Complete Hausa Novels

Adon Dawa Complete Hausa Novel

Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 10

BABI NA GOMA SHA HUDU

ranar wata talata da misalin karfe uku na yamma kaltum ta dira a kofar gidan alh Tasi'u tsohon mijin Madina,
kaltum sanye take da riga da wando sai dan hijabi shine kayan makarantarsu sai bakin kamvas da farar safa, katuwar jakar littatafanta ta baro a mota da direba a jikin wata inuwa yana jiran ta, tafiya take tana sanda kamar wacce take tsoro kada akamata
kokuma ince mara gaskiya sai taji tafiya ta bayan ta a lokacin da tashiga zauren gidan tayi firgigit ta waiga ta bayanta wata yar matashiyar yarinya tagani wacce shekarunta bazai wuce shekara sha biyu ba amma kallo daya tayi mata taga kamar Madina, babu tantama yarta ce kaltum taji zuciyarta ta harba don fargaba yadda take duban yarinyar haka haka itama yarinyan take duban kaltum cike da mamaki, kaltum ta fara magana cikin tuntuben harshe batare da tasan abun da zatace ba tace yarinya nanne gidan alh Tasi'u ?

Ta gyada kai ahankali tana mai duban kaltum a tsorace nan ne.
yaya sunanki ?
Kaltum ta tambaya,
cike da murmushi sunana shahida ta amsa mata, sai kaltum ta daina kokonto ta gasgata wannan itace yar autan Madina.

daga makaranta kike ?
Inji kaltum, shahida ta gyada kai tace eh, kaltum ta lura shahida a tsorace take da ita domin idan ta matso kusa da ita saita ja da baya kokorin guduwama takeyi, kaltum tace da ita toki gaida yayyanki Abdul hakim da Abdul Malik, sai shahida tasake dubanta cike da mamaki ta amsa da cewa to zasuji yayinda ta wuf ta fada cikin gida da sauri,

kaltum ta gaggauta barin zauren don kada
taje ta kirawo yan gidan su fito a tutsiyeta da
tambaya ace meya kawota ?
Tana fito wa sai ta dubi katafaren gidan da yake jikin gidansu shahida tana ganin sojoji biyu suna gadi ta gasgata nan gidan General Tukur, gidan su marigayi Abba taci sa a aka wangale get din gidan yayinda wata dambasheshiyar mota kalar (blue black)ta fito daga cikin gidan wani zankadeden saurayi ta gani a cikin motar sanye yake da jeans da tshirt baka hade da wani bakin glass a idanuwan sa, kallonda kaltum take masa na kwakwap shiya jowo hankalinsa ga dubanta shima har ya rage gilashin wundo ya rage tafiya suna kallon juna, kallon mamaki har sunkuyowa tayi tana lekensa bayan ya wuce ta, yayinda shi ma ya saita gilashin mudubin motarsa yana hangenta don yaga me take nema, wacece ita, kuma can yaga ta je a hankali ta leka get din gidansu, sai yaga ta da ka tsalle ta labe da alama ta hango wani da ga cikin gidansu yana tahowa, tabi jikin katangar tana shafawa a hankali yayinda takara dawowa kofar gidansu shahida ta tsaya ta dade sannan ta tafi, yana kallonta ta nufi wata camry ruwan silver ta bude kofar baya ta shiga ta kame direba yaja suka tafi, mamaki ya kama saurayin nan sai yaji ya fasa zuwa unguwan ma gara ya dawo gida domin ya tsorata da yarinyan nan yar makaranta tunda yake ko a hanya bai taba ganin mai kama da ita ba, yayi kwana ya juyo kofar gidansu masu gadi sukayi sauri suka
bude masa get sai ya canja shawarar shiga gida sai yaji gara yabi bayan yarinyan nan yaga daga ina take kuma me tazo nema a gidansu,?
saidai kash da yabi inda sukabi sai yaga wayam ko gabas ko yamma baiga ta inda sukabi ba ya dawo gida cike da mamaki shi kadai da zuciyansa ba tare da yasan yanda zai baiyana wa wani ba,

kaltum ma ta dawo gida cike da tsansar damuwa da nadamar meyasa bata bi shahida ta shiga har gidan Tasi'u ba, ta bayyanawa 'yayyan shahida inda mahaifiyarsu take kuma meyasa bata tsayar da dan saurayin nan ba, da alama dan gidan ne kanin Abba ta sanar musu labarin da Madina ta bata akan hakikanin gaskiyar abunda ya faru cewar Madina ba mayyh bace, ba ita ta kashe shiba kamar yanda suke zarginta, ta kuma fada musu inda Madina take dakuma wahalarda take ciki sai ta tuna sojoji ne, daga sanda basu gamsu da bayanintaba zasu iya afka mata da duka,
yini guda kaltum tayi cikin damuwa ko abinci takasa ci da zarar kuka yazo mata saita shige bandaki tayi ta wanke fuska ta fito bataso kowa yagane abunda yake damunta saboda babu wanda yataba tambayarta labarin sudan a cikin iyayenta.
da yamma makarantar islamiyyah take zuwa ita da kannenta dayake acikin unguwar makarantar take da kafarsu suke tafiya yayinda direba ya ajiye mota ya tafi gidansa aikinsa na ranar yakare indai ba oga Adnan bane ya aikesa cikin gari wajen yan uwansa ba sai dai ko madam salaha ce ta aikeshi gidan kawayenta ko en uwanta itama.

tafiya tayi tafiya kaltum tayi shekara da dawowa daga sudan haka har ta gama aji hudu tashiga aji biyar, ta sake gogewa ta waye saboda wayayyun kawayenda tayi a ajinsu kusan duk abunda suke dashi tana dashi saidai inbata fadawa daddy ba zai saya babu musu, kama daga sutura zuwa jaka da
takalmin makaranta masu tsada kayan kwalliya irin su hoda jan baki da sauransu,
aranar wata asabarce yan aji shida masu fita suke bikin fita (send up)amma da kayan gida kowacce taje dan haka kaltum tasa dandashen leshinta ruwan zuma mai fulawa koriya, anyi mata dinkin matsattse na riga da siket yayinda tahau kan wani dogon takalmi (high hill) saita kara tsayi sosai, gyalenta kore ne ya shiga da adon leshin yayinda jaka da takalminta suka zama ruwan zuma, ta dandasa wani farin gilashi a fuskarta, yalo-yalon gashin kanta yazubo zuwa keyarta, tayi fari jawur da ita saikazata idan kayi mata hausa bazata amsa ba, sun sha party anyi bayanai sannan akayi ciye-ciye da tande-tande bayan an cashe sai aka watse.
direba najiranta a mota don haka tana fitowa tafada mota bayan ta gaisheshi cikin ladabi sai ta shaidamasa unguwan yankaba takeso suje , tana fadar haka yasan inda take nufi domin sun doshi shekara suna zuwa kofar Tasi'u su tsaya tayita leke-lekenta su tafi wani lokacin ne idan sunga yarinyan nan shahida ta kirata tabata alewa su juya su dawo,
abun ya dade yana cinsa arai idan yayi alamar zai tambayeta saiya fasa domin kusan kullum idan sukaje gidan a hanyar su ta dawowa kuka ta keyi shi yasa ma baya samun damar tambayar ta, a yau kuwa ya sami damar jero mata dogayen tambayo yi a jejjere saidai kash guntayen amsoshi take bashi ya dubeta ta madubi yayi murmushi yace kina nufin wannan gida damuke zuwa bakya shiga?

kaltum ta gyada kai tace eh nan ne.
yayi murmushi yace yau dai zaki shiga ciki ko?
wannan karon ma gyada kai tayi tace eh zan shiga, Danladi ya fahimci kaltum bata son tambayoyin nan don haka sai yayi shiru.
a inda ya saba ajiyeta anan suka tsaya wato karkashin wata katuwar bishiya dake kallon kofar gidan Tasi'u, kaltum ta bude kofar mota amma bata fita ba, idonta ne cak akan kofar gidan Tasi'u tana fatan kuma tana addu'ar Allah Ya fito mata da Shahida,
Allah mai karbar addu'a sai ga Shahida ta fito burum daga gida sanye da hijabi kuma rataye da wata jaka mai kama da buhun sikari da alama makarantar islamiyyah zata tafi, idon shahida akan motar su kaltum a inda idanuwansu ya kyallaro junansu sai su kayi wa juna murmushi a lokaci guda.
kaltum ta daga mata hannu alamar kira babu
kokonto a zuciyar shahida saita tunkaro inda kaltum take zaune wato a cikin mota tana isowa saita zube akasa ta kwashi gaisuwa, kaltum tayi caraf ta dagota tsaye yayinda take rike da hannunta tana mai ambaton sunanta, shahida kin ini lfy?
ina zakijene da rana fatso-fatso?

shahida tayi dariya, islamiyya zan tafi.
kaltum ta tambaya cike damamaki islamiyyah da rana bada safe ko yamma ba?

shahida tace ina zuwa da safe duk ranar asabar da lahadi a taso mu shabiyun rana mu koma tahfiz karfe biyu zuwa hudu na yamma sannan bayan magrib muje na dare.

kaltum ta gyada kai tace lallai ashe yanzu kinkusa saukewa ki zama malama kamar mamarki?

shahida ta dubi kaltum cike da mamaki domin a iya saninta matan babanta dukkansu biyu jahilaine, to wacce mamar ta take nufi?

ta rike hannun shahida tace kinci abincin rana ko?
shahida ta girgiza kai tace a'a ba a gama ba
shine na taho karna makara idan na dawo zanci.

kaltum tace haba dai ya za'a yi ki iya karatu cikinki da yunwa?
shigo mota kici cake da meat pie da lemo a wajen party aka bani, shahida tashiga bayan mota kusa da kaltum ta zauna,
kaltum ta jawo ledoji dake ajiye a gefenta ta mika mata guda biyu kowanne akwai dankwalan cake da meat pie ga lemon kwali da daurin cin-cin,
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa daga yadda take cusawa kasan tana tsananin jin yunwa.
.
Allah sarki, dan halak baya manta alkhairi, ko sharri aka masa sai ya saka da alkhairi, ku dubi yadda kaltum ta sakawa Gg Ftt da alkhairi akan tsiyar da ta mata, haka ma kala,
Kuma ku duba yadda ta sakawa Madina da alkhairi akan erta da irin alkhairin da ta mata.
Da patan xamu ke lura da duk wata gaba na wannan littapin mai kyau domin mu dauka, kuskuren cikin sa kuma mu nemi tsari wajen Allah da kiyayewa. Kamar yadda yau kaltum tayi shigar ta bai dace ba, kamata yayi ko wace irin sutura ta sa ta dauko hijabi ta daura akai ba gyale ba, yadda xai suturta ta a ko ina kuma a ko wani irin biki.

Allah Ya sa mu dace.
Aamiin.

.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 34
.
TRUE LIFE STORY
.
shahida ta tsinci kanta cikin farin ciki ta karba ta fara turawa, daga yadda take cusawa kasan tana tsananin jin yunwa. dakuma marmarin abunda takeci don bata saba ci ba,
tausayinta ya kama kaltum saitaji kwalla ta cika mata ido tana tuna sanda Madina take ciyar da ita asanda takejin yunwa, Allahu akbar, haka duniya take duk abunda ka shuka shi zaka girba idan ka shuka alkhairi shi zaka girba idan ka shuka tsiya ita zaka girba ta bibiyeka 'yaya da jikokin ka,
Madina ta taimakawa miskiniyar yarinya alokacinda take da iko da halin taimako yanzu ga yarinyar tazo ta taimaki yar miskiniyar yarta ba tare da ta taba zaton ko amafarki kaltum zata hadu da ire-iren zuri' arta ba,
kaltum kallon shahida kawai takeyi tamkar Madina take gani a idanuwanta sbd kamarsu da sak hatta farcen yatsun hannunsu iri daya ne, maganarsu, kallonsu, dariyarsu duk iri daya, kaunarta ta sake harde zuciyar kaltum kamar yadda takejin Madina a ranta, shahida ta lura kallon yayi yawa saita fara takura tanajin kunya,
kaltum tayi sauri ta kawar da idanuwanta kasa, can ta dago ta dubi shahida tace ina Mamar kine?

shahida ta kora lemon kwali tace tana gida.

kaltum ta girgiza kai tace ba sa'ada ba ina nufin mamarki data haifeki Madina.

shahida ta dago da sauri ta dubi kaltum yayinda ta tsaya cak daga abunda takeyi tajima bata iya cewa komai ba sai ta fara magana cikin sanyin murya tace mamana Madina ta bata an rasata.

da kaltum ta fara hawaye sai shahida ma ta fara kuka,
kaltum ta dafa kafadarta tace shahida daina kuka mamarki bata mutu ba tana raye kuma bata bataba tana nan.
shahida ta zubawa kaltum ido tana mata duba irin na karyatawa,
kaltum ta sharce hawaye tace kinaso kiganta?
shahida ta girgiza kai tace nasan bazan taba ganinta ba don bazata sake zuwa ba har abada,
kaltum ta gyara zama tace meyasa kika ce haka Shahida?
shahida ta sunkuyar da kai kasa tace ance mamana mayya ce ita ta cinye yaya Abba.

kaltum tayi caraf ta toshe mata baki tace karki sake fadar wannan maganar, kada kisake fadawa kawayenki wannan maganar
sai ayi miki gori, sharri ce akeyiwa mamarki, Madina macece mai kirki ga hakuri Allah zai wanketa in sha Allahu daga sharrin da akayi mata, kada ki fitar da rai zaki sake ganin mahaifiyarki don haka kiyita addu'a Allah Ya dawo miki da mamarki kema ki zauna da uwa kamar sauran kawayenki.
hawayene kadai yake kwaranya daga idanuwan shahida sai gyada kai kawai takeyi, kukane yakecewa kaltum harsaida danladi yayi magana don tausayinsu don tun dazu yana zaune agabar mota yana sauraron su yaji hawaye ya cika masa ido yace kaltum yayakike kuka keda kike lallashinta ai saiki tayar mata da hankali idan taga kina kuka.

get din gidan general tukur aka bude wannan karon ma zukeken saurayin nan ne ta ranan idanuwansa kiri-kiri akan kaltum da shahida kamar yadda suma suke duban sa har ya wuce su, saiya dannan rivas ya dawo baya yazo dai dai inda suke ya zuge gilashin wundon kasa ya kwalawa shahida kira a fusace,
shahida tahau karkarwa ta fito da sauri ta nufi wajensa sai kaltum taji ta tsorita ganin yadda yake harararta saita rufo kofar mota da sauri tacewa danladi direba ya fizgi mota su kara gaba don haka yakara tabbatarwa basuda gaskiya kuma bada alkhairi suke tafe ba saiya tsorata musamman daya tambayin shahida tace bata santa ba, batasan sunanta ba kuma gashi kullum sai ta zo ta kirata tana bata alewa ko biskit kuma tana tambayarta ina mamarta Madina?

ANAN MUKA KAWO KARSHEN LITTAFI NA 3

Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu muci gaba.
In kuma naga da masu so da yawa , akwai bonanza daya a kasa sai mu ci gaba anjima.
.
Saady Dan AuntyADON DAWA

LITTAFI NA HUDU

TRUE LIFE STORY

NA JAMILA UMAR TANKO (JUT)

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.