Complete Hausa Novels

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 26 of 37

Page 25:

Tun fitar Alhaji Salihu da safe suwaiba ke zaune tana ta saqa da warwarar neman mafitar yanda za ta kubuta a gidan amma shiru bata samu mafita ba,ta yaya aka yi ta rasa albarkatun qirjin ta? Ko dai da gaske 'yan fashin ne suka yi mata wannan ta'asar, anya kuwa ba maganar Saudat bace gaskiya Alhaji É—an qungiyar asiri ne masu tsafi da sassan jikin bil'adama? WaÉ—annan tambayoyin da ma wasu tunane tunanen ne suka haÉ—u suka yi wa suwaiba yawa ta yanda ko sallah bata tashi yi ba balle ta nemi abinda za ta ci duk tsawon lokacin nan.

Shi kuwa Alhaji Salihu yana can ana sa toka sa katsi tsakanin shi da Oga Zaks akan wata yarjejeniya da suka kulla wadda ko Alhj Kalla bai san da ita ba,kafin Oga zaks ya amince za su bar suwaiba a raye ba za su kai ta d'akin duhu ba dodon tsafi Itama ya zuqe Jinin ta bayan an yanke nonon ta, sai da Alhaji Salihu ya É—auki alqawarin idan ta warke an kwana biyu zai kai wa Oga Zaks ta yi sati biyu wajen shi, wannan yarjejeniya ce ta d'aga masa hankali har ya je wajen Ogan nasu dan a bincika idan akwai wani abu sassauqa a sassauta masa ya aikata,dan kuwa a wannan karon ba zai iya bada matar shi a Kai wa wani qaton ya na kwana da ita ba ko da na kwana É—aya ne balle har tsawon sati biyu,ya kamata a kyale ta haka ta wahala kuma shi fa yana son matar shi yanzu.

Duk bayanin da Alhaji Salihu ya yi wa Oga Zaks sam ya qi aminta da shi,yace shi fa bai san zance ba, nan da sati É—aya zai buqaci a Kai Masa ita in dai ya na so dukiyar shi ta dore ba tare da ya samu matsala ba, dan kuwa idan har bai kai masa ita ba duk abinda ya same shi shi ya sani ya kuka da kan shi kar ya É—ora laifin akan kowa, hankalin Alhaji Salihu a tashe ya koma gida.

Zaune ya tadda ita ta fada dogon tinani ba ta ma san shigar shi parlourn ba, qarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita a doguwar kujera, a hankali ya zame ya É—ora kan shi a cinyar ta ya rufe idon shi, cikin kulawa da tsoro ta fara shafa kanshi sannan ta ce,

" Alhjna me ya faru? Me ke damun ka haka? Dan Allah ka barni na koma gida na amince zan rufa maka asiri ko dan darajar son da nake yi maka, ba wanda zan sanar da halin da ake ciki ni dai ina so rayuwa ta ta tsira"

Bai bata amsa ba sai ma hawaye da ta gani ta gefen idon shi suna sauka, hawaye ne na nadamar shigar shi wannan qungiya da ya yi tun farko a rayuwar sa, dan yanzu soyayyar Suwaiba ta yi masa yawan da ta sanya shi farkawa daga baccin son abin duniya da yake yi,duk  da ya san ita har yau tana nan akan bakan ta na son cin daula,matsala ɗaya wannan babban rashin kadarar qirjin ta da ta yi ya sani da zata samu wata damar da zata zauna da shi ko dan kud'in shi, a hankali ya ce,

" Baby ki kwantar da hankalin ki akwai maganar da zamu yi dake yanzu, wadda na san kin sani an kuma sanar dake gaskiya tun kan ku dawo son abun duniya ne ya rufe maki ido ki ka sake dawowa,"

Tashi zaune ya yi da kyau suna fuskantar junan su ya riqe hannayen ta ya fuskance ta suna shaqar nunfashin junan su, kanta har juyawa yake saboda tsoro, tana matuqar jin tsoron ya tabbatar mata da abinda Saudat ta faÉ—a duk da ta ga manyan alamu a yanzu,tun da gashi ya yi nasarar maida ita Nonoless and mahaifaless,tinanin ta ya katse ne a daidai lokacin da kalmar da take matuqar jin tsoron tabbatuwar ta ta daki dodon kunnen ta,

" Ni Alhaji Salihu É—an qungiyar shan jini ne, domin samun kuÉ—i É—aukaka da qarfin iko"

Wani irin ihu suwaiba ta kurma ta dafe qirjin ta da yake a shafe kamar na matashin saurayi,miqewa ta yi jiki na rawa kamar mazari dan ta nesanta kan ta da shi amma jiri da duhun da take gani sun sanya ta komawa ta zauna ,lallai maganar Saudat ta gama tabbata a yau, maganar zargi da waiwai ta qare,hannun ta ta kai jikin fuskar shi dan ta taɓa shi ta tabbatar shi ɗin ne kuwa ko dai wani ne ke tsokanar ta dan kawai a hana ta cin daular da Alhajin ya tara? shi kuwa ya na jin hannun ta a fuskar shi sai kawai ya dora hannun shi saman nata, saurin zame nata hannun ta yi tare da rushewa da kuka sosai, cikin kukan tace,.

"Me yasa ka ke sanar dani wannan mugun labari yanzu? Me yasa tun kafin aure baka sanar da ni ba na nemi wani mai kud'in na halal na aura na ci dukiyar shi da gaske ko da kuwa kullum safiya duka na yake yi? Ka sanar da ni ne yanzu saboda sun ce ka kai ni yanzu a yanken qafa ta ne ko hannu, Ko kuma kaina suke so a yanke yanzu kai kuma ba zaka iya kai ni ba? Me yasa ka zaɓi shan jinin mutane ka yi kuɗi? Ina da son kuɗi da son abun duniya sosai na sani, amma ba zan iya kashe mutum domin samun su ba, son kuɗi da abin duniya tane ya sa Saudat tana sanar dani na rufe ido ƙwaƙwalwa ta ta toshe zuciya ta ta rufe na qi yarda, mene ne hukuncin da ka yanke yanzu akaina har ka ke sanar dani wannan mummunan maganar?"

Shi kan shi Alhaji Salihu hawaye ne ke zuba daga idanun shi,tabbas so ba karya bane ba, yanzu ya gane ya na son  suwaiba so mai tsanani, cikin muryar lallashi ya ce,

"Babe Dan Allah kwantar da hankalin ki"

"In kwantar da hankali na, ta yaya kenan? Bayan wannan mummunan labarin da ka sanar da ni ka ke tsammanin kwanciyar hankali daga gare ni? Ta ya ka ke tsammanin in sake yarda da kai da duk wani abu da zai fito daga bakin ka?"

Ta qarasa maganar ta cikin matsanancin kuka mai cin rai, a idon ta kuwa ba wanda take hangowa sai Goggo Sarai, ta yi dana sanin kasancewar ta uwa a gare su a yau, da ace ta basu tarbiyyar mai kyau irin wadda ta dace da basu zama masu son abun duniya ba, da idon su bai rufe da son  kuɗi ba har su nemo mazaje masu yin kuɗi da sassan jikin mutane su aura har a dinga bata alamu sannan afito fili a sanar da ita abinda suke aikatawa duk da haka ta yarda ta sake dawowa saboda tsabar son abun duniya.

Yanzu gata a cikin babbar matsalar da bata san ta yanda za ta yi ta kub'utar da kan ta ba.

"Wayyoo Allah na rayuwa ta, yanzu ya zanyi na ci gaba da rayuwa kun riga da kun nakasa min rayuwa? ka fad'a min yanzu a wanne matsaya ake dan na tabbata wani abun aka sake buqata a jiki na za a yanke shi yasa ka damu ka ke sanar da ni gaskiya, ka faÉ—a min menene kuke buqata kuma a waje na yanzu !"

Da sauri ya share hawayen da ke kwaranya a idanun shi sannan yace,

" Ogan mu ne da muka yi yarjejeniya da shi akan in ba a kashe ki ba zan kai masa ke har na tsawon sati biyu ,shine yake da buqatar ki ko ya dauki fansa akaina, farkon zuwan ku ma sai da muka kai masa ku kuka zauna a wajen shi na tsawon sati biyu ya  huta da ku, a cewar shi Kuna da wani sirri na musamman wanda ba ya da misali, wannan shine dalilin da ya sa ya ce na kai masa ke a madadin alfarmar rashin kashe ki da ba ai ba "

Wani ihun kuka Suwaiba ta sake sanya wa sannan ta miqe  ta hau kan Alhj salihu ta na duka tun qarfin ta, qarshe da taga ko gezau bai ba sai ta kife a wajen tana ta rusar kuka ta na fad'in,

"Kaico na ni Suwaiba, kaico na, na shiga uku,yau ina zan saka kaina, ga abinda son abin duniya nan ya jawo min, a yau duniyar ta juya min baya, bata riqe ni a matsayin masoyiya ba kamar yanda na so ta, yanzu ni aka kaiwa dan shan jini har tsahon kwanaki goma sha huÉ—u bai biya sadaki na ba, sannan yanzu da aure na za a sake Kai masa ni na tsawon wasu kwanaki goma sha huÉ—un,lallai ni suwaiba yau na ga yanda rayuwa a Abuja take,"

Qanqame ta Alhj ya yi yana shafa bayan ta da sigar lallashi, fizgewa ta yi cikin son jin qarashen labarin nasa ta ce,

"Uhumm ina jin ka? Kana nufin kai masa ni É—in za ka yi shiya sa ka zo kana sanar da ni wannan mugun labarin ko me?"

Da sauri Alhaji Salihu ya ce,

"Ko É—aya suwaiba ba inda zan kai ki, da ina so na kai ki ai ba zaki sani ba ma zan kai ki, da da muke diban jinin ku dik wata sani ku ka yi?"

Zaro ido ta yi kamar su fad'o qasa dan firgita da tsoron shi, baya ta fara ja ta durqusa a guiwowin ta ta na kuka ta ce,

"Dan son ka da annabin rahama kai yi min rai kar ka qarasa ni,dan kuwa yanzu ni da mamaciya bamu da maraba, banda mahaifa, banda nono, jini na duk wata ake kwasa kamar a teku, an kaiwa wani qato ni ya gama kwana da ni kamar wani miji na, yanzu kana shirin maida ni sai ta Allah kuma, ina ga sa'i na ne ya zo,Allah ka ji qai na ni suwaiba"

Matsawa ya yi zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu ta yi d'aki ta na ihu, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,ya yi saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin ya yi mata rai ta tuba, ya maida ma baban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai shi yasa ko tunanin ta bata yi ba, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata da ya rage, tura wa ya yi da qarfi ya janyo ta jikin shi cikin ɓacin rai ya ce,

" Ke! Ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki da tini  ban kai ki ba ko kuwa sauran duk sanin an je ki ka yi? ba sai yanzu dana sanar dake bane ki ka sani? Na faɗa maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba wannan shine iya adadin soyayyar da nake maki, ina son ki suwaiba zan iya sadaukar da rayuwa ta saboda taki ta tsira"

Ya qarasa maganar shi a hankali wanda ya sa jikin ta yin sanyi, qanqame shi ta yi tana kuka sosai,Itama ta ce,

"Ba na son na rasa ka Alhajina, nima ina son ka sosai, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kud'in ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu"

Jin kalaman ta ne ya sanya Alhj Salihu kuka kamar wani yaro,haka so yake,shi  SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka suka yi ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko suka ji na asuba, kasancewar dama bai dawo gidan da wuri ba tun safe da ya fita.

Suwaiba tashi ta yi daga jikin Alhajin nata jiki duk ba k'wari,yau ce rana ta farko a rayuwar ta da ta yi alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai dan ya yaye mata damuwar ta.

Shima Alhaji daya ga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi suka yi nafila,suka hau addu'a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al'amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu'ar ne suka yi sallar subh  suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita kuwa inaaaa yaushe taga na barci ana shirin kaiwa matsafi ita, lallabawa ta yi ta buɗe wajen da take aje kud'ad'en da yake bata ta d'iba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dauki makullin mota babbar ciki a motocin shi,Saida ta loda kayan ta a ciki sannan ta hau ta nufi gate mai gadi ya buɗe mata ta fice ta bar gidan a guje.

Hanyar kano ta É—auka duk da cewar bata gama gane hanyar ba ta tabbata zata iya kai kan ta gida,haka suwaiba ta dinga bin rubutun Sunayen garuruwan da ke kan hanya tana shara gudu a Saman titi har ta isa cikin garin Kano

Haka ta isa gida a firgice, Alhj kuwa bai farka ba sai azahar, miqa hannu ya yi dan ya tab'o Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba a ran shi dan ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi ya yi ya lumshe ido,tunani yake ya kamata ya haÉ—a mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda suka yi da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa ya yi zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare ya na shiga yaga wayam ba kowa a ciki, fita ya yi palour nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan ya yi yaji shiru bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man ya ce,

"kai Audi ina Hajiya?"

" Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar tun da sassafe"

Cike da damuwa ya hau shafa kanshi, komawa ciki ya yi zuciyar shi cunkushe da tunani kala kala,shin ya take a yanzu, ta samu nasarar isa Kano lafiya ? Tinda iya sanin sa bata gama kware a tuqi ba, gashi a yanzu tana cikin halin tsoro da firgici, kar wani abu ya je ya same ta a hanya.

Ɗaya bangaren na zuciyar shi ya ji haushin yanda ta iya guduwa ta bar shi ba tare da sun yi koda sallama bane,ta san ya na son ta ba zai bari wani abun cutarwa ya sake rabar ta ba, kuma Itama  ya ga soyayyar shi a tare da ita.

Wayar  shi ya dakko ya hau kiran ta dan ya ji ina take idan kanon ma ta gudu ya ji shin ta isa lafiya ko ta na hanya ne bata isa ba,wayar na ta ringing bata d'aga ba, hakura ya yi da Kiran ta ya je ya yi wanka ya yi sallahr da ya jima da dena yi sannan ya fita ya bar gidan.

Qarfe uku na rana a qofar gidan su ta yi mata, hankali tashe ta kashe motar  ta buɗe ta fada gidan tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana'ar shi a yanzu suka je za su taro ta, sai dai ganin ta shiga da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka yi ta maza suka tsaya, tsayawa suka yi suga me ya koro ta shiru ba wanda ya biyo ta,ta na qarasa shiga ta fada jikin Salma tana kuka tare da fad'in ,

"Na shiga uku Salma na halaka kai na da kai na, Saudat kinyi gaskiya Alhj da kanshi jiya ya tabbatar min shi É—an qungiyar asiri ne masu shan jinin mutane da tsafi da sassan Jikin su, duba ku gani yanda aka maida ni mata maza"

D'aga masu rigar ta ta yi suka ga yanda qirjin ta ya koma babu komai fayau kamar filin ball,a daidai nan Goggo Sarai ta fito cike da tashin hankali sakamakon jin abinda Suwaiban ke fada............
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.