Complete Hausa Novels

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel

Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt

Chapter 22 of 34

Na jima ina kallonta tare da auna maganganunta. Yadda take tabbatar da abinda ba ta da tabbas akai shine abinda ya fi daga mini hankali da lamarinta. Wace irin kiyayyace wannan. A ganina wannan abin da take yi jahilci ne tsantsa da rashin sanin abinda ya dace. To ba ni da bakin magana domin kuwa yadda ta yi nisa irin haka babu wani kalami da zan yi mata ya sanya ta sassauto daga irin kiyayyar da take yi wa matar nan wadda alherenta suke dabaibaye damu bakidaya.
Ganin ban ce mata komai ba ya sanya ta tashi tana fad'in." Matsantawa kai ne kawai kowa ya kashe wutar gabansa. Shi kuma ai hakkin rai tun a duniya Ubangiji yake fitar da shi wallahi tallahi yanzu ta fara gani.

Sai kawai na saki bakina ina kallonta har ta fice daga d'akin ban d'auke idona ba.
Na jima a zaune Ina tufkewa da warware kafin na tashi jiki a sabule na shiga bandaki domin watsa ruwa a jikina. Gabad'aya cikina ya cushe babu dandano a bakina ko kad'an yunwar ma sam ba na jin ta, daga zarar na tuna halin da muka riski matar nan a ciki sai hankalina ya tashi.
A haka na shirya cikin kayan bacci ina tsaye gaban madubi ina busar da gashin kaina. Ya turo kofar d'akin ya shigo. Ban yi zaton shigowarsa ba. Muka had'a Ido ya nufo wurin da nake tsaye daf da ni ya tsaya na gama abinda nake yi yana ta kallona ta madubi na juyo kirjinmu ya hadu waje daya. Kusan a tare muka sauke ajiyar zuciya. Ya riko hannuna muka zauna gefan gado. Yanayin fuskarsa kadai shi ya nuna mini cewar ya ji dadin abinda na yi. Ya furta." Kin kyauta sosai kuma na ji dadin abinda ki ka yi, idan haka kuke yi mini kara akan abinda nake so mai zai sanya ni ma na 'bata muku ai babu abinda ya fi zaman lafiya dadi ko."
Kanzil ban ce masa ba. amma maganarsa ta d'an dake ni wato shi baya jin nauyin gaya mana irin son da yake yi wa matar nan tasa.
Ya d'ora hannunsa a tudun kirjina wanda tun zaman da muke yi a wurin hankalinsa yake kai. Ya nisa kafin a kasalance ya furta." Momi ba ta da lafiya Amina cikinta da wajenta wallahi."
A nutse na furta." Allah Ya yaye mata, da sauran al'ummar musulmi."
Ya amsa da Amin kafin ya dora da cewar." Kin san yanzu wani result din ya sake fitowa bayan gwajin da aka yi mata satin da ya wuce cancer mahaifa."
Da saurin gaske na dube shi. Ya gyada kansa "Wallahi ni kaina na kadu Amina na tausaya mata k'warai da aniya yanzu haka za mu yi booking domin zuwa india akwai kwararrun likitoci a can da za su caje mini ita sosai."
Jiki a masifar sanyaye na furta." Tabbas Ubangiji shi yake saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa, ina yi mata fatan alheri tare da addu'ar samun lafiya madawamiya, kai kuma Allah Ya baka ladan jinya."
Ya sake amsa da "Amin Ya Allah." D'akin ya d'auki shiru har yanzu hannunsa na saman kirjina yana dan tattabawa. Ban hana shi ba kawai dai ina mamakinsa ne a ganina yanayin alhinin da yake ciki da damuwa akan rashin lafiyar maidakinsa bai kamata a ce wani sbu na jin dad'in duniya yana bijiro masa ba, to mai ma zai fahimta bayan yana cikin tashin hankali a haukana fa kenan
Na dube shi yana lumshe idonsa kamar wanda ya samu audiga na dan ture hannun nasa muka kalli juna a sarke na ce." Dama ina son magana da kai."
Kai tsaye ya furta." Idan har akan zuwa maiduguri ne to kada ki bata bakinki babu inda zakije."
Na ce." To saboda me, kafi kowa sanin matsayin anti Yagana a wurina ko?"
Ya gyada kansa a tsanake ya ce." Da dai ban rantse ba ne sai na bari ki je, amma wallahi na riga na rantse ki yi hakuri bayan bikin sai ki je ki ga d'akin amarya."
Zuciyata ta dinga tiriri na dinga danne abinda yake yun'kuro mini domin ba ni son na nuna masa damuwata a kan haka a gaba ya samu abinda zai kuntata mini idan wata matsalar ta faru a tsakaninmu. Na gyada kaina tare da furta." Shikkenan mu ajiye wannan maganar ina so ka gaya mini matsayin zamanka da Hauwa a gidan nan, domin ni har yanzu na kasa gane abinda kuke nufi da kai da ita."
Ya dube ni sosai kafin ya ce." Ke ina ruwanki kuma?"
Na ce." Ni ce kuwa nake da ruwa tunda duk wata mas'ala da kuka samu da kai da ita a kaina ne, yanzu a matsayinka na babba mai hankali da jagoranci abinda kuke aikatawa daidai ne."
Ya ce." Ai taki ta amince da cewar ta yi lefi, sannan taki ta bi umarinina idan tana so magana ta shige mai yasa bata biyo ki zuwa duba Momi ba. Ta cigaba da zama a haka duk ranar da ta gaji sai ta nemawa kanta mafita."
"Gaskiya hakan ba daidai ba."
Ya 'bata rai yana fad'in." To nuna mini daidai Amina."
Shiru na yi ban sake magana ba. Ya ja tsaki yana fad'in." Na yabe ki sallah za ki kasa alwala, Hauwa ai ba yarinya ba ce idan tana son zama da ni ta ba ni ha'kuri ta Kuma bi umarina."
Na ce." To ai kaine babba ha'kurinka shine zai fi rinjaye."
"Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?"
Shiru kawai na yi Ina kallonsa. Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?"
Na ce." Yadda muke yi mana."
Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta."
Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya.
A daran na gurzu a hannunsa kwarai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni. Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah. Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice. Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba.
Bayan kwanaki shida mun d'an samu daidaito kad'an. A lokacin kuma sun gama shiryin tafiyar da za su yi. Har gida ya yi mata jagora domin ta yi masa sallama. Zamanta ke da wuya Hauwa ta yun'kura ta tashi ta shige dakinta. Hakan kuwa bai yi mata dad'i ba, amma dai ba ta ce komai ba, muka d'an ta'ba hira sama-sama kafin ya sauko daga saman suka fita tare. Sosai na yi mata addu'a da fatan alheri ta dinga godiya da murmushin nan nata wanda duk rintsi baya ta'ba d'aukewa daga saman fuskarta.....
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: *115*
Bayan tafiyarsu da kwana ashirin da shida Hauwa ta haihu. Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji kama da ubanshi har ta 'baci duk abinda ya kamaci ta yi wa kanta ta yi tunda haihuwar gida ta yi kuma lafiya lau ita da yaron da ta haifa, a matsayinta na ma'aikaciyar lafiya taimakon da muka yi mata kad'an ne. Sai bayan da muka samu nutsuwa gabad'ayanmu ni da tukkuna na nemi maigidan da yake koda suka tafi ba kasafai yake kiran waya ba sai dai mu had'u ta whasap to baya jurar typing sai da vedio call. Sai na ajiye masa sa'ko ta whasap din tare da hoton yaron nasan daga zarar ya hau zai gani. Ina idar da sallar la'asar na bud'eta sakonshi ya shigo yana online din muka sake gaisawa na tambaye shi mai jiki ya ba ni amsa mai dadi jiki yayi kyau domin a karshen watan da muke ciki ma za su dawo domin an d'orata akan maganguna kuma alhamdulillahi an samu cigaba.Sai ya d'ora da fad'in na yi wa yaron hud'uba da sunan Ahmadu domin shine sunan da ya rad'a masa. Rashin abin cewa ya sanya ni yi masa shiru kawai domin tunda Hauwa ta haihu take kiran yaron da sunan mahaifinta wato Ishak, ban san kuma mai zan ce mata ba gaskiyar magana kenan.
Ganin na yi shiru ban ce komai ba ya sanya shi kiran sunana na kalle shi tunda bidiyo call ne ya furta." Ko akwai wata matsala ne domin na karanci damuwa a cikin kwayar Idonki."
Na girgiza kaina a nutse na ce." Babu matsala amma gaskiya ba zan iya gaya Hauwa ga abinda ka yanke ba, mai zai hana kai ka gaya mata naga tare kuka samar da yaron nan ku biyu mai zai sanya ni ka saka ni a tsakiya. Hauwa tunda ta haihu take kiran yaron nan da sunan babanta, to ni mai kake so na ce kuma."
Ya yi shiru yana kallona kafin daga bisani ya ce." Shikkenan zan gaya mata hukuncin dana yanke hakan ya yi ko."
Na gyada kaina ina fad'in." Ya yi shine daidai sai ku tsyar da matsaya a tsakaninku, Allah Ya raya mana shi."
Ya amsa da "Amin. Yana mai zuba mini ido."
Ni ma na zuba masa nawa idon nan na fahimci canzawar da ya yi har da wani kumatu fatar nan ta sake yin fresh duk da bidiyo call yana sanya mutum muni da duhu to shi ban ga hakan ba, kamar ba wanda ya tafi jinyya ba ya yi kama da ango wanda ya tafi yawan sha'katawa da amaryarsa.
Ajiyar zuciya na sauke yayin da nake ko'karin kawar da abinda na ji yana yun'kuro mini a game dashi na ce." Na canza kammanni ne Allah Ya taimaka ka."
Sai ya rausayar da kansa yana ce wa." Sosai kuwa, wata na gani anan asibitin da muke mai kama dake duk sanda na yi ido hud'u da ita sai hankalina ya tashi wallahi yanzu ina cikin tsananin damuwa na yi missing d'inki my wife."
Na dan bata rai tare da cewa." Matar kuma idan tana da aure fa, kana raya abun da bai dace ba akan matar wani daidai kenan a wurinka."
Kansa ya girgiza kamar karamin yaro ya furta." Ba daidai ba ne, amma ba na tsammanin ai tana da aure budurwa ce, wallahi ba zan munafurceki ba Amina ba na iya d'auke kaina daga kanta domin yanayin hallitar jikinku daya 'yar duma-duma ce mai yawaltaccen kirji da tudun mazaunai."
Dariya maganar ta ba ni na danne ban yi ba domin ganin abin nasa yana nema ya wuce makadi da rawa na ce." To sai ka tuntubeta idan ba ta da aure ka aurota ko?"
Ya girgiza kansa yana ce wa." A'a ai ba musluma ba ce addinin hindu ce."
Na ce." To menene a ciki sai ka musuluntar da ita."
Kansa ya girgiza tare da furta." A a, abinda ya sa ki ka ji Ina yi miki maganarta kamar da kuke yi da ita ne ya b'aci da gaske idan na ganta ina shiga yanayi na buk'atuwa sosai."
Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ina nan dawowa my love za mu sha soyayya ko?"
Na kashe idona tare da fad'in." Sosai ma irin wadda kake so za mu yi."
Sai ya zuba mini idanuwansa babu kiftawa. Na kama dariya ina fad'in." Ka na ji kamar ka d'auko ni daga cikin wayar ko?"
Ya gyada kansa yana lumshe Ido. Hakan ya sake jefa ni a damuwa da sha'awa na sauke ajiyar zuciya a kasalance na furta." Ni ma na yi missing din Baba Yallabai baban soyayya."
Kafin ya ce wani abu kiran da aka yi masa a wayar ya katse video call din. Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefe Ina sauke ajiyar zuciya gabad'aya hirar nan da muka yi ta tayar mini da hankali wani irin nake ji a jikina.
Sai gefin magriba na fito falon daga cikin d'akin Hauwa na ji kukan yaron ya tsananta da saurin gaske na shiga d'akin na same shi kwance cikin net dinshi yana ta wutsil-wutsil towel ya toshe masa hanci. Da azama na zuge net din na d'auko shi fuskarsa ta yi jazur saboda da alama ya jima yana kukan.
Na zauna gefan gadonta ina jijiigashi gabad'aya ya shid'e a tunanina tana bandaki na tashi tsaye dashi a kafad'ata na tsaya kofar bandakin Ina Kiran sunanta shiru bata amsa ba kuma babu motsin ruwa. Sai kawai na kutsa kaina ciki wayam babu alamunta. Da sauri na fito gabana na dan fad'uwa na tsaya ina rarraba idanuwana a d'akin ban ga alamun komai ba..
Na fita kai tsaye kicin na nufa Baba Tabawa ta kammala abinci dare tana gyara kicin din. Cikin kasala da sagewar gwiwa na furta." Baba ina Hauwa?"
Sai kawai ta tsaya tana kallona kafin daga bisani ta furta." Ba ta dakinta ne Amina?"
Na furta." Kwarai kuwa, fitowa daga d'aki kenan na ji kukan yaron nan koda na shiga d'akinta bata nan."
Ta sanya hannunta ta kar'be shi a sanyaye ta biyo bayana muka tsaya a tsakiyar falon. Ina Hauwa za ta tafi to. Ni nake tambayar zuciyata dalili tunda ta haihu ban ga alamun fitina a tattare da ita ba asalima wani babin annashuwa da farinciki ta bud'e. Baba Tabawa ta sanya babban towel ta goya yaron ni kuma na d'auko hijabina na sanya na fita can harabar gidan. Daga nesa na tsaya Ina hangen securitys a bakin gate. Masa'udu ya shigo da mota ya ajiye a wurin da motocin suke ya fito daga motar ganina a tsaye ya sanya shi da sauri ya nufo ni. Ya risina yana gaishe ni na amsa tare da fad'in." Daga ina kake domin zuciyata ta fara hasashen wani abu.
Kai tsaye ya furta." Daga airport nake na kai Hajiya k'arama ne za ta bi jirgi zuwa bauchi don haka na ji tana fad'a a waya kafin mu isa filin jirgin."
Ba tare da na sake cewa komai ba na kada kaina na koma ciki gidan raina a masifar b'ace. Anya kuwa Hauwa tana da hankali ki haihu kwana biyu kacal saboda mugun abu ki gudu ki bar jaririn da ki ka sha dawainiya da wahala a kansa kafin ya zo duniya kici kwakwa. Da kuma d'aita irin ta haihuwa da rashin kwari a jiki
Baba Tabawa ta dinga salallami tana fad'in." Wannan wane irin sakarci ne Hajiya Amina, to shi wannan din da ta tafi ta bar shi ai hakkinsa ba zai bar ta, ina ruwansa da abinda ya faru.
Ban ce mata komai ba na shige na je na d'auko wayata layinta na dingi kira wayar a kashe na kira ya kai sau goma amma is switch off. Na zube saman kujera ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!"
Na jima cikin wannan yanayin kafin na d'auki wayata dake saman cinyata kai tsaye lambar dr Sailuba na nemo itace tsayayyiyar likitan da take duba ni a duk lokacin da na samu ciki mussaman cikin baby Nana ta taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske. Abu na farko da zan yi shine samarwa da yaron abinci matsalar raino wannan mai sau'ki ne. Bayani na yi mata sosai amma ban sanar da ita cewa uwar yaron ce ta ajiye shi ba.
Ba mu yi sallama da ita ba sai da ta tabbatar mini da cewa da kanta za ta shigo ta kawo mini duk abinda ya dace.
Na kashe wayar tare da zubawa Baba Tabawa idanu tana ta faman safa da marwa a katafaran falon duk domin hillatar yaron da yake ta kusurkusur da alamun kuka.
Sai da bacci ya d'auke shi tukkuna ta zo ta zauna a gefana tana fad'in." Ko a tarihi ban ta'ba ganin shashashar uwa irin Hauwa ba Hajiya Amina lallai ta gwadawa wannan yaro rashin Imani."
Shiru na yi Ina nazari kafin daga bisani na furta." Tana so ta huce fushin abinda ubansa ya yi mata shine ta dire shi ta yi tafiyarta. Abin mamaki kuma ita da mijin nata jini guda ne mamansa ta cika nono ta bawa Mamanta wace irin zuciyace wannan."
Kai tsaye ta ce." Zuciyar kafurai ce."
Muka yi shiru cikin alhini kafin ta cigaba da cewa." Ita kanta na tabbatar da cewa wallahi hankalinta ba zai ta'ba kwanciya ba ciwon jiki da ciwon nono ma ya isheta.
Murmushi na yi tare da cewa." Ciwon nono mai sau'ki ne a wurinta tunda likita ce tana da hanyoyin da zata magance abinta ciwon jiki kam zata sha ai haihuwa ba wasa ba ce."
Haka muka kasance cikin zullumi da tararrabi har Dr Sailuba ta zo ta tafi muna zaune a falon cikin wani irin yanayi na mamaki da takaici.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.