Adon Dawa Complete Hausa Novel
Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 10
BABI NA BIYU
Yan asalin garin bur sudan wasu ne da ake kira jange, akasarinsu ko ma ince dukkaninsu bakake ne wulik wulik masu tsananin tsawo da bakar fata wacce hakoransu ne kadai fari a jikinsu hatta kwayar idonsu jajaye ne ba fari ba,. Ba musulmai ba ne, don haka basu da tausayi ko kadan babu abunda suka sani sai fadace fadace, yanxu nan sai kaga fada ya tashi a junansu ko da wasu kabila daban saisu dauko wuka su soka ko su fardewa mutum ciki.
Fada na tashi xa ka ga sun fasa kwalba sun sokawa mutum don haka suka xama abun tsoro, abun kiyayewa da taka tsan tsan suna Gadara suna yiwa baki abunda suka ga dama saboda garinsu ne babu mai hana su. Ga su yawancin su shanmashune ma’ana ‘yan shaye shaye ne baya ga bin mata da suke yi, su danne su a lungu. Don haka hatsarin xaman su kaltum agarin nan ya karu.
Gidajensu ko ma in ce dan karamin kauyensu yana bayan gidan su kaltum, da akwai yar tafiya maidan nisa kasancewar gidan su kaltum su kadai ne a unguwar daga su sai ruwa a gabansu, gefensu na hagu bola ce babba, gefensu na dama makabarta ce katuwa wacce ta bullo har cikin gidansu. Bayansu kuma gidan karuwai ne da ‘yan shaye shaye. Duk ranar laraba jami’an tsaro na kawo surname suna cafke karuwai suna sakawa a mota suna tafiya dasu dan haka su kaltum basa tausayin xuwa ko bita wajen don kada kamen ya shafe su. Idan aka kama su hukunta su ake yi sosai sannan a dauresu a kurkuku.
Baya da garin jange sai kuma garin ADON DAWA suma kauyensu na gefen kauyen ‘yan jange. Sunan Adon Dawa ya samo asali ne daga wajen hausawan da suke xaune a nan, sun saka musu suna Adon Dawa saboda su wata kabila ce a cikin dawa suke xaune. Sun yi kama da bararoji, suma yarensu daban ba larabci ba ne, haka ba yaren jange ba ne, yaransu daban ne amman suna jin larabci. Akasarin su ba musulmai ba ne, amma suna da musulmai da yawa a cikin su. Arnan cikin su a shekara sau daya suke canja kayan jikinsu matansu da maxansu, yaransu da manyansu sai shekara ta xagayo. Suna da kyau sosai sun fi jange duk da suma yawancin su bakake ne amma suna da dogon hanci da gashi mai laushi ga tsawo.
Suna da kudi sosai amma kudinsu bana ci ba ne, saboda suna shiga manyan burane su gina tsala tsalan gidaje masu kyau na xamani da kudin su saisu xuba ‘yan haya sannan su dawo dawa suyi gidan katako su xagaye da kaya su xauna a ciki. Babu wani abu da xa’a iya dagawa a gidan a sayar dashi naira dubu daya, babu gado, babu katifa balle kujeru. Sai daisu xagaye dakunan su da tobe wato lafaya sai gadon karfe wanda aka yi tsakiyar da igiya babu xancen katifa akai sai tsummukarai. Yawancin kayansu bakaken yadi ne maxa su dinka ‘yar shara da wando iya kwairi, su hada da bakin rawani. Mata kuwa rigace shimi da xani da katon mayafi ko lafaya saisu yane jikinsu.
Baya da ginin gidajen da suke yi a burane su xuba ‘yan haya suna da sana’o’I kala kala, wasu suna da shanu don haka suna samun madara saisu xuba madara a doguwar buta maidan karamin baki ta tasa ce amma an yi mata kira kamar ta tulu, sai suyi ta jijjigawa har sai ya xama nono sannan su dora butocin akan jakuna su shiga gari su siyar, wasu kuwa a kasuwa suke sayar da dabino, namijin goro ko hatsi.
Su na da kasuwansu a tsakiyar kauyensu mai suna jim arab, ko da yaushe suna siye da siyarwa musamman da yamma. Yawancin abunda xaka ga ana yi a cikin kasuwar shine caca, kungiya kungiya sai kaga suna caca, suna yi suna shewa, ana ihu, suna ta shan taba da jabna.
Jabna, wani shayi ne da suke sha a dan kankanin kofi. ‘ya’yan jabna kanana ne koraye, saisu soya shi ya xama baki sannan a daka yayi laushi sai a kwarara ruwan xafi a xuba dan sikari ko a shah aka. Idan ka sha jabna xaka ji tamkar ka kurma ihu saboda bauri da daci gashi baki kirin sai daisu da suka saba sha ya xame musu tamkar naman kaxa ko soyayyen kwai don dadinsa da suke ji. Sun xamarda shi tamkar abincin su don da yawan su suna sallama abincin shi kadai suke sha saisu kora da taba shi yasa dukannin su suke sirara mararsa kiba sai tsawo tsigigi. Yini suke suna dafa jabna akan garwashi a cikin ‘yar buta suna xubawa a ‘yan kofuna suna sha iyakacin jin dadin rayuwar su kenan duk da tarin dukiyar da Allah Ya basu basa ci a cikin su ko su saka a jikin suba.
Daga nan kuwa tafiya ce mai yawa xuwa babban garin wato sudan bahari, inda suke da gine ginen siminti da benaye manya manya, titian da tsala tsalan motoci, manyan shaguna da wuraren cin abinci masu kayau, ga kasuwanni manya manya. A nan kasuwar hausawa take mai suna hajarar ases, anan xa ka ga hausawa burjik sai ka rantse a kano kake , matansu da kuma maxansu da kuma yarans. Mata na sayar da abincin hausawa iri iri, irinsu tuwo, kunu,koko,kosai, shinkafa da miya da salad. Maxa kuwa wasu suna yin kaho irin wanda ake kafa kahuhuna a bayan mutum a tattaro gurbataccen jinni sai a dan tsatstsaga a xuke gurbatacen jinni. Wasu na yin aski, wasu na sayar da magungunan gargajiya. Sunan kudin da suke kashewa ‘sudan jine’ misali kamar naira dayanmu saisu kuma su ce wahid jine.
.
AlhamduLillah,
gida yana kan parpadowa, naga mutane da dama sun bada gudumowa wajen comments da likes.
Naga sunan koma kuma nima na danbara masa like....
Godia ta musallam gare ku duka...
Ga wanda basu samu damar yin commnts ba, dan Allah yau a daure ayi koda kalma daya ce,
kowa da tasa uzurin, ban san mai yake hana ku ba, to idan baza asamu damar commnts ba pls a daure ayi like ko share kapin a pita, yazama kowa ya bada tasa gudumowar.
Ku tuna idan babu ku babu mu,
idan bakwa nan babu admin din da zai iya post, kuma haka idan babu mu babu mai karatu a cikin gidan nan,
ina kara rokon ku da kowa ya bada tasa gudumowar pls....
Sai kun jini dauke da wani sabon shirin..
Sai na gan ku....
.
Typing : Sadin Maa.
Post : Dan Aunty.❤ADON DAWA 3