Complete Hausa Novels

Adon Dawa Complete Hausa Novel

Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 10

BABI NA GOMA
RAYUWAR KALTUM A KHARTUM

Kwanakin kaltum uku a khartum a lokacin ta ji rayuwa ta fara tsananta a gareta saboda tsananin wulakanci, dabakin halin da kalah da ‘yarta lami suke nuna mata . kalah ma sana’ar sayar da kosai take yi irin na madina. Kaltum taxage tana taya su aiki, itace mai wankin wake, itace ixa wuta da wanke wanke ashe ba’a son ransu take yi musu wannan hidimar ba, suna ciyar da ita ne kawai amma ba’a son ransu ba.

Suna wajen sayar da kosai da safe sai kalah ta dubi kaltum ta tsuke fuska t ace “kaltum ina fatan dai kin san yadda rayuwar sudan take, kowa ta kansa yake kin ma fi kowa sani tunda an ce bara ku ke yi a bur sudan. Dan haka ka’idar ciyar da bako kwanaki uku ne kin cika kwanaki uku yau, don haka ki fita ki nemi naki tunda har yanxu iyayenki basu bugo waya ba balle su turo da kudin jirgi.”
Hankalin kaltum ya tashi ta rasa abinda yake damunta, ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa babu inda ta sani , bata san inda xata fara neman kudi ba don haka sai ta fara kuka ta fada cikin tashin hankali.
Ta ce “kalah, ina xan je in nemo abinci bayan ni bakuwa ce?
Ki taimaka min ki kira iyaye na a waya su turo da kudin jirgi ko mota sai in tafi………”

Kalah ta katse ta tun kafin ta rufe baki. Kin bani kudi ne da xaki ce in kira su a wayata, su baxa su kira niba sai ni, ashe ni na damu suga ‘yar su. Baxan kira ba in daisu ba xasu kira niba.
Lami ta jakunnen kaltum da karfi tace “ki bude kunnuwanki ki ji, ki sani anan khartum ba’a bara ba kamar a bur sudan ba, idan ki ka yi bara a nan kama ki xa’ayi a kai ki dajin mujawara a yarda ke, ke ba a nigeri ba ke ba a sudan ba har sai wahala ta kashe ki.”
Kaltum ta fashe da kuka ta juya ta koma gida ta shiga daki ta xauna akan buhun kayanta, tayi tagumi tayi kuka har kamar idanuwanta xasu fice. Ta yi takaici akan rabo tada aka yi da bur sudan aka kawo ta nan inda bata san kowa ba, babu mai taimakonta. Haka ta yini da yunwa ba abincin safe babu na rana saida daddare tana kallon kalah da ‘yarta suka dafa abincinsu suka juya mata baya suka ci saida suka rage saura suka bata ta ci ta sude kwano sannan ta iya samun dan barci.

Gari na wayewa bayan kaltum ta yi sallah sai ta shiga wankewa kalah wake, a fusace lami ta xo ta fuxge kwaryar da waken yake ciki ta sake maimaita mata cewar ba xasu iya ci gaba da ciyar da ita ba ta je ta nemi sana’arta. Kaltum ta koma gefe ta tsuguna tana kuka tana ganinsu suka dauki kayan suyar kosansu suka tafi wajen sayarwa.

Hantsi yayi cikinta kuwa ya dau rurin yunwa tana tunanin in da xata nufa gashi bata san kowa ba a garin sai taji an dafa kafadarta ta baya tana dagowa sai taga wata matashiyar budurwa ‘yar kusa da dakinsu ce mai suna fatsima.

Ta ce da kaltum”lafiya kike xaune kina kuka ke kadai? ”
Sai kaltum ta fara share hawaye tana murmushin karfin hali tayi sauri ta gyara xancen ta ce wai ciwon kai ne yake damun ta. Fatsima ta girgixa kai tace “babu wani ciwon kai da yake damunki mun san komai tun sanda kika xo muke tausaya miki saboda mun san xaki hadu da wulakanci a wajen kala da ‘yar ta saboda basu da kirki kowa ya san bakin halinsu ko kadan basu da mutunci gasu da rowa. Ki tashi muje kiyi irin sana’ar da muke yi.”

Kaltum ta mike jikinta a sanyaye xuciyarta cike da fargaba saboda bata san sana’ar da suke yi ba, haramtacciya ce ko halattaciya. Tafiya suke yi xugwi xugwi babu wanda yake Magana a cikinsu har suka isa bakin wata katuwar kasuwa wacce ake kira da suna makadi. Kasuwar markadi itace kasuwar da ake sauke danyan kaya mota mota irin su tattasai, tumatur, atarugu, dankali, salad, kabeji da dai sauransu. Sai suka tafi wajen wata katuwar bola in da ake jibge lalatattun kwanduna da gwalagwajin kayan miya ma’ana rubabbun kayan miyar da aka tsince aka xubar.
Sai taga fatsima ta samo Kwando ta tsugunna ta fara tsintar masu dan kyau tana Tarawa a cikin kwandon.
Kaltum ta tambaya cike da mamaki “me xa muyi dashi? ”
Fatsima tace “ke dai kawai ki samo Kwando ki xo ki fara tsintar masu kyau kina Tarawa.”
Kaltum ta aiwatar da abunda fatsima ta umurce ta su yi, suka tottona sosai da hannunsu ga wari bolar tana yi harda suka tabbatar sun tara da yawa sannan fatsima ta nuna mata fanfo suka je suka wanke tsaf, suka wanke kwandunan ma sannan tace su dauka aka su tafi kasuwar adare karamar kasuwa ce. Suna isa adare kuwa Allah Ya kawo wasu mata suka saya na kowannensu hamsin jine, ya isa su ci abincin yau ko babu nama. Farin ciki ya kama kaltum ta dinga yiwa fatsima godiya da ta nuna mata hanyar cin abinci badan ita ba, da batan san yadda xa ta yi ba.
Haka fatsima da kaltum suke yi kullum gari na wayewa saisu nufi markadi a gabansu ake sauke kwandunan danyan kaya daga mota. Suna tsaye ake ware rubabbun yayin da suma suke ware masu saukin rubar suna tarawa har sai sun tsince masu dan kyaun wani lokaci har su sami masu kyau sosai saisu wanke tas su je su sayar a adare.
Xuwan kaltum sai ya xamowa fatsima alkhairi domin a yanxu tafi da samun kudi, mai makon su siyar hamsin jine har metan jine suke yi saisu hada kudin su je su sayo danyen kaya su xo su dafa abinci lafiyayya harda kifi ko nama su ci su koshi idan da canji su kora da lemun kwalba.
Kawance ya kullu tsakanin kaltum da fatsima yayin da haushi da hassada ta kama kalah da ‘yar ta har suka daina yi mata Magana don bahaka suka soba, sun so kaltum ta rasa yadda xata yi tayi ta bin su, suna yi mata wulakanci. Ta kai ta kawo ko gaishe su kaltum tayi basa amsawa idan a taba kayansu ko buta ce sai su kwace su kyareta.
Xuwan kaltum khartum da sati uku da magaruba bayan ta idar da salla a daki sai taji muryar kalah da lami suna yiwa mutanen gidan sallama a daki daki da alama bulaguro xasu yi, nan da nan kaltum ta fito daga daki sai ta gansu niki niki da kayansu aka da alama dai kaura xasu yi. Hankalinta ya tashi ta fito a gigice ta tsaya tana kallonsu tana sauraron abinda xasu ce mata. Amma sai taga ko kallonta basu yi ba sun kada kai xasu fice, sai ta fashe da kuka ta bi su har kofar gida.
Ta ce kalah ina xaku je ku bar ni, ni kadai ban san kowa ba a nan sai ku?
Kala ta tabe baki sannan ta kai mata duka kaltum tayi sauri ta kauce.
Ta ce “ina ruwana ki mutu mana iyayenki ne suka ce a kawo ki khartu, ga khartum nan kiyi xama. Goyonki xanyi ko kuwa nono xan baki? ”
Kaltum ta fada cikin kuka “dan Allah ki kira su awaya, kice gani na xo su aiko da kudin mota in tafi, ko ki bani number su. Idan kika tafi basu san numer kowa ba sai taki ita kadai ce suke tunani xasu same ni.”
Kalah tace “ba xan bayar da lambar ba, idan kina da karfi ki xo ki kwata.”
Ta ja hannun ‘yarta lami suka yi tafiyar su, lami tana ta xagin kaltum.
Kaltum ta rushe da kuka ta shiga tsakar gida tana rusawa, kukan kaltum ya sa kowacce ta fito a gigice suka hau tambayarta me yake faruwa?
Tana kuka tana Magana t ace “kalah ceta tafi ta bar ni alhali ban san kowa ba a nan sai a bur sudan ni kuma bani da kudin da xan koma bur sudan wajen wadanda na saba.”
Gaje ta yi salati ta salance t ace “af ke ce kaltum wacce iyayenki suka aiko da kudin jirgin ki suka ce a saka ki a jirgi ki tafi Nigeria? ”
Kaltum tace “kaltum t ace “kala tace basu turo kudin jirgin ba ammam dai sun ce mata xasu turo.”
Gaje tace a’a sun turo mata kudin jirgin kasa na xuwanta da dawowarku daga bur sudan sannan suka turo mata kudin jirginki har xuwa kano. Sannan itama kalah suka bata kudi mai yawa ladan dauko ki. A gabana dan aiken ya bata kudin da hotanki, sai dai in duka kudaden ta hada xata haye don yanxu haka makka xasu tafi fitar nan da suka yi ta barauniyar hanya ake shiga kwale kwale cikin dare sai a tsallaka ruwa a shiga jidda.”
Sai jama’ar wajen suka fara Allah wadai da cin amanar da kalah tayi, suna tausayawa kaltum

Kaltum ta rushe da kuka yayin da ta tsugunna tana ihu ta rasa yadda xa tayi da ranta gashi bata da lambar wayar iyayenta balle su san kudin da suka turo bai isa gareta ba balle su turo mata wani. Ita ba a bur sudan ba, ita ba a Nigeria ba, gata a khartum bata san kowa ba kuma bata da komai……..

Nan xa mu tsaya, se mun sake haduwa a ADON DAWA NA 3

Shin yaya rayuwar kaltum xata kasance a Khartoum?
Shin wane hali iyayen kaltum xasu shiga idan suka rasa kalah a waya kuma basu ga kaltum ba, alhalin sun turo mata da isasshen kudin jirgi?
Shin wane hali mambela xai kasance daya sami labarin tafiyar kaltum alahli yana tsananin sonta, xai kori bakin gidan su madina ko xai hakura ya kyale su?
Shin yaya rayuwar madina xata kasance, a bur sudan xata dauwama ne har karshen rayuwarta, ko kuwa xata samu ta haura makka, ko dai xata canja shawara ta dawo Nigeria wajen yaranta kamar yadda ta ji bata jin dadin xuciyarta saboda tafiyar kaltum?
Shin yaya rayuwar kalah da ‘yar ta xasu kasance a makka, xasu samu su haura ko a'a?

Duk amsoshin tambayar nan suna nan tafe a ADON DAWA 3.
.
Sadin Maa.ADON DAWA 21
.
LITTAFI NA UKU
.
Jama ar gida suka tashi kaltum tsaye da kyar daga durkuson datayi tana kuka takaraji bata kaunar taci gaba da rayuwa gara ace bata raye zaifiye mata alkhairi .tafi kaunar takoma bur sudan wejan madina da mambela akan takoma nigeriya wajen iyayenta taje ta kwanta akan figeggiyar tabarmarta kukan ma yadaina fita sai ajiyar zuciya takeyi saboda tsananin tafarfasar da zuciyanta takeyi, tsanani yayi tsanani yayinda damuwa tarufi tsananin yunwa da takeji idan kanta yajuya saitaji hankalinta yagushe tamkar ba a duniya takeba

fiye da awowi uku tana kwance cikin halin tunani me kunshe da bakin ciki Saiji tayi ana zuba mata ruwa tafarka firgigit saita ga dandazon mata a tsaye akanta wasu nazuba mata ruwa yayinda wasu na yimata fifita dukda fankar da yake kadawa a saman silin,
mamaki yarufe kaltum ta dinga bin daya bayan daya tana fadi aranta lafiya kuwa meyake faruwa?
Sannu kaltum yaya jiki?
Allah ya sauwake kalamanda suke fitowa daga bakin ko waccensu .magajiya matarda tabarmar kaltum ke kusa da tata itace tadaga kaltum tsaye ta dowo da ita tabarmarta saboda na kaltum ya jike da ruwanda aka yayayyafa
ta kwantar da ita ta lullubeta da zani ita dai kaltum mamaki ne ya ke addabarta yayin da kwakwalwanta ta dinga kokarin tunano mata abunda yafaru takasa tunawa abinda zata iya tunawa shine lokacin da kala da lami suka tafi akace makkah zasu tafi sun kunshe kudin da iyayenta suka turo mata sun tafiya dasu .
sai hawaye yaci gaba da surnano mata daga idanuwanta aka fita da tabarma kultum aka tsane ruwan a waje,sannan kowaccensu ta juya ta nufi dakinta ,suna masu yiwa kaltum patan samun sauki .
Magajiya ta tura kofarsu tarufe,ta kashe fitila ta kuntsa ta tsakiyarsu hajiya zaliha ta kwanta duk en dakinne ,tabar wa kaltum tabarmanta .kafin kiftawar ido da BismiLlah gurnanin munshari yafara tashi a dakin nawanan nadukan na wancen ,hade da kyawawan mafarkai,
domin burin ko waccensu ta ganta haye makkah ta hada daurin gumama akanta tana talla tana kuma aikawa nageria ana
rabawa danginta suna tsalle suna murna ,suna cewa hajia wance tayi kudi a makkah.
yawanci da abunda ka kwanta a ranka shi kake mafarki ,don haka yawancinsu mafarkinda suka sunduma kenan .

ita kuwa kaltum a bangarenta bahaka bane da zarar ta ritse ido saitaga madina a idonta ,da ta bude saitaga kamar mambelane agabanta ,sai hawaye metarin yawa ya surnano daga idanuwanta,tayi doguwar ajiyan zuciya tana shesshekar kuka .
kaltum mehaka ?
Wata murya taji daga gefinta ,saita zabura ta waiga a tsorace .magajiya tagani a zaune duk da duhunda yake dakin
wannan amsa tagagari bakin kaltum.
magaji ta sake tambaya. "me yake damunki kike qoqarin kashe kanki?
Ke ba musulma ba ce?
Ba ki san kaddara ba, baki yarda da kaddara mai dadi da mara dadi ba daga ubangiji?
Idan an rabo ki da bur sudan ba a kai ki nigeria ba aka kawo ki khartum, ba sai ki hakura ki zauna ba har kiga yarda Allah zai yi dake ba. tunda Shi ya tsara miki haka, ya fi ki sanin dalilin yin hakan. mu
dakike zaune da mu ba mutane bane, kuraye ne,cinye ki zamu yi?
ki yi hakuri, ki fauwalawa Allah lamuranki, ki kai karan duk wanda ya zalunce ki gurinSa, shi zai yi miki sakayya. Allah ba ya zalunci, ba ya tare da mai zalunci, kuma yana bayan duk wanda aka zalunta. ki tashi kiyi alwala,kiyi sallar isha'i don bakiyi sallah ba ,kiyi nafilfili ki fadawa Allah halinda kike ciki ,don Yafiki sani.kikai karar kalah da yar ta wajen Sa,Yagaugauta yimiki sakayyar cutarki da sukayi ,domin addu'ar wanda aka zalunta karbabbabiyace.
Allah na gaugauta karbar addu'ar wanda aka zalunta,sannan ki koma gefe ki zubawa sarautar Allah ido ,kiga yadda zaiyi dasu nan gaba,

kaltum tayi shiru tana sauraron magajiya tana gaskata abunda take fadi saidai kash kaltum batada kwarin da zata iya tashi tayi sallar farillah ma,balle nafila,saboda tsananin yunwa datake addabarta .

magajiya ce ta sake magana tana umurtar kaltum data tashi tayi sallah .dole ce tasa kaltum yunkura ta tashi zaune ,saidataji dif.bata gani jiri .ta dade a zaune sannan ta dafa kasa ,game da cije baki tayunkura zata mike tsaye sai tayi taga taga zata fadi,saita koma jabar ta zauna .

magajiya tambayeta cike da kulawa kaltum,anya kuwa ba yunwa bace take damunki ?
Kaltum ta kada kai cikin jin nauyi tace yunwa nakeji aunty
Magajiya tace , Allah tsarki ,yarinya me kawaici badan jiri ya daukeki bazaki fada min ba kenan?
To tashi a hankali ki rarrafa ga tukunyanta can a bakin kofa bude da sauran shinkafa kici
farin ciki ya lullubeta zuciyar kaltum ta mike a hankali ta karasa bakin kofa ta laluba ta bude tunkunya ba ta yi wata wata bata tsundum hannu a cikin tukunyar,kasancewar shinkafar ba ta da yawa, ta fara kaiwa cikinta hakkinsa yayin da 'yayan hanjinta suka dauki ruri da kokawa,ni ban samu ba ni ban samu ba.
kowacce cuta da maganinta, cikin yan mintina ciwon jirin da ya ke damun kaltum ya ware,ta sami karfi mikewa tsaye ta bude kofa tafita bandaki .ruwa ya wadata a bandaki don haka ta bude famfo ta sharuwa ta koshi,ta dauro alwala tafito.atsaye ta kwana harsaida aka kira assalatu tana nafilfili tana mika kukanta zuwa ga mahaliccinta,tana me neman agaji da neman mafita akan mawuyacin halinda take ciki .tana mai neman Allah ya saka mata bisa cutarda kalah tayi mata ita abumda yafi damunta da aka rabota da wajen su Madina .

misalin karfe bakwai na safe fatsuma ce tashigo dakin su kaltum ta isketa ta a kudun dune akan tabarma ,bacci mai dadi ya kamata hade da maparkin abun kaunarta mambela, kasancewar kwanan da ta yi a tsaye tana sallah.

kaltum kaltum tashi mutafi " fatsuma take fada yayinda take girgiza kaltum ,ta firgigit ta tashi zaune ta murtsike ido.

fatsuma ta dube ta cike da mamaki ,sannan ta tambaya.haryanzu barci ki keyi , ko jikinne?
Kaltum ta girgiza kai,lafiyata kalau ai "ta mike game da tawo wata cukurkudaddiyar lafayarta ta lauye jikinta suka dunguma suka fita ,yayinda yan gida kakaf sun dunguma wajen neman abinci.tafiya suke zugui zugui fatsuma ce mai dan tabo hira,amma ta lura hankalin kaltum ba a wajenta yakeba .ta dubi kaltum tace ,kaltum wacece madina ?
Wanene mambela?

Nanda nan taji gabanta ya fadi ,yayinda ta waiwayo da sauri ta tsura wa fatsuma ido tana mamakin yadda fatsuma tayi mata wannan tambaya.

A ina tasan madina?
A ina taji sunan mambela?

fatsuma ta sake maimaitawa, tace, 'kin yi shiru baki bani amsaba'

kaltum ta tambaya, 'a ina ki kasan madina mambela?'

fatima tace, 'mimmikewa ki kayi kika kakkafe kina ta kiran sunan mambela da madina' sai kaltum ta fashe da kuka, ba tare da tasan amsar da zata bawa fatima ta tabbatar larurar aljanun nan ce ba su bar ta ba. Ta tuna irin hidima da kokarin da mambela yayi mata wajen nemo mata maganin aljanu, gashi yanzu bacin rai ya dawo da aljanun, ga mambela ba ya kusa kuma.
Ta rushe da kuka, ta yi ta rusawa suna tafe a hanya ana kallonsu.
Fatima ce ta dafa ta tana lallashinta tana ba ta hakuri, har suka karasa bakin bolar da suke tsintar kayan miya suka samo kwando suka tsugunna suna ta tsintar kayan miya masu rangwamen ruba, amma hawaye ne ya ke kwaranya shaf-shaf daga idanuwan kaltum.

Fatima ta dube ta, sai ta girgiza kai, saboda tausayin kaltum da ta ke ji, don a halin yanzu tafi tausayin kaltum fiye da karin kanta. Tabbas fatima abar tausayi ce,
saboda itama da kanwar mahaifiyarta sukazo da zummar zasu sallake makkah akazubesu anan.kanwar mahaifiyarta tace kowa yayi ta kansa ko lomar tuwo bata hadasu,kowa nasa yake nema.to amma ita fatsuma ta saba da khartum tana jin dadin rayuwarta tamkar a presidential bila take ,musamman ranarda taci sa'ar bolannan ta cika da rubabbun kayan miya tasamu ta cika kwandonta da kayan miya taje ta sayar ta sayo shinkafa ko taliya da kifi ,ko nama taje ta gida ta dafa tahado da lemon kwalba mai sanyi ,tabbas wannan ranar ta fiye mata ranar sallah.sabanin kaltum wacce ta tsinti kanta a Khartoum tamkar wacce akayi mata dabaibayi cikin rami ,
batajin dadin rayuwanta tarasa me yake yi mata dadi musamman daga jiya abinda kalah tamata .
idan kaltum ta tona bola ta tsinci kayan miya ,saita kifa kai a gwiwarta tayi kuka harta gaji,sannan ta cigaba da tsinta ta tuno cewar inbata tsinta ba babu ita babu cin abincin yau.
duk da haka bata tsinci abun kirki ba ko rabin kwando baiyi ba sabanin na fatsima wanda har yafi rabin kwando a haka suka tashi suka tafi famfo suka wanke suka nufi kasuwar adare.

sun dade suna zagaya kasuwar da kwado akan su suna tallata hajar su, da kyar suka samu aka saye bada wani kudin kirki ba ma,
Na fatsima da ya fi yawa yafi yawan kudi.
a hanya fatsima take tsuye kaltum akan abun da taja musu yau sun makara basu kai kayan miya da wuri ba har kowa ya gama siya asanadiyyar koke-koken data zauna tanayi tun dazu
kaltum batayi magana ba tafiya take zokai-zokai abun duniya ya ishe ta babu abunda tafi bege tafi bukata a zuciyarta irin ta rufe ido ta ganta a bur sudan ba haka bata kula irin gidan kusa da membela .
kwalla ta cika mata ido da ta tuno rayuwarta da yan gidansu na bur sudan ga kawayenta yadda suke wata yawarsu .bata damu rashin wuta da ruwa irin na bur sudan ba,haka bata kula da irin gidan katakon dasuke rayuwa ba ,bata duba yanzu a babban birni da take ba,ga wutar lantarki koda yaushe ba a daukewa ,fanka fil fil fil najuwa ,ga ruwa a famfuna yana kwaranya koda yaushe .
kaltum bata damu data koma nigeria ba don taga iyayenta da kannen ta ba,balle kuma alhaji adnan duk ta shafesu a cikin ranta basa lissafinta ta cire ran sake ganinsu a rayuwarta har abadh .

fatsuma ce da katse tunaninta da take yi tace zo muje musayo danwake muci tunda kudi bazai isa mu je mu auni shinkafa ba mu dafa

kaltum nabiye da ita har gaban me murhun me danwake.
baiwar Allah fatsuma ta karbi dan kudin dake hannun kaltum ta hada danata me yawan suka sayi danwaken chanjin suka sayi ruwan sanyi ,saboda yunwa a wajen suka tsugunna suke ci basu damu da mazanda ke zazzaune a wajenba haka basu damu da motocinda ke wurwucewa ba ana lekensu ana nuna su ,basu lura da kasar musulunci da shari'a sukeba
burinsu su warware hanjin cikinsu daya kanannade ya cure a gefe daya saboda yunwa.har wasu samari biyu da suka zo wucewa suka yada musu da magana cikin harshen Larabci.
kaltum data fi su jin larabci ta fi fahimtar abun da suka fada musu, don haka nan da nan yanayin fuskarta ya sauya, sanyin jiki ya far mata. ta bi su da kallo har suka kure.
samari biyu kyawawan fararen larabawa dayan ya dubi dayan,
sannan ya juya ya nuna masu su kaltum ya yamutse fuska ya ce, 'dubi wadannan 'yammatan a tsugunne a gefen titi, suna ciye-ciye saboda tsabar ba su san darajar da Allah ya yi musu ba ta 'ya'ya mata. rayuwa suke yi kamar dabbobi babu kamun kai'
dayan ya ce 'yan nigeria ne, ai zasu yi abun da ya fi haka ma. kai daga gani ba sai ka tambaya ba, duk haka suke rayuwa suna bata mana tarbiyyar kasa. ga su da nacin jaraba ko an kwashe su sai sun dawo ba za su zauna a kasar su ba.
ko ina dimbin arzikin kasarsu yake sukazo suka kunace mu suna cutarmu don duk yadda ka hada huldarka dasu sai sun zalunceka .
dayan yabashi ansa da cewa ,ehto baduka yan nigerian bane macuta sunada masu kirki ,kamun kai ,rikon addini da kyawawan halayya.

kaltum tayi ajiyar zuciya yayin da ta tsame hannunta tsam daga kwanon dan wake ta mike tsaye gami dacewa ,nakoshi ,ki cinye duka .

fatsuma cike da mamaki da tambayan ranta meyasa kaltum ta barma ta danwake har goma?
nan da nan ta halakasu ta tsuda kwanon ta kora ruwan sanyi suka kara gaba.

suna shiga sakar gida suka iske damdazon matan gidan kwansu da korkotansu a tsaye suna ta ce ce kuce .
hayaniya tayi yawa har ba zaka iya tsintar kalma daya ba kamar fada akeyi ko mayarda zance ,labari ne suke yi ko kuwa jajanta wani abu sukeyi wajunansu?
Allah shi Ya barwa kanSa sani.

fargaba gami da mummunar bugawar zuciyace ta fado wa kaltum asanda taga gaba daya matan sun yiwo kanta suna fadin ,yauwa ga kaltum din nan yar....

.
Sadin Maa.ADON DAWA 22
.
,yauwa ga kaltum din nan yar halak .

ta dafe kirji ta fada cikin,fargaba InnaLillahi wa'inna ilaihi Raji'un .me nayi ,lafiya?

Magajiya tafada cike tausayawa ,tace,sai kikaji abun da ya sami kalah da yar lami?

Kaltum tasake jin mummunar damuwa.tace meyasami kalah da lami?

Sai taga hawaye yana kwaranya daga idanuwan wasu daga cikin su ,saboda
tausayawa .kankace kwabo kaltum tafashe da kuka,yayinda jikinta ya dau karkarwa tana tambayarsu cikin matsananciyar damuwa mai hade da fargaba amsar da zasu bata .wai me yake faruwa ne ?
Ku fada mini.

magajiya ta sharce hawaye tace ,kalah da yarta lami ne suka yi hatsari a kwale kwale a
hanyarsu ta hayewa makkah ta barauniyar hanya jiya da tsakar dare,

kalah na asibiti rai ahannun Allah ,yayinda lami da sauran mata uku Allah Ya a
musu rasuwa kalmar innalillahi wa inna ilaihi
raji un ce ke fitowa daga harshen kaltum ,ta tsulale ta tsugunna yayinda ta hada kai da gwiwa tana rusa kuka .

magajiya tace kowa anan yasan hakkinkine yakama kalah da yarta kowa yasansu kalah suncuceki ,Allah baya Ya fe wa wani laifin
wani,sai kin yafe musu susami rahama kaltum kiyafewa lami wacce ta rigamu gidan gaskiya,kalah kuwa da bakinta take cewa anemo mata ke tanemi gafararki yanzuma daga asibiti muke bata anbaton kowa sai akiraki tanemi gafararki tasan ta cuceki mun duba duk inda zamu samoki tunda safe bamu gankiba

kaltum tafada nan da nan nayafe musu asabebe tace tashi muje asibitin taji da kunnenta ko hankalinta zai kwanta kaltum ta mike da sauri yayinda kowaccensu ta zaro gyalenta tafiya sukeyi fakam-fakam cikin sauri suna tayar da kura kai kace garken shanu aka bude aka korosu kiwo .
kowaccensu ka duba sai ka rantse daga kabari ta fito butu-butu wasu da goyo wasu da yayayyun 'yaya sunrike hannunsu mata fiye da ashirin ne suka taho duba kalah.

nan da nan ma aikatan suka taho da sauri suka tare bakin kofarda kalah ke kwance .
tambayarsu suke lafiya?

Asabe ce ta koro musu bayani ,wannan itace kaltum da kalah kecewa anemo tunda tsafe suka bar asabebe da kaltum suka shiga ragowawar aka tura keyarsu baya .akarkashin wata itaciya suka tarufi, takaici ya ishesu baza arasa tsaki da harare harareba harda yan tsirarun ashariya duk sun kutuntumawa ma'aikatan cikin harshen hausa tunda basaji ,

fargaba da kidimewane suka hadu a zuciyar kaltum dai dai lokacinda tayi ido hudu da kalah yanayin jikin kalah zai tayarwa da duk bil adama hankali musulmi harda wanda ba musulmiba saboda mugayen raunukan da ke jikinta kama daga kanta zuwa kafarta duk bandejine,
karkarwa kawai kaltum keyi yayinda taja burki tayi turus tana duban kalah.itama tana dubanta hawaye masu zafine ke kwaranya daga idanuwansu,

yayin da bakin kowaccensu ke karkarwa. kalah na kwance reran an nadeta da farin bandeji, wanda ya yi nashe-nashe da jini. kafafuwanta dukka biyun, da hannunta data dorin karaya ne. fuskarta luhu-luhu a kumbure idan ba an fada maka ita ba ce babu yadda zaka kalleta sau daya ka gane ta. da kyar kalah ta daga hannun ta fada cikin wata shamulalliyar murya marar kuzari, 'zo nan kaltum, zo wajena, kun ga yadda Allah ya yi da ni. na cuce ki, amma kaina na cuta' kaltum ta matso a hankali ta raba ta zauna a gefen gadon kalah tana mata duban tausayawa,hawayen dai bai tsagaita ba daga idanuwan kowaccensu, su ukun har da asabebe.

kalah ta kara da cewa,
'me za'a yi da halina, me za'a yi da zalunci, cin amana da damfara?

kaltum, na damfari iyayenki ,nacuce ki ,najawo kaina.shin me kudin nan dana cuce ku ya karamin yanzu?
mezamu fada wa Ubangijinmu nida lami ?

kuka me yawa ya ruftowa kalah takasa
cigaba da bayani asabebe nashafa hannunta tana bata hakuri tana cewa daina kuka kalah fuskarki duk dinkine kada ya sake kuburi yihakuri kaltum tariga tayafemuku,

kalah ta fara magana cikin nadama Allah ya yafemin ,kaltuma kiyafe min inkinje gida
kicewa alhaji adnan yayafemini domin naci amanarsa akwai wani Inuwa agent dan Daura ne wanda duk shiyakawomu nan shi alhaji adnan yaje yasamo har Daura ya tambayi inda kike inuwa agent yace ya dade baiyi wannan harkarba ta kawo mutane sudan saidai zaisa a binciko inda kike bansan inda
inuwa yasamo labarin bur sudan ba andai tabbatar masa kina cen saisuka shiga tunani yanda za ayi adaukoki da farko shida alhajinne suka shirya tahowa bur sudan dinsu taho dake sai gani kwasam nabugowa inuwa agent waya inaso yakaiwa 'yaya na wayarsa muyi magana dasu don basuda waya sai kuwa yaji dadi daganin numbata

daganan sai labari ya canja cewar intaikesu in dauko musu ke daga bur sudan in dauraki ajirgi kitafi kano nan da nan na kalallamesu da dadin baki danaji maganan kudin jirgi na
nunamusu ciwon 'ya mace na ' ya mace ne, d'a ai na kowa ne, na daukan musu alkawari zan kawo musu kaltum har gida kada ma su bata lokaci da kudin jirgi har na mutane biyu zuwa da dawowa ga wahalar zuwa bur sudan godiya iri iri da shi albarka suka dinga mini basusan abunda na kudurta azuciyata ba
mukayi lissafin kudin jirgin kasanda zai kaini bur sudan da wanda zamu dawo Khartoum ni dake da kudin abincinda za muci a hanya sannan da kudin jirgin sama nawa da naki daga Khartoum zuwa kano hatta da kudin taxi da zamu hau daga filin jirgi zuwa unguwarku saida ya lissafo ya aiko min .

Inuwa agent yasan inda suke tura kudi daga wapa zuwa nan khartum har gida suka bawa mai canjin adireshina da lambar waya ta saigashi yakawo min makuden kudi nan shaidan ya zugani naji bazan iya kashesu ta hanyarda aka umurceni ba abunda nake
nemane ido rufe shekara da shekaru muna fafutuka a sudan mun kasa hade kudi mu karasa saudiyyah .
da gudumawar shawarar 'yata lami na nade kudi na boye nayi zamana na manta da alkawarinda na dauka .yawan damuna da wayar da alhaji.adnan da inuwa agent ke yi ga wa' azi da gargadin da kawayena wadanda agabansu na karbi kudin ke yi shi yasa na canja shawara inje bur sudan in dauko kaltum insakata amota ta tafi kano ita kadai sauran kudin in rike, inasaka ranar tafiya bur sudan natsami mai tafiya Hauwa saina bata sako ta taho min dake zuwan ki khairtum naji
bazan iya cire zunzurutun wannan kudi ba in biya miki kudin motar zuwa nigeria ba don haka nacire numban wayata na yar yadda su inuwa agent ba za su sake samuna a waya ba balle su dame ni da tambaya, domin duk karairayin da nake shirga musu sun kare, ban san kuma abun da zan dinga fada musu ba.''

kalah ta fashe da kuka mai tsanani, yayin da kaltum ta ji kukan da ta ke yi ya kafe, takaici ya ishe ta, ta tsurawa kalah ido tana dubanta tana tuna irin wannan cin amana da son zuciya irin ta mutanenmu.

asabebe kuwa fadi ta ke,
''cafdijam! duniya ina zaki damu?
kalah, kin yi kuskure a rayuwarki. me kudin nan zai yi miki a rayuwa, ki ka sani idan da
kin kai musu 'yarsu su baki fiye da abun da suka turo miki tun da masu hali ne?''

kalah ta jima tana kuka kafin ta ci gaba da
magana. ta ce 'na yi niyyar yin biza ta kirki mu yanki tikiti mu hau jirgi mu shiga makkah yadda doka ta tsara sai kawayena suka bani shawarar kada in kashe kudina. ni da kawayena guda biyu da tshohuwa daya muka shirya tafiya makkah ta barauniyar hanya''

kaltum ta tambaya cike da neman karin
bayani, 'ta barauniyar hanya kamar ya ya?

kalah ta matse hawaye tace
eh ta barauniyar hanyace domin da tsakar dare ake fara tafiya alokacinda jami' an tsaro ke barci ko ince babu kowa a kogin sai ahaye saboda hatsarinda ke tattare da tafiyan da
rashin tabbas ba ama biyan me kwale kwalen harsai yasallakar da ku saboda adayan biyu kuke ko kuhaye ko akamaku, ba makkah zai tsallakar da ku bafa wasu kauyukane agefen ruwan suma en kauyen sana'ar da suleyi kenan kuna isowa cikin dare sai ku biya me kwale kwale kudinsa yacika aikinsa sukuma en kauyen sai su kwasheku cikin sanda da leke-leke sai su shigar daku cikin gidajensu cikin gidanma a cen kuryar daki karkashin gado zasu boyeku saboda jami'an tsaro na iya zuwa bincika ko akwai irinmu idan bakuyi sa a ba aka kamaku to tabbas daku da matafiya da masu gidan zaku fuskanci fushin hukuma ,
kasancewar akwai wasu daga cikin yan kauyen da suke kaiwa jami'an saro gulma idan ansami labari irin wannan sai suzo
sufara bincike gidajen daya bayan daya dan haka ake tsoron boyemu saidai wadanda suka tari aradu da ka ne basu daina ba

kaltum ta gyara zama taci gaba da kurawa kalah ido tanasonjin karshen labari .meya hada duk wannan labari da mummunan
hatsarinda suka samu harda rasa rayuka ?
takaici ya isheta da takejin hanyoyin karya doka da mutanen mu yan nigeria keyi adole sai sun shiga makkah alhali a makkah dimma a wulakance suke koda yaushe askarawa nabin su da gudu suna kamawa suna dawo dasu kasarsu suba ibadar suke samu suyi
ba sai neman kudi yaki halak yaki haram ana kyararsu ana korarsu, kaltum tafi bukatan ta dauwama a sudan da tashiga makkah saboda tasan azabarda tasha awancan karon

kalah ta katse mata tunani taci gaba da cewa kamar yadda aka mana bayanin yadda akeyi idan kukayi kwanaki kamar biyu a boye agidan kauyawan nan idan suka tabbatar yan saka ido sun daina zargin an boye mutane hankalin kowa baya kansu da tsakar dare sai su fito daku ta bayar gari sununa muku hanya ta inda zakubi ku bulla jidda sannan kubiyasu kudin aikinsu to da dabara da boye boye ga yar karan tafiya mai yawa har ku samu kushiga jidda shikenan hukuma batasan kun shigo ba daganan sai kowacce tayi ta kanta idan ajidda zaku zauna to idan mota zaku hau ku tafi makkah ko Madina to yarage naku,

asabebe tace ni abunda banganeba ku a ina
kakayi hatsari har kuka sami raunuka haka ne asudan ko a saudiyyah ?

Kalah ta girgiza kai yayinda ta zubo da hawaye daya cika mata ido tace a sudan abun ya samemu bamu kaiga hayewa ba bamu dade da fara tafiya ba a cikin kwale-kwalen mu biyar ne dukka matane sai matukin ne kadai na miji kamar yadda na fada muku da tsakar dare ake fara tafiya a lokacin da duk wata halitta ke barci a hankali yake tuka jirgin ko tari bai umurcemu muyi ba balle magana muna cikin tafiya kwasam
saiya hango haske daga nesa an haskemu da alamar babbar jirgine na ma'aikata sai mu kaji magana da lasifika ana umurtanmu
da mu tsaya a inda muke kasancewar yanada labarin irin mummunan hukunci da za ayi masa idan aka kamashi sai ya gigice ya fara azazzalarmu yana daka mana tsawa waimu fice masa daga jirgi ganin ya gigice sai muma muka fishi rudewa don haka mun manta a tsakiyar ruwa muke saisu dukansu harda lami suka daka salle cikin ruwa ba a kara ganinta ba saidai mutsu-mutsunsu tunda basu iya ruwaba suduka suka mutu nice naki fita ina ta ihu na dora hannu a kai kiran yata lami nake shiru lami bata amsa ba ta lume cikin ruwa bankara ganinta ba ashe bazan sake ganin ta ba har abada?

Su dukka ukun suka fashe da kuka a lokaci guda cikin kuka kalah taci gaba da cewa baidaina yimini tsawa infice masa daga jirgin kwale kwalensaba amma naki fita gudu yakeyi yana wuce kima musamman dayaga hasken fitilar nan ya nufo mu aguje arashin sani baisan ta inda ya nufo ba ashe wani gungumemen dutse yanufo a gaban ruwa jirginmu ya daki dutsen mu mu duka muka tarwatse mukayi sama muka fada cikin ruwa damu da jirgin namu ni kadai nayi rai gawarwaki biyar aka fitar daga cikin ruwa har da direban mu nice asume da wadannan raunukan

ina fatan nima zan mutu inje inhadu dasu lami don bani da anfanin zama aduniyannan sai kalah tarushe da kuka yayinda kaltum ta sunkuyar da idanuwanta da sauri kasa hawaye yana kwaranya saboda tausayinsu lokaci me tsawo babu wanda ya iya magana a cikinsu can kaltum ta dago da luhu-luhun
idanunta tadubi kalah tana magana cikin marainiyar murya tace kalah na yafe miki nayafewa lami Allah Ya yafe mana
gabaki dayan mu,
sai kalah ta rushe da kuka me karfi har saida
majinyatanda ke kwance asauran gadajen suka firgita yayinda ma'aikatan jinya suka yi tsawa suna cewa kalah ta rufe musu baki tana damun marasa lafiya tamkar xugata suke ai sai ta bude baki gaba daya tana rusa ihu magana take cikin harshen larabci yadda kowa zaiji tace na zalunci kaltum na zalunci
kaina akan abun duniya idan na mutu mezance wa Allah ?

ban mori kudin ba ko sisi ya watse aruwa na rasa yata lami na rasa lafiyata nibanje makka ba kuma sunana yabace a garin mu saboda inuwa agent zai fada wa dangina abun kunyarda nayi

hankalin kaltum da asabebe a tashe suka dinga rufe mata baki suna danneta don kada taci gaba da tonawa kanta asiri saboda abun ya zame mata tamkar tabin hankali daga karshe su ma su kaltum aka koresu waje yayinda aka dannawa kalah allurar barci a cikin karin ruwan da ake yimata tun tana magana har ta fara lunshe ido,

kaltum da asabebe suka fito wajen yan uwansu kallo daya suka taro su suna jero musu tambayoyi, kaltum ba ta iya magana ba
gefe dasu ta tsugunna ya yinda asabebe take kora musu bayanin abubuwan da basu sani ba muryar daya daga cikin ma'aikan jinya ce tace dasu kuje ku suyowa kalah abinci mai ruwa kamar lemo da shayi tunda aka kawo ta bataci komai ba nanfa aka hau kallo kallon aka rasa wacce zata ce wani abu

sai kowannensu tafara cewa ban fito da jaka ba a'a bubu canji da na bayar,
cikin marainiyar murya kaltum ke rokarsu tace dan Allah ku taimaka mata a suyo mata shayi tasha bakin ta ya bushe babu abinci banida kudi ni kuma,

da kyar uku daga cikin suka fitar da wahid jine dai dai salas jine kenan suka ba wa kaltum ta falfala bakin get ta siyo shayi kofi daya da gutsiren biredi ta shiga ta kai wa kalah. Ta iske ta a kwance barci na fisgarta sama-sama amma tana kokarin bude ido
kadan-kadan magana ta ke yi,amma ba a ji,tabbas ruwa ta ke cewa a bata.
kaltum ta daddage ta dago ta zauna zauna gami dayimata weji da filo a bayanta ta dan kishingide duk da karin ruwa da yake hannun ta ga karaya a daya hannun kaltum ta dinga tarfa mata ruwan shayi da cokali a bakinta duk da ta kasa tauna biredi amma ta shanye ruwan shayin tas,

a bandakin dake ciki kaltum tashiga taryo ruwan fomfo a kofi ta kawo ta dinga tarfa mata abaki sannan kalah taji dama-dama kaltum tana gyara mata kwanciyarta saikuwa
tarufe ido ta fara barci mai, nauyi kaltum ta lullube mata jiki da mayafinda ke gefemta sannan tajuya zata fita yayinda tayi arangama da ma'aikaciyar lafiya mai kula da kalah sai ta miko wa kaltum wata zungureriyan takarda ta magungunanda ake
bukatar da ruwanda za a dinga kara mata tana bukatar karin jini kije kukawo,

hankalin kaltum yatashi dataji batun kudi ko
sekon daya bata karaba tace wa matar wallahi banida kudi matar ta harareta tace daman ina kikaga kudi ?
Ki kaiwa iyayenki manya suje su sayo su kawo yanzu,

kaltum tajima a tsaye tana juya takardannan

sannan ta fara tafiya asanyaye ta isa inda har yanzu yan gidansu suke saye ta dubesu daya bayan daya ta fada cike da fargaba saboda shayin jine uku da kyar suka biya balle a ce an ambato irin wadannan makudan kudi tana ambaton musu jerin magungunan suka tabbatar kudin ne mai yawa sai ko waccensu ta fara hada yanata-yanata ma'ana kowaccensu ta zazzage zaninta ta juya ta kalli get din fita kaltum tayi narai-narai da ido kamar mai shirin yin kuka ta fada cikin damuwa ku taimakawa kalah ance bata da jini a jikinta kar ta mutu,
waye mai jini ajiki ?
ai dukkanmu nan idan aka tsaga mu baza a sami jinin kirki ba, shafa'u tafada dai-dai sanda ta fisgi hannun yayayyiyar yarta ta kara gaba ai sai duk sauran suka bi bayan shafau
magajiya ce ma dai ta dan tsaya tabawa kaltum shawara cewa ta taho suyi tafiyarsu kawai tama daina damun kanta kada ma
ta sake zuwa asibitin balle su ganta su tambayeta kudin magani idan sukaga shiru ba yan uwanta gwamnati ce zata dauki nauyinta koda kuwa anzo gida neman yan uwanta kada ta sake tace ta santa ma ko mutuwa tayi sun san yadda zasuyi su bunne ta,

kaltum ta kame a tsaye tana duban ganin
ikon Allah tana tambayar zuciyarta wai ina soyayyanda sukeyiwa kalah a da?
me dalilin rusa kukanda da su asabebe
keyi na tausayin kalah daman bana gaskiya bane ?
idan tausayin ta sukeji da gaske ai zasu siya mata magani donta warke inhar suna son ta rayu,

magajiya ta juya ta tafi da taga alamar kaltum bata da niyar binta sutafi kaltum tayi zaman ta akasa tana rike da doguwar takarda a hannu sai yanzu ta sake tuna madina wacce ta tsaya tsayindaka wajen kula da ita, da haka za a barta a yashe har sai ta zama mushe babu wacce zata taimaki wata da karfinta ba ma da kudinba?

hawaye ya kwaranyo daga idanuwan kaltum tahada kai da gwiwa tana kuka a bayyene take kiran sunan madina da mambela fadi take meyasa aka kawoni garin da wani baya
taimakon wani?

kaltum kaltum ?
muryar wata mace taji daga
wundon gadon da kalah ke kwance tayi farat ta hango ma'aikaciyar jinya a tsaye nanda nan ta mike aguje yayinda zuciyarta ta hau bugawa tana fargaban abunda zata shiga
ta iske tana karasawa kalah ta duba saitaga tana numfashi duk da idanuwanta arufe suke tayi ajiyar zuciya jin dadi tunda ba mutuwa tayiba AlhamduLillah, ma'aikaciyar jinya tadubi kaltum ta yatsune fuska tace kidubi jikin mahaifiyarki ki gyarata,

kaltum ta tambaya cike da rashin fahimta in gyarata kamar yaya?
tayi mata tsawa dakika shigo bakiji wariba?
to kashi tayi gaba daya dakin yakidime da wari kalah fa tana damun marasa lafiyanmu
mun fara gajiya wata ma'aikaciya dake bakin kofa ta toshe hancinta tace wai a tarkatasu mana sukoma kasarsu Nigeria suje cen su karanta, dayan nurse din ta bata amsa, da inafa ?
ai bazasu tafiba ko tsaga jikinsu akeyi da reza kamar baki san su wajen naciba ?
ai ita wannan ko en uwanta sunzo daukarta
baza a bari ta tafi ba saboda yansanda ne suka kawota takardan sammacinta daga kotu tana cikin file dinta da zarar ta warke
kotu zasu shiga ayi shari'a da ita saboda karya dokar da tayi wajen haurawa makkah ta barauniyar hanya,

nandai ma'aikata da leburori harda masu zaman jinya da majinyata suma suka tsoma bakinsu suna Allah wadai da irin rayuwanda yan Nigeria keyi musu akasa jikin kaltum yayi sanyi ta koma jikin gadon kalah ta tsaya tadade a tsaye tana kallonta batare da tasan yanda zatayiba har yanzu ma'aikatan tsawa suke mata wai tsayuwar me takeyi bazata fitar musu da warin nan dake damun su ba ?

kaltum taje gadonda ke kusa da kalah tace don Allah ku bani aron bokitinku idan nacire zani sai in wanke,

nan da nan suka zaburo sukace badai da
bokitinmu za'ayi wankin kashi ba, bazamu bayar ba.

ta sake matsawa gadon kusa dashi tace subata aron bokiti amsar da suka bata tafi ta wadancen muni cemata sukayi ta matsa tabasu waje ko su mareta tasake matsawa dayan gadon tace su taimaka mata da sadakar omo ko sabulu sai taje bakin
fomfo ta wanke shima sukace ta tafi tabasu waje baza subayarba

ranta yabaci yayinda ta fara jin wannan yanayin na ko a ayi rai tabbas da alama kaltum sai ta dawo da halin nan nata na baya na yar agulla sannan zata kwatowa kanta yanci da yancin kasarta ta cije baki ta gyada kai tajuya a fusace ta isa gadon da kalah ke kwance bata damu da ciwuka dake jikin kalah ba sai ta dagata ta fara goge mata jikinta gaba daya zanin jikin ta da mayafinda akafuta ya baci don haka ta warware lufayarta ta raba gida biyu ta tsaga ta daura rabin a jikinta yayinda ta lullubawa kalah rabinta ta cukuikuye kayan kashin a hannunta
ta fice a fusace wari ya turnuke dakin musamman idan ta zo giftawa sai kowa ya toshe hanci tafice daga dakin harta kai baranda waje sai taji an kwalla kiran sunan ta tajuya da sauri sai taga ma'aikaciyar daya ce tabiyota dauke da wani gumtun
sabulu ta wurga mata a wulakance game da cewa ga sabulu nan sai ki dauka kije ki wanke mana zanin gadonmu wani kallon
sama da kasa kaltum tayi mata ta kada kai tayi gaba ko kallon sabulun batayiba mamaki yakama ma'aikaciyar ta rike baki tana mamaki kaltum ta wuce zuwa wani bandaki dake tsakiyar asibiti zata shiga kenan saitaji an dafa bayanta ta juyo da sauri sai taga wata matace wacce gadonta ke kallon gadon
kalah me suna Aishah bata cikin wadanda suka hanata aron bokiti da sabulu amma tana zaune a dakin sanda ake maganar daga dukkan alamu kaltum ta bata tausayi shine ta biyota da bokiti da kullin omo tamikawa kaltum kaltum ta girgiza kai tace banaso kibar shi kawai Aishah tayi kasake da alama bata ji dadi ba dan kaltum bata karba ba tasake bin kaltum cikin bandaki tace ai fushi ma bai kamakiba tunda baki dashi,
kaltum ta juyo afusace tafada cike da takaici tace idan saida sabulunku da bokitinku yan dakinnan zanwanke zannuwan nan to gara asani gaba ace insude da harshena har sai sun fita,
mezanyi da sabulunku ko bokitinku ?
zanfita inyi bara in samo omo tunda daman munsaba sudan bakasarmu bane kunyi
gaskiya nacinda kuke ambato gaskiyane munzo mun nace muku a kasarku bamuda zuciya duk abunda ake yimana mun ki tafiya ku yi hakuri ba dukanmu bane ma....
.
Typing : Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 23
.
TRUE LIFE STORY
.
masu son zaman kasarkuba dayawanmu
kaddarace muma badason ran mu ba dolece,

a bakin bandaki aka tsatstsaya ana kallon su kaltum yayinda mamaki ya rufe yan kallo suna tambayar meyake faruwa ne meyakawo zancen zama akasar sudan?

kaltum ta wuce wajen fomfo batare da ta iya tsayawaba tabasu ansa ba Aisha ce ta tsaya tana bayanin abunda yafaru, gaba daya suka bawa kaltum gaskiya suka bawa ma'aikatan da yan dakin rashin gaskiya koba yan kasa bane ba ai musulmai ne, wulakanci bashi da dadi kuma yan sudan nawa ne a nigeria sunacin arziki abun duniya suke tarawa a Nigeria su dawo sudan suna zagawa,
akwai auratayyah asakaninsu dan haka
anzama daya,

aka cika bandaki ana bawa kaltum hakuri akanta karbi bokiti da omo tayi wanki taki karba tace ai ta rantse indai bokitin yan dakinne bazatayi anfani dashiba

saida wata tabata sabulu sannan ta karba na
aishane bazata karba ba tunda tana dakin tana ganin wulakancin da akeyi mata bata fitar da ita kunya ba sai daga baya zata biyota saboda kar yan dakin su tsaneta kome?

kaltum rigima da kyar ta karba sabulun ta wanke taje ta shanya igiyanda dake gaban dakinsu tashigo dakin tana kallon kowa daya bayan daya jira takeyi ayi magana tayi tsiwa babu mai iya hada ido da ita domin Aisha
takawo musu labarin abunda kaltum tafada abandaki

ta isa gadon kalah har yanxu shirkif take cikin barci, ta fada abayyane cikin harshen larabci kalah zantafi cikin gari insamo miki abunda zakici nabar amana agurin ALLAH domin Shi Ya halacci talaka Ya halacci me kudi ya halacci dan sudan ya halacci dan Nigeria

sai kowacce tayi kiri-kiri tana duban kaltum sunsan magana ta yasar musu ta wuce kere-kere ba mayafi kasancewar taraba mayafinta gida biyu ta rufa kalah

ma'aikatar daya ta dubi kaltum ta gyada kai
tace lalle yarinyarnan batada mutunci ashe.
kaltumta murguda baki ta fice yayinda suduka suka bita da kallo kaltum nashiga gidansu matan gidan sukayo kanta suna tambayan yaya jikin kalah an sayi magungunan kuwa?

Wannan tambayan nasu ta bata mata rai don haka bata basu amsar tambayarsu ba ta kada kai tayi daki,
buhun kayanta ta jawo ta bude ta daura wata lafayan tacire ta jikinta, yau zancen wanka babushi tafice ko wacce taja bakinta tayi shiru babu wacce ta sake tambayarta komai sunga ranta yabace kuma sunsan basu kyauta ba kallonta sukeyi harda lekenta akofar gida su ga inda zata nufa asibiti ko
kasuwa,
hanyar kasuwa ta nufa don haka suka gaskata neman kudi zataje

nan suka dasa kujerar gulma cewa banda
yarinta ma meyasa kaltum zata damu kanta akan kalah, matarda ta cuceta takawota Khartoum ta wulakantata ita da yarta , kaltum babu abunda basuyi mataba na wukanci

fatsumace ta hango kaltum ahanya yayinda tafito daga wani gida ta bullo da gudu ta iso inda kaltum ke tafiya ta dafa bayanta firgigit ta tsorata ta waigo da sauri sai taga fatsumace sukayi murmushi alokaci guda fatsuma tace yaya jikin kalah, kin san fa tsoron asibiti gareni shi yasa banbiku asibiti ba,
kaltum ta tabe baki tace bai kamaki bane dole dakinje,
fatsuma tace banda abunkima inake ina zuwa duba kalah duk irin muguntan da tayi miki mezakije kiyi mata koda mutuwa tayi ma ina ruwanki?

kaltum tayi murmushin karfin hali tace muna yiwa Allah laipi muroke Shi Ya yafemana meyasa bazan yafewa kalah ba?
yarta lami ta mutu meyasa bazan taimaketa ba tunda bata da kowa?

fatsuma ta tabe baki tace lallai kaltum dama haka kike da tausayi kamar lokacin Sahabbai?

kaltum tayi daria, saboda na hadu da lalurar rashin lafiya nima Madina ta taimakeni yayinda sauran suka gujeni shiyasa na kudiri niyyar taimakon duk wani mara lafiya acikinmu tunda muna kasar da ba namu ba, babu iyaye babu dangi,

fatsuma tayi ajiyar zuciya tace gaskiyane yanzu ina zakije ?

Kaltum tace kasuwa zanje na nemo wa kalah abinci kafin magariba fatsuma ta yamutse fuska tace mezaki sayar kisami kudi?

kaltum tace bara zanyi .

fatsuma ta dafe kirji tafada a bayyane cike da fargaba bara?
Bara fa kikace kaltum to Wallahi ba'a bara anan sai akamaki akaiki Chad ko maiduguri ayar, nan ba bur sudan bace babban birninsu ne ba a wannan rashin hankali kame akeyi.

kaltum tayi kasake tana tunani to in banyi bara to mezanyi na sami kudi tunda sana'ar tamu ta sassafene kawai muma sau daya samu muci abinci ko sau biyu saikuma wata goben....

fatsuma ta katse tunaninta tace yanzu nan da ganni daga cen gidan nafito nasami sabon aiki da yamma zandinga zuwa kuma kudi da abinci matar tace zata dinga bani kullum.

kaltum ta tambayeta cike da fara'a wanne
irin aikine ?

*fatsuma tayi murmushi tace gidan kunshi ne
da gyaran jiki (alewa da dilke )matane dankar suke taruwa ana bin layi ita kadaice don haka aiki yayi mata yawa take neman masu tayata kamar masu yi mata aikin gida da masu wanke wa mutane lalle da shafa mahallabiya nidai renon jaririyarta neke yi mata yanzu ma aikena tayi insayo mata mahallabiya akasuwa zo muje ki rakani saimuje gidan tare ki dinga tayani aiki idan kikaci sa'a kema saita daukeki aiki,

tafiya sukeyi fatsuma hira takeyiwa kaltum yayinda ita kuma addu'a kawai takeyi azuciyarta tana fatan Allah Ya taimaketa matarnan tadauketa aiki asirinta yarufu ,

akusa da mai sayar da mahallabiya akwai masu sayarda madarar turare anan ne kaltum tahadu da wani farin saurayi mesuna Abbas,
kallo daya ya wa kaltum yaji zuciyarsa taharba ta tsansar kaunanta ya dinga shisshige mata yana tsoma baki acinkin cinkinsu ko kallo bai isheta ba domin ita duk abunnan da akeyi hankalinta na gun aiki da tunanin halinda kalah ke ciki, saida Abbas
yamiko mata kwalbar turare sannan ma ta daga ido ta dubeshi ta sa hannu takarba batare datasan manufarsaba ta manta ana godiya idan anwa mutum kyauta ta kada kai tayi gaba fatsuma tace ta tsaya tana surutu dasu sannan can ta taho suka tafi a hanya take shaidawa kaltum cewa Abbas ne ya tsaryar da ita yana tambayarta gidansu wai kaltum yakeso,
kaltum ta tabe baki ta fada a yatsune au shine yabani turare ai danasan manufarsa da
bazan karba ba,

fatsuma ta zungureta tace ke wawuya ce ki so shi kawai yadinga zuwa zance yana kawo mana kudi, abinci,sutura da kayan dadi,

kaltum tace Allah Ya sawake na so wannan.
fatsuma ta harareta tace yafiki kyau fa, balarabene fa kobaki kare masa kallo bane?

kaltum tace bai dameni bafa ya kyaleni,
haka dai suke tautauna harsuka isa gidan me kunshi katafaren tsakar gidane aka malale da kafet hade da manyan fululluka mata birjik kowacce a kishingide an yarda mata kunshi a laulausan fatarta da alama mai kunshin ta bunkasa domin matan manyane duk a wajen daga dukkan alama motocinsu da direbobinsu a waje kofar gida suna jiran su,

kallonsu kawai kaltum keyi tana sha'awar baiwarda Allah Ya yi musu dama nice nasami
kwanciyan hankali da daula irin wannan, kaltum tafada azuciyarta dai-dai lokacinda ta durgushe gabansu tana kwasar gaisuwa.
fatima wannan fa?

ina kika samo yar kyakyawan kawa itama yar
nigeria ne ko yar mali?
Inji Jawahir me kunshi.

fasuma tayi dariya tace kawatace kasarmu daya gidanmu daya kaltum sunan ta,

gaba daya suka zubawa kaltum ido sai ta sunkuyar da kanta kasa ta fada cikin marainiyar murya hajiya kitaimake ni ki bani aiki mahaifiyata na asibiti akwance abinci na
fito nemar mata,
sai hawaye ya kewa kaltum gaba daya suka tausaya mata harda masu tayata kuka,

kankace kwabo sunfara bude jaka ana zaro
sabbabin kudi ana mika mata sadaka tamike tana bi tana karba tana tarawa ta durkushe a gabansu tayi godiya gami da kwawawan addu o I,
Jawahir takara mata da albishir da daga gobe tafara zuwa aiki ta dauketa aiki zata dinga biyan ta,

kaltum tayi sauri ta dubi fatsuma farin ciki ya lullubeta su kayi dariya lokaci daya sannan sukayi godiya tare,

kaltum tamike tsaye ta kara godiya tace zan koma asibiti wajenta gobe zan fara zuwa. Jawahir tayi murmushi,
Ta ce Allah Ya kaimu kiyi mata sannu Allah ya sauka ke.
kaltum ta amsa da amin ta fice tana murna yayinda tafara kidaya kudinta metan wa tamanin jine ma'ana dari biyu da tamanin saita kyalkwale da daria saboda farin ciki tashiga tunanin abunda zata sayawa kalah wanda zataci tana tafe tana tunani saita yanke shawara taje restourant ta sayo mata gasheshshiyar kazar da ake gasawa a inji mai laushi da tiriri, marar lafiya zaiji dadin taunawa don haka kai tsaye ta wuce al-amana resturant ta sayo wata dankwaleliyar kaza gashesshiya mai zafin gaske har tiriri takeyi ta ashara jine tashiga super market ta cefano kayan shayi na hamsin wa ashirin jine fal leda ta nupi asibiti ta ayyanawa a ranta cewar yan dakinsu na asibiti zasu sha mamaki idan sukaga ta tilowa kalah wadannan kayan dadi a gaban ta kamar ba yanzu suka gama mata wulakanci ba akan guntun sabulu saita yi murmushi ta gode wa Allah daya dubeta Ya turo mata kudi nan mai dimbin yawa cikin dan kankani lokaci tsaka nin la'asar da magrib, Allah Shine abun godiya kaltum ta fada abayyane tana shiga cikin get din asibiti saita nufi dakin da kalah ke kwance ta duba igiyar data yi shanya saitaga an kwashe zannuwan data shanya saita yi mamakin wayezai kwashe zannuwan nan bata tunani sace wa aka yi tafi zaton
bushewa suka yi aka kaimusu kan gadon kalah,
tashiga dakin teburin ma'aikata ta duba da ke daf da kofar shiga har yanzu masifaffun matan nan ne akan aiki ta dube su ta fada cikin gadara ina takardar maganin nan?
Kubani insayo sai taga sun turus da alama suna mamakin kalam kaltum,
can daya daga cikinsu tace kibarshi an bar matashi kyauta, kaltum ta wuce tana gyara jibgegiyar ledar da ta shako da kayan dadi yayinda duk gadon da tazo giftawa marasa lafiya da masu zaman jinyar su suka bita da kallo,
dadi yakama kaltum ta huce takaicin bakin cikin talaucin da ya addabesu , ita ma
yanzu zata jera kayan shayi akan lokarsu kamar yadda kowanne gado ake jerawa,

kallon ta suke ita ma tana baza ido tana dubansu duba irina ku kallah da kyau nice dai ta dazu wacce ba ta da guntun sabulun wanki,
yanzu Allah Ya hore mata abunda yafi sabulunku,
dadi ne yayiwa kaltum yawa hartayi batan kai
tarasa gadonda kalah ke kwance kokuwa idone yayi mata yawa tafiya take hartakai karshen dakin bataga gadon kalah ba saita juya ta kara tahowa tana baza ido dukka bangarori hagu da dama saigata abakin kofar fita mamaki marar misaltuwa zaka iya gani afuskarta ta fada abayyane ko ba dakin bane?
yayinda ta kara duban fuskokin yan dakin da ma'aikatan, hakika yan dakinne dan haka
daki ma shine babban abun tambaya ina gadon kalah?
Ina kalah ?

Shine kokarinda kaltum takeyi gashi babu wanda yace mata uffan.
.
Kai... 😊
Wannan part din ya min dadi sosai, irin yadda kaltum ta nuna GIRMAMAWA tare da jan AJIN ta a paskar en dakin su,
Girmama kai ba girman kai bane, ta burge ni sosai da ta kasance mai xucia kamar JAN NA MIJI, sai ta kara mugun shiga raina 😍....

Saura kadan kuga katin gayyatar auren mu 👫 ❤️
.
Sadiya Sadiq.
Abbas Abdulkadir Hada Hada.ADON DAWA 24
.
Babban abin tambaya shi ne, ina gadon kallah? Ina kallah ta ke? Shi ne kokarin da kaltum take yi, ga shi babu wacce tace mata uffan, Kallonta suke tamkar a talabijin take ba a zahiri ba. Ta koma ta dawo, se ta je kansu ta tsaya, tana musu duba irin na mamaki da Al'ajabi. Can taetambaya, "don Allah ina mai gadon nan, kallah? "
Caraf ta ji an dafa bayanta, sai ta yi farat ta juya a tunanin ta kallah xata gani da kafarta tana tafiya ko bsndaki ta shiga da kanta, juyawar ta, se ta ga masipappiyar ma'aikaciyar jinyar nan ce, mamaki ya kama kaltum matuka ta bude baki tana dubanta.

Matar ta fada cikin marainiyar murya, "kaltum ki yi hakuri Allah Ya yiwa kalah rasuwa dazu dagafitar ki,ko get baki kai ba. An leka da gudu ba a ganki ba.... "

Duk wannan dogon bayanin da matar ke yi bai shiga kunnen kaltum ba, kalmar da ta rike ita ce, Allah Ya yi wa kalah rasuwa.
Rim! Ka ke ji ledar hannunta a cike da gwangwani ta bare, yayin da lakar hannunta ta saki sai ga himilin kudin da takunso damke a hannunta sun watse a kasa. Ita kuwa sharaf tafado akan ma'aikaciyar sai suka tare ta. A kasa ta mike zunbut kamar mai suma, amma ba suma ba ce, tsabar tashin hankali ne ya tayar mata da mutanen boye jikinta masu naci, ashe ba su bar ta ba.

Kan ka ce kwabo an kinkime ta an dora ta akan wani gado an kira likita ya hau aikin ceto rayuwarta. Idanuwanta a kafe amma duk abun da ya soka mata sai ta fusge, kuma magana take barkatai ga tsananin karfi, sai ta yi tazubar damasu danne ta. Masana suka shaidawa likita ya daina wahalar da kansa, wannan ciwon ba layinsa ba ne, aljannu ne don haka aka gewaye ta ana tofa mata addu'a.
Sai bayan sallar isha'i ta farfado, ta tashi zaune daram zuciyarta cike da mamakin ganin yadda jama'a suka zagayeta, mata da maza, ta lura da an burbursina mata wasu abubuwa a kofar hancinta, sai ta tuno matsalar bugun aljannun da take da su a baya. Sannan ta gaskata su ne suka tashi, sai dai tambayar da take yiwa kanta, me ya tayar da aljannun? Tana tunaADON DAWA 25
.
TRUE LIFE STORY.
.
Tunanin matsananciyar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ba ta son khartum haka ba dadin xaman garin take jib a, dama-damarta dan ta hadu ds fatsima kawa mai kaunarta, mai karfafa mata gwiwa. Ba don fatsima bad a rayuwa ta kara yi wa kaltum xafi a khartum kasancewar BABU RUWAN WANI da rayuwar wani , babu taimako ko kadan a xaman gidan nan.

“ya na yi miki Magana”. Fatsima ta xunguri kaltum a lokacin da suke tsugunne a bakin katuwar bola suna tsintar kayan miya.

Kaltum ta daga idanuwanta da sauri ta dubi mutumin da ke tsaye a kanta, Abbas ta gani tsaye a kanta yana murmushi sanye da jallabiyarsa fara tas! Da rwaninsa fari kal irin na larabawan sudan. Murmushi ya sakar mata gami da cewa, “marhaba kaltum.”
Sai ta ji ranta ya dungunxuma y abaci, bakin cikin day a dankare xuciyarta ya sake karuwa. Kallon fuskarta kawai xaka yi ka tabbatar da labarin xuciyarta. Ya yi ta Magana ko daga idonta b ata yi ba balle tab a shi amsa. Da ya dame ta, sai ta yanke shawarar hakura da tsintar kayan miyar, gara kawai ta bar masa wajen. Ta kinkimi kwandonta aka, ta yi tafiyarta ko fatsima bat a yiwa sallama ba saboda ta fuskanci ita ke goyon bayansa. Sai da ta yi nisa sannan ta ji fatsima ta kwalla mata kira. Kaltum ta juyo sai tag a fatsima a guje tana murna.

Ta iso inda kaltum ke tsaye ta mika mata kudi, kaltum ta mika hannu ta karba a sanyaye, sannan ta tambaya cike da mamaki, “waye ya bani”!
Fatsima ta yi dariya ta xaro nata kudin t ace, “ashara jine ya bani, ke kuma ashirin jine y ace in kawo miki.”
Kaltum ta tabe baki sannan ta yi mata tambaya, bad an bata ta sani ba sai don ta ja mata kunne.
“waye ya ba mu kudin!”
Fatima tace, “Abbas mana”.
Kaltum ta ci gaba da Magana cikin fushi da cewar, Abbas ya fita harkarta, ba ita bas hi, ya sami dama ne daga wajen fatsima dab a xai ci gaba da nace mata ba.
Fatsima t ace, ita kuwa ko yanxu idan ya bas u kudi sai ta karbo musu sai dai idan ta bata ta xubar.
Fatsima ta ci gaba da yiwa kaltumtsiya tana cewa, “duk wnnan fadan da kike yi, ban ga kinyi wurgi da kudin ba a damke a hannun ki yake.”
Sai kaltum ta sake damke kudinta b a tare da ta kara cewa uffan ba. Ba ta son Abbas, amma tana da bukatar taimakonsa.
Fatsima ta dinga yi wa kaltum tsiya don t ace bat a son kudin, amma shiru kake ji bat ace komai ba. Suka isa famfo suka wanke kayan miya, sannan suka nufi kasuwar adare don su sayar. Yau bas u dmu da sai sun siyar da tsda ba, saboda aljihunsu da nauyi, kudin da Abbas ya bas u ya ishe su cin abincin yau hard a nama da lemo.

Da rana suka tafi gidan jawahir mai kunshi kamar yadda ta umurce su bayan sallar axahar xa su dinga xuwa saboda mai gidanta bai yarda ta fara xaman kunshi ba sai t agama aikin gida kakaf.
Jawahir tana murna da xuwan kaltum matuka, saboda kaltum ta iya kitso ashe, tabbas xata kwashi kudin kitso. Kaltum da fatsima suna taya ta aikin gida, ko rainon yaranta, suna tayata da wanke lalle idan ya yi da shafa mahallabiya, ko su hura mata garwashi idan xata yi wa mata dukkan.
Ba sa barin gidan jawahir sai bayan sallar isha’I, bayan tab a su abincin dare sun cika cikinsu, sun share mata gidanta tas! Sannan su nufi gida.
A halin yanxu sun rage tafiya markadi tsintar rubabbun kayan miya, saboda dan kudin da suke samu daga wajen jawahir. Babu laifi tana biyansu duk da dai aikin da suke shirga ya fi kudin aikin yawa, tana bas u abinci anda shi ne babbar matsalarsu. Kaltum mai farin jinni, ladabinta da kwaxon aikinta gami da fara’arta sun sa wadanda ta ke yi wa kitso da wankin lalle suna kaunarta, har suna yi mata kyauta akai-akai.

Allahu Akbar! Allah ma ji rokon bayinSa, Allah Yana taimakon duk wanda ya tashi ya neama, haka Yan a bawa duk wanda ya roke Shi. Babu talaka sai mai matacciyar xuciya. Allah ba Ya hana bawanSa lomar da xai kai bakinsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.