Complete Hausa Novels

Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 37

Page 7:

Juwairiyyah na nan tsaye cike da tarin tambayoyi da mamaki ta ji Innarmu na fad'in,

"Shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba É—aya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida ya yi da mun gaisa wuf ya tashi ya tafi wajen ta, ya dan zauna ma mu yi hira yanda muka saba sam ai yake yi,to an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min d'a kamar yanda uwar ki ta yiwa uban ki ba in dai ina raye, haka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa tsakanin ni da ke"

Kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma?

" Ya Allah ka taimake ni na ci wannan jarabawar"

Abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen ta yi tai wanka, ta yi brush sai ta koma daki ta tsaya cikin madubi ta gyara gashin ta da ta wanke ta shafa wa mai sannan ta taje shi ta daure a bayan ta, buÉ—e wardrobe É—in ta tayi ta tsaya kallon kayan ta ta na nazarin wanda zata saka, kafin daga qarshe ta yanke shawarar dakko wasu riga da wando rigar pink wandon baqi siriri Wanda ake kira da pencil, Inna Deejee ce ta siyo mata su a 'yan gwanjo,tin su dai basu da halin siyan sabbi,kayan sun amshi jikin ta ba kadan ba, fita ta yi ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta feshe jikin ta da tirare ta qara da humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan wato kayan qamshi, kafin kace me sai ga Juwairiyyah ta fito chass da ita,da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ce, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo tana murmushi ta ce,

"Dad'i na da ke matar Yaya ba dai tsafta da qamshi ba,kina burgeni fa ba kaÉ—an ba,ko ta wacce gab'a aka latsa ki kina nan kyam, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da wani babban ma bai da shi, duba kiga yanda ki ka yi mana dabara d'azu, Innar mu da ta koma d'aki da ta ga abincin da ki ka kai mana ban san me ya razana ta ba, dan na ji harda ashar ta baza mana a dakin dazun"

Nafee ta qarasa maganar ta cikin dariya, Juwairiyyah ma dariya ta yi ta ce,

" kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai"

Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa ta yi ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi,tare da wani lumshe ido kamar mai jin bacci ta isa wajen shi, ledar hannun shi ta Karb'a, sannan ta jawo hannun shi zuwa d'akin su, suna shiga kamar jira yake yi ya d'aga ta sama ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta ta yi a kan tashi, tare da hade bakin su waje É—aya, sai da tayi masa kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa,

" Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena"

Hura masa iskar bakin ta ta yi a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi suka zauna ya na sauke ajiyar zuciya,cikin kasalalliyar murya Jabeer ya furta,

" Agaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahalake É—aya ce tamkar ba iyaka, samun kamar ki a cikin mata million zai wahala, in zance zan tsaya fad'an wacece ke bakina zai rasa kalaman magana,so kawai ke kadai ce ba ta biyun ki , kuma ke É—aya Yah Jabeer din ki ya ke so har abada ba na jin zan so wata kamar yanda nake son ki"

Wani irin daÉ—i ne ya lullube Juwairiyyah, kamar yanda kullum take son faranta mashi rai shima qoqarin shi kenan ya ga ya faranta mata rai, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zata yi daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi sannan ta miqe, gwalo ta masa ta tafi da sauri zata yi d'aki, binta ya yi a baya yana fad'in,

" Ai baki isa ba ki tsokanen ki gudu yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai"

Dariya take tana bashi hakuri,dan ta san tabbas ya na jin yunwa,

" Dan Allah Babe ka bari kaci abinci ka yi wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau sai abinda ka ce shi za a yi"

Tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa ta yi ta haÉ—a masa ruwan wanka,kafin ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga suka yi bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta masa da kyau ta sa masa toothpast a brush din shi ta bashi dan ya wanke bakin shi.

Mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanin ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki yi, ki haÉ—a maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a ba, daga nan sai ku yi wankan tare, in ba ku yi tare ba ma saboda maybe yanayin gidan naku, sai ki saka masa ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musamman yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har ya yi feeling bad kuzo kuna samun sabani.

A d'aki ma Juwairiyyah Bata bar jabeer ba sai da ta gyara mai jiki tare da feshe shi da tirare, palour ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumi da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi

" kaiiiii amma ba qaramin birge ni ki kai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?"

"Alhamdulillah na ji dad'i da yabawar ka Hubby"

kusa da ita ya matsa sannan ya ce,

"Ai dole in yaba saboda ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare har a aljannah"

Murmushi suka yi dikan su suka ci gaba da cin abincin su, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi kiran sallahr suma, bayan an idar ne suka yi addu'ar da ake yi ba yan idar da kiran sallah,wato

" Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah."

Sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addu'a suka d'aga hannayen su sama suka yi a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi suka yi alwala, shi ya tafi masjid ita ta yi sallar ta a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu ta yi kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je d'akko dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta had'o da ruwa da komai da ya dace ta ajiye a gefe, d'aki ta shiga ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta É—ora zani akai da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 Jabeer ya shigo,abinda ya tsayar da shi kuwa sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta ne ke damun ta sai ta yi qaryar kanta ke yi mata ciwo, dan yau wuni tai da yunwa bata ci abinci ba, can kuma sai ta saki fuska ta ce,

" kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba"

" Ba komai Inmar mu kawo na kai mata za ta yi maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba"

Dan haka da sallama ya isa sashen su riqe da ledar shinkafar a hannun sa,daidai Juwairah ta fito daga d'akin ta ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki ya yi kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa ya yi ya aje ledar shinkafar a qasa still idon shi na kan Juwairiyyah, juyawa ta yi ta koma d'aki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana masa wani mayen kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar ban qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake yi, sayyarar qafa ta na ja na yi waje, ji nake kamar na kai wa Innarmu gulmar me ke faruwa.

Qarfe hudu na asuba suka fito suka yi wanka tare da alwala mai kyau suka koma dakin su, bayan sun shirya ne suka fara gabatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu ya yi dan yaga meye a wajen, dagawar nan da zai yi sai ya ga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, cikin damuwa da tashin hankali ya ce,

" Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni ta yi fa jiya na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba É—aya na manta"

"Haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi ai bayan haka Innarmu ce fa ta baka umarnin a yi abu be kamata ka shagala ba gaskiya ban ji daÉ—in abinda ka yi ba,"

A qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dad'a mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa ne mai tinawa da shi a kowanne hali yake musamman idan bawan na yawan neman taimakon Allah a dikkan lamuran shi, da bata zama mai neman taimakon Allah a komai ba da bai taimaka mata jiya ba,gashi bata san me aka qulla mata ba Allahn ta ya kare ta, kiran sallar asuba ne ya katse su daga mayar da magana akan abinda ya faru jiyan Jabeer ya tashi ya fita masjid ana yin sallah ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tayi azkar da karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, daki suka shige suka É—an miqe dan su maida bacci,tund Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha a ci gaba da rayuwa, har bacci mai nauyi ya fara É—aukan su suka jiyo sallama daga bakin kofa.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA.  💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.