Complete Hausa Novels

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel

Reading file: Gudun Aure Part 5 Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 34

"Mai ya yi maka kuma?" Na tambayeshi jikina sanyi kalau domin kuwa wani yanayi na shiga na tsananin tausayin yaron ba komai ne ya janyo hakan ba sai maraici da rashi domin kuwa duk abinda Salim yake yi yana yi ne domin ya ga a cikin rigar arziki sa yake.

"Salim tare da abokansa suke yi mini dariya har na ji daya daga cikinsu yana kirana da 'kolo, dayan kuma yana cewa mini criminal." Sai hawaye suka fara kasa tsare a kumatunansa.

Zuba masa ido na yi Ina kallo a yayin da hawayen ke ta zarya a dakalin fuskarsa bai goge ba, ni ma kuma ban ce masa ya yi shiru ba sanin da na yi cewar kukan shine zai sassauta masa takaicin abinda aka yi masa.
Idan an kira shi da 'kolo ai ba damuwa ba ne, ni na ji dad'i ma da ya zama 'kolon mahaddaci kuma marubucin al'kur'ani. Kalmar criminal din ce ta hargitsa dukkanin lissafina, Salim abin har ya kai haka. Abinda ya faru shekaru kusan shida yaro ya samu nutsuwa ya zama mutum shine yanzu za a tayar da shi.
Cikin jan ajiyar zuciya ya ce." Mama Salim na b'akinciki da yadda Allah ya yi mini jama'a a area nan, sannan yana kishi sosai ya ga na bude massalaci manya mutane na bina sallah suna gaisawa da ni. Wannan na ji da kunnena yana fad'in duk wanda ya bi b'arawo sallah shi ma bashi da maraba da 'barawo, Mama yaushe wannan sunan zai goge a tarihin kuruciyata."
Na ji kwalla ta ciko mini ido. Na daure ban yadda ta zuba ba, na ce." To share hawayenka ka daina kuka ka ajiye abinda yake faruwa a matsayin cigaba, domin kuwa haka siddin ba zaka cimma wata nasara ba tare da kalubale ba. Ita hassadar ai itace matakin komai. Kada ma ka damu, kuma ina mai tabbatar maka da cewa watarana Salim zai bi ka salla, zai kuma nemi fatawa a wurinka, wannan ni ce na gaya maka, domin kuwa Ina nan ina roka maka d'aukaka da shura ta fanninin addini anan gidan duniya, Kamalu idan Allah Ya yarda duniya da mutanan dake cikinta za su amfana da kai."
Hannu yasa ya goge hawayen dake zuba a kumatunsa. Na ce." Ka kyale mini komai a hannuna, ka ji ko ka cigaba da hakuri, ni kaina a wannan ga'bar ba zan ha'kura ba dole a yi wani abu kai, amma kada ka nunawa Momi komai, ka bar abin a zuciyarka."
A sanyaye ya ce." Shikkenan Mama, zan yi yadda ki ka ce din, amma ni ina so na koma can kano zan fi samu nutsuwa cigaba da gudanar da neman ilimina."
Na ce." Idan har hakan shine alheri za ka koma Kamalu, ka cigaba da addu'a ka kuma bar maganar tsakanina da kai."

To a daran na nemi maigidan a waya duk da nasan ba sosai yake amsa waya da daddare ba amma yadda nake jin zuciyata ba zan iya bari sai gari ya waye ba. Wayar ta katse bai daga ba sai na yi masa text na cewa Ina son magana dashi yanzu.
Wajan goma da rabi ya kira ni da kansa. Na daga muka gaisa a nutse.
Na ce." Baba ina son magana da kai amma kada ka juya mini don girman Allah da Annabi ka dubeta ta fuskar hankali da maslaha."

A nutse ya ce." To ina jinki ai ni mai hankali ne ba mahaukaci ba, kada dai ki ce mini kin yi 'bari domin kwana biyun nan mafarkai nake yi marasa kan gado, Ina ganin ma farkon watan nan za mu zo."
Na ce." Ban yi 'bari ba, amma ka sani cewa ni da kai ba mu da ikon komai akan abinda Allah Ya zartar. Idan har kaddara ta gifta cikin ya samu matsala ba za ka d'auki kaddara ba kenan?"
Ya ce." Zan d'auka mana, ai mafarkan da nake yi ne ya sanya ki ka ji na yi miki wannan maganar. Na tuba ga Allah duk yadda ya yi daidai ne."

Shiru na yi Ina sauraransa har ya gama maganganunsa. Na ce dalili ne mai karfi ya sanya ni kiranka a daran nan, kuma ni kaina zan ji dadin zuwanka domin ka gyara abinda yake faruwa Kamalu ne da Salim....... Duk abinda yake faruwa na zayyane masa. Ya jima yana nanata maganar da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Yaushe Salim ya lalace haka, kuma abu ya faru tunda kuruciya saboda rashin hankali ka tara abokai kana gaya musu criminal?" Ya sake maimaita kalmar tabbacin hakan ya bashi mamaki.
Na ce." Kamalu ya ce zai koma kano da zama can wurin Hamusu."
Gyaran murya ya yi tare da cewa." Wannan kuma abinda yake cikin ranki ne shekara da shekaru shine ki ka samu mafaka dalilin wannan matsalar. Na gaya miki Amina idan har Kamalu zamansa zai koma kano to Yusi ma zai bi shi. Nusaiba da Salim Adam amana ne a hannuna. Haka zalika tunda Ina auranki yaranki ma amana ne a hannuna koda ubansu yana raye to balle kuma baya raye. Idan har kina ganin za ki yi iko da abinki ni ban iya ba sai na ce Allah Ya taimaka."
Na ce." To yanzu ya kake so a yi? Kasan dai cigaba da zaman Kamalu a gidan Momi akwai matsala watarana za su iya yin abinda bai da ce ba."
"Babu abinda zai faru, ki kyaleni da yaran dukkaninsu tunda kin gaya mini kin gama aikinki."
Jiki babu karsashi na ce." Shikkenan sai da safe." Sai kawai na kashe wayar domin kuwa jikina yana ba ni kamar ba zai d'auki tsatstsauran mataki ba.
Da lamarin na kwana na kuma wayi gari dashi dalilin da sanya kenan na kasa barin abin iyakacinmu. Na kira anti Yagana na gaya mata halin da ake ciki. Sosai kuwa ranta ya 'baci ta dinga fad'a tana cewa babu lallai babu dole muddin da cin zarafi da cin mutuncin da kuma tozarci Kamal dole ya bar gidan. Arziki ai ba hauka ba ne.
Na ce." Anti Yagana tun farko fa ni dama abinda na guda kenan, shiyasa da matar nan ta bukaci zaman Kamalu a wurinta na dinga gocewa. Karin abin kuma maigidan ya'ki ya fahimceni, wai muddin Kamalu zai bar gidan sai dai su tafi da Yusi wanda na tabbatar da cewar hakan matsala ce babba. Da ya zauna mun yi magana da fahimta tuntuni da tun farko wannan matsalar bata kunno kai ba. Abu na biyu kuma ga yanayin bayanin da Kamalu ya yi mini yadda na fahimta shine shi Salim yana adawa da yadda Allah ya d'aukaka Kamalu fiye dashi, ai nasan yaron yana da kirki tun kafin ya tafi karatu dawowarsa al'amura suka lalace kishi ne shi mai yasa Allah bai yi masa ba."
Ta ce." Wannan kuma Ubangiji zai kalubalanta. Wace irin wahala da gwagwarmaya ce Kamalu bai sha ba. Yanzu kuma Ubangiji Allah Ya d'aukaka darajarsa wannan duka ba dabararmu ba ce ikonsa nd, gaskiya a wannan ga'bar ni ma bana goyan bayan mijinki Kamalu dole ya tafi ya bar musu gidansu idan sun ce ba haka ba sai ya dawo hannunki shine karshen magana.

Na ce." Anti Yagana ni na fi so fa ya koma kanon ko ya dawo nan wurinku hankalina zai fi kwanciya gaskiya, domin ai ko yana gidana ba a kashe matsalar ba tunda duk lokacin da ya fita zai iya yin karo da Salim din kin ga matsalar ai bata mutu ba."
"To ni da kaina zan kira Yallabai din a waya na bashi shawara yadda za a yi.
Jin haka ya sanya na ce." Kada ki kira shi yanzu anti Yagana mu bari ya zo mu ga hukuncin da zai yanke idan babu adalci sai ki yi masa magana."
Ta ce." Shikkenan haka za a yi in sha Allah, na manta ma ban gaya miki ba shekaran jiya amaryar Babandi matar da ya aura ta uku ta haihu." A takaice na ce.'' A yi masa barka Allah Ya raya, domin ni yanzu ko lambarsa ma ba ni da ita yadda maigidan ya tsaneshi haka ya tsani mutuwarsa shiyasa na goge lambarsa daga wayata a gabad'aya duk domin a zauna lafiya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.