Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 10 of 21
Cigaba yayi da kallon sashin nata lokacin da zuciyar sa ke kitsa masa wataƙila ita ma wannan ɗin da aka liƙa masa , ta riga ta gama sayar da nata mutuncin a waje ,
ya dangana kome da ya faru a matsayin hakkin baiwar Allah yakaka da ya É—auka , ya jagorance ta suka aikata mummunan laifi , shi daman Alhaki ai kuikuyo ne .!
*****
Asubar fari ya hau shiri , garin baki É—aya yayi masa wari , so yake ya tafi , yana son zuwa ya ga mama yasan ganin fuskar ta ne kaÉ—ai zai iya sassauta masa zafin da ran sa ke yi ,
Daga sashin sa kai tsaye cikin gida ya tasamma sashin hajiya umma ba tare da ya dubi sashin kowaccen su ba tsakanin sashin gimbiya maimouna da tun barin sa da yayi cikin dare da sashin siyama wacce bai ko kai da sanin launin kayan da suke cibge a ciki ba ,
Yana ratsa sararik gidan yana amsa gaisuwar bayu da hadiman da suke kai kawo suna gyaran gidan da sanyin safiyar .
A falo na ciki ya tadda hajiya umma tana Azkar , gefen ta ɗan ƙaramin tire ne da aka jera gorar ruwa da ƴan kofunan gilashi ,
Tana ganin sa farin ciki ya bayyana kan sa bisa fuskar ta , cikar haiba da mutuntukar da ta hango tare da shi ya sa ya yi mata ƙwarjini a yau , tabbas aure cikamakin addini ne , cikin sa akwai martaba tare da girma me yawa ,
Gaishe ta yayi sai dai saɓanin da da yake shigewa kusa da jikin ta , yau ɗin tanƙwashe kafafun sa yayi a gaba kaɗan da ita ya sunkuyar da kan sa ,
Kallon tsanaki tayi masa ba sai ya faɗa mata ba ta san yana tare da damuwa me girma wanda a jiya kafin rabuwar su da yamma babu wannan damuwar a tare da shi , dan haka take hasashen ko menene damuwar sa tana da alaƙa da iyalan sa , ita kuma bata da burin zama ɗaya daga cikin iyayen da suke bincikar rayuwar gidan auren ƴaƴan su dan haka sai ta yi kamar bata ga damuwar ta sa ba , ta matsa zuciyar ta da ke son sanin meye ya same shi ?
Yaya kwanan ɗiya na su dukkanin su da fatan kun tashi lafiya ? Basu da buƙatar wani abu ?
Duk kowa lafiya umma na basu buƙatar kome ,
 Umma zan tafi bakin aiki doumin an ƙira ni daga niamey bisa ga wani aiki na gouggawa da ya taso ,
Aiki ? Ba an baka houtu ba na tsawon sati gouda ?
Umma aikin mu na kare rayuka da dukiyoyin al'umma ne koyaushe ana iya ƙiran mu kuma a kowanne yanayi da lokaci , !
Shiru tayi tana nazarin sa , kafin ta jefo masa tambayar da ta sanya shi É—ago kai
Tare da siyama zaku tafi kou ?
Shiru yayi kafin ya tattaro ƙarfin halin da ya yi masa saura
   Niamey zan tafi ba dosso ba Umma , idan na dawo daga niamey zamu tafi dosso tare.
bata jaa ba tayi masa addu'o'i kamar yadda ta saba tare da ƴan nasihohi , ƙarshe ta sake tunasar da shi girman nawin da ke kan sa a yanzu , !
****
Tunda ya hau kujerar zaman sa a jirgin da zai É—aga da shi zuwa niamey ya zurfafa cikin tunani daki-daki ,
Da hantsi ya samu isa ƙofar gidan , kan layin shiru , da yake unguwar babu yawan mutane , ya cire ƙuɗin me taxi ya biya shi , ƙarasawa yayi jikin ƙofar gidan ya ƙwanƙwasa
Hajja wacce take tsakiyar sharar ƴar harabar gidan ta saurara da kyau ta tabbatar cewa gidan nasu ake bugu , ta ajiye tsintsiyar ta ƙaraso jikin ƙofar ta tambaya wanene ??
Hajja ni ne ,
  Ta shaida muryar sa dan haka ta zare sakatar ƙofar ya samu shigowa gidan , sai fara'a take masa tana lale marhabin da shi ,
  Shiga ciki Babban soja bari na ƙarasa ture ɗan wajen nan zan zo mu gaisa , sannu ka sha doguwar tafiye ince kwana kayi a hanya ?
Murmushi yayi ba tare da ya amsa mata ba ya sanya kai cikin gidan ,
Ƙiiii
  Ƙarar turo ƙofar sa ta sanya ta ɗago kan ta ta dubi sashin da ta ji motsi ,
  Hajja sannu da aiki !
Tace cikin Æ´ar muryar ta ,
Bai amsa ba saboda baki ɗaya hankalin sa da idanun sa na ga fuskar mama wacce take jingine da jikin falmata akan cinyar ta , su duk biyun suna fuskantar ,
Taku ya fara yi yana jin yadda shauƙin son ta ke ɗibar shi , da sassarfa ya ƙarasa gaban su ya tsugunna gami da kai hannun sa ya kama ƴan kafafun ta da suke sanye da ƴar safa ya sunkuyo da fuskar sa ya sumbata yana me rufe idanun sa da jin yadda ƙaunar ta ke sake ratsa shi tare da wata nutsuwa ta musamman , me yake ƙauna irin ta tsakanin ɗa da iyaye ƙarfi tare da tsafta ??.
Lokacin da ya É—ago kan sa falmata ta kawo hannunwan ta duk biyu ta É—ora akan fuskar sa , a hankali tayi yawo da hannuwan ta tana shafar fuskar sa da idanun sa ke rufe ,
Tamkar wuta ta jaa ta ta janye hannuwan ta da sauri , tana É—auke mama ta É—ora kan kafaÉ—ar ta ,
 Da farko tayi zaton hajja ce ta shigo, sanin cewa daga ita sai hajja a gidan .
Wa-waye ne ? Tace tana ƙoƙarin miƙewa ,
 Â
  Koma ki zauna Fatima ni ne ,
Ya kai hannu yana ƙoƙarin karɓar mama ,
Ta gane muryar sa dan haka ta sakar masa mama a hankali , tana dai-daita numfashin ta da firgici ya sa shi hargitsewa ,
Yana karɓar ta yayi mazauni akan ɗaya daga cikin kujerun wajen ba tare da ya janye idanun sa daga kan ta ba ya shiga sumbatar kumatu zuwa goshin ta ,
Bai ko ji gaisuwar da falmata wacce ta zauna daga ƙasa a gefe take yi masa ba ,
  ita ma shiru tayi ganin bai amsa ba
Shigowar hajja ya sanya shi rungume mama a jikin sa suna gaisawa shi da hajja ,
   Soja garin nan na ku kuwa ya karɓe ka , ka ga yadda kayi fes da kai kana ƙyallin fuska sai ka ce sabon ango ? Ah lalle miyar umma da zaƙi ta sa kayi shar da kai duk wannan hautsinewar sojin sun kau , ke Fatima kin kuwa gaishe da maigidan naki ??
Na gaishe shi hajja ,
To ban ga kin kawo masa ruwa ba , ?
Zata miƙe ya dakatar da ita ƙyale ta hajja ita da take da larura baza ta iya aike ba !
Ƴar dariya hajja tayi
Zata iya Babban soja ai matar ta ka ba dama akwai lura da kaifin ƙwaƙwalwa saurin gane waje ne da ita , ka ga dai ba mu rufa wata guda ba a gidan nan amma ta haddace kusan muhallin kome da kome da yake cikin gidan nan ,
ita da kan ta take zuwa ta É—au ruwa a firiza ko ta je kitchen ta haÉ—a madarar mama , kullum addu'a nake mata Allah shi kawo mata waraka .
ÆŠan murmushi yayi yana duban falmata wacce ta koma ta zauna ta juyar da kan ta gefe ,
Kalaman hajja sun tuno masa da abunda ya so mantawa , watau kai falmata asibiti tare da samar mata gurbin karatu ,
Ya zama dole yayi duk wani abunda zai iya yi gurin kyautata rayuwar falmata ko domin ya samu girman laifin sa ya ragu a wajen Allah .
Hajja ku shirya zamou tafi babban hospitalisé a duba lafiyar idanun fatima yanzu. !
  To to yanzu kuwa , falmata tashi ki shirya bari nima na ɗan kintsa , !
Niamey national hospitalisé nan suka je , inda basu wani ɗau dogon lokaci ba suka ga ƙwararren ophthalmologist , bayan haske-hasken da tarin tambayoyin da yayi mata akan idanun nata , a ɗakin gwaje-gwaje .
Suka dawo ofishin sa inda youssouf ke jiran su , bayani ya soma yi masa daki-daki
A sakamakon binciken da nayi a zahiri ban hango wata cuta ba a idanun nata sai dai raunin ƙwayar idanun nata watau ainahin jijiyoyin idanun suna da rauni , a tambayoyin da nayi mata nayi ƙoƙarin sanin tayaya ta fara samun rashin gani ko da shi aka haife ta ? amma sai ta shaida min bata da masaniya akan mafarin samuwar rashin gsnin ta ,
A takaice cikin binciken da muka gudanar da kuma sakamakon amsoshin da ta bayar yayin yi mata gwaji da akwai yiyuwar dawowar wani kaso daga cikin ganin ta idan har za'a samu ƙwararrun kayayyakin aikin da zasu taimaka wajen dawo da ganin nata ,
Sai dai a halin yanzu bamu da waɗannan kayayyakin a nan gida niger da sauran ƙasashe masu tasowa , sai a manyan ƙasashen duniya da suka yi fice wajen samun ingantattun asibitoci masu isasssun kayayyakin aiki tare da ƙwararrun likitoci ,
Dan haka a yanzu abunda zamu iya yi mata kaɗai shine zamu bata magungunan da zasu iya taimakawa wajen bada kariya ga idanun nata daga kamuwa da wasu cututtukan da zasu iya kassara sauran ƙarfin jijiyar idanun da kuma hana idanun yin ciwo ƙaiƙayi da zubar ruwa ,
  Da fatan kun fahimce ni ?
Mun fahimta Doctor mun goude zamu dawou gare ka idan buƙatar neman taimakou game da asibitin da ya kamata a kai ta a wata ƙasar ya tasou mun goude ƙwarai Madallah .
Washegarin ranar Biyamuradi bai zauna ba , ya shiga binciken makarantar makafi me kyau da yake son ya kai falmata ta fara karatu kafin lokacin da zai sake yunƙuri me ƙarfi akan lafiyar idanun nata a karo na biyu .
Association Nationale Pour la promotion des aveuglés , nan ne inda ya ji gamsuwar sa akan ya kai falmata nan ta fara ɗaukar darasi , wacce jibiya ce ta koyar da makafi tare da basu tallafi me tushe daga ƙasar amurka , da ta tanadi ƙwararrun malaman makafi ,
Cikin sati guda yayi mata rajista da duk wasu abubuwan da ya kamata , ya samar mata da direba bayan ya sa an kawo masa ɗaya daga cikin motocin sa da suke maradi ya danƙa makullin ga hajja wacce take cike da farin cikin wannan cigaba da falmata zata samu a rayuwa .
Ranar da zai bar garin zuwa bakin aikin sa jahar dosso , ya yi musu sayayyar kayan abinci da abubuwan da zasu iya buƙata tare da ƴar ƙaramar waya me sauƙin amfani ya ba wa hajja bayan ya zuba mata lambobin sa a wayar ya adana ta su a ta shi wayar ,
Suna zaune a falo yana musu sallama akan yau zai koma bakin aikin sa , sai kuma zuwan ƙarshen wani watan zai komo
Godiya me tarin yawa hajja ta yi masa ,
  Ya amsa tare da waiwayawa sashin falmata da take ta faman lila mama akan ɗan lilon ta wanda baban ta ya sayo mata su tarkacen kayan wasan yara iri-iri har da wanda ya fi ƙarfin shekarun ta , tun daga kan lilon yara , kekunan koyon zama har zuwa ƴar mota ta yara da ƙananun kayan wasanni irin na ƴaƴan gata na sosai , bayan suturun da ya daɗa jibgo mata.
  Fatima baki da wata matsala kou ?
Shiru tayi tana É—an lila mama a hankali ,
 Falmata hala kin samu kurunta ? Kina jin Babban soja na magana kin yi shiru ? Uhum yau ni naga abunda ya shallake tunani na ,
   Babu kome kawai ina son unmh
  Uhum ina jin ki me kike so ??
A kaini makaranta
 Ai na sanya ki makaranta fatima sati me kamawa zaki fara zouwa ,!
Na islamiya ? Ina so a cigaba da koya min karatun addini ma ,!
Toh babu damouwa idan Allah ya yarda zan bincika a samu me koyar da ke na Islama ma ,
Akwai wata damouwa bayan wannan ?
Daman ka gaya musu zan dunga zuwa da mama makarantar ko ?
Babu inda zaki dunga goyon ta kina tafiya da ita anan waje na zaki dunga barin ta idan ya so kafin ki dawo na sauya ta , ko kuwa na gudu da ita, kina nufin baza ki maida hankali kan karatun naki bane ? Zaki dunga ɗaukar ta kina zuwa da ita makaranta ki ɓige da raino memakon karatu ni ke meyasa ana nuna miki hanya kina daɗa bauɗewa ne ??
Æata rai tayi ta É—auke kai
Murmushi youssouf yayi , shi dai rigimar hajja da falmata na ba shi dariyaÂ
Duba fatima ki bar mama a wajen hajja har ki tai école ki dawo Kin ji kou ? Ba'a tafiya da yara école.
Shiru tayi idanun ta na kawo ƙwalla ita dai bata ƙaunar abunda zai raba ta da mama ko na ƴan mintoci ne bare fa makaranta da awanni zata yi a can , kai anya zata iya , ?
To hajja mu dunga zuwa tare da ke mana makarantar ? Sai ki dunga riƙe min mama nayi karatun na fito ?
Ke raba ni da wannan gudun birin , gotai gotai da ni zani makarantar ? Yaushe rabon duniya da ayyaraye ? Babu inda za ni ke kaɗai zaki tafi makarantar ki ki dawo ki same ni ina nan , ilmin ai shine Babban gatan ki falmata kin ji ko ?
Naji hajja
Yauwa mutuniyar ai shiyasa nake son ki akwai ki da saurin fahimta ,
Sallama suka yi da youssouf yana sake yiwa hajja godiya me tarin yawa tare da ɗanka mata ƴan kuɗaɗe wanda da kyar hajjan ta yadda ta karɓa sai da yayi ta roƙon ta da Allah .
Daga nan Dosso yayiwa tsinke bai jin marmarin zuwa maraɗi duk da cewa fiye da kaso talatin na ɓacin ran sa game da sha'anin sa da gimbiya maimouna ya kau , domin har sun yi waya ma cikin kwanaki biyun .
 Â
Assalamu Alaikum kowa da kowa !
Da fatan kuna lafiya ?
Ina neman afuwar ku bisa jinkirin zuwan wannan shafin , hakan ya faru ne sakamakon tafiya da ni zuwa gida , ban samu zama ba ziyarar dangi da sauran Al'amuran yau da kullum .
Da fatan zaku cigaba da haƙuri da tsaikon da ake samu cikin ajizanci irin na ɗan Adam ?
Nagode
 Â
[9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
32
Bayan Shekaru Biyar
Lokaci baya jira sai dai a jira shi , ba'a masa shamaƙi a yayin wucewar sa , Lokaci gudu ne da shi fiye da saurin bugun zuciyar ɗan adam ,
Lokaci yayi juyi ya juya ya zo da sauyi ta mabanbantan fuskoki a rayuwar mutane a cikin tsawon shakaru biyar .
Yakaka tana ɗaya daga cikin mutanen da suka samu sauyi ta fuska me kyau tare da tarin nasarori daki-daki cikin rayuwar ta , wanda a yau ta kawo matakin kammala makarantar ta secondry wacce ta rayu tsawon shekaru biyar tana faɗi tashin neman ilmi a cikin ta , da jajircewar ta tare da nuna ƙwazo ya sa aka ɗaga ta aka mata tsallaken aji na shekara guda daga jss3 zuwa ss2.
Da hakan ya kawo kammaluwar karatun nata cikin shekaru biyar kachal .
Ta fito da sakamako mafi kyau da ya sanyata farin ciki ita da duk wasu makusantan ta musamma malama maryam da lubna waÉ—anda da jajircewar su cikin taimakon yakaka a harkar ilmin ta har ta kawo wannan matsayin .
Samy baby ma wacce ta tashi daga matsayin samy baby ta koma ,Hajiya samira ," ita ma ta taya yakaka farin cikin kammala karatun ta wanda duk wasu kuɗaɗen hidindimun karatun daga farkon sa har ƙarshen sa ya fito ne daga aljihun Alhaji Gali da har kawo yau suke liƙe a naniƙe da juna , bata da wata maraba da matar sa , kai har ma ta zarta matar sa ta aure iko da shi tare da samun kuɗaɗen hannun sa , Alhalin kuwa har yau da suke samun wajen shekaru takwas tare sun gaza yin aure ."illar bariki kenan ,!
Karo na uku yakaka ta ajiye ƴar madaidaiciyar taɓaryar hannun ta da take dakan fura da ita , ta murza tafin hannun ta da suka yi ruwan hoda hoda saboda dakan da basu saba yin irin sa ba ,
  Ta ɗago fuskar ta tana yamutsa ta ,
Ummi wallahi nagaji da dakan nan É—an Allah ummi a min sassauci ki yadda na tafi ko'ina ne cikin garin nan na nemo furar nan nayi sadakar nan da ita , Allah bazan iya yin fura da hannu na ba ,
Malama maryam wacce take zaune daga gefe akan kujerar tsakar gida tana karatun littafin Al'mauduat Al'kubra , ta É—an janye littafin daga fuskar ta
  Fuskar ta babu alamun wasa ta ce ,
  Sai fa kin daka furar nan yakaka kiyi sadaka da abunda kika sha wahala wajen samun sa yafi ɗaukaka darajar sadakar ki a wajen ubangiji , tsawon shekaru biyar kina faɗi tashin neman ilmin nan , a yanzu kin samu kin kai wata gaɓa me kauri ashe baza ki iya dakan fura kaɗai kiyi sadaka domin nuna godiya ga ubangijin ki ba ??
Jikin yakaka a sanyaye ta amsa
  Zan iya ummi ,
To maza kiyi sauri ki gama dan shabiyu ta kusa , kar har a sauƙo daga juma'ah baki gama ba kin ga kamata yayi a ce ki rabar da ita ga mabaratan da suke bakin masallacin juma'ar unguwar nan kin ji ko ?
 To ummi tace tana saɓar taɓaryar ta fara daka ,
  Lubna wacce take zaune a gefe kusa da ita kan ƴar darduma tana yankar ƙumba , ta ɗago kan ta fuskar ta da murmushi ta sanya hannu cikin faffaɗan kwanon silver da aka ajiye guntun dafaffiyar furar da ba'a kai ga daka ta ba , ta gutsuro wata ƙatuwa ta sake jefawa cikin turmin da yakaka ke daka ,
  Yauwa ƴar ummi yi maza ki daka, na ɗebo madara na fara damu ni ce ta farkon sanya Albarka a result ɗin nan kin sani ko ?
  Ummi kina ganin ta fa ? Tana ƙara min wata bayan na kusa gama dakan
 Lubna maza ajiye nails clipper nan ki karɓi dakan nan ki taya ta ,
  Ta furta hakan tana gyara zama gilashin idanun tana cigaba da karatun ta .
 Ummiii , dan Allah ni lokacin da nayi nawa dakan futar gama makarantar ta taya ni Haba ummi dan Allah,Â
 Wallahi na taya ki kin manta ranar ....
  Yanzu aikin samun ladan kuke yiwa haka ?
  To shikenan duk ku bari ni zan zo na ƙarba nayi tunda da alamu ku lada yayi muku yawan da ya sa har kuka fara gudun sa ,
 Da sauri lubna ta zaburo tana ƙoƙarin karɓe taɓaryar hannun yakaka ita kuma yakakar ta riƙe gam ta hana ta ,
 Dan Allah ki bar ni na taya ki kin ji sahiba ta.
  Tare da marairaice murya
 Naƙi ɗin , nima zan daka kaya na duk na mulmula na ɗau abuna a kai naje na rabar , kin ji sahiba ta .
Wayar lubna da ta É—au kiÉ—a ita ta raba musu gardama
  Cikin sauri lubna ta ɗau wayar ta ta yi hanyar falo tana satar kallon ummi wacce bata nuna alamun ta san duk abunda suke a wajen ,
 Yakaka ta bi bayan ta da kallo tana murmushi
Ta kai gaf da shiga falon ta É—aga murya tana cewa ,
  A gaishe min da yayan namu da kyau da kyau kin ji sahiba ta ?
Da gudu lubna ta ƙarasa shigewa falon tana dariyar jin kunyar ummi .
Ƙarfe biyu dai-dai da idar da sallar juma'a yakaka da lubna sun kammala ɗaura fura guda uku uku a cikin farar leda tare da kindirmo me ɗan dama shima a ƙulle a leda daban , suka haɗa su suka zuba a ƴar bakar leda daban daban , ba laifi dayawa ,
Yakaka ta jaa hijabinta saka lokacin da ta gama saka socks ɗin ta a kafa ta zura hijabin tana kallon lubna wacce take ƙoƙarin ɗaura niƙaf ɗin ta ,
  Sahiba dan Allah muyi sauri kar mabuƙata su watse ,
  Taku biyu tayi ta ɗauko niƙab ɗin ta ruwan madara , mahaɗin hijabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa a fuskar ta ,
Da sauri lubna ta riƙe niƙaf ɗin ,
 Haba sahiba ta ? Ina mun yi cewa kin daina saka niƙab ɗin nan haka sai bayan kin yi aure ??
Hararar ta tayi
  Shiyasa na ga ai kema yanzu da za ki fita babu naƙib ɗin a fuskar ki , ni dan Allah sakar min mahaɗin kwalliya ta , cikamakon martaba ta ,na sanya abuna ,
  Amma ai ni kin san dai an riga an sanya rana , babu sauran wani ɗa namiji da zai sake cewa yana so na na kula shi ,
  Ok to maza yi min gorin aure sahiba ,
  Ta furta hakan muryar ta babu alamun wasa .
 A hankali ta sakar mata niƙab ɗin , Allah ya baki haƙuri sahiba ba manufata ba kenan . Mu tafi .
Yakaka wacce bata furta zancen da wata manufa ta daban ba daga cikin ran ta sai domin ta samu lubna ta sakar mata niƙab ɗin ta da take neman ƙarfi da yaji ta hana ta sawa a cewar ta shi yake hana samari kula yakakar tunda ba ganin fuskar ta suke ba , duk sai ta ji ta ba daɗi da ta ga kamar zancen ta ya sa aminiyar ta a damuwa .
Tafe suke akan hanyar su ta dawowa daga rabar da furar suna tafe suna hirar su hankali kwance irin ta shaƙiƙan ƙawayen da halin su da ra'ayoyin su suka zo ɗaya suke kuma ƙaunar juna domin Allah ,
Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon ,
Su biyun suka haÉ—a ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar ,
Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za'a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa ,
Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,
 Suleiman meye hakan kake kuma ?
Yace yana kai kallon sa gare shi ,
  Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,
 Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar ,
Da sauri suleiman ya fice daga motar ,
A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya ,
Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba ,
Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da Æ™warjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taÆ™i amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar saÂ
Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,
 Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su .
Dan Allah kayi hakuri,
tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu
Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama ,
Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra'ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari .
Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani .
Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya Æ™afa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa'ar haÉ—uwa da Æ™awar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta ,Â
na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta ,
Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi ,
A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba ,
To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha'awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba ,
Wuce su suka yi a hankali ,
Lokacin da suleiman ke bashi amsa
Hamza kenan kai dai na rasa wanne irin tabo mace tayi maka a duniya kake musu irin wannan kuɗin goro , duk kuwa da yadda safiyya take tarairayar ka tare da lelen ka kamar wani jariri sabon haihuwa , bana jin ta taɓa saɓa maka a rayuwar zaman auren ku .
Ya ƙarasa zancen tare da dariyar shaƙiyanci .
Murmushin takaici doctor hamza yayi ,
  Baza ka taɓa ganewa ba suleiman !
Ya maida ganin ga madubin motar sa , yana hango ta ta jikin madubin ƙwarai tafiyar ta ta ɗau hankalin sa , mace ɗaya ya taɓa gani da salon takun nan , wacce bai ko son giftawar tunanin ta cikin ran sa sai fa yau da ya sake ganin wata wacce fuskar ta take a rufe Bai kai ga ganin kamannin ta ba .
Yakaka ashe daman irin zaman da kike da ni kenan ??
 Cewar lubna idanun ta na bayyana ɓacin rai ,
A kaikaice yakaka ta dube ta , kin ga sahiba bana ciki da rigima , daga kawai mutum ...
 Hmm
 Lubna ta katse ta ,
Wallahi sahiba abu É—aya zan faÉ—a miki a matsayin ki na wacce na É—auka Æ´ar uwa ,
Kar ki yadda kiyi wasa da damar da ta zo miki , idan har wannan mutumin da gaske yake ki bashi dama ku fahimci juna , aka yi bincike bashi da wani aibu wallahi ki bada dama kuyi auren ku shekarun mu sun fara tafiya ishirin da biyu mun rufa ta da uku muke hari ,wallahi wasa ba namu bane dama kuma sau É—aya take zuwa a rayuwa ,
 Shiru yakaka tayi
Kalmar ,"Dama," na maimaituwa a cikin kan ta , ita har tana da wata dama da ta rage mata kuwa ? Ai damar guda ɗaya da take da ita ta riga ta zo ta wuce tun a shekarun baya , " damar da mahaluki ɗaya ya bata wanda ta tabbatar baza ta taɓa samun makamancin sa ba, bata yi amfani da damar ba a maimakon haka ma sai tayi masa mummunan sakamo da har yau idan ta tuno shi kunya tare da nadama basa ƙasa a guiwa wajen danne ta ,
ina ma ina ma ina ma ?? Da ace dama zata dawo mata ? Da ace zai sake ba ta dama ko da gutsire daga irin damar da ya bata a baya ? Wataƙila da ta gyara kuskuren ta ta wata fuskar ,
, abunda ta sani shi ɗin ya riga ya mata nisa ita ta zama wata shuɗaɗɗɗan lamari da ya taɓa giftawa cikin rayuwar sa ,
Bata da wani shauƙi ko tunani mai armashi akan wani ɗa namiji har yau ta gaza sake son wani ɗa namiji , " zata iya cewa ta ƙi maza ," ƙi irin na wanda kunama ta taɓa harbin sa babu shakka idan ya ga gizo-gizo kakkaɓe shi yake , dangantakar nesa nesa ce ke tsakanin ta da maza ,
shiyasa har yau ta gaza samun saurayi ɗaya tak , ita ce bata saurarar su bata bada fuska , take boye kan ta tare da killace surar ta daidai da fuskar ta a rufe take , ta zaɓi hakan , ta kuma fi son tayi tsarayuwar ta a haka ba tare da wani ɗa namiji ya sake ratsa rayuwar ta , burin ta ɗaya ne shine tayi ilmi kuma tana godiya ga Allah tana godewa malama maryam tare da addu'ar Allah saka da alkhairi ga baki ɗayan zuri'ar ta ,
Ko da ko kusa bata sahun malumma amma kai tsaye a yau ta wuce a ƙira ta da jahila , ta nemi ilmi tana kan nema kuma zata cigaba da nema har.....
  Har suka kawo gida bata cewa lubna ƙala ba ,
  Sai da suka shigo gidan ta ruga da ɗan gudun ta ta rungume malama maryam wacce take tsaye daga ƙofar kitchen tana amsa sallamar su .
 Ni bazan yi aure ba har sai nayi ilmi na zama kamar ummi malama ta , sai ki san yadda zaki yi da mutumin da kika ba wa phone number .
Murmushi ummi tayi ,
  Anya kuwa yakaka ? Aure ai shine cikar darajar ɗiya mace
Lubna wacce take zama akan kujera ta shiga bada labari tiryan tiryan tana yi tana hararar yakaka wacce take yanka musu cabbage da zasu ci abincin rana da shi .
Sosai malama maryam ta yiwa yakaka faɗa daga ƙarshe ta ƙarƙare da yi mata nasiha tare da faɗa mata fa'idojin aure da girman matsayin sa a addini .
Jikin yakaka yayi sanyi har idanun ta na tara ƙwalla , ta gaza cin abinci na kirki .
A ƙarshe ta jaa kunnen ta akan daga yau kar ta ƙara ƙin saurarar duk wani namijin da yake da kamala da ya nuna yana son ta , ta ƙoƙarta ta saurare shi na ɗan wani lokaci ta fahimci wanene shi , daga nan idan ta yarda da halayen sa na ƙwarai ta bashi dama ita ma tayi aure , ko kusa kar ta kawo aƙidar ƙin aure kusa da ran ta saboda wani shuɗaɗɗan dalili nata , .
A ladabce ta amsa mata da zata yi yadda ta faÉ—a mata .
Bata wani jima ba saboda yadda walwalar ta tayi ƙaura ta musu sallama tana barin gidan ƙarƙashin rakiyar lubna wacce duk ta damu da rashin walwalar ƙawar ta ta , sai faman jan ta da hirar raha take ,
Har ƙofar gida ta rako ta ,
Zata tura ƙofar gidan ta shige lubna ta riƙo hannun ta , ta waiwayo tana kallon ta da sakakkiyar fuska .
Sahiba idan baƙya son sa idan ya ƙira insha Allah zan faɗa masa dan Allah ki bar damuwa .
Murmushi yakaka tayi ,
  Ni dai ban ce miki ba , kawai ....shiru tayi ,
  Baza ki gane ba sahiba .
Zan gane dan Allah ki faÉ—a min meye ne ? Duk banji daÉ—i ba da naga ranki a jagule
Ni bana son kowanne É—a namiji ilmi me zurfi nake da burin yi saboda ina da mummunan rauni a zuciyata wanda jahilci ne ya assasa min ina so na samu ilmin da zai warkar min da ciwon da na ji akan jahilci ,
A hankali lubna ta gyaÉ—a kai tana sakin hannun ta ,
 na fahimta,
ta furta hakan ba domin ta fahimce ta da gasken ba , abunda ta daɗe da sani cewa yakaka tana da wani binannen ƙuduri wanda take dakon sa boye cikin ran ta da ita bata riga ta san wanne irin kuɗiri ne ba .
Daga cikin niƙab ta sake yin murmushi ,
  Sahiba sai gobe zan zo ki bani labarin yadda kuka yi da ,"direba,"
  Ta ƙarasa zancen da dariya cikin muryar ta , ko kafin lubna ta bata amsa wacce ta yamutsa fuska tare da ƙanƙance ido
 Ta shige gidan da ɗan gudun ta tana jin lokacin da lubna ke cewa daɗin abun ma direban jirgin sama ne .
Da sallama ta shiga falon duk da cewa tayi ne ba domin tana sanya ran za'a amsa mata ba sai dan sanin muhimmancin sallama a musulunci da ta riga tayi .
Kamar yadda ta zata kuwa daga samira har hamshaƙiyar ƙawar ta da take haƙimce akan kujerar falon babu wanda ya amsa sallamar ta , hirar su suke cigaba da yi da take cike da shewa da dararraki irin na yaran matan da suke juya duniya a tafin hannun su .
Rage tsawo tayi ta ɗan durƙusa ,
Anty samy sannu da hutawa ,
Ke ke yaks wanne irin iskanci ne wannan ?? So nawa zan faɗa miki bana son kina shigo min gida da wannan maya-mayan yadikan da kike yawo da su a jiki , musamman ma na fuskar nan taki kamar wata korarriya daga makka ? To na faɗa miki yau ce rana ta ƙarshe .
A hankali yakaka ta kai hannu ta kunce niƙab ɗin fuskar ta , lokacin da sofi take kai ganin ta kan ta ,
Kiyi hakuri anty na cire .
To ya dai fi miki , yo Allah na tuba na sanya wannan mayanin a fuskata ai ya shaƙe min numfashi ya sheƙa da ni barzahu ban shirya ba ,
Kallon kallo suka yi a tsakanin su , kafin sofi ta janye idanun ta tana yatsina fuskar da ya zama halittar ta ,
Kirjin yakaka yayi dakan lugude , tsawon shekaru biyar bai isa a ce ta manta fuskar sofi ba matar da ganin farko haɗuwar su ta fari ta ɗau karan tsana ta aza musu ita da ƙanwar ta falmata , dan haka cikin hanzari ta miƙe tare da haɗiye kalaman gaisuwar da tayi niyyar miƙa mata , ta juya tana nufar ɗakin ta .
Friend wannan wacece ? Aina kika samo ƴar ƙwara ? Ko dai ko dai .... Ta ƙarasa zancen tana sakin wata shashashar dariya .
Ɗan murmushi samy baby tayi cikin ran ta bata mamakin rashin gane yakaka da sofi ta yi , ko ita da kan ta bata gajiya da kallon yakaka , wata irin fata ce da ita wacce bayan haske tana ɗauke da wani irin taushi tare da ƙyalli a idanu , ya haɗu da gyara tare da jimaka me kyau da take samu daga ita samy baby , haɗi da girma tare da cikar macen da take kan ganiyar ƙuruciyar ta , sai ta zama tamkar farin wata idan ta gifta dole ta ɗau hankali , ɗan tsararren jikin ta da yake a murmure kowanne irin kaya ta sanya masa kyau yake .
Ai ba domin tirjiya da yakakar take gwada mata ba da tuni maƙudan kuɗaɗe sun fara shigo mata ta hanyar yaks , amma wani ɗan lokaci kaɗan take jira wanda zata kammala aiwatar da nufin ta , ta kuma fara kwasar adashen da ta dunga zubawa a dalilin ta ,
 Friend wannan wata haja ce da nayi tsintuwar ta a gari ,
  Kalaman samy baby suka zo daidai da zaman yakaka a bakin ɗan gadon ta , daga inda take tana iya jin muryoyin su ,
  Daɗi ta ji da samy baby bata jaa dogon bayani ta sanar da sofi ko ita ɗin wacece ba .
Taɓ kina nufin wanna ƙatotuwar budurwar kika bawa mafaka a gidan ki ? Ah lalle ,
 ta ƙuta
   Kawai dai dan ke ma ba miji ke gare ki ba , idan ba haka ba ina ke ina kawo annoba muhallin ki ?
  Ai ni tsakanina da ire-iren waɗannan matan masu kama da barbarar yanyawa ko gaisuwar kan titi babu ,
  Ai ko sama da ƙasa zasu haɗu bazan bar ido irin na yarinyar nan ya gauraya da na doctor na ba ,
  Wai Allah har bugun numfashi na ya fara sassarfa bala'i .
 Dariya samy baby ta kwashe da shi , daɗi na da ke freind akwai bala'in kishi ,
  Sha kurumin ki sanya ranki a sassanyar inuwa tunda har kika mallaki doctor hamza a matsayin miji ke da kan ki kin san naki ne ke kaɗai mutuniyar ,
  Wata sakaryar dariya sofi ta sake tare da ba wa samy hannun suka tafa .
Ni yanzu kin ƙi ki faɗa min sirrin friend wai tsakani da Allah wacce duniyar kika samu haka a Boston da har kika ajiye waɗannan manyan kayan haka ? Kin gan ki kuwa sofi cikin shekaru huɗu jal kin sauya ta jiki ,
ai wallahi wanda duk ya san ki a da da kike bulugari bazai gane ki ba a yanzu da kika koma wata katafila, ke ni anya kuwa doctor yana iya yin nisa da ke wannan irin abebaɗan more rayuwa da kika haɗa a jiki ahayye duniya gidan daɗi ɗan Allah ƙawata bani sirrin !
  Kalaman samy baby na kusa da ƙarshe ya sa fara'ar fuskar sofi raguwa ,
Cikin jimami tace ,
  Ai lamarin doctor ajiye shi gefe guda friend , kullum jiya iya yau ke wataran ma jiya ta fi yau ɗin domin ko yanzu kafin su kawo ni nan su ajiye baki ga yadda ya nemi min cin fuska a gaban abokin sa ba , akan sutura , wai kayan da na sa sun matse ni , bazan hau masa mota a haka ba sai dai na tafi na hau taxi shi babu abunda ya dame shi , ya dunga balbalin bala'i da daman ƙiris yake jira tun kafin mu baro US yake kumburi shi ɗaya uwa fulawar da yis yayi mata yawa, ina dai lallaɓa sa ne ,
Wallahi tsawon shekaru uku da muka yi a US da zan lissafa miki irin baƙin cikin bawan Allah nan da na ƙunsa sai kin ji tausayi na , gangar jikin sa kaɗai na mallaka , ruhin sa na wani waje wanda nake zaton ya min nisa duk kuwa ƙoƙarina akan kome nasa , ke dai kin san yadda daman aka yi auren nan namu , to duk da haka ban zauna ba malamai da bokayen yi nake na ƙarƙare miki ƙanƙat ɗin tsafi dai har india na je akan a min yadda zan yi na samu mazauni na dindin a gurin sa na amshi sararin zuciyar sa,
Zuwa na karnataka india ne ma fa da aka min wani mugumugun aiki aka min filla filla da tunanin sa na samu yake kula ni har muke iya haÉ—a shimfiÉ—a ,
A hakan ban zauna ba kullum ni ce a gyara saƙo da lungu na jikina tare da matso kyau , rana ɗaya na lura kamar
Yana son mace me manyan kaya , saboda bin wata mata da kallo da na ga yana ta yi a gidan cin abinci a boston , na dubi matar na ga idan banda himilin cinya da É—uwawu bata fi ni kome ba , tun daga ranar na shiga faÉ—i ta shi ganin yadda zan yi nima na ajiye manyan kayan nan ,
magungunan ɗago ɗuwaiwai da ƙara faɗin cinya babu irin wanda ban afa ba , amma da yake jikin nan nawa marke ne , shiru maƙatau bulunbuƙui , jiya iya yau , na kasa haƙuri na faɗa miki tare da jagorar wata ƴar * ƙawa da nayi a boston balarabiya ce ƴar duniya ta ƙarshen ƙarshe , ita ta kai ni aka min aiki me ƙanƙat ,
aka tatso tare da É—ago tudun bayan nan da kike gani , azaba babu irin wacce ban sha ba a lokacin aikin nan da bayan gama yin sa ,
amma na shanye , kuma babu shakka ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu , domin wasu cin kashin da yake min da yawan fushin sun ragu , duk da dai da farko ya tada ɓallin sai na faɗa masa me naje nayi jikina ya koma haka ya dunga bincikata , da yake lokacin aikin nan na karnataka na kan zafin sa , zancen bai yi nisa ba ya manta ya kuma haɗu da shima yana son manyan kayan ai hajiyata shiru kike ji malam ya haɗiyi shirwa !
  Sai dai ki ga idan na gifta yana zaune yana haka da ido ,"ta wani yi ƙasa-ƙasa da ido tana kwatance , " yana bin abebaɗan da kallo , ni kuwa sai na sake jujjuya masa su da kyau yadda zan sake kamo sa , a raina ina "faɗin kai da abubuwan ka ai daman sakin jiki kayi ka ƙure musu kallo meye na wahalar satan kallo kamar ba naka ba " ah to abun duniya menene ?? Sarkin fawa da kyautar ƙaho !
  Wata ƙatuwar dariya me ɗauke da haniniya samy baby ta kwasa sofi tana taya , suka chafke
 Shegiya tawan baki da kyau ! Watau shi tsuntsu me wayo ta wuya ake danƙar sa ,
  Charaf kuwa
  Ah to ai na faɗa miki friend babu abunda bazan yi ba babu kuma inda bazan shiga ba akan soyayyar doctor buri na ɗaya , shine ya kasance nawa ni ɗaya har abada ..
  Kin kuwa kamo hanyar , ko ma nace kin isa ga matakin .!
  Wata dariyar suka sake saki kamar sabbin mahauk....
Yakaka wacce dararrakin su ya mugun takurawa , saboda rabo da tayi da jin hayaniya sosai ya haka da kuma kalmomin su da basu mata daÉ—in saurare ta sanya Æ´an yatsun ta biyu ta toshe kunnuwan ta ,
hakan bai mata ba sai ta ɗauko ƴar ƙaramar wayar ta wacce samy baby ce ta saya mata tana da memory a ciki wanda yake ɗauke da ƙira'o'in Alqur'ani izifi sittin tare da wa'azizzikan manyan malamai ta jawo ear plugs ta maƙala a kunnuwan ta , ta sanya ƙira'ar AlQur'ani ta fara saurara bayan ta jingina da jikin gadon nata .
Niamey
A
ɗakin zaman marasa lafiya na musamman dake cikin national hospitalisé , mata biyu ne bisa kan ɗan gadon marasa lafiya , babbar ta jinginu da jikin sa ƙarfen gadon yayin da ƴar ƙaramar take kwance a jikin ta kan ta na bisa ƙirjin babbar dukkanin su biyu idanun su a rufe suke ,
Ɗan motsawa ƙaramar tayi tana yamutsa ƴar fuskar ta da take fayau !
Kafin ƴan daƙiƙai babbar ta buɗe nata idanun tare da tallafo ƙaramar ta miƙe zaune da ita sosai daga kishingiɗar da tayi ,
  Sannu Mama , ya kike ji yanzu jiki ya daina ciwo ?
  Duban fuskar maman ta tayi da raunanan idanun ta , ta kai ƴan hannuwan ta duk biyu ta ɗaura bisa fuskar mamar ta shafa tun daga goshin ta zuwa haɓar ta ,kafin cikin ƴar muryar ta me zaƙi irin ta yara masu wayo tace
     Na ji sauƙi maama kin ji ko ?
Da É—an raunannan murmushi a fusksr falmata ita ma ta sanya hannu ta shafi fuskar mama yadda tayi mata ,
  Naji daɗi mama na ta ji sauƙi ,Allah ya ƙara miki rangwame tare da sassauci , me zaki ci kafin ki sha magungunam ki ? ,
  Mayar da kan ta tayi ta kwantar bisa Æ™irjin mamar ta ,Â
  Maama bana cin kome , !
Idanun falmata suka kawo ruwa tana jin wani irin ciwo daga ƙasan ran ta , ƙaƙƙarfan tausayin mama kamar kullum yana sake cin ran ta , da ace tana da dama da tayi musanyan jinin jikin ta da na mama wanda ke gauraye da ƙwayoyin ciwon da a kullum yake barazana ga rayuwar ta tare da sanya ta a tsananin ciwo , to sai dai bata da dama ciwon mama muƙaddari ne daga Allah tun lokacin samuwar halittar ta .
Bai tare da cikakkiyar nutsuwa ya turo ƙofar bakin sa ɗauke da sallama , jin muryar sa ya sanya mama ɗagowa daga jikin falmata , ta waigo shi da buɗaɗɗun haƙoran ta ,
 Papa !
 Da sassarfa ya ƙaraso , ciɗak ya ɗaga ta tare da rungume ta tsama cikin jikin sa yana shafar lallausar sumar ƙan ta da take a tsefa an tufke mata ita a ƙeya .
A hankali yayi baya yana zama kan kujera ɗakin ya tare da ajiye ta kan ƙafafun sa ya riƙo fuskar ta da hannayen sa biyu idanun sa na bayyana tsantsar damuwa da soyayya yace mata .
  désolé ma chérie comment tu te sens maintenant ? ( sannu my dear ? Me kike ji yanzu?Â
Je me sens mieux maintenant papa! ( naji sauƙi yanzu papa )
  Ta furta hakan tana me shigar da kan ta zuwa ƙirjin sa ta kwantar da alamun rashin ƙarfi a tare da ita ,
 Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana jin yanayin da ya gan ta a ciki na narkar da ruhin sa ,
 A hankali ya ɗago kan sa yana duban sashin falmata daidai lokacin da ta kai ƴan yatsun ta tana ɗauke hawayen da ya biyo kan kumatun ta ,
     Tausayin ta me ƙarfi ya taso masa ,
   Fatimah ,
Ya ƙira sunan ta a ƙasan maƙoshi
 Sashin da take jin tashin muryar sa ta waiga ba tare da ta amsa ba .
 Meyyasa ba'a sanar da ni tashin ciwon mama ba ? Sai doctor ta ne daga nan ya ƙira ni yake sanar min ?
Muryata ƙasa-ƙasa ta ce
  Hajja ce ta hana a faɗa ma tace duk shekaranjiya ka tafi daga niamey , !
   Miƙewa yayi tare da ƴar sa a kafaɗa bai ce kome ba , sai da ya kai bakin ƙofa yace mata
  Bari mu tai ga likitan ta !
   Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin .
  Kichiɓus suka yi da hajja wacce take kan hanyar dawowa ɗakin bayan ta ɗan zaga ta motsa ƙafafun ta.
Riƙe baki tayi nuna alamun mamaki !
O Ni , yanzu ashe Babban soja sai da ka taho ? Kai da shekaranjiya jiyan nan ka tafi bakin aiki ? Banda abunka ai mun riga mun saba mun kuma fahimci kan ciwon mama tana fara nuna alamun rashin lafiya da hanzari muke zowa da ita asibiti , ai da kayi zaman ka bakin aiki .
Gaishe ta yayi a ladabce
  ta amsa da sakakkiyar fuska .
 Babu kome hajja ai lafiyar mama ta sa'a wuce aiki muhimmanci bari mu je ga likitan ta .
  Bayan dogon bayanin da kamar maimaici ne gare shi akan cutar ƴar ta sa wacce take ɗauke da ciwon Amosanin jini , " da a turance ake ƙiran sa da Sickle Cell Anemia,
Ya ɗora da yi masa bayani akan binciken da shi youssouf ya sanya likitan ya yi masa akan wannne asibiti ne mafi kyaun kayan aiki tare da ƙwararrun likitoci da zai iya kai ƴar sa ayi mata aikin da ake sanya ran idan har anyi sa da dacewa masu cuta irin na ta kan iya warkewa baki ɗaya .
Fitaccen asibitin nan a duniya da yake ɗauke da ƙwararrun likitoci dake ƙasar amurka ,"Mayo Clinic ," shine asibitin da likitan ya tabbatar da ƙwarewar su akan aikin dashen ɓargo ga marassa lafiyan da ya shafi manyan cutukan cikin jini .
Miƙawa likitan hannu yayi suka yi musabaha lokacin da yake miƙewa akan ƙafafun sa domin barin ofishin .
Likitan ya kai duban sa ga mama wacce tayi luf a jikin baban ta tana wasa da adon gaban rigar sa na soji .
Madame Safiyya Baskore sommes-nous bien maintenant? pas plus d'injection non?
  dariya tayi kafin ta amsawa likitan dai-dai lokacin da suke ƙarasa barin ofishin ita da baban ta .
  oui je me sens mieux maintenant plus d'injections .
Dariya likitan yayi yana É—aga mata hannu alamun ! bye bye !
   A hankali ta motsa laɓɓan ta tana kwantar da kan ta kan kafaɗun baban ta
 au revoir ! ( Bye ) ..
 Â
  Assalamu Alaikum kowa da kowa !
  Surprise ?? 😂
Ina gaisuwa agare ku baki daya masu karatun da suke faranta min wajen Danna dan tauraron nan tare da ajiye min sharhin su a karkashin kowanne shafi na rubutu na, ina son Sanar da ku cewa ina godiya me dinbin yawa agare ku.
Okay ghost readers, Makaho bai San Ana ganin sa ba sai an zungura shi ko ?? ðŸ˜
Kun san bakwa kyauta min koh?Â
 Â
Amma ba kome a dai juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe, 😂
[9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
33
Wannan shafin na bada tukuicin sa baki daya ga " ZULAIHAT RANO " MEELAH " RALIYA GARBA. #I MORE THAN APPRECIATE YOU SISTERS#
Bayan an sallami mama daga asibiti sun dawo gida , idan banda lelen ta babu abunda falmata take rabon ta da makarantar ta ma yau kusan sati guda kenan ,
Domin duk yadda hajja ta so falmata ta tafi makarantar ta bar mata kulawar mama ta ƙiya ,
gani take daga ta matsa daga kusa da ita ciwon nata zai iya tashi .
A zaune suke a falo hajja tana kishingiÉ—e tana hutawa bayan ta gama Æ´an kananun aiyukan ta na safe ,
Mama tana kalmashe bisa cinyar falmata , wacce take bin duk gaɓoɓin maman tana tausa mata su sannu a hankali , jikin ta sanye da ruwan hodan kayan sanyi na yara mata me adon ƴan ƙula-ƙulai farare , ƙafafun ta a ƙunshe cikin fararen safar ƙafa .
Biyamuradi ya shigo falon , a shirye yake tsaf cikin kakin sa na soji , fitowar sa kenan daga sashin sa da yake sabon gidan da ya saya musu wanda ya fi wanda suka fara zaman haya a cikin sa girma da tsari , domin wannan sashi uku ne da shi ƴan madaidaita , sashin da su falmata suke da sashin baƙi wanda ba'a amfani da shi sai kuma sashin biyamuradi da idan ya zo garin yake sauƙa a cikin sa a wasu lokuta , musamman a lokacin da ya tarar da rashin lafiyar mama , wasu lokutan kuwa a hotel yake zaman sa .
Mama tana jin sallamar sa ta miƙe daga jikin falmata wacce take ƙoƙarin riƙe ta ,
Mama ki tafi a hankali kin ga ba wani ƙwarin jiki kika samu sosai ba ,
Bata kula ba
Ta taka da ɗan gudun ta , da sassarfa shima ya ƙaraso ya chafe ta sama ya cillata ,
Yana juyi da ita kafin ya sauke ta zuwa ƙirjin sa yana dariya ,
Bonjour papa , ina kwana papa .
tace daidai lokacin da take kai hannu tana ƙoƙarin cire hular kan sa ,
Taya ta cire hular yayi ya É—ora mata bisa kan ta da aka mata manyan kitson kalba suka zubo har kan kafaÉ—un ta ,
Bonjour mon cher ," yaya kin ka tashi ?
Lafiya papa
tace da shi daidai lokacin da take ƙoƙarin sauƙa daga ƙirjin sa ,
Ya sauƙe ta yana riƙe da hannun ta suka ƙarasa cikin falon , ya samu mazauni kan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana gaisawa da hajja wacce ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi ,
Kamar yadda ta saba , yanayin ta babu walwala idan har yana waje ta gaida shi , tana riƙo hannun mama wacce take ƙoƙarin ajiye mata hular baban ta a kai ,
Bata iya hana ta ba sai da ta É—aura mata hular akan hular da take rufe akan ta wacce take mahaÉ—in doguwar rigar jikin ta ruwan madara me É—an nawi saboda tashi da aka yi da É—an sanyi garin sakamakon ruwan sama da aka kwana yi daren jiya .
Shafa fuskar ta mama tayi , kamar yadda yake al'adar su ita da mamar ta .
Maama kin yi chau dayawa ,
Papa ka ga maama na tayi chau , donne-nous des photos ,
ta ƙarasa zancen tana hayewa kan kujerar da falmata take ta zagaya ta bayan ta gami da sarƙafa hannuwan ta biyu ta wuyan falmatan ta cusa fuskar ta gefen wuyan ta .,
Biyamuradi wanda ya fara yiwa hajja bayani game da shirye-shiryen da yake na tafiyar su US , ya juyo da duban sa kan su idanun sa suka sauƙa kan fuskar falmata wacce haƙoranta ke buɗe tana murmushin da yake bayyana farin cikin ta da ganin walwalar mama ya assasa mata ,
Kamar maganaɗisu ya riƙe shi , ya kasa janye idanun sa daga kan ƴar fuskar ta da komen ta yake ɗan madaidaici idan aka cire manyan idanun ta ,
Ba tare da ya iya É—auke ido daga kallon ta ba ya zaro wayar sa daga aljihu , ya juyo baki É—ayan sa ya saita cemara ya haska musu hotuna wajen kala shidda ,
Da gudu mama ta sake sauƙowa ta dawo wajen baban ta , tana cewa zata ga hoto ?
Ta É—are cinyar sa ,
Batare da ya sake mata wayar ba ya nuna mata hotunan , da sauri ta sanya hannu tana sake tura huton gaba , fuskar wata Æ´ar baby me kyau kamar ta ya cika fuskar wayar , Æ´ar yarinya ce da bata wuce shekaru biyu ba tana tsaye a hoton ,
A hankali mama ta É—ago kan ta tana duban fuskar sa
Papa bebe waye ?
Zare wayar yayi daga hannun ta ba tare da ya bata amsa ba, daidai lokacin da hajja ta ke cewa ,
Wannan yarinyar da surutu kike kamar aku , duk kin bi kin tsare shi da surutu kin hana shi ya yi magana , bayan kuma yayi shirin tafiya aiki , ni zo nan ki zauna na miki tafiyar tsutsa a ƙafar ki .
Sauƙa tayi daga jikin sa , maimakon ta tafi wajen hajja , sai ta nufi mamar ta , tana zuwa ta zauna a gefen ta gami da kwantar da kai a jikin ta tayi shiru ,
Boyayyar ajiyar zuciya Biyamuradi yayi , cikin ran sa yana hamdala da hajja ta katse masa tambayoyin mama , domin Alƙawari ya ɗaukarwa kan sa ba zai taɓa yiwa ƴaƴan sa ƙarya ba , akan duk wata tambaya da suka masa , sai dai ko ya sakaya amsar idan kaifin hankalin su bai kai su fahimce ta ba , amma a yanzu bai shirya amsa ba ga tambayar da mama tayi ma sa .
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.