Complete Hausa Novels

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 36 of 37

Ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta ya yi da sigar lallashi,a haka bacci mai daÉ—i ya É—auke su.

*****************************

"Ki taho da fidar yaran nan da tissue love"

Salma amsawa ta yi shi kuma Ibraheem ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su ta miqa masa abinda ya ce ta kai, cikin tura baki irin na shagwab'ar nan Salma ta ce,

" Ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe zan zauna su kuma a cinyar ka?"

Driya ce ta kama Ibraheem, sai ya dauki Hassana ya É—ora a wuya, sannan ya d'ago Salman ya saka a cinyar shi ta na facing É—in Hussaina,murna ta hau yi tare da sumbatar kuncin shi ta ce,

" Na goooode na zaci ai ce min za a yi na yi hakuri yaran su zauna na yi girma kamar yanda ka saba,da kuwa yau ba zan yarda ba sai dai a maida su d'aki ni na hau"

Ta ƙarasa maganar ta tana sauka daga cinyar tashi, dariya yake sosai dan ya kula da Salma ta na kishi da yanda yake share ta idan ya na tare da yaran, gani take yi gaba ɗaya ya kwashe soyayyar ta ya basu dika, lokacin shi gaba ɗaya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin daɗi take ji ba saboda yanda yake son yaran kamar nashi, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai taɓa aure ba kuma gidan su babu qananan yara balle ta ce ya iya reno.

A cikin kujerar basu abinci ya saka su,ya É—orawa kowa nata abincin a gaban ta, sannan ya damqa masu cokulan su a hannun su na dama,da kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, yana tsaye a kan su in ya ga zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta,

"I love u"

Shima waiwayar da kan shi ya yi suka hada ido yace mata,

" I love u more my wife"

Tare da sumbatar goshin ta ya juya ga yaran su suma ya yi musu,Salma ta tura baki ta ce,

"Na hakura ni dai na saddaqar an fi son su akai na, ba za a taɓa yi min abu ba sai an yi musu suma"

Dariya ya yi kawai dan ya san idan zai biye mata haka za su kwana ta na masa qorafi.

Jama'a ina so mu gane cewa shi d'a na kowa ne, baka san wa zai more shi ba,shi yasa bahaushe ke cewa da d'a da dukiya ba a yi masu mugunta, in ka lalata su wataqila kai ka lalata wa goben ka da al'umma, idan kuma ka kyautata musu wataqila su amfane ka a gaba ko su amfani al'umma, wani sai ya gama tarbiyyar yaron ya girma saura qiris ya fara morar shi sai ya rasu ya bar wa duniya ta mora,wani kuma sai ya lalata tarbiyyar sai ya mutu ya bar wa duniya mugun iri ko rayuwar shi ta yi tsaho ai ta shan wahalar da shi,wanda ya kyautata ya na da lada mai yawa a wajen Allah, wanda kuma ya munana shi ma ya na da zunubi a wajen Allah .

*****************************

Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, ko ma dai me ta haifa zai kai mata kayan ya fi ya je hannun shi na dukan cinyar shi,sallama suke yi da Marka wadda can cikin qasan ranta kishi ne danqare,sai ta danne kishin nata saboda yanzu ta waye ba duhun qauyanci da mummunan jahilci a tattare da ita, miqa masa leda ta yi wadda ta daka kuka,daddawa, da kub'ewa, tace ya kai wa Salame, godiya ya yi mata,Huwaila ma shiga sashen nasu da qullin ledar gyada soyayyiya itama ta bashi, dan sana'ar ta kenan a yanzu, tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa ya yi ya fita bakin shi É—auke da addu'ar fita daga gida........

*To masu karatu Talle fa ya yi shirin zuwa Ta dabo,kun dai ga ya koma islamiyya har da addu'ar fita daga gida...*
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏻 'YAN ABUJA 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.