Complete Hausa Novels

Adon Dawa Complete Hausa Novel

Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 10

BABI NA GOMA SHA DAYA.
BUR SUDAN.
Rayuwar mambela da madina a bur sudan ta xama tamkar gayan tuwo ne marar miya cinsa haka babu dadi. Haka suke rayuwa amma xukatanu babu dadi saboda rashin kaltum din su.
Mambela ya fada ya sake maimaitawa, yyin day a lailayo rantsuwa yam aka a cikin bayanansa a dai dai lokacin day a tara ‘yan gidan su madina kakaf kofar gidan su da sanyin safiyar wannan rana. Yana Magana hawaye na yi masa tsartuwa, hakika daga jin kalamansa xaka tabbatar a cikin matsanancin fushi yake Magana da matukar damuwa. Tabbas babu maganar wasu a cikin lafaxansa, Magana yake cikin gadar da basu tabbacin xartar da hukunci mai tsanani akan duk wanda ya karya masa doka. Ba wai rokarsu yake das u bi abunda yake umartar suba, har ya fi son kada su bi don ya yi was an kura das u.

Ya dube su daya bayan daya ya kawar da ido gefe, yayin day a runtse ido ya xubar da hawayen day a cika masa ido, ya fada cikin harshen larabciwanda yake tunanin kowannen su xai gane, wanda bai gane sosai bad an uwansa xai fassara masa.
Ya ce, “yan Nigeria da niger a da ina sonku fiye da yadda nake son yan kasata sudan. Amma a ynxu bna son ganinku, ban ki in bude idona in ga an kwashe ku ba kada a bar mutum daya saboda xamanku a kusa da ni babban fami ne a cikin xuciyata.
A duk lokacin da nag a irin ku, ko na ji yarenku na hausa sai gabana ya yanke ya fadi, in ji xuciyata ta buga saboda kuna tuno min da KALTUM. Da xarar na fito da safe na hango ku kun fito da kayan sana’arkukamar haka, sai in ga kamar xan hango kaltum a tsugune a can tana wanke-wanke.”
Se ya nuna gefen da madina ke xaune, yayin da kuka ya kece masa, kuma ya kecewa madina.
(NIMA SE DA MAJINA YA KECE MIN)
Mambela ya cije leben ya ci gaba da cewa, “kun ci manata da ku ka bar kaltum ta tafi Nigeria, aka rasa mutum daya da ai tashi ya ruga ya xo ya sanar da ni halin da ake ciki, haka kuka kori yarinyar nan, ku kuma kuka mike kafa a kasarmu. To ba ku isa ba, yadda kaltum ta bar sudan sai kun bar sudan, yada na rasa farin cikin rayuwata, sai kun rasa farin ciki kuma.”
Hankalin kowannensu ya tashi, kana dudan idanuwansu xaka ga sun firfito waje don fargaba.
Kalmar “ma’alesh, ma’alesh ya mambela”. Suke Ambato.
Ma’ana kayi hakuri kai mambela. Sai Kalmar ta xame masa tamkar ashar suke danna masa saboda masu iya magan na cewa, da xarar an fara ba ka hakuri to tabbas an cuce ka.

Ya daka musu tsawa cikin fushi, y ace, su rufe masa bakin su, bay a bukatar bada hakurin su. Tsit kake ji ko tari babu wanda ya sake yi.
Ya share hawaye y ace, “ba ku da imani, ba ku da tausayi, ko wannenku yasan tsakanina da kaltum kun san babu abun da na fi so a duniya irin kaltum ba ni da Magana sai ta kaltum, haka ba ni da wurin xuwa sai ajen kaltum. Ina kwance ba ni da lafiya kaltum ta o ta duba ni, a ranar na kai ta wajen mai martaba ya yaba da hankalinta, tya amince min in aure ta. Mun fara shawarar yaya xamu je kasarsu saboda madina t ace, sai na je gaban iyayenta xan aure ta, tana barin gidan mu kuka tura keyrta ku ka kore ta.
An fada min tana kuka bata so ta tafi, madina kika hada mata kyat a tafi, to ku sani babu ku babu xaman lafiya a garin nan. Kaltum ta tafi ta bar ni, ban san ta inda xan fara nemo Nigeria ba, da garin da kaltum ta ke a Nigeria.
Ni mambela na yi alkawarin takura muku, kun daina walwala kamar yadda na daina, ciwo nake yi a kwance a ranar da kaltum ta xo duba ni, na warke da nag anta, daga lokacin da na ji an dauke ta a lokacin ciwona ya dawo har yau na kasa samun lafiya. To daga yau kun daina xaman lafiya don duk sai na kakkarya kafafuwanku daya bayan daya.”

Kiri-kiri suke yi da ido, yyayin da kowannensu yah au kammala sangalalinsa kada a fara ta kansa. Madina kuwa ta yi tsuru a gefe kanta a sunkuye a kasa, tasan kowanne hukunci xai xartar daga kanta xai fra, don haka ta fara tunanin inda ake siyar da sandar guragu, gara tun da wuri ta tanada.
Mambela ya ci gaba da Magana cikin kakkausar murya, y ace, “babu sana’ar sayar da komai a kofar gidan nan, haka kada inga kafarku a bakin kogi, wajen kamun kifi. Haka kada inga kafarku a kasuwarmu jim arab, kad a wata ta xo garinmu bara, sai na karya duk wanda ya saba wannan doka. Sannu a hankali idan yunwa tai she ku xaku tarkata ku tafi inda kuka fito, yadda kaltum ta tafi ta bar ni.”
Malam nura wani tsoho daga cikin su madina xai yi Magana, mambela ya dunkule hannu xai kai masa bugu, abokansa da ke tsaye a gefensa suka rike shi. Suka ja shi suka tafi, da kyar mambela yake daga kafarsa don tananin tashin hankali. Ya rasa akan wanda xai huce, takaicin rashin kaltum amma ya fi jin haushin madina wacce ta hana su su yi aure tuntuni. Sannan da yaradarta aka dauke masa kaltum dinsa.
Suka rushed a kuka suna kiran, sun shiga uku sun lalace, ya ya xa su yi su rayu idan ba sana’a, ba bara! Madina ta mike a fusace ta fara Magana cikin fushi.
Ta ce, ‘haba jama’a kamar ba musulmai ba, kun manta Allah ne mai rayawa, Shi ne mai kashewa!kun manta Shi Ya ke tsare mutum, Ya yi masa Katanga da duk wani mugu! Ko gexau ban yi bad a mambela ya hana mu sana’ar da xamu ci abinci, Allah da Ya haliccemu Shi xe fito mana da wata hanyr da xa mu ci abinci mu rayu. Jahilci ne ku dinga kiran shiga uku, ku kira Kalmar “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah Xai yi mana jagora.

Ko me ya samu bawa mukaddari ne, shan ruwan kaltum ne yak are a bur sudan dole ta tafi, da shan ruwanta yak are a duniya da wayar gari xa a yi a tarar ta mutu ma karewar tafiya Nigeria.’
Sai suka ji xuciyar su ta yi dan sanyi, sannan kowannensu ya dinga kinkimar kayan siyarwarsa yana shiga gida don kada mambela ya xagayo ya iske su a kofar gida sana’ar yau dai ba a yi ba. Sai asarar da suka yi, saboda mai kosai ta yi markade, mai koko ta dama, haka mai danwake ta kwaba, har gara ma masu shayi da biredi ruwan xafi ne kadai da lipton suka dafa.
Kwanaki biyu haka su madina suke xaune babu mai sayar da komai, babu bara, babu xuwa kogi kamun kifi har sun fara jin jiki.
“mambela ya cuce mu, mugu marar imani”. Kalmomin da suke ta nanataw ken an, duk dakin da ka xo giftawa xaka dinga jiyowa. Suka ga Magana, xage xage a bayan fage ba xai yi musu magani ba sai suka shiga tunanin hanyar neman sulhu, domin komai da sulhu ya fi sauki.

Shawara day ace suka tsayar, maxa su hadu su yi kungiya su je su sami mai martaba sarkin ADON DAWA su kai kukan su, ba kuma karar mambela xa su ce sun kawo ba, a’a neman a rokar musu mambela ya taimaka ya janye takunkumin day a yi musu, ba laifin sub a ne da kaltum ta tafi suma bah aka suka so ba.
Haka aka yi said a suka tabbatar mambela ya fice, an tabbatar yana jim arab shi da abokansa suna shan jabna sannan suka dunguma suka tafi fada, da kyar dai aka yi musu iso, suka fadi gaban sarki suka yi gaisuwa cikin yaren ADON DAWA, sannan suka koro masa bayani cikin harshen larabci don shi suka fi iyawa. Suna gama bawa sarki labara sai ya bushed a dariya ya fada a bayyane har sau uku, “mambela! Mambela!! Mambela!!!”
Ya ce su tashi su tafi duk su fito da kayan sana’ar su, xa su iya xuwa bakin kogi, haka xa su iya xuwa jim arab ba damuwa. Babu abunda mambela xai yi musu, su kwantar da hankalinsu xai yi masa Magana har sai ya huce, daman kuma xafin rabuwa ne.

Godiya suke, addu’ar fatan alkhairi iri-iri suke jerowa sarki. Suka shiga gida suka fesawa mata bayani, yayin da buda da kidan kwarya ya gauraye gidan nan da nan aka sami masu taka rawa mata da maxa.
“ga mambela nan da tawagar san an xuwa”. Inji walidi ya rugo da gudu daga kofar gida.
Gudu da buga kafa a jikin katako kararaf ka ke ji ana karo, yayin da aka yi cilli da kwaryar kida. Wasu suka shige dakuna yayin da wasu bandaki suka cunkusa suka rufe kofa, wasu kuwa da suka gudu suka buya, ashe karya yake yi, xolayarsu yake. Dariya hard a faduwa yake yana fadi, “wasa ne ba mambela ba ne”.
Ran kowa y abaci suka firfito daga maboya suna masu jan Allah Ya isa, saboda tsorata su da yayi, har wasu da yawa sun karkace kafa da jinni.
Washe gari da safe aka rasa wanda xai fara fitar da kayan sana’arsa, kowa ya fito da kaya tsakar gida amma sun kasa karaswa kofar gida. Wannan ya leka ya dawo, wancan ma ta leka kofar gida ta dawo daga karshe aka sami xakakura daya ta fara firfita da kayanta, it ace madina, sannan sauran suka fara firfitar da kayansu su ma. Suna yi suna waige-waige da suka ji shiru sai suka saki jikinsu suka kwantar da hankalinsu, mambela ya hakura.
Kan ka ce kwabo jama’ar jange da ADON DAWA dauke da kwanukansu suka taho siyan abinci domin su ma kwana biyu rashin siyar da abincin ya shafe su.

“ga mambela nan!”. Sama’ila ya fada da karfi, yayin da yake rugawa cikin gida. Dogon tsaki suka yi yayin da ko waigawa bas u yi ba saboda sun san karya ne, tsorata su yake so yayi irin yadda walidi yayi musu jiya.
Dif! Kamar an jeho shi gaban su haka suka ga mambela da tawagarsa a tsaye a kansu. Xancen sama’ila gaskiya ne ashe ba wasa yake yi ba.
Madina bata yi karya ba, Kalmar innalillahi wa’inna ilaihi raji’una tana sanyaya xuciyar mugu ya xamanto mai tausayawa.
Yawancinsu Kalmar da ta xo bakinsu ken an a tare suka fada, kuma a bayyane. Wasu kuwa cewa suka yi, “ihu mun shiga uku, mun gat a kanmu”.
Suka yi wuki-wuki haka kake ganin idanuwansu a waje saboda tsorata.
Ya tsaya cak! Ya na duban rawar jikin da suke yi ba tare day a ce uffan ba.
Malam gali tsohon da yake sayar da goro ya kasa goronsa a fai-fai. Ya ce, “yaro ka yi hakuri, na samo maka labarin kaltum. Kaltum na sudan xata dawo kwanan nan”.
Mambela ya tuntsire da dariyar da bai shirya ba, ya sake kyakyacewa da dariya.

Ya ce, “baba, ka sayar da goronka ba xan hana ku sana’a ba, amma kaltum bat a sudan tana Nigeria. Ko xaka fada min a inda take idan tana sudan!”
Baba ya marairaice y ace, “fada na yi dan ka ji sanyi a ranka don mu ma mu sami sauki”.
Sai gaba daya suka rude da addu’a suna fadin “in Allah Ya yarda kaltum sai ta dawo. Kuma da yaradar Allah kaltum matarsa ce, duk inda take sai ta dawo.”
Mambela ya ji dadin addu’arsu, sai jikinsa ya yi sanyi, ya sunkuyar da kansa kasa yayin da kwalla ta cika masa ido. Ya dade a tsaye yana sauraron dadin bakinsu sai ya yi murmushi ya juya ya dubi madina wacce ke xaune ta sa kaskon kosanta a gaba ta kasa Magana ta kasa sakin kosan sai hawaye take xubarwa kawai. Ya juya ya dubi gefenta sai ya ga kamar xai ga kaltum a tsugunne a kusa da ita tana yi masa murmushin nan nata. Sai ya girgixa kai ya juya ya tafi, yayin da abokansa suka bi bayansa.

Doguwar ajiyar xuciya kake ji a jere a jere. Su madina na yi saboda farin ciki day a same su, sai kiran hamdala suke da godewa mambela.
A yammacin wannan ranar madina ta sami sammacin kira daga mambela cewar, ta same shi a bakin teku. Xuciyarta ta harba, amma sai ta yi addu’a ta xari gyalenta ta tafi ta yrada da cewa Allah xai kare ta, kuma mutum ba xai iya yi wa mutum abunda Allah bai kaddara xai same shiba.
Rayuwarta da mutuwarta duk suna hannun mahaliccinta. Labarin gixo dai bay a wuce na koki, ta san xancen bai wuce na kaltum ba. Ita kuwa duk inda gaskiya ta ke ita xata fada komai dacinta, ba xata fada masa karya ba don yaji dadi. Iyakar abunda ta sani shi xata fada, abun da xai yiwu shi xata fada masa. Haka idan kaltum matarsa ce xai aureta, idan ba matarsa ba ce duk inda ya kai ga mayatar sonta sai dai ya mutu ba xai aure tab a, kamar yadda Abba ya kasance. Har ya rasa rayuwar sa a dalilin damuwar so.

Tana tafe tana matse hawaye yayin da irin wannan kidimewar da mambeala yake yi suke tuno mata da yanayin da Abbanta ya shiga a lokacin da yake raye a sanadiyar so.
Madina ta isa bakin teku ta karasa inda mambela ke xaune turmus cikin yashi yana rike da wani dan karamin kara a hannunsa yana wasa das hi a cikin tashi tamkar yaro.
Ya dago ido ya dubi madina, sai tag a ya yi firgita domin hankalinta a tashe tamkar ta fi shi shiga tashin hanakali. Sai ya yi xumbur ya mike tsaye ya dub eta cike da damuwa ya tambaye ta cike da damuwa da kuma fargabar amsar da xata bas hi.
“madina lafiya!”
Sai ta rushed a kukan dab a ta shirya ba, jikin mambela ya dau rawa, yayi sauri ya warware rawaninsa ya shimfida mata. Ta xauna yayin da shima ya xauna a hankali yana fusakantarta. Ya dafe haba da hannayensa biyu yana dubanta xuciyarsa cike da mamaki da kma faragabar jin abun day a saka ta kuka daga kiranta.
“madina, me yasa kike kuka! Ki kwantar da hankalinki ba cutar da ke xan yi ba, tambayar ki kawai xan yi, kuma in nemi shawarar ki game da yadda xan yi in sami kaltum’. Mambela ya fada cikin sanyin murya.
Madina tad ago da jajayen idanuwanta ta dube shi xuciyarta cike da tausayi. Cikin kuka mai yawa ta fara Magana.
Ta ce, “mambela, ba kukan tsoron ko xaka cutar da ni nake yi ba, nasan ba xaka iya cutar da nib a saboda xuciyoyinmu suna son abu daya, ba wani abu ba ne illa kaltum.

Ina son kaltum, ina mata kaunar da nake jinta raina tamkar ‘yata shahida. Ina tausayin kaltum fiye da yadda nake tausayin kaina. Kana son kaltum na shaida son da kake so ta xama uwar ‘ya’yanka kana so ku kasance tare har sai mutuwa ta raba ku, ita ma na lura tana sonka haka.

Mambela ba xan so in xama sanadin raba wannan kyakkyawar soyayyar taku ba, haka ba xan yi wa xuciyata manakisa ba in raba tad a yarinyar da take kauna tamkar ‘yar da na Haifa ba saboda ba ni da kowa a nan, ita kadai nake gani inji dadi. A duk lokacin da nag a kana tayar da hankalin ka akan kaltum sai hankalina ya fin aka tashi, saboda kana tuno min da Abba wanda ya rasa rayuwarsa a sanadiyar soyayyar soyayya. Mambela na fi son ka bi abun a hankali kada ka halaka kanka akan rashin kaltum”.
Hawaye ya fara kwaranyowa daga idanuwansa, sai ya tambaye ta cikin sanyayyar murya, “madina waye Abba!”
Ta dade tana kuka kafin taiya fara ba shi labarinta. Ta bas hi labarin rayuwata tun daga farko har karshe kamar dai yadda tab a wa kaltum a baya.
Mambela ya dade yana duban madina ya kasa Magana saboda tsananin tausayinta, yayi nadamar takura musu da yayi, yayi nadamar laifinda ya dora mata a game da tafiyar kaltum. Ya tsunduma tsundum! Wajen tunanin yadda rayuwar Abba ta kare, ya kuma sake firgita akan yadda rayuwarsa xata kasance a nan gaba dan ya lura cewar soyayya ba abu b ace da xa’a ce maka ka rage ko ka kara, ko kuma ka daina.
Yana matukar iya kokarinsa wajen cire son kaltum da dannewa amma abu ya ci tura, kullum sonta karuwa yake a xuciyarsa. Ba ya addu’ar haka ta faru, amma daga dukkan alamu haka ne xai faru, yana ganin xai rasa ransa a hanyarsa ta xuwa nemo kaltum kamar yadda Abba ya rasa ransa a hanyar sat a xuwa garin su madina.
Madina c eta katse tunanin da yake yi t ace “abun da nake so da kai , ka yi hakuri, ka yi ta addu’a ka xubawa sarautar Allah ido, Ya yi muku hukunci akan abunda Yak e so.”
Mambela ya dub eta y ace, “ina so ki taimake ni kiyi min alfarma daya bad an kina so ba, sai don ki ceto rayuwata don gudun kada in rasa raina kamar Abba. Ki janye ra’ayin nan naki nab a xa ki kara komawa Nigeria ba har abada, saboda ni da kaltum xa ki janye, mu shirya ki rakani kano in nemo kaltum a jirgi ko a mita, duk wanka kike so.”
Tashin hankali marar musaltuwa xaka iya ganewa daga duban idanuwan madina. Ta ji kirjinta ya harba “bum!” saboda bata kaunar ta koma kano, bat a fatan ta sake yin ido hudu da duk wanda ya santa da.
Mambela ya sake nanatawa, ‘ki taimake ni madina mu tafi a satin nan. Don yau wata hudu da kwana hudu kenan da tafiyar kaltum kada mu dade aje ayi mata miji ko wannan Alh. Adnan din ya aure ta don daga labarinda ta bani na lura yana sonta, damuwar da yayi a kawota na san auren ta yake so ya yi.”

Madina ta ci gaba da kallon mambela tana mamakin yadda ya san labarin Alh. Adnan , tabbas kaltum na son shi da yawa tun da hart a saki jiki take yi masa hira duk wannan xurfin cikin nata.
Can ta nisa ta sunkuyar da kai kasa, don tambayar da xata yi masa ba xai yiwu ta iya hada ido das hi ba, saboda nauyinta, ta tabbatar ba xata yi masa dadi ba.
Ta ce, “misali idan ka je Nigeria aka nemo gidan su kaltum ka ci sa’a ka iske kaltum ka tambayi aurenta, iyayenta suka ki amincewa ko kuma ka je ka tarar har an ba wa Alh. Adnan ya riga ya aure ta. Yaya xaka yi, kuma me ne amfanin xuwanka!”
Kallo daya xaka yiwa mambela ka tabbatar xuciyarsa c eke tafasa saboda xaxxafan kalamanta. Ya kasa ba ta amsar tambayarta .

“mambela ina mai baka shawara ka yi hakuri ka kara hakuri, ka yi addu’a Allah Ya xaba muku abun day a fi alkhairi”. In ji madina.
Ya sunkuyar da kansa kasa saboda takaicin furucinta, don idan ya ci gaba da kallonta xuciya xata iya daukar say a yi mata diban karan mahaukaciya.
Madina ta yi ajiyar xuciya t ace, “a rayuwa babu wanda ya fi mahakurci cin riba, babu wanda ya fi mai tawakkali nasara, haka babu wanda ya fi mai yarda da kaddara morewa a nan gaba. Ka sake hakuri kuma ka tsananta addu’a…..”
Mambela ya katse tad a cewa, “shin xan mike kafa in dinga kallon gajimare ina jiran kaltum ta fado gabana! Ba sai na je nemanta ba Allah Xai dubi xuciya ta sannan Ya amsa addu’ata in nemota ba! Xaki raka ni kasar ku ko ba xaki raka nib a!”

(DARIYA, SU ‘DAN ANTY HO!)

Madina ta yi murmushin karfin hali, t ace, “mambela, ban san kaltum ba sai a mota, haka ban san daga inda ta bullo ba.”
Ya fada a fusace, “amma dai kasarku daya, kuma garin daya, kano ko! Idan muka je kano mun yi mai wuyar. Ni kadai xan iya xuwa kano, amman ban san kowa ba, ban san ko’ina ba, idan babu ke ina nasan hanyar da xan fito daga airport ko tasha! Gara da ke a kalla kin san garin kano, kin san sunan unguwar su kaltum. Kin iya yaren ‘yan garin yadda idan kika tambaya xa a nuna miki. Ban day arena sai larabci nake ji, wanda kun ce ba a larabci a kano sai hausa sai turanci, ni kuma ban iya ba. Shine taimakon da xa ki iya yi min a rayuwata madina.”

Ta girgixa kai ta sharce hawaye t ace, “mambela, ba xan yaudare ka ba, baxan boye maka ba, ko gawata ban a so a kai ta kano saboda abun kunyar da jama’a suka lika min. ka yi hakuri ba xan iya xuwa Nigeria ba, har abada.”
Mambeala ya ji tamkar ta dauko wuka ta kirba a kirjinsa. Ya dub eta, duba na takaici ya cije lebe hawaye yana xuba.
Ya ce, “babu wani taimako ko amfani da xa ki yi min a rayuwata wanda ya wuce wannan, kum kin ce ba xaki yi ba, alhali kina da halin yi min. madina ba kid a sauran amfani a wajena, ba kya kaunar kaltum, ba kya kaunata ki sani duk halin da na shiga ke ce sila. Bana so in sake ganinki a gabana, bana fatan mu sake xama ni da ke irin wanan tun dab a kid a niyyar ceto rayuwata.”
Madina ta fashe da kuka cikin mummunan tashin hankali, don jin kalaman mambela.”
Ya daga hannu ya dakatar da uta, yayin day a nuna mata hanyar gidansu, ma’ana, ta tashi ta tafi. Xata yi Magana ya daka mata tsawa y ace, ta yi shiru bay a bukatar bayananta ta tshi ta tafi kawai.
Madina ta mike cimak ta saka takalminta, t ace, ‘ka yafe min, ka yi min afuwa.”
Ya dago da jajayen idanuwansa ya dubeta y ace, “madina, ba xan yafe miki bat un da kika raba soyayyata da kaltum. Ba na kaunar duk wanda bay a so na tare da kaltum. Ba xan ragawa duk wanda ya raba ni da abar kaunata kaltum ba.”
Madina ta girgixa kai t ace, “Allah Yan a tare da mai gaskiya, Shi xai fitar da ni daga cikin wannan dabaibayi.”

Ta sharce hawaye ta wuce, kamar daga sama ta ji mambela ya kira sunanta. Ta waiwayo a hankali ta ganshi har yanxu a xaune a inda ta bar shi, ya jya mata baya kansa a sunkuye a kasa.
Ya ce, “da aka dauki kaltum daga nan ina aka ce xa a kaita!”
Madina t ace, “jirgin kasa suka hau suka tafi khartum babban birni.”
Ya ce, “khartum a ina, wacce unguwa!”
Madina t ace, ban taba xuwa khartum ba, ban san ko’ina ba, dan haka ban tambaya ba. Saboda bas hi da amfani in sani don an tabbatar min da xarar sun isa khartum ba xai wuce kwana biyu xasu yi ba xa su tafi Nigeria, don kudin jirginta da na ‘yan rakiyarta na hannu an turo musu daga nigeria.”
Mambela ya fada cikin fushi, “bana son bayanan ki, ya ishe ni haka, tafi kawai.”
Xungwi-xungwi ta kama hanyar gida ba tare da sake waiwayowa ba. Mambela yaji takaici a ransa har ya fin a kullum. Ya ji wani tsananin son kaltum ya kara mamaye xuciyarsa. Ya ji ya tsani madina, ya ji daman ace xa a wayi gari a ga gawar sa shi ya fi masa sauki. Ya yi kuka, ya dinga kwalla sunan kaltum shi kadai a bakin teku tamkar tababbe ga magaruba ta yi, duhu ya bayyana. Ya tuna ranar day a tare kaltum a dai-dai inda yake xaune, ranar da ta dinga ynakasa da wuka, kuma a ranar ta fara sonsa.
Bai bar wajen ba said a gari yayi duhu sosai. Ya isa gida ransa a bace. Sallah kadai yayi, ya rufe kansa a daki ya kwanta ba don yana jin barci ba, sai don kawai xuciyarsa ba xata iya jure surutun mutane. Xuciyarsa ta raunana, ji yake tamkar ta hadu da lahani tamkar xata buga.

Sarki ya dinga aike a tambayar masa, anya mambela lafiya ya kwanta da wuri! Ta wundo yake bas u amsa lafiyarsa kalau, barci yake ji.
Talatainin dare daf da asuba sannan barci ya dauke shi, sai ya gan shi tare da kaltum a mafarki suna hirar so da kauna. Farin cikin sa a mafarki bay a musaltuwa, amma day a farka ya ganshi shi kadai ba kaltum a xahiri, sai ya ji tamkar ya kurma ihu don takaici.
“me yasa kika tafi kika bar ni kaltum! Me yasa da aka xo daukarki ba ki rugo kin xo kin fada min mun tafi tare ba!”
Haka mambela yake fada a bayyane a cikin yarensa na adon dawa.

(DAN ANTY, SE YAYA KE NAN! KA HAKURA KAWAI A KAN KALTUM SE NA NEMAR MA WATA KAWAI, KAR A WAYI GARI MAMBELA KO ALH. ADNAN DAYAN SU YA YI NASARA AKAN AUREN TA HAWAN RUWA YA KAMA KA lol)

Typing: Sadin Maa.
Posting: Oga ‘Dan Anty.ninADON DAWA 26
.
TRUE LIFE STORY
.
haka mambela yake ta fada abayyane a cikin yarensa na ADON DAWA.

KHARTOUM

lokacinda mambela yake neman dan rakiya zuwa Nigeria wajen kaltum dinsa ya nema ya rasa badon babu kudin jirgiba ko guzirinda zai rike ba,
ita kuwa kaltum bata bukatar dan rakiyar da zai rakata bur sudan wajen mambela matsalarta shine kudin jirgin kasa take fafutukar tarawa abu yaci tura, duk abunda take samu baiwuci ta ci abinci dashiba sauran tasayi omon wanki da sabulun wanka da sauran su,
idan taci sa a ta tara kudi mai dan yawa tafara tarawa sai wani abu ya bullo mata wanda dole sai takashe kamar sayan magani idan batada lafiya ko idan takalminta silifas ya tsinsinke dole ta sayi wani ko idan rigunanta ko lufayanta sun yayyage dole takai dinki.

yau idan akace maka babu mai taimakonka
kodada loman tuwone komai kaiza nema da kanka to babu sauki, kaltum na aiki tukuru don neman abunda zatasa a yan hanjinta kokuma wanda zata iya shiga jama'a ba a toshe hanciba saboda wari ko datti bata hutawa saboda haka tarame tayi kurket tayi duhu rabonta da kitso tun na bur sudan saboda batada lokaci dakuma wanda zaiyi mata amma ita ta iya kitson har gida gida ake kiranta tanayi ana biyanta.

watan azumi ya kama kaltum bata hutawa yini takeyi tana neman abumda zasuyi buda baki saboda azumi.
yau babu masu zuwa gyaran jiki don haka jawahir ta sallamesu tace su daina zuwa sai a satin sallah sannan zasu dawo saboda haka sukafi mayar da hankalinsu wajen tsinta lemo da abarba sufere wajen rubar sukasa a faranti suje su sayar, kasancewar azumine ba acika sayan kayan miya ba akan da, anfi sayan kayan marnari .
sak almajirai ga yunwa ga kishiruwar azumi gasu sun yini a Kasuwa.

wataran suyi sa'a su sayar wataran su yini suna yawo ba a saya ba, dagaa lasa an ya ruba sai afasa saya daman dai masu rangwamen men kudi ne suke sayen irin wannan masu kudi basa dosar nakan farantin yan talla sai wankanku ajere akan tebur ko acikin firij.
ranarda rana takwabe musu kuwa babu mai saya idan akasha ruwa sai su zauna su shanye abunsu babu kudin cefane bare su dafa abincin buda baki da sahur don haka saisu zarzaya gidanda ake raba sadakar abinci da kwanukansu tun kafin dare yayi abincin sadakan yakare,
kunu dagurasa ko sinasirne sukebin dogon layi ana raba musu shizasuci kobasu koshiba su rage na sahur.
kaltum takanyi kuka cikin dare saboda masananciyar rayuwa da take ciki dumin
a bur sudan tawuce irin wannan rayuwarda ta
fatarar abinci. mambela yakara musu jari ita da madina suna sana'arsu kowannensu abinci ya wadaceshi

sun daina bara asatin da azumi zai kare satin
sallah kenan alokacin watan cinikin jawahir ta
bude ake tururuwan zuwa gyaran jiki da gyaran kai saboda kwalliyar sallah a wannan satin kaltum suka kaura gidan jawahir har kwana suke yi suna aiki saboda jama'a,
dogon layin babu masaka tsinke sakar gidan saboda mata a lokacin kudi yayi ta shigo musu baja-baja duk da jawahir ce mai amshewa,
kalilan da ciki take guntsira musu su ta murna.

wasa wasa kuwa suka tara kudi da yawa ana jibi sallah fatsuma ta shawarci kaltum suje
kasuwa su sayi lafaya da takalmi mai kyau suyi kwalliyar sallah kaltum tace ita tara kudi takeyi akwai abunda zatayi dashi bazatayi kwalliyar sallah ba.

fatsuma tayi tambayarta mezatayi da kudi da har bazata ki sayan sutura da sallah ba wacce ko almajirai suna wanka su canza kaya ballesuda suke kudi mai dama.

kaltum taki fada kuma taki saya fatsuma ce tashiga kasuwa tayi sayayyarta tsaf harda sarka da yan kunne

baya ga lafaya da takalmi coge chanjin kuma
taje kasuwa da ake sayar da wayan tafi da gidan ka (g.s.m)tsohowar waya gwabjejiya wacce aka daina yayinta ta saya aka makala mata sim card yadda zataji dadin waya da musa saurayinda take matukar kauna shima a kasuwar markadi yake dako su suke sauke kwandunan kayan miya daga mota zuwa cikin kasuwa.

ranar sallah kowa ya caba ado cas gwanin sha'awa duk wanda yaga fatsuma sai yayi mamakinta kamar ba fatsumar jiya bace mai
barkakkiyar riga da kanannandaddiyar lafaya
saboda rashin guga kanta duk gunji yau kuwa tayi tsaf bakinta har shekin dangwalin yaba yake.
zanen fuskarta wato bille da uku ukun bakinta sunyi radau saboda jar hoda da ta rarrangada ta dambara baki a bakinta da girarta kaikace tabarya ce masayin kwallin,
ta fito kwas kwas kwas daga dakinsu ta leko dakin su kaltum jama'ar gidansu suka ta mamaki kyawun datayi a yau suna tunanin inda ta sami kudi haka,

fatsuma ta dubi kaltum ta girgiza kai don takaicin kin daukar shawararta datayi datakiyi da tuni sunyi anko yayinda kaltum ta fito daga wanka tana shiryawa a tsaye akan buhun kayanta tsofofin riga da siket ta saka burguza burguza sai ta dauko lafayarta koriya itace mai rangwamen tsufa duk da tawanke tas tayi musu karin guga tana kwana akansu kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sofaffi
ne don haka batayi kyauba surutu da gori babu wanda fatsuma bata yiwa kaltum ba akan taurin kan da tayi nakin yarda da shawararta.

kaltum bata damu ba shirinta take yi kawai ta linke dukkanin kayanta ta cusa abuhun ta hada bakin buhun ta daure tace da fatsuma zo muje waje na fada miki wata magana suka fito kofar gida suka tsaya kaltum ta dubi fuskar fatsuma taga yadda tayi wuri wuri tanaso taji labari saita tuntsire da dariya tace fatsuma yau zantashi daga garin nan zan kaura garinmu bur sudan

kaltum ta dafa kafadarta tace ki kwantar da
hankalinki zan dinga kawo miki ziyira akai akai ko kinaso kibini idan naje indawo in daukeki muje can mu zauna?

fatsuma ta girgiza kai tace bazan iya zama
da wadannan mutanen naku na ADON DAWA ba,

kaltum ta harareta tace ADON DAWA ba mutane bane ko ba musulmai bane?

fatsuma tace ADON DAWA saike nikuwa sai ADON BIRNI sukayi daria dukansu.

kaltum tace don bakisan suwaye ADON DAWA bane kike fadar haka musulman cikin su sunada kirki, kyauta, sadaka, zakka, sallah, azumi, tausayi, sunada ilimin addini,
masu kudi kuma kyawawa hanci zuwit..

fatsuma tace tunda kina son mambela fa ai dole kifadi haka nikuma bana son ADON DAWA,

kaltum tace ashe bakya sona tunda ni inason ADON DAWA, a kabila daga hausa sai ADON DAWA nafi so,

fatsuma tace inasonki tunda ke bahaushiyace amma fa banason ADON DAWA gashi kuwa sun janyeki zaki koma wajensu duk abunda nafada miki kinki ji sai kintafi din,
suka isa tashar da kafarsu duk da nisa basu damuba sun saba da tafiyar kafa basajin wahalarta.
suka jira har bayan la'asar jirgi kuwa sai bayan magarib zai tashi kaltum ta umurci
fatsuma tazauna acikin wata rumfa wacce aka tanadar don zaman matafiya gasu nan reras a zauzaune suna jiran jirgi,
zataje tayi fitsari idan ta gama zataje wajen ma'aikatan jirgi ta tambayesu adadin kudin tikiti da yadda ake sayansa,
fatsuma ta zauna da buhun kaya a gabanta tana duban kaltum hartayi nisa ta daina hangota tadade bata dawo ba sannan ta dawo tana zuwa fatsuma ta mike tsaye tace gida zata tafi saboda tafiyar mai nisa ne, ita kadai kada dare ya mata,

kaltum tayi tayi su sake zama suyi yar hira fatsuma taki tace gara ta tafi tayiwa kaltum fatan alkhairi da Allah kiyaye hanya tajuya ta tafi.

kaltum tayi kuri ita kadai taci gaba da kallon
masu wucewa kowa da dan uwansa yana hira amma bata damuba, zama kadanne ya rage mata a shiga jirgi tunda magrib ta kusa farin ciki mara misaltuwane ya bayyana azuciyarta ya huda ya fito ta fuskarta musamman da jirgi ya iso anfara bin layi don yankar tikiti kaltum cike da fara'a tabude bakin buhunta don dauko kullin ledar da ta daure kudinta zataje itama tabi layi ta yanki nata tikitin idan ta tuna jirgi zata shiga yanzu bur sudan tana wayar gari zata ganta kusa da mambela da Madina sai taji farin ciki ya lullubeta jitake kamar rufe ido ta bude idanuwanta ta ganta a bur sudan,
ta kasa kwatanto irin farin cikinda su mambela zasu shiga idan sun ganta ta luma hannu acikin kowane sako lungu da kusurwar buhun kayanta taji har yanzu bata jiyo kullen ledar kudinta ba nan da nan ta fara zazzakulo tsummokaran ciki da sauri tana zazzagawa tana ajewa akasa har buhunya zama wayam ba komai amma babu ledar kudin

don haka hankalinta yatashi matuka ta sake bin kowani zani daya bayan daya ko kudin yamakale ajiki amma shiru kakeji bai fadoba, ta tsake wargaza kayanta akasa kowanne siket riga zani ko lafaya saida ta shimfideshi akasa sanka-sanka babu ledar kudin ta,
saita rushe da kuka na takaici yayinda jama'a suka tabbatar ba lafiya ba tabbas akwai
matsala aka taru ana tambayarta bayani take cikin gigita da dinbun damuwa wasu sun yarda ta ita sun kuma tausaya mata wasu kuma bayanenta yamusu kama da tatsuniya gizo da koki ta mallece kawai domin sun saba ganin irin wadannan mutane wadanda dazarar talauci ya ishesu sai suzo tashar suna ihu suna neman taimako kudin mota suce nasu ya fadi idan aka hadamusu taimakon sai su zame su gudu daman ba motar zasu hauba damfarane kawai,
wake daya yake bata gari inji masu iya magana sun shafawa masu gaskiya kamar yanda suka shafawa kaltum kowa ya kalleta
saiya watsar yawuce abunsa ma'ana sunsaba ganin irinsu tuntuni,
kuka take haikam bayani take bilhakki rokon taimako take yi da duk karfin ta amma dakyar ta samu jine goma sha daya ta garzaya bakin wundon mai sayar da tikiti cikin kuka tayi masa bayani game da fayyace masa abunda take nema agareshi tace tana son ya
taimaketa yabata tikiti tatafi bursudan wajen yan uwanta batada kowa a Khartoum, ansace mata kudinta kakaf sai yanzune ma jama'a suka taimakamata da jine goma shadaya ya
taimaka ya karbi abunda take dashi idan jirgin nan yatafi ya barta batasan yanda zatayiba...

wani takaici yarufeshi tikitin jine dari biyu dahamsin ne zai bata a jine goma shadaya?
kallon tara saura kwata ya mata don haka basai yamata magana ba tasan abunda
ke ransa cikin fargaba ta sharce hawayenta ta sake neman wata alfarma cewar to ya bata rancen tikiti suna isa bur sudan yasawani ya bita gidansu ya karbi kudinsa..

cikin wata dankararriyar murya ya fada cike da takaici ke matsami daga jikin wundo kada ki sake dawowa, kika sake lekowa kika min zancen banza sai nasa yan sandan can sun kamaki, kaji mahaukaciya tikitin gwamnatin ne zan baki bashi ?

Sum sum sum kaltum tayi tabar jikin wundonsa batare da ta sake cewa komaiba daman itama tsausayine yasa ta tambayeshi don daga ganin bakar fuskar nan tasa baki kirin da jajayen idanuwansa tasan bazaiyi mutumci ba ga wani tulelen ciki da kiba da kyar yake juyi kuma tun nan kasa tsinke ka huda yace tush haka yake kamar katuwar balobolonda aka cika da iska saita daina
kuka ta sharce hawayenta da yayi mata face face a fuska batada sauran dabaru ko tunani bata da sauran wani tunani kuma ta cire burinta data kudira saitaje kayanta da ta watsar akasa tana kadewa tana linkewa tana zurawa a buhu jikin ta kalau data gama lenkewa saita koma gefe jikin wani dakali ta jingina da buhunta a gefe tana duban jama ar da Allah ya musu rahma wadanda ya yalwatasu da kudin sayan tikiti sai yanka suke suna shiga jirgi,
dukan uku uku kirjinta takeyi tamkar zata fashe...
.
Saady and Dan Aunty.ADON DAWA 27
.
TRUE LIFE STORY
.

ta fito waje yayinda takejin wani jiri na takaici na neman yakayarda ita kasa,
kuka yaki zuwa saboda abun yafi karfin kuka, don idan tashin hankali ya afku akayi kuka to akwai sauran rangwamen masipa, amma idan masifa yayi masifa to kukama takansa yake abun yafi karfinsa,
nasihar Madina ta tuna wacce a koda yaushe take shawarta ta yawaita addu'a tana neman tsari daga masifun rayuwa, wanda ko Allah Ya aiko da masifa zata zo da sauki kuma da maganinta ta shawarceta data yawaita karanta InnaLillahi wa ina ilaihi raju un
ako yaushe musamman sanda wani abu naki yafaru,
nan da nan kaltum ta cafko kalma InnaLillahi
wa inna ilaiyi raju un a harshenta tana fada
tanasake maimaitawa saita farajin wanan kululun nan daya shaketa awuya yafara lafawa, bugun da zuciyarta ke famanyi ta sausauta tanaji tana gani jirgi ya cika ya tashi yatafi ya barta, yayinda kuka ya kwace mata tana yi ta nanata kalmar InnaLillahi wa inna ilaihi raju'un ta dade a zaune anan har karfe
sha daya na dare.

saida wani dan sanda ya zagayo ya sake zagayowa ya tabbatar ba tada niyyar tashi daga wajen nan sannan ya tsaya ya tambayeta lafiya take zaune haryanzu cikin kuka?

tamasa bayani yace to ai gara ta tashi ta koma inda tafito saboda zamanta anan bai dace ba, ga dare ya fara nausawa gara takoma ta tara wani kudin zaifi mata sauki saita dawo ta yanka tikitin ta tafi baki alaikum don ba wanda zai dunkule wannan makudai kudin ya bata, don kowa takansa yake yi,

kaltum ta mike ta daura buhunta aka tana zubar da hawaye tafiya take amma dakyar take jefa kafarta ta isa gida zuciyarta tamkar tafashe taci sa'a duk yawancin ankwanta
saboda gajiyar sallah , ta sadada tashiga dakinsu ta ajiye kayanta a lungu tayi sallah ta kudundune alungu yayinda duk sanda ta rintse ido saita tayhango Madina da mambela sai ta fashe da kuka.

washegari da safe kaltum taci karo da yan gidan a lokacin da ta fito daga bandaki zatayi alwalar sallar asuba, mamaki mara misaltuwa zaka gani a fuskokinsu
musamman ma kawarta fatsuma,
lah kaltum baki tafi ba?
Meyasa baki tafiba ?

Amsa ya gagari bakin kaltum saitayi shiru tana tunanin abunda zata fada sai can tayi dan murmushi karfin hali tace fasawa nayi ai tun jiya da daddare na dawo,

kika fasa meyasa ?

Suka sake tambayarta ko amsa bata basuba taci gaba da alwalarta kawai,
fatsuma tayi dariya tace gaskiya naji dadi dakika fasa don har ina tunanin yanda zandinga yawo nikadai a garin nan gara muyi zamanmu anan, kaltum ga wuta ga ruwa ga titina ga wayar sadarwa ga samarin birni mezakiyi a bur sudan?
kince babu wuta baruwa babu network na waya gaku a zaune a makabarta duk kabarurruka a dakunanku na katako kamar yadda kika fada min...

sai ko wacce ta tsoma bakinta tanayiwa kaltum nasihar tayy zamanta anan kada ta koma kauye suma yan kauyen addu'a sukeyi sudawo birni.
ta mike sam ta shiga daki batare da tare da tayi musu magana ba, takaicinda ya isheta ya isheta kauyen nan da suke kushewa ita yafi mata birninnan dasuke muradi

kamar yadda suka saba kaltum da fatsuma suka bazama neman na abinci duk da sallah ce amma sunyi sammako suntafi kasuwar markadi , ahanya suna tafiya kaltum ta dubi fatsuma ta langwabar da kai gefe tace bakisan abunda ya sameni bako?

Fatsuma ta dubeta cike da mamaki tace bansaniba me yafaru?

Kaltum tayi ajiyar zuciya tace sace min wannan kudin nawa duka akayi ban gan su ba shiyasa bantafi ba .

fatsuma ta zabura ta dauki dogon salati game da dafe kirji ta tambaya cikin gigicewa yanzu wannan kudin an sace su dukka?

Fiye da jine dari bakwai nefa yanzu wa kike zargin ya dauke miki a dakinku ko atasha aka
dauke ?

Hawaye ya sirnano daga idanuwan kaltum
ta girgiza kai tace bansan inda aka daukeba ni dai nasan ko a daren shekaranjiya ana gobe zantafi kenan saida naga kudin harna sake kirgawa na daure na mayar asanda zamu tafi tasha dai ban duba ba wata kilan sanda nashiga wanka aka dauke,

fatsuma tace watakilan sanda kike kirgawa wata ta ganki kina tashi ta dauke,
nidai kina ganin sanda na dauki buhunki bansaka hannu acikiba agabanki na ajiye miki a tasha natafi, kuma niban hudaba nazakulo da Kinga buhunki huje....

kaltumta zabura tace nifa bance kekika daukanmin kudina bafa ko a mafarki nasan
baza ki min sataba,
suka cigaba dajajatawa har suka isa masana'antarsu wato babbar bolan da suke
sintar kayan miya suka fara gudanan da ayyukansu kamar kullun,

Abbas dai yanakan bakansa na naci dabin kaltum aduk inda take, a yau ma ya riskesu a inda yake tunanin zai samesu adaidai lokacin daya san zai riskosu , yakwada sallama cikin wata kamilalliyar murya mai sanyaya zuciya
lokaci guda suka daga kai don gani mai wannan sanyayyiyar murya sai sukaga fuskar Abbas cike da murmushi irin wannan murmushi fatsuma ta mayar masa gami da amsa sallamar itama a yayinda abangaren kaltum akasamu akasin haka, domin jitayi ranta ya baci nan da nan ta tsuke fuska takawar dakai gefe yasake tsungunawa kanta ya rafka sallama don dama ita yakewa sallama, kuma ita yakeso ta ansa ba fatsuma ba,

kaltum ta fusata ta mike afusace tafada cikin fushi Abbas karabu dani kakyaleni in sake saboda ni ina da mijina a bur sudan don haka kaje kanemi wata,

fatsuma tarike baki don mamaki game da
fargaban kada kaltum tajawo musu dan kudin da dan turaren da yake basu ya pasa,
fadi take ke kaltum me haka karya takeyi batada miji a bur sudan,kaltum taji tamkar ta zageshi,

kishi da tsantsar fusata suka damki zuciyarshi yacije lebe yace nikike fadawa wannan magana kizo kasarmu kinacin arzikinmu dan kin samu anasonki shine zaki zageni?
To zan nuna miki ko ni wanene, ya juya yatafi afusace.
fatsuma na kwala kiran sunan shi tana bashi hakuri yayinda kaltum ke tunzurashi tana cewa ya tafi din wazai tsoratar babu abunda
zai sameta sai alkhairi,
fatsuma ta fara yiwa kaltum fada itama dayake zuciyar akusane saita hargitsa suka hau hayaniya kamar zasu cinye kansu,
ranar dai kowa gabanta takama ba a tafi tallar tareba haka basu daura tukunya dayaba sai washegare fatsuma tabiyo wa kaltum suka hadu suka tafi tare kowaccensu ta huce sai hira suke suna wasa suna daria,

gidan jawahir mai kunshi suka fara zuwa don suji sanda zasu fara zuwa aiki tunda tace musu sai bayan sallah zasu dawo sai suka tarar ana zaman makokinta, Allah Ya mata rasuwa ranar biyu da sallah sukata kuka da ihu ana basu hakuri sannan suka yi shiru a gidan, suka nufi kasuwa jikinsu a sanyi kalau suna isa wajen sana'ar su sai suka iske labari yasha bamban don yau ana kwashe bolan da suke tsintar kayan miya yau a manya-manyan abun kwashe shara ana tarawa sai aje ajuye a motar kwashe shara,
suna isowa wasu ma'aikata masu uniform suka taso sukace oh kune daman masu tsintar rubabbun kayan miya ku wanke ku sayarwa mutane suci ko?
Don haka yanzu zamu wuce daku wajen hukuma a hukunta ku,

hankalinsu yatashi sai suka hau rokonsu afuwa da alkawarin sun daina daga yau, da kyar suna koke-koke aka kyalesu suka tafi akace kada su sake dawowa, daga wanna ranar su kaltum basu sake zuwa bola ba sai suka shiga tunanin sabuwar sana'ar da zasuyi su dinga samun abinci,

aranar kaltum da fatsuma suka jeru ajikin bangon kofar gidan su yunwa ya addabi hanjinsu fatsuma ta daga kai da kyar ta dubi kaltum tace meza mu dingayi muna samun abinci ?

Kaltum tace ni bakuwa ina na sani, kece yar gari kikasan kowa suma suka sanki,
fatsuma ta zabura ta mike tacewa kaltum taso muje wani waje kaltum na biye da ita abaya har suka isa wani gida alungu gidan wata hajiya Maryam mai saro kaya daga makkah sababbi da gumama, ,
fatsuma ta lankwashe kafa ta langwabe kai ta koro mata bayani cewar suna neman sana'a suna so tabasu tallah ta dinga biyansu

dayake tasan kanwar babarta asabebe tasan
gidansu saboda haka tasan ko sun cuceta ta san inda zata zakulosu, ta amince ta daura musu tallah, idan sunyi ciniki dayawa ta biyasu dayawa idan ciniki kadane ta biya su kadan,

bayan sati guda ne sukaje daukar tallah sai hanasu dauka tayi, tayi musu korar kare batare da sunsan abunda yake faruwaba, kuma bata fada musu daliliba suka koma wajen mai sayar da gurasa suna yimata tallah, bayan kwana biyu ta koresu,
duk Abbas ne yake hada musu tuggu ashe,

kwanci tashi watannin kaltum bakwai cur a Khartoum haka shekarunta uku kenan rabonta da Nigeria,
wulakanci da walagiigi sai karuwa sukeyi maimakon suragu al-amura sun cunkushe musu har gara da abincin da zasukai bakinsu yazam wahala kasancewar anhanasu tsintar kayan bola sannan jawahir mai kunshi da gyaran jiki ta rasu har maigidan yasake aure ko gidan ba a shiga balle su sami wadanda
zasuyi wa gyaran jiki,
Abbas sisinshi ya daina basu tunda batasonshi tuggu iri iri yake hada mata duk wata hanya da yasan kaltum zata bi ta sami
taro ko lomar tuwo sai yaje ya toshe ya batata da bakin shi,
gobe idan ta dawo sai kaga anyi mata korar kare ta shafawa fatsuma, '' idan bera da sata daddawama da wari, idan babu rami mai yakawo zancen rami ?
Inji akuyarda kura tace ta tsallako babu rami abun nufi shine duk wata tsanarda sangwama da akeyiwa mutanenmu yan Nigeria su suke jawowa kansu saboda sau tari idan suka gingimo wata badakalar saikaga ko a labari ko a mafarki yan wannan kasar basu tabajinta ba abubuwa rashin gaskiya da rashin da'a akasashen jama'a mutanenmu ke nunawa, wadanda abun kunya ne da bata sunan wadanda babu ruwansu kuma mutanen kirki ne kamar su kaltum sun zaune agidan amma basusan me
yake faruwaba, kashin kaji aka shafa musu aka hadasu akayi musu hukunci iri daya koda yake wasu masu irin mugayen dabi'u ba yan Nigeria bane wasu yan Niger ne,Ghana ,Togo ,Cameroon ,Chad ko Kenya amma sai ahadasu ace yan nigeria ne,

jama'a da gwamnatin Khartoum ta fara gajiya da rashin bin doka da rashin da ar yan gidansu kaltum aka kira malam Abdulkadir mai gidan su kaltum, ance yamusu gargadi bisa munanan halayen da akace suna kamar zubarda shara a ko ina, kafa teburin sana'o'i ko ina, sayarda rubabbun kayan dasuke tsinta abola kamar irin sana'arsu kaltum,

maza suna haura gidaje suyi sata haka ana ganin mata suna fita karuwanci yan kasa suna daukar su amotoci atafi dasu.

malam yatarasu mazansu da matansu ya shaida musu abunda aka umurceshi daya gargadesu dashi duk da wasu ya sani wasu kuma bai saniba wasu gaskiyane wasuma
karyane koma ma menene aka kara acikin maganar gaskiyar tafi yawa haka ba bukatar
bincikensu waye suke aikata wannan badakalar kosu waye babu ruwansa burinsa kawai su daina idan bahaka shizai kori kowa agidanshi,
sai su kayi kamar sun gamsu suka yi ta bashi hakuri,
gobe wani sabon rashin mutuncin zasu suka,
yasake kiransu yayi wa'azi yayi lallashi ya jawo ayoyi daga AL QUR'ANI MAGIRMA yayi fadan da kumfar baki,

in shaa Allahu jibi ta'andanci saiya karu
saboda sabbabbin mutane suke zuwa su yada zango agidan ba yan zangon daura kadaiba ko yan daura harda kanawa,zazzagawa,zamfarawa,sakkwatawa.gida yazama gidan baitil mali bangaren maza daban saboda malam yace kowa azauna
sadaka ga wuta ga ruwa ga dakuna lailaye da
siminti ba biyan ko sisi abinci ne kawai zaku nema shine suke bin gurbatacciyan hanyarda suke zubarda mutuncin su data kasarsu abunda yake tambaya anan shine wai mutane idan suka bar kasarsu cikin en uwansu inda akasansu sai suyi tayin abunda suka ga dama don ba asansu ba balle ayi musu gori ko ayiwa yayansu gori?.

me yasa mutanane basa kare mutuncin kasarsu aduk inda suka tsinci kansu ?

dadine ace yan kasa kaza basu da gaskiya ko karuwai ne marasa tarbiya ne.
masu iya magana sukace shadda bata wari banza dole muma da halinmu shiyasa ake tsanarmu, babban tabon ma shine ha'inci da rashin gaskiya

Duk yanda kahada hulda da mutanen mu sai
ancuceka wannan itace illarmu babba a kasashen waje da cikin gida,

wani sabon salo kuma wanda su kaltum basu san shiba shine gudun gardi irin nawasu makarantun kwana da akeyi a wasu makarantun kwana na yan mata da akeyi garada ne suke tubewa tsirara su hauro dakunan mata da talatainin dare suyi ihu gardi.

asabebe alokacinda taji motsi a bayanta tana juyowa taga sarkacecen mutum akan akwatinta bayan ya tsinke musu wayoyinsu da suka jona a chaji a bakin kofar dakin yafice da gudu yahaura katanga yayinda gida ya rude da kururuwa matan kowanne daki sun firfito tsakar gida a firgice, dole malam Abdulkadir da sauran mutanen anguwa suka firfito hankali a tashe ana hashaskawa ba a ganshiba,
a safiyan wannan ranar ne kuma fada ya kaure tsakanin wasu mata biyu akan shiga bandaki harda dambe da fashe fashen kai, nan ma dakyar aka kirawo wasu mazan suka rabasu don haka yansanda suka diro
gidan suna kama duk wanda suka samu idan
kukaga irin gudunda kaltum da fatsuma su kayi da tsalleka katanga saikuyi mamaki amma da kyar sukasha bayan gurgurjewa da bubbugewar dasukayi a kafafuwansu, wani sharcecen yankane a gwauri kaltum dajini jage jage amma bata lura ba saida suka isa maboya suka tabbatar sunsha sannan ta duba tagani asanadiyyar radadi mai tsanani da takeji awajen hankalinsu yayi matukar
tashi a sanda suka yi arangama da jinin mai yawa,
fatsuma ta fashe da kuka mun shiga uku kaltum yaya zamuyi da jinin nan kada jinin jikinki fa ya kare ki mutu,?
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 28
.
TRUE LIFE STORY
.
kaltum ta matse hawayenda ya cika mata
ido tace Allah Ya biye bakinki fatsuma,
dama jinin jikina yakare in mutu in huta, banajin dadin duniyar nan banaso na koma nigeria haka ma yanzu banaso nakoma bur sudan dama in mutu abayan garin nan kada intashi daga inda nake yanzu,
suka rushe da kuka lokaci guda, fatsuma tace gara muyi addu'a mukoma kasarmu ke ai iyayenki sunsan bakya makkah harsun aiko miki da kudin jirgi ki koma, nifa da iyayena suke zaton ina makka inajin dadi kanwar babatace ta dauko ni asabebe muguwace ta gaske.
harkokinta kawai takeyi na iskanci, dama akamata yanzu akaita nigeria idan taje gida zata fada inda nake nima azo a dauke ni, fatsuma ta sake rushewa da kuka tace kaltum kiyafe min don Allah nina jawo miki duk wannan abun da kin tafi dabakyanan akayi wannan rigima, dabaki yage kafa abanza ba,

mamaki mara miraltuwa zaka iya gani a idanuwan kaltum ta dubi fatsuma da sauri tace me kika jawo min ?
ai ni baki jawomin komaiba kalah tajawo min ta tafi tabarni...

fatsuma ta girgiza kai tace bawan nan zuwan naki nake fada ba kaltum da tuni kina bur sudan nice nadauke miki kudinki a jakarki don kada kitafi ki barni.

kaltum taji ta tsani fatsuma harbataso tasake ganinta ta runtse ido don takaici yayinda taji zuciyarta kamar zata fashe da alama fatsuma ta gane haka sai taja da baya ta lankwashe kafa ta zurawa kaltum ido tana jiran hukuncinda zata yanke mata,

kaltum tayi shiru ba tare data furta komai ba sai hawaye dayake fita daga idanunta,
fatsuma tacire dankwalinta ta kama
kafar kaltum ta daure saboda jininda yake zuba haryanzu.

kaltum ta runtse ido yayinda ta jingina kanta
ajikin bishiyar da suke rabe tayi shiru kamar mai gyangyadi nan kuwa rayuwa ce ta tsananta a gareta,
fatsuma ta nisa tace da na dauke kudin ba
wani abun nayi dashiba ajiya nakai da niyar in an kwana biyu inbaki wacce nabawa ajiyar daga baya tace min wai an sace nikuwa nasan karya take cinyewa tayi don haka nayi shiru banfada miki ba don babu kudin..

kaltum dai har yanzu bata bude idanun ta ba bare tabata amsa,
fatsuma ta mike tsaye tace zomuje mu leka kofar gidan mu ga ko an gama kame,
kaltum bata ansa ba sai ta sake cewa kokuma kizauna tunda kafarki nada ciwo inje
indawo shiru ta mata fatsuma ta tafi sannan kaltum ta bude ido tabita da kallo yayinda kuka mai yawa ya kece mata marar kakkautawa tayi ta kuka tana tuje kososon gashin nan nata dake dandankare asanadiyyar rashin kitso har tsawon watanni bakwai daman kanta bata ba dankwali dayar
ahanya wajen haura katanga burgujejen skirt ne da bakar t shirt duk a huhuje itama sadaka aka bata kafafunta babu takalmi kallo daya zakamata ka tabbatar almajirace ko kuma tababbiya sabon kamu, fatar jikinta kososowa yake ana ta abinci waketa man shafawa abincin ma dazasuci shima badon dadi ba sai donsu rayu,
data tsagaita dakukanta saita bingire ta kwanta tana barci bata damu da kashin tsunsaye da suke tsarto mataba haka bata damu da tika tikan jangwale gwadar katangaru da suke dauki ba dadi da matansuba sunata zagayeta barci take kuma kamar bugun aljanu datasaba ta dai fita daga haiyacinta koma dai menene batacikin haiyacinta,
cikin barci kamar ido biyu taji muryan fatsuma tana fadin ga kaltum din ta bude ido da kyar ta dubi mutanen da ke tsaye akanta dusu dusu take ganinsu don haka bata gane ko suwayeba ta komawa jabar tayi ta kwanta
saitaji an girgizata antasheta zaune kaltum kaltum bude idonki ki gani taga fatsumace rumgume da ita cikin larabci, murya tayi magana wacce nan da nan taji ta wartsake gaba daya daga barcin kai wannan ba kaltum dinda nake nema bane daya daga cikin mazajen biyu da suke tsaye akansu ne ya fada, ta dubeshi ya dubeta duba na ido cikin ido yayinda gaba dayan su suka rude mamaki ya bayyana fuskokinsu mai tafe da tsananin farin ciki ya fada cikin wata murya mai sauti abayyane yace kaltum kece kuwa?
AlhamduLillah
yayinda ya durgusa gwiwoyinsa biyu akasa ya daga hannu da idanunsa sama yana gode wa Allah, itama ta zabura ta mike tsaye ta dafe kirji ta fada cike da mamaki lah mambela ya akayi kasan ina nan ?

Fatsuma tafada cike da murna au kaine mambela daga bur sudan ?

Yaji dadi ya dubi fatsuma cikin murya mai sanyi yace nine mambela ashe kinada labarina ?
ya juya ya dubi mutumin da ya rakoshi yace malam itace yarinyanda nake nema, yau sati biyu kenan muna yawo a Khartoum tare dakai saiyau Allah Ya yanke min nagode malam
Allah Ya biyaka sannan mambela yasa hannu a aljihu ya debo kudi mai yawa ya bashi saida
mutumin ya bude baki don mamakin wannan kyauta mai tsoka mambela yakara dacewa kaje masaukina ka dau jakan kayana karike na baka kyauta don bazan koma cikin gariba daganan sai tashar jirgi zamu tafi daman ita nazo nema Allah Ya taimaka na same ta.

farin ciki da godeya ba adadi mutumin nan ya
dinga yi yana mai yimusu adduar Allah Ya basu tare yana tafiya yana nanatawa kamar karatu,

mambela ya tsunguna agaban kaltum yayi tagumi yazura mata ido yana dubanta sama da kasa yayinda itakuma kunya ta rufeta tana rurrufe jiki,
hawaye yacika masa ido ya fada cike da tausayawa yace kaltum yanzu kece kika zama haka kin rame kinyi daka-daka kamar bakece mai tsaftar nan ba?
dubi kanki yanda ya zama duk kura babu kitso har kawarki tafiki kyawun gani,
yasake dubanta sama da kasa yayinda yayi arangama da dankwali jage-jage da jini a daure akafarta yasa hannu ya kwance sai ga yankan namar kafanta awaje, ya firgita ya
tambaya cikin gigita meyasameki akafa haka?

kaltum ta sunkuyar da kanta kasa yayinda hawaye ke zuba a idanuwanta, mambela yazubo da hawayen daya ciko masa ido magana yake har cikin zuciyarsa yace yanzu kaltum daman irin matsananciyar rayuwarda kike ciki a Khartoum?
amma kikaki ki hado kayanki kidawo bur sudan?
yanzu kaltum ina raye a sudan amma kika zauna kika zama almajira?
.
Littapin kamar ya daina dadi, dan an rage comments.
Y?
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 29
.
NA JAMILA UMAR TANKO (JUT)
TRUE LIFE STORY.
.
PART 29
.
kamar bola, yanzu kaltum kika kasa daukar shatar mota kitaho bur sudan inyaso inkinzo nabiya ko nawane?

kaltum ta dago da sauri ta dubi fatsuma yayinda fatsuma tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa gami da haduwa da matsananciyar faduwar gaba kada kaltum ta fadawa mambela cewar ita tasace mata kudin tafiyar,

kaltum tamayar da kanta kasa batare datace
komaiba ya juya ya dubi fatsuma yace akwai wani chemist ne anan kusa dazasu dinke mata wannan ciwon?

fatsuma tace akwai sai dai da dan nisa.
mambela ya dubi kaltum duba na tausayi hade da kulawa da tsansar so da kauna ya fada cikin laulausar murya zaki iya takawa ko muje mu taho da masu chemist din?

ta langwabe cukuikuyeyyen kan nan nata tace zan iya tafiya, tayunkura zata mike tsaye mambela yacewa fatsuma yimaza ki riketa karta fadi.
fasuma ta cafketa ta taimaka mata ta mike tsaye yayinda ta shiga tsakanin hannun ta suka dinga takawa a hankali mambela na binsu abaya ransa yana matukar baci idan ya dubi jikin kaltum da kayan jikin ta,
saiyaji tamkar ya kurma ihu, taya akayi yana
raye aduniya kaltum tazama haka?
menene anfanin dimbin dukiyarsa tunda kaltum na nan abincin da zataci ma ya gagareta?

sunyi tafiya mai yawa sannan suka shigo gari suka isa wani chemist karami da sukaga girman ciwon sai suka ce bazasu iya dinkewaba gara sukaita asibiti,
mambela ya tambayesu a inane asibitin?

aka kwatanta masa asibitoci guda biyu,
daya na yaku bayi daya kuma na masu hannu da shuni ne amma kowanne sai anshiga mota,
suna fito daga chemist mambela yatare musu taxi yashiga gaba su biyu suka shiga baya babban abunda yabashi mamaki shine yadda ya hasko fuskokinsu ta madubi suna murna suna dariya sai rade sukeyi suna kashewa da hannu,
Ya rasa dalilin yin hakan bayan dazunnan suke hawaye ko bayan fitowarsu daga chemist kafin su shiga mota, yakasa daurewa dai sai ya juya ya dubi fatsuma yayi murmushi yace fatsuma murnan me kukeyi?
Ki fada mini gaskiya don nima na taya ku murna,

kaltum tayi sauri ta kiftawa fatsuma ido alamar kada tafada, sai fatsuma ta tunsire da daria tace ba komai,
mambela yace kaltum ce ta hana ki ki fada ko?
Ai naganta tana kifta miki ido ki fada min gaskiya babbar suna ne garekifa masu sunanki basa karya,
fatsuma tace to bari na fadi gaskiya murna mukeyi saboda yau munshiga moto don rabonmu da mu shiga munfi shekara uku tun sanda muka taho daga nigeria, saidai muga ana hawa bamu taba hawa ba, duk inda zamuje saidai muje da kafa....
kaltum ta ririketa saida ta tona musu asiri,
mambela da direba suka kwashe da dariyar da basu shirya ba, direban ya juya yadubesu dan lekensu ta madubi bai isheshiba gara yasake duban kyauyawan nan ya juya ya dubi mambela yace yan Nigeria ne ko?
masu shigowa sudan da niyar tsallaka ruwa su shiga jidda suke zube wa akasarnan suna wahalar tsince-tsince da bara daman ina sukaga kudin shiga mota wani aiki zasu makane ka dauko su?

Nan da nan mambela ya tsuke fuska yace wadannan ba irin almajiranda kake fada bane daya matata ne dakuma kanwata,

sai direba yayi shiru bai sake cewa komai ba yayinda kwakwalwarsa ta rude yace aransa yaya za ayi yace wadannan yammatan jininsane alhali yanayinsu ya bambamta kana ganinsa kasan dan sudan kana ganinsu kasan yan nigeria ne daga ganin jikinsu kasan almajiraine to amma meyasa zai boye masa wadannan?
tambayoyi fal a zuciyar direba saidai kash baiga fuskar tambayaba ya isa asibitin masu mulki da masu arzikin kasar ne ke iya biya saboda tsadarsa da kwararrun likitocinsu,
suka firfito yayinda mambela ya biya kudin mota sannan suka nufi cikin asibitin, haryanzu fatsuma da kaltum basu daina hada ido suna dariya ba, wannan karon dariyar shiga hadadden gini suke mai benaye kamar london,
hadaddun matayene suke shiga asibitin da yayansu da mazajensu ajere-ajere cikin sutura na alfarma da kamshin turare, fatar jikinsu jawur a simulce ko kurji daya babu balle kasamu kirci irin nasu kaltum don haka mambela ya tsayardasu ajikin wata mota ya hana su shiga yacesu jirashi anan yana zuwa,
cike da mamaki suka saya suna kallonsa ya fice da sauri wajen get ya dan jima bai dawoba sannan ya dawo rike da ledoji guda biyu ahannunshi sannan ya mika wa kowaccesu leda daya cikin sauri ku bude saiga lafaya (pink colour) mai kyan gaske da
takalmi masu kyau (flat shoe)suka zura masa ido lokaci daya, sai yayi murmushi yace kusa wannan akan kayan jikinku ku nada sunfi kyau yayinda ya masu dagun don su kimsa akan kayan da suka maka amma duk dahaka sunfito fes bakamar da ba,

yadawo sukabi bayansa har cikin asibitin,
kudi mai yawa aka karanto masa nayankan file da kudin ganin likita kawai ba ama zancen aikin da za'a mata dana magun-guna, mambela yabiya sannan aka nuna masa dakin da zasu shiga suga likita,
sanyin A.C ne da kamshi kawai yake tashi yana ratsa kasusuwan jikin su, farin ciki ya bakunci zuciyoyinsu kasancewar sun gansu a cikin yan kasa suna wadakarsu kamar kowa wanda a da basuda damar yin hakan,

kaltua ta manta da katon ciwonda ke kafanta ta biyewa fatsuma sai yake hakora sukeyi suna murna bayaga kalle kalle da tabe-taben da sukeyi saidai idan mambela zai gansu saisuyi sauri su daina su sunkuyarda kai kasa,
likita ya duba kafar kaltum sannan ya shaidawa mambela cewar zasu shiga da ita dakin tiyata za awanke ciwon a yanyanke fatocinda suka babbako sannan a dinke wajen sannan zai rubuta musu magunguna, dan haka ga takarda yaje kan kanta ya biya,
kudi mai yawa amma bashi yadami mambela ba illa wahalarda kaltum zatasha ji yake dama ace ciwon yadawo kafarsa yaji zafin kaltum tahuta, kallo daya zaka masa kasan ya shiga damuwa, jikinsa yayi sanyi kalau ya isa wajen biyan kudin da sayin magunguna sai ya saka mai sayar da magunguna agaba da tambayoyi kala-kala yaci sa'a yasamu mace mai fara'a domin tana bashi amsar tambayoyinshi harma takara masa bayani ta tabbatar masa wadannan allurai da likita ya rubuta masu kashe zafin ciwone, ko ana dinkewa bazataji zafin komaiba, sannan mambela yaji sanyi aransa ya biya kudin ya karba yakawowa likita yayinda likita da ma'aikatan jinya mata suka shiga da kaltum dauke da almakashi da tasoshi abaya ga iodine da shashshabalin, abunka da nauyin aljihunkane darajanka a yanzu sai lallashi da wasa da daria sukewa kaltum babu kyara balle zagi irin na asibitin yaku bayi ba irin wanda kalah ta kwanta ba.
aka umurci mambela da fatsuma su zauna akan wasu kujera na alfarma mambela ne zaune ya rike kai da alamar damuwa atattare dashi,
fatsuma ta lura da hakan ta nisa tace kayi hakuri zataji sauki in shaa Allahu,
mambela yaji sanyi da kalaman fatsuma sai
ya gyara zama yace bakomai fatsuma mu tayata da addu 'a Allah Ya sausauta mata,

sukayi shiru na wani dan lokaci ba wanda yasake magana sai dai bakinsu yana motsawa da alaman addu'a suke yi,
mambela ya dubi fatsuma yayi murmushi yace fatsuma naga alamar kina son kaltum, kun shaku, kin san tane dama tuntuni ko anan kuka hadu?

fatsuma tayi dariya tace anan nasan ta gidanmu daya dakinmu yana kusa da nasu tun zuwanta su kalah suka wulakantata suka hana ta abinci shine nace tazo mu dinga zuwa wajen sana'ata don itama tasamu abunda zataci,

mambela ya yatsune fuska yace menene sana arki?

Fatsuma tace kasuwan markadi muke zuwa da sassafe a lokacin da ake sauke kayan miya kwando-kwando ana ciccire masu kyau ana zubar da rubabbu, idan an zubar mukuma sai mu dinga tsintar masu saukin rubar mu wanke muje kasuwar adare mu sayar mu saya abinci.

mambela ya dafe kai yayi shiru don tausayawa takaici ya isheshi can ya dago ya dubi fatsuma fuskarshi cike da damuwa yace kinyi maganan wata kalah da ta wulakanta
kaltum ta hanata abinci wacece kalah?
kibani labarin kaltum kakaf a Khartoum tun daga ranarda tazo Khartoum har rana irin ta yau dana ganku abayan gari naje gidanku na iske yansanda suna kame wai meya farune ?

Fatsuma ta gyara zama ta fayyacewa mambela rayuwar kaltum kakaf a Khartoum bata boye masa komaiba tunda bata boye masa sace kudin kaltum datayiba ai bazata boye masa wani abuba,
hawayene ya dinga digowa daga idanuwan mambela saboda tausayin abar kaunansa kaltum,
tambaya daya yasake yiwa kaltum da alama ita tafi tsaya masa arai itace game da ABBAS,
yace kin tabbatar kaltum batason Abbas ko kadan aranta?

fatsuma tayi mamakin wannar tambaya nasa tabashi amsa cike da tabbatarwa kaltum batason Abbas kokadan duk da irin nacin da yayi da irin lallabata danayi ta yarda amma taki yarda don hakane ma yafara takura mana, har yasa aka hanamu tsintar kayan miya shinema ya dinga turen ya sanda gidanmu don akoremu, yaji haushi kaltum bata sonshi,

mambela yayi murmushi ya juya ya dubi fatsuma yace kinci sa'a da kaltum bata yarda taso Abbas ba duk lallabata dakikayi saboda nasha alwashin takurawa duk wanda yayi kokarin raba ni da kaltum.

fatsuma taja da baya atsorace tana rawan jiki mambela yayi dariya yace kada kiji tsoro babu abun da zan miki yanzu amma da ace da kika lallabata tayarda taso Abbas da ina mai tabbatar miki da gaske har Abbas bazan raga muku ba,
don saina nemoshi koshi wayene kuma kodawa yake takama.

su dukka sukayi shiru nadan lokaci sai mambela yasake dagowa ya dubi fatsuma yace kaltum bata taba baki labarin wata mata Madina a bur sudan ba?

fatsuma ta gyada kai ta fada cikin fargaba tace tabani labarin Madina.
Yace AlhamduLillah tunda kinsan shakuwa da soyayyarda ke tsakaninsu da taimakonda Madina tayi wa kaltum a irin zamansu dakowa takanshi yakeyi ina girmamata kuma ina matukar kaunar duk wanda yake kaunar kaltum kamar Madina amma yanzu bana raga mata ko kadan saboda sanadin da tayi na rabani da kaltum.

fatsuma tayi caraf tace kayi hakuri bansaniba da farko amma daga ranarda kaltum tafadawa Abbas cewar yarabu da ita, ita da mijinta a bur sudan mai suna mambela tundaga ranar bansake takurata ta kula shi ba, shima daga ranar ya tabbatar akwai wanda take so bazai sami soyayyarta ba don haka yatakura mata,

daga dukkan alamu mambela yaji dadin bayanan fatsuma saiya tuntsure da dariya yace dagaske kike kaltum ce ta furta haka da bakinta takirani da sunan mijinta?

fatsuma ma dadi ya kamata ta gyara zama ta
bararraje akan kujera don ada a takure a karshen kujera tana gudun kar yakaimata bugu tace duk abunda nafada maka agame da kaltum ba karya bane tayi niyyar komawa wajenka Allah baiyi ba,
mambela yace tunda kika bani wannan labari mai dadi har nayi dariya tokema zansaki dariya a rayuwar ki in shaa Allahu daga yau kindaina kuka fatsuma.

farin ciki ya rufe fatsuma tafara godia tunkafin ya fadi abunda zai yi mata,
mambela ya nisa yace menene matsalarki yanzu ?
Me kike so arayuwarki?
kinaso kikoma kasarku Nigeria inbiya miki kudin mota kokuwa a Khartoum kike son zama nabaki jari?

Fatsuma tayi caraf tace nafiso nazauna a Khartoum inyi aure ni da mijina mutara kudi mu tsallaka saudiya saboda abun kunyane yanzu in koma garinmu babu hakorin Makkah, ace banje saudia ba dadinta ma nakoyi larabci a sudan, idan suka ji ina larabci wasu zasu yarda amma kuma nayi baki na rame bazasu yarda saudiya naje ba.

mambela yayi dariya ya girgiza kai yace yaranta mai dadi, nikuwa aganina babu gatanda za amiki kamar asaki a mota kikoma wajen iyayenki sune gatanki sai kiyi aurenki a mutunce.

fatsuma tace ai saurayina da nake bala'in so musa anan garin yake yace bazai koma nigeria ba saiya koma makka don da niyyar haka yataho.
mambela yace shima dan garinku ne?

fatsuma tace shi dan maigatarine nikuma yar
malam madorine duk acikin jahar jigawa muke bamuda nisa.

mambela yayi shiru kamar mai tunani can ya
nisa yace tunda haka kikafiso bari nafara ganin sa tukunna sai inji a ra'ayinsa game da shawarar da kikayanke idan naga yanada hankali kuma yanason auren sai kuyi ku zauna inbashi jari ya rike ki in Allah yasa kuntara kudi saiku shiga makka.

fatsuma ta kwashe da dariya tace bari inkirashi awaya ma yazo yasamemu anan asibitin, nasan yanzu yataso daga gun aiki.

mambela yace har aiki yakeyi kenan aibakuda matsala ma sosai.

fatsuma tace eh dako yakeyi akasuwan markadi anan muka hadu bari na kirashi ka ganshi ta zaro wannan gwabjejiyar wayanan ta ta wanda sai andaki bayanta take kawo wuta takira abun kaunarta musa ta fara koro masa bayani kenan yahango ma'aikatar jinya sun riko hannun kaltum suna fitowa da ita daga dakinda akayi mata aiki dan haka yataso da sauri ya iso garesu cike da kulawa kalma daya ne ya fito daga bakin shi shine sannu ,sannu kaltum da ciwon har yanzu ko ya daina?
da sauki tafada a kunyace

fatsuma ta taso da sauri ta rike hannun kaltum suna hada ido sai suka tuntsure da dariya wannan dariya tasu tabawa mambela mamaki dominshi ya rasa abun dariya anan.
magunguna cike da leda ya saya mata suka dunguma suka fito daga asibiti,
tafiya sukeyi ahankali saboda dingishinda kaltum keyi, fatsuma na rike da ita mambela kuwa a gabansu yake yana tafiya a hankali suna isa bakin titi sai mambela ya nufi wani katafaren kanti a tsallaken titi, su dai suna biye dashi suna jiran suji abunda zai fada musu suka shiga ciki sai suka iske kata faren waje ne a lailaye da tiles fari mai dauke da teburi kashi-kashi masu kujera hurhudu a
kowani teburi fulawowiyi ne a kowace kusurwa ga A.C mai sanyi da fankoki kana tura kofar gilashi sanyi da kamshi ne zai bugi fuskarka, da alama kamshin abinci ne na alfarma ke tashi,

ma aikata suka taresu da fara'a yayinda aka
nuna musu wajen zama suka zauna doguwar
takarda aka mikamusu mai dauke da hotunan abinci kala-kala da sunayensu da farashin ajiki ma'ana su zabi wanda sukeso sai akawo musu,
mambela ya zaba ya nuwawa ma'aikaciar, sannan ya mikawa su kaltum,
fatsuma ta zaba, kaltum kunya ya hanata ta zaba don haka mambela ya zabar mata, shinkafa da taliya mai tiriri aka fara kawowa farati uku sai ga farantin miya kala-kala, kifi ne a bankare game da wasu dakwalen kaji sun yi rashe-rashe akan faranti , salad ne hadadde gami da kayan marmari a yanyanke wato fruit salad . lemuna (freshe juice )a kofuna aka kawata shi da tsinken tsotsa.

kamar a mafarki haka sukejin kansu yayinda
farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu,
mambela da fatsuma basu jira komai ba suka fara ba cikinsu hakkinsa yayinda nauyi da kunya ya hana kaltum ci ya juya ya dubi fatsuma yace me ya hana kawar ki cin abinci ?

Fatsuma tayi dariya tace tun dazu take taka min kafa tana mintsinina wai intashi mu
chanza tebur ba zata iya ci a gaban ka ba,

mambela yayi dariya ya dauki farantin abincinshi ya canja tebur ya juya musu baya
sannan kaltum tazage ta dinga tura abincin nan, kasancewar da dad'addiyar yunwa ce atattare da ita rabonsu da cin abinci tun na jiya da rana basuci ba suka kwanta da safe suka farka da gagarumar rigima a gidansu, don haka da kyar suka tsira babu zancen nemo na karin kumallo,
suka ci suka yi nak duk cikinsu babu wanda bai yi cinda da kyar yake juyiba.
mambela ya biya kudi mai dunbim yawa saboda restaurant ne mai tsadar gaske yana daya daga cikin wajen cin abinda yake tashe a babban birnin Khartoum,
kai saye bakin titi suka nufa a inda suka tsayar da taxi suka shiga suka zauna kamar dazu,
mambela ke zaune a gidan gaba ya juyo ya
dubi fatsuma fada masa sunan anguwanku da mu saukeki, nida kaltum zamu wuce tashan jirgin kasa zuwa bur sudan,

cikin fargaba ta dafe kirji tace '' yanzu da kaltum zaka tafi yaya zanyi ni kadai?

sai hawaye ya surnano daga idanun ta, kaltum kuwa farin cikine mara misaltuwa ya kamata sai itace tafadi sunan anguwan domin fatsuma ya hanata magana, kaltum ta dafata tana lallashinta game dayimata tayi idan tanaso ta biyosu ta kaura bur sudan suje cen suyi zamansu,
fatsuma ta girgiza kai cikin harshen hausa tace aure zamuyi da musa bari ma insake kiransa awaya kafin ku wuce yazo kofar gidanmu su hadu da mambela, yace yanason
ganinsa zaiyimasa zancen auren mu idan da gaske yana son aurena mambela yace zai bamu jari mu zauna,

farin ciki ya rufe kaltum ta mika mata hannu suka tafa ta ce ai shikenan tunda duk muna tare anan, kizo nima inzo,
fatsuma tayi murmushi dadi ya lullubeta tazaro wayanta ta bugawa musa kafin tayi magana yace na shirya ganinan zuwa wanne asibiti zanzo yanzu?

fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,...
.
Allah sarki, har mambela ya bani tausayi, yadda naga yana ta rawar jiki akan kaltum bai sai ina dap da kwace ta ba..
Yayi abu mai kyau tunda yana kiwata min mata 😊 😊.
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 30.
.
TRUE LIFE STORY.
.
fatsuma tace kazo gida ka same ni yanzu mun taho yama fi kusa,
suka isa kofar gida yayinda mambela da direba suka tsaya a mota, fatsuma da kaltum suka nufi cikin gida harsun kusa shiga gida mambela yayi kiran sunansu suka waiwayo atare sai suka ga mambela ya tunkaro inda suke,
suka tsaya suna dubansa suna mamakin Kiran, yakaraso inda suke yace kaltum ki shiga kiyiwa mutanen gida sallama kifito mu tafi kada mu rasa jirgi, duk tarkacen kayan nan na tsummakarai kibarsu zan saya miki wasu a can,
kaltum da fatsuma suka hada ido suka tuntsure da daria,
kaltum ta ce wanka zanyi da sallah kawai na fito,
mambela yace nidai bazan sallami direba ba bari inje nima inyi sallar azahar kafin ki fito...
kafin mambela ya rufe baki fatsuma tace lah ga musa yazo kuzo mu gaisa, musa ya karaso inda suke gami da mika wa mambela hannu suka gaisa, musan sun kuwa dace da fatsuma dai-dai gajere bakikirin shan koko daukan rai shine wanda takeso duk duniya bata ganin ko wanne namiji da gashi sai shi, shine gwaninta, musa babu kamarsa musa ya mikawa mambela hannu suka gaisa duk da fatsuma ta fara masa bayani amma bai gama fahimta dukka ba don haka sai ta fara kara masa bayanin tunda gashi ga mambela, wata murya ne abayansu akace yauwa ga kaltum din don haka dukkansu suka waiwoyo atare cike da mamaki,
mariya sukagani daya daga cikin yan dakin su kaltum tare take da wasu dattijai guda biyu mai kiba da siriri senye suke da manyan rigunan malum-malum da alama dai hausawa ne, tafiya suke suna sabe riga suna sauri kamar zasu kifa da kasa, da alama awahale suke mariya tace kaltum ina kika shiga wadan nan mutanen tun tsafe suke neman ki?

kaltum ta dubesu cike da mamaki amma bata san su ba don haka sai ta zura musu ido tana sauraro taji meke tafe dasu haka mambela ya sankare a tsaye yana sauraronsu kafin su yi wata magana sai wayan mai kibar ta fara ruri yayi sauri ya duba sai ya latsa gami da cewa AlhamduLillah ga kaltum din muna tare da ita sai yanzu aka nemo mana ita, rike wayan ya mikawa kaltum waya ta mika hannu ta karba a sanyaye kafin ta daura a kunne sai ta kalli mambela ya gyada mata kai alamar ta amsa sannan ta daura waya a kunne tana sauraro batare da tayi magana ba, kaltum ta zazzaro ido ta dafe kirji da alama zuciyarta ce ta buga saboda mummunan firgitan da tayi, kan kace kwabo ta fara karkarwa idanunta ya kawo nan take su zatonsu mutuwa aka fada mata, mambela ya fada cike da damuwa cikin larabci kaltum lafiya dawa kike waya?
meyake faruwa?

Ta katse wayar da sauri dan gigicewa ta fashe da kuka.
yaya kika kashe wayan bayan baku gama magana ba?
inji katon mutumin ya karbi wayan ya sake latso lambar ya mikawa kaltum a fusace ya fada cikin fushi ki amsa waya malama ana nemanki tun tsafe meyasa zaki kashe wayan?

ta karba ta sake karawa akunne haryanzu batayi magana ba sauraro kawai take mutuminda yake mata magana awaya ya sake magana yace hello kaltum kina ji kuwa?
ni ne alhaji Adnan daga kano kitattaro kayanki ki biyo wadannan mutanen yau din nan ku taho Nigeria, nabasu kudi zasuje office din immigration ayi miki passport ku hawo jirgi ku taho gida kinji na fada miki kada ki yarda ki sake subucewa a rasaki arasa yan aike.

kaltum ta juyo ta dubi mambela ta cigaba da sauraron abunda alhaji Adnan yake fada yayinda tashiga rudani mai yawa takasa tantance yanda zuciyarta ta karkata, saboda tana matukar son mambela tanaso ta zauna dashi don tana da kyakkyawar zato akansa zai riketa amana, ta yarda da tsantsan sonda yake mata saboda Allah haka bataso ta sabawa alhaji Adnan a matsayinshi na mutum da yake kulawa da ita wanda bayaso yaga ta tozarta, mutuminda yake ta salwantar da dukiyansa wajen kokarin nemota ta dawo gida, ya damu da ita kamar yar da ya haifa ta cikinsa shine cinta da shanta iliminta da lafiyarta, magana yake mata cikin damuwa da fargaba don kada ta subuce..

kwakwalwar kaltum ta dinga jujjuyawa a kokarinta na tantance da tattace abunda zaifi alkhairi a rayuwarta don gudun fadawa dana sani nan gaba, sai ta tuno kyakkyawan kulawa da alhaji Adnan ke bata tasan tabbas idan ta koma Nigeria makaranta zata koma ta karasa sakandari harzuwa jami'a, babban burinta kuwa a rayuwa shine ta ganta a jami'a ta hada digiri amma data tuno halin ko inkula da iyayenta ke mata da irin gallazawa irin na goggo fattu da take mata don kadan daga cikin halin goggo fattu ta dawo daga makka tace zata dauketa sukoma makkah iyayenta kuwa ko musu bazasuyi mata ba yarda zasuyi,
sai ta dubi dayan bangaren kuma wato mambela mutum ne mai kyauta da kyautatawa yana sonta yana bata duk abunda takeso basai ta roka ba sannan ta tuno rayuwarta da madina a bur sudan rayuwar yanci dajin dadi wasa da dariya da tsalle-tsalle, abinci ya wadata babu yunwa ko kishir ruwa tace aranta bazan koma Nigeria ba gara ingama rayuwata a bur sudan...

alhaji Adnan ya katse tunaninta data tsunduma tanayi yace kaltum magana fa nake miki bakice dani komai ba?

cikin kuka da sanyin murya tace na'am dady,
jin muryan kaltum ne yasa alhaji Adnan doguwar ajiyar zuciya game dayin hamdala a cikin zuciyarsa domin sai yanzu dayaji muryanta ya tabbatar da cewa da kaltum dinsa yake magana saboda yana kokonto ko ba ita bace, ya yi farat ya mike daga luntsimemiyar kujerar daye juyi a babbar offishinsa dake Abuja babban birnin tarayyah yafada cikin zumudi da farin ciki kaltum kece ?
To naji dadi yanzu abunda nakeso dake shine ki biyo alhaji sa'adu da alhaji jabiru ku taho nigeria sauran bayanai in anzo za ayishi wahala da gallazawa da su Fattu suke nuna miki a da ya wuce rayuwa ce mai kyau da kyanciyan hankali zaki samu a Nigeria, me zakiyi da rayuwar wahala har bara akace kinayi ni, alhaji Adnan ina raye a duniya kaltum kiyi bara?
InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un..
sai kaltum ta fashe da kuka ta girgiza kai tace daddy ka yafe mini banyi niyyar saba maka ba, nasan kokarin da da kayi akaina amma bazan iya dawowa Nigeria ba, yanzu zanbar Khartoum inkoma bur sudan inda nafi sabawa dasu zan auri mambela domin shine mai taimakona..
acan alhaji Adnan ya dafe kirji yafada cikin gigita kaltum waye kuma mambela ?

Kaltum ta sharce hawaye tace mambela dan ADON DAWA.
ne alhaji Adnan ya sulale yayi zaman dirshan a kafet yayinda yasa hannu ya fisgo hulan kansa don tayimasa nauyi a halin yanzu wayar ya ajjiye a gabansa yana duba batare dayasan abunda zai yi ba, ji yake tamkar ya huda wayar ya ganshi a Khartoum kusada kaltum ya damkota ya dawo da ita gida, zufa yaketa hadawa duk da babbar rigace a jikin sa ai akwai sanyin split A.C a offishin,

tsabar tashin hankaline kawai kaltum ta mikawa mai kibar wato alhaji sa'adu wayansa ta koma bayan mambela ta labe har yanzu mambela acikin rudani yake don bai tsinci kalma daya ba a cikin duk wannan bayani da akeyi ba, ya juya ya dubi kaltum cikin harshen larabci yake tambayanta wai meyake faruwa ne?

saita rushe da kuka yayinda kukanta yake sake daga masa hankali.

alhaji sa'adune ya duba wayarsa har yanzu sekonni na tafiya ma'ana alhaji Adnan yana kan layi saiya kara wayar a kunnensa ya dinga magana sautin maganan ne ya ankarar da alhaji Adnan cewar su kaltum nakan layi basu kashe ba, saiya rarumo wayar ya kara ta akunnensa muryan alhaji sa'idu yaji yana magana, alhaji sa'adu yace yanzu ranka ya dade haka za a kyale yarinyar nan tayi abunda ta ga dama ?
Mufa da muke zaune a sudan mu mukasan wahala da wulakanci da mutanen mu suke gani,
alhaji Adnan yayi tambaya cikin fushi wai wani irin yare takeminne naji tace mambela zata aura kuma wai daga ADON DAWA anya kuwa ba aljanine ya auri yarinyannan ba domin a bil'adama babu mai suna mambela kuma aduniyan nan kakaf ban taba jin wata kasa ADON DAWA ba saidai in a garin aljanu, don haka kuriketa kada tashiga daji bada mutum take zama ba.

alhaji sa'adu yayi dariya ya subuce masa yace ranka ya dade mutum ne mambela, ADON DAWA kuwa kabilarsu ce, a bur sudan suke.
alhaji Adnan yace kai ya akayi ka sani ?
kana ganin mambela da idonka ko itace take fadamaka ?

Alhaji sa'adu yace ina ganinsa alhaji.
"alhaji adnan yace ka tabbata shi mambela datake fada kana ganinsa?

Alhaji sa'adu yace tabbas mutum ne saidai idan kuka kuskura kuka bar yarku ta auri wannan dan ADON DAWAn to mu'amalanku da ita har abadah, a cikin dawa suke rayuwa gidan katako da 'kaya, abincin su dabino da madarar shanu ce kawai.
hankalin alhaji Adnan yakara tashi baisan sanda ya yaye babbar rigar sa ya wurgarba ya mike saye yana magana cikin daga murya da dukan bango har ma' aikatansa suka dinga rugowa a guje zuwa offishinsa don suga abunda yake faruwa sunsan ba lafiya ba, basu tabajin yana irin wannan hayaniya ba da daga murya kasancewar mutum ne mai sanyin magana cikin kamilalliyar murya, mutum mai hakuri da fara'a yau bacin ran kaltum yana sashi ruri tamkar zakin da yaga nama,
alhaji Adnan yace alhaji sa'adu da kai da alhaji jabiru nabaku amana kuma kun karba nace ku yanke da kanku yawan kudin da kukeso da kanku kunyi kokari kunnemomin kaltum kamar yanda kukace inyi zamana basai nazo ba zukuyimin komai gaku ga kaltum ga kuma aljanin saurayin ta mambela kuna tare ni ina Nigeria sannan zaku dinga tambayana abunda zakuyi?
alhalin kunsan ra'ayina shine ku kawo mini kaltum gida ko tana dariya ko tana kuka duk yanda zukuyi kuma duk yanda za ayi karkubar kaltum ta subuce muna bukatarta anan, idan kwatarta zai muku wuya to ku kira yan sanda su kaiku kotu a fara shari ' ah nikuma kan a gama zanshigo sudan din ayi dani kungama aikinku.

alhaji sa'adu ya tuna makudan kudinda alhaji Adnan yayimusu alkawari mai dumbin yawa sai jikinsa ya hau makyarketa kaikace dan taure ne.
yace alhaji Adnan kwantar da hankalin ka daman ra ayinka nakesonji ko ka canja kuma ina neman izini kar rigima ta kwabe kace baka sani ba ace mana mu masu satar mutane ne hukumar sudan kuwa tanada zafafan hukunci akan masu aikata irin wannan kazaman laifi, kabani nanda minti goma zan sake kiranka kaji halinda ake ciki sannan suka kashe waya.

mambela ne ya fusata ya damko gashin kaltum ya wujijjiga yana magana cikin gigita dazubo da hawaye mai yawa yace kifamin abunda yake faruwa anan kunzamar dani mushe a tsaye bansan meyake faruwa ba kuma gashi sai anbaton sunana akeyi wai shin laifi nayi dana baro garinmu nafito nemanki a Khartoum don in ceto rayuwarki da kuma nuna miki kaunar da nakeyi?

kaltum ta rusa kuka harda kurma ihu kaikace rai ake fitar mata,
fatsuma ta karaso da gudu ta kwaci kaltum a hannun mambela abun mamaki saiyaga fatsuma kukan takeyi sannan ta fara yi masa bayani abunda yake faruwa,
data kira sunan alhaji Adnan sai ya tuno da sunan wato kishiyarsa don haka sai yayi shirin gagarumin rigima a zuciyarsa yasan yau za ayi dayan biyu koya kashe ko akasheshi wajen kwatar kaltum,
sai yayi wani irin dariya mai ban mamaki ya juya yadubi kaltum wanda har yanzu tana rungume ajikin fatsuma yace kaltum kije kishiga cikin motar can taxi ki zauna gani zuwa..

jikin kaltum na karkarwa ta juya aguje ta nufi inda motar take yayinda alhaji sa'adu ya cire babbar rigarsa ya hada da hular dake kansa ya wurgar akasa ya damkara da gudu ya damko kaltum ta baya saiya fisgota tamkar kaza saboda rashin nauyi..
da mambela yaga haka sai ya fusata ai ko sekon daya ba karaba ya kaiwa alhaji sa'adu wani dankareren naushi a hanci yayinda jini ya wanke masa fuska nan da nan ya saki kaltum ya rike hanci ya durgushe.
da abokinsa alhaji jabiru yaga haka sai shima ya ya fisgo hannun kaltum ya tura keyarta cikin gidan su,
mambela ya yunkura zai hana sai alhaji Sa'adu ya mike a fusace ya cafki mambela da dambe...
.
Yayin da ni kuma Dan Aunty na tsaya kallon mafadata akan abar kaunata,
Wannan shi ake cewa '' kura da shan bugu... ''
A gama komai nazo na aure ta, shi kenan.
.
Sai kuma wani satin xaku jimu dauke da ci gaban .
.
Saady Dan Aunty 👫.ADON DAWA 31
.
TRUE LIFE STORY
.
jama'a suka farga kan kace kwabo an shiga tsakaninsu,
mata da maza sun firfito, masu wuce a kafa, babura ,keke da masu motoci duk sun tsaya kallo da neman ba'asi don a sulhuntasu,

zage zage ake tsakanin mambela da alhaji sa'adu yayinda dukkansu jikinsu na tsuma sunaso a sake su su kaure, zuciyoyinsu sun hargitsa karfine yazo musu yayinda hannayensu ya hau kaikayi, naushi kawai sukeso sukaiwa junan su,
larabcine ke tashi inda mambela yake dukan kirji yana cewa kaltum tasa ce babu mai dauke masa ita,
shima alhaji sa'du yana ikirarin baban yarinya ne mahaifi yasa a dauko masa ita don haka duk kotun da za aje sai dai aje amma bazai bar kaltum ta subuce masa ba, bayan watanni shida da suka kwashe suna nemanta a Khartoum gida-gida,

malam Abdulkadir aka kira ya fito daga gidansa da sauri hankalin sa atashe ance yazo ana wani fada a kofar gidansa,
dazu mata ne yanzu kuwa maza ne ke casuwa ransa abace sai karanto InnaLillahi wa inna ilaihi raji'un yake, yana ta jan dogon carbinsa, yana karasowa ya dubi mambela ya juya ya dubi alh.sa'adu yaga babu wanda ya sani a cikinsu, sai bacin ransa ya fadada cikin harshen larabci yace kukuma su waye daga ina ku kazo kofar gidana kuna dambe?
Dazu yan sanda sun zo ana can ana shari'ar fadan dazu ba a gama ba yanzu ma an ce antafi kira suzo su iske a kofar gidan ne kuma ?
Yanzu daman abun alkhairi zai zama sharri?
don nace duk mutanenmu wadanda ba su da gida suzo su zauna kyauta sai in zama abun tozartawa a garin nan?
sunan gidana ya shiga tsinuwa a bakin jama'a ?

Alhaji sa'adu ya fara jawabi cikin harshen hausa ya yiwa malam dalla-dalla akan abunda ake ciki

Kowa ya gamsu don haka kobin ta bakin mambela ba ayiba malam ya yanke hukunci nan take kaltum baza tabi mambela ba, kasarsu za a mayar da ita domin shima babban burinsa kenan, duka manyan matan nan da yammata da kananan yaran dake zube a gidansa su wa kansu fada su koma kasarsu cikin gata da yancin kai.

kaltum tanajin haka saita kurma ihu ta fadi tana kuka, fatsuma na riketa itama kukan take taya ta, sauran matan gidan kuwa hayaniya sukeyiwa kaltum suna dungure mata kai suna cewa keba dadinki bane da har kika sami iyayenda suka damu dake su aiko a daukeki ko ba kece mai kuka da ihuba a sanda kalah ta karbi kudin iyayenki ta arce ta bar kiba?
Me ya yi miki zafi da zaki koma bur sudan da rayuwa kauyen da babu wuta babu ruwa babu wayar sadarwa, kakaf garin babu gidan siminti sai na katako, amma ki koma Nigeria kasarki a najeriyan ma a babbar birnin kano ai kin caba don haka ki tashi kibi mutanen nan kawai.

cikin kuka kaltum tace saceni zasuyi malam bazan bisuba.

sai jikin malam yayi sanyi ya dubi Alh.sa'adu yace da kamshin gaskiya idan anbi ta barawo sai abi ta mabi sawu, ku su waye ?
Kuma daga ina kuke ?

Alh sa adu yace nima mutumin kano ne amma bazan ce muku komai ba bari na hadaku da mahaifinta awaya kuyi magana, ya latsa number alhaji Adnan nan da nan ya amsa alhaji sa'adu ya ce alhaji rigima fa aketa tafkawa yanzu haka an fasamin hanci yana jini saidai yarinyan tace bata san mu ba saceta zamuyi shine nakeso kayiwa wani dattijo bayani wanda kusan kaltum a hannunsa take don ya gamsu, a gabansa abawa kaltum waya kayi mata magana don idan ita bata san mu ba mu barayin mutane ne kai ai baza ta kiraka barawo zaka saceta ba, alhaji sa'adu ya mikawa malam Abdulkadir waya suka dade suna magana daga karshe malam Abdulkadir ya fahimci ashe kaltum jikar fattu ce, fattu kuwa tare sukayi wasa a zangon Daura .
don haka ya yarda kaltum tabi wadannan mutane,
da yan sanda sukazo malam ya kora musu bayani cewar ba rigima bace don haka basai an tafi police station ba,

mambela yanaji yana gani aka tafi da kaltum cikin gidan malam tana waiwayensa yayinda shi kuma mambela a tsaye, musa da fatsuma da mai taxi suna lallashinsa hawaye yana zuba daga idanunwansa zuciyarsa kamar zata fashe dan tsananin tafarfasar da takeyi,

fatsuma ta sharce hawaye tace da mambela yayana mambela zantaimake ka ka sami kaltum, kamar yadda baka san mu ba ba nida musa ka kudiri aniyar zaka taimake mu.

mambela ya koma ya zauna a cikin taxi gidan gaba yayinda ya jingina da kujera, ya daga kansa sama ya cije lebe wannan shine ake kira ga samu ga rashi ya samo kaltum da kyar amma ta subuce masa yana ji yana gani,

mambela ya yunkura zai tashi a fusace musa ya mayardashi,
yace da musa kabarni inshiga cikin gidan malamin nan muyi duk abunda za ayi kosu kasheni ko in kashe su saboda alkawari nayi saina lahanta duk wanda zai rabani da kaltum...

musa da direba su kayi kukan kura suka danneshi ya koma ya zauna,
sunfi minti talatin suna bashi baki sannan ya yarda zaitafi,
Su fatsuma suka shiga motar suma aka tafi dasu zuwa tashar jirgin kasa ta zuwa bur sudan,
cikin hawaye mambela ya zaro kudi mai yawa ya bawa mai taxi, farin ciki ya rufe direba ya dinga yi masa addu'ar Allah Ya bashi kaltum Ya kwato masa ita daga hannun wadancan. mambela ya amsa da Ameen ya juya ya dubi musa da fatsuma yace ina yi muku fatan alkhairi a shirin aure da kuke yi, kuma ina baku goyon baya dari bisa dari nayi alkawari zan taimake ku ba ku kadai ba ma duk wasu masoya da suke son junansu zan taimaka masu duk rintsi su auri junansu duk na sadaukar wa kaltum.....
sai hawaye ya kara kwaranya harya kasa ci gaba da magana.

saisuma suka fara kuka don tausayinsa, can ya juya ya dubi musa yace a halin da nake ciki yanzu bazai bari muyi wata magana ba
saidai kawai duk sanda ka shiryo kazo wannan tashar kahau jirgi kazo Khartoum Tutti ka gangaro bur sudan kusa da ruwa zakaga garin yan kasarku hausa, sai kace sununa maka garin yan ADON DAWA gidan sarki kokace musu mambela kake nema, ko karamin yaro ka tambaya mai shan nono indai ya iya magana to yasan sunan mambela, idan bana gida to za a rakoka bakin kasuwarmu Jim Arab nanne kadai wajen zuwa na, kazo mu zauna muyi magana game da auren ku, nayi alkawarin zancanja muku rayuwarku da izinin Allah amma da sharadi guda daya, idan har kasan bada gaske kakeson fatsuma ba yaudaranta kake kada kazo inda nake, kaga fatsuma amanace a wajanka inhar ka yarda ka aureta kaine uwa Kaine uba a gare ta, don batada kowa a kasar nan, tunda wuri ka fadamin gaskia sai inbiya mata kudin jirgi tabi kaltum su koma Nigeria.

nan take suka zaburo don tashin hankali saboda suna kaunar junansu baza su iya rabuwa ba sai su duka suka durgusa a gaban mambela suna rantse-rantse cewar zasu zauna amana,
sai mambela ya sake shiga damuwa yasake tausayawa kansa da kaltum, ku mike tsaye kada ku damu zaku zauna tare, Allah Ya baku zaman lfy da zuri a ta gari, sukace kaima Allah Ya baka kaltum ya kwatota ta dawo wajenka ka aureta da yardar Allah.

mambela ya girgiza kansa yace ada dana rabu da kaltum zuciyata ta kasa fitar da ran zanganta kuma nazo naganta a halin yanzu banji ajikina zan sake haduwa da kaltum ba har abada, nasan na rasa ta kenan ko bayan mutuwata kuka hadu da ita ku shaida mata ina sonta bazan daina sonta ba kowa na aura kuma kome na zama a wannan dunia,
kuka da hawaye yabe-yabe mambela , musa da fatsuma keyi harsuka rabu.
ya yanko tikiti yaje yahau jirgi ya zauna yayinda suke tsaye agefe suna daga masa hannu basu baro tashar jirgin kasa ba sai da jirgi ya tashi sannan suka juyo gida Jiki a sanyaye.

al amarin malam Abdulkadir dasu alhaji sa'adu kuwa suna shiga gida a falon malam Abdulkadir aka zauna aka sake mayar da magana da alhaji Adnan a waya aka tsayar da shawarar kaltum bazata sake fitowa kofar gida ba, a dakin matar malam zata zauna har tsawon kwana biyu har a gama cuku-cukun tafiya,
malam yace da kansa zai rakasu har filin jirgi yaga tashinsu.

kaltum ce zaune a falon Manal amaryan malam Abdulkadir kenan, budurwa ya aura yar kasar sudan ce,
kaltum tayi kuka ta gaji don haka ta hada kafafuwanta ta kifa kanta ta kanannade don takaici, abinci mai lfy ne a gabanta miya ce nashe-nashe da kaji masu maiko amma ko kallo basu isheta ba balle ta dandana.
Manal tayi larabcin duniyan nan wajen lallashin kaltum don ta daina damuwa taci abincin nan abu bai yiyuba, saita shiga yi mata nasiha akan to ta tashi tayi sallolin da ake binta sannan tayi addu'ar abunda yafi alkhairi.

kaltum batada mafita ita kanta tasan addu'a ce kadai mafitarta don haka ta tashi tayi sallah tana kuka tana fadawa mai duka, amma idan tayi addu'ar Allah Ya zaba mata abinda yafi mata alkhairi sau daya sai ta roki Allah Ya mayar da ita wajen mambela sau goma dan shi zuciyarta tafi so.
kaltum tana son mambela a halin yanzu tafi sota zauna dashi data koma cikin yan uwanta data zauna da alhaji Adnan abun kaunar ta.

tsowon kwana uku kaltum na cikin gidan malam daga daki sai bandaki duk inda tayi ana biye da ita ana zuba mata ido, a cikin gida ma kenan balle a kofar gida inda yake dankare da malamai da almajirai ta ina zata fice ai bazai yiwu ba, kamar yadda ba a bari ta fita ba haka aka hana kowa ya shiga ya ganta, duk irin nacin da fatsuma tayi don a barta taga kaltum ba a barta ba.

ranarda kwanaki uku suka cika a lokacin komai na tafiya ya kammala alhaji sa'adu ya iso gidan malam dauke da tikitin tafiyarsu a hannu, yazo ya nuna wa malam yace karfe takwas na dare ne buking din su,
don haka karfe shida na yamma kaltum dasu malam suka dunguma suka fito yayinda fatsuma da yan gidansu suka yo waje a guje, waje ya dauka da hayaniya cewa ake ku fito na cikin gida kaltum zata tafi...

lah kaltum tafiya zakiyi?
da dai sauran surutai irin na mata.
malam ya umurci kaltum da ta shiga gidansu ta dauko buhun kayanta tazo su tafi, sai ta girgiza kai ta sharce hawaye tace nabarwa fatsuma dukka tayi amfani dasu.

fatsuma ta kamkame kaltum tana kuka tana cewa yanzu kaltum tafiya zakiyi kibarni?

Sai da malam Abdulkadir ya hada da shauda mata carbin hannunsa sannan ta saki kaltum, dan anyi mata maganar duniyar nan ta saketa taki, malam ya dubi fatsuma cikin fushi yace wannan yarinya rawar kanki tayi yawa ke kike sake tunzura kaltum kike kara sata kuka idan bakiyi wasa ba sai na koreki daga gidana yau din nan,

fatsuma najin maganar kora saita nitsu don idan aka koreta yanzu ina zata nufa?
musan nata da take takama dashi su shidane a shago daya suke haya.
a ina za a cashe idan bikinta ya tashi inba a
makeken tsakar gidan nan na malam ba?

saita koma gefe tayi tsuru da ido, da niyyarta dama ta tubure tace saita shiga motar tabisu airport, kaltum ce ta shiga gaban taxi malam da alhaji sa'adu suka shiga gidan baya,
yan gidan suna dagama kaltum hannu itama tana daga musu yayinda direban mota ya fizgi mota,
kaltum kuwa jiniyar kukanta ta barke, malam da alhaji sa'adu kuwa sukace dawa Allah Ya hadamu inbada kaltum ba sukatayi mata surutu har suka kai filin jirgi suna cewa inbanda yarinya da rashin hankali ina za a hada zaman sudan da Nigeria?
ke a najeriyan ma yar gata ce yar gidan masu hali zakiyi iliminki asirinki a rufe ki zauna kina wulakanta kanki a nan?
daga bara sai tsince-tsince a bola.

kaltum dai tayi mukus tana sauraron su kukanne bazata daina ba.
kaltum taga yanda mata suke cin ado a filin jirgin nan na Khartoum ai sai ta raina kanta ta ganta tamkar daddawa a cikinsu duk da wannan pink lafayan nan da mambela ya siya
musu ita da fatsuma ce ta wanke ta saka takalmin ma sabo ne wanda mambela ya saya mata ga matar malam ta bata sabon siket da farar t shirt daga ciki ta saka ta cire yagaggu na da, ashe da bata carallee ba abar gudu da kyama zata zama a cikin jirgi, nan sabon brush matar malam ta siya mata ta wanke bakinta tas turare kawai bata samu ta shafaba saboda yanzu Abbas baya bata, matar malam kuma bata bata ba amma duk da haka kayanta na kamshin koren sabulu na wanki ,
ina laifinta abunda kaltum ta dinga zaiyanowa a zuciyarta kenan don haka ta saki jikinta a cikinsu bayan anyi musu screening sai aka yi bording suka shiga cikin jirgi suka zauna duk da ta taba shiga jirgi tana karama amma sai taga kamar bata taba shiga ba.
Domin ganin jirgin tayi tamkar aljannar dunia do kyau saita tsinci kanta tana mai farin ciki harda murmushi, Alh sa'adu ya juyo ya dubeta ya tabbatar murmushin takeyi ba gizau ba yayi dariya yace ja'ira waya fada miki borno gabas take?
ana so a ceto ki kina ki har kika ja wannan aljanin saurayin naki yake kokarin ya cire min hanci,

sai kaltum ta sha kunu ta tura baki don taji ya fara cewa abun kaunarta mambela mutunci.

kujeru masu zaman mutum uku ne, alh sa'adu ne a jikin wundo kaltum a kusa dashi sai wata matashiyar mata mai suna Hajir a karshe, tunda suka zauna Hajir ta dinga surnanowa kaltum larabci tana jero mata tambayoyi.

kaltum bata bata amsa ba saboda a tunanin Hajir kaltum yar sudan ne hutu zai kaita Nigeria,
Hajir ta shaidawa kaltum cewa ita yar Khartoum ce ta auri wani hamshakin dan kasuwa a kano yanzu haka kakarta ce ta rasu tazo tayi gaisuwa zata koma.

kaltum tayi murmushi tace ni kuwa yar kano ce aure ya kawo ni bur sudan mijin ADON DAWA ne mai suna mambela.

Hajir ta damke baki don mamaki tace keko meya miki zafi da zaki baro kano birnin garin
arziki ki taho sudan a sudan dinma a bur sudan?

alhaji sa'adu ya zabura yace karya fa takeyi bata da wani miji abur sudan.
sai aka hau kalon kalo tsakanin Hajir da kaltum da kuma alhaji sa'adu batare da wani yasake magana ba a cikinsu.
mamaki mara misaltuwa zaka iya gani a cikin idanuwan Hajir, ta shiga tunanin meyasa kaltum zata mata karya irin wannan alhali karyan ma bata dadi bace ?
ko kuwa wannan mutumin ne ya ke karya ?
To ko babanta ne yaje ya raba auren ya dauko ta zai mayar da ita garinsu ita kuma tana son mijin ta?
kwarai haka ne ma don daga gani kaltum anga wanda ta kwaso da talauci. abun da Hajir ta dinga sakawa kenan a cikin ranta kenan,
jirgi ya tashi ya bar Khartoum ya lula cikin gajimare da izinin Ubangiji yayinda fasinjoji suka hau tofa addu ar nan ta matafiya wacce shugaban halitta ya koya mana, '' Allahu Akbar, Allahu akbar , Subahanaanal laziii sakkhara lana hazaa wama kunnaa lahu mukrinina wa innaa ilaa Rabbina lamunkalibuuna, Allahumma innaa nas'aluka fii safarinaa hazaa birra wat tak'waa wa minal amali maa tardha ,Allahumma antas saahibu fis safari wal khaliifati fil ahlil ,Allahumma innii a uzu bika min wa,asa'a'is safari ,wa ka aabatil manzari wa suu il munkalabi fil maali wal ahali.''

yayinda kaltum ta runtse ido hawaye mai zafi ya dinga zubowa daga idanuwanta tana fadin wayyo mambela a zuciyarta.

KANO NIGERIA

misalin karfe shida na safiyyan alhamis jirginsu kaltum ya sauka a malam Aminu international airport dake birnin kano, kaltum ta shaki iskar kasarsu saita lumshe ido taji sanyi a ranta atake taji ta fara farin ciki zataga kannenta da alhaji Adnan, ta tuno mahaifiyarta sofi da mahaifinta saleh sai taji tanaso ta gansu ma, tafi kowa sauri wajen shigewa gaba don saukowa daga jirgi da fitowa daga wajen bincike akayi aka gama suka fito waje inda kaltum take duban kanawa sai hausa sukeyi yayinda suma suke dubanta a matsayin bakuwa ba yar kasarsu ba,
musamman da suka ji ita Hajir sun juye harshe suna larabci, Hajir ta rubutawa kaltum nonbar wayanta a takarda ta bata tunda kaltum ta shaida mata batada waya,
Suna tsaye mijin Hajir da ya yanta biyu sukazo daukar ta, tana murna suna murna ta shiga mota suka tafi, sha'awarsu ta rufe kaltum ta ayyana a ranta dama ita da mambela ne suka sami sukuni haka..

kinsan hanyar gidanku idan muka shiga taxi?
alhaji sa'adu ya tambaye ta,
tayi shiru kamar mai tunani, yace idan bazaki ganeba zansaka layina na MTN na shaidawa alhaji Adnan munzo aiport ya aiko a dauke mu,
kaltum da zabura tace zangane gidan, domin bataso alhaji yazo tsoron haduwarsu take yanzu, kunyan bijire masa datayi takeji domin
ita kanta tasan baikamata ya turo azo daukarta kiri-kiri tace bataso tazo wajensa ba tafiso tabi mambela ba, alhaji sa'adu ya tsayar da taxi ya shiga gaba kaltum na baya tayi tsuru da ido, fargaba ta hadu mata da farin ciki suka cakude da takaicin rabuwa da mambela, tace da direba nasarawa G.R.A zaka kaimu babu bata lokaci direba ya manna da gudu yayinda kaltum ta tsura ido a jikin glashin wundo tana duban kanawa matan su da mazansu yara da manya sai hidindimunsu sukeyi, akasarinsu fara'a garesu kuma duk sun fito neman na kansu ga kasuwa iri-iri, haka ma'aikatan gwamnati kala-kala.
babu inda yafi kasarku dadi da yanci kaltum tafada azuciyarta yayinda ta hango almajirai akan bola suna tsintar gwangwanaye, taga ba'a hana su ba kuma zuwa zasuyi susayar ba bu mai hana su saboda suma yan kasane, sunada yanci ba kamar yadda su aka saka musu takum-kumi aka tsorata su da hukuma ba,
kaltum tana nuna musu hanyan tiryan-tiryan har bakin gidan ashe bata manta ba, a tunaninta ba zata gane ba duk a akwai canje-canje a unguwar da gidan amma bata manta ba, suka firfito daga mota, kaltum ji take tamkar a mafarki data ganta a tsaye a kofar gidansu, alh sa'adu ya fito da naira dari biyar ya mikawa direba sai kaltum ta zurawa kudin ido tana kallo domin ganin kudin tayi bambarakwai ba irin na sudan ba.

Muhammad da makwabcinsu ne yafara ganinta tsohon saurayin tannan nata, da farko baiganeta ba yayi mata kallo daya ya watsar sai tayi masa dariya har ya kawar da kai gefe, saidai yasake waiwayowa ya dube ta domin fararen hakoran nan nata masu haskawa har yanzu basu dafe ba suna kyalli duk sanda tayi daria, yace kamar kaltum?

ta amsa nice, sai da yahau salati yana mamakin yadda kaltum ta zama haka kamar ba ita ba, ta rame tayi baki ta zama bakauyiya, tundaganan jikin kaltum yafara sanyi tasan tazama wata halitta ba irin ta mutane ba tunda har Muhammad bai gane ta ba kuma ya tsaya yana tausaya mata,
suka tura gate sukaji akulle daga ciki ko bude gida ba ayi ba, bugu daya sukayi saleh mai gadi ya fito daga dan dakinsa na gadi ya bude musu da sauri da yake daman sun san da zuwanta don haka yau babu wanda yayi barcin kirki a gidan yaransu da manya, daga sunji motsi sai kowa ya bude ido,
alwalar asuba kuwa sun yi fiye da sau uku sai su ga ashe assalatu batayi ba saboda matsuwarda sukayi gari ya waye suga kaltum.

kallon-kallo ne tsakanin kaltum da mahaifinta, hankalinsa yatashi yadda yaga yarsa ta fige ta zama kaza ita kuma sai taga ya tsufa.

alhaji sa'adu ya fusata yace da malam saleh
matsa mu wuce kazuba mana ido inni ba kasan ni ba ai ita kasanta idan kuma batanan aka kawoka to yar gidan ne, yar gidan alhaji Adnan ce, daga sudan muke yasan da zuwanmu,
sai yaga kaltum da mai gadi sun hada ido sunyi dariya kaltum tace kai alhaji sa'adun nan kaci ka fada, babana ne fa,
ta durkusa ta gaishe shi sai yau yataba ambaton sunanta yana rawar murya yace AlhamduLillahi, kaltum naji dadin dawowarki da kika dawo kafin in mutu, Allah mai amsa addu'ar bayinSa, ki yafe mana kaltum..

sai su dukka suka rushe da kuka malam sale yasa hannu ya tashi kaltum tsaye daga sunkuyon da tayi suka dunguma cikin gida kai tsaye boys quaters ya nufa yana kwalla kiran sunan sofi!!
cewa yake ku fito ga kaltum ta zo, sofi ta manno da gudu abunka da mara kiba tazo ta rungume kaltum kuka take ta sharba ita ma taga uwar bari ko ina kunyar fulanin nan?

yayinda kaltum taga dandazon kannenta manya da yara da wasu guda biyu bata san su ba matane amma ko ba fada mata ba tasan kannenta ne, su kadaine sukayi kama da ita sak ta rumgumesu yayinda suke rera mata wakarda suka dade suna shiryawa ta marhaba da zuwanta, dadi ya rufeta ta shiga cikinsu tana tafi itama tana amsawa babu shakka hayaniyan nan ta isa kunnen makwabtansu ma balle wanda suke cikin gida,
daga ganin luntsumemiyar motar da ke tsaye a farfajiyan gidan kasan mai gidan yana gari wato alhaji Adnan fari mai farar aniya matashin dattijo mai tumbin naira,
.
Nima Dan Aunty baxa a barni baya ba wajen waka da tapi cikin murna, tunda ga masoyiya ta ta iso babu abun da xa'ayi sai shirin bikin mu ☺ ☺...
Masu son ganin wannan gaggarumin bikin su gyara xama, marassa so su gyara idon su dan gani....
.
Saady Dan Aunty 👫.ADON DAWA 32
.
TRUE LIFE STORY
.

Alh Sa'adu ya kosa yaga Alh Adnan don yasan karshen talaucinshi yazo yakawo masa kaltum har gida shima kuma yau zai cika masa aljihunsa da makudan kudin da yayi masa alkawari zai basu bayan kudin jirgi
daya tura masa na zuwansu da komawarsu.

malam saleh yayiwa alhaji saadu iso zuwa katafaren falonsa yace ya zauna kafin alhaji ya fito daga daki.
idonsa biyu bajimawa saiga alhaji Adnan ya fito sanye da doguwar riga jallabiya fara sol fuskarsa cike da murmushi, tafiya ce irin ta kasaita da nutsuwa, yazo ya zauna a luntsumemiyar kujerar da take tsakiyar falon, malam saleh ya sake durgusawa yayi gaisuwa yayinda alhaji sa'adu ya sulmiyo daga kan kujera ya zube ya kwashi gaisuwa, alhaji Adnan yaji duk baiji dadi ba dasuka zube a kasa yayi-yayi su zauna akan kujera sunki daman malam saleh duk yadda za ayi dashi bazai zauna akan kujerar mai gidansa ba don haka yakeyi tuntuni babu yanda za ayi ya zauna akan kujer mai gidan sa ko agabansa ko a bayan idonsa saboda
girmamawa.

Shi kuwa alh sa'adu daman baisan alh Adnan ba sai a waya, wani ya hada su dan haka baisan matsayinsa ba sai yayi abunda yaga yan gari sunyi yashiga tunani anya alhaji adnan ba gwamnan kano bane?
saboda haduwarsa da haduwar gidansa.

ina kaltum?
tambayanda alhaji adnan yafara kenan kafin yace komai nan da nan mahaifinta ya mike da sauri ya leka ya kwala kiran sunan kaltum
saida alhaji adnan yaji kansa ya daure don iya
saninshi baitaba jin ya kira sunanta ba. kaltum tashigo cikin falon a nutse cikin sanyin jiki tazo ta durkusa a gabansa ta gaisheshi idanuwanta a sunkuye a kasa, alhaji adnan yadau dogon salati fadi yake kaltum haka kika zama ba kya cin abinci
ko wanka ne bakyayi kika zama koso-koso haka?
subhan Allah, alhaji sa'adu 'kaya take ci a acan ne ta bushe haka ko azumin wata uku takeyi?
ai wannan ba tada jini ajiki sai ankara mata, jeki gida kiyi wanka ki cire dabaibayin nan iska mai sanyi ya shigeki ki shirya keda sofi direba ya kaiku asibiti bakida lafiya,

kaltum ta mike cikin sanyin jiki ta fice sai yanzu ta sake tabbatar wa ta tashi daga aiki,
tabbas tazama abun kyama abar kallo da nunawa a cikin yan Nigeria, duk talaucin gidansu ta gansu bul-bul sunfita kyawun gani, wanda yasan kaltum ada idan ba a fada masa itace a yanzu ba babu yadda zaiyi ya gane ta, farar yarinya dirarriya ta zama baki
kirin zololo kamar anyaga summa.

alh sa'adu yayi murmushi yace ai tayi kyawun gani a kwanaki ukun nan saboda a ranar da muka fara ganin ta abun yafi haka lalacewa don malam ya killaceta agidansane yabata abinci tayi wanka da wanki kuma ahaka take kokarin komawa kauye taci gaba da rayuwa, tabbas yakamata akaita asibiti domin wani sharcecen gyambone a kafarta da bandeji a yanzu haka,
alhaji adnan ya girgiza kai don tausayawa yajuya ya dubi malam sale yace ka naji da kunnuwanka kokuma kana gani da idanunka abunda kuka jawo wa yarku ta cikinku ko?
yanzu kaga illar kin bin shawata ai?

Malam saleh yadukar dakai kasa fadi yakeyi hakane alhaji ayi hakuri anyi kuskure babba baza a sake ba in shaa Allahu .
alhaji sa'adu ya gyara zama yanaso yaji lbr domin kansa ya daure yanda alhaji Adnan ya damu haka ashe ma kaltum bayarsa ta cikinsa bane yar mai gadin sace?
Lallai samun mutane masu kirki irin na alh adnan azamaninan sai an tona, taimakon talakawa saboda Allah alhaji sa'adu bai sami nasara an ansa masa tambayoyinsa ba alh adnan yace abar zance kawai su koma zancen abunda ya shafi tsakaninsu daman komai a lissafe yake alh adnan ya tura musu kudin jirgi da kudin wahalhalunsu na can yanzu makudan kudin da yayi alkawari zai basu ne ya rage inhar suka kawo masa kaltum har gida ba sako ba shine zunzurutun kudi har naira dubu dari biyu da hamsin. chafdi jam in fulani haka malam saleh ya bude ido da baki yana kallon kudin da bai taba rikewa a rayuwarsa ba,
alhaji adnan ya mika wa alhaji saadu batare da neman ragi ko gibi ba lalle alhaji sa'adu yaji wani iri, sai washe baki yake yana godiya amma malam sale yafi yawan godiya tunda saboda yarsa yafitar da wadannan makudan kudi, hawayene ya dinga zuba daga idanuwan malam saleh saboda farin cikin kaunarda alhaji adnan yake nuna musu,
alh sa'adu ya bude makamakan aljihunsa yadura kudin saf suka shige aljifan ya mike tsaye yana mai shirin tafiya yayinda alhaji adnan da malam saleh suka mike suma suna taka masa zuwa bakin get din fita,
alhaji sa'adu ya dubi alhaji Adnan yace idan irin haka ya taso a neme ni a shirye nake wajen taimakawa,
alhaji adnan yayi dariya ya ce Allah ma Ya kiyaye ai bama fatan Allah ma Ya maimaita mana irin wannan,
malam sale yace ai shi irin haka gaba takaishi don haka addu'a suke haka ya faru mukuma neman tsari mukeyi..
meyayi zafi ne haka maigadi ?
Ai ba abun bakar magana bane inji alh sa'adu.

alh adnan yace ya isa haka mungode da kokarinda kayi mana mukuma muna neman tsari da sake faruwar irin wannan, alhaji saadu yayi godiya ya tari babur ya haye yayinda alh Adnan yana yimasa nasiha dasu cire duhun kannan nasu nada su rungumi yarsu su nuna mata soyayyah kamar yadda kowacce ya take samu daga iyayenta, jahilci ne wannan kunyar ba addini bane,
da alama malam saleh yana gamsuwa kuma yana daukar gyaran kuskuren da ya tafka a baya,

kaltum kuma tana cikin gida ta fesa wanka da ruwan Nigeria, sabuwar atamfa sofi ta dauko mata abun mamaki musamman dan ita aka dinka aka ajiye mata, kannenta suka dinga biyo layi suna jera mata abinci kala-kala a daki kamshi tururu, taci ta koshi.

yayinda malam saleh yake faman duke-duke
yana zubawa alh adnan gunduma gunduman
godiya da shi albarka a jejjere, shikuma alhaji Adnan hankalinsa nacan wajen sofi yayinda take rike da gashin kaltum tana yanyankewa da almakashi a tsakar gida, sofi tayi-tayi ta warware bukuikuyayye hargitsattsen gashin nan da yayi wata bakwai ba a taje ba abu yaci tura don haka tayanke shawarar gunguntuleshi kawai kowa yama huta saboda yakoma wata halitta kamar ba gashi ba,
Sai bayanda aka aske gashin ne ma sukaga wani sabon abun tashin hankali a kokon kan sai kaga wata farar kura, ta dago sofi ta rushe da kuka yayinda kaltum ma tafara kuka hankalin alh Adnan yayi matukar tashi yayi magana cikin gigicewa da daga murya yace sofi maza tashi maza ki dauko gyalenki kikaita asibiti dan ladi direba yana nan zuwa, ba kuka zaki sata agaba kinayi ba ashe kinason yartaki kika wulakanta ta tuntuni ?
Ga illar da neke nuna muku kenan, zanyi waya asibitin infadi abunda yakamata ayi mata, kamata yayi ma su kwantar da ita har tsawon sati biyu ma suna dubata kuma don ta huta (bed rest) bai rufe bakinsa ba sai dan ladi ya bayyana ajikin get a inda yamasa horn malam saleh ya zabura zai ruga ya bude masa get alh adnan ya dakatar dashi yace karka bude basai ya shigo ba ku dunguma ku tafi tare asibitin tunda Abdul zai iya kula da yara harku dawo nima zanje nayi wanka in same ku acan, idan ba sai da zaman jinya ba da sai sofi ta dawo,
tafiya kaltum keyi zalo-zalo kamar mara laka ajiki harta shiga moto kanta a sunkuye akasa inda take gaskatawa tabbas ta tashi daga aiki tunda tazama abun kai wa asibiti akwantar don a bincika lafiyarta alhalin lafiyarta kalau babu inda yakeyi mata ciwo, ta
tabbatar tashiga rayuwar kulawa ba kamar rayuwar rashin gata datayi a sudan ba, tasan
tazama abar tausayi a gidansu kuma mai karancin lfy abar bincike don kada ta yada masu cututtuka,

alhaji adnan bai gushe daga bakin kofar gidan nan ba har saida ya daina hangen motar da kaltum da iyayenta suke ciki ya shiga gida yasa hannu ya rufe get yayinda ya
kwala kiran Abdul ya zaro kudi mai dan yawa ya bashi yace su sayi duk abunda suke bukata har iyayensu su dawo, ya durgusa harkasa ya karba yana godia,
alh adnan ya juya ya shiga gida yayinda ya lalubi numbern doctor ya buga batare data dade tana ringinba yaji ta amsa cikin ladabi docta Anisa ta gaisheshi ya ansa cike da kasaita domin yau ita kanta tasan tukunyar gidan ta saita kara zaki tunda mai girma alhaji adnan ya kira ta,
'' farin mutum mai farar aniya amma banda farar kafa, mai yayyafin kyauta kamar yayyafin ruwa acikin shuka sai ya raba har sai kowa ya samu '' kirarin da jama'a ke masa kenan,
yayi gyaran murya yace kanwata idan kina asibiti ki jirani idan kina gida marmaza ki garzaya asibiti yanzu na turo wasu yan uwana gurinki inaso ki bincikemin kaltum ciki da waje,
na farko inaso kiyi mata gwaji na ciki ,dana kanjamau ,sannan ki bincike ta shin cikekkiyar budurwace ko an lalatata?
Sannan ki duba ta taba haihuwa kota zubarda ciki ?

Dr Anisa Yahya ta dafe kirji ta bude baki don fargaba da tsananin mamaki duk da batayi magana ba yajiyo hucinta har saida ya fuskanci tashiga dimuwa, yayi ajiyar zuciya sai yayi dan murmushi yace nasan zakiyi mamakin irin wadannan bayanai nawa to dolece tasa za ayiwa yarinya budurwa irin wannan tonon silili, bata tayi har tsawon shekara uku sannan aka nemota cikin almajirai masu bara a can kasar sudan kinga komai zai iya faruwa saboda talauci.

Dr Anisa tayi ajiyar zuciya tace ayyah nafahimta ranka ya dade za ayi duk abunda ya kamata,
yayi murmushi yace idan kika gama ta bangarenki inaso ki hadata da kwararren likita da zai binciki gaba daya lafiyarta kamar koda,hanta,zuciya,sugar,gishirin jikinta da sauransu agani ko akwai wani organ da yatabu sannan abincika nasan ba zata rasa irinsu Ulcer ba saboda yunwa ko hawan jini saboda damuwa, idan aka gama sai ahadata da likitan kwakwalwa a bincika ko hankalinta ya tabu saboda tashin hankali idan duk babu matsala sai ki kaita wajen likitan fata yabata magani da mayuka da sabulai masu kyau wanda zasu fitarda kuraje,kirci,makero ,amosanin dasuka yayyame jikinta ta kokon kanta, daga karshe ku bata daki ita kadai ta kwanta tahuta sannan ku tsara mata time table na abincin da zasu gina mata jiki su kara mata jini,
idan kuma jininta yayi kasa sosai har sai an kara mata jini to saikiyi magana anemo asaka mata,
don Allah doctor kikula da ita sosai duk abunda ya kamata ayimata kudi ba matsala bane akwai isassun kudi a file dina adauka, amsa daya dr Anisa ke bayarwa na'am ranka ya dade an gama,
daga karshe suka yi sallama har suka kashe waya sunawa juna godia,

wanka kawai alhaji adnan yayi ya shirya ya fito ya zari luntsumemiyar motarsa ya nufi international hospital wajensu kaltum abunka da harkar naira gaba daya likitoci da aka bukacesu su duba kaltum sun hallara wannan najiran wancan ya gama da ita ya miko masa,
alh Adnan yaji dadi har ya yaba musu,
da yaga dr Anisa zata iya kula da ita sai ya umurci sofi da malam sale su tafi gida inyaso kullum Dan ladi ya dinga kawosu suna dubata har a sallameta, sofi da sale suna godiya cike da farin ciki suka shiga mota suka koma gida.

sakamakon dr Anisa ya kammala ta shaidawa alh Adnan kaltum tanada cikakkiyar lfy duk abunda yake zargi babushi a tare da ita,
sai yaji wani sanyi aransa da alama yana cikin farin ciki kudi mai yawa yabawa dr Anisa yace ta sayawa kaltum kayan sakawa masu kyau ta dinga dafa mata abinci masu gina jiki har tsawon zamanda zatayi a asibiti, baima sami ganin kaltum ba saboda tana can a dakin gwaji, yayi sallama da likitoci bayan ya gwangwajesu da naira ya buga motarsa ya nufi babbar burnin tarayyah Abuja, saboda yabar aiki dayawa zuwan kaltum ne yakawoshi.

kaltum tana kwance luf asibiti cikin kayataccen daki da bandaki aciki ita kadai tana kallon talabijan (settelite)baya ga kayan sanyi fal a firiji dinta, lemo sai wanda takeso zata bude tasha baya ga zuka-zukan kayan sakawa da tsukewa (english wears)akwati guda dr Anisa tasayo takawo mata kamar yanda oga Adnan ya umurceta,

likitocine da ma aikatan jinya (nurses)suketa kai kawo adakin suna duba lfynta da tambayar ko akwai inda yake mata kaikayi su sosa mata bama ciwo ba, ko kaikayi taji sunce ta fada musu su kawo mata agaji dariya kawai kaltum keyi domin taga gatan yayi mata yawa idan ta tuno rayuwarta abur
sudan, ta tuno rayuwar Khartoum sai taga akwai bambaci,
hakika tazo gida domin masu iya magana suna cewa '' kowa yabar gida gida ya barsa '' kayan dadi harsunyi mata yawa ci takeyi ta yada filo ta kwanta, wanka ne kadai da sallah yake rabata da lumtsumemiyar katifa da aka dora mata akan luntsumemen gado,
idan tasha magunguna ta shafa na shafawa a kircin jikinta da kanta saita kora lemo (juice)tayi gyatsa ta jawo cinyar kaza ta koma kan gado ta kishin gida tana matsa remote tana ganin tashoshi kala-kala, turawa ,india ,
amma tafi duban tashoshin larabawa kamar
saudia da sudan sai tayita duba tana ayyanawa a ranta da man a nuna mata Madina da Mambelanta a gansu?
a saudia kuwa saita dinga ware ido ko zata ga goggo fattu da sauran wadanda suka haye
tare,
bata taba sa'a ta hango ire irensu ba.

farin cikin ya lullube alh adnan a sanda kowanne likita ya turo masa sakamakon gwaje gwajen da akeyiwa kaltum ta e-mail dinsa sun tabbatar masa komai na jikin kaltum lafiya kalau yake ko maleria bata dashi rashin kuzari ne kawai da rashin wadataccen jini a jikinta a sakamakon cin gabza babu blance died shi kuwa wannan lokaci ne idan ta cike gurbin yunwa ta koshi jini zai gudana,

satinsu biyu a sibiti ta shana dayawa tayi kiba tayi haske kirci ya fara neman hanyar garinsu kura da dankararriyar daudar da taki fita a sakamakon rashin sabulu mai kumfa ayanzu sabulu mai kamshi da kumfa ya kore su tuni fatarta ta fara garai-garai.
hasken jikinta ya fara dawowa, kamshin turare designer ya fara kama tufafinda ta cire, kaltum ta dawo gidansu sai ta sake cika da mamaki a lokacinda ta tarar an canja fasalin da tsarin gidansu bakamar yanda tabarshi ba kafin ta tafi asibiti.
da ta tambayi sofi ya akayi?

saita bata lbr cewar alh adnan ya umurcesu da su fitar da rubabbun gadajensu da katifansu da duk wani shirgi su kai bola su zubar, aka yi fenti aka sake kofofi da gilasan wunduna aka zuba musu sababbin kaya, dakuna uku cur suka bayyana a gidan kowanne da gado da labule, , ledar daki mai kyau aka malala, daya dakin na sofi ne da saleh daya na kaltum ne ita kadai yayinda dayan na tarkacen kannenta ne baya ga kicin da bandaki duk a barandar hatta da abincinsu ya canja a gidan, duk saboda kaltum ta murmure.
alh adnan ya dauki nauyin aiko musu da kudi da kayan abinci, aiki yayi masa yawa don haka sai da ya shafe watanni biyu cur baizo kano ba bayan tafiyar sa Abuja kuma har da gudun zarginda matar sa madam salaha ke yi a kan kaltum.

Labarin dawowar kaltum kakaf a kunnuwanta don haka tafara yimasa tsiwa akan bata yarda yayi ta yawan zuwa kano ba, maganarta bazata hana shi shigowa garinsu ba a duk sanda yaga dama, yafi danganta rashin shigowarsa kano da yawan aikinsa dakuma cuku-cukun tafiyar dansa Mashkur karatu london, har Mashkur yagama sakandari yasami admission a combrigde university zai karanci computer, yabar kaltum a baya tana fama da kokon bara.

Allahu akbar rayuwa kenan wani ya fi wani saboda yatsun hannayenmu ma ba kansu daya ba, Allah Ya na azurta wani akan wani duk a cikin kudirarSa da kudirarSa, fadin AlhamduLillahi ala kulli halin shine kawai ya kamace mu a duk halinda muka tsinci kanmu,

mahaifan kaltum su kayi tunani sukaga ya kamata duk bayan wani lokaci sukira oga Adnan a waya su gaisheshi suyi masa godiya
sannan su mikawa kaltum waya ta gaisheshi tayi masa godiya bisa abubuwan alkhairi dayake musu, alh Adnan bai cika son inyayi kyauta agode masa ba don haka yawanci dasun fara doguwar godia sai ya katse su da cewar don Allah yakeyi kuma Allah ne zai biyashi su daina damuwa dayi masa yawan godiya,
Allahu akbar. kaji bayin Allah salihan bayi masu bayar da kalilan ranar gobe kiyama Allah Ya basu kasiran, Allah Ya sa mudace Aamiin.

la'asar sakaliya babu zato babu tsammani alhaji adnan ya diro masu ba tare da sunsan zai zo ba, bayan saleh yaji horn din mota sai yayi zuruf ya mike daga kan dogon bencinda yake zaune ya leka wajen get sai yayi mamaki da ganin mai gidansa ya runtumo da
gudu ya wangale get yayinda alh adnan ya kutsa da kan mota cikin gidan sa,
a farfajiyar gidan ya iske kaltum da kannenta kakaf suna wasa da ball suna tsalle-tsalle da guje-guje cikin tankiya da daria, sanye take da wata tsaleliyar riga da siket kayan kanti duk acikin kayanda Doc Anisa ta jifgo mata harma dawasu kayan 'yayanta duk ta hada mata, kanta babu dankwali sai dai wani lallausan gashi mai kama dana larabawa ne ya fara tahowa saboda mayuka masu gyara gashi data samu tana murtsukawa, tana hada ido da alh Adnan sai ta sa hannu ta dafe kanta alamar kunya, ta runtuma da gudu cikin gidansu yayinda kannen ta suka runtuma da gudu gare shi suna fadin oyoyo..
yataresu da murna yana shafa kan kowannensu kamar yanda yasaba yi musu,
saboda mutum ne mai tsananin so da tausayin yara, ya bude boot ya umurcesu da su kwashe duk abunda suka gani a ciki sukai gidansu, doya ce himili guda kuma manya-manya da dankalin hausa dana turawa baya ga manja kayan miya harda nono kwarya biyu aka juye masa a manyan ledoji, duk tsarabane yayi musu daga hanyar Abuja.

kaltum ta fito sanye da hijabi ta karaso da farin ciki gabansa takwashi gaisuwa...
tashi tashi tsaye inji alhaji Adnan domin bai cika so a zube a gabansa ba, ya dubeta yayi murmushi da alama yaji dadin ganin kyawun da jikinta yayi bai kashe kudinsa a banza ba, rama da baki kirin din nan datayi sun gushe saiyace da ita kaltum babu wata matsala dai ko?

Ta amsa da babu wata matsala dady.

yayi dariya yace to AlhamduLillah haka akeso kici gaba da cin abinci sosai sai kiyi kiba kinji ko?

ta amsa da to daddy.

malam saleh me kake fadamin ne dazu a waya ina hanya banajinka sosai?
alh Adnan ya tambayi malam sale wanda yake tsaye agefe nan da nan malam saleh ya duka ya fara bayanai cikin ladabi bansan zaka taho kano a yau ba nake shaida maka cewar jikin goggo fattu fa ya tsananta a can zangon Daura suna tamin waya ko asibitin kano zan kawota?
shine nace musu a'a subari tukunnn na shawarceka..
sautin ajiyar zuciyar kaltum ce taja hankalin su suka juyo su dukka suna duban ta, ta dafe kirji don mummunar fargabar data riske ta alokaci guda domin koda wasa bata zata goggo fattu na Nigeria ba tsawon watanin nan biyu da dawowarta iyayenta ko kannenta basu taba fada mata ba, ko amboton sunan goggo Fattu ma ba ayi agidan.
.
Kai! Ni kam ku taya ni parin ciki jama'a, sai kara pito min da mata ake gari, ku shaidawa Alh Adnan Dan Aunty yana kara godia,
Lokacin auren mu sai kara matsowa yake, kowa ya xauna cikin shirin shan biki.... 😊
.
Saady Dan Aunty.ADON DAWA 33
.
TRUE LIFE STORY
.

.....ganin su duka sun kalle ta sai ta dukar da kai kasa ta gaggauta barin wajen. Ta shiga gida ta iske sofi a gaban risho tana faman tuka tuwon shinkafa kamar kullum, kamar yadda ta saba da yamma. Kallo daya ta yi wa kaltum ta tabbatar tana tafe da damuwa don haka ta tsaya cak da tukin tuwon tana duban 'yar ta tana sauraron abunda zata fada. Cikin sanyayyar murya kaltum take tambayar sofi.

"mama, daman Goggo fattu ta dawo daga makka har ma tana kwance a zangon daura ba lafiya? "

Sofi ta nisa ta ce, "fiye da shekara guda Goggo fattu ta dawo sharkab babu lafiya, babu hannu ba kafa, ai sai a lokacin muka san ba kwa tare da ita, don mu a tunaninmu kuna tare. Sannan ta tabbatar mana da cewa ta baro ki a Sudan. "

Kaltum bata sake magana ba cikin sanyin jiki ta wuce zuwa dakinta ta shiga lungu ta takure, ta rasa abunda yake yi mata dadi. Sai ta ji kuka ya rufto mata wanda yake tafe da sakonnin zuciyarta kala-kala. Ta tuno azabar da Goggo fattu ta gana mata a baya, sai ta tuno da ranar da ta shige jirgi ta kyaleta, ta tuno rayuwarta a Sudan ta wahala, sai ta ji tausayin wadanda ta baro a can a cikin wahala, don haka kuka ya rikito mata ba kakkautawa. Abayyane take fadin, "wayyo madina, wayyo mambela na, wayyo fatsima ".

Daddy da baba Saleh ne ke zaune a falo suna ta shawarwari kala-kala bayan an gama shawarar yadda za a shirya tahowa da Goggo fattu sai aka shiga shawarar shigar kaltum makarantar boko don ta karasa karatunta. Shekaru sun nausa tun da yanzu shekarunta goma sha takwas kuma daga J.S.S 3 ta tsaya don haka shawarar da suke yi ta ina zata datsa.

Alhaji Adnan ya zaro waya ya fara bubbugawa mutane daban-daban yana tambayar tsare-tsaren makarantu daban daban don tantance makarantar da ta dace da kaltum. Ya nemi shawarwarin abokansa masana makarantu ya hada da shawarwarin shugabannin makarantu daban-daban, daga karshe ya yanke shawarar ya saka ta a wannan makarantar da take tashe, wato "crescent". Ajin da za a saka ta ne aka ce sai an yi mata jarrabawa za a tantance, aka tsayar da shawara jibi littinin a kawo kaltum makaranta don zana jarabawa.

Alhaji Adnan ya umurci malam Saleh da ya kira kaltum ya shaida mata halin da ake ciki. Fitarsa babu dadewa sai gashi ya shigo da 'yar sa. Kallo daya zaka yi mata zaka kula da jajayen idanuwanta alamar ta yi kuka. Ta durkushe a kasa kusa da mahaifin ta wanda shi ma a durkushen yake suka nutsu suna jiran abun da uban gidan su zai fadi.

Ya sake luntsumewa a cikin lallausar kujerar da yake zaune, yace.

"Kaltum, kukan me kike yi? Ashe har yanzu akwai abunda yake bata miki rai a duniya? A tunanina kukanki ya kare tunda kika dawo gida ga mahaifan ki, ga mahaifiyarki ga ni nima ina tare da ku. Me nene matsalarki, ko me kike nema kika rasa in yi miki? "

Sai mahaifin ta ya fara zubar da hawaye, yace
"Alhaji babu gata da kulawar da baka yi mana ba, ko mu muka haife ka ko kai ka haife mu iyakacin abunda zaka yi mana kenan. Kukan da take yi kuwa ba wani abu ba ne, maganar Goggo fattu ce da ta ji muna yi cewar, tana kwance babu lafiya, sai dai ta yi komai akwance a kwashe. Ka san kaltum da tausayi shine ta je daki ta fara kuka".

Alhaji Adnan ya girgiza kai, ya ce "Allahu Akbar, haka mutum ya kamata ya kasance. Ya zama mai yafiya da maye gurbin mugunta da alkhairi. Ba komai kaltum, ki daina kuka ki yiwa fattu addu'ar Allah Ya bata lafiya, kuma ki yafe mata domin ta zalunce ki, idan ba ki yafe mata ba Allah ba zai yafe mata ba. Don Allah ba ya yafe laifin wani, ko yafiyarki zata sa ta sami rangwame daga ukubar da take ciki yanzu."

Kaltum ta fada cikin kuka.
"na yafe mata duk abunda ta yi min".

Malam Saleh ya dora da, "Alhamdulillah, Allah Ya miki albarka ke ma, Allah Ya baki 'ya'yanda za su miki biyayya ".

Kaltum ta amsa da, "Ameen ". Yayinda Alhaji Adnan ya shaida mata dalilin kiran da yake yi mata shine, a kan karatu. Ya bayyana mata cewar ta je ta sami 'yar makwabtarsu Nana ta fara koya mata karatun da ta manta kamar "Maths da English" saboda ranar litinin zataje tazana jarabawa don asan ajinda za a sata.

farinci mai baiyani zaka dinga hangowa afuskar kaltum kankace kwabo hawayen kuka ya kafe, idanuwanta sun washe sai
fararen hakwaranta ne ke haskawa afili don
dariyarda take kyalkyalawa, na gode dady inason makaranta daman,
kalmar da kaltum ke maimaitawa kenan ta kaura gidansu nana tana koya mata aikin yan aji biyar domin aji biyar takeda niyar farawa
duk da a kureren lokacine, kwana biyu kawai
amma yin karatun ya tuttuno mata da abunda ta manta abaya dayawa saboda tunda taje sudan ko biro bata taba rikewa ba balle tayi wani abu waishi rubutu, ta kanta kawai takeyi.

ranar litinin duk da alh Adnan baya gari amma yabar musu komai harda Danladi direba don haka sassafe kaltum ta shirya ta shige bayan mota direba ya kaita makaranta ta hadu da yan mata kamarta a cikin makarantar tana yi musu kallon suna jin dadi daman itace su suma sunayi mata kallon yar gata dama zasu sami gatanta yarinya karama da mota da direba.

a offishin shugaban makarantar aka bata jarabawar ta zauna tayi tsaf ta gama ta mika, kwanaki biyu kacal suka bata ta fara zuwa bayan sun duba jarabawanta zasusan ajin da zasu sakata, awaya suka shaidawa alh adnan cewar kaltum tayi kokari ta amsa musu jarabawan su wasu kuma ta fadi don haka a aji hudu ta cancanta a ajiye ta, ya amince yace ba damuwa ya riga ya biya kudin komai don haka direba yaje yakarbo mata kudin uniform da littatafai da yawa,
akace ta fara zuwa duk da haka tayi farin ciki kuma ta kudiri niyyar dagewa wajen gyara kuskuren jarabobi data fadi,

Dan ladi dai a fakaice yazama direban kaltum aikinsa kawai yakai kaltum makaranta da sassafe ya dawo gida ya ajiye mota idan karfe biyu na rana yayi ya dauki mota ya daukota, umurni daga alh Adnan don haka kallo daya zakayi mata ka tabatar rayuwa takeyi mai dadi da kwanciyar hankali yayinda damuwa ta kau sai kwakwalwa ta washe karatu tayi ta shiga babu duka babu zagi babu bauta ga abinci a wadace,
kaltum babu sauran kuka goggo fattu kuwa
ankawota asibitin malam aminu kano ana kulawa da lafiyarta duk da akwai wata tsohuwa a wajen ta kullum sofi sai ta kai abinci, kaltum kuwa duk ranar asabar da lahadi a asibiti take yini tana taimakawa da dagata abata abinci, kwashe kashi da wankin
fitsarin da take yi a shimfida duk da goggo bata iya magana bakinta ya juye amma da hankalinta tana fahimtar komai,
saitayi ta kallon kaltum tana hawaye da alama tana nadamar abubuwanda tayi mata abaya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.