Adon Dawa Complete Hausa Novel
Reading file: Adon_Dawa_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 10
BABI NA TAKWAS
Yau kaltum ‘yar agulla ta dira a bakin kogi a inda masu kamun kifi suke ta damko manya-manyan kifaye wanda girmansu xai kai girman yaro dan kimanin shekaru fiye da bakwai. Ta tsaya tana jiran abokinta mai suna karim ya fito daga ruwa ya bata kasonta daman ya saba bata kullum sai ta je gida ta gasa su ci.
Karim saurayi ne wanda shekarunsa bai wuce ashirin da biyu ba, dan asalin garin katagun ne a jahar bauchi a kasar Nigeria. Amma bai san kowa a garinsu ba kasancewar iyayensa sun taho dashi sudan tun yana da shekara daya kamar yadda aka bashi tarihin cewa mahaifinsa ya tsaya a n’djamena da niyyar neman kudi sai ya turo karim da mahaifiyarsa su xo sudan su jira shi idan yayi aiki ya samu kudi sai ya same su a sudan su haura saudiya. Tundaga lokacin basu kara haduwa ba, bai xo ba, ana kyautata xaton a n’dajsmena ya rasu yayin da itama mahaifiyarsa Allah yayi mata rasuwa ta barshi shi kadai dan kankanin yaro a hannun wani tsoho abokin tafiyarsu mai suna baba lado.
Karim na xaune shi da tsohon a bur sudan a dakin katako, kwali kadai a shinfide a dakin har ya girma ya fara sana’arsa ta kamun kifi yana sayarwa, a halin yanxu tsohon ya rasu dan haka karim shi ne uwa shine uban kansa.
Ya hadu da kaltum jininsu ya hadu yana farin ciki da ganinta sai ya ga kamar yaga kanwarsa musamman idan ya ji tana yi masa hausa. Da yake babu kalma daya ta soyayya da ke tsakaninsu ita da karim sai ta saki jiki dashi su kayi ta labari haka kuma yana matukar taimaka mata da manyan kifaye gasassu ko danye, ko ma ya bata kudi idan ya sayar ya samu.
Karim yana fitowa daga ruwa sai ya kalli kaltum yayi dariya, itama ta yi masa murmushi cikin harshen hausa take yi masa Magana tace yayana, yau ragon ruwa xaka bani, katon kifi me tsoka. Sai yayi dariya yayi Magana cikin harshen hausa duk da hausar bata fita sosai, yace yau kifin duk manya ne, ki xabi duk wanda kike so.
Kafin karim ya rufe bakinsa sai ya ji wani mummunan duka a kuncinsa har saida ya tuntsura ya fadi kasa. Kaltum da karim suka daga ido lokaci daya suka duba bangaren da dukan ya fito. Sai ga mambela a tsaye ransa a bace mamaki da tsoro gami da fargaba ya rufe xuciyoyin su. Mambela ya sake cacubo karim ya nika da kasa yana shirin hawa ruwan cikinsa da duka, sai kaltum ta yi kukan kura ta xaro wukarta ta yanka mambela a kwairin kafarsa.
Mambeala ya xabura ya rike wajen yayin da karim ya yunkura ya mike tsaye da sauri yana shafa kuncinsa suka yi jawur dan xafi. Mambela ya dago ya dubi kaltum yayin da jini yake bulbulowa daga inda ta yanke shi.
Karim ya fada cikin harshen hausa “kaltum ki gudu kada mambela ya kama ki, wannan mugu ne, ya addabi kowa a garin nan.” Kaltum tace “ba xan gudu ba sai dai ya kashe ni, ka gudu kada ya kara dukan ka, ka bar ni dashi.”
Karim ya arta da gudu ya bar wajen ya tafi can nesa yana duban su, yana tsananin fargabar kada mambela ya tashi ya shake kaltum . har yanxu mambela yana tsugunne yayin da kaltum take tsaye kem a gafe da wukar ta a hannu ta rike kugu, babu alamar tsoro a tare da ita. Mambela ya yago gefen ‘yar sharar rigarsa ya daure kafarsa wajen ciwon sannan ya dago ya dubeta yayi murmushi ya fada cikin harshen larabci yace “yar agulla, kin cika ‘yar agulla, yau na tabbatar ke ‘yar agulla ce. Kin yanki abokaina da yawa yau yankan naki kaina ya dawo kuma, kin yanke ni har jini ya xuba a kasa.”
Sai ya tuntsure da dariya mai fitar da sauti mai kara ya gyada kai y ace “ni mambela, ni ne yau yarinya karama ta yanke ni a kafa, yarinyar ma bakuwa baiwarmu, almajira mai bara. Tabbas baki sanni ba, baki samu mai xaunar dake ya baki labarina ba yadda ya kamata daga nan har cikin gari babu mai taba ni ya kwana lafiya, babu mai yi min musu duk duk abunda nace dai dai ne. ‘yan jange masu barka cikin mtum da wuka, masu fada da kwalba suna tsoron mambela domin ni aka fi sani da yanka. Babana ya fi kowa kudi ya mallaka min gidaje kala kala a kartum bayan na wasu manyan burane a sudan, babu abinda na nema na rasa sai ke, a kanki baxan fara ba dole sai kin amince. Ina biye da ke a duk inda kika saka kafarki, ina ganin mu’amalarki da jama’a sai naga kin fi hulda da wancan tsintaccen yaron karim marar gata, da alama kin damu dashi don haka sai na raba shi da hannunsa ko kafarsa kacukan yadda ba xai sake moruwa ba.”
Kaltum ta fusata ta fara Magana cikin fushi muryarta sama sama tana nuna shi da hannu tace “mambela karya kake yi, baka isa ka ce xaka raba ni da karim ba saboda karim dan uwana ne kasarmu daya, karim ne mai taimako na yana ba ni abinci. Ka sani duk sanda ka taba karim ka yanke shi, ni kuma sai na barka cikinka hanjin ka ya fito waje sai dai nima a kashe ni.”
Ya mike tsaye ya na murmushi yace “na yarda xaki aikata abunda yafi haka ‘yar agulla na tafi sai haduwarmu ta biyu, sai dai ina so ki sani baki isa ki kula wani ba idan ba niba, saboda ina sonki kuma baxan rabu da ke ba.”
Ta Harare shi ta ce “ bana sonka, na tsane ka kuma har abada ba xan so ka ba.”
Ya juya ya tafi a fusace yana dingishi, ta xaro tsumma daga jikin xaninta ta goge jinin da yake jikin wukar ta like ta mayar cikin rigarta ta adana.
Karim ya taho da gudu inda kaltum take tsaye yana ta mamakin karfin hali irin nata, tambayarta yake, “daman kin san mambela, ya aka yi mambela ya sanki har kika yanke shi da wuka bai dauki mataki ba? ”
Kaltum ta ci gaba da ciccibar kifinta ta nufi gida ba tare da ta bashi amsa ba.
Bayan anyi haka da kwana uku misalin karfe goma sha daya na safe, karim na wajen sana’arsa ta kamun kifi sai yaga mambela a tsaye a kansa yayin da mambela ya jawo hannunsa ya fito dashi daga cikin ruwan, kan kace kwabo hantar cikin karim tadau rawa cikin yaren ‘yan ADON DAWA yake bashi hakuri, yana tuba yana neman afuwa.
Mambela ya dukar dashi kasa yace “baka da labarin kaltum tawace?
Ba ka da labarin ni nake sonta kuma babu wanda ya isa ya so ta bayan ni, balle kai bawana? ”
Karim ya daga kai yace “naga alamar haka mai gidana babu mai ja da kai, kaltum kanwata ce kuma na yi alkawarin sai na sa ta so ka.”
Dadi ya lullube xuciyar mambela ya yi murmushi ya tashi karim tsaye, ya karkade masa kasar da ke jikinsa.
Ya ce “ina son kaltum son da bashi da adadi, ina son ka sata ta so ni itama, idan ta ki xan hukunta ka.”
Karim yayi murmushi yace “an gama mai gidana.” Mambela ya juya ya tafi, farin cikin xuciyarsa ya nuna a fuskarsa kai ka ce kaltum din aka bashi kyauta. Mambela na juyawa kaltum ta karaso inda karim yake a tsaye ta tsuke fuska ta tambaye shi “meye mambela ya xo yi a nan, me yace maka? ”
Sai karim yayi dariyaya ce “mu xauna mu yi Magana kanwata kiji labarin abunda baki sani ba.”
Kaltum ta cire sharbabben takalminta silifas wanda ya fi girman kafarta sau biyu gashi a tsinke harta daure da leda. Ta xauna akai yayin da ta baxa wani katon siket dinta burgujeje kore da wata riga t-shirt ruwan dorawa, dankwalinta kuwa ya hadu da cikurkudadden gashinta ya dankare, ta dubi karim tace “ina sauraronka, me nene? ”
Ya durkusa a gaban kaltum sai fara’a yake tamkar gonar auduga yace “kaltum kin yi sa’a da mambela yace yana sonki saboda kin wuce wulakanci, fatara da yunwa a garin nan.”
Kaltum ta ji kamar ya daba mata wuka a kahon xuciyar ta, ta ja dogon tsaki, ta fusata xata mike. Karim ya mayar da ita ta koma ta xauna.
Ya ce “shawara nake baki, ki so shi saboda yana sonki. Meye laipin sa? Gashi kuma dan gidan masu kudi da sarauta, gashi dogo kyakkyawa, laifinsa daya bashi da mutumci shima sai idan ka tsokane shi, ada ne yayi shaye shaye yanxu ya daina.”
NI SADIN MAA ME TYPING NACE “DU KYAWUN MAMBELA, BE KAI BOSS INA DAN ANTY ME POSTING BA, SANNAN KUMA GA CIKA, KAMALA, DA MUTUMCI, DAN ANTY SAI TUBARKALLAH.
Kaltum ta ci gaba da hararar karim har saida ya gama tsara ta sannan tace “ka gama tsara ni?
To ba xan so shi ba har abada, ni na tsani mambela da abokansa kamar yadda na tsani mutuwata.”
Hankalin karim ya tashi yana tambayar ta “saboda me bakya sonsa, me ya miki?
Mambela yana da kirki idan Allah Ya tsaga da rabonka har kyautar saniya sai yayi maka ko kudi mai yawa musamman a lokacin axumi yana da rikon addini kuma.
Kaltum ta fusata ta mike ta ce “ban sani ba, ka je ka tambayi mambela me yayi min shi da abokansa ba ni xaka tambaya ba . kai ma tunda bakinku daya dashi na daina kula ka ba xaka kara ganina a wajenka ba.”
To masu karatu.
Kaltum data yarda da tayin mambela kuwa,?
ya data kasancewa karim idan har kaltum ta ki amincewa mambela?
Domin jin duk amsoshin wa’ennan tambayoyin se ku ci gaba da hakuri da biyo mu.
Mune na ku har kullum masu son dasa nishadi a xukatanku.
.
To jama'a yau Sadin Maa da tsokana ta xo mana.
Madina kuma... am kaltum har ina Madina, kun san masoyan nawa biyu ne
Kaltum kuma taya zata yarda da Mambela bayan da ni a xuciyar ta?
Karshen tika-tika tik, saura kadan auren mu.
DMK ( Dan Aunty, Madina da kaltum).
Allah Ya saka da alkhairi Saadin Maa.
Aamiin.
Typing : Saadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 2 (P 17)
.
Ta juya ta tafi a fusace yayin da karim ya bi ta da gudu yana bata hakuri, ta ki sauraransa, yayi yayi ma ta xo ta karbi kifi tace bata so.
A lokacin dasu kaltum suka cika shekara guda a bur sudan, a lokacin kasar ta fara yi musu dadi dukkaninsu. Saboda da yawancinsu sun sami jari sun fara sana’a sun daina bara, wasu matan suna sayar da kosai, wasu na yin koko, wata waina, wata awara. Wani na dafa shayi da biredi, wani na sayar da rake, wani yayi ‘yar tireda yana sayar da sabulu, omo man shafawa, makilin da brush da dai sauransu. Kofar gidan su kaltum ta xama kamar ‘yar kasuwa ana ta saye da sayarwa. Jange suna xuwa su saya, haka ADON DAWA ma suna xuwa su saya.
Madina ta sami sana’a itama ta daina bara, kosai take toyawa da safe, sai ta sayar da tuwo da daddare. Kaltum ceke tayata wajen xubawa da mikawa da yin wanke wanke. Bayan wannan babu wani abu da kaltum take yi amma komai baya gagararta kyauta ake bata saboda sabon da tayi da jama’a kowa yana sonta.
Kaltum ta manta rabon da ta sayi ruwa da kanta saboda alkwari ne kullum tsohon nan mai sayar da ruwa akan jaki sai ya bata jarka daya ko biyu kyauta. Haka ko ta je bakin kogi ko bata je ba sai karim ya kawo mata katon kifi guda daya ko biyu danye ko gasashshe kyauta, haka wani Muhammad mai sayar da nono akan jaki yake tsiyayo mata nono kyauta, ga makudan kudi da mambela yake cusa mata amma bata taba karba da hannunta ba sai dai ya bawa karim yayi mata dabara ya bata ba tare da tasan kudin mambela bane ta karba ta kashe, ko mambela ya bawa madina ta saya mata wani abun ba tare da ta san mambela ne ya saya mata ba. Duk wanda ke karkarar nan ya san mambela yana son kaltum so na hakika yayin da kowa ya shaida kaltum ta tsane shi, ta tsani ta hada ido dashi, ta tsani ta hada ido dashi a duniya.
Madina ta san komai ma’ana tasan abunda ke gudana tsakanin kaltum da mambela amma ta xuba mata ido bata taba furta mata wata Magana wacce ta shafi mambela ba haka itama kaltum bata yiwa Madina maganar sa ba.
A lokacin da suka cika shekara guda ne ake sake kawo wasu baki wadanda suka taho mota guda suma sun fi su dari uku daga Nigeria ‘yan kasar sokoto ne wasu kuma daga kano da jigawa. Wasu matan da goyonsu, wasu da ciki haka wasu ‘yan mata ne, ga manyan maxa, samari da tsofaffi amma da aka tashi tafiya makka sai aka dauki kalilan aka hayar dasu yayinda aka bar jifgi guda suna ta koke kokensu. Su kaltum suka yi dariya suka ce dasu “xa ku saba kamar yadda muka saba har muke jin dadin xama muka fi son xama a nan damu je makka ko mu koma Nigeria.
Don haka dakuna duk a ciccike suke a kalla mutum ashirin ne yanxu a daki daya, saboda bakin da suka karo. A tattakure ake xaman yayin da hayaniya ta karu. Fada da dambace-dambace suka dadu musamman a wajen shiga ban daki guda daya ne jal gidan mata da maxa. Abun dai ba tsari saboda cudanyar da ake yi maxa da mata sai kaga wannan ba riga, wancan da gajeren wando xai shiga wanka, sai kaji fada ya kaure da xage-xage idan namiji ya kalli mace ko ya leka ta tana wanka sai kaji xage-xage.
Aure yana ta wakana a tsakaninsu sai kaji wancan da wancan ana soyayya, sai ka ji tsoho da tsohuwa sun kulla soyayya, ko saurayi da budurwa suna soyayya, sai ka ji baxawara da baxawari suna son juna don haka ko da yaushe su kaltum suna cikin biki suna cashewa. Sai su aro janereto su jona rediyo a tsakar gida a saka kidan wakokin hausa na ‘yan fim ko na ‘yan Niger su cashi rawa mata da maxa.
Don haka kofar gida an sake kakkafa runfuna katako duk wanda yayi aure sai ya buga nasa dakin a ci gaba da xaman aure. Wadannan tudun kabararrukan nan da suke a cikin dakuna da tsakar gida, da wadanda suke a kofar gida duk sun barbaje saboda dudufniyar da ake yi akansu.
Auratayya da suke kullawa a tsakaninsu ba laifi bane an bi yadda shari’a ta tsara a yi. Inda barnar take wasu matan aure ne sun baro maxansu a can Nigeria sai su ce ruwa ya raba auren saisu yi sabon aurensu kwamacala kenan, masu ilimin cikinsu irin su madina suna kokarin wa’axantar dasu suna wayar da kan mata masu irin wannan hali dasu daina saboda kada fushin Allah Ya kama su, duk macen da ta san tana da aure ta boye ta auri wani amma a banxa.
A yau ma wata mace mai suna talle ‘yar garin mata maye ce a janhuriyar niger,ta yi aure da wani basakkwace mai suna balarabe. Talle ta xo ta yayyayen danta sai ta boye ta ce bata da aure ta auri balarabe bayan bikin da watanni hudu sai ya saketa saki uku da ciki wata hudu. Ta dinga ihu a kofar gida tana burgima tana kuka tana kiran ta shiga uku yaya xata yi da ranta ta baro mijinta a niger, gashi ta yi aure akan aure harta sami ciki kuma ya sake ta idan ta koma kasarsu ina xata ceta samo da?
Kowa ya dinga yi mata Allah wadai, tur da halinta.
Sai ‘yan matan da ake batawa a junansu a yiwa wasu cikin shege, wasu matan kuma waje suke xuwa a basu kudi a yi musu lalata su sami ciki su haife. Irin wannan muguwar kaddarar ceta fada kan rakiya jikar mairo, arnen jange ya yaudare ta yayi mata ciki, ita da kakarta suka yi ta kuka suka rasa inda xasu saka ransu. Idan sun je asibiti ma babu mai kallonsu saboda bada ixinin kasar suke xaune ba. Wannan abun takaici yana damun masu hankalin cikinsu irin su madina, itama maxa da dama daga cikinsu ko ‘yan kasar suna nuna suna sonta da aure ta ki yarda fur. Ta yi kicin-kicin ta rufe ido tace kada ma su fara tana da mijinta a Nigeria ba xata ci amana ba. Haka madina ta sakawa kaltum takunkumi da tsaro gami da sa ido a duk shige da ficen ta, tana yawan bata shawarwari da nasihu wajen kamun kai da gudun xina, tayi taka tsan-tsan da mayaudaran samari.
Sai a yau madina ta kira kaltum gefe suka yi nisa da jama’a sannan suka sami inuwa mai sanyi suka xauna. Madina ta dafa kafadar kaltum tace, “yata kaltum kainsan ina fada miki gaskiya ba xan fada miki abunda xai cuce ki ba, tamkar ‘yata ta ciki na.”
Kaltum ta gyada kai tace “haka ne anty, me ya faru? ”
Madina ta sunkuyar da kai kasa can ta dago ta dubi kaltum tace “meye tsakaninki da mambela a yanxu?
Na san tsakaninku ada.”
Kaltum ta xaxxare ido yayin da xaka iya gane damuwarta a fili. Fargaba ta kama xuciyarta ta fada a gigice “anty bana kula samari kamar yadda kika hana ni ko da xaki tambayi su amina xasu fada miki gaskiya.”
Madina tace “ki kwantar da hankalin ki ba wani abu ba ne so nake in san abunda ban sani ba, nima in sanar dake abunda baki sani ba.”
Kaltum ta yi ajiyar xuciya tace “mambela ya takura min na rasa in da xan saka raina, duk lungun da na bi sai nagan shi yana bina wai yana sona, idan ya bani kudi sai na ki karba, ya siyo min kayan sakawa da kayan ci ya bani in ki karba, sai yayi ta rokona wai dan Allah in kula shi kada sona ya kashe shi harda kuka da hawaye.”
Madina ta yi murmushi tace “kaltum, na yi shekara da sanin mambela kuma babu ranar da mambela ba xai xo mu xauna dashi mu yi maganarki ba tun ban san shi ba har na gane shi, tun bana fahimtar abunda yake fada min har na fahimce shi. Tun yana bani haushi har ya fara bani tausayi. Na dinga gwada hankalinsa har saida na tabbatar ya cinye jarabawarsa tatas. Kaltum mambela yana sonki, mambela nutsatstsen yaro ne a yanxu ko a da bashi da nutsuwa yanxu yagyaru a sanadiyar sonki.”
Kaltum ta ji mamaki ya rufe ta dalili kuwa madina ke hana ta yin samari. Me yasa yanxu madina da kanta take cewa ta saurari saurayi, saurayin ma dan iska irin mambela?
Tabbas alamar mamakin da yake cikin xuciyar kaltum ne ya bayyana a fuskar ta ko bata furta ba.
Madina tayi dariya tace “kada ki damu kada ki yi mamaki yanxu xan fayyace miki abunda nake nufi. Ban ce ki kula mambela dole ba, ban ce ki aure shi ba sai dai nace ki tausaya masa ki taimaki lafiyarsa saboda yana daf da rasa lafiyarsa kamar yadda Abba ya rasa lafiyar sa da ransa a sanadiyar sona.”
Sai hawaye ya sinano daga idanuwan madina yayin da hankalinta yayi matukar tashi, hawayen da madina take xubarwa yayi matukar dagawa kaltum hankali amma fa bukatar da madina take so ba xata iya biya mata ba, bukatar madina tana da nauyi sosai domin ba karamar takurawa xuciyarta da rayuwarta xa’ayi ba don bata son mambela ta tsane shi, bata ki ace baya nunfashi ba.
Kaltum ta matse hawaye tace “anty, me yasa ki ke kuka?
Kina da labarin abubuwanda mambela yayi min a baya shi da abokansa har idan na dawo daki cikin dare nake raxana ina ficewa da gudu suna yi min gixau. Sai kwanan nan na daina wannan raxanar duk akan mambela. Yaya xan yi in kula shi, shi da yake son ya bata min rayuwa? ”
sai ta rushe da kuka.
Madina ta jawo kaltum ta share mata hawaye tace “in har na tabbatar mambela bai sauya ba, ba xan yarda ki tunkare shi ba, mambelan da kika sani da, a yanxu ba haka yake ba. Ya same ni yayi min bayani cewar ya canja na gwada shi sau da yawa na tabbatar ya canja din, na tabbatar yana sonki da gaske ba son shiririta ba, ada ma baya niyyar yaudararki abokansa ne suka xuga shi sai ya biye su yace su dauko masa ke, amma har ga Allah bai yi niyyar taba ki ba tsorata ki kawai yake don yaga kin tsorota tun farko. Ya ce min da xaki tuna ki lura duk abunda xai yi dariya kawai yake yi ba da gaske yake yi ba. Ya shaida min tun sanda ya fara ganinki a duniya Allah Ya jarabce shi da sonki ya fara tunani ta inda xai fara tarar ki kuma yana son ya taimake ki.
Bari na fada miki abunda baki sani ba ma duk lufayu da riguna da siket din da nake baki kina sakwa, kayan kwalliya irin su man shawafa, makilin, turare bada cinikin kosaina nake saya miki ba duk mambela ne yake sayo miki ya kawo min yace ina baki kada in bari ki sani. Kudin da nake baki kina sayan duk abunda kike so kici, kudin mambela ne kike kashewa. Ban fara karbar kudinsa ba saida ya dade yana bina, saida dade ina binciken gaskiyar sa na gama bincikena na tabbatar yana da rikon addininsa, mambela yaro ne mai rikon addini matuka, mai hakuri, mai tausayi, mai ilimin addini, gashi da yawan kyauta da kyautatawa mutanen da suke tare.”
Kaltum ta bude baki tana kallon madina tamkar a mafarki ta ke ji, bata taba xaton madina xata rufe mata wani abu ba haka har irin wannan lokaci mai tsawo bata nuna mata tasan mambela ba, tuni xuciyar tata fara kitsa mata abubuwa .
Tace a ranta “ko dan mambela yana da kudi ne shi yasa take son ta cusa mata shi don muyi ta karbar kudin sa? Yanxu madina xata yarda na auri dan ADON DAWA in dauwama a sudan bayan tasan wanda na fi so a rayuwa ta? ”
Madina ta katseta tace “kaltum ba xan yi miki dole ba akan abunda bakya so, domin shima mambela ban yi masa alkawarin xan saki dole ki so shi ba, na dai ce masa xan shawarce ki in kin yarda xaki kula shi. Ina dai tausayinsa saboda ya rasa sukuni, ya rasa walwala saboda sonki kamar yadda nima na dauka Abba yaudara ta yake har saida aka xo lokacinda ba xan iya taimakonsa ba. Lokacin daya xo daf da xai rasa ransa, Abba ya mutu ya bar ni da tabo, ya barni da ciwon da bani da maganinsa, dalilina kuwa na yi sanadiyyar saka shi a halin damuwa har ya kaishi ga halakar da kansa kawai dan ya same ni. Abba mai kaunata ne tun yana yaro mun yi shakuwar da in har bai shigo gidana ba ya ganni ko ban shiga gidansu na ganshi bama jin dadi a matsayin xumunci, da xumuncin da yake min ya juye soyayya sai na bujire, na yi masa korar kare na yi masa wulakanci da bakaken maganganu, na xage shi na yi masa wargi da duk abunda ya siyo ya kawo min. na tsane shi tamkar wani kumurcin macijin da yake shirin halaka ni. Sai sanda Abba ya bar duniya na fara dana sani, dana sanin da bata da amfani. Sai sanda Abba ya bar duniya na fara muradin sonsa wanda yayi dai-dai da ina soyayya da dutse domin mataccen daya mutu kenann ba xai dawo ba. Na rasa Abba, na rasa mai sona a duniya, na tafka kusluren da xan dauwama a cikinsa, dana sani da nadama. Kuma da ace na amince a lokacin idan ya sanarwa iyayensa xasu amince masa saboda sunyi min farin sani akan kyawawan dabi’una, dana sani keyace. Madina ta rusa kuka.
Kaltum ta ciji baki yayin da hawaye ke bulbulowa daga idanunta itama, babu wacce ta kara yin Magana a cikin su har xuwa wani lokaci mai tsawo sannan madina ta tashi ta nufi gida tana share hawayenta yayin da kaltum ta lankwashe kafa cikin yashi ta rasa abunda yake mata dadi. Ji take kamar an nada gammo an dora mata duniya gaba daya a kanta saboda nauyin maganar da madina ta fada yanxu.
Ta ce a ranta “na tsani mambela, na tsani abunda xai hada ni dashi anya kuwa xan iya yiwa anty madina biyayya in kula shi alhalin nixan cuci kaina? ”
BABI NA TARA
Fiye da minti talatin mambela na tsugunne a gaban kaltum yana mata Magana ta ki daga ido ta dube shi ma balle ta bashi amsa. Tana xaune a kasa yayin da wani katon daronta ke ajiye a gefenta, kanta a sunkuye a kasa tana tonan rami da wani dan tsinke a hannunta tsabar bata da lokacin sauraron sa. Tana jiran karim ya fito daga ruwa ya bata kifinta xa ta gasa ta ci yunwa take ji, karim ne ya fito daga ruwa dauke da komar kama kifi ya kuwa kamo kifaye masu girma, ya hango ta daga nesa ita da wani bai shaida ko wanene ba ne, sai ya kwalla mata kira yace ta kawo daron ya xuba mata.
Ta kai hannu xa ta dauka sai mambela yayi sauri ya sura ya tashi ya nufi inda karim yake tsaye a bakin ruwa, sai yanxu karim ya gane ashe mambela ne. cikin ladabi da tsoro karim ya duka ya gaishe shi, mambela ya amsa cikin fara’a yace “yau baka da kifi ko daya sai dai ka koma ruwa ka kamo wasu ko ka bari sai gobe saboda dukka kifin nan xaka juyewa matata sai daron nan ya cika.”
Karim yayi murmushi yace “an gama ranka ya dade.”
Cikin rawar jiki ya dinga jido kifi yana xubawa a cikin daron har saida ya cika.
Mambela ya yunkura xai dauki daron sai karim yayi sauri ya dafe daron.
Ya ce “bari in kai maka ranka ya dade.”
Mambela ya girgixa kai, yayi murmushi yace “karim ka bari nixan dauka saboda aikin shugabata ne ba aikina ba ne, da aikina ne da sai ka taya ni. Ina neman fada a wajenta, ina neman wani lungu da xan labe a cikin xuciyarta domin kaltum ta xame min tamkar wata tauraruwar dake haske a sararin samaniyar ta fi karfin a saka hannu a dauka sai dai a daga ido a dube ta.”
Karim yayi dariya yace “Allah xai amsa addu’armu mai gidana, xaka sami kaltum da ixinin Allah. Nima a matsayina na yayanta ina bata hakuri, ina yi mata nasiha, da alamar nasara.”
Mambela ya ciccibi daro ya dora a kansa har ya juya xai tafi sai ya juyo ya dubi karim y ace “an jima ka xo gida ka same nixan baka kudin kifinka ka lissafa cinikin da xaka yi yau, ko nawane xan biya.”
Karim ya ji dadi ya kama shi sai yayi dariya ya duka yayi godaiya. Mambela ya isa in da kaltum ke xaune har yanxu.
Ya ce da ita “tashi mu tafi gida ga kifin na karbo miki.”
Ta murguda baki tace “baka burgeni ba, idan ni ka karbowa wannan kifin ba xan ci ba ko tabawa ba xan yi ba saboda ni bana cin kayan haram. Me yasa kai kullum kake axxalumi sai ka cuci na kasa da kai?
Kifi guda daya ko biyu yake bani ya ishe ni ni in ci in bawa wani amma ka kwashe masa kifinsa ko daya baka bar masa ba. Me xai sayar ya sami kudi yau? ”
Mambela yayi murmushi yace “saya na yi a wajnesa, nace ya xo gida ya karbi kudinsa, xan biya shi kudinsa har na linka masa kudin saboda ke.”
Ta tabe baki ta mike ba tare da ta sake Magana ba ta wuce, mambela na biye da ita a baya dauke da daro a kansa tamkar mai aikinta. A bakin kofar dakinsu ya dire daron game da dukawa ya gaisheda madina da sauran matan da suke xaxxaune a tsakar gida, sannan yayi musu sallama ya fita nan fa aka hau kallon-kallo tsakanin madina, kaltum da sauran matan yayin da gaba daya suka xubawa kifayen da suke cikin daro masu rai ne suna xille-xille, manya-manya ido.
Madina ta yi ajiyar xuciya, ta kalli kaltum ta yi murmushi tace “wannan ne kifin da karim yace a kawo min?
daman na bashi kudin, kifin siyarwa nake shirin farawa da ranar nan.”
Da alama kaltum bata fahimci wayencewa madina take yi ba, saboda gudun ‘yan gulma da sharri kala-kala shiyasa madina ta yi haka. Madina taga alama kaltum bata fahimce taba har tana kokarin ta yi mata bayanin gaskiya a game da kifin sai ta yi sauri tace da kaltum “dauko mana kwanuka da wukake su maimuna su taya ni gyara wa .”
Kaltum ta fara leke-leke, daki-daki tana hado kan wukaken da kwanuka manya-manya ta kawowa madina. Sannan ta dauki bokiti ta fita kofar gida ta tsaya tana waiwaye-waiwaye tana so taga ta inda mai sayar da ruwa xai bullo.
Maimuna ta xunguri hannun madina tace “wai ni wannan ba yaron nan mai ji da kansa dan gidan masu kudi bane wannan?
Yaya aka yi ya xama dan aiken kaltum? ”
Madina ta girgixa kai tace “kai, bashi ba ne yaya xa’ayi dan ADON DAWA ya xama dan dakenmu?
Ina jin hausawanmu ne maxauna wadanda suka saba da ita.
Tani tace “ni fa yaron nan tabbas na sanshi, dan ADON DAWA ne don har ya sha bani sadaka a kasuwa ko a gidansu.”
Madina ta tabe baki tace “watakila abokin karim ya dauko mata saboda nauyi ko kuma a hanya suka hadu ya tausaya mata ya dauko mata kinsan ‘yan ADON DAWA musulmansu suna da imani.”
Mekudi tace “anya, ‘yan kasar nan yadda suka raina mana ajawli har xasu yarda su xama ‘yan dakon mu? ”
Madina dai tayi sauri ta kawar da xancen nan don taga kokari suke su kureta, tabbas sun fahimci wani abu so suke su ji kwakwaf su yi gaba su yada.
Da sanyin safiya misalin karfe shida da rabi yayin da kowacce mace da namiji suke cuku-cukun fitowa da kayan sana’arsu, kaltum kuwa a lokacin take kara kudundunewa a cikin mayafi saboda tsananin xaxxabin da ta tashi dashi hade da hararwa. Ta tashi a guje ta fito tsakar gida ta fara kelaye amai a tsakar gida tana yi tana tila kasa akai sai ta canja waje, idan ta canja waje sai ta sake kelaye wani shima ta bunne ta sake waje. Kowa ya tausaya mata sai sannu ake yi mata da addu’ar Allah Ysauwake sai da ta amayar da duk abincin da ke cikinta ya xamto ko tayi yukurin aman babu abunda yake fitowa. Tana xaune tsuru a gefe yayin da ta doka tagumi tana sauraran yadda Allah xai yi da ita nan gaba.
Madina ceta xo ta dafa kafadarta yayinda ta ambaci sunanta t ace “ki daina tagumi, ki yi addu’a Allah Ya baki sauki, ga koko nan da kosai ki ci ko guda biyu ne idan na gama dani xan je in siyo miki magani. Hawaye ne ya kecewa kaltum domin tana tsananin son taci abinci amma tana tsoron amai madina ta sa gefen xaninta ta goge mata hawaye ta ci gaba da lalashinta har saida kaltum ta daina kuka ta fara kubar kokon sannan madina ta bar ta, ta koma kofar gida inda suke saye da sayarwarsu. Kaltum ce kadai a tsakar gida cikin dabara take dan gutsirar kosai tana korawa da koko saboda tsananin yunwar datake damunta.
Kafin ta cinye kosai biyu cikinta ya burkice ya hautsine yayin da amai ya bulo, ta yi sauri ta kai bakinta kasa don kada ya bata mata jiki sai taga an tare aman maimakon ya xuba a kasa sai ya xuba a jikin wani yadi wahalar yunkurin aman ya hana ta dago ido ta dubi wanda ya tare aman, sai bayan da ta gama hawayen daya cika mata ido ya xubo sannan ta dago ido ta dubi wanda ke tsaye a kanta domin tabbas taga hannaye da kafar mutum ne a tsugunne a kanta. Tana daga kai sai ta hada ido da mambela ne ya bude rigarda ke jikinsa ya tare aman da take yi. Sai ta ji gabanta ya fadi, mamaki ya kamata ta rasa dalilinsa na yin hakan, abunka da kiyayya sai ta danganta yin hakan da iskanci ne kawai ba tausayi bane ba kuma kulawa bace.
Ya fada cikin siririyar murya “ya jiki? sannu, tashi in kai ki asibiti.”
Kaltum ta ji ranta yabaci haushinsa ya kamata, ta rasa abunda ya kawo shi wajenta. Da alama magiyar da yake yi mata ta ishe ta, tayi masa tsawa ta yi Magana cikin fushi tace ba xata je asibitin ba ya rabu da ita, ta mayar da kanta ta kunshe a cikin gwiwowinta ta daina kallon inda yake. Ya gaji da Magana shi kadai sannan ya juya xai fice, xai wuc eta miko masa buta da ruwa tace ya wanke aman jikinsa. Ya karbi butar gami da yin godiya ya wanke wajen sanna ya fice daga gidan hankalinsa a tashe .
‘yan gidan suka dinga ‘yan gulmace kungiya-kungiya domin sun fahimci tabbas mambela yana son kaltum ita kuma bata ra’ayinsa. Wasu kuwa tuni sun kulla sharri suna cewa daman dan kasa take so shi yasa bata kula baki duk wanda yace yana sonta a cikinsu bata kula shi. Watakila amaye-amayen nan da take yi ciki yayi mata sai take nunawa mutane bata kula shi. Kowa dai yana nasa xargin.
Fitar mambela babu dadewa sai gashi dauke da ledoji biyu a hannunsa daya dankar da magani, dayar kuma shake take da kayan marmari irinsu ayaba, abarba, gwanda da lemo. Har yanxu kaltum na xaune a inda ya bar ta, ya xo ya ajiye a gabanta ya fada cikin ladabi.
“ga magani ki sha tunda ba xaki je asibitin ba.”
Ta kawar da kai gefe bata dube shi ba ya ajiye a gabanta sai ya fice bayan ya yiwa madina sallama a kofar gida ya wuce xuwa garinsu, daga dukkan alamu bai ji dadin yadda kaltum tayi masa ba domin jikin sa yayi sanyi, sannan ga kuma yanayin da ya same ta a ciki na rashin lapiyarta na matukar damunsa.
.
Typing Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 2 (P 18)
.
Madina ta shigo ta iske kaltum xaune da ledoji a gabanta ga rana ta iske inuwar da take xaune sai ta rikota ta tasheta tsaye ta shiga da ita dakin da ledojin. Ta dinga bare mata ayaba da gwanda tana ci yayinda take yi mata nasiha mai ratsa jiki, ta nuna mata duk abubuwan nan da mambela yake yi mata itace soyayyar, son gaskiya ne yake yi mata.
A yammacin wannan rana su kaltum sun hallara a wajen baki a teku suna budirin bikin amina ‘yar dakinsu da Ado shima a gidan yake. Makadan hausa ne suke kada ganga yayinda mata suke tike rawa, masu gasa kifi suna ta gasawa a gefe ana rabawa ‘yan biki. Bikin ya hallacci mutane da yawa daga wurare daban daban wasu daga garin jange, wasu daga garin ADON DAWA wasu kuwa hausawa ne maxaunan khartum bahari. Mata da maxa, manya da yara ne suke xagaye makada wasu a tsatstsaye.
Kaltum tana daya daga cikin wadanda ke xaune a gaba ita da kawayenta ‘yan mata, ta ci ado da wata lufaya koriya tana daya daga cikin kayan da mambela ya bawa madina ta bata ba tare da ta sani ba. A xaune suke suna girgixa saboda dadin kida sai dai basu samu sun shiga fili ba saboda manyansu ne a ciki filin.
Kamar daga sama ta ji wata murya a gefenta tamkar rada aka yi mata a kunne, ta yi sauri ta waiga gefenta sai taga mambela ne ya rufe kansa da wani katon mayafi tamkar mace idanuwansa kadai ake gani. Nan da nan taji ranta ya baci, farin cikin da take ciki ya dasashe, kafin kace tak annurin fuskarta ya gushe sai ta fara murgude-murguden baki tana Harare-harare.
Ya fada cikin lallausar murya “kaltum yau ranar farin ciki ne, ranar da kowannenmu yake cikin nishadi. Me yasa ranki ya baci daga ganina alhali ni mai kaunar ki ne, mai son ganinki a cikin farin ciki.”
Kaltum ta yi sauri ta dubi huwaila dake xaune a dayan gefen nata sai taga huwaila bata ma ga mambela ba, tana kallon rawa. Ta sake daga kai ta dubi jama’ar dake tsaitsaye a kansu sai taga kowa sha’anin gabansa yake yi, hayaniya ce kadai ke tashi baya ga sautin kida da wake wake.
Sai ta juya ta dubi mambela duba na takaici, ta cije baki alamar xata keta masa rashin mutumci, tana so ta tabbatar masa ita ‘yar agulla ce sai ta saka hannu a riga kan kace kwabo ta ciro ‘yar wukarta ta danna gefe sai tsinin wukar ya fito, nan da nan mambela ya ja gefe yayi tsuru yana dubanta.
Ta fada cike da bashi tabbaci tace “ka matsa daga kusa da ni in ba haka ba xan jinyata ka. Mambela, na tsane ka, na tsani wanda yake sonka saboda kai macuci ne axxalumi.”
Takaici bayyananne xaka hango daga idanuwan mambela, ya dade a tsugunne yana dubanta can ya mike ya tafi da alama ransa y abaci. Biki yayi biki mata da maxa, yara da manya sun cakuda sai rawa ake ana juyi dan haka su kaltum sun sami dammar shiga fili sun cashe suma saida magaruba ta yi waje yayi duhu har baka iya shaida na kusa da kai sannan suka fara shirin watsewa. ‘yan mata irin su kaltum ne aka sa su tattaro farantai da cokulan da aka yi ciye ciye, su biyar ne suka rage a filin suna faman tattare kaya dakyar suke iya gano farantan saboda duhu.
Kaltum na tsugunne ita kadai tana jera farantan roba akan babban faranti tana shirin mikewa ta dora a kai ta tafi gida yayinda sauran ‘yan matan hudu har sun dora nasu aka sun yi gaba. Sai ta ji kamar an jeho wani abu gabanta da karfi, sai ta yi sauri ta duba kasa inda abun ya fadi, sai taga kafar mutum ce nan ta raxana ta fadi xaune dabas tana karkarwa. Ta daga ido da sauri sai taga dogon mutum ne a tsaye duk ilahirin jikinsa a rufe da wani bakin mayafi.
Ta fada a tsorace “waye kai, me kake nema a waje na? ”
Ya ce “mambela ne, soyayyarki nake nema.”
Sai ta mike a fusace tana shirin barin wajen cikin gaggawa, ya shiga gabanta ya hanata wucewa, kan kace tak harta xaro ‘yar wukar ta, ta keta masa a dantsan hannunsa, saboda tsananin kaifin wukar har saida ta tsaga mayafin ta shiga namansa. Yayi kara ya tsugunna ya rike wajen yayin daya dangwalo jini jajawur a hannunsa ya haska da fitilar da ke hannunsa sai yaga jini ne. har yanxu kaltum tana tsaye a kansa da wuka a hannunta jira take ya mike ya mike ya tabata ta sake yankarsa tana tsoran juya baya kada ya cafko ta. A halin yanxu xuciyarta ta kekashe take, ji take a ranta ko aljani ma idan xai fito fili saisu fafata balle bil adama dan uwanta. Bata jin tsoran kowa kuma bata shakkar fada da kowa sai dai ita bata neman fada amma muddin aka tabata xata yi wa mutum illa ba tare da bata lokaci ba.
Ya dago ya dubeta ya haska fuskarta da fitila sai ya sake haska mata dantsan hannunsa inda ta yanke shi, taga sharceccen yankan da tayi masa jini jage jage, bai ga alamar nadama a fuskarta ba. Ta cije baki tana rawar jiki tamkar so take ta kara masa.
Ya tambaye ta cikin harshen larabci ya fada cikin wata lallausar murya yace “kaltum a ganinki kinyi daidai da kika yanke ni da wuka?
A she dama soyayya laifi ce a wajenki, har ki ka nemi ki kashe ni don nace ina son ki? ”
Ta fada cikin kakkausar murya tace “bana sonka axxalumi.”
Ta juya baya a fusace xata tafi sai ta ji ya xo da gudu ya finciko ta sai kuwa ta sake kai masa yanka wannan karon ma ta same shi a dan yatsa daya nan ma jini ya fito. Tana shirin yankarsa a kirji sai ya rike hannunta da sauri ya murde da karfi ya kwace wukar yayin daya warbar da ita gefe ta fadi akasa rim. Ya cafko gashin kanta ya hada da lufayar da ta lullube kanta ya damke, inda ya kawo wukar saitin hancinta xuwa wuyanta.
Ya ce, “ke yarinya karama, duk irin wadannan ta’addancin mun yi mun daina yanxu naki ma wasa ne idan kin ji labarin irin wanda muka yi.”
Ta hau fusge fusge amma ta kasa kwacewa. Ya ce “yau ni da ke kadai xamu kwana a cikin duhun a bakin kogin nan, duk abunda xai cinye mu sai dai ya cinye mu idan kuma ki ka yi kokarin guduwa sai na fusgo ki mun fada cikin ruwan nan mu mutu dukkan mu kowa ya huta.”
Sannan ya saketa yayin da ta mike a fusace xata tafi a guje, bata san yadda aka yi ba sai ta ji ta a kanannade a cikin mayafi an xargota ta fadi kasa sannan ta yi sauri ta yaye mayafin daga fuskarta ta waiwaya mambela ta gani a tsaye a kanta ashe shine ya xargo ta da mayafin.
Ta fada a fusace “wai kai me ka ke nema ne a wajena, me xan yi maka? ”
Mambela ya xauna a kusa da ita yana fuskantar ta yace “yau ni da ke babu mai raba mu sai Allah, yau sai na fahimtar da ke ko ni wa nene kuma ko me yasa na kasa rabuwa da ke. Yau sai kin bani tarihin rayuwarki, asalinki, daga inda kika fito da kuma dalilin xuwarki kasar nan.”
Kaltum ta Harare shi, hakika ta kara jin tsanar mambela tace “bana bukatar in san ko kai wa nene, kuma ba lallai ne kasan ko ni wa cece ba. Mambela na gane ka tuntuni so kake ka bata min rayuwata, burinka ka yi min fyade tun bayau ba. To bari ka ji in fada maka da wannan abu ya fara tsakanin mu gara ni da kai mu mutu ko kuma ni in kashe kaina, kar ka ga ka kwace wukata ka xata ba xan iya halaka ka ba……”
Bata rufe bakinta ba mambela yayi sauri ya katse ta y ace “kaltum, mambela da ki ka sani a da yanxu ba haka yake ba, haka kuma xargin da kike yi min ba haka ba ne a xuciyata tun asali ma. Tabbas na san ba xaki yarda dani ba saboda tun farko abunda ya faru a tsakaninmu duk da ba xaki yarda ba amma xan fada miki gaskiya. tun farkon haduwarmu dake kallo daya nayi miki na ji haka kawai ina sonki, har cikin raina so na gaskiya bada niyyar cuta ko yaudara ba. Ban yi Magana ba da farko sai abokai na suke shawarta ta da suke kai min ke cikin shago, babu yadda xan yi dasu haka nan na amsa musu amma nayi haka ne dan idan mun shiga shagon xaki tsaya ki saurare ni har na isar miki da sakon xuciyata gare ki ashe na yi kuskure da na bari suka dauko min ke a ka., shi ya jawo kike min wannan tsanar. Madina ta sheda min cewar kin koma gida kina firgita kina ambaton sunana wai xan kashe ki. Ta fada min kin sha jinya a sanadiyyar yanka hannunki da kika yi da wuka. Ina rokarki dan Allah ki yafe min ki manta da wancan abubuwanda suka faru tunda Ubangijina Allah Ya halicce ni ban taba haduwa da yarinyar da nake so ba har cikin raina sai ke. Na yi iyakar kokarina wajen cire sonki abu ya gagara, na kasa dainawa, kullum sai karuwa yake.
Wallahi kaltum bani da niyyar cutar dake, ban taba sha’awar yi miki fyade ba, tsoratar dake nake yi kawai a haukata idan kika ji tsorona xaki so ni, na shaidawa abokaina abunda yake xuciyata ko da xaki tambaye su xasu ce na fada musu bada gaske xasu kamo ki ba tsorata kawai xasu yi saboda ina sonki na hakika. Dan baki sani ba ne na bata da samarin garinmu da yawa, haka nayi ta fada da samarin jange masu shirin su cuce ki, ko da yaushe ina biye dake duk inda kika shiga bana bari wani abu ya cuce ki sai dai in ban ga giftawarki ba. Kaltum burina a kanki shine na aure ki, in fitar dake daga irin wannan matsananciyar rayuwar da kuke ciki ta rashin galihu, sannan tun asali, duk rashin ji na ban taba kusantar wata mace ba, balle ace na yi fyade.”
Ta dago da sauri ta dube shi duba mai tafe da mamaki hade da rashin fahimta. Ya gyada kai yace “ban taba ganin matar da ina ganinta na ji a raina naga matar da xan aura ba sai sanda na fara ganinki a duniya sai kawai na ji a jiki na ke kika dace da xama mata ta.”
Kaltum ta mike tsaye ba tare da tace dashi komai ba, amma da alamar sanyin jiki da kunya a tare da ita, mambela ma ya mike yana dubanta yana sauraron abunda xata fada sai yaga ta fara tafiya a hankali yayin da yayi sauri ya nada gammo da mayafinsa ya dauki farantin akansa yana biye da ita a baya.
Gari yayi duhu kirin babu kowa yana cikin gidansa sai kukan tsuntsaye da kwari kadai kake ji saida suka isa kofar gidan su kaltum sannan suka hango hasken fitila da alama akwai maxa kofar gidan wadanda suke xama suna hira. Sai ta ja burki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin me xasu xarga idan suka ganta da mambela a cikin daren nan babu mai fitar da ita daga mugun sharrin da xa’a kulla mata ba. Ta dube shi ta sosa keya ta sunkuyar da kai kasa.
Ta ce “ka bani farantin in shiga gida saboda bana son a ganmu tare a cikin daren nan. “bai yi mata musu ba don ya fahimce ta sai kawai yayi sauri ya dora mata farantin a kanta. Yayi murmushi ya fada cikin sanyayyar murya mai ratsa xuciyar masoya y ace “nagode saida safe kaltum.”
Ba tare da ta waiwayo inda yake ba ta ce “Allah Ya kai mu mambela.” Ta ci gaba da tafiya.
Mambela ya sankare a tsaye cikin duhu yana kallon kaltum har saida ta yinisa ya daina hangota sannan ya motsa, saboda tsabar farin cikin daya hadu dashi a yau ya samu kaltum ta tsaya ta saurare shi harta fara gamsuwa da bayanansa gashi ya samu ta amsa sallamar da yayi mata. Bai damu da jini jage jagen da ya bata masa Kaya ba ya wuce xuwa garinsu yana mai tsananin farin ciki.
Kaltum ta isa tana fargabar kada a tuhumeta da laifin dadewa amma sai ta iske kowa yana sha’anin gabansa saboda hayaniyar biki ba a kwanta da wuri ba. A lokacin da kaltum ta kwanta hakarkarinta ta lumshe ido sai ta fara hango hannun mambela dai-dai inda ta yanke shi da wuka jinni yana xuba, sai ta firgita ta tashi xaune. Madina ta daga kai ta dubeta sai ta tambaye ta ta ce “kaltum lafiya, bakya addu’a ko? ”
Kaltum ta tuna ashe bata yi addu’a ba sanda xata kwanta sai ta karanta addu’o’I ta shafe jikinta ta koma ta kwanta.
Washe gari da safe mambela ya bayyana a kofar gidansu kaltum a lokacin da duk masu sana’ar da abincin safe suka fara firfito da kayan dahuwarsu, shi kuma ya fara ware ido yana neman abar kaunarsa kaltum amma bai ganta ba sai dai ya hango madina tana kosai. Ya isa gareta yana mai yi mata sallama fuskartsa cike da fara’a. a halin yanxu madina ma ta koyi larabci don haka suka fara yarawa, ya dade a tsugunne a gabanta suna ‘yar hira amma yana jin kunyar ya tambaye ta kaltum harta lura da hakan.
Ta ce dashi kaxo duba jikin kaltum ne?
sai ya xabura cikin furgici y ace “bata da lafiya ne? ”
Ganin hankalinsa ya tashi sai ta yi sauri ta fara gyara xancen. Mambela ya girgixa kai ya fada cikin damuwa.
Ya ce “anty kada ki boye min komai a game da kaltum, ta xama ni na xama ita matsalarta tawace, ki fada min me yake damunta.”
Madina tayi shiru can tace “gaskiya kaltum ta hadu da ciwon aljanu xuwan mu garin nan ba ita kadai ba jama’ar mu da yawa suna fama da wannan larura kasancewar muna xaune ne a cikin makabarta,nan da nan saisu bugeta ta fadi.”
Mambela ya maimaita cike da mamaki “aljanu kamar yaya?
Daman ana ciwon aljanu? ”
Madina ta gyada kai tace “ana yi mambela .”
Ya ce “ciwon yana da magani, ana warke wa? ”
Ta gyada kai tace sosai kuwa ai kowanne ciwo yana da maganinsa kafin Allah Ya sauke ciwo saida Ya saukar da maganinsa, da xa’a sami babban malami wanda ya haddace Qur’ani xai iya maganinsu.”
Mambela ya mike da sauri ya nufi garinsu yayin da madina ta shiga juyayin ina xai je ne daya tafi da sauri haka?
Tafiyarsa da kamar awa guda sai gashi ya dawo shi da wani mutum da alama mutumin malamin addini ne a sanadiyar dogon carbin daya rike a hannunsa. Mambela ya kirawo madina gefe ya sanar da ita ya taho da mai maganin cire aljanun don haka tayi musu iso xuwa wajen kaltum. Ba tare da bata lokaci ba ta wuce gaba suka bi ta har cikin dakinsu, hankalin mambela ya tashi daya ga muhallinsu, suka iske kaltum a kudindine akan kwali rabin kanta a kasa cikin yashi tana barci mai kama da suma.
Malamin mai rukiya ya xaro wani dan gwabgwani ya bude, sannan ya lakuto wani mai dan kadan ya lakutawa madina a yatsanta y ace ta samu ta cusawa kaltum a hanci. Jikin madina na karkarwa ta je ta durkusa a kusa da kaltum ta kai yatsanta a hankali har kofar hancinta sannan ta bursuna mata man a kofar hancin.
Kafin kace kwabo kaltum ta firgita ta mike xaune a gigice. Ta fara atishawa a jere a jere sai malam ya fara yi mata tofi yayin da madina da mambela suka xagaye ta idan ta yi kokarin yunkurawa xata tashi sai madina ta danne ta har malam ya fara karatu yana daga murya da karfi. Kafin kiftawar ido da budewa hankalin kaltum ya tashi ta rasa inda xata saka ranta tana ta buge buge da haure haure yayin da muryarta ta koma wata murya wacce bata taba ba. Ta fara Magana cikin yaren larabci, ta dawo yaren ‘yan ADON DAWA , ta mako yaren jange ta ci gaba da fulatanci, (TANA NEMAN DAN ANTY) ta hado da hausa sannan ta juye indiyanci. Koma dai da wane yare take Magana abunda take fada shine waisu aljanu ne a jikin kaltum suke xaune saboda ta kwanta akan gidansu kuma ta tattaka musu yara shi yasa suka shige ta. Sannan suka kara da cewa akwai wani mambela wanda yake yawan bata mata rai da xarar ya bata mata rai sai mu kuma mu bugeta ta fadi, sun kara da cewa su suke hanata yin ibada don tana yawan kona su da addu’o’I shi yasa yanxu suke daure bakinta bata son yin addu’a sosai.
Malam ya tuntube su yaya batun fita daga jikinta kuma!? Sai suka ce ai sun samu gidan xama a jikinta baxa su fita ba. Nan fa aka fara dauki ba dadi tsakanin aljannu da malam ya dinga kona su da ayar Allah yayinda suke ta ihu da bubbuge bubbuge. Wannan karon saida jama’ar gidan suka kawo agaji wajen kaltum domin abun ya fi karfin madina da mambela su kadai, don xubar da mutane take yi kasa.
Da axaba ta tsananta ga aljannun sai suka hau ihu suna bashi hakuri gami da daukan alkawarin idan ya daina kona su xasu fita yanxu ba xa su kara dawowa jikinta ba. Sai suka dinga ficewa daya bayan daya sai ga kaltum ta mike ras kamar ba ita bace a kanannade ba daxu. Malam ya bawa madina magungunan da kaltum xata dinga sha da na shafawa da kuma na hayaki. Ya kuma gargadi kaltum da ta dinga suturta jikinta ta daina yawo ba dankwali, ta xama mai yawan karatun Qur’ani da yin addu’o’I musamman a lokacin kwanciya barci ko shiga bandaki. Malam da mambela suka tafi suka bar kaltum a xaune tayi tsuro-tsuro tana tunani ta rasa abubuwanda suke faruwa a tare da ita domin duk abunda ta yi bata sani ba tun jiya da daddare da ta kwanta barci bata sake sanin abunda ya faru da ita ba sai dai taga jama’a kewaye da ita ana rike da ita suna yi mata sannu sannan ta tabbatar lallai bata da lafiya. Sannan ta yi matukar mamakin yadda mambela ya shigo har dakinsu bayan bai taba shigowa ba.
Tafiyar mambela da malam ba dadewa sai ga mambela ya dawo dauke da jakar kalanxi da kaskon turaren wuta, ya kawowa madina yace ta dinga yiwa kaltum turaren magani sannan ya tafi. Can da yamma kuma sai gashi a wata mota tifa dauke da wasu manyan kataye da wasu maxa guda hudu a kofar gidansu kaltum a kace ana sallama da madina a kofar gida. Sai ta ji gabanta ya fadi ba shiri ta janyo mayafinta ta fito, mambela ta gani cikin katuwar mota sai mamakin da take ji ya karu. Ya gaishe ta sannan suka kebe gefe ya shaida mata ya xo da ma’aikata ne yana so a shinfide musu katako a kasan dakinsu kasancewar ya ga kaltum daxu a kwance a kasan yashi shi yasa yak e so a buga katako saisu daina kwana a cikin yashi madina tace to amma sai ta shawarci sauran ‘yan dakin tunda basu biyu ba ne a dakin suna da yawa sun doshi su goma sha biyar. Mambela y ace ta je ta tambaye su idan sun amince sai ma’aikatan su shiga su fara.
Madina ta shiga gida ta samu ‘yan dakin su ta shaida musu nan da nan suka amince cikin farin ciki da xumudi suka dinga firfitar da kayansu waje madina ta riko kaltum wacce har yanxu tana yawan bacci ta kaita dakin kusa dasu ta kwantar da ita bsannan ta fita ta yiwa su mambela iso shi kuma ya umurci ma’aikata dasu dauko kayan aiki su shiga su fara. Mambela sai kai kawo yake daga daki xuwa tsakar gida xuwa kofar gida yana ta haska ido yana ta hangen mata reras a xaxxaune a tsakar gida amma bai hango abar kaunarsa ba kaltum ya kasa tambayar madina kuma.
Kafin magaruba an lelayewa su kaltum daki ras da katakwaye masu santsi, aka tottoshe musu hudojin rufin daki inda ruwa yake shigo musu lokacin damuna, aka huda musu window inda iska xata dinga shigo musu sannan aka gyara musu kyauren kofa aka yi musu sakata da wajen makala kwado.
Sai tururuwar lekawa dakin ake yi ana gani, sha’awa ta kama ‘yan sauran dakunan suna cewa dama suma a dakin suke. ‘yan dakin kuwa farin ciki suke harda tsalle yayin da suka kewaye mambela suna yi masa buda da kirari suna masa fatan Allah Ya bashi kaltum. Gogan naka sai ya ji babu kamarsu a duniya tunda suka Ambato masa sunan kaltum sai ya shiga rabon kudi saboda su sosa masa inda yake masa kaikayi wato xancen daya fi so a duniya.
Mambela da ma’aikatansa suka shiga mota suka tafi, da daddare bayan sallar isha’I sai ga mambela shi da direban mota sun dawo a cikin wannan katuwar motar karon ma a kofar gida ya tsaya ya aika a kira madina kofar gida, sai ta fito cike da mamaki. Mambela ta sake gani sai ya karaso inda take tsaye ya shaida mata cewar katifu biyu da fululluka ya kawo musu ita daya kaltum daya maimakon su ginga kwanciya a kan kwalaye saisu dinga kwanciya a kan katifa. Hawaye ne ya sirnanawa daga idanuwan madina dan tausayin mambela, sai ta tuno irin rawar jikinda Abba yake yi mata a sanadiyar son da yake yi mata.
Mambela da direban mota ne suka kinkimo katifun da fululluka kowa ya kinkimi daya daya suka shigar musu har kofar dakinsu. Mambela ya koma cikin mota sai gashi dauke da tobe (sakatara) labulen da yake kewaye daki gaba daya. Madina ta dinga addu’a da godiya har ya fita daga gidan yayin da mata suka cika dakinsu madina dankar suna ta yabon halin mambela kaltum tana xaune tana kallonsu tana kuma sauraron nasihohin da kowacce take mata, babu wacce bata bata shawarar ta kula mambela ba saboda karshen so mambela yana nuna mata, suka ce gara tayi karatun ta nutsu ta yiwa kanta fada tun kafin damar nan ta kufce mata.
Kwanakin kaltum uku sannan ta warware ras ta samu sauki , kallo daya xa kayi mata ka tabbatar ta samu lafiya. Kana ganinta xa ka ga t a dawo nutsatstsiya mai kunya, hankali da sanin ya kamata. Ashe daman yawan fushin da take yi da rashin son shiga mutane harda gudunmuwar aljanu suke tunxurata.
Hantsi yayi duk masu sayar da abincin safe sun gama don haka kowa yana cuku cukun kwasar kayan sana’arsa xuwa cikin gida. Kaltum ce a xaune kofar gida tana wanke kwarya, kaskon suya da kwanukan da ake xuba kosai. Sai ta ji sallama a bayanta, tayi sauri ta waiwaya sai taga mambela ne sai ta sunkuyar da kanta kasa alamar kunya tayi murmushi ta gaishe shi. Ya xagayo ya tsugunna a gabanta sai ya tsoma hannu ya fara yi mata dauraya yayin da yake yi mata hira iri-iri (SU DAN ANTY SE HAKURI) gyada kai kawai take yi ba tare da tayi Magana ba har suka gama wankewa dukka, ya taya ta kwashewa xuwa cikin gida. Tundaga wannan lokacin mambeala ya tabbatar kaltum ta fara sonsa badan komai ba saidan kunyarsa da take matukar ji, alamomin so kuwa shine kunya da jin nauyi, ladabi da biyayya.
Mambela kan daddagewa yayi fashin kwana daya xuwa biyu bai xo yaga kaltum ba saboda gudun kada ya takura mata amma badan xuciyarsa tana da sukuni ba har sai ya xo ya ganta yake samun nutsuwa. Sannan bai taba xuwa hannu haka ba, ba tare daya riko mata wani abu ba. Ko da yaushe yana taho mata da wani abu kamar sutura, kayan marmari, ko kayan sanyi irin su ice cream, lemo iri-iri (juices) sai kuma kudi mai yawa wanda xata dinga kashewa.
Yau ma kamar kullum yadda ya saba xuwa da yamma suna xaune akan wani dan dakali a gefen kofar gidansu kaltum suna hira. Kallo daya xaka yiwa kowannensu ka tabbatar yana cikin farin ciki da tsananin kaunar juna. Kana doso inda suke xaune xaka fara hango annurin fuskokin su musamman mambela wanda ke yawan kallonta yana yi mata magana kasa-kasa a setin kunnenta, sai dai duk inda ka kai da iya labe dan kaji abunda suke fada ba xaka iya jiyowa ba sai dai ita wacce ake yi dominta ita kadai take ji. Xaka iya ganin murmushin ta cikin kunya take gyada kai yayin da sonsa ya hana ta daga ido ta dube shi. Kanta a sunkuye yake a kasa da ‘iman.
Mambela ya dubi kaltum yace “yau ne ranar da muka yi alkawari cewar xaki bani tarihinki tun daga farko har karshe nima nayi miki nawa tarihin ba tare damun boyewa juna komai ba. Haka ne ko? ”
Kaltum ta gyada kai tayi murmushi tace haka ne.
Ya ce to bismillah, ina sauraronki.
Kaltum tayi shiru na dan lokaci sannan ta dago ta dubi mambela wanda ke dubanta duba irin na shaukin so da xumudin sauraron xaxxakar muryarta baya ga tsantsar kaguwa ya ji abunda xai fito daga bakinta, sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa. Ta laluba wani dagon kara da ke ajiye a gefenta ta fara wasa dashi a kasa tana tona rami yayin da ta fara da fadar asalin sunanta da sunan iyayenta, garinsu da asalin kasarsu. Hakika labarin kaltum ya fara tsumama xuciyar mambela don ya fara jiyo abubuwan da al’adaun da bai taba jiba. yana sauraronnta yana yi mata tambayoyi kala-kala akan abinda bai gane ba sai ya ji a ransa yana son Nigeria yana son al’adun hausawa. Ta bashi labarinta tsab bata boye masa komai ba kamar yadda ta bawa madina, tun daga sanda mahaifanta suka hadu suka yi aure har ixuwa ranar daya fara ganinta a duniya. Sai dai kash! Kafin tagama bada labarinta hawaye yayi mata face-face a ido shima haka, sun dade suna xubar da hawaye dukkaninsu saboda tausayin wahalar da kaltum ta sha a rayuwa. har aka rasa wanda xai lallashi wani a cikinsu, mambela yayi matukar tausaya wa kaltum sai ya ji ya kara sonta da kaunarta ya sake kara daura dantsen xakulo ta daga cikin rayuwar kangin da take ciki. Ya kasa kwatanto yadda xai jiye mata dadi idan suka yi aure, ya kasa auno irin tattalinta da xai yi don ta huce takaicin maraici da tayi a baya. Sai ya shiga lallashinta yana bata baki cewar ta kwantar da hankalinta komai ya wuce.
Amma ya tuhumi iyayenta da rashin kyutata wa wajen kin janyo ta a jiki da suka yi kamar dai yadda madina ma ta fada sannan yayi Allah wadai da hali irin na goggo fattu, y ace bata kyauta ba musamman da yaji irin axabar da ta gana mata a makka. Ya ce shi da ita su godewa Allah daya sa ba’a tafi makkan nan da ita ba, da wannan karon ma wahalar da xata bata sai tafi tada. shi kuma da aka yi haka sai ya fiye masa alkhairi tunda gashi ya sami dammar haduwa da ita.
Mambela ya dubeta yayi murmushi sai yayi mata wata tambaya wacce tasa saida ta dago idanuwanta kacokan ta dube shi yayin da amsa ta kauracewa kwakwalwarta.
Tambayar da yayi mata itace “kaltum anya kuwa alhaji adnan ba sonki yake bada gaske?
A ganina ba xargi matarsa keyi ba da gaskiyarta. Anya kuwa kyautatawar nan da yake yi miki da shakuwar da ku kayi ba xata juye tsantsar kauna ba har ya kai ku ga yin aure? ”
Wannan tambaya tasa bata da amsa sai kaltum ta mayar da kanta kasa bata iya cewa komai ba. Mambela yayi shiru na dan wani lokaci sai yayi ajiyar xuciya.
Ya ce “xan baki tarihina, yanxu xa kiji ko ni wa nene.”
WA NENE MAMBELA!
Domin jin wannan amsar se ku ci gaba da hakuri da biyo mu dan jin amsa.
.
Ni kuma Dan anti nace babu amsa, dan daga nan ba inda xanyi da Membela sai cikin teku kipi da kada su andame shi,
Shi kenan...
.
Typing : Sadin Maa.
Posting : Dan Aunty.ADON DAWA 2 (P 19)
.
WAYE MAMBELA!
.
Ya ce “sunana Ahmad, sunan mahaifina Mahmud, mahaifiyata kuma Aisha. Iyayena sun fito daga dangi guda, jinin sarauta, sune suke da sarautar garinmu iyaye da kakanni. Mahaifin Aisha shine kanin mahaifin Mahmud uwa daya uba daya, mahaifin Mahmud shine sarkin garinmu yayin da mahaifin aisha shine waxirin sa. Tun kafin a haife ni suke kan sarauta har rana irinta yau suna nan basu rasu ba, Mahmud da aisha su kadai ne ‘ya’ya a wajen mahaifan su yayin da suma kadai suka Haifa don haka ni kadai ne ‘da kuma ni kadai ne jika a gidanmu gaba daya. Kamar yadda kika sani abu ne mai wuya a garinmu kiga namiji ya auri mata biyu, kowa mace daya yake aure balle a haifar min dan uba.
Gata yayi gata, ta ko ina nuna min kauna kama da kakannina xuwa iyeyena, danginmu harda mutanen gari masu neman fada.
Kaltum ta gyara xama da alama tana jin dadin labarin. Sai ta dube shi tayi murmushi tace Ahmad sunanka, me yasa ake kiranka da mambela? ”
Yayi dariya yace yawancin ‘yan garinmu idan kin lura xa ki ga duk an boye mana sunayenmu na gaskiya. an saka mana wani suna na kirari a yarenmu. Mambela suna ne wanda kakana ya saka min domin na yi kama da mahaifina sak, mahaifinna kuma ya yi kama da mahaifinsa sak shima, dan haka mu uku kamanmu daya. Kasancewar auren wuri dukkaninsu su kayi sai ki xata sarki shine babana, shi kuma babana sai ki xata shine yaya na. sarki yana ganin ni ne xan gaje shi ba mahaifina ba, tun ina dan karami sai ya sauko daga kujerar sarauta ya dora ni akai yace mambela ma’ana SAI KA YI shine jama’ar gaba daya suke kirana da mambela.
Kakanninmu basu yi karatun addini sosai ba, amma mahaifina yayi karatun addini sosai, yayi yawon neman ilimi gari-gari, lungu lungu dan haka babban malami ne sosai wanda bana jin akwai mai iliminsa duk garinmu. Amma ni kuma na ki karatu fur tun ina yaro, idan ya takura ni sai inyi ta kuka ina kururuwa har sai sarki ya jiyo ya aiko a xo a dauke ni, da yake gidan gado ne, na sarauta duk ilahirin danginmu a cikin gida daya muke xaune bangare bangare. Ba xaki iya sanin yadda gidanmu yake ba saboda ba’a barin kowa ya shiga gidan sarki saida wani muhimmin dalili kuma sai anyi maka iso shi yasa idan kuna bara bakwa shiga gidan da kin ga yadda tsarin ginin yake.
Na tashi a shagwabe babu mai saka ni babu mai hana ni, haka babu ilimin addini balle na xamani tunda garinmu babu makarnatar boko. Dan haka babu wanda yayi ilimin xamani. Sarki yaki yarda a gina mana makarantar boko a garinmu yayin da wadanda ba musulmai ba suma suke koyarda na su karatun addini a gidajen su. Mu ma muna da makarantun allo kalakala. Mahaifina yana da tasa tsangayar amma naki karatu, kakana kuma yace a kyale ni.
hakika kamar yadda kika samu wasu labarum a kaina cewar bani da kirki, ni dan shaye shaye ne, dan agulla mai fada da yanka jama’a tabbas ba karya ba ne duk abunda aka ce nayi lallai na yi din…………..”
Kaltum ta dago da sauri ta dubi mambela a gigice, kallon nan da tayi masa shi ya katse shi ya kasa ci gaba da maganar da yake yi. Sun dade suna kallon juna sannan suka dukar da idanuwansu kasa kowannensu yana nasa tunanin a xuciya. Kaltum ta ji hankalin ta ya tashi da ta ji kalaman mambela gashi ta fara sonsa saboda son da yake mata da kyautatawa ya jawo itama ta fara sonsa har take tunanin da sharri ake yi masa, ashe da gaske duk abubuwan nan ya yi dan haka ya amsa gurbataccen sunan nan nasa na tantiri……..”
Mambela ya katse tunaninta ya ci gaba da cewa “kaltum naga alamar damuwa a tattare da ke dan na fada miki yadda nake a baya. Kin manta mun yiwa juna alkawarin xamu fadawa juna gaskiya, ba xa mu boye komai ba?
Kaltum ina yi miki son da ba xamu xauna yau gobe mu rabu ba, bana yi miki son da xai xo ya shude, ina yi miki son da xan xauna dake harda mutua xata raba mu, xama na dindindin ba xaman boye boye ba ko xaman karya wanda dadewa wani xai fada miki ko ban fada miki b a.”
Wannan karon ma sai ta dago da ido ta dube shi duba na mamaki da ta ji yana kokarin ambaton aure. Mambela ya narairaice ido kamar mai shirin fashewa da kuka y ace “kaltum, anya kuwa ba son ma so wani na ke yi ba har yanxu?
Kaltum ki tausaya min ki tausayawa rayuwata, ko ba kya son dan ADON DAWA ki fara saboda na kasance mai sonki kuma ba xan iya rabuwa da ke ba. Na fada miki gaskiyar halayyata ada saboda xaman gaskiya nake so muyi ni da ke. Mambela ada da mambelar yanxu ba daya bane, ba yabon kaina nake yi ba xan iya kiran kaina nafi duk wani saurayi a garinmu ilimin addini da rikon addini da kuma nutsuwa a yanxu, sabanin da ko karatun sallah ban iya ba sai tsokane tsokane da rashin kunya.”
Kaltum ta dube shi duba irin na rashin fahimta t ace “yaushe ka nemi ilimi? ”
Mambela yayi dariya ya gyara xama yace “Alhamdulillahi da kika tambaye ni. Ina da shekara goma sha biyar a duniya a lokacin na addabi jama’a idan naga dama sai na tsare kofar garinmu ba mai shiga ba me fita a ranar. Haka idan naga dama ni da abokaina ‘yan agulla xamu shiga kasuwa mu raraka duk wani mai saye da sayarwa ba xa’ayi cinikin ba a ranar kuma mu kwashi kayan jama’a mu ci mu xubar da wasu. Sannan idan naga dama xan je bakin kogi in hana kowa kamun kifi a ranar babu wanda xai hana ni kuma, ko anje an fadawa sarki sai yace yarinta ce ke damu na a kyale ni.
Na addabi kowa daga baki har ‘yan gari haka duk rashin mutunci irin na jange saida suka sara min wajen iya fada da kwalba da wukake, gashi fadana baya mutuwa. Dan in cinnawa gidan kara wuta ba komai ba ne a wajena.
Wannan hali nawa yayi matukar tayarwa da mahaifina hankali ya rasa yadda xai yi gashi mahaifinsa ya hana a kai ni makaranta. Cikin dare ina barci a dakina na sha nayi mankawas sai mahaifina ya xo da gardawa uku suka taya shi cicciba ta suka saka ni a amalanke suka fita da ni daga garin xuwa khartum bahari in da aka saka ni a jirgin kasa ba tare da na sani ba sai muka tafi khartum. Tun da daddare muke tafiya har gari yawaye rana tayi sannan muka isa yayin dana bude idona na ganni a cikin jirgi, xan xabura da gudu mahaifina ya cafke ni ya fara lallashina yace xamu je xiyara ne gobe xamu dawo. Na yi ta mamaki amma sai na fara murna saboda naga burni, naga abubuwanda ban taba gani ba. Tunda nake ban taba shiga burni ba , tunda aka haifeni ni a kauye nake sai dai ‘yan garinmu da yawa suna da gidaje a burane suka xuba ‘yan haya amma basa xama a ciki saboda dokar da kakana sarki ya saka cewar dole ne kowa ya xauna a garin dan kada tarihin garin ya rushe, idan kowa ya tafi sai a wayi gari wata rana babu kowa. Tabbas sarki ya fi kowa kudi haka yana da gidajen a garuruwa da dama jiragen ruwa da ake yi masa haya, wasu nasa ne, wasu kuwa ya mallakawa babana, wasu da sunana aka siya du kina da labari sai dai ba’a taba xuwa da ni ba sai daisu ke xuwa. Don mahaifina baya wata uku bai shigo birni ba, yana kuma yawan kai dabino da nono cikin birni ya sayar ya dawo.
Da farko gidan wani amininsa da suka yi karatu tare ya kai ni mai suna sheikh El-Mustapa. bayan mun gaisa aka bamu masauki mu kayi wanka, mu ka ci abinci, muka yi salla. Sai naga mahaifina da sheikh El-mustapaha sun kebe suka dade suna Magana sannan aka ce na dauki jakar na biyo su, sannan muka fita daga gari muka fara shiga dawa a ka kaini wani gida, suka yi min wayo suka sulale suka tafi suka bar ni ban san ko ina ne ba ashe gidan gagararrun yara ne. a nan fa na hadu da ‘yan iskan burni dana kauye wadanda suka fini fitina, saida na raina kaina na tabbatar ashe niba dan iska ba ne.ga ‘yan iskn da suka fini wato wato a cikin dare lokacin da duk ma’aikata suka yi barci manyan suke tashin mu daga bacci su yi ta bugunmu b mu isa mu fadawa kowa ba kuma. Bayan dauri da duka da ma’ aikatan ke yi mana gashi dole mu tashi da asuba mu yi sallah sanman a fara karatun kur’ ani. Daga fatiha ake fara koya mana mu duka babu wanda xai iya karanta fatiha tiryan-tiryan a cikin mu balle mu iya hada baki dan haka tun daga alifun aka fara koya mana, aka koya mana fatiha da karatun sallah da yadda ake yin sallar. In takaice miki said a na shekara biyu cur ban ga wanda na sani ba balle in fito in ga hasken waje muna ciki a kulle. Tsakar gidanmu, bandakunanmu, dakuna, filin wasanninmu da ajujuwan karatunmu duk suna cikin gidan.
Wata rana kwatsam aka ce min in xo ana nemana a bakin get nayi bako, na fito cike da mamaki sai naga ashe mahaifina ne da amininsa sheik el-mustapha. Na fashe da kuka dan murna na rungume su. Tabbas sun tausaya min saboda irin maka-makan tabo da shatin bulalan da suka gani a jikina amma sun ji dadin ganin yadda na shiryu. Su ka nemi xasu tafi da ni, da kaina naki saboda na saba da gidan da abokaina. Malaminmu ma ya shawarce su a kyale ni xuwa wata shekarar xamu yi sauka harmun fara hadda don haka suka tafi suka barni na ci gaba da xama bayan sun bani sababbin kaya da kayan abinci kalakala. Ashe akwai wani kudi da ake biya duk shekara masu dimbin yawa, yana xuwa ya biya duk shekara ni ban ma sani ba.”
Kaltum tayi ajiyar xuciya ta cire tagumin data doka ta dube shi ta yi murmushi tace “yaya kakan ka yayi da yaga an shekara biyu bai ganka ba, yaya ya yi tunda bai san in da aka kai ka ba da ya sani daya sa an xo an dauke ka saboda baya so a takura maka? ”
Mambela yace “bai san inda nake ba tabbas daba xai bar niba, da da kansa ma xai xo ya dauke ni. Ai tun a ranar da muka fito daga garin ni da mahaifina bai koma ba shima, doguwar wasika ya rubuta ya bawa mahaifiyata y ace ta kaiwa sarki washe gari. Ya shaida masa ya tafi da ni yawon karatu shi da ni duk xamu nemo ilimi a kasar saudiya wata shida xamu yi. Ba’a ganmu ba, babu labarin mu har sai bayan shekara biyu sannan ya je garin shima saida ya samu labarin hankalin sarki ya tashi yasa ana ta addu’o’in Allah Ya bayya na mu, ya baxa jama’arsa gari gari ana neman mu kwatsam sai gashi ya xo, ya shaida musu nima ina cikin koshin lapiya nace xan dawo kwanan na. sarki ya yiwa mahaifina fada sosai, ransa yabaci lallai lallai yaje ya taho da ni. A daddafe dai na cika shekaru uku a gidan kangarrun yara a lokacin na sauke Qur’ani har nayi haddar fiye da rabi baya ga sanin hadisai da tauhidi. Xuciyata ta canja na xama mai tsoron Allah, banda Allah babu abunda nake hange a xuciyata, sai ibada nake yi koda yaushe.
Jama’ar garinmu duk sun tsorata dana dawo suna fargaba annoba ta dawo xan takura musu amma sai suka iske niba mambelan daba ne, wannan mambelan babu abunda yake yi yanxu sai salama-salama. Sarki ma ya ji dadin wannan canjin nawa, ina xama tare dashi mu yi maganar hankali da fahimta ya gaskata na samu nutsuwa yayi farin ciki da abunda dansa ya min daga baya.
Xuwa na garinmu da wata biyu muka sake yin shwara da mahaifina xan koma garin khaltum wajen abokin nan nasa shiek el-mustapha in sake samo ilimi. Na yiwa sarki bayani ya gamsu ya bani ixini na tafi. Rayuwata a khartum rayuwa ceta ‘yanci, farin ciki da wayewa. Na yi karatu yadda ya kamata haka na xauna da ‘yan burni na waye, nayi hankali, na san me yake faruwa a cikin al’umma. Na koyi siya da siyarwa, na kuma sami ilimin xamani kadan, na iya rubutu da karatu duk da daman mu komai da larabci muke yi sabanin irin rubutun bokon da naga ‘yan kasarku na yi.
Ganin na nutsu mahaifina ya nunnuna mi gidajenmu da muke dasu a khrtum duka da akwai ‘yan haya a ciki amma daya bayan daya saida muka xagaya. Akwai wasu abokai na da muka yi karatu tare a wajen sheik el-mustapha suka ce jami’a xasu wuce akwai yadda ake su sami certificate daga gwamnati, nima na kutsa muka samu aka dauke mu a jami’a. saida muka cika shekara uku sannan muka kammala daegree dinmu duk akan Qu’ani. Komai a saukake yake xo min dan na rika na horu a gidan kangararru, na fito da sakamako mai kyau daga nan na wuce saudiya inda na shekara biyu a jami’ar madina na hada masters dina. Sannan na dawo gida, na dawo da wata biyu muka hadu da ke.
Na shiga cikin abokaina da watsatstsu don in shiryar dasu, cikin dubara nake so in cusa musu ra’ayina su dai na shahsanci, su kintsu su koma makaranta. Na xo da niyyar wa’axantarwa ga duk marasa ilimi da kafuran garinmu amma sai dai da dabara bada karfi ba. Shi yasa nake shiga cikinsu mu xauna a kasuwa muna caca a haka nake yi musu wayo duk sanda lokacin sallah yayi sai in ce to a tashi ayi salla sai aci gaba. Wancan yayi nan, in taro shi wanca yayi can in kamo shi dole mu musulman mu yi sallah, kafuran kuwa suna gefe suna kallonmu idan mun idar sai mu sake xama in dinga wa’axantar dasu cikin wayo ina fadar axaba ga wanda baya sallah, Alhamdulillah na samu da yawa sun shiga musulunci yayin da wasu sun fara karkatowa da alama xasu yarda da ni wata rana. Har yanxu wannan tsoran nawa da suke ji da yana nan, haka idan na fada ba’a kin bi don haka na tsawatar dole an rage shaye shaye da iskance iskance a garinmu.
Sanin da suka yi min, shiyasa da suka ganki suka ce ga wata mai kyau su kai min ke shago mana, na biye musu don in samu in yi Magana da ke, in san matsalarki, in taimaka miki ke kuma baki fahimce niba.”
Kaltum tayi ajiyar xuciya ta gyada kai alamar labarin ya tsuma mata jiki tabbas ta yarda mambela yasan Qur’ani don baya jimla daya ba tare daya ja ayar Qur’ani ba ya fassara.
Daga karshe ya dubeta yace “kaltum, xaki yarda ki auri mambela, mu koma gidana a khartum mu xauna in saka ki a jami’a kiyi degree kema daga nan in kai ki saudiyya kiyi masters? ’
Sai ta yi sauri ta ja mayafinta ta rufe fuskarta da alama dai dariyar jin dadice ta kamata. Magaruba tayi don haka mambela yayi mata sallalma ya nufi garinsu, ita kuma ta shiga gida xuciyarta ta kara shaker kaunar mambela.
Kwanci tashi su kaltum sun cika shekaru biyu cur a bur sudan, sun mike kafa sun baxa kayansu suna jin dadin rayuwarsu basa tunanin komawa gida. Masu aure da haife haife sai yi suke suna sakewa. Gidan su kaltum sai ci gaba yake yi koda yaushe suna kara bunkasa yadda xasu sami ci gaba da dadin xama. An kara bandaki haka an lailaye kowanne daki da katako kamar dai yadda mambela ya bude musu hanya.
Mambela ne ya iske madina a kofar gida tana xaune tana jin hantsi, bayan tagama sayar da kosanta. Bayan ya gaisheta sai ya tambayi abar kaunarsa kaltum, t ace masa ta aike ta kasuwa. bayan ya jima suna ta hira sai ya tuntubi madina xancen aurensa da kaltum, kan kace kwabo hankalin madina yayi mummunan tashi har saida mambela ya gane ta shiga wani hali shima ya tashi nasa hankalin.
Ya fada a furgice”anty madina lafiya? ”
Ta xubo da hawayen daya cika mata ido ta girgixa kai tace “mambela ba xan boye maka ba a gaskiya bana son in jefa rayuwar kaltum a irin halin da na jefa rayuwata, saboda ni babba ce babu abunda ban kammala bana rayuwa tunda na yi aure na hayyayafa, na girma nayi hankali kaltum kuwa yarinya ce karama wace bata fara sanin rayuwa ba.”
Mambela ya fada cike da damuwa “anty madina, ina son kaltum ba xan cuce taba, xan riketa amana tamkar ni ne ubanta ni ne danginta.”
Madina ta girgixa kai tace “ba haka ba ne mambela, ba wai don ba xa ka iya rike taba na fadi haka. Ba na son ace a mtsayin ta na yarinya mai karancin shekaru ace ta rabu da iyayenta da danginta ta kauro wata kasa ta gina rayuwa ita kadai. Da xarar ta yi aure ta fara haihuwa ko kudi aka bata ba xata iya tafiya kasarta ba saboda yaranta. Ka ga daga nan ta xama tsintacciyar mage wacce ba’a san asalinta ba, a iya kiranta shegiya marar uba, xa’a iya ce mata ma ‘yar iska, ko bata da asali a bola aka tsince ta.
Mambela ya dubi madina ransa ya fara baci ya cije baki ya fada cike da kasaita “me ki ke son yanxu ki fada min? ”
Madina ta tabe baki ta fada cike da isa tace “ina son sanar maka ba xata yi aure a nan ba sai dai in ka bi ta kasarsu gaban iyayenta ka nemi aurenta a can; subaka ita da kansu.”
Ya fada cikin daga murya yace “kaltum ta fada min ba xata koma kasarsu ba a nan xata dawwama.”
Madina ta girgixa kai tace “rashin hankali ke damunta amma ni na yanke shawarar tura ta gida. A yanxu haka na kusa tara mata kudin mota, xan hada tada masu tafiya a mayar da ita gidansu ko tana so ko bata so.”
Mambela ya xubo da hawaye mai xafi daga idanuwansa ya dubi madina duba irin wacce take kokarin ta raba shi da rayuwar sa yace “me yasa xaki tura kaltum ita kadai ke baxa ki tafi ba? ”
Madina ta yi shiru can tace “saboda na fi son in ceci rayuwar kaltum akan in ceci rayuwata. Na fi kaunar in saka kaltum cikin farin ciki da kwanciyar hankali da in nemi nawa farin cikin.”
Mambela ya mike tsaye a fusace yace “babu inda kaltum xata je, saboda muddin kaltum ta koma garinsu iyayenta ba xa su bari ta dawo ta yi aure a sudan ba. Ki na nufin in bar kaltum ta koma kasarsu anan in je in nemi auren ta?
Kema kin san ba xa su yarda ba sai dai idan na aure ta idan ta haihu sannan mu je da ita a lokacin babu mai raba auren. Ko kina nufin alhaji adnan xai bari wani ya aureta in bashi ba yadda yake nuna tsananin sonta………..
Kafin yarufe baki sai ga kaltum a tsaye a tsakaninsu yayin da aka hau kallon kallo tsakanin kaltum da mambela, kaltum da madina. Kaltum ta rushe da kuka, ta dora hannu aka tana rurawa.
Ta ce “mambela ya isa haka, bana son irin wannan, anty madina ce uwata, ubana a kasar nan ba dan ita ba da ban kawo yanxu ba, babu wahala da wulakancin da ban gani ba a baya ita ta kwace ni da tuni an kashe ni. Me yasa xaka dinga yi mata tsawa da ihu akan tana fadan ra’ayinta tasan abunda take hangowa wanda mu da dukka ni da kai ba xa mu hango ba. Mambela ba xan iya auren ka ba tunda ka fara yiwa mahaifiyata haka.”
Sai mambela ya sulale kasa ya durkusa yana rokar madina da kaltum afuwa.
Madina ta rushe da kuka ta jawo kaltum jikinta ta rungume ta, su dukka ukun kukan suke yi, har yin hakan ya jawo hankalin jama’a suka taho suna tambayarsu lafiya. Nan da nan kowannensu ya share hawaye, ya nuna babu komai.
Sai madina ta mike tace dasu, su biyo ta suka yi tafiya mai nisa xuwa bakin ruwa can gefen da babu kowa sai yashi turmus da iska mai tafe da feshin ruwa mai sanyi yake firfita su. Suka samu inuwa suka xauna a kasa yayin da madina ta saka su a tsakiya. Ta dubi mambela ta juya ta dubi kaltum sai hawaye ya sirnano mata daga idanunta, ta sa gefen mayafinta ta goge sai ta yi murmushi.
Ta ce “mambela xan baka labarina wanda nake ganin ban ji dadin abunda ya faru da niba shi yasa bana son irinsa ya faru da rayuwar kaltum.”
Sai ta gyara xama ta bawa mambela tarihin rayuwarta kacokan kamar yadda ta bawa kaltum a baya, ta bashi labarin haduwarta da tasi’u, xamansu, har xuwa rabuwarsu. Sannan ta bashi labarin Abba da yadda ajalinsa ya xo.
Ta nuna masa irin halin da ta shiga da irin wulakance wulakancen da ta fuskanta a garin da ba’a san asalinta ba, ta nuna masa irin gorin da korar Karen da ake yi mata don an san bata san kowa ba kuma bata da kowa. Ta nuna masa irin tsananin son da tasi’u ya ya nuna mata amma da xama ya yi xama ya sake ta, ya kore ta alhalin ya fi kowa sanin bata da kowa a garin shi yasa bata son kaltum ta xama haka itama. Ta kuma nuna masa cewar ba xa ta so ya fadi halin da Abba ya shiga ba sanadiyar son kaltum, ba xata so ta dauke masa kaltum ba, ya rasa taba, amma ta amince ya bi kaltum kasarsu wajen iyayenta ya nemi aurenta idan sun amince su aura masa ita, su biyo su xo aga muhallinta; yin haka ba wahala ba ne a wajen Ubangiji.
Mambela ya sirnano da hawaye ya girgixa kai yace “abu ne mai wuya iyayen kaltum su yarda su su bani ita, ko sun amince alhaji adnan ba xai bari ba. Don in bi kaltum Nigeria nida iyayena ba wahala ba ne amma xai yi wahala su yarda in auri ‘yarsu in taho da ita alhali suna can suna neman ta ido a rufe hankalinsu xai tashi idan suka ji labarin cewar tana sudan ba’a saudiyya ba.”
Kaltum tayi shiru tana kallon mambela hawaye kadai yake kwarara tana sake gaskata abunda mambela yake fadi gaskiya ne cewar tabbas ko iyayenta sun amince ta auri mambela to alhaji adnan ba xai amince ba ko ba xai aure taba.
Madina taci gaba da lallashin , mambela amma fa tana nan akan bakanta na dole sai dai yabi kaltum Nigeria ba xai aureta anan ba. Yayin da kaltum a xuciyarta take sake tabbatarwa cewar ita kuwa sai dai a kai gawarta Nigeria amma ba xata koma ba don tafi jin dadin xamanta a nan akan a gaban iyayenta. Rugumutsi kenan yaya xa’ayi ken an , tunda kowa da nasa ra’asyin a cikin su ukun ?
A hka aka rabu ba tare da kowa ya san a wacce shawara aka tsaya ba.
Tun daga lokacin mambela ya shiga damuwa, walwalarsa ta ragu, fara’arsa ta disashe ya xama tamkar mutum mutmi gashi dai a xaune amma xuciyarsa tana tunanin yadda xa’a ayi ya auri kaltum.
Haka ko ya xo hira wajenta hirar bata wuce kaltum karki tafi kasarku ki bar niba, idan kika tafi ban san yadda xanyi in yi rayuwa ni kadai ba, ba ke. Bata bashi amsa ba, amm sai dai ta lankwabe kai tayi kamar xata yi kuka saboda itam bata san mafita ba. Kwanaki uku bata ga mambela ba sai taji labarin ashe bashi da lafiya sosai, ko kofar gida baya iya fitowa. Hankalinta yayi matukar tashi kana kallonta xaka tabbatar da a cikin damuwa take. Da yamma kaltum tayi jugum akan katifarta yayin da abincinta na rana na gefe bata iya ci da yawa ba, sai madina ta xo ta tsaya a kanta ta dubeta tayi dan murmushi yayin da itama kaltum tayi mata murmushin karfin hali.
Madina t ace “tashi ki shirya, kiyi kwalliya ki sami kawayenki biyu su raka ki garin ‘yan ADON DAWA gidan sarkinsu ki gaishe da marar lafiya yarima mambela sai hankalinki da nasa ya kwanta.”
Kaltum ta kwashe da dariya ta kifa kai akan filo, ta rufe fuska alamar kunya. Madina ta janyo hannuta.
Ta ce “wallahi sai kin je kunyar karya ce kike yi, gashi nan kin kasa cin abinci tun jiya da aka fada miki bashi da lafiya kika shiga damuwa. So kike ayi majinyata biyu keda shi? ”
Kaltum ta tashi tana farin ciki amma fa tana wayencen har cewa har cewa take yi “ni na mantama an ce mambela bashi da lafiya.”
Kaltum da kawayenta biyu amina da hansai ne suka ci ado suka nufi garin ADON DAWA . Tabbas kana hango ‘yan matan nan uku xaka san wacce tayi kama da amrayar yarima mambela. Amina ta saka riga fara (t-shirt) da siket baki, da shudin gyale. Yayin da hansai ta saka farar riga (t-shirt) da xanin atamfa, ta ci dammara da gyale kore. Kana ganinsu kasan wadannan basu taba shiga aji ba, a kasarsu ma ‘yan talla ne. kaltum kuwa baya ga kyakkyawar halittar da Allah Yayi mata ta iya tsara ado, saboda daman can tana da wayewa da ajinta ta xo.
Kaltum ta ci kawalliya da wasu riga da siket matsatsu farare, sai ta nada lufaya fara wacce akayi mata xanen fulawa baki, ta saka wani takalmi mai tsini baki duk mambela ne yakesaya mata. Kananan kitso ne a kanta yirin yirin wanda ya xubo goshinta yayinda fuskarta ta dauki hoda, jan baki, da kwalli rangadadai.
Kaltum ce a tsakiyar kawayenta suna tafe suna hira har suka isa garin ‘yan ADON DAWA fadar sarki suka nufa. Sai suka fara takawa a hankali sakamakon dandaxon samarin da suka hasko a kofar gidan suna xaxxaune akan wata katuwar tabarma.
Kaltum t ace da kawayenta su juya su koma gida ita ta fasa xuwa dubiyar, yayin dasu amina suka ce su je kawai dn suna so su shiga gidan sarki daman basu taba shiga ba. Ko ba’a fada musu ba daya daga cikin samarin ne ya hango su ya wafto sauran ya nuna musu su saisu kaga gaba daya sun waigo suna kallon su. Harda wasu da suke kwankwance sai suka mike xaune suna duban su. Suka daure suka ci gaba da tahowa amma fa suna nonnokewa.
Sai daya daga cikin samarin ya fada cikin yarensu y ace kalli ta tsakiyar ku gani yadda take da kyau . dama a kauyukan nan akwai hadaddiya haka?
Wannan ai itace ADON DAWA sai suka kwashe da dariya su duka.
Amma dasu kaltum suka kusn isowa karkashin bishuyar sai suka gane su waye yayin da suma samarin suka gane ashe kaltum ce.
Mambela na daya daga cikin samarin shine wanda yake kwance sai ya tashi ya xauna nan da nan farin ciki ya kama shi ya hango abar kaunarsa kaltum, yayin da ita ma ta ji sanyi a ranta da ta ganshi. Suna hada ido sai suka yiwa juna murmushi, mambelan da ake rikewa idan xai tashi, shine yayi xumbur ya tashi da kansa ya taho da sauri ya tare su tun kafin su karaso.
Ya fada cikin murna ‘yau sai kun shiga kun gaisa da sarki daman ina bashi labarin ki yana so ya ganki.”
Kamar kaltum ta nutse a cikin kasa haka taji nauyi da munyar dandaxon matan da suka dinga diddigowa daga dakunan su suna fitowa kallon amaryar mambela, sai buda ake ana yabon kyawunta da hankalinta. Don daukaka sai ga kaltum a gaban sarki tana kwasar gaisuwa. Sarki yasa hannu ya dafa kanta, ya dafa kan mambela yayi musu addu’ar fatan alkhairi sannan suka tashi suka fito yayin da aka saka bayin gidan suka rako su da kwaryar dabino daya da kwaryar nono biyu har kofar gidansu.
Mata su ka taru a tsakar gida suka kewaye su kaltum suka dinga bayar da labarin yadda suka isa gaban sarki. Yayin da sha’awa ta kama ta kama sauran mata kowacce tana cewa dama itace ta sami dan sarki mambela.
Sallamar wata bakuwa ceta katse hayaniyar da ake yi, suka waiwayo gaba daya suna duban ta.
Jama’a wace ce wannan matar? ,
daga ina ta xo? ,
wa take nema?
Domin jin amsoshin, se ku dada hakuri da biyo mu.
Naku masu son ku har kullum.
Typing:Sadin Maa
Posting:Dan Anty.ADON DAWA
LITTAFI NA 2 (PART 20)
.
Matar dai bakuwar fuska ce amma kuma bahaushiya ce, hausar katsina take yi. Bayan ta karaso tsakar gidan ne aka mika mata karamar kujera ta xauna yayin da ta yi jam’I ta gaishe da kowa. Sai ta fara gabatar da sunanta da kuma garinsu. Ta ce sunanta Hauwa’u ‘yar asalin garin ‘yan tumaki ne a jahar katsina, sanna ta ambaci sunan wata mata wai shatutuwa ta xo nema. Sunan matar da ta ambata babu ita a cikin gidan nan don haka suka tabbatar mata basu san taba. Sannan ta fara dogon kwatance sai can suka gae shatutuwar da take nufi it ace matar da ta mutu a hanya a wajen haihuwa, sauran ‘yan uwanta kuwa sun haye makka. Sai suka shaida mata shatutuwa ta mutu tun a hanya a garin haihuwa.
Sai ta fashe da kuka tana cewa “kanwata ce uwa daya uba daya. Ni ce na aika mata da kudi nace ta xo mu hadu a khartum mu tara kudi sai mu wuce makka, na ji shiru shiru bata karaso ba har yanxu kuma bama waya dasu tunda kauyen namu babu waya sai na xata so take ta haihu sannan xa ta xo. Shekaranjiya na hadu da ‘yar garin mu itama ta xo kwanan nan shine nake tambayarta shatutuwa sai tace ta dade da tahowa tuntuni. Aka ce in xo nan bur sudan akwai mutanenmu wadanda basu sami tafiya ba in duba ta tabbas tana cikin sudan bata da kudin da xata haura makka.”
Ta sake rushewa da kuka mai tsanani, su kuma suna ta lallashin ta.
Can ta tsagaita da kuka sai tasa hannunta a jaka ta xaro wani hoto a ambulan. Ta ce “ga hoton wata yarinya, ‘yan uwanta sun ce inyi musu cigiyarta a nan.”
Xaibu tasa hannu ta karba ta bude ta xaro hoton, yayin da kowaccensu ta xuro kai suna kallon hoton, saisu dukka suka bude baki suna mamaki yayin da kallo ya dawo kan kaltum. Gabanta ya fara kwaranya daga idanuwanta ta fara kiran “inna lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un.”
Hauwa’u tace lafiya, me ya faru da yarinyar, kar dai itama ta mutu?
don an bani tabbacin batahaye ba tana bur sudan shine aka ce lallai lallai a kaita khartum wajen wata mata mai suna kalah itama ‘yar xangon daura ce, kalah ta dade a khartum. Kudin jirgin yarinyar da komai yana wajen ta., iyayenta sun turo da isasshen kudi suka ce lallai a kai musu ita. Shine kalah ta ji ina cewa xan taho tanan sai ta bani hoton nan in taho dashi in cigiyarta, ga sunan yarinyar nan a bayan hoton.” Madina ta karbi ta juya bayan ta karanta sai ga kaltum saleh baro baro a rubuce. Madina tace “Alhamdulillah, Allah Ya yankewa kaltum wahala don haka kaltum shiga daki kiyi marmaxa ki hado kayanki ku tafi.”
Yayin da kowa ya fara taya kaltum murna wasu kuwa suka fara koke koke dama ace suma nasu ‘yan uwan su kawo musu irin wannan agaji wajen aiko musu da kudin tafiya. Wasu kuma suka fara kukan rabuwa da kaltum saboda yarinya ce mai dadin xama.
Kaltum ta ja gefe ta cije takiyin gaba ta ki yin baya ta tsaya kawai tana karkarwar jiki yayin da ta rushe da kuka wanda saida hankalin kowa ya tashi.
Madina ma kukan take yi, ta mike da sauri ta shiga hadawa kaltum kayanta a buhunta kama daga kayanta na sakawa xuwa takalma, soson wanka, sabulu da sauransu. Ta xo ta ja hannun kaltum, sai kaltum ta makale hannu alamar ba xata tafi ba. Cikin fushi da kuka mai tsanani madina tadaka mata tsawa ta ce “ki xo ki wuce ku tafi kafin raina yabaci. Wa kika ajiye, ko wa kike dashi anan da xa kice baxa ki tafi ba?
Ban da larura ma me xai kawo ki cikin wannan rayuwar ta kangi da wulakanci a matsayinki na ‘yar boko?
Da tuni yanxu kina jami’a don haka dole ki tafi, fatana ki koma gaban iyayenki ni kuma in ji da kaina.”
Kaltum ta mika hannu ta karbi Jakarta ta wuce gaba yayin da sauran suka biyo bayanta, tafiya suke jiki sanyi kalau ana tayi mata fatan Allah kiye hanya. Mata da maxa a kofar gida suka fito suka tsaya crko carko ana kallon kaltum sai hawayen da yaketa firfitowa daga idanuwa da yawa daga cikinsu. Iya mairo da jikarta rakiya suka bata sako ta shaidawa ‘yan uwansu na xangon daura cewar suma su hado kudi su aiko musu su koma gida.
Hauwa’u ta dubi kaltum ta yi murmushi tace “banda yarinta keda xa’a kai ki gida cikin gata ina ke ina koke koke kuma?
Mu yi sauri mu tafi kada mu rasa jirgi, da magaruba yake tashi.
Kaltum ta kasa waiwayowa ta dubi jerin mutanen da suke daga mata hannu sai dai ta dora buhun kayanta aka tayi gaba. Madina da hauwa’u ne suke biye da ita a baya suka nufi khartum bahari anan ne xasu hau jirgin kasa.
Suna isa suka iske layin yakar tikiti saura mutane kadan saboda jirgin ya kusa cika. Nan da nan hauwa’u ta shiga layi ta yanko tikiti biyu ita daya, kaltum daya.
Madina ta rushe da kuka yayin da kuka ya ci karfin kaltum itama sai ta ajiye jakar kayanta a kasa ta rungume madina tana kuka. Ta ce anty, bana so in tafi ni kadai in barki a nan. Ki xo mu tafi tare xan fadawa iyayena su aiko da kudin jirginki ko mu shiga mota mu tafi kudin xai ishe mu.”
Madina ta girgixa kai ta sharce hawaye cikin kuka mai tsanani ta ke Magana t ace “ba xan je Nigeria ba kaltum, ba ni da kowa a Nigeria saboda kowa ya guje ni in yi rayuwata anan har lokacin da mutuwata xata xo ta dauke ni ki yi min fatan alkahiri kamar yadda nake yi miki ko bakya tare da ni, ki yafe min duk abunda nayi miki a rayuwa kamar yadda na yafe miki. Ina addu’a Allah Ya hadamu a gidan aljanna bayan mutuwarmu domin xai yi wuya mu sake haduwa har karshen rayuwarmu. Daga karshe ina yi miki nasiha da ki rike addininki, ki tsare kanki daga aikata xina har Allah Ya kawo miki mijin da xa ki aura na gari, kada ki manta da labarina da na baki ki koyi hakurin xaman aure da tattalin miji baya da ladabi da biyayya.
Ki yi min alkawari xa ki sakawa ‘yar ki sunana madina don karki manta da ni a rayuwa.”
Kuka mai tsanani ya ruftowa kaltum sai ta yi sauri ta duka ta dauki jakar kayanta suka nufi kofar shiga jirji saboda axalxalar da hauwa’u take yi mata wai suyi sauri su shiga jirgi su tafi kada a tafi a bar su.
Madina na tsaye tana kallon su yayin da kuka ya ci karfinta sai ta kwalla kiran sunan kaltum. Kaltum ta waiwayo da sauri sai ta tsaya cak su duka kuka suke yi. Madina tayi dan murmushi karfin hali.
Ta ce “kaltum, me xan cewa mambela? ”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai!”
Kaltum tayi shiru ta tsaya tana kallon madina kawai can tayi ajiyar xuciya yayin da hawaye xaxxafan hawaye ya xubo sharrrr daga idanuwanta, ta girgixa kai t ace “k ice masa na tafi gida.”
Sannan ta juya ta juya ta shiga jirgi, suka sami waje suka xauna, sun xauna ba dadewa sai aka rufe kofar jirgin aka kunna aka fara tafiya yayin da kuka marar kakkautawa ya ruftowa kaltum da madina. Sai da madina ta tabbatar jirgi ya tafi gida lokacin dare yayi. ‘yan gidan sun dade basu kwanta barci ba suna ta jajen rashin kaltum yayin da madina ta bude shafin kuka kai kace mutuwa kaltum din tayi. Taji hankalinta ya tashi ko sanda ta rabu da ‘ya’yanta bata ji irin wannan ciwon rabuwar ba kamar yadda take jin radadin xafin rabuwa da kaltum a yau. Tunda ta koma gida kalma daya ta kasa furtawa dan takaici sai aka kewaye ta ana bata baki da nasiha kala kala.
Sai washe gari su kaltum suka isa khartum da sassafe amma kaltum bata daina kuka ba. Kaltum taga kayatattun birane masu titi da gine ginen dogayen benaye. Ta shiga mamakin kyawun sudan ashesu a kauye suke ba a sudan ba, don inda suke babu ruwa, babu wuta, birni kuwa ga lantarki nan tarr, ga ruwa afanfuna bayan motoci tsala tsala da mata masu kyau a tituna suna wurwucew kamar su suka yi kansu. Duk da irin wannan kyakkawan gari da kaltum ta gani bai sata daina jin dankararriyar kunar da take ji a ranta ba. Tana tunanin madina da mambela, sai taji tafi son ta xauna dasu da ta koma gidansu. Ko sanda ta baro gida bata ji irin wannan kunar ran ba kamr yadda take ji a halin yanxu.
Sun isa wani gida kato a wata unguwa mai kyau, babban gida ne a lailaye da sumunti mai dauke da dakuna bijik da katon tsakar gida . hausa ne xalla a gidan kuma mata xalla, suna xaune a dakuna kasha kasha kowace da sana’arta wacce xata kula da kanta. A kalla a daki daya akwai mutane takwas xuwa goma da tabarmi a shinshinfide a kowace daki. Gida ne mai kyau na sumunti xalla sabanin irin nasu na bur sudan.
Tabbas kaltum taga fuskoki da yawa da ta sani sai dai ta manta a inda ta san su, suna shiga cikin gidan kafin su isa cikin dakin sai ta tambayi hauwa’u.\
Ta ce “nan gidan haya ne? ”
Hauwa’u t ace “gidan Abdul kadir, dan asalin xangon daura ne ya kauro sudan da xama fiye da shekara talatin anan yake, ya xama dan kasa. Shine yayi arxiki yamaka gidan nan ya barwa baki nan bangarensa dana iyalinsa kuma suna can baya. Kyauta kowa yake xama musamman ‘yan xangon daura sun fi xama a nan kowacce ta xo nan garin sai ta nemi nan gidan ta xauna, har ana kiran gidan da suna gidan xango.”
Sai da suka dade suna jira sannan kalah ta dawo gida, ta tare su da murna gami da yiwa hauwa’u godiya marar adadi data nemo mata kaltum. Babu tantama duk wanda ya dubi hoton kaltum yaga fusakarta kuma axahiri ya san itace, ga kamanninta nan rangadadai. Hauwa’u ta danka kaltum a hannun kalah su kayi sallama ta koma garin da take don ita ba a khartum take xaune ba.
Kaltum ta sake dukawa ta gaisheda da kalah sannan ta gaisheda ‘yarta budurwa sa’ar kaltum din ce mai suna lami. Suka amsa mata cikin sakin fuska sannan kalah ta fara yi mata bayani cewar itama ‘yar xangon daura ce babarta kawar goggo fattu ce.
Kalah ta ci gaba da shaidawa kaltum t ace “an kamo goggo fattu daga makka yanxu haka tana xaune a xangon daura saida aka kamo ta ne kwanan nan sannan iyayenki suka san bkya tare da ita a makka, dan haka hankalinsu yayi tsananin tashi suka dinga tunanin yadda xa’ayi a samo ki. Sai Allah Ya sa musa agent din da yayi muku aikin bisa yana da lambata shi suka nemo suka tambayi yadda xa’ayi a same ki. Sai yace bashi da yadda xai yi ya samu wani a bur sudan saboda babu waya kwata kwata a kauyen amma yana da lambata sai dai ni a khartum nake, don haka suka kira ni a waya. Na ce musu gaskiya bana xuwa bur sudan amma idan sun tabbata kina bur sudan to su aiko min da kudin motarki da nawa na xuwa can sannan su aiko da kudin motarki sai in saka ki a mota har kano.
Akwai wani Alh Adnan dashi muke waya shine yace gara a sako ki a jirgi, to dai yanxu sun aiko da hotonki da kudin jirgin kasa na xuwa bur sudan, da ban sami lokaci ba, shine kawata hauwa’u t ace daman tana so ta je ta je ta nemo ‘yar uwarta shine na bata kudin ta je ta taho dake don haka sai ki xauna ki saurari sanda xasu turo da kudin mota ko jirgin xuwa kano sai in je har tasha in turaki.”
Kaltum tayi shiru a lungu tana sauraron abinda kalah take fadi mata, jikinta yayi sanyi kalau ta saddakar ta fawwalawa Allah komai tana fatan Allah Ya xaba mata abinda yafi alkhairi ba abunda ranta ya fi so ba.
Al’amarin mambela kuwa sai washe gari ya samilabarin an tafi da kaltum Nigeria, har cikin dakinsa wani abokinsa ya je ya kwatsa masa wannan mummunanlabarin. Duk da tsananin xaxxabin da ciwon kan da yake yi saida ya taso da kyar ya taho gidansu kaltum, kai tsaye ya fada tsakar cikin gidan ya kuwa ci sa’a ya iske madina a xaune tayi gum tayi tagumi itama da alama takaicin rashin kaltum ya dame ta. Yana ganinta sai ya fara hawaye itama ta fara xubar da wani xaxxafan hawaye mai radadi.
Ya fada cike da fargaba yace “da gaske an tafi da kaltum Nigeria? ”
Madina ta gyada kai tace “haka ne, kaltum ta tafi Nigeria, iyayenta ne suka aiko a tafi da ita…”
Bata rufe bakinta ba sai suka gay a yi juyi ya daki katakon dakin har saida dakunan su kayi girgixa.
Ya fada cikin fushi yace “tunda kaltum ta tafi daga garin nan, ko wacce sai ta tafi babu wacce xata sake xama a kasarmu.
Nan da nan kowa yayi carko carko suna duban mambela a tsorace, hankalinsu duk ya tashi kan ka ce kobo sai jikinsu ya dau makerketa. Ya dakwa duk wanda yayi kokari matso kusa dashi xasu bashi hakuri.