Complete Hausa Novels

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 13 of 37

page 13:

Alhj Salihu da Alhj Kalla Mazajen su suwaiba da Saudat ne ke zaune a wani wajen shan iska da suka tanada na musamman dan tattaunawar sirri,bayan doguwar shawara da neman mafita ne suka  samu nasarar tsayar da  hanya ɗaya da za su samu jinin su suwaiban da qungiyar asirin su ke da buqata a duk ƙarshen wata cikin sauqi,bayan samun mafita da nasara antattaunawar da suka yi sai suka bushe da dariy a tare suka tafa tare da furta kalmar

" 'YAN ABUJA"

 Tashi suka yi suka shige motocin su masu gadin wajen shaqatawar nasu suka buɗe gate su ka hau daga masu hannu tare da yi masu addu'a da fatan alkhairi, direct clube suka wuce kamar kullum,sai dai yau basu wani dad'e ba dan kuwa sha ɗayan dare suka dawo gida.

Cikin kwalliya ta alfarma kowannen su  ya tadda iyalin shi, an sha kayan ado masu tsada, fatar nan har wani sheqi take sabida jin daɗi da hutu.

Kowaccen su kamar abin had'in baki tashi ta yi ta nufi mijin ta domin yi masa barka da dawowa, dan kuwa qorafi ba nasu bane yanzu tsoro suke ji kar su sha jibga a banza.

Bayan sun gama kulawa da Mazan nasu an ci an sha an yi wanka sun zauna su na hutawa a parlour suwaiba ta hau wata karairaya ta zauna a gefen Alhaj Salihu kamar za ta shiga cikin shi, cike da shagwab'a ta fara gabatar da uzurin ta a kunnen shi kamar yanda Goggo sarai ta koya mata,

" Mine "

"Na'am"

Sake mannewa ta yi a jiki shi sannan ta ce,

" Dama cewa na yi ko zamu je asibiti a duba mu ne ni da kai saboda a ga ko lafiyar mu qalaou kuwa har yanzu shiru ba ciki ba komai, dan ni fa har period na dena yia zatona ma ciki ne amma kuma gaskiya ban ga wata alama ba ni dai ina jin tsoro dan Allah za ka kai ni asibiti mu ga likitan? Ko ka san yanzu haka qanwar mu Juwairiyyah da aka yi bikin mu tare ta na da ciki,hakan zai zame mana abin gori mu da mahaifiyar mu ace mu uku babu mai ciki har yanzu"

Wani wawan mari ya antaya mata, ya hankada ta qasa sai da ta kifa,cikin ɓacin rai ya kalle ta ya na nuna ta da yatsa ya ce

" Dan uwarki ni zaki mayar qaramin mutum qaramin yaro? Wanda bai san me yake yi ba? Ohh wato ki haihu na samu magaji ko? Ko kuma ki kashe ni ki karɓe dukiya ta ko? To bari kiji wani abu, wannan dukiyar daga karuwai sai masu saida giya su zasu more ta in dai ba Zaki kwantar da hankali ki ci arziqi ki barshi a mazaunin shi ba,ni babu tsarin yara a rayuwar nan tawa, ban sani ba ko a gaba, amma a yanzu kam ban da wannan burin da kwadayin yaran da ke zaki sani neman haihuwa kamar ni an faɗa maki Banda ra'ayin kai na sai naki,"

Cikin kuka suwaiba ta rarrafa ta kama hannun shi ta ce,

" Dan Allah ka saurare ni ka kuma fahimce ni"

kafin ta qara magana kwakkwara ya rufe ta da mugun duka ko ta ina tare da fad'in ,

" Ke kin zama jaka ko? Baki yarda ki daina sa in sa da ni ba ko, ina faÉ—a kina faÉ—a kamar ki na magana da sa'an ki, yau kuwa Zaki ji a jikin ki sai soyayyar yara ta fita a zuciyar ki har abada",

Wayar charging phone ɗin shi ya ciro ya dinga zabga mata, tin tana kuka ta na bashi haƙuri karshe ma sai faɗuwa ta yi ta rufe idon ta a wajen ta daina motsawa, a haka ya samu damar ida qudirin shi na yi mata allurar bacci, ya debi jinin ta dan mugunta har leda uku, yana gamawa ya yi ma mijin Saudat magana ta waya dan sanin halin da suke ciki, mijin saudat tambayar shi ya yi ko lafiya ya ji ya na haki, nan take ya bashi amsa da cewar,

"Sai da jakar taci duka tukunna, wai ni zata yi wa zancen haihuwa"

" Ale  Salihu ka dinga rabuwa da ita ba laifin su bane laifin wannan shegiyar uwar tasu na tabbata ita ce zata zugo su dan kuwa in baka manta ba ba kalar labarin son kud'in uwar su da Basu bamu ba , na samu na deb'o Leda hudu ai dai ta gina jikin ta da kayan kud'in da ake samowa ko?"

Dariya Alhj Salihu ya yi sosai sannan ya ce,

"Ni kuma hudu da diba"

"Shgeb sama, to shi kenan sai mun haɗu yanzu zan fito,tsallake ta ya yi ya fice dakin shi ya saka jinin a inda aka basu su saka, wata jakar fata ce da akai mata ado da ja kamar an qara riƙa ta sai rubutun Arabic a jiki wanda ko mutum ya karanta ba zai bashi wata ma'ana ba, rataya wa ya yi a jikin shi dan kuwa ba a son su aje ta a qasa ko da da mistake ne sai sun ba da wani wannan ya tashi aiki kenan idan jakar  ta taɓa qasa,ko kuma idan ba haka ba sai an kaiwa Oga Zaks matan dan ya diba da kan shi,domin ko kusantar su ya yi jinin nasu diban shi ake yi.

Sun isa wajen Oga zaks da misalin ƙarfe ɗaya na dare, suna isa suka miqa masa jinin wata dariya ya barke da ita kamar ana yaga zani, ba ko daɗin saurara daga baya kuma ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce,

"Aikin ku ya na kyau, shiyasa kuka fi sauran abokan harka shanawa, bakuda tsoro sam ,sannan bakwa jinkiri, ku gaggauta maza muje a bawa Dodon tsafi jinin kyawawa ya sha"

Ta shi suka yi suka shiga wani daki, dan tsoro ina leqawa nai baya a 360 ba zan iya dakko maku rahoton komai ba anan, gidan Saudat na je, tana kwance rabin jikin ta na kujera, rabi na qasa, fuskar ta ta kumbura ta yi sintim, dan tafi ta kwanaki hayewa ashe Itan ma jibga ta sha amma yake wa abokin shi magana akan ya dena biye wa suwaiba ya na jibgar ta, nan take na ayyana a rai na wato shi Alhj  kalla hukuncin shi Kalla mari ne kawai, mari kam iya mari ta shashi da dikkan alamu, dan ina jin shi ya sata suma ma, ruwa na yayyafa mata na labe, a firgice ta miqe tana fad'in,

"Ni bana son Yaran ma har abada, kayi hakuri ka daina kallan mari"

Tana fadin hakan tana kuka fuska dagaje2 da hawaye ga majina da yawun azaba duk suna ta tarara,dube2 ta hau yi taga ba kowa a gidan sai ita kaÉ—ai ,ta na miqewa ta ji wani irin jiri ya na ' dibar ta tare da tsananin ciwon kai, komawa ta yi ta kwanta, tana maida nunfashi, suwaiba ko bata farka ba sai da suka koma gida wajen qarfe hudun asuba.

Yana isa d'aga ta ya yi ya kai ta toilet ya hada ruwan zafi ya saka ta, ihu ta saka na azabar da ta ziyarci jikin ta, dan kuwa jikin ta duk ya farfashe,kuka ta fashe da shi ta na ja da Baya a cikin kwamin wankan ta na fadin,

" kayi hakuri mai sunan Annabawa na tuba, ba zan qara maka zancen yara ba har mu mutu, ka yafeni sharrin shedan ne d'azun ma Allah ya ƙara nesanta mu da sharrin la'ananne jefaffen Allah"

Rufe mata baki ya yi yana hawayen munafurci yana bata hakuri shima, harda in ya sake ko taba hannun ta da sunan duka ne duk hukuncin da ta ga za ta masa ta masa, runtse idon ta ta yi tana jin yanda zafi ke shigar ta, nan take zuwa Abujan ma ya sire mata a rai, wannan wace irin azaba ce, in kaci daÉ—i na wata É—aya sai an zai zaye maka shi a kwana daya? Yanzu yanda take jin ta kamar wadda akaiwa yasar wani abu, bata da qarfi ga ciwon kai da take ji kamar kan ya fice, barin ta ya yi ya tafi kitchen ya samu fruits ya markade ya tace ya kawo mata ya sa mata abaki yace ki sha zaki samu qarfi sosai a jikin ki, bangaren da masu aikin su suke yaje,ya tashi mai girke2 dan ya mata farfesu, ko na naman meye ma a samu ta samu kwarin jiki, ai ko ba komai ta maida mugun yawu, sannan abinda ya kawo ta kenan, in ji shi, farfesun naman rago ya yi mata da yaji kayan haÉ—i, irin farfesunnan ne wanda mutum zai zaci gashi ne, yasha kayan lambu a ciki, qamshi da maiqo sai tashi yake, fresh milk ya zubo mata, ya koma toilet din bata shanye jus din da ya mata ba dika, dakko ta ya yi a hannu daure da towel ya dawo da ita gado ya cire towel din ya samo riga iya guiwa mai dan fadi ya zura mata, kanta ta jingina da frame din gadon idon ta lumshe, zuwa ya yi ya d'akko wannan had'in ya shigo da shi, ai tana jin wani qamshi mai daÉ—i sai ga idon Suwai a buÉ—e, wani yawu ta hadiya na kwad'ayi, Alhj Salihu ya ayyana,

'Shegiya dangin maita, ji fa uban dukan da taci amma ta ga nama har ta miqe'

Isa ya yi gaban ta ya aje mata ya fara bata a hankali,ita kuwa sai taga baya sauri, d'aga masa hannu ta yi ta saka nata dayan hannu ko ta kan spoon din bata bi ba ta hau ci kamar tsohuwar mayya, ci take ba ko tsayawa sai da ta yi nak, ta kora da fresh milk, ta zame ta kwanta, lokacin Subh payer ta yi amma ko a jikin su daga shi har itan, haka suka kwanta bacci, manne da junan su,abin ku da wadda ta dad'e miji na gabza in ta nemi haqqin auren ta, yau ta samu a bagas dik da zafin da take ji haka ta miqa mai kanta, ranar ta yi murna da farin ciki ba iyaka, tini ta nemi zafin ciwon ra rasa, kusan abinda ya faru kenan a gidan Saudat,sai dai akwai wani plan da Suwaiba ta haÉ—a a qasan ranta na ganin me yasa ba su son su haihu,dole sai ta binciko dalilin da ya sa ba su son haihuwa.
****************************

A gidan Talle kuwa cikin dare Salma ta ji kamar buga qofa ake yi,dan haka a hankali ta miqe ba tare da ta yi wanai kwakkwaran motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tayi ta qaramar bular jikin qofar d'akin nata,ta bular ta hango Yayan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fall cikin ta na me ya kawo shi d'akin Marka da tsohon daren nan, dan kuwa duk yan kwanakin nan marka ke zuwa wajen shi, yau fushi take yi da shi shi yasa ya biyo sahu, saboda  daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake,jikin shi har wata rawa yake  sanda yake kwankwasa qofar, budewa ta yi tana magana qasa2 ta ce,

" Dalla can sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gama ka tafi jarababbe kawai"

Jan shi ciki ta yi su ka rufe qofar, aiko akan idon salma, kame baki salma ta yi tana fadin,

"Tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da maqiyi da rana da ya wuce Baban Bangis,amma kuma ashe  da dare bata da masoyin da ya wuce Baban bangis, lallai ran da Su Badamasin suka sani akwai case a gidan nan ko kuma idan Talle ya ji labari"

Tana cikin wannan tinanin ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya shi yasa ma basu san wainar da ake toya wa ba, to an wuni shiririta kuma anyi bacci  late dole in sun kwanta su zama kamar gawwaki Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka, kafin Salma ta zo ne d'akin tan yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka haɗe su waje ɗaya maza da matan,motsin qofa Salma ta ji Baban Bangis zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa masa hannu ta na wani gantsaro girji, shi kuma yana qara shafawa, ya ce,

" kamar na koma mu yi ta yi sai asuba na tafi"

"Lallai ma Yaya kaima a gaida ka, duk wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera dari kacal"

Murmushi ya yi haqoran shi jajaye suka bayyana ya ce,

" Aaaa dari tab na gama baki dari ukun yau, ni dai gaskiya ban da su" 

"To kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa gobe"

Yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya tashi gaba É—aya da ganin ta tsaye ta na murmushi ta na bin su da wani shu'umin kallo,jiki na rawa baki na karkarwa su Marka suka zube a Saman guiwowin su suna roqon Salma,

" Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan"

Cikin Isa da gadara Salma ta ce,

" Anawa zan yi shirun ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin baku ban ko sisi ba tunda ke na ji É—ari uku ma aka baki"

Jiki na rawa Baban Bangis ya sa hannu a aljihun shi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa wa Salma ,

"Ke ma ina naki  kud'in?"

Da sauri Marka ta shiga d'akin ta ta d'akko dari biyar ta haÉ—a dana hanun ta ta bawa Salma, "

Kallon su ta yi ta na juya kud'in ta ce wa Marka,

"Marka ina son ki sani Talle ya kusan dawo wa dan jiya baki nan kina yawon ta zubar Badamasi ya faɗa sun yi waya ya ce zai dawo nan ba da jimawa ba, in ya dawo kika kuskura na ganku tare har kika haɗa  wannan qazamin jikin baki da shi warin ki ya mannu a jikin shi saina faɗa masa, dan ba zaki sa yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai kuma ba biyan buqata, kinji ni ko baki ji ba?"

Wani yawu Marka ta had'iya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarzon maza Talle, sannan a hankali tace,

"Na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri"

" Baku da matsala in ma komawa zaku yi sai asuba din zan iya yi maku gadi"

Da sauri suka furta,

"Aaaaa tafiya zai yi/zan yi"

Fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu, ita kuma salma  ta koma d'akin ta ta  bar Marka da cizon yatsan an amshe yan kudaden ta kuma gashi ba wai ta wani samu biyan buqatar ta bane, yau ta yi biyu babu, tura qofar ta ta yi ta koma dakin ta.

Salma na shiga d'aki ta datse qofar ta zauna ta dinga babbaka dariya, a ranta ta na ayyana,

'Shikenan yanzu sun dawo hannun na sai yanda na yi da su'

Shikenan yanzu da ta ji tana son kuÉ—i zata neme su kuma dole su bayar ko ta tona masu asiri, cikin murna ta dale gadon ta ta miqe.

****************************

Yau garin na Kano an tashi da ni'ima sakamakon sanyi da ya É—an fara shiga, garin ya yi daÉ—i ya yi kyau gwanin sha'awa,rana ta yi sanyi babu kuma zafi.

Shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ce ta kawo ma Juwairah ziyara ta musamman dan tana son ta qara bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na zuba, bangare É—aya kuma abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun cinkin da ta yi, murna take yi sosai itama da jin hakan.

Shiryawa ta yi bayan ta gyara gidan ta tsaf kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa ya kai ta har gidan su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga ta gaishe ta, bayan sun gaisa ne ta mata murnar abun alkhairin da ya same su sannan ta shiga ciki wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la'asar, Juwairah na d'aka tana gabatar da tata sallahr.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼
 

     

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.