad ya koma saboda Hajiya da take a gurin tana ta faɗar maganganu akansa, Alhaji ne yace shi yaje ya kwana da Jafar ita da jama'arsa kowa ya watse ya koma gida. Daze tafi ya tafi masa da wayarsa wadda yaga Missed calls ɗin Afeeyah sunfi Ashirin ga messages nan birjik na ban haƙuri akan laifin da besan me ta masa ba.

Ya jefa wayar a Aljihu, besan password É—insa ba daya buÉ—e wayar ya kirata ya sanar mata abinda yake faruwa kodan hankalinta ya kwanta. Yana dabda shiga Asibitin ta sake kira ya amsa cikin nutsuwarsa yayi sallama.

FATIMA
Tana shiga cikin gida kaitsaye É—akinta ta shige tana jiyo Umma da Baffah suna magana Baffa yana cewa
"Wlh Ruƙayya ban taɓa zaton haka zanji nauyin yaron nan ba, badan fa ya rigada ya ganni ba juyawa nayi niyyaryi amma babu dama"

Umma tayi shewa tace
"Malam, ai baka ma soma jin kunya ba se ranar daya fahimci yaudarar daka shirya masa kaida yarka, billahillazi in bakayi wasa ba seka gagara fita na wasu kwanaki saboda zancen mutane da nunaka da za'a ringayi". Sama sama take jiyo mahawarar Baffa da Umman, ta zauna kan katifa tana dafe da ƙirjiz seda ta nutsu kafin ta latsa kiran layin Jay tana so taji ina ya tsaya tunda Allah ya taimaka ta sallami Ahmad yanzu se yazo. Wayar ta ƙaraci ringing be amsa ba ta sake kira nan ma dai shiru seta ajiye a zuwan ko yana hanya idan ya iso ze kirata amma shiru shiru har sha ɗaya babu Jay babu dalilinsa kuma be biyo kiranta ba zuwa sannan kuma hankalinta idan yayi dubu ya tashi to me ya faru? Kar dai yazo ya ganta tareda Ahmad shiyasa yayi zuciya ya tafi kuma yaƙi amsa wayarta.

Data sake kira tana fara ringing aka katse, cikin sauri ta sake gwada kiran a zatonta ko garin ya amsa ne ya katse ita bama zata iya jira ya kirata ba sedai a karo na biyun aka shaida mata wayar a kashe take. Ta kwanta lamo hawaye na zubowa daga idonta, rejecting yayi kuma ya kashe wayar dan karta dameshi ta tannata yazo ya ganta tareda Ahmad kenan.

Tsohuwar wayar dayace ta dena amfani da ita ta ɗauka ta saka sim ta kunna Data, WhatsApp ta shiga dan ta duba ko yana online bata tsaya duba duk saƙonnin da suke ta tuntuɗowa ba ta wuce kan number sa. Mamaki ya kamata ganin Dp sa ya sauka sannan babu about hakan kuma tasan yana nufin yayi blocking nata kenanseta saki wayar a Ƙasa ta rushe da kuka, Umma na tsakar gida tana tattare kaya saboda hadari daya taso har an fara iska ta jiyo kukan nata da sauri ta leƙa ɗakin,
"Lafiyarki Afeeyah? Kukan me kikeyi me ya sameki?" Umma ta tambayeta. Cikin kukan tace mata

"Jafar ne Umma" Umman taja wani shegen tsaki ta sakar mata labule ta cigaba da abinda takeyi ranta na suya, idan ta buɗe baki zagi zata zunduma mata shiyasa tayi shiru. Afeeyah tasha kuka ta gode Allah a daren kafin safiya ta ɗora da kiran layin Jay da jera masa Texts na ban haƙuri da rantsuwar duk abinda ya gani yake tunani ba gaskiya bane ba amma shiru kamar an shuka dusa be amsa kira ko guda ba haka be bata amsa ba. Zazzaɓi ne da ciwon kan gaske itama ya lafketa haka ta wuni a ɗaki Umma bata bi ta kanta ba seda Allah ya taimaketa Anty Sauda taje ita ta bata abinci da magani tasha harta samu ƙarfin cigaba da kiran Jay ɗin. Kiran ƙarshe da tayi shine Ahmad ya amsa, ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi sanda taga sakanni sun fara tafiya.

Muryar Ahmad me sanyi ta ratsa kunnenta, ba muryar Jay bace seda ta zare wayar ta duba dan ta tabbatar da wata kirane taga number Jay ce. Cikin muryarta data dashe dalilin kuka ta amsa sallamar kafin tace
"Dan Allah Jafar fa? Yana kusa?"
"Bashida lafiya yana kwance a Asibiti" Ahmad ya bata amsa, a rikice tace

"Yaushe? Meya sameshi? Wane Asibiti yake?"
"Relax, malaria ce inaga sauron gidanku ne basu san baƙo ba suka cijeshi, yanzu zan shiga gurinsa zan bashi wayar seya kiraki ok?" Ahmad ya faɗi. Ta sake sauke ajiyar rai, muryar kama take mata da ta Ahmad amma babu dalilin da ze sanya Ahmad ya samu wayar Jay
"Nagode toh ina jira" ta faɗi kafin ta sauke wayar ta doka tagumi tana jiran taga an kira kamar yanda yace, tunani take tana ƙarfafawa kanta guiwa dukda hankalinta ya tashi dajin bashida lafiya, ta yuwu ma beje ba jiyan ba ganinta da Ahmad bane ya ɓata masa rai, ƙila ma ko be hau Online bane shi yasa taga kamar yayi blocking nata a WhatsApp amma ba haka bane. Shiru tana ta tunani har minti kusan ashirin ya wuce ba'a kira ba kamar yanda wanda ya amsa wayar ya ce mata ze kai masa yanzu se kawai ta yanke shawarar ta sake kira kodan taji ya jikinsa da kuma abinda yake damunsa.

AHMAD
Sau biyu kenan da yake jin muryar budurwar Jay tamkar ta Fatima, daya isa ɗakin ya tarar da Manager shi tareda sauran jama'arsa wannan tasa be bashi wayar ba ya ajiye masa ita kawai akan Drawer ya fita zuwa gurin Dr Hassan, Jay kuwa bayan ya sallami baƙinsa ya ɗauki wayarsa da through out yau be riƙe ta ba. Missed calls ɗinta ya fara gani, wani abu ya soki ransa, daga safiyar zuwa yanzu yayi ƙoƙarin ganin ya rage damuwarta a ransa, a maimakon matsantawa kansa da son gano dalilinta na aikata musu wannan abun seya mayar da hankali gurin tunanin ta yanda ze hukuntata dan ba zata ci banza ba tilas ya maida mata da mugun nufinta akansu. Tunaninsa ɗaya yanda Ahmad ze karɓi Al'amarin idan ya sanar masa, baze bari taci gaba da cutar da shi ba daga ƙarshe ta karya masa zuciya tamkar yanda tayi masa.

Shi yana da taurin ran da ze shanye damuwarta amma baya tsammanin Yah Ahmad ze iya, he is so much into the girl.
"Kaima kana sonta" zuciyarsa ta raya masa, se yayi saurim kawar da tunanin daga ransa domin shine rauninsa. Allah ya sani yana Son ta, so na gaskiya saboda Allah badan wani abu ba amma kuma kash koda ace babu wata manufa game dasu a ranta, ya zama ace abinda ya faru Arashine daga Allah tilas shi ze haƙura da ita domin Ahmad ya rigashi zuwa gurin kai ko ba haka ba ko da ace tasa ce Yah Ahmad yace yana so ze bar masa. Ringing da wayar ta fara ya katse masa tunani, yana kallo harta katse kafin ta sake kira yayi adding nata to blocklist, a fili yake so ya wanke ta, face to face yake so ya warware mata komai ta yanda zata fi ji a jikinta.

Haka yayi jinyar kwana biyu aka sallameshi kullum a Asibitin Hajiya da jama'arta suke wuni tamkar wani biki se dare Ahmad kuma yaje ya kwana dashi. A taƙin kwanaki biyun yayi rama fuskarsa kuma ta gagara ɓoye abinda yake ransa amma se yake boyewa da sunan ciwo. Kwanansa biyu da dawowa gida ya fara shirin komawa France. Da niyyar sati huɗu yazo gida, sati huɗun da yake cewa kafin cikarsu za'a ɗaura musu Aure da Afeeyah se gashi komai ya canza ko cikakken sati biyu beyi ba yana cewa ze koma. Hajiya daman cewa tayi gara ya tafi, Turai tace anyi Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya shiyasa ma ya samu sauƙi ya tashi saboda an san ko an bashi magani ko hayaƙi bayi zeyi ba se aka masa aikeb kai tsaye wai Malam ya saka hadimansa sun saka maganin a jikinsa.

Ahmad ne kaɗai ya damu da konawar da zeyi domin ya gagara yarda wai Malaria ce take damun Jafar, akwai wani abu daya ɓoye masa kuma ya gagara tambayarsa kamar yanda shima Jay ya kasa furta masa abinda yake ci masa zuciya. Yayi Ƙoƙarin magana da Ahmad tun yana Asibiti, ya tambayeshi kan yanzu ace masa Fatima yaudararsa takeyi bayanshi da akwai wani da take kulawa kuma shi take so yaya zeji?
"Already na sani, bayan ni da akwai wani da take tare dashi kuma shi take so bani ba, ya ci ace na haƙura da ita Jafar, amma na kasa. Ni da kaina bansan irin son da nakewa yarinyar nan ba kawai dai ina cigaba da addu'a idan rabo na ce Allah ya bani idan ba tawa bace Allah ya musanya mun da wadda ta fita Alkhairi" amsar da Ahmad ya bashi kenan data sanyaya masa jiki tasa kuma ya fasa faɗa masa gaskiyar abinda ya faru to ta ina ma ze fara? Ya Ahmad zeji? Se kawai ya shanye damuwarsa shi kaɗai ya kuma cigaba da addu'ar Allah ya tarwatsa tarayyar su da Ahmad domin ita ba Alkhairi bace a rayuwarsu.

Ranar talata data kama saura kwanaki biyu Jay ya wuce Baba Alƙali ya kirashi akan yaje gida ya same shi yana son magana dashi. Shi kaɗai ya tafi yauma daman Ahmad baya nan ya tafi Jigawa inda yake noman shinkafa dan da tare ma zasuje Hajiya ta hanashi binsa.

"Shiru baka sake cewa komai ba dangane da full address da nace ka samo na gidansu yarinyar da kake nema" Baba Alƙali ya faɗa, ya sunkuyar da kansa yace
"Amm daman an samu matsala ne Baba so kuma na manta ban dawo na gaya maka ba"
"Matsala wace iri kenan?"
"Ita yarinyarce da akwai wanda suke tare kafin ni kuma bata gayamun ba se daga baya nayi finding out so i felt thar she betrayed me kuma bata da gaskiya if she could hide such important things to me may be bada gaske take so na ba nima".

Baba Alƙali ya ringa kallonsa kafin yace
"Kodai uwarka ta shiga tsakani ba?"
"Wlh babu ruwanta Baba bata san komai ba har yanzu kawai wannan dalilin yasa nayi blackout saboda ni bana son Ƙarya a rayuwata" Jay yayi saurin defending Hajiya. Alƙali yayi murmushi yace

"Amma ko zaka daɗe kana bincike kafin ka samu budurwa da take kula saurayi guda ɗaya, daman ai se anyi takara wanda yafi ƙarfi ya kayar da yan uwansa" cewar Baba Alƙali. Jay yayi murmushi, kamar ya sanarwa da Baban abinda ya faru amma baze so ya zama silar raba Ahmad da abinda yake so ba dan Baban baze bari ya aureta ba ya sani, gara ace ita da kanta taji kunya tace ta fasa tayi biyu babu so that bazeyi blaming kowa da cewar shi ya hanashi auranta ba.

"Ai ita Baba har iyaye sun san maganar fa for almost 3 years suke tare yana wahalta mata amma bata gaya mun ba seda naje gurin Babanta and from the way yayi maganar se naji kamar yafi son wancan ma akaina"

"Allah ya baka haƙuri ya musanya maka da wadda ta fita Alkhairi, shikenan zamu jira daga gurin mahaifin yarinyar da Ɗan uwanka yake nema shi saura sati Ɗaya wa'adin daya bamu ya cika, idan kuma duk an kasa ku ne se ku ɗauki haƙuri mu tafi Bechi a nema muku mata" ya ƙarasa maganar cikin raha Jay yayi dariya.

GIDAN MALAM HAFIZU
Kamar yanda na sanar miki sati biyu na bawa wanda kika kawo a matsayin zaɓin ranki, yau kwanaki goma sha biyu kenan tun zuwan da yayi be sake dawowa ba, ina sake tuna sar dake kwana biyu rak ya rage miki idan suka cika ba tareda ya gabatar da kansa ba karkiyi kuka da duk hukuncin da zan yanke domin na baki dama a matsayinki na Ya dan haka nima zan gwada iko na na uba akanki" Baffah dake tsaye akan Fatima ya faɗi.
"Kinji me nace ko?" Ya sake jaddada mata seta gyaɗa kai alamar taji ya juya ya fice daga ɗakin. Kwanciya tayi kan katifa ta fashe da kuka amma mara sauti, bata sake samun Jafar a waya ba tun ranar da wani ya amsa yace ze haɗasu. Ta tabbata kuma yayi blocking nata a WhatsApp da sauran social media handles ɗinsa dan duk inda ta masa magana bata tafiya sedai ta gaji da jira ta haƙura.

A ɗan lokaci ta fita a hayyacinta, zuciyarta zafi take mata ga ciwon kan da tayi ƙaryarsa ya aureta da gaske me azaba irin wanda ko idanu idan ya tasar mata bata iya buɗewa. Yanda Umma tayi banza da ita tamkar ta manta da wanzuwarta a gidan ne yake sake ta'azzara mata ciwo da damuwa, bata da wanda zata tattauna dashi, Anty Sauda ma ta juya mata baya, Badar Babansu bashida lafiya har an fita dashi India suna can dukansu tunda ta mata sallama basu sake magana ba kusan kwana goma bata san layin da zata sameta acan ba shi kansa Ahmad da take ganin ya zame mata ƙuda ta rasa yanda zata yaki ceshi a yanzu da take buƙatar ɓangaren da zataji sanyi shima ya kaucez tun randa yaje be sake komawa ba haka waya befi sau huɗu sukayi ba saboda ayyuka da yace mata sun masa yawa baya samun lokaci sosai wannan shi ake cewa rana zafi inuwa ƙuna babu inda zata tsoma ranta taji daɗi ga wani sabon batu da Baffah yazo mata dashi ita ya zatayi????

Daga kwancen da take ta janyo wayarta ta buɗe Tiktok, a can ne take zaton be rufeta ba kai tsaye tayi searching account ɗinsa ta shiga profile ɗin. Ƙirjinta ya buga dum da ganin video da yayi pinning a farko, hannunta har yana rawa ta buɗe, videonsa ne da wata yarinya, Jaa ce dan kalar fatarta farace irin me sirkin jini. Ƙirarta irin jikin yayan madarar nan da zaka gansu fatarsu luf kamar an hura musu iska a cikinta, kyakykyawa ce bata cika tsayi ba, tana da cikar ƙirji sosai da mazaunai wanda fitinannen ɗinkin doguwar rigar data saka ya bayyanar dasu. Hannayensu sarƙe da juna tana masa magana yana doka murmushin nan nasa me tsada. Ta ringa maimaita karanta Caption ɗin daya rubuta
# FatiyyahJay#

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.