Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 37
Page 23:
Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo gida daga wajen interview da ya je yi a Abuja, waya suke yi da Juwaireren shi wadda ke kwance a gadon ta da ya sha gyara kamar Jabeer na gida dan,bata daga cikin matan da ke qin gyara d'akin su saboda taqamar miji ya yi tafiya,hira suke sha ta soyayya gaba ɗaya Juwairiyyah ta shagwab'e masa ta susuta masa lissafi, ji yake yi kamar ya dawo a daren ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi, kwantar masa da hankali ta yi da cewar gobe suna tare da junan su da yardar Allah dan haka kar ya damu ya qara haƙuri,dole jabeer ya hakura ya daina yi mata shagwab'ar da ya ke sanya ta nishad'i da dariya, Itama ta na jin ta kai wata a wajen miji tinda duk girman shi ya yarda ya amince ya bayyana mata yarintar shi.
Suna gama hirar su ta soyayya ta tuna masa kar ya manta fa ya yi addu'ar bacci kafin ya kwanta,sai su ka yi addu'ar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love u", haka suka yi bacci cike da matsananciyar kewar junan su.
Da sassafe bayan tayi sallahr asuba tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, taso yau ta bar gyaran lambun ta da ta yi a cikin gidan saboda sauqaqa masu wahalar rayuwa sai ta ga dacewar ta gyara É—in in yaso daga baya ta gyara gidan ta da girke girken tarbon mijin nata.
Da misalin 9:28am Juwairiyyah ce sanye da doguwar riga mara nauyi mai hannun shimi, ta dauki kayan gyara lambun ta ta fara gyara abubuwan da suke da buqatar gyaran, da ke ta na da saurin aiki cikin qanqanin lokaci ta gama cire ciyayi da bawa shukokin nata ruwa sannan ta ajiye komai inda ya dace ta wuce d'akin ta ta gyara shi ta hanyar sauya wankakken zanin gado da sauya wankakkun labulaye.
Tattare zanin gado da labulayen da ta sauya ta yi zata fitar Nafeesa ta yi sallama, cikin É—an haÉ—e fuska Nafeesa ta ce,
" Haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe Zaki zauna ki na aiki mai wahala haka? Salon kawai ki ja mana wani aikin, habaa gaskiya ban ji daÉ—i ba"
Ta qarasa maganar ta ta na karb'ar kayan hannun Juwairiyyah, murmushi Juwairah ta yi ta dafa kafadar Nafeesa da ke kumbura baki ita a dole Fushi take yi sannan ta ce,
"Kar ki yi fushi da ni 'Yar qanwata,na jima ina so in sanar da ke ina matuqar jin daɗin yanda ki ke bani girma a gidannan ba dan na girme ki da shekara ba sai dan sanin darajar ɗan uwan ki da kuma mutunta shi da ki ke yi har ta dalilin haka nima ki ke daraja ni,na jima ina mamakin yanda ki ka ajiye duk wata quruciya da yarinta da muka ci ki ke kasa Kiran suna na kai tsaye sai idan kin so tsokana ta, sannan tunda muke baki taɓa yi min abu cikin gadara da isa ba dan ganin ke qanwar miji na ce ki na da 'yanci da iKon yin duk abin da ki ka ga dama a gidan yayan ki,a gaskiya Nafee samuna irin ki sai an tona Allah ya barki da masoyin ki kema ya nuna mana ranar auren ku,Allah ya sa ki samu kwanciyar hankalin da tafi tawa a dangin mijin ki,Allah kuma ya qara mana zumunci ina son ki 'yar uwa ta,maza taho to ki taya ni aikin ki dena Fushi da ni,abinda ya sa ma ban kira ki ba na dauka kina taya Innarmu aiki ne shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa ko? And dan Allah ki dena fad'ar min da gaba dika dika fa yanzu cikin ya shiga wata takwas"
Murmushi suka yi wa junan su Nafeesa ta ji daÉ—in maganganun Juwairiyya sai kawai ta nufi inda Juwairiyyah ke yin wanki ta ajiye kayan ta koma ta tattaro sauran 'yan kayan da ba su da wani yawa ta fara wankewa,ranar dai kusan a tare suka ci gaba da aikin su, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su,Saida ya rage sauran wanke band'aki kawai Juwairiyyah ta deb'i ruwa a bokiti ta É—auki omo da tokar murhun da ta zuba wa gishiri kaÉ—an ta matsa lemon tsami ta zuba ruwa akai ta nufi hanyar band'akin.
Nafee na ganin haka ta bi bayan ta ta amshe wankin toilet É—in, bayan ta kammala ta fito da komai ta ajiye inda ya dace ta kalli Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam me zaki dafa wa Yah Jabeer ne naga baki fara batun girki ba ga shi yamma ta yi"
"Abinda ya fi so zan dafa masa, da kud'in da ya bani kafin ya tafi, jiya na yi aike kasuwa aka siyo min k'wai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kin san bani da su a lambu na dama zan iya noma su har su zan saka tinda Yah Jabeer na so a yi girki da su, sai flour ina da mai dama, an siyon yan kayan qamshi da maggi, É—an wake zan yi mishi mai ajiiiii Hajiyata kin san shi a duniya na kula yana son abunnan"
"Waiiii sosai ma kuwa, baki gan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innarmu da sai kin sha dariya, Innarmu in ta kama shi sad'af sad'af take tafiya ta damqe hannun shi ta matse da ludayin tsamar danwaken, shi kuma ya yi ta ihu dan azaba ita kuwa ta qi saki sai ya wahala ta sake shi ta na bin shi da zagin ya na mata satar É—an wake a tukunya ni da baba mu yi ta musu dariya"
Dariya suka yi tayi sosai dan kuwa Juwairiyya bata taɓa jin labarin ba sai yau, miqewa suka yi suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata da zai tafi da kalar girkin da zata yi,musamman alayyahu da albasa mai ganye, sai da suka yanka komai ta wanke tsaf ruwan jikin su ya tsane sannan ta shiga soya dankalin turawan da ta yi wa yanka a tsaye,sannan ta dakko dafaffen naman ta da ta yanka qanana-qanana ta soya sama-sama ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ta sanya tumatur guda biyu jal ta zuba, ya na tsaka da soyuwa ta zuba kayan qamshi da na dandano,bayan miyar ta soyu ne ta dakko wannan veges din ta zuba, ta bari ya dahu har sai da ruwan jiki ya qame tass sannan ta zuba dankalin ta soyayye da dafaffen k'wai a ciki ta juya ya haɗe jikin shi da kyau.
A gaban Nafeesah ta d'akko flour da wani gari ta zuba kuka ta juya sosai sannan ta fara kwab'a wa da ruwan kanwa, cike da mamaki Nafeen ke bin ta da kallo, cikin tuhuma ta tambayi Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam Matar yayah wannan garin meye ne naga kin zuba a cikin flour É—in kuma?"
"To Hajiya tambaya an fara tambayar ko, to garin wake ne na niqa da yar dawa kadan sai alabo shine na haÉ—a da flour din, É—an wake yafi dad'i sosai idan aka saka su"
" Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina ba gashi yanzu na qaru ba?"
" Ban ga laifin ki ba Hausawa sun ce matambayi baya bata ai"
Hira suka ci gaba da yi ita kuma ta na kwab'in danwaken ta,bata bar kwab'a wa ba har sai da ta ji ya yi laushi sosai sannan ta buɗe tukunya ta ga ruwan ya fara alamun tafasa sai ta fara jefawa qanana, dan yafi son a jefa d'an wake qanana, rufewa ta yi sai da ya tafaso ya yi kamar zai zube ta buɗe marfin ta bari ya ɗan qara dahuwa sai ta kwashe a ruwa Mai kyau daga nan kuma ta tsame shi a mazubin ta mai riqe zafi, ta zuba wa su Innarmu ta bawa Nafeesa.
Nafeesa ta barwa wajen dan ta gyara ita kuma ta dakko nunannen tumatur ta wanke ta raba shi biyu tare da baɗe shi da sugar a tsakiyar shi ta hau goge fuskar ta da shi, nan da nan fuskar ta ta dau kyalli kyan ta ya qara fitowa.
Lalle Juwairiyyah ta deb'o ta zuba masa man kwakwa ta kwab'a shi da É—an ruwa kaÉ—an ta dinga bin ko ina na jikin ta ta na murjewa,gaba É—aya lamarin ta ya gama bawa Nafee mamaki,kasa shiru ta yi sai da ta yi magana,
"Tab a gaskiyar magana Yayah na shan daÉ—i aradun Allah, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane kamar yanda ki ke tsara abubuwan ki, bama fa ki wani dad'e da yi ba amma ji yanda ki ke faman dirzar fata kin koma kamar wata tauraruwa mai haske da kyau"
" Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta ya yi tafiya ko na kwana ɗaya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko da sauyin ba yawa, balle kuma Nafee muna magana ne fa akan Yah Jabeer d'ina, My love, my everything"
Dariya suka fashe da ita tare da tafawa,Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka abun ta ba tare da ta biye wa tsokanar Nafeesan ba.
Ta na fitowa ta tsane jikin ta tare da shafa mayukan ta masu kyau da ta haÉ—a da kan ta dan gyaran fatar ta sannan ta yi shigar da yake matuqar so, doguwar rigar material ne aka mata irin na masu ciki ma'ana mai faÉ—i ta yanda ba za ta takura ba,an d'aure hannayen rigar dika ta wuya daga qirjin ta É—an kama ta kaÉ—an, cikin nan ta bi ta shafe shi da mai sai kyalli yake gwanin sha'awa,kwalli da powder kawai ta shafa sai man leb'e, wani irin sassanyan qamshi mai ratsa zuciya take fitarwa saboda bata amfani da turare mai karfi.
( kwalli na da matuqar tasiri a idon mace, macen da ta saka kwalli ta kuma iya sarrafa idanun ta ta daban ce)
Dogon hijab ta saka akan kayan ta tada sallar magrib bayan ta idar ne ta zauna ta na azkar a hankali ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar isha'i ta kabbara zata yi sallah kenan Sallamar Jabeer ta daki kunnuwan ta dake buÉ—e suna jiran su ji muryar shi da ta yi kewa.
Jin shiru bata je tarbon shi bane ya sanya Jabeer leqawa parlour ganin tana sallah ne ya sanya shi ajiye kayan shi a cikin palourn ya tafi ya d'aura alwala shima ya tafi masallaci.
Ta jima ta na gode wa Allah da ya dawo mata da mijin ta lafiya qalou kafin ta yi tahiya ta Sallame sallar ta, ninke hijabin ta take yi bakin ta na tasbihi ga Allah ta shiga d'aki ta dan sake shafa humra da powder sannan ta hau kallon kanta a madubi, murmushi ta yi wa kan ta kafin ta koma parlour, É—auke kayan da ya dawo da su ta yi ta hau dubawa nan take ta hau ware komai ta na ajiye wa a mahallin da ya dace da shi,hatta da kayan wankin da ya dawo da su sai da ta yi masu mazauni sannan ta dawo ta É—auke wata leda da bata buÉ—e ta ga meye a ciki ba ta kai ta ajiye.
Ruwan wanka ta haÉ—a masa mai d'umi, fitowar ta kenan ta shiga parlour kafin ta kai ga zama Jabeer ya sallama ya kulle sashen nasu, kafin ya gama karanta ayatul kursiyyun a qofar gidan ta tashi da sauri ta na dariya qasa qasa ta b'oye a bayan qofa.
Shigowa jabeer ya yi bakin shi É—auke da sallama fuskar shi cike da annuri saboda ganin gidan qal fiye da yanda ya saba ganin shi,cikin murmushi ya hau dube -dube alamun neman ta yake, gajiya ya yi da tsayuwar ya kama qugun shi ya ce,
" Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa na yi ta maki kukan wahal da idanu da ruhi na da ki ke yi, dan na kula da alama baki son gani na ni kaÉ—ai ne na yi kewar ki"
Ta bayan shi ta lallab'o ta fito ta yi masa wata iriyar runguma wadda tasanya shi sauke ƙanƙk'arfar ajiyar zuciya, juyawa ya yi gaba ɗaya ya d'aga ta sama, suna ta dariya, sumbatar ta ya dinga yi ya na nuna tsantsar yanda ya yi kewar ta,daga baya ya tafi suka samu waje suka zauna a kujera,inda Jabeer bai bar Juwairiyyah ba sai da ya zaunar da ita a Saman cinyar shi, yana shafa cikin ta tare da yi wa cikin nata hira kamar wanda yake hira da mutum babba, dariya kawai take yi ita kam, daga baya ta rage sautin dariyar ta tace da shi,
"Sannu da zuwa fitilar da ke haske cikin gida na, a gaskiya dole na dinga godewa Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer tafiyar nan ta kwana biyu da ka yi ya sa na tabbatar wa kai na ba zan iya rayuwa mai ma'ana ba idan babu kai, i missed u so very much"
Ta qarasa maganar ta tare da qanqame shi tana hawayen farin cikin dawowarsa lafiya kamar wani wanda ya shekara baya gari, d'ago ta ya yi yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan kuwa kalaman ta sun ratsa zuciyar shi sun samu wajen zama ya kuma tabbatar da iyakar gaskiyar ta ta faÉ—a masa,
"Yi shirun ki my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kaɗai har abada, bana fatan na wayi gari na ga baki kusa dani,ke ce farin ciki na Juwairiyyah ke ce komai na, dan haka kar ki taɓa jin tsoron rasa ni saboda ni naki ne har abada,na mallaka maki gangar jiki na, ruhi na da zuciya ta ki yi yanda ki ke so da su dika "
Wata sabuwar runguma ta qara yi mashi da ta saka shi jin daÉ—i sosai, d'aga shi ta yi ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi ya yi wankan ya yi brush suka fito, sannan ta taya shi shiryawa.
Bayan sun gama ne suka nufi kan shimfid'ar da suke cin abinci suka zauna, duk abinda take yi masa ba qaramin daɗi yake ji ba, qima daraja da mutuncin ta na qaruwa a idanun shi,ita mace ce mai yawan kyautatawa,shi kuma namiji ne mai son a kyautata masa kuma mai yaba kyautatawar da ake yi masa,dan haka binta kawai yake kamar raqumi da akala.
Ta na buÉ—e mazubi na farko idon shi ya sauka a kan d'an wake murmushi ya saki mai sauti sama ya kalla cikin ran shi ya na godewa Allah tare da tunanin shin me ya aikata mai kyau a rayuwar shi Allah ya bashi Juwairiyyah a matsayin mata ya ninka wannan aikin alkhairin dan Allah ya bar masa ita su yi ta rayuwa tare har abada?
Hadiyar yawu ya yi dan ganin ɗan waken da har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da ta yi na dankali, zobon da ta dafa da abarba, cittta kaninfari, cucumber, goruba da sugar ta zuba masa, kafin ta gama dubawa Jabeer ya fara ci yana lumshe ido kawai tsabar yanda abincin ya yi masa daɗi, sai wani sautin santi yake fitar wa dan kuwa bata gane abinda yake faɗa, Juwairiyyah kuwa dariyar jin daɗi ta dinga yi.
Kowacce mace ta na so idan ta yi abun kwarai a Yaba mata, dan haka yabon Jabeer a wajen ta ba karamin abu bane, hannu ya miqar ya ɗauki zobon da aka saka a randar sanyi ya yi sanyi dan kuwa Juwairiyyah bata da fridge ya kai bakin sa ya kurba, saurin buɗe idon shi ya yi sannan ya mayar ya kulle, ya ci gaba da santin da yake yi, a hankali Juwairiyya ta ce,
" Yah Jabeer menene, yayi d'aci ne ko wani abu ka ji da be yi maka ba a ciki na ga ka buÉ—e ido da sauri?"
Ta yi maganar tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko ba yi masa bane,da hannu ya yafice ta ya ce,
"Matso kiji me ya yi"
Yana ɗan yatsina fuska saboda ya ja wasan da kyau,nan take ta ɗan ji zuciyar ta ba daɗi, saboda gani take ta b'ata zob'on garin iyayin yi masa had'e-had'e, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira ta yi, matsawa ta yi kanta a qasa, Jabeer ya ce,
"To ai sai kin rufe idon ki sannan zaki iya jin me na ji nima ba ido rufe ki ka ga na sha ba ? matso sosai na baki da kai na ki ji ya ya yi"
Matsawa ta sake yi ta rufe idon nata, ji ta yi ya hau sumbatar ta har sai da ta ga wasu taurari na gilmawa a idanun ta ta kasa motsawa, a hankali Jabeer ya ce mata,
"To buɗe idon naki mana Princess wannan tukuicin kyautatawar ki a gare ni na baki duk da na san ba zan taɓa iya biyan ki ba,ni ba mai kuɗi bane bare na maki kyautar kuɗi gida ko mota, albarka kawai zan yi ta sanya maki tare da fatan alkhairi,sannan zan yi qoqarin sanya ki farin ciki har qarshen rayuwar mu"
A tare suka kammala cin abincin su ya na ta santi tare da yaba mata, anan ne Juwairiyyah ta gane lallai mace ta yi sa'ar mijin da idan ta kyautata masa ya yaba mata ma ba qaramin abu bane, duk wahalar da za ta yi dan taga ta kyautata masa ba zata tashi a banza ba.
(Abinda ya yi qaranci kenan yanzu ya na wahala maza su yaba wa matan su, mace sai ta jima ta na wahala dan faranta ran namiji amma kallo ma bata ishe shi ba balle ya yaba mata,amma idan ya ga wata a waje wadda ba muharramar shi ba ya dinga yaba mata ta na gwale shi, kuma haka zai ci gaba da yabawar wataqila ma har da tukuici kamar wani mara zuciya, ya bar halal ya tafi yabon haram)
Sad'af sad'af na miqe zan bisu amma 'yar nan ta banko qohwa ta ruhe wai kar na bi su sai gobe mun haÉ—u.............
[22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅ðŸ¼Â  ' YAN ABUJA  💅ðŸ¼
 Â
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.