Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel
Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 34
**
Bayan sati biyu al'amura suna cigaba da tafiya da dad'i babu dad'i. Har zuwa lokacin Salim bai kyale Kamalu ba. Kusan kullum da b'acin rai yake shigo mini duk da yana ko'karin daurewa amma ina fahimta. Ha'kurina yana daf da k'arewa domin tun ranar da na kira maigidan a waya na gaya masa abinda yake faruwa bai sake nema na da maganarba duk kuwa da cewa kusan kullum sai mun yi bidiyon call. Ni ma ban sake tayar da maganar ba na bari ne kamar yadda ya ce mu jira zuwansa. Amma koyaushe idan na dubi Kamalu na ga yadda ya rage walwala da kuzari zuciyata takan yi zafi. Ina dalili haka kawai saboda gudun b'acin ran wani a 'kuntata zuciyar yaro. Babu lallai fa babu dole muddin ba zai d'auki mataki ba wallahi sai Kamalu ya tafi ya bar garin da gidan gabad'aya.
Ranar litinin da yamma suka sauka shi da Hauwa. Baiwar Allah ta kuma samo wani cikin domin yanayinta kadai ya tabbatar mini da cewa laulayi take yi ta yi mugun haske dama idan tana da ciki d'ashewa take yi. Macace mai kwainika Minal na da wata goma sha takwas. Allah Ya sa tana da san girma, tana yawo da kafafunta da yake abincin gwangwani take ci a can ta zama rusheshiya kataf-kataf haka take yawo uban yana tsokanarta da 'yar sukuta. Wai na washeta har ta fi su Hassana girma jiki tunda su jikin irin nasa ne. Kwana biyu da zuwansu na fahimci rashin jituwa a tsakaninsu. Kamar ma basa magana da juna. Na yi dai shiru ina kallon ikon Allah. Ita yini ma take yi a d'aki sai yamma take fitowa falo shi kuma har ya yi kwana biyunsa a wajena bai ce mini komai ba.
Na cika da mamaki sosai. Lallai ma wannan mutumin wato maganar tabi shanun sarki kenan Salim ya yi daidai babu kuskure akan abinda yake yi.
Ba zan lamunta ba domin kuwa har yanzu a cikin matsalar ake sai abinda ma ya yi gaba. Kamalu bai rasa madogara ba hakama Yusi idan har ba zai gyara abinda yake faruwa ba to na yarda ya ba ni yarana su kuma can hannun Babansu Hamusu.
Cikin wannan nazarin Hauwa ta shigo d'akina ta same ni. Ta zauna gefan gado tana fad'in." Ko jikin ne?" Na tashi zaune Ina fad'in." A, a ni kam ai na warware na bar miki Hauwa."
Kwafa ta yi tare da cewa." Ban ji dad'in shigar cikin nan ba wallahi.''
Na dubeta a tsanake tare da cewa." Mai yasa Hauwa ki godewa Allah da fatan samun masu albarka."
"Humm!" abinda ta ce kenan kafin ta ce." Ban shigo domin na tunzuraki ko tayar da husuma ba. Idan kin lura da yanayin yadda muka zo da ni maigidan babu dadi don wallahi mugun haushinsa nake ji."
Na ce." Menene kuma ya kamata ki manta da matsalar matar nan Hauwa, ki yi ta kanki haihuwa ta uku za ki yi da mutumin nan duk abinda zai yi ya je ya yi haka ya ga zai iya."
"Wallahi Amina ko kaffara ba zan yi ba matar nan ba haka ta bar mutumin nan ba."
"Mai yasa ki ka ce haka Hauwa, zato zunubi ne fa Koda ya kasance gaskiya ne?"
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 102
"Amina maganar gaskiya zan gaya miki na gaji da zaman nan da muke yi na rashin 'yanci da kaskanci wallahi tallahi ba zan jiya jure ba, wannan shine dalilin ma da ya sanya ki ka ji na ce ina b'akinciki da takaicin samuwar wannan cikin na jikina, in banda ina gudun sa'bawa Allah wallahi da sai na zubar da shi."
Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Hauwa mai ya yi zafi haka, ha'kuri fa ya zame miki dole na farko mutumin nan d'an uwanki ne kuma mijinki uban yaranki, idan kin rabu dashi ki auri wa kenan, ke ce ya kamata ki zauna dashi Hauwa saboda haduwar jini da kuma zuri'ar da take tsakaninku."
Cike da takaici ta furta." Shi ai baya ganin yadda muke yin hakuri Amina, a ce mutum bashi da wani mutunci da daraja. Shikkenan sai ka ajiye mata uku ka za'bi daya ka fifita saboda wata banzar hujja."
Dariya na yi na gane dama duk wannan hayaniyar da take yi akan Momi ne, har yanzu ita ta kasa d'auke kanta daga sha'aninsu. Na ce." Hauwa da za ki d'auki shawarata wallahi da kin daina girmama al'amarin nan kin sanya shi a ranki, ki yi abinda yake gabanki kawai ki rabu da duk abinda zai yi, ai duk wanda ya gyara ya sani kuma duk wanda ya 'bata ya sani."
Shiru ta yi tana kallona kafin ta gyada kanta ta ce." Idan kuwa har ina da hakki to Allah Ya isa ban yafe ba wallahi, domin ni don ba yadda zan yi ne na ha'kura da wannan sintirin haka kawai sai ta toge da ri'ke mana yara ita tana kamile a waje daya saboda shafaffiyace da mai."
Na ce." Ai kin fi ta samun ladan aure Hauwa, don Allah maganar nan ta mutu haka haba."
"Magana ba za ta mutu ba Amina, ba ni na haifi Kamalu ba amma zahiri sai inda karfina ya kare a kan sharrin da yaron nan Salim ya yi masa."
Na dubeta a nutse." Wane irin sharri kuma Hauwa?"
Shiru ta yi tana kallona da yanayi na damuwa sai ta gyada kanta cike da b'acin rai ta ce." Abin da akwai daure kai Amina, nasan kuma ba zai gaya miki ba saboda yadda ya nuna kamar ya yarda da maganar yaron. Nuna masa hakan ba daidai ba ne ya yi aiki da maganar mutum d'aya sai ya janyo mana rikici shine fa muke ta yi har yanzu ba ma ga miciji"
Jikina ya sake yin sanyi a nutse na ce." Ki gaya mini Salim din ya nemi wani abu nasa ya rasa ne, ko kuwa ita ma Momin ta nemi wani abu bata gani ba?"
Ta ce." A a babu d'aya Amina, ni kaina ina jin nauyin gaya miki wallahi, Amma ya zama dole ki sani domin ki nemi mafita Salim din ne yake gayawa maigidan wai Kamalu yana lalubensa a cikin dare har yana cire masa gajeran wando!"
Wani irin yamm! na ji tun daga tsakiyar kaina har zuwa kafafuna. Yawun bakina ya tsinke gabana yana fad'uwa na ce." Hauwa wace irin magana ce wannan don girman Allah!"
Ta dafa cinyata a hankali ta ce." Maigidan ya kira Salim domin jin 'karin haske dangane da maganar da ki ka gaya masa a waya tsakaninsa da Kamalu bud'ar bakin yaron sai ya ce masa Kamulu yana nemansa wai har yana cire masa gajeran wando."
Shiru kawai na yi kaina yana juyawa. Abubuwan da suka shud'e a shekarun baya suka dinga dawowa kaina. Yusi da Kamalu. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! maraici maraici maraici! an ce Yusi ya lalata yarinyar mutane, yau kuma an ce Kamalu zai yi luwadi.
Hannu nasa na tallafe ha'bata gabad'aya tunanina ya tsaya cak!
Ta dafa kafadata a sanyaye ta ce." Nasan dole ne ki kadu da jin wannan mummunan labari Amina, ki yi hakuri ban gaya miki da zummar na daga miki hankali ba, wallahi tallahi wannan shine dalilin da ya assasa mana rikici mai zafi saboda na gaya masa cewa wannan sharri ne kawai, kuma bai kamata ya yarda da maganar ba."
Na dube ta a hankali na ce." Kenan ya yarda da abinda Salim din ya gaya masa."
"Ya saurare shi dai a waya bayan sun gama shine yake gaya mini. Na ce to ya sanar dake kuma ya nemi Kamalu shima ya ji daga gare shi ya ce babu daya da zai yi a ciki. Jin haka sai kawai raina ya b'aci na fara nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa daga lokacin zamanmu ya rikice wai ban isa na nuna masa yadda zai yi ba. Tunda babu wanda na haifa a cikinsu na ja bakina na yi shiru shi ya san hukuncin da zai yanke."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.