Adon Dawa Complete Hausa Novel
Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 10
ADON DAWA
.
BABI NA DAYA
.
Rana ta fadi daf da magaruba dogayen motoci kirar j5 har guda bakwai ne suka shigo jahar Maiduguri daga kasar daura, dauke da fasinjoji dari uku da hamsin manya da yara, mata da maxa. Tafiya yankin axaba, hakika matafiyan cikin motocinnan a gajiye suke kallo daya xaka yi musu ka fahimci haka. A layin suke firfitowa daga cikin motocin yayin da duk wanda ya fito sai ya yi mika ya yi hamma saboda yinin da suka yi cur a hanya suna tafiya.
Kaltum ‘yar kimanin shekaru goma sha biyar tana daya daga cikin matafiyan cikin motar nan. A galabaice take a sanadiyar amaye-amayen da ta dinga yi a mota, baya ga matseta da aka yi a lungu kafafuwanta sun kumbura sumtum kamar mai cikin watan haihuwa.
A tsaye take a gefe tana jiran kakrta ta fito daga bayan bishiyar da ta kewaya don rage tumbinta daya cika da fitsari itama ta bata buta ta kewaya. Sai ta ji muryar wasu samari guda biyu suna Magana a bayanta suna Magana dogo da gajere, dogon saurayin ne ya tambayi gajeren. Ya ce “wadannan fa daga ina suke kuma ina xa su je riki-riki da kaya kamar masu gudun hijira!”
Gajeren ya bashi amsa y ace “ ‘yan gudn hijira ne ma ba kamar ‘yan gudun hijira ba. Daga nan ma gaba xasu kara har xuwa sudan xa su tafi a mota, daga sudan kuma su haura ruwa su shiga saudiya. Haka kawai mutanenmu suke wahalar da kansu saboda kwadayi, yanxu wadannan da ka gansu wahala ce xata kashe rabin su a hanya.”
Kaltum ta waiwayo da sauri ta dube su hankalinta ya kara tashi yayin da suka yi ido hudu da kyakkyawar fuskarta wacce ta basu matukar sha’awar dubanta ba kakkautawa. Dogon ya sake tambayar abokin sa gajeren, y ace, “kai, kalli wata kyakkyawar yarinya. Ba dai itama sudan din xa ta je ba!”
Gajeren ya amsa masa da cewa “sudan xata je mana, baka ganta a cikin suba!
A banxa xa a wargaxa mata rayuwarta duk kyakkyawar halittar nan tata a wulakance xa ka gansu a sudan ko makka idan sun samu ma sun haye kenan., rashin tawakkali ne kawai irin namu na ‘yan Nigeria, ba xasu iya hakuri da talaucinsu ba sai sun je kwadayi.”
Kaltum ta sukuyar da kanta kasa yayinda hawaye ya fara bulbulowa daga idanunta tana tausayin kanta tana tausayin rayuwarta. Ganin hawayen da take yi ne samarin biyu suka karaso wajenda take tsaye, suka yi mata sallama sannan suka fara tambayarta sunanta, daga inda ta fito da kuma inda ta nufa!
Babu amsa se kuka take yi kawai da suka ga halamar bata da niyar Magana sai suka fara bata shawara. Gajeren cikinsu y ace, “ ni dai a matsayi na na musulmi dan uwanki shawarar da xan iya baki shine kada ki sake ki tarki wannan tafiyar shiga makka ta sudan a matsayinki na yarinya budurwa gara ki xauna a kasarku gaban ‘yan uwanki koda ace baki da iyaye saboda bala’in dake tattare da irin wannan harkar.”
Muryar kakarta goggo fatu ta jiyo a bayanta ta kwalla kiran sunanta gami da jan dogon salati harda ihu da dora hannu a ka.
Tace, “na shiga uku, kaltum me xan gani! Me nake jiyowa ana fada miki! Ina kika samo wadannan ‘yan iskan da har suke so su baki shawara ki bujire ki fasa tafiya!”
Kan ka ce kwabo kaltum ta fara rawar jiki saboda tsoro da firgici gami da gigicewa duk suka far mata a lokaci guda. Ta fara bayani cikin rawar murya “gwaggo ban san suba wucewa suke suka xo yi suka ganni tsaye, ba xuga ni suke yi ba.”
Goggo fattu ta cije baki ta dunkule hannu ta duma mata dundu a baya gami da wurga mata butar dake hannunta a kafarta. Kaltum ta yi tsalle ta ruga da gudu gefe ta tsuguna tana kuka. Hankalin samarin ya tashi suka fara yiwa goggo bayani cewar ba laifin kaltum ba ne, suma bada niyyar xuga ta suka xo yi ba wucewa kawai suka xo yi suka ganta tsaye. Goggo ta koma kansu ta rufe su da fada tana musu korar kare wai su tafi su bata waje kafin ta farfasa musu kai. Magana daya suka fada mata wacce ta kashe mata jiki.
Suka ce “ke tsohuwa, ki ji tsoron Allah ki san xa ki mutu, Allah xai tambaye ki dalilin da ya sa kike wahalar da yarinyar nan xa ki kai ta makka ki jefa ta a wata matsananciyar rayuwa kin rabo tada iyayenta. Kuma idan ki ka yi wasa sai mun je mun hada kida hukumar NAPTIC da take da alhakin kwatarwa yara hakkin su daman suna neman irin ku masu wahalar da yara musamman ‘ya’ya mata. Kina ganin yarinyar nan ko bata fada ba kowa ya san bata son tafiyar nan dole aka yi mata saboda tsoro gashi a gabanmu mun ga irin dukan da ki ke yi mata da xagi.”
Tsohuwa ta gaggauta barin wajen da sauri gami da fixgar hannun kaltum suka kutsa cikin jama’arsu ma’ana ‘yan tawagar su ta matafiya domin ta tsorota da abinda samarin suka fada mata. Hakika sun yi gaskiya kaltum bata son tafiyar nan tilas aka yi mata.
A wannan wajen su kaltum suka yi alwala suka yi sallolin da ake bin su Axahar, La’asar, Magaruba da Isha’i. kowa ya bude jakarsa ya dauko guxirinsa yana ci, wasu buredi da miya, wasu suka jika garin kwaki da sukari da gyada wasu kuwa fura ce wacce aka murtuke da nono aka shanya ta bushe suka jika da ruwa suka xuba sukari suke sha.
Misalin karfe takwas na dare suka sake duruwa a cikin motocinsu suka ci gaba da tafiya. Kai tsaye garin gamborin gala suka nufa, basu isa ba saida tsakar dare anan suka yada xango. Garin barebari ne amman akwai wasu yaren daban daban, a bayan gari akwai wasu tsofaffin gidajen kasa anan ake sauke su daman an yi su don sauke matafiya irin su, kuma daga nan garin motocin da suka kawo su suka juya xa’a sake musu motocin da xasu ci gaba da tafiya dasu.
A gambori aka wagarar dasu dakunan mata daban na maxa daban, amma a daki daya ana xuba mutane fiye da goma sha biyar, kar ku dauka daki ne mai gado da leda da labule a’a babu ko daya, ciccirarun tabarmi ne na kaba kawannensu sai yayi matashi da kullin kayansa ko jakar kayansa.
tafiya se da suka share sati biyu cur a gambori, jagorin tafiyar su, wato (agents) suna ta yi musu karairayi kala kala su ce yau xa’a tafi gobe xa’a tafi, wasu da yawa sun kusa cinye guxurinsu don haka suka fara sayen abinci da dan kudaden da suka boyo. Saboda gashi ba’a yi rabin tafiya ba ko Nigeria ba’a bari ba guxurin ya kusa karewa. Mutane biyu ne suka riga mu gidan gaskiya a cikin matafiyan tsoho daya da yarinya matashiya daman tun a hanya basu da lafiya anan aka sallace su aka binne, ‘yan uwansu suka sha kuka.
Matafiya sai mita suke yiwa agents babu ranar da yawa daga cikinsu basu yi kuka ba saboda wahala. Daga inda suke xuwa cikin gari yana da nisa haka suke faman tafiya kafin su je su siyo abunda xa su ci ko debo rowan da xasu yi wanka da wanki. Kowa ta kansa yake, babu babba ba yaro, babu mace babu na miji, babu mai taimako ko tausayin dan uwansa. Akwai mata masu ciki da yawa wasu karamin ciki wasu kuwa tsohon ciki ne, wasu masu goyo amma dole kowacce ta fita ta yi doguwar tafiya sannan ta nemo abinda xa ta ci, ta debo rowan da xata yi wanka da wanki.
A ranar da suka cika sati biyu aka kawo musu katuwar motar nan da aka yi ta musamman don daukar kaya wato tirela. A bayan motar aka dura su gaba dayansu su da kayansu kamar wasu shanu. Bayan haka aka jibga masu buhuhunan gyada da ridi wadanda xa’a sayar a sudan har buhu dari duk a bayan motar. A cunkushe suke a tattakure kafada a marmatse babu wanda xai iya mike kafarsa, da yawan su basu sami waje ba a bayan motar sai a saman mota aka loda su.
Kwalta ta kare don haka cikin kasa (sahara) ake tafiya, tafiya suke yi a mota amma a wahale suke tamkar da kafarsu suke tafiya sun jigata don haka rayukansu kowannensu a bace yake, babu abinda yake tashi a cikin motar sai kyara da bakaken Magana a jima kadan ka ji fada ya tashi ana sursurfawa ashar gunduwa gunduwa. Wannan tace waccan ta matseta sai wannan yace wancan ya shure shi aikin kenan.
Bayan sun yini suna tafiya suka isa kusuri, a dawa aka sauke su a nan ma saida suka yi kwanaki biyu. Sai dai kowannensu ya shimfida xaninsa ya yi filo da kullin kayansa. Babu famfo ko rijiya a kusa don haka jarkokin ruwa agents suke kawo musu jarkoki hudu a tartarfawa kowa a kwanonsa ya sha ya jika gari, alwala kuwa sai taimama babu batun wanka.
Daga kusiri sai suka nifi chadi (N’DJAMENA), basu yi niyyar kwana a N’djamena ba amma dole suka kwana a sanadiyyar ruwan da ya dates hanyarsu ta wucewa. Rowan daga cikin dutse yake bulbulowa ya dates hanyar wucewa dole motoci suka dakata har saida rowan ya tsaya, ruwa ya kafe hanya ta bude amma se da shirin tafiya ya wargaje dole suka sauke kayansu daga cikin mota a sanadiyar wasun su guxirin su ya kusa karewa sai sun nemi kudi sannan a ci gaba da tafiya. Nan fa matansu da maxajensu suka baxama cikin gari neman kudi sune dako, wankau faskare da dai sauransu. Satinsu uku a Ndjamena sannan suka kama hanya, a boda kuma ake sake duba takardarsu wato anan ake duba passport da visa sannan su wuce.
Daga N’djamena sai suka shiga Abbashe nan ma a bayan gari suka yada xango cikin rubabbun gidan katako, tabbas basu yi niyyar wuce kwana daya ba a Abbashe amma hakan bai yiwu ba a sanadiyar nakuda ta wata mace ke yi, yini guda ana abu daya da kyar aka samu dan da yake cikinta ya fito, ya fito da rai amma bayan awanni ya rasu.
A ka’idar garin duk wanda ya mutu sai an sanarwa da maigari ya rubuta takarda an nunawa hukumar da abunda ya shafa sannan xa’a yarda a binne gawa. Don haka hankali ya tashi ana tunanin yadda xa’ayi doguwar tafiya xuwa cikin gari, sannan a yi ta dogon bayani kafin su yarda a binne yaron. Daga karshe aka yi shawara a nannade gawar jaririn a kunshe a tsumma sai a sami mutum daya ya xagaya dawa ya binne gawar jaririn. Haka kuwa aka yi aka binne cikin dare. A daren kuma Allah Ya yiwa mai jegon rasuwa itama daman tunda ta haihu bata da lafiya.
Nan fa hankalin kowa ya tashi ‘yan uwanta sai suka yi ta kuka suna kururuwa. Da yawa daga cikinsu kaltum suma suka yi ta kuka duk da basu santa ba, haduwar motace kawai sai dai don tausayin rai da tausayawa kansu da kansu. Dakin da kaltum take shine dakin da aka yi mutuwar don haka a xaune suka kwana tangarai ko gyangyadi basu iya yi ba. Kaltum na lungu jikinta sai tsuma yake, hawaye ke kwaranya saboda tunda take bata taba ganin gawa ba,. Ta ji dama ace itace ta rasu kamar yadda wannan baiwar Allah ta rasu. Tana tunanin yadda rayuwa xa ta kasance mata nan gaba.
Da gari yawaye direban da jagorannin tafiyar (agents) suka hadu suka tafi wajen maigari ,dan gari ne ya jagorance su cikin yarensu mai suna wadai dan rakiyar ya yiwa sarki bayani cewar wadannan baki ne suka xo daga Nigeria xasu wuce sudan, suka yada xango a wajen gari sai Allah Ya yiwa mace daya rasuwa suna so su binne ta a nan. Sarki ya yi amanna ya basu takarda suka je suka nunawa masu jiran makabarta, sannan aka yarda suka binne ta bayan suna sallace ta kamar yadda ake yiwa kowane musulmi.
A ranar suka sake kama hanya suka ci gaba da tafiya, yini guda cur a mota har dare ba tsayawa saida kyar direban ya yarda ya tsaya a wani gari da ake kira Adre suka yi sallah suka ci guxurinsu garin kwaki ne dai, sannan suka ci gaba da tafiya. A xaune suke tangarai, se gyangyadi kowa ke yi a xaune. Gargada ce a dukkan hanyar a sanadiyar rashin kwalta, idan mota tadaka tsalle sai ka ga mutum ya yi sama ya dawo ya xauna dabas, idan aka yi rashin sa’a wanda ke xaune sai ya dawo sama dororo a jikin mutane matsi ya hana direwa a xauna daidai sai dai idan motar ta sake daka tsalle adan ka yi sa’a sai ka sami wajen xama wani kuma ya xama derere shi ba xaune ba kuma ba tsugunne ba, shi ba a kasa ba shi ba a sama ba.
Sai cikin dare suka isa jinene bayan sun yi sallolinsu suka haba garin kwaki da busashiyar gurasa sai suka ci gaba da tafiya, kwana daya da yini daya da yini daya guda cur suka yi a hanya suka isa wani gari da ake kira mukwar. Bayan sun huta a mukwar sai suka ci gaba da tafiya babu abun da yake kan hanyar nan sai namun daji, xuma caba caba ga ‘yan fashi. Basu tsaya a ko ina ba sai da dajin majawara.
Dajin majawara daji ne wanda yake shiru, tsit ko kukan tsuntsu babu balle gidajen bil’adama. Daga nan kowa dakatawa babu mahalukin da xai iya tsallakewa a sanadiyar tsantsar hadarin da ke tattare da ci gaba da tafiya. Dole ne duk motar da ta xo dajin majara sai ta ja ta tsaya a doka har sai motoci saba’in sun cika sannan sojoji su xo su tsallakar dasu saboda mugaye, kasurguman ‘yan fashin da suke fashi a hanyar. Don haka said a ‘yan tawagar su kaltum suka yi kwanaki uku a nan suna jiran motoci saba’in su cika sannan a hayar dasu.
A ranar da suka cika motoci saba’in sannan aka shirya ci gaba da tafiya a lokacin da xa su tafi da yamma wani dankareren maciji ya sari daya daga cikin ‘yan twagar su kaltum, kan ka ce kwabo mutumin ya sassankare kumfa na xubowa daga bakinsa. Jama’a suka bi macijin da jifa amma tuni ya sulale ya shige dawa basu kashe shi ba, daga karshe mutumin ya mutu a wajen, a nan aka binne shi suka shiga motocinsu suka fara tafiya. Amma a kowace mota said a sojoji bibbiyu suka shiga suna harba bindiga sama har sai an wuce mugayen daxuka da barayin suke. Tun da yamman da suke tafe ba tsaya ba har se da gari yawaye, sannan sojojin suka sassauka daga motocin da suka rako suka shiga motocinsu suka juya. Sannan su kuma matafiya suka ci gaba da tafiyarsu.
Tafiyar kwana biyu suka yi ba kakkautawa sannan suka shiga kartum tutu babban birnin sudan. Sun kwana daya a kartum, a wajen garin akwai dakunan katako da aka yi musamman don kwanan matafiya. Da suka waye a nan sannan suka ci gaba da tafiyar, kwana guda cur suka yi a hanya sannan suka isa kartum bahari sai suka nufi bur sudan nan ne inda ruwan daya hada sudan da makka ,ruwanne ya hade da ruwan maliya. Daga bur sudan kuma tafiyar mota ta kare don haka masu mota suka sauke su su da jifgin kayansu suka juya.
Daki ne na guntayen katakwaye joni joni, rufin dakin ma duk hudaddun katakwaye ne baya da katakon nan babu ko kwayar dakunan sai wanda ya ci sa’a ne xai tarar da kwalaye a shimfide a dakin. Ga duhu a sanadiyar rashin fitila gashi tsakar dare suka iso don haka babu wata wata kwanciyar kowa yake so ya yi. Aka ware dakunan mata da na maxa daban, amma a kowane daki mutane ashirin ne xuwa ashirin da biyar duk da haka wasu a xube suke a tsakar gida wasu maxan kuma a xube a kofar gida. Su dai fatansu su kwantar da hakarkarinsu su mike a sanadiyar kagewar da bayansu ya yi saboda kwana da yinin da suke yi a xaune a mota a tattakure.
Misalin karfe daya na dare suka isa bur suban a gajiye suke don haka idanuwansu a rufe suke burin kowanensu ya sami inda xai yada hakarkarinsa. A guje suke rububin hayewa kan wasu tudu da suka iske a cikin dakunnan katakon cikin rashin sani basu san kabarurrukan suka kwanta yayin da wadanda basu sami hawa ba suka bi layi suka doddora kansu a kan kabarurrukan.
Kaltum da kakarta sun yi sa’a sun sami daki, a cikin dakin ma kaltum ta yi sa’ar samun hayewa kan tudun dake tsakiyar dakin. Dan tudun maidan tsawo ne da fadi daidai kwanciyar mutum daya don haka da ta shimfida xaninta aka ta yi filo da dan karamin bacco dake dauke da kayanta sai ta yada kai xata kwanta. Kakar tace ta daka mata tsawa tace “kaltum, kina da hankali kuwa! Ina kasa cikin kasa turmus ke ki sami mulmulallen tudu ki kwanta harda shimfida xani ki yi filo da jakar kayanki ni babu ko daya, to ki sauko kasa cikin kasar ki kwanta nixan haye tudun.”
Kaltum na karkarwar jiki don tsoro ta sauko da sauri, goggo fatu ta haye tudu harda juya baya ta yi kwanciyarta, kaltum ta mike a kasa cikin yashi ta kwanta, burinta ta kwanta da hakarkarinta ma kawai ta huta gajiya. Nan ma manyan mata suka dinga yi mata carin masifa wai sai ta matsa lungu ta babbake musu fili. Ba ta tankawa kowa ba ta takure a lungu ta yi shiru.
Bayan da kowa ya gama cuku-cukun kwanciya sai kowa ya yi shiru ya rufe ido kafin kiftawar ido barci mai dadi ya kwashe su, kan ka ce kwabo minshari ne iri iri ke tashi tun daga kofar gida xuwa tsakar gida har cikin dakuna kai ka ce busa sarewa ake ko kuma goga gurmi ake yi saboda tsabar gajiyar dake jikinsu.
Kaltum na runtsa idanunta barci mai dadi ya kwashe ta amma fa bata kai minti talatin ba ta ji ta yi wata mummunar firgita, ta xabura ta bude ido a xaune dabas ta tsinci kanta. Duhu kirin dakin ko tafin hannunka ba ka iya gani, ta duba gabas da yamma kudu da arewa sai taga kamar wani mutum dogo da fararen kaya a tsaye a bakin kofa yana tunkaro ta, nan da nan ta kwanta ta kudundune, jikinta na rawa tana makyarkyata ta fara addu’a kafin ta karasa wannan sai ta kama waccan addu’ar.
Irin wannan raxanar ceta afkawa goggo fattu wacce ta haye kan tudu. Gara ma kaltum akan goggo fattu saboda ita har girgixata aka dinga yi kai ka ce wani ne ya danketa yake wujijjigata. Ta galabaita sosai tun tana salati a cikin mayafi harta fara salati da karfi sai ta fara kwalla kiran sunan kaltum da duk wacce ta san sunanta a dakin. Can kaltum ta yi karfin hali tana cikin mayafinta tace “goggo, menene!”
Goggo tace “kaltum, xo ki sauke ni daga kan tudun nan shake ni ake yi ana girgixa ni kamar xa’a kifa da ni cikin kasa na kasa motsa jiki na.
To pa!!! ko me nene ya kawowa su goggo fattu gaisuwa, ban sani ba, se ku biyo mu dan jin yadda xata kaya.
.
To da patan littapin ya muku?
Kamar yadda na pada pls koda kalma daya ce ayi kokarin rubutawa kapin a pita... 🙏
.
Typing : Sadin Maa.
Post : Dan Aunty .👩ADON DAWA 2
.
Hankalin kaltum ya tashi yayin da tsoron da take ji ya sake karuwa ta bude ido a hankali ta waiga inda ta ke ganin farin abun nan sai taga babu kowa, ta tashi xaune a tsoroce duhu ne dai dumdum babu abunda take gani. Ihu dai kakarta ke rusawa har yanxu don haka kaltum ta bi inda sautin muryar ke fitowa tana lalube, can ta riko hannun goggo fatu kamar shokin din wuta haka kaltum ta ji a jikin hannun goggo. Ta yi karfin hali ta fisgo ta rim tsohuwa ta rikito kasa sannan ta ji salama.
“ihu waiyo kaina”. In ji shatu, matar da ke kwance a kusa da tudun ta dora kanta a kusa da goggo fattu. Kanka ce kwabo daki ya rikice da kace nace ashe kowace idonta biyu ashe tsoron ne ya hana su Magana tun daxu. Yadda barci ya gagari idanuwan kaltum da kakarta haka barci ya gagari sauran, matsalar ma iri daya ce ji suke tamkar an saka musu wayar lantarki, aka dinga wujijjiga su ana hajijiya dasu.
A waje daya suka taru suka cunkushe suka xauna saboda tsananin tsoro. Masu salati na yi, masu kuka suna yi, haka masu jawo Allah Ya isa na yiwa agents din da suka kawo su wannan daki duk da ma basu san a makabarta suke kwance ba har garin Allah Ya waye tangarai, sannan kowa ya fito tsakar gida, suma ‘yan sauran dakunan suka yi nasu bayanin cewar suma fa basu iya yin barci ba saboda tsoro, amma duk da haka da yawansu sun yi barcin su basu hadu da wannan matsala ba, basu ma san abunda ke faruwa ba.
Ana cikin wannan hali na jimami kungiyar Madigan tafiyar su (agents) suka shigo daga cikin gari suke inda suka kwana. Goggo ta ja agent dinsu cikin dakinsu ta nuna masa wannan gado nata wato dan tudun data haye xata yi barci aka dinga wujijjiga ta. Sai ya yi ajiyar xuciya, ya yi shiru can ya dago ya dubeta.
Ya ce “ai duk wani tudu da kika gani kama daga kofar gida xuwa tsakar gida har cikin kowannen daki to kabaruruka ne, domin nan tsohuwar makabarta ce”
Suna jin kabari sai kowace ta daka tsalle tayi gefe yayin da salati da koke koke ya barke.
Goggo fatu t ace “ka cuceni musa agent da baka sanar mana batun jiya cewar akwai kabari a cikin dakunan nan ba, da ban haye kai na kwanta ba. Daman ina ni ina kwana akan kabari da raina, ai dole in ji ba dadi. Amma ba laifin kowa ba ne sai shegiyar yarinyar nan kaltum ita ta jawo min, har nayi kwanciya a kasa na hango tat a liliye ta haye xata kwanta na sauko da ita na haye. Da bata hau ba ina xan yi tunanin hawa nima!”
Ta jawo kaltum tana ta duka kamar kullum yadda ta saba yi mata dukan tsiya dakyar mutane suka kwace ta. Kaltum ta yi kuka har ta godewa Allah ta rasa yadda xata yi da rayuwarta. Tabbas guxirin wasu ya dade da karewa, wasu ke taimakon wasu su dan samusu dan abinda xa su afa a bakin su don kada su mutu amma badan koshi ba. Irin wannan matsala ta fatara ce ta far ma kaltum da kakarta babu sauran garin rogo haka babu furar da xasu jika su sha.
Nan dai wasu agents su ka sissiyo gayan gurasa suka rarraba musu, ruwan sha ma na siyarwa ne masu sayar da ruwa akan jakuna ne suka kawo musu kudi aka sissiya musu aka tattarfawa kowa ya jika makoshinsa. Tundaga wannan lokacin dayawan su suka kwashi aljannu, fuf sai kaga an buge daya ta fadi fuk a kasa in anjima sai a buge wata. Kaltum na daya daga cikin wadanda suka gamu da irin wannan larura, furgita take yi tana xabura kamar xata arta da gudu sai a cafko ta a danne.
Bayan xuwansu da kwana uku da yamma jirgin ruwan da xasu shiga ya iso, daga kofar gidansu suke hango shi a cikin ruwa saboda girma gareshi sosai tamkar gida ne mai benaye hawa hawa.
Sai suke jiyo wani kara ‘tu tut u tu’ jirgin na yi kamar an kunna inji mai kara, da suka tambaya, me yasa injin din ke kara kada ya tafi ya barsu, sai masana suka sanar musu cewar ba tafiya xai yi ba kwana biyu xai yi a kunne ana wasa manyan manyan wukaken wadanda ke sakale a karkashin jirgin, amfaninsu saboda su dinga yanyanka manya manyan kifayen da ke cikin ruwa wadanda xa su iya tuntsirar da jirgin.
Sai da inji wasa wukaken nan yayi kwana biyu yana wasa su sannan aka kashe. Daga bisani aka umurci fasinjojin kowannen su ya kinkimo jakar kayansa ya taho bakin teku don tantancesu xuwa saudiya.
Kallo daya xaka yiwa fuskokin su ka tabbatar da labarin xuciyoyinsu ko ba komai dai xa su je suga ka’aba su yi addu’a baya ga albarkar dake cikin makka. Ba’a yunwa, ba’a kishirwa ballantana rasa mahalli mai kyau, duk tsiya dai a makka ba xa kai su cikin makabarta ba a kwantar das u, don haka sun fi son su tafi maimakon su yi xama a nan duk dab a su san wane irin kaskanci xa su tarar ba a makka.
Kaltum na dauke da jakunkuna biyu a hannayenta, nata da na kakarta har suka isa a bakin teku a inda su ka iska dogon layi mata da maxa a cakude kowa ta kansa yake, fargaba da harbuwar xuciyoyin jama’a ke faman tashi a wajen, musamman da jami’an bincike suka fara ware wadanda bisar su bata yi kyau ba, bisar bogi kenan. Duk wanda passport dinsa da bisa suka yi dai dai sai ya sungumi jakarsa ya shige jirgi yana murna, duk wanda kuwa tasa ta bogice sai ka ga an ce ya koma gefe ya tsaya.
Da aka xo kan goggo fattu aka duba passport dinta da bisa sai suka ga komai ya yi daidai don haka aka ceta nuna kayanta xa’a saka mata a jirgi ta nuna jakunkunansu nata dana kaltum ma aikaci daya ya dauka ya loda a karkashin jirgi ita kuma aka umurce ta da ta shiga jirgin.
An shafe fiye da mintuna goma sha biyar a kan passport da visa , kaltum ana bincike bincike yayin da dogon larabci ya balle tsakanin ma’aikatan da agents dinta musa daga karshe suka gaskata visar kaltum ta bogice, baya ga passport din wani aka lika hotonta, don haka suka turata gefe. Haka itama kawar kakarta da take bayan kaltum mairo matsalar visar bogece ta far mata don haka aka tura ta gefen su kaltum, itama ta dauki kuka ta je ta tsaya ita da jikarta rakiya.
Goggo fattu na cikin jirgi a xaune shiru shiru kaltum da kawarta mairo basu shigo ba don haka ta fara tambayar wadanda suke shigowa.
“ina kaltum! Ina mairo da rakiya!”
Aka sanar mata kaltum da mairo an ware su gefe saboda rashin visa mai kyau, don haka basu tafiya. Goggo fattu ta yiwa ma’aikata magiya su taimaka mata su barta ta fito daga jirgin ta xo ta iske su kaltum xata yi musu Magana, da kyar suka bar tata fito ta taho da sauri in da suke tsaye a gefe. Kaltum na ganin kakarta sai ta fashe da kuka ta rike ta, tana cewa”goggo fattu xa ki tafi ki barni anan ban san kowa ba, ban san inda xan je ba!”
Goggo fatu ta girgixa kai t ace “babu yadda xan yi, ba laifina bane, laifin agent ne, ni dai na bashi kudin komai don haka ga ku ga agent ku rike shi, shi xai san yadda xai yi da kawo ku.”
Ta juya ta dubi mairo kawarta tace “mairo ga kaltum nan amana a hannunki”
Kuka ya hana kaltum da mairo Magana, jikin goggo fattu yayi sanyi da alama ta tausaya musu ta juya ta koma cikin jirgi yayin da kaltum ta fasa kuka mai tafe da tsananin takaici. A haka har aka gama duba kowa masu shigewa suka shige, mutane arba’in da takwas ne kadai aka rage a kasa ,talatin mata, goma sha takwas maxa, suna ji suna gani aka rufe jirgin sannan suka daina kallon sa.
Sai su sai sauran agents din da basu tafi ba, nan fa kowa ya rike rigar agent dinsa yana hayagaga. Suka tabure akan basu yarda ba a tafi a bar su, wannan ai ha’inci ne bayan suma kudi suka biya yadda wadancan suka biya. Bayani dai daya ne agents suke yi musu shine suyi hakuri su kwantar da hankalinsu xa’a je a gyaro musu nan da kwanaki biyu xa su tafi suma. Akan wannan sharadi ne su kaltum suka hakura suka saki rigarsu da suka cukuikuiye suka rike.
Da agents suka samu aka sake su sai suka sulmiye suka gudu, yayin dasu kaltum suka koma cikin dakunan su suka xaxxauna suna jiran tsammani.
Babban tashin hankaln da kaltum ta shiga shine gaggo fattu ta tafi da jakar kayanta sannan bata bata ko sisi ba, dan sauran kudin guxurinsu kacokan yana aljihunta ta tafi dasu don haka kaltum daga ita sai kayan jikinta.
Riga da xani da dankwali ne na atamfa nichem koriya saidan yalolon mayafinta baki da sidadden silifas wanda ya fara hujewa a sanadiyar wahalar da suka sha a hanya.
Yanxu mutane tara ne a dakin su kaltum, iya mairo da jikarta rukayya ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu, sai amina, jidda’u, huwaila suma ‘yan mata ne iyayensu sun haye sun barsu shekarunsu basu wuce tsakanin goma sha hudu xuwa sha shida ba, gaba dayansu daga garin kwalfau suke a janhuriyar niger. Sai kuma hajara baxawara ce shekarunta ashirin da biyar ‘ya’yanta uku suka rabu da mijinta ta xubar dasu ta xo niman kudi ita kuma er garin matamaye a jamhuruyar niger. Sauran biyun kuma manyan mata ne maimuna daga xangon daura sai madina daga kaxaure dukkaninsu tsakanin shekara talatin da uku ne xuwa talatin da biyar, suma sunyi aure aure sun hayayyafa sannan suka ballo suka fito neman salamar rayuwar saboda al’amura sun tsananta a gare su. Sauran dakunan ma haka suka karkasa kansu wasu su goma, wasu su biyar, wasu su bakwai suka xauna suna xaman jiran agents.
Hakika kaskanci da wulakancin dasu iya mairo suke yiwa kaltum a dakin abun ya kaxanta a sanadiyar bata da guxuri, sukan bata dan abun da xata kai makoshinta amma bai taka kara ya karya ba, haka idan suka sayi ruwan sha mukurwa daya kacal suke bata ta jika makoshinta da alama yunwa da kishirwa sun fara cin jikinta a galabaice take baya ga datti da kura da suka addabi jikinta tamkar tababbiya xaka ganta, hawaye kadai ke yawan wanke kurar fuskarta. Tana manne a lungu a takure babu eh babu a’a, ga tsananin tsangwama da carin da rakiya , jidda’u, da amina da huwaila ke yawan yi mata saboda sun ga bata ramawa tsananin hakuri da tsoron da take ji. Mace dayace ke raga mata a dakin itace ke tausaya mata, mai hana yawan tsangwamar da ake yi mata itace madina, wani lokaci su ji maganar madina su bari wani lokqci su ki bari, itama ta sami rabon nata na rashin kunyar su.
Madina ceke xubawa kaltum dan abinci a murfin kwano idan sun xo cin abincin, amma sauran saisu juye mata baya idan sun tausaya mata ne suke yafito mata lauma daya su bata a hannu ta karba da sauri tana godiya da murna sannan ta ci ta lashe hannu.
Tafi tafi suka cika sati guda cur agents suna yi musu karairaye daga wannan satin basu sake ganin agant ko daya ba dukkansu sun sulale sun gudu Nigeria sun barsu anan a yashe babu tafiya babu alamarta . don haka suka tabbatarwa da kansu sun shiga tsaka mai wuya su basu je saudiya ba su basu ba’a dawo dasu Nigeria ba saboda haka hankalinsu ya kara tashi matuka babu wanda baya kuka matansu da maxansu, yara da manya. Daga nan suka sakawa a ransu nan ne garinsu na dun dun dun, xama ne xa su yi shi marar iyaka, sun fitar da xaman tsammanin yau ko gabe xa su bar sudan, don haka suka fara tunanin abunyi, ta ina xasu fara neman abunda xasu ci gaba da rayuwarsu.
Yadda suka sami tarihi daga wajen hausawa maxauna garin cewa babu wata sana’a da xasu iya yi anan su samu kudin da xasu iya rike kansu in dai ba bara ba sai kamun kifi a kogi wato ‘su’. Don haka barace ta kama su dole su xama almajiran karfi da yaji.
Hankalin dukkanninsu ya yi matukar tashi da suka ji Kalmar “bara” sun yi nadamar barin kauyukansu da kasarsu suka taho sudan. Haka su ka yi kuka mai tsanani da suka ji tarihin cewar dukkanin hausawan dasu ke gani a garin suma irin wannan abun daya same su shi ya faru dasu tun suna goye iyayensu suka xo suka yada xango anan da ximmar tafiya saudiya, su basu tafi ba sannan ba a komar dasu Nigeria ba. Iyayensu suka mutu suka bar yaran a xube suna walagigi har suka girma basu san danginsu ba suma har suna aure aure suna hayayyafa a junansu. Don haka ana basu tabbacin ba lallai ba ne su haye saudiya kuma ba lalle ba ne su koma Nigeria har abada.