Complete Hausa Novels

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 37

Page 8:

Nafeesa ce ta tsaya tun daga bakin kofar shiga sashen su Juwairiyyah ta kwankwasa tare da yin sallama,bayan an bata izinin shiga ne ta qarasa shiga ciki,gaishe da Jabeer da Juwairiyyah ta yi sannan ta kalli Jabeer ta ce,

" Yah Jabeer Innarmu tace wai ka bada shinkafar na kai mata tin da ta yi wuyar dahuwa"

"Inna lillahi,  kin gammu yanzu haka zancen shinkafar muke yi ni gaba daya mantawa na yi shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa mata a kawo"

Dariya Nafee ta yi sannan ta ce,

"Tace idan ka faÉ—i haka na ce ka bata ta fasa wataran an dafa mata"

"Oh my God yau ya zan yi na iya zuwa gaida Innar mu? Dan Allah Nafee ya kika ga fuskar ta ta yi fushi sosai ko?"

Cikin jimamta lamarin Nafee ta sauke ajiyar zuciya ta ce,

"Hmmmm ba kadan ba kuwa Yah Jabeer, amma tace kar na fada maka ta yi fushi"

Juwairah a ranta kuwa sai tace

'Ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa'

Ba yanda ya iya haka Jabeer ya ya miqa mata shinkafar yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita ta yi da ita tana masa dariyar zaka amsa ne in ka shigo kai da Innarmu ka san halin ta ba ta da sauqi.

Sai da su Juwairiyyah suka taɓa baccin su sannan suka tashi suka yi wanka tare da brush, d'aki suka shiga su ka shirya cikin shiga mai kyau da burge junan su ta qananan kaya, hijab Juwairiyyah ta ɗora akan kayan ta matsattsu da ta yi ma mijin ta kwalliya da su kafin ya fita kasuwa, a tare suka shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama raba abin karyawa tace akai masu sai ga su sun shiga, duqawa Juwairah ta yi har qasa suka gaisa,

" Ya jikin naki Juwairah,ai Nafeesa ta ce min ba ki ji daÉ—i bane shi yasa ya ajiye shinkafar bai baki kin dafa min ba duk da tsananin yunwar da nake ji jiyan"

Zare ido Juwairiyyah ta yi cikin duqar da kai da sauri ta furta,

"Da sauqi Innarmu na ji dama sosai alhamdulillah"

" To Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lafiya sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana?"

Innarmu ta fada a matsayin wasa take yi, amma duk wanda ya kula ya san magana take faÉ—a mata, murmushi Juwairiyyah ta yi sosai sannan tace,

" Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka"

Tana fadar haka ta miqe ta yi wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu ta yi ta na bin Juwairiyyah da kallon mamaki, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, daÉ—i ma yake ji a ganin shi Innar shi da matar shi sun fahimci juna sosai akwai shaquwa ta musamman a tsakanin su, tun da har suke irin wannan maganar ga junan su, matsawa ya yi kusa da Innarmu ya ce,

"Akwai abinda zan taya ki ne Innata?"

Murmushin qarfin hali ta yi sannan ta furta,

"Eh toh ba a rasa ba ai,

A qoqarin ta na hana shi ya koma wajen da matar shi take,

Can bangaren kuma Juwairiyyah da Baba Balarabe ne ke gaisawa cikin sakewa da mutuntawa,

" Babana ina kwana?"

"Lafiya qalaou d'iyar albarka, kina lafiya dai ko?"

" lafiya qalaou nake babana"

"To madallah, Juwairah ina son ki yi ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta d'akko  na daban wanda har ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi yuwuwa, da dukkan alamu daga can ta samo wadannan sabbin halayen dan kawai kar a zauna lafiya"

" Babu komai Baba , ai ita É—in uwa ce a wajena ko da ace ba matar ka bace ba mahaifiyar Yah Jabeer ai uwa ta ce, tinda ita ta haife shi kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai yi min, dama kuma ko da asalin mahaifiyar mutum ma ai ana samun sab'ani dan haka ita ma uwa ta ce,watarana ba zata yi ba"

" Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki sak ki ka dakko ba wanda ki ka baro"

Murmushi suka yi dikan su ita da Baba Balaraben, bayan Jabeer da Juwairiyyah sun gama gaishe2n su sai suka koma sashen su suka karya, suna gamawa ya sauya kayan da zai fita kasuwa da su sannan ya É—auki makullin shagon shi da duk abinda yake da buqata ya fito hannun sa riqe da hular shi ya na gyara karin ta, ya na gamawa ya kafa ta akan shi ya kalli Juwairiyyah ya ce mata,

"To ni fa na fito zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki da yawa Allah ya yi miki albarka "

Tashi tsaye ta yi ta isa gaban shi cikin yanga da kashe ido da murya sannan  ta zagaye hannayen ta a wuyan shi ,shi kuma ya zagaye qugun ta, sannan  ta ce,

"Allah ya kiyaye hanya, zan yi kewar ka da yawa a cikin waÉ—annan awannin da za mu yi ba ma tare"

Cike da shagwab'a da tura bakin ta kaÉ—an gaba take maganar,Jabeer na ganin haka kuwa ya qarasa da fuskar shi jikin ta ta suka hau sumbatar junan su, da kyar Juwairiyyah ta kwace kanta a hannun Jabeer, sai wani shinshina ta yake ya na jin kamar kar ya fita,cike da shagwab'a ta furta,

" Yah zaka makara fa, ka tafi cikin kariya da amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya haÉ—a ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokacin ta, in kaji yunwa ka taimake ni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane, ba abubuwan da zan iya ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji Yayana?"

" Karki damu,duk abinda ki ka ce an ma gama shi kawai ur higness"

Yanda ya duqar da kai a gaban ta da girmamawa ne ya bata dariya, ai kuwa sai suka fashe da dariya a tare, ta sanya hannun ta cikin nashi ta raka shi har waje,bata dawo ba sai da ta ga tafiyar shi sannan ta dawo d'aki ta hau gyara wajen da suka ci abinci.

****************************

A can gidan Baba Baballiya kuwa Goggo ce ta fito daga d'akin ta ta na qarasa d'aura dankwalin kan ta, cikin masifa ta duqa ta d'aga wani food flask Mai kyau sannan ta ce,

" kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan a can amma  na zo na tarar an d'aga an kai min shi nan, ko uban wa ya ce a taba min kaya oho, shikenan mutum idan yana jin haushin talaucin da ya yi masa katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishe ni yau"

kamar Mama ba zata amsa ta ba amma sai taga dacewar ta bata amsar, dan haka ita ma sai ta ce,

" Hmmmm Allah nawa in ji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga ɗaya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake jiya iyau, ba wani hura hancin da za ai mana kuma, flask ne fa tun wanda aka samu a gudummawar biki ba wata tsiyar ba, sannan ban taɓa sanin gyara kayan ka zai zama sauke mu raba ba da ban kawar maki da shi ba na bar awaki sun tattake"

kamar dama Goggo jira take Maman  ta tanka mata, sai kuwa ta hau masifa da bala'i kala kala har ta na jin kamar ta ari baki dan tsabar masifar da ke cin ta,nan da nan ta taso wa Maman a lokaci daya ta dinga zage zage da kira mata alkaba'i kala kala, har da su gori ta dinga yi ta na fad'in ai abinci ma wataran ita ke taimakawa da shi a gidan ba dan haka ba sai dai yunwa ta kashe su, 'yan Abujan da aka sanya wa ido su ne suka bata kud'in da take ci da su sai dai baqin ciki ya kashe Mama, Mama tace daga yau in Goggo ta haifu cikin Mahaifiyar ta karta qara taimakawar ta ga in bazata rayu ba ita da danta.

Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka dan kuwa su na tsorata shi da hayaniyar da suke yi baya son hayaniya shi sam, É—aukar shi Mama ta yi suka yi daki abun su suka bar Goggo na kumfar baki ita kaÉ—ai.

*************************

Oga Zaks ne da mazajen su Suwaiba tafe sun fito daga wani d'aki mai tsananin duhu sosai, Alhj Kalla dauke da Saudat a hannun shi sai kallon fuskar ta yake yi abokin shi kuma aminin shi Alh Salihu na dauke da Suwaiba, suna fitowa daga dakin, Oga Zaks ne ya furta,

" To ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su da sun farka su yi tozali da ku, domin wannan magungunan da suka yi ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su na wannan watan, za ku yi kuÉ—i na ban mamaki, domin kuwa kuÉ—i kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo masa irin wannan ba, nima kuma shaida ne, hahhahaahhha"

Cikin farin ciki su Alhj Ƙalla suka haɗa baki wajen fad'in,

"Godiya muke Oga Zaks"

Sannan suka ajiye su suka canja masu kaya suka yi mota da su sai cikin garin Abuja, suna isa cikin gari kowa ya É—auki hanyar gidan shi, fad'ar kyau da tsaruwar gidajen nasu ma b'ata baki ne kawai, gidaje ne irin ginin qasashen turai wanda ko a turan ma sai masu kuÉ—i ke da irin wannan gidan, ko ta ina ka gilma masu hidima ka ke gani sun gyara sun tsaftace gidan sai sheqi da kyalli tare da É—aukan ido yake yi ga qamshi kamar a qasar Arab.

Bayan gaisawa da masu aikin gidan ne kowannen su ya shige da matar shi d'aki ya ajiye ta a gado sannan suka kwanta a gefen su suka hau baccin asara ba sallah  ba salati,basu suka farka ba sai wajen la'asar, miqa Suwaiba ta yi ta na hamma, tana kallon d'akin nata, yanda ta zaci za ta zo Abuja ta zauna a gida mai kyau sai ta ga gidan ya wuce zaton ta da tunanin ta,ko ta ina d'akin ya gama rud'a ta da kyau da qayatuwar shi, shiru ta yi ta na son ta tuna abubuwan da suka faru tun da aka gama dinner bikin su ta kasa, lokaci take kallo ta na tunani anya time na tafiya daidai kuwa? Qoqarin kawar da wannan tunanin ta yi ta miqe ta hau takawa kamar mai koyon tafiya ta na so ta ga ya wannan gidan na ta mai dimbin kyau yake, taku ɗaya biyu ta yi a na uku ne ta ji wani irin ciwo a cikin ta  mai tsanani da sauri ta komawa ta zauna, tana fad'in ,

"Wasssshhhhhh Allah na ciki na, me ya samen a ciki kuma nake ji na haka? Gashi ina jin duk jikina ya na min ciwo"

Kusan a tare suka farka su ke yin wannan maganar ita da 'yar uwar ta Saudat, Saudat da tafi Suwaiba raki ma harda kukan ta, a rude mazajen nasu suka tashi kamar ba abinda ya faru suka hau tambayar su da me ya faruwa, Suwaiba ce ta langwab'e jikin mijin ta ta na wani karya wuya sannan ta ce masa,

"Ciki na na min ciwo"

Tashi ya yi ya duqa gaban ta ya d'aga rigar ta ya leqa cikin tare da shafawa a hankali, sannan ya ce,

" Ayya kiyi hakuri zai warke ne a hankali hatsari muka samu a hanyar mu ta dawowa gida daga wajen dinner  sai muka kai ku asibiti ke da 'yar uwar ki, kwalbar glass ce ta yayyanke ku shine muka wuce da ku asibiti aka yi maku dinki a wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko?"

Ya qarasa maganar shi tare da jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta ta yi a jikin shi, ta na tunani ya akai shi babu ciwo ko ɗaya a jikin shi? Da sauri ta kawar da wannan tunanin sakamakon tashi da ya yi ya fita dan ya hado mata abinci, tana daga kwance a gadon ya dawo ɗauke da wani ɗan qaramin teburin cin abinci Saman shi an aje plate ɗin abinci da cup ɗin juice sai mug ɗin tea,gefe kuma ga wani plate nan an yanka fruits a Kai sai ya ajiye mata a saman cinyar ta,sannan  ya zauna yana bata a baki, wani daɗi ne ya lullub'e Suwaiba yau mafarkin ta ya zama gaske ta samu fiye da abinda ma take kwadayin samu a auren d'an Abuja.

Tana gama wa ta dauki wayar ta da ke kashe ta kunna ta kira Goggo,wayar na shiga Goggo ta É—auka kamar wadda ke gadin wayar ta na jira a kira, cikin kuka Goggo ta ce,

"Haba 'yar nan yau wata biyar kenan da kwana uku, kun tafi shiru ba waya ba aike meke faruwa ne Suwaiba?"

Cike da Mamaki Suwaiba ta furta,

"wata biyar da kwana uku kuma Goggo?????............
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.