Adon Dawa Complete Hausa Novel
Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 10
BABI NA SHIDA
LABARIN MADINA
Madina ta dubi kaltum yayin da take Magana cikin muryar kuka amma ba hawaye sai dai idanuwanta sun kada sun yi jawur da alamar tashin hankali a tattare da abunda take shirin fada.
Ta farad a cewa “kaltum, xa kiyi mamaki idan n ace miki ni inyamura ce ko!”
Kaltum ta dafa kirji t ace “inyamura!”
Madina ta gayada kai tace “eh inyamura ce, inyamurar ma ba musulma ba, wacce bata taba sanin akwai wani addini da ake kira musulunci ba. Ni yar asalin garin Onitsa ce. Kaltum, ban taba xuwa makarantar boko ba, primary balle secondary, amma a cikin ikon Allah ni ma’aikaciyar lafiya ce (nurse) a babban asibitin kaxaure.”
Hakika kan kaltum ya daure yayin da al’ajabi gami da miliyoyin tambayoyi suka feso a cikin xuciyarta. Ta tamba ya cikin mamaki “ta yaya!” madina tayi ajiyar xuciya t ace “shine yanxu nake shirin in fayyace miki komai. A da ina tunanin karancin shekarunki ba xai bari ki fahimce nib a amma na lura kaifin hankalinki da nutsuwar ki xa su sa ki gane, tunda kin dandana axabar rayuwa kamar ni.”
Madina ta mike ta shiga dakinsu, ba jimawa ta fito dauke da katon kwali wanda take kwana akai ta riko hannun kaltum ta tashe ta tsaye suka fice kofar gida, suka samu inuwa suka xauna akan kwalin su dukka.
Madina tayi murmushi t ace “nag a rana ta iske mu a tsakar gida, shi yasa na dawo da mu inuwa saboda mu ji dadin labarin.”
Tana rufe bakinta mai ruwa ya kwada talla akan keken jakunansa. Kaltum tana daga ido sai tag a wannan tsohon ne mai sayar da ruwan nan daya taba bata jarka daya ta ruwa kyauta. Sai suka yiwa juna murmushi a lokaci guda. Ya fada cikin harshen larabci y ace “yarinya ga ruwan dadi.”
Ta ce “babana ina jin kishir ruwa sai dai yauma bani da kudi.”
Ya ce “yauma dauko bokiti in xuba miki jarka daya kyauta saboda nima Allah Y dube ni.”
Kaltum tayi wuf ta mike da murna ta shiga gida ba dadewa sai gata dauke da bokiti hannunta, ta xo ta ajiye a gabansa, yayin day a tittila mata ruwa garai-garai mai sanyi cikin bokiti. Madina dai ta tsura musu ido tana duban bakinsu sai magan suke bata san mai suke fada ba, xuciyarta a cike da mamakin inda suka hadu har suka saba wasa da dariya haka. Tana mamakin yadda kaltum xata samu kudin da xata biya mai ruwa dan a iya saninta kaltum bata da kudi. Mai ruwa yah au keken jakunnansa ya kada su suka tafi, kaltum ta kinkimo bokitin ruwa ta kawo gaban madina. Ta shiga cikin gida ta samo kofi ta dauraye ta ciko kofi da ruwa ta mikawa madina, ta karba ta sha sannan itama kaltum din ta ciko kofi ta kwankwada yayin da hanjin cikinsu ya fara karkadawa saboda a yau ko kwayar gero bata bakunci cikinsu ba.
Madina ta gyara xama ta kalli kaltum t ace “ina kika samo tsohon nan, har kuka saba ya baki ruwa kyauta!”
Kaltum tayidariya t ace “yanxu ma ce min ya yi in jira shi anan idan ya sayar da ruwansa xai sayo min abinci, da na ce masa ba xan sha ruwansa ba saboda ban ci komai ba, cikina xai yi ciwo.”
Madina ta sake tambaya “kin san shi ne!” kaltum ta bata labarin yadda suka hadu rannan t ace yau ne haduwarsu ta biyu.madina t ace “to ai shine abunda nake fada miki daxu kenan, maxa suna sonki, a wajen mata ne kike dab akin jinni, matan ma, ba duka ba.
Kaltum ta gyada kai t ace “tabbas haka ne, na lura da haka da kika ankarar da ni. Anty ina sauraronki ki ci gaba da labara, tun daxu labarin yana yi min yawo a kwakwalwa. Kince ada ke bama musulma b ace, amma yanxu kin fi asalin muslman sanin addini, ga karatun Qur’ani ga salla, a ina kika koya!”
Madina t ace “na karance Qur’ani tas na sauke kamar yadda kika sauke, na san baki a duk inda aka buda min a cikin Qur’ani xan karance shi tsab, na iya hadisai da dama da fassararsu ban san adadin sub a, sannan nasan tauhidi da hukunce hukuncen musulunci. Ke in takaice miki ma ni malama ce a gidana mata suke cincirindo suna xuwa daukar karatu.
Kaltum ta gyara xama tace “yaushe kika koyi duk wannan, a Onitsa ko a kaxaure! Sannan kin c eke baki taba xua makarantar boko ba amma kin iya rubutu da karatu da turanci har ma kina aiki a asibiti kina allura da dinkin ciwo, ta yaya kika koya!”
Madina tayi dariya ta dafa kafadar kaltum t ace “Allah kenan, idan mutum y ace “Allah” to karshen Magana ta xo. Kaltum, Allah ne Ya bani duk wannan a cikin dan lokaci kankani. Ya mayar dani musulma ina kafura, Ya mayar dani mai ilimi alhali ina jahila , Ya mayar da ni me gata alhalin ina marainiya, Ya axurta ni da miji da ‘ya’ya alhali ina ni kadai. Allah ne mai yawan kyauta, mai jin kan bayinSa, banda Shi babu mai mayar da yaro babba, ya mayar da babba tsoho. Mai axurta talaka, mai talauta mai arxiki a duk sanda ya so.”
Kaltum ta gyada kai t ace “hskiks haka ne, tsarki da aminci sun tabattata ga Ubangijin talikai.”
Madina t ace Alhamdulillah, da kika yadda da wannan. Yanxu xan fara baki kadan daga cikin labarina, xa kiji kadan daga cikin dinbin ni’imomin da Rabbussamawati Yayi min, xa kiji yadda Allah Yake ikon Sa akan bayinsa.
Da farko ni sunana chidimma, haifaffiyar garin onisha ce, addinina addinin gargajiya ne ma’ana mu ba musulmai bane ba kuma masu xuwa coci ba ne. akwai bokan da yake yi mana duba da gumaka, shine yake iso mana da sakon abunda xamu yiwa gumaka da wadanda xamu bari kada gumaka suyi fushi sai bala’I ya same mu. Wa’iyyaxu billah, haka na taso na tarar kakannina da iyayena suna yi, kuma a haka suka koma ga ubangijin su cikin tsantsan jahilci. Shiyasa nake kuka duk sanda na tuna asarar da suka tabka a rayuwarsu a lokacin da suke duniya. Musamman idan na ji hukuncin makomar wanda ya mutu yana shirka. Babu yadda xan iya nemar musu gafara a wajen Mahalicci Ya gafarta musu kamar yadda naji a kisser Annabi Ibarahim da mahaifinsa da kuma shugabanmu annabi Muhammadu (saw) da kawunsa.” Sai madina ta rushed a kuka mai hade da tsantsar takaici, yayin da idanuwan kaltum suka cicciko da hawaye itama.
Madina ta tsagaita da kukan ta ci gaba da cewa “sunan mahaifiyata chioma, mahaifiyata wada ce.” Kaltum ta tambaya cike da rashin fahimata “wada!” madina ta gyada kai t ace “wada dai da kika sani wadanda ake haifarsu gajeru masu katon kai da guntayen gabobi wadanda aturance ake kiransu dawarf.”
Mamaki a bayyane xaka iya hangowa daga idanuwan kaltum, yayin da tambayoyi suka cika xuciyarta amma ta rasa daga ina xata fara tambayar.
Madina tayi dariya t ace “ki kwantar da hankalinki xan baki labarin komai. Mahaifina kuma sunansa emeka shi dogo ne sosai kamr duk wani dogon mutum da kika sani dais hi kuma wani dogon mutum da kika sani sai dais hi kuma xabiya ne wanda a turanci ake kiransa da albino.”
Kaltum ta xabura t ace “xabiya kuma!” madina ta kyalkyale da dariya, har kaltum ta fara tsorata da dariyar da madina take tuntsurawa ta kasa dainawa kaltum tad an ja da baya a tsorace, yayin da kwakwalwarta ta fara tunano mata abubuwa da yawa akan madina. Ta ce a ranta “shin wannan wacce irin mat ace duk kwabe-kwabe, ‘yar gidan xabiya da wada, inyamura, masu bautar gumaka!”
Madina ta katseta tunaninta da take yi ta ci gaba da cewa “dube ni sosai kaltum, kin ga nayi kama da wadanni! Ko kinga alamar hasken fatata tayi kama da kalar xabiya! Ko kinga alamar kamannina na inyamurai a fuskata ko harshena! Kon kin ga alamar arnanci a dabi’una! Kin ga babu duk wannan, shine ma’anata cewar Allah Y canxa ni a cikin dan kankanan lokaci.”
Kaltum ta gyada kai t ace “haka ne anty, babu duk wannan alamun da kika xayyano min. a tunanin ke bafullatana ce.”
Madina tayi murmushi t ace “to haka yayana innamani yake, har ya fini tsawo da fari don kamarmu daya sak. Da suka tashi haifar na uku sai aka Haifa wada aka saka masa suna xuka, da aka sake haifar mai binsa sai aka mata suna Enena. Daga nan sai rigima ta hautsine tsakanin dangin uwata da dangin ubana. Kinsan basu san tawakkali ba saboda jahilci, sai dangin ubana suke cewa mama na mayya ce sai an kasha ta, saboda me xata haifi wada kamar ta?
Suma danginta suka ce ai an haifi xabiya saboda haka baba na ne maye. Rigima taki ci taki cinyewa, cikin dare dangin babana suka je suka kasha kanina xuka, bayan kwana biyu aka tsinci gawar kanwata Enena a dawa suma dangin mahaifiyata sun rama kenan. Aka tashi rigima kamar xa’ayi yaki a jinanasu, tsakanin dangin wada da dangin xabiya daga karshe aka ce sai dai a raba auren sannan a raba yaran wato ni da yayana kenan, mu masu lafiyar ana sanmu. Da iyayena suka ji haka sai suka gaba xasu iya rabuwa da junansu ba saboda suna mutuwar kaunar junansu, su suka san irin tsana da takaicin da suka sha a wajen ‘yan gari kowa yaki aurensu, saboda ita wadace shi kuma xabiya har saida Allah Ya sa suka hada kansu suka xabi su rufawa juna asiri su xauna tare suka yi aurensu babu mai yiwa kowa gori.
Cikin dare ya dauki ‘yar wadar matar sa, daman ya saba daukarta a kafadar sa duk in da xasu je, ya shiga dawa suka gudu har yau ba’aji labarin suba. amma ana kyautata xaton sun shiga wani kungurmin kauyukan arna sun tsafe su. Kinsan kudu da arewa ba daya ba ne, yanxu a kudu sai kiga an kamo mutum an yi tsafi dashi musamman aga irin wannan halittar ta wada da xabiya suna tafiya tare, cewa xa su yi annoba ne ko su ce arxiki ne a kama su a yanka ko a binne su da rai. Bawai na gaskata ba amma dodonsu y ace an kashe su a wani kauye don haka aka yi bikin mutuwarsu aka raba gadon abunda suka bari, harda ‘ya’yan da suka bari a rabon gadon wato ni da yayana. Shike nan gaba daya gidanmu ya waste daga ni sai yayana muka rage, ba uwa, ba uba, babu kanne. Dangin uwata suka dauki yayana, yayanta ya dauke ta ya dauke shi ya tafi dashi enugu garin da yake aiki, dangin ubana suka dauke ni a nan cikin onisha nake. Kamar yadda kika sani da xarar ance babu uwa, babu uba, a duniya to fa sai a hankali saboda gata yakare sai wanda ya duba Allah xai dube ka.
A lokacin shekaruna takwas a duniya don haka na fara kiran kaina marainiya domin na fara dandana maraici. Ba’a taba saka ni makarantaba sai talla da noma koda yaushe, nice rainon ‘yayan ‘yan uwa, nice shara da wanke wanken a gidajen ‘yan uwa ba a gida daya ba. Baya ga duka, xagi da cin mutunci harda kala sata, yau ace an ganni a gona na saci rogo gobe ace na balli ayaba a gonar wani ko kuma ace na bude tukunya na saci naman miya. Kaltum ina bayan gari ina kuka ni kadai gashi yayana innamani yayi min nisa baya onisha ya ci sa’a shi an saka shi a makaranta. In takaice miki dai da wuya tayi wuya babu wanda bai san labarin wahalar da nake sha ba a garin, ina tafe jama’a na nuna ni suna tausaya min. kayan jikina a yayyage, tallar safe daban in koma in dauko abincin rana, idan na sayar na koma na daukko na dare.
A kasuwa nake sayar da abinci anan ne na hadu da hausawa masu sayar da gyada, man kulikuli, ridi, barkono da dai sauransu. Ta in da jini na ya fara haduwa da hausawa shine suna da tausayi, suna da kirki, suna da kyauta, ga yawan fara’a. muna xama tare muna sabawa sai na fara fahimtar ashe wadannan wadannan mutane wato hausawa suna da wani addini da ake kira musulunci, suna bautawa Ubangijinsu shine Allah madaukakin Sarki. Hakika idan musulmi y ace Allah xan yi abu kaxa, tabbas suna tsoron Allah xa su yi din. Wannan al’amarin nasu yana burge ni kuma yana matukar ba ni sha’awa, na ji ina son in yi huddar cinikayya dasu. suna siyan kayana su bani kudina basa hanawa sabanin inyamurai ‘yan uwana saisu cinye abincina su hana ni kudin, su ce in je in yi abunda xanyi, basa tsoron Allah. A wanan dalilin ne yasa na fi so in sayarwa da hausawa abincina.
A haka muka saba da wani yaro saurayin mai suna Tasi’u, dan asalin wani kauye ne da ake kira gurjiya, a hanyar wudil akwai wani kauye da ake kira kanyar babba, daga nan ake daukar hanya sai ayi ta shiga kusurwa-kusurwa babu kwalta, sai rigagen Fulani da kauyukan hausawa iri iri har a isa garin gurjiya.”
Kaltum t ace “yanxu daga surkukin kauyen na su tasi’u suke fitowa su tafi har onisha neman kudi? ”
madina t ace “dabi’ar ‘yan garin ne duka shekara bayan amfanin gona yayi, anyi roron gyada da wake saisu hada buhuhunan amfanin gonarsu maxansu da matansu su hau mota su je garinmu onisha. Matan suna gida suna gyara gyada suna yin man kuli da karago ko soyayyar gayada, maxan suna sayarwa a kasuwa.”
Kaltum t ace “har gidaje gare su a garinku kenan? ”
madina ta e “ba wasu gidajen kirki ba ne, tamfol ne suke bugawa a bayan gari, ko suyi gidajen katako ko kuma su sami dakuna na kasa su kama haya. Suna xama kamar watanni hudu ko uku sannan su hada kudinsu su sari manja, kwakwa, garin kwaki, su juya garin su sai wata shekarar sannan su dawo.
Kaltum ta gyada kai tace “Allah mai hada mutum da mutum, idan ba ikon Allah ba ta ina, ta yaya mutumin da yake hanyar wudil ya hadu da wacce take onisha. Yaya kuka kare da mutumin da kika ce sunansa tasi’u dan garin gurjiya? ”
Madina tayi murmushi t ace “duk shekara muke haduwa da tasi’u, da yake bashi da mata a wajena yake siyan abincin safe, rana da na dare ya siya ya bani kudina cas har ma ya kara min, y ace na rike canjin komai yawan sa.
.
Typing : Sadin Maa.
Posting : Dan AuntyADON DAWA 11
.
TRUE LIFE STORY
.
Don haka da xarar naga baki ‘yan garinsu sun fara xuwa sai nayi ta tambayarsu “ina tasi’u?
ba xai xo ba ne?
yau she xe xo?
Me yasa bai xo bad a wuri? ”
haka kullum nake tambayar abokansa har sai ya xo hankalina yake kwantawa. Duk da baya jin turanci sosai, amma duk da haka yafi sauran kokarin harhadawa in fahimce shi ya fahimce ni don nima babu hausa a lokacin.
A lokacin da muka tabbatar wannan shakuwar tamu soyayya ce, sai a sannan na cika shekara goma sha hudu. Na ji ina sonsa saboda yana tausayina ya fahimci ina shan wahala a gidanmu, yana lallashina idan ina kuka haka yake cika min kudi idan cinikina bai cika ba ina tsoro xa’a dake ni a gida. Haka yake kawo min atamfofi da soyayyiyar aya da gyada duk sanda xai xo daga garinsu. Nima idan xai tafi sai in je gona in tsunko masa kwakwa, abarba, ayaba da gwanda. Da kuka muke rabuwa duk sanda xai koma garinsu sai inji duk bana jin dadin kasuwar idan baya nan.
Bana sha’awar samarin garinmu saboda ba abunda suka sani sai yiwa budurwa ciki, idan taki amincewa sai suyi mata fyade (wa iyyaxu billa Allah Ya tsare mu da xuri’armu baki daya.) da karfin tsiya ba’a kuma daukar matakin kirki idan haka ta faru dan haka nayi ta taka tsan-tsan da duk namijin da yake kusanta ta. Da yawa samarin garinmu sun sha kawo min hari, Allah Yak e kiyaye ni.
Wata rana na je na iske tasi’u a dakinsa bashi da lafiya yana cikin bargo yana makyarkyata saboda tsananin xaxxabi mai xafi. Na xuba masa abinci nace ya tashi yaci, yace ba xai ci ba idan yaci xai yi amai. Na kasa tafiya talla in bar shi cikin wannan hali sai na xauna a gefen katifarsa ina shafa kafarsa. Sai naga ya xabura ya janye kafarsa. Ya ce da ni baya so ina taba shi saboda haramun ne mace ta taba namiji idan ba mijin taba ne, haka bai ma kamata in shigo dakinsa ba in xauna saboda gudun shaidan xai iya shiga tsakaninmu, a takaice dai yana nufin in tashi in fita.
(ALLAH SARKI, JAMA’A SE A KIYAYE DOMIN KUWA WANNAN ITACE ADDININ MU KUMA AL’ADARMU, DA YAWA MUTANE YANXU SUN XAMA DA SHI GANIN DAMA, DOMIN GUJEWA SHARRIN SHAIDAN, JAMA’A SE A KIYAYE, A DAU DARASI, ALLAH YA SA MU DACE, KUMA MU PI KARPIN XUCIYOYIN MU.
Aamiin )
Raina yabaci na dauki kayan talla na fice a tunanina yayi min wulakanci baya sona. Ina shiga wani gida talla sai mutumin gidan ya rufe kofa da ni yana neman yi min fyade, da kyar na kwaci kai na bayan da muka yiwa juna jini da majina. Ya fasfaska min mari, ni kuma na rurrusa masa daron abincin tallar, na juye masa abincin aka duk abincin ya xuxxube, da kyar na kwaci kaina na fito yaro-yaro kayana a yayyage. Sai a lokacin na sake tabbatarwa da lallai tasi’u mai so na ne kuma baya niyyar cutar da ni, kuma al’adarsu da addininsu yana da kyau yafi namu.
Kai tsaye dakin tasi’u na nufa ina rusa kuka, wannan karon sai na ki shiga cikin dakin sai dai na kwankwasa masa kofa, ya fito da kyar yayin da hankalinsa ya tashi daya ganni a cikin wannan halin. Yana tambayata cikin gigita dakyar na lafa da kukan na fada masa abunda ya faru, na shaida masa cewar kwanukan abincin yana can a gidan mutumin kuma abincina ya xube dukka ko cinikin sisi ban yi ba ina tsoran in je gida dan xa’a kashe ni idan ban kai kudi ba. Haka tasi’u ya harhada duk ‘yan kudaden sa ya bani ya saka ni a gaba na nuna masa gidan, muka iske gidan a rufe amma an watso min kwanukan waje. Tasi’u ya harhada ya bani na tafi gida, duk da haka saida na ci duka akan kayana da aka gani a yayyage.
Tun daga wannan lokacin na ji na kara son tasi’u kuma shi ya dace da rayuwata. Na shiga tunanin ta yadda xamu fara domin na san ko a mafarki a gidanmu da wajen bautarmu ba xa su bari na auri tasi’u ba ko xan mutu. Shima ya nuna min yana sona amma fa ko xan mutu ba xa’a bar shi a gidansu ya su ya aure niba, a lokacin ma ya fada min cewar har an bashi wacce xai aura shi ne baya so yake jan abun da tuni ma anyi bikin.
Tasi’u ne ya koya min saka suturar da xata rufe min ilahirin jikina, na daina yawo da shimi dadan siket iya gwiwa, shi ya nuna min kamun kai da kintsa jiki idan ina gaban maxa saboda gudun sha’awa, muna son juna sosai har takai ta kawo sanda ya xo xai tafi garinsu na rike shi ina ihu nace sai dai mu tafi tare ba xai tafi ya barni ba, dole ya fasa tafiyarsa a ranar abokan tafiyar sa suka tafi suka barshi ya xauna yayi ta lallashi na dakyar na yarda na koma gidanmu a bisa sharadin gobe xai jira ni mu tafi tare.
Cikin dare na sulalo na fito daure da kayana a dan buhu na xo na buga masa kofar dakinsa nace ya fito mu gudu saboda gobe da safe xa’a a tashi a fadawa ‘yan uwana su xo su kama ni. Da farko ya nuna ba xai tafi da niba, kukana da kalaman da nake fada masa cewar ina so in musulunta in xauna da musulmai In baxe aure niba na yarda, na shaida masa na gaji da wahalar aiki, talla, da duka kullum, in har ba xai tafi da niba to ya sani kafin ya dawo wata shekara xan kashe kaina. Dole ya ji babu yadda xai yi sai ya tafi da ni din. A daren muka shiga tasha muka kwana, da asuba muka shiga doguwar mota xuwa kano. Babu wanda ya ganni har muka bar garinmu, daga kano muka hau motar wudil kafin a isa wudil muka sauka kanya babba muka hau Babura suka shiga damu garin gurjiya, garinsu kenan. Bamu isa gurjiya ba sai kimanin karfe goma sha daya na dare a lokacin kowa yayi barci, sai ya kaini gidan wani abokinsa mai suna Dauda da matarsa ramma itama mun saba da ita a garinmu, suma basu dade da dawowa ba daga onisha. A nan na kwana shi kuma ya tafi gidansu har gari yawaye”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya ta gyara xama t ace “yaki na gaba ahse, yaya kika kasance a garin gurjiya da dangin tasi’u musamman ga wacce aka bashi ya aura ya bujire ya kawo ki, ke ba bahaushiya ba, ba muslma ba?
Kuma can gidanku yaya xasu ji idan suka ji an ce kin gudu? ”
Madina ta digo da kwallar data cika mata ido ta yi murmushin karfin hali tace, “idan ki ka ce yaki daya kenan. Yake-yake xa kice. An tafka yaki badan kadan ba tsakanin tasi’u da ‘yan uwansa harta kai ta kawo dole ya dauke ni muka gudu kano saboda sun ki su tsaya su fahimce shi. Ba su ma saurari abunda yake fada musu ba, yana kokarin shaida musu ba aurena xai yi ba. Ya kawo ni ne dan a musuluntar da ni in xauna a cikin musulmai dan ni yanxu kafura ce. Sai gudu da tsallake Katanga ake yi a garin duk gidan daya shiga da ni wai ga arniya, ko giftawa nayi ta gefen randa sai an fasa randar ko an kwalfe ruwan an xubar. Kiyayya iri-iri har naji jikina yayi sanyi, dan ban dauka haka wasu musulmai suke ba. A tunanina duk musulmai masu kirki ne da son jama’a, sai naga suna kora ta suna guduna har nace masa ya mayar da ni garinmua na fasa xama da musulmai. Tasi’u yaki yace in dauko kayana mu gudu cikin garin kano, haka kuwa aka yi ya kawo ni kano unguwar yan kaba wajen limamin unguwar. A nan aka musuluntar da ni kuma a lokacin tasi’u ya biya kudin sadakina aka daura mana aure a take
A lokacin ‘yan uwa musulmai suka dinga tallafa mana, masu bamu sababbin suture kala-kala. Aka bamu kudi masu yawa sannan wani attajiri a unguwar mai suna general tukur ya bamu aron wani dan karamin gida a jikin gidansa, gidan mai kyau kuwa daki biyu, sai kicin da bandaki ga tsakar gida a sumulce da sumunti. Matan unguwar suka hada kudi suka dinka min hijabai aka ce in dinga xuwa makarantar islamiyya a unguwar. Ni da mijina muka sayi katifa, labulaye da kayan kicin muka xauna, xaman aure cikin farin ciki. Turanci ya fara ratsa bakin tasi’u yayin da ni kuma hausa ta fara kama bakina don haka muka dinga fahimtar juna.
Tasi’u yana jin dadin xama da ni saboda duk sanda matar bahaushe ta hadu da matar kabila tabbas kabilar nan xata kwacewa matar bahaushe miji badan komai ba saidan mu mun saba da aikin karfi ba aikin gida ba ma kawai. Kinga daga inda aka kira sallar asuba nagama barci sai wani daren kuma. Ni ce shara, wanke-wanke, wankin bandaki, wankin kayana, wankin kayansa, gugar kayansa dama sauransu. Ladabi da biyayya kuwa ba iyaka domin ba ma mikawa miji abu a tsaye sai mun durkusa, idan ya ajiye min tsinke yace, kar in tsallake bana tsallakawa, ban taba yi masa musu ba balle mu yi fada duk abunda yace min ko bana so haka xan yi. Ina jin dadin xamana da tasi’u saboda bana aikin wahala irin na da wanda nake yi a garinmu. Tsakanina da makwabtana sai gaisuwa da hirar mutumci, haka na yi kawaye da dama a makarantar islamiyya. Kwakwalwata kuwa tar ta bude duk wani karatu da xa’a koyamin sai ya shige, gani da nacin koyo.
Tasi’u ma bashi da ilimin addini sosai shima makarantar maxa ya shiga da daddare suke yi a masallaci. A kasuwar bakin asibitin murtala tasi’u yake kasuwancinsa yana sayar da danyen abinci kamar shinkafa, masara, gero, citta da ma sauransu. Sai a lokacin damina yake xuwa garinsu ya noma gonar gadonsa domin babansa ya dade da rasuwa mahaifiyarsa ce kawai sai ‘yan uwa jibgi guda mata da maxa. Tun mahaifiyarsa na kin amsa gaisuwarsa har dai ta huce ta fara amsawa, ta huce amma koda wasa baya marmarin kai ni garin, nima bana marmarin xuwa garinmu. Shima tasi’u bai sake waiwayar onisha ba sai dai labari ya kai kunnen ‘yan uwana cewar ina tare da tasi’u a kano. Da sun yi shawarar su xo su tafi da ni, sai bokansu yace a kyale ni xan dawo da kaina, akwai tsibbun da xai yi xan dawo da kaina. Amma fa karya yake domin addu’ata tafi tasu karfi.
Na dade ban samu haihuwa ba don haka na dinga kokarin neman ilimi ta dukka bangarorin biyu Qur’ani da boko.”
Kaltum ta tambaya cike da mamaki tace “ta yaya kika shiga makarantar boko alhali kina matar aure kuma ko primary baki yi ba?
To, mu hadu a #LITTAFI kashi na biyu, domin jin cigaban labari.
Taku me son ku da kuma son nishadantar da ku har kullum .
Sadin Maa...
Kunji ta pa?
Wai mai son ku? 😏
To ai nima dan Aunty dan aikenta ina son ku duka baki daya.
Allah Ya sa mu dace.
Aamiin
.
Yawwa AlhamduLillah, gida ya parpado daga parin da ya shiga, mutane sun para dawowa,
Ada ana samun masu karatu bayan anyi post sama da 4k xuwa 6k, akwai post din da naga masu karatu sama da 10k, sai yanzu kuma da gidan yayi shiru dakyar ake samun 1k, daga 700 xuwa 800 ake tsayuwa,
To AlhamduLillah mutane sun bada hadin kai wajen comments, likes da share har yau naga mutane sama da 3k sun karanta littapin, Allah Ya saka muku da alkhairi.
Aamiin.
Naji dadi matukar gaske, ha ila yau muna mai kara janyo hankalin wanda basa yi a taimaka ana yi ko da like da share ne idan baka so agan ka, amma mun pi son comments din da share, ta haka ne xai kara jawo hankalin mutane su kara shigowa gidan.
.
Sadin Maa Allah Ya saka miki da alkhairi da wannan na mijin kokarin da kike magana,
Aamiin.
.
Yawwa, xamu tapi hutun kwana biyu kamar yadda wani ya sanar dani wai an gaji da karatu.
koya kuka ce?
😊 😊
.
Abbas Abdulkadir Hada Hada (Dan Aunty)ADON DAWA LITTAFI NA 2 (P 12)
.
TRUE LIFE STORY
.
Madina t ace “da kyau, na ji dadin tambayarki, wannan yana nuna min kina fahimtar labarin da nake fada miki. Da farko dai ban taba xuwa makaranta ba kamr yadda na fada a baya amma duk yaran gidanmu ‘yan boko ne don haka tun ina karama na koyi A B C D har xuwa xed sannan na iya 123 har xuwa dubunnai, xan iya kirgawa kuma na iya rubutawa. Sannan nasan yadda ake rubuta sunan abubuwa da yawa kamar su hen, cup, ball da dai sauransu. Dalilin da yasa ba xan wahala a boko ba saboda na iya turanci duk da turancin ba turanci ba ne sak (broken English) ne amma muna jin mai kyan din, duk abun da ka fada min da turanci xan ji kuma xan mayar. Don haka satifiket din primary na je aka yi min a dakata special primary school.
A makwabtan mu wato gidan attajirin nan daya bamu aron gida wato general tukur . akwai wata budurwa ‘yarsa mai suna sumayya tukur. Sumayya sa’ata ce shekarunmu goma sha takwas har ta gama secondary, ajinmu daya a islamiyya. General tukur mahaifin sumayya babban soja ne, mai arxiki ne, gawurtaccen dan boko ne, gidansa rayuwar turai ake yi tsantsa. Yana da ilimi matarsa hajiya hafsa cikakkiyar lauya ce har ma tana koyarwa a jami’ar bayero ta kano, don haka su sumayya da kannenta ‘yan gata ne basu san talauci ba balle wahalar rayuwa.
Sumayya tukur itace babba a gidan kuma itace kadai mace, duk kannenta maxa ne har guda hudu. Mai bin ta sunansa tukur tukur ana kiransa da abba shekarunsa goma sha uku a lokacin, kinga kenan sumayya ta girme masa da shekarunsa goma sha daya, sai Hassan da hussain ‘yan auta shekarunsu bakwai bakwai. Tabbas mun shaku da ‘yan gidan duk unguwar ana mamakin ni da mijina kadai muke wadaka a gidan, mu shiga gidan mu fita a duk lokacin da muke so, haka suma yaran suke safa da marwa a gidana koda yaushe. Duk da sojojin da suke gadinsu suna hana kowa shiga gidan amma ni basa hana ni saboda hajiya hafsa tukur ta ce kada su hana ni shiga komai dare. Maigidana ma duk sanda ya bukaci ganin general tukur kai tsaye yake shiga ayi masa iso, ya shiga ya gan shi ya taimaka masa da duk abunda yake nema.
Allah ne gatanmu, general tukur da iyalansa sune gatanmu. Barrister hafsa itace uwar dakina itace tamkar uwata a kano tunda bani da kowa a kano. Ita take ba ni shawara, ita take fada min gaskiya idan na kuskure. Abubuwa da yawa idan ta sayawa ‘yarta sumayya nima sai ta saya da ni musamman dinkunan sutura ko bata yi mana iri daya ba tana kwatantawa nima tayi min. yawanci duk abunda suka dafa xata sa masu aikinta su xuba su kawo min. nima kuma ina iya kokarina wajen xage karfina in tsaftace mata gida ko tana nan ko bata nan xan hau sama bangarenta ko bangaren mijinta in tsaftace shi tsaf,
(TAB!!! NI SADIN MAA ME TYPING NA CE “SAM, BANNA YARDA WATA TA GYARA MIN DAKIN MIJI EHE. DAN ANTY ME POSTING, KO KUWA DA KA YARDA WATA TA GYARA DAKIN KA BAYAN MATAR KA? )
( tab 🤔, ai ni Sadin Maa ko er aikin ma baxan yarda da ita ba, idan kawai naga aikin xai yi wa mata ta yawa sai na karo wata ta biyu ta xo a taimaki juna 😊)
Har bata so masu aikinta suyi mata gayarn daki idan ba niba, bata ganin dai-dai saboda na fi su iyawa. Haka take aikawa in xo in yi mata wankin bandaki ko goge gogen kura, ko dahuwar abinci kala-kala irin na garinmu musamman dakan sakwara.
Daga in da na fara sha’awar boko sai yadda naga ana rugurguxa turanci, ana xaxxankada rubutu a gidan ni ban iya ba sosai. Kullum mummy hafsa t ace min “madina dama ace kin yi boko da kyawunki ya kara futowa, haka da kin fi xama ‘yar gayu da gogewa.” Sai na ji na fara tunanin ta ina xan fara karatun boko dan haka na sauke girman kai na xauna xaman dirshen da biro da littafina, kawata sumayya take koya min idan bata nan kaninta tukur (abba) yake koya min idan na iske mummy hafsa a gida bata je aiki ba itama sai ta koya min, kan ka ce kwabo na fara gane me nene boko, ko ina gida na abba yana shigowa ya koya min ni kuma ina nacewa ina tilawa har cikin dare. Tasi’u mijina baya hana ni duk abunda nake so shima dai bai yi boko ba amma bashi da niyyar koya kuma bai hana ni inje in koya ba. To kin ji yadda na koyi boko daga wajen makwabtana don karfin hali ma harda biology da chemistry sumayya take koya min da yake science tayi.
Ina da shekaru goma sha tara a duniya na haifi dana na fari, aka saka masa suna Abdul malik, na yaye shi kenan na haifi kaninsa Abdul hakim. ‘ya’yana biyu kenan tamkar ‘yan tagwaye kamarsu daya sak. Farare sol da ni suka yi kama basu dauko kamannin mahaifinsu ba. Sumayya kuwa karatun likita take yi a B U K yayin da kaninta abba ya kusa kammala secondary, shima dai ya dage yaketa koya min karatu, ni dole sai na koyi boko nima. Yana matukar burge su, su duka har daddy su ya fada ya sake maimatawa cewa shi kuwa in har xan dage in koyi karatu in nemo makaranta duk tsadar ta xai biya min. sumayya da abba kaninta suka shiga tunanin ta in da xan fara karatu a makaranta.”
Da muka nemi shawarar mummy hafsa wacce makaranta ya kamata in shiga , gani harda ‘ya’ya, sai t ace tunda ina da kokari har ma na fi wata wacce ta gama secondary sanin karatu, to inje in yi register a wata private school wacce ake yin lesson a duk lokacin da jarabawar WAEC ta karato wacce ake koyar da darussan da akayi a SS3, ana amsa past question papers na WAEC.daddy ya biya min nayi register WAEC sannan nake ta xuwa daukar darasi har na tsawon watanni uku kafin ranar jarabawar.
Na xana jarabawar WAEC na sami credit shida aka bani certificate da testimonial, kamar yadda na fada miki daman na sami certificate da testimonial na primary school tutuni.
Kaltum tayi dariya t ace “’rabo ne wannan, ba kiyi boko ba amma kin xama ‘yar boko dole.”
Madina t ace “sa kai ance ya fi bauta ciwo in ji masu iya Magana. Naci ne da son karatun na saka a xuciyata sai kuma kwarin gwiwa da na samu daga masu koya min, musamman abba yana mutukar karfafa min gwiwa.
Haka xa kiji yana cewa sister madina xa ki iya karatu ki dage.
To ko jikina yayi sanyi na daina koyo sai yasa in dauko littafi in ci gaba. Da yake abba yana matukar jin turanci ya taimaka min wajen gane abunda yake koya min, haka irin tsadaddiyar makarantar da suke yi mai kayu ita ta kara musu sanin abubuwa da yawa suma suka koya min, ga lesson teachers dinsu ko wane subject suna da malaminsa.
A bamgaren addini kuwa idan ban koya musu ba, su ba xasu koya min ba, islamiyyarmu daya dasu haka malamin da yake koya musu a gida nima ina shiga ya koya min , bikin saukar mu tare aka yi mana da muka sauke Qur’ani mu uku, ni sumayya da abba babu abunda suka bambata ni.
Abu kamar wasa sakamakon jarabawar WAEC dina ta fito, ina da credit shida da pass uku haka ya taimaka min na shiga school of hygine inda na karanci aikin jinya. To kinji yadda na xama ma’aikaciyar asitbiti kenan shi yasa na iya dinke miki ciwo, na iya allura da bada magunguna.
Kaltum tace “na ji duk wannan sai dai na damu in ji dalilin da yasa ki ka rabu da mijinki da ‘ya’yanki ki ka taho nan alhalin kina cikin rayuwar jin dadi da kwanciyar hankali. Mijinki mai sonki, ‘ya’yanki a hannunki kina kula dasu ga makwabtanki masu son ki suna taimakonki. Ba dai mai gidanki ba ne ya rasu, ‘yan uwansa suka debe ‘ya’yanku suka kore ki?
Madina tayi murmushi sai ga hawaye yana ta sirnanowa daga idanuwanta. Hankalin kaltum ya tashi ta shiga yiwa madina tambayoyi “me yasa kike kuka?
Ma ya faru da tasi’u? ”
Madina ta rushe da kuka tana Magana cikin kuka mai tsanani t ace “kaltum, dole ne inyi kuka dole ne in ji ciwon abunda ya faru da ni har bakin cikin abun ya fito dani xuwa nan.
Kaltum ta tambaya “anty me nene ya far? ”
Madina ta sharce hawaye da gefen hijabinta t ace “na kammala school of hygien nakarbi certificate dina yayi kyau cinye dukka. Haka sumayya ta xama cikakkiyar likita ta auri abokin karatunta shima likita dan gidan shahararren masu kudi ne sunansa dr basher, gidansu na korau road. Kaninta abba kuma ya yi nisa da karatunsa na lauyer a BUK har yaje law school .
Ni kuma har na sake haihuwa na haifi ‘ya mace mai suna shahida, yarinyar nan duk ta fi mu kyau duk da itama ta yi jawur da ita mai hanci dadan karamin baki, mahaifinta ya fi sonta haka su sumayya da mahaifiyarta suke son shahida, musamman abba ko da yaushe yana yi mata siyayya ya dauketa a mota ya xaxxagaya da ita. Alhamdulilla duk da tasi’u bai yarda inyi aiki ba amma na yi karatun na ajiye kwalin shi kuma harkar kasuwancinsa ta bunkasa dan saida ya sayi gidan da muke ciki na genersl tukur, duk da yayi masa rangwame sosai amma ya biya fiye da rabin kudin gidan na xahiri, har ma ya kara da wani fili da yake bayanmu ya hade yakere mana gidnmu ba laifi dai irin na rufin asiri ga ‘yar motarmu a gareji. ‘ya’yana suna karatu a makaranta me kyau don haka hankalina a kwance in ci mai kyau ga sababbin kayan daki dana falo duk tasi’u ya canxa min, sutura sai dai in bawa talakawa jace.
Sumayya na taimaka min da kayan sawa kal-kala haka ma duk sanda na je ko ta xo tana ba ni, haka abba kaninta aminina ne sosai, duk wata damuwata ko ta yarana idan na fada masa xai yi min komai yawan kudin. da yake mahaifinsu yana wadata su da kudi mai yawa. Ni da ‘yayana shar damu, bana tunanin wani abu wanda xai batamin raina in ba tunanin dan uwana ba innamani, sai takaicin rashin sanin addinin musulunci da iyaye na suka mutu cikin rashin sani da jahilci bana marmarin daidai da rana daya in leka garinmu. Amma dangin mijina sun huce dani suna xuwa nima ina xuwa sai daga baya ne ma surukata ta rasu.
Abu na farko da tasi’u ya fara shine bayan ya wadata mu ni da ‘yayana sai ya tarki Karin aure don daman na lura da yanayin gini da yayi (MAXA……….) na xaman mata biyu ne ban yi masa Magana ba sai na xuba masa ido har sanda ya gama xagayensa ya sanar min xai kara aure. Dole ne in jiba dadi amma ban isa in nuna masa ba saboda tsoronsa da nake ji, ban isa yana fada ina fada ba sai dai nayi kukan xuci sannan nayi kukana a daki na lallashi kaina saboda ban ga inda na ragi tasi’u ba da har xai yi sha’awar kara aure, nayi addu’a Allah Yasa ya auro min ta gari wacce xamu xauna lafiya.
Allah cikin ikon Sa aka auro min kishiya mai suna sa’ada ‘yar cikin garin kano ce sai dai kash bata kaunata bata kaunar ‘ya’yana, bata so a xauna lafiya. Duk da bana kula ta muyi fada amma duk shiru na sai tayi abunda sai na yi Magana. Tasi’u har mamaki yake bani, bamu taba fada da sa’ada ba tasi’u yabi bayana koda yaushe nice marar gaskiya itace mai gaskiya kullum ina ta hakuri ko sumayya bana fadawa haka ban taba fadawa mahaifiyar sumayya ba halin da nake ciki ba sai dai sun kula ina ta rama, walwalata ta ragu kamar ina cikin damuwa, ko sun tambaye ni sai in ce babu komai.
Abu yayi taci gaba kullum wulakanci karuwa yake, tasi’u da matarsa suna yi min abunda suka ga dama bana iya ramawa harta kai ta kawo tasi’u ya fadawa sa’ada asalina da yadda muka hadu. Sai na ji yarinya kullum tana yasar min da habaici tana cewa da ba’asan asalin balbela ba da sai tace madina ne sunanta na asali kuma madina ne garinsu.
Na san madina sunana ne amma kuma madina garin ne baxan kulata ba sai taga kamar dai ita kadai take rawarta take kidanta bani da lokacinta don haka ta tare ni kiri-kiri ta goranta min cewar ni arniya ce inyamura, shegiya ce marar uba, na biyo saurayi kano na musulunta. Ko a mafarki yadda nake da tasi’u ban xaci xai kwance min xani a kasuwa ba komin dadin xama komin duk dadin xance da amaryarsa ba, amsa daya na bata shine nace “nagode Allah da har na gane na dawo hanyar gaskiya na musulunta har na xo nafi ta ilimin sanin Ubangiji ita da take takama asalinta musulma ce, n ace tayi asara tunda aka haife ta a musulma ta girma a musulma amma bata iya karatun sallah ba har yanxu, kuma kar kice nayi mata sharri da gaske nake, jahila ce bata iya ba din.”
Kaltum tayi dariya ta yi tafi hade da shewa harda buga kafa kasa tace, “kin burge ni anty, amma abun da kika fada mata yayi mata ciwo ko? ”
Madina t ace “lallai kuwa abun ya kona mata rai sosai harma ta fini damuwa, ta dauki kuka ta shiga daki ta dauko gyalenta ta fice ta tafi gidnsu kinsan me tace?
Kaltum tace “a’a”.
Madina tace, “gayyar ‘yan uwanta ta dauko min mata da maxa suka iske ni har falo suka xage ni harda yayarta daya da take kokarin dukana aka rirriketa sannan suka fita daga gidan da kyar, suna kira na da arniya.”
Madina ta fashe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kuka t ace “sa’ada ta bi ‘yan uwanta suka koma gidan su, tasi’u ya dawo daga kasuwa da rana, na kawo masa abinci ya fara ci sai ya tambaye ni ina sa’ada yaga dakinta a rufe? Na c eta tafi unguwa amma ina tunanin gidansu ta je. Nan da nan ya buga mata waya, sai ta fara fada masa cewar xamansu yakare tunda matarsa take xaginta. Kinsan fasa cin abincin nan yayi, ya mike jiki na rawa ya figi mota sai gidansu, a can ita da iyayenta suka shiryo masa karya da gaskiya, ya dauko matarsa suka shigo gida bai tambayeni me ya faru ba sai duka da saki daya yayi min.
Ya kure ni cikin dare ina kuka, yarana suna kuka, na tafi na barsu. Dana fita ban san inda xani ba don ba inda nake dashi wanda yafi makwabtan mu amma ba xan iya shiga in fada musu duk abunda ya faru ba saboda ban taba fada musu matsalata ba tsakanina da mijina sai xaman lafiya nake nuna musu. Hak basu taba sanin asalina ba duk da dai sun san daga inda na fito da yadda aka musuluntar da ni a unguwar basu san kundin tarihina ba.
Don haka sai na tafi gwammaja gidan wata aminiyata hajiya hadixa na yi mata karya n ace mijina ya tafi da yaran garinsu sai ni kadai a gida kuma gyaran bandaki ake yi min shiyasa na rufe dakina na xo inyi mata kwana biyu, tayi mamakin amma tayi murna.
Mami hafsa kuwa yarana ne suka kai mata labari suna kuka suka shaida mata an saki mamarsu, hankalinta a tashe ta aika akira tasi’u ta tambaye abunda ya hada mu. Ya xauna ya shirya mata karaye da nasa dana matarsa data shirya masa, idan ki ka ji abubuwanda yake cewa a kaina sai ki rantse ban taba yi masa abu daya na kirki ba a iya xamana dashi na shekara da shekaru. Yana gama bayanansa, mommy hafsa t ace “karya kake yiwa madina wannan halaye ba halinta ba ne kuma ko Qur’ani xan dafa baxa tayi haka ba.”
Ta bashi shawarar ya tashi ya nemo ni don idan ya rasa ni ya rasa mace ta gari har abada. Babu inda shi da ita basu jejje nema nab a, inda suke tunanin ina xuwa basu same nib a, sai gani kwatsam da yamma na dawo da kaina saboda na rasa inda xanje ma, sai na yanke shawarar in dawo gidana in ba tasi’u da matarsa hakuri in xauna da yarana. Tasi’u na gani na kafin in ce wani abu yace in shiga dakina ya mayar da ni. Ni da ‘yaya na muka yi ta murna.
Mommy hafsa ta aiko in je tana nemana na je, na iske ta a xaune a falonta sai ta fara jero min tambayoyi akan me tasi’u da matarsa suke min?
Na boye mata nace “babu komai”
Data takura da tambaya sai taga na rushe d a kuka kawai, ta girgixa kai.
Ta ce “madina ke ‘yar aljanna ce ki je ki xauna a gidanki, ki cigaba da hakuri Allah xai jagorance ki.”
Na tashi na tafi gida ba tare dana fada mata komai ba. Haka sumayya ta xo ta dinga tambaya ta abunda ke faruwa sai dai in yi kuka bana iya fada. Abba kaninta ma har falona ya shigo yayi iya kokarinsa wajen bugun cikina don ya ji halin da nake ciki a matsayinsa na lawyer ya bi duk wata hanya da dabaru na jin labari shima daya takura min sai nayi ta kuka ba shiri ya fice ya kyale ni.
Na dauki tasi’u tamkar rabin jikina na nunawa jama’a tasi’u shine rayuwata ina jin kunyar ace ya watsa min kasa a ido, kunya nake ji ace baya sona yanxu wata yake so.”
Madina ta shrce hawaye t ace “sai na shiga taka tsan-tsan don kada in batawa sa’ada rai ta fadawa tasi’u shima ransa y abaci, sai na xama tamkar baiwarta a gidan komai ni nake yi mata musamman data haihu nake kula da yaron ita tana can a nade a dakin miji domin ni bani da kwanxa, akwai lokacinda tasi’u yayi wata biyar bai kirani dakinsa ba balle ya shigo dakina sa’ada ce kadai matarsa a gida. Namiji kenan idan kika kalli sa’ada kika kale ni sai ki rasa dalilinsa na son sa’ada, shi da yake da mace kamata a matsayinki na mace ba namiji ba ma sai kice me xai yi da sa’ada baka kirin, xololuwa mai kama da tabarya ko dan kyawun fuska ma bata dashi amma it ace mace ni kuma bora.”
Madina ta rushe da kuka yayin da kaltum take tayata. Madina ta daga idanuwanta ta dubi sama.
Ta ce “Allah kana ganin halindana shiga ada da wanda na ke ciki yanxu. Kaltum ba xaki gane wasu abubuwa da nake fada miki ba saboda baki yi aure ba, baki san rayuwar aure ba, haka gidanku ba mata biyu ba ne balle kisan ma nene kishi da kishiya.”
Ni da ‘yayana mun xama tamkar bayi, ni ban huta ba suma basu sake a gidan ubansu ba. Kaltum, bari in takaice miki tasi’u saida ya sake sakina akan yarinyar nan sa’ada, shi kuma akan abinci ne. ranar girkinta ya bata naira dubu biyu tayi cefanen rana dana dare. Sai ya tafi kasuwa, ita kuma a ranar xata je gidan suna dan haka ta kwada mana gayan tuwo na jiya da mai da yaji tace abincin ranarmu ne ni da ‘ya’yana ta shirya tayi tafiyar ta. Saboda muna jin yunwa haka muka ci nace suyi hakuri xata xo ta dafa mana da dare. Da ta dawo da daddare sai ta shigo da kwano dauke da alala dauri uku ashe mijinta ta daukowa abincin darensa mu banda mu kuma ko sisi bani dashi balle in siya mana abinci ko in yi cefane in dafa mana mu ci ga uwa-uba ina gudun bacin rai dan haka ko farar shinkafa ban dafa mana ba.
Mijinta ya dawo suka shiga daki suna ci suna hira suna shewa har karfe goma na dare. Abdul malik yana xaune a daki yana min juye juyen ulcer sa na kokarin tashi saboda yunwa haka shahida ma kukan yunwa take yi. Na tashi na nufi dakin tasi’u, bayan na yi musu sallama suka bani ixinin shiga, na shiga sannan na durkusa na gaishe shi. Na ce dan Allah ya bani naira dari daya in siyawa yara biredi yunwa muke ji. Ya tambaye ni cike da mamaki y ace ba’ayi abinci bane?
Na ce ai gidan suna sa’ada ta je shiyasa bata yi girki ba.
Sai sa’ada ta hau fada da gatsine gatsine tana min rashin kunya wai ina yawan hada mata gulma, dan haka in fita daga idonta ta rufe. Ya ce in tashi inje dakina yana xuwa yanxu. Na tashi na fice xuciyata na tsananin kuna da radadin bacin rai, sai naji jiri ya dauke ni ina kokarin faduwa a kofar dakin nan da nan na sulale na xauna saboda na san idan na ci gaba da tafiya faduwa xanyi hawan jinni ne dani ya hadu da yunwa. Sai na ji yana ce mata “karki damu kishi ne yake damun madina saboda taga na fi son ki shiyasa take so ta hada mu, kin san rabon da wani abu ya hada ni da ita an doshi wata takwas bana ma kusantar ta.” Sa’ada tayi shewa ta tafa hannu tayi girgixa taji dadi.
Sai na tuno soyayyarmu da tasi’u a da, na tuna yadda na xama haka a wajensa sai na rushe da kuka in tashi ma tsaye ya gagare ni saboda jikina ya mutu. Sai gasu sun fito sai suka yi cikibis da ni a bakin kofa, ya dube ni a sheleke.
Ya ce “kukan me kike yi?
Bana son munafunci ba ni n ace ki je dakinki ki jira niba meye abin xama a nan? ”
Na share hwaye n ace “tasi’u me nayi maka a duniya ka tsanani?
Me nake yi maka yanxu wanda a da bana yi maka yanxu, dan in sani in daina. Tasi’u yanxu baka tausayina ashe, baka nadamar abinda kake yi min ashe?
Na ji kana fada mata baka sona shi yasa baka kula ni ya dace ka fadawa kishiyata haka alhalin ina yi mata boye-boye bana bari ta fahimci halin da nake ciki. Ka daina yi min haka tasi’u nima matarka ce, ni mai sonka ce, har abada ba xan fasa sonka ba kome xaka yi min. tasi’u na yafe maka, tsakani na da kai sai addu’a ta alkhairi domin bana so Allah Y tashe ka da shanyayyen bari jiki ranar gobe kiyama saboda rashin adalci a tsakanin matanka don ana xalunta ta.”
Da alama jikinsa yayi sanyi da farko, saida sa’ada ta kama shi da fada ta inda ta shiga bata nan take fita ba, t ace wai ya tsaya yana kallona bayan labe nake yi musu kullum daman ta sha ganina ina yi musu labe ina jiyo duk abunda suke fada. Tasi’u ya kama ni da fada akan me yasa nake yi musu lae?
Na ce ba labe nake yi musu ba, jiri ne ya dauke ni na ji xan fadi sai na xauna a kofar daki. Sai ya shiga daki y rubuto min takardar saki daya, kinga ya xama saki biyu kenan yayi min.
Na karbi takardar na dauki gyalena na fita ban yiwa ‘ya’yana bayani ba. Ina fita nahau acaba na tafi korau road gidan sumayya kawata na iske tana call a asibiti sai mai gidanta dr basher da yaransu biyu mami da Khalid sunan mommy hafsa da daddy tukur ne aka saka musu, sai a wajensa na karbi kudi na biya dan acaban daya kawo ni. Na ce masa bani da lafiya ne na xo ta duba ni, ina tunanin jinina ne yahau. Ya dauko abun auna jinni ya auna, yana auna ni kuwa sai ya girgice ya kwashe ni a motarsa ya kai ni asibitin su, da yake sun bude asibiti nasu na kansu shi da matarsa a lamido cresent.
Allah sarki madina ko me ya sameta oho.
Se a biyo mu dan jin yadda data kasance.
.
Maza wasu da sanin su wasu ba da sanin su ba, abun da mata yasa suka tsani kishia kenan, inda maza zasu na adalci tsakanin matan su da mata sun so kishia sun dauke ta abokiyar xama, shi yasa ni dan aunty bana ganin laipin mata akan rashin son kishia, kuma duk wata matsalar dake kai kawo cikin gida tsakanin mata na miji shine ummul kaba'isin sa, dan duk na mijin da bai budewa mace kopar iskanci ba a cikin gida bata isa tayi ba, idan ta para ya dakatar da ita ya nuna mata duk matan sane su ai baza ta sake ba, amma akwai wanda ake musu pin karpi da asiri basu san su nayi ba.
Nuna banbanci tsakanin su shine babban abun dake haipar da rashin zaman lapia.
.
Allah Ya tsare mu da mata marassa imani, Ya azurta mu da salihai na gari, kuma matan Allah Ya albarkace ku da maza je na gari Ya kare ku da muguwar kishia Ya hada ku da ta gari.
Aamiin Yaa Rabb 🙏
.
Typing : Sadin Maa
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA2 (P 13)
.
Sumayya tukur ta bani gado na kwanta ta ci gaba da kula da ni, ta fara shawarar neman number tasi ‘u a waya xata shaida masa halin da nake ciki sai na hana ta, nace ko mami hafsa bata san na xo ba kuma bana so ta sani. Na dauko takardar saki na nuna mata, ta yi matukar raxana hadi da gigita tayi ta salati sannan ta ci gaba da bani hakuri tana gargadina da cire son tasi’ u raina kada ya kashe ni a banxa.
Saida na shafe kwanaki biyar a asibiti, sai da suka tabbatar nayi ras sannan muka koma gidanta na xauna bana sakewa a giban ina ganin kamar ina takura musu gobia- gobia da ni na wuce xaman gaban wasu. Sai na yanke shawarar in koma gidana in xauna tunda ban san kowa ba sai Tasi’ u. sumayya ta hana ni ta ce sai dai ta kira mami Hafsa a sanar mata halin da nake ciki sai ta xo ta dauke ni ta mayar da ni maimakon ace da kaina na koma don yin haka xai sake kawo raini da gore-gore a wajen kishiya .
Haka aka yi, mami hafsa da kanta ta dauko ni daga gidan sumayya ta shiga da ni har falon tasi’ u muka iske shi a xaune shi da matarsa. Ta yi masa fada sosai hade da gargadi da wa ‘axi mai ratsa jiki akan ya ji tsoron Allah saboda idan bai yi wasa ba hakkina xai kai shi wuta
Sai sa’da ta hau botsare-botsare tana kokarin yiwa mami hafsa fitsara wai an kori mutum ba xuciya dan naci an dawo da ita. To ita baxa ta xauna da niba in har xan dawo in xauna in ci gaba da xama a gidan ni kadai ita xata wuce, a take ta dauki gyalenta ta fice tabar ‘ya’yanta guda biyu kanana, wannan lokacin tasi’u bai bi bayanta ba washe gari ya aika mata da takardar ta ya sake ta saki daya. Ai kuwa wannan saki ya girgixa ta, yayi musu ciwo ita da danginta gaba daya.
Sa’ada ta shiga damuwa dan bata taba xaton xai iya ya mata haka ba saboda yadda taga yana tattalinta kamar gwal. Tana takama da asiri, asirinta ba xai bari a saketa ba, dan abinda ta dogara dashi kenan.
Kaltum t ace “wannan rayuwa akwai wahala sai ki kayi xamanki ke kadai a gidan, hankalinki a kwance ko? ”
Madina tace “na sami sauki dai kadan saboda tasi’u kwata –kwata ya canxa, hankalinsa baya wajena baya raga min, baya sona, ya xama mutum mai mako ko abincin wadatacce baya bamu ni da ‘ya’yana ga kananan ‘ya’yan sa’ada da nake rikewa. Daga nan ma ya sake sabon aure, ni din ce dai ba xa xauna da ni kadai ba.
Ya auro wata baxawara ta girme ni tama gama haife haifenta a wasu gidajen bama a gida daya ba. Sunanta hajiya talatuwa, ita ma jahila ce ba arabi ba boko, gata katuwar gaske ce xama da kyar tashi da kyar, fuskarta a cike da tsage suffer mata ‘yan duniya dai, itama dai na rasa gane mai ya gani a jikinta, har gara sa’ada da yarinta a jikinta.
Itama ta shigo da nata salon iskancin, shima bai isa ba balle ni da ‘ya’yana a haka muka shekara ana ta tafkawa. Bana kula ta sai dai addu’a ni ke Allah Y daidaita mu amma abu yaci tura. Sai ma wata masifar ya kara lalubowa wai xai dawo da sa’ada gidan don haka yasa na kwashe kujeruna na cusa su a daki daya. Ya toshe ya hade mata da falonsa, su duka suna da daki bibbiyu ni kuwa daya jal amma ban damu ba, ina ta hakuri ina ta addu’a Allah Ya ganar dashi, duka da haka bana nadamar aurensa da na yi saboda idan na tuna daga inda na fito da yadda nake a da, na ci riba dana samu na musulunta kuma ga ‘ya’yana nan hausawa musulmai sun sami ilimin dana boko yadda ya kamata.
Amma duk nacin nan nawa saida dole na fita a sanda yayi min saki uku, tasi’u ya yi min karya wai dukkanmu ukun mu tafi gidajen mu ya gaji da rigima ya miko min takardar saki. Ya ce min suma sauran ya basu takardar saki. Suka hau shirye shiryensu a jaka suka fice ashe dana tafi sun dawo gidan ni din ce dai yake so ya saki shine suka hada baki aka kore ni.
Tun sakin yana bani tsoro har ya daina, saboda nasan Allah Shi ne gatan bawa. Tasi’u bai isa yayi min arxiki ba, bai isa ya yaye min maraici da talauci ba, xuciyata ta kyankyashe tunda yayi min saki biyu ban yi masa komai ba sai na sadakar nasa a raina xai karasa ukun daman. Sannan na ji bana sonsa saboda yana cusguna min na xabi gara in xauna lafiya da in cusa takaicin da namiji a raina ya janyo min ciwo a banxa, ba kula ni xai yi ba hankalinsa na wajen matansa in ji da hawan jinin da na hadu dashi akan sa’ada. Na shirya kayan sawata tsab a jakuna da akwatina, ‘ya’yana suka taya ni diba na shiga gidan general tukur domin sune uwata, su ne ubana bani da inda xanje.
Wannan rana itace ranar farko dana xaunar dasu duka na basu labarina naci sa’a kuwa duk suna gida. Daddy da mami hafsa, sumayya da mjinta sun xo su ma haka abba ya xo gida daga inda yake bautar kasa. Kannensa na gida. Ga ‘ya’yana nan gaba daya su ukun suna tare da ni, na fayyace musu tarihin rayuwata tun daga ranar da aka haifeni har ranar da tasi’u ya sake ni saki uku.
Hankalin dukkanninsu ya tashi matuka babu wanda bai xubar min da hawaye ba musamman ‘yayana sun gigita da suka ji tarihina koda wasa basu taba sani ba. Don su a tunaninsu mami hafsat ‘yan uwana ne na jini saboda yadda suka taso suka ga yadda muke yi dasu.”
Kaltum tace “a lokacin ‘yayanki sun yi wayo kenan har sun san ciwon Magana? !”
madina tace “shekara guda ken an da yin abun ba’a dade ba sosai ba, sun girma mana har sun girme ki yanxu. Abdul malik, shekarunsa goma sha bakwai yana kokarin shiga jami’a, Abdul hakim ne yake dab da kammala secondary shekarunsa goma sha shida, shahida ce take primary ita kuma shekarunta goma a duniya, su dukka sun yi hankali sun san komai.
Daga karshe nayi musu ban kwana nace xan koma garinmu. Su duka suka hana ni, shawara daya suka tsayar shine in yi xamana a gidan general tukur ga dakuna nan birjik in xaba in darje duk inda yayi min, ko in kaura bangaren sumayya tunda tayi aure babu kowa har yanxu. Falo ne kato da daki mai dauke da bandaki, ga dining area, nace bana so in xame musu wahala tunda na girma ba xan ji dadin irin wannan xama ba.xan fi son daddy ya taimaka ya samar min aiki a asibiti in kaura can gara in yi nisa da tasi’u domin bana so mu dinga haduwa dashi ko da matansa idan ina ganinsu fami ne babba a xuciyata don xan dinga tuna abubuwan da suka yi min a rayuwata. Sannan idan ina kusa xasu dinga batawa ‘ya’yana don in ji haushi amma idan bana unguwar koma bana garin xan fi jin dadi da sakewa, hankalina xai fi kwanciya.
Suka gamsu da bayanina, daddy ya bani goyon baya akan bukatuna sai dai yace bai san kowa ba a bangaren health a kano amma a jigawa yana da abokai a bangaren health, nan da nan na amsa masa ina so a jigawar na ma fi son haka, ya karbi takarduna yace in saurare shi. Tsawon watanni biyu cur ina xaman jiran aiki amma tamkar a daure nake Allah-Allah nake in samu aiki in bar unguwar. Kinga kuwa abunda nake gudu saida ya afku, tasi’u ya hana ‘ya’yana xuwa wajena duk san da suka shigo sai an fada masa ya dake su musammam karamar ba xata iya daurewa ba sai ta shigo sai dai ya kashe ta. Haka suma kishiyoyi na ina samun sakonnin bakaken maganganunsu musamman daga sa’ada. Sannan na kan jiyo muryar tasi’u daga dakin da nake shima babban bacin rai ne domin na tsane shi bana son ganinsa.
Aka kira ni interbiew a dutse na ji nayi, abunka da hanya ba’a dade ba aka bani offer an dauke ni aiki sai dai kaxaure suka tura ni. Naji dadi nan da nan na hada kayana daddy yasa direbansa ya kaini kafin in tafi mami hafsa ta dauki lokaci mai tsawo tana yi min nasiha cewar in kama kaina in rike mutuncina idan na samu miji in yi aure in cire son tasi’u a raina, na ci sa’a na samu gida a staff querters din asibitin, daki biyu da tsakar gida ga kicin da ban daki.
Hakika na ji dadin aikina ina xaune da abokan aikina mata da maxa lafiya. Dan albashi na yana isata in ci abinci, in dinka ‘yar sutura har in kunshe in kawowa yarana wani kudin ko su shigo mota idan babansu baya gari su xo su karba. Na ci gaba da kama kai na ina rike addinina yadda ya kamata ina cikin walwala fiye da a gidan tasi’u. labari ya iske kunnen makiyana cewar na samu aiki har na murmure na yi kyau sai haushi ya ishe su, suna hassada dama ban samu ba sun fi so kullum in shiga wahala da wulakanci amma Allah Ya fi su.”
Kaltum tayi dariya tace “na ji dadin labarin nan naki matuka da na ji karshen ki alkhairi ne. Allah Ya dube ki ya rufa miki asiri musamman da kika yi tawakkali kika cire son tasi’u a xuciyar ki. Ta amma me yasa kika bar aikinki kika taho nan bayan aikin yafi tahowa ki? ”
Madina ta yi ‘yar dariyar karfin hali ta cije leben kasa tace “kaltum, kema kin san in har babu matsalar da tafi karfina, ba xan baro aikina in taho ba. Gagarumar matsala ce ta fado min wacce har tafi matsalolin da na hadu dasu a baya. Tsanani yayi tsanani wanda har mami hafsat da daddy tukur da sumayya kawata masoyana wa anda bani da kamar su a duniya suka kini suka kira nida MAYYA. In takaice miki hatta da ‘ya’yana dana Haifa a cikina saida suka ki ni suka guje ni, suka ce ni ba uwarsu b ace. Kaltum tun daga ranar da Abdul malik ya furta min haka, na jawo hannun Abdul hakim ya fisge yace min bana sonki mama, nace to ba ni da amfani a duniya, rayuwata ta xo karshe gara in shiga duniya kawai xai fi ye min sauki.” Sai madina ta rushe da kuka.
Kaltum ta ji hankalinta ya tashi, tuni ta shiga surkukin tunani ta tambaya cikin damuwa “anty, me yasa haka?
Me kika yi musu haka ko asiri aka yi miki kowa ya tsaneki ? ”
Madina ta goge hawayen ta ta yi dan murmushi t ace “ba asiri ba ne kaltum kaddara ce kawai ta hau kaina sai dai in xama me godewa Allah a duk halin da na tsinci kaina. Xaki ji dalili kema idan kika ji dalilinsu baxa ki xarge suba, watakila ma k ice sunyi daidai da suka yi min haka amma nima ba laifina ba ne an yanke min hukunci bisa rashin sani.”
Madina na rufe bakinta sai ga baba tsoho mai sayar da ruwa ya dawo akan jakunansa, ya ja ya tasaya a gabansu kaltum, daya dubeta sai yayi dariya.
Cikin harshen larabci yace “’yar baiwa dawowa nayi in cika alkawarin dana dauka , dana ce idan na sayar xan siyo miki gurasa da xuma gashi na kawo miki. Na sayar da ruwan dukka har xan koma in karo wani.”
Kaltum ta tashi da murna taje ta durkusa ta karba tana godiya ya wuce ya tafi. Ta xo ta ajiye a gaban madina tana mai fassara mata abunda suka fada cikin harshen larabci.
Madina tayiwa tsohon nan addu’a suna ci suna yabonsa har suka cika tunbinsu, saboda gurasar mai yawa ce, badan suna jin yunwa ba da ba xasu iya cinyewa duka ba, suka kora da ruwa.
Madina tace “muje muyi sallah na lura axahar tayi sai mu dawo mu ci gaba da labari . Kaltum, labarina akwai abin al’ajabi nan gaba, ai ba ki ji komai bama a baya.”
Kaltum t ace “tabbas na shiga wani hali na xumudin son in ji wannan labarin, kaina gaba daya ya daure tamkar an yi min dabaibayi.”
Suka shiga gida da ruwansu don suyi alwala suyi sallah, saida suka idar da sallah sukayi nafiloli da addu’o’insu sanna suka dawo wajensu na da wato kofar gida suka xauna yayin da wata iska mai dadi take kada su baya ga tumbinsu daya dau lodi, don haka mai sauraro, da mai bayar da labari suka sami nutsuwa labarin ya fara tafiya yadda ya kamata.
Kaltum ta dubi madina ta fada cikin kaguwa tace “anty ci gaba ina sauraron ki.”
Madina ta nisa tace “watanni shida da fara aiki a asibitin kaxaure yayin da shekarata talatin da uku a duniya. Tukur tukur wato Abba kanin kawata Dr sumayya tukur, ya kawo min xiyara har kaxaure wajen aikina da misalin karfe tara na safiyar wata littinin. Yaro matashi a tseleliyar motar da mahaifinsa ya saya masa a satin saboda farin cikin kammala bautar kasarsa da yayi ya xama cikakken lauyer.
Banyi mamaki ba da naga Abba a kaxaure a daidai wannan lokacin, kuma ban yi mamakin ganin tsaleliyar motar nan tasa ba saboda nasan mahaifinsa xai iya bashi wacce ta fita ma saboda general tukur mutum ne mai son ‘ya’yansa da yawa. Sai na dauka Abba ya xo don ya nuna min sabuwar motarsa ne, ban yi mamaki ba idan haka ne saboda Abba mutumi na ne sosai, abokin labarina ne a yi wasa ayi dariya ayi shewa saboda ni mai yawan Magana ce da xolaya.
Abokan aikina har guda biyu suka shigo office dina suna shaida min cewar nayi bako a waje yace daga kano yake sunan sa Abba tukur, sai nace su ce masa ya shigo amma Abban na tsaye a bakin baranda bai shigo ba. Na aika masinjanmu har sau biyu yace masa ya shigo amma Abba bai shigo ciki ba, ni kuma ina ta faman aiki ina shigar da sunayen da sakamakon wadanda muka yiwa gwajin hawan jinni da ciwon suga cikin wani file. Kafin su xo su karbi sakamakon su. Dole tasa na ajiye biron na fito da kaina, ina ta murnar ganinsa ina ta hayaniya ni kadai. Haja ina ta shafa mota ina doguwar addu’a ni kadai Abba na tsaye kikam bai ce da ni komai ba.
Ya xura hannu a aljihun wandon yayin da yayi shar a cikin suit dinsa baka da farar shirt a ciki mai dogon hannu, wuyansa makale da nektie, sai wani bakin takalmi kafa ciki sai sheki ya keyi. Abba ya yi kiba, ya murmure yayin da kalar fatarsa mai hasken duhu (chocolate colour) ta sake haskakawa, dogon hancinsa da habarsa wato (quarter million) sai abun salla baki a goshinsa ya dinga walkiya babu musu kana ganinsa ko ba’a fada maka ba kaga cikakken lauyer ko likita.
Na dube shi tsab sai na kwashe da dariya nace “barrister Abba, nutsuwa ceta xo maka ne, saboda an girma aka daina Magana sai sunkuyar da kai kasa?
Ni yayarka ce fa na san tsarkin kashinka, ni kuma xaka jawa aji?
Wuce cikin office ka taya ni aiki, idan na gama sai mu je gidana ka ci wani abu.”
Na wuce gaba Abba yana biye da ni har cikin office dinmu. Mu biyu ne a offishin kowacce da kujerarta sai na ci sa’a a ranar dayar bata xo aiki ba sai ni kadai. Na jawo masa daya kujerar kusa da ni nace ya xauna, ya xauna a hankali. Idan Abba ya dube ni sau daya sai ya sunkuyar da kai kasa da sauri wanda ada baya yi min haka. Ya gaishe ni cikin siririyar murya mai tafe da tsantsar ladabi da biyayya. Na amsa masa a sanyaye, sai na gyara xama a hankali ina fuskantarsa na dube shi na tambaya cikin fargaba. Na ce “Abba lafiya?
Waye bashi da lafiya ko kuma waye ya rasu, ‘yayana ne ko? ”
ya girgixa kai yace “babu wanda ya rasu kowa lafiyarsa kalau.” Na xungure shi na yi dariyar farin ciki nace “shegantakar banxa, wai meye haka ko yunwa kake ji in je in sayo maka abinci? ”
ya sake girgixa kai a sanyaye alama baya ci.
Na ce “to yanxu xaka warware dole idan na saka ka aiki, karbi biron nan ka fara shigar min da sunayen nan cikin file din nan.” Abun mamaki sai ya karbi biron hannunsa ya hau karkarwa ya kasa rubutun, ina daga nesa na jiyo bugun xuciyar sa ke yi saboda tashin hankalin da yake ciki. Na mike tsaye da sauri na fashe da kuka na tambaye shi cikin kakkausar murya Abba, ka fada min abunda yake faruwa kafin xuciyata ta buga, kasan ina da ciwon xuciya da hawan jini idan ba so kake na mutu ba, ka fada min abunda yake faruwa. Ni musulma ce Abba na san kaddar na yarda da ita kuma ‘ya’yana ne suka mutu ko?
Ko kuwa mami ce ko daddy? ”
Shima sai ya fara hawaye yace wallahi babu wanda ya rasu, xauna in fada miki abunda yake tafe da ni.”
Na xauna da sauri jikina na rawa na xura masa ido hawayena yaki ya tsaya, amma sai naga yahau kame kame, yayin da yana Magana numfashinsa ya na kokarin tafiya gaba daya saboda fargaba. Bana jin abunda yake fadi, sai na tabbatar Abba bashi da lafiya yau har maganarsa na hardewa baya ga bugun da kirjinsa ke yi tamkar xuciyar sa xata fito sarari in ganta. Na dora hannuna a kirjinsa na dafe yayin dana dafa kansa na fara tambayarsa ina ne yake masa ciwo?
Sai na ji ya ja dogon numfashi yayi ajiyar xuciya da karfi tamkar ransa xai fice. Na figa da gudu xanje in kira likita, sai naji ya jawo hannuna ya dakatar da ni yace “lafiyata kalau sister madina, dawo ki xauna xa muyi wata magan.”
Na dauka abin gwada jini na auna dantsensa, hakika jininsa yahau kadan. Na ce “Abba me yake damunka kai kuwa a duniya da har ka hadu da hawan jin kana karamin ka?
Abba me kake nema ka rasa a duniya daya wanda ya dameka a xuciyar ka?
Kada ka kashe kanka a banxa ka tashi iyayenka tsaye bayan iyayenka gaba daya burinsu da tanadin su akan ka, ka gama karatunaka kai na miji ne babban namiji, ka dube ni mana ka dubi irin matsananciyar rayuwar da nake ciki amma na yi hakuri da tawakkali.”
Sai ya sirnano da hawaye yace “ai kuwa sun kusa su rasa ni, shine ma abunda na xo in bayyana miki. Sister madina, ajalina ya xo tabbas na kusa mutuwa.”
Sai na fashe da kuka na dauki dogon salati, shima kukan yake. Na ce “Abba me nene matasalarka inyi maka maganinta in har xan iya? ”
Ya girgixa kai ya yi murmushi yace “ba xaki iya ba sister madina, abu daya nasan xaki iya taya ni dashi shine addu’a, itama sai bayan na mutu xaki tabbatar abun nan da nake fada miki bada wasa nake yi ba. Ba ni ne na jawowa kaina ciwon da gangan ba, sister madina na dade da kamuwa da ciwon nan a kalla xai yi wata shida ina fama da abu daya ni kadai amma daidai da rana daya ban taba samun sassauci ba sai dai ma karuwa da ciwon yake yi. Na rasa yadda xan yi har na tsani kaina da kaina kafin jama’ar gari su ji su tsane ni suma.” Sai kuka ya ci karfinsa, ya rushe da kuka me tsanani..
Ni kuka, shi kuka. Na tambaya cikin kuka “kai kuwa Abba wannan wane irin ciwo ne?
me yayi xafi haka ka fada mini ko mene ne irin ciwon ne, na yi alkawarin xanyi iyaka kokarina wajen taimaka maka, xan yarda da abunda xaka fada min ko da ace duniya gaba daya xasu karyata ka. Me yake damunka kanina ka fada min, Abba ciwon kanjamau ka dauko? ”
Sai yayi murmushi yace “kanin ki? Anya kuwa yau xaki bi bayan kanin nan naki kuwa, alhali ya bi baudaddiyar gada mai Burma wa?
Ke ceta farko da xaki fara karyata kaninnan naki a yau koda ace duniya gaba daya xasu gaskata shi. Ciwon kanjamau sassaukan ciwo ne tunda yana da maganin da xa’a sha a xauna lafiya a ci gaba da rayuwa cikin kwnciyar hankali.”
Sai na fara tsorota da jin irin wannan sababbin lafaxai daga bakin dan uwana Abba. Na koma jikin kujera na jingina na langwabe kai ina dubansa, na ji alamar jini na ya fara hawa.
Ya ga alamar na damu sosai sai ya shiga lallashina yana bani hakuri. Na fada cikin sanyayyar murya nace “Abba bana bukatar hakurinka, laifin me kayi min da xa ka bani hakuri?
Sai dai ina mamakin wannan al’amari naka, idan wasa ne ka daina. Wannan watan September ne ba april ba balle kayi min April full na kasa gane manufarka. Ka xo ne kawai don ka tayar min da hankali tunda baka tausayi na yanxu, bayan kasan tashin hankalin da nake ciki na rabu da mijina, na rabu da ‘’ya’’yana, ba ni da kowa sai Allah , sai kuma ku da iyayenku.” Na fashe da kuka.
Ya girgixa kai yace “ba April full ba ne ba, ba ma irin wannan wasan dake sistr madina. Ki gafarce ni akan abunda nake shirin fada miki domin nasan ba xai yi miki dadi ba ko kadan.”
Sai na ji xuciyata ta sake harbawa na shiga tunanin abunda xai fito daga bakinsa marar dadi da yadda kunnuwana xasu xukowa kwakwalwata. ‘ficik’ na jiyo wata kakkausar mummunar kalamai sun fito daga bakinsa xuwa kunnuwata yayin da xuciyata ta harxuka, kaina ya sara, kan kace kwabo gumi ya keto min, tsigar jikina ya mike tamkar an kwara min ruwan kankara a lokacin hunturu, na ji kamar na shake shi ya mutu, nima idan ya so a kashe ni, har na gwammace mutuwata da wannan mumunar kalaman daya fada min.
‘wukit’ na bude dara-daran iduwannan nawa na dube shi yayin da nasa dara-daran idanuwan suka tsugunna kasa da sauri. Na fada cikin fushi n ace “Abba ban jiba, maimaita min abunda ka fada.”
To pa, ko wace irin mummunar kalma Abba ya padi, bamu sani ba, nima se dubawa nake na kasa sanin me ya padi mata....
.
Kai Sadin Maa da iya datse labari kike..
Allah Ya kai mu goben muji me ya sanar da ita...
.
Typing : Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 2 ( P 14)
.
TRUE LIFE STORY
.
Me Abba ya padi ne?
Tabbas kunnuwana ba suyi min karya ba Kalaman daxu ce ya maimaita min itace “SISTER MADINA ALLAH YA DORA MIN CUTAR SONKI.”
Na ce “Abba kamar so na ji ta fi fito daga bakinka ixuwa gare ni kunu wata?
Ashe xaka iya duban sumayya ka ce kana sonta so iri na soyayya? ”
Sai ya durkushe a kasa yana neman gafrata, yayinda yake nuna min kuskure yayi ba haka yake so ya fada min ba, kubcewa Kalmar tayi.
Na fuskanci xai raina min hankali don haka na mike a fusace na nuna masa hanyar waje, ma’ana ya tashi ya fita daga office dina. Simi-simi ya mike yana tuntube ya fice, na yi kukan takaici har na gaji a wannan rana. Na ji na tsani Abba har na fi tsanar kai na, ina tunanin Abba yana yi min kallon ‘yar iska don ba ni da miji kuma bani da kudi don haka xai xo ya sauke tashen balagarsa akaina. Na tunano tonan sililin da xa’ayi min idan har maganar na ta fito fili, mutuncina xai xube a idon mutane. A yi min mummunar fahimta da fassara ace yara nake bi kanana sa’annin kanne na ko ‘yayana.
Maganr nan ta dame ni sosai a raina, kwana biyu bana xuwa office ina gida ina xulumi ni kadai babu wacce xan iya fadawa. Abun mamaki sai ga Abba na turo min sakonnin soyayya ta waya, yana bayyana min mummunar halin da yake ciki a sanadiyar rashin amincewata.
Bana bashi amsa sai dai in yi kuka in goge sai takai ta kawo ya daina turo sakonnin saboda bana bashi amsa ya fara kiran lambar. Watarana da daddare misalin karfe goma da rabi ya kira ni, a wannan lokacin ne na fara amsa wayarsa don da rejecting nake yi sai a lokacin na samu daman amayar da duk abundake xuciyata. Na ja masa kunne nace Abba, saboda talauci da rashin gata da rashin asali mai kyau ne har na xama haka a wajen ka?
Ko rashin miji da rashin kudi shine kake tunanin xan xubar da girmana da mutuncina in yi lalata da kai?
Ko dan a gidanku ne ake taimakona shike nan na xama wulakantacciyar baiwa wacce xaka iya daukarta wajen biyan bukatar ka ta banxa? ”
Sai ya rafka salati yayin daya hau rantse-rantse cewar ba haka ba ne. ya shiga yi min bayani wallahi shima ya tsinci kansa ne a cikin wannan hali wanda da farko bai yarda ba sai da abu ya ci tura bayan yayi addu’a da kansa haka yasa abokansa sun taya shi akan Allah Ya yaye masa amma abu sai karuwa yake yi shine ya yanke shawarar bayyana min ko xan taya shi addu’a daman yasan ko da wasa ba xan amince ba.
Na sake jin na tsane shi fiye da da, na shaida masa koda har abada babu wani namiji a doron kasa saishi to wallahi gara in koma ga mahliccina banyi soyayya ba da na yi soyayya dashi. Na fatattake shi na ja masa kunnuwa koda wasa kada ya sake kirana ko ya turo min sako balle ya tako ya xo kaxaure. Nima har abada na daina xuwa gidansu.
Sai na ji ya fashe da kuka yana fadin inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, na murtsuke wayar gaba daya na kashe. Sai da aka yi sati guda sannan na kunna abun mamaki sai ga sakonninsa ba adadi. Hakuri dai yake bani, lallashina yake in saurare shi, wai ya kasa daina sona.
[TAB “SO” BALA’I YA ALLAH KA MANA BAIWAR WANDA XUCIYAR MU TA XABA DA DUKKAN KHAIRI, amen]
(Aamiin thumma Aamiin Sadin Maa)
Wanna al’amari na Abba ya fara tsorata ni sai na shiga tsayuwar dare ina mai neman tsari daga sharrin Abba. Hankalina ya tashi dana ji kiran wayar yayarsa sumayya ta dinga damuna da tambaya wai me yasa bana xuwa week end yanxu sunga na dade ban je ba. Na lura dai bata san abunda yake faruwa ba, haka daga mami hafsa ta kira ni sai kirjina ya harba sai idan naji ba wannan ba ne dalilin kiranta sannan in ji sanyi a xuciyata, ina ta faman yi musu karairaye cewa aiki ne ya yi min yawa amma xan xo.
Wani week end sai ga Abba har cikin gidana ya shigo ya iske ni kadai a xaune atsakar gida, ya yi baki sosai kuma ya rame. Yana shigowa sai ya tsugunna ya gaishe ni, ban amsa ba, sai ya koma gefe ya tsugunna rabe har abin tausayi.
Ban kula shi ba, na tashi na ci gaba da aikace aikace na na tsakar gida, almajiri na ya shigo na mika masa tsintsiya xai yi min shara sai Abba yayi xuruf ya dauki tsintsiyar ya fara shara. Cikin fushi na Harare shi na daka masa tsawa nace ya ajiye min tsintsiyata bana son shararsa, ya ajiye da sauri ya koma gefe ya tsugunna. Almajirin yakare shara sai na dauko kayan miya nace ya gyara min ya kai markade, sai Abba ya taso da sauri yahau tsinke hancin tattasai. Ko kallonsa ban yi ba don na fuskanci takalo abunda xan fara yi masa Magana yake yi. Ya ja alamajiri suka tafi markade a inji.
Takaici ya sana rushe da kuka ni kadai a tsakar gida, na rasa abunda yake yi min dadi suka dawo suka iske ni ina kuka Abba ya xo ya durkusa a gabana yana furta min kalaman sanyaya rai dan hankalina ya kwanta amma sai suka xame min tamkar wuta yake hura min a xuciyata. Na hasala na mike tsaye na dakawa almajiri na tsawa nace ya fice min daga gida, ya fice da gudu saboda yaga yadda raina ya baci kada in kai masa mari duk da yasan bai yi min laifin komai ba. Yayin da na juya na dubi Abba a durkushe a gabana na sake jin haushinsa da tsantsar tsanar sa suka hadu, na fashe da kuka mai tsanani.
Na ce “Abba, idan sha’awa ce ke damunka me xaka yi da tsohuwa er shekaru talatin da uku kana saurayin dan shekara ashirin da takwas?
Me xaka yi da ni wacce na tsufa na gama haife-haifena, wacce ba ni da sauran amfani na wanda har shi kansa mijina yaga bani da amfani ya sake ni, yakore ni, yace baya sona. Me xaka yi da sauran alhali ga sababbin ‘yan mata can a gari wadanda ido rufe irinka suke nema. Na yaye hijabinda yake jikina daga ni sai siket da t-shirt ko eaner wears ban sa ba. Na ce me kake sha’awa a jiki na?
Idan sha’awata ka ke yi mushiga daki in har daga yau xaka rabu da ni in huta.”
Sai Abba ya sa hannu ya rufe idanunsa da sauri yaki dubana, ya girgixa kai ya fada cikin tashin hankali da damuwa y ace “wallahi sister ba wannan ba ne manufata, ban taba sha’awarki ba kuma da xaki yarda ki aure ni ki gindaya min sharadin kada in dangwali hanuna a jikin ki, har karshen rayuwar mu to xan amince, don ni ke nake so kawai.”
Hankalina ya gushe yayin da haushi ya ishe ni, na rufe ido na na yi ta cusa masa ashar babu kakkautawa. Na ce ya tashi ya bar min gida kafin na dauko tabarya in fasa masa kai. Ya tashi sadan sadan ya kama hanyar waje saida ya kai bakin kofa, ya waiwayo ya dube ni yana hawaye yace “madina idan na mutu kece ajalina, nagode da duk abubuwanda kika yi min, ki yafe min, ki yafe min nima ba haka na soba.” Sai ya fice ya bar ni a nan a tsaye kamar gunki.
Bayan sati biyu da faruwar wannan al’amarin a bisa takurawar mami hafsa da sumayya akan na xo week end dan na dade ban je ba, dole tasa na ebo ‘yan kayana kala biyu na taho gidansu Abba. Abba na fara iskewa a falo yana xaune sai gumi yake yi shi kadai duk da AC dake kunne a falo, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar yana cikin matsananciyar rayuwa. yana ganina sai ya xabura ya gyara xama sai dai kash ya kasa hada ido da ni, ni nake yi masa duba irin na tsantsanr tsana da jan kunne ma’ana niba sa’arka bace.
Na wuce shi ba tare da na yi masa Magana ba na isa kofar dakin mahaifiyarsa na kwankwasa mata kofa gami da yi mata sallama.
Kasancewar tasan ina tafe nan ta dau muryarta t ace “madina ki shigo mana.” Na shiga muka gaisa, na tambaya duk ‘ya’yanta sai ban tambayi Abba ba, tace “mutuminki ma Abba ya dawo daga bautar kasa. Bai je ya nuna miki motarsa ba? ”
da xata lura da ni a lokacin da xata ga yadda na raxana yayin da a gigice n ace “be je ba.”
Sai ta dan gatsine fuska tace “Abban ma kamar wanda aka yiwa jifa a kudu nan daya je wajen bautar kasa, daya dawo duk ya susuce kamar bashi ba, baya son shiga mutane haka nan baya walwala da kyar sai da lallashi yake dan cin abinci. Sai daddy ya dauko mai aski da gyaran fuska, sai kaga ya tara kasunba yumu-yumu yana muxurai kamar wani bunsuru, kai gaskiya Abba ba lafiya ba. Shiga dakinsa ki ganshi ko ke da yake mutuniyarsa ce xai yi miki bayani.”
Sai na ji gabana ya yanke ya fadi tabbas al’amarin Abba ya fara bani tsoro ya wuce xolaya kamar yadda nake tunani. Kan kace kwabo hankalina ya tashi na shiga xulumi, abu daya nake tsoro kada Abba ya sake ya furta musu damuwarsa, yana furtawa kuwa mutuncin dake tsakaninmu dasu ya rabu har abada saboda ba abu ne mai yuwa ba, a dukka bangarorin biyu ko da’ace su xasu yarda niba xan yarda da yaron da na girma ba koda wanda ma ban sani ba ne, balle Abba yaron da na sani, na san yarintar sa. Baxan iya ba har abada, da in yi soyayya da Abba gara Allah ya dauki raina shi ma na fada masa haka. A haka na share xancen xuwa dakin Abba, na yi saurin xakulo hira kala-kala daga nan ma ‘yayana suka shigo muka hau murnar ganin juna daga karshe suka rako ni har wajen motoci direba ya kaini gidan sumayya.
Ina xuwa gidan sumayya muna hira sai da ta maimaita min abunda mahaifiyarta ta fada min akan Abba cewar ko an jefe shi ne a wajen bautar kasa, saboda ya susuce. Itama tana so na tambaye shi cikin dabara kasancewar sun san mutumi na ne, na amsa mata amma badan xan yi ba. A daddafe na yi kwana biyu a gidan su Abba, na je ranar juma’a da yamma na koma kaxaure ranar lahadi da yamma.
Naga yarana na basu abin da suke bukata, shima Amma mun harhadu a falon gidan musamman da safe idan zamu karya sai dai baya iya yi min Magana nice ke faman washe masa baki ina yi masa wasa a dole saboda a gaban iyayensa ne kada su gane akwai wata ‘yar takaddama a tsakanin mu na sulalo na dawo kaxaure da xummar a wata shida ma ba xan je kano ba, ai dai na yi tunda na je.
Haka kuwa aka yi na dade ban je kano ba sun yi min xancen xuwa week end sai na fake da aiki yayi min yawa. Kusan watanni uku ban ga Abba ba, ban ji kiransa ba a waya sai hankalina ya kwanta na dauka ya hakura da ni. Wata rana da daddare ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya. Na rufe gidana tun kafin magaruba, ina dakina akan salla na idar da sallar isha’I ina wuridi da addu’o’I kala kala ina fadar bukatuna, saboda Allah Yana amsa addu’a a lokacin da ruwan sama yake sauka. Na ji yo da gaske ana buga min kofa sai jikina ya dau rawa, kwallawa nake yi ina tambaya “waye? ” shiru ba amsa, sake bugun kofar ake yi da karfi na wawuri lema na fito tsakar gida na tsaya, can dai na isa bakin kofa na yi Magana “waye? Waye? ”
shiru sai bugun da ya karu. La’ilaha illa Anta subhanaKa inni kuntu minaxxwalimina” na yi ta karantawa sannan na bude kofar jikina na rawa.
Dogon namiji sanye da shadda taxarce koriya da hula na gani a tsaye yaro-yaro yana digar ruwa ya jike sharaf. Ban gane ko waye ba na tambaya cikin firgici “bawan Allah wa kake nema ne, ko kayi batan kai ne? ”
sai yace “ke nake nema.” Na jima a tsaye ina dubansa saboda duhu ba wuta ban gane ko waye ba ne amma ni xuciyata bata bani mutumin nan xai cuce niba saboda nayi addu’a Allah xai kiyaye ni. Sai na ji ya bani tausayi saboda yana tsaye har yanxu a cikin ruwa, yana dukansa. Na sa Allah daya a raina ko daya xo da niyyar cutar da ni Allah xai kare ni sai na matsa ya shigo xauren. Ban de rufe kofar ba muka iso falo a inda na kunna fitila sai ga Abba duban farko na gane shi sai na ji tamkar an hura min wuta a xuciyata dan haushi.
Na fada a hasale “Abba, baka rabu da niba ko? Sai ya fada cike da tabbaci “ba xan iya rabuwa da ke ba, har sai ranar da na rabu da raina.” Sai a lokacin na tabbatar na hadu da alakakai, na hadu da masifar rayuwa.
Na ce “ni kuwa gara a raba ni da raina da in yi soyayya da kai.” Sai kuma ya rushe da kuka harda dora hannu a kai, yana tambaya ta waishi a duniyar nan me yayi min haka nake yi masa wannan wulakancn?
Wai me yasa na tsane shi alhalin yana so na?
sai naga ya dafe kirji da alama xuciyar sa ke yi masa ciwo, yaro yana kokarin kakkafe min xai fadi ya mutu.
Nan da nan na fara lallashinsa ina cewa ya kwantar da hankalinsa na amince. Wannan Kalmar na fitowa daga bakina sai naga Abba ya lafa, ya koma ya xauna ya mike kafa a tsakiyar falon. Da yake babu kujeru a falon leda ce da labule kawai, ni ma na samu lungu na xauna muka yi jugum kamar a gidan makoki. Idan ya dago ido ya dube ni sai yayi murmushi ya sunkuyar da kai kasa da alama yau farin ciki ya same shi kasan cewar na amsa masa . ni kuwa tuni takaici ya dame ni.
Fiye da awa guda muna xaune a cikin wannan yanayi, sai na dube shi na ce “ruwan sama ya tsaya sai ka tafi gida ko? ” ya juyo ya dube ni yace “a ina xan hau motar kano? ” na fusata na harare shi na ce “da ta ina ka biyo ka xo? ”
sai ya dukar da kai kasa cikin ladabi yace “nagode xan tafi saida safe.” Ya mike ya fara tafiya, ban amsa masa ba na saka shi a gaba muka fita har kofar gida. Na waiwaiga ban ga motar daya xo da ita ba, ashe da gaske bada mota ya xo ba a motar haya ya xo. Ina lekensa ya nufi hanyar get xai tafi tasha ga nisa, gashi garin tsit babu ‘yan Babura, ga tsananin iska da sanyi, ga kayan jikinsa a jike sharkaf. Yana ta rawar dari ya tafi yayin da ni kuma na ji ko a jikina bai dameni ba shiya dorawa kansa wahala, na jawo kofata na rufe na shiga daki na kwanta. Ina ta sake sake a raina, idan na fara saka soyayyata da Abba sai na yi maxa na warware baxan iya soyayya da kanina ba sai dai duk mu rasa rayukan mu ni dashi gaba daya.
Wayata ceta hau kara na xabura na duba Abba ne, sai na yi sauri na katse dan ba xan amsa ba , ya ci gaba da kira, ina ta rejecting. Sai ya turo rubutaccen sako yana shaida min ya isa gida lafiya. Na tabe baki nace “ina ruwana, ni na aike ka.” Yaron nan bai iya barci ba haka har cikin dare bai daina turo sakonni ba, har saida nayi masa reply, sannan ya runtsa. Ka da ki dauka wata Kalmar soyayya na rubuta masa kalma daya na rubuta itace. “ok” sannan ya kyale ni na runtsa.
Kaltum na rike haba ta afka cikin mamaki tace “cafdijam, haka soyayya take daman ko a fim din indiya ban taba ganin irin wannan soyayya ba.”
Madina ta yi dariya tace “so ya wuce haka ma kaltum, ai ke yarinya ce karama baxa ki sani ba sai dai nan gaba. Ke in takaice miki duk wannan halin da Abba ya shiga ban fada miki komai ba ma saboda kwakwalwarki karama ce ba xaki fahimta ba, kadan nake takaice miki, kuma duk wannan rigimar da aka yi ba’ayi komai ba. Bala’I na gaba sai kin tausayawa Abba, ko makiyinsa xai tausaya masa idan ya ga halin da yake ciki.
Hakika daga baya na tabbatar bada gangan yake yi ba da gaske Allah Ya saukar masa da jarabawar sona wacce ta xame masa matsala a dukkanin lamarinsa. Na fuskanci shi kansa baya son nacin da yake yi min yana iya kokarinsa wajen danne son da ture shi amma abu ya ci tura, ko baya so xuciyarsa xata tursasa shi sai yayi min waya idan ban amsa ba sai ya taso ya xo ya ganni. Bayan na amsa gaisuwarsa bana kara kallonsa balle na kara yi masa Magana, a gidana ko a office, da daddare ko da rana ya kara ci xamansa ya karaci xamansa ya kara ci satar kallona in yi kamar bansan yana yiba, daga karshe sai yayi min sallama ya tashi ya tafi idan ya dame ni da waya in amsa in ce masa “menene? ” sai yace ya kira ya gaishe ni ne.in ce “nagode”. In kashe wayata, idan ya fara turo sakon daya danganci soyayya sai na ja masa kunne cewar ya daina niba sa arsa ba.
Sai gashi rannan a gidana shi da wani amininsa mai suna mukaddam. Na san mukaddam sosai abokinsa ne tun suna sakadire suna shigowa gidana, tare ma suka yi jami ‘a shima lauya ne.bayan sungaishe ni sai mukaddam ya kai-kai –ce xai tsara ni cewar abokinsa ya shaida masa komai game da halin da muke ciki, wai in daure in kula shi ba hargetse na daga musu hankali gaba dayansu, na xage su tsaf na kore su daga gidana. Na ce da mukaddam ya fadawa abba kada ya sake nemana ko a waya balle a ido biyu, jikinsu na rawa suka tafi.
Abba yayi ta kuka ya dinga turo sakonnin bada hakuri kala-kala a waya, na ce duk halin da xai shiga ya shiga baxan cuci kaina ba na aikata abunda xai dame niba.
Wata rana da yamma ina cikin garin kaxaure ni da abokan aikina nurses muna bikin wata abokiyar aikin mu. Sai wata kawata da muke xaune tare tace “wayar ki na ringing tun daxu fa.”
Na yi sauri na bude jakata na dauko wayar sai naga 30 missed calls. Sai na ji gabana ya yanke ya fadi na fara dubawa sai naga missed calls din Abba 19 ne 6 kuma na mukaddam abokinsa, 5 kuma wata bakuwar lamba ce. Na fito gefe saboda kidan da ake yi a wajen da kuma hayaniya, ina kokarin kiran lambar da ban sani ba amma ban damu da in kira Abba ba balle mukaddam na san dai abu daya ne, shine su yi min magiyar soyayya ni kuma ba xan yi ba, kuma bana yi. Na kira number na ji number busy ana amfani da layin, ba’a jima ba sai naga lambar tana kara kirana na yi sauri na dauka sai na ji muryar wani inyamuri yana Magana cikin harshen turanci.
Ya ce dani “madina ce? ” na amsa cike da mamaki “eh, madina ce.” Ya ce “to gamu a kofar gidanki, kofarki a rufe.” Na tambaya cike da mamaki “waye kai? Lafiya? ” ya fada cike da damuwa “madam, ki yi sauri ki xo, emergency ne muna tare da marar lafiya ne yana neman taimakon gaggawa.” Na fada cikin mamaki marar lafiya a gidana kuma? Me xan yi masa ni da ba likita ba, kuma ko ni likita ce gidana ya kamata akawo shi ba asibiti ba?
Sai na ji mutumin ya hargitse yana Magana a fusace y ace “ina Magana ne akan mai gidanki daya yi hadari a hanyarsa ta xuwa onisha, gashi nan rai a hannun Allah be san ma a inda yake ba, jini ne ke xuba.”
Na ji gaba daya tunani naya hautsine na rasa me yake fada, kafin in ce wani abu ya kara da cewa “muna nan a kofar gidanki ki xo idan baki xo ba nan da mintina goma sha biyar xamu ajiye miki shi a kasa mu tafi da motar asibiti ce na roka aka kawo mu tun daga onisha dan kawai na ceci ransa ya na gama fada ya kashe waya.”
Kaltum ta dafe kirji t ace inna lillahi wa inna ilaihi ra ji’una, waye wannan marar lafiyar ko dan uwanki ne daga onaca? ”
Madina ta share hawaye t ace “xaki ji ko waye, ki ci gaba da saurarena. Mutumin na kashe wayarsa sai ga lambar mukaddam ta shigo na yi sauri na amsa jikina na rawa. Sai na ji y ace “sister madina wai me yake faruwa ne da Abba? Na ji ana ta kirana da lambar sa idan na dauka sai na ji muryar wasu inyamurai daga karshe ma naji wayar a kasha.”
Na ce “nima ban sani ba, amma ka je gidan su ka duba shi ka gani.”
Sai mukaddam yace “ai Abba baya gida tun da asuba na kaishi tasha yahau doguwar motar xuwa onisha.”
Sai na dora hannu a ka, n ace “inna lillahi wa inna ilaihi raji’una. Mukaddam me Abba xai yi a onisha? ”
Sai y ace “babu yadda ban yi ba kada ya je y ace sai ya je wajen ‘yan uwanki su bashi kwatancen inda xai samu yayanki innamani a enugu, yana ganin idan ya nemo miki yayanki uwa daya uba daya wanda shine kadai dan uwanki wanda rashin sanin inda yake yana damunki to yana ganin xaki dan tausaya masa ki aure shi ki tabbatar da gaske yake sonki da aure. Abba yace kada na fada wa kowa a gidansu baya so ki ji.”
Ai ko rufe bakinsa bai yi bana katse wayar na rusa ihu na yi bakin titi da gudu, saura kiris mota ta kade ni na tsayar da mai babur nahaye da sauri, kawayena da gudu suna kirana tuni mai babur ya figa da ni, ce masa nake kara gudu malam yi sauri bamu tsaya a ko ina ba sai kofar gidana, a inda na hango motar asibiti da marar lafiya a kwance abaya tamkar gawa sai wadansu maxa guda uku. Na karasa gare su ina karkarwa suka bude min bayan motar na leka dakyar na gane Abba daga kafarsa na shaida shi amma babu mai gane fuskarsa saboda ta yi kaca kaca da raunuka. Kunnensa ma an manne shi dan saura kiris ya fadi dan haka fuskar ta kunbure sumtum an nade da bandeji fari, bashi da riga se dan gajeren wando saboda dorin karayar da aka yi masa a hannun hagu da kafar dama kara bibbiyu sai kafadarsa wani katon rauni ne, an like shi da bandeji, sanna duka ilahirin jikinsa babu inda babu rauni jini jage jage, a jikin shinfidarsa farare gasu nan a gefansa a yayyage jawur da jinni tamkar an tsoma su a bokitin jinni a ka tsame su suna ta diga.
Na tsala ihu na gigice ina tambayarsu me ya faru das hi? Ya aka yi haka ta faru, yaya xan yi in kwaci kaina idan Abba ya mutu a dalilina?
Tambayarda na rirrike su nake yi kenan a gigice suka shiga lallashina suna shaida min babu lokacin batawa saboda marar lafiyan nan yana neman taimakon gaggawa a inda suke nuna min suna neman kudin su da suka karkashe wajen kaishi asibiti da xuba mai wajen kawo shi tun daga can har nan. Yayin da gabana ya fadi saboda na san bani da kudi, kudin da ke jakata bai wuce duu biyu ba saboda bikin nan duk na kashe kudaden kakaf.
Na tambayae su cikin kuka me yasa basu kaishi gidan suba suka kawo shinan? Sai suka ce min ai sanda yayi hatsarin yana Magana shine ya fadi sunanki yace matarsa ce, yana so mu kira ki kuma ke ce last call dinsa da muka gani a wayarsa, ke yake kokarin kira a sanda hadarin ya afku shi yasa muka kira ki, baki dauka ba daga nan muka ga wani lambar mukaddam shima mun kira baya jin mu har cajin wayarsa yakare ta mutu shine ya bamu adireshin ki yace idan muka xo kano mu nemi kaxaure mu shiga general hospital staff quarters mu tambayi madina. Sai kuka ya ci karfin madina ta katse labarin.
Nima na huta hannu, Allah sarki Abba, ko ya mutu ne, ya na nan da rai ban sani ba, se mu saurari ci gaban labari.
.
Wai mai yasa Madina baxa ta yarda da Abba ba tunda ba haramun bane dan ta aure sa ba?
Misali idan kece haka ta paru dake xaki yarda ki auri Abba tunda Kinga har yana neman rasa rayuwar sa akan ki?
Misali kuma idan Kaine duk yadda ka nuna mata kana tsananin son ta har kana neman rasa ranka xaka yarda Kaci gaba da son ta kuwa duk da bata son ka?
Tambaya gare ku mutanen gidan Al-Hada Hada maza da mata kowa muna son jin ra'ayin sa...
Akapta..
.
Typing Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA
TRUE LIFE STORY
LITTAFI NA BIYU (P 15)
NA JAMILA UMAR TANKO
GABATARWA SADIQ HALIMA (Sadin Maa)
DAGA Al-Hada Hada Hausa Book stories
.
Kaltum ma hawaye take inda ta dafe wuya tace “Allah sarki bai ce a kai shiwajen iyayen sa ba sai ke, gaskiya yana sonki. Amma dai kin tausaya masa da kika gan shi a cikin wannan hali? ”
Madina tayi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum t ace “na tausaya masa har na fara nadamar wulakancin da na yi masa a baya. Dan na tabbatar ba son wasa yake min ba. Allah sarki so, shi burinsa na karbi gawarsa ba iyayensa ba don in tabbatar a dalilina ya mutu kamar yadda ko da yaushe yake ce min idan ya mutu in sani a sanadiya ta ya mutu.
Na rasa yadda xanyi dasu sai na kira mukaddam ina rusa kuka ina fada masa halin dana ga Abba. Shima sai ya rushe da kuka yace min mu garxayo dashi asibitin malam aminu kano xamu iske shi a nan yana jiranmu, haka aka yi kuwa, na roke su dasu kaimu asibitin a kano na shiga gidan gaba su biyu suka shiga baya wajen Abba direba ya tuka muka tafi sai xura gudu muke yi kamar xamu kifa saboda su da suke xaune a kusa dashi suna shaida mana cewa yana kokarin cikawa yana bukatar oxygen.
Tsananin kukan da nake rusawa da irin addu’o’in da nake xubawa shi ya ja hankalinsu suka dinga lallashina suna tausaya min kamar yadda suke tausayawa Abba. Muka isa aminu kano, na kira mukaddam na shaida masa mun shigo asibiti sai ya kwatanta mana inda xamu same shi. Kafin mu karaso har ya tanadi likitoci da nurses da leburorin da xasu kula dashi, a tsatstsaye suke suna jiranmu, motar na tsayawa aka dauke shi aka dora shi a gado mai taya aka tura shi aka shiga dashi dakin tiyata.
Abunka da masu hali domin baban mukaddam ma wani hamshakin mai kudi ne ga mulki saboda yayi gwamnan kano a lokacin mulkin soja. Na shaida masa cewar wadanda suka kawo shi suna bukatar a biya su kudin da suka kahse, ya je ya same su suka yi mar lissafi ya dauko kudi masu yawa ya basu, suka shiga motarsu su ka tafi, sai ni sai mukaddam a bakin dakin tiyata, xullumi nake, addu’a muke yi kada ya mutu, idan ya mutu bamu san me xamu fadawa iyayensa ba.
Nayi ta kuka, tamkar raina xai fita ba mukaddam ba, hatta jama’ar da ke wucewa da ma’aikata saida suka taru suke bani hakuri suna kwatantani da marar tawakkali, basu san ba rashin tawakkali ba ne, rashin sanin bayanin da xan yiwa duniya da kaina ne dalilin da Abba ya je ya ragargaje a hanyar garinmu wajen nemo yaya na.
Mukaddam ya dauko waya yana kokarin kiran iyayen Abba xai shaida musu halin daya ke ciki sai na yi caraf na rike wayar na hana shi . tambayata yake me yasa baxa’a fada musu ba, halinda yake ciki ba?
Ai doloe su sani ko bai mutu ba balle yaga alama da wuya Abba ya tashi a yadda yaga numfashinsa yana sama yana kasa. Ni dai na hana shi kira kuma ban san dalili ba, har aka fito dashi daga dakin tiyata likitoci sun duba shi tsaf sun sake dora wasu karayar da ba a dora shi ba da sannan suka sake like ciwukan amma sun hango buguwa a kirjinsa, akwai kashin daya goce a hakarkarinsa sai gobe xa’ayi wannan aiki sannan xa suyi masa hoton kwakwalwa itama su duba ko ta tabu saboda raunin da yake kansa a haka suka kwantar da mu a amenity dakin mutum daya.
Mukaddam yabiya kudin daki mai tsada lafiyayya mai AC, fanka, firij da kujerun alfarma. Mukaddam ya fita ya sissiyo mana abinci da abin sha , shi ma be iya ci ba balle ni, balle kuma shi marar lafiyar wanda babu abunda yake yi sai suma an sakala masa roba a hanci ana xuko numfashi, sai Karin ruwan da ake yi masa leda leda.
Ina xaune a gabansa a kan kujera yayin da nake rike da hannunsa na gaji da kuka sai addu’a nake tofa masa Allah Ya tashi kafadarsa.
Yayinda mukaddam yake lungu yana ta sa addua’ar hankalinmu a tashe bamu Ankara ba sha biyun dare agogon dakin ya buga ya yin da daidai wannan lokaci wayata da wayar mukaddam tadau ruri. Ina duba tawa naga sunan sumayya tukur yayin da mukaddam na duba tasa lambar mami hafsa tukur ce, maman Abba . sai gaba dayan mu muka mike tsaye muka dafe kirji, muka xaxxare ido muka kalli juna. Na ce sumayya ce, yace, mami ce, sai na yi saurin na karbi wayarsa dan kar ya danna . suka yi ta ringing har suka katse yayin da na murtsika wayoyin na kashe gaba daya, duk na bi na rude, ban san me ya kamata na yi ba.
Mukaddam na kokarin nuna min bai dace na kashe wayoyin ba saisu xaci ba lafiya ba ko mun hada baki mun kashe shi musamman idan suka xo suka iske mu tare dashi a asibiti cikin wannan halin, sai na cakumi kwalar rigarsa na matse shi a jikin bango Magana nake yi cikin fushi da kururuwa ina kuka, nace kai ne duk munafukin da ka janyo mana, saboda me xa ka kaishi tasha yahau mota ya tafi garinmu baka sanar min ba, baka sanarwa iyayensa ba?
Dan haka baxa ka amsa wayarsu ba, in kuwa har Abba ya mutu ka sani gawa biyu xaka kwashe domin ni ma sai na kashe kaina.
Kaltum ta tambaya “kuma ke lokacin da gaske kike xaki kashe kan ki? Duk wanda ya kashe kansa dan wuta ne fa.”
Madina ta share hawaye ta yi dan murmushi tace “ba kashe kaina xan yi ba, bacin rai ne kawai da tsantsar jin haushin mukaddam.”
Kaltum t ace “yaya kuka kare? ” madina t ace “kinsan kasa kwacewa yayi daga shaker da na yi masa yana ta bani hakuri har saida Abba yayi Magana. Nan da nan muka dungumo da gudu wajen gadon da yake kwance muna kiran sunansa idonsa a rufe amma sunan madina ya ambata a hankali nan da nan na rike hannunsa na matso da bakina saitin kunnensa na ambaci sunansa nace “Abba, ka ganni bude idanunka ka ganni. “sai yayi ta kokarin bude idonsa amma ya kasa. Hawaye ne kawai yake tsiyayowa daga idanunsa.
Ya fara Magana cikin sanyin murya wacce take fita a hankali y ace madina, ki yafe min abubuwanda nayi miki sannan ki sani duk abunda ya same ni dominki bana nadamar son da nake miki. Burina da fatana ki yadda da gaskiyar son da nake yi miki don kina xaton yaudararki nake, ina so ki kasance akan gawata yayin da Allah Ya dauki raina tamkar yadda mace ta gari take yiwa mijinta addu’a bayan ya mutu nima ki yi min saboda na lissafa ki dan haka na ci burin na aureki Allah baisa kin fahimta ba.”
Na sulale na durkusa na dora hannuna duka biyu a ka ina rusa kuka gami da salati fadi nake Abba na amince xan aureka, ka tashi kar ka mutu ka bar ni. Ya na cikin magana sai jini ya ambulo daga baki da hancinsa, a guje na xura na kira likita. Ya na xuwa sai yace xa su yi masa wata allura kafin gobe a shigar dashi tiyata idan iyayensa sun xo. Dan mukaddam yace musu iyayensa ne xasu saka hannu, tun daga nan Abba bai sake farfadowa ba barci kawai yake bai san inda kansa yake ba.
Jikina ya dauki karkarwa har saida na bawa mukaddam tausayi ya jawo ni ya xaunar da ni akan kujera yayin daya durkusa a gabana yana xubar da hwaye yace, “sister madina, naga kin rikice kin damu da yawa, na san abunda kike tsoro kada iyayensa su xo su ji a dalilinki haka ta faru da shi kin manta da Allah ne Yake shedar bayinsa a nan duniya da gobe kiyama?
Kin manta iyayen Abba musulmai ne, dole su yadda da kaddara mai kyau da marar kyau?
In har bakya so su ji abunda ya faru na amince ba xan fada ba ki dauki jakarki ki fice daga asibitin nan, kafin gobe su xo su ganki.”
Na girgixa kai na ce “idan na gudu shine xa su fi xargina su ce da sanina hakan ta faru saboda dole sai ka fada musu a inda yayi hatsarin saboda ga motarsa nan daya fita da ita a hannunka bada ita yayi hatsarin ba kuma dole likitoci sun dauki statement din yan sanda da suka kawo shi cewar a hanyar onisha suka dauko shi. Don haka gudu ba nawa ba ne duk daran dadewa gaskiya xata fito. Mukaddam, a ganin ka yaya iyayen Abba xasu ji a ransu idan aka ce musu Abba ni yake so har ma dalilina xai rasa rana?
Me yasa ka bari Abba ya jefa kansa cikin wannan hali nima gashi nan ya jawo min? sai na rusa kuka.
Mukaddam ya gyara xama ya bani labarin yadda abun ya faru daga farko har karshe.
LABARIN ABBA.
Mukaddam yace “tun muna yara idan kika lura Abba na sonki, ba son soyayya ba, yana matuakr son ya xauna dake. Baya gajiya da sauraron labarinki haka baya gajiya da kallonki, baya gajiya da yabon kirkin ki ko a bayan idonkine. Haka kawai kike burge shi yadda ya ga kina da tsafta, kina kula da gidanki, yaranki da mai gidanki, yace baki da kwadayi dan bakya roko sai abunda aka baki ki ke karba, baya ga rikon addininki bakya wasa da sallah. Abba ya shaida min cewa ko ya girma xai yi aure sai ya duba mace me tsafta da ladabi irinki sannan xai aura.
Bayan mun girma ya shaida min yana matukar damuwa da irin wahalhalu da wulakancin da mijin ki da kishiyoyinki ke yi miki, hakan bai sa kin fice ba saboda biyayyar aure. Idan muna xaune muna hira, sai ki ji ya tambaye ni yace, “mukaddam, anya kuwa a xamanin nan xan samu mace kamr Madina? ”
sai n ace masa “rabo ne ai, kai dai kayi addu’a kawai. Abba yayi ‘yan mata da yawa amma tun kafin aje ko ina sai dangantakar ta kwabe saboda bata da hali irin na madina. Kinsan gidansu rayuwar turawa ake yi bai tashi ya ga mahaifiyar sa na yiwa mahaifinsa hidima ba komai sai kuku da masu aiki ke yi, ke kuma ya ga komai ke ki ke yiwa mijin ki hatta tsinke xaki mika sai kin taso da gudu kin durkusa har kasa sannan ki bashi haka idan ya kiraki da gudu xa ki bar abinda kike yi ki je ki durkusa. Ba ki da lokacin kowa sai kin salami mai gidanki ko kadan ba kya bata masa rai baki da kiwar aiki.
‘yan mata da dama sun so Abba sai sun fara sai ya daina yace baya son su, har Allah Ya kawo lokacin rabuwarku ki ka bashi tarihin rayuwarki, ki kayi matukar bashi tausayi musamman daya ji kince kin rasa inda xaki nufa baki da iyaye. Sai yace min yana tausayinki yana matukar son yaga ya tallafawa rayuwarki kin koma cikin farin ciki kamar kowace mace mai miji da iyaye.
Daga nan bai sake cewa komai ba sai da aka dade, sannan na lura yana cikin damuwa na, na yi juyin duniyar nan ya ki fada min abunda yake faruwa sai ranar da muka je kaxaure wajen ki kika kore mu nima ranar ya shaida min halinda yake ciki nayi ta bashi hakuri kafin mu rabu yayi min alkawari xai hakura dake amma sai ya kirani a tsakar dare yace ya kasa hakura dake gashi tunaninki ya hana shi barci. Muna ta addu’a amma abu sai karuwa yake yi.
Ya ce min ya fi so ya auri matar daya ke tausayinta dan ya riketa amana. Burinsa ya raya sunna kamar yadda Manxon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija a baxawara, ta grime shi, burinsa ya haifar miki da farin ciki, fatansa ya sami soyayyarki, ta iyayensa duk mai sauki ne yasan yadda xai bullo musu su amince kin ki sauraransa ma balle ki fahimce shi.
Sai shekaranjiya ya same ni yace ya tuno wata dubara, xai je garinku ba xai ce ya sanki ba amma xai tambayi inda yayanki innamani yake a enugu sai ya nemo miki shi su xo tare , yin hakan xai faranta miki rai. Na ce kada ya je, yace in kyale shi xai je ko da kuwa xai rasa ransa ne a hanya. Ashe ya fada da bakin mala’iku, haka ta same shi.”
Na juya na dubi Abba, na yi kuka na yi kuka, na ji dama a dawo da rayuwa baya da banyi masa abunda na yi masa ba. Mu dukka bamu runtsa ba har asuba, na yi alwala a bandakin cikin dakin nahau salloli ba adadi kafin assalatu, addu’a nake kada Allah Yasa Abba ya mutu.
Yayinda mukaddam ya tafi masallaci ashe ya dauki wayarsa, yana idar da salla sai ya kunna a inda ya hadu da sakonnin iyayensa da iyayen Abba. Hankalinsu a tashe suke tambayar ina suka shiga shi da Abba tun jiya?
Sai ya yanke shawarar ya kira mahaifiyarsa ya yi mata bayani ita kuma ta yiwa mahaifan Abba bayani. Tun da asuba, kafin gari yawaye xance ya xagaye dangi hankalin kowa ya tashi yayin da motoci na alfarma suka dinga tsayawa a gaban dakin da muke.
Muryar mukaddam na jiyo yan magiya yan bada hakuri game da dogayen bayanai cikin kuka da rawar murya a jikin wundon dakin, na meke da gudu na daga labulen wundon na leka, sai ga en gidan su Abba kakaf da danginsa da ‘yan uwan su mukaddam, yayinda baban mukaddam yaketa sharar masa mari ba adadi da kyar a ka rike shi. Aka sako mukaddam a gaba ya xo ya nuna musu daki, su ka dungumo suka nufo inda muke. Na takure a loko ina karkarwa ina kiran “laa haula wala kuwwata illa billah.”
Suna shigowa suka kalle ni a sheleke babu wanda ya amsa gaisuwata, yayinda suka nufi kan gado da sauri wajen Abba duk wanda ya leka Abba sai yayi baya ya dafe kai yana salati saboda Abba yayi kwatsa-kwatsa. Ina kuka na taso ina shirin in yi musu bayani sai kuwa sumayya tukur ta sharara min mari, sannan ta kira ni da suna karuwa, mahaifiyarsu mami hafsa ta kirani da suna maiya na cinye mata da, wai daman ashe nice na kama shi ya dinga ramewa sannan na yi asirin da sai da ya kai kansa onisha aka tsafe shi dan haka sai hukuma ce xata raba ni dasu.
Alhaji tukur kuwa allurer soja ceta tashi saboda motarsa ya je da sauti ya dauko bindiga yace sai ya harbe ni, abokinsa na rike shi yana fusgewa, sauran ‘yan uwa suka xagaye ni suna yi min cari aka, wai in ba mutuwar xuciya ba da kwadayi irin nawa yaya xa’ayi in tarki yin soyayya da dan yaron nan?
Wai ashe daman yaudarar mutane nake yi ina nunawa ni baiwar Allah ce, daman har yanxu da sauran tsafin da maita a jikina. Ba ni da bakin bayani saboda babu mai sauraro na.”
Sai madina ta rushe da kuka, Yayin da tausayinta yasa kaltum xubo da hawaye mai yawa, tagumi kawai ta yi ta kurawa madina ido , can ta nisa tace ‘gaskiya baki da ta cewa Allah kadai ne xai fitar da ke.”
Madina taci gaba, haka wasu mata biyu daga cikin dangin su Abba suka watso min takalmana da jakata sai gani a gaban tasi’u da yara na Abdul malik da Abdul hakim. Tasi’u yana ta Allah wadai da halina sai kara tunxura su yake yi yana cewa ai shi ya fi sanin wacece madina kuma yaya yake xaune da ni muguwa ce ni.
Alhaji tukur ya fara buga waya yana cewa ayi musu tanadin jirgi xuwa London yanxu yanxu nan xasu fita dashi kasar waje. Mami kuwa wani dan sanda ta bugawa waya tace ya xoya same ta a aminu kano xai kama mata wata mayya. Ban gudu ba kuma ban ji tsoro ba saboda babu kuma wani cin mutunci daya rage min yanxu a duniya wanda ba’a yi min ba, har na fi so ‘yan sandan su kamani su rufe idan Abba ya mutu ni ma a kashe ni na huta.
‘ya’yana da suka ji xa’a kamani sai suka sulalo suka ja hannuna wai sai na tashi mun fice daga asibitin, ni kuma naki tafiya na xauna a barandar dakin nace gara ma a kama ni a kashe ni xai fiye min, da kyar suka ja ni muka tafi,ina jin wasu daga cikinsu suna cewa ga mayyar can xata gudu sai na ji sumayya tace rabu da ita aimun san duk in da xata je yanxu ta lafiyarsa muke yi.
A bakin get din aminu kano ‘ya’yana suka ja burki suka tsaya, sai nima na tsaya a kusa dasu cikin kuka na fara yi musu bayani suma kukan suke yi. Abdul malik ya fada cikin fushi yace “mama ki ja mana abun gori a gari, kin cuce mu har karshen rayuwar mu.” Ya juya ya tafi a fusace, sai na kamo hannun karamin shima ya fusge yace “bana sonki ke ba uwata bace daga yau.” Sai na saki baki ina kallonsu suka tafi suka bar ni a tsaye. Tunda ‘ya’yan da na Haifa a cikin cikina suka fada min haka na san na xama abar gudu a duniya, na san bani da amfani ga duk wata halitta. Na tabbatar na xama abun gudu a duniya, abun mamaki sai na ji kukan da nake yi ya tsaya yayin da na fara murmushi ni kadai na ji ina fadin Alhamdulillah.”
Madina ta fashe da kuka mai tsanani.
Kaltum ta share hawaye ta tambayi cike da mamaki t ace, “me yasa kika ji kin daina kuka kina murmushi? ”
Madina ta dago da luhu-luhun idanuwanta ta dubi kaltum tace “masifa ce tayi masifa amma dukkan wani musulmi da yayi imani ya san Allah ne mai yaye duk wata masifa, na sallama duniya ne kwata-kwata sai na tuna xan mutu in je in tarar da Ubangijina wanda xai yi min sakayya sai naga duk wannan abun kamar ba’ayi ba, shine kawai na ji na daina kuka na yi ta murmushi. Menene dadin duniyar ne?
dadin duniya shine ‘ya’ya, dukiya sai mata, to duk na rasa su a duniya dan haka sai na yi tawakkali na cirewa raina rayuwar duniyar kwata-kwata ina sauraron ranar da Allah xai yanke min wato ranar da xan mutu.
Ina fita daga asibiti na hau acaba na tafi tahsar ‘yan kura, daga can nahau motar kaxaure. Ina isa gidana na xaxxabi ‘yan kayayyakina kadan na xuba a jaka na shiga tunanin inda xan je, bani da inda na sani wanda xan iya kaura. Daga karshe na yanke shawarar nima in tafi enugu in nemo yayana innamani in har yana raye in xauna tare dashi don shi kadai ya rage min. na shiga sake-saken ta inda xan fara nemo su sai nace a raina idan naje enugu na tambayi sunan kawuna exe wanda yake rike shi idan kuwa ya mutu nasan shima innamani watakila a san shi idan yayi kudi tunda yayi karatu, sai dai kash bani da kudin motar tafiya.
Sai na tashi na shiga gidan makwabciyata mai suna sha’atu itama ma nurse ce, baxawara kamar ni. Na iske tayi bakuwa daga Daura suna xaune suna hira. Ta na ganina tace, ina na je tun jiya ake ta nima na ba a ganki ba, kuma me ya same ki kika rame sannan idanuwan ki suka kumbure?
Se nace mata xaxxabi na yi da ciwo ido kuma na je kano tun jiya.
Nan dai muka xauna mu uku suna hirarsu ina sauraran su hankalina baya wajen su, ina tunanin halinda Abba yake ciki.can se mariya kawar shafa’atu ta dauko hirar xuwa makka ta mota xasu bi ta sudan wani satin. Sai kuwa nayi carafna tambaye ta na ce, nawa ne kudin?
Kuma ina ake biyan kudin?
Ta yi min bayani dalla dalla, sai na ji gara kawai in tafi kasar da ba’a sanni ba. Shafa’atu na yi min tsiya tana cewa wai me yasa na ke tambaya ni daba xuwa xan yi ba?
Na ce wallahi da ina da kudi da nima xuwa xan yi.”
Sai mariya ta dubi hannuna tace “yaya xaki ce baki da kudi kuma kina sanye da tafka-tafkan awarwarayen gwal har guda biyu a hannunki ga sarka da ‘yan kunne da xobuna ai ya ishe ki kudin motar har ma yayi saura.”
Sai a lokacin na tuna ashe ina da kadarar gwal, ai nan da nan jikina ya dau rawa nace “wallahi idan mariya xata tafi daura tare xamu tafi”
Mariya tace “ai ni a yanxu xan koma ba xan kwana ba.”
Shafa’atu sai ta fara tuntsirewa da dariya a xaton ta wasa nake yi. Ta ce ta yaya xan bar aikina, da mutunci na, da kuruciyata, ga yarana amma in tafi saudiyya yawon wanke-wanke da shara? ”
Ai sai suka ga na shiga gidana na dauko jakar kayana na rufo gidan na shigo na tsaya akansu na cewa mariya ta taso mu tafi daura, abu kamar wasa sha’atu taga na rikewa mariya hannu muna ta sauri mun bar ta a baya mun nufi bakin titi, ta gaji da bin mu ta juya gida. Tace min “in kin je ma xaki dawo nasan karya kike yi ba wata makka da xaki je.”
Ai kuwa har ya shafa’atu bata ga dawowata ba kuma nasan sun hadu da mariya ta fada mata cewar na tafi. Na bawa mariya sakon mukullin gidana ta bawa shafa’atu ta budeta dibi sauran kayana ta rabar sadaka, ta fada a wajen aikina na daina aiki, a cire ni daga cikin albashi.”
Kaltum tace daga kaxaure se ku tafi daura?
Madina ta yi murmushi tace daga kaxaure sai muka hau motar kano, nace ta xo ta raka ni bakin asibitin murtala in sayar da gawala gwalaina. Mu ka je na sayar kudi da yawa ko xobe daya ban rage ba, sai muka hau motar daura daga kano, muna shiga mota sai na ji wayata na ringing, na yi sauri na dauka, mukaddam ne, hankalina ya gama tashi, na dauka na fara salati ina kuka, dame kuma mukaddam ya ke kira na?
na yi sauri, na koma kira ya daga babu abunda nake jiyowa se koke koke da alama ba lafiya, ina fara tambayarsa lafiya, sai kudin wayata yakare, sai gashi ya kirani daga jin muryarsa kuka yake yi. Ni ma na fashe da kuka nace inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Mukadda lafiya, ina Abba?
Sai ya sake fashe wa da kuka yace “sister madina Abba ne ya………..”
Sai cajin wayata ta kare dif naji shiru wayar ta mutu. na rusa kuka ba kakkautawa har saida hankalin duk wanda yake cikin motar ya tashi, ana tambayata mutuwa aka yi ne?
nace “eh, kanina ne a asibiti kuma ana fada min halin da yake ciki wayar ta mutu, da alama dai ya mutu dan na jiyo koke koke.
A haka aka taimaka min da waya na kira na ji halin da ake ciki, amman bani da number kowa a kai, sannan kuma sunayen ba a sim card suke ba, sannan kuma babu wanda muke da waya iri daya dashi balle na ari batir. dole na hakura se kuka nake yi, ina tuna Abba se kawai addu’a nake masa Allah Ya jikansa da rahama. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai, haka Allah Ya rubuto mana, a haka yake so ya ganni.
Kaltum kinji dalilin xuwana sudan kenan. Wannan shine abunda ya rabo ni da yarana na shiga wannan hali.
Madina taci gaba da kuka marar adadi yayinda kaltum ta takure kanta acikin gwiwowinta ta xubawa madina ido tana kallonta. Xuciyarta ce take xugi da radadin kunci hade da damuwa, da alama mutuwar Abba ta sosa mata rai sosai. Hawayenta ne ke disowa daya bayan daya. Kaltum ta nisa tace “anty madina, amma sanda na ganki a mota da kuma sanda muka xo muka xauna daki daya sai nake gani kamar ke baki da matsala saboda sai in ga koda yaushe kina fara’a, dariya da walwala kullum kamar babu abinda yake damunki. Har nake mamakin yadda kika shiga cikin mu don naga babu alamar wahala a jkinki kwata-kwata.”
Madina tayi murmushi tace “wadatar xuci ce kawai, idan xaki tuna yadda Annabawa da Sahabbai suka yi rayuwa xaki san duniya da abunda ke cikinta gaba daya ba komai bane, ba kuma dauwamammiya bace. Shudewa take wataran tamkar ba’ayi ba. To idan na tuna haka imani yana wanxuwa a xuciyata nasan duk abunda yayi tsanani maganinsa Allah ina matukar farin ciki da Allah yayi ni musulma duk wahala da bakin ciki basa sa ni ni na manta da addinina, ko da ace gaba daya mutanen duniya xasu kini nasan mahaliccina Yana sona kuma Yana tare da ni. Ina jin dadin ni’imar da nake ganina a cikin ta, a mafarkaina, ina yawan mafarki da Shugaban halitta MANXON ALLAH (SAW) don haka na ci riba a rayuwata. me mutum xai yi min in damu kaina, fatana in tashi a cikin al’ummarsa ranar gobe kiyama.”
Kaltum taxare ido ta bude ida ta bude baki tana duban madina duba irin na sha’awar da ma nice ke.
Madina ta yi dariya t ace “kaltum, muddin kina tare da ni hakika xaki koyi yadda ake juyar da bakin ciki ya koma farin ciki. Lokacin sallar la’asar yayi muje mu yi salla.”
Sai suka kwashi shinfidarsu suka shiga cikin gida, domin bada faralli.
ALLAH YA KARA MANA IKHLASI AMEEN , EN UWA RAYUWAR DUNIYA BA KOMAI BACE, PATANA DA MU KARU DA DUK ABUNDA LITTAPIN YA KOYAR NA TAWAKKALI, DA IMANI AKAN KADDARA, KAHAIRI KO SHARRI. ALLAH YASA MU DACE.
AMEEN..
.
Nima Dan Aunty nace Aamiin thumma Aamiin Sadin Maa.
Allah Ya saka miki da alkhairi Ya biya miki dukkan bukatun ki na alkhairi damu baki daya.
Aamiin.
.
Typing : Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 2 (P 16)
.
TRUE LIFE STORY
.
BABI NA BAKWAI
Xaman su kaltum a bur suda yadore babu alamar karshensa don babu wani labarin tafiya Saudiya ko komawa Nigeria don haka sai kowaccensu ta cire ranta da tunanin komawa gida. Duk sanda garin Allah Yawaye mata da maxa yara da manyan su saisu fifito neman abunda xa su kai bakin salati, basu cika son su tafi a kungiyance ba saboda rigima ake yi da xarar an miko sadaka sai ka ga ana rigaye rigayen karba har ya kaisu da kaurewa da kokawa kamar wasu dabbobi. Don haka madina take kama hanyarta ta tafi bararta ko aikatau ita kadai yayin da take cewa kaltum ta shiga cikin yara su tafi saboda gudun ‘yan iskan da suke yawan binta.
Wata rana a wajen bara fada ya hautsine tsakanin kaltum da amina, abunda ya hada fadan kuwa shine an miko musu sadakar dabino guda hudu kaltum ce kusa sai ta sa hannu ta karbo tana shirin miko musu sai amina ta warto daga hannunta.
Ta ce mata “mayya, kawo nan an miko min kika yi sauri ki ka karba. Sai kaltum ta yi shiru ta bata dabino ta koma gafe suka ci gaba da tafiya, sai suka xo wucewa ta kofar wani gida a garin ADON DAWA sai suka ga wasu samari guda biyu, samarin suka fada cikin harshen larabci “ku xo ku karbi sadaka.”
Kaltum na dago ido sai taga abokan mambela ne don haka sai tayi saurin matsawa daga wajen sauran ne suka je da sauri suka mika hannu, sai samarin suka ce basu xasu bawa ba su je su kirawo waccan da ta matsa gefe ta xo ta karbar musu kudin wato kaltum suke nufi. Suka dungumo wajen kaltum suka yi mata bayani sai tace “ku xo mu tafi ba baku sadakar suke son yi ba ‘yan iska ne.”
Sai amina ta harari kaltum ta yi gatsine t ace “wai ke dalla kaltum din nan me ki ke ji das hi don kinga kin fi kowa kyau samari na sonki shine kike yiwa mutane wulakanci. Haka rannan a kasuwa wani saurayi ya fito da kudi yawa xai baki kika ki karba. Na san kuma daga baya xaki dawo ki karba bakin ciki ne kawai da wayon banxa.
Kaltum na gaba tafiya kawai take yi yayin da xuciyarta ke tafarfasa tana kuna saboda bakaken maganganun da ta saka ta a gaba tana fada mata harda xagin iyayenta. Kaltum ta tuno da hudubar da madina ta yi mata in da take ce mata “ki kwaci ‘yancinki danke ma ‘ya ce ba baiwa ba.” Ta sake tuno maganr matar da ta bata wuka in da take ce mata “ki fara kashe duk wanda yake da niyyar kashe ki, ki yanki duk wanda yake da niyyar cutar ki.”
Wani xaxxafan hawaye ya sirnano mata yayin data dunkule hannunta cikin fushi ta jiyo sai kake jin ‘dum’ duka ta kai bakin amina kan ka ce kwabo jini yayi faca-faca a rubabben bakinta da baya samun makilin. Amina ta durkushe kasa ta rike baki tana kururuwar kuka saboda tsananin xugi.
Gaba daya sauran suka yi caa akan kaltum suna xaginta, sai ta gada hannu ta dakatar dasu.
Tace “kada wacce ta sake ta fada min bakar magana, ko ta xageni balle ta dake ni, kada ku dauke ni wawuya, marar wayo wacce bata san ciwon kanta ba . kada ku dauka bana jin xafin kyara da cin mutuncin da kuke yi min ada. Na gaji, hakurina ya fara karewa xan taba duk wanda ya taba ni.”
Ta rushe da kuka ta ci gaba da Magana cikin kakkausar murya tace “ku hantare ni, ku xage ni, ku dungure min kai, ku aike ni duk bana kuskure muku kawai don a xauna lafiya, bana son in bata muku rai badan ina tsoranku ba, amma kuma nice na xama abar wulakantwa a wajenku. To ku sani daga yau na daina saurarawa duk wanda baya sarara min, wannan abunda na yiwa amina somin tabi ne kuma xai xama darasi ga dukkanninku.”
Tana rufe bakin ta sai amina tayi kukan kura ta daka tsalle akan kaltum kan ka ce tak sai ga amina a kasa, kaltum ta murde ta, ta nika ta a kasa ta hau ruwan cikinta tana duka.
Su rakiya suka xo suka banbare kaltum daga kan amina da kyar. Kaltum na tashi sai ta bibbige hannayen masu riketa kowacce ta daka tsalle ta koma gefe tayi cirko-cirko tana tsoro kada dukan ya shafe ta. Hakika sun yi matukar mamakin ganin yadda take da karfi haka. Ta juya ta tafi a fusace ta bar su a tsaye suna kallonta.
Tun daga ranar nan babu wacce take marmarin sake takalar kaltum da fada, babu wacce take mata gatsalu, ko tsawa balle xagi da dunguri. Madina ma ta lura da haka taga yadda suke rawar kafa suke nan-nan da kaltum, shishshigi iri-iri kowacce na son shiga harkarta musamman amina. Tunda kaltum bata fada mata komai ba shi yasa tayi shiru bata tambaye taba amma tabbas tasan akwai abunda ya faru aka sami canjin nan.
Kaltum ta samu salama a cikin gida sai ta ji da wadanda suke takura mata a waje, bayan mambela da abokansa ta hadu da wasu batattun samarin jange. Don haka kaltum tayi shiri sosai wajen kare kanta har wata jaka ta samu tana ratayawa cike da makamai.
Da yamma likis kaltum da haule ne suke yawon bara a garin jange sun yiini yau basu samu ba, tunda rana suka rabu da sauran abokan tafiyarsu a jim arab, da suka ga sun yi yawa sai suka raba kansu wasu suka shiga garin ‘yan ADON DAWA wasu suka tafi jim arab, wasu suka tafi hajarar ases, su kaltum kuma suka tafi wajen jange.
Arashin sani su kaltum suka shiga wani lungu, ashe lungun baya bullewa sai suka juya da sauri, xa su fito, suna juyowa sai suka ga samari biyu sun tare su a cikin lungun ko basu ce musu komai ba sun fahimci abunda suke shirin yi musu. Su ka takure a lungu suka makale juna suna ta kururuwa yayin da samarin suka nufo su a hankali suna Magana cikin yarensu.
Kaltum tayi larabci tace “bama jin yarenku, kuyi mana larabci.”
Sai suka fara Magana cikin harshen da xa su fahimta suka ce musu “kun shigo da kanku lungun da baya bullewa, kun yi kuskuren shigowa gidanmu domin babu budurwar da xata shigo nan ta fita lafiya ko ‘yar garin nan ce balle ku baki marasa gata.”
Kaltum ta fada cikin bacin rai “mu baki ne ba mu san ba’a biyo tanan ba, bara muke muna neman abunda xamu ci.”
Sai suka ce “to yanxu xamu baku abunda xaku ci amma fa sai mun gama da ku.”
Yayinda da daya ya wawuri hannun huwaila kaltum kuma daya ya cafko gashin kanta ya damke yace da ita.
“tun farkon xuwanku na ganki naga kin min, baki da labarin na dade ina binki a baya?
Yau ne na ci sa’a na hadu dake a wajen da babu hayaniya babu yadda xa’a yin a barki.”
A cikinku ki tambaya mata nawa ne suke bayar da jikinsu a basu kudi tsofaffi ma balle ku yara masu kyau irinku. Me xai ragu a jikinku idan an taba ki, ki samu kudinki hankalinki kwance. Sai kaltum ta hasala ta hau fuffuka tana fisge-fisge xata kawace, ya bankare wuyanta yana kokarin kai ta kasa, yayinda dayan tuni ya durkusar da huwaila kasa.
Kaltum ta laluba ta ciro wukarta daga cikin rigarta kan kace kwabo ta danna gefen wukar kaifin ya fito fet ka ke ji ta sharba masa a hannu ba shiri ya ske ta ya daka tsalle gefe ya rike hannu yana ihu jini yayi masa face-face a hannu. Kaltum ta sake bude jakar dake makale a hannunta ta xaro wata katuwar kwalbar lemo ta rusa a jikin bango ta fashe rabi ya rugurguje sai ta rike rabin a hannunta ta nufi dayan da yake rike da huwaila, shima a guje ya sake ta suka xabura suka fara ja da baya.
Kaltum ta fada cikin kakkausar murya tace ‘xan kashe duk wanda ya tabo mu, sai na farka cikin duk wanda ya nufo ni.”
Tana xare ido tana nufo su, sai suka tabbatar da gaske take farka cikinsu xata yi dan haka sai suka juya a guje suka fita daga lungun. Kaltum da huwaila suka arta da gudu suka kama gabansu suma. Mamaki ya kama huwaila akan abunda kaltum tayi tana matukar mamakin yadda kaltum ta tanadi irin wadannan mugayen makamai a jikinta. Huwaila taje ta dinga yada kaltum a cikin gida cewar a yi hankali da yin fada da kaltum domin cewar wukake ne da kwalabe a jikinta da xarar fada ya hada ta da mutum xata farka shi da wuka.
Su ka tabbatar kaltum ta xama ‘yar daba yayin da ‘yan gari ma suke kiranta da ‘yar agulla, wato ‘yar daba saboda har ‘yan iskan gari sun gane ta. Ta ketawa samari da dama hannu ta fasa wa jama’a da dama kwalba akai sai dai idan ba’a rutsa taba a lungu ana kokarin a cimmata ba yanxu ne xata yaga fatar mutum.