Complete Hausa Novels

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel

Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt

Chapter 32 of 34

Ta girgiza kanta tana jimantawa domin ita da ta fi mu yawan shekaru ma abin ya tsaya mata a rai. Hauwa ta fito ta same mu muna tattauna maganar. Taja tsaki kafin ta dube ni a nutse tana fad'in." Amina don girman Allah ki kyale shi ki daina damun kanki wallahi nasan ko ya aureta da wuri gayyar za ta watse shiyasa ban damu ba. Ki daina damuwa haba Nabilan me bagidajiyar banza da wofi."
Murmushin takaici kawai na yi cikin raina na ce magana kam na bar ta shima na daina nuna masa damuwata a fili amma ina nan na kudire abu a raina.

Satinsa hud'u ya dawo a cikin kwanakin bai fi sau hud'u muka yi waya ba. Ya dawo a tsananin bukace lokacin ni kuma laulayi ya lafkar da ni domin abinda nake zargi ya tabbata ya kuma bayyana kansa domin mai azaba ne da son kad'aici na tsiri zaman d'aki da rashin son hayaniya da k'unci. Sai masifar son abinda ya danganci yaji da manja. Koda ya tabbatar da cewa ciki ne da ni ya yi murna sosai ya fito da farincikinsa kowa ya sheda hakan. Kuma ya rage takura mini a duk ranar girkina saboda ya fahimci ba ni son damu abin ma gabad'aya baya ba ni sha'awa. Sai ya zamana bai fi sau biyu yake kwanciya da ni a sati ba.
Laulayi sosai ya tisa ni a gaba har da su karin ruwa kusan sau uku. Anti Yagana ta ce mini za ta zo dubani domin da muka yi bidiyo call ta tsorata da ganin yadda na zabge. Na ce ta yi zamanta ba sai ta zo ba tunda itama tana tare da mai juna biyun Fadila tunda watan haihuwar ya tsaya a ka dawo da ita gida tunda ta fari ce. Hatta da Sahura ba ta san ina da ciki ba, itama anti Yagana yawan yin bidiyon call din da muke yi ne ta fahimta shine babu yadda na iya na gaya mata.
Wataran alhamis da yamma ina kwance a d'aki da busheshshiyar agwalima a bakina ina tsotsa wata masifa ta ciki gari na waye wa da bushshiyar agwalima nake farawa kafin nasa komai a cikina ina nan da su a bushe da yawa bata yanke mini tunda akai-akai nake aika Masa'udu ya sayo mini.
Kamalu ya kira ni a waya muka gaisa sosai cikin Kamala da nutsuwa na ji ya ce." Mama amma dai za ki zo walimar bude makarantar da Baba ya gina mini ko."
Da mamaki a tare da ni na ce." Makaranta kuma Kamalu yaushe aka yi hakan ai ban sani ba ."
Ya d'an yi murmushi kafin ya ce." Ai dama tun da na ji ba ki yi magana ba na ce wata'kila ba ki sani ba. Mama Baba ne ya gina mini babbar makarantar islamiyya da massalaci a hade anan unguwar Kadawa gobe Juma'a in sha Allahu za a yi bikin bud'ewa."
Na yi shiru ina mamaki ko da wasa bai ta'ba gaya mini ba, nasan dai da maganar tafiyarsa Kano gobe amma bai ce mini ga dalili ba
Na ce " wallahi ban sani ba Kamalu don bai gaya mini ba, na ta ya ka murna sosai kuma na yi addu'a Ubangiji Allah Ya yi maka jagoranci
Ya amsa cikin jin dadi ya cigaba da cewa." Ai yana jin dadin irin yadda yake ganin bidiyona yana yawo a kafafan sadarwa. Ya ce mini har wasu daga cikin abokanansa suna tura masa tare da taya shi murna. Da ya tambayeni menene burina a duniya na gaya masa makaranta islamiyya da massalacin da zan cigaba da yad'a da'awata da sauran koyarwar addinin musulunci."
Na gyad'a kaina ina mamaki duk yadda aka yi hakan ban sani ba na ce." Da yake ni social media bata dame ni ba yanzu kuma dai ba'a ta'ba gaya mini ga wani bidiyonka ba. Kwanaki can dai Sahura ta ce mini Maigidanta ya ganka tare da wannan malamin shaik ma'kari a lokacin da ya zo gaisuwar ta'aziyya. Daga sannan dai ban sake jin wani labari ba."
Ya ce." Mama ai adduarki ta kar'bu alhamdulillahi. Mutane sun fara kar'bar abinda muke yi kuma suna mubayaa sannu a hankali za mu fara shiga kauyika domin wattanin da suka shige mun yi wa shaik Abdullahi G kaya rakiya zuwa gombe can wani kauye da arna suka yawaita wallahi ni kaina mama na musuluntar da mutum sama da ashirin a kauyen."
Cike da farinciki na ce." Alhamdulillahi! lallai kana tare da nasara da d'aukaka Kamalu ka dage ka yi aiki tukuru ka kuma kula sosai kada ka shiga rigar da ba taka ba. Kada na ji ana fad'a da kai akan addini. Ka yi iya yinka kamar yadda annabin rahama ya fad'a shiriya ta Allah ce."
Ya ce." In sha Allahu rabbi Mama zan kula sosai kuma yanzu zan turo miki irin bidiyon da nake yi ina sanyawa a shafukana na social media YouTube fecebook TikTok Instagram Whasap."
Na ce." To ka turo mini na k'alla, Ubangiji Allah Ya sanya albarka Kamalu Allah Ya sa kafi haka."
Ya amsa da "Amin Ya Allah "
Na tashi zaune sosai a lokacin da ya turo mini tarin bidiyos din ta whasap na dinga bud'ewa ina kalla. Na farko yana koya yadda ake yin alwala na biyu yana koya yadda ake yin temama ga matafiya. Na uku yana koya yadda ake wankan janaba dana haila. Na uku yana koya yadda ake yin sallah tun daga kabbara tsayuwa ruku'u sujjada zaman tahiyya. Na dinga maimaita kallon bidiyos din hawaye suna silalowa a kuncina. Ni kaina na rasa hawayen menene na farinciki ne. Kamalu na ya zama gwani ya zama alarama kur'ani izifi sittin akan shi da ka yake d'auko aya ya dire ta. Na daga hannu sama ina kuka ina fad'in."Allah na gode maka, lallai kai ne masananin abinda yake boye. Na gode maka da ba ka sanya ni kaucewa hanya akan wannan bawa naka ba. Allah Yadda ka shirya mini yarona Kamalu ina ro'konka ka shirya sauran yaran al'ummarka."

Na so a ce a ranar girkina na yi wa maigidan godiya ta mussaman domin duk abinda nake ji a zuciyata game dashi ya yi abinda lallai dole a yaba masa. Ko bai fad'a ba duniya ta sheda hakan ba yayin kyautar fariya ko ta ganin ido. A baka hannun hagu bai san an bayar ba. Ka zo yau a yi maka gobe ma ka dawo a yi maka ba za a ce an baka jiya ba. Baya ta'ba alheri ya fad'a sai dai duniya ta fad'a.
Washe gari da safe dana daidaici Hauwa ta sauko daga saman tunda dama koda ba ni da girki na kan hau mu gaisa Wani sa'in ko shi ya biyo ni d'aki. Sai da laulayin nan ya tsananta ne ya sanya ni b'akincikin hawa saman nasa domin idan na kalleshi haka kawai sai na ji haushinsa ya kamani. Duk kuwa da kokarin lallabani da yake yi gudun kada cikin ya samu matsala ya zube kamar na baya. Baya yi mini abinda zai ba ni haushi duk abinda na ce ba na so zai bari duk son sa da ya kusance ni idan na nuna a a sai kawai ya ha'kura ya shiga wata sabgar shiyasa ganina da sassafe ya ba shi mamaki ya shirya tsaf cikin manyan kaya har da nad'i a saman jar darar da take kansa ya yi kyau ainun cikin shadda wagambari mai kalar sararin samaniya babbar rigar tasha aiki kafafunshi sanye da ba'kar safa yayin da takalmansa sahu ciki suke gefe sai kyalli suke yi. Gabad'aya d'akin ya game da kamshin turaransa wanda ya riga ya gama zaunawa a jikinsa. Na kàrasa a nutse na zauna a gefansa. Ya dinga kallona kamar ya ga sabuwar hallita ya ma kasa d'aura agogon da yake hannunsa kawai ya 'kura mini idanuwansa da suke cike da tambayoyi.
[12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: *123*
Agogon da yake ri'ke a hannunsa na kar'ba na ri'ke tsintsinyar hannunsa na dama wanda anan na lura yake daura a gogo na fara daura masa a tsanake zuciyata na kara yin sanyi da lamarinsa. Tabbas na yarda d'an adam tara yake bai cika goma ba. Kuma ko na'ki ko na so wannan mutumin tarin alheransa sun rinjayi sharrinsa ya yawa. Domin da wahala na ji suka da zambu a kansa ta ko'ina sai yabo da fatan alheri. Bai ce mini komai ba har na gama daura masa agogon yana kallona na kai hannun bakina na sumbuta kafin na dube shi fuskata a sake na ce." Barka da asubahi Babanmu."
Yana k'ayatattacen murmushi ya amsa da "Barkanmu dai Aminatu my princess." Na dariya kawai ina kallonsa kafin na gyada kaina na ce." Da gaske?"
Ya ce." Kwarai kuwa ai babu wata sarauniya a birnin zuciyata sai ke." Ban ce komai ba kawai na ri'ke hannunsa tare da had'e yatsunmu wuri d'aya.
Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya yana kallona ya ce." Amma ni ba babanki ba ne Amina, kin manta ni duniyarki ne fa, ni ne mai k'urewa jin dadinki lamba mai yasa za ki kira ni da baba."
Na danne kunyar da ta taso mini na dube shi da 'yar dariya na ce." Na rasa da wane suna ka dace ina ganin kiranka da Baba shine karshen mutuntawa."
Yana murmushi ya dubi agogon dana daura masa ya gyada kansa yana fad'in." Yau ni dake kamar wasu sabbin masoya, kina so ki shagaltar da ni, jirginmu ya kusa tashi bakwai da minti goma yanzu takwas daidai za mu tashi in sha Allahu kuma yau zan dawo sai mu kàrasa soyayyar don na ga alama addu'ata ce ta kar'bu a kanki."
Na dube shi a hankali haka kawai sai wani tausayinsa ya rufe ni, wai aka ce sai da so ake kishi da tausayi to amma in ba haka ba ai wannan mutumin ba abin tausayi ba ne, mutumin da Allah ya wadata da suttura da jin dadi na gidan duniya.
Hannuna na kai fuskarsa ina dan jan gemunsa da ya yi 2colors fari da baki ya kwanta sosai ya kuma k'awata masa fuskarsa. Na furta." Ka yi kyau sosai, kamar ango."
Ya kanne idonsa yana fad'in." Shine ai ba ki ga na yi gayu ba."
Murmushi na yi tare da fad'in." Haba da Nabilan kenan?"
Ya daga kansa yana kallon yanayina. Na ce." Mai yasa ka boye mini abinda lallai kasan ba zai 'boyu ba."
Ya yi jim yana kallona, sai na girgiza kaina ina ko'karin mayar da k'wallar da take ko'karin zubowa na furta." Jiya Kamalu ya kira ni a waya ya gaya mini abinda ka 'boye mini. Ba ni da bakin godiya Baba, Allah Ya saka da alheri, Ubangiji Allah yadda ka dubi marayun yaran nan ina ro'kon Allah Ya dubi naka abinda ka yi na alheri Allah Ya sanya maka a mizani, na gode na god....! Ban kàrasa ba kukan da nake dannewa ya kufce. Da saurin gaske ya janyo ni jikinsa ya rike ni sosai yana d'an dukan bayana a hankali cikin sigar rarrashi yake fad'in."Daina kuka Amina, ai bake na yi wa ba kaina na taimaka, bakin san da cewa hakkin yaranki a kaina yake ba ai a musulce ni ubansu ne tunda ina auranki, babu buk'atar godiya a tsakaninmu. Yaranki da wani namijin ki ajiye a ranki kamar da ni ne, ai Aminu Salihi da k'arfi da lafiyarsa muka hadu muka nemi dukiyar tare don haka don na sake yin wani abu akan yaran nan ki ce za ki yi mini godiya ko ki yi kuka ni ma na sauke hakki ne, na kuma gode da kyawawan addu'oinki, Allah Ya shirya mini ku bakidaya.
Ri'ke shi na yi sosai a ajikina ina sauke ajiyar zuciya amma hawayen dake zuba daga idona sun kasa tsayuwa.
Ya dago ni yana duban fuskata ya sanya tafin hannunsa yana goge mini a d'an sanyaye ya furta." Ya isa na ce, ki yi shiru humm!, yawwa ko kefa, ki yi mini murmushi nan kin ji tawan"
Murmushi na yi irin mai tafe da kuka na sake rungume shi a jikina kam kukan da k'arfi ya k'wace mini.
Ya diririce sosai yana ta jijjigani "Menene haka Amina na gaya miki akwai abinda yake gabana, kukan na menene haka?"
Na dago kaina Ina kallonsa cikin kukan na ce." Don Allah ka yi hakuri da abinda na dinga yi maka ka ji."
Ya ce." Ni ba ki yi mini komai ba kuma ban ta'ba rikonki ba, ai ni ne zan ce ku yafe mini."
Na ce." Mune dai za ka yafe wa tunda aljannar mu tana kasan kafafunka don Allah ni ma koda na mutu ka dinga yabona kana fad'in alherina irin na Momi."
Ya b'ata rai yana fad'in." Me ya kawo zancen mutuwa kuma?"
Na yi shiru ban ce komai ba domin ni ma jin maganar kawai na yi ta fito daga bakina.
Ya tashi yana gyara babbar rigarsa ni ma na tashi Ina kallonsa yanayinsa ya canza. Na ce." Ka na son ka auri Nabila ko?"
Wani irin duba ya yi mini kafin ya gyada kansa ya mik'a hannu ya debi wayoyinsa dake zube a gadon ya kama hanya zai fita.
Na bi shi da sauri Ina fad'in." Ka tsaya ka ji."
Ya ja ya tsaya yana dan hararata kafin ya ce." Ke ba a fara magana dake a kare lafiya Amina, wanene ya sako Nabila a cikin maganar mu?"
Na ce." Dama zan ce ne na amince idan kana sonta ka aureta wallahi."
A hanzarce ya furta." Ai dama can ku ba ku isa ku hana ni auranta ba idan ina da ra'ayi. Nabila ta bi ta hanyoyi da yawa domin kamun kafa ta had'a kai da su Salim ta nemi Hajiya Ayya mahaifiyar abokina Alhaji Amadu duk akan tana so ta maye gurbin 'yar uwarta na ce a a saboda wasu dalilina. Ba wai tsoronku ne ya hana ni auranta ba."
A sanyaye na ce." To shikkenan, Allah Ya bata wani."
Ya amsa da "Amin yana ko'karin bud'e 'kofar d'akin
Tare muka sauka kasa wanda ya yi daidai da fitowar Hauwa daga dakinta cikin shiri. Ganinsa a shirye da shirin tafiya ya sanya ta ce." Da gaske dai ba za ka yi breakfast din ba kenan?"
Ya ce." Idan na je gidan Hajja sai na yi na gode da kokarinki."
Daga haka sai ya nufi kofar fita a d'an gurguje. Muka had'a baki wurin fad'in." Allah Ya tsare hanya a gaishe da Hajja." Ba tare da ya juyo ba ya amsa da "Za ta ji in sha Allahu rabbi."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.