Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 37
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: https://chat.whatsapp.com/G0Tst06uPc12T74oZhhCa2
💅 ' YAN ABUJA 💅
   Â
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Assalamualaikum my beautiful mutanen kwarai, ga Editing É—in littafi na na biyu da na farayi a duniya, a karanta da hankuri*
*2018/2024*
*Dan Allah da kun ga an fara posting ku É—an dinga adanawa saboda ba sai na yi nisa ba ku tambaya a dawo baya, Na gode.*
PAGE 1:
Gidan malam Baballiya gidane mai girma na qasa a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi mata biyu, Goggo Sarai itace uwar gida, sai Mama Bilkisu itace amarya, malam Baballe yana da yara guda huɗu dika mata ne, se dai a kullum ya na roqon Allah da kuma burin Allah ya azurta shi da d'a namiji mai albarka, wanda ko bayan ba shi zai kula da wannan zuri'a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata 'yar ta tilo ba wato Juwairiyyah, dan haka in dai aka ji rikicin ta to fa akan 'yarta ne, ko shi ma ba zata tsaya aita bala'i ba , za dai ta tabbatar ta karb'ar wa 'yar ta 'yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu, Goggo Sarai nada Suwaiba mai shekara 19 ,se Saudat me shekara 18, sannan Salma me shekara 16, Mama Bilkisu kuma na da Juwairiyyah wadda take sa'a ce ga Salma kwana uku ne tsakanin su kawai,a yanzu ta na dauke da tsohon ciki gashi nan haihuwa ko yau ko gobe.
Sai dai muyi fatan Allah ya amsa addu'ar Abba Baballiya wannan karon a samu biyan buqata wato ya samu d'a namiji,domin kullum fatan shi Allah ya dube shi ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali saidai sanyin halin shi be hana shi yin iya qoqarin shi na ganin ya isa da gidan shi ba, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan.
*****************************
Da misalin 11:45am Juwairiyyah ce ke ta aikace aikace a tsakar gida, inda Mama Balki ke d'aki ta na naquda ba tare da sanin kowa ba, azaba ta yi azaba ta ga abun ba zai yiwu ba kawai sai ta buÉ—e murya ta na neman taimakon Allah da na 'yar ta ta da ke taya ta aiki.
"Wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje"
Yarinyar da aka kira da sunan Juwairiyyah ce ta miqe tsaye da sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita, a bakin kofar gidan ta tadda mahaifin nata zaune ya na sauraren rediyo, sai ta durqusa cikin ladabi sannan ta ce,
"Abba Maman mu na kiran ka,ka yi sauri Abba bata da lfy kamar ma haihuwar ce ta zo dai ina jin"
Ya na jin haka ya miqe tsaye da sauri ya shura takalman shi dan ya saka,gaba ya yi ya bar su a wajen dan kuwa takalmin ma yaqi qarasa shiga qafar tashi sai kawai ya afka cikin gidan direct ya wuce sashen Mama Balki,labulen d'akin ya buÉ—e ya shiga, ganin mawuyacin halin da take ciki ne ya sanya shi cewa,
" Subhanallahi Gimbiya, haihuwar ce ta zo mana bagatatan haka? Sannu Gimbiya"
( Yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai daÉ—i sunna ne, inda yake kiran Goggo Sarai Sarauta)
Cikin tsananin azabar da take ji ta na ratsa ta ta ce,
" Malam taimaka min na samu na kai uwar d'aka bana son zama a nan na haihu a rumfa"
Cikin sauri ya kamata ya riqe da kyau a jikin shi sannan ya ce,
"To Gimbiya, bismillahi,amma kuma mun shigo d'aka ko dai muje asibiti ne ?"
Murmushi ta yi kawai dan sanin cewa qarfin hali ya yi dan ya kwantar mata da hankali ya fad'i hakan ta san bashi da kuÉ—in yin hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwad'ayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo Balki, dan 'ya'yan ta kyawawa ne dukan su su na kawo mata kuÉ—aÉ—en da bai san ta hanyar da ake samo su ba shi yasa baya ci,ita kuwa Goggo Sarai ta kan ce, ta gode wa Allah da ya bata 'ya'ya 'YAN ABUJA , dan haka ne auren su sai mai kudi, dalilin wannan ne yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa samarin banza, amma se suka yi kunnen uwar shegu da gargad'in shi, da taga ya yi musu wuta2 kuma ya fara kullen su a gida , sai ta fito da dabara tunda shi mai son ilimi ne musamman na addini sai ta saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba É—aya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai 'ya'yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasarar samun mazajen aure yan Abuja, kullum su na cikin zuwa biki da partyn qawaye na birthday.
Kukan jariri ne ya dawo da Abba daga tinanin ina zai samo kuÉ—in kai ta asibiti ta haihu lfy?
Da hanzari ya qarasa taimaka mata yaro ya fad'o har da mabiyya, nan take ya taimaka mata ya gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida da hanzari ya na hamdala, Mama kuwa cikin raunananniyar murya ta ce,
"Juwaira ɗora min ruwan zafi da ya tafasa ki sanar da ni , Allah ya sauke ni lafiya"
"Alhamdulillahi... Alhamdulillahi to Mamana sannu"
Cikin zumud'i da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da hushirya a saman su ta nufi gaban murhun nasu dan cika umarnin mahaifiyar ta na É—ora ruwan zafi, se dai ta na zuwa ta ga ba icce, amma duk da haka bata karaya ba ,sai ta je ta dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta ajiye, zata juya kenan ta ga mahaifin ta na shigowa da icce a hannun shi na dama, hannun shi na hagu kuma riqe yake da baqar leda qarama, da hanzari ta isa ta karbi iccen tana mai yi masa sannu da zuwa, komawa ta yi ta haÉ—a wutar ta É—ora ruwan shi kuma ya yi d'akin da mai jegon take.
Kamar saukar aradu ta ji an yi tsaki a gefen ta, qin juyawa ta yi dan tasan ba zai wuce É—aya daga cikin 'yan uwan ta ba koma Goggo da kan ta.
"Aikin banza sai rawar qafa ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihu"
"Hhmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika idan ku na da rabon shiriya, to bari ki ji Salma 'yar baqin ciki, wannan karon namiji Mamana ta haifa, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda"
Wani uban ashar Salma ta saki ta saki jikin ginin da ta riqe tai sashen su da hanzari,kafin ta isa cikin rashin sa'a bokitin gaban ta ya bige tukunyar da take girka masu farfesun naman kaza,ai ko tini komai ya zube a qasa, nama ne na kaza cike da tukunyar wanda da gani yafi qarfin kaza É—aya, ko kulawa ba ta yi ba ta shiga d'akin su da gudu tana faÉ—in,
"Goggo ! Goggo ! Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?"
Da saurin su suka fito dikkan su daga d'akin,ana can an qule a d'aka ana hasafin kuÉ—in da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai zancen auren su da su, cikin d'aga murya Goggo ta ce,
"Ke meye haka duk kin bi kin fadar min da gaba kamar an ce maki matar uban ki Bilki ta haifi saurayi"
"Hhmmmm ai kin ji ashe kece ke yi mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya tabbata ai Mama Balki ta haifi yaro namiji"
Damqo Salma Goggo Sarai ta yi da qarfi cikin zare ido take tambayar ta
"Me kk nufi salma?"
Cikin rashin kunya da murgud'a baki da idanu Salma ta ce,
" Ina nufin Mama Balki ta haifi saurayin d'a namiji,tunda ke kullum kk mana mugun baki akai to gashi ta tabbata"
Wani wurgi Goggo ta yi da Salma gefe, ta kuwa qume kai da gini ji ka ke quuummm,Goggo da sauran yaran nata dika suka yi gaba zuwa dakin Mama Balki, Salma ma miqewa ta yi ta na lailaya goshi ta bi bayan su, babu ko sallama suka afka d'akin, daidai Abbah Baballiya ya dauki gasasshen naman rago ya sa wa Mama Balki a baki, Goggo ce ta dafe qirji saboda abinda idon ta ya gane mata ta buɗe baki ta ce,
"Me nake ji ne da gani yau kuma ni saratu? "
Suwaiba 'yar boko kuma 'YAR ABUJA ce ta karkata baki ta ce,
"No i can't believe this, what is going on here, ina jaririn yake?"
Suwaibah na da kwalin ta na NCE ,ita kuma Saudat kwalin secondary ne kawai a hannu wanda duk daya take da su Salma da Juwairiyyah ,sai dai Juwaira tana son ta ci gaba da karatu amma ba halin yin hakan saboda babu arziqi,wannan shine dalilin da yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, ganin yanda suke wani cika su na batsewa ne ya sanya Abbah Baballiyaya ce,
"Haba Sarauniya ta ya zaki shigo d'akin ma'aurata da yaran ki gaba É—aya haka babu ko sallama? Kuma bama ki tambayi yaya ko ta haihu lfy ba? Aa tambaya kuke ina jaririn? Anya wannan rayuwar da ku ke yi ta dace kuwa?"
Cikin yatsine baki da fari da ido kamar wata qaramar yarinya Goggo ta ce,
"Eh ban ga zan iya sallamar ba ne shiyasa banyi ba, tambaya É—aya kuwa da zan yi shine me aka haifa? Da gaske ne namiji aka samu?"
"Eh na miji Allah ya bani, me za ki yi, me zai faru? Me ya sa ba zaki yi hakuri kema Allahn da ya bani ya baki naki ba ,ai ba wai ya manta ki bane kema in ki ka yi hakuri watarana samu za ki yi,dan haka ku fita min a d'aki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba"
Gaba dayan su shewa su ka É—auka sannan suka tafa kamar wasu 'yan daudu Goggo ta ce,
"Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi d'a na miji na gani tabbas, shine ya sa zaki fara min kitifi ko Balki ? to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma a yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta tass, Shi Uban yaran me ya ke da shi, me ya tara da zan damu raina akan haihuwar d'a namiji da girma na haka? Bayan ga 'Ya'ya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Ki kalla da kyau duka Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba"
Bakin ta suwaibah ke son rufewa tare da faÉ—in " Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su in komai ya kankama, ko kin manta halin yan baqin cikin ne? Se a shiga malamai a hana lamarin faruwa ai"
"A'a Suwaiba banni na fada masu su ji duk wani d'an baqin ciki se dai ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin su turo magabatan su a zo ai komai nan kusa ba da jima wa ba"
Abbah Baballiya ne ya ce
"Hhmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan za su ce mazajen da za su aure su turo ko? Ba bincike ba komai kawai su turo, to bari ki ji na fada maki zan ba 'ya'yan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsararriya mara kunya mai raina mijin ta a gaban 'Ya'yan ta dan su koya suma"
Ranshi a bace ya ke sanda ya yi maganar kawai se ya matsa kusa da Maman yana ci gaba da bata naman a baki
Shewa Saudat tayi tace
"Ikon Allah wai na kwance ya faÉ—i"
Dariya Suwaiba ta yi ita da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai ta yi a ranta tace,
'Kun yi ku gama da 'ya'yana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan'
A kwana na bakwai da haihuwa aka yi suna yaro ya ci sunan Ammar kyakkyawa da shi sak mahaifin shi,ba wani taro aka yi ba da yawa saboda babu abin hasafin, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen iyayen shi da yayar shi Juwairiyyah ba, zaune suke a shimfidar tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi ta na masa wasa kamar ya na jin ta, can cikin d'akin su kuwa qamshin turaren wuta na tsinke ne ke tashi, Sallama Abban su ya yi ya shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da ya yi masu Juwairiyyah wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira sannan ya shiga cikin d'akin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira ya yi yace ta kira mishi Goggo Sarai.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅ðŸ¼Â  YAN ABUJA  💅ðŸ¼
  WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.