Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel
Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt
Chapter 2 of 34
"Mama ina ta kiran Lambar wayar Baba Hamusu bata shiga tun safe fa." Ya fad'i maganar yayin da yake kallona da wani irin yanayi.
Na ce." Wata'kila network ne, amma Hamusu ai baya kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa."
A sanyaye ya ce." Ina tsammanin hakan."
"Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa. Bai dube ni ba ya furta." Ina son zuwa kano din ne na kwana biyu a wurinsa" Na ce." To ka gayawa Baban?" Ina nufin maigidan.
Ya gyada kansa a nutse ya ce." E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama."
"Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Mun yi maganar dazu har ta fara had'a mini tsaraba."
Shiru na yi kawai ina kallonsa. Har yanzu yanayinsa bai canza ba. Na ce." Ka ga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?"
Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce." Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu. Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?"
"Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa. Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin rai ni dashi, abinda maigidan ya tsana kenan. Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa. Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyaleshi.
"Mama ba zan rufe miki ba, tunda Salim ya dawo daga karatu yake yi mini wasu abubuwa na rashin kyautawa da nuna k'yama. Ba zai ci abinci tare da ni ba, ba zai kwanta d'akin da nake ba, haka zalika a cikin kwana biyun nan baya bina jam'in sallah a massalaci, ina kallonsa ya ke tafiya wani massalacin na daban. Ban san menene dalili ba, Mama amma kuma baya nunawa Yusi k'yama, wannan dalilin ya sanya ni yanke shawarar barin gidan gabad'aya domin ba na so watarana na kasa jurewa muddin a haka zamu dinga tafiya dashi babu kyakykyawar ala'ka, babu musabaha da girmama juna sai k'yama, zuciyata ba zata iya jurewa ba, Ina jin tsoron mu yi fad'a hakan ya ta'ba zumuncinku da zamantakewarku. Kin ga Momi babu komai a tsakanina da ita sai alheri Ina sonta sosai wallahi irin yadda nake sonki Mama, amma ba na so mu yi abinda duka zai bata muku rai shine dalilana."
Nasan dama ruwa baya tsami banza. Amma kuma sanin da na yi wa yaron a baya kafin ya tafi karatun ba haka yake ba. Yaro ne mai nutsuwa da son mutane irin d'an uwansa Adam ga barkwanci. Nusaiban dai ce mara fuska.
Na daure ban nuna b'acin raina a fili ba na ce." Kenan ba ku taba magana ba tunda ya dawo?"
Ya ce." Idan na mik'a masa hannu domin musabaha baya kar'ba. D'azu da safe a gaban Momi ya yi. Hakan ya 'bata mata rai sosai ta yi masa fad'a. Shine ya tashi ya fita bai dawo ba har na fito, wallahi mama kada ki so ki ga yadda hankalinta ya tashi, shine take cewa kada na gaya miki."
Shiru na yi ina nazarin al'amarin. Kamalu bai yi lefi ba domin kuwa anan ya yi aiki da hankali da kuma iliminsa. Na kuma ji dad'in abinda ya yi da har ya iya danne zuciyarsa bai biye masa ba. Shawarar da ya yanke itace mafita muddin kuwa ana son zaman lafiya. Idan har Salim bai gane abinda yake yi kuskure ba ne, to babu mamaki wataran gagarimar matsala ta faru tunda ni nasan wanene Kamalu a fagen zuciya.
Amma yadda zan yi na sanar da maigidan halin da ake ciki shine matsalata. Na riga nasan rikice ne akwance domin kuwa baya d'aukar abinda ya shafi matarsa da wasa. Maganarsa daya amanarsa ce 'ya'yanta ma amana ne, a wannan ga'bar kuwa ya zame masa dole ya bincika domin tabbatar da gaskiyar abinda yake faruwa ya kuma gyara matsalar kafin ta yi nisa.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 101
Na ce." Abinda za a yi yanzu shine ka d'an daure kad'an, ai ni ka burgeni sosai da har ka yi irin wannan tunanin wannan ya sake nuna mini cewa Kamaluna ya bambamta sosai da wanda na sani a baya. Ka cigaba da yi masa magana kada ka biye masa ni kuma zan yi magana da Baban nasan dai haka kawai ai ba zaka kirkiri karya don jin dadi ka gaya mini ba ko?''
"Wallahi Mama babu karya cikin maganata gaskiyar abinda yake faruwa na gaya miki, menene ribata idan na yi k'aryar kuma me ya yi mini da zan 'bata shi."
Na ce." To kada nunawa Momi damuwarka a fuska ka daure ka ji ko."
Ya ce." In sha Allah Mama.
Daga haka sai muka bar maganar muka shiga wata ina d'an jansa da wasa duk domin ganin ya manta abinda yake damunsa. Amma zahiri ni a can 'kasan zuciyata cike nake da fargabar yadda zan tunkari maigidan da maganar. Wala'ala ya fahimceni, wala'ala kuma ya juya mini manufa, amma dai tun yanzu ya kamata a ce ayi wa tufkar hanci kafin lamarin ya yi tsamari rayuka su zo suna 'baci.
Daf da magriba ya tashi ya fita da zummar shirin shiga massalaci.
Bayan kwana biyu ina cikin nazari domin har yanzu na kasa tsayar da abinda nake ganin shine daidai. Ba na so na yi magana ne a ce na goyi da bayan yarona wata'kila shi kansa zai iya ganin haka shiyasa hankalina bai kwanta ba har yanzu sai dai na gaza daurewa na sanar da Baba Tabawa abinda yake faruwa domin kuwa macace mai tsinkaye da nisan tunani.
Ta jima tana jimantawa kafin ta ce." Ai shurun ba shine mafita ba, gwara ki gaya masa tunda shine jagoran kowa a gidan ya yi wa tufkar hanci kada lamari ya yi k'wari hatsaniya ta tashi ya ce mai yasa ba a gaya masa ba. Ina ganin duk wanda zai ce kin so kanki da zummar kawo gyara to ya zalinceki domin kuwa abinda ki ka yi shine daidai, ai ba ki za'bi Kamalu kin fifita akan Salim ba, duka naki ne kamar yadda itama Momin take nunawa, to ya kamata a ce wannan 'barakar da take ko'karin kunnowa an yi maganinta.
Ajiyar zuciya na sauke bayan duk na gama sauraran maganganunta. Na ce." Shikkenan Baba, in sha Allah zan sanar da shi halin da ake ciki duk kuma yadda muka yi aki ji."
Ta ce." To shikkenan, Allah Ya maganta."
To daddare ina d'aki a kwance misalin takwas da rabi ya shigo mini cikin tsananin b'acin rai. Na tashi zaune da sauri gabana na fad'uwa. Ya zauna samar kujerar madubi na ce." Kai lafiya Kamalu."
"Mama barka da dare." Da abinda ya fara kenan. Na amsa a takaice na ce." Menene?"
Duk dauriyarsa sai da muryarsa ta yi rawa ya ce." Mama ba zan iya ba, ba zan iya jurewa ba, zan tafi kano gobe domin kuwa Salim baya neman zaman lafiya da ni."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.