Yan Abuja Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yan_Abuja_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 37
Page 17:
Tun da Jabeer ya sai wa Juwairiyyah waya ba su samu suka haÉ—u da Nafee ba sai da aka kwana biyu,domin kuwa a washegarin ranar Nafee ta tafi gidan wata qanwar Innarmu ta yi masu kwana biyu, dawowar ta da yammar ranar ke da wuya Juwairiyyah ke nuna mata wayar cike da zumud'i da murna,cikin fara'a ta amsa sallamar Nafeen sannan ta qara da,
"Wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya sai min da bakya nan"
Da sauri Nafeesah ta qarasa shiga itama cike da d'okin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama 'yar qaramar qarar murna ta yi ta haye kujerar da Juwairah take tare da fad'in ,
kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye"
"To malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa"
"Hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna ɗauke ta kema kin San zan ririta ta, yanda kk san jariri haka zan kula da iya sai kin neme ta sannan zan miqo maki, ko kuma idan tana buqatar a sa mata kudi"
Dariya suka yi a tare sosai, sannan Nafee ta ce wa Juwairiyyah,
" Yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi? Tunda na shigo nake jin kamshin na tashi ko shayi za mu sha ne na musamman"
Dan dafe kirji Juwairiyyah ta yi sannan ta ce,
" Oh ashe ban cire ba dama? Dan je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambai"
" Ah tohhh dole ki min bayani dalla dalla dan kin san in baki fad'an ba baki da zaman lfy yau"
Fita ta yi ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, zama ta yi tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace,
" To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi"
" ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike yi ni fa ina zaune a gida kullum ba wani ci gaba da karatun da na ke"
" kema zaki ci gaba ne watarana komai lokaci ne sis kar ki damu,oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?"
Dariya Juwairah ta yi sosai sannan tace,
" ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan "
"To na ji magani ne amma ai baki fad'an ya ake haÉ—a shi ba ko"
"Haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana É—auke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin ana sha, kin ga na ciki na mutuwaaa na waje ma ana kashe shi, amma idan mace bata da ciki zata iya neman sassaqen sanya,bagaruwar mata,lemon tsami, d'anyar citta,kaninfari,masoro,kimba,danyen kurkur, ganyen magarya,sai ta haÉ—a su waje É—aya ta dafa ta dinga shan ruwan, ta yi na sati biyu ita da mijin ta da kishiyar ta idan mai kishiya ce saboda su yi maganin abin a lokaci d'aya, in shaa Allahu Zaki ga an samu sauqi gefe d'aya ana tsarki da wancan ruwan garahunin,sannan wannan had'in ga masu neman haihuwa in dai matsalar ta danganci infection to da yardar Allah zai wanke mahaifa a samu ciki, sai dai kuma idan matsalar ba wannan bace sai a nemi maganin matsalar,"
"Yauwa 'yar albarkan Yah Jabeer ko ke fa, ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma na san wannan abun in ba yanzu ba, yauwa rannan ma na ji kina faÉ—a ma shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba dan Allah ki yi min bayani akwai wata a department din mu ba zaki so zama kusa da ita ba sam saboda wari"
" Ohh wannan ai ta na tare ko da babbar matsala gaskiya,in ki na so ki yi maganin matsalar warin gaba dole sai kin san kala kalar shi,na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta"
"Hhhhhh ka ji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta to kamar yaya? Kana sane kabar jiki ya yi ta tsami"
Dariya suka yi a tare sosai suka tafa, sannan Juwairiyyah ta ce,
" Allah da gaske nake yi, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant É—aya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai ki ke mayar wa, ki fadan min shi pant din d'an uwan ku ne da zai qi yin wari?"Â
Wata iriyar dariya Nafee take yi, cikin dariya ta ce,
" Whhhhhh alqur'an dole yayi wari, amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma"
" wulaqanci Yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan daÉ—i an manta da dangi"
" Hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi"
" Ameen dai"
" To yanzu fad'an ya za ai ayi maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu na faÉ—a maki, da kin zauna kusa da ita sai kin ji wannan warin,ni ba zan ji kunyar faÉ—a mata duk bayanin da Zaki yi min ba, da azo ana ta gulmar ta ko ana gudun ta ta na jin haushi ai gwanda a faÉ—a mata matsalar ta da maganin matsalar ta gyara ko? Wataqila bata samu iyayen da ke koya mata ba kin san wasu iyayen ba su koya wa yara su komai kin dai gane me nake nufi"
Ta faÉ—a tana nuna hanyar sashen Innarmu,qunshe dariya suka yi sannan Juwairiyyah ta ce
" Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi idan ya ga irin haka na faruwa da shi,to kina ji ba,na son a rana a baki canja pant ba ki canja sau biyu, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in ki ka yi fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan bayan kin yi tsarki tunda yanzu yawanci banɗakunan na masu da shi ne tsarin ginin za ka iya ajiye qaramin towel,sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki yi komai ba, sannan baya ya zama na qarshe, karki hade wajen a lokacin wankewa, in kika gama ki goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kika yi wanka sai ki canja,in da hali da dare ma kan ki kwanta ki caja, ba yanda za yi a same ki da wari ko da baki shafa misk ba, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da ki ka zuba musk, ko ki saka ruwan d'umi kaɗan bayan kin gama wanka ki tsiyaya zuma asalin mai kyau ki wanke gaban ki da shi,yana daga taskar magunguna da ya kamata muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki gaba ɗayan su yanzu Hajiya tambai"
"Hhhh kwarai da gaske Juwaireren Mama da Yah Jabeer kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lafiya"
Cikin jin daÉ—in addu'ar Nafee ta hau shafa cikin ta sannan ta amsa, tashi ta yi ta shiga bayi dauke da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee,
" Nafee na ga kina zare ido, kar fa ki je ki yi fitsari ko ba haya ki hau tsarki da ruwan almiski kin dai san ba ya tsarki , ana tsarki ne da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa,ah toh gwanda na yi maki bayani dalla dalla kamar yanda ki ka ce, yauwaa kin San fa gobe ne ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare,dan Allah in an samu ki zo ki taya ni kin dai ga yanda na koma ba zan iya yi ba ni kaÉ—ai"
"Haka ne bayanan ki, maganar dankali kuma kar ki damu zan samo maki kan goben in shaa Allah,in ba ke ba ma wa yake ta wani gyaran jiki a wannan yanayin,ji cikin ki fa ya girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana"
" Tab a'a ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar sai na yi amfani da su kawai lemon zaqi ko É—aya ne ko biyu Zaki samo min"
"To Allah ya kaimu da rai da lafiya bari na yi wanka na fita makaranta"
"To Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".
*****************************
A Abuja garin shugaban qasa kuwa Talle ne ya sanya manya kaya har da hula shiga dai ta kamala ya yi ranar ya sanya Salma yin shigar kamala Itama suka shiga sashen uban gidan shi dan ya gabatar da Salma a matsayin iyalin shi, cikin wata murya mai cike da ladabi Talle ya ce,
" Alhj wannan itace mata ta da kuka Karb'a min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni É—ayan ba daÉ—i"
Talle ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi ya yi sannan yace,
" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da ka yi kayi tinani mai kyau,sannan kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba"
" Ameen"
Gaishe shi salma ta yi kanta a qasa tana wasa da gyalen ta,shi kuma ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kuÉ—i ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa ta yi hannu na rawa,dan kuwa rabon ta data riqe kuÉ—i haka ai ta manta, tashi suka yi suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu fuskar nan ba walwala, ita ma ta d'aure tata fuskar ta ce,
"Me zan maka kuma"
Ta karasa maganar ta cikin tsiwa,
" Kee! ni za ki tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan"
Alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa masa kud'in tana hawayen baqin cikin ganin samu ga rashi a lokaci d'aya, murmushi ya fara yi saboda jin dumus É—in kuÉ—i da ya yi,
" Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko"
Juyo wa ta yi cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa yin maganar da ke bakin ta ,wani irin tsoron shi ne kamata saboda yanda yake kallon ta,gani ta yi yana cire kayan shi ya na nufar ta, hankalin ta ne ya tashi dan ko bata shirya ba masa ba har a wannan lokacin ciwon jikin da take fama da shi bai tafi dika ba, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana fad'in,
"Ni na bar maka É—ari biyar É—in dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lafiya fa ka sani"
Dariya Talle ya yi sosai ya maida kayan shi, ya kalle ta ya ce,
" Da kyau matar manya matar ÆŠan Abuja, ku baku da buqatar kuÉ—i ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma a ciki"
Nera É—ari biyu ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka Salma ta durqusa a wajen tana yi tare da fadin,
"Wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin daɗin su sun manta da rayuwa ta, basu san a halin da nake ciki ba,Oh Allah ka kawo min ɗauki, Allah na tuba, Juwairah kin huta, da baki bi zabin aure irin nawa ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin auren a cikin shi, na manta da neman zaɓin alkhairin Allah a lamura na,wataqila da na nemi zaɓin Allah da ko mummunar jarabawa Allah ba zai haɗa ni da ita ba a Abuja,sai na biye wa son zuciya gashi ina ganin b'acin zuciyar har da gangar jiki na, wayyooo Allah na na shiga uku ni Salma ina zan saka kai na?"
kuka take ta yi mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita cikin hayyacin, tashi ta yi ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, haɗawa ta yi tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su a can gidan iyayen ta ba su shan gari, amma yau gata da gari ba isasshe sugar , share hawayen ta ta yi, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta.
****************************
Parlour ne na alfarma da ya sha kayan more rayuwa kala da kala, matan biyu masu ji da kyau da nera na zaune su na shan kayan marmari da lemo irin na manyan kwalaben nan mai tsada, saudat ta kalli yayar ta ta da tsabar kwanciyar hankalin da take ciki ya sa ta dan yi qiba kaÉ—an irin mai ban sha'awar nan ta murje fata sai sheqi take, alamun bata da wata matsala a rayuwar ta, dan gyara zama Saudat ta sake yi a karo na ba adadi sannan ta ce,
"Ni kam Adda Suwaiba ki na tunanin kai ziyara gida kuwa? Ina gani fa ya kamata mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa muna cikin na tara amma bamu taba zuwa gida ba sannan ba a taɓa zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu ko waya bamu yi mun ji daga gare ta ba"
Iska Suwaiba ta furzar sannan ta kora jusi ta ajiye glass cup É—in ta ce,
"Hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su a qasar waje da dikkan alama, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan fa"
"Haka ne kuma Allah dai ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki mana,"
"Uhumm Ina jin ki"
"Dan Allah baki taɓa zargin komai game da mazan nan namu ba kuwa?"
ÆŠan yatsina fuska Suwaiba ta yi sannan ta ce,
"Kamar ya fa?"
Tina wa da ta yi in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe, dan haka sai ta yi saurin kauda zancen ta basar tace,
"Ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu je gida"
" Ba rana balle wata"
Amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo,cikin haɗe fuska Alhj Ƙalla ya kalli Saudat ya ce,
" Ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku in ban manta ba, Saudat kan mu yi aure cewa fa ki kai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka yi ba?"
Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace,
" Anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata"
Wani hatsabibin kallo ya watsa mata wanda ya sa ba ta san sanda ta durgusa ta dauki jakar ta ba ta yi hanyar fita, sallama ya yi wa abokin shi wanda daga jin warin da suke yi zai sa mutum ya san sai da suka biya suka yi mankasss sannan suka dawo gida.
Nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......😂
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅ðŸ¼Â   'YAN ABUJA  💅ðŸ¼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.