Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel
Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt
Chapter 23 of 34
Ba ni da niyyar sanar da kowa wannan lamarin a ganina hakan kamar bai shafe ni ba, yaro da na d'auka tunda ta tafi ta bar shi zan yi iyakar bakin kokarina. Amma tabbas Hauwa rikici da gangami ta shiryawa kanta kuma a zahiri naga wautarta domin ta aikata abu irin na marasa sanin ya kamata.
Cikin hukuncin Allah lafiya lau muka kwana da yaron bai yi kuka ba domin kuwa Baba Tabawa ta bada dukkanin kulawarta a kansa. Ni kaina cewa ta yi na tafi na kwanta za ta kula da shi. Ban kwanta ba kuwa sai da na nuna mata yadda za ta dama masa madararsa idan Allah ya sa ya farka ta ajiye komai a kusa da ita wanda za ta buk'ata.
Da safe kuwa kafin na fito ta shirya shi tsaf yana goye a bayanta yana bacci lukwi hankalina ya kwanta sosai domin duk juyin da zan yi sai ya fado mini a rai tare da takaici da b'acin ran abinda uwarsa ta aikata.
Sai bayan sallar azuhur tukkuna na samu Hauwa a waya. Ta daga hankalinta a kwance domin ban ji alamun nadama da danasani a muryarta ba.
Jikina ya mutu sosai da kyar na furta." Kina ina Hauwa?"
Kai tsaye ta ce." Ina nan Bauchi."
Na danne takaicina tare da cewa." Ashe kin shirya hakan tuntuni to hakan da ki ka yi a ganinki daidai ne ko?"
Da d'an murmushi ta ce." Shine daidai Amina, domin wa'adin zamana ya kare a gidan tunda na haihu yaro kuma ai gidan ubansa ne tunda ba dashi na zo ba, mai zai sanya na d'auko shi na kawo shi inda babu tarbiya Amina sunan Amadu fa ya fi sunan ubana an ce mini ubana ba komai ba ne a lokacin da na nuna shi din wani abu ne, tuntuni na gaya miki dama ba zan jure wannan rashin mutuncin ba."
Cike da takaici na furta." Amadu fa aka ce shine Mahmudu Muhammadu. Ki tuna mai wannan sunan shine wanda aka yi duniya dominsa Annabi Muhammadu S.a.w a ganina wannan abin alfahari ne a wurinki."
Ta yi murmushi tana cewa." A a ba da wannan niyyar ya sanya sunan Amadu ba. Abokinsa mai rasuwa fa shi yayi wa takwara na ce masa Ina son sunan mahaifina tunda na farko ya sanya sunan mahaifinsa daga fad'in haka ya fara gaya mini magana tabbacin dama haushina yake ji to menene saura a tsakaninmu na fita daga iddarsa da dama."
Na gyada kaina ina danne abinda nake ji a raina na ce." To kina ganin Allah ba zai kama ki da hakkin yaron ba shine ina ruwansa."
Ta yi Dariya tare da furta." Allah Ya yafe mini shi kuma idan rayayyene Allah Ya raya shi."
Na yi shiru domin kamar kalaman bakina sun kare da kyar na ce." Yanzu mai ki ka gayawa inna Uwani."
Da sauri ta furta." Tun daga farko a har karshe wallahi ban boye mata komai ba, Amina ai na yi hakuri na yi kuma biyayya, ke kan ki ban shure shawararki ba, na yi ta ha'kuri tsayin wattanin dana d'auka a matsayin sakakkiya mutumin nan baya kula ni kuma bai furta ya mayar da ni ba, duk wata dama ya samu bai yi magana ba yanzu kuma ai komai ya zo karshe na gaya mata komai haka zalika ma babu wanda bai sani na a family din Babanmu."
"Kenan Hajja ta ji komai?"
Na tambayata cikin zullumi.
Ta furta." Kwarai kuwa d'azu nan suka gama waya da Inna." Na yi shiru Ina nazari kafin daga bisani na furta." Hauwa idan zu'kata sun huce a daidaita don Allah kuma yaron nan da kaina zan kawo miki shi gobe in sha Allahu rabbi, ki yi hakuri don girman Allah ki kar'bi d'anki kada ki wulakantashi domin bakisan baiwar da take tare dashi ba."
"Na rantse da girman Allah a yanzu dai Amina ko kin zo da yaron nan sai dai ki koma dashi don wallahi tallahi ba zan karbe shi ba sai ubansa ya zo da k'afafunsa ya nuna nadama akan abinda ya yi mini, idan har ke za ki iya jure wulakancinsa ni kam ba zan iya ba. Ki ri'ke shi kawai na bar miki."
Bakina ne ya mutu murus na rasa abin cewa tunda har ta riga ta rantse nasan abu ne mai mutukar wahala ko na kai mata yaron ta kar'ba.
Zuwa yanzu kuwa na tabbatar da cewa tunda Hajja ta ji fasuwar maganar to babu shakka wanda ya asassa ma ya sani. Zan jira yi ji daga gare shi domin kuwa babu wani bangare da zan tuntunba Allah Ya ga zuciyata na yi iyakacin bakin k'okarinta.
Kwana daya biyu har uku ban ji daga gare shi ba. Gabad'aya ma yau kusan kwanaki biyar kenan rabon da mu yi magana tun ranar da na sanar dashi haihuwar Hauwa ban sake ganinshi a online ba. Sai na fara trying din lambar da yake kirana da ita busy bata shiga hankalina ya d'an tashi domin tunda suka tafi bai ta'ba kwana biyu bai ta'bo ni ba.
Na gaza ha'kuri har sai da na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa lafiya ina amsawa da Amin.
Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba. Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo. Amma kalmar Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu. Na bude gabana na bugawa da karfin gaske...
_"Allah Ya yi wa Maryam rasuwa bayan sallar la'asar ki sanar da duk wanda ya kamata Amina."_ Abinda yake rubuce kenan
Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga Ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! Hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata. Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta." INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne."
Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje! Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in." Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!"
Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas
Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce." Hauwa Momi ta rasu d'azu da la'asar yanzu nan maigidan yake sanar da ni....
[12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: *116*
Cike da rikicewar murya ta furta." Wac...wace Momin kike nufi Amina?"
Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take... Na ce." Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam."
Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana. Na daga wayar na duba tana ta tafiya. Sunanta na kira ta amsa a sanyaye "Na'am. Na ce." Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa."
Ta yi shiru dai bata tanka ba. Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali.
Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace.
Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya. Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska. Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi. Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule.
Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can. Na sameta ta ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa. Rashin kwarin kafafuna ya sanya ni zubewa gabanta na furta." Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?"
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace." Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne." Hanci na ja tare da furta " Baba tunda ranar da muka je duba baiwar Allah nan wallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai."
Ta girgiza kai cike da kasala ta ce." To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi."
Da "Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma.
Mun jima muna cikin alhini tare da tariyo kyawawan halinta kafin mu yi sallama babu batun cin abincin dare domin gabad'ayanmu babu wannan kuzarin a tattare da mu.
Ban ta'ba tsoron mutuwa ba sai a kan matar nan ni kadai a d'aki ta dinga yi mini gizo. Dana rintse idona sai na ga suffarta mussaman karshen ganina da ita lokacin da ta shigo yi manna sallama da za su tafi. Na cigaba da kiran sunan na d'auki waya na kira Sahura ganin kiran bagatatan cikin dare sai ta tsorata ta fara tambayata a ki'dime! Da kyar na iya gaya mata halin da ake ciki. Ita kanta sai da ta rude tana fad'in." Amina ban ta'ba ganin matar nan ba Amma wallahi mutuwarta ta gigitani. Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya sanya karshen wahalarta kenan, mu Kuma da muka d'auki zunubinta Allah Ya yafe mana, amma ni kaina na jima da sanin cewar matar nan baiwar Allah ce duk kazafin da wasu daga cikin mutane suke yi mata ba gaskiya ba ne, kin san haka siddan Ubangiji ba zai d'aukaka bawansa ba sai da jarrabawa. Allah Ya yi mata rahama.
Babu kuzari na ce." Amin suma Amin Sahura ni kaina a gigice nake wallahi a yanzu a cikin raina sai nake tunanin mai yasa na yi abinda na yi a baya dana sani na ha'kura kawai tunda duniyar guda nawa take. Zahiri matar nan alherinta na sani ban san wani sharrinta ba, domin idan zan bude baki na furta ga abinda tayi mini na rashin kyautawa wallahi na yi mata sharri Sahura, ba ki ki yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta. Ita kanta Hauwa tana can cike da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita wallahi sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa furta komai."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.