Complete Hausa Novels

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 21 of 21

Cigaba yayi da zama a wajen yana riƙe da ita tamkar wanda ya samu ɗaukewar tunani .

Ganin haka ya sa likitocin da suka rage su biyu suka fita , Hajja ta ƙarasa wajen su Yakaka tana ba su baki , da har yanzu basu bar kuka ba .

Turo ƙofar aka yi Tafeeda ya shigo tare da shi dattijo ne wanda yana sanya ƙafa a ɗakin ƙamshinsa ya gauraye ɗakin da ya sa Youssouf ɗago kansa suka haɗa ido ,

Maimartaba Sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore , ya taka ya ƙarasa gaban gadon da Youssouf yake zaune riƙe da Gawar ƴar sa ,

"Youssoufa ,

Ya ƙira sunan sa .

Ɗago da kansa yayi a karo na biyu , laɓɓan bakin sa na karkarwa da kyar ya fisgo kalmomin da a tun farkon samuwar Mama yake tsoron Furta su ga Maimartaba a tsa-tsan idanun sa , a yau neman tsoron ya yi ya rasa a lokacin da Mama ta ƙare ta zama Babu .

" Baaba , É—iyata ce , wannan Mama ce , É—iyata ce , ta rasu , Mama ta rasu ta barni Baaba .

Kuka ya sake fashewa da shi idanun sa na zubar hawayen da suke É—iga akan gawar Mama ,

Maimartaba sai ya zare gilashin idanun sa , da bayyanuwar sabon yanayi akan fuskar sa saɓanin wanda ya shigo da shi ,

Yayi tsumu ! yana kallon Youssouf da yake cigaba da kuka marar sauti , zuciyarsa ce ta rau-rawa saboda dalilai biyu da suka haÉ—e mar a lokaci guda .

a hankali ya kai hannu ya dafa ƙafaɗar Youssouf ɗin, cike da tausasawa a muryar sa mai ƙwarjini yace ,

"Youssoufa kayi haƙuri dukkanin mai rai Mamaci yake , Rayukan mu kuma ababen aro ne a gare mu da babu shakka masu komawa ne ga Ubangijin da ya bamu aron su a domin mu bauta masa , Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani , a cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da yake daidai , Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata saɓo , Idan ka kiyaye wannan, zai zamar maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake ciki ,

"Miƙata ga Tafeeda ka taso mu tafi ga yi mata sutura zuwa miƙata ga kabarinta ,Allah ya jiƙanta , Allah shi sa ta zama dalilin samun afouwar Ubangiji a gareka  .

Kalaman Maimartaba sunyi tasiri ga duhuntatciyar zuciyar sa mai ciwo , dan haka sai ya sasssuta riƙon da yayi wa gawar Mama , ya miƙata ga Tafeeda zuciyar sa na tuno masa rana ta farko da ya fara karɓar ta da tafukansa , ya rungumeta a ƙirjinsa ,  sai ga shi a yau ya zareta daga jikinsa da hannunsa ,  zarewa irin ta har Abada , ji yayi tamkar bazai iya ba , tamkar wani sashi na ransa ne ya bar jikinsa .

A hankali Tafeeda ya samu damar zareta daga jikinsa , wanda shima tasa zuciyar tayi laushi tausayin Youssouf ɗin ya cika zuciyar sa tare da ƙarin tsoron Allah , da ya tuna irin ƙauna da tsantsar son da Youssouf yake yiwa wannan ɗiyar , da har ta kai ya zaɓe ta bisa ga kowa da kome nashi , duk a domin ya rayu tare da ita .,

Sai ga shi domin Ubangiji ya yi masa babbar jarabawa sai ya sanya mutuwa ta raba tsakanin su , a kuma lokacin da kome ya rinchaɓe masa a dalilinta , lalle wannan jarabawa ce maigirma ,

Mayafin da aka rufe mata fuska da shi ya buÉ—e lokacin da yake É—aga ta , Maimartaba ya dubi fuskarta da tsantsar tausayi cike a ransa ,

"Ubangiji yasa ki zamto dagga Æ´a'Æ´an da zasu zam silar samun afouwar Allah ga iyayen su daga tarin zunuba su ,

"Amin Amin Amin,

Hajja ta amsa tana sharar ƙwalla ,

duba guda Maimartaba yayi musu ita da su Yakaka yayi wucewar sa , Tafeeda ya bi bayansa da gawar Mama , Youssouf ma ya sauƙa ya nufi ƙofar ficewa , ya zo ficewa ya waiga garesu da har lokacin suke ƙasa dirshen a zube , muryarsa a ciki yace

"ku tasso mu tai ku wanke ta ,

Shiru suka yi babu wacce ta amsa masa ,

Ganin ya fita yasa Hajja cewa ,

"ku tashi mu tafi Falmata , Yakaka kuyi haƙuri kun ji , haka Allah yake ikonsa uwa ta haifo ɗan da ta fi nisan kwana, kuyi haƙuri kuyi ta addu'a mutuwar Mama hutu ce a gareta , kuyi haƙuri .

Zuciyoyin su a lokacin basa aikin da ya wuce na kuka da jin raɗaɗin mutuwar ƴar da suka shirya sadauƙarwa a domin ta sai gashi mutuwa ta ɗauketa a lokacin da kowaccen su take jin rayuwarta kachokam zata sadauƙar domin ta tsaya tare da ita ,

Suka miƙe ƙafafun su babu ƙarfi suka rufa masa baya , a motar da suka zo a ciki suka koma sai dai wannan karon wani ne ke jaan motar da basu kai ga sanin sa ba ,

Gidan suka tarar da yalwar mutane da suka wuce yadda suka barsu a farko yawa ,

Mutane maza da suke sanye da kaya mai launi guda , da kuma mata a falon nasu , Yakaka da Falmata ratsawa suka yi basu dubi kowa ba suka wuce É—akin da yake na Falmata , suna shiga su duka biyun kuka suka sake sawa , a tsakanin su an rasa mai rarrashin wani ,

Shigowar Tafeeda É—auke da gawar Mama shi ya dakatar da Æ´an guna-gunin da ya fara tashi bayan wucewar su

Kai tsaye ya miƙata ga Hajja wacce take raƙube daga gefe tunda ta shigo babu wanda ya dubeta bare su amsa gaisuwar ta'aziyyar da take yi musu da basu kai ga sanin wa ya rasu ba , ganin sun yi biris da ita ya sa tayi shiru tana sharar ƙwallar ta ,

"Ki miƙata ga uwayenta sui mata wanka , su shirya ta yanzou za'a kawo likkafani ,

Sai ta ƙarbeta ta ratsa ta tsakanin su ta wuce ɗakin Falmata , zuwa lokacin hankalunsu baki ɗaya ya koma ga Tafeeda ,

Bai jira sun tambayeshi ba , ya ce 

"Diyar Biyamuradi Youssoufa ce da Allah ya amshi ranta a yanzou ,
Daga haka bai É—ora kome ba ya juya ya fita ,

Shiru wajen ya ɗauka , kafin lokacin da Hamshaƙiyar matar da ita ce ƙwal ɗaya a bisa kujera ta motsa , fuskar ta da wani yanayi da kai tsaye ba'a iya fassara shi ba ta soma da cewa ,

"Allahu Akbar innalillahi wa inna ilaihi raji'oon , kaico yarinya wahalar ki ta ƙare kin kuma huttashe da wasu dagga samuwar baƙin-ciki sanadin duban ki , to Allah shi jiƙan ki , ta tabbata dai Youssoufa yana da ɗiya mai shekarun ya wannan da kuma Amre ko ba Amre ?

Bata tsaya ba ta cigaba da cewa , "Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, wautace babba a ɓatar da lokaci akan aikin banza , mutumin da ya ƙamnaci zunubi ya irin haka , ai ya shiryawa hukunci ne , zunubi da kunyata kuwa tare suke rungumar mai su, shiyasa asharari bashi da wata ƙima  ,

Ta murza zoben hannunta , tana wani ɗan guntun murmushin cikar buri , ta  ɗora

" gaskiya ita dawwamammiya ce ƙarya kuwa ai ƙurarriya ce , ɗan da ya jawo wa Mahaifinsa ɓacin rai ya haka ,? Ai abun baƙin-ciki yake ga Mahaifiyarsa , to wanne farin-ciki za'a yi da samuwar baragurbi cikin 'ya'ya ?

A hankali Adda Ammi ta ɗaga kai ta kai ganin ta gareta bayan gama jawabinta lokacin da ƙaramar jakadiya tace ,

" Babu shakka ko kokonto cikin kalamanki ranki ya daÉ—e , kowa ya aikata abunda ransa ke so zai ga abunda bai so a lokacin da bai so ba ,

Kallon-kallo aka yi tsakani Ammi da Ubbo da kawo yanzu suka rasa halin da zuciyoyin su ke ciki kan mutuwar ƴar ɗan uwansu da ake duk wani ƙiƙi-ƙaƙa akanta ,

Sai dai kalaman Matar da take mazaunin uwa agare su , Matar Mahaifinsu , da kuma ta wakilci Mahaifiyar su wajen wanzuwarta anan , da kalaman nata ke nuni ƙarara da tazorci gami da kausasawa ga ƙaninsu , ko kusa bai musu daɗi ba , duba da cewa wajen gauraye yake da bayun su ,waɗanda Youssouf shugaba yake a wajen su duk da laifin sa ,

sai dai su basu da ikon tankawa ,"Hajiya Mama uwa take kuma shugaba a gurin su 

Ba'a ɗau lokaci ba Tafeeda ya dawo hannunsa riƙe da likkafani , ya miƙawa Ubbo ba tare da yace kome ba ,

Sai ta karɓa ta nufi ɗakin da ta ga sun shiga ta tarar da su su ukun suna kewaye da gawar Mama da take shimfiɗe a ƙasa ,

Yanayin da ta gansu ya taɓa ranta , bata ce ƙala ba ta miƙawa Hajja likkafanin ,

Ta juya , har ta kai ƙofa ta juyo , "kun iya wankan ? Ta tambayesu

Babu jinkiri Yakaka ta gyaÉ—a kanta , sai ta juya tayi ficewarta tana É—auke ganinta daga kan hoton Mama da yake bangon É—akin Falmata , tsananin kamannin da yake tsakanin Mama da nata Æ´a'Æ´an ya girgiza ranta .

Yakaka ita ta wanki gawar Mama da take rungume a jikin Falmata , ƙwarar idanun su bata huta ba wajen zubar hawaye ,

Tunawa Yakaka take tun daga ranar da suka ɗora ƙazamtatciyar alaƙa da Youssouf , har zuwa ɗaukar rainon cikin ta da ta samun ta ta haramtatciyar hanya , zuwa da ranar da ta haifeta , da ko fuskarta bata kai ga gani ba , ta tuno da ranar da ta zo irin kallon da tayi mata dake bayyana tsoro da rashin sanayya ,

' tsawon rayuwar da Mama tayi shekaru shida a duniya bazata ɗorar da kome na daga rayuwar yarinyar ba , ƴar da ta ƙi kallonta lokacin farko da ta fito duniya , ta kuma tafi ta barta bata ji tausayin ta tayi tunanin me zata ci ta rayu alhalin abincinta na jikinta ba , ina zata ji ɗumin jikin uwa irin wanda jariri ke buƙata a lokaci na hunturu ?

Babu shakka Samy Baby ta zalunceta da ta cisgeta daga cikin Æ´ar gajeriyar rayuwar Æ´arta , ta yi mata yaudara mafi girma da ciwo , irin ciwon da ba zai rabu da ruhinta ba har ta koma ga Maliccinta ,

" Mama Allah ya jiƙan ki yasa kin samu hutu dawwamamme daga barin rayuwarki mai cike da jinyar gangar jiki , ki yafe min Mama , ki yafe min , addu'o'i ta cigaba da yi mata tana wanke ta .

Bayan sun shiryata suka fito da ita , Hajja ta fita ta ƙira Ubbo , zama tayi a ɗakin sannan ta ƙira Tafeeda ta sanar da shi an shiryata ,  babu jimawa suka shigo su biyu da wani , suka ɗau gawar Mama zuwa waje da za'a sallaceta ,

Falmata kasa riƙe kukan da yazo mata tayi ta fashe da kuka mai ƙarfin gaske , dake bayyana jin ciwon rabuwarta da ƴar da ta ƙwallafawa rai fiye da abunda ke cikin cikinta ,

Ƴar da ta so tare da sadauƙar da kome a domin ta , ƙaunar da ta mata ta fara daga ranar da ta rungumeta a jikinta bayan rashin mahaifiya da tayi , ta ɗau alwashin maye mata gurbin uwa da ta rasa , ta dunga tuno da yadda suka ƙaunaci juna ita da Mama , da bata san tana da wata uwa ba bayanta har ta koma ga mahaliccinta ita ce mahaifiyarta ɗaya tal, tabbas Mama ta bar mata gurbi a zucia sa babu ranar cikata shi .

***

Tamkar wutar daji haka labarin mutuwar ɗiyar Biyamuradi Youssouf/MaJor Youssouf da mutane basu san da wanzuwarta ba ya dunga kewaya ko'ina ɗauke da mummunan tambarin da Youssouf ya ƙi tabbatuwar sa ga rayuwar Mama sai ga shi bayan mutuwar ta labari ya bayyana an kuma ƙira ta da sunan da bai so ba .

Zaman makoki sosai ya kankama tun yammacin ranar da aka bizneta da kuma tun bayan jana'izar da Maimartaba sarkin Maraɗi da kansa yayi limanci , ya bar wajen tun kafin dawowar su daga maƙabarta ,

Ƙarƙashin rakiyar maƙarrabansa da suka zo tare suka koma , waɗanda mafi yawa manyan fada ne , masu faɗa a ji a harkar sarautar masarautarsu da amintattun manyan bayunsa , zaɓaɓɓu da aka aminta da Amanarsu

Da tafiyar tasu musamman ta samo asali ne kan zuwa su ganewa idanunsu inda Youssouf ɗin ya ɓoye yana rayuwar banza kamar yadda aka yi ta jita-jita a kwanaki zancen kuma ya dawo kunnuwansu Amma suka yi binciƙe basu samu shaida ba ko guda a wancen lokacin

Sai fa da yanzu shaida ta bayyana ta hannun Mouhammadou da yace shi ma fa bayani aka ba shi ,

Mafiya yawan masu zuwa ta'aziyyar abokan aikinsa ne da matan su sai kuma tsirarun mutanen gari da yake mutunci da su , daga masarautar su babu mutum guda da ya ƙiraye shi ko kuwa ya zo yi masa ta'aziyya tun bayan juyawar tawagar sarki da kuma ta su Hajiya mama ,

Tsakanin Hajiya Umma ko matansa babu wacce ta ƙira shi , haka ma 'ƴan uwansa idan aka cire Ubbo da Ammi da kawo yau da ake kwanaki biyu da mutuwar Kullum suna zuwa gidan nashi su yini a karɓi gaisuwa da su duk a ƙoƙarin su na son ganin sun rufa asirin ɗan uwansu daga mutanen da basu riga da sun san ta hanyar da ya samar da Mama ba ,

Sai dai a yau su ma sun kudurce cewa sun yi zuwan ƙarshe dan haka suka yanke shawarar yi masa magana ,

Har falon sa suka shiga suka tarar da shi , tare da Tafeeda da tunda aka yi mutuwar yana tare da shi , duk da cewa babu wata doguwar mu'amala ko da kuwa ta maganar baki ce da take shiga tsakanin su ,

A zaune suka tarar da su shiru tamkar kurame , shi Tafeeda yana aikin latse-latsen waya shi kuma Youssouf yayi tsumu irin yanayin da yake ciki tun bayan mutuwar Mama ,

Babu karsashi suka gaisa , bayanan suka yi shiru ,suna nazarinsa da ya sunkui da kansa , baki ɗaya yayi wani irin sanyi har ƴar rama yayi , ba kaɗan ba mutuwar ƴar sa ya taɓa rayuwar sa ,

Cikin taushin Harshe Ammi ta fara masa nasiha kan laifinsa na aikata zina da ta kai shi ga haihuwar Mama , har zuwa yin aure ba tare da sanin iyayensa ba , bayan haka ta tambaye shi tsakanin Yakaka da Falmata waye uwar Mama ?

Nan ya basu amsa da cewa Yakaka ce mahaifiyar ta ,

Ta tambayeshi kuma ta yaya yake auren Falmata alhai ƙanwace ga Yakaka kuma suna tare guri guda ?

   Nan ya basu labari a taƙaice kan yadda aka yi ya auri Falmata da zaton cewa Yakaka ta mutu ne , sai kuma kwanakin da suka dawo daga USA ya ganta a gidan bashi da wani masaniya kan labarin da ya shafe ta .

  Duk shiru suka yi , kafin ubbo tace
" to tunda Allah ya gwada karshen kome da ya zare wannan ɗiya a tsakani domin kawo maslaha a gare ka, sai kayi ƙoƙarin gyara duk wasu kuskuren ka ,

"tunda daman domin riƙon ita ɗiyar kake amren innar ta ai sai yanzou ka sau amren su yi tafiyar su , kai ma ka koma ga iyayenka ka biɗi afouwarsu , su yafe ma sabadda rayuwa tayi maka kyau Youssoufa , ka fuskanci aikin ka cigaban rayuwarka ka ji kou ?

Ba tare da ya É—ago kan sa ba yace

" to naji ,

Kallon rashin gamsuwa da amsar sa suka bi shi da shi , amma basu jaa zancen da tsawo ba suka rabu da shi , saboda sun san muddin ya tafi Maradi sai ya saki auren Falmata ba zai yiwu ya bijirewa iyayensa ba bayan tarin laifin da yayi masu muni .

Basu bi ta kan su Falmata ba bare su yi musu Sallama suka fita a gidan cikin motar Tafeeda , suka bar Youssouf shi ɗaya tal a ƙofar gidan ,

Matsawa gefe yayi ya samu waje ya tsugunna , kewar É—iyar sa tare da ciwon rashin ta suna taso masa ,

kwanakin da suka biyo bayan mutuwar ta basu zo masa da sauƘi ba sanin da yayi bata raye a duniya yana murƙushe duk wani kuzarinsa ,

baya iya bacci daga ya rufe ido fuskarta ke yi masa gizo muryarta na amsa kuwwa a kunnuwansa ,

baya son doguwar magana da zata katange shi daga yin addu'o'i  , ko abinci sai yunwa ta kai masa maƙura yake iya tsakura ya ci .

Ƙaunar Mama dabance a wajen sa ko cikin abubuwan da yafi so a duniya tana a sahun farko , yasan a cikin 'ya'ya ba zai samu ya ita ba a samun zallar so da ƙauna daga wajen sa tayi zarra , sai ga shi tafiya bata miƙa ba , mutuwa ta shafe tsakanin su , ta ɗauke masa sanyin idaniyar sa .

'yar da silar ta ya haɗu da Fatima zahra har tayi sanadin ƙulluwar aure a tsakanin su ta wanzu tsawon lokaci tana ƙulla kusanci a tsakanin su  , har sai da ta sa bai farga ba ya faɗa tsundum cikin ƙaunar innar ta ,

Tunanin Falmata ya zo masa , a tun ranar mutuwar Mama rabon da ya sanyata a ido ko ya ji muryar ta , ya san tana cikin halin ɗimuwa kwatankwacin wanda yake ciki tana kuma buƙatar lallashinsa , 

Sai dai ba shi da wani sauran dauriyar sake fuskantar wani tashin hankalin da zai iya tasowa daga gareta bayan sanin da tayi cewa shi da Yakaka sun rufeta akan alaƙarsu da haihuwar Mama , bashi da tabbaci kan yadda ta ɗau lamarin , Dan haka ya zaɓi ya bata iska ,

Kafin zuciyar sa ta gama yanke shawara kan hukuncin da yake son zartaswa a gobe .

***

Yakaka da Falmata sun yi kwanaki biyun cike da kewa da jin ciwo na rashin Mama ,

Koyaushe su na ƙule a ɗaki , basa fitowa falo wajen da su Ubbo suke bare su ga juna , Hajja ita ke kai kawon kula da lamuran gidan, ko abinci kai musu take har ɗaki , duk kuwa da cewa basa yi masa wani cin kirki ,

Wani irin zaman shiru suke yi marar armashi da tunda suke su biyu irin shirun mai kama da na tsakanin baƙi juna bai taɓa gifta tsakanin su ba , kowacce tana jinyar ruhinta

Yau bayan sun idar da Sallar Azahar, suna bisa sallayun su , Falmata ta dubi sashin da Yakaka take , ta ƙira sunanta a hankali ,

" Yakaka ,

Yakaka ta ɗago kan ta ,daga karatun da take yi , ta amsa ƙiran da tayi mata tare da tasowa ta dawo kusa da ita ta zauna ta riƙo hannun ta da irin kulawar da ta saba bata tun tasowar su ,

Falmata ta ƙure kallonta ga Fuskar Yakaka da take iya hango haskenta , tace

"Yakaka , ki faÉ—a min , ki bani labarin tsakanin ku ,
   Tayi shiru kaɗan ,
"ki bani labarin na gaskiya tsakanin ku da Baban Mama , kuma ki bani labarin rayuwar da kika ki bayan haihuwar Mama Alhalin bakya tare da mu ? Ki bani labarin gaskiya Yakaka .

Shiru Yakaka tayi cike da zullumi sai dai ta san abune da tasan da faruwar sa ,tun gabannin ta tambaye ta dan haka ya zama dole ta sanar da ita dukkanin wata gaskiya da ta nemi da ta sani ,
Muryar ta babu kuzari ta fara bata labarin tun daga Rana ta farkon haɗuwar su da Youssouf , har zuwa ranar rabuwar su ta ƙarshe , ta ɗora da cigaba da sanar da ita irin gadar zaren da Samy Baby ta haɗa mata tun kafin zuwan ranar haihuwar Mama da a ƙarshe tayi nasara ƙarƙashin jagorancinta da mummunar huɗubar ta tayi tasirin rabata da rayuwarsu ita da Mama 'yan mintoci kaɗan bayan haihuwar ta ,

dakatawa tayi tana jin tashin hankalin yadda Falmata ta zare hannunwanta dake cikin nata , ta É—ago kai tana kai kallon ta ga fuskar ta ganin yadda hawaye suke zuba daga gurbin idanun Falmata ya ruÉ—a ta ,

Sai dai bata da wani zaɓi illa cigaba da sanar da ita gaskiyar kome kamar yadda ta alƙawarta , bata tsahirta ba ssi da ta gama tas da bata labarin rayuwarta a garin Abuja gidan samy baby , taimakon da Malama Maryam da ƴar ta Lubna suka yi a rayuwarta ,  har zuwa komawarta gida Maiduguri wajen Prof .

Ta ɗago kanta tana nazarin Fuskar Falmata wacce tayi ƙasa da idanunta ya zuwa yanzu ta daina hawaye ,  riƙe hannunta ta sake yi muryarta na rawa ta cigaba da cewa

" Falmata na san ni mai laifi ce a wajen ki , amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min , nayi kome ne gurin ƙoƙarin na baku rayuwa mai kyau bansan cewa ace na kama hanya ne na rusa mana rayuwa ba , ki yafe min ki zo mu koma Nigeria wajen Baba prof shine kaɗai mutumin da ba zai kore mu ba , ki rabu da Rayuwa da Youssouf kamar yadda Mama ta bar mu , shi ɗin ba kowa bane da ya wuce Maƙaryaci Mayaudari da ......

Miƙewar da Falmata tayi ita ta hana Yakaka ƙarasa zancenta , da kallo ta bi ta lokacin da ta nufi ƙofar banɗaki ta tura ta shiga ta rufo ƙofar ba tare da ta waiga gareta ba , zama tayi cikin wani irin yanayi mai cike da rashin madafa , nadama na sake lulluɓar ta , ko Falmata bata buɗe baki tace mata kome ba ta fahimci tana fushi da ita , fushi kuwa mai tsanani , da ya sa taji tsoron sake yin wani yunƙuri domin tana gudun faruwar wani abu marar daɗi a tsakanin su ,

Fiye da minti talatin ta kwashe a zaune tana jiran fitowar Falmata daga banɗakin da tunda ta shiga bata jiyo motsinta ba , har ta fara tsorata tana tunanin tashi ta ƙira ta , sai ta ga ta murɗo ƙofar ta fito , daga fuskarta har tufafin jikinta a jiƙe suke , sai tayi kasaƙe tana bin ta da kallon tsoro , ganin yadda idanunta suka kumbura alamun kuka tayi mai tarin yawa ,

Kayan jikinta ta sauya ta zo ta janye sallayarta da take gaban Yakaka ta matsa gefe guda ta fara sallah ,

Gaɓɓan jikinta baki ɗaya sun daɗa sanyi Shirun Falmata kuma ya sa ta ɗeɓe tsammani , cikin zuciyarta sai ta fara tunanin mafita ,

Ta shiga bijiro mata da kome da ya wakana daki-daki tsakanin da Youssouf wanda tuni ta fahimci kason nata laifin yana neman zarta na Youssouf tun a farkon fari , ai ita ta fara bada kanta cikin salama , sannan ta cigaba da zama rakuma da akala wajen biye masa aikata zunubi , mafi girman laifin da ta aikata shine gudu da tayi ta ƙyale Mama da Falmata ,

wanda ta nan Youssouf ai ya fita amfanarwa ga Rayuwar Mama da ya haɗa su da ita da Falmata ya tallafa har ma ya zamto sanadin samun lafiyar idanun ta wanda tun akan hanyar su ta zuwa Niger Hajja ta sanar da ita samun lafiyar idanun Falmata , ranta kuma ya cika da farin-cikin da ta ƙi nuna shi a fili saboda kada ta nuna yabawa ga Youssouf bayan tarin laifin da take tuhumar sa da shi da kuma ƙudirin da take tafe da shi na son raba zaman su ,

Sai dai a yanzu da irin yanayin da Falmata ta nuna bata hango alamun zata samun haɗin kanta cikin sauƙi ba , ita kuwa ai bata da sauran ƙarfin zuciya , mutuwar Mama ta kwace mata duk wani karsashi nata ,

Jin an ƙira sallah ya sa ta miƙewa ta ɗaura Alwala ita ma ta tada sallar la'asar ,

Bayan sun idar gani tayi Falmata ta miƙe ta hau gadonta ta kwanta tare da jaan bargo har kai ta rufu , duk kuwa da cewa garin babu sanyi ,

Jugum tayi tana hangenta , kafin ta ce Falmata , garin ai babu sanyi meyasa kika rufu haka ?

Biris tayi da ita bata amsa ba , jikinta sai ya sake yin sanyin sanin da tayi cewa Falmatan tana jin ta sarai ƙin tankawa tayi ,

Sai ta miƙe ta naɗe sallayar , takunta ba ƙarfi ta fita ta ja mata ƙofar ɗakin bata yi taku uku ba ta ji ƙarar sanyawa ƙofar makulli da Falmata tayi ,

Sai ta waigo tana kallon ƙofar , tayi murmushi mai bayyana ciwon da zuciya ke yi , hawaye na taruwa a gurbin idanunta ƙwarai abunda ta fuskanta daga Falmata a yau ya taɓa ran ta , ɗakin Hajja ta koma bata sake bin ɗakin Falmata ba .

Daren ranar babu wanda ya ci abincin dare a tsakanin su Ukun Youssouf , Yakaka ,da kuma Falmata haka kowannen su ya kwana yana saƙa abunda yake ganin zai fissheshi ,

Ƙarfe huɗu da rabi da Hajja ta farka ta tarar Yakaka ta haɗa kayanta kaf , cikin ƴar jakar da ta zo da shi da tana zaune shiru ta jingina kanta da jikin bango ,

Tausayinta ya kama Hajja , bayan ta É—aura Alwala ta fito sai ta zauna a gefenta ,

"Yakaka uwar Mama

Ta ƙira sunanta , bata amsa ba amma ta maida hankalinta gareta ,

" Ya naga kin É—auko jakar kaya haka ?ko..

" Tafiya zan yi Hajja , yau zan koma Nigeria , daman domin na gansu na zo kuma ai na gansu , na ga mutuwar Mama a idanuna , babu sauran zama da zan sake yi zan tafi yau .

Ta ƙarasa zancen hawaye masu ɗumin gaske suna sauƙa daga idanunta

Kamo hannun ta Hajja tayi , muryar ta a tausashe tace

" kiyi haƙuri Yakaka dukkanin abunda kika ga ya faru ga Rayuwar Bawa tun gabannin a halicce sa yake a rubuce cikin kaddarar rayuwar sa ,  kar ki bari shaidan ya raba tsakanin zumuncin ku ke da ƴar uwar ki , kan abunda ya gabata ku duka uku kaddarar rayuwar ku ce ta zo a haka , ke kece Babba ki riƙe zumuncin ku ƙam kar ki bari kowanne mahaluƙi ya shiga tsakanin ku , ku biyu ne rak a duniya ko kuwa kuna da wanda ya wuce junan ku ne ??

Girgiza kai Yakaka tayi alamun a ah , sai kuma tace " Hajja Amma Falmata ta samu wanda ya fini tu.....

" kul kar ki bari zuciyarki ta miki mummunar saƙar da zata wargaza muku zumuncin ku , kiyi haƙuri ki maida kome ba kome ba , kiyi haƙuri da jarabawar Ubangiji Allah zai miki tukuici da mafificin abunda duk kika rasa kin ji ko ?

" to
Ta amsa tana share hawayenta , Hajja ta cigaba da cewa , "yadda kuka haɗu kuna murnar ganin juna kar ku rabu kuna zargin juna ku rabu da farin-cikin da zai ƙara danƙon zumuncin ku kin ji ko ?

" naji nagode Hajja ,

Shiru suka yi suna saurara lokacin da suka ji an taɓa ƙofar falon , sai dai basu kawo kome a rai ba ga zaton dukkanin su Falmata ce ta dawo daga turakar Mijinta ,

Hajja ta ɗora da cigaba da yiwa Yakaka nasiha tare da gwada mata girman zumunci. Da ya sa ta jin sabuwar ƙaunar 'yar uwarta na game mata jini ,

Lokacin da gari yayi shaa , sai ta fito falo da jakar kayanta tana jiran fitowar Falmata domin suyi sallama ta kuma sake neman yafiyarta , 'yan kuɗaɗenta kimsnin dubu goma sha uku a ƙulle a marar ta , sai ta ware dubu uku da ɗari hudu zata bawa Falmata kyautar su ita kuma ta san dubu goma zai sada ta da birnin Maiduguri har ƙwaryar gidan Prof .

Zaman fiye da mintoci goma ta yi lokacin da ta ji an shigo Falon a hankali ta kai ganinta kan sa yana shirye tsaf cikin kakinsa na soji , sai ta tuno da ganin da tayi masa a baya can ,

Da sauri ta ɗauke kanta ta mayar da ganinta ƙofar ɗakin Falmata ,

Shima a ɗarare ya ƙaraso falon fuskarsa babu walwala , a kusan tare suka furta kalmomin

"ina kwana ?

Shi ya riga ta amsawa da "lafiya ,

Sai duk suka yi shiru , shi bakinsa É—auke yake da jawabi duk da cewa a yau ya hango sassauci daga gareta a karon farko ,

Ƙarasowar Hajja wajen ya sa shi zama akan kujerar da take kusa da shi , gaisawa suka yi tana sake yi musu ta'aziya su duka biyun , har ta miƙe sai yace

"Hajja ina Fatima ?

Hajja tace tana ciki Babban soja , a ƙirata ne ?

"eh Hajja a ƙirata ,

Hajja ta nufi É—akin Falmata ,

Haka kawai Yakaka ta ji zuciyarta ta tsinke , a karo na farko ta ji tsoron kar Youssouf ya furta cewa ya saki Falmata da tun-tuni ta fahimci ta faɗawa son shi , tausayi take ji , ita ta san yadda raɗaɗin so yake , bata fatan Falmata ta ɗan-ɗana zogin rasa masoyi , a yanzu zata so Falmata ta tsira da masoyinta , abunda ke cikinta kuma ya rayu kusa da mahaifinsa ƙarƙashin gatan uwa da uba a lokaci guda ,

Dan haka ta yunƙuro da zummar yin magana ta shaida janyewar ƙudirinta akan sa ,

fitowar Hajja ya katse ta , inda take sanar da su Falmata bata É—akin ,

"tana ina Hajja ?

Youssouf ya tambaya da É—an shakku a muryar sa ,

"ban sani ba Babban soja kuma bata can sashin naka ?

Ya miƙe tsaye lokacin da yake cewa

"bata can ai Fatima batta je ga sashi na ba ,

su dukkanin su sai suka yi tsaye cikin É—arsuwar sabon tashin hankali a rayukan su

Kamar haɗin baki sai suka bazama neman ta , lungu da saƙo na gidan , Youssouf da Yakaka suna haɗawa da ƙwalla ƙiran sunanta , amma ko alamu babu kurwar ta a gidan , dawowa suka yi suka haɗu a falon zuwa lokacin Yakaka kuka take yi , shi kuwa Youssouf idanunsa ne suka kaɗa jawur ,  da wani irin tasowar mummunan ɓacin rai lokacin da tunanin sa ya gama hasaso masa abunda ke faruwa ya dubi Yakaka da wani irin sauti yace

" Ina kika kai ta ? Ina kika ɓoye min Matata ?  Kiyi gaugawar sanar da ni kafin ki riski fushina Yakaka ..

Yakaka ta zaro ido da maÉ—aukakin mamaki tana kallon sa ,

"ita Youssouf yake nufin ta sace Falmata ƙanwarta ? Wanne irin mummunar kalma ne wannan yake jifatan ta da su ??
   Saɓon ɓacin rai ya bijiro mata .

Assalamu Alaikum masu karatu dafatan kuna lafiya ?

Wannan shafin kachokam ɗinsa sadauƙarwa ne ga duk wasu iyayen masu ɗauke da cutar Amosanin jini ,( Sickle Cell Disease)

Ku sani ya ƴan uwa Allah ya ɗora mana ne domin ya san zamu iya , wataƙila kuma domin hakan ya zamto hanyar samun Rahamar Ubangiji a  gare mu mu iyayen da kuma su da suke ɗauke da cutar ( muna fatan haka )

Ku sani cewa cuta irin wannan mai wahalarwa baiwa ce da ba kowa Allah ke ɗorawa ba , dan haka muyi ƙoƙari wajen basu kulawa tare da haƙuri domin cinye jarabawar da Allah ya yi muna ta dalilinsu .

Kada mu danƙwafar da su , kada kuma mu banbanta su da sauran ƴan uwansu masu lafiya , ƙarfafawar mu tamkar ƙara musu lafiya da walwala take yi a gare su, saɓanin haka zai iya sawa suyi rauni su ji tamkar su basu da amfani a lokaci guda su ji sun gaji da duniya .

Cuta bata nuni izuwa ga mutuwa kamar yadda lafiya bata nufin tsawitar rayuwa ( nisan Kwana )  fatan mu Allah shi iyar muna , ya yi mana maganin abunda ya gagare mu , ya wadace mu da lafiya mai amfani .

Ina miƙa ta'aziyya ga dukkanin iyaye ,kakanni 'ƴan uwa na waɗanda suka rasa rayukan nasu ta sanadin ciwon Amosanin jini Sickle Cell Disease .

Jinjinar kuma ta tafi gare ku gawurtattun mayakan da Allah ya ratayawa cuta mai wahalarwa,  Da ku nake ( sickle cell Warriors ) ku din ai JARUMAI ne da suka banbanta da saura , ku cigaba da nuna jarumta watarana akwai waraka zata zo inshaAllah .

Nagode .
[12/10/2019, 2:44 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

44

Cikin motar ƙirar Golf 2 Wagon da take shilla gudu akan titin da zai sadu da jahar Tahoua .

Falmata ce a zaune daga kujerar da take daura da Direban da bakinsa yake cike da goro ,  yana ta bin wakar Sa'adu bori mai taken 'soyayya abun yi ce ,da take tashi ta cikin sifikun motar kamar zai fasa mata dodon kunne ,  ta  kare fiye da rabin fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar jikinta da ta sanya hijabi a madadin sa

Ita ɗaya ce ƙwal mace a cikin motar sauran mazauna gidan baya na motar duk maza ne matasa majiya ƙarfi

***

Lokacin da ta samu isa tashar mota na birnin Niamey da misalin ƙarfe biyar da rabi na asubahi , babu yawaitar mutane a tashar da kyar ta samu wani dattijon ɗan kamasho inda ta shida masa Maidugurin Jahar Bornon Nigeria take son zuwa ,

A mamakance dattijon yake kallon ta , kafin yace mata ,

"kai tsaye Borno zaki tai dagga nan yarinya ?ko dai Sokoton Nigeria zaki tai dagga nan , a can kuma ki tai Borno ?

"Maiduguri zan tafi daga nan Baba, dan Allah ka kaini motar da zata tafi can .

ta bashi amsa tana share ƙwallar da taƙi tsayawa a idanunta ,

Da sauri ya tare ta da cewa ,

"a ah yarinya batun ba na kuka bane kin ga itta motar Borno dagga nan ai wahala take batta samuwa haka a sauƙaƙe , sabadda Borno daga nan tahiya ce miƙaƙaƙƙa ya ta mai yada shege , sai kin tai zouwa zender dagga nan ki shiga ta diffa kafin ki tsallaka boda ki shiga yankin Mobar ta jahar Bornon Nigeria , anya yarinya kina mace budurwa ɗanya shakaf kya iya wagga tahiya ta mazaje ?

" zan iya Baba , Allah zan iya , zan tafi ga taimaka min .

Tace , zuciyarta na sake haƙaƙewa kan tafiyar ita ce kaɗai mafita a gareta ,

" to babu laifi , bara shi malam Amadou gayu ya isso domin shi É—ai yake wannan dagon zagon Allah sa dai Æ´an tangaran basu riga sun kama kujerun motar ba , dawo dagga nan ki zauna , nan ba da jimawa ba ike isowa ,

A ɗarare ta zauna akan wani ɗan dandamali ba dan ranta ya so ba domin a matse take ƙwarai da ta bar yankin ,

Zaman mintoci goma kawai tayi sai ga motar Ahmadou gayu , wata wankakkiyar golf wagon ce da ta ci uban dilken da ake yiwa tsoffin motocin da ake son tada musu da komaɗa tare da ɓoye musu tsufan su .

Tayi zaton za ta ga wani matashin saurayi jin ana masa inkiya da "gayu , sai ta ga wani dattijon da ya tasamma shekaru sittin amma ya ƙi sarewa daga yin gayu domin kuwa a tsuke yake cikin ƙananun kayan da suka ɗau guga , ya ci zanzaro ,  kan nan nasa da sanƙo ya cinye rabi rabin kuma gashi ne a tare himili guda da aka yiwa shamfo a taje tsaf-tsaf yana sheƙin Mai .

Da fitowar sa gurin ya ɗau ƙamshin ƙaƙƙarfan turarensa na 999 for male .

Bai jinkirta ba ya fara goge jikin motar da a zahiri babu wani datti sai ƴar ƙura da ba'a rasa ba ,

ÆŠan kamashon nan shi yayi sauri ya samar mata wajen zama domin kuwa , kamar yadda yayi zato har an riga an kama kujeru huÉ—u na bayan motar ,wajen mutum É—aya tak ya rage ,

Dan haka Falmata bata jaa ba lokacin da aka yanka mata adadin kuɗin da zata biya , ta ƙirga kuɗin daga ciki ƴar karamar jakar hannunta da ita ce tal abunda ta riƙa , ta basu ta shiga gaban motar ta zauna .

Sauran mutane huɗun da yake daman sun riga sun kama kujerar motar suna zuwa shiga suka yi ba ɓata lokaci ..

Ƙarfe shidda cif motar su ta bar cikin tasha ta ɗau hanyar da tafiyar da zata iya kai su kwanaki biyu kafin isar su Yankin jahar Borno Nigeria  .

***

Tunda suka kama hanya ta kwantar da kanta jikin gilashin , bayan ta rufe rabin fuskar ta , A zahiri ta ɗora idanun ta ne bisa kan titi da ƙura irin ta juyin yanayin shigowar bazara ke tashi daga kan rairayin hamadan dake gefen titin ,

Sai dai can cikin tunanin ta ruhi da ƙwaƙwalwarta sun zurfafa ne cikin tsinkayen makomar rayuwarta tare da rarrabe fari da baƙi ,

Tun a jiya da ta san haƙiƙanin gaskiyar kome take jin tamkar mafarki ne tayi ba ido biyu ba ,

Tayaya za'a ce Mutane biyu masu girman daraja a rayuwar ta sun yi mata irin wannan mummunan rufa-rufa ?

Ashe Baban Mama da ta ɗau duk wani aminci da yarda ta ba shi , ta riƙe shi a matsayin mafi nagarta cikin mutane ,

shi ɗin mayaudari ne , fasiƙi , yayi zina da yayarta , ya gudu ya bar ta da cikin , tsakanin rayuwa da mutuwa , sannan daga baya ya dawo yayi ƙarya ya aure ta , ? Shiyasa mana yake shiga gigita da ɗimuwa a duk lokacin da tayi yunƙurin sanin irin alaƙar da ta kullu tsakanin sa da Yakaka , ashe Azzalumi ne .

Yakaka ta cutar da ita tun farko da bata taɓa sanar da ita irin alaƙar da ta kulla har ta kai ga samar da Mama ba ,

Ashe son da Yakaka take iƙirarin tana yi mata bai kai nan ba , tunda har ta iya gudu ta bar su ita da Mama jaririya akan ɗa Namiji bata ko tausaya musu ba  ,

ta tuno irin yadda fitar Yakaka daga rayuwarta ya jiggata mata rayuwa , ta tuna irin halin ƙunci da ciwon rai da tayi fama da shi , ta tuna da cikin kowanne irin yanayi na farin-ciki ko baƙin-ciki a rayuwarta tana yin su ne tare da tarin kewar Yakaka , bata taɓa sabawa ba da rashin ta , bata taɓa daina kukan mutuwar ta ba kamar yadda cikin duk wasu sallolinta bata tashi ba tare da tayi mata addu'ar samun rahamar Ubangiji ba , da yafiyar sa .

Amma ashe wai duk tsawon lokacin nan Yakaka tana raye cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali bata taɓa waiwayar su ba ? 

kuma wai da son ranta ta bar cikin rayuwar su ?  shin wanne irin so ne maigirma haka Yakaka take yiwa Youssouf ? Babu shakka tana iya tuno kaɗan daga cikin soyayyar da Yakaka take yiwa Bature kam silum ɗin ta ,

Dan haka tun jiya ta riga ta sulluɓe Youssouf daga ran ta , take kuma kankare duk wani ɗiso na ƙaunar sa daga ran ta , tana ƙenƙesawa zuciyarta Youssouf ya haramta a gareta .

Tunanin irin cutar da su biyun suka yi ga ɗiyar su Mama yana nuƙurƙusar ran ta tare da ƙara mata baƙin-ciki a duk bayan ƴan daƙiƙoƙi ,

Cikin ƴar taƙaitatciyar Rayuwar da Mama tayi babu shakka bata yi maraicin uwa ba , ta cikace mata gurbin da Yakaka ta bari ƙarƙashin son zuciyar ta ,

A ganin ta daga Youssouf har Yakaka bata su dace da zama Iyayen Mama ba , mutuwar Mama kuma hutawarta ne daga shan takaicin gori da aibatawan mutanen duniya ,

Ta zaɓi da ta tafi ta barsu tare tunda su biyun babu abunda suka sani sai tsananin son zuciyoyinsu , su zauna tare domin su biyun ai sun dace da juna ,

Ita zata koma Maiduguri , ta roƙi Prof kan ya raba auren su da Youssouf , babu wani sauran zama a tsakanin su tunda wacce ta aure shi a domin ta bata raye a duniyar ,

Abunda yake cikinta kuma ko Mace ko Namiji nata ne , zata riƙe abunta tayi rainon sa ita kaɗai ko da kuwa zata ɗora kwanon talla ne akanta tayi yawo bakin kasuwanni zata kula da ɗiyanta ba zata taɓa barin ɗan ta yayi maraici ba Alhalin tana raye .

***

Duk tafiyarta tsakanin Niger da Nigeria ta yi su ne a halin makanta , ƙarƙashin kulawa da jagorancin Hajja , kuma a motar gida da suke sake babu wata takura ,

Dan haka bata san kome ba game da hanya , ba gani take ba lokacin da aka yi tafiyar , yanzu kuma da take ganin hanyar dusu-dusu ba zata iya fahimtar cewa an nausa da ita wata hanya ta daban ne saɓanin wacce suka saba bi ba ,

Tsakanin Niamey da Diffa tafiya ce ta yini da kwana , kusan awanni ishirin , kuma hanyoyin ba sosai suka cika kyau ba musamman idan hanya ta sauƙa ta tsakanin rairayin hamada ,  ga kuma ranar da ta buɗe sosai take bada zafi .

Dan haka a wahale sosai take ga kiɗa da ya ƙi yankewa a motar tamkar ɗan wani ƙaramin gidan rawa , waƙoƙi daga na Sa'adu bori , sai na Hajiya Sa'adatu Aliyu "Barmani mai-coge"

bayan ƙarar kiɗan ga ta muryar shi kansa Ahmadou gayu da yake bin kowacce waƙa tamkar da shi aka rereta , bakinsa ko gajiya baya yi ,

Tafiyar su tayi nisa kasancewar Amadou gayu ƙwararren direba ne , azahar tayi musu suna wucewa ta cikin garin maraɗi ,

Falmata tayi lamo a motar gajiya gami da yunwa da ƙishirwa sun kai ga jiggata ta , babu kome a cikinta sai ruwa da ƙosai da suka saya tun safe a hanya da ba wani cin kirki ta yiwa ƙosan ba .

Lokacin da Amaudou gayu ya tsayar da motar sa , a gefen titi kusa da wani wajen sayar da abinci , domin a ci abinci , ayi sallah , daga sama ta tsinci muryar sa , yana cewa ,

"Maraɗi muke , cibiyar noma da ciyar da Al'umma to ayi harama , ayi sallah a ci abinci ayi kuma gurinsa , idan da mai laruri , ya tai ya sauƙe , domin idan na danna totur , banni dakatawa nan kussa sai mun dangana da Diffa , dan hakka kowa ya ɗau shiri , yauwa .

Ji tayi tamkar ta cigaba da zaman ta cikin motar , kar ta taka ƙafar ta a ƙasa domin tunda ya ambaci sunan Maradi tashin hankalin ta ya sake hauhawa , domin idan ba ta manta ba , Maradi shine sunan garin su Youssouf , ita fa a yanzu ƙyamatar duk wani abu da ya shafe shi take yi .

ganin idan ta cigaba da zama ita zata kwan ciki , yasa ta yunƙura ta fito , zagayawa ta fara yi neman banɗaki , saboda mararta da take cike .

Bayan ta idar da Sallar da tayi akan mayafinta , sai tayi zaune jugum daga inda take tana iya hango kai kawon jama'a ko ta ina a farfajiyar wajen tamkar ƙaramar kasuwa , masu abinci da masu shayi zuwa kan masu sayar da kayan sanyi sune birjik a wajen ,

Tashin hankalin da take ciki ya hana ta ji wata yunwar kirki tun ranar rasuwar Mama , sai dai tausayin abunda yake cikinta da tasan zai samu ne kaɗai daga abinda ta ci , ya sa ta miƙe ta ƙarasa wajen wata ƴar rumfar sayar da abinci da ta ga mutane na saya sosai , tuwo ta ce a kawo mata miyar yauƙi da kuma kunu bayan ta miƙa kuɗinta ga wata matashiya .

Bata san ita kanta a matse take da son cin abincin ba sai da tayi arba da fari sol ɗin tuwon garin shinkafa da miyar kuɓewa busasshiya da aka ɗan ɗiga mata man shanu a ciki , babu laifi abincin su bai cika tsada ba da ɗan aukinsa , domin 'yan madai-daitan curi/mal-mala ne biyu kuma har da nama yanka biyu .

Da zaƙuwa ta fara cin abincin bayan ta juya baya daga mutanen da suke wajen ,

Tas ta cinye tuwon , ta É—an sha kunun gyaÉ—a da É—anyar shinkafa da yake fari sol shima ba'a cika sugar ba .

Kamar yadda Ahmadou gayu yace su yi guzuri bayan ta gama cin abincin sau kuma ta sayi gasasshen nama da ruwan roba biyu bata jinkirta ba koma mota , nan ta samu duk kowa ya dawo ita É—aya ake jira dan haka tana shiga , Gayu ya danna totur suka sake É—aukar hanya .

***

Biyamuradi Youssouf tare da Yakaka da Hajja babu inda basu nemi Falmata ba a tsuƙin unguwar suna haɗawa da cigiya , basu haɗu da ko wanda yace musu ya gan ta ba ,

Iyakar gigita Yakaka ta shige ta , hawaye da gumin zafin rana sun haɗar mata , tsoronta ɗaya ne kada Falmata ta yanke hukuncin tafiya yawan duniya , kamar yadda ita tayi , ta san halin Falmata sarai , tana da zafin rai idan har aka taɓo ta .

Tun a jiyan yadda tayi mata daman ya bata tsoro , sai dai bata yi tunanin zata iya yanke É—anyen hukunci irin haka ba , meyasa Falmata zata yi mata haka ? Meyasa baza ta yafe mata ba ?

Zuwa ƙarfe goma na safe sun gama cire rai da ganin ta , haɗuwa suka yi a falon kowannen su ya yi jugum ,

Youssouf ya É—ago kansa yana yiwa Yakaka kallon da yafi kama da harara ,

" Ina sake faɗi miki muddin ke kin ka ɓoye ta , ki fiddo ta kafin na kai ga sani da kaina,

A zuciye Yakaka ta katse shi ,

" Ka daina faɗa min maganar da bata da tushe , Falmata ƙanwa ta ce tare ka gan mu idan har ni ban ce sai ka nemo Falmata ba kai baka isa kace na sace ta ba Dan Allah ka barni na ji da damuwa ta .

"Kuyi haƙuri ku duka , lamarin ba na sa'in'sa bane mu ji da tashin hankalin da muke ciki , Babban soja ko za'a kai cigiya kafar watsa labarai ?? Abun yafi kama da sace ta aka yi idan ba haka ba ina Uwarɗakina ta san gari bare har ta fita da kan ta , to ta tafi ina ? Ita da ba lafiyar ido da ta jiki ta cika ba , O Allah gamu gareka , ka iyar muna. 
   Hajja ta ƙarasa zancen ta tana sake rafka tagumi

Tamkar an tsikareta Yakaka ta miƙe tana cewa

"muje tasha , tashar da ake hawa motar barin gari , wataƙila Falmata ta tafi Nigeria ne ,

Cikin ƴan mintoci suka cimma tasha ,  gurin da ake lodin fasinjan zuwa Nigeria suka nufa , suka tarar mafiyawan motoci sun riga sun tafi sai ɗaya ce bata kai ga tafiya ba ita ma mutane biyu ake jira ,

Babu Falmata a cikin su , dan haka Youssouf ya dunga bin Æ´an kamashon yana nuna musu hoton Falmata dake fuskar wayarsa tare da tambayar ko ta hau motar zuwa Nigeria ?

Kowa yace bai ganta a tashar ba , zuwa lokacin duk wani firgici da tashin hankali sun zana kansu ɓaro-ɓaro a fuskar sa da tayi jaa , jijiyoyin kansa kuma suka bayyana ruɗu-ruɗu , a sarari ya furta

" Fatima ina kin ka tafi ??

Dattijon ɗan kamashon da ya sa Falmata a motar Mallam Ahmadou shine ya ƙaraso gaban Youssouf da yake tsaye riƙe da kunkumin sa , sai duban gabas da yamma yake cikin rashin samun madafa,

" ance kun taho ne neman watta É—iya ko ta tai Nigeria kou ?

Cikin sarewa Youssouf ya amsa da "eh , yana share gumin goshin sa ,

"itta ce wata 'yar baƙa kakkaura mai matsakaicin tsawo tana da zanen barebari a fuskar ta ?

Youssouf da Yakaka a tare suka yi rige-rigen amsa masa da cewa "ita ce , tana ina ?
   Youssouf ya dora da nuna masa hoton Falmata domin ƙarin tabbatarwa, ya karɓi wayar bayan ya kashe idanu ya ƙure mata kallo , miƙawa Youssouf wayar yayi da yake ta bin sa da kallo cikin zaƙuwa ,

"Babu shakka itta ce wannan ta zou nan da gefen Alfijir, tana biÉ—ar motar zouwar jahar Borno Nigeria dagga nan kai tsaye , nan nayi mata togaciyar kan nisan dake tsakanin Niame....

   "Baba ina take yanzou ? Ta tahi ne ko kuwa tana ina ?

A kaikaice dattijon ya dubi Youssouf da ya katse masa hanzari , ya ɓantari goron sa kafin yace

  " ta taihi tun motar farko dagga nan kai tsaye zouwa Borno ta yankin diffa zasu ɓulla Nigeria zuwa yanzu wataƙila sun kusan cimma sandamun Maraɗi , ai Ahmadou gayu zaƙaƙurin direba ne ,

  " nufin ka dagga nan Fatima ta tai Borno ta yankin Diffa ? Yankin da yake cike da hatsarin ƴan tawayen Boko Haram suna kama mutane suna garkuwa da su bayan sun kashe wasu ? Bodar da take a rufe , sai ta ɓarauniyar hanya ake bi ? Shine kun ka turata baku hanata tafiya ba , ba kuyi yi la'akari da ƙarancin shekaru gami da rauninta na ɗiya macce ba ?

Wani irin raruma ya kaiwa Dattijon kafin ya ankara ya É—ago shi , cewa yake ,

  "ko waye direban kayi ƙiransa maza ya dawo da matata , kadda ya yarda ya jefa rayuwarta ga wannan mummunan hatsarin da kai da shi da zuri'ar ku baki ɗaya sai na ɗaure ku muddin wani mummunan abu ya afku ga matata ,

Da kyar mutane suka ɓanɓare hannuwan Youssouf daga wuyan dattijon nan da kawo lokacin numfashin sa ya fara ƙaƙarewa ,

Da ban baki gami da lallashi jama'a suka danni Youssouf ya nutsu aka nemo number Ahamdou gayu aka bashi ya shiga ƙira jikinsa sai tsuma yake ,

Da kyar ya samu wayar ta shiga , sai dai ko da aka ɗauka waƙar Barmani Mai-coge ce kawai take fitowa tarwai ta cikin wayar sai kuma iska irin na hanya ,

  Ya dunga "Alo , Alo , Alo ,
Bai ji muryar kowa ba , ya kashe ya sake ƙira nan ma an ɗaga amma "Alo, Alo , kawai ake cewa daga ɗaya ɓangaren , duk maganar da yake yi ba'a jinsa ,

Haka ya dunga ƙira cikin gigita tsawon lokaci ba'a ɗagawa daga baya ma daina shiga wayar tayi , cikin tashin hankali ya ɗago kansa , sai dai duk mutanen da suke tare a wajen ya tarar babu ko guda sun watse, sai fa Yakaka da take durƙushe a ƙasa tana hawaye sai kuma Hajja da take tsaye ta rafka tagumi idanunta da guntayen ƙwalla ,

Rasa wanda zai sake tunkara yayi , dan haka suka jiyo gida idan banda kuka babu abunda Yakaka take yi , jin cewa Falmata ta hau hanya mai tattare da hatsarin Æ´an Boko Haram , ya kaÉ—a Æ´an hanjinta ,

Zuciyarta ta cika da tsoron sake rasa ƙanwarta , Youssouf ma tunda suka dawo gida kai tsaye sashinsa ya shiga yana sake gwada ƙiran layin Ahmadou gayu , sai dai har chajin wayarsa ta kai ga sauƙa bai samu nasarar sake samun layin ba ,

Ajiye wayar yayi lokacin da wasu hawaye masu zafin gaske suka sauƙo masa a karo na biyu cikin tarihin rayuwar girmansa , yayi kuka .

***

Su Falmata sun kwana a wani ƙaramin gari dake yankin zinder kusa da garin Diffa , anan suka yada zango , cikin motar ita ta kwana yayin da sauran mazan suka fita ba tare da ta san ina suka yi ba .

Asubar fari bayan tayi Sallah , suka sake damƙar hanya , tafiyar yini guda ta kai su ga kaiwa ƙarshen yankin diffa ta gabashi , inda suka sau hanya tare da nausawa cikin daji  ,

Gudun da motar take alhalin kan tuddai da kwari ne yasa motar take buga tsalle lokaci zuwa lokaci , da hakan yasa cikin falmata ya wani irin riƙewa tare da fara yin ciwo , ga buguwar da jikinta yake yi da motar , gami da warin sigari da bata san yaushe ya gauraye motar ba yana ƙoƙarin sanyata haraswa .

Duk da bata gani sosai ta fahimci dare yayi saboda duhu da ya mamaye É—an guntun hasken da idanun ta suke iya gani , ya zama dilum bata ganin kome .

Sun kai kimanin awanni biyu a daji suna wannan gudun kafin ta ji motar ta tsagaita gudu , ta tsaya a hankali ,

Hasken da ya dallare mata idanu mai ƙarfi ne da yasa ba shiri ta jaa hijabin ta ya rufe mata idanu , gami da runtse idanun .

Tana jin lokacin da duk na cikin motar suka fita harda shi direban , a hankali ta buÉ—e idanunta ta cikin motar tana iya ganin mutanen wajen dusu-dusu da taimakon hasken wasu manyan dogayen tociloli da suke hannuwan wasu gungun mutane ,

Abunda ya bata mamaki bai wuce ji da tayi sun juya harshe cikin yarenta ba na kanuri , tar-tar suke magana da Ahmadou gayu da sauran mutanen cikin motar da tunda tafiya ta haÉ—a su bata ji sun cika hira ba ko da kuwa a tsakaninsu ne , bare har ta fahimci yare su É—aya ..

Ba sosai ta kai ga Fahimtar maganganun su ba , har kawo lokacin da suka ƙaraso wajen motar , da hausa Ahmadou gayu yace ta fito za'a ɗau saƙo daga ƙarƙashin kujerar da take ,

Cikin sauri ta ziro ƙafar ta waje ta fito , cikin rashin sa'a ta gurɗe ta kusa faɗuwa ,

'yarinya ki kula ,

Cewar Ahmadou ,

Muryarta na Æ´ar rawa tace

"Baba inada matsalar ido bana gani idan dare yayi wajen babu ramuka ko ?

" Au to to ashe ma musaƙa ce , to babu laifi , ai daman irin ki ake so marasa idon yarinya yau makantar ki ta miki rana , ko kuwa ?

Ya juya ga mutanen da suke bayan sa yana tambayar su ,

amma babu wanda yace ƙala a cikin su , biyu daga ciki suka matsa jikin motar tare da fara ɗaga cikin ramukan kujerun motar suna fito da wasu ƴan madai-daitan kwalaye da basu cika girma ba ,

Falmata da ta durƙusa tana ɗan murƙususu saboda marar ta da take mata ciwo , ta cikin hijabinta tana iya hangen kwalayen da bata san da su ba a motar  kafin zuwa wani lokaci an tara su da ɗan yawa ,

Ɗaya daga cikin mutanen da fuskar sa ke naɗe da mayafi ya sunkuya tare da ɗaukar Ammo box ya buɗe ya zazzago wasu alburusai da suke ciki a jere , hannu ya miƙa na gefen sa ya miƙa masa tocilar hannunsa , ya haska harsashin sosai yana jujjuya shi a hannun sa ,

Cikin Falmata ya bada wani sautin ƙululu lokacin da ta ga an miƙo masa bindiga ya zura harsashin a ciki , wani irin tsoro mai girma ya ziyarceta , meye yaje shirin faruwa da ita ? aina ma wai take ?

Magana suka fara yi bayan sun É—an yi gaba kaÉ—an da inda take tsugunne ba tare da wani ya kulata ba daga cikin su ,

Tsantsar tsoro yasa ta daina fahimtar me suke cewa duk kuwa da cewa da yaren da tafi fahimtar sa bisa ga sauran yaruka suke magana  , idanunta sun fir-fito , bindigogin hannuwansu kawai take bi da kallo da zuwa lokacin ta lura fiye da rabinsu suna riƙe da bindiga .

Da É—aya-É—aya suka jide kwalayen , tana ganin lokacin da suka É—aga kujerar da take baya suka maida wata jakar bacco gurbin da suka cire kwalayen ,daga haka ta ga sunyi musabaha tsakanin Ahmadou Gayu da wasu daga cikin tawagar ,

Da gudu-gudu suka hau bayan motocin su ,suka tada tare da nausawa cikin daji .

Amadou gayu ya ƙaraso kanta lokacin da yake cewa ,

" 'yar dindimi sai ki tasso mu tai na sauƙe ki daga bakin hanya inda zaki iya samun motar da zatta sada ki da cikin garin Maiduguri ni iyakatai bakin daji kome da kin ka ji motsi nai anan ki manta da sautin anan muddin kin biɗarwa kan ki lahia , kin ji kou ?

GyaÉ—a kai Tayi da sauri , ta shiga motar suka sake nitsawa cikin daji , sai lokacin ta lura babu kowa a motar sai su biyu , ko ina sauran mutane huÉ—u na bayan motar ? Ta tambayi kan ta .

**

Ƙarfe sha ɗaya na safe yayi mata a cikin babbar tashar garin Maiduguri , bayan Ahmadou gayu ya sanya ta a mota daga ƙaramar hukumar Mobar da ta kawo ta cikin garin .

Duk tayi busu-busu da ita ta fita hayyacinta , yunwa da firgici sun maida ita firka-firka , amma duk da haka .

Hamdala ta dunga yi lokacin da ta samu tabbacin tana cikin garin Maiduguri ne ta samu ƙubuta daga hannun mutanen da tun-tuni ta fahimci ko su waye su .

tunanin inda zata dosa kuma ya rufe ta , domin ita dai bata san takamai-mai sunan unguwar gidan Prof ba , duk rayuwar ta cikin garin ta yi ne a halin tana makauniya ,

Wata rumfa ta hango ana tuyar doya da ƙwai a bakinta,  ta ƙarasa ta zauna daga ƙasa tana kallom mutanen wajen da fiye da rabin su maza ne hatta mai tuyar da mai rabawar duk samari ne ,

Da zamanta a wajen , wani matashi da ya ciko ɗan farantin roban hannunsa da soyayyar doya mai kwai , ya mata duban ƙasƙanci , kafin ya ajiyewa wani mutum doyar a teburin gaban sa , ya ƙaraso inda take

"Ke baiwar Allah ki tashi daga nan , idan bara za kiyi ki shiga cikin tasha ko kuwa ki nemi wani wajen amma ba nan ba wajen sana'ar mutane .

'kayi haƙuri dan Allah hutawa nake yi , ga kuɗina ka bani abunda kuke sayarwa na duka ,

Ta miƙa masa kuɗaɗen da bata san adadinsu ba da ta zaro daga cikin jakar hannunta ,

Kallon kuÉ—aÉ—en da bana Nigeria bane ya yi , kafin yace

"waÉ—annan takaddun fa ? KuÉ—in ina ne ?

Kafin ya rufe baki ubangidansa ya ƙwalla masa ƙira

   " Bashari wai kana ina ne ?wannan wanne irin tsagoron zunzurutun walaƙanci ne zaka tafi hirar banza ka barni da ayyuka , to wallahi idan har ƙazar nan ta ƙone a mai , na rantse sai ka biya ni dan ni da asara kullum saɓani muke .

Da sauri Bashari ya bar kan Falmata ba tare da ya karɓi kuɗin da take miƙa masa ba ,

Ya ƙarasa da gudu wajen ogan sa ,

"kayi haƙuri oga wata mata ce kamar mahaukaciya dai haka ta zo da wasu kuɗaɗe kamar na landan a hannunta wallahi oga wai ta miƙa min su na bata doya , kuma kuɗin dayawa oga

Da sauri ÆŠanliti ya saki matsamin da yake hannunsa acikin mai ba tare da ya tsame doyar ba ,

"kai Bashari na fa sanka da sakin ƙwai , kuɗin landan fa kace ? Dala fa kenan ? Yau a masu sayen doyar tawa har da masu Dala ? Ina take ? Nuna min matar ?

Nuno masa Falmata yayi da har lokacin take takure a zaune ,

Cikin ƴar marairaicewa Ɗanliti ya kwararo mata sallama , da sauri ta ɗago kanta jin muryar wanda ta taɓa sani a baya ,

Suka yi arba da fuskokin juna, shirun ƴan wasu daƙiƙoƙi suka gifta kafin Falmata ta miƙe tsaye da sauri tunowa da tayi da ko wanene Ɗanliti.

' wa nake gani haka kamar un-un Ɗankachallari ?  Wai kece ko kuwa kamanni ne ? Ah ai babu zancen kamanni ma ga ƙwala-ƙwalan idanun nan daga ina kike ƴarkachallari haka kamar 'yar bina ?

Muryar ta na É—an rawa , tace

" Ba sunana ba kenan , sunana Falmata ,

' haka fa ashe sunan ki kenan , to dawo daga nan a kawo miki doya ki ci ki sha ruwa ko kya samu nutsuwa , na ga yunwa na tanɗar bakin ƙirshirwa a fuskar ki .

A ɗarare ta zauna a inda yake nuna mata kan wani benci , aka kawo mata zazzafar doya da ƙwai har da dafaffen ƙwai guda biyu da aka soya su da ƙwai ,

Tas ta cinye ta sha ruwan leda biyu , tayi hamdala

ÆŠanliti da yake gurin suyar sa ya bari tare da sake dawowa yana sake tambayar ta daga ina take ?

A takaice ta faÉ—a masa daga inda take , daga haka tayi shiru

ÆŠan jimm yayi yana kallon ta , kafin yace

" wai , tabÉ—i yanzu nan daga Niger kike ? shiyasa mana na ga kin koma busu-busu , ashe rairayin hamada ne ya turbuÉ—e ki , ai kin ma kaima barka da sahara bata haÉ—iye motar ta ku ba kamar yadda nake ji ana labari wai-wai , koda yake da kuma kun yi mutuwar shahadar nan da kowa ke nema ,

" nima kin ga ai yanzu duk na tuba na daina abunda yake jawo min tsinuwa , na kama Æ´ar sana'ata da nake rufawa kaina asiri da ita , aure ma nake shirin yi , O ni ÆŠanliti mutuwar Saly Fara ta zamanto min alherin da na samu shiriya a domin ta ,

  Ya ɗaga hannun biyu sama , yana ƙara cewa
      "Allah na ƙara gode maka da ka kashe Saly Fara ni kuma ka shiryar da ni .

Shiru Falmata tayi tana sauraren bayanin da bata nemi jinsa ba , ji tayi ya cigaba da cewa ,

" ai Æ´ar danginku ma zan aura wallahi kuwa ,

ÆŠago kanta tayi ta dube shi ,

"Æ´ar dangin mu ? Tambaye shi da mamaki ,

" eh Ƴar uwarku Yagana ba , ni kuwa ina Yakaka wallahi habibiya tana nemanta ruwa a jallo tace tayi ta zuwa gidan da kuke bata samun ku , can gidan wani mutum mai kuɗi wai a Danboa road ko ina ?

Da sauri Falmata tace ,

  "Ina Yagana take ? ta san gidan Prof ? Ka kaini wajenta ta kaini gidan Prof ,

Kwantar da hankalin ki indai habibiya kike nema kin same ta tunda kika ganni , nan da mintoci talatin ma zaki ganta anan ta zo , ai tare muke sana'ar mu , ita take yi mana wanke-wanken farantan kayan sana'a , kinsa rayuwar nan cuÉ—anni na cuÉ—eka ne .

****

Yagana ita ta sada Falmata da gidan Prof da misalin ƙarfe biyu na rana , har falon prof ta so shiga da ita sai dai aka hana su saboda yana tare da baƙi , amma an musu iznin shiga ciki sashin matar gidan domin su jira shi .

"Falmata ai tunda na kawo ki ni zan iya tafiya ko ?

Yagana take neman iznin Falmata bayan sun kawo ƙofar sashin su Rahima ,

"Yagana , Nagode , Nagode zaki iya tafiya ,

"Babu kome Falmata ai mun zama Æ´an uwa banda sharrin shaiÉ—an da ya rinjayeni a baya na aikata kuskure , Dan Allah idan Yakaka ta dawo zan zo na nemu gafararta ta yafe min .

Nan suka yi sallama ,ba tare da Falmata tasan wanne kuskure Yagana ta aikata ba da take neman yafiyar Yakaka ,

Jikinta babu ƙarfi ta nufi cikin gidan , a zuciyarta tana saƙa yadda zata yi ta tunkari Prof da zancen ya raba aurenta da Youssouf batare da ta bayyana mummunan laifin da suka aikata ba shi da Yakaka ,

Saboda bata so wasu su dubi Yakaka da wannan mummunan laifin , zata zama abun aibatawa a wajen Al'umma ,

A hankali ta tura ƙofar falon ta shiga sanyi da ƙamshi mai daɗi ya buso ta , daga ciki kaɗan ta tsaya tayi sallama da zazzaƙar muryarta ,

Cikin nutsuwa matar da take zaune a kan ɗaya daga cikin sabbin kujerun falon tana saƙa da zaren ul da kwarashi, ta ɗago kanta , idanun ta suka sauƙa akan Falmata da itama take iya hango alamun farar fatar ta daga inda take ,

Muryarta bata fita sosai ta amsa sallamar ,

Su dukkanin su shiru suka yi suna kallon juna ,

Cikin sanyin jiki falmata ta kalato murmushi ta É—ora bisa fuskar ta, zuciyar ta na bata cewa Rahima ce wannan take hangowa A hankali tace

"Rahima ni ce fa, ni ce Falmata ƙanwar Yakaka baki gane ni bane ?

Kwarashin hannun Khaalty Rahima ya faɗi ƙasa bata kula ba ta miƙe tsaye ta nufi inda Falmata take , zuciyarta na bata tabbacin cewa mafarki take , wataƙila kuma gizo take yi mata ,

Tana zuwa ta miƙa tafukanta biyu ta dafa kafaɗun Falmata idanunta suna jiran ɓacewar ta daga ganinsu ,

Ƴar dariya Falmata tayi , kafin tace ,

"Rahima kina mamakin gani na ko ? Yakaka ma ai tana zuwa wataƙila gobe zata iso ba tare muka zo ba Rahima....

Hannun Rahima da taji yana tattaɓa mata fuska , yasa ta haɗiye sauran kalmomin ta , ta riƙe hannuwan tana ƙoƙarin sauƙe su daga fuskarta , da wani irin sauti ƙasa-ƙasa , Khaalty Rahima tace

"Falmatana ke ce ? Ke ce wannan Falmata ? Ke ce ? Ina Yakakana ?

Rungumo ta tayi gaba É—aya zuwa cikin jikinta tana fashewa da kuka mai sauti ...

Assalamu Alaikum masu karatu .

Da fatan duk kuna lafiya ??

Ina mai baku haƙurin ji na shiru da kuka yi wasu hidindumu ne suka sha kaina , da fatan kun min uzuri ? ❤

Nagode .
[12/16/2019, 6:36 AM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

45

Da rashin yadda a fuskar Falmata , ta ɓanɓare jikinta daga na khaalty Rahima , Muryar ta na ɗan ƙyarma tace ,

"wacece  ? Rahima kece ?

Zuwa lokacin Murmushi Khaalty Rahima take , murmushin da har ya bayyana haƙoranta , sake riƙe hannun Falmata tayi , da sautin muryar ta mai ɗan ƙarfi tace , "Falmatana ni ce Mamar ku , ni ce , ashe kuna raye Falmata , ina Yakaka ?

Da wani irin yanayi Falmata take sake wara idanunta tana ganin dusu-dusun fuskar matar da take gabanta , tana jin wani irin bugu da zuciyarta ta sauya a take da ziyarta ruÉ—ani a tare da ita tace, "Mama na ? Ke ce Maman mu ?
   Sai tayi baya da sauri kamar zata gudu , ta waiga dama da hagunta , da wani sauti tace , "Yakaka ina kike ? Kina ina ? Ki zo ki ganta wai wannan Maman mu ce ? Wai da gaske ita ce ?

Murmushin fuskar Khaalty Rahima bai ɗauke ba lokacin da hawayen fuskarta suke cigaba da sauƙa ta matsa tana sake kusantar ta , sai ta miƙa hannu ta jaa hancin Falmata da bai wani ciƙa tsayi ba , ta zarce da riƙe kumatunta duk biyu da hannuwanta , sannan ta haɗa goshin su guri guda , tana sake cewa ,"Ni ce Mamanku Faɗimah-Zahra ni ce Ina Amina ?

Wani irin yanayi ne na zallar Farin-ciki mai tafe da sanyi mai samar da nutsuwa ,  taji yana bin duk wata jijiyar jikinta , a sanyaye ta karkata kanta , muryarta da rangwamen sauti tace ," Maman mu ke ce ? Ke ce Mama da gaske ba mafarki ko gizo ba ? Mama daman kina Raye ? Mamana .
   Bata jira ta amsa mata ba ta zarce da rungumeta ,tana sakin kuka da ƙaramin sauti , irin kukan da Ɗa yake irin sa a lokacin da ya tsinci kansa a gaban Mahaifiyar sa bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗiyar baƙin-ciki cikin kewar ta .

  Khaalty Rahima ta sa hannu biyu ta rumgumeta , tana jin wani irin tarin farin-ciki marar misaltuwa , ashe daman rayuwa zata sake iya yi mata sauyi mai tattare da farin-ciki irin wanda ta fidda rai da samun sa , ashe watarana zata zo da zata sake ganin ƴa'ƴan ta ? Allah abin godiya .

   Sauƙowar Amnee daga Sama ita ta jaa hankalinta, da mamaki ta ƙaraso tana kallon su , da har zuwa lokaci , Falmata take kwakume da Mamanta bata bar kuka ba , da alamar tambaya a muryarta tace

   "Ukhtee Rahima me ya faru ? wacece wannan ?

, jin sautin muryarta yasa Falmata ɗago kanta , kafin ta bi bayan Khaalty Rahima da take riƙe da hannunta , suka ƙarasa gaban Amnee , da murmushi Khaalty Rahima ta haɗa hannun Falmata da na Amnee , tana cewa

   " wannan ita ce 'Ya ta Falmata da na baku labarin su ina zaton sun mutu ita da yayar ta mai sunanki Amina da ake mata laƙabi da Yakaka , ikon Allah da girma sai ga shi ya kawo min ita har gabana .
     Sai ta waiga ga Falmata , tare da cigaba da cewa , "Fatima ya akayi kika san ina nan ?

  Da bayyanuwar murna Amnee ta zarce da rungume Falmata , kafin ta ɗora da cewa , Alhamdulillah , Alhamdulillah , ashe ba haka nan ba na so yaran nan tun a rana ta farko da na fara ganin su , ace 'ya'ya nane , jini na , 'ya'yan 'yar'uwa ta , Ukhtee Rahima ai nasan Fatima da Yakaka tun shekarun baya suke rayuwa tare da 'yan uwansu a gidan nan ba tare da sun san dangantakar su da juna ba , kai Alhamdulillah .

Saman kujerun wajen suka zauna ,suna sanya Falmata a tsakiyar su , khaalty Rahima ta ce ,

     "Ikon Allah Ukhtee ashe ma kun san su ? Ashe suna hannun ku ?

    " ƙwarai na san su , ai yayan Zainab ( Doctor Hamza )  shine ya kawo su gidan nan a matsayin ƴan gudun Hijira , a gidan nan suke tsawon shekaru kusan biyar zuwa shidda  ,  ikon Allah kenan ai kuwa  ko zuwan Yakaka na kwanan nan taje har wajena ta gaishe ni ,  ai itace wacce kika ji na tambayi Rahima shekaranjiya kan ina take ta shaida min ta tafi Niger wajen Ƙanwar ta da 'yar ta , Allah ya saɓa haɗuwar ku ai da gidan nan zaki tarar da ita .

   "Ikon Allah ,  to Alhamdulillah , Alhamdulillah , sune kalmomin da Khaalty Rahima take faɗi farin-ciki na sake gauraya ta , ji da tayi ashe ma 'ya'yan ta gida suka dawo , ashe ma tare suke da yayun su , ƙarƙashin kulawar mutumin da yake mazaunin Uba a wajenta , Babu shakka tare da dukkanin tsanani akwai sauƙi , kuma ba'a fidda rai daga Rahamar Ubangiji .

  A kusan tare suka jefawa Falmata tambaya ,
    "Fatima ina Amina da 'yar ta ?

Shiru Falmata tayi da famin raunin cikin ranta , a hankali ta ce da su ,
    "Allah ya yiwa Mama rasuwa kwanaki huɗu da suka wuce ,
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon,  Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon,"  suka haɗa baki wajen cewa , shiru kuma ya gifta tsakanin su cike da jimamin rashin jikar su da basu kai ga samun damar ko da ganin fuskarta ba a zahiri , babu shakka Allah baya barin wani domin wani ya ji daɗi .

   " Ina Maisunan Ukhtee ita kuma ? Ba wajen ki ta tafi ba ?

      Ƙhaalty Rahima ta sake tambayar Falmata ,
   Shiru Falmata tayi tana sunkuyar da kanta ,

  Wani busasshen yawu Khaalty Rahima ta haɗiye tana jin tashin hankalin da yake farmata , kada dai ace wani mummunan lamari ne ya afku ga ɗiyar ta mafi soyuwa gareta ?

    Matsa hannun Falmata dake cikin nata tayi da ɗan ƙarfi , ta ɗan ɗaga sauti tana sake maimaita tambayar " Falmata ina kika baro Yakaka ??

***

A Niamey tunda Yakaka ta dawo daga tasha , bayan samun tabbacin Falmata ta riga ta tafi Nigeria ta wannan mummunar hanyar mai cike da hatsarin Æ´an kungiyar Boko Haram ,

bayan kuka babu abunda take yi , gabadaya ta ɗora laifin gudun Falmata akanta , tayi danasanin zuwanta ƙasar baki ɗaya yafi a ƙirga , ganinta da ace bata zo ba da Falmata bata gudu ba , sai ta ji inama da ta zauna akan batun Youssouf da yace su rufa asirin tsakanin su kada Falmata ta sani a tun farko , ƙila da suna da damar da zasu haɗu ita da Youssouf su wanke kansu a wajen Falmata bayan sun ƙaryata ƴan uwansa a gabanta ,  da kuma lamarin bai kwaɓe ya haka ba ,

Ganin kuka ba zai mata magani ba yasa ta miƙe tsaye ɗauke da jakar kayanta , Hajja wacce take zaune zugum ta dube ta tare da cewa ,
     "Babba uwar Mama ke kuma ina za ki ? Kadda kice min kema gudun fanfalaƙin za kiyi ? Kiyi wa Allah ƴar nan ki tsaya mu ji da damuwa ɗaya kadda ki ɓaro mana wata sabuwa , guje-gujen nan ba kana bane , 'ya'yan nan ai ƙwarya ta gari tana ragaya , kamar yadda darajar ɗiya mace ɗakin Mijinta kar ki tafi ko'ina Dan Allah ,

Ba tare da Yakaka ta dubi Hajja ba tana share hawayenta da gefen hijabinta tace ,

"Hajja gara na tafi saboda Falmata fa ko da taje Maiduguri lafiya , bata fa san hanyar gidan Baa prof ba, kuma bata san kowa ba a garin bayan shi , dole zanyi hanzarin tafiya nima ko Allah zai sa na haɗu da ita a tasha , na tarye ta Hajja ina ƙaunar Falmata ita ce kaɗai jinina a duniya ina tsoron rasa ta Hajja , zan tafi bazan iya zama ba nima .

Guntuwar ƙwallar da ta tarawa Hajja a ido ta sa hannu biyu ta shafe fuskarta ta muttsuƙe ,

" To Shikenan Yakaka tunda kin ce haka bari nima na haɗa ƴan kananun kayan buƙatu na mu tafi tare , ai nima zama bai ganni ba , to na zauna nayi me ƴar nan ? Ai tunda ganga ta fashe sai ƴan rawa su watse ,

Da hanzari Hajja ta shiga harhaÉ—a kayanta, tana cewa ,
       "bari na tafi da waɗanda dole zan iya buƙatar su , sauran kuma idan Allah ya min dawowa na cigaba da Amfani da abuna idan kuwa ma tafiyar kenan , to a biyo ni da tsunmokara na , wannan lamari dai da ɗaure kai yake babu shakka da walakin wai goro a miya .

Yakaka da har lokacin a tsaye take akan ƙafafunta bata ce da ita ƙala ba ,

Cikin ƴan mintoci kaɗan ta haɗe kayanta a cikin wata babbar jakar matafiya da Youssouf ya taɓa saya mata , tana shirin yafa mayafinta suka tsinkayo sallamar Youssouf daga ƙofar falon , Hajja ta amsa tana nufar falon

A tsaye ta tarar da shi shirye tsaf cikin riga da wondo na kaftani da ya sha aiki irin na saraki , ba tare da ya yadda Hajja ta ga ƙwarar idanunsa ba fuskarsa babu walwala ko kaɗan sai tarin damuwa da tashin hankali da suka bayyana kansu ɓaro-ɓaro , cikin Amonsa da a yau ya sake kaurara da buɗuwa yace
    "Hajja ni zan tai Maraɗi yanzou Hajiya Umma tai ƙirana , don Allah ku zauna a gida har na kai ga dawowa nan da kwanaki biyu , lamarin Fatima kouwa zan yi dukkanin ƙoƙarina da Yardar Allah babu abunda zai samu Matata da abinda ke cikin ta .

ÆŠan karkata kai Hajja tayi da sigar tausayawa tace ,

" Babban soja Allah ya tsare hanya , sai dai kuma yanzu na gama fama da ita yayar Falmata kan cewa da tayi a yanzu itama za ɗau hanyar Nigeria saboda ko Allah zai sa su gamu da ƴar uwarta a tasha idan sun isa Maidugurin dan ita Maiɗakin naka ai kasan bata san ko'ina ba a can ko gidan shi mariƙin nasu bata sani ba , ana gudun kar ta ɓata ko ta shiga wani mawuyacin hali kuma a can , da naji haka sai nace to fa nima zama bai kamani ba tare zamu tafi , to kaga shirin nan da nayi ma na tafiyar ne ga kayana ma can na haɗa su gu ɗaya .

Bayan ya gama sauraron Hajja da tayi shiru tana tsumayen iznin sa , sai yace ,
    " hakka ma shawarace mai kyaou Hajja , to idan hakka ne ku taho na sauƙe ku ga tasha na sanya kou a mota , nima sai na tai gida ,

   "Amma Hajja doumin Allah dagga kun cimma gida kun tadda Fatima ki sanar min ta téléphone , sabadda na san halin da kuke ciki a can , duk da nima ba da jimmawa ba zan tai can Nigeria ɗin , kuma a nan sojin mu zasu yi bakin ƙoƙari wajen duba hanyar da ita Fatima zasu bi , sai dai kouma idan har ta ɓarauniyar hanya ta daban zasu ɓulla yanzou fatan mu dai yana ga Fatima ta cimma gida lahia .

" to babu laifi Babban soja ai sai mu tafi ɗin , Allah dai ya sassauta wannan lamari , bari na ƙira ita Yakaka ,

Mota É—aya suka tarar wacce zata tafi Kano kai tsaye daga Niamey dan haka Youssouf ya biya musu gidan baya na motar su biyu rak da daman mutum É—aya suka tarar a gaban motar dan haka nan take aka shiga neman direba ya zo kuÉ—in kujerun mota sun kammala ,

Laluba aljihunsa yayi ya fiddo kuɗaɗen ciki da baki ɗaya CFA ne , mayar da su aljihunsa yayi saboda sanin da yayi daga sun bar shiyar ƙasar su ba zasu musu wani amfani na sosai ba , ya zaro wallet ɗin sa da dalolin Amurka ke ciki a miƙe , ya matsa kusa da gilashin motar da yake sauƙe ta sashin da Yakaka take ,

Ba tare da ya dubi fuskar ta ba yake miƙa mata kuɗin da bai riga ya ƙirga ya san adadinsu ba ,

Yakaka wacce tunda ta shiga motar ta ɗauke kai daga barin kallon sashin da yake tsaye , amma tana ankare da shi ta kuma ga tsayuwar sa akanta yana miƙa mata ƙudi , bata son sake kallon fuskarsa ne dan haka taƙi ɗago kanta ,

Hajja wacce take raba ganinta a tsakanin su biyun , ta É—an zunguri Yakaka ,

  "Babba uwar Mama , Babban soja yana baki saƙo ,

  Da wani irin yanayi na gargaɗi a fuskarta ta kafe Hajja da idanunta da suke da kaifin kallo masu kamar gilashi ,

  Galala Hajja tayi tana mayar mata da martanin kallonta , sai kuma ta muskuɗa ,tana cewa

"Ajabba inji kanurai, o ni hauwa'u ,
   sai kawai ta maida ganinta can gefe tana kyeɓe baki .

A hankali Youssouf ya zura hannunsa kaɗan ta cikin motar ya sauƙe mata kuɗaɗen akan cinyarta yana cewa "Hajja Allah shi kiyaye muku hanya don Allah Hajja duk yadda lamari ya kassance muku ki jisheni ,

" Amin Amin Babban soja , da yardar Allah zan sanar da kai duk yadda ake ciki , kaima kuma Allah ya tsare maka hanya , mungode , mungode sosai Allah shi yiwa rayuwa Albarka .

"Amin Hajja nima nagoude , yace yana kama hanyar barin wajen ,

Yakaka wacce tunda ya ajiye mata ƙuɗin ta runtse idanunta tana tuno da lokaci na farko a haɗuwarsu , yadda ya ajiye mata kuɗin da ya sayi martabarta da su akan cinyarta ya haka ,

    Hannunta ta kai tana ture kuɗin da ya ajiye mata a yau zuciyarta cike take da rauni mai tarin yawa , sanin da tayi a yanzu Youssouf ya haramta a gareta , ta kuma Haramtawa kanta shi koda kuwa babu ran Falmata .
      Tashin ƙugin motar su yazo dai-dai da sauƙar hawaye a idanunta , haƙiƙa so gaskiya ne , so halitta ce da Allah yake sarƙawa a tsakanin zuciyoyin bayin sa domin ya samar da Salama a tsakanin ƴan Adam , yafiya , haƙuri tare da tsusayawa tafe suke a cikin so na domin Allah ,

Babu shakka Youssouf shine mutum ɗaya da Allah ya ɗarsa mata son shi tun bata san menene so da kansa ba , ta kuma so shi ba domin kome da ya mallaka ko ya taɓa mallaka mata ba , cikin rashin sanin ta jarrabawa ce Allah yayi mata kan soyayyar sa ,

   Tun ranar da ta san laifin da Youssouf yayi mata kan Yaudarar ta da yayi ya ɓata mata rayuwa bata taɓa jin tsanar sa tsana irin ta ƙiyayayya ba , sai dai ta ji tsanar shi bisa ga laifin da tasan ya aikata mata, take kuma neman yadda zata yi ta hukunta shi domin ta goge wannan tsanar da tayi masa a dalilin laifin sa ,

Dawowa da tayi ta tarar ya auri Falmata , ya rugurguza mata zuciya , lamarin ya girgiza ta fiye da duk wani abu da ta taɓa cin karo da shi cikin rayuwarta ,

Tashin hankalin da ta hango tare da Youssouf lokacin da tayi tattaki ta same shi take masa togaciyar ya saki Falmata , tare da tirjiyar da yayi mata sun shaida tare da bata tabbacin cewa Youssouf yana son Falmata , so kuma mai  tarin yawa , abunda ya kassara mata duk wani karsashin ta ,  ya kuma ƙara mata hau-hawar ɓacin rai ,zuciyar ta ta shiga tuhumar ta kan yaya zai yi mata haka ?

Rana ta farko da ta san da tabbatuwar cikin jikin Falmata sai ta ji ta tsani kanta tana kuma tir da zuciyarta da ta gagara yakice shi baki ɗaya daga cikinta , alhalin tuntuni ya zama mallakin ƙanwar ta ,

A yau saƙo-da-lungu take bi tana zaƙulo duk wani ɓurɓushi na son sa tana zarewa daga cikin ranta  , duk wani gurgun tunani ko hasashen da ta dunga yi a baya na zasu dawo suyi rayuwa tare da ita da shi da ɗiyar su har ma su haifi wasu ƴa'ƴan ,  yana zagwanyewa tare da gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta , ta rabu da Youssouf da sunan so kamar yadda Allah ya rabata da Mama ,

Youssouf ba nata bane ,  ya taɓa zama nata ne kaɗai akan shimfiɗar da shaitan ya shimfiɗa musu .

Youssouf na Falmata ne tare da Æ´a'Æ´an da zasu haifa nan gaba da kuma sauran matansa ,

Takurewa tayi a jikin ƙofar motar tamkar zata tsaga ta koma ciki saboda wani irin zogi da zuciyarta ke yi , babu shakka cikin sadauƙarwar soyayya ta gaskiya akwai ciwo mai tsanani .

***

Ya juya tare da tarin tausayinta cikin ransa , yaso ko da sau É—aya ta bashi dama ya nemi yafiyar ta bisa ga laifin da shi yasan ya aikata mata , har abada ita ai uwa ce ga É—iyar sa mafi soyuwa a gare shi , bai so ba suka sake yin rabuwa makamanciyar ta farko ,

A shekaru da girma gami da hankali nashi irin na cikakken Namiji , ba sai ita ko wani ya taɓa faɗa masa cewa tana son shi ba so kuwa mai tarin yawa da shi yake iya hango shi a kwance cikin idanunta ɓaro-ɓaro koyaushe ta dube shi , 

Sai dai shi da ita dukkanin su sun faÉ—a ne ga jarabawar rayuwa , kuma shi bai mata so irin na auratayya ko kaÉ—an , sai dai yana tausayawa mata sanin yadda ciwon so yake ,ga wanda duk Allah ya jarabta .

gefe guda kuma yana jinjina Yakanah irin tata da bata taɓa furta masa kalmar so a gaban sa ba ko sau ɗaya , ta kuma yi ƙoƙarin dannewa ta ɓoye hatta ga shi kansa bata yadda cikin saninta ta nuna abunda ke binne cikin ranta ba , bare kuma ga ƙaunarta da yasan abadan baza ta taɓa bari ta fahimata  , daga ƙasan ransa ya furta "Madallah da ƙarƙƙarfar kyakkyawar zuciyar da take iya danne tasirin So , ƙwarai ita ɗin ai jaruma ce . "

Ƙarfe uku na ranar ta yi masa a cikin Masarautar su inda ya tafi kai tsaye ga fada ya kai gaisuwa gurin Maimartaba wanda ya amsa masa fuskarsa ba yabo babu fallasa , sai dai saɓanin baya da idan har ya shigo fada ƙirarin da manyan fadawa da kansu ke yi masa har ya tashi , yau dai shiru babu wanda ya kambama shi da ƙirarin sai fa dogarai da suke tsaye daga bakin-fada .

Shiru yayi kansa a sunkui yana jiran Maimartaba yayi masa umarnin dawowa daga gefensa kusa kamar yadda ya saba a koyaushe , sai dai har ya kusan mintoci ishirin a zaune maimartaba bai sake duban sa ba , dan haka ya miƙe yana mai sallama da Maimartaba da sauran jama'a da suka amsa a sama-sama ,

Idanunsa suka kai inda yake mazauninsa ada kusa da ƙafafun Maimartaba , karaf suka haɗa ido da Mammadou da yake zaune a gurbin sa , wanda yake jifan sa da wani ɗan guntun murmushin ƙeta , ɗauke kansa yana ƙarasa barin Fadar .

A sanyaye ya taka yana yana nufar ciki sashin Hajiya Umma , a hanya babu abunda ya sauya na yadda bayu ke zubewa gaishe sa , sai dai yana lure da wani irin kallo da wasun su ke binsa da shi wasu kuma yana iya jiyo ƙus-ƙus ɗin su daga ya gota .

Ita ɗaya ya tarar da ita a falonta na ƙurya da yawanci sai zata yi ganawa ta sirri take shigarsa ,

Zama yayi a gabanta yana mai sunkui da kai cike da ladabin da yake halayyar sa ya gaishe ta , muryarta babu amo sosai ta amsa gaisuwar sa ,

Shiru ya É—an gitta kafin da murya mai kaushi tace da shi ,

    " Ina kouma itta ɗiyar da kake amren ?

Shiru yayi kaÉ—an kafin ya ce
     " sun tai ga ƙasar su baki ɗaya ,

Sake tsare shi da ido tayi , duk kuwa da ta ɗan yi farin-ciki da cewa da yayi "sun koma ƙasar su , sai ta ɗora da cewa  " ka sau amren ta ko kuwa ?

   Shiru yayi cikin fargaba , yana tsoron kadda ta tilasta shi ya saki Fatima , wani sashi na zuciyar sa ya ji yana gargaɗin sa daga sake yin ƙarya ,

wani busasshen yawu ya haɗiye , ya ɗago da kansa ya dube ta , a hankali ya mayar da kansa ƙasa kafin yace ,
    "Ban sau amrenta ba sun tai gida ne kafin al'amura su dai-daita anan ,

"Youssouf ,
   Hajiya Umma ta ƙira sunan sa , a tsorace ya amsa "Na'am Umma , zuciyarsa tana mai tsananta bugu yauce rana ta farko a iyakacin sanin sa da ta taɓa ƙiran sunan sa kai tsaye .

  " na maka oumarni ka sau amren ɗiyar nan ka aika mata da shikan ta can zouwa ga ƙasar su , muddin kana ƙamnar da na yafe ma kouma Mahaifinka shi maka afouwa , idan kouwa ka ƙi bin umarni na Youssoufa , shiru tayi bata ƙarasa ba ,
   sai dai ya fahimcin munin abunda ka iya biyo baya ganin yadda ɓacin rai ya ƙara hauhawa a kan fuskar ta bayan ta kawar da kai daga barin duban sa , 

  Gumi ne ya shiga keto masa kota'ina cikin jikin sa , ya sanya hannun sa yana share zufar goshinsa ,
   Muryarsa can ciki yace , " Na amshi oumarnin ki Umma, ki yafe min bissa ga kuskuren da na aikata .

Muryar ta da ɗan sassauci tace , " Laifin ka ga Allah kayi ka nemi Yafiyar sa , doumin shi mai yawan afouwa ne ga bayinsa ,  sannan ka kyautata tuban ka , ni kam abou ɗai nake so kayi shine sakin auren ɗiyar nan idan kayi hakka shikenan .

  Shiru yayi baice kome ba , saboda zallar tashin hankalin da yake ciki , duk wata ƙafa ta isar da saƙo a jikinsa jinya take da amsar umarnin Hajiya Umma .

  Ganin yadda ya zamto tamkar wanda aka zarewa lakka a gabanta yasa tayi gyaran murya tana mai ƙarfafa zuciyarta daga tausayi irin na tsakanin ɗa da mahaifiya daya soma mamayarta , musamman kasancewarsa mafi soyuwa a gareta cikin 'ya'ya ,
    " ka tashi ka tai ga matanka bayan ka tanadi kyawawan kalmomin da za ka yi amfani da su wajen tausasa zuciyar su doumin laifin ka mai nawi ne a wajen su .

Kamar jira yake tace ya tafi , sai ya miƙe a hankali bayan ya mata bankwana ya fito daga falon , baya sanin takamaimai ina yake jefa ƙafarsa ya nufi shiyar gidan sa ,

Sashin Siyama ya tasarwa ba tare da ya haƙiƙance meye zai je ya sanar da ita ba ,

Da shigar sa Yumna ta taso da gudunta daga inda take wasa a tsakiyar falon da tarin kayan wasanta ,

  Da sauri ya sunkuya ya ɗauke ta yana matse ta a cikin jikin sa kewar Mama marar adadi na taso masa ,

   "Papa ,
   ta ƙira shi da ƴar muryar ta ,
"Yumna , ya amsa yana ɗora idanunsa akan Siyama da ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take kishingiɗe Rakiya na mata tausar ƙafafunta ,

Da sauri Rakiya ta miƙa gaisuwar ta kafin ta bar falon zuwa can waje sashin su na ma'aikata ,

A hankali Siyama ta tako gaban sa bayan ta ƙirkiro wani guntun murmushi akan furskar ta ,

"Sannu da zouwa Biyamuradi,  da fatan ka iske mou lafiya ?
  Tana ƙarasowa ta kama hannun sa guda , kafin ta cigaba da cewa ,
    " Mu tai kayi wanka Baban Yumna kafin a samar da abinda zaka taɓa ,

Yanayin rashin kuzari bai bar shi ba ya bi bayanta zuwa sama É—akinsa ,

Bayan ya yi wanka ya shirya , cigaba yayi da zama akan kujerar ɗakin ya zurfafa cikin tunanin umarnin Hajiya umma , da kowacce daƙiƙa guda tashin hankalinsa daɗuwa yake , gefe guda ga rashin sanin takamaimai halin da ita kanta Fatima ke ciki tare da ɗiyansa dake maƙale a marar ta ,

   Ƙarar wayar sa ya sanya shi janye tagumin da yayi ya ɗau wayar ganin mai ƙiran nasa daya daga cikin manyan kwamandojin sojin su ne na yankin Diffa ,

Magana suka sake yi kan tsaron da zasu daɗa a tsakanin boda saboda motar da take ɗauke da matarsa da zasu bi ta Boda zuwa Nigeria , bayan ya gama wayar da bai ɗau lokaci yana yi ba ya ajiye wayar a gefe yana baya da kan shi ya ɗora kan bisa  allon kujerar ya ɗora dogayen ƙafafunsa akan ɗan teburin gilashi da yake gaban sa ,

Idanun sa ya runtse yana jin yadda kansa  ya ke sara masa musamman ta goshin sa ,

   Siyama wacce ta ji shirun sa yayi yawa bayan ga abinci ta haɗa masa a shiyar cin abincin su , sai ta miƙe ta hau saman , cikin ranta kuwa ƙoƙari take tayi aiki da shawarwarin da Rakiya ta bata na danne kishinta daga barin bayyana shi a sarari ,

Tana murɗa ƙofar ɗakin ta hango shi a kujerar ya dafe kan sa da hannunsa guda , wani irin yanayi na zallar tausayi da ake samu ga abunda ake ƙauna ta gaskiya , shine ya tsigar mata , babu shakka a tun shigowarsa ta fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki .

Bai ji shigowarta ba har zuwa zaman ta a gefen sa , sai da ya ji hannunta mai tsananin taushi ta É—ora akan nashi hannun da ya dafe goshinsa da shi ta janye shi ,

  "Baban Mama , ta ƙira sa , ɗas ! Zuciyarsa ta buga da jin sunan Mama da ta masa inkiya da shi da Falmata kaɗai ke ƙiransa da sunan ,  sai ya dawo da ganin sa kanta ,bayan ya gyara zamansa yana jin wani irin yanayi mai tasari matuƙa ,

   "Baban Mama ina miƙa ta'aziyyata kan rashin da muka yi na ɗiyar mou , Allah shi jikan Mama shi sa ta ceto mou .

Sai tayi shiru tana neman dai-daita nutsuwar zuciyar ta daga tarin baƙin-cikin da yake bijiro mata na zallar kishin Falmata , ta ɗora da cewa ,

   " Ina ƙamnata Fatima ? Da fatan ka baro ta lahia ?

Da wani irin yanayi ya matse hannunta dake cikin nasa , cikin muryar dake cike da rauni yace
    " nagoude sai dai a halin yanzou Fatima ta gudou ta barni zuwa kan hanya mai matuƙar haɗari , Hajiya Umma kuma ta min oumarni na sau amren Fatima , ki min addu'a Siyama lamura agareni sun tsaurara , kowa ba shi fahimta ta bisa jarabawa ta rayuwa .

Ƙwalla ta ji sun tara mata a ido , tunda take bata taɓa ganin Biyamuradi cikin halin ɗimuwa tare da rauni makamancin haka ba , sai fa yau ta dalilin ɗiya Mace , babu shakka wagga ɗiya Fatima ta kai ayi gangamin tafiya kallon ta .

Gagara cewa kome tayi illa kanta da ta kwantar bisa ɓarin jikinsa , cikin tausayin kai tace , " kayi haƙouri da ikon Allah lamura zasu dai-daita maka a tsakanin hakka nayi Alƙawarin taya ka da addu'a , Allah shi dawo maka da Fatima-zahra .

Hannunsa duk biyu ya sa yana rungumeta tsam a jikin sa , ransa cike taf da ƙauna ta musamman gami da ƙarin ganin ƙimar ta a idanunsa , babu shakka shi masoyi na gaskiya abun riƙo da hannu biyu ne .

" Nagoude ƙamnata kouma Matata , ya furta hakan yana sumbatar kan ta ,

    Idanunta ta runtse da hakan ya bawa ƙwallar dake cike a gurbin idanunta damar zubowa , tana sauƙa akan kirjin sa .

Kanta take tausayawa yadda zuciyarta ta afu ga son maso wani irin haka , ta san zafi da raɗaɗin rashin abun so dan haka take tausaya masa babu shakka ita bata da makaman yaƙin tunkarar ko wacece wannan Fatima da ake ta ƙiƙi-ƙaƙa akan ta da ta sanya Mijinta ya ɗimauce tare da jan ɗamarar yaƙi da duk wasu masu son shiga tsakanin sa da Abar son sa , labarin kome da ya faru tuni ya iske ta ta bakin Ubbo ,

Da tundaga lokacin tayi kuka tare da jimaminta ta har ta kusa faɗuwa jinya da taimakon Mai aikinta Rakiya da ta riƙa tamkar ƙawar shawarwarin ta , ta samu dawowar nutsuwar ta da Rakiya tayi ta bata shawarwari masu inganci tare da kwantar mata da hankali .

" Baban Yumna mu tai ka ci abincin ,

  " Bani jin Yunwa yanzou sai ko anjima kaɗan ,

  Bata ƙara cewa da shi kome ba ta miƙe , tana barin ɗakin , zuciyarta baza ta juri ganin sa haka cikin ciwon son wata daban ba .

Haka Youssouf ya ɗebe awanni cikin yanayi na bacci-bacci ido biyu , ( yayi likimo😂 )

Zuwa gefen la'asar ya sake yin wanka tare da shiri ya tafi Masallaci.

***

Nan ya cigaba da zama yana addu'o'i tare da karatun Alkur'ani har zuwa shigowar lokacin Sallar magariba , da idarwar sa ɗan sako ya zo masa cewa Maimartaba yana son ganinsa a can turakar sa ta ganawa da baƙi .

Da azama ya miƙe ƙarƙashin jagorar ɗan aiken suka cimma turakar Maimartaba , inda ya tarar da shi , shi kaɗai .

Bayan sun sake gaisawa yayi shiru a zaune , daga ƙasa gaban kujerar da Maimartaba yake zaune ,

An ɗauki lokaci Maimartaba yana kallon shi baice da shi ƙala ba , yana nazarin tashin hankalin da ya bayyana a suffar sa , sai bayan wasu ƴan mintoci yayi gyaran murya
  "Youssoufa , ya ƙira sunan sa ,
   "Na'am ranka shi daɗe , yace yana sake ƙan-ƙan da kai ,
   "Matso kussa Youssouf ka samrari abounda zan ce da kai ,

Da sauri ya muskuɗa ya dawo kusa sosai da ƙafafun Maimartaba,

Cikin muryar da take cike da ilhama tare da tarin ilmi maimartaba yace ,"Youssoufa  sa'ad da Ubangiji ya tsawatar maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa, Ubangiji yana tsawatar wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsawatar wa ɗan da yake fa'ariya da shi,

"Kada ka zurfafa wajen biyewa tunani tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja,

"Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗarwa, ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai ,

Idan har kayi haka ? ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare, ba za ka damu da masifar da za ta auko farat É—aya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri , Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka faÉ—a cikin tarko ba

jinkirtawa yayi ya nisa tare da gyara zama , ya kai dubansa ga Youssouf wanda  fuskarsa tayi jaa idanun sa suka ciki-ciki .

Ya cigaba da cewa ,

" Kada ka yadda Mazinaciya ta sake ruɗar ka , kada kayi duba ga ƙilbasar ta ko kuwa daɗi na daga kalmomin hilatar da suke kan harshenta.

   "Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi , amma ka sani bayan an gama , duka ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba , za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba ,

" kayi nesa da zina Youssoufa kada ka yarda ka sake kusanta kan ka da zina Idan kuwa ka ƙi girmamawar da ake yi maka za ta zama ta waɗansu , mazinata ba kome bane su face walaƙantattu ababen walaƙantarwa ,
    
      "Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba? Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba? Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani , duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala .

"kuma ai a yanzu ka gani , ka ga bala'in dake cikin zina , kome na tsanani da ya sabko maka ka sani cewa kankarane na daga zunuban ka ,zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi , kayi gaugawar tuba ga Allah kafin lokaci shi ƙure maka .

   Zuwa lokacin hawayene ke sauƙa a idanun Youssouf , nadama marar iyaka ta sabko masa , daga can ya tsinkayi muryar Maimataba yana sake cewa ,
   " ina ka baro ɗiyar mutane da kake amre ?
    Muryarsa na rawa yace
   "ta tafi ƙasar su , kouma a yau Umma tai oumarni da na sau amren ta , zan sake ta Ranka shi daɗe ,

ÆŠan murmushi Maimartaba yayi kafin yace ,
    "mata sai abar su da lamarin su na ƙarancin hikima da tunani , anya ana gyaran ɓarna da ɓarna ?  Tafeeda ya gwada muna duk wasu shaidu na ɗaurin Amren ku , mun kuma gamsu da su ,

" dan haka baka sau amren matarka ba Youssouf ,  yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta , ka amro ta ne domin kana ƙaunar ta Alhalin kana da damar hakka , kai Mijin mataye ne ,

"Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro, kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa , ka bari kyanta ya ɗau hankalinka, daga ɗauke gani bisa matayen banza ,  Bari ƙaunarta ta kewaye ka , daga kwaɗayin macen titi , ƙwarai kana da damar haka ita halaliyar ka ce ,

  Wani irin sanyin daɗi ne ya fara tsartuwa a zuciyar Youssouf sai ya ɗago kansa kamar wani soko-soko yana duban Maimartaba da kokonto ko kunnuwansa gaskiya suka jiye masa ? 

  Ɗorawa Maimartaba yayi da cigaba da cewa ,

      " Amma ka tsahirta har abubuwa su dai-daita Mahaifiyarka kuma ta sabko daga fushin ta daga nan sai ka tafi ka zo da matar ka , mafi girman lamari a gaba ka tsaida adalci  a tsakanin Matayen ka babu shakka Allah yana farin-ciki da adalai .

   Youssouf a lokacin ji yayi kamar ya tashi ya sungumi Maimartaba ya shiga shilla shi sama yana chafewa saboda tsabar daɗi da zumuɗi ,

   " Nagode ranka shi daɗe, Nagode , nagode , nagode  kawai yake ta maimaitawa ,

  " Youssouf kada ka manta kalmomin da na furta su gare ka zasu inganta halinka, su zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau ,
    "Ban manta ba ranka shi daɗe , Allah shi saka da  Alheri Ranka shi daɗe ,

   Gyaɗa kai maimartaba yayi

" kana iya tafiya ga iyalin ka .

    " to na barka lafiya ranka ya dade mu kwana lafiya .

  Da tarin farin-ciki ya nufi sashin sa , da sassarfa ya shiga falon Siyama wacce ta ɗau kwalliya cikin ƙananun kaya riga da siket , jajaye da suka amshi fatar jikin ta mai matsakaicin haske.

Da mamakin ganin sa a shiyarta da daren nan , Alhalin kuma yau ɗakin Gimbiya yake kwana , ta miƙe tsaye tana masa sannu da zuwa ,
Da sassarfa ya taka ya isa gareta ya rungumeta tsam a jikinsa yana shaƙar ƙamshinta mai sanyin daɗi , shafa bayanta ya yi a kunnenta ya ce da ita , 
    " ki tayani farin-ciki ƙamnata Maimartaba ya yarda da aurena da Fatima , har ma ya min iznin nan ba da jimawa ba na tai na zo da itta , kwanan nan za ki ga ƙamnar ki .

Murmushin yaƙe tayi tana rintse ido , muryar ta da ɗan rawa tace ,
   " Alhamdulillah , Madallah da adali mai yawaita Adalci da kyautayi , nayi maka murna Biyamuraɗin maraɗawa ,
  Zare jikinta tayi tana ƙin haɗa ido da shi saboda ƙwallar da cika taf a ƙwarmin idanun ta tana daf da kwaranyowa .

  " mu tai ka ci abinci
  ta ce da shi tana jaan hannuwan sa ,

Tare suka ƙarasa gaban teburin cin abincin da yake cike taf da kayan cimaka na alfarma .

***

Zuwa lokacin Gimbiya Maimounatu ta kai maƙura wajen shaƙar baƙin-ciki , jin ya zo ya yini a gidan bai ko neme ta ba bayan irin laifin da ya aikata mai muni .

Ta kasa zama sai kai kawo take , gaba ɗaya yau mummunar zuciyar ta ta ƙeƙeshe ita ke jagorar ta ,

   Ko ƙwalliyar da ta saba yi domin taryarsa yau ta gaza , saƙa take da warwara , a ganin ta abunda yayi mata iyaka ne a cin fuska dan haka ta ɗau alwashin cimma manufarta a yau .

Duban ta ta mayar ga gnala wacce ita ce ta zo mata da labarin sake shigowar Yarima Youssouf gidan da sake shigar sa sashin Siyama .

  Da kaushin murya tace ,
   Gnala ,
   " na'am gimbiyar matar yari...

a tsawace ta katse ta ,
    " ki tashi ki tai ga shiyar matar can ki ce ina biɗar ganawa da Major Youssouf  Abdoul-azuzou Youssouf Baskore .
  A ɗan firgice Gnala ta ɗago kan ta tana duban uwargijiyar ta , jin yadda yau ta ƙira sunan Yarima garan-gatsau babu wani sakayawa bare girmamawa , sai dai yadda ta ga fuskarta ta tsorata ainun , dan haka ta miƙe jiki na rawa ,ta fice tana cewa ,

  "  Allah shi huci ranki Gimbiya ɗiyar Sarki .

sanin da tayi bata da ikon shiga sashin Siyama kai tsaye , sai da kamun ƙafar Rakiya shugabar hadiman sashin da ita ce zata yi mata jagora , yasa ta ratsa dogayen bishiyoyi da shuke-shuken farfajiyar gidan ta cimma Rakiya a shiyar ƴan aiki ,

  Da kallon banza suke bin junan su , tamkar kishiyoyin da suke zama bala'i,  kamar Mai ciwon haƙori Gnala ta buɗe baki da kyar tace ,
   " saƙo dagga Gimbiya tace a shaidawa Matar Yarima , gimbiya na biɗar kaɗaicewa da shi .

  Rakiya wacce take cin gyaɗa ƴar marau-marau , ta karkaɗa ƙafa bayan ta afa gƴaɗar ta a baki ,  ba tare da ta dube ta ba tace ,
   " kin ga Gnala ki ɗaga sauti kiyi magana yadda zan iya ji amma kin zo kin tsaya akaina kina wani mui-mui da baki ,yo ce miki aka yi aka yi kunnen nawa zuƙo sauti yake ? Aikin banza .

  Gnala ta ƙuta , cike da takaicin rashin mutuncin Rakiya.

da ƙaƙƙarfan sauti ta ɗaga murya cikin faɗa-faɗa tana maimaitawa mata saƙon Uwargiyar ta ,

   " ah ke saurara haka kar ki fasan dodon kunne ki fallasheni , kin zo kina min hargagi akai ya ruɓaɓɓan radi'o ,

   " Naji , sai ki wuce mu tafi , tace tana miƙewa ta zira takalman ta ,

  Da wani mummunan kallo Gnala ta bita kafin ta dafa mata baya , suna tafe Rakiya na rera waƙar Barmani mai coge "cikin waƙar ɗuwawai ," inda take cewa ,

      A hayayye ɗuwaiwai dole a zauna da ku , to ko ana so , to ko ba' a ƙauna ,ko da sun tsiyaye ,  wayyo ladi ko a tsidau , kai koma cikin kwata ne .

Daga bakin ƙofa ta nemi iznin shiga wajen Uwargijiyar ta ta hanya matsa mata ƙararrawar dake shaida isowar ta ,

Siyama wacce ta zuba abinci da zummar fara ciyar da Youssouf sai ta miƙe bayan ta ɗau izni daga wajen sa , fahimta da tayi wani saƙo muhimmi Rakiya take tafe da shi a dai-dai wannan lokacin .

Da buɗe ƙofar ta ci karo da Gnala wacce take tsugunne a gaban ta , ba ɓata lokaci ta isar da saƙon Uwargiyar ta .

  Murmushi Siyama tayi cikin ran ta tana aiyana " ai shi daman wanzami bai son jarfa ,

  Da baya ta dawo tana sanar da Youssouf saƙon Uwargidan sa , jim yayi ," shi ba da gangan yaƙi zuwa wajen nata ba , rigimar ta yake gudu , baya son ta ƙara masa damuwa akan wacce yake ciki ,

  Miƙewa yayi tare da yin baya da kujerar dake gaban teburin , tunda har ta sauƙe girman kan ta na ɗiya mace ta ƙira shi , duk kuwa da laifin sa , shi ya zama dole ya tafi gareta ,yayi aikin rarrashi da neman Afuwar ta tunda zuwa yanzu ai yana da ɗan ƙarfin jikin ɗaukar duk wani bore da zata iya yi masa ,

  Sai da ya kai tsakiyar falon ya waigo ga Siyama wacce take tsaye jikinta a sanyaye  tana bin sa da kallo , dawowa baya yayi , a hankali ya rungume ta , tsawon wasu daƙiƙai , ya sake ta tare da sumbatar leɓɓan ta a tsanake ,
    Daf da fuskar ta , ya kawo tashi fuskar cikin muryar da take tsakanin maƙoshin sa yace ,
    " Nagode da kome Ƙamnata , je t'aime pour ça, tu es spécial pour moi seulement ,

  Ya saketa a hankali ya juya yana barin falon ,

   Tsaye tayi a gurin tana shaƙar ƙamshin sa da yayi saura a gurin , ta lumshe ido tana murmushi kaɗan cikin ran ta farin-ciki ne fal ,
     " Da gaske yake da yace yana son ta ? Ita ɗin kuma ta musamman ce a wajen sa ? Ko dai duk farin-cikin kusantar dawowar masoyiyar sa ne ?

****

Bayan shigar sa falon Gimbiya Maimounatu wanda yake da rangwamen haske sakamakon ƙasa da aka yi da hasken fitulun falon sosai a tsaye ya hango ta ta juyawa ƙofar baya ,

A hankali ya taka ya isa inda take tsaye , hannunsa ya sanya ya kewaye cikin ta tare da haɗa bayanta da ƙirjin sa sosai ,

Da sigar rarrashi yace ,
      " Bana cikin Farin-ciki da ganin ɓacin ran ki princesse,  ina bakin-cik...

Da wani sauti daban da wanda ta saba yi masa magana da shi ta katse shi ,
        "  ya ya kake son samun farin-ciki lokacin da ka kwashi tsawon wasu shekaru kana assasa baƙin-ciki a zuciyar wasu mutanen  ?
"  ka baranta da farin-ciki ba zaka yi farin-ciki ba har abada kai ma .

    Da ƙarfi ya juyo da ita yana laluben ganin fuskar ta , sai dai hasken wajen ya masa ƙaranci .
      " kiyi haƙuri Maimounatu ni ɗin mai laifi ne a wajen ki na sani ,

Wani ɗan ƙaramin murmushi mai sauti tayi ,
    " haƙuri , laifi ?
    Ta ce da sigar tambaya ,
Dariya tayi mai sauti , dai-dai da shigowar ƙira a wayar sa ta cigaba da cewa ,
   " Ai ni baka min laifin kome ba kan abunda ka aikata ma rayuwar ka ?  To ma menene dan ka rage dare da yaya ka kuma zo ka amri ƙamna ?  Ai babu wani laifi ga hakan ni dai ta ɓangarena , dan haka kada ka bani haƙuri bisa wannan ba damuwa ta ce ba .

  Jiki a sanyaye Youssouf yake bin ta da kallo , sai yake ganin baki ɗaya ta sauya masa ,
     Hasken wayarsa ya kunna tare da cewa ,
    " Maimounatu meye ya samu fitilun sashin nan ne ? Hala sun mutu ?  Bari za'a sauya wasu ,

    " fitilin sashin nan na taya Uwargijiyar su baƙin-ciki ne kamar yadda zuciyata tun-tuni ta kasance a cikin duhun da yake matsananci fiye da wannan , tun a  wata ɓakar-rana cikin ranaku da ka sanya bakin bindigar ka ka tarwatsa min fitilar zuciya ta ,

   Wayar sa ya mayar aljihu bayan ya ssnyata a silent , da alama sai yayi da gaske da alama ran Gimbiyar ta shi ya kai ƙololuwa a wajen ɓaci , jin yadda take amfani da wasu kalmomin da ya gaza fahimtar su ,

Jawo ta yayi ya zauna tare da ita tana bisa cinyar sa ,
     "  Duk ki bar waɗannan kalaman Maimounatu , Fatima-zahra ƙaramar yarinya ce , ba zata ƙi ku zauna lafiya ba sann....
    katse shi tayi ta hanyar ɗora yatsanta manuni akan laɓɓan sa ,
     "shitt , Yarima Youssouf nace kada ka damu ,
   Miƙa hannu tayi ta ɗauko tatatcen ruwan 'ya'yan itatuwa da ta sarrafa da hannun ta , ta nufi bakin sa da kofin ,

    Jimm yayi yana kallon sheƙin idanunta ta ɗan hasken wajen , dariya tayi yana iya ganin hasken haƙoranta kafin tace da shi
    " Sha mana Yarima , abun shan ka ne mafi soyuwa , ni da hannuna nayi sa musamman domin kai .
   Ƴar ajiyar zuciya yayi jin alamun ta fara sauƙowa , hannun sa ya ɗora akan nata ya kai kofin zuwa bakin sa , yayi Bismillah ya kafa kai ,
    Ya sha sosai saboda ƙishirwar tare da yunwar da ya yini yana ji , ya kuma gagara cin kome sai fa yanzu da ya fara samun nutsuwar zuciya ,
    Wata irin damƙa da cikin sa yayi masa kamar kiftawa ido bayan gama sha , shiyasa ya zame Gimbiya maimounatu daga jikinsa ,

  Da sauri ya fidda wayar sa daga Aljihu da har lokacin ƙiran Tafeeda bai bar shigowa ba , da hasken shigowar ƙiran ya kai hannu ya ɗau kofin yana haska ciki .

Da wata irin muryar yace ,
    "Maimounatou menene cikin wannan juives din ?  Meye a ciki ? Meye..  Kasa ƙarasa magana yayi
    Gumi ya shiga karyo masa saboda wani irin ciwo mai tsanani da ya ji ya turnuƙe shi tamkar ana filla-filla da kayan cikin sa , zamewa yayi daga kan kujerar bayan ya saki kofin hannunsa zuwa ƙasa ,

  Cikin azaba ya ke duban Fuskar ta , yana iya hango wani ɗan guntun murmushin cikar buri da take yi , bata yi motsi ko kaɗan ba wajen ba shi wani taimako 

   Wani irin gurnanin nishi ya fara yi , ya miƙe a ƙasa yana murƙususu ,ciwon da yake ji bai taɓa jin makamancin sa ba , wani irin duhu mai tsanani yake ji yana sabko masa daga can wani waje mai nisa a kwakwalwarsa Alhalin kunnuwan sa sun samu ƙarin ƙarfin ji ,
   Domin yana iya jiyo sautin murmushin laɓɓan Maimounatou , so yake ya buɗe baki yayi ko da addu'a ne amma ya gaza ,

Wani ciwo mai kaifi da ya yanki uwar hanjin sa shi yasa shi burtso da Amai ta hanci da bakin sa , da yasa duhun da yake sabko masa hanzarin ƙarasa saukowa ya rufe masa ido ya daina ganin kome alhalin idanun sa na buɗe da hakan ya yi dai-dai da tsayuwar jijiyoyin jikinsa , kome kuma ya tsaya masa chak .

Da gudu Maimounatou ta tsallake shi tana lalubar wayar ta , jikinta na rawa ta shiga ƙiran wata number ,
    Ana ɗaga ƙiran bata jira ance kome ba tace
      " ka tahou yanzou aiki ya cika sauran ka ƙarasa naka , ni nagama nawa .

  Daga ɗayan ɓangaren Mammadou zuruf ya miƙe tsaye tare da kewaye matar sa ya fita ,
     A harabar gidan sa ya tsaya , cikin yin ƙasa da murya yace
    " kina nufin yau kin yi nasarar kashe Youssoufa ?
  Jin jina kai tayi kafin tace "ƙwarai yau na cimma manufata ta amren sa .
  
 

 

  

  
 

    

Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wayi gari lafiya ?

Alherin Allah ya sadu da mu baki É—aya .

Nagode

  

[12/25/2019, 9:11 AM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

46

" Yakaka tana nan zuwa ita ma ,

Ita ce amsar da Falmata ta bawa Maman su , daga nan hira ce ta sarƙe a tsakanin su mai cike da labarin yadda rayuwa ta kasance musu bayan rabuwar su da juna .

****

Tiryan-tiryan Falmata ta basu labarin duk wasu bala'o'in da suka afku ga rayuwar su bata ɓoye kome ba illa mummunar rayuwar da Yakaka tayi da har ta kai ga haihuwar Mama da take jin har abada laɓɓan bakin ta baza su taɓa iya bayyana wannan mummunan labarin ga kowa ba .

   Ta cigaba da bata labarin ɓacewar Yakaka bayan haihuwar Mama ba tare da ta faɗi ainahin silar barin su da tayi ba har zuwa kan auren su ita da Youssouf yadda kome ya wakana , da rashin lafiyar Mama har zuwa tafiyar su USA da samuwar lafiyar idanun ta , komawar su Niger da kuma dawowar Yakaka , zuwa kan Mutuwar Mama .

  Shiru su duka ukun suka yi bayan gama sauraron ta , zuciyar Khaalty Rahima ta girgiza da jin yadda rayuwa tayi walagigi da 'ya'yan ta mata , tsakanin ƙarya da gaskiya , rayuwar rashin gata ta tsantsar wahala abu ɗaya ne mafi ciwo a gareta yadda duk su biyun suka auri Miji guda a wannan ƙarancin shekarun nasu , lalle wannan ƙaddara ce mai girma .

  Babu wanda ya fita sanin halayyar 'ya'yan ta duk kuwa da cewa sun jima da rabuwa daga yin rayuwa guri guda , amma ai ita ta haife su dan haka ta san halin kowaccen su tun kafin su mallaki hankalin da zasu iya boye abu a ran su .

  Daga zaman Falmata a gabanta kawo yanzu ta fahimci lalle akwai wata damuwa mai girma da take cinta a rai , wanda farin-cikin haɗuwar su bai sa ta manta da damuwar ta ba , ji tayi hankalin yana neman tashi , tana jin kamar akwai wani abu da Falmata take ɓoye mata da tafi danganta shi da Yakaka , dan haka ta muskuɗa tana kallon fuskar ta cike da nazari tace ,

  " Falmata kin samu labarin bayyana ta ne kika zo ?  Ko kuma kawai dai kin zo ne ?

Murmushin yaƙe tayi kafin tace
   " Maman mu ban san kin zo ba , ban San kina nan ba, ta cigaba da cewa Mama ina Yaana da Bulama suke ?  nayi kuka nayi kuka na damu akan sanin ina kike ko kina raye ko kin mutu ?  shekaru suka yi ta tafiya ba tare da mun san halin da kike ciki ba , har na fitar da rai da sake haɗuwar mu a duniya , na koma yi miki addu'a iri ɗaya da wacce nake yiwa Baban mu , kan Allah ya jiƙan ku .

   Ƙwallar tausayin ta ya taru a idanun Khaalty Rahima , kafin tace
    " Yaana ta rasu a kan hanyar mu ta shigowa maiduguri , Bulama kuma yana nan ya girma , anjima kaɗan ma za ki gan shi ya dawo daga islamiya ,
   Ta cigaba da cewa ,

" Falmata ni na wanke gawar Mahaifin ku a cikin gonar na binne shi , ban yarda gawar mutumin kirki irin sa ta walaƙanta a hannun dabbobin daji ba , bayan na koma neman ku ban same ku ba , na dawo wajen ƙabarin sa mun rayu kwana biyu ni da Yaana da Bulama ina yi ma sa addu'a , kafin mu bar gurin , Allah sarki Mutumin ƙwarai mai tawali'u Allah ya masa Rahama ,

   " Amin Mama Amin ,
   Falmata ta amsa tana share hawayen da suke zubo mata ,

  Amnee ita ta katse musu hirar ganin duk fiye da rabin ta koke-koke suke yi da jimamin rayuwar su da ta wuce .

    " Ukhtee Rahima ku bar koke-koken nan haka , Fatima mu tafi ɗaki kiyi wanka ki shirya kafin a kawo miki abinci , "me zaki ci 'ya ta ?
  Ɗan murmushi Falmata tayi "kome ma zan ci , amma da zan samu tuwo miyar kuka da man shanu ,

    Dariya Amnee tayi tana kama hannun ta " muje kiyi wanka ki shirya , abinda kike so shi zaki ci .

  Bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da zanen da Amne ta zaɓo mata daga cikin kayan Rahima , tsumu tayi zaune a kujerar gaban madubi ,

   " wani irin yanayi take ciki marar kan gado , ga dai ta a gida ta dawo kamar yadda ta zaɓarwa kan ta , take kuma ganin hakan shine zai raba ta da ɓacin-ran da take ciki , daɗin-daɗawa ma ta dawo ta tarar da farin-ciki mafi ɗaukakuwa a wajenta watau haɗuwar ta da Mama ,

Amma sai farin-cikin nata ya gaza kaiwa ga matakin da take so , baki ɗaya a hagunce take jin zuciya da ƙwaƙwalwar ta sun gaza tsayuwa gu ɗaya bare su taya ta samun gamsasshen farin-cikin da zai wanke mata rai .

   Ƙiran sallar La'asar da aka yi , yayi dai-dai da gilmawar tunanin da take ta yunƙurin danne sa tuntuni , wani sashi na zuciyar ta ya tunbuƙo da tambayar ta ƙarfi da yaji ,
   " a wanne hali Yakaka da Youssouf suke ciki ? Wataƙila sunyi ta neman ta sun gaji , wataƙila kuma ba su ma wani neme ta ba , dama ce suka samu ta tsara yadda rayuwa zata musu a gaba , ƙila ma ya saki auren ta zuwa yanzu ,
  Nan take ta runtse ido Zuciyar ta na tsananta bugu ,
   Da sauri ta miƙe ta shiga banɗaki gami da ɗauro Alwalar La'asar ,

Har ƙarfe huɗu tana kan Sallaya tana addu'o'i domin yaƙi da tunane-tunane , sai da Amnee ta matsa mata ta zo ta ci abinci sannan ta tashi suka koma falon tare , inda suka tarar da Khaalty Rahima ita ma ta idar da sallar ta nan bisa darduma ,

idanun ta kan falmatan tana duban ta da murmushi irin na zallar farin-ciki ,da ƙauna , ita ma falmatan da murmushi ta tafi a hankali ta zauna a gefen ta ,

Farantin da aka jera abinci akai amnee ta tura mata gaban ta , " ki cinye duk kin ji ko ?

Sama-sama take chakalar abincin duk kuwa da an girka shi yadda take so , miyar ta sha haɗin kayan ƙamshi na gargajiya , ga kuma man shanu gangariya ,

Sallamar Yakaka da ta sauka a kunnen ta daga bakin ƙofar falon shi yasa ta mayar da lomar da ta ɗauka da nufin kaiwa bakin ta ,

A hankali ta É—ago kan ta tana ganin shigowar ta ,da kai tsaye Yakaka ita ta doso bata kai ganin ta kan kowa da yake wajen ba ,

Ganin yadda ta taho yasa Falmata ta tsorata , dan haka ta janye kwanon abincin gaban ta , zuciyar ta na bugawa bata taɓa ganin Yakaka a fusace ya irin haka ba .

   Yakaka tana ƙarasowa ta riƙo kafaɗun Falmata da karfi ta jijjigata , muryarta a tsaurare tace ,
     " Falmata me yasa kika min haka ? Meyasa kika tafi ki ka barni ? Ashe kinyi girman da za ki iya yin gaban kan ki a rayuwa ? Ashe ni matsayina a wajen ki daman bai wuce na ƴar jagora ba da yanzu kuma lafiya ta samu wajen ki shine kika sanya kan ki a hatsari wajen yin gaban kan ki ? Wallahi da wani abu mummuna ya same ki bazan yafe miki ba Falmata .

   Kukan da take riƙewa ya taho mata , sakin kafaɗun ta tayi ta zauna daɓas akan kujerar gefen ta ,  muryar ta cikin kuka ta cigaba da cewa ,
     " Falmata kin manta ne da kusancin dake tsakanin mu ? Ashe har akwai wani laifin da ni zan miki ki kasa yafe min ?

   Zuwa lokacin ita ma falmatan hawaye ke sauƙa a idanun ta , ganin kukan Yakaka ya karya mata zuciya , a hankali ta zauna a gefen Yakaka , muryar ta na ɗan rawa tace  " Yakaka , kiyi haƙuri ba yadda zan yi ne , kin san... Kawai bazan iya zama bane .

  Da wani irin yanayi Yakaka ta ɗago tana kallon ta , baza ki iya zama a gidan auren ki ba saboda ni ko Falmata ? Saboda mummunan kuskuren da na aikata ko ? Saboda...
    Da sauri Falmata ta katse ta tana nuno mata inda Khaalty Rahima da Amnee har da Hajja duk suna tsaye suna bin su da kallo ,
   "Yakaka kin ga fa Maman mu a tsaye , ga ta nan tana kallon ki , bata mutu ba ,ga Maman mu Yakaka .

   A hankali Yakaka ta bi inda take nuna mata da kallo cikin ran ta da ɗarsuwar tunanin ko dai Falmata ta samu jirkituwar tunani ne ?

Tunanin ta ya tsaya chak na wasu ƴan daƙiƙoƙi lokacin da idanun ta suka kai kan fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi tana raba ganin ta a tsakanin su biyun cike da nishaɗin sake samun damar ganin su tare a gaban ta .

A hankali Yakaka ta mike tana kusantar inda take bayan tsayuwar kukan ta chak , zuciyarta cike da wasi-wasin gaskanta sake ganin ta , sai dai kuma ko a cikin mafarki ta ga Mahaifiyar su ai ba zata gagara gane ta ba ko me kuwa jirkituwar kamanni da ta samu mai-kyau ko mai-muni .

Tana ƙarasowa gurinta ta kai hannu a hankali tana tattaɓa jikin Khaalty Rahima, muryar ta a dishe da kukan da tayi tace ,
   "Maama ke ce ? Ke ce Mama ?

   Hannun ta da yake taɓa jikinta khaalty Rahima ta riƙe , tana cewa , "Ni ce Aminatu , Yakaka na , ni ce ,

  Yakaka tana wata ƴar Dariya-dariya , kuka-kukan da yake fallasa tsantsar ruɗanin farin-cikin da take ciki , ta waigo ga Falmata tana mai mancewa da Falmatan ta riga ta haɗuwa da Mama , ɓakin-cikin da ta shigo da shi yana zagwanyewa tace ,
    "Falmata wallahi Maman mu ce , kin ga Maman mu ? Zo ki gan ta , ta ƙarasa magana tare da yafito Falmatan da hannu ,
   Sai kuma ta juya ta rungume ta da ƙarfi tana cewa ,"Mama na, Alhamdulillah , Alhamdulillahi .

****

Daren ranar ba suyi wani baccin kirki ba su duk huÉ—un hira kawai suke yi inda cikin labarin da Yakaka ta basu ta bayyana musu ainahin yadda haÉ—uwar ta da Youssouf ya kasance da yadda ta haifi Mama , samy baby ta yaudare ta, da kuma duk abubuwan da suka kasance tsakanin ita da Youssouf da danginsa baki É—aya bayan zuwan ta Niger har zuwa guduwar da Falmata tayi ta bar ta a Niger .

A Zuciyar ta ta ƙudiri aniyar tsage gaskiya kome ɗacin ta , ita bata ga Alfanun ƙarya ba , babu wata rana da ƙarya zata iya yiwa mutum illa sada shi da ranar Nadama .

Daga Khaalty Rahima har Amnee sun koka kan yadda mummunar kaddara ta faɗawa Yakaka sanadin duhun jahilci tare da zun-zurutun rashin wayo , haɗi da raunin wayewar mu'amalantar jama'ah , da kuma rashin wani babba majiɓanci a cikin rayuwar su .

Yadda zuciyar Yakaka ta cika da tsoron ko zasu yi mata faɗa ko ma su yi fushi da ita sai ta ga akasin haka , domin daga mamar su har Amnee tausayi kaɗai take iya hangowa a fuskokin su , dan haka sai ta ji ta samu nutsuwar zuciya irin wanda bata taɓa samu ba tunda igiyar rayuwa ta fara jan ta .
  A gareta yau ce rana ta farko da wasu nata makusanta na haƙiƙa suka fahimce ta ba tare da sun ƙalubalance ta ba , babu shakka babu kamar uwa Mahaifiya, ƙaunar ta ga abunda ta haifa daban ne , haka ma yawan sani da fahimtar ta ga 'ya'yan ta daban ne kamar yadda yawan uzuri da afuwar ta gare su ya hauhauwa .
   Amnee ita ta katse shirun tsakanin su inda ta cigaba da cewa ,
    "Amma takwarata , raba auren ƙanwar ki da Youssouf da kika so yi , ko kusa ba hanyar samar da mafita ba ce ba , idan kika duba yadda sharri ya biyo ta hannun sa haka nan ma Alkhairi ya zo ta hannun nasa , ki duba yadda ya riƙe auren ƙanwar ki har ma ya zama hanyar samar da lafiya a gare ta ? Bai walaƙanta ta ba duk kuwa da tazarar banbancin matakan matsayi ta kowacce fuska na rayuwa da yake tsakanin su , Baki ga yadda ya jajirce kan rayuwar ƴar sa ba har sai da Allah ya ɗauke ran ta ba tare da ya bari ta walaƙanta ba , kamar yadda sauran mafi akasarin ƴaƴan da aka samar ta wannan hanyar suke rasa tudun-dafawa iyayensu duk biyu na kƴamatar su musamman ma uba , amma sai shi ya kasance mai bata kariya da dukkanin ƙarfin sa , hatta a gaban dangi da Al'ummar sa .

"Babu shakka laifin sa maigirma ne sannan alkhairin sa kuma mai yawa ne , na fahimci irin ciwon da kika ji , kike kuma kan ji bisa dalilin faruwar kome , ina nufin auren sa da Fatima , to amma kiyi haƙuri ki rungumi kaddarar ki , ki yafe masa domin 'yar uwar ki da ya alkintawa rayuwa , ki bari su cigaba da zaman su na aure , Ubangiji Allah zai dube ki kema takwara zai baki Miji nagari wanda zai tallafawa rayuwar ki , ya rufe duk wani aibunki , ya ƙi duba zuwa duk wasu shuɗaɗɗun laifukan ki , ya zamar miki abun Alfahari , Allah yana son bayun sa masu yawan yafiya kin ji ko ?

Ta ɗago kan ta a hankali tana murmushin da iyakar sa bisa siraran laɓɓan ta , idanun ta na sheƙin hawayen da suka cika gurbin su ta ce ,

"Amnee nagode , nagode da addu'ar da ki ka min , kuma inshaAllah na yafe masa Allah ya yafe min nima ,

   Hannu ta kai ta riƙo hannun Falmata wacce tayi lamo a kwance kusa da Mamar su , ta juya musu bayan ta , duk zaman su a ɗakin bata cika cewa kome ba , a sarari damuwa mai-yawa take bayyane a fuskar ta ,
     Cikin sanyin murya Yakaka tace ,
    " Falmata ke ma ki yafe min duk wasu laifukan da nayi miki da saka ki a damuwa da tashin hankalin da nayi , ki yi haƙuri kin ji ko ? ban yi da gangan ba .
    Miƙewa zaune  tayi tana riƙo hannuwan Yakaka duk biyu , muryar ta na rawa ta ce ,
   "Yakaka meyasa za ki bani haƙuri ? Bayan ke kika cike min gurbin Mahaifiya , Mahaifi ,dangin da kowa namu lokacin da muka rasa kowa ?Bayan ke ce kika dunga ɗawainiya dani Alhalin ina musaƙa ? Ke ce kike zama da yunwa domin ni naci , ke ce kika sadauƙar da rayuwa ƙarƙashin rufin ɗaki kan katifa kika zaɓi kwanan cikin zaure domin ni na kwanta ? Yakaka, ke ce fa Mamar Mama 'yar da dalilin ki samar muna da rayuwar jin daɗi kaddara ta sa aka samar da ita , 'yar da ni kuma ban so wata halitta sama da ita ba , dalilin Mama na samu lafiyar idanuna , tsawon zamana da shi Albarkacin Mama nake ci ,...

  Hannu Yakaka ta kai da nufin rufe mata baki , " ya isa Falmata ki ce kawai kin yafe min nima ,
   Janye hannun Yakaka tayi daga kan bakin ta hawayen idanun ta da suka taru suna zubowa tace ,

    " Yakaka ai ni ce zan nemi yafiyar ki akan butulcin da nayi miki , shaiɗan ne ya min huɗuba da har ya sa nayi fushi da ke , ruɗewa nayi Yakaka ban taɓa zaton abinda ya cutar da ke ni kuma zai kyautata min ba , ban yi zaton sanadiyyar shan wahalar ki ni zan samu salama ba , ban so ba kika zamto mafarauciya ni kuma cima-zaune ba , Yakaka nima bazan iya cigaba da zama da shi ba ..
    Kuka ya ci ƙarfin ta , zuciyar ta na mata zogi ,

Yakaka ma hawayen take yi a dai-dai lokacin bata da sauran kalmar da zata yi amfani da ita ta rarrashi Falmata , ta ta zuciyar ma jinya take .

****

Washe gari da safe bayan sun shirya sun yi karin-kumallo Amnee ta musu jagora zuwa wajen Prof da daman tun a jiya labarin zuwan su ya same shi , haÉ—i da dangantakar su da Amnee da Rahima .

Bayan ya amsa gaisuwar su , ya dunga bin su da kallo cike da tausayi , can daga ƙasan ran sa yana jin tamkar yana da kamasho mai yawa na kasancewar rayuwar su a haka ,

Ba domin shi da danginsa da suka ƙi auren  Rahima da ɗan uwan su ba da hakan ya kawo barin Rahimar gidan da wataƙila yaran basu tashi 'ya'yan ƙauye marasa galihu irin haka ba ,

Da ace ko da mahaifiyar su da sauran 'yan uwan su sun ƙi auren , shi bai biye musu wajen nuna tsanar lamarin ba da har ya kawo saɓani tsakanin sa da Matar sa ba , ya tsayawa Rahimar har ta samu wani mijin ko da ba ɗan uwansa ba , da Rahima da yaranta basu sha wahalar rayuwa irin haka ba , da suka faɗawa hatsararruka da dama mafi munin su hatsarin Ƴan tawayen Boko Haram , da ko babu kome mutumin birni zai aura mata mai daraja da ƙima kamar ta sa .

Yana jin yanzu lokaci ne yayi da zai gyara kuskuren sa , har yanzu yana da damar sake zaɓowa Rahima wani mijin muddin ta amince , 'ya'yan ta kuwa daman Allah ya faɗo da taimakon su ta hannun sa , ashe akwai abunda Ubangiji ya ɓoye ,

Dan haka ƙudirin haɗin Auren Hamza da Yakaka da ya yi niyyar yi tuntuni ya ji ya sake kaurara a cikin ran sa , har ma ya ji dacewar matso da lamarin kusa , wataƙila da jajircewar da zai yi cikin Rayuwar Rahima da 'ya'yan ta a sauran rayuwar da ta yi masa saura zai samu ya ragewa kan sa girman laifin da yayi wajen tayawa a wargaza rayuwar Marainiyar yarinyar da take amana a wajen sa .

Cike da nuna tsantsar kulawa ya shiga jan su da hira ba tare da ya shigo musu da wata tambayar da ta shafi ɓangare na rayuwar su ba , cikin hirar da kusan su biyun ke yin ta a tsakanin su Amnee tace ,

    " Baa Alaji , a ƙira yaran nan duk a sanar da su dawowar ƴan uwan su , saboda a sa rana su zo su gana da juna ko kuwa ?

  " Hakane , to amma tun da daman nan da ƙasa da sati huɗu ya rage bikin ita Rahima ƙarama kuma a halin yanzu ita da Zainab ɗin duk basa ƙasar suna can Dubai ko da an sanar da su dawowar ƴan uwan nasu sai a bar batun haɗuwar su har zuwa nan da sati biyu da duk zasu hallaru domin bikin Rahima .

    " to shikenan Baa Alaji bari yanzu zan ƙira idan mun koma ciki idan ma ya kama a haɗa su a waya su fara gaisawa ,

   " to babu laifi , ya zarce da cigaba da cewa,
     " Rahima baku da wata damuwa ko ? Da sauri Khaalty Rahima ta amsa ,
  " babu damuwar kome Yaya , Allah ya saka da Alheri ya ƙara nisan kwana .
  Amin yace yana Gyaɗa kai ya mayar da ganin sa kan su Yakaka ,
     " Yarana kuma babu wacce take da wata matsala ko ,? Idan kuna da ita ku sanar da ni , ni tamkar Mahaifi nake a wajen ku Mahaifiyar ku ƙanwata ce ,
   Girgiza kai Yakaka tayi , a hankali tace "Baa babu matsalar kome mun gode , Falmata wacce kan ta yake sunkuye ta ɗago kai kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru tana sake sunkui da kai ,
   Prof da duk yake kallon su yace ,
  "Fatima akwai matsala ko ? Meye kike son ki faɗa min , ina jinki ƙaramar 'yata ?
  Dukkanin su sai suka mayar da ganin su kan Falmata wacce kan ta ke sunkuye ,

  'Baa so nake Dan Allah ka raba auren mu , bana son cigaba da zama da shi ko kaɗan Dan Allah Baa ka sa ya sake ni .

   Muryar Falmata ta ratsa wajen cikin alamun da take gaf da fashewa da kuka ,

Shiru ne ya ratsa falon , tamkar ruwa ya cinye su , kafin Prof yayi gyaran murya yana karantar yanayin ta yace ,
   "Fatima shi mijin naki laifi ya yi miki ? Ko kuwa wani abu aka miki daga danginsa ? Ko kun samu saɓani ne da shi ?
  Shiru tayi bata amsa ba , sake maimaita mata tambayar yayi nan ma tayi shiru , Khaalty Rahima zata yi magana ya dakatar da ita ,
   Ya sake cewa
   "ko kuwa kawai daina son shi kika yi ? Ko gajiya da zaman ku tare kika yi  ? Ko kuma can ƙasar tasu ce bakya so ?
  Da sauri ta gyaɗa kai ,

murmushi mai sauti yayi , cike da tausasawa yace " to babu laifi , ki ƙira shi kice na ce ya zo ina son ganin shi , idan ya zo sai a yi miki yadda kike so kin ji ko ?

" to Baa nagode .

Murmushi yayi bai ce ƙala ba .

    ****

Niamey Police nationale

Maimounatou wacce take zaune daga kan wani ɗan dandamali da aka tanada shi musamman domin zaman waɗanda ake tuhuma da laifi a cikin babban ofishin 'yan Sanda na ƙasar Niger baki ɗaya .

Ta muskuɗa tana cigaba da wasa da awarwaron hannun ta , tayi kunnen uwar shegu da duk wasu manya da ƙananun tambayoyin da babban ɗan Sanda da yake tsaye daga kan ta yana jefo ma ta ,

Ganin taƙi yin magana ya sa ɗan Sandan ƙutawa cike da kaiwa maƙura a jin haushin ta , ya mayar da ganin sa kan Mammadou bayan ya ɗaga takun sa zuwa gaban sa ,

   " Mammadou ko za ka iya faɗa mana dalilin da yasa ku ka ciyar da ɗan ouwan ka guba ?
     Da sauri Mammadou ya ɗago da kansa ,

   " Wallahi ni bani da wata masani kan abunda yake faruwa a shiyar gidan Youssouf , matar sa ita tayi ƙira na kan cewa na zo fa ga ɗan ouwana ya faɗi yana biɗar taimako na , shine na runtuma da niyyar kai masa ɗauki , da shigata na tadda shi a halin da ku ma kun ka zo ku ka taddo shi , wallahi ni iyakar abunda na shina kenan ban.....

Wata dariyar mai sauti da Maimounatu ta sanya , ita ta katse masa jawabin sa ya mayar da ganin sa kan ta yana ƙif-ƙifta ido , ba tare da ta dube shi ba tace

   " Mammadou wallashi cikkin ragwaye kai na ƙurya ne , yo me kake tsoro idan ya tabbata gubar da shi wannan Azzalumin ya ci ta hannun ka ta fitto ? hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kouwa ɗaurin rai da rai muddin rayuwa ?
     " Burina labarin mutuwar sa ta jishe ni , daga nan koume shi faru dai-dai ne , ai hukuncin wadda ya kashe a kar shi , shi da kansa bisa turba nasa hukuncin yake , fansar ran Ghaddafi tare da gudan jina na da na rasa na ɗauka bissa kan sa , kai gudumawa ka bada bisa turbar naka cikar buri ko kouwa ?

     Laɓɓan bakin Mammadou har rawa suke cikin in'ina yace ,
    " kadda ki mini ɓakin sharri ɗiyar nan , ni yaushe na kawo miki gubar da kika ciyar da ɗan ouwa na da itta ? Ki yiwa Allah kadda ki tunkuɗa ni cikin masifa ,

   Wani kallon banza Maimounatou ta wurga masa , idanun ta jajir tace .
    " Yau ba rana ce ta yin wassan ƴar boye ba Mammadou ka daina yin kamar baka san kome ba , kamar kai da Mahaifiyar ka baku taya ni ba , bana son muyi rabuwar tsiya doumin kun bani taimako wajen biya hakkin Ghaddafi tukuici ya kamata na baku .

   Ɗan sanda da yake rubuta duk wasu kalamai da suke yi , ya ɗan karkato ga Maimounatou , ganin kamar ta shirya bada wasu bayanai ,
   
   " Wanene Ghaddafi menene kouma alaƙar sa da kashe Mijin ki da kika yi ta hanyar ciyar da shi guba .

  " Ghaddafi masoyina ne .

****

Ghaddafi Yacouba Dango asalin iyayen sa ƴan ƙasar Mali ne da suka hauro sahara suka shigo ƙasar Niger , suka yada zango a yankin Agades , inda suka yi mazauni cikin wani kongon gida da yake daga baya sosai da Babban gidan sarkin Agades ( fadar Maimartaba sarkin Agades ) .

Bayan shi iyayensa suna da wasu 'ya'yan sai dai tsantsar talauci ya sanya su fantsama a cikin gari yin barace-barace , duk kuwa da cewa a lokacin shi Ghaddafi saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da É—oriya ,

Lokacin da ya fara bara sai ya fahimci babu mai kula shi bare har a ba shi , dayawa daga cikin mutanen da yake roƙo ma ƙorar sa suke da zagi kowa na faɗin ya tafi ya nemi sana'a .

Ganin haka ya sanya shi daina bara ya koma tsince-tsincen matattun ƙarafuna a kan bola yana kaiwa yana sayarwa ,( jari bola ) babu laifi yana tallafawa iyayen sa da hakan .

a wannan yawon ya haɗu da wasu kangararrun yara sa'o'in sa da suke jeruwa bisa tsohon hanyar wucewar jirgin ƙasa wajen da aka mayar sa bola su kuma suka mayar da shi matattarar ƙananun shaye-shayen su da yin karta .

Su suka jawo sa cikin su ba ɗau lokaci ba ya zama ɗaya daga cikin su ya kangare , tsince-tsincen ƙarafunan ma ya daina ,  basu da wani aikin yi sai zaman banza a bakin layin jirgi ko kan katagun kwangayen gidaje , suna ƴan shaye-shayen su ,  babbar sana'ar su ita ce ƙananun sace-sace , daga sun ga gidan da ake barin sa galala sai su faɗa su yashe mutanen cikin sa , ƴan ƙananun dabbobin mutanen unguwa basu tsira ba , akuyoyi ,talo-talo kaji , agwagi , a taƙaice dai su Ghaddafi sun addabi mutane sun hana su sakewa .
 
Ganin haka yasa Mutane suka yi ɗango suka kai ƙarar su wajen Maimartaba ,

Da kansa Maimartaba ya sa aka kamo su , aka basu horo tare da haɗa su da aiyuka a cikin gidan sarkin mai wahalarwa na tsawon satika biyu duk saboda a hora su 

Ghaddafi yana cikin samari huÉ—un da aka tura bargar dawakai domin kula da su da share musu waje gami da basu abinci .

Kafin kwanaki huɗu Ghaddafi ya saba da aikin yana kuma jin daɗin aikin saboda ko babu kome yana ci ya ƙoshi fiye da sau uku a rana

Ranar da yake cika sati a kan aikin sa , Babban bawan da ainahin kula da bargar yake ƙarƙashin sa ,  ya danƙa masa linzamin wani kyakkyawan matashin jan doki ,

Yace ya kaÉ—e jikin sa da kyau dokin gimbiya ne , yau zata É—an hau ta kewa akan sa nan cikin filin dake gaban bargar .

Zuwa la'asar sakaliya , gimbiya Maimounatou tare da bayunta biyu suka iso

Ba ɓata lokaci ya jaa limzamin dokin zuwa gaban ta yana mai tsare ta da kallo ganin ta da yayi yarinya ƙarama da bata wuce sa'ar ƙanwar sa ta uku ba ,

Gimbiya Maimounatou tana ɗago kai ta sauke ganin ta a kan sa , zuciyar ta ta wani irin bugawa , a iyakar shekarun ta goma sha shidda alokacin bata taɓa ganin wani ɗa Namiji mai kyaun sura irin sa ba , kasancewar Ghaddafi kyakkyawan balarabe ne na sosai jazur da shi .

Tun daga wannan lokacin sai ta faɗa jarabar ƙaunar sa , bata da aiki sai zuwa barga dan kawai ta kalle shi , a lokacin ita tana hutun kammala makarantar ta ta secondry ,

Sai dai kamar ɗaukewar ruwan sama sai ta rabu da sake ganin sa bayan wasu ƴan kwanaki , duk yadda ta so ta daure ta manta da shi , ta gagara a hankali damuwar rashin cigaba da ganin sa ta fara duƙushe walwalar ta , saboda wannan ne karo na farko da zuciyar ta ta fara son wani ɗa namiji ,

Ganin damuwar ta na neman kai ta ƙasa , sai ta nemi Gnala da ta bincika mata wanene wannan sabon balaraben bawa ? me kuma yasa ta daina ganin sa ? Ko an sauya masa shiyar aiki ne ?

Ba'a ɗauki wasu kwanaki ba ta samu duk wasu bayanai game da Ghaddafi , sunan sa , asalin sa , iyayen sa da laifin da suka yi har aka kawo ƙarar su ga Maimartaba aka hukunta su .

Kuka ta zauna tana yi sosai , so take ta tunbuƙe son shi daga ran ta ji da tayi ko kusa basu dace da juna ba , shi ɗin maƙasƙanci ne ko a cikin maƙasƙanta ko ɗaya ba shi da nagarta da ya dace da samun soyayyar ta .

To sai dai ita zuciyar da so na farko ya fara fasawa ya dasu a cikin ta tauri ne da ita tare da ƙwalafaci , dan haka bayan wasu kwanaki kaɗan sai ciwon son shi ya dawo mata sabo fil ,

Jin ba zata jure rashin ganin sa ba yasa bayan ta samu tabbacin inda yake zama da la'asar sai kawai tayi badda-kama cikin baƙaƙen kayan su na buzaye ta rufe rabin fuskar ta da mayafin ta , ta ratsa sorayen gidan su ba tare da ta bari kowa ya gane ta ba ta fice daga gidan su rana tana daf da faɗuwa , bata ko damu da iskar hunturu wacce ke tayar da rai-rayi da take ta busawa tana tila ƙasa a idanu hanci har ma da kunnuwan al'umma ba ,

Kasantuwar bata saba fita ita kaɗai ba hasalima yau ce rana ta farko da ta taɓa tako ƙafafun ta shiyar unguwar da take baya da Masarautar su da take ta talakawan liƙis , sai tayi ɓatan kai , ta gagara gane kwatancen da Gnala ta yi na inda aka ce Ghaddafi yana zama , ta nemi hanyar jirgin ƙasa ta rasa .

Ƙura tayi buɗu-buɗu da baƙaken kayan jikin ta , magariba kuma ta kawo kai , da kyar ta samu ta tsayar da wata budurwa ta tambaye ta ina ne tsohon hanyar jirgin ƙasa ?

Budurwar ta gwada mata hanyar da hannu, juyawa tayi da sauri ba tare da ta ko yi mata godiya ba ta fara taku zuwa kan hanyar da ta mata nuni ,

  " hala can kike noufin zouwa ? Ko kouwa kin san da kwai hatsari bissa hanyar kou ? Kin san fa an sau waɗannan tsinananan samari da suke ratse bissa hanya nan , a shawarce kadda ki bi ta wannan hanyar war hakka .

   Tsayawa tayi cak , ba ta juyo bata kuma ce ƙala ba , sai ta sake kaɗa kan ta tayi gaba ta miƙa sosai a hanyar har ta tarar da matattciyar hanyar jirgin ƙasan da duk bola ta mamaye ta ,

Warin da yake wajen ya sanyata rufe hancin ta tana tsallaka tsumi-tsumin bolar da take wajen ,

Shal hanyar take babu kowa ko Æ´an dabbobin da suke kiwo akan bolar babu kowa ya kaÉ—a dabbar sa gida kafin a sibare masa ita gobe kasuwa .

Sai hange-hange take yi cike da burin son ganin sa ,

Taku ta fara ji daga bayan ta kafin warin taba ya mamaye ƙofofin hancin ta ,

Da sauri ta juyo karaf suka haÉ—a ido da shi tare da waÉ—ansu samari biyu daga dama da hagun sa ,

Daga cikin mayafin ta ta saki tattausan murmushi zuciyar ta na cika da farin-cikin sake ganin sa ,

Warware mayafin fuskar ta tayi , ranar da tayi jazur gaf da faɗuwa ta haske ta tana ƙarawa farar fuskar ta jaa da kyau , cikin siririyar muryar ta tace " Ghaddafi wajen ka na taho .

Zaro ido yayi yana daɗa kallon ta , babu shakka wannan gimbiyar nan ce ɗiyar sarki to me ya kawo ta wajen nan me kuma take nema a wajen sa ?? Hayaƙin tabar da ya cika bakin sa da ita ya fesar ta hanci ta baki .

Tun bayan wannan ranar sai soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin ƙananan matasan biyu ba tare da tunanin me ke je ya dawo ba , soyayyar junan su ta rufe musu ido daga hango tarin banbancin dake tsakanin su ,

Cikin watanni shidda sun yi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki duk kuwa da cewa daga ɓangaren ita Gimbiya maimounatou babu wanda yasan da batun soyayyar su ita da Ghaddafi  , sau biyu kawai suka taɓa haɗuwa , rana ta farko da ta je wajen sa sai kuma rana ta biyu da ta kai masa kyautar wayar tafi da gidanka sabuwa dal , da ta sa Mahaifiyar ta ta saya mata lokacin ma wayar sai hannun wane-da-wane tare da wasu kuɗaɗe masu yawa .

Zancen tafiyar ta makarantar jami'a ta babbar birnin Niamey shine ya tayar da hankalin su , saboda nisa da zasu yi da juna .

A gobe zata tafi makaranta , ta saci jiki kamar yadda ta saba ta je wajen sa da hantsi ,

Akan Æ´ar rusasshiyar katangar wani kangon gida ta tarar da shi , a shirye tsaf yake cikin wandon gonjo da rigar sanyi mai haÉ—e da hula da ya saya daga cikin kuÉ—in da ta masa kyautar su .

Yana daga sama yayi mata nuni da gefen sa kan katangar akan ta hauro ta zauna ,

Dariya tayi da haƙoranta tana kaɗa kai tace
    " Bani iya hawa bissa nan ai kaima ka sani ,

Murmushi yayi ya diro ƙasa bata ankara ba ya ɗaga ta ya ɗora ta kan katangar runtse ido tayi zuciyar ta cike da tsoro ,

Bata san zaman sa a gefen ta ba sai da ya zunguri kafaɗar ta , a hankali ta wara ido tana kallon sa , sam ta kasa sabo da takaɗarancin Ghaddafi ita bata saba irin wannan rayuwar ta ƙarancin tarbiyya ba .

   Cikin muryar sa mai sanyi sosai ba'a ce daga bakin sa amon ta ke tasowa ba yace ,
     " ranki shi daɗe ai bashi kamata ba ke kina ƙasa ni ina sama tsololo , ke ai gimbiya ce ɗiyar sarki ni tamkar bawa nake a gare ki ,

   Hararar sa tayi sai kuma tayi murmushi , a hankali tace
   " bana so kana taɓa min jikina , kuma kai baka cikin jerun bayun gangar jikina amma zan yi farin ciki da zaka zama bawan zuciyata .

    Murmushi yayi mai sauti , " ai tun-tuni nake hadimi ga zuciyar ki gimbiyata , amma meyasa bakya son ina taɓa ki ? Ya tambaye ta yana kallon gefen fuskar ta

   " kawai ba yanzou ba , ta bashi amsa

" sai yaushe ,  yace yana shilla ƙafar sa

   " sai mun yi amre kou ? Ta ce tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta duk biyu .

  Ganin sa ya dawo kan ta , kafin ya ɗauke kan sa zuwa sama kaɗan da wata muryar dake bayyana ciwon zuci yace
   " Maimounatou bani da matsayi , nagarta  , kyaun asali kou dukiyar amren ki , ke ɗin kouma ai shaida ce bisa hakka .

Ganin ta ta mayar kan sa , tana jin yanayin ta na nishaÉ—i na jirkituwa zuwa tashin hankali da damuwa tace ,

  " Amma ai muna ƙamnar juna , abunda ka lissafa bai issa hana amren mou ba , tunda ai zaka iya sauya halaye sannan kouma kai Namiji ne kana da ƙarfi neman dukiya ko baka iya zage damtse wajen neman dukiyar amre na ?

  Idanun sa da suka fara yin jaa ya nitsar cikin nata raunanan idanun ,
  "  ta wacce hanya zan nemi dukiyar amren ki maimounatou baya.....

   Katse shi tayi jin yana shirin ɓata mata walwalar ta ta yau baki ɗaya alhalin kuma bankwana ta zo su yi , tace da shi

   " ka nemi dukiyar Amren Maimounatou ko ta wacce hanya Ghaddafi , buƙatata kawai muyi aure dagga na kammala ecole .

****

Bayan tafiyar Maimounatou sun cigaba da kasancewa a waya ita da Ghaddafi suna sake cinye zuciyoyin juna da so da ƙaunar juna ,

Basu sake haÉ—uwa ba sai bayan shekara guda a ranar da take ta zagayowar haihuwar Maimounatou ,

Babu zato aka sanar mata da sakon ƙiran da wani baƙo ke yi mata a can filin makaranta , tayi mamaki sosai saboda duk cikar jami'ar babu wani ɗa namiji ɗaya da suke ko da gaisuwar kirki ne .

Amma haka kawai ta ji zuciyar ta na son zuwa amsa ƙiran koma wanene , dan haka ta kama hanyar inda aka kwatanta mata

A tsaye ta tarar da mai ƙiran nata ya bada baya a jikin wata ƴar ƙaramar mota ƙirar golf da ta sha jaan fenti tana ta ɗaukar ido .

Daga sama har ƙasa take kallon sa zuciyar ta na kai-kawo wajen tantance shi ɗin ne ko ba shi bane ?

Juyowar da yayi ya hutatshe da zuciyar ta daga tunanin tantance shi , saɓanin haka zallar farin ciki ta ji yana tunbuƙowa daga ƙasan ranta , tamkar tayi tsalle ta rungume shi take ji a lokacin

   Hannunta biyu ta kai tana rufe bakin ta da haƙoranta ke buɗe tana dariya , sai kuma tayi ɗan tsalle tana matsawa daf da shi ta haɗo haruffan sunan sa cikin wani irin sauti mai nuni da ɗoki da farin-ciki da take ciki tace.
      " Gha°ddafi ? Kai ne ? je ne peux pas croire mes yeux mon amour ,

   Dariya yake lokacin da ya zare baƙin tabarau ɗin dake idanun sa , cike da murnar ganin ta ya kai hannu ya riƙo hannuwanta ya jaa ta yana ƙarasa rufe tazarar dake tsakanin su ya haɗa ta da jikin sa , cike da salon son ya burge ta ya harhaɗo kalmomin da ya shafe tsawon wata guda yana koyon su yace ,

     " tu m'as tellement manqué chérie ,

Bayan sun gama ɗokin ganin juna , Maimounatou ta kasa ɗauke idanun ta daga kan sa duk wani motsin sa ƙara burge ta yake yana sake nutsar da ita cikin ƙaunar sa ,

Yadda yayi shar da shi yayi gayu ya sake fiddo tsantsar kyaun sa , da cikar zatin sa na matashin Namiji , kasa jurewa tayi ta tambaye shi ,
    " Ghaddafi ina ne ka samou dukiya hakka mai yawa har ka sai moto ta hawa , ka gan ka kouwa yadda kayi gayu tamkar ɗiyan saraki wallahi ka burge ainun ,

  Ƴar dariya yayi ,kafin yace da ita
   " cikin dukiyar amren mu da na fara taru na ɗauki kaɗan na sayi suturu doumin nayi kwalliya na burge ki , kadda samarin jami'a ƴan gayu su kwace min ke ,

Ba tare da ta damu da ta tambaye shi wacce sana'a ya fara yi ba ta washe ƙaramin bakin ta tana cewa
   " Duk faɗin babban birnin Niamey babu namijin da zai iya kwace maka ni Ghaddafi ,
 
Da murmushi a fuskar sa ya buÉ—e kujerar motar sa na baya ya shiga fiddo manyan kwalayen da yayi mata birthday gift yana jera mata a gaban ta ,

Zuciyar ta tana sake bunƙasa da ƙaunar sa take bin sa da kallo bata ƙi ba ace cikin wata mai kamawa a ɗaura auren su .

*****

Cikin shekaru huɗu na karatun ta Ghaddafi ya bunƙasa ya zama hamshaƙin attajiri , ya ma ɗauke iyayen sa da ƙannen sa daga Niger ya mayar da su can ƙasar su Mali ya gina musu sabuwar rayuwa ya ƙere musu gida na zamani .

Zuwa lokacin ita da kan ta Maimounatou tasan Ghaddafin ta ya sha kwana , ana kuma damawa da shi a harkokin masu dukiya , sai dai ita da kan ta ba zata ce ga takamaimai sana'ar sa ko aikin sa ba , baza ta ce ga inda yake samun kuÉ—aÉ—en da yake mata wasa da su cikin kyautuka na bajinta ba da har wasu lokutan takan yi masa faÉ—an kuÉ—aÉ—en sun yi yawa , amsar da kullum yake bata shine
       " wannan kaɗan ne dagga cikin dukiyar Amren ki da nake biɗa ina tarawa Maimounatou,

Soyayyar su kuwa sai abunda yayi gaba kusan kowa da yasan Maimounatou yasan da soyayyar ta ga Ghaddafin ta , idan aka cire iyayen ta amma hatta Æ´an uwanta makusanta kowa ya san sunan sa , sun kuma shaida wasu daga cikin manyan kyautukan da yake yi mata ,

Haka shi ma ta ɓangaren Ghaddafi tun daga kan iyayen sa da ƴan uwa zuwa abokanan sa tun na farko da suka riga daman suka san da Gimbiya Maimounatou har zuwa kan sabbin abokan sa babu wanda bai san labarin Gimbiya Maimounatou ba ,

A cikin shekarar ne kuma gwamnatin ƙasar Niger tayi hoɓɓasa kan gagararrun ƴan fashi da makamin da suka addabi baki ɗayan kusurwowin ƙasar ta Niger ta kan kowacce boda guda bakwai da kasar ke da su ta Nigeria, Chad, Algeria, Mali, Burkina Faso, Libya, da Benin. sun hana duk wani ɗan kasuwa shan ruwa ya tsirga masa cikin ƙasa da shekaru biyar , da har suna ne da su na musamman da ake ƙiran su da shi escouade de lions .

escouade de lions sun gagari kananun sojoji su waye kuma ƴan sanda ? bare kuma ma'aikatan hana safara da miyagun kaya ,  ƙananan ƙwari a wajen su kenan ,

Kisa suke tare da ɓarna yadda suka so suka ga dama , gwamnati ta rasa yadda zata yi da su , dayawa daga cikin su ɓoyayyun fuska ne da su babu takamaimai wanda ya san fuskokin su , sannan an gaza gano takamaimai madakatar su da za'a iya taƙile su ta nan .

Youssouf Abdoul-Azizou Baskore ,shine sojan da babban hafsin soja na ƙasar Niger ya wakilta a matsayin wanda zai ja tawagar aikin da zai kawo ƙarshen waɗannan gungun ƴan fashi da makamin , lokaci kaɗan bayan dawowar sa daga ƴakin da aka tura su Libya.

Cike da zuciyar jarumta da son kare hakkin ƴan ƙasar sa Youssouf ya karbi aikin da aka ba shi , inda ya nemi taimakon haɗin guiwar ƴan sandan ciki da dole sai da taimakon su za'a kai ma nasarar cafke ƴan fashi da makamin .

A dai-dai lokacin rayuwa ta yiwa Ghaddafi da Maimounatou daɗi domin watanni uku kaɗai ya rage mata ta kammala karatu baki ɗaya ta bar makaranta , abu na gaba shine ta gabatar da Ghaddafi ga iyayen ta , a ɗaura musu aure daga nan su shilla zuwa ƙasar France da suka zaɓe ta a matsayin kasar da zasu barji amarcin su a can.

Kafin cikar watannin wani irin liƙewa Ghaddafi ya yiwa Maimounatou koyaushe yana sintiri tsakanin garin da yake da Niamey ,

Duk da cewa Maimounatou tana jin daɗin yadda yake yawan ziyartar ta a ganin ta ƙaunar da yake yi mata ne take sake hauhawa a zuciyar sa da daman take tantamar kamar ƙaunar da ita take yi masa yafi wanda yake yi mata yawa ,

Sai dai yadda yake yawan taɓa ta tare da bayyana mata cewa shi fa a sarari a matse yake da ita yana da muradin ta , lamarin yana damun ta , domin ita ta san bata cika ƙarfi ba muddin akan ƙaunar Ghaddafi ne , sannan.ta ɓangaren gangar jikin ta ma rarrauna ce .

Cikin haka abunda take ƙoƙarin gujewa ya auku , shaiɗan tare da tsantsar son da take yi masa ya sa ta bashi kan ta a wani dare ,

Daga lokacin kuma sai gurɓacewa ta shigo cikin soyayyar tasu domin tamkar busa ake musu ko umarni , koyaushe suka haɗu sai sun yi ta'asa kafin su rabu , a hakan daga zuciyoyin kowannen su niyyar auren juna bata sauya ba , a ganin su zinar da suke ba kome bace tunda aure zasu yi illa ƙarawa juna so tare da ƙoƙarin kiyaye juna daga zuwa ga waɗansu mutanen daban  ( abunda matasa dayawa suke ta'alaƙa ƙazamtatciyar rayuwar su akai , ba kome bane illa tsagoron son zuciya da rashin shan tsabga da ace ana zane matasan mazinatan da duk aka kama da laifin zina a nahiyar mu kamar yadda addini ya tanadar da abun ya ɗan ragu ) .

Daren yau bayan sun gama fasiƙancin su a ɗakin otel ɗin da musamman Ghaddafi yake da ɗakin sa ,
   Yake sanar da Maimounatou kan cewa tafiya ta kama shi zouwa Benin da zai iya kaiwa tsawon kwanaki goma kafin dawowar sa da zuwa lokacin kwanaki biyu kachal ya rage tayi jarabawar ta,  ta ƙarshe  .

   Ba domin ran ta ya so ba suka yi bankwana washegari da safe da alƙawarin zasu dunga yin waya koyaushe ,  ya kama hanya bayan ya ajiye ta a bayan makarantar su .

Sun cigaba da yin waya har kwanaki uku bayan tafiyar sa kafin daga baya kuma ta daina samun wayar sa , shima kuma bai ƙira ta ba , ta damu ainun saboda hakan ɓakon lamari ne a gare ta su shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da sun yi magana a waya ba ko da kuwa baya ƙasar .

Wasa-wasa sai da suka shafe tsawon kwanaki shida babu waya a tsakanin su zuwa lokacin hankalin maimounatou ya kai ƙurya wajen tashi , jarabawar ta ma sai tayi da gaske take iya rubutawa ,

Bata da aiki sai gwada ƙiran layukan sa da duk take da su , cike da fatan ko Allah zai sa ta same shi ,

Bayan ta fito daga jatabawar ta ta yau waje ta samu daga can gefe ta zauna tana cigaba da lalubar layin Ghaddafi , amma kamar koyaushe cikin kwanakin duk layukan sa basa tafiya  ,

Tsumu tayi a zaune idanun ta cike da ƙwalla , hirar da ta ji wasu matasa na yi daga gefen ta ta ɗan ɗauki hankalin ta , inda ta ji suna labari akan jajirtatcen sojan ƙasa Youssouf ɗa a wajen sarkin Maraɗi wanda cikin watanni da basu cika uku ba , a kwanaki biyar da suka wuce tawagar sa da yake jagoran ta ta tarwatsa gungun ƴan fashi da makamin da suka yi mafaka akan tekun rairayin saharar tenere da yake boda tsakanin Niger da Chad ta yankin Bilma dake ƙarƙashin jahar Agades.

An kashe mafi yawa daga cikin ɓarayin manya daga cikin su kuma sun gudu , ciki har da shugaban su da ba'a kai ga sanin cikakken sunan sa ba amma bayanai sun tabbatar da cewa ɗan asalin ƙasar Mali ne .

Kalmomin yabo iri-iri suka dunga yiwa Biyamuradin maraɗawa , bayan sun gama tsinewa ƴan fashi da makamin suna kuma fatan Allah yasa a kai ga samun nasarar kashe sauran da suka rage ko Al'umma sa yi kai-kawo a tsakanin ƙasashe cikin kwanciyar hankali ,

Ita bata wani ji abun burgewa ba , idan ba lalacewa ba me yakai É—an sarki Yarima a yadda ta ji sun faÉ—a , yin aikin soja bauta ?wannan ai shine a aiki kare ya aiki wutsiya .

Miƙewa tayi tana nufar wajen da ɗakin kwanan ta yake sai dai kafin ta ƙarasa ta ji wayar ta na kiɗan shigowar ƙiran Ghaddafi , cike da ɗoki ta daga wayar tana ajiyar zuciya tamkar wacce tayi gudu .

Cikin abunda ke ƙasa da mintoci goma sha biyar tayi shiri cikin doguwar ɓakar rigar ta ta rufa hula baƙa a kan ta tare da rufa ɗankwalin rigar da ta kare rabin fuskar da shi tundaga kan ta , ta nufi babban wajen hutawar da Ghaddafi ya sanar mata yana jiran ta a wajen ta je ta same shi .

Yadda ta gan shi duk a firgice da ƙananun raunika a fuska da hannuwan sa da suke sarari ya duƙushe tasirin farin-cikin ganin sa da tayi , sai ta shiga tambayar sa kan ko hatsarin mota yayi ? Ko kuwa ƴan fashi ne suka tare sa akan hanya ,?

Bai bata takamai-mai É—in amsa ba a madadin haka wata sabuwar sallama ya shiga yi mata cikin sanar da ita sabuwar tafiyar da yake da nufin yi a yau zuwa France , da yace yana iya kaiwa watanni biyu zuwa uku ,

Da wani irin yanayi na tsoro take kallon sa , yaya zai tarki yin tafiya haka mai nisa bayan yasan suna mataki na ƙarshe ne na gaf da cikar burin su me hakan ke nufi ?

Duk yadda ta so ta masa rigima yaƙi bata dama , dole ta yadda suka yi sallama ,cikin kwantatciyar muryar sa ya cigaba da rarrashin ta kafin wayar sa take danƙe a hannun sa tayi ƙarar alamun shigowar saƙo , yana karanta saƙon ya miƙe a ɗimauce yana raba ganin sa a da'irar wajen hankalin sa baki ɗaya ba'a kwance yake ba ,

da ido ta bi shi ƙwalla na taruwa mata , yadda ya juya bai ko saurare ta ba , ya taɓa mata rai babu shakka akwai abunda yake faruwa da shi da bata kai ga sani ba , taku biyu yayi ta ƙira sunan sa , a hankali ya juyo yana ɗora ganin sa akan ta tsayayyun idanun sa na bayyana wani irin yanayi na tsoro .

" Ghaddafi , kada ka manta da ni zan jira ka koume tsawon lokaci , ta furta hakan tare silalowar hawaye daga kwarmin idanun ta ,

Daga inda take ta hango yadda laɓɓan sa suka motsa ko da kunnuwan ta basu iya jiyo mata amon sautin kalmomin sa ba ta fahimci cewa cewa yayi ,
    " Maimounatou ina son ki .

Ƙarar harbin bindiga da ya gifta ta kunnen ta shi yasa ta kusa hantsilawa daga kan kujerar da take zaune ,  kafin ta farga harbe-harbe sun yawaita a sararin wajen da nan take mutane suka kaure da guje-guje , akan idanun ta Ghaddafi ya ɗaga kafafunsa ya taka da gudun gaske yana barin wajen kamar fitar kibiya .

Ta miƙe tsaye amma ruɗani ya sa ta koma da ƙarfi ta sake zama tana toshe kunnuwan ta biyu , ta gaban idanun ta takun ƙafafun sa da suke sanye da manyan takalman sa na soji ya wuce da gudun gaske ya dafa baya akan hanyar da Ghaddafi ya bi .

Ba zata iya sanin iyakar adadin mintocin da tayi durƙushe a gurin ba, zuwa lokacin da harbin bindugogin ya tsagaita , lokacin ta samu damar miƙewa daga durƙuson da tayi a ƙasan teburin gaban kujerun wajen .

Ba tare da ta tantance yanayin da take ciki ba ta fara taku da sauri da niyyar ficewa a wajen , can gefen zuciyar ta na son sanin halin da Ghaddafi ke ciki , sai dai bata saurara ba domin tana buƙatar nutsuwa mai tarin yawa a dai-dai lokacin .

Kamar ance ta ɗago kan ta lokacin da ta ɗaga ƙafa tana barin wajen , idanun ta suka sauƙa kan dogon sojan da yake sanye da kakin sa da jini ya ɓata gaban rigar , har yana ɗiga ta wajen hannun sa ,  yana tafe da takun sa na jarumta a hankali ta sauƙe ganin ta ƙasa inda ya riƙo ƙafar mutumin da ya harbe yana jaan sa tamkar kayan wanki , idanun ta suka sauƙa kan fuskar Ghaddafi da jinin da ya ɓata fuskar sa zuwa ƙirjin sa bai hana ta gane shi ba ,

Duk wasu jijiyoyin jikin ta ne suka tsayawa yin aiki , jinin ta ya daskare , kamar yadda kunnuwanta suka toshe , numfashi kuma ya fara kokawar kufce mata , ƙafafun ta taji suna mata girgiɗi.

    " Ya kashe min Ghaddafi , Ya kashe min Ghaddafi .

Sune kalmomin da suka ƙwanƙwashi ran ta suka farkar da ita daga suman zaune da tayi , wani irin ihu ta sa mai sauti da ya jawo hankulan tsirarun mutanen da suka rage a wajen da zuwa lokacin daman ma'aikatan wajen ma korar jama'a suke .

Babu wanda ya saurari kukan da take yi da ake zaton na firgici ne aka tisa ƙeyar ta zuwa wajen park ɗin .

Mutuwar Ghaddafi bata zowa Maimounatou da sauƙi ba domin tamkar hauka tayi , surutai kawai take yi tana sambatun da ba'a wani fahimtar me take cewa , bata rubuta jarabawar ta ta ƙarshe ba hukumar makarantar ta turawa da Maimartaba mummunan saƙon rashin lafiyar ƴar sa ,

Nan take aka tado da mutane ciki har da manyan yayun ta suka zo Niamey suka  ɗauke ta zuwa gida Agades .

Kowa ya ga yadda take yi a lokacin cewa ake gamo tayi , aljannu ne suka taɓa ta, dan haka aka shiga magungunan iska ba ji ba gani ,

Ganin ana ta banka mata hayaƙi babu gaira ba dalili , ya sa ta rusuna ta bar surutai da ƙiran sunan Ghaddafi , sai ta koma ba un ba un'un , bata iya ci bata iya shan ruwan kirki wanka ma bata yi ,

Ba'a tsahirta da magunguna ba , aka cigaba da kawo magani iri-iri , na wanka da na sha da na turare , kai har da na shafawa da shaƙawa ,

Mafi yawa zubda su take yi , ta kuma kasa sanar da kowa dalilin tashin hankalin ta , to cikin iyayen ta biyu wanene ya san Ghaddafi ?? Ya san Alaƙar su ? Babu .

Tsawon wata guda ta fara dangana sai kuma rashin lafiya Mai tsanani ya taso ta a gaba , ciwon ciki mai tsanani duk ɗan abunda ta samu ta ci sai tayi aman sa , ga zazzaɓi mai zafi tare da ciwon kai ,

Kasancewar ta wayayyiyar ƴar jami'a ita da kan ta ta fara bincikar kanta game da sauyin yanayin da take ji a jikinta  , a sirance ta aiki Gnala ta sayo mata abun awun tabbatar da samuwar ciki .

Da zaton motsuwar kwakwalwar ta Gnala ta karɓi kuɗin ta sayo mata ,

Kamar yadda tayi zato gwajin farko ya nuna mata samuwar ciki a jikin ta ,

Ranar damuwa ta dawo mata sabuwa dal , tayi kuka irin wanda tun mutuwar Ghaddafi bata samu damar yin irin sa ba sai ranar ,

" ina zata da cikin jikinta tana É—iyar Martaba É—iyar Asali É—iyar sarki ?? Ya zama dole ta rabu da cikin , ina ma da ace aure suka yi ita da Ghaddafi ta samu cikin nan ? Da zata fi kowa murna da samuwar sa ,

Ita da kanta ta saci hanya ta fita , wani babban ɗakin sayar da magani ta je , bayan ta wadata mai sayar da maganin da maƙudan kuɗaɗe ya ɗau maganin zubar da ciki mai ƙarfi  ya bata ,

Tun da ta saya maganin sau uku tana yunƙurin shan maganin tana kasawa , cikin satin gaba ɗaya ta sake lalacewa ta rame tamkar wacce take tsananin ciwo ,

A karo na huÉ—u ta runtse ido ta haÉ—iye maganin , ta yi kamar yadda pharmacist din ya faÉ—a mata ,

Cikin ƙasa da mintoci arba'in kachal jini ya fara sauƙa mata kafin ciwon ciki mai tsanani ya biyo baya , jini kuma ya ɓalle mata ,

Kasancewar ta kulle ƙofar falon ta bayan ta kori bayun da suke kula da ita sai Gnala kaɗai ya sa babu wanda ya san irin wahalar da ta sha da irin zubar jinin da tayi daga ita sai Gnala ,

Da kyar jinin ya dai-daita ciwon cikin kuma ya lafa ta samu bacci ,

Sai zuwa la'asar ta farka ta ji ƙarfin jikinta duk wasu kasala da rashin ƙarfi irin na masu ƙaramin ciki ta rabu da jin su ,  dan haka tayi wanka ta shirya tana jin raguwar damuwar da take ciki da kaso goma cikin ɗari ,

Kai tsaye sashin Mahaifiyar ta ta yiwa tsinke , inda ta tarar da ita a babban falon ta tana kishingiɗe bayu na mata hidima , ganin ta ya sa ta miƙe zaune cike da jin daɗi ta rungume ta tana murnar ganin alamun samun lafiyar ta ,

Duk da cewa ta hango wasu yanayi da bata gane da su ba a tare da ita amma ta danganta kome da larura irin ta jinnu da babu abunda basa sawa .

Suna zaune aka hasko fuskar Colonel Youssouf Abdoul-azizou baskore a babban tv da yake kafe a gaban su , ana bayani akan ƙarin girman da ya samu sakamakon samun nasarar kawo ƙarshen gungun 'yan fashi da makamin nan da ake yiwa take da escouade de lions , inda bayan rundunar su ta tarwatsu su daga terene , ya samu nasarar kashe manyan huɗu daga cikin su , ciki har da shugaban su Ghaddafi Yacouba Dango .

  Raba hoton aka yi biyu , gefe hoton gawar Ghaddafi ne , gefe kuma hoton Youssoufa ne yana dariya lokacin da ake masa ƙarin girma .

****

   Gimbiya Maimounatou ta sanya hannuwanta biyu ta share hawayen ta , kafin tayi ƴar dariya da take nuni da tasowar miƙin ƙasan ranta ta cigaba da cewa

" Tun daga wannan ranar na kuɗurci aniyar ɗaukar fansa akan sojan da ya kashe Ghaddafi da hannun sa , nima so nake na kashe shi, so nake na ɗanɗana masa baƙin-ciki irin wanda ya samar a gareni .
     " Ban damu da laifin da ake tuhumar Ghaddafi da shi da yasa aka kashe shi ba , a ganina Ghaddafi bai cancanci mutuwa a yanzu ba kome kuwa girman laifin sa , akwai sasauci hukuncin kisa yayi tsanani ga Ghaddafi , mafi girman sashi na raina ma ban yadda da laifin da aka danganta Ghaddafi da yi ba , saboda ni ban taɓa ganin sa yayi kisa a gabana ko satar kayan wani ba .

  " daga lokacin na shiga bin hanyoyin da duk nasan zasu taimaka min wajen cimma nasara kan ƙudiri na , a ƙarshe kuma nayi nasarar sanyawa Youssouf so na da har ta kai ga ya amre ni sanin da nayi wannan ce hanya mafi sauƙi da zata kaini ga kashe shi ,

" ga jin daɗina lokacin da nake bibiyar rayuwar sa ina kafa masa tarko bayan auren mu , sai na fahimci ba ni kaɗai bace ba ke farautar rayuwar sa , ciki har da kai da Mahaifiyar ka Mammadou , babu ɓata lokaci muka haɗa hannu wajen ganin ƙarshen maƙiyin mu , kuma ga shi a ƙarshen ƙarshe mun yi nasara ,

  Wata ƴar dariya ta sake yi tana tsare ɗan sanda da ido , tace " wai ya ƙarasa mutuwa ne ko kuwa har yanzu yana shan wuya ?

    Wani ƙaƙƙarfan marin da aka ɗauke ta da shi da ya sanya ta yin tangal-tangal tare da giftawar walƙiya a idanun ta ya sanya ta rufe bakin ta ruf ,

Da wani irin yanayi a muryar Tafeeda yace ,
  " Babu shakka kin kasance mayaudariya , azzaluma ban yarda ke kina da ɗigon imani ba a ran ki , kamar yadda kika ce hukunci wanda yayi kisa ko ta yaya ne a kashe shi a irin naki ƙwaƙwalwar mai cike da duhun jahilci , da ke da duk wasu masu hannu cikin wannan mummunan aikin da kuka yiwa Youssouf muddin ya kai ga rasa ransa kamar yadda kuka so , wallahi baki ɗayan ku sai na kashe ku da bakin bindiga ta koda kuwa hukunci ya so muku sassauci , ni sai na kashe ku , sai na ....

  Muryar sa ce ta sarƙe jikinsa har tsuma yake idanun sa sun koma ciki tsabar tashin hankali , ya juya da sassarfa ya fita zuciyar sa cike da ruɗani ashe masoyin ka da ka yadda da shi kan iya zama mai farautar ranka ? Da ya tuno irin tsananin son da Youssoufa ke yiwa Maimounatou sai hawaye ya sauƙa a idanun sa ,

wacce irin zuciya ce haka a ƙirjin Mammadou da Hajiya Mama da zai sa a haɗa baki da su wajen kashe mutum irin Youssoufa shin me ya taɓa yi musu da zafi da ya cancanci ƙiyaya irin haka ? Babu shakka mutum ya tsoraci maƙiyin sa da yake ƙin sa babu wani dalili bayan ta hassada , irin wannan ƙiyayyar mai zafi ce , tsawon zamani baya tasiri wajen goge ta .

Yana kai ga ficewa daga harabar ofishin motar su Maimartaba da kansa ta sawo kai dan haka yayi baya da tasa motar tare da sake kashe ta ya fito ,

Sama-sama suka gaisa da Maimartaba a tare da shi da mahaifin shi kansa Tafeeda , sai kuma Hajiya Mama su uku ne kawai tare da direba ,

Hajiya Mama tayi firi-firi da tashin hankali ta bi bayan su Maimartaba , Tafeeda ya dafa musu baya yana jin kamar ya shaƙe Hajiya Mama ,

A ciki kai tsaye suka nemi da a haÉ—a su da Maimounatou da Mammadou ,

Bayan shigar su inda suke da har lokacin kowannen su bai rusuna ba , Mammadou yana ganin iyayen sa ya fashe da kuka yana ƙaryata duk wasu kalmomin da Maimounatou ta yi , akan yana da hannu wajen kisan Youssouf ,

  " Ranka shi daɗe wallahi ƙarya take min ban san kome ba , bani da hannu wajen mutuwar ɗan ouwana wallahi Abba ƙarya take min ,

Cike da nutsuwa Maimartaba yake kallon sa , kafin yace

   " Mammadou , Youssoufa bai kai ga mutuwa ba , har kawo yanzou yana asibiti , zuwa nan nayi saboda na fidda kai ne daga nan muddin ta tabbata baka da hannu cikin lamarin nan , muddin kuwa aka kama ka da laifi ni bani da ikon hana mahukunta aikin su , zaka cigaba da zama a nan har zuwa yadda hali zata kasance ga Youssoufa tsakanin rayuwa da mutuwa , daga nan sai mahukunta suyi hukuncin su yadda ya dace .

   Wani irin runtse ido Maimounatou tayi , tana son cewa wani abu sai dai cikar kamala da ƙima irin ta Maimartaba ya wuce ta yi wargi a gaban sa ,

Hajiya mama wacce ganin hawaye tare da tashin hankalin da ɗan ta yake ciki tare da kalaman da Maimartaba ya furta suka haɗu wajen ƙara mata tashin hankali kan wanda take ciki , ta zaburo tana cewa ,

  "  Ni nasani Mammadou ba zaka yi yunƙurin kashe ɗan ouwan ka ba , na san irin tarbiyyar da na yi maka , ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yiwa ɗan ouwan ka sai dai idan wannan makirar ce take ƙoƙarin samun abokin da zata raba laifin ta da shi , shine zata maka sharri , tsinannan ibilishiya ta Allah ba taki ba Youssouf zai tashi bai mutu ba ,
    Ta ƙarasa zancen tana fashewa da kukan wanke kai ,

  Kukan nata bai tsawaita ba ta tsinkayi muryar Maimounatou tana cewa ,

  " Hajiya kenan, ai ibilisan muna da yawa , amma ke ce shugabar mu , idan kin ce sharri na yiwa ɗan ki akan gubar da na zubawa Youssouf dan an samu tangarɗar cikar aiki , asirin da kika yiwa Youssouf na shan giya da neman mata domin ya tozarta ya rasa damar samun sarauta shima sharri ne kenan ? Duk da cewa kowa ya shaida saboda har ɗiyar banza Youssoufa ya ajiye aikin ki kuma ya kai ga matakin nasara kamar yadda duk kika tsara Youssoufa ya rasa martabar sa a idanun Al'umma ,

Kukan kura Hajiya Mama tayi ta shiga dukan Maimounatou , tana cewa ,
   " sharrin ki kaina zai dawo ? wallahi ranka ya dade ƙarya ɗiyar nan take min so take ta ga bayana , so take na tozarta shi yasa take faɗe-faɗen surruka masu nawi .

Maimartaba bai ce ƙala ba ya juya ya fita , yana fita , Maimounatou ta tunkuɗe Hajiya Mama da ƙarfi , cikin tsawa tace ,
    " Saurara ɗiyar talakawa , mai gajaren asali ni nan da kike gani na ɗiyar sarki ce , sarkin da ya yafi duk wani sarki ƙarfin mulki a ƙasar nan ,  dan haka ahir ɗin ki da ki sake taɓa lafiyar fatar jikina , kiyi ta kan ki da ramin da yake gaban ku ke da ɗan ki,  idan ku ka faɗa babu mai iya cire ku , ni kuwa kin ganni kome girman ramin da na faɗa daga Mahaifina ya ziro hannu zai tsamo ni .

Kamar wacce aka yiwa umarni Hajiya Mama tayi hanzarin barin É—akin zuwa inda su Maimartaba ke tsaye suna sauraron muryar duk labarin da Maimounatou ta bayar ,da Æ´an sanda suka naÉ—a a waya .

Bai jira karshen labarin ba Maimartaba yace su tafi kawai , jami'an tsaro su cigaba da yin aikin su duk ta yadda ya dace da ƙa'idar aiki ,

shi hankalin sa baki ɗaya yana ga Youssoufa da yake asibiti cikin mummunan yanayin mutu-kwakwai rai-kwakwai  da a halin yanzu an gama shirin kome na fita da shi ƙasar India , lokacin tashin jirgin su kawai ake jira nan da awanni uku .

A gidan baya na motar da Hajiya Mama da Maimartaba suke zaune , banda raba ido cike da rashin gaskiya babu abunda take yi ƙwarai Kalaman Maimounatou a gaban Maimartaba suka shammace tare da ƙara mata tashin hankali , ganin kome na shirin kwaɓe mata cikin ƙanƙanin lokaci .

Muskuɗawa tayi tana kallon Maimartaba tayi ƙanƙan da kai ta fara cewa ,
    " wannan ɗiya lamarin ta abun tsoro ne, dukkananin kalamanta cike suke da ƙarairayin....

Da hannu ya dakatar da ita ba tare da ya dubi sashin da take ba yace
"  Su kalaman mutum suna iya zamar masa tarko su fallasa ko wanene shi , ita hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare , da har sukan faɗi a cikin turbar su amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba , sukan manta da cewa ita mugunta rami ce mai zurfi da a ƙarshe da mai tonon ta take ruftawa ciki , ki adana kalaman ki akwai wajen yin su ba nan gabana ba .

Muƙut ta haɗiye busasshen yawun tashin hankali , ta san irin wannan zaurancen na masu hikima da mafiyawancin lokuta Maimartaba ya fi amfani da su cikin kalmomin sa .

Hasashen manufar kalamansa ya sa gumi karyo mata yana tsiyaya ta cikin jikin ta , " Babu shakka kwaɓarta tayi ruwa tsululu .

****

Ƙarfe biyu na ranar jirgin da zai tafi ƙasar India ya ɗaga da Youssoufa yana a halin rashin sanin ina yake ?  A tare da shi da Maimartaba da kansa , da Hajiya Umma da kuma Tafeeda .

Tamkar wutar daji haka labarin gubar da Matar Biyamuradi Youssoufa da ɗan ouwan sa Mammadou suka ciyar da shi ya shiga ratsa kowanne lungu da saƙon ƙasar Niger baki ɗaya ,

Cikin kwanakin duk wasu kafar yaÉ—a labarai zancen ake ana sake maimaita sa , har wani sashi na daga muryar Maimounato cikin labarin da ta bayar kan dalilinta ake sakewa ,

A halin haka labari ya shiga sauya salo da launi iri-iri dake ƙara munana sa , wasu ma cewa suke ai fasiƙanci Maimounatou da Mammadou suke yi , da kuma sanin ita uwar Mammadou ita ce ma ta bada gubar da aka ciyar da Youssoufa ita .

Tozarta da ɓacin suna irin wanda Hajiya Mama bata taɓa zaton afkuwar sa a gare ta ba , ita ce ta faɗa mata lokaci ɗaya ,

Tuntuni labarin irin auka-aukar da Maimounatou tayi ya iske kunnen iyayen ta , da hakan ya sa take jinin Maimartaba sarkin Agades ya hau , aka ciccɓe shi ranga-ranga zuwa asibiti .

Nan take wasu daga cikin dangi suka fara Allah wadarai da ita .

 

    Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kuna lafiya ?

Ina sane da haƙurin bibiyata da kuke yi , ina kuma godiya bisa yawan ƙaunar ku ga rubutuna nagode irin sosai ɗin nan , nima ina ƙaunar ku a duk inda kuke ina muku fatan Alkhairi .

Nagode
[12/26/2019, 9:58 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

47

Falmata tun tana zuwa É—akin Hajja tayi ta zama ba tare da ta iya faÉ—in abunda ke kaita É—akin ba ,

Har dai a kwanaki shida bayan zuwan su ta daure bayan sun gaisa da Hajja wacce take kishingiÉ—e akan Æ´ar katifar É—akin ta , ba tare da ta yadda sun haÉ—a ido da Hajja ba tace ,

" Hajja daman zuwa nayi nace miki , un'un wai inji Baa , sai kuma tayi shiru ,

Hajja wacce ta tashi zaune , tace ,

"UwarÉ—akina faÉ—i mana , me kike son faÉ—a min ?

"Daman nace Hajja idan kun yi waya da shi ki ce masa akwai saƙon da nake son faɗa mi shi inji Baa ,

Kallon tsanaki Hajja take yi mata kafin ta ce , " Shi wa fa ?

  Ɗago kanta tayi ta saci kallon Hajja , tana sake gintse fuska tace , " shi Baban Mama ko ?

Salati Hajja ta sa tana tafa hannuwa , kafin tayi ƙanƙan da ido tace ,
   " Ke Fatima ki fita idona na rufe ,nace ki fita idona ,  idan ba kin mayar da kanki wata bi ta can ba , har kya bani saƙo wajen Mijin ki ? Cewa nake ke kika fi kusanci da shi fiye da kowa a ƙasar nan ? To bari na faɗa miki daman ina cike da ke akan irin sakarcin da kika yi na gudowa daga ɗakin auren ki , akan wannan mummunar zuciyar taki mai ƙullaci da bauɗaɗɗan halin ki na miskilanci idan baki gyara kin nutsu kin san ina ke miki ciwo ba ke ce da Nadama marar amfani wataran , ni nagaji da nuna miki gabas kina daɗa bauɗewa,

Zunburo baki Falmata tayi , ƙasa-ƙasa tace " to ai ba komawa zan yi ba ,

Ashe maganarta ta shiga kunne Hajja , sai ji tayi tace ,
  " Auho aikin kawai kike domin shima kuwa wannan karon kin kai shi bango da iyashegen ki , dan tunda muka taho yau kwana shida muna yini na bakwai bai biyo sawun mu ba ko da da ƙiran waya , ni kuma na ƙira layin nasa da nake da shi bai tafiya , ai kin ga sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha , idan zaman gidan daɗi ne ki zauna ga waje kiyi ta zama har mahadi ya bayyana .

Daga haka ta jaa bakin ta ta tsuke tana kawar da kai .

Rai a ɓace Falmata ta miƙe ba ko sai anjima ta fice a ɗakin , Hajja ta bi bayan ta da kallo , cikin ran ta cike da tausayin ƙuruciyar dake ɗiban ta tana shirin sanyata yiwa kanta sakiyar da ba ruwa , ita a karan kanta ba ƙaramin damuwa tayi ba da rashin ji daga wajen Youssouf kamar yadda yace kafin rabuwar su zai ƙira domin jin labarin halin da suke ciki , rashin ƙiran nasa ya ɗaure mata kai , tsoron ta ɗaya kada ace ya sau auren Falmata , ko kaɗan bata fatan hakan , tayi ƙiran wayar sa aƙalla sau goma bayan tahowar su amma bata shiga fatan ta Allah yasa lafiya .

Haka kawai ta ji damuwa tana mamayar ta kan cewa da Hajja tayi tunda suka taho wai bai ƙira ba , ita a nata zaton su na gaisawa da Hajja ta waya , kawai bai neme ta bane sanin da yayi tana fushi sosai da shi dan haka ko an kawo mata wayar ma ba karɓa zata yi ba kamar yadda ita ma ta kuɗurce a ran ta ,

To ashe ma ita take zaton haka shi yana can ko tunawa da sha'anin da ya shafe ta baya yi , ya riga ya yada da ita da abunda ke tare da ita , duk sai jikin ta ya sake yin sanyi ƴar hirar da suke yi ma ita da Yakaka da Rahima ƙarama kafin tashin ta zuwa ɗakin Hajja,  sai ta gagara cigaba da sa baki tayi lamo a kwance tana jin yadda abunda ke cikinta yake dunƙulewa waje guda ,

Yakaka ita ta lura da shirun da tayi dan haka ta kai hannu ta jaa yatsar ƙafar falmata tare da cewa ,

  " Maman baby yaya ne ? Akwai damuwa ne ?

  Janye ƙafar ta tayi ba walwala a muryar ta tace ,
   " Maman mama kin san dai na ce ku daina ƙirana da sunan nan bana so ,

Rahima ta kwashe da dariya "  to Yakaka mu daina cewa Maman Baby , mu koma ƙiran ta da Matar soja yafi daɗi ko Hajja Falta ?

Kuka ta fashe da shi da a farko suka yi zaton na wasa ne , sai da suka ji har tana jaan hanci tukun suka tsahirta daga dariyar da suke duk kuma sai hankalin su ya tashi jikin Yakaka har rawa yake ta tallafo Falmatan zuwa jikin ta suna rige-rigen tambayar ta " me ya same ta take kuka ??

   Ba tare da ta daina kukan ba tace ," Nace muku bana so  , bana so bana so , kun ƙi dainawa .

  Da sauri Rahima tace , " Yi hakuri ba zamu sake ba dan Allah ki daina kuka daga wasa ? Haba Fatima-zahra Maman Baby ,
   Da sauri Yakaka ta ɗago tana hararar Rahima ,
   Dariyar da Rahima take bata tuƙe ba ta dafe baki tare da cewa
   " Au So nake nace Mamar Mama ta biyu , yi haƙuri ba zamu sake ba kin ji ƴar ƙanwata ?

Batare da ta amsa ba ta zame daga riƙon da Yakaka tayi mata ta koma ta kwanta a inda ta tashi , wani irin yanayi marar daɗi na sake mamayar ta baki ɗaya bata jin daɗin kome , abu kaɗan sai ya ɗaga mata hankali ya ƙara mata damuwa .

  Fuskar Yakaka cike da damuwa take kallon ta , damuwar da ta hango tare da ita ya ɓata mata walwalar da take ciki mai daɗi , cikin ran ta ta haƙiƙance akwai abunda ke damun Falmata haka kawai ba zata yi kuka ba daga ɗan wannan wasan , ji tayi ta damu da son sanin damuwar ƙanwar ta  .

Tun daga ranar sai duk walwalar ta ta ragu damuwa ta bayyana a cikin suffa da mu'amalar ta , kome take yi babu nishaɗi duk kuwa da cewar basu taɓa tsintar kan su a cikin gata da riritawa irin na wannan lokacin ba , daga kan Mamar su har zuwa Amnee da Baa , Rahima da kusan kowa na gidan nan-nan ake da su ,

Sai dai damuwar ta mai zurfi ce , kullum cikin kasa kunne take ta ji ko Hajja zata ƙira ta tace ga Youssouf ya ƙira su yi magana ko kuwa ma tace ya ƙirata ita sun gaisa amma ko alama ta yin ƙiran nasa bata ji ba , ita kuma tsoron surutun Hajja ya sa ta kasa tambayar ta .

***

Yau tana zaune a tsakanin mamar su da Amnee suna Æ´ar hira , su ukun ne kawai a wajen , Rahima da Yakaka sun tafi amso sabbin É—inkunan su da Baa ya bayar da kuÉ—i aka kawo musu atamfofi da lesika aka kai É—inki domin su yi amfani da su wajen bikin auren Rahima da yanzu bai fi kwanaki goma sha biyu ba suka rage .

Amnee ta É—an dube ta tana murmushi tace ,
   " Fatima zahra , cikin nan naki wata nawa yake ciki ne ? Anya bai kamata ki fara zuwa awo ba ?

  Da sauri ta ɗago kai ta dubi Amnee sai kuma ta sunkui da kai batare da tace kome ba ,

Khaalty Rahima ta É—an dube ta , tace Fatima ba dake ake ba ?

  A hankali tace , " Nima ban sani ba Amnee ,

Jimm Amnee tayi kafin ta ce , " to ai ya kamata ki fara zuwa awo banda ma dai shirme irin naki Fatima cikin fari da ake ɗokin sa da yi masa ƙirgen ƙwaƙwaf amma ke kyace baki san watannin sa ba ?

Hajja wacce take ƙarasowa falon daga waje inda ta gyara shanyar alkamar da ta wanke ta yin kunun Baa , sarai ta ji wasu daga kalaman Amnee , tace
   " Wallahi uwar masu gida ke ma dai kya faɗa , wannan uwarɗakin tawa da kike gani kome nata daban ne bata ajiye kome ba sai wauta , cikin nata yana gaf da cika watanni huɗu a yadda lissafi na ya nuna min , sai dai kuma kin san cikin fari ɓuya ce da shi amma lokacin da suka dawo dai daga can turai cikin bai wuce watanni biyu ba da ƴan ɗoriya , daga can ta yo cikin ,  yanzu kuma kin ga dawowar tasu kusan kwanaki talatin .

Dariya ce ta so kama Khaalty Rahima jin wannan ƙokari na Hajja na ƙididdige kwanakin cikin Falmata da ko ita kakar ɗan ko ƴar ba ta iya haka ba ,

Ran ta cike da jin daɗin tsantsar ƙaunar da ta lura Hajja na yiwa ƴa ƴan ta tace ,
  " Hajja baki da dama ke da Uwarɗakin ki ba mai shiga tsakanin ku , wannan zuwa awon ma ai ke zaki dunga raka ta  .

  Ƴar dariya Hajja tayi kafin ta harari Falmata tace ,
    "  can dai su ƙarata ita da Babba Uwar Mama ita zata raka ta bana iya miskilancin fatima ba .

Dariya Amnee tayi kafin tace,
  " zan yi maganar da Baa Alaji idan ya so sai ya nema mata iznin mijin nata , kan fara zuwa asibiti saboda kuwa zuwa awo abune mai matuƙar muhimmanci ga mata masu ciki , yadda duk muka yi sai ki shirya a fara kai ki kin ji ko ƴata ?

A hankali ta gyaÉ—a kai kurum , tausayin abunda ke cikin ta kan yadda Mahaifin sa yayi banza da su ya fara kamata .

Daga haka Amnee da Mama suka cigaba da yin hirar su , a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin su , domin kuka da take jin yana taso mata ,

Tana shiga É—akin ta sanya tafukan ta duk biyu ta rufe fuskar ta tana fashewa da kuka marar sauti .

Tana tsakiya da yin kukan ta tsinkayo Sallamar Doctor Hamza , shuru tayi tana saurarawa jin tashin muryar gaisawar da suke shi da iyayen su ,

Jin sun gama gaisawa sai ta miƙe tan share hawayen ta , Doctor Hamza yana sawun gaba na mutanen da ba zata manta alherun su ba a rayuwar ta ,dan haka ya zama dole duk inda ta ji shi ta je ta gaishe shi ko da kuwa babu ƴan uwantaka a tsakanin su bare yanzu da suke ƴan uwan juna makusanta ,

A hankali ta fito , ta tako zuwa tsakiyar falon ta zauna tana gaishe shi ,

Da murmushi yake amsawa yana jin daÉ—in ganin ta samu lafiya , yace
   " Fatima ƙanwata ke ce haka kika girma ? Alhamdulillah lafiya ta samu .
Ƴar dariya tayi , kafin tace " Ni ce Yaa dakta ,

  Dariya shi ma yayi yace " lalle girman 'ya mace ba wuya , Al'amarin Ubangiji kuma ya zarta yadda duk muke zato , Khaalty lokacin da na kawo yaran nan gidan nan ko kusa bani da masaniyar muna da wata alaƙa tsakanina da su , kawai nayi niyyar taimakon su ne domin Allah , ashe kin ga ma abun farin-ciki ƙannena ne su , lokacin da Amnee take sanar da ni ba ƙaramin mamaki nayi ba da farko ma ni na shiga ruɗani ne su waye Amina da Fatima ? Sai da ta min bayani sosai ,

Ya nisa kafin ya cigaba da cewa , " Khaalty nayi murna da Allah ya haÉ—a ki da Æ´aÆ´an ki , Allah ya kuma kare ku baki É—aya , ya sa bakin wahalar ku kenan .

  " Amin Amin ɗana , tace da sigar zolaya ,
  Shima dariyar yayi da sauti sanin cewa ta ƙira shi da ɗanta ne dan tasan bai son haka tun yana ƙaramin sa a cewar sa tayi ƙanƙanta ta ƙira kanta Mamar sa ina ma laifin tace ita yayar sa ce  ?

  Khaalty Rahima ta cigaba da cewa , " kawai sai muka gan ka babu sanarwar zuwa ? Ko wani aikin ka zo yi ?

  Jingina kansa yayi da kafaɗun kujerar da yake kai , yace
  " Baa ne ya ƙirani tun shekaran jiya , yace lalle na zo cikin kwanaki biyun nan , to nima daman kuma ina shirin zuwa saboda shirye-shiryen bikin nan ban sani ba ko akwai abunda za'a iya buƙata mai muhimmanci ayi a gama akan lokaci tunda ga ku , kar ya zama irin na bikin su zainab kome a hagunce , aiki ne ya tsare ni ban iso da wuri ba .

  " Na fara shiga wajen Baa ɗin amma na tarar da shi da mutanen nasa kin san sai kuma ya sallame su da abunda suka saba , kai mutanen mu sai a hankali , wai kawai sai ku mayar da wani mutum ɗaya wajen zuwa ku faɗi buƙatun ku da damuwar ku kamar wani shi ɗin injin buga kuɗi gare shi ? To wai wanene bashi da buƙatu da damuwowi ?

Sallamar Rahima da ta shigo da ɗan gudun ta , ya sa shi mayar da ganin sa kan ƙofar , dai-dai da shigowar Yakaka , wacce tunda ta ji Rahima na murna tana cewa ga motar Company ya zo , ta ji jikinta yayi sanyi duk taku ɗaya na kafafun ta da jin ƙarin hauhawar bugun zuciyar ta ,

Idanun ta ta sauƙe kansa da shigowarta falon , karaf suka haɗa ido ,

Kowanne su yayi saurin janye ido Doctor Hamza ya haɗa da kawar da kai ita kuma ta sunkui da kan ta , cikin raggon taku ta ƙaraso ta bayan kujerar da Amnee take kai , tayi durƙuso da kyar ta haɗo kalmomin ,
   " Ina wuni ,
  Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da zolayar Rahima da yake cewa " ke little idan ana shirye-shiryen aure ramewa ake yi ke kuwa ga ki sai sake kumbura kike , me takwarar ki take baki haka hala ɗure take miki ??
   Dariya Khaalty Rahima da Rahima ƙarama suka sa a tare , kafin Rahima ta zagaya ta kujerar da Amnee take ta saƙalo hannuwanta a wuyan ta , tana haɗa fuskokin su tace ,

   " Khaalty kar ki faɗa masa , abun sirri ne ko ?
 
Amnee wacce ta lura da yadda yayi watsi da Yakaka , kuma bata ji daÉ—in hakan ba sai ta ce ,
   " Takwarata tana gaishe ka fa ?
Wani wur-wur yayi da ido , sai kuma yace " Ok Lafiya , ba tare da ya dube ta ba illa haÉ—e girar sa da yayi , ya zaro wayar sa daga Aljihunsa , kaf fara'ar fuskar sa ta É—auke .

A hankali Yakaka ta miƙe tana murmushin yaƙen akan wasan da Mamar su da Rahima suke yi , sum-sum ta wuce ɗakin su .

Ƙiran wayar Amnee da aka yi yasa suka ɗan tsahirta daga hayaniya , bayan ta ɗaga wayar sai ta saurara ,
  " to Baa Alaji tace. 
Duban Khaalty Rahima tayi , tace
  " Ukhtee , da ke da Ɗan ki ku zo muje Baa alaji yana ƙiran mu .

***

Bayan sun sake gaisawa a tsakanin su ,a ƙagauce Amnee da take zaune daga gefen sa tace
  " Baa Alaji lafiya dai ko ? Wannan ƙiran Allah ya sa Alheri ne. 

Prof ya dube ta da É—an murmushi , yace " inshaAllah Alheri ne Aminatu ,
ganin ya mayar kan Hamza da Khaalty Rahima da suke zaune a ƙasa kafin ya fara cewa .

" Dalilin da yasa na ƙira ku ba kome bane sai kan wata magana ko kuwa nace shawarar da na yanke tun watanni baya , amma ban sake haƙaƙewa akan abunda nake niyyar yi ba na haɗa Aure tsakanin Ƴaƴa na biyu kai Hamza da kuma ƙanwar ka Amina ba , sai da tabbatuwar yaran nan ƴan uwan ka ne ba wasu bare ba da ba'a san asalin su ba , hakan ya sa na sake ganin dacewar lamarin fiye da farko ,

" Duk da cewa batun ƙarin auren da nace kayi ba sabon abu bane a wajen ka , tun kwanaki na sanar da kai ka kuma yi na'am kawai wacce nake burin ka aura ɗin ne baka kai ga sani ba , sai a yanzu nake sanar da kai Aminatu ƴar Rahima ƙanwar Mahaifiyar ka ita ce matar da nake son ka aura a matsayin matar ka ta biyu , da fatan ba zaka yi gardama ba ??

Daga Khaalty Rahima har Doctor Hamza baki ɗaya idanu suka zuba suna kallon sa , a hargitse sosai ƙwaƙwaƙwar Doctor Hamza take , meke nan yake ji ? Yaya Baa zai masa haka ?

A hankali ya sauƙe ganin sa daga kan prof ya sunkuyar da kansa ƙasa , ta wutsiyar ido yake hango yadda Khaalty Rahima ta dawo da ganin ta kan sa , zuciyar sa na shaida masa cewa amsar sa kowa a wajen yake jira , kan ya amince ko kuwa a ah  ?

abunda ya bi duk wasu gaɓɓai na jikinsa ya kassara bai wuce kaifin idanun Khaalty Rahima ba , matar da tunda ya buɗi ido ya gansu tare da Mahaifiyar sa a matsayin shaƙiƙan juna , ƙaunar ta a gare shi kuma mai tarin yawa ce , jin daɗin wasannin ƙuruciyar sa duk ya yi tare da ita , shi kuwa ta yaya zai iya cewa yaƙi ƴar da ta haifa daga cikin ta a tsatson idanun ta ?  wallahi ba zai iya ba , Baa ai bai kyauta masa ba da ya titsiye shi da wannan batun a gaban idanun Khaalty Rahima ,

Satar kallon Amnee yayi yaga yadda ta nutsu fuskar ta da wani irin yanayi na nuna  zaƙuwa tana kallon sa .

Yawan ƙaunar da Amnee ke yiwa Rahima ya san kuskure kaɗan idan yayi kan lamarin nan zai matuƙar sanyata a ɓacin rai , shi yaya zai yi ne ?

Muryar Khaalty Rahima da ta ratso shirun  wajen ya katse masa tunani ,

  Da wani yanayi cikin muryar ta da ya sha banban da murmushin yaƙen da yake fuskar ta a lokacin tace ,

  " Yaya , mun ji daɗi mun kuma yi farin-ciki da wannan haɗin da kayi niyyar yi , Sai dai Yaya , Hamza ai tuni ya riga ya zaɓi abokiyar zaman sa har kuma tafiyar su ta fara miƙawa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna ba tare da yana da niyyar  ƙara yin wani auren ba , dan haka ni ina ganin Yaya da dai an bar yarona ya zauna da matar sa ɗaya kar a ɗaura masa nawin mata har biyu da bai shirya ba .

Prof da yake kallon duk su biyun , ya gyara zama , yana mayar da ganin sa gaba É—aya kan Khaalty Rahima .

" Rahima wannan ba hujja bace da zata hana auren Hamza da Aminatu , sai dai idan kin nuna min Aminatu ba ɗaya take da sauran 'ya'yan da na haifa da nake da ikon zaɓa musu abokan rayuwa ba, ko kuwa har yanzu baki huce daga abunda ya gabata ba shiyasa zaki gwada hakan ta hanyar hana wannan al'amarin tabbatuwa ko Rahima ?

Da taruwar hawaye a idanun ta muryar ta cike da tashin hankali , ta shiga girgiza kanta tana cewa " Haram ko kusa ba haka bane Yaya , dan Allah kar kace haka , a tun kafin bayyanata Aminatu da ƴar uwarta suna da wani majiɓanci da ya wuce ka tsawon wannan shekarun ? kayi haƙuri ba nufina ba kenan , ni shi nake...

"  idan ba haka bane to ki barni nayi abunda nake da manufar yi inshaAllah alheri ne a garemu baki ɗaya ,

Bai saurara ba ya juya ga Doctor hamza da zuwa lokacin gumi ke tsattsafo masa a goshi , da murya dake cike da gargaÉ—i Prof yace ,
   " Likita kai nake saurare kai kuma me kace ?

   Ɗago da kan sa yayi ya dubi iyayen sa , yanayin da ya gani a kan fuskokin su,  su duka biyu ya razana shi musamman ma Amnee dake masa wani kallo mai kama da harara , da sauri ya mayar da kansa ƙasa kafin muryarsa cikin rashin amo sosai ta fito ,
       " Na'amince Baba , Na Amince Baa .

Daga haka yayi shiru yana jin wani irin ɓacin-rai da ya taho masa tare da Amincewa auren yarinyar da ta gama yawon ta shekara da shekaru dan kawai tana ƴar uwar sa ,

Daga sama ya tsinkayo muryar Prof yana cigaba da cewa ,
   " To Alhamdulillah Allah ya maka Albarka , ya baka 'ya'yan da zasu maka biyayya fiye da yadda ka min , Ubangiji Allah ya jiɓanci lamarin ka ya raba ka da sharrin duniya, Allah ya sa Albarka a zaman ku ya baku zuri'a masu yawa da Albarka , ka faranta min rai sosai .

Ya nisa lokacin da Amnee wacce haƙoranta ke washe tana ƴar dariyar dake nuni da zallar farin-cikin da take ciki take amsa addu'o'in sa ya cigaba da cewa ,
  " za'a haɗa auren naku da na Rahima ayi shi duk a rana ɗaya dan a rage hidima idan ya so ko bayan sati guda ne idan ka samar mata muhallin da ya dace da ta zauna a can Abujan kusa da kai sai ka taho ka ɗauke ta hakan yayi ko ?
  Yace yana mayar da ganin sa kan Amnee , wacce ta gyaɗa kai da sauri da maɗaukakin fara'a a fuskar ta tace , "Yayi sosai ma Baa Alaji , cikin sati uku masu zuwa ai su zainab sa iya zuwa Dubai yiwa takwarata kayan ɗaki .

Da wani irin bahagon yanayi Doctor hamza ya É—ago yana kallon su ,

Khaalty Rahima da duk hankalinta ke kan sa ta yi gyaran murya kaɗan , cikin ƙanƙan da kai tace ,
  "Yaa ka min izni nayi magana wannan karon a matsayina na innar ango madadin uwa ,
   Murmushi Prof yayi , "An miki izni , yace

" Yaya Dan Allah a mana alfarma , bayan an ɗaura auren a bamu ko da watanni biyu ne ya kammala shirin sa , kamar samar da wajen zama a tsanake , ya kuma sanar da uwargidan sa cikin kwanciyar rai ,  ya ɗan samu ya dai-daita lamuransa ,tunda nawi ne zai ƙaru masa kar a tsawwala yafi kyau yayi kome cikin lumana tunda indai ta zama matar sa ai kome ya kammala .

Cike da amincewa Prof yace , " To shikenan tunda kun nemi wannan Alfarmar an muku , amma ya tabbar kafin cikar watanni biyun ya kammala duk wasu shirye-shirye tunda É—an naki ai Babban likita ne albashin sa ya kai wani mizani amma duk da haka na É—auke mar nawin sadaki da duk wasu hidindumu da suka shafi biki na shi hidimar shine ya samar mata da muhalli mai kyau tare da É—aura aniyar kulawa da duk wasu hakoki nata da suke kan shi daga ranar da zata shiga gidan sa har zuwa ranar da mutuwa zata É—auki É—ayan su , kaji ko ?
  Ya ƙarasa zancen yana juya akalar tambayar sa ga Hamza ,
  " Gyaɗa kai yayi nagode Baa Allah ya ƙara girma ya furta hakan yana miƙewa yayi hanyar ficewa daga falon , Khaalty Rahima ma godiyar tayi musu sosai kamar zata zubda ƙwalla dan farin-cikin gatan da ake shirin yiwa ƴar ta ,

Tafe yake baya sanin ina yake ajiye ƙafar sa ,  Jacket ɗin sa riƙe a hannun sa saboda zafi da yake ji yana damunsa kota'ina cikin jikin sa tsabar tashin hankali , abunda ya faru yanzu a falon Baa so yake ace wani rarraunan mafarki ne daga cikin jerin shuɗaɗɗun mafarkan da ya dunga yi a shekarun baya , domin tuntuni ya wanke tabbatuwa hakan daga zuciya da tunanin sa .

Har ya kusa sashin sa ya tsinkayo muryar Khaalty Rahima tana ƙiran sa , juyowa yayi yana ƙirkiro wani rarraunan murmushi ya ɗora a fuskar sa ,
  Ta ƙaraso idanun ta akan fuskar sa tana nazarin sa , muryar ta cike da nutsuwa tace
   " Hamza kada fa ka damu kan ka wajen yin duk wasu hidindimu ko da gidan da zata zauna ɗin ma ka kama muku mai sauƙi idan ma ba hali ko ɗaki guda sai a bata a cikin gidan da kuke zaune nasan 'yata safiya ba zata ƙi ba , idan kuma duk hakan bata samu ba , zan sa Ukhtee ta roƙi Yaya ko anan sashin naka na gidan nan ai sai a barta tayi zaman ta ba ma sai ta tafi can Abujan ba , shi zaman aure ai bautar Ubangiji ce wurin Mace da Namiji baki ɗaya .

  Tausayin ta ya kama shi , bai bar murmushin da yake yi ba yace " kar ki damu Khaalty yadda duk Baa ya ce haka za'a yi inshaAllah babu abunda zai gagara ,

  Murmushi tayi , sannan ta cigaba da cewa , "Nagode, Nagode , yadda ka rufa min asiri kaima Allah ya rufa maka, ya baka 'ya'yan da zasu maka fiye da abunda kayi ga iyayen ka , nagode nag...

Hannunta ya riƙo ," haba Khaalty godiyar me kike min haka , ai ni...
  Da sauri ta katse shi , tana cewa "Godiyar kome ma , ka yi kome da yakamata nayi ta gode ma Hamza Allah ya ma Albarka ,

  " Amin ya amsa yana sakin hannun ta ya juya ya nufi sashin sa ,

A hanya komawa ciki Khaalty Rahima da Amnee suka haÉ—u , cike da farin-ciki suka rungume juna ba sai bakunan su sun furtawa junan su ba babu makawa sun san zucoyoyin su cike suke da farin-cikin faruwar wannan lamari.

" Baa Alaji yace a tambayi takwarata ita ma, ko ta amince ? Ko kuwa tana da wani wanda take so ya shirya yin aure , dan fa ba za'a mata dole ba ,

Ɗaure fuska Khaalty Rahima tayi , " wanne irin ma a nemi amincewar ta Ukhtee ? Shi namiji ma aka masa dole bare ita mace ?ai koma waye take so dole ta haƙura tunda Yaya ya yanke hukunci .

Murmushi Amnee tayi , " wa yace miki dole aka yiwa É—an ki ? Ba soyayya bace ya sa ya É—auko ta ya kawo ta gidan nan lokacin ma bai san ko suwaye su ba ? Ai kawai dan dai kaddara ta gifta tsakani badan haka ba da auren su ma zaki gan su ,

Ƴar fara'a Khaalty Rahima tayi , " duk da haka Ukhtee kin san fa irin aibun da yake tare da takwarar taki , ni gani nayi kamar an tauye shi da aka liƙa masa auren ta , kuma a yadda ma na lura yanzu ɗan nawa baya yi da takwarar taki ko da a baya ya nuna ra'ayin sa akan ta ,

Wucewa gaba Amnee tayi tana cewa " koma menene dai idan aka yi auren ai sa shirya kan su , so na gaskiya ai baya kankaruwa sai dai wani abu ya dusashe tasirin sa , ni bari naje na samu takwarata na shawo kanta ta amince ayi abun nan ranta na so , ba zan so ba a takuramin ita da auren dole ,

Ƴar ajiyar zuciya Khaalty Rahima tayi tana murmushi ta bi bayan Amnee zuciyar ta cike taf da ƙauna tare da farin-ciki marar misaltuwa da rabon ta da irin sa shekarun dayawa .

***

A É—aki Amnee ta tarar da su ukun suna gwada É—inkunan su , Falmata tana mitar burguza-burguzan riguna da siket É—in da telan ya yi mata , " mai sunan Mama dan Allah ki ga wannan siket É—in yadda ya min yawa ba ko fasali ni É—ai gaskiya a mayar ya rage min , naku ke da Yakaka cas-cas irin na Æ´an mata amma ni shine ya min haka siket kamar buhu ?
   Dariyar da tuntuni Yakaka take riƙewa ita ta ɓurtso kanta , cikin dariyar take cewa ,
   " Kai Falmata gaskiya ba'a iyar miki , ke kome aka miki bai yi ba, yanzu da matsattsu aka miki cewa za ki yi sun matse ki sun hana Baby sakewa yanzu kuma anyi wanda Baby zai wataya kince an miki buhu , Allah kana gani dai ,  ka shirya min Falmata ,

   " zunɓuro baki Falmata tayi dai-dai da shigowar Amnee da Mamar su ,
   " Maama kin ga ku faɗa musu su daina tsokana ta kullum Rahima da Yakaka basu da abun yi sai tsokana ta, yanzu ku ga irin ɗinki da suka kai aka min ,
ta É—aga siket É—in ta ,
"ku ga kuma nasu ,
tace tana ɗaukar siket ɗin Yakaka ta nuno , ta ɗora da cewa  " dan Allah Amnee za'a ce tela ɗaya ya ɗinka ? Nawa kamar wata gani garau , nasu kuma na yayi ?

  Karɓar kayan Amnee tayi tana ajiyesu gefe , tace " sun yi girma kam , kiyi haƙuri za'a mayar ya rage miki wannan ɗinki ai ko a Niger ayi wanda ya fi shi tsari bare anan Nigeria gidan cancara ɗinki ,

Ganin ta ta mayar kan Yakaka da take kallon su tana dariya da haƙori ,

   " Zo nan ki zauna takwara ta magana nake tafe da ita mai muhimmanci , duk ku nutsu ku bar shirmen nan ,
  Amne ta furta hakan lokacin da take zama a bakin gadon , tana yiwa Yakaka nuni da gefen ta kusa .

A nutse Yakaka ta taho kusa da ƙafafun Amnee ta zauna a ƙasa maimakon gefen ta da ta nuna mata ,

Cikin nazari Amnee tace ,
   "  Takwara akwai wanda kuke tare ne ? Ina nufin akwai wanda kuka yi wata magana ta aure da shi ??

Dumm Yakaka tayi , zuciyar ta na sauya bugu , a lokacin ba wanda ya faɗo mata sai wannan mutumin da yayi ta nacin bibiyar ta shekaru kusan biyu tana zille masa a abuja , kafin barinta Abuja dai Lubna tace ta ba shi number ta Amma ko sau ɗaya bata taɓa riskar ƙiran sa ba , wataƙila daman wasa yake , ita kuwa bayan shi ai ba wanda ta taɓa saurara mafi yawan masu cewa suna son ta duk gani take fasiƙanci zasu yi da ita , domin tunda tasan illar zina da zunubin ta take jin tsoron maza ma gaba ɗaya .

Tunanin ta ya katse lokacin da taji Amnee na maimaita mata tambayar , a hankali ta girgiza kai , " Babu kowa Amnee ,
    " kin tabbata ?  Ki fa faɗa min idan akwai ,
  Amnee ta sake furta haka domin haƙaƙewa ,
   Zuciyar Yakaka ta fara shiga ruɗu da son sanin dalilin da ya kawo wannan maganar ta sake cewa , " Allah babu kowa Amnee ,
  " To Alhamdulillah , Aminatu kina jina ko ?
  Bata jira ta amsa ba ta cigaba da cewa , " Baa Alaji , Baban ku na gidan nan ya yanke shawarar haɗa aure a tsakanin ku ke da Yayan ku Hamza , muna fatan ba za ki bijirewa Umarnin mu ba ?

  A razane ta ɗago kan ta saboda yadda zancen ya zo mata baga-tatan , ta shiga raba ganin ta tsakanin Mamar su da Amnee cikin wani irin jirkitatcen yanayi ,

Ganin yadda fuskar ta ta nuna yasa Khaalty Rahima hanzarin tare ko wanne irin sakamakon da zai biyo baya ta hanyar cewa ,
   " kuma har an riga an gama yanke magana za'a haɗa bikin ku rana guda da na takwarata nan da kwanaki goma sha biyu , babu sauran wata magana .

Ihun da Rahima ta sa tana tsalle ta taho ta rungume Yakaka  shi ya katse zancen khaalty Rahima ,
   " Alhamdulillah burin Big bro zai cika , Masha Allah Baa mun gode sosai wallahi , sai ta sake ta da gudu tana barin ɗakin tana cewa , " bari naje na taya bro murna wayyo Allah ,

   Shiru ne ya ratsa ɗakin sai tashin sautin murmushin Falmata da farin-ciki mai tsanani ya bayyana kan sa a fuskar ta ,

" Takwara baki ce kome ba ? , Amnee ta sake katse shirun ,

A hankali Yakaka ta É—ago kan ta ta É—an dubi Amnee muryar ta can ciki tace , " Shi ya yarda ?
  Tambayar da ta karya zuciyar iyayen nata biyu har ma da Falmata , kafin Amnee ta amsa ta sake cewa , " Idan har shi ya yadda shikenan Amnee ni ai koyaushe mai muku biyayya ce Baa kuma nima Babana ne , nagode da duk abunda kuka min .

Hannuwanta duk biyu Amnee ta sanya ta É—ago ta , ta zarce da rungumeta a jikinta ,
  " Allah ya miki Albarka takwarata Allah ya baku 'ya'yan da zasu muku fiye da irin biyayyar da kuka yi mana ,

Addu'o'i ta cigaba da yi mata Falmata na amsawa da Æ´ar muryar ta dake bayyana amon murna ,

Miƙewa Amnee tayi tare da cewa ," bari naje na sake sabunta tsari da shiri bikin ya zama biyu , kai wannan shekarar ta zo min da ɗinbin Alheru Alhamdulillah Allah nagode ma ,

Bata jira cewar su ba ta fita ta bar su , su ukun ,
   Yakaka ta ɗago idanunta dake cike da ƙwalla damuwa ɓaro-ɓaro a fuskar ta take kallon fuskar Mamar su tana son ko yaya ta bata damar da zata ce wani abu ,

A hankali Khaalty Rahima ta tako ta zauna a inda Amnee ta tashi , bata yadda sun haɗa ido ba tace " Naji daɗi da kika nuna halacci baki yi butulci ba , abu na gaba shine ki ɗauko haƙuri da juriya akan duk wani ƙalubale da za ki fuskanta a gaba ki riƙe su a matsayin makamin ki , sannan a ko'ina kika tsinci kan ki cikin kowanne hali ki ji tsoron Allah , Allah ya miki Albarka Amina .
   " Amin,  Yakaka ta amsa hawayen idanun ta na sauƙa bisa ƙuncin ta ,

Miƙewa khaalty Rahima tayi saboda zuciyar ta ba zata juri ganin irin wannan damuwar mai tarin yawa da take hangowa daga Yakaka ba , abunda ta riga ta sani inshaAllah cikin auren nan nasu akwai alheri mai tarin yawa ,

Tasan abunda Yakaka take tsoro bai wuce illar dake tare da ita ba akan irin abunda ta aikata , ita ta ɗau hakan a matsayin kaddarar Yakaka, kuma inshaAllah a wannan gaɓar ta ƙudurci aniyar yakice kunya irin wacce iyaye mata ke nunawa ƴaƴan su , zata ɗauri ɗamarar gyara ɗiyar ta ciki da bai tare da mata darussa masu inganci cikin ɗan zaman da ya rage musu tare , da zai taimaka wajen sauƙaƙa mata duk wasu ƙalubalen da ka iya taso mata a gidan aure .

Kayan gyara kuwa daga nan har N'Djamena, zata ɗau hanya ta tafi domin ta ga ta yiwa ƴar ta gyara mai kyau da zai taimaka ko kaɗan ne wajen samar mata da ɗan matsayi ko yaya a wajen Mijinta, sanin da tayi tana da abokiyar zama ko kusa ba zata so ƴar ta ta walaƙanta ba . ( Khaalty Rahima nima ina da saƙo zuwa N'Djamena nan amma ni turaren wuta nake so 🙄🤐 )

Tana bada baya daga ɗakin Falmata ta taso da sassarfa ta isa inda Yakaka take zaune kamar an dasa ta ko motsin kirki bata yi , tana zuwa ta rungume ta tana ƴar dariya-dariya tace , " Yakaka na Alhamdulillah , kin ga Al'amarin Allah ko ? Allah baya bacci Yakaka nayi murna , nayi murna , a kunne ta ta raɗa mata ,"Félicitations Mme Hamza Mustapha Dilmari,

Kukan da tun-tuni ke cin Yakaka a rai shi ta saki lokacin da tashin hankali yayi nasarar lillisa zuciyar ta , " Aure ? Aure tsakanin ta da Doctor hamza mutumin da ya tsani kallon ko fuskar ta ?  mutumin da yake zargin ta da tafiya yawon banza ? Mijin sofi ƙawar samy Baby ? Anya Mamaa ba zasu kaita inda za'a kashe ta bane tun kwananta bai ƙare ba , a gareta wannan ba gata bane ba .

****

Duk yadda Rahima ta dunga ƙwanƙwasa ƙofar falon Doctor Hamza bai taso ya buɗe ba duk kuwa da cewa yana zaune dirshan a ƙasa a falon sai dai damuwar da yake ciki ta toshe masa kunne daga jin hayaniyar Rahima , ya zurfafa cikin tunani .

  Wani irin yanayi marar daɗi ya tsinci kansa a ciki , ko kusa da yasan abunda zai riska kenan a garin da bai zo ba ,

Yarinyar da ta gama yawon banzan ta bai sani ba ma ko ta maƙalo wata cutar ita ce dan kawai Baa yana son gyara wani shuɗaɗɗan kuskure sai ya laƙa masa auren ta ?

Wannan da bata ajiye kome ba sai tarin ƙarairayi da yaudarar banza , har ita ce ake so ya gatata ? To wanne gata zai mata da bai nuna mata sumfurin sa ba a baya ?

Shi ya sani a da ya so ta amma yanzu ko alama baya jin ɗigo na son ta sai ma baƙin-ciki da yake ji a duk lokacin da ya gan ta .

Babu yadda zai yi , bashi da wata mafita shiyasa ya amsa auren ta da aka liƙa masa , da ace ba Khaalty Rahima bace uwar ta da Wallahi da ko ta halin ƙaka sai ya cisge wannan liƙin da ake son yi masa ,

To amma kasancewar ta 'ya ga Khaalty Rahima ya sa dole ya amince , zai aure ta , su zauna a yadda yanayi ya zo musu shi da ita ..!

Assalamu Alaikum masu karatu

Da fatan kun wuni lafiya ? Ina miƙo saƙon gaisuwa tare da fatan alheri agare ku baki ɗaya .

To ga fa abun yazo , wai inji mai tsoron wanka , Ina nufin bikin Yakaka da Hamza 😂
sister J , da Raly Garba , ku ne fa masu rabon anko , sai dai kuma ga lokaci ya zo a ƙure kwana goma sha biyu kachal ai ya muku kaɗan. 🤔

  
  
[1/4, 12:40 PM] +234 816 886 5113: MAFARI
( HARGITSIN RAYUWA )

UMM'MUAZ

48

MAFI TSAWON DA BAI ZAMA KARSHE BA.

A washegarin ranar da aka tabbatar masa da haɗin Auren sa da Yakaka nan da kwanaki goma sha ɗaya masu zuwa , Doctor Hamza ya tattara ya nasa ya nasa ya koma Abuja da sassafe , duk yadda Amnee ta dunga son shigo masa da zancen Yakaka tana son ta haɗa su , lokacin da ya shiga yi musu sallama ita da Baa , ƙi yayi , ko Khaalty Rahima sai ta wajen Amnee ya bar mata saƙon tafiyar sa .

Gaba É—aya baya cikin nutsuwar sa garin ya masa wani irin zafi .

Prof da Amnee basu wani damu da yadda alamun ɗan nasu ya nuna dake bayyana bai yi farin-ciki da auren da ake shirin yi masa ba , suka cigaba da yin duk wasu tsare-tsare da shirye-shiryen yadda bikin zai kasance , an riga an buga katin auren Rahima har ma an rabar , ganin cewa bikin Hamza ba na farko bane ,na biyu ne ,ya kuma zo a ƙurarren lokaci , sannan abun nasu tuwona maina ne , saboda sune dangin uwa da na uba saboda a cikin baki ɗayan dangin Uban su Yakaka har yau an gaza samo ko guda duk kuwa da cewa sau uku Khaalty Rahima tana bin sansanin ƴan gudun Hijira ko Allah zai sa ta ci karo da wasu daga cikin tsirarun dangin Mahaifin su Yakaka duk kuwa da cewar tsawon zaman su ba zaman daɗi suka yi ba , saboda karan-tsana da suka ɗora mata ita da yaranta , haka siƙau , sai dai Allah bai sa ta gamu da ko wanda ya san su ba , kai ko mutanen ƙaramin garin nasu ma Allah bai haɗa ta da su ba .

Dan haka sai basu wani damu da a sanar da dangi ba kawai suka bar lamarin a tsakanin su .

Amne ta ƙarfafa da a rufe zancen auren a tsakanin su ne saboda tsoro da take yi kar danginsu suyi wani yunƙuri na hana auren sanin da tayi tun da can daman ba ƙaunar ta suke ba ita da Rahimar ta , tayaya kuwa zasu so 'yar Rahima ta auri Hamza ? musamman da ya kasance Hamzan ai tasu yake aure 'yar yar'uwar su .

Dan haka ta dage akan a rufe zancen har sai É—aurin auren ya matso a yadda ta so ma sai sanarwar É—aurin auren kowa zai ji ,sai dai da alama hakan ba mai samuwa bane , koma menene ita dai zasu tsawaita addu'a ita da Khaalty Rahima kan Allah ya tabbatar da lamarin nan tare da Aminci

Shiri suke sosai a tsakanin su , lokaci ne yanzu na wayar tafi da gidanka , da saƙo ke saurin isa inda ake buƙata , ta waya Amnee ta sanarwa da dangin su na can N'Djamena labarin bikin da ya zama uku ba ma biyu ba , watau Hamza ,Yakaka da kuma Rahima ƙarama .

Murna ta ishe su a can nan take suma suka shiga sabunta shiri , da daman suke tsakiya da yin sa , saboda dayawa daga cikin su ,wannan karon suna shirin zuwa saboda su gana da ƴar uwar su wacce ta ɓace shekara da shekaru har aka fidda rai da sake ganin ta ,

Cikin masu zuwan har da yayun su maza da matayen su da wasu daga cikin 'ya'yan su , sai kuma dangin su na wajen uwa da na uba duk gasu nan dai gayya guda ,

Nan take labarin auren ya sake bazuwa a tsakanin su , jin cewa har da na 'yar Rahima mace da Hamza ɗan Aminatu, da za'a musu haɗin gida, nan take suka yi sabon zama na musamman , inda suka sake ninka gudummawar su da zasu tafi da shi da daman turaren wuta ne da turaren jiki na ruwa ( Humra ) har ma da na wanka da mayukan jiki da na gashi , ( kulaccan da karkar ) suka ɗau nawin yiwa Rahima ƙarama gudummawar sa ,a matsayin su na dangin uwa sai suka sake ninkawa da wani haɗin turaren wutar da humran , su kulaccan da karkar makamancin wanda yake ajiye duk suka haɗa acikin manyan mazubai suka rufe ,

Sannan suka sake ƙarawa da kayan ƙamsasa girki da daɗaɗa shi irin nasu na can , haɗi da ingantattun ganyayyaki haɗin shayi ( tea ) da suke ƙara lafiya da kuzari tare da sanya nishaɗi, shima roba-roba suka keɓence shi .

Bayan haka matar baban wan su da ake ƙira Hajje khalsum ta ƙira Amnee tana sake tambayar ko akwai kuma wani abunda suke so a taho musu da shi daga nan N'Djamena ?

Nan Amnee tayi amfani da wannan damar take sanar da ita buƙatar ta na son a haɗo mata kaya gyaran jiki tare da magagungunan mata ,irin nasu masu ɗauke da sunadaran da suke ƙamsasa kowanne saƙo na jikin duk wata matar da take amfani da shi , bayan sun mata gyara ciki da bai .

Amnee ta cigaba da cewa a faɗa mata adadin kuɗin da zai isa a kawo kayan gyaran kashi uku , kafin ta gama bayani Hajje Khalsum ta katse ta , tana sanar da ita cewa ai wannan ta kawo cuta inda ake da tushen maganin ta , domin kuwa ƙanwar ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya , ƙwararriya ce ta wannan fanni na gyaran mata ciki da waje , domin kuwa faɗin ƙasar su ansa da ingantattun magungunan ta , babban shago ne da ita anan babban birnin N'Djamena da taƙe sayar da irin waɗannan magungunan da kayan , har kuma ƙasa-da-ƙasa ake ɗaukar ta tana zuwa gyaran jikin , tare da haɗawa mata ingantattun magunguna dan haka kada ta damu , nan da kwanaki biyar inshaAllah zasu taho tare da ita .

Zuciyar Khaalty Rahima ta daɗa cika da ƙaunar 'yar uwar ta , domin ko bata faɗa ba tasan cewa dan Yakaka ne Amnee ta ƙira Mai gyara , da daman tuntuni take son tayi wani yunƙuri akai , amma kunya da kara suka hana ta ganin cewa duk wasu ragamar bikin na hannun Amnee , sai kuwa ga shi zata sa a gyara mata Yakaka ,

Duk abunda ake na zafafa shirye-shirye , Yakaka ta maida kan ta mai zaman ɗaki , daga kuma ta samu sarari sai ta shige banɗaki taci kukan ta , tsoro da damuwa sun hana ta walwala , tuƙuru tsoron rayuwar da zata riska nan gaba kaɗan take ,

Daga Amnee har Khaalty Rahima ba wacce ta bata sarari bare ta ji damuwar ta saboda sun riga sun san ko damuwar ta mecece ?dan haka suka kyale ta suna sabgogin su ,

Ganin bata yin wani shiri , ko alamun gayyatar ƙawaye koda na mutunci ne yasa suka fara lallashin ta kan cewa " yakamata ita ma ta gayyaci mutane , ranar auren ta rana ce mai ɗimbin tarihi wacce yakamata mutanen da duk tayi ko da zaman mutunci da su ne su shaida wannan ranar ,
Yakaka tace " ita fa bata da ƙawaye , ƙawarta ɗaya Lubna kuma tayi aure , bayan ita bata da wata ƙawa , da suka matsa mata ma kuka ta sa tana cewa " Amnee Mama kun san fa irin rayuwar da muka yi , ina mutane suka mu'amalance mu da mutuntawa bare har su kai mu kusa da su ? Da zamu iya ɗorar da zumunci idan bayan Malama Maryam da Lubna babu wasu mutane ta wajena ,

sai ta basu tausayi suka bar maganar , amma daga baya sai suka sa ta ƙira Malama Maryam ,bayan sun gaisa ta miƙawa Amnee wayar dan ita kunya take ji ta faɗi ranar auren ta da kanta , ta baki da baki Amnee ta shaida mata sanya ranar bikin 'yar ta kuma ɗalibar ta ,

Ba ƙaramar murna Malama Maryam tayi ba har ma tayi Alƙawarin halartar bikin ,

basu bi ta kan Yakaka ba wacce take faman ƙwalan-ƙwalan da ido tana son sake yin wani kukan , suka yi ficewar su daga ɗakin suka bar ta , dumuwar ba zai sa a fasa kome ba , domin na ɗan lokaci ne kuma gata ne babba ake shirin yi mata .

Cikin kwanakin nan Falmata sai ta fita walwala , domin ita labarin bikin Yakaka da Yaya dakta yayi awo gaba da kaso kusan talatin na damuwar ta , duk da cewa ba wai ta daina jin damuwa da rashin ji daga Biyamuradi bane , farin-cikin auren Yakaka ne yake saisaita mata damuwar ta .

Doctor Hamza kuwa tun ranar da ya isa Abuja ya so sanarwa da Sofiya halin da ake ciki kan lamarin aure da ya taso masa , saboda hakkin ta da yake kan sa ya zama dole ya sanar da ita .

Sai dai yadda ta tare shi cike da ɗoki kamar wanda ya shekara rabon sa da ita ba kwana guda ɗaya tal ba , sai ya kashe masa ƙwarin guiwar sanar da ita labarin da yake tafe da shi sanin da yayi ba abun farin-ciki bane a wajen ta,

Sai yayi zaune kawai yana bin ta da kallon yadda take ta ririta shi tana tarairayar sa , tayi kwalliyar ta fes-fes cikin riga da siket , ta mammatse manyan kayan da yafi so tare da ita sun firfito ko yaya ta motsa suna rangaji tare da dusashe masa ƙarfin gani suna tayar masa da kwaɗayi .

Shi dan ta shi tuni ya haƙura da ya zauna tare da ita ,ita kaɗai saboda a halin zaman su na aure babu ta inda ta kuskuro shi sai ta wajen girki wanda shi kuma hakan bai wani dame shi ba saboda shekarun girma da ya fara shigo masa , a matsayin sa na likita shekara arba'in ya kamata ya fara kiyaye kansa daga ciye-ciye barkatai da sunan jin daɗi .

Rashin haihuwar su kaɗai ke ɗan taɓa ransa , kuma yayi-yayi da ita taje asibiti ya haɗa ta da kwararrun likitocin mata su duba ta taƙi , daga baya yayi watsi da ita lokacin da ya fahimci akwai wata matsala tata da take ɓoye masa , koma menene ita ta sani shi dai ya san lafiyar sa rass , domin a farko-farkon shekarun auren su yayi gwaje-gwaje da dama kan rashin haihuwar su domin gano ina matsalar take ? Ta haka suka tabbatar masa da ingancin lafiyar ƙwayayen halittar sa dan haka shi bashi da fargaban kome ,

Yawan ƙaunar da take gwada masa salo-salo yasa yake ɗaga mata kafa , domin kuwa ta san ta kan sa sosai bai wani cika murɗe mata ba muddin ta raɓu da jikin sa ,

Domin a yanzu ma kasa sanar da ita labarin ƙarin auren sa yayi , maimakon haka kawai sai ya ɓige da neman samun nutsuwar gangar jikin sa ya shiga shinshinata yana gwada mata soyayya irin wacce ita dai tunda take da shi bai taɓa yi mata makamancin haka ba , zuciyar ta ta ji ta kunburo tana daɗa tunbatsa da ƙaunar sa , gefe guda kuma wani irin tsantsar farin-ciki take ciki , "yau Doctor ne yake nuna mata zallar so tare da kalamai masu tausasa zuciyar masoyi ? Babu shakka masu iya magana suna cewa daɗewa a mabauta ma ƴanci ce ."

Shi kuwa a ɓangaren sa zuwa washegari ya tabbatar dai ba zai fa iya sanar da ita ba , sai ya kuɗurce zai tura ta can Maiduguri da wuri , su da suka rakito auren sa san yadda zasu yi su sanar da ita domin shi Allah ya sani ba zai iya ƙarawa kansa damuwar haukar da sofiya zata iya yi ba akan ta shi damuwar da yake ciki , gara tayi haukar ta acan idan yaso ma ta huce akan ita Yakaka , shi duk wannan ba damuwar sa bace tsuntsun da ya jaa ruwa .

Saɓanin yadda ya zaci damuwar sa zata zama ƙanƙanuwa sai lamarin ya zarce tunanin sa domin tunda aka yi batun auren su kullum tsaffin laifukan ta daɗa sabunta kan su suke a zuciyar sa , baki ɗaya sai ya susuce kamar farkon lamarin .

Ya zama ko office ya tafi baya wani taɓuka aikin kirki , har waɗanda ke tare da shi suka fara fahimta , Suleiman Amininsa shine ya fara farga da yawan damuwar da yake ciki ya kuma matsa masa da tambaya ? a farko Doctor Hamza ba shi da niyyar sanar da Suleiman da kan sa , sai ko bayan auren , sai dai yadda ya matsa masa da tambaya yana nuna damuwar sa a fili ya sa shi sanar da shi cewa "aure zai ƙara da ƴar Innar sa da aka ba shi , "

Wani sasakai Doctor suleiman yayi yana kallon Hamza , kafin ya wani kwashe da dariya , sai da yayi dariyar ta ishe shi , Doctor Hamza bai ce masa ƙala ba illa ma rubuce-rubucen sa da ya shiga yi , yana jin yadda ransa ke ɓaci da dariyar walaƙanci da suleiman ya sanya shi a gaba yana yi .

" Ka ce dai alƙadarin Safiya ya karye , zaka yi wani yunƙuri dan ganin ka fara tara naka zuri'ar , lamari yayi kyau haka ake son Namiji to amma nayi mamaki ina kuma kan yi ko yaya zaka yi da mata biyu ?

Da wutsiyar ido Doctor hamza ya dube shi , ba tare da ya bar abunda yake yi ba yace ,
" Su masu mata biyun me suke yi da na su ?

Wata dariyar Doctor Suleiman ya sake kwashewa da ita kafin ya É—ora da cewa ,
" wataƙila jera su suke suna ado da su a gidajen su , ya ɗora da cewa watanni nawa aka sa lokacin bikin ? Banda abunka abokina to menene abun damuwa ? Ai hurhuɗu ya kamata ma mu ajiye , domin ko nima ba domin tafiyar nan da na ɗan yi ba da yanzu batun auren mu yayi nisa da Aminah ta , wataƙila ma sai dai mu haɗa ayi rana ɗaya tunda kuwa ita ma ƴar Maidugurin ce , wata nawa aka sa ?

Muryar Doctor Hamza can ƙasa yace , " kwanaki goma kachal suka rage har da yau da muke ciki ,
Tsumu Doctor Suleiman yayi yana kallon sa wannan karon kamar bai yadda da abunda yace ba , ganin haka yasa Doctor Hamza cigaba da cewa ,
" tare za'a haɗa da na ƙanwata Rahima , saboda ayi a huta , tarewar kuma sai yadda hali ya min wataƙila ta kai watanni huɗu a maidugurin ko ma fiye da haka kasan dai kome daki-daki ake yin sa .

Da fara'a sosai a fuskar sa Doctor Suleiman ya shiga taya shi murna yana taya sa shi da fatan alheri cikin raha ya É—ora da tsokanar sa ,
" kace ciwon so kake ciki mana tare da kewa , shiyasa duk ka wani zama haka , babu shakka wannan ƙanwar tamu mai sa'a ce , to sabon shiri kenan zamu fara dan angwanci ya same mu da rana tsaka ba tare da mun shirya ba , amma duk da haka ma ɗan yi wasu tsare-tsare a gurguje me da me za'a yi na biki ?

Kallo mai kama da harara Doctor Hamza ya masa , kafin yace
" Dan Allah zan roƙe ka Alfarma Suleiman, kar ka ƙara min damuwa , duk garin nan bayan kai ba wanda na faɗawa zancen nan , ko ita sofiya bata san da zancen ba dan haka ka ma bar maganar wani biki zancen ya tsaya kawai a tsakanin mu , bayan kai da daman zaka je bikin Rahima babu wanda zan gayyata .

Da wani irin yanayi Suleiman ya dube shi kafin yace " ko meyasa ?
" kawai ra'ayina ne , mu ba yara bane da za'a yi wani raye-rayen biki ina ma muka ga lokutan ɓatawa ?.
GÆ´aÉ—a kai Suleiman yayi cike da shakku yace " to shikenan tunda kace haka Allah ya kyauta .
" Amin nagode abokina , Doctor Hamza ya amsa masa , domin ya sauƙaƙa yanayin rashin daɗi da ya hango a tare da Suleiman sai yace , " ina aka kwana kan batun lamarin ita Aminar taka ? ko idan muka je Maidugurin za'a yi wani motsi mai ƙarfi ne ? kasan fa kun jima da yarinyar nan ya ci ace anyi auren nan .
Cike da zaƙuwar jin an masa susa inda ke mar ƙaiƙayi Doctor Suleiman yace ," bari kawai abokina wannan yarinyar ko yau aka kawota gidana ta walashe ni , gyara zancen nan ka ma , saboda ai ni na jima ina son ta ba wai mun jima a tare ba , domin kuwa ai ita har yau bata wani bani dama ba , ni kaɗai ke fama ,
Ya dubi fuskar Doctor hamza da yayi kasaƙe cike da takaicin yadda ya zauna gotai-gotai da shi 'yar yarinya ƙanƙanuwa na masa yawo da hankali wajen shekaru uku , sai kace ƴa gwal ?
Doctor Suleiman ya katse zancen da Doctor Hamza yake son ɗorawa ta hanyar cigaba da cewa , " kar ka ga laifina Abokina , Amina ta cancani da kowanne ɗa Namiji yayi sha'awar ajiye mace mai nagartartun halaye da Addini haɗi da nutsuwa irin ta , wallahi ko kai da kan ka idan na baka labarin irin rayuwar da yarinyar take yi mai cike da tsantsanin kiyaye kan ta duk kuwa da cewa inda take rayuwa ƙazamtatce ne , halayyanta na ƙwarai nake kwaɗayi ba kome ba , saboda na sha gwada ta ba sau ɗaya ba , na kuma sa mutane wasu daban ma sun gwada ta amma ko sau ɗaya ban taɓa kamata da wani laifi saɓanin zahirin ta da take bayyane kullum cikin kamala da nutsuwa ba .

a yadda kake ƙyamatar halayen wasu matan nasan zaka yi mamakin nagartar da ita take da shi , kuma zaka bada goyan baya ɗari bisa ɗari akan na auro ta , musamman idan ka ji irin hali na tausayawa da suka riski kan su a ciki ita da ƴar uwar ta ,

Cike da gajiya da yadda ya zauna yana yabon wata wacce har yau shi da kan sa bata bashi darajar da za ta saurare shi ba , bare kuma su abokan sa Doctor Hamza yace " to Allah ya tabbatar da Alheri abokina .

Kamar yadda suka yi alƙawari ana saura kwanaki biyar ɗaurin Aure Mutanen N'Djamena suka iso ,sun tasamma mutane ishirin da ɗoriya , domin sun kusan cika falon Prof da anan suka fara ssuƙa , bayan an gaisa murnar sake ganin juna ta kachame a tsakanin su har da 'yan koke-koke , banda yaren su na larabaccin Chad babu abunda ke tashi a wajen ,

Zainab , Hafsa da suka iso tun jiya , har Rahima haÉ—i da Yakaka da Falmata , a tsakanin su duk babu wani mai jin yaren har sosai , dan haka sai suka tsaya kallon su fuskokin su É—auke da murmushi ,

Bayan sun ɗan nutsu sun sha ruwa da lemu , sai Matan suka shiga ciki inda za'a musu masauƙi ,

Mazan kuma suka tsaya anan Sashin Prof .

A ciki Amnee ta sake gabatar da Yakaka da Falmata , nan aka fara rungumar su ana sumbatar kumatun su da goshi , cike da nuna zallar ƙauna , daga baya kuma aka sake sabuwar gaisuwa har da su Hafsa da mafi yawa sun riga sun san su , su Yakaka ne baƙi .

Ba'a kwana ba Hajje Nadiya tare da tawagar ta mata huɗu da ta taho da su domin su taya ta suka buƙaci da su fara aikin da ya kawo su na gyaran Amare .

Tun ana saura kwanaki biyu ɗaurin Aure Sofiya ta iso Maiduguri , amma sai ta ƙi ƙarasawa gidan su Doctor Hamza tayi zaman ta a gidan su tare da Mamar ta Hajja kori , da ita ta zuga ta tace tayi zaman ta sai ana gobe ɗaurin auren da Yamma sai su tafi tare , ba dan kome ba kuwa sai dan rashin shirin da yake tsakanin su da Amnee da Khaalty Rahima .

Da ko kusa basu so Auren Amnee da yayan su ya sake ƙulluwa ba , kuma duk yadda suka so hana tabbatuwar lamarin fir Prof yaƙi saurarar su , ita kanta zuwan ta wajen sa biyu da zummar yi masa famfo amma bata samun fuska dan haka ta haƙura .

Babu abunda yafi ƙara basu haushi irin dawowar Khaalty Rahima da suka fi tsana gidan wannan karon har ma da marayun 'ya'yan ta kamar yadda labari ya iske su

Dan haka suka tsara zasu janye jikin su daga sabgar gidan sosai , sai ranar juma'a da Yamma lis , ana tsakiyar yin sakun lallen Amare tukun suka iso , ba su kaɗai bane ƙungiya suka yi da ɗan yawan su domin baki ɗayan ƙannen Prof matan sai yanzu suka zo tare da wasu daga cikin ya'yan su mata , sauran dangi kuwa mafi yawa sai gobe zasu zo .

kai tsaye iyayen suka yiwa sashin Prof tsinke ba tare da sun bi ta kan jama'ar sauran Jama'ar Amnee ba mutanen N'Djamena da su Malama Maryam wacce ta iso jiya da Yamma .

Suma kuma basu kula su ba , suka cigaba da gudanar da sakun lallen da aka tsara shi cikin irin Al'adun su na mutanen Chad ,

Kota'ina ƙamshin turaren wuta ne ke tashi da ake zuba shi ta kowacce kusurwa na filin wajen , haka Sofiya tare da wasu daga cikin yaran mata 'yan uwansu suka ratsa taro zuwa ainahin inda amaryar take zaune

Abunda ya ɗaure musu kai bai wuce ganin Amaren su biyu ba tare da wacce su sauran basu kai ga sanin ko wacece ba ? ko ita Sofi sai da ta bar yatsine-yatsinen da take yi ta nutsu sosai tukun ta iya shaida Farar balarabiyar da take zaune daga gefen Rahima da aka musu ado iri ɗaya cikin jar lafaya , tundaga kan su har wuya da hannuwa zuwa ƙafafun su adon sarƙoƙi ne masu ruwan gwal irin wanda shuwa arab ke adon bikin su da shi , ( baki ɗayan kayan gudummawa ne daga Hajje Khalsum )

Muƙut ,! Sofiya ta haɗiye busasshen yawun da ya mata saura a baki , kafin ta ɗora da ɗan siririn tsakin da ya bayyana fili .

Da ɗan sauri ta matsa kusa da Hafsa zuciyar ta na ƙara ƙarfin bugun da bata san dalili ba , " kamar nasan wannan kuma Bikin biyu ne wai ? Ta ce tana nuno Yakaka a walaƙance ,

Murmushin yaƙe Hafsa tayi sannan tace " ƙanwar mu ce 'yar Auntien mu Rahima ,
Da sauri ta sake cewa , " Ok daman wannan yarinyar ita ce ƙanwar taku da aka ce an tsinto su ? Kuma bikin ta itan ma ake yi na gan ta anan kusa da Amarya ko duk shisshigi ne da cusa kai ya bawan gado ?

Wata daga cikin ƴar dangin su da ta zo ta jaa hannun Hafsa ɗin tana bata saƙon Amnee na ƙiran ta , ita ta hutatce Hafsa daga bada Amsar da take ƙoƙarin harhaɗowa cike da zullumi .

Zare hannuwanta tayi daga cikin na Sofiya ta bar ta nan a tsaye ,

Ji tayi sam ba zata iya tsayuwa a wajen ba tana kallon Yakaka wacce sai ƙirƙiro ƴar fara'a take a tsakanin ƙawayen Rahima da suka zama kamar nata sai zuwa suke ana yin hoto , tare da yi mata fatan Alheri

Bata sake bi ta kan kowa ba ta zare jiki ta nufi sashin Amnee inda ta tarar ba yawaitar mutane a falon , mutane basu wuce huɗu ba ƙawayen Amnee , kai tsaye ta nufi ɗakin Amnee da take jiyo muryoyin su daga ciki ,

Amnee da Khaalty Rahima haÉ—i da Hajje Khalsum duk shiru suka yi daga tattaunawar da suke suka bita da kallon ganin yadda ta shigo musu É—aki bagatatan babu neman izni .

samun waje tayi ta zauna kafin ta fara gaishe da Amnee , da Æ´ar fara'a Amnee ta amsa , daga haka shiru tayi tana latse-latsen waya bata da niyyar gaishe da sauran mutanen , dan haka fuskar Amnee ta É—an sauya daga fara'ar da take tace ,
" Safiyya baki ga 'yan uwa na bane ? Wannan ƙanwata ce wannan kuma matar wana maza ki gaishe su .

Yanayin ta na bayyana rashin jin daÉ—in yadda Amnee ta disga ta a gaban mutane kamar wacce aka toshewa baki tace " Sannun ku ina wuni ?

Fuskar Khaalty Rahima ɗauke da murmushi sosai ta amsa mata har tana ƙarawa da tambayar ta Mamar ta ?

Bata bata amsa ba ta mayar da kan ta ga fuskar wayar ta ,

Sun cigaba da tattauna yadda wasu al'amuran da suka shafi bikin zasu kasance , kafin su tsinkayo muryar Hajja kori da take ƙwalawa Amnee ƙira tundaga ƙofar falo ,

A kusan tare suka miƙe da sofi wacce ita ma tashin hankalin da ta ji a muryar Mamar ta ya firgita ta ,
Suka fito falon a tare kichiɓus suka yi da tawagar su Hajja kori tare da sauran ƴan uwan su na kurkusa da suka zo tare ,

Kamar zata cukumo Amnee haka ta tsaya a gaban ta tana huci , sannan tace
" Amina baza ki taɓa sauyawa daga mummunar zuciyar ki mai cike da baƙin-hali ba ke da wannan Annamimiyar ƙanwar taki , da daga dawowar ku ke da ita shine kuka haɗa kai kuka maƙalawa ɗan mu auren Shegiyar ƴar da ....

A tsawace Amnee ta katse ta bayan ta matsa baya kaÉ—an tace ,
"Hajja kori ki dakata , ya isa kar ki sake ki ce za ki tozartani ko ki tozartamin 'yar uwa ta , wanda kuka yi a da can ma ya isa wannan masifar taku da bala'in a yanzu bazan ɗauke shi ba domin kuwa kunne ya sake ƙaho ya girma .

aure kuma tsakanin Yakaka da Hamza babu wanda ya isa ya hana ƙulluwar sa muddin ni na tsugunna na haifi Ɗana nayi ɗawainiyar sa sai ya auri Amina Yakaka , idan kuma a wannan karon ma za ku hana ne to Bismillah sai mu gani .

Ƙara matsowa Hajja kori tayi jikinta har tsuma yake tace " tsohuwar kilaki haka kika ce ? Babu shakka dole kice ƙaho ya girma saboda kin gama yawon banzan ki a bariki kin dawo za ki laƙawa....

" Momy kori ki saurara haka nan Dan Allah duk abunda za kiyi kada ki aibata min uwa da mummunan ƙazafi ,

Muryar Doctor Hamza a kausashe ta ratso falon wanda sauƙar sa kenan a garin ya nufo gida yana faka motar sa bai ko gama tsayawa ba Hafsa ta ƙira shi hankalin ta a tashe tana shaida masa rigimar da ƴan uwan Baa suka zo su nayi musu .

Cikin takun sa na nutsuwa ya ƙaraso wajen , yana zuwa ya shiga tsakanin su yana fuskantar Amnee , hannuwan sa duk biyu yasa ya dafa kafaɗun ta , cikin kwantatciyar muryarsa marar amo yace ,
" khaalas Amnee , Dan Allah kar kiyi hayaniya ki bawa kan ki stress kiyi haƙuri kin ji ?

Ganin ta ta sauƙe akan sa idanun ta cike da ƙwallar ɓacin rai , jin irin mummunan ƙazafin da Hajja kori ta yi mata a gaban jama'a , zata yi magana ya katse ta " Kiyi haƙuri Ummii mu je ki huta .

Hajja kori wacce ta ƙulu da yadda ya juya mata ƙeya yana rarrashin uwar sa alhalin ita tudu biyu take ci a wajen sa na babar sa kuma surukar sa , a fusace tace " Kai Hamza ƙaramin marar kunya munafikin maza , tare da kai watau aka haɗa baki aka munafunce mu kana sane , watau kai gaka mai uwa ko ? To ka tabbatar da cewa sai ka zaɓa tsakanin 'yata da wannan koɗaɗɗiyar shegiyar yarinyar da ake shirin aura maka , ƴar da ba'a san asalinta ba .

Bai juyo ba , yace " Momy kori kema kiyi haƙuri Dan Allah .

"Amnee mu tafi É—aki ki huta , yace yana juya kafaÉ—un ta suka fara taku ,

" Doctor ,
Chak ya tsaya lokacin da sautin muryar Sofiya ya doki kunnuwan sa ,da sassarfa kamar ana tunkuɗa ta ta ƙaraso ta zagayo ta gaban su , idon ta da suka firfito da ke bayyana tsantsar firgicin da zuciyar ta take ciki ta tsattsare sa da su , cikin wata irin murya tace
" Da gaske za ka ƙara aure ? Kai ne za ka auri yarinyar nan Yakaka ? kuma wai gobe ne auren naku ?

Ganin sa ya kai kan Amnee da take raba ganin ta a tsakanin su , fuskar ta na bayyana ciwon da ran ta ke ciki, muryar sa can ƙasa yace
" Gaskiya ne Amma ki bar maganar nan daga baya zamu yi .

Kewaye ta yayi suka wuce cikin ɗaki , Ukhtee Rahima da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakin idanun ta cike da ƙwallar tuno da wata rana mai kama da wannan a cikin wannan falon lamari mai muni ya haka ya faru ta silar dangin Prof da sanadin haka ne rayuwar su ita da 'ya'yan da ta haifa suka faɗa a garari , sai ga shi a yau tarihi yana sake maimaita kan sa sun kuma gwada hakan akan 'yar ta, daga ƙasan ranta take tambayar kanta wai laifin me ta musu ne da suka tsane ta , tsana mai muni ya haka ? Juyawa tayi ta rufa musu baya suka rufo ƙofar .

Wani irin zaman 'yan dabaro Sofiya tayi a ƙasa dirshan kafin ta ƙwala wani irin ihun da yasa Rahima da Yakaka hanzarin ƙarasa shigowa falon da suke daf da ƙarasowa daman .

" Ƙarya ne , inaa no no wallahi ƙarya ne , Doctor baka isa ka min haka ba , Momy kice mafarki nake dan Allah ?

Ta ƙarasa sambatun da take tana miƙawa Momy kori hannu daga inda take kamar 'yar yayen da take son uwar ta ta ɗauke ta,
A fusace Momy kori ta ƙaraso wajen , ta fara jaan hannun ta tana ƙoƙarin ɗaga ta , bakin ta har kumfa yake lokacin da take cewa ,
" sai ki tashi mu tafi ai shugabar 'yan taurin kai marar zuciya , tun farko ai na faɗa miki akwai ranar ƙin dillaci muddin kika yadda kika auri ɗan wannan Annamimiyar matar , amma da yake kafiya ce da ke kika nace kika liƙe masa kika ƙi kowa kika zauna zaman jiransa shekara da shekaru .

"to ai ga shi nan kin fara gani kishiyar rana tsaka ,baki da ko darajar da za'a sanar dake bare a miki abunda ake yiwa mata a al'adance idan aka tashi musu kishiya , idan baki bar gindin auren ɗan Amina ba kaɗan ma kika fara gani daga cikin irin ƙiyayyar da zata zuba miki ,

A haukace Sofiya ta warce hannun ta daga cikin na Momy kori , da ƙaraji a muryar ta tace ,
" ki bar ni Momy , nace ki bar ni wayyo Allah na na shiga uku Doctor meyasa za ka min haka duk irin kula da son da nake nuna maka irin sakayyar da za ka min kenan ?

Wani mummunan tsaki Momy kori ta jaa a fusaace tace , " to kar ki tashi dan uban ubanki ki zauna kina kuka anan , kina sambatun wofi akan wani lusarin yaron da bashi da zaɓin kan sa , shegiya mahaukaciya zauna anan nace ,
Daga haka ta fice a fusace , wasu daga cikin dangi da suke 'yan kanzagin ta suka rufa mata baya , wasu kuma duuu suka yi kan sofiya wacce take ta rafsa ihu kamar wacce uwar ta da ubanta suka mutu a haÉ—arin mota .

Yakaka wacce duk haukar da Sofiya take yi tana kallon ta , a hankali ta fara jaan ƙafafun ta tana yin baya-baya zuciyar ta kuwa cike da tsoron kar Sofiya ta gan ta ,

Ai kuwa bata yi nasara ba domin kamar ancewa Sofiya É—ago kan ki karaf ta sauke idanunta akan Yakaka ,
Wata irin zabura tayi ta miƙe har tana ture matan da suka taru suna rarrashin ta dayawa daga cikin su rayukan su a ɓace yake da irin cin zarafin da suke ganin an yiwa 'yar uwar su , yi mata kishiya ba tare da an sanar da ita ba , sai a wajen bikin ta samu labari babu shakka a wajen mata wannan shine iyakar cin zarafin da ɗa Namiji zai iya yi musu .

Kukan kura tayi ta kaiwa Yakaka cafka , da gudu Yakaka ta kewaya ta bayan kujeru tayi ɗakin Amnee dai-dai da murɗo ƙofar da Doctor Hamza yayi ya fito daga ɗakin ,

Tana zuwa ta shige jikin sa ta ƙanƙame shi , a bazata ya ji shigar sa jikin sa , dan haka ya ɗago kai a firgice dai-dai tahowar Sofiya , a cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwar sa ta fahimci abunda ke faruwa dan haka ya juya baya da sauri , dukan da Sofiya ta kawo gami da chafkar da taso yiwa maƙogoron Yakaka ya sauƙa a bayan sa ,

Tun ƙarfinta ta shiga dukan bayan sa da ya yiwa Yakaka rumfa da shi , tana ɗura ashar tare da shan alwashin a kan sai ta kashe Yakaka ,

Da kyar ya ɓanɓare Yakaka daga jikin sa wacce ta shige masa jiki ta runtse ido gam zuciyar ta bayan bugu ba abinda take yi , addu'o'i iri-iri bata gama wata take kama wata .

Ƙofar ɗakin Amnee ta murɗo ta leƙo , lokacin da yake zare Yakaka daga jikin sa ,
" Menene kuma hakan ?
Amnee ta tambaya a tsawace , Yakaka tana jin muryar ta ta juya da gudu ta kutsa ta bayan ta ta tsaya tana kallon Sofiya , tsintar kan ta tayi da kwashewa da irin dariyar nan ta na tsira , da kuma ƙarin ganin yadda Makeup ɗin da Sofi tayi duk ya mata muzu-muzu a fuska ya kwaɓe mata , kamar wata dodo .

Ganin Amnee bai sa Sofiya ta bar zage-zagen da take yi ba , sai ma daɗa zabura da take yi tana son kamo Yakaka , wacce har lokacin dariya take yi da gajerun fararen haƙoran ta ,

Dariyar ta ta shagaltar da Doctor Hamza wanda yake ta faman rirriƙe Sofiya kamar wata tunkiyar da take rawar turke , fuskar sa da ɓoyayyen murmushin da ya barranta da yanayin da yake ciki a zahiri a sace yake kallon Yakaka , yaƙi matsawa daga wajen kamar wanda aka dasa shi banda kokawa babu abunda yake da sofiya .

Muryar Amnee ce ta dawo da shi cikin hankalin sa , inda take cewa ,
" ka jaa ta ku bar nan wajen nace bana son hauka da rashin kunya kana jina ko ?

Da ƙarfi ya murɗa hannun sofiya , muryarsa cike da gargaɗi yace " ki nutsu Sofiya meye kike ne haka ? Ki zo mu tafi .

Ta tsakanin Mata da yaran da suke tsaye carko-carko suka wuce yana riƙe da tsintsiyar hannun ta

Sun zo kusa da sashin sa ta warce hannun ta da ƙarfi , muryar ta tana rawar kuka tace
" Ka daina jana Hamza , ina wai za ka kaini ? so nake kawai ka faÉ—a min gaskiya , dan ni har yanzu ban yadda da abunda yake shirin faruwa ba .

Matsowa yayi daf da ita yana satar kallon tsirarun mutanen da suke sabgogin su a harabar gidan yace " Sofiya kiyi haƙuri dan Allah muje ki nutsu na miki bayani..

Da ƙarin ƙarfin kukan da ta take yi tace " Bayani ? Bayanin me za ka min ? Doctor meye bana yi maka a zaman mu na aure da za ka min kishiya da wannan ƙazamar kuchakar Yarinyar ? Kuma ma wai har ka ɓoye min Doctor ka ƙi sanar da ni tun wuri da na yiwa tufka hanci .

Kwantar da murya yayi yace " Sofiya wallahi ba ni nace zan aure ta ba Baa da Amnee ne suka haÉ—a lamarin nan , ki bari zan miki bayani sosai idan mun zauna, yanzu ki bar kukan da kike muje cikin É—akina ki wanke fuskar ki , kin ga magariba ta gabato bana so na rasa jam'i ,

Juyawa tayi maimakon ta É—au hanyar cikin gidan sai ta kama hanyar sashin Prof , a tsorace ya sha gaban ta wannan karon fuskar sa babu alamun wasa yace " Ina za ki ?
Ita ma da wata irin faffaɗar murya tace " wajen sa zan je naji dalilin da zai sa ya mun haka , sannan kuma na roƙe shi dan Allah ya warware wannan mummunan ƙullin da yake son yiwa rayuwata ,

Muryar sa a dake da bayyanuwar ɓacin rai yace " Sofiya ki nutsu ki shiga hankalin ki , iyayena fa ba abun wasan ki bane , naga duk irin haukar da kika yi a gaban Amnee dan na miki uzuri dalilin cewa ke ma an miki kuskure ba hakan ne zai sa ki dunga yin duk abunda kika ga dama ba akan su , ki nutsu nan gaba zan iya ɗaukar mummunan mataki akan ki muddin kika nemi cin zarafin iyayena ,

Daga haka ya wuce ya bar ta a wajen , wajen famfon dake zubar ruwa ya nufa yana daura alwala ,

Da saurin da ya wuce ƙima Sofiya ta tasamma ƙofar gidan ta fita tamkar zata kifa ,

Zuciyar sa babu daɗi ya bita da kallo , wannan tashin hankalin yake gudu daga gareta yasa tun farko ya kasa sanar da ita , sam shi ba mutum bane mai ƙaunar hayaniya .

Yana kammala Alwala ya shiga motar sa ya tayar aka buɗe masa ƙofa , yana fita kafin ya dai-daita kan motar a bisa titi ya hango motocin su Doctor Suleiman tare da na wasu abokan sa su huɗu , motoci biyar kenan , a sarari yayi tsaki kafin yace " wannan kuma Uban 'yan didimar sai da ya min gayyar da na ce bana so .

Hannu kawai ya É—aga musu tare da matsa ham , ya bi bayan sofiya wacce ya hango har ta kusa titi .

Da kyar ta yadda ta shiga motar ya miƙa ta gidan su , sai dai ko ficewa a layin gidan nasu bai yi ba ita ma ta sake fitowa a cikin motar Momy kori da gudun gaske ta ɗau hanyar gidan gogaggen Malamin ta da ta yadda da shi ɗari cikin ɗari aikin sa na ci , aifa zama bai gan ta ba .

Matar mutum bata zama ta wanin sa , washegari da misalin ƙarfe goma na safe taron jama'ar da suka cika suka tumbatsa suka shaida ɗaurin auren Hamza Mustapha Dilmari tare da Amina Muhammad Kalama .

Bayan ɗaurin Aure walima ta biyo baya , abokan Doctor Hamza da suka tasamma su ishirin sun sanya shi a tsakiya gami da sauran dangi , bayan fara'a babu abunda yake kamar ba shi bane ya sha ɓacin-rai da jin labarin auren ,

Shi da kansa bai san takamaimai me yake bashi nishaɗi ba illa yasan wani ɗan tsiron farin-ciki ne daga can saƙon zuciyar sa da ya zata ya mutu tun-tuni yake sabunta kan sa a yau .

Ɗan gefe guda Suleiman ya jaa shi bayan ya gama tsokanar sa yadda ransa ke so a ƙarshe yace masa ya kamata Amarya ta fito su gaisa saboda su anjima kaɗan zasu juya .

Baya so ko kaɗan Suleiman ya fahimci akwai wani abu marar daɗi a tsakanin sa da ita saboda ko babu kome ita a yanzu wata ɓangare ce ta rayuwar sa ba zai so ya zubda mata da ƙima a wajen wasu nasa ba dan haka yace ," Abokina mu je daga sashi na a ƙira ta ta gaishe ka kai kaɗai amma sauran sa haɗu watarana kawai .

" Ayi haka kuwa abokina ? Doctor Suleiman yace da ɗan shakku , hannun sa Doctor Hamza ya jaa tare da cewa "ai anyi ma , suka fara tafiya zuwa sashin sa yana ƙiran Amnee a waya , bayan ta ɗaga yake sanar da ita buƙatar sa na son a turo Yakaka sashin sa zasu gaisa ita da Suleiman .

Cike da murnar da tunda aka ɗaura auren lafiya yake mamaye ta , Amnee ta miƙe daga bakin gadon ta da take suke zaune ita da wasu ƴan'uwanta suna tattaunawa ta nufi ɗakin da ta bari a ɗazu Hajje Nadiya tana shirya Amaren a ciki ,

Tana tura ƙofar idanun ta suka yi farin gani da kyakkyawar farar fuskar ta da yau hasken ta ya ninku har wani sheƙi take , tana ɗaukar idanu iyakar kyau Yakaka tayi sa cikin farar Lafayar da aka naɗa mata mai adon ƙananun flowers baby pink da ash color akan sissilkan yadin da aka mata siririyar doguwar riga da shima launin baby pink , kan ta an naɗa mata ɗaurin ɗankwali simple an soke mata shi a gashin ta .

Rungume ta Amnee tayi ta sumbaci goshin ta kafin ta kamo hannuwanta da suka sha ƙunshi irin zanen ƙunshin mutan chadi jazur da su sun yi gwanin sha'awa , da manyan awarwarayen zinaren da Amnee ce ta bata su , suka daɗa fiddo martaba da kyaun hannunwan nata .

" da hannu ta yafito Falmata wacce take tsaye daga bakin window da alama akwai abunda yake taɓa ran ta a dai-dai lokacin , taƙi yadda a mata makeup sai yar hoda da man baki masu kyau aka shafa mata a cewar ta idanun ta basu cika lafiya ba bata son makeup , ita ma shirye take cikin wani pink ɗin leshi da aka mata ɗinkin Buba da zane tayi kyau fes da ita an mata ɗaurin ɗankwalin da ya fiddo zagayayyar cikakkiyar fuskar ta da ta sake yin tuɓus-tuɓus tana sheƙi sakamakon gyaran Hajje Nadiya da fatar ta ta karɓa .

Haɗa hannuwan su waje ɗaya tayi , tana cewa Falmata ," ki je ki raka Yayar ki sashin Yayan ku Babba zata gaisa da baƙi , idan sun gaisa ki tabbatar kin dawo min da ita hannu na yadda na ɗanka miki ita kin san yau ita tafi lu'ulu'a daraja .

Ƴar kyakkyawar dariya Falmata tayi kafin tace " an gama Amnee watau yau ni ce ƴar jagora ba ni za'a jagoran ta ba kai Alhamdulillahi Allah mun gode maka da ka nuna mana wannan ranar,

Amnee tana dariya ta roko su har ƙofar sashin ta ko'ina suka gifta ana ga Amarya ga Amarya ana bin ta da kallon sha'awa har da masu yi mata hoto ,

Falmata ita ta fara yin sallama a ƙofar falon , da aka musu iznin shiga ma sai da ta kai kusan minti guda a ciki kafin Yakaka ta saɓile takalman ta ta sanya ƙafafun ta ciki kan ta a ƙasa ta samu gefe zata zauna daga ƙasa , da sauri Falmata ta riƙo ta dai-dai lokacin da Doctor Suleiman ma yake cewa
" Kai kai Amarya ya za ki zauna a ƙasa ? Tashi-tashi ƙanwata yau ai ranar ku ce kamata yayi ma a dunga miki yawo da kujera ta musamman dan zaman ki kin san yau ke da sarauniyar England matsayin ku kai-da-kai yake .

A hankali ta É—ago kanta bayan ta zauna akan kujerar da Falmata take kai suna gaisawa da Doctor Hamza

jin muryar sa raɗau tayi mata kama da na wanda ta sani , shima Doctor Suleiman yana ƴar dariyar tsokanar ta da yake sauran Kalaman bakin sa suka maƙale masa a maƙogoro ganin fuskar ta ɗauke da kwalliya da sheƙin Amarci bai hana shi ya gane ta ba duk kuwa da cewa ganin sa da fuskar tata sau biyu ne rak , amma ta riga ta zanu a zuciyar sa mafarkin ta a yanayi ya irin haka a gaban sa abune da ya jima yana yi ,

Sai dai a wannan karon zahiri ita ce a bayyane a gaban sa amma ba a matsayin ta sa ba da kullum yake hari , a matsayin matar aminsa na ƙud da ƙuɗ take , cike da ruɗanin da ya gagara ɓoyewa bayan ta ɗauke ido daga kan sa da sauri , yace

" Abokina daman wannan ce Amaryar ta ka ?

Daga Yakaka , Youssouf har falmata sai da zuciyoyin su suka sauya bugu da mabanbanta tunaninnika da ya musu dirar mikiya ,

Ɓangaren Doctor Hamza a take ɓakin-cikin sa ya nemi dawowa sabo abunda yake gudu kenan tun farin farko da kuma ya sashi tsanar ta , cuɗanya da tayi ta yi da mazaje .

Da sautin da shima bai ɓoye ɓacin-ran sa ba a daƙile yace " eh ita ce , ki gaishe shi mana ku koma ciki .

Muryar Yakaka na maƙyar-ƙyartar da ta ƙarawa Doctor Hamza tabbacin rashin gaskiyar ta ta gaishe da Doctor Suleiman da gumi yake tsattsafowa a goshi , yana share gumin ya amsa da " lafiya lau Aminatu , nayi muku murna kin ji Allah ya sanya Alheri .

A ɗan kaikaice Doctor Hamza yake kallon sa lokacin da Yakaka da Falmata wacce jikinta yayi sanyi laƙwas da yanayin da ta gani a tare da su biyun suka fice daga falon .

Kafin Doctor Hamza yayi wani yunƙuri Doctor Suleiman da ya miƙe tsaye cikin wani irin yanayin da yake bayyana alhinin da zuciyar sa ke ciki yace " Hamza ka min shigar sauri , why ? Amina da nake baka labari ita ce wannan Abokina ita ka Aura .

Da sauri Doctor Hamza shima ya miƙe , kafin yace kome Doctor Suleiman ya sake katse shi cikin yanayin da yafi na ɗazu rauni , ya cigaba da cewa , " Na taya ka murna Abokina babu shakka Allah ya arzuta ka da kamilar Mace mai nagartattun halaye , ina taya ka murna sosai ina kuma yi muku addu'ar samun ɗorewar zaman lafiya babu shakka matar mutum daga gare shi take ...

Katse shi Doctor Hamza yayi a mamakance yake cewa ," kana nufin wannan Aminar ita ce Amina , Amina da kake bani labarin ta ?

" ƙwarai da gaske ita ce .

Shiru su biyun suka yi baƙon yanayin da ya ziyarce su yana samun damar mamayar tunanin su , muryar Doctor hamza ta sake ratso wajen da yake cewa " Abokina Dan Allah ka bani labarin haɗuwar ku da duk wani abunda ka sani game da Amina .

Bayan komawar su Yakaka cikin gida gaba É—aya sai ta rasa sukuni sarai ta gane ko wanene abokin Yaya dakta , shine mutumin da ya dunga bibiyar ta da sunan soyayya tsawon shekaru wanda har Malama Maryam da Lubna sun san shi , sai yau ta tuno rana ta farko da ta fara ganin shi a duniya ranar da suka fara haÉ—uwa da shi da kan sa Doctor Hamza tare ta fara ganin su , shine wannan abokin nasa da ya ji tausayin su a lokacin da Doctor Hamza yake hora su kan fitsarin da Falmata ta yi masa a office har ma ya basu kuÉ—i yace su sayi hijabi su suturta jikin su .

Sai yau ta gane shi gaba É—aya , amma yanayin da ta hango a fuskar Doctor hamza kafin barin su falon bayan Suleiman ya nuna ya san ta ya bata tsoro , sanin da tayi daman ita a wajen sa abar tuhuma da zargi ce , tsoronta ya ninku lokacin da tayi hasashen kar Suleiman ya sake dasa zarginta a zuciyar Doctor Hamza .

An cigaba da shagalin biki zuwa Yamma aka fara shirye-shiryen tafiya Dinner da dangin Mijin Rahima ne suka shirya saboda su nan Baa baya son ire-iren bidi'o'in baya yarda a kama waje a tafi biki kome za'a yi a harabar faffaɗan gidan ake yi , sai dai fa idan dangin miji ne suka shirya abunsu ko kuwa bayan an miƙa amarya gidan ta ayi ta can .

Shiri ake ta yi sosai saboda har Amnee da Khaalty Rahima ma zasu su a karon farko saboda ta roƙi Baa yau ɗaya tal ya bari su tafi tare har da Yakaka da Falmata tunda shi yaƙi yadda a shirya ayi daga Aljihun sa .

Albarkacin farin-cikin da yake ji na wannan ranar bai jaa gardama sosai ba yace su je amma a kula a kuma dawo da wuri .

Ana gaf da tafiyar bayan isha'i Doctor Hamza ya shigo gidan da tunda ya fita raka abokansa bai dawo ba ya zarce gidan su sofiya wacce tunda aka ɗaura auren take ƙiran sa a waya daga ya ɗaga sai ta fashe da kuka tana ihu tare da cewa sai ta kashe Yakaka ,
Tun abun na ba shi dariya har ya fara damuwa sosai tausayin ta ya tsirga masa , shi shaida ne akan irin son da take yi masa yana tsoron kar wani abu ya samu Æ´ar mutane ta dalilin haka dan haka da yayiwa su Suleiman rakiya suka rabu cikin raha da barkwanci sai ya kama hanyar gidan su Sofi

Kacha-kacha ya tarar da ita tayi manƙas cikin ƙwayoyin da ta dunga afawa , tun lokacin da labarin ɗaurin auren ya zo ma bayan a jiya sai da ta bi malamai kusan biyar akan lamarin duk kuma suka tabbatar mata kan cewa za'a yi aikin da zai sa a fasa auren a daren kafin gari ya waye , sai dai ga shi babu wanda aikin sa ya ci sai asarar kuɗi da ta tafka .

Tun kuma a jiyan ta dunga ƙiran layin Samy baby amma bata samun ta , damuwar ta ta ninku ba adadi .

abunda ya mummunan kaɗa masa ƴan hanji bai taɓa sanin Sofin sa na shan kayan maye ba , ashe duk ihun da take masa a waya bata cikin hayyacin ta ? Kwayoyi ta fara sha a sanadin ƙarin auren da yayi ?

Ƙwalla ne suka tarar masa a ido yana jin takaicin uwa irin Hajja Kori da baza ta iya tanƙwara ƴar ta ba , tayi ko ta bari , da ya shigo gidan ma bai ganta ba ko tana ina ? oho

Haka da kyar ya sha kokuwa da ita tana doddoke shi tana zagin Yakaka wasu lokutan har da Amnee da Baa , haka dai ya daure ya sa tayi wanka ya taya ta shirya yana yi yana rarrashin ta , ya rubuta Allurar da yake son yayi mata ya bawa maigadi ya sayo ya kawo ya danna mata , bayan ya haÉ—a mata tea ta sha kaÉ—an tayi bacci .

A gajiye liƙis ya baro gidan , zuciyar sa cike da tunanin maganganun da Suleiman ya faɗa masa game da Yakaka yana zakwaɗin samun tabbacin sahihancin su .

Bayan ya zauna akan kujerar falon sa a kasalance ya ɗau wayarsa tare da ƙiran layin Amnee Khaalty Rahima ce ta ɗaga ƙiran saboda Amnee ta shiga wanka , bayan sun gaisa yace da ita " yunwa yake ji dan Allah a samar masa da abinci ,"

Abincin sa na musamman da daman yake kitchin ɗin sama a ajiye can ta hau ta ɗauko masa tana saukowa suka yi kichiɓus da Yakaka wacce ta fito daga ɗakin su zata shiga ɗakin Amnee ,

Da sauri ta ƙarasa ta karɓi tiren hannun Mamar su tana mata sannu , cike da jin daɗi Khaalty Rahima ta amsa , kafin ta ɗora da cewa yauwa Yakaka ga abincin yayan ku ɗauki ki kai masa , banda ma shirmen ki kina nan kina ta kai kawo mijinki yana can zaune da yunwa ,ki sauya wannan ɗabi'ar tun wuri dan naga alamar duk jaan kunne da nasihar da ake miki ba ganewa kike ba ki sa hijabin ki ki kai masa .

Saƙare Yakaka tayi tana kallon Mamar su , so take ko yaya ta samu ƙafar zillewa amma babu dama , ji tayi ta cigaba da cewa " ki kai ki dawo yanzu idan kuma ba haka ba a tafi a barki na ga ma ko gama shirin baki yi ba .

ÆŠaki Yakaka ta koma ta saka dogon hijabin ta akan doguwar rigar da take jikin ta mai guntun hannu da fitowar ta kenan a wanka ta zira ta a jikin ta ta fito É—aukar kayan ta a É—akin Amnee shine wannan tsautsayin ya gifta mata , " ah tsautsayi mana haÉ—uwar ta da Yaya dakta ai ita tsautsayi ne a wajen ta mutumin da babu wanda ya tsana ya ita ?

Cikin takun rashin kuzari ta nufi sashin nasa riƙe da tiren da aka jera abincin akai , tana taɓa ƙofar ɗakin da nufin ƙwanƙwasa ta ƙofar tayi baya a buɗe take ,

Sai ta shiga a hankali siɗak-siɗak ta ajiye abincin aka ƙasa , zuciyar ta ta ɗan yi sanyi ganin baya falon , tana ɗaga ƙafa da zummar barin wajen ta tsinkayi muryar sa a ɓakin ƙofar ɗakin sa , "
Yace " ina ruwa ? Dan Allah a kawo min ruwa , ruwan cikin Fridge na ya ƙare .

Bata juyo ba tace "akwai ruwa a É—aya cooler É—in ,

Jin muryar ta ya sa shi É—ago kai da sauri daga goge kan sa da yake yi da towel fitowar sa kenan daga wanka jikin sa sanye da jallabiya ,

Da sauri ya dakatar da Yakaka wacce ta ɗaga sawu tana son ɓacewa daga falon ,
" zo ki zuba min , yace da sauti marar ƙarfi , kanta a ƙasa ta juyo ta ɗau daya daga cikin plate biyu da suke kan faranti ta fara ƙoƙarin zuba aɓincin ,
Da sauri ya dakatar da ita , " kar ki zuba , chak ta tsaya zuciyar ta na harbawa , jinsa tayi daf da ita ya kai hannu a hankali ya zare plate ɗin daga hannun ta , banɗakin sa ya koma ya ɗaureye plate ɗin tare da chokula biyu , ya dawo ya miƙa mata, ta miƙa hannu biyu ta karɓa , da ido ya bi hannun ta da ya sha ƙunshi .

" Ya isa yace , lokacin da ya ga tana ƙoƙarin cika masa Plate har ya tunbatsa , kan ta a ƙasa ta miƙa masa , ya karɓa yana kallon fuskar ta , kafin tayi wani yunƙuri yace mata " ki dakata na gama ci kar ki tafi ,

A ɗarare ta zauna daga gefe a ƙasa ta sunkui da kai , yana daf da kammala cin abincin Amnee ta ƙira wayar sa , yayi hanzarin ɗauka ," tambayar sa tayi ina Yakaka ? Ka turo ta yanzu ta gama shiri kowa ya shirya ita ake jira har wasu sun tafi ,

Cike da nutsuwa da kwantar da kai yace " Amnee wani wajen za'a tafi ne ?
A gaggauce ta amsa masa da " eh wajen Dinner ɗin Rahima zamu tafi tare baki ɗaya , ta ƙarasa da cewa " ka turo ta yanzu kaji ko ,"
"Amnee , amm Amma kuma zuwa dinner har da ita ? Da dai ita ta zauna a gida Amnee ba wani amfanin fitar ta a daren nan tun...

Muryar ta a É—an sama Amnee tace "kai kar ka min tsarin wofi ka turo ta mu tafi yau dai É—aya tal taje , tunda ita ba'a shirya mata nata bikin ba .

Zai sake yin magana ta kashe wayar tana cigaba da yiwa Khaalty Rahima mitar meyasa ta aiki Yakaka sashin Doctor Hamza ? Ga shi zai kawo mata wani iyayi irin na shi .

Murmushi kawai Amnee tayi tana mamakin rigimar Amnee marar tushe , mutum da matar sa a hana ta yi masa hidima ?

Hankalin sa kwance ya ƙarasa cin abincin sa , cikin ran sa neman hanyar da zai hana fitar Yakaka zuwa wajen wani taron can daban yake , a haƙiƙanin gaskiya baya son ta fita da auren sa cikin wasu ƙattin wofi ,su gama ƙare mata kallo , wanda aka kalla a da ma ya isa , duk da cewa dai wasu maganganun da Suleiman ya faɗa masa sun saɓa sosai da zaton da shi yake mata .
Yakaka ta durkusa ta tattara wajen ta haɗe kome yadda ta zo da shi , a hankali ta miƙe zata fita , cikin rashin sanin ta ta taka bakin dogon Hijabinta , saboda sauri da take ta bar inda yake ,

bata ƙarasa miƙewa ba Hijabin ya taɗile ta tayi ƙasa baki ɗaya farantin hannun ta ya bigi ɗan teburin gabanta , miyar da bata rufe sosai ba ta buɗu cooler ɗin yayi ɗan tsallen da yasa miyar tankwaɓewa ta fallatsuwa har cikin idon ta kafin ta kwaranye mata baki ɗaya a jikinta .

Ɗumin miyar tare da zafin attaruhun ciki da ya shiga mata ido yasa bata san lokacin da ta saki wani ɗan ƙaramin ihu ba .

A ruɗe Doctor Hamza ya miƙe yana jera mata sannu , amma azabar da take ji a idanun ta yaƙi barin ta nutsuwa bare ta ji me yake cewa , ihu ta shiga yi tana cewa " wayyo idona ,

Da sauri ya riƙo ta ya kama hannuwanta duk biyu zuwa cikin ɗakin sa ya zarce da ita cikin bathroom , gefen Bath ya zaunar da ita , duk a ruɗe yake da ihun da take yi ya kunna fanfo lokacin da ya ɗauki handle ɗin shower yana tara ruwa a hannun sa , ruwan ya kai ya wanke mata fuskar da shi ya sake cika hannun sa ya wanke mata ,

Yayi hakan sau kusan huÉ—u amma bata daina kukan da take yi ba , sai kawai ya juya shower É—in ya shiga fesa mata ruwan a fuska yana haÉ—awa da wanke mata idon sosai da ma fuskar ta baki É—aya ,

Hannun sa ta ture lokacin da ta ji raɗaɗin ya ragu sosai , ta fara ƙoƙarin buɗe ido ,
" ya ya ? Ya fita ? Ya tambaye ta cikin taushin murya bayan ya ɗan yi durƙuso a gaban ta yana leƙen idon nata so yake ya ga ta buɗe su ,

Tana buɗe idon ta runtse su da ƙarfi jin har yanzu da sauran raɗaɗi , bata ankara ba ta ji ya ɗago haɓar ta ya matso da fuskar sa daf ta ta , hannu ya sa ya tallafe ƙeyar ta ya fara hure mata idon a hankali

Sassanyar iskar bakin sa tayi tasiri sosai wajen rage mata raÉ—aÉ—i , ta kuma taimaka wajen dawo mata da nutsuwar ta , har ma ta fahimci irin kusancin da yake tsakanin su , zuciyar ta ta ji ta buga É—as!

Da hanzari ta buɗe idanun ta da suka ɗan rine suka kunbura kaɗan , suka yi musayan kallo da ita da shi , nitsar da idanun sa yayi cikin nata yana yawo da ƙwarar idanun sa a tsakanin nata , ji yake tamkar wata dama yau ya samu na gano tare da tsamo abunda yake hangowa a cikin ƙwarar idanun ta da yake kashe masa jiki a duk lokacin da ya fiye kallon su ,

Tsintar kan ta tayi da gaza janye idanun ta , fuskar sa dake daf da ta ta take ƙarewa kallo , sajen da ya bari da yake ta sheƙi a hasken lantarki ya ɗau hankalin ta , kamar ta kai hannu ta taɓa ,

Ganin yadda ta shagaltu da kallon fuskar sa yasa shi hure mata ido , da sauri ta sake rufe idanun nata ,
Kamar an farkar da ita sai ta miƙe tsaye da sauri , ta ɗan matsa daga kusan shi sosai sai lokacin ta ankara da jiƙewar da kayan ta yayi sharkaf ,tundaga kan hijabin jikinta har rigar ta ta ciki .

" shine ka jiƙa ni haka ? Yanzu ya zan yi ?

Ta furta hakan muryar ta cike da shagwaɓar dake nuni da damuwar da zuciyar ta ke ciki ,

Miƙewar shima yayi ya ɗan wara hannu kafin ya nuna mata nasa jikin da yake jiƙe shima , yace
" ku ji ta kamar ba ke kika ruɗani ni ba kika sa na jiƙa jikina , raguwa kawai kin sa yanzu dole na sauya kaya .

Kewaye ta yayi ya fita kai tsaye wardrobe ya nufa ya zaro wata jallabiyar ya tuɓe ta jikin sa yana warware ɗayar Yakaka da ta matse ruwan jikin kayan ta ta murɗo ƙofar a hankali ta fito ,

Da fitowar ta da hango shi ba riga da komawar ta cikin banɗakin ta rufo ƙofar da ƙarfi duk cikin abunda yake ƙasa da minti guda ta yi su ,

Doctor Hamza da duk abunda tayi akan idanun sa , har A'uzubillah da tace kafin komawar ta cikin banÉ—akin duk ya ji ta ,

Ɗan wani guntun murmushi yayi lokacin da wani tunani ya gifta masa nan take , rigar da yayi niyyar sawa ya ajiye a gefen gadon , a nutse ya nufi ƙofar banɗakin , ba tare da ya taɓa ƙofar ba yace ,
" ki fito ki tafi kar a gaji da jiran ki .
Daga ciki ta ce " to ka gama shiryawa ko ? Dan Allah kayi haƙuri ɗazun ban san kana shiryawa bane ,
Ɗan mitsitsin murmushi ya kuma yi yana cije leɓensa na ƙasa a taƙaice yace " eh na shirya ki fito .

Kan ta a ƙasa ta fito , a ɗan sace ta ƙyallo sa ,ta gan shi yadda yake a ɗazu da sauri sake juyawa sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya naɗo ta ta cikin jiƙaƙƙen Hijabin ta ya haɗa ta da jikin sa ,
A ruɗe Yakaka ta fara ƙoƙarin ƙwacewa , bakin ta ya gaza furta ko kalma guda , matsera kawai take nema ,
" Meye kike haka , kamar wacce bata saba ganin Maza a tuɓe ba ? Kar ki min kinibibin ku na mata .

Doctor Hamza yace haka laɓɓansa ɗauke da murmushin da yafi kama da na mugunta , cikin zuciyar sa yana sake haƙaƙewa da abunda yayi niyya , ya juyo da ita da ƙarfi ya ɗago fuskar ta da idanun ta ke runtse , hasken da ya haske fuskar shi ya bashi damar ganin hawayen da suka jiƙa mata fuskar ta ,
Shagala yayi da kallon kowanne ɗigo na tudu da ƙwarmin da yake fuskar ta , kallo yake mata irin wanda bai taɓa yi mata irin sa ba , a idanun sa kome na fuskar ta tsararre ne da ya dace ƙwarai da muhallin da Ubangiji ya ajiye mata shi .

Zuciyar sa take buÉ—uwa tare da tashin tsikar jikin sa, bai san lokacin da ya haÉ—e tazarar da bata wuce tudun yatsa guda da yake tsakanin fuskokin su ba , ya haÉ—e fuskokin su waje guda , tare da ratsa hannuwan sa ya kewaye ta da su sosai ,

Da wani irin yanayin da ya zarce yadda yake da nufin yi , ya shiga yin abubuwan da zuciyar sa ta raÉ—a masa da ya yi a matsayin gwada Yakaka ya ga ko kalaman Suleiman gaske ne Yakakar kamilallar mace ce , tsautsayi tare da kaddarar rayuwa ce suka faÉ—a mata ?

Sai ga shi ya gaza tantance Yakaka yake son gwadawa ko kuwa martabar sa ta ɗa Namiji yake aunawa ? Domin kuwa a tsakanin lokacin jin sa yake kamar wannan ne lokaci na farko da gangar jikin sa ya fara raɓar na wata ɗiya Mace .

Yakaka da ake yiwa gwaji ita ta yunƙura ba tare da tayi amfani da ƙarfin kirki ba , ta zare jikin ta daga na shi , bata tsaya ba kamar yadda bata yadda ta bari idanun su sun haɗu ba ta taka da gudun gaske ta fice daga ɗakin da sashin nasa ma baki ɗaya ,

Bata tsaya daga gudun da take yi ba sai da ta tabbatar ta bada tazara mai É—an yawa daga sashin sa .

Zama tayi akan wani É—an tudu tana mayar da numfashi harabar wajen babu mutane alama dake nuna an riga an tafi Dinner an bar ta .

Kalaman Doctor Hamza ta tuno ," me yake nufin da cewa ta saba ganin maza a tuɓe ? Kenan nufin sa ita wata ƙasurgumar karuwa ce da ta saba cuɗanya da Maza , shi yasa ya mata abunda ya yi mata yanzu .

Hawayen ɓakin ciki ya zubo mata , tayaya zata yi rayuwa da mijin da yake zargin ta irin wannan mummunan zargin ?

Da jaan ƙafa ta nufi cikin gida , kai tsaye ta zarce ɗakin su inda ta tarar da Falmata ita ɗaya ƙwal tana kwance lamo akan gado

Bata ce mata ƙala ba kamar yadda ita ma Falmatan bata nuna alamun ta san da shigowar ta ba , ta cire jiƙaƙƙun kayan jikin ta sauya da wasu , a hankali ta zo bakin gadon ta zauna , ta ɗan dubi Falmata da jikinta yake bata ba bacci take ba ƙoƙarin haɗiye damuwar ta take lokacin da tace , " Falmata baki tafi wajen Dinner bane ?

Ba tare da ta motsa ba muryar ta can ciki tace " Ban tafi ba Yakaka Amnee tace na zauna nima tunda ke ma Yaya Dakta ya hana ki tafiya , kuma ma bana jin daÉ—in jikina bayana ciwo yake min .

Shiru su dukkanin su biyun suka sake yi , zuciyar kowaccen su na sake ƙuntata da damuwar dake cin ta a rai , can ta tsinkayi muryar Falmata tace , "Yakaka yau kwanan mu ishirin da ɗaya da dawowa daga Niger ko ?
Ɗan waigowa Yakakar tayi ta dube ta , ba tare da ta bata amsa ba tausayin ta ta ji ya kama ta , babu shakka tasan damuwar Falmata ba zata wuce akan Youssouf ba da shima yake gwada nashi walaƙanci a zaton ta ta hanyar yin shaƙulatin ɓangaro da ƙanwar ta .

Washegari duk baƙi na nesa suka fara watsewa ciki har da Malama maryam da duk wasu dangi na nesa suka yi tafiyar su bayan Amnee ta cika su da kayan biki fal .

Zuwa yammaci gidan ya rage sai su isu 'ya'ya da dangin Amnee , lokacin ne kuma Baa ya aika aka ƙira masa Doctor Hamza , bayan sun gaisa nasiha ya shiga yi masa mai ratsa jiki tare da tarin tunasarwa akan nawin da ya ƙaru akan sa , da kuma wuyar da yin Adalci yake da shi wanda kuma dole ne ya tsayar da shi a tsakanin matansa muddin yana son dacewa da samun Rahamar Ubangiji .

Bayan ya gama masa nasiha da hannu ya masa nuni da saitin akwatuna biyu da adadin su yake kai ɗaya kawai launi da sumfurin su ne ya shabanba , kowanne guda takwas , ya ɗora da cewa " Wannan lefen Matan ka ne ɗayar ka kaiwa Safiya da hannun ka , ɗayan kuma na Amina ne , kamar yadda muka yi da kai nan da ƙasa da watanni biyu nake so ka samarwa da matar ka wajen zama a kusa da kai , idan ma kuma wajen zaman ya samu a yau
ko gobe ne ka dawo ka É—auke ta ku tafi abun ku Allah ya bada zaman lafiya .

Godiya Doctor Hamza ya dunga yi ƙaunar Mahaifinsa na daɗa ratsa shi tare da ƙarin ganin ƙima da darajar sa , har ya miƙe zai tafi Baa ya sake dakatar da shi wata ɓakar leda da take nannɗe ya miƙa masa "wannan kuma wasu kuɗaɗe ne da aka bani na baka a matsayin gudumawa , ka ƙara wajen kula da gida ,

Da sauri Doctor Hamza ya noƙe hannun sa ," Baa ka bar su ayi amfani da su anan , ni ina da kuɗin da zasu isa nayi kome da su Nagode Baa nagode .

Da murmushi a fuskar sa yace" karɓi mana ai ni na baka .

Ƙarfe biyun rana Doctor Hamza yayi Sallama da iyayen sa zai koma Abuja a yau ɗin saboda gobe yana da tarin aiyuka a office da bashi da damar ɗaukar musu uzirin jinkirta yin su .

Dangin Amnee ma ya musu Sallama bayan ya bada kuÉ—aÉ—e masu yawa da yace ayi musu sayayyar duk abunda suke so kafin tafiyar su , sannan ya tsawaita godiyar sa a gare shi .

Da Khaalty Rahima ma sallamar su ta musamman ce da suka keɓe suna yi ta inda ita ma ta ɗora masa 'yar nasihar ta a ƙarshe ta ba shi shawara kan ya lallashi Safiya sosai kar ya bari ƙarin auren da yayi ya ɓata zamantakewar su .

Ƙannen sa mata ma duk Sallamar yayi da su har da Rahima amarya da ba'a riga an miƙa ta gidan mijin ta ba saboda iyayen sa ba 'yan nan bane 'yan ƙasar katsina ne , kuma a halin yanzu duk suma shirye-shiryen komawar su suke can ƙasar America inda suke rayuwar su a can , nan da ƙasa da sati biyu zasu tafi tare duk har da Rahima .

Lokacin da ya gama Sallama da kowa da ya dace , ciki har da Falmata, sai ya shiga ɗan jefa ido waje-waje ya gagara tashi ya tafi , sai daɗa jaan hirar su yake shi da ƙannen sa .

Hajja wacce ita ma tun a waje da ita ya fara cin karo tana tattara harabar gidan suka gaisa har ma ya mata sallamar tafiyar sa ta jero masa addu'o'in da yake jin daÉ—in irin su ,

Ita ce ta shiga tana ganin sa tace ," Babban likita har yanzu baka tafi ba ? Kai kuwa na ga baka saba tafiyar dare ba garin Abuja ai ba kusa ba , dan ma dai ku manya ne .

" yanzu zan tafi Hajja , yace yana ƙoƙarin miƙewa , Hajja ta shige ɗakin ta tana cewa " Allah ya tsare hanya Babban likita .

Tana shiga É—akin tayi turus ganin Yakaka kwance akan katifar ta tana buga game da wayar Rahima ,
Salatin da Hajja ta É—auka sai da ta dire shi da tafa hannuwa sannan ta É—ora da cewa " ni hauwa'u me zan ji me zan gani ? 'yar nan kan ki É—aya ?

Yakaka ta É—ago kai tana kallon Hajja ,
" me nayi Hajja ko dan na hau 'yar katifar ki ? to bari na tashi , ta ce tana miƙewa ta sauƙa daga katifar ,fatan ta shine Hajja tayi shiru kar a jiyo muryar ta a san tana nan .

Hajja ta ɗora da cewa " tambayar ki nake kan ki ɗaya ? Yanzu ace Mijinki na can shirin ɗaukar doguwar hanya ke kina nan kina latse-latsen wofi ? Bawan Allah shi yasa mana ya gagara tafiya ashe ke ce baki masa abunda ya dace ba wanda zai ƙara masa kuzari da nishaɗin tafiya , tashi nace sakaryar mata , tashi ki fice min a ɗaki , ki fita ga mijinki can yana jiran ki kuyi sallama .

Hafsa da zainab da duk abunda Hajja ke cewa daga ɗaki suna jin ta sarai saboda sama-sama take maganar sai suka haɗa ido kafin su duka ukun su kwashe da dariya , Falmata ma sai da ta ɗan dara , a ran ta tana aiyana wannan kaɗan ne daga halin Hajja , yadda aka san bata da wani aiki sai na faɗin yadda mace za ta farantawa miji Ho Hajja , ya dace a bawa Hajja shugabantar wata ƙungiya ta faɗakar da mata kan yadda ake tafiyar da Miji .

Hafsa ita ta rage dariyar ganin yayan su na tsaye yana kallon su , ita ma sai ta ɗan ɗaga murya lokacin da take miƙewa tsaye tace , "Ƙanwata Amarya ki fito kuyi sallama big bro zai tafi idan kuma ma mu kike jin kunya , kun ga ku zo mu bar wajen tace da sauran 'yan uwan ta , nan take suka miƙe suka yi ɗaki suna ƴar dariya tare da sake yiwa yayan su fatan Allah kiyaye hanya ,

Doctor Hamza da yake tsaye hannun sa a zube cikin Aljihun rigar rigar jumfa jikin sa , ya ɗan gyaɗa musu kai da murmushi a fuskar sa , shi ɗaya ne ƙwal ya rage a falon .

Ganin sa ya mayar kan ƙofar ɗakin Hajja lokacin da Yakaka ta buɗo ƙofar ta fito kan ta a ƙasa fuskar ta kadaran-kadahan , ɗan matsawa kaɗan tayi ta bayan kujerar falon ta ɗan durkusa , " ina yini yaya dakta ,
Bata jira ya amsa ba ta ƙara da cewa " Allah ya kiyaye hanya ,

Bata yarda ta dubi sashin da yake ba bare ta san cewa ya matso kusan ta sai da ta miƙe tana shirin wucewa ta shige ɗakin su da yake kusa da ita , sai kawai ta ji ya riƙo hannun ta ,

A hankali ya jawo ta ya kusan haɗe jikin su , hannuwan sa yasa ya kewaye kunkumin ta , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda ta ɗago kai , muryar sa ƙasa-ƙasa yace " haka ake yin sallama ? Babu addu'a ? Baki ji Hajja tace ki min abunda zai bani kuzari bane ?

Da sauri ta ɗago kai , signal ya mata da duk girar idanunsa biyu , yana 'yar dariya da fararen haƙoran sa da suke da kyau sosai akan fuskar sa mai rangwamen haske .
ÆŠauke kai Yakaka tayi gefe can cikin ranta tana mamakin meyasa ta hango kamar sauyin mu'amala a tare da shi daga jiya zuwa yau ? muryar ta cikin sanyin tace " ai nace Allah ya kiyaye hanya na yi addu'a ,
Hannun yasa ya sake juyo da fuskar ta saitin sa , ya zarce da sanya É—an yatsan sa ya shafa saman idon ta , da yasa Yakaka ta lumshe idanun ta da sauri , " Ya idanun ki sun wuce ko ? Basu sake damun ki ba ko ? Ya tambaye ta da ragwan sauti ,

gyaɗa kan ta tayi tana ƙoƙarin kautar da fuskar ta , amma ya ƙi bata damar haka sai ma hannuwan sa duk biyu da yasa ya tallafi fuskar ta yana shafa kumatun ta masu taushi yace ," to ina saurarar ki ki min Duas kuma ki min abunda Hajja tace ki min , ko bakya so na samu kuzarin tuƙin ne ?

Sallamar wata baƙuwa ya sa Yakaka ta fisge jikin ta da ƙarfi da daman baki ɗaya a takure take damar gudu take ta son samu ,

Sai dai bai bata damar gudun ba ya riƙe hannun ta lokacin da suke gaisawa da matar ya san ta ɗaya daga cikin mutanen Amnee ce , ta zauna akan kujera.

" Ba za ki min Duas É—in ? ba yace yana jaan hannun Yakaka su fice daga falon , babu yadda ta iya ta bi shi sai dai suna fitowa suka hango Amnee na tahowa daga sashin Baa ,
" Yaa Doctor Allah ya kiyaye hanya ya kai ka lafiya , ya kare ka , ta harhaɗo kalmomin cikin sauri tana ƙoƙarin kwace hannun ta daga cikin nasa , kafin ƙarasowar Amnee ya sake ta da sauri ta taka tana komawa ciki , da murmushi ya bi bayan ta da kallo wani irin nishaɗi ne mai daɗi yake huɗa shi .

Ƙarfe uku ya ɗau hanyar Abuja tare da sofiya wacce ya biya gidan su ya ɗauke ta dole bayan ya mata jaan ido tare da barazanar barin ta ta cigaba da zama a gidan su na wasu kwanaki da take son yi dai-dai yake da rabuwar su baki ɗaya , jin haka ba shiri ta tattaro ƴan kayan ta ta bi shi, ba tare da ta kula Momy kori sun yi wata sallamar kirki ba saboda haushin ta da momy kori take ji .

ASSALAM ALAIKUM MASU KARATU DA FATAN KUNA LAFIYA ?

INA GODIYA DA YADDA DAI HAR KULLUM KUKE HAƘURI DA NI .

INSHA ALLAH SHAFI NA GABA SHINE ƘARSHEN LITTAFIN MHR DA ZAI BIYO BAYA NAN BA DA JIMAWA BA.

NAGODE
[1/17, 9:40 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

49

MARADI-NIGER

Kwanakin da suka biyo bayan bayyanuwar mummunan aikin da Gimbiya maimounatou ta aikatawa Biyamuradi Youssouf , tare da sa hannun Mammadou da Hajiya Mama ,

Masarautar maraÉ—i ta kasance cikin alhini mai tarin yawa , kusan kullum aka yi zaman fada da Waziri ne ke jagoranta ba'a da wani batu da ya wuce na sake tattaunawa kan wannan mummunan lamari haÉ—i da yiwa Biyamuradi Addu'ar samun lafiya tare da fatan dawowar Maimartaba .

Da har yau da suke cika kwanaki ishirin da ɗaya basu baro india ba , Amma ana saka ran dawowar tasu a yau ko gobe saboda saƙon yiwuwar dawowar tasu ya iso musu .

Akwai labari daga majiya mai tushe cewar gimbiya Siyama tare da ƙanin Biyamuradi Youssouf , 'Bilal wanda shine mai binsa a haihuwa sun fara shirin tafiya India domin cigaba da jinyar sa da har kawo yau babu wanda yasan takamaimai a halin da lafiyar Youssouf ɗin ke ciki .

Ta ɓangaren Hajiya Mama kuwa duk yadda ta kai ga sanyawa idanun ta toka ta mustsiƙe ta cigaba da yin harkokin ta yadda ta saba , amma ta gagara domin yadda labarin sa hannunta da na ɗan ta wajen yunƙurin kisan da Matar Biyamuradi tayi masa , ya bazu ba a bakin bayu da hadiman cikin masarautar Maradi kaɗai ba har jama'ar gari da na wasu jahohin labari ya kai musu .

Ake kuma kucin-cina labarin tare da sake liƙa masa baƙaƙen sassa ana sake munana sa ba ƙaramin tasiri hakan yayi wajen kassara mata duk wani karsashi haɗi da ɗagawar da take tinƙaho da shi na kasancewar ta matar Sarki .

Dan haka gaba ɗaya sai take neman zama mujiya , tsarguwa take da irin kallon da bayun gidan suke mata , gefe guda ga dumuwowi birjik da suka mata ƙawanya , wanda bata saba shiga makamantan su ba , mafi girman su halin da ɗan ta tilo namiji yake ciki wanda yake tamkar ga ƙoshi ga kwana yunwa a wajen ta , domin kuwa tasan muddin Youssouf ya rasa ransa, cikin hakan akwai yiwuwar shima Mammadou ayi masa huƙunci mai tsauri da ka iya kawo ƙarshen shima tasa rayuwar .

Ga Maimartaba da bata san matsayin ta takamaimai a wajen sa ba , bayan tonon sililin da Maimounatou tayi mata a gaban sa , gefe guda kuma ga Mairamar sarki da take autar ta sannan mafi soyuwa a wajenta cikin 'ya'ya da tun bayan faruwar wannan lamarin da ta samu labarin kome bayan kuka bata wani taɓuka abun kirki ,

Rufe kanta take a ɗakin ta da yake sashin uwar-riƙon ta , ( Hajiya Umma ) ta ci kuka ,domin lamarin ya mata tsauri wajen ɗauka duka biyu a lokaci guda ,

dan kuwa bayan kasantuwar Youssouf yayan ta mafi kusanci da yawan ƙauna a tsakanin su fiye da duk sauran 'yan uwan ta , ta shaƙu da shi tunda ta buɗi ido ta ga kanta riƙe a hannuwan sa , shiga hatsarin rasa shi ba abune mai sauƙi a wajen ta ba .

Damuwar ta tana sake hauhawa da hango rugujewar zancen auren ta , tare da ma guntilewar alaƙar su ita da masoyinta da suka ɗibi tsawon shekaru uku suna soyayya wanda yake yaya ne ga gimbiya Maimounatou , uwa ɗaya uba ɗaya gaf ma ake da yanke ranar auren su cikin watannin gaba kaɗan a sha biki , sai ga shi wannan mummunan lamarin ya shata layi a tsakanin su , domin kuwa ko ba'a sanar da ita ba ta san makomar soyayyar su ita da Khaalifa , sannan tun kafin a hana ta ita ya kamata ta fara zare soyayyar sa daga ran ta , bayan abunda ƙanwar sa ta aikata ga Biyamuradi ai babu wani sauran alaƙa mai girma da zai sake shiga tsakanin masarautun nasu biyu .

Ba tun yau ba ta riga ta san wasu daga cikin munanan halayen Mahaifiyar su da ita koyaushe huɗubar ta tare da yunƙurin ta bai wuce na ganin ta raba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ta da uwar-goyon ta tare da sauran ƴan uwan ta da suka haɗa uba ɗaya ba ,

da ita kuma ko kusa bata ganin aibun su , sannan duk wasu laifuka nasu da hajiya Mama ke faɗin sun aikata ko suna kan aikatawa , ita bata kai ga kama su da ko guda ba dan haka koyaushe take biris da huɗubar ta , tare da toshe kunnuwan ta , ƙaunar ƴan uwanta a jinin ta yake tana ƙaunar su kwatankwacin ƙauna tare da zallar kulawa da su ma suke nuna mata a matsayin ta na ƙaramar ƙanwar su ,

ga hajiya Umma kuwa ba zata ce kome ba da ya wuce fatan alheri tare da godiya ,riƙo ta mata na haƙiƙa ba irin riƙon ƴar kishiya ba , dan haka take jinta basu da wata maraba da Hajiya Mama , sau dayawa ma tafi kusanci da Hajiya Umma akan ita Hajiya Mama ,( goyo guba )

Amma ace sanadin son zuciya irin na Hajiya Mama duk ta rusa mata farin-cikin ta a lokaci guda ? Gani take kamar Hajiya Umma da sauran Æ´an uwan ta duk zasu tsane ta akan laifin Mahaifiyar ta da É—an uwanta , a tsakanin hakan take yawaita tambayar kanta anya kuwa tayi sa'ar uwa ???

An cigaba da tsare Gimbiya Maimounatou tare da Mammadou a Niamey , saboda rashin sanin halin da Youssoufa ke ciki ya hana a tura su ga kotu ,

kawo yanzu kuwa Mammadou iyakar nadama ya yita , ko abincin da ake ɗan kawo masa , baya iya ci duk ya lalace yayi duhu , bai taɓa zaton akwai wani lokaci da zai zo yayi danasanin zazzafar ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan sa ba irin wannan lokacin da ya sarƙe cikin sharrin Gimbiya Maimounatou da ta tsaya kai da fata kan shi ya kawo mata gubar da ta ciyar da Youssouf da a zahiri ba gaskiya bane ba shi ya kawo mata ba ,ba shi kuma da wata masaniya akan haƙiƙanin me ya faru ga Youssouf a wannan daren , iyakar abunda ya sani shine yaje gidan Youssouf mintoci kaɗan bayan ƙiran sa da tayi saboda kusancin da yake tsakanin gidajen nasu biyu da wuri ya isa , ƙarƙashin jagorancin gnala da ta tare shi tun a babbar ƙofar gidan ya cimma har falon da Youssouf ke yashe a ƙasa cikin halin fitar hayyaci , a lokacin shi da kansa ya shiga ruɗani ganin halin da ɗan uwansa ke ciki , a ɗimauce ya shiga tambayar gimbiya Maimounatou

" Ya mutu ne ?
Da gaske Youssoufa ya cimma kushewa tai ?

Bai gama tantance da abunda ke faruwa ba lokacin da suka tsinkayo jiniyar 'yan sanda ,

Kallon-kallo aka yi tsakanin su ukun , da ruÉ—ani ya bayyana a fuskokin su sannan da wani irin sauti Gimbiya Maimounatou tace ,

" Mammadou ka shigo da ha'inci cikin lamarin mu amma kayi kuskure ka kuma yi shuka a idanun maƙwarwa , muddin kuwa baka yi wani yunƙuri ba tarkon da kayi na iy afkawa har da kai da makusantan ka ,

Cikin ruÉ—ewa yace ,

"ki bar surutan banza ki faɗi wanne tanadi kika yi kafin ki aikata wannan aikin domin nayi gaugawar shafe girman laifin ki kafin lokaci ya ƙure miki , ko kin manta Yarima ɗiyan sarki kin ka kashe ?

Kafin yin wani yunƙuri mai girma jami'an tsaron da bai kai ga tantance kakin soji ne a jikin su ko kuwa na 'yan sanda ba , suka dunga tururuwar shigowa falon kafin ya farga sun cika falon , bai shaida fuskar ko ɗayan su ba , sai fa Tafeeda da shi kuma tun shigowar sa ya rufu ga Youssoufa bakin sa ɗauke da sallalami gami da addu'o'i .

Hanjin cikin sa ya kaɗa lokacin da ya lura jami'an tsaron wajen riƙe suke da bindigogin su da suke ɗane a saitin su shi da gimbiya Maimounatou , tsoro mai girma ya ziyarce shi lokacin da ya farga da tsaka mai wuyar da yake ciki , da dukkanin alamun da suka bayyana ya taka sawun ɓarawo .

masaniyar sa ɗaya shine yasan gimbiya maimounatou tana da mummunar manufar kashe Youssouf tun shekarun baya da ta taɓa furta musu hakan shi da Hajiya Mama lokacin da suka yi wata ganawa ta sirri da su da ita wanda a lokacin suka haɗa hannu wajen ganin sun kai Youssouf ɗin ƙasa da shi da Hajiya Mama ba burin su kashe shi ba , ( kashe shi abune wanda ba sa hangowa kansu hanya mai ɓillewa ta nan ) kwaɗayin su tozarta shi suke irin tozartuwar da zata kai shi ga rasa damar sa ta hawa ƙaragar mulki burin su ya bar nahiyar su yayi nesa da sarauta , yayi rayuwa mai cike da baƙin-ciki tare da rashin nasara to ko'ina Mulkin Maradi ya zama na Mammadou .

Ga rashin sa'ar su sai ta ritsa da su munafunci shi ai daman dodo ne ubangidansa yake cinyewa , Mammadou ba shi da wata kafar kufcewa daga zargin da yake ciki , Maimonatou kaÉ—ai ita ce ke iya fidda shi ita kuwa bata shirya hakan ba ,

kafin a raba musu ɗakin da ake tsaron su cikin a cikin sa , babu irin roƙo da magiyar da bai mata ba kan ta tausaya ta faɗi gaskiya , amma tayi funfurus sai yaɓa masa baƙaƙen kalmomi masu cike da raini take yi wanda a lokacin shi basu ishe shi sauraro ba bare yayi hanƙoro akai , nadamar son zuciyar da ya aikata cikin kowanne sa'a guda na sake yi masa dabaibayi .

Gimbiya Maimounatou kuwa ? Zuwa yanzu lamura sun fara zuwa saɓanin tunanin ta , dan kuwa har kawo yau da take cika satika uku , sau ɗaya bata ji daga wani nata ba wanda kuma tana da masaniyar tuntuni labari ya je musu , to yaya haka ta kasance mata ? Tana sane ko kowa ya iya kauda idanunsa daga gareta sakamakon laifin da ta riga ta aikata , Abban ta ba zai iya ba , saboda sanin da tayi tauraruwar ta ta ɗara ta kowa haskawa a zuciyar Mahaifin su sumfurin ƙaunar ta kuma mai banbanci ce da ta sauran ƴaƴa , duk kuwa da kasancewar ta ɗiya mace ,

Tun tana sanya ran za'a buɗo kofa ace ta zo ga Maimartaba mahaifinta yazo ganinta da kansa ,tare da Mahaifiyar ta , daga nan ta san zasu nemi belin ta tana da tabbacin za'a basu idan yaso daga baya sun haɗu a kotu su da mutanen Youssoufa da take jin ba wani nisa shari'ar zata yi ba za'a kawo ƙarshen ta sanin da tayi tasu masarautar ai tafi ta su Youssoufa ƙarfi har ma da dukiya .

shiru ya tsawaita babu wani motsi daga iyayen ta .

ta sassauko burin ace ko da wani daga cikin tarun yayyunta maza da mafi yawa basu wani cika shiri da ita ba musamman waɗanda suke yan uba , amma duk da haka tana harin ko uku daga cikin ne su zo ko da kuwa ace zasu ƙare mata zagi, ita dai ta yadda su zo su ƙarbi belin ta .

Har ta kai cikin ƴan kwanakin nan ta fara burin ina ma da ace ko da wani babba daga cikin masarautar su ne ya zo ganin ta ? ko da ace bai nemi belin ta ba ya jishe ta labari na daga abunda ke faruwa ga iyayen ta da ma masarautar su baki ɗaya da yasa suka yi watsi da ita a cikin wannan maƙasƙancin wajen da yafi dacewa da wajen hora maƙasƙanta daga cikin bayun ta .

Jita-jita ya kasance gaskiya domin kuwa a daren ranar Maimartaba sarkin Maradi tare da Hajiya Umma suka dawo cikin masarauta .

Da dawowar su bai fi da awa guda ba labarin samun lafiyar Biyamuradi ya kewaye masarautar , inda ake da tabbacin farfaɗowar sa daga magagin ciwo sai dai an yi masa aikin da yasa zai ɗan sake yin wasu kwanaki a can ƙasar India kafin ya warke baki ɗaya ya dawo .

Tamkar rana haka masarautar ta ɗauki murna har da ƴan bushe-bushen algaitu na bayyana jin daɗin samuwar lafiya ga Biyamuradin Maraɗawa wanda tamkar hatsarin rasa shi da aka shiga ne ya wanke duk wasu laifukan sa na baya da ake ganin sa da shi tare da haɓɓako da ƙaunar sa a zuciyoyin Al'umma .

ruwan ƙiyayyar kuma da ganin aibun sai yayi tsallen alkafira ya wanke Hajiya Mama tare da Mammadou , ta ukun su Maimounatou babu wasu abun aibatawa da ya wuce su lungu da saƙo na birnin na maradi murnar dawowar Maimartaba ake tare da farin-cikin jin cewa Yarima yana samun sauƙi .

Siyama wacce tunda Hajiya Umma ta shigo sashin nata da daman ita ma tun bayan faruwar lamarin ta baro ɓangaren gidan su ta dawo ɗakin ta da yake sashin uwar riƙon ta ,

Ita ta bi bayan Hajiya Umma har zuwa ƙuryar ɗakin ta ta kuma shiga Hidimar abincin Hajiya Umma , tana sauraron duk wasu amsa waya da Hajiya Umma ke yi da 'ya'yan ta da sauran jama'ar ta , da duk dai batu ne kan samuwar lafiyar Youssoufa , cikin wayar ne ta ji Hajiya Umma na lissafa sunayen waɗanda zasu tafi India domin cigaba da zama da Youssoufa na ƴan wasu satika kaɗan nan gaba , ƙannen sa maza biyu kawai ta lissafa bata ji sunan ta a cikin masu tafiyar ba.

amma duk da haka zuciyar ta cike take da farin-cikin jin lafiya ta fara inganta ga Mijinta , bayan irin tashin hankali tare da fargabar rasa shi da ta shiga da har ta kai ta ga kwanciya rashin lafiyar sati guda sai da ta fara samun labarin samun sauƙi a gare shi sannan ita ma ta fara gyagijewa .

Bayan ta kammala haɗawa Hajiya Umma abincin a can ɗakin ta na ƙurya inda ba wani mai shigar sa cikin bayu sai fa su 'ya'yan ta da kuma makusanta na sosai , fitowa tayi daga ɗakin ta dawo ɗan madaidaicin falon da yake tsakanin ɗakin da sauran manyan faluka ta zauna .

Hajiya Umma bayan ta idar da sallah ta ɗan taba abincin sama-sama , sai ta ɗaga waya ta ƙira Siyama , nan take kuwa ta shigo tana rike da hannun Yumna , wacce da shigar su ɗakin ta saki hannun mahaifiyar ta tayi wajen kakar ta da gudu ta faɗa mata akan ƙafafu ,

Da ƴar dariya Hajiya umma ta ɗago ta tana cewa , " ke zainaba ki ɗagga ni kadda ki ƙarasa min ƙafafu ki sa ni ɗingishi dagga dawowa ta daman yaya lafiyar ƙafar ?
Birgima yumna ta sake yi akan ƙafar Hajiya Umma kafin cikin 'yar muryarta mai cike da wayo tace ' Umma na faɗi miki ni suna na ba Zainaba ba suna na Yumna ko Mamaa ?

Da murmushi Siyama ta ɗan yi gurfano daga gefe tana ƙoƙarin janye Yumna daga kan Hajiya Umma tace , " Yumna bakya jin magana ko idan baki ɗagga Umma ba gobe ban tahiya dake unguwa .

Da sauri ta É—aga Hajiya Umma ta faÉ—awa uwar a jiki tana cewa ," kin ka ce wajen Baba na zamu tai ba unguwa ba ?

Shiru Siyama tayi bata amsa ba , illa ƙafafun Hajiya Umma da ta fara dannawa a hankali tana mata tausa .

Da tausayi a ƙwayar idanun Hajiya Umma take kallon Siyama , sarai ta fahimci yadda Siyamar take a ƙagauce da ta ji halin da Mijinta yake ciki ta kuma ji wani batu kan tafiyar su da aka tsara har da ita a waɗanda zasu ganin lafiyar Youssouf ɗin , sai dai zuwa lokacin tahowar su da Youssouf ya nanata kan cewa kada a taho da Siyama cikin masu tahowa wajen sa , tayi zamanta kawai har zuwa lokacin da Allah zai sa ya dawo yasa aka fasa tafiyar Siyama .

Hajiya Umma ta so ƙin amincewa saboda ita tafi ganin dacewar zuwan Siyaman da take matar sa fiye da sauran ƴan uwansa , sannan kuma ita ma Siyamar hankalinta zai kwanta muddin ta gan shi da idanun ta saboda tun a india su na da labarin irin mawuyacin halin da ta shiga na fargabar rasa Mijinta .

Sai dai duk yadda ta so Youssouf ya amince da zuwan Siyama ƙi yayi a ƙarshe da ta dame shi ana gobe dawowar su , yana kwance kan gadon sa na asibiti Hajiya Umma da Maimartaba kuma suna daga kan doguwar kujerar da take falon ,

Hajiya Umma ta sake tada batun zuwan Siyaman , da jin haka yasa Youssouf miƙewa a hankali ya zauna yana ɗan cije baki saboda wajen da aka yanka aka masa aiki a uwar hanjin sa har yanzu bai kai ga warkewa ba cikin kwana biyun nan ne ma yake iya miƙewa zaune da kansa

Fuskar sa da tayi fayau ta ƙara yin haske babu walwala , bai yadda ya dubi Hajiya Umma sosai ba yace ," Umma , Dan Allah Siyama kadda ta zou , babu wani alfanu a zouwan na ta .

Da ƙaruwar mamakin ta take kallon sa ,muryar ta da ɗan fushi wannan karon tace , " to wai mene ne dalilin ka ? Ina sane fa tunda ka farfaɗo baka yadda kun yi kou da waya ta kirki da yarinyar nan ba dagga ta gaishe ka sai ka ajiye waya , me zai sa ka dunga yi mata haka , ita ai wankakkiya ce bata da wani laifi cikin abunda ya afku .

Kan shi ya mayar gefe , muryar sa can ciki yace ," kiyi haƙuri Umma , amma Siyama ma ai macce ce , kaidin macce kouwa abun a gudu ne , hatsarin ta mai girma ne baka sanin abounda ke binne cikin ruhin ta , zahirinta cike yake da ƙarairayi da hilata , Allah kaɗai ya san abunda macce take iya ɓoyewa .

A lokacin Maimartaba ya É—ago kan shi daga karatun jaridar Hindustan Times da yake , ya kai duban shi ga Yousouf da yake komawa ya kwanta bayan gama zancen sa ,

Yunƙurowa Hajiya Umma tayi zata sake yin magana , Maimartaba ya dakatar da ita , fuskar ta a marairaice take kallon sa tana son ya ce wani abu ga Youssouf a lokacin , amma sai bai ce kome ba ya komawa karatun jaridar sa .

Ko da suka keɓe shi da ita , ƙorafi ta shiga yi masa kan hukuncin da take tunanin Youssoufa ya yanke wanda bai kamata ba ko kusa laifin da Maimounatou ta aikata ya shafi Siyama .

Murmushi kawai Maimartaba yayi ,kafin yace " Ki kwantar da hankali , a ba shi lokaci zuwa lokacin da zai gama dawowa ga nutsuwar sa daga ruÉ—anin da ya shiga , Macce ai mahaÉ—in rayuwa ce ga ÆŠa Namiji , shi da kansa zai safko .

Muryar Siyama ta katsewa Hajiya Umma tunanin da ta faÉ—a , " Umma babu abunda zan sake yi miki ?

Girgiza kai tayi , " babu kome É—iya ta , sai magana da nake so mu yi da ke ,

Da sauri Siyama ta gyara zama zuciyar ta cike da É—okin ko zancen tafiyar ta wajen Youssoufa za'a mata ? tace " To Umma ,

Da tausasawa a muryar Hajiya Umma ta cigaba da cewa , " Nasan kina son zuwa ki ga jikin mijinki to amma saboda halin da zuciyar sa ke ciki yasa aka dakatar da zuwan naki har zuwa lokacin da zai dawo dai-dai, kiyi haƙuri kin san dai yadda wannan mamagunciyar ɗiyar ta zuba masa dafi a zuci da gangar jiki, to sai a hankali zai koma dai-dai dan ma Allah yayi kwanan sa na gaba da zouwa yanzou sai tashin zance , Allah ya ƙara ɗaura mu akan maƙiyan mu na fili da na ɓoye , kiyi haƙuri kin ji ko ?

Da murmushin da ta ƙalato Siyama ta gyaɗa kan ta , tana shafar kan Yumna da har ta fara bacci a jikinta idanunta na kallon ƙasa tace ," Umma Allah ya ƙara girma oumarnin kou abun bi ne a gareni shi kouma Allah shi daɗe shi da lafiya .

"Amin ,Amin Siyama Allah shi miki Albarka ya dauwamar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin ku ,

Umma ta amsa tana mata duba mai cike da so da tausayi ,
A zuci ta amsa lokacin da take miƙewa saɓe da Yumna a kafaɗun ta tana barin ɗakin ,

Lokacin da ta shiga ɗakin ta dake falon tsakiya , kwantar da Yumna tayi a kan gado , a hankali ta zame ta zauna a ƙasa ,hawayen da take riƙewa tuntuni ya samu damar shimfiɗowa da gudu , tunanin abu biyu zuwa uku suka fara mata ƙaraƙaina a zuci .

"anya ba jikin Biyamuradin bane babu daɗi shiyasa aka hana ta zuwa ta gan shi amma Umma ke ɓoye mata ? Amma kuma ai ta ji sun yi waya da duk wasu makusanta ta kuma tabbatar musu da samun lafiyar sa .

" ko kuma ba ita yake son gani ba matar sa Fatima yace a kai masa ?

" kadda dai ace abunda Maimounatou ta yiwa Mijinta ya ɗarsa masa tsanar mata da yasa shi gudun su ? idan kuwa hakane babu shakka ba zata taɓa yafewa ɗiyar Agades ba ,da bayan tsawon shekarun da ta kak-kange ta hana ta damar samun gamsasshiyar soyayyar mijinta , ta himmatu wajen hilatar sa da salon soyayyar ta na ƙarya, tsakanin karya da gaskiya har ya aukawa son wata daban ba ita ba ,

Bayan kuma ga ta ita da ta ɗauki shekaru wajen ƙoƙarin ginawa kan ta matsugunni kome ƙanƙantar sa a zuciyar sa , ta haɗiye duk wani ɓacin rai ta kawar da kai ta danne tasirin kishin ta , amma sai da lokaci ya gabato mata da zata girbi ladan haƙurin ta , sai mummunan nufin Maimounato ya nemi mayar mata da hannun agogo baya ?

Runtse ido tayi tana jin ƙauna tare da tausayin Mijinta gefe guda tsoron sake rasa kulawar da ya fara nuna mata take yi .

, tunowa da lokacin rabuwar su taki kaɗan kafin tafiyar sa sashin Maimounatou , yadda ya riƙe ta ajikin sa , irin kalmomin da ya furta mata da suka zama tamkar magani ga wani daɗaɗɗan raunin da take fama da shi a rai , da hakan yasa ta jin kwaɗayin son cigaba da samun makamancin daɗaɗan kalmomin sa ya haka , cikin rashin sanin ta mummunan lamari na gaf da afkuwa musu .

BuÉ—e ido tayi tana karanto addu'o'in samun nutsuwar zuci .

Washegari da sanyin safiya saƙo ya isowa Hajiya Umma cewa " Hajiya Mama na mata barka da zouwa sannan kouma tana nan tafe zuwa sashin Hajiya Umman ,

fuskar Hajiya Umma bata nuna wani yanayi ba na farin-ciki ko saɓanin sa tace "a je a ce tana yiwa Gimbiya Saratu Maraba .

Zuwa hantsi misalin ƙarfe tara da rabi hajiya Mama ta iso , ƙarƙashin rakiya bayun ta su huɗu ,waɗanda tun daga falon farko suka dakata ,

Ita ɗaya ta taka zuwa Falon gaba inda ta tarar da Mairamar sarki tare da Siyama suna karin kumallo , kallo ɗaya Aisha Mairama tayi mata ta mayar da kan ta gefe , Fuskar Siyama kadaran-kadahan ta gaishe ta , ita ma tata fuskar babu fara'a ta amsa tana mayar da ganin ta kan Aisha da tayi tsam daga barin cin abincin da take , kafin tayi magana Aisha ta gaishe ta lokaci ɗaya ta miƙe zuwa cikin ɗakin Umman .

Ita ta yiwa Hajiya Mama iso ta shiga wajen Hajiya Umma .

Bayan gaisuwa shiru ne ya biyo bayan ɗan taƙaiccen zaman da suka yi kowacce tana saƙa a zuci , kafin Hajiya Mama ta gama auna kalmomin da take tafe da su da zummar ajiye su a muhallan da suka dace tace

," Sai kuma wannan lamari mai cike da sarƙaƙiya ya faru ? Wannan yarinya tayi ƙarƙon kifi , ta ɓata nasabar ta , ai kome kyaun nasabar macce muddin bata da hali kamar zoben zinariya take a hancin alade, shiyasa fa ni ban fiye zaƙewa wajen tsantsame zuri'a tafannin auratayya ba, wannan ƙwarya ta bi ƙwaryar bata cika yin ƙarƙo ba sai ki ga anyi gamdakatar da bara gurbi , amma ɗiyan saraki masu son tsalkin nasaba basu gane ba , ai ga irin ta nan Allah dai shi taƙaita , yaya shi jikin Youssoufa? Ya fa kamata ayi wani abu kan Yaron nan Mammadou sabbada kowa ya shaida sharri ne wannan ɗiya take yi masa .

Tunda ta fara maganar Hajiya Umma bata dubi sashin ta ba tana a kishigiɗe yadda take , ɗaya bayan ɗaya kalmomin Hajiya Mama suke sukar zuciyar ta tare da bijiro mata da mummunan fushin da take ƙoƙarin tausa zuciyar ta ta danne kamar yadda ta saba haɗiye dayawa daga cikin munanan abubuwan da Hajiya Mama ta sha yi mata ko a kanta ko akan 'ya'yan ta .

Fuskar ta na bayyana fushi mai tsanani ta miƙe zaune lokacin da zuciyar ta gama aiyana mata "shi fa maƙaho bai san ana kallon sa ba sai an haɗa da zungurin sa,

" Saratu ki dakata daga waÉ—annan maganganu naki marasa tushe da makama , shi wawa bai san zuru ba sai ya tsinka , ki sani cewa duk wasu kaidi da makirce-makice hadi da ja'iba da ta'annakin da kike bibiyata da zuri'a ta da shi ina sane , ina sane nasan kome tun kafin yau , na yi miki shiru ne saboda nasan shi munahinci dodo shike , muguntar mutum kuma ita ke kawo hallakar sa har inda yayi zaune yana kitsa sharri, sannan akwai ranar da hadari zai taso tare da guguwar da zata wargaza mugaye .

Cikin tsakar idanun Hajiya Mama da ta tsare ta da ido ta kai duba suka yi musayan kallo ,
ÆŠan guntun murmushi tayi kafin ta cigaba da cewa ,

"Saratu kika ce akwai aibu cikin tsantsame zuri'a ? To ai rashin tsantsame zuri'a yasa kin ka kawo matsayin da kike bisan sa a yau , rashin tsantsame zuri'a yasa kin ka zama muguwar uwa mai kitsa sharri , Matar kirki 'yar Nasaba da ita Miji ke fariya yana ado da ita tamkar rigar silki , amma Annamimiya mai haɗa bakin wuta a tsakal gida ita ke saka shi cikin ɗimuwa ta dauwamar masa da shiga kunya da baƙin-cikin da har abada zai kasa samun farin-ciki da ita .

" Ya isa Hajiya Safiyya dan na tako na zou shiyar ki ba shi zai baki damar da za ki ci mutunci na ba , Hajiya Safiyya babu yadda za ki iya da ni , banbancin nasaba da ki ka É—au shekaru kina É—aga shi sama kina tutiya da shi bai isa ya sauya mana daidaituwar matsayi ba a cikin gidan nan kuma ko kin ki ko kin so Inkiya ta ita ce Gimbiya Matar Sarki .

Tana huci ta miƙe tsaye ta fara taku tace " na zo nan ne dan na sanar da ke ki sa a gaugauta sakar min ɗa ya dawo saboda ina da masaniyar ke kika sa aka cigaba da garƙame shi ba tare da ya aikata laifin kome ba .

A tsakanin kwanakin da suka biyo baya Bilal da Ubbo tare da Maigidan ta suka tafi india , washegarin tafiyar su kuma Tafeeda shima ya juyo , saboda yanayin aikin sa da bazai bar shi ya cigaba da zama ba a can .

Bayan an gama zaman fada da Maimartaba ya tsawatar akan hana cigaba da batun abunda ya faru da Youssoufa , aka fuskanci abunda ya shafi fada da al'amuran ta kaÉ—ai ,

A daren ranar misalin ƙarfe takwas saƙon ƙira daga Maimartaba ya riski Tafeeda , babu ɓata lokaci ya cimma turakar Maimartaba ƙarƙashin jagorancin jakadiya .

Bayan ganawar da bata wuce mintoci talatin ba Maimartaba ya masa iznin tafiys bayan ya samu duk wasu bayanan da yake son samu daga wajen sa .

Duk da cewa Hajiya Mama ce take da turaka a ranar amma kasantuwar buƙatar ganawa da Hajiya Safiya ya taso yasa Maimartaba aika jakadiya ta masa ƙiran Hajiya Umma .

Lokacin da saƙon ƙiran ya samu Hajiya Umma tayi mamakin Ƙiran nasa sai kuma ta cika da fargabar ko dai wani lamarin ya afku ?

Batun da Maimartaba ya zo mata da shi a lokacin da ta isa turakar sa ya busar mata da maƙwallato , da wani irin yanayi cikin muryar ta tace ,

" Ranka ya dade amma sai nake ganin rashin dacewar Yarima ya cigaba da riƙon amren ɗiyar nan ta Nigeria , wacce ba'a ma kai ga sanin matsayi da tushen ta ba , Ranka ya dade a duba wannan lamarin ayi duba da yadda wannan ɗiya ta agades tazo da ha'inci ita wacce ma take da tsarkin Nasaba ɗiyar girma , ina ga kouma ita wannan da take tsintattar mage a yadda labari ya iske mu ko a can Nigeria basu da wata nasabar da za'a iya haɗa jini da su , ba'a ma san dangin su ba 'Yan Gudun Hijira ne kaddarar rayuwa tare da maƙirci irin na maƙiyan mu ne kawai ya haɗo kasantuwar su tare da ɗan mu me zai hana kawai a raba wannan Amren ?

Cikin tsanaki Maimartaba yake kallon ta har ta gama zantukan ta tayi shiru ,
"Safiyya , ya ƙira sunan ta yana gyara zaman gilashin ƙara karfin gani idon sa .

" Na'am , ranka ya dade ta amsa tana mai kaucewa haÉ—uwar idanun su , cigaba yayi da cewa
"Yanzou ashe abunda ya faru bai isa zamar miki ishara ba ? Bai isa miki nuni da cewa kyaun nasaba bai nuni da kyaun ɗabi'a da cikar mutuntaka ba ? Bai isa sanar da ke cewa halin ƙwarai baiwa ce da ubangiji ka iya bayarwa ga bayinsa tsakanin talakawa da masu kuɗi , masu mulki da bayun su Iyaye kouma su taya wajen ƙarin gyaruwar halayya da taimakon gwargadon irin kyaun tarbiyyar da suka yiwa ɗiyan su .

"Nasaba ba ita ke tsalkake mutum daga aikata halin banza ba , shi halin Mutum mallakin sa ne daga lokacin faruwar halittar sa da bai da wata alaƙa da wata Nasaba ko ni'imar rayuwar da zai zo ya taras nan duniya .

" Domin ɗiyar Nasaba tayi zalunci bai nufin ɗiyar ƙananun mutane tayi fiye da munin abunda ta aikata mai yiwuwa ne ita ɗiyar talakawan ta bayar da mamaki wajen zuwa da ɗabi'u mafiya kyau wajen ƙwaiƙwayo , wannan ɓangare ne na baiwar Ubangiji kamar yadda na shaida miki , dan haka umarni nake bayarwa kan a tai a zo da ɗiyar da Youssoufa ke amre dagga Nigeria ta kasance ƙarƙashin kulawar mu kafin dawowar Mijinta hakan shine zai nuna cikar ƙima da darajar mu , sam ba dattaku irin namu bane mu bar ɗiyar mutane dauke da amren ɗan mu can a ƙasar su batare da sanin halin da take ciki ba , ba'a kuma sanar da ita halin da Mijinta ke a ciki ba da hakkinta ne ta sani .

Hajiya Safiyya da tayi zugum tana jin sabon damuwa na mamayar ta Allah ya sani bata son cigaba da kasancewar yarinyar nan a matsayin surukar ta ita da son ran ta ne Siyama kaɗai ce zata cigaba da zama a matsayin matar auren Youssoufa , ta ƙuta sannan tace ,
" Ranka ya daÉ—e a halin da Youssoufa yake ciki yanzou babu tabbacin ko yana son cigaba da zama da yarinyar nan tunda ka ga kou Siyama ai....

" Safiyya ta ban san ki da gardama ba kar kuma ki sakayo ta cikin ɗabi'un ki a yanzou , Youssoufa yana son matar sa duk kouma tunane-tunanen da kike yi kiyi watsi da su domin zai zo miki da saɓanin su , dan haka kamar yadda nace a shirya tafiya a zaɓi mutanen da suka dace cikin matayen da zasu tai Nigeria dole ya zama da na jiki ne sosai zasu yi tahiyar nan , sannan a tanadi kome da ya dace domin zouwa tahowa da ita , a yi kome cikin girma idan ta iso a mata masauƙi a sashin ki kussa da ke daɗa ita ɗin ai ɗiya ce Mai girma a wajen mu , Waziri shi zai jagoranci tafiyar tare da shi da Ɗan Malikin Maradi da wasu zaɓɓaɓu amintattun fada.

Kallon ba yadda zan yi Hajiya Umma take bin Maimartaba da shi har ya gama jawabinsa da cikin muryarsa ta fahimci a tsaurare yayi maganar cike da sautin umarta dan haka bata da wani zaɓi sai yin yadda yace , sai ta miƙe a hankali bayan ta ce " Ranka ya dade da yardar Allah yadda kace haka za'a yi .

MAIDUGURI-NIGERIA .

Fatima , ta ji ya ƙira sunan ta can a ƙasan maƙoshi ,
"Na'am ta amsa tana ɗago kan ta da ta kwantar a ƙirjin sa ,

" Ranar da duk za ki haihu tare zamu yi naƙuda kiyi rabi nima nayi rabi kin ji ko ?

Murmushi mai sauti tayi tana mayar da kanta ta kwantar "Daman ana yin haka ? Ta tambaye shi ,
"Nima ban sani ba Fatima , sabbada duk É—iyana biyu bana wajen lokacin haihuwar su , amma wannan ya furta hakan lokacin da yake kai hannun sa marar ta ya shafa , "tare zamu yi haihuwar sa , É—iyana ko É—ana zasu safko a hannuna idan macce ce kin san sunan wa zan sanya mata ?
A hankali ta girgiza kai yace, "Rahamatullah , sabadda haɗuwata da Mahaifiyar ta Rahama ce mai girma Allah shi yi min , Idan kouma ɗa Namiji ne ?, shiru yayi kaɗan , da yasa ta ɗago kan ta tana leƙen fuskar sa , wani irin farin-ciki kalamansa suka ɗarsa a ran ta ," dagaske yake ita tamkar Rahama ce a wajen sa ?
Sumbatar goshin ta yayi a hankali yace " na bar miki zaɓi Fatima ke za kiyi masa zaɓin sunan , wanne suna za ki sa masa ?

Hannun ta da yake kan ruwan jikin sa ta matsar ta lalubi hannun sa ta haɗe tafukan su waje guda kafin ta sarƙe ƴan yatsunsu cikin na juna kamar mai raɗa tace " Babana .

Hannun Yakaka da ta ji ya taɓa fuskar ta shiyasa tayi firgit tana kirkiro murmushin yaƙe , ganin ta ta mayar inda wasu ma'aurata dake zaune suke ta zuba soyayyar su Mijin sai tarairayar matar sa wacce take ɗauke da ƙaramin ciki yake yi kamar zai tayata ɗaukar cikin ita kuma sai zuba shagwaba take tana daɗa narke masa , wayam ta ga basa nan da alama sun shiga wajen likita .

tun zuwan su Asibitin da yau zata fara awu da Yakaka tare da Amnee suka rako ta Amnee ita tayi duk wasu kai kawon da bai cika wahala ba kasancewar Asibitin private ne yasa nan da nan ta buɗe mata file tare da biyan duk wasu kuɗaɗen da aka buƙata sannan aka turo su gurin likitan da zai dunga ganin ta .

mata Uku kawai suka tarar da a wajen , biyun tare suke da Mazajen su sai ita da wata mata wacce da gani ba haihuwar fari bace sune kaÉ—ai ba mazajen su a wajen .

Soyayyar da ta tarar waɗannan ma'auratan na yi ya taɓa ranta , kewar sa da take ta dannewa kuma ta bijiro mata , baki ɗaya a lokacin , "Falmata meyasa kike kuka ? Kin san fa damuwa zata iya sa ki samu ciwo a halin da kike ciki .

Shiru tayi bata amsa ba , kamar yadda hawayen ta ya ƙi tsayawa , a dai-dai lokacin zuciyar ta tayi rauni wajen riƙe ciwon da yake damunta a rai ta hana shi bayyanuwa.

" Kiyi haƙuri zai zo ku tafi ,yana son ki dayawa Falmata inshaAllah a gidan ki za ki haihu .

" bai taɓa ƙiran mu ba tunda muka zo fa Yakaka , watakila ma ya sake ni bansani ba ni tausayin abunda yake ciki na nake yi ban..

" Youssouf ba zai taɓa sakin auren ki ba ya furta hakan da bakin sa kuma a aikace ma ya nuna ki kwantar da hankalin ki kiyi ta addu'a kin ji ko ?

GyaÉ—a kai tayi tana share hawayen ta dai-dai da dawowar Amne da ta shiga cikin asibitin yin dubiya , damuwar da take damunta ta É—an ragu .

Da layi yazo kan ta ita kaÉ—a ta shiga , su ka gaisa da likitar mace ce , ta yi mata duk wasu tambayoyin da aune-aunen da suka dace , bata da matsalar kome dan haka magungunan da yakamata masu ciki su dunga sha kawai ta rubuta mata .

Rashin ji daga Youssouf ba Falmata kaɗai yake damu ba , har Khaalty Rahima , Amnee da Prof da kan shi , rashin jin wani bayani ko da na ƙiran waya ne daga Youssoufa ya sa su a tunanin makomar auren sa da Falmata ?

Sau biyu Prof da Amnee suna tattaunawa a tattaunawar su ta ƙarshe prof ya yanke shawarar kan cewa idan har Falmata ta cika watanni biyu a gida , zai tashi ɗan aike zuwa masarautar Maradi dan sanin halin da Youssouf yake ciki da kuma makomar auren 'yar su , saboda rana ɗaiɗaiku ne bai ƙiran layin wayar Youssouf ɗin amma bai tafiya , ya zama dole yayi wani abu akai a matsayin sa na waliyyin auren kuma a yanzu shi matsayin Uba yake a wajen ta .

Falmata taso a bar ta ta dunga bin Yakaka Islamiyar da ko bayan auren ta da Doctor Hamza bata daina zuwa ba .

Da farko Prof ya ƙi yarda domin yace babu iznin Mijinta , tayi zamanta kawai a gida sai dai yadda a kwana biyun take yawan zaman shiru damuwar ta kamar ƙaruwa tayi tun bayan zuwanta awu , har 'yar rama tayi gaba ɗaya bata walwala .

daga Yakaka ta tafi islamiyyar da take kusan yini a can dan ƙarfe tara na safe take tafiya sai huɗu da rabi na yamma suke tashi kafin ta iso gida biyar saura .

Shikenan Falmata sai ta zama shiru a ɗaki ita ɗaya ƙwal, tun Khaalty Rahima na nunawa Amnee kar ta damu kan ta indai Falmata ce daman tun asali ita ba mai yawan son shiga jama'a bace kamar Baban ta take marar son hayaniya

Har ita da kan ta Khaalty Rahima ta fara damuwar saboda sai ta yini a É—aki abinci ma da kyar take fitowa ta ci , Hajja ce daman mai shiga É—akin ta dame ta har sai ta fito da ita , ita kuma wannan satin duk tana wajen danginta ana biki bata zauna ba .

Dan haka sai Amnee ta sake yiwa Prof maganar shiga islamiyyar Falmata ta sake masa ƙorafin zaman kaɗaicin da Falmatan take yawan yi kar ya sa mata ciwo .
Prof yace " zai duba lamarin .

Ranar asabat da safe kafin lokacin tafiyar Yakaka makaranta , Amnee ta shiga ɗakin su Yakaka hannun ta riƙe da baƙar leda da kaya a ciki ,

" Yakaka har kin fara shiri ne ?
Amnee ta tambaya tana ɗora ganin ta kan Yakaka wacce take sanya safa a ƙafar ta , da sauri ta ɗago fuskar ta da murmushi tace " Eh Amnee sannu da shigowa ,
" Yauwa sannu takwara ta furta hakan tana sauƙe ganin ta akan Falmata da take kwance akan gado ta basu baya ,

Ledar hannun ta ta ajiye a bakin gadon , kafin tace " Fatima tashi ki shirya yau dai ke ma za ki fara zuwa islamiyyar , tun kwanaki biyu na sake yiwa Baa Alaji zancen kin ga ashe an miki register ga Uniform É—in ki ma da litattafan ki duk kin samu sai tafiya makaranta kawai ..

Falmata wacce tunda Amnee ta fara bayani ta tashi zaune tana murmushin da ta zarce da dariya jin ƙarshen bayanin Amnee da sauri ta sauƙa daga gadon tana cewa ," Amnee nagode , nagode Allah ya saka da Alheri ki yiwa Baa godiya , inason islmiyya sosai wallahi .

Ta ƙarasa zancen da nufar banɗaki domin watsa ruwa , Yakaka da Amnee suka bi bayanta da kallo fuskokin su ɗauke da murmushi .

Sosai fara zuwa makarantar ta ya rage mata damuwa domin kuwa yini suke karatu bata samun damar zurfafa tunani ,

Yau da ƙafa ma suka taho daga makarantar da yake tazarar tsakani ba mai yawa sosai bace Falmata tace, "Yakaka nafi jin daɗin makarantar nan fiye da Ecole ɗin mu ta Niamey wallahi ,

"Meyasa ko kin fi gane karatun nan ?

" A ah saboda a can ko na tafi ecole tunanin Mama baya bari na gane karatun sosai , Allah sarki Mama ta kusa watanni biyu da rasuwa amma koyaushe ji nake kamar É—azu ta bar ni .

Murmushi Yakaka tayi , "ke da Mama ƙauna ku mai girma ce ai, nima naso Allah ya bani damar yin rayuwa tare da ita ko da ba mai yawa bane da nima na samu ladar jinyar ta da sanadin haka Allah zai bani lada mai yawa .

" da kuma za ki so ta dayawa fiye da son da kike mata domin Mama 'yar baiwa ce a cikin yara sa'o'in ta wayon ta daban ne kaifin hankalin ta yafi na shekarun ta .

Murmushin Yakaka tayi tana jin kewar 'yar ta na zagaya jinin ta , kewa kuwa mai tarin yawa ,

Ajiyar zuciya Falmata tayi daga nan ta shiga ba wa Yakaka labarin wayo da iyayin Mama wanda daman kusan rana É—aiÉ—aiku ne da ba ta bata wasu labarai da suka shafi Mama .

Tun a harabar gidan suka fahimci akwai baƙi a gidan saboda baƙin motoci da suka gani har uku ,
"yau baƙi ne a gidan ko su waye ?
Yakaka ta furta hakan tana bin motocin wajen da kallo , can daga ƙasan ran ta tana fatan Doctor hamza baya cikin su .

" To Allah yasa baƙin alkhairi ne ,
Falmata ta furta hakan lokacin da suke nufar ciki

Tun kafin su shiga falon ƙamshin da ya karaɗe illahirin harabar wajen yake basu tabbacin baƙin na girma ne .

Da Sallama suka shiga falon , idanun su akan hamshaƙan mata huɗu da suke kan kujerun falon sai kuma Amnee da take a tsakanin su fuskar ta fal fara'a .

Ɗan taƙaitattcen kallo Falmata ta yi musu da taimakon gilashin idanun ta ta shaida fuskar Ammi , yayar Biyamuraɗi Youssouf , fuskar ta na nan zane a zuciyar ta kamar yadda munanan kalmomin da suka jefa musu yake rubuce tsaf a cikin kwakwalwar ta ,

Dan haka sai taƙi tsayawa kamar yadda Yakaka ta tsugunna gaishe su ,duk kuwa da cewa ita ma ta gane Ammi ,

sai ita ta ratsa ta bayan kujerun falon tayi hanyar É—akin su .

Yadda tayi sam bai yiwa Amnee daÉ—i ba , dan haka ta É—an É—aga sauti tace " Fatima zo nan , zo ku gaisa da surukan ki mana ko baki gane su bane ? Yanzu suka iso .

Jaa tayi ta tsaya kafin ta waigo cikin rashin kuzari ta dawo baya kaɗan ta yi durƙuso daga nesa tace " Ina wunin ku ?
" Kadaran-kadahan Ammi ta amsa ,"da lafiya lau , tana janye ganin ta daga kan ta

Asma'u wacce tun shigowar su take faran-faran cike da kissa tace " tashi tashi ƙamna ta durƙuso ba naki ne ba , ɗaga yayar ki daga durƙusso Mairama .

Da sauri Aisha Mairama ta miƙe fuskar ta ɗauke da faffaɗan murmushin ganin Falmata , kafin ta ƙaraso Falmata ta miƙe akan ƙafafun ta guntun murmushi ta yiwa Aisha bata tsaya ba tayi juyawar ta ba tare da ta yadda ta sake duban kowa ba ta nufi ɗaki .

" Mama kar ki tafi ki barni ki jirayeni Mama , nan ina ne muka zo Mama ?

Chak ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin zuciyar ta na sauya bugu wannan muryar ta Mama ce , Mama ce take ƙiran ta , da kitsima hakan cikin ranta ta juyo da sauri laɓɓan bakin ta na ƙiran Mama .

Idanun ta suka sauƙa kan 'yar yarinyar da bata kai Mama a girma da wayo ba sai tsantsar kamanni da take yi da Mama , tana kokawar riƙe hannun Mamar ta da suke sauƙowa tare daga ƙafar benen a tare Khaalty Rahima na bin su a baya ,

"Yumna
Ta ƙira sunan ta da ƙaramin sautin da bai hana Yumna ta jiyo ta ba , a hankali ta ɗora ganin ta kan ta tana wara manyan idanun ta masu cike da wayo , sai ta sake matsawa jikin mamar ta tana riƙe hannun ta da kyau lokaci guda ta haɗa da maƙale kafaɗa .

" Yumna ki je wajen Mamar ki tana ƙiran ki , Siyama ta furta hakan tana ƙoƙarin zare hannun ta daga cikin na Yumma ,

A hankali Falmata ta É—aga idanun ta ta É—ora ganin ta kan kyakkyawar doguwar matar da take tsaye gaban ta tana jifan ta da tsadaddan murmushin da yake sake fiddo zallar kyau da wayewar ta , ba sai an faÉ—a mata ba ta fahimci ita ce Mahaifiyar Yumna , kenan wannan ce Siyama matar Youssouf tuno da matsayin da suke kai a wajen juna ya sa tayi saurin juyawa ta É—aga taku tana barin wajen , zuciyar ta cike da tunanin abunda ya kawo su haka ? Ko sakin nata aka zo kawo mata tare da matar tasa ?

Karɓa irin ta girma da girmamawa ita iyalan Maimartaba suka samu daga wajen Prof da nasa iyalan , duk kuwa da cewa ba'a san da zuwansu ba , hakan bai hana a shiga hidima da su ba ka'in da na'in babu ƙyashi Prof ya buɗe bakin Aljihu aka shiga hidima da su kamar daman can an san da zuwan su dan haka basu tarar da gidan tare da wata alama ta ƙasƙanci ba .

Gidan Attajiri suka tarar da ya matuƙar birge su a matsayin gidan su Matar da Youssoufa yake aure , duk sai jikin Ammi da Asma'u '( yar Hajiya Mama ) yayi sanyi da daman su biyun ne suka zo da wata manufa ta daban , sai suka ga ko su sai dai su gwadawa gidan su Falmata sarauta amma ba dai su ƙasƙantar da su ba . ( Daman Bare-bari ai ba daganan ba indai fagen bajinta ne ) .

Tunda Falmata ta shige ɗaki bata fito ba a ciki tayi sallar ta ta magarib da isha'i ta hau gado ta lulluɓu bayan ta kashe wutar ɗakin , ta rasa takamaimai halin da zuciyar ta take ciki , farin-ciki ne ko saɓanin sa ?
"watau sai yau ya waiwayo ta ? Bayan yasan ya mata laifi , yasan cewa dole tana jiran sa , yasan kuma a halin da take ciki da halin da ta baro wajen sa a ciki .
Can ƙasan ranta kuwa , So take ta ji ko da tashin ƙamshin sa ko kuwa amon muryar sa dan ta san cewa ya zo amma ko alama bata ji ɗuriyar sa ba a gidan .

Sai juye-juye take yi akan gadon , juyi ta sake yi lokacin da taji an turo ƙofar an shigo gami da kunna wutar ɗakin haske ya gauraya da sauri ta miƙe zaune bayan ta yaye mayafin da ta rufu da shi ,

Khaalty Rahima ta gani a tsaye a bakin ƙofa , daga inda take tana iya hango ɓacin ran da yake shimfiɗe kan fuskar ta ,
" Mama sannu da shigowa .
Khaalty Rahima bata amsa ba sai da ta ƙaraso kusa da ita , sannan tace " me kike a ɗaki ke kaɗai ? Kina sane da baƙin da suke gidan nan domin ki suka zo , "yan uwan mijin ki ne na jini , wai me yake damun ki ne ? Aina kika koyo wannan mugun halin na walaƙanta mutane ?

A ɗan tsorace Falmata tace , kiyi haƙuri Maman mu , un daman ai naga Yakaka tana wajen su suna hira .

Daƙuwa Khaalty Rahima tayi mata da hannuwanta duk biyu , " kin ci gidan ku Falmata, dangin Mijin Yakaka ne ko naki ? To bari na faɗa miki gara tun wuri kiyi watsi da wannan banzan halin ki daina dan kuwa ba inda zai kai ki , Mijin ki ɗan Manyan mutane ne gaba da baya ɗan sarauta ne shi da 'yan uwan sa halin girma da girmamawa cikin sa suka taso , shi aka saba gwada musu , muddin kika ce zaki je musu da saɓanin sa ke ce za ki sha wahala kiyi baƙin jini a wajen su ba ke ba har ya'yan da zaki haifa musu .

Shigowar Amnee bai sa Khaalty Rahima ta tsagaita ba ta cigaba da cewa , " ki tashi ki shirya ki fito kije ki gaishe su da kyau da kyau biyu daga ciki yayun mijin ki ne ɗaya kuma ƙanwar sa ce ƙaramar su , ɗayar kuwa kishiyar ki ce nasan ba zaki gagara sanin cewa 'yar uwar sa bace da suke 'ya'yan Mace da Namiji dan haka gara ki nutsu kiyi hankali ki daina wannan futsancin naki da tsagerancin wofi ,idan ba ma Allah yayi ba ina ke ina su ?

Unm, unm , unm Rahima banda gori kuma , ai shi arziƙi da ɗaukaka na Allah ne , amma 'yata ke ma baki kyauta ba baƙon ka ai abun girmamawa yake a wajen ka , bare kuma waɗannan da suke tafe tun daga wata ƙasa musamman domin tafiya dake , ki shirya kije ku gaisa har can falon Baa Alaji za'a raka ki akwai Manyan mutane da suka zo tare ɗaya daga cikin su Baffan Maigidan ki ne kuma shine waziri garin su sai kuma wasu manya daga wajen su dan haka kiyi shiga ta kamala sosai ko na shirya ki ?

Sai a lokacin Falmata ta ɗago kanta da hakan ya bawa ƙwallar idanun ta da suka taru damar zubowa faɗan da Khaalty Rahima ta mata ya haɗu mata da tasowar miƙin irin cin mutuncin da 'yan uwan Youssoufa suka masu a Niamey da yana daga cikin dalilan da yasa ta bar shi wutsiya a zage.
Muryar ta na rawa tace " Maman mu da Amnee ku yi haƙuri ku yafe min , amma ni bazan koma ba.

Kallon da suka bita da shi bai sa ta tsaya ba cikin kuka ta cigaba da cewa
" 'yan uwan sa basa sona zagin mu suka dunga yi suna min gori har iyayena suka aibata sun ce É—an uwan su ya sake ni me zai yi da ni 'yar gudun Hijira 'yar matsiyata Mama har cewa suka yi ...
" Khalass Amnee tace tana zama a gefen ta ta riko ta zuwa jikin ta , kukan da take yi ya taɓa ran su sun kuma fahimce ta , daman Khaalty Rahima ta riga ta san akwai wani dalilin da yasa falmata ta yi mu su yadda tayi , tasan halin 'yar ta Falmata mutum ce mai zuciya da gudun raini , ko kusa bata yadda a taka ta ba tare da ta rama ba .
Amnee ta cigaba da cewa
"Ko ma me suka ce miki ai ga su dai yanzu iyayen su sun taso su da aiken zuwa su koma da ke cikin girmamawa saboda kin riga kin zama wata ɓangare na jikin su , kiyi haƙuri ɗaukaka bata zuwa a sauƙaƙe , sai an zage damtse an ware ƙwanji wajen neman ta an kuma haɗa da haƙuri da juriya , wa ya faɗa miki inda samun ɗaukakar ka yake zai kasance kewaye da masoyan ka ? Ai ɗaukaka mai tasiri ita ce wacce aka ratsa tsakanin maƙiya wajen samun ta .

" ki zama jaruma Fatima-zara gidan sarauta kike aure , Yarima kike aure watarana idan da rai Matar sarki za ki zama dan haka saurin fushi ai ba naki bane .

"Sau da dama akwai wuraren da fushi baya yin tasiri sai fa saɓanin sa watau kwantar da kai da kawaici , hannun da ya juri miƙo maka gorar duma kana shan ruwan ciki da ɗaci , sannu kan hankali watarana shi zai miƙo maka gorar zuma tattaciya ka kwankwaɗa daga zaƙin ta , muddin kayi haƙuri saboda kome na duniya ɗan haƙuri ne kiyi haƙuri ki maida kome ba kome ba , kin ji ko ?

Gyaɗa kai tayi tana share hawayen ta , zuciyar ta taji tana sanyaya daga ɗacin da ya cunkushe mata rai , ko ba kome yau sun tako sun ga tushen ta inda Mahaifiyar ta ta taso gidan wanda yake matsayin Mahaifi a wajen su , sun kuma san cewa ita ba walaƙantatciya bace har irin yadda suke zato tare da yin iƙirari , daidai gwargawdo Prof ya zama inuwar fakewar su .

" shiga wankan maza ki fito na shirya ki kin ji ko ?

Amnee ta sake cewa hakan lokacin da Khaalty Rahima ta juya tana barin É—akin .

Da taimakon Hasken da yake falon tar kamar rana Siyama ta ɗora ganin ta akan Falmata wacce tun kafin ƙarasowar ta wajen ƙamshin sassanyan turaren wutan da Amnee ta turare ta da shi iri daban-daban da kuma humra ya ratsa ƙofofin hancin su .

'yar ƙibar da tayi bai sa takun tafiyar ta mai kyau sauyawa ba , tana shirye cikin turarriyar koriyar lafaya mai adon manyan furanni launin jaa mai duhu , da ta naɗa ta akan wata doguwar rigar atamfa mai launin kore mai haske tayi ɗaurin ɗankwali sassauƙa fuskar ta babu wata kwalliya sai ɗan kunnen ta dogo ruwan silver da ya amshi 'yar zagayyar fuskar ta mai ƙaramin kyau .

fuskar ta ɗauke da 'yar madaidaiciyar fara'a ta ƙaraso .

Yanzu ne ta ga Fatima-zahra sosai , sai dai bata hango abu guda da ya razana ta game da ita ba da ya wuce yarintar ta , ko ba a faɗa mata ba ta ga alamu da dama a bayyane yarinya ce ɗanya da bata wuce shekaru goma sha tara zuwa ishirin ba da in kuwa hakane a kiyaste zata iya girme mata da shekaru aƙalla takwas zuwa tara , ba shakka tauraruwar ta zata daɗe tana haskawa .

Murmushi tayi lokacin da take miƙewa , kafin falmata ta ƙarasa durkuson da take shirin yi ta ɗago ta , ɗago kan ta Falmata tayi suka yi musayar kallo kowaccen su da taƙaitatcen murmushi akan fuskar ta ,
" Kul ki daina yawan durƙuso ƙamna ta , so kike ki yiwa ɗiyan mu lahani ? Ƙaraso ki zamna ni na amshi durƙuson na gaishe da yayun mu ,

Hannun ta ta jaa suka ƙarasa kujerar da ta taso daga kai , maimakon Falmata ta zauna akan kujerar da take mata nuni sai ta zauna a ƙasa ta shiga gaishe da Ammi da Asma'u da suke bin su da kallo , suka amsa mata kamar ɗazu a taƙaice suka ɗora da tambayar ta lafiyar jikin ta ? Murmushi tayi bata amsa ba .

Ta waiga ga Siyama wacce take kallon ta fuskar ta cike da murmushi , "sannu ku da zuwa Mamar Yumna yaya hanya ?

"lafiya lau Fatima ƙamna ta da fatan mun cimmuku ƙalau ?

"Lafiya .

Falmata ta amsa mata a ɗan taƙaice , a mutunce suka gaisa da Aisha Mairama .

Shiru ya ɗan biyo baya kafin Asma'u ta juya ga Amnee da son jin ƙarin bayanin da take mata kan haɗin wani turarurruka ( humra )na musamman da matan N'Djamena ke amfani da shi a sassan jikin su da tun shigowar su Amnee ta tare su da tururrukan humran launi-launi cikin wasu 'yan ƙananun kwalabe da aka jera su akan ɗan wani faranti na musamman , ta basu suka shasshafa da daman haka al'adar su take na tarar ɓako da turare musamman idan baƙon na girma ne ,

Ƙamshin sun yiwa Asma'u daɗi kamar yadda ruwan turaren da kansa ya burge ta launi-launi gwanin sha'awa ga turaren ya zauna musu a jiki ko yaya suka motsa ƙamshin sake tashi yake .shine take son sanin yadda ake harhaɗa su , Amnee kuwa tayi alƙawarin koya mata .

Ita kuwa Ammi takaicin Siyama ne fal ya cika mata rai cikin ran ta cewa take "haba me ake da lusaranci irin na Siyama ? Yanzu kishiyar ce abun tarairaya da gatatawa ya haka ? Tun a can ta so a hana Siyamar tahowa saboda ita bata ga dalili ba zuwa bikon kishiya , amma Siyama ta kafa naci har da yin fushin da guntuwar ƙwallar ta , ganin haka yasa Umma amincewa aka taho da ita domin da farko ita ma ƙin amincewa tayi da tafiyar ta Siyama .

" en loi kin yi kyau sosai , ƙwalliyar ki ta burge ainun .
Mairamar sarki ta furta hakan lokacin da take baro inda take zaune ta dawo kusa da Falmata ta zauna , gani na farko da ta yi mata ta ji ta burge ta ,tana ƙaunar ta musamman da ta gan ta yarinya kamar ma zata girme mata .

"Nagode , Falmata tace tana 'yar dariya idanun ta ta sauƙe kan Yumna da aka mata Shimfiɗa da wani lallausan bargo daga gefe tana ta baccin ta da alamun gajiya a tattare da ita ,

" tayi bacci ne ?
tace da ƙaramar murya ,
Murmushi Siyama tayi tana cewa "É—iyar ki tayi baccin gajiyar hanya bata saba ba , ga shi kouma baku ko gaisa ba da alama dai yau a É—akin ki zata kwana da dare idan ta farka kun gaisa ...

"Da gaske ?
Falmata ta furta hakan tana dariya cikin zumuÉ—i ta É—ora da cewa
"bata ƙuiya sosai ko ? Ba zata yi rikici ba ko ? Tunda bata sanni ba Bana so tayi kuka .

Siyama tana murmushin jin daɗin ganin zallar ƙaunar 'yar ta a fuskar Falmata tace

" A haka zaku saba ai 'ɗiya ba ta ƙi mamar ta ba...

Kafin ta ƙarasa faɗin abunda tayi niyya Muryar Ammi ta katse mata zancen ta ta hanyar cewa .
"So kike tayi ta ihu kenan ? Wannan ai É—aukar hakki ne ki bar 'yar ki a katarar ki sai yafi alheri .

Shiru wajen yayi na É—an wani lokaci kafin muryar khaalty Rahima ta ratso wajen fuskar ta da É—an murmushi tace

" gaskiya kam bare ga baƙunta ga baƙuwar fuska abun zai zama bibbiyu , gara ta zauna a wajen Mamar ta cikin Alheri .

" Yakaka da ta lura da sanyin da jikin Falmata yayi sai tace " Falmata da son yara kike wallahi, anya ma kuwa za ki yarda a ɗau naki , zamu gani ai lokaci kaɗan ya rage ke ma ki riƙe naki a hannu inshaAllah .

Mairamar sarki ma da abunda yayar su ta ta so yi ya É—an sanyayar mata da jiki sai tace

" ai kuwa ni ce mai raino dole ma ta ba mu ɗan mu ko 'yar mu ko mon beau-père ?

Dariya Siyama tayi tana waskewa hararar da Ammi take jefo mata ta ƙasan ido tace

" É—akina ai nan ne wajen ajiyar kayan sa , ni zan dunga shirya shi , kafin a yaye shi daga an yi yaye kuma zai dawo wajena gabaÉ—aya sai dai Mamar su ta kawo mana wasu kuma .

Amnee ce katse musu hirar da suke yi lokacin da ta ce , " Aisha raka ta ta gaishe da baƙi a sashin Baban su .

Bayan dawowar su daga gaishe da su waziri Falmata bata tsaya a falon ba ta musu sai da safe kawai ta shige É—aki , tana warware lafayyar jikin ta zuciyar ta na ga tunanin bata gan shi ba ,Ina yake ? ko dai bai zo bane ?

GabaÉ—aya sai ta nemi É—an farin-cikin da ta tsinci kan ta ciki ta rasa da daman zuwa yanzu ta fahimci kusanci da shi da ta samu sanadin ganin 'yan uwansa da zaton ta tare suka zo zata gan shi shine ya sata murna .

A yanzu kuma da ta fahimci bai zo ba duk sai ta ji ƙunci na safko mata wani sashi na zuciyar ta taji yana raɗa mata , " Falmata ke fa kike damuwa da shi dan rashin zuciyar irin taki , shi bai damu da ke ba tunda ga shi ya ƙi zuwa wajen ki sai wasu ya turo wai su tafi da ke sai kace wata kaya , zuwan nasu da bai wani burge ta ba , a gurin ta da shi kaɗai tal yazo , ta gan shi suka yi komawar su tare da hakan ne zai sanyata farin-ciki akan waɗannn da aka turo ga shi tun a gaban iyayen ta ma wannan yayar ta shi sai wani hararar take , ko meyasa ta tsane ta ? Oho .
Mts
Tayi tsaki lokacin da take zama bakin gado , tana ƙoƙarin ture tunanin sa dake damun zuciya da kwakwalwar ta .

" Falmata na , ai damuwa kuma ta ƙare tunda ga 'yan uwan sa sun zo tafiya dake , za a mayar da ke gun angon ki mu huta da jin kukan ki da ganin ƙuncin ki "oh su soyayya manya .

Yakaka ta furta haka da dariyar tsokana lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin ,

Yamutsa Fuska tayi ta kawar da kai gefe kafin tace " waye yake cika miki kunne da kukan Yakaka bana so .

"Rabu da ita en loi , jibi war hakka kina cikin masarautar mu bayun ki na miki hidima daÉ—a ai ke É—in sarauniya ce matar Yarima ,

Murmushi su duk biyun suka yi da ganin shigowar Aisha da ta cigaba da cewa

" kun yi waya da Biyamuradi ko ? Ya jikin na shi da sauki kou ? Ni dai nan tunda munka tasso da mun ka baro shiyar ƙasar mu Téléphone carte sim pas de service .

A hankali Falmata ta É—ago kanta zuciyar tana sauya bugu , da wani yanayi a muryar ta tace " Daman ba shi da lafiya ne ? Me ya same shi ?

Da sauri Aisha ta dafe kai tunowa da tayi da farkon zuwan su a can falon Prof bayan Waziri ya yiwa Prof taƙaitatcen bayani kan rashin lafiyar Youssoufa da shine dalilin da ya kawo jinkirin zuwan su , amma zuwa yanzu lafiya ta fara samuwa gare shi da yardar Allah , a ƙarshe suka daɗa neman afuwa tare da neman iznin tafiya da Falmata a gobe .

Prof ya jajanta musu sosai ya kuma yi musu addu'o'i sannan sai shima ya shigar da neman Alfarma kan a ƙara masa kwana guda tal a bar tafiyar tasu zuwa jibi , sannan kuma ya nemi da a sakayawa ita Falmata batun rashin lafiyar Mijinta tunda bata riga ta sani ba saboda halin da take ciki da ba'a son abunda zai tada mata da hankali .

A take duk suka yi Na'am da shawarar Prof kan cewa za'a rufe rashin lafiyar Youssoufa har sai Allah ya masa dawowa sannan kuma zasu É—aga komawar su zuwa jibi .

"Aisha daman Youssouf jinya yake ?

Yakaka ta tambaya tana dafa kafaÉ—ar Falmata da ta lura ta shiga damuwa sosai .

Da ƙoƙarin sauya akalar zancen Aisha tace " eh ,Ah ah ba wani ciwo bane ya dai tafi india ne , kai Mutanen Maiduguri kun ji daɗin ku ko'ina turaren wuta yana ci
Ta ƙarasa zancen tana musu nuni da ɗan burner da take cin turaren wuta a hankali .

" yayi tafiya ? Kuma kika ce ba shi da lafiya ne , dan Allah ki faÉ—a min mana ,

Falmata ta furta haka tana jin wani gagarumin tashin hankali na rufar mata , muryar ta har 'yar ƙyarma take yi .

Da sauri Aisha ta zo gefen ta ta zauna , ta dafa kafaÉ—ar ta sannan cikin taushin murya da alamar rarrashi tace ,

" en loi kadda ki damou Biyamuradi ya shiga haÉ—arin rayuwa ne Amma Allah ya fidda shi , doumin kouwa yanzu yana samun lafiya sosai , cikin watan ga mai kamawa shi ke dawowa da yardar Allah kin ji kou ?

Gyaɗa kai kawai Falmata tayi daga haka ta miƙe daga tsakanin su , su duk biyun da kallo suka rakata har ta shige banɗaki .

Yakaka ta sauƙe ajiyar zuciya tana dawo da ganin ta kan Aisha , cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace .
"amma ciwon da yake damun sa ba mai tsanani bane ko ?

Ita ma cikin raɗa Aisha tace " ya fa fara samoun sauƙi nima dai baƙina ya subce min .

Miƙewa tayi tana ƙarasa cewa " bari na kouma ga masauƙin mu daman na tou yi muku sai da sahe .

" ku huta gajiya Aisha mun gode ,

Yakaka ta furta hakan da 'yar dariya ganin yadda duk Aisha ta ruÉ—e da ganin sauyawar Falmata .

bayan ta fita a sarari Yakaka tace "Hmm indai wannan 'yar rigimar ce ba ku ga kome ba .

" wa kenen ?

Falmata ta tambaye ta lokacin da take takowa cikin ɗakin kai tsaye ta nufi ɗan saƙon da suke yin Sallah ta hau Sallaya bayan ta zura dogon Hijab har ƙasa ta fara haramar tada iƙhamar sallar shaf'i .

" Ni kaÉ—ai nake zance na Yaa Falta .

Yakaka ta furta hakan tana miƙewa ita ma ta tafi ɗauro Alwalar ta .

Washegari tun asuba masu aiki suka shiga hidimar abincin Baƙi Amnee da Khaalty Rahima basu zauna ba suna tsaye a kan su suna sa hannu a inda ya dace suna kuma gwada musu .

Kafin ƙarfe takwas illahirin harabar gidan har maƙota ya ɗau ƙamshin girki da sumfurin ƙamshi iri-iri na daga sunadaran ƙamsasa girki na mutan N'Djamena .

Mutan Niger sun ci sun gyatse sun kuma yaba sun zuba santi ba kaɗan ba domin kuwa Ɗan Malikin Maraɗi Mai ruwan kuɗi lokacin da ya gama ƙurbe shayin da aka cika masa 'yar butar shayi ( kettle ) cewa yayi " shi kuma wannan ruwan me sunan sa ? 🤔 ga shi dai yana wani zaƙi-zaƙi kamar tattaciyar zuma farar saƙa , ga kuma wani tsami-tsami da yake yi kamar matsatsen ruwan ɗan itaciyar inabi , ga kuma wani garɗi-garɗi da yake kamar ruwan zam-zam , ƙamshin da yake tashi a cikin sa ai mai samar da nutsuwa ne irin wannan idan kana shan sa kullum ai ka tsufa da ƙarƙon ka 😂

Amnee bata zauna ba ita ta shiga gyara Falmata ta sake goge mata jiki da sauran kayan gyaran jikin Amare da ya rage , kasantuwar bata iya zanen fulawa ba hakan bai hana bayan ta gama murjewa Falmata jiki ta kama kwaɓa lalle da turarurrukan ƙunshi irin nasu bayan ta jiƙa ganyen 'yar itaciyar "Sofan " ta ɗiga ruwan sa da yayi jawur a ƙwabin lallen ta ɗan ajiye shi ya jiƙu kaɗan ta kama ƙafafun Falmata ta rangaɗa mata lallen gargajiya a tafin ƙafar da kan yatsu .

Sha ɗayan rana Hajja ta iso da daman tun jiya Amnee ta ƙira ta a waya take sanar da ita batun zuwan dangin Mijin Falmata da zancen komawar su .

Da gama wayar su Hajja ta hau shiri ran ta cike da farin-cikin jin cewa Uwarɗakin zata koma ɗakin ta , daman bikin ya ƙare dan haka yau tun safe ta bi dangi ta yiwa kowa Sallama .

Prof ya nemi ganawa da Amnee tare da Khaalty Rahima bayan sun amsa ƙiran su ya tambaye su kan me da me ake buƙata da Falmata zata tafi da shi ?

Amnee tace " Baa Alaji ai lokaci ya ƙure na yin wani babban shiri sai dai kawai za'a ɗiba mata su turaren wuta a cikin na 'yar uwar ta ..

"Meyasa ita baza'a mata nata ba kada a taɓawa 'yar uwar ta kayan ta .

Prof ya katse ta , cikin kwantar da murya Amnee tace " to ai lokaci ne ya ƙure yau ne fa kawai ? Idan aka ɗibar mata kaɗan na Amfani idan ya so bayan sun tafi sai nayi waya can N'Djamena ayi mata nata a kuma ƙarowa Takwarata nata a tsanake idan Allah ya sauƙe ta lafiya sai mu tafi mata da kayayyakin ko kuwa ?

Ta tambayi khaalty Rahima . "Hakane Ukhtee ,

Prof ya ce to kayan É—aki fa da na Amfanin gida ba za'a sauya mata wasu ba ?

"duk su ma idan ta haihu sai a mata sabbi tunda yanzu tafiyar ba ta shiri bace .

"Hakane to Allah ya kai mu kafin lokacin duk za'a tanadi kome ko ke da kan ki sai ki tafi Dubai yi mata sayayya .

Godiya mai yawa Khaalty Rahima ta yi masa bai amsa ba sai cigaba yayi da cewa a cikin ku biyun waccece zata raka ta ?

'Yar Dariya Amnee tayi kafin tace " da wai ni cewa nayi ko Zainab ma tunda ita take kusa anan sai ta kawo yaran idan Mijinta ya yarda sai su tafi tare tunda ga Hajja da daman tare suke , idan ta haihu mu sai mu je .
Cike da Amincewa Prof yace
"wannan shawara ce mai kyau bari zan ƙira shi Maigidan Zainab sai na nemi iznin sa da kaina , Allah ya kai mu .

" Amin Amin , Amnee ta amsa cike da jin daÉ—i

Bayan fitowar su daga sashin Prof a harabar gidan suka ci karo da Yakaka sai kai-kawo take a mamakance Khaalty Rahima tace " ke kuma me kike yi anan ?

Da sauri ta matso tana riƙo hannun Amnee ta ɗan rangwaɗa kai sannan tace " Amnee Dan Allah zan raka Falmata Niger ɗin ? Bana son ta tafi ita kaɗai nasan duk takura zata yi a tsakanin su tunda basu wani saba ba .

Kallon kin cika sakarci Khaalty Rahima ta mata kafin tace " Da iznin wa za ki tafi ? Kin san dai da Auren ki idan kuma gaban kan ki za kiyi to ,
Mayar da ganin ta tayi kan Amnee ta cigaba da cewa
" Ukhtee mai sunan ki dai sai kina yi kina taro ta sam bata da wayo .

Daga haka ta shige ciki ta bar su a tsaye , Amnee ta dubi Yakaka fuskar ta cike da murmushi tace ," takwara kema ai Amarya ce duk yaushe aka yi bikin ki ,? Ki bari idan ta haihu sai mu tafi tare .

" Amnee kawai raka ta zan yi fa Wallahi tausayin ta nake ji ace ta sake tafiya ita É—aya , sai Hajja .

" Zainab ma zata raka ta .

Ta katse ta .

Zata sake yin wata maganar Amnee tace " ki tambayi iznin Mijin ki idan ya bar ki sai ku tafi tare .

"Ɗan tsallen Murna Yakaka tayi ta ƙanƙame hannun Amnee da yake cikin nata tana cewa "Nagode , nagode Amnee naa .

A hankali Amnee ta zare hannun ta ta wuce ciki tana dariyar rashin wayon Yakaka , ita yanzu idan an bar ta sai ta sake kwasar ƙafa ta bi Falmata ita bata tunanin gina nata gidan auren da har yanzu bata da takamaimai matsugunni a cikin sa ? Ita kenan kome na rayuwar ta zai biyo bayan uzurin Falmata ne .

Jinjina kai tayi cikin ran ta ta kasa ƙiyasto iya adadin girman ƙaunar da Yakaka take yiwa Falmata , can sashi guda na ranta dariya take dan tasan ko kusa Hamza ba zai Amince da tafiyar Yakaka Niger ba bare kuma Prof .

Bayan wucewar Amnee Yakaka tsumu tayi a tsaye , ita sai yanzu da aka ce ta ƙira Doctor Hamza ne ma ta tuna ko number sa bata da ita a wayar ta , gaskiya tana son raka Falmata Niger ɗin nan saboda ko a hanya wannan ƙatuwar matar zata nemi ɓata mata rai ta tare mata .

Zama tayi akan dan dandamalin da aka yi shukar furanni ta cikin sa tana tunanin ina zata samu layin Doctor hamza , ita dai ba zata iya tambayar Amnee ba kunya take ji , ba kuma ta son ta tambayi Rahima ko da a waya ne tasan sai ta sille ta ta mata tsiya .

Wayar Mamar su ta faɗo mata a rai tasan babu tantama akwai number sa a kai , to ko zata ɗauka ta ƙira shi kawai ma ta wayar ta ta ƙila yafi ɗagawa da wuri fiye da idan ta layin ta ta ƙira da bai san layin ba .

Da sauri ta miƙe ta shiga ciki , ta hau sama ɗakin Khaalty Rahima da sa'ar ta babu kowa a ɗakin , daga gefen gado ta hango wayar , da sauri ta ɗauka ta shiga neman sunan sa cikin jerin sunayen dake kan wayar bata sha wahala ba ta samu sunan tare da number sa .

Shiru tayi ta gagara danna ƙiran , tana son tattaro kalmomin da zata yi amfani da su wajen yi masa magana ,

Idon ta ta kai kan agogon wayar ta ga sha biyu saura tasan dai duk tsiya yanzu ya tashi a bacci duk kuwa da cewa yau lahadi ce ba aiki .

Fargaba bai rabu da ita ba ta danna ƙiran layin bayan ta kai wayar kunne ta runtse ido gam tana jin wani yanayi mai ƙarfi na shigar ta , daga can ƙasan ran ta addu'ar samun nutsuwa ta fara yi .

Wural ta buɗe idanun ta lokacin da ta ji sautin muryar computer na bata tabbacin babu kuɗin da zai isa ƙira a wayar .

Dariya tayi da ƙaramin sauti , kafin tace " kai Maman mu sai a bar ta ko meyasa take barin waya ba kuɗi ? Ita kamar ma bata wani damu da wayar ba .

Numbers ɗin ta kwafa a wayar ta , sai da ta zauna a bakin gado sannan ta danna ƙiran .

ABUJA

Daga can Sofiya ce a É—akin Doctor Hamza tana gyara gadon da basu wani jima da tashi a kai ba Doctor Hamza ya shiga wanka .

Tana gyara bargon su lokacin da wayar sa dake gefen gado ta ɗau kiɗa alamun shigowar ƙira .

Ba tare da ta dau wayar ba ta leƙa fuskar ta ga lambobi ne reras ba suna , ɗan yamutsa fuska tayi ta gatsina guntun hancin ta kafin tace "yau Sunday ma ba za ku bar mutum ya huta ba shi kenan cikin jigila tsakanin asibiti da gida yau kam rana ta ce sai na more lokutana da aka cinye na sauran kwanaki tsawon sati .

Har wayar ta gama ƙara bata ɗaga ba .

Daga can Yakaka tayi jim da waya a hannun ta , cike da tsoron kar ta dame shi ta daure ta sake danna ƙiran a karo na biyu ,

Wannan karon har Sofiya zata fice a ɗakin sai ta dawo baya , ta ɗau wayar kai tsaye ta ɗaga ƙiran tana kara wayar a kunne tace " Hello who's on the line ?

" Mukut
Yakaka ta haÉ—iye yawun firgici , jim tayi kafin tace " amm ni ce Yakaka ina kwana ? bata tsaya ba ta zarce da cigaba da cewa "ki kaiwa Yaya doctor wayar .

Ba domin Sofiya tana shakkar kar Doctor Hamza da tasan kunnen sa yana iya jiyo ta ba da ba abunda zai hana ta É—uÉ—É—urawa Yakaka zagi .

Baki ɗaya fuskarta tayi jaa a take tana huci tayi ƙasa da murya kafin tace " To akuya sarkin naci ana ƙorar ki kina daɗa naniƙewa , shugabar 'yan rashin zuciya Miji bai damu da ke ba sai ke ce ke neman sa jarababba , to ƙwalelen ki ke da Doctor sai gani sai hange daga nesa-nesa dan kuwa zaman ki kenan a inda kike 'yar .....

Ƙit !

Ta ji Yakaka ta katse ƙiran ,

Daɓas ta zauna a bakin gadon baki ɗaya ranta ya cunkushe har wani raɗaɗi take ji a hancin ta kamar ta shaƙi barkono ," wannan jarababbiyar yarinyar watau har ƙiran Mijinta take yi ?

" Sofi waye ya ƙira ni naji kamar kin ɗaga wayar ?

Da sauri ta waiga kafin ta miƙe tsaye ta ƙarasa zuwa gaban shi inda yake tsaye yana goge kansa da towel ,

Tana zuwa ta karɓi towel ɗin ta shiga goge masa jiki , bata yarda sun haɗa ido ba fuskar ta babu walwala tace , " Akuya ce ta ƙira ka ? 🙄

"Akuya fa ?

Ya tambaye ta yana duban ta da mamaki ,

Cike da bagararwa ta kai hannun ta ƙirjin sa tana ɗan tsikarin sa tace " eh dan kukan akuya nake ta ji tunda na ɗaga wayar ina Hello , Hello , Hello . Ba'a cewa kome sai Kukan Akuya .

Jawota yayi ya haɗe tsakanin su , yana kallon cikin tsakar idon ta yace " Sofi baki fa da kirki a wasu lokutan nasan daga Office ne aka ƙirani , Ni yanzu muje ki bani abinci na ci yunwa nake Ji ina son na fita akwai wani waje muhimmi da nake son zuwa yau .

Kicin-kicin tayi da fuska jin cewar zai fita yasa ta sake jin tasowar ɓacin rai da ya ɗan fara lafa mata sanadin haɗuwar fatar jikin su .

Bai kula ɓacin ran ta ba yayi shirin sa cikin wani yadi mai ɗan nawi ruwan zuma ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa sai lokacin ya juyo ya dube ta da take zaune a bakin gado ta kumbura suntum .

Fushinta bai wani taɓa masa rai ba yace " mu je ki bani abincin ba daɗewa zan yi ba zan dawo nima so nake na huta yau ɗaya .

Bayan ya ɗan cac-cakali Omelet da kidney Sauce ya ɗan kurɓi ruwan tea ya miƙe a gurguje ya mata sallama yana barin gidan .

Da fitar sa ta yi jaɓar ' akan kujera tunanin ƙiran wayar sa da Yakaka tayi ya bata tsoro , ita da ta saki baki ta zauna malumman ta sun ce mata an yiwa Yakaka da Hamza farraƙu to tayaya Yakaka ta iya samun damar ƙiran sa ? Kada dai ace asirin nan bai ci ta ba ?

Wani irin huci take yi lokaci guda ta tashi da gudu ta hau sama ɗakin ta ta shige laluben wayar ta , ya zama dole ta sabunta aikin ta .😂

***

Doctor Hamza kuwa yana fitowa hankali kwance ya dai-daita motar sa akan titi unguwar su Malama Maryam ya tasamma da bata kasance ɓaƙuwar unguwa a wajen sa ba , ya sha kai sofiya gidan ƙawar ta Samira .

Tsawon sati biyu da yayi yana bin duk wasu Matakai daki-daki domin tabbatar da zancen da Suleiman ya sanar da shi game da Yakaka gaskiya ne ko ba gaskiya ba ? Duk da cewa yana da tabbacin Suleiman ɗin ba zai masa ƙarya ba amma yana da buƙatar samun ƙwararan hujjoji ko dan ya wanke zargin ta daga ransa da hakan shine kaɗai zai ba shi damar samun nutsuwa tare da ita da zai iya rungumar ta hannu bibbiyu , tun usul ƙaunar ta bata tunbuƙe ba daga ransa girgiɗi kawai tayi da a yanzu kuma ta dawo ta tsaya chak da ƙafafun ta ta kuma shiga kaiwa duk wasu gaɓɓan jikin sa mamaya .

ASSALAMU ALAIƘUM MASU KARATU .

Da fatan duku kuna lafiya ? Sakamakon saƙonnin da nayi ta amsa daga masoya masu karatu kan taƙaice ƙarshen MHR da wasu ke ƙorafi wasu kuma suka nemi Alfarmar na ɗan sake jaan zaren labarin nayi dalla-dalla ko da kuwa ban yi filla-filla ba , hakan yasa na karɓi ƙorafi na kuma ɗan jaa kaɗan ba mai yawa ba da nan gaba kaɗan mu kan iya rufe bangon littafin mu adana shi Insha Allah

A ƙarshe ina godiya sosai da sosai ga dukkanin makaranta MHR na fili da na ɓoye daɗa nasan na ɓoyen sun ninka na filin yawa "ghosts readers barkar mu dai ina gaisuwa fa 😜❤nasan kuna tare da ni domin ina ganin inuwar ku , ko da kuwa baku bani tukuici ba .

Nagode.    [2/3, 9:34 PM] +234 803 083 8792: Mafari
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

50

Lokacin da Doctor Hamza ya isa unguwar su Malama Maryam dai-dai layi da gidan da Doctor Suleiman ya kwatanta masa sai ya ga ashe ma ya taɓa sanin gidan duk kuwa da cewa da dare ya taɓa zuwa amma bai manta da yarinyar da ya taɓa taimakawa ba a wani dare ana ruwan sama babu shakka a ƙofar wannan gidan ya sauƙe ta .

Kasancewar ana haramar sallar Azahar a lokacin dan haka a masallacin da yake kusa da gidan nan yayi Sallah .

Bayan ya idar sai ya matsa ya miƙawa Liman hannu suka yi musabaha , nuni ya yi masa kafin ya ɗora masa bayanin gidan da ya zo , to amma kasancewar an sanar da shi matar tana da aure ya zama dole sai da iznin Mijinta zai gana da ita , tunda ba sanin juna suka taɓa yi ba dan haka yake son sanin Mijin ta da farko , a zahiri wata buƙata ce ta son samun wasu bayanai daga bakin Matar da ake ƙira Malama Maryam yasa shi tasowa musamman domin ganawa da ita .

Dan jim liman yayi yana sake nazarin Doctor Hamza , kafin yace " bawan Allah lafiya dai ko ? Ba dai wani al'amari bane marar daÉ—i ya auku da har yasa kake neman Malama Maryam ?

Da sauri Doctor Hamza ya girgiza kai kafin yace ' ah ah ba wani abu bane marar kyau , kawai tambayoyi nake so nayi mata akan wata É—alibar ta da ta koyar wacce aka ce daga baya ta zama kamar 'yar ta saboda kusanci da ta samu da ita , sunan yarinyar Amina .

Shiru Liman ya sake yi kafin yace 'Kana nufin Amina Mustapha Dilmari yarinya 'yar Maiduguri ?

" ita fa Malam .

"Allah sarki yarinyar kirki ce ai Amina , ta koma can garin su a halin yanzu har an aurar da ita sati biyu da suka wuce , Malama Maryam da kake nema ai Mata ta ce , kuma ita ce Malamar Amina tsawon shekaru Shida da suka yi tare , bari na shiga gida sai nayi mata bayani na haÉ—a ku , amma kafin nan zan so jin ko kai wane ne ? Kuma daga ina kake ?

Cike da jin daɗin ganin sauƙaƙuwar lamura Doctor Hamza yace " Malam ai ni ne Mijin Amina bayan haka kuma ni wan ta ne da muke 'ya'yan mata biyu .

" Masha Allah ka ce babban baƙo ne da mu , to Bismillah mana mu shiga daga cikin Falona kafin na yi mata magana .

Ganawar Doctor Hamza tare da Malama Maryam ya zo masa da wani irin sauyi mai girma da yake sauraren bayanan da take yi  masa game da baki ɗayan rayuwar da Yakaka tayi tare da ita har ma da wanda tayi gidan uwarɗakin ta samy baby da a farko su kayi zaton yayar ta ce , kafin daga baya lokacin da ta faɗa musu haƙiƙanin gaskiyar kome game da ita ,su gane cewa basu da wata alaƙa ta 'yan uwantaka .

" alaƙar ta da Samy Baby da duk irin Yaudarar da tayi mata . har yadda daga baya Samy baby take son tilasta ta shiga harkar banza amma ta ƙi yarda da hakan shine ya kawo sanadin komawar ta Maiduguri .

Nisawa Malama Maryam tayi tana murmushi ta cigaba da cewa " Abu mafi daÉ—i da yasa nake yin Alfahari da Amina shine jajircewar ta wajen neman ilmin addini fiye da na boko , Amina ta fara karatun addini bata kai ga sanin ayoyi bakwai na Suratul-Fatiha ba amma sai ga shi cikin shekaru shidda da Yarjewar Allah ta samu cikakkiyar kyakkyawar Haddar izif talatin .

" bata san yadda ake yin cikakkiyar Alwala ba a shekaru shidda baya a yanzu Amina daga kan farillai , sunnoni da mustahabbai har makruhi na alwala ta sani , haka kuma sharuɗɗan Sallar ta sun inganta ta kuma san yadda zata yi gyara ga Sallar ta idan ta ɓaci.

" Amina ta san baƙi , ta iya karatu da rubutun Arabic ta kuma samu tarin ilmi daga littatafan addini da hadisai masu inganci dan haka ta san dukkanin haƙoƙin Ubangiji dake kan ta .

" Alhamdulillah shine kawai abunda zance da Allah ya rataya min nawin tallafa mata ta hanyar samu ilmin addini , ya kuma bani ikon koyarda ita tare da ni da sauran Malaman da ta É—au ilmi a wajen su , nagodewa Allah da kafin barin ta wajena ta fita daga duhun jahilci .

"Halaye da É—abi'un Amina mafi rinjayen su masu kyau ne ababen koyi , tundaga lokacin da tasan irin tarin zunubin da yake cikin kuskuren da tayi na baya bata sake kwatanta aikata makamancin sa ba , tayi kyakkyawan tuba da irin sa ake son duk wani mumuni ya yi .

" babu shakka kayi sa'ar Mata , Allah ya ɗorar da zaman lafiya a tsakanin ku, a ƙarshe shawarata shine kayi ƙoƙarin ganin ta samu cigaban karatun ta na addini kamar yadda ta ke fata a koyaushe watarana ta haddace Alkur'ani Mai girma Dan Allah ka bata dama ka taya ta wajen samun cikar burin ta irin Amina sune Al'umma suke amfana da su .

" Ya Rabb lakal-Hamdu ,  Alhamdulillah , Masha Allah .

Doctor Hamza yake furta haka fuskar sa É—auke da wani irin annuri na farin-ciki , har wani irin zillo yake ji zuciyar sa na yi masa .

fuskar sa ɗauke da faffaɗan murmushi ya miƙawa Malam Idris ( Mijin Malama Maryam ) Hannu suka yi musabaha , lokacin da yake miƙewa da shirin tafiya , bakin sa ɗauke da duk wasu kalmomin da ake iya amfani da su wajen godiya ga mutumin da ya kai maƙura wajen yi maka Alkhairi .

Da farin-ciki su ma suke amsa masa suna masa rakiya , fitowar su tsakar gida ya zira hannuwansa duk biyu a Aljihu , kuɗaɗen ciki da bai ƙirga su ba su ya tattaro baki ɗaya ya danƙawa Sadiq da yake tsaye a gefe cike da ladabi ya sanya hannu biyu ya amsa yana godiya .

Sun rabu cikin mutunta juna ya jaa motar sa yana barin unguwar , daga cikin zuciyar sa yake jin ɗaguwar wani abu mai kama da nannauyan dutse da ya danne masa zuciya ya taƙaita masa walwalar sa shekara da shekaru ,

ji yake kamar an tsamo sa daga cikin wani zuzzurfan ramin da ya faɗa a ciki , yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a ciki ba soyayya mahaɗi ce ta rayuwar kowanne ɗan Adam wanda da zarar an samu tangarɗa ta bangaren ta sai rayuwa ta zama kamar lami babu armashi a cikin ta .

Tuƙin da yake yi yaji yana neman gagarar sa zuciyar sa na neman abokin taya ta murnar da 'yancin da ta samu , dan haka ya gangara gefen titi ya tsaya , jingina kansa yayi da jikin kujerar motar bai ankara ba ya tsinci kansa da yin murmushi lokacin da ya ji wani ruwa-ruwa na taruwa a gurbin idanun sa ( ƙwallar farin-ciki ) shi kaɗai kawai yake ta murmusawa wanda bai san shi ba wanan lokacin zai zaci mutsa-mutsai ne suka hau kan sa .

" Alhamdulillah ,yace yana kai hannu kan wayar da take ajiye a gefen sa ya ɗauka laluben wanda zai ƙira a dai-dai lokacin yake yi ,

Doctor Suleiman shine wanda ya fara faɗo masa arai domin ya raba farin-cikin sa da shi, saboda sanadin sa ya samu kubta daga ramin da zargi ya haƙa masa a zuci ya faɗa .

sai dai tunowa da ya yi da alaƙar da ta taɓa giftawa a tsakanin sa da Yakaka ya sa shi fasa ƙiran sa , daga ƙasan ran sa yake jin tasowar kishin son da Suleiman ya taɓa yiwa Yakaka .

Ajiyar zuciya yayi yana jin yadda zuciyar sa ke bijiro masa da wacce tafi dacewa da ya ƙira a lokacin .

Tunowa yayi da ba shi da number ta , ba ma shi da tabbacin ko tana da waya,ko babu , shiru yayi jim ! Yana tunanin ina zai samu layin ta ? Yana jin nawin Amnee da Khaalty Rahima ba zai iya tambayar su ba .

Rahima ƙarama ita ce ta faɗo masa , yasan muddin dai tana da waya zai samu layin ta wajen Rahima '

Yana ƙiran ta kuwa ta ɗaga , bayan sun gaisa ya ɗan yi gyaran murya kafin yace " Rahima kina da number Mata ta kuwa ?

ÆŠan shiru Rahima tayi kafin tace " eh Big bro ina da number Auntie Sofiya...

" Ba sofiya nake nufi ba Number My Pure Woman nake nema ai tana da waya ko ?

Murmushi Rahima tayi lokacin da ta fahimci wacce yake nufi amma dan ta sake tabbatarwa sai tace " number Yakaka ko Big Bro ?

"Yakaka ba suna bane ku daina ƙiran ta da wanan sunan ku dai samar mata da wani sunan da ya dace da ita mai daɗin saurare idan ba za'a ƙira ta da Aminah ba. Ya zarce da cewa "ki turo min da Number ta yanzu . bai saurari dariyar da take yi ƙasa-ƙasa ba ya sauƙe wayar sa .

Ba'a cika mintuna biyu ba Rahima ta turo number , cikin zumuɗi ya danna ƙiran yana fatan Allah yasa ta ɗaga da sauri .

Yakaka wacce tunda ta ji irin zagin da Sofiya ta biyo ta da shi , ta tsorata jikin ta kuma yayi sanyi lakwas daga haka tana iya hango kusancin da suke da shi da Matar sa tunda har tana iya ɗaga wayar sa idan an ƙira , wani sashi na zuciyar ta ma raɗa mata yake cewa duk a gaban sa sofiya ta ƙira ta da Akuya .

Hawaye ta ji yana neman zubo mata , ita kam wannan auren nata bata hango jin daÉ—in sa ba .

Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin,  ta sauƙa ƙasa inda ta tarar Amnee na yiwa Falmata ƙunshi a ƙafafun ta da ƴan yatsu zama tayi tana taya Amnee gyarawa Falmata tsaruwar layin ƙunshin , fuskar ta babu walwala sosai tace " Falmata naso raka ki har ɗakin ki , na mayar da ke saboda ni nayi sanadin tahowar ki , amma ban samu dama ba Yaa Dakta bai barni ba , amma insha Allah idan kin haihu zan je kin ji ko ?

Gyaɗa kai Falmata tayi da ɗan murmushi tace " Yakaka ai daman nasan Yaa Dakta ba zai yarda ba  Amaryar sa ta kama hanyar ƙasar Niger rairayin ƙasa ya turbuɗe masa ke ..

" ki min shiru , Yakaka ta katse ta tana 'yar hararar ta tare da satar kallon Amnee wacce tayi kamar bata jin me suke cewa ,

Dafe baki Falmata tayi kafin tace "to nayi shiruna Allah ya kai mu.

Daga haka tayi shiru daga ƙasan ran ta tana ji rashin daɗi da bata samu rakiyar Yakaka ba saboda duk guri idan har da Yakaka tana jin wata irin kariya ta musamman daga jiki har ruhin ta .

Bayan Yakaka ta idar da Sallar azahar tana zaune akan sallayar wayar ta ta fara ƙidan shigowar ƙira .

Da sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wayar zuciyar ta na ƙirgo mata waɗanda zasu iya ƙiran ta a dai-dai lokacin , number da ta gani ta sa bugun zuciyar ta sauyawa, take zuciyar ta ta bijiro mata da tambayar "me kuma Sofiya ta ƙira ta sake cewa ? Ko cin mutuncin da tayi mata ne bai ishe ta ba ?

Har wayar ta tsinke bata ɗaga ba , a take kuma aka sake ƙira , tsoron ta ya sake ninkuwa da ta tuno ko dai shine yake ƙiran nata ? Kar kuma tayi laifi idan taƙi ɗagawa Dan haka kafin wayar ta kai ga katsewa sai ta ɗaga ƙiran a ɗan tsorace ta kara wayar a kunnen ta tayi shiru .

Doctor Hamza da ya ƙagauta da ya ji muryar ta ya saita sautin sa ƙasa kaɗan kafin yace " Hello Wafaa , ya kike ?

Shiru Yakaka tayi tana son daidaita nutsuwar ta dan ita gaba É—aya ma a gigice take da jin muryar sa dan haka sai tace " Salamu Alaikum Yaya Dakta , ba Wafaa bace ba ni ce .

Shiru ta ji yayi kamar baya kan wayar É—an dubawa tayi ta ga yana nan akan layin tsoron kar ya kashe wayar ba tare da ta faÉ—a masa abunda take son cewa ba yasa ta cigaba da cewa " Daman ina so ne Dan Allah.....

" Shiiit ki tsaya mu gaisa Wafaa , ko haka ake gaishe da Masoyi?

Saƙato Yakaka tayi da wayar tana jin mamakin sa a take tayi tunanin ko dai bacci yake yana mafarki da wata can wai wafaa ?

Dan haka cikin sanyin murya ta sake cewa "Yaa Dakta ni ce fa ?

Dariyar da take taso masa ya danne yana sake ƙasa da murya yace "  ke ce wa?

Kamar zata fashe da kuka tace " Ni ce fa Yakaka yayar Falmata .

Murmushi yayi yana rufe idanun sa cikin ran sa cewa yake " tana son sunan nan tana kuma son ƙanwar ta .

" sunan ki ba Yakaka ba , sunan ki Amina kin ji ko wafaa ?

Shiru tayi , tana son haɗa kalmar da za ta faɗa a lokacin fahimta da tayi zuwa yanzu ya gane ta kawai walaƙanci ne ya sa shi ƙiran ta da wata wai wafaa , ɓata rai tayi kamar yana ganin ta tace
. "Ni dai daman iznin raka Falmata Niger nake nema a wajen ka ? 'Yan uwan mijin ta sun zo zasu koma da ita shine zan raka ta .

Wani irin bugu zuciyar sa ta shiga yi kamar tana gaban sa ya tattare girar idanunsa cikin muryar sa da bata cika ƙarfi ba yace " Wafaa me kike son cewa ?  Da auren nawa akan ki za ki tafi har Niger ? Ki je ki ga wannan ɗan....

Shiru yayi yana son dawo da nutsuwar sa da kishi yake neman raba shi da shi nan take , da wani irin sauti yace " baza ki tafi ba kina jina ko ?

A tsorace tace " ina ji .
. "Good .
yace kafin ya kashe wayar sa .

Wani irin zafi yake ji a zuciyar sa kan cewa da tayi zata je Niger garin su wannan É—an iskan sojan har cikin gidan sa kuma ?

Alhalin da yau yana da iko bayan duk labarin da Malama Maryam ta sanar masa har auren sa da Falmata a halin yanzu ko Fatima ba zata sake kwana da igiyar auren sa ba , tunani ma ya dunga yi kan me yasa Baa ya ba shi auren Fatima ? Alhalin shi É—in bai can-canta ba .

Ko ma meye shi dai zai killace matar sa daga yin duk wata mu'amala da shi ko dangin sa duk kuwa da cewa yana auren ƙanwar ta ba zai jura ba ya ga ko da kalmar gaisuwa ta sake shiga tsakanin su.( anya kuwa likita ayi haka ?? )

Bai bari maganar da ta faɗa ta ɓata masa farin-cikin sa ba saboda zuwa yanzu yasan wacece haƙiƙanin ta , mace ce mai kyautayi da son kyautatawa mai saurin yarda da yawan sadauƙarwa halinta kenan halittar ta ce shiyasa ya raɗa mata suna ( Wafaa ).

Abun da ya ɗan so tayar masa da hankali bai wuce rashin sanin matsayin sa ba a wajen ta ? sai dai ya yarda da kan sa shi ai Namiji ne zai iya sauya ta zuwa yadda yake so ya koyar da zuciyar ta ƙaunar sa da hakan shi zai samar da nishaɗi a zaman su tare da taimakon sassanyar zuciyar ta mai cike da tausayi da jin ƙai .

Tayar da motar sa yayi yana nufar gida cikin ran sa cike da ƙudirin zuwa Maiduguri a ƙarshen sati mai zuwa ya fara kafa gwamnatin sa tun yanzu kafin nan da ƙanƙanin lokaci da zai dauƙe ta ta dawo kusan sa .

Har zuwa lokacin da ya koma gidan ya tarar da Sofiya yadda ya bar ta , sai daÉ—uwar damuwa da tashin hankalin da yake iya gani akan koÉ—aÉ—É—iyar fuskar ta

Kamar wacce take jiran sa yana zama ta zo ta zauna a ƙafafun sa tana kaɗa ido tace " Doctor na har ka dawo ? .

"Har na dawo Sofi ta daman ai na faÉ—a miki ba zan daÉ—e ba .

Murmushi tayi tana raɓa kan ta a kafadar sa ta cigaba da cewa " Doctor na bayan fitar ka na yi mana wani tunani , akan yarinyar nan ƙanwar mu Yakaka take ko wa ? 

Bata tsaya ba ta cigaba da cewa " me zai hana ta dawo nan gidan ta zauna a ɗakin nan na 'yan aiki kafin a samu wajen da za'a wurga ta tunda kaga fa irin halin ta na cuɗanya da maza ta riga ta saba da 'yan taɓe-taɓe da tsotse-tsotse da kwakule.....

" kin ga bana son shirita ki faÉ—a min magana kai tsaye kawai .

Ya furta hakan a taƙaice fuskar sa na bayyana wani yanayi na daban saɓanin wanda ya shigo da shi '

Ajiyar zuciya tayi shirin da suka haɗa ita da Samy baby yana mata yawo a zuci , sannan makirar zuciyar ta na cigaba da mata huɗhuba tace " ina nufin tunda Yarinyar nan kowa dai ya riga yasan irin rayuwar da take yi kafin a laƙaba maka auren ta dan haka na ga gara ka dawo da ita nan kana lura da ita dan saboda kar ta cigaba da yin ''yan harkokin ta tunda dai mai hali bai fasawa daga haka kuma ta kwaso mana ƙajaga ta shafa mana ko kuwa a maƙalo  baragurbin ƙwai a liƙa maka ya ƙyanƙyashe ya zamar mana bala'i a doron ƙasa ko me ka gani Doctor na ?

Shiru ta ji bayan gama bayanin ta , sai ta É—ago kanta a hankali ta É—aura ganin ta kan fuskar sa .

Yanayin da ta hango akan fuskar sa ya tsinka mata zuciya ta ɗan yi yaƙe sanan ta ce "Docto....

Da hannu ya dakatar da ita wani irin murmushi yake da ya mata wuyar fassara yace , " Sofi kin yi tunani mai kyau , wanda na riga ki yin makamancin sa .
. Ya É—an yi shiru yana kallon yadda faffaÉ—an murmushi ya cinye fiye da rabin fuskar ta , ya cigaba da cewa

" Fitar da nayi a ɗazu gidan da tayi rayuwa tsawon shekarun da tayi bata gida nan naje , kuma Alhamdulillah Amina ta samu shaida saɓanin wanda ni da ke da wasu tsirarun mutane wataƙila ka iya hasashe , Amina ba rayuwar banza tayi ba , asalima yaudarar ta aka yi aka taho da ita Abuja .

" babu wata hujja ɗaya da zata sa a cigaba da yi mata kallon wacce tayi yawon banza, da ya wuce mummunar ƙaddarar da ta faɗa mata da kuma Allah ya iyakance mata shi , dan haka ina so daga yau ke ma ki cire wannan zargin daga ran ki Wafaa nitsattsiyar mace ce wacce ta tafi neman ilmi kuma ta samu dai-dai gwargwado da fatan kin gane ?

Ya ƙarasa zancen yana kallon cikin idanun ta da suka yi wani irin mitsi-mitsi tana kallon sa , bai jira amsar ta ba ya cigaba da cewa
"Amma duk da haka na karɓi shawarar da kika kawo na dawo da ita kusa da mu dan haka ina ga ranar juma'ah zan tafi Maidugurin sai kawai mu zo tare amma ba a ɗakin 'yan aiki zata zauna ba ɗakin 'yan aiki na 'yan aiki ne ita kuma Mata ta ce dan haka zata zauna a ɗakina kafin na samu gida nan kusa da .....

Zuruf! Sofi ta miƙe daga kan ƙafafun sa jikinta har mazari yake ta fara cewa.

" wallahi Hamza baka isa ba , baka isa ka mayar da ni wata wacce bata san kanta ba , dan ka je an faɗa maka ƙarya da gaskiya shine zaka hau kai ka zauna ba bincike ba kome ni nan na san har gidan da tayi rayuwa a ciki tana sheƙe ayar ta a 'yan iskan samarin garin Abuja kaf ɗaya-ɗaya ne basu kwana da ita ba dan haka wallahi ba zan yadda ina zaman-zamana a kwaso min ciwo a yarɓa min ba sai dai ka zaɓa wallahi ko ni ko ita .

Da sauri ta juya har tana tuntuɓe kome yana shirin kwaɓe mata dole ta yi yunƙurin ɗaukar mataki mafi tsauri da zai kawo mata ƙarshen kome

****

Mutanen Maraɗi sun juya tare da Falmata da Hajja a ƙarƙaahin rakiyar Amnee da zainab  wadanda kwana biyu kawai zasu yi su wuce Chad Amnee zata je yiwa dangin su na can gaisuwar bangajiyar biki tare da godiyar hidindimun da suka yi musu..

Sun samu tarɓa mai kyau daya shafi wajen kwana tare da cimaka masu kyau da kuma tarin girmamawa daga bayu da hadiman gidan sarauta.

Daga Hajiya Umma kuwa babu yabo ba fallasa tun zuwan su sau uku kaÉ—ai ta zauna da su waje É—aya. Ranar farkon zuwan su da kuma washegarin zuwan su da suka je gaishe da Maimartaba sai kuma yau da suke yi mata Bankwana

nan ma kadaran-kadahan suka gaisa Amnee ta É—anka mata amanar Falmata , tana sake jaddawa akan a yi kiwon ta saboda yarintar ta kada a bar ta da kankin kanta .

Amsar da Hajiya Umma ta bayar ya sanyayawa Amnee jiki domin kuwa cewa tayi " ÆŠa ai na kouwa ne itta kouwa É—abi'a ta mai itta ce hali kuma shi ke samar da gurbi .

" Babu Shakka.

Amnee ta amsa mata .

Tafiyar su ta karya zuciyar Falmata yadda bata zata ba , ta dunga kuka tana hangowa kanta rayuwar da zata yi a cikin wannan makeken gidan alhalin shi wanda take zaune domin sa bai ma san da zuwan nata ba.

Tun bayan tafiyar su sai Falmata ta zama shiru koyaushe tana cikin babban É—akin da aka mallaka musu ita da Hajja , wanda yake cikin falo na farko a shiyar , abunda ke fitar da ita gaishe da Hajiya Umma da suke zuwa yi kullum safe ita da Hajja daga sun dawo bata kuma fita sai kuma wata safiyar ,

Bayi biyu da aka ware mata su ke hidimar abincin ta tare da kula da tsaftar É—akin da take , babu abunda take daga zama sai kwanciya , baki É—ayan rayuwar bata mata daÉ—i ga zaton ta idan sun iso zata samu ko da damar da zata dunga yin waya da Biyamuradi Youssouf sai ta tarar da rayuwar masarautar ba yadda ta saba ba , kowa a cikin gidan bisa umarnin na sama da shi yake aiwatar da lamura .

Duk yadda Siyama da Aicha suka so su dunga jaan ta fira zuwa falo taƙi yarda ,dan haka suka ƙyale ta lokaci-lokaci Siyama kan shiga ɗakin su gaisa sannan su ɗan taɓa hira saboda gidan sarauta suke kome kake idanu na kan ka zai iya zama abun magana ko ma gorantawa ace kullum ita ke zaryar shiga wajen Falmata a matsayin ta na kishiyar ta .

ita kuwa Aicha daman bata cika zaman gidan ba saboda tana shirin kammala karatun ta , dan haka Falmata kaÉ—aici ya mata yawa .

har gara Hajja da daman ita bata É—au zaman É—akin ba ficewar ta take can shiyar Bayin gidan su sha hirar su duk da cewa ba wai aiki take yi ba .

Yau tun safe ta tashi da ciwon baya da ƙafafu saboda cikin kwanaki biyun abunda ke cikin ya fara mata nawi ga yawan motsi da yake yi dan haka sai ta gagara ko da zuwa gaishe da Hajiya Umma kamar yadda ta saba tayi kwance lamo tana jin yadda abunda ke cikin ta ya cure gefe ɗaya.

Hajja ita É—aya ta tafi gaishe da Hajiya Umma ita ma ba wani sakar mata fuska Gimbiyar take yi ba "ah to Hajiya Umma ce fa É—iyar Saraki matar Sarki ?

Hajja ta so ta sanar da Hajiya Umma rashin jin daÉ—in da Falmata take fama da shi a yau sai dai yadda tayi wofintar da ita ya sa ta gaza shigar da batun Falmatan, ta ga sai umarni take bayarwa ga bayu ga Alama dai wani shiri na musamman ake yi yau a gidan .

Dan haka sai Hajja ta miƙe jiki a sanyaye ƙasa-ƙasa tace "bana iya ba wannan gurfanon ya na me neman gafara ni ba lafiyar ƙafa na cika ba , a ƙare ƙalau wannan bautar mai ciwo ? ai ni ba sayo ni aka yi ba dan haka ba baiwa bace da za'a isheni da wani ƙaburi, duk na gundura da zaman gidan nan  Babban Soja Allah ya baka lafiya mu samu mu koma gidan mu inda muke a sake ba wata takura .

Bata koma É—akin ba sai ta fita can inda ta saba hira cikin bayu amma yau sai bata same su sun yi sansanin hira ba kamar yadda suka saba , sai shiga da fita kowaccen su take yi akan aiyukan su hankalin su bai kan ta.

Ɗan zaman mintoci tayi ta miƙe domin komawa ciki kan hanyar ta suka ci karo da Babbar baiwar da take kula da shiyar abincin gidan wanda a shekaru aƙalla zasu yi sa'o'in juna bayan sun gaisa har Hajja ta gota sai Tabawa ta dawo da baya tayi ƙasa-ƙasa da murya tana ɗan leƙen baya tace " Hajja Hauwa da fatan dai kin taya Uwargiyar ki shiri ? Dan Kin kouwa san ɗiyan yanzu ba irin mu bane masu duƙufawa bauta ga Miji .

A É—an jahilce Hajja tace "Shirin me fa Tabawa ?

Kama haɓa tabawa tayi tana ɗan karkata kai tace "kada dai kice min Uwargijar ki Gimbiya batta da sanin Yarima na daf da shigowa Masarauta ba ? dan kouwa a halin yanzu ma suna Niamey zuwa yammaci kouwa suke shigowa nan .

Da hannu biyu Hajja ta dafe ƙirji muryar ta na bayyana mamakin ta tace  " Dan Allah fa Tabawa?

A mamakance ta cigaba da cewa "yo ina kuwa muka sani muna zaune bonono , ai tsayuwa bata ganni ba dole na yi hanzarin komawa ciki, ke dai tabawa nagode miki.

A zaune ta tarar da Falmata tana mammatsa yatsun ƙafafun ta da suke mata tsiko , ba tare da ta ɗago kai ba ta amsa Sallamar Hajja wacce ita ma kai tsaye ta zarce banɗaki ,bata tsaya yi mata dogon bayani ba  .

ruwa mai zafi ta tarawa Falmata ta tuttula duk turarurrukan wanka da ta tarar da su a guri na musamman a jere da wasu ma ƙila ba na wanka bane ita dai Hajja ta zuba ƙamshi gum kuma ya cika banɗakin ya ratsa har waje .

"Fatima tashi ki je kiyi wanka maza-maza zama bai gan ki ba 'yar nan .
Hajja tace haka lokacin da take dawowa cikin É—akin

Falmata da ta riga ta saba da subaɗaɗin Hajja ta ɗan dubi Hajjan tana komawa ta kishingiɗa a ƙasa tace "Hajja duk yaushe nayi wanka da safe ? Sannan kuma wanka da tsakar ranan nan ƙarfe ɗaya saura Hajja lafiya dai ko ?

" lafiya lau sai Alheri 'yar nan domin kuwa yau UbanÉ—akina ke dawowa Babban soja Baban Mama yau amaryar ki kike uwarÉ—akina wankan taryar miji za kiyi .

"Da gaske Hajja ?

. Falmata ta tambayeta tana miƙewa  zaune fuskar ta ɗauke da yanayin da tashi ɗaya ba'a ba shi matsayi ba .

bata jira Hajja ta bata amsa ba ta cigaba da cewa " Amma kuma ba wanda ya faÉ—a mana ko Maman Yumna ma bata faÉ—a min ba anya Hajja da gaske ne ? wa ya faÉ—a miki ?

. " mts , ahaf ai ga irinta nan ke wa ya faɗa miki kishiya tana zama abar dogaro ɗari cikin ɗari ? Wa yace miki ana bada amanna da Amana baki ɗaya ga kishiya ? Ni daman daga ganin yadda take miki nan-nan nasan tsagoron kissa ce da kilbasa ai kin ga ga shi da tasamu labarin dawowar mijin ku ɗif ta ɗauke ƙafa tana can ta duƙufa shirya kan ta , ta bar ki baki sake ,

"Yanzu kiyi maza ki tashi ki gyagiije dan waɗannan ƙananun muri-mirin kowacce mai ciki sai tana yin su basu isa hana kome ba ai ciki ba cuta bace , kiyi azamar yin wankan ki fesa ado irin na shiga gasa ki tafi gaida Mahaifiyar sa daga nan ki zauna a falon ciki wajen ta , ta yadda daga ya sanyo kai falon zai gan ki tunda kuwa dai daga ya iso gidan gaishe da ita shine abu na biyu da zai yi bayan gaishe da Mahaifinsa , kin ga ita Siyamar take ko wa ? Da take miki ƙafar ungulu kin riga ta ganin sa , tashi maza uwarɗakina ba'a bori da sanyin jiki ...

"Hajja ni dan Allah ki rabu da ni , kina ganin dai yadda koyaushe muka je gaishe ta ɓata rai take yi dakyar take ansawa sannan .....

Kafin ta ƙarasa Hajja ta katse ta "banda abun ki uwarɗakina faɗan da ya fi ƙarfin ka ai mayar da shi wasa kake , idan ta amsa yau da kyar watarana da fara'a zata tare ku ke da 'yan jikokin ta kiyi haƙuri kin ji  inda ba'a son ka anan arziƙin ka yake ke dai gwada mata ɗa'a sai ki ribaceta da kyawawan ɗabi'u kin san su saraki ne sai ana musu bangirma kin jii ko?  .

Turo baki Falmata tayi da cigaba da cewa "  sannan Hajja shi ma ɗin ai bai ma san mun zo ba tunda kin ga fa bai taɓa neman mu ba gaskiya ni ba zan kai kaina wajen sa ba idan shi ya zo shikenan idan bai zo ba ma ni.....

Wannan karon a hasale Hajja tace "to ai shikenan zauna kiyi ta jiran sa anan shi da yayi yi jinyar ya zo ya gaishe ki Iya-gwamma , tunda ni dai ba ki É—aukeni bakin kome ba a zaman mu ban isa baki shawara ba ai shikenan .
Daga haka tayi ficewar ta

Bayan fitar Hajja a ɗakin sai duk jikinta yayi sanyi , tunda take da Hajja bata taɓa ganin tayi fushi ya haka ba duk sai ta ji ba daɗi dan haka ta miƙe a hankali ta shiga banɗakin

Bayan fitowar ta da daga banÉ—akin da ta kwashi wajen mintoci talatin a ciki tana wanka.

jikinta ba kuzari ta zauna a kujerar gaban gadon , har yanzu Hajja bata shigo ɗakin ba , tunanin da yake nuƙurƙusar ta sake yawaita yake yi

"da gaske yau yake dawowa amma bai neme ta ba ? Tun rabuwar su har yau bai taɓa jin kewar ta ba kenan ? Shiyasa bai neme ta ba , tunda Aicha tace suna yin magana a waya kuma ko bayan dawowar su maradi rannan da kunnen ta taji suna waya da Aicha , kenan ita ce bai nema saboda baya buƙatar ta ko me ?  to meyasa ita kuwa zata damu kan ta da tunanin sa ? Har Hajja zata matsa tayi wani shiri na musamman a domin taryar sa .

Har ruwan jikinta ya bushe bata shafa Mai ba , agogon ɗakin ta duba ƙarfe biyu har da kusan rabi dan haka ta miƙe ta sake komawa banɗakin tayi Alwala ta zo tayi Sallar azahar bayan ta idar bata miƙe akan sallayar ba ta cigaba da zama akai tana istigfar lokaci-lokaci tana murza idanun ta da suke mata mil-mil tunda tayi wanka da alama sabulan da tayi amfani da su wajen wankan sunfi ƙarfin lafiyar idanun ta .

Tana zaune har aka ƙira la'asar bata jinkirta ba tayi Sallar kawo lokacin rashin jin motsin Hajja ya fara damun ta dan haka ta miƙe ta buɗe Babbar wardrobe bango guda da aka zube mata suturunta ciki ta dauko wata doguwar baƙar riga ta sanya a jikin ta ba tare da ta shafa ko hoda ba sai ɗan mai da ta mutsiƙa a fatar ta .

Dawowa gaban Babban mudubin tayi ta tsaya tana duban kan ta cikin ta da ya É—an tasa ya bayyana a sarari ta cikin rigar ta tsirawa ido.
"Kunyar fita a haka ana gane mata cikin ya kamata ta .
"Mts shi cikin nan ma duk ya bi ya hana mutum sakewa .
tayi mitar haka lokacin da take cire rigar jikin ta ta zaro wata doguwar riga har lau launin ruwan zuma mai duhu da ya ɗan sirka da zane a tsai-tsaye launin farar ƙasa , rigar faffaɗa ce da take da rufaffen wuya sannan tana da ɗan nawi kaɗan a can Rochester ta taho da ita ,

lokacin da ta Sanya a jikinta ita da kan ta sai da ta ɗan murmusa saboda yadda rigar ta amshi zubin jikinta na dirarriyar mace mai matsakaicin tsawo da 'yar ƙiba kaɗan sai cikin nata ya ɓuya a rigar

Rigar bata da mayafi dan haka ta ɗau wani babban mayafi launin farar ƙasa da aka masa adon duwatsu ta yafa akan ta ya rufe mata jiki kirif , har zata matsa daga gaban mudubin idanun ta suka kai kan 'yan kunnayen ta da tunda ta taho da su daga Maiduguri ta cire su ta ajiye ana,  su ta kai hannu ta ɗauka 'yan gajeru ne ta maƙala su a kunnuwan ta a hankali ta sanya ɗan yatsa ta lakaci mai ta shafe siraran labbanta marasa tudu .

Takalmanta masu kama da silifa 'yan madina amma wannan daga Rochaster ta zo da su su ta zira a ƙafar ta ta fito bayan ta shafe jikinta da Humra da kamshin ta ke tashi kaɗan-kaɗan .

Boyayyar ajiyar zuciya tayi lokacin da ta fito falon ta ga Hajja zaune daga gefe da alama Salla ta idar .

Da fara'ar jin daÉ—in ganin ta ta matsa kusa da ita kafin tace " Hajjata anan kike ?

ÆŠan waigowa Hajja tayi kamar bata san da fitowar ta ba tace " uhm anan nake .

" to sannu da hutawa Hajja nima yanzu na gama shirin zan shiga na gaishe su yadda kika ce .

. Wannan karon Hajja ta ɗan saki fuska jin Falmatan tace zata yi yadda ta sa ta dan haka ta ce " to Madalla ko kefe fa uwarɗakina ? Maza je ciki ki zauna idan son samu ne ma ki samu wajen da yake fuskantar ƙofar shigowa ki zauna kin ji ko ?

. " to Hajja
Falmata ta amsa cikin ran ta tana gujewa rigimar Hajja ne amma idan ba haka ba ita ba wani niyyar zama tayi ba .

Da kallo Hajja ta bi bayan ta cikin ran ta kakkabin wannan rigar ta Falmata take yi taɓe baki tayi kafin a fili tace " ana yi yafi ba'a yi tsarkin mahaukaciya da kunu , idan ba haka ba wannan riga da kika sako ai bata da maraba da buhu .

A ɗarare Falmata tayi sallama a bakin  falon da daga inda take tana jin tashin hayaniya da dararrakin mutane da alama akwai wasu baƙi masu ɗan yawa a ciki .

Ɗan jim tayi jin babu wanda ya amsa mata duk kuwa da tasan ana jin ta,  sake sallamar tayi a karo na uku sannan ta tsinkayo muryar wata daga ciki ta amsa , dan haka ta sanya ƙafafun ta ciki a hankali  .

Da ɗai-ɗaya suke mayar da hankalin su kan ta tana tahowa har ta ƙarasa daga gefe kaɗan tayi ɗan gurfano tana gaishe da Hajiya Umma wacce tunda ta shigo ta rage fara'ar da take yi , kamar yadda ta saba amsa mata gaisuwar ba wata kulawa haka yanzun ma ta amsa tana janye ganin ta daga kan ta zuwa gefe kafin ta yunƙura  tana barin wajen baki ɗaya zuwa wata ƙofa daban .

A hankali ta waiga tana É—an kallon sauran matan da suke wajen biyu daga cikin su kawai ta gane "Ubbo da Ammi sauran mata ukun bata gane su ba amma dai suna mata yanayi da su Ubbo , cikin nutsuwa ta gaishe su a kunnen ta Ammi ce kaÉ—ai ta amsa da mutunci sauran matan sama-sama suka amsa ita kuwa Ubbo ko amsawar ma bata yi ba .

Fitowar Siyama daga ɗakin Umma yasa ta ɗago kan ta " sœurs wannan fa ? Kamar ya fi zama a jikina kou ?
Ta ƙarasa zancen tana ɗan yin juyi cikin dakakiyar Shadda "Boo" da ta sha aiki aka mata ɗinkin doguwar riga , nan take wajen ya ɗau ƙaramar sowa suna yaba kyaun da tayi .

cike da burgewa Falmata take kallon ta tana murmushi sosai ta yi mata kyau kwalliyar ta kuma ta ƙayatar da ita .

" kin yi kyau Maman Yumna , muryar Falmata ta ratsa wajen .

Da sauri Siyama ta waiga inda ta ji tashin muryar ta da farkon fitowar ta wajen bata lura da wanzuwar ta ba .

Tana murmushi ta ƙarasa kusan ta kafin tace " Fatima nagoude sosai, yaushe kika shigo ?
"Yanzu na zo . Ta amsa mata a taƙaice
Murmushi tayi kafin ta ɗan yi ƙasa da murya yadda Falmatan ce kaɗai zata iya ji tace " Yau Yarima Biyamuradi ke dawowa , da fatan kin masa shiri ?

Da yanayin ta na rashin magana sosai falmata ta girgiza kan ta kawai tana janye ganin ta daga kan Siyama ta sunkui da kan ta ƙasa duk jin ta take a takure sakamakon  kallon ƙasƙancin da ta lura matan wajen na jifan ta da shi .

Muryar Ubbo ta ratso wajen da take cewa " Siyama kiyi maza ki shirya mana kin tsaya inda bai dace ba , kin san fa Mijin ki na daf da shigowa , kin kuma san ke tauraruwa ce  ba tururuwa ba , ke tauraruwa mai hasken alkhairi ce ba tauraruwa mai wutsiya ba .

Cikin sanyin jiki Siyama ta juya fuskar ta ɗauke da yalwatatcen murmushin jin ɗadin yabo mai kama da ƙirari da Ubbo tayi mata sai dai gefe guda tana jin wani iri da shaguɓen da ta lura Ubbo ta yiwa kishiyoyin ta .

Har tayi taku biyu ta waigo Falmata wacce kanta ke sunkui har lokacin ba tare da ta iya haƙaƙe halin da take ciki ba , ta saita muryar ta sama kaɗan kafin tace " Fatima taho mu tai ki sauya kaya akwai Boo irin ta jikina da tai min yawa nasan zata iya miki dai-dai tunda kin fini ƙiba kuma launin zai amshe ki'...

" ahir É—in ki da arawa kishiya sutura solobiya hala ita batta da sutura ta ratayo wagga tsumma a jikin ta ta taho muna nan tana barin mouna tsamin gwanjo ?

. " ko da shike ba laifin ta ba nan gurin ta ƙurewa kenan , talaka daman yaushe yunwar ciki nashi ya lafa bare ya san suturar da ta amsa sunan sutura ? Bar ta cikin tsummokaran ta da shi yafi dacewa da itta ..

"s'il te plait Adda amm Dan Allah .

Da yanayi na rashin jin daɗi tare da chakuɗuwar tausayi Siyama ta juya ga Falmata lokacin da take mikewa tsaye ,  tayi saurin riƙo hannun ta tana cewa " kiyi haƙuri ƙamnata mu tai na miki le maquillage ki sauya kayan kin ji kou ?

Idanun ta cike da ƙwalla wannan karon cikin wani irin yanayi ta zame hannun ta daga riƙon da siyama ta mata , tana ƙoƙorin danne hawayen da suke neman ɓallowa tace " Nagode Maman Yumna sannan ba sai na sauya kayana ba na jikina ma masu tsarki ne kuma kyauta ce daga Mijina masoyina ,dan shi na saka dan ya gani yaji daɗi ba domin na zama tauraruwa ba ina so ya ganni da su rataye a jikina dan yasan cewa na yaba da kyautar sa .

Dan murmushi tayi kaɗan tana mayar da gani. ta kan su Ubbo daga inda take tana hango ɓacin rai akan fuskokin su da take iya gani dusu-dusu .

" Nagode sosai Maman Yumna , ta sake faÉ—in haka lokacin da take barin wajen .

Dusu-dusu take ganin hanya saboda idanunta da suke cike taf da ƙwalla ga kuma zogin da suke mata.

bata tarar da Hajja inda ta bar ta ba , tana zaton tana ɗakin su a yadda zuciyar ta take yanzu so take ta samu waje ta ɓuya tayi kuka , ciwo ke sasuƙar rarraunar zuciyar ta da daman tana kusa jiran kiris take .

Dan haka a karon farko tun zuwan su gidan ta fito ta ɗau hanya ba tare da tasan takamai-mai ina ta nufa ba bata kuma damu da bayun da suke binta da kallo har  wasun su na yin ƙus-ƙus ba so take tayi nesa da mutane ta samu maɓoyar yin kukan ta masha'in '

Can wani sashin da ta lura da ɗaukewar ƙafa ta shiyar nan ta nufa ,lokacin da ta doshi mashigar sashin tun kafin ta ƙaraso masu gadi biyu suka dakatar da ita , tambayar ta suka yi wacece ita ? Ta basu amsa da ita ce Fatima , suka ce daga ina take ? Tace daga Maiduguri Nigeria .

Juyawa suka yi gefe suna ƙus-ƙus

Cike da gundura ta juya da nufin fasa shiga ta nemi wani wajen saboda gaba ɗaya cikin gidan ne bata son komawa sai ta tsinkayo ɗaya daga cikin bayun yace " Ranki shi daɗe uwargijiyar mu afouwa muke biɗa ki maouna sassauci rashin sani ya sanya mu turjiya ga oumarnin ki baa in miki jagora ƙofa a buɗe take ga Iyalan Yarima Biyamuradi..

Sai suka buɗe mata ƙofar gidan daga inda take tana iya hango ƙawatuwar harabar gidan da shukoki masu furanni da bata ga irin su ba a kan hanyar ta ta zuwa nan , dan haka sai ta sanya ƙafar ta a hankali cikin harabar gidan ƙamshin furanni tare da na sabon fenti da wankin da aka yiwa gidan ya sanya ta lumshe ido ta fara taku tana jin yadda sanyin wajen yake ratsa ta shirun wajen yana samar mata da wata nutsuwa ta musamman sai kawai ta miƙa hanya ba tare da tasan inda zata je ba .

Bakin wasu manyan gine-gine uku ta bullo tana ƙare musu kallo gini ne mai matuƙar kyau da tsari , ta tafi a hankali kan barandar ginin da yake fuskantar ta a tsakiya ta zauna daga bakin barandar ba tare da ta damu da shirun da ya yawaita a wajen ba bare ta ji tsoro sai kunnuwan ta da suke tarwai tana jin sauƙar kukan tsintsaye .

Tana zama ta ji ƙuntatciyar zuciyar ta ta fara warwarewa lokacin da kuka mai ƙarfi ya zo mata , ta dunga tuno yadda baki ɗayan 'yan uwan Youssouf basu son ta ciki har da Mahaifiyar sa kan ta . Sannan shi ɗin ma da ake kome domin sa bai damu da ita ba a halin yanzu ma bata san matsayin ta ba a wajen sa .

A hankali ta kai rigar jikinta hancin ta ta shinshina lokacin da take tuno da kalaman Ubbo da tace duk ta cika musu waje da warin gwanjo , ita bata ji warin da rigar take yi ba sai ma ƙamshi irin na tsadaddun kayan da aka sayo su daga manyan shagunan da suka amsa sunan su da ya chakuɗu da ƙamshin humrar ta yake bada wani irin launin ƙamshi mai sanya shauƙi'

Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin ran ta tana tambayar kan ta ko sai yaushe ne su zasu huta daga gorin mutanen duniya ? Sai yaushe ne za'a fara musu kallon mutuntawa ?

Hawayen ta ta shafe da hannun ta tana jin damuwar ta tana raguwa da tayi kukan , daga gefe ta hango bakin fanfo ta yunƙura a hankali ta nufi wajen wanke fuskar ta tayi kuma ta tari ruwan da tafukan ta ta sha , ta kulle fanfon ta dawo ta zauna inda ta tashi .

Wasu kyawawan duwatsu farare kal-kal ta gani daga gefe a É—an gurin da aka killace domin yin shuke-shuke ta sa hannu a hankali ta tsinto su , ta zube su a gaban ta tana kallo cikin ran ta tana tunanin me ake yi da su kuma ?

Jingina kanta tayi da jikin barandar tana rintse idanun ta saboda iskar wajen da take jin ta mata yawa kamar tana ƙara mata ciwon idon .

Da ta rufe idon sai taji daɗi sannu kan hankali taji zaman ya fara mata ba daɗi saboda bayan ta da ya fara ƙagewa , bata damu da ta buɗe idanun ta ba da daman tafi sabawa da duhun dake cikin su.

sai ta kishingiɗa kaɗan da nufin bawa kanta hutu na wani lokaci ,  sassanyar iskar wajen haɗi da shirun da wajen yake da shi da kuma yanayin jikin masu ciki yasa bata jima ba baccin da bata san yaushe ne ya kawo mata ziyara ba ya ɗauke ta a wajen .

Lokacin da Biyamuradi Youssouf ya iso baki É—ayan Masarautar sai ta É—auki murna da kiÉ—e-kiÉ—e tamkar wanda ake gagarumin biki .

Da kyar ya samu ya zille daga fada nan ma domin uzurin da Tafeeda ya shigar ne na cewar da yayi ya kamata ya samu hutu tunda bai cika lafiya ba har yanzu .

Da ya shigo gida sashin Hajiya Umma nan ɗin ma a cike ya tarar da sashin da katafainin 'yan uwansa waɗanda dai suke cikin ƙasar kama daga waɗanda suke ciki ɗaya har 'ya'yan Hajiya Mama da suke gidan tuni sun yi zangon a ɗakin mamar su labarin tabbatuwar shigowar sa yasa suka yi ɗango zuwa sashin Hajiya Umma.

Haka ya dunga gaisawa da wasu wasu na rungume shi wasu har 'yar ƙwalla suke na jin dadin sake ganin sa a tsaye kyam bisa diga-digan sa irin taryar da suka masa ya sanya shi jin hawaye bai taɓa sanin haka yake zakara a cikin 'yan uwansa ba sai yau , babu shakka da mutuwa yayi da ya bar musu miƙin da bazai gogu ba a zuci .

Daga can lungu ya hango Siyama ita ma ƙwallar farin-cikin ganin sa take tare da tasowar ciwon kewar sa da take yi , ɗan bakin nan nata yaƙi rufuwa daga murmushin da take kamar yadda ta kasa janye idanun ta daga kan sa.

da hannu ya yafice ta yana 'yar dariya tare da jin raguwa ciwon da yake ji a cikin ran sa kan abunda ya same shi yana yin ƙasa da kusan kaso 50% ganin soyayyar 'yan uwan sa ya ishe shi farin-ciki .

Tana murmushi ta ƙaraso zata tsugunna daga gefen sa ya sa hannu biyu ya ɗago ta ya matsa tare da yi mata wajen zama daga gefen sa da fara'a cikin sautin sa yace " Mata ai geufen Mijinta take da mazauni ƙaƙa za ki ɓuya bayan Aicha kina leƙe na ?  Ina ɗiyata ban ganta a masu tarɓa ta ba .
" tana bacci'  ta bashi Amsa tana sake riƙe hannun sa da yasa cikin nata a lokacin ji take kaf duniya ba wanda ya kai ta jin farin-ciki har wani narkewa take jin zuciyar ta na neman yi bata ƙi ba kowa ya watse a bar su tare .

Wajen ya ɗau dariya wasun su na tsokanar Siyama suna cewa kunyar kinibibi take yi bayan tun ɗazu ta ishe su da leƙe-leƙe .

A cikin su duk babu wanda ya tado da batun abunda Maimounatou tayi masa da wannan kuma umarni ne daga Maimartaba da kan sa da yace " kada a maida zancen labarin tattauna akai .

Hajiya umma ta miƙe tana barin wajen zuwa cikin ɗakin ta a lokacin Allah kaɗai yasan Halin da zuciyar ta ke ciki tayi rauni bata taɓa zaton zai dawo haka ras da shi da lafiyar sa ba babu shakka Allah shine mai yin yadda yaso da bawan sa wani ɗan Adam can bai isa tasiri ba.

Bayan Miƙewar ta bai fi mintoci uku ba shima Youssouf ya mike cikin ran sa ya fahimci Mahaifiyar sa na son ganawa da shi dan haka ya bi bayan ta zuwa cikin ɗakin .

Bayan yayi Sallama ya tura kai ciki , bisa sallaya ya hango ta riƙe da Alkur'ani  , ta ɗago kan ta tana saita ganin ta a kan shi fuskar ta ɗauke da Murmushi ya ƙaraso daf da ita ya zauna yana riƙo hannuwanta baki ɗayan raunin da yake ji a lokacin shine ya taso masa " Umma Allah shi min dawowa ban mutu ba kamar yadda suka so .
.. ya furta hakan hawayen da suka cika idanun sa na sauƙa , yana jin yadda zuciyar sa ke yin kuka.

a take ita ma zuciyar ya ta karye tun faruwar lamarin yau ne rana ta farko da Youssouf É—in yace wani abu yau ne kuma rana ta farko da ta ga kukan sa a tunda ya zama cikakken mutum.

Kan shi ta ɗora hannun ta kafin tace " ka dawo Youssouf ita cuta ai ba mutuwa ba wani kuma bashi da tasirin datse rayuwar wani sai fa idan kwanaki sun ƙare ka yi godiya ga Ubangiji doumin shi ya baka kariyar da basu idda nufin su ba Allah ya sa hakan ya zama kankara na daga zunuban ka .

" Amin-Amin Umma,  ya amsa yana goge ƙwallar sa da hannuwan ta duk biyu ta taya shi tamkar dai lokacin da yake ɗan yaron sa.

" Kar ka yiwa maƙiya kuka kamar kai ba jarumi bane ? Hakan zai iya barantaka da matsayin da kake kai na Soja mazan Fama sannan kuma Yarima sarkin watarana jarumi bai yiwa maƙiya kuka idan sun kai shi ƙasa ya samu dama miƙewa yake ya gyagije a cigaba da fafatawa .

" hakan ba kome bane da ya wuce ƙarin ilmi cikin zaman duniya ka lura ka gane ba kowanne so bane yake zama na gaskiya , ba kowanne murmushi bane yake zama na ƙauna wasun ai shiga suke irin ta burtu suyi aron halayya da kamanni domin cimma wata mummunar manufa tasu su idar da mugunta ka kiyaye Yossoufa .

Kallon ta yake bai ko ƙifta idanun sa zuciyar dake ƙirjin sa ya buɗe yana ƙarbar duk wasu kalmomin ta yana musu adana saboda dayawa daga cikin zantukan ta  bai kai ga gane me take nufi ba a yanzu ? Har kawo yanzu cikin ruɗani yake mai yawa '

har kawo yanzu zuciyar sa bata bar nacin tambayar sa me yasa Maimounatou tayi masa haka ba ?  yana son ganin ta domin ita kaɗai take da amsar tambayar nan .

Ga mammadou ya kasa amincewa kiyayyar da yake masa har ta kai ya kashe shi ? Mammadou É—an uwan sa ne da yake kusa da shi a haihuwa cikin jerin 'ya'yan gidan mutane biyu ne kaÉ—ai a tsakanin su Bilal da kouma Yacouba da suke É—aki guda.

Hajiya Mama kouwa da É—ai ba zai yafe mata ba da ta zama jagora na lalacewar rayuwar sa da zama tsanin faÉ—awar sa a duk wasu munanan aiyuka da yayi a baya.

Muryar Hajiya Umma ta katse masa zurfin da yayi cikin tunani inda take miƙa masa 'yan mukullin ɗakunan sa tana cewa "Magarib ta gabato ka tai kayi haramar Sallah nasan Maimartaba zai nemi ganin ka doumin ku tattauna ya ji ra'ayin ka kan duk waɗanda suka maka ƙeta kada ka cutar da kan ka wajen hanawa a bi ma hakkin ka ,  ka yafewa wanda duk zuciyar ka ta amince da yi masa yafiya , kada kouma ka ɗaukarwa kanka aniyar zama da wanɗanda zuciyar ka bata aminta da su ba ka saukakewa kanka sake faɗawa ga hatsari irin wanda ka fito a baya Allah ya ƙara ƙiyaye mouna kai sannan ka tsanan ta addu'a .

"Amin Umma na kouma gode sosai Allah ya ƙara nisan kwana tare da lafiya .

Lokacin da ya fito mafi yawan 'yan uwansa  sun watse sun tafi hidindimun su wasu kuma suna haramar sallah Ubbo ce kaɗai a zaune da ya fito dariya suka yiwa juna shi da ita yana wucewa tace " Fita kake yi Yarima ?
" zan tai Sallah , ya ce mata yana ƙarasa ficewa .

Bayan ya idar da Sallah gajiya duk ta taso masa tun yana sallar yake hamma dan haka bai tsaya sauraran masu son gaisawa da shi ba ya nufi cikin gida sashin sa ya tasamma saboda so yake yayi wanka da ruwa mai É—umi ya É—an huta kafin lokacin isha'i da yasan bayan sallar isha zasu gana da Maimartaba .

Masu gadin shiyar sa suka buɗe masa ƙofa ya shiga , haske ya wadaci harabar da taimakon security lights dan haka ya nufi sashin sa kai tsaye yana janye ganin sa daga shiyar da Maimounatou tayi zama da ƙoƙarin son raba zuciyar da damuwar da take rufto masa ya hau kan 'yar barandar sa ya kai hannu yana kunna wuta domin ya samu damar buɗe ƙofa .

Zuciyar da tai masa wani ɗan ƙaramin tsalle lokacin da ya lura da wanzuwar mutum kwance akan barandar kusa da ƙafafun sa ,

"Wanene nan ? ya tambayi zuciyar sa yana yin baya kaɗan cike da mamaki yana kure kallo zuciyar sa a dake da ƙoƙarin ganin fuskar ta da ta juya baya tana baccin ta hankali kwance

Motsin sa da yayi da ɗan ƙarfi yasa ta motsawa ta juya zuwa rigin-gine tana motsa idanun ta da suka yi nawi .

Saƙare yayi yana duban ta karo na farko da ya ji ya yarda cewa akwai Mafarkin ido biyu domin shi yake yi a yanzu.

. "Fatima-zahra ya ƙira sunan ta a can ƙasan maƙoshi bata amsa ba saboda baccin da yake son sake danne ta .

Tsugunno yayi a hankali kamar mai tsoron kar ya taɓa ta ta ɓace ya kai yatsun sa biyu kan fuskar ta ya shafa .

Da sauƙar hannun sa a fuskar ta ta buɗe idanun ta da suke luf-luf cike da rauni ta ɗora ganin ta akan fuskar sa da

"Fatima-zahra est-ce vrai ? Ehm ? est-ce vrai ?  Ya furta hakan muryar na 'yar ƙyarma .

Hannun sa da yake cigaba da mata yawa a fuska ta riƙe da nata hannun kafin ta fara yunƙurin tashi sai dai kwanciyar da tayi a kan floor ba tare da shimfiɗa ba yasa jikin ta yin ciwo musamman haƙarƙarin ta .

Lura da yadda ta kasa tashi farar ɗaya yasa shi tallafar ta gaba ɗaya ya zaunar da ita lokacin da shima yake yin zaman dirshan a ƙasa ya jingina ta da jikin sa kamar wanda ya tuno sai ya ɗaura dukkanin hannuwan sa biyu akan tudun cikin ta yana shafawa da buɗaɗɗiyar muryar sa yace

"Fatima ki min magana mana don Allah , kece kuwa ?

Kewar sa mai girma da take ta faman yaƙa tsawon watannin da suka yi basa tare ita ce ta taso mata baki ɗaya a yanzu ta kassara duk wata juriyar ta sai ta juyo a hankali rana ta farko da ta ɗaro hannuwan ta a fuskar sa ta riƙe shi da sanyi murya tace " Baban Mama est-ce vrai ? Meyasa ka tafi ka barmu tsawon lokaci baka neme mu  ba ?  meyasa ? Ka sa min ciwo a zuciyata ta , kasa kullum ina ta kuka . ƙarasa zancen tana janye hannuwan ta daga fuskar sa hawayen ta suka fara sauƙa .

Riƙo ta yayi lokacin da ya lura tana jaa baya daga kusan sa cike da tsoron kar ta sake tafiya ta bar shi ya shiga share mata hawayen ta yana cewa " ke kika bar ni Fatima kin manta ke kika tafi ba tare da izni na ba ,  baki ko min sallama ba kika bar ni ? Fatima ke ma bakya sona ko ?

Kan ta ta mayar kirjin sa da ƙarfi tana jin farin-cikin sake ganin sa tana jin kamar an bata maganin wata cuta dake cinye mata nishaɗin ta , ta kewaye shi da hannuwan tana riƙe shi ƙam-ƙam .

"Oshh , yace yana É—an É—aga ta daga jikin sa saboda raunin sa da ta fama .

"Fatima ina da rauni a jiki , baki san nayi jinya ba kou ?

Idanun ta suka yi rau-rau tana kallon a hankali ta motsa bakin ta tana faÉ—in "sannu ,
Da ido ya amsa mata da yasan ba lalle  ta gani ba da nishaɗi cikin muryar sa yace "Ya babyn mu ? Lafiyar shi lau kou ? Naga yayi girma , ya zama babba alhalin bana ganin sa .

Bai jira ta ba shi amsa ba ya ɗaga ta suka miƙe tsaye yana ɗora faɗin " mu tai ciki ki bani labarin yadda kika zou nan kuma ki nuna min Baby na na gan shi sosai .

Ƙin motsawa tayi a hankali ta zare hannun ta daga cikin nashi kafin tace " nan ba shine masauƙin mu ba a can wajen Umma muka sauƙa can zan koma .

Sake riƙo hannun ta yayi ya ja ta jikin sa ɗan tunbin ta ya tokare haɗuwar fuskokin su muryar sa a ƙasa da wani irin yanayi yace "to ai nan ne gidan ki nan da muke tsaye nan ne shiyar gidana nan shine ɗakina ya mata nuni da ƙofar ɗakin su .

Cike da son samun haÉ—in kan ta ya cigaba da cewa ko kin koma yanzu tunda na dawo gobe nan za'a kawo ki , kin ga nayi rashin lafiya ma baki ko min ya jiki ba , muje ciki na nuna miki inda aka min fiÉ—a .

Da sauri ta ɗago kan ta muryar ta tana rawa tace "yanka ka aka yi ? Aina ? Amma ka warke yanzu ? Ni fa ban san kana rashin lafiya ba sai da suka je tahowa da ni  suke faɗa .

Langwaɓe kai yayi da son ta tausaya masa yace " nayi jinya iriyar wacce ban taɓa makamanciyar ta ba Allah shi ɗagga ni da war haka na daɗe a kushewata .

Ta buÉ—e buÉ—e baki zata yi magana suka fara jiyo muryoyi ana hira da dararraki ana kusanto su ,

A tsorace Falmata ta zare jikinta daga nashi  a kunnuwan ta masu saurin ɗaukar sauti ta tsinkayo muryar Ubbo cikin masu maganar  ,

Muryar ta tana É—an rawa tace " ni ni zan tafi ga mutane suna zuwa kar a ganni ace kuma na biyo ka .

Yana ƙokarin sake riƙe ta taƙi yadda da sauri ta sauƙa daga barandar tayi bayan shuke-shuken da suke kusa da ita .

Da wani irin yanayi yayi tsaye hannuwan sa biyu zube cikin aljihun wondon sa har Siyama da Ubbo suka ƙaraso wajen bayan su bayu ne su uku suna bin su ɗayar saɓe da Yumna a ƙafaɗar ta biyun suna riƙe da manyan tire-tire da aka jera abinci bisa .

Kallon su yayi kafin ya É—auke kai ya juya yana buÉ—e musu É—akin

"Biyamuradi daman kana ta tsayuwa nan ?  Ko kouwa yanzou kaima kake isowa ?

Ubbo ta tambaye shi ,

Bayun da suke gaishe shi ya amsawa gaisuwar kafin su wuce ciki Siyama na gaba tana musu jagora.

"Tun-tuni na zou Ubbo , ya amsa mata yana satar kallon inda Falmata take maƙale ran sa sam babu daɗi damuwar sa kar wani ƙwaro ya cije ta .

" To ni zan koma sai da Safe ku kula da kan kou .

GyaÉ—a mata kai yayi lokacin da take juyawa Bayun da suka ajiye sakonni hannuwan su suna rufa mata baya bayan Siyama ta sallame su daga ciki .

Suna ɗan bada tazara ya sauƙo daga kan barandar da sauri ya nufi inda Falmata take kafin ya ƙarasa daga bayan sa Siyama tace " Baban Yumna wani wurin kake tahia ?  Na haɗa ma abinci fa kouma ga wanka ma na tsumayen ka .

Juyowa yayi yana kallon ta ya ga yadda ta ƙarya wuya tana tsare shi da idanun ta , a dai-dai lokacin ya rasa takamaimai amsar bata yana ganin ta ta taho har gaban sa tana murmushi ta saƙala hannun ta cikin na shi .
"Ka bar koume zouwa gobe yanzou lokacin hutu ne Maimartaba da kan shi yace Umma ta sanar da kai ka huta yau sai daren gobe za ku gana .

Jan hannun sa tayi tana 'yar dariya ta sake cewa "mu tai ciki na kula da kai Vous êtes mon patient pour aujourd'hui et je suis votre médecin.( kai marar lafiyan da zan kula da shi ne a daren yau nice likitar ka )

Cikin idanun ta ya mayar da duban sa yana lalubo fassarar kalmomin ta a cikin su,  murmushi ta sake yi masa tana kashe masa ido da yasa shi yin dariyar da bai shirya mata ba , cikin ran sa yana mamakin yaushe Siyama ta falle ya haka ? ya jaa ta jikin sa hannun sa riƙe da kugun ta suka juya tare muryar sa ƙasa-ƙasa yace mata " Fille, es-tu sûre que tu peux prendre bien soin de ça, ta patiente? ( Yarinya kin tabbatar za ki iya kula da wannan marar lafiyan naki da kyau ?

Dariya ita ma ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta cike da jin kunya gefe guda zuciyar ta na madallah da 'yar uwa irin Ubbo da duk wasu shawarwarin ta basa wuce akan yadda zata yi ta karkato da hankalin mijin ta kan ta.

Sun kai kan barandar sa ya juyo yana sake kallon inda Falmata take a idanun sa ya ga motsawar ta a wajen .

Siyama ta jaa hannun sa zuwa ciki suka turo ƙofar .

A hankali Falmata ta fito daga inda tayi maɓoya idanun ta shaɓe-shaɓe da ƙwalla zuwa yanzu ta tabbatar ita 'yar karo ce a wajen sa da kaddara ta haɗa su marar yanci ce ita da koyaushe take duƙunƙune a gefe.

Siyama ita ce matar da take da 'yanci na yin duk yadda ta so da shi a lokacin da duk ta so amma ita ai a ɗosane take da kuskure kaɗan zata yi dangin sa su tunɓuke ta .

Idanun ta suna ruwa ta baro sashin da kyar saboda bayan ta da yake rirriƙewa sai dai lokacin da ta tasamma komawa masaukin ta sai ta rasa hanya ,

Sai lokacin ta lura da sashi-sashi ne a ainahin gidan da duk gine-ginen su iri É—aya ne sai ka lura da kyau zaka iya tantancewa ko kuwa idan daman ka san gidan sosai .

A idanun ta da suke da rangwamen lafiya ga kuma duhun dare ba zata iya tantance ina ta fito ba sai dai tayi amfani da hagu da dama dan haka tayi hasashen sashin da yake hagu daga nan ta fito dan haka ta kama hanya .

Ko a tsarin harabar sashin bata ga sauyi daga wanda ta gani a É—azu ba shiru sashin yake babu kowa duk hadiman sun kammala aiyukan su sun tafi ga makwantan su .

dan haka kan ta tsaye ta dunga ratsa falukan da ita take tura ƙofofin su da hannun ta har ta tarar da wanda ya mata iri ɗaya da nasu sai dai wannan ta lura kamar ba wancen ɗin bane saboda wannan babu kujeru sai wasu irin katifu da aka yiwa falon ƙawanya da su da ta tsaya da kyau ta lura sai ta ga kamar har labulayen falon ba irin waɗancan ɗin bane .

Tana ƙoƙarin juyawa ta nemi wanda zata tambaya ko nan ne sashin Umma kamar yadda ta ji ana ƙiran surukar ta da wannan sunan , dogon kunnen ta ya fara jiyo mata tashin muryar wata mace daga ɗakin da tayi zaton masauƙin ta ne dan haka ta ɗan taka gaba kaɗan zuwa kusa sa ɗakin tana saurarar kalaman matar da take yin su cikin tashin hankali da hargagi .

" Hafsatouwa ya zamo dole ki kouma wajen sa ki daɗa masa bayani da jaan kunne kada a samou watta matsala ga wannan karon wannan shegiyar ɗiya ta mutan agades da ta ɗora min jakar tsaba kaji sunka bini da tsattsaga ina buƙatar ya lalata min ƙwanyar ta , ta wanke ni ta wanke ɗiyana da bakin ta da ta min wannan sheri ta tona min asiri na da shike binne tsawon lokaci ina so ta lahe ɗoɗɗoyan aman da tayi da bakin ta .

" shi kouwa wannan taƙadarin yaro ɗan tamri Youssoufa da ake kome bisa kan sa ina so a sabunta min aikin sa yayi tsamri fiye da na baya a ƙara hargitse shi a gigitar shi ya fice hankalin sa , itta hegiyar ɗiyar da ya amro dagga Nigeria a sanya shi i mata shika ukku russ tunda na lura shina ƙamnar ta sosai hakan zai ci ran sa ya zaburar sa komawa ga ruwa ina so ya zama tamre wurin bibiyar mata a baya ya kwana da ya ya auri ƙamna gaba 'ya da uwa nake fatan ya haɗa kada kouma ya saurarawa barasa ya zuƙe ta tamkar nonon uwatai ya zama lalattace irin lalatar da zata sa iyayen sa su yahe shi dagga cikin 'ya'ya mutanen gari su masa korar kare dagga birnin Maradi .

"Daga nan na san baƙin-cikin haka shi zai kai Safiya ramin ta...tayi wata dariyar hango cikar buri .

Daga ƙasan ta inda tayi gurfano Hansatuwa da take sauraron ta tana taya ta dariya tace " Ranki shi daɗe maganin kukana ai wannan kullin magani da na kawo miki shi ita uwar ta su anka ce ana so ta ci domin barin ta haka nan tsakani yana lalata mussu aiki kin san ta da ibadar ganin ido .

" ar can kyale ta mu da muke ɗiyan liman ma munka saurarawa ibadar nan bare itta da haye tayi ɗaukar duman magaji da nishi dan kawai ace itta ta Allah , maganin ta nake yi wallashi sai na hana ta ga yin ibadar naga ƙaƙa ta ka yi ta lalata mouna aikin 'yar tselen uwa .

"Hafsatouwa muddin aiki shi tafi dai-dai da tsarin mu ki tabbata shekarar gaba ke ai babbar jakadiyar birnin Maradi doumin kouwa waccen kaucewa take ta baki guri da hannuna zan sallame ta da wani mummunan sharri ta yadda zuri'ar ta basu yin gadon matsayin ta sannan ban tsaya nan ba cikin jama'ar ki ɗai-ɗaya ne ba za su Makka ɗakin Allah ba sai fa wanda Allah bai ƙira ba .

Wata mitsi-tsiyar guɗa Ƙaramar jakadiya ta sake da hakan bai hana su jin motsin Falmata ba wacce a kokarin ta na yin baya ta ture 'yar randar da aka ajiye 'yar bishiyar fulawa daga sama kaɗan da inda take tsaye tana sauraron su tukunyar ta faɗo ta fashe .

A tare suka zaburo ƙirjin su na dakan tara-tara da jin tsoron ko dai an musu laɓe ?

"Idan kuwa hakane muddin ta kama mai mata laɓe sai ta sabauta shi kafin ta ɓadda shi ko wanene kouwa da dai ya fasa wannan sirri na ta mafi girma .Hajiya Mama ta aiyana hakan cikin ran ta lokacin da take nufar falon a ɗimauce .

ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU

DA FATAN KUNA LAFIYA TARE DA FATAN ALHERI .

KUYI HAƘURIN JINA SHIRU DA KUKA YI UZURIN DA YA GITTA MIN MAI GIRM ne .

A gaskiya bana jin daɗin ku masu karatu ta yadda bakwa musayan ra'ayoyin ku hakan ma na ɗaya daga cikin abunda ke duƙusar ni daga nayi yunƙurin yin typing sai nace "ah to yaya zan matsa kaina Alhalin ba'a nuna yabawa ?  Sai kawai na ajiye na fuskanci wani lamarin da ya zarta haka , da fatan kun fahimceni za kuma kuyi duba izuwa koke na ?

Nagode '
[2/27, 9:35 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
(Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

51

Da baya-baya Falmata ta fara taku tana jin wani tsoro-tsoro daga ƙasan ran ta kafin ta juya da hanzarin son gujewa haɗuwar su da ita da mamallakan muryoyin da ta ji suna kitsa sharri da bata kai ga sanin su waye ba .

Sai dai taku biyu kawai tayi ta ji an fisgo rigar ta ta baya da matuƙar ƙarfi da ba domin rigar tana da faɗi ba da babu abunda zai hana ta yagewa bayan ta jefar da ita a ƙasa warwas .

A tsorace ta juyo da taimakon hasken lantarki suka yiwa juna kallon tsakar ido tsakanin ta da Hajiya Mama ,

Ba tare da Hajiya Mama ta saki rigar Falmata ba tana ƙanƙantar da idanun ta da suke cike da tashin hankali tace "wacece ke ? Me kuma kike nema anan ? Wa ya aiko ki ? Sannan me kika ji ana cewa ?

Falmata ta kif-kifta idanun ta da basu cika karfi ba kafin ta fara kici-kicin kwacewa cike da dakiya a muryar ta tace " Ni ce Falmata , matar unh ' Umh Yarima Youssouf Abdoul-aziz , kuma ki sake min riga ta na tafi .

Wani irin zillo Hajiya Mama tayi a take gumi ya karyo mata ta shiga juya kan ta daga ɓangaren hagu zuwa dama baki ɗayan jikin ta tsuma yake .

Idanun ta da suka fir-fito a halin yanzu su ta gwalalo cikin kufcewar nutsuwar ta ta shiga jijjiga Falmata da wata muryar da ta fi kama da raÉ—a take cewa "Annamimiya ke kuma salon ki kenan ? Da salon da kika zo kenan ?? Lalle kin yi kuskure mafi girma da da É—ai wallahi baki sake maimaita makamancin sa .

Juyawa tayi tana jaan ta ita kuma tana turjewa , cikin ɗakin da suka fito ta koma jaye da ita tana shiga ta ingiza ta ba tare da ta kula da cikin jikin ta ba da sauran ƙiris ta faɗa kan cikin ba dan ta riƙe gadon da ta samu damar ƙarasawa gaban sa ba.

Hafsatouwa da tuntuni bata samu damar cewa kome ba illa fargaba da ita ma ya cika mata ciki maƙil jin wacece Falmata , da matsayin ta a gidan da kuma alaƙa mai girma da take da shi da zancen da suke tsakiyar yin sa ita da uwargijiyar ta da babu shakka Falmata ta ji kome .

Tana shiga ɗakin ta rufe ƙofar ta murza ɗan makulli da hanzari ta juya jin sautin mari da ya karaɗe ɗakin .

Akan Falmata ta sauke ganin ta wacce ta durƙusa akan guiwar ta riƙe da ƙuncin ta da Hajiya Mama ta zage iya ƙarfi ta mare ta .

Sake chakumota tayi ta ɗaga ta tana sake chukui-kuiye ta tace "za ki faɗa min me kika zo yi nan wajen a dai-dai wannan lokacin kuma wa ya turo ki ? me kuma kika ji ina cewa ? ko kuma sai na shaƙe ki kin mutu ?

Falmata da zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska zuciyar ta kuma ta cika da tsoro cikin rawar murya tace "wallahi ban zo yin kome ba kuma ba wanda ya aiko ni nan , mantuwa nayi na kasa gane hanyar komawa sashin da aka sauƙe mu saboda tunda muka zo ban taɓa fita ba kuma kin ga idona , idona wallahi bana gani mai kyau dan Allah kiyi haƙuri ku mayar dani sashin da Hajja take .

"Ƙarya kike yi munafuka , me ya fito da ke a daren nan idan da gaske dindimin kike yi ? Baki bani amsa ba me kika ji muna tattaunawa nace ? Kuma uban waye yace ki min laɓe ?

Mukut ! Falmata ta haÉ—iyi yawun tsoro cikin rashin sanin takamaimai amsar bayawar tayi shiru .

Cikin rashin sanin ta shirun da tayi shi ya basu tabbacin ta ji kome , abunda suke gudun kuma yana gaf da faruwa watau fallasuwar asirin su .

Falmata bata ankara ba taji sauƙar wani marin kafin tayi wani yunkuri ta ji sauƙar duka da dundu ta ko'ina kusan gabadaya Hajiya Mama bata hankalin ta dai duka kawai take kai mata .

Ihun da Falmata ta buɗe maƙogoro ta rafsa shi yasa Hajiya Mama dakatawa daga dukan ta , idanun ta jawur ta juya ga Hafsatouwa tace "Hafsatouwa tai ki ɗauko min wuƙa mai kaifi ki kawo min .

Da gudu Hafsatouwa ta miƙe daga durƙuson da tayi ta fita .

Cak Kukan Falmata ya tsaya ta shiga wara idanun ta da ganin su ya sake yin ƙasa saboda kukan da take yi , ta fara taku tana laluben hanya so take tayi wani yunkurin tseratar da kan ta .

Fizgota Hajiya Mama ta sake yi ta warɓar da ita a bakin gado da muryar da take cike da bushewar zuciya tace "ƙwarmato kike yi min ? Kina son tara min jama'a ? Yarinya baki sanni bane , amma za ki sanni dagga lokacin da na guntule miki halshe .

Cikin neman agaji Falmata ta zube guiwar ta a ƙasa dai-dai da dawowar Hafsatouwa da take riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙar yanka dabba a cikin kuɓen ta

hawaye na tsiyayo mata ta haɗa hannuwan ta biyu da sigar migiya tana cewa "Hajja dan Allah kiyi hakuri ki barni na tafi wallahi duk abunda naji ba zan faɗawa kowa ba , wallahi bazan faɗa ba , kiji tausayina ki ƙyale ni ko dan abunda ke cikina .

"Ki min shiru hegiya , ina ruwana da hegen cikin ki ? Kar na kuma ji kin ƙira ni ba suna na Hajja ba .

"faɗa min me kika ji ana cewa ? Maimaita min idan kuwa kika min ƙarya sai na yanka ki billahil azim.

Tiryan-tiryan Falmata ta maimaita musu hirar su kamar yadda ta haddace akan ta ba kalma guda da ta manta duk a ƙoƙarin ta na son suyi mata afuwa bata tsaya da bayani ba sai da ta dire sannan ta ɗora da cewa "wallahi shikenan abunda naji kuma nayi Alƙawarin bazan faɗawa kowa ba .

Sai dai tunanin ta ya tsaya chak lokacin da Hajiya Mama tayi wata gajerar dariyar da ke bayyana irin halin É—imuwar da take ciki.

"Bayan duk kin ji wannan sirrin nawa da mutane uku ne suka san shi bayan ni a din duniya ? Sirrin da 'ya'yan cikina ma basu san shi ba , sirrin da yake ginshiƙi na rayuwata baki ɗaya , da na ta'alaka duk wasu nasarorina akai , shine kike tunanin zan bar ki ki tafi ? Na barki ki tafi kiyi rayuwa a cikin gidan nan ɗauke da sirrina a hannun ki ? Ko a hankali irin naki na dabbobi hakan abu ne da zai yiwu ?

Wata dariya ta sake yi kafin tace "yarinya wannan ba mai yiwuwa bane dole nayi abunda zai sa na kuɓutar da sirrina da yake hannun ki ...

"Wallahi Hajja bazan faÉ—awa kowa ba .

Falmata ta furta hakan tana sharar hawaye da rigar ta .

"Ni da kaina zan goge shi daga kan ki ko da kuwa ace hakan ba zai samu ba sai na raba kan ki da gangar jikin ki ne '

"Hafsatouwa ban wuƙar nan .

Da sauri ta miƙa mata ta sake komawa tana Sake jaan labulen windows din dakin.

A hankali Falmata ta ɗago kai zuwa lokacin ta karaya cikin ran ta ta saddaƙar mutuwar ta ta kusanto ,

Idanun ta ta sauƙe akan Hajiya Mama , tana jin yadda zuciya da ƙwaƙwalwar ta ke adana hoton kamannin fuskarta , a matsayin matar da zata raba ran ta da gangar jikin ta .

Fitsarin da take riƙewa ya kufce ya shiga bin ƙafafun ta lokacin da ta sauke ganin ta akan kakkaifar wuƙar da Hajiya Mama take jujjuyawa a hannun ta .

Wani murmushin mugunta Hajiya Mama ta mata kafin tace "ke kina jina ?

Cikin mutuwar jiki liƙis Falmata ta gyaɗa kan ta .

"Kina da zaɓi biyu ko dai na yanka ki a yanzu na kar ki na kar banza , na sa a ɗau gawar ki a yasar , ko kuwa kiyi duk abunda nace da ke ba tare da gardama ba , sannan ba kuma na son na sake jin tashin sautin muryar ki, ko numfashi mai ƙarfi kika jaa sai na yanke miki hanci bare ta kai ki ga magana babu makawa za ki tsinci halshen ki a ƙasa kina jina ko ?

Da sauri ta sake gyaÉ—a kai, wasu sabbin hawaye na sake tsiyayo mata .

"Hafsatouwa ki je ki kawo min rigar bayu da mayafi .

Kafin ta rufe baki Hafsatouwa ta yi waje ,

Nisawa Hajiya Mama tayi tana karkaɗa kafa cike da izza da mugunta tace "yarinya duk abun da kunnuwan ki suka jiye miki na kaddamar ina kuma kan gaɓar shirya wasu game da surukuwar ki da shi kan sa mijin ki haɗa da 'yal uwarki gasken gaske ne .

"Ki kuma tabbatar zan iya yin abunda yafi haka akan ki muddin kika yi kuskuren yi mini gaddama ko da sau É—aya ne .

"ÆŠauke idon ki daga kaina fitsararriya kin wani tsattsareni da ido uwa budurwar mujiya .

Ta ƙarasa zancen da tsawa da hargagin da yasa abun da ke cikin Falmata murɗawa.

Da sauri Falmata ta sunkuyar da kai tana jin tausayin kan ta na kawo mata , ita kuma irin tata kaddarar kenan mutuwa a hannun wannan azzalumar mata , da ita da abunda ke cikin ta , domin zuwa yanzu ta tabbatar babu wani mai tsaratar da ita sai fa Allah .

Dawowar Hafsatouwa riƙe da wasu tsummokara yasa Falmata sake tsorata "ka dai toshe mata hanci za suyi su hanata mumfashi har ta mutu ?

Saukar taunmokaran a jikin ta ya sa ta É—ago kan ta a firgice.

"Ki tashi ki saka kayan nan da gaugawa .

Babu yadda ta iya haka ta lafta waɗan nan kayan akan na jikin ta tana yi tana yunƙurin aman da yake taso mata sakamakon tsami da ɗoyin datti da kayan suke yi .

"Kiyi lulluɓi da kyau ki biyo ni a baya muddin kika yi wata alamar da tasa aka gane akwai wani abu wallahi kafin ki farga na soke ki.

Haka suka dunga ratsa sashi-sashi na gidan suna cin karo da bayu tsilla-tsillan da suke zubewa su gaishe da Hajiya Mama .

Har suka dangana da wani sashin da yafi kama da kango da yake can ƙuryar gidan da daga shi sai maƙabartan da take cikin gidan ta ɓaryar dama .

Da wani ɗan makulli Hajiya Mama tayi amfani ta buɗe ƙofar ainahin tangamemen falon da yake cikin sashin .

Ta ingiza Falmata wacce bata kai ga sanin cewa falon ya shiga ƙasa ba dan haka tana jefa ƙafar ta ta faɗa ciki ta gurɗe a ƙafa kiris ya rage ta faɗa a kan cikin ta Allah ya sa ta tokare ƙasa da hannuwan ta .

Lokacin da ta É—ago kai bata iya ganin fuskokin Hajiya Mama da Hafsatouwa saboda duhun da Falon yake É—auke da shi , da raunanan idanun ta hasken da yake shigowa daga can harabar gidan yayi kaÉ—an su iya gani tare da shi .

ÆŠallare mata ido da hasken wayar hannun ta da Hajiya Mama tayi yasa ta saurin runtse idanun ta kafin ta buÉ—e su da sauri jin abunda Hajiya Mamar take cewa .

" anan za ki cigaba da zama har zuwa lokacin da zan gama yanke hukunci kan matakin da zan ɗauka akan ki., idan kika yi yadda nake so ta hanyar zama salin-alin ba tare da kin yi wani motsin da zai sa asan kina nan ba , wataƙila na iya barin ki bayan na kafa miki sharɗaɗun cigaba da rayuwa a gidan nan .

"Muddin kuwa kika yi yunƙurin yin wani motsi da zai sa asan kina nan wallahi , wallahi , wallahi , ni ina iya kashe ki da hannu na kuma na sa a ɓatar da gawar ki .

Daga haka ta juya da sauri suka fita ita da Hafsatouwa daga inda Falmata take yashe tana iya jiyo saƙala ɗan makuba da aka yi aka kulle ta ta baya kafin ta fara jin sautin takun sawayen su akan busassun ganyayyakin bishiya su na barin wajen har dai zuwa lokacin da sautin su ya ɓace a kunnuwan ta .

Wani irin karkawa tsokar jiki zuwa gundarin zuciyar su ka shiga yi na tsananin tsoro da firgicin da ruhin ta ke ciki , kafin da wani irin sauti ta fashe da kuka , ta shiga rarrafawa da hannunwan ta da guiwar ta zuwa inda take tunanin nan ƙofar take ,

Lokacin da tayi karo da bango da hannuwanta duk biyu ta shiga bugun bangon cikin ɗimuwar rashin fahimtar ƙofa ce a wajen ko kuwa jikin bango ? .

Washegari da Asuba a Masallaci bayan sun idar da Sallah, Maimartaba tare da Youssoufa yana biye da shi a baya, kai tsaye sashin Maimartaba suka yiwa tsinke domin ganawa ta musamman .

Maimartaba yana sake tambayar Sa yanayin lafiyar jikin sa ?

Shi kuma yana amsa masa da cewa "yana cigaba da samun sauƙi sosai .

Bayan sun isa turakar Maimartaba Youssoufa zai zauna daga gefen shimfiÉ—ar da yake kai , yace masa "dawo nan kussa gareni mu tattauna yana masa nuni da kan shimfiÉ—a kusa da shi .

Da jin daÉ—i mai yawa Youssouf ya matsa kusa da shi .

Gyaran murya Maimartaba yayi kafin yace .

"Youssoufa wanne mataki kake É—auka bissa ga waÉ—an da suka ha'ince ka ?

Shiru Youssouf yayi kafin yace "Ranka shi daÉ—e dukkanin hukuncin da ka zartar .

Shiru mai martaba yayi kafin yace " Ubangiji Mai yawan yafiya ne , yana kuma ƙaunar bayin sa masu afouwa ga junan su a duk lokacin da aka zalunce su , shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci babu wani mugun abu da zai same su, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala bayan ubangiji ya bar su da kan su , Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.

Youssoufa da yayi shiru yana sauraron sa , jin ya dakata ya sa shi É—ago kan sa a nutse

A kalaman maimartaba ya fahimci shawarar da ya ba shi cikin hikima ransa kuma ya sanyaya daga zafin da yake masa a duk lokacin da ya tuno da abunda aka masa dan haka sai yace "Nayi musu afouwa ranka shi daɗe amma ita ban iya sake riƙon Amren ta zan sauwaƙe mata daga can ta tai yankin su , mammadou kouma zan tafi mu dawo tare .

"Madallah da kai Youssoufa yadda kayi afouwa ga 'yan Adam da sunka maka ƙeta kai ma Allah shi maka afouwa bisa tarin laifukan ka .

"Amin Amin Baba .

Murmushi maimartaba yayi yana jin ƙaunar ɗan sa na kawo masa tabbas zuciyar wasu sassauƙa ce mai yawan yafiya .

"Yaushe za ka tafi Niamey domin kawo ƙarshen zaman su a magarƙama ? Ko kouwa saƙo za'a aika musu ?

"Da kaina zan je doumin na sanya hannu a takardar da zai sa a sake su sannan ita kuma zan sahale mata amre na , cikin kwanaki biyu masu zuwa zan tafi .

"Kafin tafiyar ka a sanya a tattara kayan ita wannan ɗiya a aika da su garin su , shiyar ta kouwa ni da kaina zan sa a shirya shi ga ita ɗiyar da muka amso amanar ta daga ƙasar su insha Allah ita tana cikin amintattun mu Allah ya cigaba da baku kariya baki ɗayan ku ya kuma dauwamar da zaman lafiya tare da zuri'a masu Albarka tsakanin ka da matayen ka .

Wani irin farin-ciki Youssouf ya ji yana ratsa shi jin cewa ashe Maimartaba da kan sa ya sa aka dawo da Falmata har ma kuma ga shi zai sa a shirya mata wajen zama a gidan hakan yana nufin samun 'yanci tare da tabbacin zaman sa har abada da Fatima , idan hakane yana godiya ga Allah da duk wasu hatsararruka da ya tsallaƙe tunda ya tsira da Fatima-zahra.

"Amin Nagode Nagode ranka shi daɗe Allah ya ƙara girma tare da nisan kwana .

"Allah shine abun godiya Youssoufa .

Sun jima suna tattaunawa Maimartaba yana ba shi shawarwari cikin hikima tare da yi masa nasiha har hantsi ya É—aga lokacin zaman fada ya gabato ,

Tare suka yi karin kumallo kafin yayi bankwana da Maimartaba zuciyar sa cike taf da farin-ciki gami da nutsuwa ta musamman , tabbas wanda duk yayi dace da iyaye na ƙwarai ya samu rabi na daga nasarar rayuwar sa .

Gefe guda yana sake jin haƙaƙewa akan rabuwa da Maimounatou bayan ta amsa masa tarin tambayoyin da kullum yake bitar su cikin ransa tare da burin jin amsa daga bakin ta .

Bai koma sashin su ba sai ya zarce shiyar Hajiya Umma zuciyar sa cike da ɗokin son ganin Fuskar Falmata a hasken ranar da ta fara ɗagowa , yana da tabbacin a shiyar Hajiya Umma anan aka mata masauƙi .

Abun Mamakin da ya tarar lokacin da ya riski falon Hajiya Umma bai wuce ganin ta tare da Hajiya Mama da sauran 'yan uwan sa baki É—aya ciki har da 'yan É—akin Hajiya Mama duk suna karin kumallo tare da hakan sosai yake sabon lamari a wajensu baki É—aya .

Cike da jin daɗin ganin su haka a tare ya ƙarasa falon kai tsaye kusa da Hajiya Umma ya zauna , yana gaishe ta kafin ya juya ya gaishe da Hajiya Mama wacce ta amsa cikin nuna tsantsar farin-ciki kafin ta ɗora da tambayar sa ƙarfin jikin sa ? A ƙarshe ta bi shi da wata doguwar addu'ar da yasa zuciyar Hajiya Umma haske har ma ta fara samun 'yar nutsuwa akan ta karo na farko , fuskar ta ta cika da annashuwa tana amsa jerin addu'o'in da Hajiya Mama ke yi .

Da wata irin kulawa da ta zarce ƙa'ida Hajiya Mama tace

"Yarima Magajin sarki me za ka ci a zuba maka ? Da jin ɗaɗin kulawar da take masa ya ɗan yi taƙaitatcen murmushi kafin ya bata tabbacin tare da Maimartaba suka yi karin kumallo .

Wani murmushin yaƙe tayi ta jaa bakin ta tayi shiru sakamakon wata kibiyar baƙin-ciki da ta ji ta soki ran ta .

Sallamar da Hajja ta rangaɗo daga bakin ƙofa bai sa wasun su sun tsagaita daga hirar da suke ba , sai fa Youssoufa da Hajiya Mama sune suka yi hanzarin amsa Sallamar da su biyun daman kunnuwan su tarwai yake ga sauraron mai iya shigowa a dai-dai lokacin .

Daga inda Hajja ta saba tsugunnawa ta gaishe da Hajiya Umma yau ma daga nan tayi gurfano ta miƙa gaisuwar ta .

Hirarrakin su suke cigaba da yi ba wanda ya kula gaisuwar Hajja bayan ita Hajiya Umma da ta amsa sama-sama sai fa Youssoufa da ya amsa a mutunce cikin girmamawa.

Jim! Hajja tayi a zaune tana juya zancen da take tafe da shi a ran ta na rashin ganin Falmata ko sanin inda take a tun yammacin jiya .

Wanda ba ƙaramin tashin hankali ya jefa ta ba , domin kuwa ko baccin ta rabi-da-rabi tayi duk kuwa da cewa wani ɓangare na zuciyar ta na shaida mata cewa Falmatan tana tare da Youssouf ne tsakanin Mata da Miji bare ma a haɗa dai da 'ya'yan zamani.

Sai dai ganin Youssoufa a yanzu shi ɗaya ba tare da Falmatan ba ya sa taji cewa gara kawai ta tambaya domin samun tabbacin da zai bata nutsuwa dan haka ta gyara murya kafin tace "Ranka Ya dade Yarima ince dai Fatima ta kwana lafiya ? Domin kwana biyu tana fama da ciwon ƙafafu na saba mata tausa da asubar fari saboda ta ɗan ji dama-dama .

A É—an jahilce Youssouf yake kallon Hajja kafin yace "Hajja ina itta Fatima ta fita da safe hakka ita da bata cika lafiya ba ?

Kalaman sa sun zo dai-dai da bugawar zuciyar Hajja a take ta ji wani tashin hankali mai girma yana durfafar ta cikin ruɗewa tace "ha'a ? Ai tun jiya bayan ta shigo nan domin taryar ka bata sake komawa ɗakin da aka mana masauƙi ba , ban sake ganin ta ba , yau Fatima bata kwana a ɗakin da aka sauƙe mu ba , ban kuma san inda take ba .

Hajja ta ƙare zancen da baza hannuwan ta biyu cikin tashin hankali.

"que de diable racontes-tu ? Youssouf ya furta hakan cikin ƙaraji tare da miƙewa akan ƙafafun sa da hakan ya jaa hankalin duk sauran mutanen dake wajen bayan Hajiya Mama da daman tuni take sauraron bayanan Hajja .

Muryasa cikin tashin hankali ya cigaba da cewa "Hajja wanne zance ne wannan ? Ina Fatima ta kwana ? Tare da wa aka gan su sun fita ina kuma suka tafi ?

Watsa hannuwa biyu Hajja ta kuma yi kafin tace "Allahu shi ya barwa kan sa sani ni dai ba shakka ban san inda ta tafi ba .

Cikin nutsuwa Hajiya Umma da zuwa lokacin ta ji abunda Hajja take cewa ta dubi Youssouf "Mene ne ya faru ?

Ta tambaye shi , wani É—an taku É—aya biyu yayi kafin yace "Fatima, elle est partie, elle est perdue.

"comme quoi ? Ubbo ta furta hakan tana tsare Hajja da ido kafin ta É—ora da cewa "kuma sai dai idan da kan ta ta tai wani wuri .

Hajiya Mama ta muskuÉ—a tare da cewa "wai meye ya faru ? Wace ce Fatima ?

Damuwa na bayyana a fuskar Hajiya Umma tace "É—iyar Nigeria da Youssoufa ke amre ita ce ta ba'a gan ta ba .

Salatin da Hajiya Mama tayi ya sake dilmiyar da Hajja da Youssouf cikin ƙarin wata damuwar kafin tace "to ina ta tafi ? An kuma duba ko'ina ba'a gan ta ba ? Bai fa kamata a zauna ba a yi oumarni maza a fantsama neman ta cikin gida ba'a rasa inda tayi ba.

Kafin a ɗau wani lokaci baki ɗaya bayu masu ɗauke da alhakin tsaron gidan sun fatsama neman Falmata lungu da saƙo na gidan ƙarƙashin umarnin Biyamuradi .

Kasa zama Youssouf yayi ya kama hanyar komawa sashin sa zuciyar sa cike da fatan zuwa ya tarar da ita a inda jiya ta shiga ta ɓuya .

A bakin ƙofar sashin suka ci karo da Siyama wacce ta ci kwalliya cikin riga da zani na wani sassalkan leshi sai zuba ƙamshi take fatar ta na ƙyalli .

Da fara'a ta tare shi zuciyar ta da koyaushe ke kwaÉ—ayin ganin sa tana cika da farin-ciki .

Sai dai ga mamakin ta bai ko saurare ta ba ya wuce ta da sassarfa da alamun rashin nutsuwa a tare da shi .

Da sauri ta taka ta bi bayan shi bayan ta É—auki Yumna da tasan ba zata iya sauri ba .

"Baban Yumna lafiya kouwa ? Me yake faruwa na gan ka haka hankali tashe ?

"Wai Fatima-zahra ta ɓace tun jiya ba'a gan ta ba .

Ya furta hakan lokacin da yake ƙarasawa gaban bishiyoyin da a jiya ta ɓuya bayan su , bai jinkirta ba ya tsallaka bayan bishiyoyin yana ƙiran sunan ta da wani irin sauti .

Sasakai! Siyama tayi tana cikin yanayi mai kama da almara wai Fatima ta ɓata shi kuma Youssouf ya zo neman ta nan bayan shukoki anya Youssoufa ba matsala ya samu cikin ƙwaƙwalwar sa ba ? idan ba haka ba me zai kawo Fatiman nan bayan shuke-shuke'?

Haka ya gaji da bankaɗa ganye ya fito jikin sa duk ya ɗau ƙura idanun sa sun yi jawur .

"Baban Yumna Fatima kake nema anan kuma ?

Cikin duƙusasshiyar murya yayi mata nuni da wajen yana cewa "anan jiya mun ka shiga ɗaki mun ka bar ta, kafin zouwan ki ina tare da itta a can
Ya ƙarasa zancen da nuna mata bakin barandar sa kafin ya ɗora da cigaba da cewa " Ina Fatima zata sake tafiya ta bar ni ?

Kamar ruwa ya cinye ta Siyama tayi shiru , zuwa yanzu ta fahimci abunda yake nufi da neman ta anan ashe ma jiya sun haÉ—u har sun gana? Ita har sokuwar zuciyar ta ke kambama ta a matsayin wacce ta fara kasancewa da Youssouf É—in a jiya ashe hasashen ta bai zama gaskiya ba koyaushe alfarmar Fatima take ci daga wurin sa muddin ta samu cikakkiyar kulawar sa to Fatima ce ta mata tubalin ginuwar farin-ciki da nishaÉ—in sa .

Bata ankara ba ta ga ya sake wuce ta yayi hanyar fita daga sashin nasu , da sassarfa ta bi bayan sa .

Bayan kamar awa biyu labarin ɓatan Falmata ya fara zagaye masarautar bayan shafe fiye da awa guda da bayun gidan suka yi suna neman ta a cikin gidan amma ko wanda yace ya gan ta ma ba'a samu ba bayan masu gadin shiyar Youssoufa da suka bada tabbacin shigar ta da fitar ta daga sashin .

Zaman dirshan Youssoufa yayi a falon Hajiya Umma yana jin wani irin bugu da ya wuce ƙima da zuciyar sa ke yi .

Hajja kuwa zuwa lokacin ta fara sharar hawaye da gefen mayafin ta .

Ubbo wacce take cike da takaicin damuwar da É—an uwan ta yake shiga ta sanadin Falmata tace

"To wai za ta ɓata ne ? Sai dai idan da ƙafafun ta ta fice doumin kouwa ai hakan bai zama sabon abu ba wajen ta .

Kallon ta Youssouf yayi zai ce wani abu Hafsatouwa wacce ita ce ƙarshen dawowa daga neman Falmata da aka fantsama su tayi gurfano a gaban su hannun ta riƙe da cukurkuɗaɗɗen Mayafi.

Da hannu biyu ta miƙawa Youssoufa kafin ta ɗora da cewa " wannan mayafin can wajen ƙofar fita gida ta ɓangaren kudu na tsinto shi wanda kuma nayi hasashen ya.....

Miƙewar da Youssouf yayi riƙe da mayafin ya sa ta yin shiru duk suka zuba masa ido .

Yana riƙe da mayafin ya kai shi ga hancin sa yana shinshinawa kafin ya ɗago kan sa da wani irin sauti yace "lalle wannan shine Mayafin da ta rufu da shi a jiya .

Ita ma Hajja gyaɗa kai tayi cike da tabbatarwa tace "ƙwarai wannan mayafin Fatima ne to ita tana ina ?

Muryar Hajiya Mama da ta ratso wajen ta katse musu hanzari inda take cewa "wannan alama ce da take nuna yarinyar nan an fita da ita daga gidan nan ne ta ƙarfin tsiya kuma babu makawa sace ta aka yi .

Wani ƙaƙƙarfan kuka Hajja ta sa wanda ya ratsa zuciyar Youssouf ya tarwatsa duk wata nutsuwa da ta masa saura .

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon yanzu wanne azzalumin ne ya ɗauke yarinyar nan a wannan yanayin da take ciki na shiga uku ni hauwa'u 'yar mutane ta ɓata a hannun mu .

Hajja ta furta hakan tana rufe fuskar ta da mayafin ta ta shiga rera kuka .

Shigowar Babbar jakadiya yasa kallon su ya koma kan ta , saƙon Maimartaba ta isar inda take shaida musu kan cewa baki ɗaya yana neman su a shiyar sa a yanzu-yanzu da gaugawa.

Ba a É—au lokaci ba dukkanin su daga kan Hajiya Umma , Hajiya Mama da su Ubbo duk suka cika falon Maimartaba suka yi zaune suna sauraron sa .

Bayan duk sun nutsu yace "wani labari ya zo mana Fada kan cewa wannan ɗiya ta Nigeria ta ɓata a cikin gidan nan yaya gaskiyar lamarin yake ?

Shiru duk suka yi kafin Hajiya Umma tace "Hakane ran ka ya dade amma duk cikin mu babu wanda yake da masaniya kan haƙiƙanin yaya lamarin ya kasance domin ba'a gan ta a gida ba ba'a ga kuma wanda ya ce ya ga ficewar ta ba .

"Rashin tsaro a gidan har ya zama haka da za'a nemi mutum sukutum a rasa ?

Maimartaba ya furta haka da bayyanuwar matsanancin ɓacin-rai a fuskar sa .

A hankali Ubbo tace "Ranka ya dade Allah ya daɗa maka nisan kwana ka cigaba da jagorar mu ni nafi tunanin Yarinyar nan ba ɓata tayi ba sai dai tafiya tayi da kan ta kamar yadda ta taɓa yi daga Niamey zuwa ƙasar su dan...

Da wani irin sauti saɓanin wanda aka saba amfani da shi a masarauta yayin da ake gaban sarki Hajja tace " 'Yar nan wannan zancen naki ba gaskiya bane muddin kuma ya zama gaskiya to kune sanadi , saboda abubuwan da kuke yiwa yarinyar nan na tozarci kaɗai ya isa yasa ta zuciya ta bar gidan nan haba mana shin shi talaka ba mutum bane ? Ko kuwa laifin tayi domin ta auri ɗan uwan ku ? Fatima baiwar Allah yarinya ce ƙarama da take da larura wanda idan har baku gwada mata ƙauna ba bai kuwa dace ace kuna tozarta ta ba yanzu me za'a ce ga iyayen ta da kuka yi sanadiyar da ta gudu ba'a san halin da take ciki ba ?..... kasa cigaba tayi da magana saboda kukan da ya ci ƙarfin ta

Hajiya Umma ta yunƙuro zata yi magana da hannu Maimartaba ya dakatar da ita .

"Me yake Faruwa a gidan da ni ban kai ga sani ba ? Waye yake tozarta Al'umma ciki har ma da mutanen da suke amintattun mu da muka amso amarnar su daga hannun mutanen su ?

Shiru aka yi babu mai tsaurin idon iya amsawa .

Kamar daga sama Muryar Youssouf ta ratso wajen inda yake cewa " Fatima ba gudu tayi ba babu makawa É—auke ta aka yi ..

Ya ɗan jinkirta lokacin da idanun kowa ya dawo kan shi zuciyar Hajiya Mama ta fara sauya ƙarfin bugu tana dik-dik-dirim-dim.

"Wa kake tunanin ya É—auke ta ?

Maimartaba ya furta haka cike da nazarin sa ,

Shiru yayi da yasa gumi ya shiga zarya ta cikin rigar Hajiya Mama .

"Maimounatou .

Ya furta hakan da tasowar matsanancin ɓacin rai a muryar sa , ya cigaba da cewa
"Maimounatou ita ta sanya a zo a É—auke Fatima domin cikar burin ta ta wani fanni sai dai a wannan karon ba zan kyale ta ba dole ne na gwada mata ainashin É—abi'ar da na É—au shekaru a wajen koyar ta cikin aikina na na soji .

Muryar Hajiya Mama ita ta ratso wajen cike da wani boyayyen farin-ciki a sautin ta tace " Yarima ni da kaina tunanin da ya fara zowar min kenan ba shakka wannan ɗiyar ta Agades ita ta sanya anka ɗauke wannan yarinya ta ƙwarai kuma dole ayi hanzarin ɗaukar mataki akan haka.

Shiru Maimartaba yayi cikin son yin nazari sai dai hayaniyar da ta fara tashi a tsakanin iyalan sa da duk suka aminta da cewa Maimounatou ce ta tura aka sace Falmata duk kuwa da babu hujja ɗaya da aka samu wanda yake bada tabbaci ga hakan ya dukusar da hanzarin sa musamman lokacin da Youssouf ya miƙe a safure ya taho gaban shi yayi gurfano .

"Ranka shi daÉ—e zan tai Niamey yanzu zan tai na tadda Maimounatou ta faÉ—a min ina ta kai iyalina ?

"Youssoufa ka nutsu wannan batu ne da yake buƙatar nutsuwa da tsawaita bincike , ina maka oumarni da ka jinkirta hanzarin da kake yi har a ƙarƙare bincike a samu madogara .

Da kyar Maimartaba ya shawo kan hayaniyar su bayan ya tabbatar da za'a tsananta bincike kafin tunkarar koma waye da aka samu shaidar yana da hannu a ɓatan Falmata

Bayan fitar su daga Sashin Maimartaba Hajiya Mama bata koma sashin Hajiya Umma ba kai tsaye sashin ta ta koma ba tare da ta zauna cikin 'ya'yan ta da suke ta hira kan batun ɓacewar Matar Youssouf da wasu daga ciki ma daɗin lamarin suke ji saboda ta riga ta gina ƙaƙƙarfar ƙiyayya tsakanin su da Youssouf da duk wani abu na bakin-ciki da zai faru da shi su murna suke yi .

Can ƙuryar ɗakin ta ta shiga ta fara kai kawo cike da tunanin kan mataki na gaba da zata ɗauka wajen cigaba da tsare Falmata dan kada a samu wani lamari ya gifta da asirin ta zai shiga hatsarin tonuwa

A ɗan firgice ta waiga jin motsin shigowa ɗakin Hafsatouwa ce ta ƙaraso gaban ta da sassarfa bayan ta rufe ƙofar .

"Hafsatouwa sirrina yana cikin haɗari ya zama dole ki shirya ki tafi Zuru wajen mai jar-tawada ki amso min wani gagarumin aikin da zai kurumtar , ya makantar idan ya kama ya gurguntar da duk wasu da zasu iya kawo min tsaiko kan ƙudiri na ne ma duk ayi .

" a min aikin da zai shafe tunanin ita kan ta yarinyar nan da ta san sirrin na sannan a mantar da duk wasu makusanta nata daga tunanin ta har sai lokacin da na gaji dan kaina da hukunta ta na sake ta , ke Hansatouwa ina so na zama ni nice , kowa kuma ya zama ba kowa ba , ina nufin kowa da kowa na cikin masarautar Maradi su dawo ƙasan iko na a baɗini da fatan kin gane ?

Cike da jin tsoron yanayin da take hango uwargiyar ta a ciki hafsatouwa ta shiga gyaÉ—a kan ta .

"Oumarnin ki abun bi ne ranki shidaÉ—e uwargijiya ta mai girma .

"Da kyau to ya ya kin yi abunda nace kiyi ?

"Ranki ya daÉ—e tuni nayi .

"Kin ji motsin ta ko kaÉ—an daga inda take ?

" ba wata alama dake nuni da cewa akwai rayayyen mahaluki a bigiren da alama yarinyar bata da taurin kai .

"Idan ta yi haka ta sauƙaƙawa kan ta riskar wasu daga cikin tarin horon da nake mata tanadin su .

"Kina iya tafiya yanzu , idan buƙatar son ganin ki ya zo zan aika a min ƙiran ki .

" To ranki ya daÉ—e godiya nake .

Gaf da Azahar bayan hankulan mafi yawan mutanen gida ya tafi ga haramar sallah Hajiya Mama ta kashe jiki ta nufi tsohon sashin babar ta kuma Uwargidan Sarki Azizou Baskore "Hajiya Uwa .

Da tun bayan rasuwar ta sama da shekaru goma sha takwas babu wanda ya sake zama a sashin ya zama tamkar kufai , sai fa Hajiya Mama da jifa-jifa take zuwa sashin tana yin wasu abubuwan da ta ce raya sashin take yi da yake a matsayin na uwa a gare ta wanda kuma a baɗini daga Allah sai ita sai kuma tsirarun mutanen da tayi haɗakar ƙulla sirrukan ta da su , suka san ainashin abunda take aikata a sashin a duk ƙarshen kowanne wata .

Bayan ta gama nazarin wajen ta tabbatar babu wani mahaluki a wajen da zai iya jin abunda za ta yi ta sanya ɗan makulli ta buɗe ƙofar falon bayan ta ɗau wata leda da take yashe daga kusa da ƙofar .

Kan ta tsaye ta shiga falon ta tura ƙofar ta rufe tana mayar da ganin ta kan Falmata wacce take takure daga can gefe cikin datti da ƙurar da ta maye gurbin shimfiɗar ɗakin ya zama duk inda ka ɗora ganin ka datti ne da tankaɗaɗɗiyar ƙasa kamar an kwaso an zuba ba'a ko iya ganin ainashin dandaryar ɗakin .

A hankali Falmata ta É—ago kan ta dake tsakanin cinyoyin ta da ta haÉ—a su ta takure ba'a ce mai ciki bace .

Taku tayi ta ƙarasa gaban Falmata tashin sautin ta ya biyo bayan ledar da ta wurgawa Falmata

" wataƙila kina jin yunwa ki ɗau abinci ki ci ya rage naki ki cinye shi duk ko kuma ki rage dan anjima .

Falmata da fuskar ta ta kumbura saboda kuka ta buÉ—e bakin ta da take ji ya mata nawi muryar ta bata fita sosai tace "Sallah nake so nayi ki nuna min wajen da zan yi Alwala .

Wani kallon banza Hajiya Mama ta mata kafin ta ƙuta , sai da ta mula sannan tace " ga rairayi nan kina zaune a cikin sa ki buga ƙasa kiyi taimama .

Bata jira ba ta cigaba da cewa " ina sake jaddada miki muddin kina son tsira da rayuwar ki to ki kiyaye abunda zai sa a san kina nan , idan kuwa kin ƙi ji .?

Da zubowar sabbin hawaye Falmata tace "Hajiya Dan Allah ki tausaya min , ki ji tsoron Allah mahalicci da yake kallo tare da jin kowa da kome , ban yi miki kome ba .....

"Ke .

Hajiya Mama ta daka mata tsawar da ya sa Falmata yin shiru " kina son karya doka ta ne ?

Da sauri Falmata ta girgiza kai .

"Tashi , tashi nace ko ?

Da kyar Falmata ta miƙe saboda ƙafar ta da ta ji ciwo a jiya ga yunwa da ƙishirwa , sun sa har jiri take ji bayan ciwo mai tsanani da kan ta yake yi , ta ɗingisa dakyar ta bi bayan Hajiya Mama wacce tayi gaba zuwa wata ƙofa ran ta cike da fatan "Allah yasa afuwa zata mata ta fitar da ita daga wannan wajen .

Da kallo ta bi ɗakin da su shiga wanda ba kome a cikin sa bayan tulin ƙura da yanar-gizon da ya zarta na falon sai fa wani karmamin gadon katako da duk gara ta cinye shi shi ɗaya ƙwal a ɗakin.

"Anan za ki cigaba da zama , ga banÉ—aki nan a ciki amma bani da tabbacin rasa macizai da kunamu a ciki sai ki kula wajen amfani da shi idan ba haka ba kin ga sun hutar da ni daga kashe ki.

Daga haka Hajiya mama ta juya da kusan tare suka juya da Falmata wacce ta zube a ƙasa tana wani irin kuka ta riƙe ƙafar Hajiya Mama tana shisshiƙa kamar ran ta zai fita tace "Hajiya Dan Allah , Allah .....

Hanɓare ta Hajiya Mama tayi ta taka da sauri kafin Falmata ta yunkura ta fita ta rufo ƙofar ta murɗa ɗan makulli .

Tare suke da page 51b
[2/27, 9:35 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( hargitsin Rayuwa )

Umm"muaz

51b

Duk yadda Maimartaba yake tunanin za'a yi samu wata alama da zai nuna ina Falmata take anyi amma babu nasara har aka kwana aka yini babu wani bayani takamaimai na inda take .

Zuwa lokacin kuwa Biyamuradi Youssouf gaba É—aya ya gama birkice musu ya kuma matsa lamba kan son zuwa Niamey wajem Maimounatou dan ta faÉ—i inda ta kai Falmata.

A ƙarshe ba yadda maimartaba ya iya ganin yadda ɗan nasa ya zama yasa ya masa umarnin tafiya bayan ya masa nasiha akan haƙuri da mallakar zuciyar a duk lokacin da rai ya ɓaci sannan ya gargaɗe shi da gujewa ɗaukar mataki cikin fushi .

Ƙarfe goma na ranar jirgi ya ɗaga da shi da Bilal da zai masa rakiya zuwa Niamey .

Bayan tafiyar Youssouf Hajiya Mama ta ƙira Hafsatouwa ta umarce da cewa gobe da sassafe ta kama hanyar Zurun Jahar kebbin Nigeria bayan ta danƙa mata isassun kuɗin da zasu ishe ta .

Duk da cewa Falmata baƙuwa ce a masarauta Maraɗi amma hakan bai hana masarautar ta zama cikin alhini ba kasantuwar ta riga ta zama wani ɓangare na gidan , ko'ina ka ratsa za ka ji bayun gidan suna batun ɓacewar Gimbiya Fatima da cikin jikin ta .

Hajiya Umma da kan ta ta shiga damuwa musamman da ya zama Maimartaba yana ganin har da sakacin ta wajen ɓatan Falmata da har a jiya da dare ya tabbatar mata da hakan cikin fushi .

Hajja kuwa ƙurewar tashin hankali ta shiga tayi kuka har ta bawa aku lada ta haƙura ta rungumi charbi tana addu'ar Allah ya baiyana mata uwarɗakin ta a halin lafiya .

Niamey .

Lokacin da Youssouf ya isa Niamey daga airport kai tsaye babban ofishin 'yan sanda ya nufa inda har lokacin ake cigaba da tsare Mammadou da Maimounatou sakamakon rashin sanin halin da shi yake ciki da hakan ya kawo jinkirin miƙa su kotu a musu hukunci .

Bayan ya cike takardu aka masa iznin ganin su da Mammadou ya nemi ganawa a farko .

Lokacin da aka fito da Mammadou , Youssouf da yake zaune bai san lokacin da ya miƙe ba da sauri ya taka ya taro Mammadou da yake tangaɗi , ba tare da ya damu da tsami da warin da yake tashi daga jikin Mammadoun ba ya kama shi suka zauna .

Da wani irin yanayi a fuskar sa mai tsauri yace "Mammadou ƙaƙa ka zama hakka ? Shin baka da lafiya ne ? Ko kouwa horo ake maka ?

Mammadou da zuciyar sa ta cika taf da farin-cikin ganin Youssouf ya riƙo hannuwan sa duk biyu kafin ya fashe da matsanancin kuka cikin kukan yake cewa "Youssoufa kai min gafara , ka yafe min ɗan ouwana na tuba ka yafe min , nayi nadama marar amfani na kouma yi tir da muguwar uwa irin tawa tare da.....

Da sauri Youssouf ya katse shi yana cewa "Mammadou kar ka tsawaita zance domin ba shi da wani amfani dan kouwa ba zai yi gyara cikin abun da ya wouce ba kouma zouwa ma nayi mu tai gida tare nan ba wajen yin zance bane Mammadou .

Cikin wani irin sauti Mammadou yace "da gaske Youssoufa zowa kayi ka tafi da ni gida ?

Miƙewa Youssouf yayi yana zube hannuwan sa cikin aljihu ya fara taku yana barin wajen ƙarƙashin rakiyar idanun Mammadou da ya bi shi da kallo sai da ya kai ƙofar ficewa daga wajen bai jiyo ba yace "ƙwarai yau kake kwana a gida Mammadou .

Daga haka ya fita yana jin yadda tattaurar zuciyar sa ke son tasowa ta hana shi duk wani afuwa da sassauci da yayi niyyar yi ga É—an uwan nasa .

Ya juya baya ga ƙofar shigowa lokacin da aka taso ƙeyar Maimounatou ta shigo inda yake idanun ta da suka shige ciki ta ware tana kallon sa a take ta shaida ko wanene a gaban ta , sannan 'yar murna da ta fara safko mata jin cewa an zo ganin ta ta koma ciki fargaba mai girma ya mamaye ta da yasa har wasu siraran gumi suka fara tsiyaya ta cikin rigar ta .

cikin raggon taku ta nufi inda yake sai dai kafin ta ƙarasa ya juyo baki ɗayan sa yayi tsaye ƙem a gaban ta da juyowar sa tayi hanzarin sauƙe idanun ta ƙasa tana jin wani yanayi da ta gagara tantance a wanne matsayi zata ajiye shi "kunya ce ? "Nadama ce ? Ko kuwa tsoro ne ?

Bata ankara ba ta gan shi daf da ita kamar an tunkuɗo shi hannuwan sa zube cikin aljihun wondon sa da sautin sa mai amo da ya sake kaurarara yace "Madame, êtes-vous surprises ?

Wani murmushin yaƙe Maimounatou tayi da ya taho da ɗoyin da bakin ta ke yi , ta ɗago kan ta ta saci kallon sa kafin ta wani karya kai gefe ɗaya cikin muryar da ta saba hilatar sa da shi wacce yau ta sake matsewa tace "Pas vraiment, tu ne m'as pas surpris, je sais que tu reviendras vers moi.
Hannun ta ta miƙa da nufin taɓa shi ya jaa baya da sauri yana kokuwa da ɓacin ran sa da idanun sa da suka yi jaa ya mata wani kallon gargaɗi da ya kaɗa mata ciki .

Da baya-baya ya dangana da kan kujerar da take gaban ɗan teburin da yake cikin ɗakin ya zauna yana harɗe ƙafafun sa ɗayan kan ɗaya yace.

" idan kin ka yi tounanin kina da watta sauran dama guda da ta rage miki a gareni kin yaudari kan ki yau ba rana ce ta wassa ba don haka Arrêtez de jouer avec votre propre cœur et de vous dupe.

Wani murmushin ta sake yi kafin ta yi ɗan taku kaɗan tana juya baya ga barin fuskantar sa cikin ƙarfin hali tace " Bana neman watta dama dagga gare ka a yanzou sabbada kuwa duk watta dama na riga na same ta har ma......

Tsawar da ya yi haÉ—i da buga teburin gaban sa shi yasa ta juyowa a firgice , a tsaye ta gan shi fuskar sa da ta duba a lokacin ji tayi marar ta ta cika fam.

Ya matso daf da ita yana nuna ta da yatsan sa ya ce "kadda ki min wassa , ni damisa ne da ban juri wasa ba ban ɗauki wargin mazaje ba a fagen daga na sanya bakin bindiga na fasa ƙoƙon kan su na sa ƙafafu na taka cikin su kar kiyi zaton zan miki sassauci ,

hannun sa ɗaya da yake cikin aljihun sa ya zaro da yake riƙe da ƙaramar bindiga , yayi taku kaɗan zuwa baya kafin ya cigaba da cewa "zan iya tarwatsa kan ki da harsashi bayan na tattaka ki muddin kin ka cigaba da min fi'ili .

Kafin ya mayar da numfashi Maimounatou ta zube akan guiwowin ta ta haɗa tafukan ta biyo tana sakin wani mitsi-tsin kuka mai tafe da sautin tsoran da ruhin ta ke ciki tace jikin ta na ƙyarma tace ,

" Dan Allah kayi haƙuri kar ka kashe ni , wallahi sharrin shaiɗan ne ya sa na aikata abun da na maka ka yafe min .

Wani guntun murmushi Yayi kafin tace
"Ashe kina tsoron Mutuwa ? Ni kuma kin ka nemi kashe ni ? Babu yafiya a tsakanina da ke ko afuwa ba zan iya miki ba muddin baki sanar dani dalilin da yasa kin ka nemi raina ba?

Da sauri Maimounatou tace "wallahi zan faÉ—i dalili .

Komawa yayi ya zauna yana ƙoƙarin sassauta fushin zuciyar sa yace "Vous avez seulement 30 minutes.

Kamar an kunna radio Maimounatou ta shiga ba shi labari tiryan-tiryan tana yi tana kallon sa tana karya wuya da sharar hawaye .

Bai katse ta ba har sai da ta kai ƙarshe

Kan sa a ƙasa yace "menene gaskiyar cewa da kika yi Mammadou ya kawo gubar da kin ka ciyar da ni ?

Girgiza kai tayi cikin ƙaramar murya tace .

"ba shi bane ni na aiki Gnala ta sayo min . sannan cikin kuka ta cigaba da cewa

"Amma wallahi nayi nadama iyakar nadama dan Allah ka min afouwa ka sake bani dama na gyara kuskurena wallahi wannan karon da dukkanin zuciya ta zan zauna da kai zan tallafi soyayyar da kake '.....

ÆŠago da kan sa da yake sunkuiye yayi yana É—an buga tafin hannun sa akan teburin gaban sa yayi wani murmushi mai ciwo .
"Soyayya ? Yanzu kina zaton har kawo yanzu akwai sauran ɗigon na alamar son ki a raina ? Bayan duk abun ƙi da kin ka wanzu wurin aikata shi a gareni..

Huci yayi yana danne ƙiyayyar ta da yake ji mai karfi tana naso a cikin ran sa daga lokacin da ta ambaci sunan Ghaddafi Yacouba Dango a matsayin mutumin da ta nemi kashe shi a kan sa bayan irin ha'intar sa da tayi ta dunga yaudarar sa da sunan soyayya har ya aure ta bayan sun gama tanbaɗewar su da wannan riƙaƙƙen ɗan ta'addan haƙiƙa Maimounatou guba ce ba domin yana yaƙar zuciyar sa da babu abunda zai hana ya harbe ta a lokacin .

Ya tsaya faɗa mata matsayin da take kai a wajen sa a yanzu tamkar ɓata lokaci ne ko kuwa bata wani matsayi na daban da ya wuce wanda takai kai yanzu a wajen sa dan haka ya mayar da ganin sa gefe daga kan fuskar ta da alokacin yake ganin ta da muni fiye da duk wani mummunan abu da ya taɓa cin karo da shi a tsawon rayuwar sa .

"Ina kin ka sa a ka kai Matata ?

A dabar-barce Maimounatou tace wacce matar ka ?

Taku ɗaya yayi ya miƙa hannu ya figo ta tayi zaman 'yan dabaro a gaban sa ya shaƙe wuyan ta kafin ya danna mata bakin bandiga akan ta wata irin razananniyar tsawa ya daka mata yana sake maimaita tambayar ta.

" Ina ki ka kai Fatima-zahra Mata ta nace ? Ki faÉ—a min ko na fasa kan ki .

Baki ɗayan jikin ta ɓari yake ta kasa magana saboda maƙogoron ta da ya shaƙe ya sa ta fara jin ƙamshin mutuwa .

Ta kai mintuna biyu a haka a shaƙe a hannun sa , sai da yayi da gaske tukun ya iya haƙura ya sassauta shaƙar da ya mata ya ingiza ta ta faɗi .

Kan sa ya sake sauƙewa ƙasa yana huci bai ɗago ba yace " za ki faɗa min ko kuwa na kashe ki ?

Tana wani irin kuka Maimounatou tace "wallahi Allah ɗaya kenan bani da watta masaniya kan ɓatan ta .

Cikin tsawa yace "to waye zai sace ta? Waye maƙiyi na da ya wucce ke ? Ina da wani Maƙiyi bayan ki ? Za....

"Wallahi kana da Maƙiyiyar da ta wucce ni wacce ita tayi sanadin faruwa duk wassu abubuwa marasa kyau da sun ka samu rayuwar ka .

"Wacece itta ?

Ya tambaye ta a daƙile

Da sauri ta amsa masa da "Hajiya Mama.

Yamutsa fuska yayi kamar yana son tuna inda ya taɓa jin sunan .

Ganin haka ya sa Maimounatou cigaba da cewa " Baka da wata maƙiyiyar da ta wuve Hajiya Saratu , Matar Mahaifin ku Mahaifiyar Mammadou Hajiya Mama.

"Ita ta wanzu tsawon shekaru tana bin ka da sharri da ita da Tsohuwar Matar kakan ku Hajiya Uwa su biyun sune suka fara lalata rayuwar ka ta hanyar yi maka mummunan sihiri,

" su suka sa ka zama mashayin giya "giyar burkutu , su suka sa kayi zina da yarinya Amina wacce take 'yar uwa ga É—aya daga cikin matan da za ka aura,

Su suka yi ma Asiri tun kana É—an shekaru biyar bai fara aiki ba sai da ka shekara goma sha takwas , ranar da ka cika shekaru goma sha takwas a ranar ka fara shan barasa, ranar da ka cika shekara talatin a ranar ka fara yin zina a kuma ranar ...''

Ɗago ta Youssouf yayi ya haɗa ta da jikin bango gaba ɗaya jikin sa tsuma yake cikin ɗimauta yake cewa "ƙarya kike yi , ke maƙaryaciya ce maha'inciya munafuka ki faɗa min gaskiyar aina duk kika samu wannan bayanin ? .

Idanun Maimounatou sun fito waje amma bata haƙura da magana ba ta cigaba da cewa " kuma Hajiya Mama bata daina sabunta aikin asirin ba ko bayan mutuwar Hajiya uwa babban burin su ka rasa ƙima da darajarka ta ɗan sarki da hakan zai sa ka gaza wajen hawa kujerar mulkin Maradi , a wayi gari Mammadou shi ne Sarki.

"Duk abunda nake faɗa maka a yau gaskiya ne babu ɗigon ƙarya ko ɗaya a ciki, ita da bakin ta ta faɗa min idan kuma kana son samun tabbaci da kuma hakan zai kai ga karya duk wasu sihiri da aka maka kuma har yau suke aiki a kan ka , ka koma Maraɗi ki tafi tsohon sashin Hajiya Uwa a babban falon ta cikin ɗaki na biyu daga hannu hagu ka bincika ɗakin a cikin armoire asirin da aka maka yake .

" Ka je ka fasa kome , Ka ɓata kome , muddin kana son cigaba da yin rayuwar da babu dabaibayin sihiri a cikin ta .

"A ƙarshe ina baka tabbacin Hajiya Mama tana da hannu wajen ɗarsuwar duk wani baƙin-ciki a rayuwar ka dan haka ba tamtama a wannan karon ma ita ta sace Fatima .

Sakwaf ! Youssouf ya sake ta ta faɗi a ƙasa kalamanta na ratsa duk wasu jijiyoyin cikin ƙwaƙwalwar sa suna aikawa da saƙon gaugawa zuwa cerebrum na kwakwalwar sa har zuwa temporal lobe da anan take ya fara ƙoƙarin tuno masa da duk wasu motsi da lamurarran Hajiya Mama a kan sa .

"Yadda take kyarar sa tun yana ƙanƙanin sa , da ya fara girma ya mallaki hankali sai yana lura da ko ganin sa bata son yi sannan duk wani abu na farin-ciki idan ya same shi bata taya shi murna haka kuma na baƙin ciki , kai ko jinyar da yayi na kwanan nan ma bata taɓa masa ya jiki ba , bare ta jajanta masa , a duk lamuransa idan ba ɓacewar Falmata ba bai taɓa jin ta sanya bakin ta ciki ba ya daɗe da sanin bata ƙaunar sa .

"To amma anya hakan ya isa ya sa shi yarda da cewa Hajiya Mama Matar Mahaifinsa ita ce ta sace Matar sa ?

Girgiza kan sa yayi yana jin haÉ—uwar kalaman su su biyun masu cin karo da juna a can Maradi Hajiya Mama tace Maimounatou ce ta sa aka É—auke Fatima , anan kuma Maimounatou tace Hajiya Mama ce ta sa aka É—auke Fatima .

"Waye mai gaskiya a tsakanin su ?

Abu mafi girma da ya fahimta a tsukin lokacin shine wata ɓoyayyar alaƙa da take tsakanin su biyun da bai taɓa kaiwa ga sani ba .

Kalaman Maimounatou akwai ɓurɓushin gaskiya a cikin su Musamman cikakken bayanin da tayi masa kan lokutan da munanan al'umuran da suka faru a rayuwar sa suka fara faruwa .

"Ya zama dole na koma Maradi , na koma domin samun tabbaci tsakanin ƙarya da gaskiya .

Da sasaarfa ya juya yana barin wajen , Maimounatou da take zaune dirshan a ƙasa tana mayar da numfashi cikin wata irin murya tace "Youssouf ka min afouwa ka yafe min ka sake bani dama .

Tsayuwa yayi ba tare da ya juyo ba yace "Na sake ki saki Ukku Maimounatou kada kuma kiyi fatan abunda zai sake nuna mana fuskokin juna a zahiri .

Ihun da Maimounatou ta sa sai da ya ƙarade harabar ofishin kafin ya bar da'irar wajen yana iya jiyo hargowar ta tana ƙiran sunan sa .

"Youssoufa.
"Youssoufa ka dawo wallahi nayi nadama .

Bata taɓa sanin cikin wasanni ta ta haɗo da zuciyar ta ba sai a yau da Youssoufa ya rayu bayan so da tayi ta gille masa rayuwar sa ya kuma dawo ya sake ta irin sakin da babu kome , a dai-dai lokacin da ita kuma zuciyar ta ta haƙaƙe da cewa ta daɗe cikin mayen son sa tun tana ƙaryata kan ta akan haka har a ƙarshe ta saduda ta kuma shiga addu'a ka'in da na'in Allah ya tashi kafaɗun sa ya dawo su cigaba da rayuwar su .

haƙiƙa tayi asarar Miji irin wanda ba zata samu madadin sa ba . To wa ma zai sake auren ta ?

Kenan ita bata ci ribar kome ba sai fa ta lalacewar suna a idanun al'umma ta zama mujiya abar zunÉ—e .

Zuciyar ta taji tana wani irin narkewa da nadama marar iyaka , tsoron halin da zata tafi ta tadda a rayuwar gidan su na huda ta da tun da ta kwashi tsawon satika bakwai a kulle babu wanda ya leƙo daga gidan su ko wani dangi nata ta san cewa kurar ta tayi kuka ta kuma riga ta dusashe tayi duhu a idanun kowa na ta .

Kwanciya tayi a ƙasa tana wani irin kuka tare da jin yadda zuciyar ta ke zogi kamar zata fashe a tsukin lokacin zaɓar mutuwa take son yi akan rayuwar da zata tarar a gaba .

Kai tsaye Youssoufa ainashin cikin ofishin ya koma inda ya nemi da a ba shi takaddun neman belin waÉ—an da ake tsare da su .

Baya cikin nutsuwar sa ya ciccike inda ya bada tabbacin yin afuwa ga Masu laifin su biyu da ake tuhuma da yunƙurin kashe shi a matsayin sa na wanda suka yiwa laifin ya sanya hannun ya janye ya musu afuwa a sake su .

Bayan gajerar muhawarar da Youssouf bai bada hankalin sa ba ya ƙirgo wasu kuɗaɗe ya ajiye a gaban teburin ya miƙe yana barin wajen bayan sun yi Sallama.

A waje ya tarar da Bilal cikin motar direban da Mijin Ubbo ya turo ya ɗauke su idan sun gama bai shiga motar ba ya ƙira Bilal ya fito .

"Ka shigga ciki za'a fito da Mammadou ku tafi gidan ubbo tare ni akwai inda zan tai .

Bai jira amsar sa ba ya taka da sauri yana barin wajen .

Wani ƙaramin Hotel ya je ya kama ɗaki na kwana guda (HOTÈL TÉNÉRÉ) tun da ya shiga ɗakin ya kashe wayoyin sa yayi sallah yayi zaune tunaninnika na masa rubdugu .

ji yake kamar ya buɗi ido ya gan shi a maraɗi wani irin hali ya kasance a ciki tsawon ƙarshen yinin zuwa cikin daren da ya tsinci tsawon sa fiye da na darare uku a wajen sa .

Asubar farko ya miƙa mukullin ɗakin ya bar otel zuwa tashar mota .

Mota ta farko da ta tashi zuwa Maraɗi da misalin ƙarfe shidda na safe cif sun kama hanya tare da Youssoufa da ya kasa jiran karfe biyun ranar jirgi ya tafi da shi .

Ya zaɓi tafiyar motar saboda ya san duk inda ƙarfe biyu na ranar tayi yana cikin Maraɗi .

Maradi .

Tun ajiya da Hajiya Umma da shi kan sa Maimartaba suka kasa samun layin Youssoufa suke cikin fargaba duk kuwa da cewa sun yi waya da Bilal har ma da Mammadou cewar suna lafiya kuma Youssoufa ma yana lafiya sai dai su ma basu san inda yake ba kuma basu samun wayar sa.

Bayan addu'a babu abunda Hajiya Umma take yi saboda jikin ta yana bata wani abu ya faru ko kuma zai faru ko mai kyau ko marar kyau .

kuma kawo yanzu ta fahimci ƙaunar da ɗan ta yake yiwa Falmata marar misaltuwa ce ba yadda ta iya dan dole ta fara addu'ar Allah ya bayyana Fatima ko dan Youssouf ya samu nutsuwa .

Ga Hajiya Mama kuwa yau ranar farin-ciki ce a wajen ta dan kuwa har 'yar ƙaramar walima ta haɗa na farin-cikin dawowar ɗan ta mafi soyuwa a wajen ta da aka yiwa sharri aka garƙame ta gayyaci ƙawayen ta na ƙud da ƙud dan su zo taya ta murna .

Matar Mammadou da ake ƙira Zainaba ita ma a nata gidan sai murna tare da shirin taryar Mijin ta .

Kamar kullum yau ma bayan an tafi Sallar Azahar Hajiya Mama ta kashe jiki ta nufi shiyar Hajiya Uwa ta buÉ—e ta shiga .

Ƙarfe biyu saura mintuna goma taxi da ta ɗauko Youssoufa daga tasha ta sauke sa baya cikin nutsuwar sa ya biya mai taxi .

Da sassarfa yake taku ya nufi cikin gidan kallo É—aya zaka masa ka matsa daga hanya ko da kuwa ba ka san ko shi wanene bane .

Ta gaban Fada ya zo ya wuce akan idanun Maimartaba da kowa na cikin fadar wanda hakan shine na farko da Youssoufa ya zo ya wuce ta gaban Mahaifin sa bai ƙarasa ya gaishe shi ba , abu ne da bai faruwa mutum ya taka ƙofar fada bai shiga ya kai gaisuwa ba .

Shiru Fadar ta ɗauka kafin cikin abunda yake ƙasa da mintuna biyu wani daga cikin manyan bayun gidan ya taho a sukwane ya yi gurfano yana kai gaisuwa kafin ya ɗora da cewa "Ran Sarki ya dade yau da alamun ɓacin-rai mai girma ga Yarima Biyamuradi domin kuwa ga shi can riƙe da bindiga a tsirarar ta ya nufi shiya......

Miƙewar da Maimartaba yayi babu shiri ita ta sa sauran 'yan Fada suka miƙe tsaye su ma su na cewa "Allah ya huci zuciyar ka jagoran Al'umma Yaa Sarkin mu mai Adalci .

Cikin É—ago taku Sarki Abdoul-azizou ya wuce gaba bayan yace "mu tai ka min jagora zuwa inda yake .

Hajiya Mama da Biyamuradi Youssouf ƙiris ya rage su ci karo a tsakanin hanyar sashin Hajiya Uwa ,

ita tana fitowa shi kuma yana ƙoƙarin shiga da sauri ta jaa baya idanun ta a waje take bin sa da kallo .

Shi ma tsare ta yayi da ido yana bin ta da wani irin kallo mai kaifi da yasa nan take laɓɓan ta suka ɗauki rawa kamar wacce take gaban alƙali .

"Kai..kai kuma la..lafiya ? Ina..ina za ka tai ?

Bai amsa mata ba ya wani irin kewaye ta ya wuce , wani mummunan bugu zuciyar ta ta hau yi ganin inda ya nufa kai tsaye ƙofar falon Hajiya Uwa .

Taƙi barin fargabar da take bin duk lakkar jikin ta tana kassarawa tayi nasarar duƙusar da hanzarin ta , ta bi shi da ɗaga takun da ta ƙara da gudu ta sha gaban sa lokacin da yake ƙarasawa gaban ƙofar ta shiga tsakani sa da ƙofar ta raba hannuwan ta cikin wata irin buɗaɗɗiyar murya tace

" Ba zaka shiga ba ka koma inda ka fito nan ba hurumin ka bane , nace ka koma.

Idanun sa da suka yi jawur ya É—ago yana kallon ta da wani irin yanayi da ya fara fita a saiti na hankalin sa ya sanya hannun sa É—aya ya ture ta gefe tayi taga-taga zata faÉ—i amma ta tokare.

Sai dai me ? Ture ta da yayi da ƙarar ɓalla ƙofar da yayiwa duka ɗaya da kafar sa ya shiga falon basu ruguza mata zuciya kamar taron mutanen da ta hango sun yi ɗango suna tahowa ba wanda halin ɗimuwar da take ciki bai hana ta gane Maimartaba , Hajiya Umma tare da kakaf 'ya'yan su da suke gida a dai-dai lokacin zuwa manyan bayu da ma ƙanana da suke danno musu baya ba .

Jin ƙarar kamar Youssoufa yana karya wata ƙofar ya sa ta runtumawa da gudu ta faɗa falon ba tare da ta damu da taron mutanen da suke iya hango duk abunda yake faruwa ba , hankalin ta a dai-dai lokacin ya kasa yarda da abunda ke shirin faruwa da ita .

Tana shiga ta riƙo rigar Youssoufa ta baya tamau ta cukuikuye shi ta hana shi shiga ɗakin da ya riga ya karya ƙofar kawai sai ta saki wani irin ihu dai-dai da shigowar Maimartaba .

"Maimartaba ka hana shi ka hana shi nace wayyo Allah na , nace ka hana shi kar ya min lahani ga rayuwa ta.

Wata irin fincika da Youssouf ya yiwa rigar sa sai da ya kai Hajiya Mama ƙasa da sauri Hajiya Umma ta tare ta cikin ɓacin rai tace

"Kai Youssoufa mene ne kake yunƙurin yi hakka ? Hala bakka cikin hayyacin ka ?

Bai saurari kowa ba sabod idanun sa daga na zuci har na zahiri a makance suke.a lokacin ƙudirin da yake gaban sa kawai yake son cimmawa .

Yana danna kai a ɗakin ya shiga yin fatali da duk abunda ya tarar a cikin ɗakin da bai wuce wasu itatuwa da wasu ƙwarrai da babu kome a cikin su ba.

Dube-dube ya shiga yi har idanun sa suka sauƙa kan wardrobe irin ta jikin gina na shekaru aru-aru .

Duk da ƙarfin da yake da shi da jarumta irin na sojin ƙwarai da kyar ya iya buɗe ta ya shiga yawo da idanun sa a ciki lokacin da Hajiya Mama ta sake yin kukan kura ta kufce daga Hannun Hajiya Umma ta faɗa ɗakin .

Idanun sa suna sauƙa akan wata ƙatuwar ƙwarya da take ajiye daɓas da duwawun ta bata wani tangaɗi ba'a ce ƙwarya bace lokacin kuma Hajiya Mama ta sake riƙo rigar sa ta baya cikin wata irin murya mai firgitarwa tace

" Kar ka taɓa , wallashi ina kashe ka idan ka taɓa .

Kalmomin ta suka sauƙa a kunnuwan Maimartaba da Hajiya Umma da suke shigowa ɗakin sauran mutane na biye da su domin kowa ya shiga ɗimuwa tare da ƙaguwa kan son fahimtar wai me yake shirin faruwa ?

Hannun sa biyu ya sa ya cicciɓi ƙwaryar yana juyowa Hajiya Mama ta jawo rigar sa da iyakar ƙarfin ta da har sai da ta ɓarke .

Ƙwaryar kuma tayi tangal-tangal a hannun sa lokaci ɗaya ya sake ta ta tafi baki ɗaya ta kwaranye a rabin jikin Hajiya Mama kafin ta kai ƙasa ta tarwatse .

Wani fitinanne wari marar daÉ—i da yake tada hankali ya cika É—akin da yasa sai da kowa ya toshe hancin sa wasu suka yi baya da sauri .

Maimartaba da yake tsaye ƙiƙam da idanu ya bi wasu kwaɗi biyu da suka fito daga cikin ruwan mugunyar sai tsalle suke suna neman wajen ɓuya .

Kafin yayi wani yunƙuri Liman da shi ma hankalin sa ya kai kan su nan take ya fara addu'a .

Chak suka tsaya suka bar tsallen yayin da warin da ya cika wajen kuma ya fara raguwa sai tsamin giyar burkutu da ya maye gurbin warin gum kai kace a tsakiyar gidan Madam Saly -fara ake .

Umarni yayiwa wasu bayi biyu da su ɗauke su su fita da su su riƙe .

Jin haka yasa Hajiya Mama da tayi suman tsaye tun lokacin da ƙwaryar ta fashe cikin wani irin sauti mai faɗi fashe da matsanancin kuka tana duban jikin ta cikin tashin hankali da wasu zuƙa-zuƙan tsutsotsi da suke yama-yama a cikin ruwan suka hau jikin ta .

Ihu ta sake kurmawa lokaci guda ta fara cewa "ku bani ruwa dan Allah kar su shige min cikin jiki wayyo Allah na shiga uku , Youssoufa Allah shi tsine maka É—an bala'i .

Jikin sa yana mazari ya taho gaban ta ya tsaya yana gyara riƙon bindigar sa yace

"ina Mata ta ?

"Ina kin ka kai min Mata ta ?

"Ina Mata ta nake tambayar ki ?

Bangaje shi Hajiya Mama tayi cikin yanayin da yake nuna ta daina fahimtar kome da gudu ta nufi hanyar fita mutane suka dare a tsorace suka buÉ—a mata hanya ta fita a guje .

Wani irin duka Youssouf ya shiga kaiwa bango da hannun sa yana wani irin huci gaba ɗaya jijiyoyin jikin sa sun miƙe yana wani irin tsuma da duk ya tsorata mutanen wajen .

Nan take hawaye ya fara sauƙa a fuskar Hajiya Umma .

Maimartaba ne ya tako a hankali ya dafa kafaɗun sa kafin ya zarce da riƙe hannun sa da har ya fara fitar da jini .

"Innalillahi wa inna ilahi raji'oon ,Lahaula wala kuwata illah billah huwal aliel azim ya fara maimaita masa cikin nutsuwa kafin ya kai hannu ya zare bindigar da yake riƙe da ita a ɗayan hannun sa .

Wani irin kuka ya fashe da shi yana damƙe hannun Maimartaba da yake cikin nasa yace " Baba me na mata ? Meyasa ta min hakka ? Itta ta ɓata min rayuwa ta tayi sanadin da suna na ya ɓaci ƙima ta ta zubbe , iyayena sun ka yi fushi da ni , Baba me na mata ?

" Ka ƙira ta ta dawo ta faɗi inda ta kai Mata ta , Ita tayi enlevé na Fatima

" Me Fatima ta mata zata badda ta ? Ina ta kai Fatima ?

Ya ƙara cewa haka da wata irin buɗaɗɗiyar muryar da tayi amsa kuwwa a baki ɗayan sashin .

Falmata da take tsakiya da yin kuka cikin tsoron ko Hajiya Mama ta turo mata Aljannu ne su kashe ta kamar yadda ta faÉ—a mata a yanzu? domin da ta shigo ta ji tana karatun Alkur'ani .

Shine ta mammake Mata baki ta ɗora da tsorata ta da cewa zata mata turen ifiritai su zuƙe jinin ta muddin ta sake karatun kur'ani .

Jin tashin muryar Youssouf yana ƙiran sunan ta ya sa ta zabura ta miƙe zafin da ya ratsa ƙafar ta ya sa ta saurin komawa ta zauna wasu sabbin hawaye na sake zubo mata .

Da rarrafe ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ta soma bubbugawa da ƙarfi tana ƙiran sunan Youssouf .

Da gudu Youssouf É—in ya fito saboda shirun da wajen ya É—auka ya bashi damar jin muryar ta a kusa .

Duka ɗaya ya yiwa ƙofar ta karye da ƙiris ya rage bai faɗa mata akai ba .

Yana shiga ɗakin ya zube guiwowin sa a ƙasa ya ɗago ta "Fatima-Zahra Est-ce que ça va? Alhamdulillah , Alhamdulillah '

Wani irin kuka ta fashe da shi tana ƙan-ƙame shi kamar zata koma jikin sa cikin kuka ta fara cewa " Dan Allah ka fitar da ni anan ka mayar da ni gida wajen Mamana, waccan matar ita ce ta kawo ni nan ta kulle ni yau kwana huɗu tace min zata kashe ni ,idan na yarda nayi magana , kai ma ita ta yi ma asiri kai da Yakaka ita tayi , ita tayi muguwa ce bata da kirki ....

Jijjiga ta yayi da sigar rarrashi yace "va bien mon amour Votre protégé en toute sécurité maintenant babu abunda zatta sake iya yi miki kin ji Fatima ki nutsu ki daina kuka ? Tayi miki ciwo ? Ina yake miki ciwo ?

Ya furta hakan yana ɗaga kallon sa zuwa kan Maimartaba da Hajiya Umma waɗan da suke ganin kome kamar a shirin film wai Hajiya Saratu da suke rayuwa da ita shekara da shekaru ita ce ta yiwa ɗan su duk wannan mugun ƙullin ?.

Ko Hajiya Umma bata taɓa zaton sharri da muguntar Hajiya Saratu , bayan irin mummunan asirin da ta yiwa ɗan ta har ya kai da zata iya enlevé surukar ta ?? Wacce irin ƙiyayya ce wannan Hajiya Mama take mata ?

Da hannu Hajiya Umma ta ƙira Ubbo da Siyama waɗan da suma suke tsaye kasaƙe kamar ruwa ya cinye su tace " ku kama ta zouwa sashi na .

Cikin sauri Youssouf ya girgiza kai kafin yace " zan tai da ita da kaina.

Gyaran murya Maimartaba yayi kafin yace

" bar su su tai da ita kai kouma ka biyo ni .

Daga haka ya juya bayu da sauran al'ummar gidan da har kawo yanzu babu wanda ya iya cewa ƙala wasu suka rufa masa baya .

Youssouf bai saki hannun Falmata ba duk da cewa tun da ta ji muryoyin mutane a wajen ta raba jikin ta daga na shi amma ya ƙi sakin hannun ta .

Har Sai da Hajiya Umma ta kama hannun Falmatan ɗaya ta rike sannan tace masa " ka tai ga ƙiran Mahaifin ka , itta tana ƙarƙashin kulawata .

A hankali ya miƙe yana waiwayen Falmata da ta sunkuyar da kan ta ya fita zuciyar sa cike da jin tausayin falmata da ya lura har rama tayi ta fita a kamannin ta duk wai a sanadin sa Hajiya Saratu ta mata haka ?

Ubbo da kan ta ta haÉ—awa Falmata ruwan wanka kamar yadda Hajiya Umma ta umarce ta ,

Hajja wacce yau ta samu damar shiga har uwar ɗakin Hajiya Umma tana sharar hawaye tace " mu je na gasa miki ƙafar ta ki uwarɗakina ko kya ɗan ji daɗin ta sannu kin ji Allah ya miki sakayya .

Hajiya Umma da take kallon Falmata cike da tausayi cikin ran ta wani irin yanayi take ji zuwa yanzu ta fara yarda da cewa kamar da sakacin ta har Hajiya Mama tayi nasarar kama Falmata yarinyar da zuwa yanzu ta fahimci da ita da danginta baki ɗaya basu da wata alaƙa da halin da rayuwar ɗan ta ya kasance a ciki kamar yadda take zato a baya , ashe Hajiya Mama ita ce mafarin kome ba Falmata da 'yar uwar ta ba .

Fuskar ta bata ɓoye halin da zuciyar ta ke ciki ba tace " kar a taɓa mata ƙafar za'a ƙira mai gyara yazo ya duba idan ma kuma asibiti za'a kai ta sai a tafi .

Ɗan lankwasa kai Hajja tayi tace "to bari a jira , O' ni hauwa'u yau na ga kura da fatar akuya ganin idona , wasu mutanen launin hankaka ne da su gaban su fari bayan su baƙi ai ba ƙaramin marar imani bane zai yi kinnafin ɗin ɗan adam ba , yo ai tazarar da take tsakanin kinnafaa da boko haram kaɗan ce , Allah ya raba mu da miyagun mutane .

A hankali Hajiya Umma ta amsa da "Amin dai , tana mayar da kallon ta kan Hajja.

A can ɗakin ganawa ta musamman Maimartaba tare da manyan mutanen Fada nasiha suka dunga yiwa Biyamuradi Youssouf suna tausar zuciyar sa , sun gwada masa girman haƙuri tare da matsayin da mutanen da Allah ya yiwa baiwa da haƙuri suke shi tare a gurin sa

da kusanci da haƙuri ke kawo wa tsakanin Mutum da Mahalccin sa Sannan suka jawo masa ayoyi da hadisai .

A ƙarshe suka bashi tabbaci kan cewa jarabawar Rayuwa ce Allah ya masa domin ya gwada ƙarfin imanin sa dan haka ya bar kome ga Ubangiji da idanun sa zai ga sakayya .

A hankali ya dunga jin nutsuwa na safko masa da kafin wani lokaci ya ji baki ɗaya zuciyar sa ta sauƙa wani irin nutsuwar da ya jima bai ji irin ta ba tana safko masa .

Liman da yake malami masanin Alkur'ani ya cigaba da cewa

"sannan shi sihiri gaskiya ne da masu aikata shi kaÉ—ai suka yi imani da shi ,

"babu shakka cikin kur'ani duk wani magani da warakar kowacce cuta yake dan haka ga ayoyin Alkur'ani masu warware sihiri zan faɗa maka idan za ka iya kayi da kan ka Yousssouf idan kuma ka gaza ka bayar a yi maka ina mai tabbatar maka da cewa dukkanin wani sihiri da anka maka sai ya karye da iznin Allah sannan kuma Allah zai baka kariya daga dukkanin wani mgunta da za'a sake nufar ka da shi ta hanyar sihiri ba zai yi tasiri akan ka ba, ka samu takarda da alƙalami ka rubuta a yanzu Youssoufa ayoyin sune kamar haka :

1). Ta'awwizi da Basmala.

2). Fatiha kafa 7.

3). Aya biyar Ta farkon Suratul Bakara sau 7.

4). Ayoyi biyu ta tsakiyan suratul Bakara wato - Wa ilahukum ilahum wahid la'ilaha illa huwa har karshe sau 7.

5). Ayatul kursiyyu Suratul Bakara aya ta 255 sau 7.

6). Ayoyi uku a karshen Suratul Bakara wato daga baikin Amanarrasul Bakara 284-286 sau 7.

7). Shahidallahu a chikin Al Imran aya ta 18 da 19 sau 7.

8). Inna Rabbakumullahi Ladhi khalaqas samawati wal ardh.. acikin Suratul Al'araf aya ta 54 da 56 sau 7.

9). Afa hasibtum Annama khalaqanakum Abasan suratl Mu'minin aya ta 115 da 118 sau 7.

10). Wa Annahu ta'ala Jaddu rabbina mattakhadha..." a cikin Suratul Jinni aya ta 3 zuwa ta 9 shima kafa 7.

11). Aya goma na farkon Suratul Saffat shima sau 7.

12). Aya Uku na karshen Suratul Hashri wato "Lau anzalna hathal Quran.

13). Aya ta 10 na karshen suratul Yasin su ma sau 7.

14). Kulya ayyuhal kafirun sau 7.

15). Qul huwallahu ahad sau 7.

16). Falaqi sau 7.

17). Nasi sau 7.

A rika tofawa a ruwan zamzam ko ruwan sama ko ayi a duka biyun amma dabam dabam a samo ganyen magarya a dandaka guda bakwai-bakwai har gida 7 wato na kwana 7 Safiya da maraice ana sha ana shafe jiki dashi.

Da fatan ka Fahimta Yossoufa ? Sannan a kome kake kada kayi wassa da ibadar ka domin itta ɗin kariya ce mai girma daga dukkanin abun ƙi , ka faɗaɗa ibarda ka yalwata ta , sannan ka yawaita sadakha domin ita ma kariya ce .'

Youssouf da yake gama rubutu ya É—ago kan sa fuskar sa a nutse yace" na fahimta Malam kuma Nagode Allah shi saka da alkhairi .

Daganan ya baro sashin maimartaba bayan ya musu godiya mai tarin yawa , ya bar su suna cigaba da tattunawa .

Sashin sa ya nufa kai tsaye yayi wanka ya ɗaura alwalar sallar la'asar zuciyar sa da take cike da tausayin Falmata da son sanin halin da take ciki ta sa shi dole ya miƙa hanya zuwa sashin Hajiya Umma .

A zaune ya tarar da Hajiya Umma , a falon ta na ciki da Hajja sai kuma Ubbo suna sake jimamin lamarin banda ɓarin nauyayan kalmomi babu abun da Hajja take yi da lokaci-lokaci ubbo kan yi dariyar wasu kalmomin na Hajja .

Zuciyar Hajiya Umma ta sanyaya da ganin Yousouf ya dawo cikin nutsuwar sa har ma ta gagara ɓoye jin dadin ta .

Tayi hamdalah a bayyane .

Bayan sun gaisa ta ɗan dube shi kafin tace " ƙafar Fatima da akwai ciwo domin kouwa da kyar take iya takawa duk da dai na mata tambayoyi cikin amsar da ta bayar tacce bata da wata damuwa sai ta ƙafar da daman akwai tsohon targaɗe a gurin kuma ta sake gurɗewa dan haka nayi magana a ƙira mai gyara a duba ƙafar ko kuwa asibiti za'a ?

Cike da jin daÉ—in kulawar da ta nuna a karon farko ga Falmata , Youssouf yace "duk wanda kin ka ga yafi dacewa Umma.

"Ka shiga ciki ka gan ta suna É—aki tare da Siyama.

A bisa ɗaya daga cikin gadajen Hajiya Umma biyu da suke ɗakin ya hango ta a zaune tayi wankan ta fes jikin ta sanye da doguwar riga ta atamfa daga gefe Siyama ce a kusa da ita hannun ta riƙe da wani ɗan kyakkyawan tasa ( Bowl ) da aka zuba ferfesun ƙaza a ciki da chokala biyu a ciki fork da soup spoons,

Ganin shigowar sa bai sa Siyama ta fasa kai soup spoon É—in da ta cika da ruwan ferfesun bakin Falmata ba sai dai ta amsa sallamar sa da murmushi akan fuskar ta .

Ƙarasowa bakin gadon Youssouf yayi ya zauna a ɗaya gefen yana bin ƙafar Falmata da kallo wanda ta kumbura daga idon sawun .

Kallon sa ya mayar ga Siyama yana jifatan ta da É—an kyakkyawan murmushi yace

"Siyama kina gatata ƙamnar ki hakka ? Da har kin ka ciyar da ita ba tare da ni kin tuna da cikina ba ?

ÆŠan murmushi Siyama tayi kafin tace " ai itta a yanzu marar lafiya ce kai kouwa ka samu waraka insha Allah .

Murmushi yayi yana mayar da ganin sa kan Falmata yace "Fatima yaya ƙarfin jiki ? Ina ke miki ciwo bayan sawun ki ?

Cikin 'yar ƙaramar murya tace "ba ko'ina sai ƙafar tawa.

Tashi yayi daga bakin gadon ya ɗan yi durƙuso kafin ya kama ƙafar falmata a hankali ya ɗago ta ,

Ganin haka yasa Siyama tayi saurin miƙewa bayan ta ajiye kwanon hannun ta akan ɗan teburin gefen gado (bedside cabinet) .

Ta nufi ficewa daga É—akin " Maman Yumna ina za ki tai ?

Youssouf ya furta haka yana bin ta da kallo

Lumshe idanun ta tayi ba tare da ta jiyo ba tace " zan tai na kawo ma abinci .

Daga haka ta ƙarasa barin ɗakin tana jin yadda suke kokawa tsakanin ta da zuciyar ta da take son ganin baƙin Youssouf da Falmatan.

A hankali ya mayar da ganin sa kan ƙafar Falmatan ya kai ɗan yatsan sa babba ya shafa gurin da ya ɗan kumbura a hankali da yasa Falmata rufe idanun ta a hankali tana jin yadda tsiƙar jikin ta ke tashi tare da wani yanayi da take ji na tausayi mai girma yana huda zuciyar ta , yana bin duk wani saƙo da lungu da ɓurɓushin jin haushin Youssoufa ya maƙale a ran ta kan laifin da take zaton duk yayi su a bisa son rai cikin sanin sa da yin kan sa .

Ji tayi laifukan sa na gogewa suna shafewa , ƙaunar sa , son sa , tare da tarin tausayin sa masu nawin da bata taɓa jin makamancin su ba saboda ji da tayi kamar zuciyar ta ba zata iya ɗauka ba , kamar sararin dake ran ta yayi kaɗan.

da wani irin tasiri mai girma suke maye gurbin duk wani ɗan taƙi da ta bar wa soyayya mallaki a cikin ran ta .

Tasirin so da take ji a lokacin ya fi ƙarfin rarraunar zuciyar ta da take sabon shiga a fagen soyayya .

Ɗago da kan sa yayi yana kallon ta bayan ya gama tofa mata addu'o'i a ƙafar ta .

Ya ɗan dau lokaci yana kallon ƙaramar fuskar ta da take sake zama 'yar firat yana jin tausayi tare da wannan son nata mai yawa yana masa yawo a zuci .

Jin sa shiru ya sa ta buÉ—e idanun ta a hankali suka haÉ—a ido .

"Sannu Fatima insha Allah za ki samu sauƙi kin ji kou ?

GyaÉ—a kan ta tayi

A hankali ya miƙe ya ƙarasa ya ɗauki bowl ɗin da Siyama ta ajiye ya dawo ya zauna , ya fara bata ferfesun tana ci a hankali , har sai da ta ɗan ci dayawa kafin tace masa "ta ƙoshi .

Bayan ya ajiye kwanon ya dawo ya zauna tare da riƙo hannun ta ya sarƙe 'yan yatsun su waje ɗaya "Fatima kiyi haƙuri da abunda ya same ki Allah zai miki sakayya cikin gaugawa kuma insha Allah zan zamar miki garkuwar da babu wanda shi issa ya taɓa ki a rayuwa na ƙyale shi , kiyi haƙuri Fatima .

Matsa hannun sa da yake cikin nata tayi kafin ta É—ago kan ta tana saka idanun ta cikin nashi tace " Meyasa bata son ka haka ?

"Nima ban sani ba Fatima cikin rayuwata ban taɓa yi mata laifi ba amma ta zuba min ƙiyayya mai zafi da har da taimakon ta anka nemi raba ni da raina bayan ita ta gurgunta rayuwata ta rarraba ƙiyayyar da take min tsakanina da ɗiyan ta da suke 'yan ouwana .

Kan ta ta mayar ta kwantar a ƙafaɗar sa tana kaucewa kallon cikin idanun sa da suka fara sauya launi tace

"Kayi haƙuri ƙiyayyar ta ba za ta sa ko ta hana kome ba sai fa abunda Allah ya rataya alhakin faruwar sa akan ta .

"Idan ita bata son ka Allah da Manzon Allah su na son ka , Maimartaba yana son ka , Umma tana son ka sauran 'yan uwanka suna son ka , Siyama tana son ka , yaran ka ma zasu so ka .

ÆŠan jim tayi kafin ta É—ago kan ta tana kallon cikin idanun sa tace " kuma ni ma ina son ka , Ina son ka , ina son ka dayawa .

A bazata ya tsinkayi kalmomin da bata taɓa furta masa ba , zuciyar sa tayi wani ɗan ƙaramin zillo da yasa shi sake ɗago fuskar ta da sauri ya riƙe ta yana kallon ƙwarar idanun ta , muryar sa a tsakani maƙoshin sa yace "me kika faɗi Fatima sake faɗi naji ? Maimaita min ?

"Ina son ka dayawa dayawa ba adadi
Ta sake furta hakan tana kallon fuskar sa cikin ranta " godiya take yiwa Ubangiji da idan ba shi ba da ƙarfin ikon sa wa ya isa mallaka mata wannan mutumin ma'abocin kyau da cikar zati tare da kyaun nasaba ?

Muryar sa tana sake nitsewa saboda ƙasa da yayi da ita yace "dagaske Fatima ?

Hannuwan ta tasa akan nasa kafin tace "da duk gaskiyar zuciyata ina son ka dayawa ,

Wani irin sanyi yake ji tun daga ƙasan ran sa yana taso masa yana nitsar da idanun sa cikin nata yace " son da nake miki yafi wanda kike min yawa Fatima , son da nake miki ba shi da iyaka , ni ban san iyakar sa ba, kin yarda na gwada miki ɗigo dagga cikin sa ?

Kan ta ta gyaɗa masa tana murmushin da yake bayyana haƙoranta ,

Tazarar dake tsakanin su ya haɗe yana manne fuskar sa da ta ta , tare da shauƙin son da suke yiwa junan su suka himmantu wajen gwadawa junan su tatatciyar soyayyar da suke yiwa juna .

Ƙwanƙwasa ƙofar da Aka yi yasa su sa rabuwa da jikin juna ,

Ba'a jinkirta ba aka murɗo ƙofar a hankali ta shigo bakin ta ɗauke da Sallama .

Siyama ce ta shaida musu zuwan mai gyaran ƙafa .

Yousaouf ya masa iznin shigowa bayan ya gyara mata mayafi.

Ba ƙaramar azaba Falmata ta sha ba kafin ƙashin da ya fita ya koma saboda tsamin da ƙafar tayi kwana huɗu da targaɗe .

Siyama da Youssouf su suka dunga rige-rigen share mata hawaye da gumin da ta haÉ—a sharkaf duk kuwa da sanyin É—akin .

Bayan ta dawo cikin nutsuwar ta lokacin Youssouf ya bar ɗakin daga ita sai Hajja da ƙaramar murya ta cewa Hajja " Hajja ki bani wayar ki zan ƙira Mamana da Yakaka .

ÆŠan jim Hajja tayi kafin da sigar rarrashi tace "UwarÉ—akina Amma fa kar ki shaida musu abunda ya faru da ke domin ba'a sanar da su ba tun da Allah yasa kin fita lafiya kar ki faÉ—a musu kuma zuciyar su ta kasa nutsuwa da zaman ki anan .

"Ba zan faÉ—a musu ba Hajja kawai so nake naji muryar su mu gaisa .

"To babu laifi ga wayar ki ƙira su .

Sun jima suna Hira da ita da iyayen ta Khaalty Rahima da Amnee inda har suka yi ƙorafin cikin kwana biyun sun yi ta ƙiran layin Hajja bata ɗauka musamman ma a jiya da Yakaka ta koma Abuja .

Cikin É—oki Falmata take sake tambayar su 'Yakaka ta tafi gidan ta ?

Amnee ta bata amsa tana dariya da cewa "jiya suka tafi tare da yayan naku takwarata an zama 'yan Abuja ( kamar Ammi Haseen 🤣)

Cikin zaƙuwa Falmata ta fara ƙiran layin Yakaka bayan sun yi Sallama da su Amnee.

Sai dai ƙira biyu tayi ba'a ɗauka ba , yamutsa fuska tayi tana sake danna ƙiran take mitar " Yakaka ko ina ta ajiye wayar ???

ABUJA NIGERIA

Kai-kawo Yakaka ta cigaba da yi a cikin banɗakin da take tsaye , karo na barkatai ta sake sunkuyawa tana leƙe ta ƙafar ɗan makulli , da sauri tayi baya tana sakin wani ƙaramin ihu ƙiris ya rage ta faɗi saboda santsi jikin ta na karkawa ta dafe ƙirjin ta tana mayar da numfashi .

Idanun ta ba ƙarya suka mata ba tirƙeƙen karen da take hangowa tun safe a can nesa daga tsakiyar ɗakin wani lokaci kuma ta hango shi a gefe shine ta gan shi daf da ƙofar a yanzu kamar ma shima leƙen ta yake ta inda take leƙawa dan babu shakka sun yi ido huɗu ita da shi..

Zamewa tayi ta zauna a ƙasa dirshan cikin banɗakin daga inda take tana iya jin wayar ta dake ƙara lokaci zuwa lokaci tsawon yinin amma ba damar fitowa ta ɗau wayar saboda tirƙeƙen karen da yake ta shawagin sa a ɗakin har gado yake hawa yana sauƙa .

A hankali ta saki wani sabon kukan da aƙalla tayi irin sa fiye da sau goma daga safe zuwa yanzu da ta tabbatar yamma tayi rana kuma tana gaf da faɗuwa .

Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kuna lafiya ?

Yau dai bakina da goro ba zan ce kome ba bayan fatan alheri da nake muku a koyaushe.

Nagode.[3/7, 3:55 PM] +234 706 503 6187: Mafari
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

52

Ƙarar Turo ƙofar daƙin da Yakaka ta ji yasa ta tashi da sauri daga inda ta rakuɓe tana kuka ta zo jikin ƙofar ta ƙafar ɗan makulli ta leƙa .

Sofi ta hango ta shigo, duk da halin firgicin da take ciki bai sa ta kasa ganin irin kwalliya ta É—aukar magana tare da jaan hankalin duk wani É—a namijin da ya É—ora idanun sa akan ta ba da Sofia tayi .

Wani ɗan fito Sofi ta yiwa ɗirkeken karen nan ( Working dog ) sai ga shi ya dako tsalle daga kan gadon da Yakaka bata san yaushe ya haye ba , ya taho jikin ƙafafun Sofi yana kaɗa jela tare da sunsuna ta .

Ƙaramar dariya Sofi tayi kafin ta ɗan yi sunkuyo ta shafa kan karen da farin ciki a sautin ta tace " oh Sam do you know how handsome you are ? You've got the best underbite, and the best butt muscles , Oh Sam I Love you , you really did a good job baby.

Lokacin da ta ɗago kan ta wata ƙatuwar harara ta wurga a saitin ƙofar banɗakin kafin ta jaa wani dogon tsaki tana juyawa akan ƙafafun ta Sam ya bi bayan ta da ɗan gudun sa suka ƙarasa ficewa a ɗakin.

Wata doguwar ajiyar zuciya Yakaka ta jaa tana dafe ƙirjin ta kafin ta ƙarasa zama a ƙasa tana jin wata 'Yar nutsuwa na safko mata, "Anty sofi Muguwa ce , ta aiyana hakan a cikin ran ta lokacin da ta tuno yadda tsakanin su yakasance a ɗazu da safe bayan fitar Doctor Hamza da yayi sammako ƙarfe shida na safe ya bar gida .

Bayan fitar sa ta tashi tana son tattara ɗakin kafin ta fita gaishe da Sofi ta dawo ta hau gado ramuwar baccin gajiyar hanya da suka sha saboda a jiya basu iso gidan ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare dan haka ko da Matar gidan basu gaisa ba .

Ƙarar turo ƙofar da aka yi yasa ta ɗago kan ta Sofi ta gani jikin ta da rigar baccin da take bayyana rashin kamun kan ta a sarari kan ta ko ɗan kwali babu , da sauri ta sunkuyar da kai tana janye ganin ta .

Ta buɗe baki da nufin gaishe ta kalmomin ta suka ƙaƙare lokaci ɗaya numfashin ta ya shiga kai kawo yana ƙoƙarin fisgewa daga jikin ta lokacin da tayi ido huɗu da wani ƙaton mummmunan baƙin kare da ya taho yayi tsaye a bayan Sofi kamar ɗan matashin zaki .

Kamar wacce aka soka da tsinin mashi ta tsala wani irin ihu lokaci ɗaya kamar mai fiffike ta hau saman gadon ta maƙure a ƙarshen gado ko'ina na jikin ta rawa yake yi .

Da hannu ta shiga nunawa Sofia karen wacce tayi tsaye kiƙam tana kallon ta tashin hankalin da take ciki a lokacin ya hana ta fahimci yanayin da ke kan fuskar Sofi , ko kalma guda ta gagara fitowa daga maƙoshin ta sai da hannu take ta nuni tana wani irin takure jiki .

Wata shashashar dariya Sofi tayi kafin tace "Ah Amarya ya da ihu da karkawa haka ? Sam ne fa ya zo yiwa sabuwar uwarÉ—akin sa sannu da zuwa.

'Sam .

Sofia ta ƙira shi sai ga shi ya zagayo daga bayan ta ya tsaya tare da zubawa Yakaka jajayen idanun sa da yasa fitsari fara bin ƙafar ta .

Wani ɗan guntun abu da har yanzu bata san mene ne ba , shi Sofia ta wurga mata a jiki da yasa karen yin wani irin tsalle sai ga shi akan ta yana buɗe haƙora .

Daga lokacin bata san me ya kuma faruwa ba kawai sai farkawa tayi ta gan ta a ƙasa a yashe kusa da ƙofar banɗaki da ta miƙe zaune tana ƙoƙarin tuno abunda ya faru , tunanin nata bai je ko'ina ba haushin da karen ya yi yasa ta neman wajen tsira da ta faɗa cikin banɗaki ta rufe .

A ciki ta ƙarasa tuno kome da ya faru kamar yadda ta gama yinin ranar a ciki , ba cin abinci , ruwa ma na banɗakin take tara daga fanfo ta sha .

Tana sharar hawaye ta sake sunkuyawa ta leƙa sai da ta tabbatar babu kowa a ɗakin sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta leƙo tana sake dube-dube .

Da ta tabbatar babu kowa sai ta fito a hankali tana jin yadda jiri ke safko mata saboda mummunar yunwa da take ji rabon ta da abinci tun jiya a hanya da ta ɗan tattaɓa abincin da Doctor Hamza ya saya mata da ba wani na kirki ta saki jiki ta ci ba saboda 'yar kunyar nan ta Amare .

Kai tsaye babbar jakar kayan ta ta nufa wanda ta zuba kayan ta masu amfani a ciki ta ɗau pad ta koma banɗakin ta gyara jikin ta , lokacin da ta fito bakin gado ta zauna ta rafka tagumi ɗakin da kan sa tsoro yake bata gefe guda kuma tana tsoron fita falon , ɗan kasa kunne tayi ta fara jin kamar muryar Doctor Hamza daga falon , tsam ta miƙe ta nufi ƙofar kai tsaye ta murɗa .

Abun da ta hango ya sa tayi turus! Sofia ce a zaune ɗare-ɗare akan ƙafafun doctor Hamza tana iya hango haɗuwar fuskokin su daga inda take tsaye , cikin sauri ta janye ganin ta daga kansu saboda a lokacin ita yunwar da take ji yafi kome damun ta musamman da yakasance tana Menstruation period dan haka wata irin gigitattar yunwa take ji .

Da dabara Doctor Hamza ya janye fuskar sa daga ta Sofi wacce tun yana sanya ƙafa cikin falon ta bi ta kanainaye shi da kissa ta katse masa hanzari da zumuɗin da ya shigo da shi na son ya isa ga Yakaka .

da tsawon yinin duk ya yi cikin kewar ta da son sanin halin da take ciki musamman ma dai da ya dunga ƙiran wayar ta bata ɗauka , hankalin sa tashi yayi, sai da ya ƙira Sofi ta ba shi tabbacin lafiyar ta ƙalau kawai baccin gajiya take yi duk da dai yayi mamaki amma ya samu nutsuwar zuci .

Sannan kuma ya ji daÉ—in jin muryar Sofi cike da kwanciyar hankali da raha ba kamar yadda yayi zato ba da har yake jin shakkun barin su a tare .

"Sofi kyale ni haka nan duk a gajiye nake jikina ma duk ciwo yake min ke kuma kin zo kin sake É—ora min nawin waÉ—annan kayan naki .

Ya ƙarasa faɗin hakan yana ɗan dukan bayan ta cike da tsokana .

Matsar da fuskar ta sofi tayi tana wani É—an mitsitsin murmushi .

Karaf idanun sa suka sauƙa kan Yakaka wacce take ta raragefe ta bayan kujeru cike da tsoron sake ganin karen nan take neman ƙofar kitchen .

Ware idanun yayi kafin ya ƙira ta "Wafaa .

Sofi bata ankara ba ta ji ya tunkuɗe ta gefe ya miƙe da ɗan sauri ya isa ga Yakaka wacce idanun ta da suka yi zuru-zuru suke bayyana halin ruɗani da tsoron da zuciyar ta ke ciki .

"Wafaa , me ya same ki ?

Yakaka wacce ta ɗan sake jaan baya , tana ƙin haɗa ido da shi kan ta a sunkuye tace "Yaya Dacta yunwa nake ci tun safe ban ci kome ba .

Kafin ya buɗe baki Sofi wacce har ta baro inda take a ɓingire ta gyagije tayi wuf tace "Ah Amaryar Ya-ka-ka har an gama baccin asarar an tashi ? To ke kuwa kya fito haka ? Dagaje-dagaje ? Yarkace-yarkace fuska duk yawun bacci kina Amarya....

Da hannu Doctor Hamza ya dakatar da ita , "Sofi ina Abincin ta ? A Bata ta ci yunwa take ji...

Wani irin kallon sheƙeƙe Sofi ta masa tana ƙanƙantar da ido ta ɗaga yar mitsitsiyar rigar ta ɗan shafal ɗin cikin ta da manyan cinyoyin ta suka sake shanye shi ciki ya bayyana .

"Doctor ka ga fa nima nawa cikin haka yake empty ba kome ka dai san bana jurar shiga kitchen na girkawa kaina ma bare wannan gantsareriyar .

Bai saurare ta ba ya matsa da sauri ya taro Yakaka da take ƙoƙarin durƙusawa saboda duhu-duhu da take gani.

"Wafaa duk yunwar ce ? Sannu muje ki shirya sai mu tafi mu ci abinci kin ji ?

Da sauri Yakaka ta zamewa riƙon da yayi mata tana jin nawin kar hancin sa ya shaƙo wani mummunan yanayin da bai dace ba daga jikin ta duk kuwa da tasan ƙamshi irin nasu na gado ya zauna mata a sassan jiki amma ai jikin ɗan adam ruwa ne .

"Yaa Dacta a nuna min kitchen É—in jiya Amnee ta min miya na taho da ita sai na É—umama na dafa mana wani abu mu ci da sauri ba ma sai an tafi wajen sayar da abinci ba '

Sofi wacce ta shaƙa har wuya sai cewa tayi "ɗumame za ki mana da daren nan ?

"Za ki iya Wafaa ? Yace yana ɗago haɓar ta da ɗan yatsan sa , da son ganin ƙwarar idanun ta

"Zan iya Ya dakta , tace tana zame fuskar ta

"To muje na nuna miki.

Kyale ta zan nuna mata kai muje kayi wanka Doctor kayi shirin Magarib tunda ta gabato kai da baka yarda jam'i ya wuce ka '

Har zai ce wani abu sai kuma ya fasa yana ɗaukar briefcase yace "ki taya kuyi please jikin ta ba ƙarfi sosai .

Wani mugun Kallo Sofi ta bi shi da shi kafin ta dawo da ganin ta kan Yakaka da tayi ƙulus tana jiran ta.

"Muje

Ta ce tana yin gaba hannu dama suka bi sai ga su a cikin É—an wani Straight kitchen da bai cika girma ba.

Suna shiga Sofi ta hankaɗa Yakaka , ƙiris ya rage ta ci karo da cabinet.

ta matsa gaban ta tana rangaji cikin irin takun ta , muryar ta cike da kaushi tace

"Barkan ki da shigowa cikin rayuwata , ina yi miki barka da shigowa cikin gona ta , ban iyakance miki iyakar adadin nau'ikan azabar da nake kan yi miki tanadin su ba na dai san babu shakka za ki iya zaɓar mutuwa ta hanyar rataya akan rayuwar da za kiyi a gidana .

Idanun ta da suka yi jawur Sofi ta tsare ta da su da suke tabbatarwa da Yakaka sahihancin zantukan da ta furta kafin ta cigaba da cewa

"Kuskure mafi girma da kika yi shine auren Mijina , tsautsayi da ya hau kan ki kuma har kika tako kafafun ki cikin gida na da zummar yin rayuwar aure da Mijina , yaudarar kai ta sa ki tunanin samun kwanciyar hankali a rayuwar gidana , wuce iyakar da zai kai ki ga faÉ—awa cikin bala'i Mai girma shine ki haÉ—a shimfiÉ—a da Mijina .

Guntu murmushi sofi tayi kafin ta ɗora da cigaba da cewa " wautar da za kiyi kuwa ita ce ƙoƙarin shiga tsakanina da Mijina ko kuwa nace ki nemi kai ƙara ta anan za ki ga ainahin launi zuciya ta da ta ɓoyu cikin bayyanannar fuskata .

Juyawa tayi ta ɗau wata wuƙa kakkaifa daga cikin jerin wuƙaƙen ta da suke block a jere ta juya tsinin wuƙar saitin Yakaka wacce take tsaye kamar mutum-mutumi .

"Kin ga wannan wuƙar ita zan saka na farka cikin ki duk ranar da kika yi kuskuren sakarwa Mijina jiki har ta kai ki ga ba shi wannan busasshen jikin naki Marar maiƙo banda ma jarabar namiji me zai ci a wannan wajen ? ta ƙarasa zancen tana nuna ƙirjin Yakaka da tsinin wuka .

"Wafaa .

Sautin Doctor Hamza ya ratso wajen daga bayan su hannun sa riƙe da wani ɗan babban cup da chokali a cikin sa yana juya tea mai kauri da ya haɗa .

Jallabiyar jikin sa bata boye sauran danshin ruwan da yayi wanka da shi ba , ya ƙaraso cikin kitchen ɗin lokacin da Sofi take ajiye wuƙar a gefe ta juyo da murmushi a fuskar ta tace

" kar ki manta da abunda na faÉ—a miki ki kiyaye Bari nima nayi Sallah .

Bata dubi Doctor Hamza ba ta bar kitchen ɗin saboda zuwa lokacin kishin ta ya fara kaiwa matakin da ya wuce kissa ta ɓoye shi , zuciyar ta ba zata juri ganin Hamzan ta yana ko da yiwa wata mace magana bane bare bata kulawa kuma ma wai a matsayin matar sa ita ganin ƙoƙarin kan ta ma take yi da bata fara yunƙurin kashe Yakaka ba , ko da yake Samira ce take hana ta a cewar ta kissa da kisisina kaɗai ya ishi Yakaka .

Bayan fitar ta Dactor Hamza ya matso kusa da Yakaka wacce har lokacin kalaman Sofi ke mata yawo a kunne suna É—arsa mata wani mugun tsoro a cikin ran ta .

Sanyin hannun sa ta ji a cikin nata ya sa tayi firgit tana zame hannun ta , bai bata dama ba ya riƙo hannun ta ya jaa ta zuwa kan standard-chair bayan ya ajiye tea ɗin ya taimaka mata ta zauna.

Ɗaukar tea ɗin yayi ya kurɓa ya ji ɗumin sa yayi dai-dai ɗumama ciki.

Dan haka ya kai kofin bakin ta a hankali muryar sa a ɗan ƙasa yace "ki shanye zai taimaka wajen dawo miki da kuzari bayan ya rage miki yunwa .

Hannun ta ta kai zata karɓi kofin , amma sai ya janye ya hana ta , da hannun sa ya sake kusanta kofin da bakin ta .

Ba yadda ta iya haka ta buÉ—e baki ya fara bata , har sai da ta shanye

A take gumi ya tsattsafo a goshin ta ta sanya bayan hannun ta da ya sha jan ƙunshi da aka mata tsararren zane da ya zanu akan farar fatar ta tare da ƙara fiddo zallar kyaun zara-zaran yantsun hannun ta masu tsini , ta goge gumin kan ta ɗauke hannun ta taji sassanyan hannun sa yana taya ta .

Ganin haka ya sa ta fara ƙoƙarin miƙewa amma sai ya sake matso ta ya hana ta tashi , a hankali ta ɗago kai tana kallon fuskar sa cikin sa'a idanun su suka haɗu wani yanayin da ta gaza jurewa a cikin idanun sa take hangowa dan haka tayi saurin sunkuyar da kai .

"Meyasa kika ta yin bacci haka kika zauna da yunwa ? Bakyau zama da yunwa kin ji ? Nan gaba kar ki sake bacci mai yawa haka da rana , an fison mutum yayi irin wannan baccin da dare kin ji ko wafaa ?

So take ta ce ba bacci tayi ba so take ta faɗi ainahin abinda ya faru sai dai rarraunar zuciyar ta da take maƙare da tsoron Sofi tana tunasar da ita kalaman Sofi tare da sake faɗa mata makomar ƙaryata Sofi da zata yi muddin ta fadi gaskiya .

"Wafaa.
ya sake ƙiran sunan ta

"Unm ta amsa .

"Ki daina min shiru-shirun nan ki dunga amsawa idan na miki magana kin ji ko ?

" To Yaya Dacta bazan sake ba.

Goshin ta ya sumbata a hankali kafin yace "Ni zan je masallaci na dawo Miyar da muka taho da ita jiyan tana fridge kin ji ?

A hankali ta gyaÉ—a kai .

Ya juya yana barin kitchen ɗin , kafin ya ƙarasa falo Sofi ta bar gurin da take laɓe da gudu ta hau sama ɗakin ta .

A gurguje Yakaka ta tafasa shinkafa ta nuna ta tsantsame ta juye a warmer ta ɗauko miyar bayan ta juye a wata tukunyar ta daban ta ɗora ta tana fara dumamuwa ƙamshi ya ɗume gidan .

Kafin wani lokaci ta dumamu ta zuba miyar a wata warmer da bata kai waccan girma ba ,

So take ta koma É—aki ta yi wanka ta kintsa jikin ta amma tsoron haÉ—uwa da Sofi ya hana ta fita , dan haka tayi zaune kawai a kitchen É—in.

Idanun ta ya sauƙa kan babbar jakar bacco da suka taho da ita a jiyan wanda kayan kamsasa girke-girke ne a ciki da kuma na shayi wanda Amnee ta haɗa mata su tana sake jaddada mata amfanin su sosai da sosai .

Ganin tana zaune kawai sai ta sake miƙewa ta haɗa ruwa a tukunya bayan ta zuba haɗin kayan shayi wanda Amnee ta nuna mata su dalla-dallah dan haka ta ɗau wanda ta nuna mata shine na dare saboda cikin ganyen akwai sinadarin wartsake gajiya ,

sugar kaɗan ta diɓa daga sugar-bowl ta zuba saboda shayin ma bai cika yawa ba kuma Amnee ta faɗa mata cikawa shayi sugar yana rage daɗin sa ya hana garɗin sinadaran da aka yi amfani da su fitowa .

Daga lokacin da ta ɗora shayin zuwa mintoci biyar da suka biyo baya da fara tafasar shayin wani irin ƙamshi ne mai samar da nutsuwar zuci ya cika gidan har maƙota .

Doctor Hamza da tun yana waje ya fara shaƙar ƙamshin da kai tsaye ya masa jagora zuwa kitchen daga bayan ta ya tsaya yana kallon ta lokacin da take juye shayin a wani stainless steal tea-set ƙirar Retro Titanium da Sofi ta saya a wani zuwa da tayi UK .

Amma tunda ta kawo su sai dai koyaushe a goge su a ajiye ba'a taɓa amfani da su ba .

A hankali ya tako ba tare da ta ji sautin takun sa ba sai ji tayi ya mata rumfa da ƙirjin sa da yasa ta saki wani ihun tsorata da tayi .

Da sauri ya juyo da ita da hasken lantarki yake kallon ta , yana É—an nazarin ta yace "Wafaa me ya tsorata ki haka ? Na lura tun zuwana a tsorace kike ko wani abu ya faru ?

Girgiza kai tayi kafin ciki ƙaramar murya tace "Kai ka tsorata ni na ɗauka kare ne .

"Kare kuma ?

Yace da mamaki a muryar sa .

Sake gyaÉ—a kai tayi alamar "eh

" Wafaa bani da kare a gidan nan mai zai kawo kare ?

Da sauri ta É—ago kan ta da son ran ta ne tace "akwai kare mana yau ma da shi muka wuni a É—akin ka "

Hannun sa da taji akan ƙirjin ta ya katse mata tunani da sauri ta ɗora hannun ta akan nashi idanun ta na fiffitowa ta fara kokawar janye hannun sa.

"Shittt yace mata yana dauke hannun ta daga kan nashi ba tare da ya janye nasa hannun ba ya saurara kadan, kafin yace

"Ki ji yadda zuciyar ki ke tsananta bugu ? Ba kyau saka tsoro haka a cikin rai yana da hatsari ga lafiya.

Firgicin jin hannun sa a ƙirjin ta ya hana ta fahimci bayanin da yake mata.

So take kawai ya ɗaga hannun sa , a hankali ya janye yana nazarin baƙon yanayin da ya bayyana a fuskar ta , ɗan murmushi yayi kafin yace .

"Muje kiyi wanka ki shirya , Amarya sukutum ba kwalliya Wafaa ? Nayi zaton zan dawo na same ki kin min kwalliyar da zata mantar da ni duk wata guntuwar damuwa , oya muje kiyi wanka .

Shi da kansa ya haɗa mata ruwan wanka kafin ya fito tayi shirin wanka bayan zanin da ta ɗaura ta zura dogon hijabin ta har ƙasa ta dawo bakin ƙofar banɗakin ta tsaya a ɗarare baki ɗayan ɗakin tsoro yake bata.

Yana fitowa ya gan ta a tsaye da sigar tsokana yace "muje na miki ?

Da sauri ta girgiza kai "zan yi da kaina.

Har ta murɗa ƙofar ta shiga sai kuma ta dawo ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba tace "Dan Allah ka jira ni kar ka fita .

GyaÉ—a kai yayi cikin ran sa ya fara mamakin tsoron ta yace "bazan fita ba kiyi wanka da kyau kin ji ?

Ko da ta shiga banɗakin kasa rufe ƙofar tayi sai ta tura ta kawai .

tana tsakiya da wanka ta ji kamar ya fita jikin ta duk kumfa ta matso bakin ƙofar

" Yaya Dakta

Ta ƙira suna sa da 'yar ƙaramar murya dan ta tabbatar yana nan.

Shiru yayi bai amsa ba duk da cewa ya ji ta sai ya taso a hankali ya bar aikin da ya fara yi a laptop É—in sa.

Sake matsowa tayi tana buɗe ƙofar kaɗan ta ƙira sunan sa da ɗan ƙarfi dai-dai da ƙarasowar sa wajen .

Karaf suka haÉ—a ido da shi .

Salati ta sa tana yin baya da gudu ta rufo ƙofar tana jin wata matsananciyar kunya na neman sa ta kuka .

"Shine kana jina ba zaka amsa ba wallahi ka bani tsoro meyasa za ka leƙo ni ina banɗaki ?

Muryar sa tana bayyana dariyar da ta taho masa yace "ah leƙa ki nayi ? Ba ke kika ƙirani ba ?

"To meyasa baka amsa ba kawai ? Ta furta hakan muryar ta a shagwaɓe da jin haushin sa .

"Gani nayi zuwa da kai yafi saƙo , kuma ban sani ba ko ƙira na kike na wanke miki baya .

Ya furta hakan lokacin da ya koma ya zauna har yanzu dariyar shirmen ta yake gefe guda wani irin nishaÉ—i ne yake ji yana ratsa shi .

bayan ta gama wankan tana ƙudindine cikin Hijabi ta fito kai tsaye wajen da akwatin kayan ta yake ta nufa tana ƙin kallon sa .

Bata wani bincika ba ta É—au wata jar atamfar ta da take sama sabon É—inki ne fil acikin kayan da Baaa ya mata .

BanÉ—akin ta koma ta sanya kayan bayan ta É—an shafa mai da ta gani a ajiye gaban makeup-mirror da yake banÉ—akin .

Riga da siket ɗin da ta sa sun zauna mata ɗas a ɗan tsararren murmurarren dogon jikin ta da mazauna ƙasar Amurka ke kiran mata masu zubin jikin ta da Miss-champagne, Mutan ƙasar ingila kuwa suka ƙira ta da Miss-Magnificent.

Lokacin da ta fito tana gyara É—aurin É—ankwalin ta Doctor Hamza shagala yayi wajen kallon ta ya manta da abokin aikin sa da suke yin wata tattaunawa da shi a laptop.

Gaba ɗaya kyaun ta ya ɗau hankalin sa kafin ƙamshin sassanyar haɗin Humra ya game masa hanci da ta buɗe cikin kayan ta ta ɗauko ɗaya daga cikin kwalaben da ta taho da su ta tsiyaya kaɗan a tafin hannu ta shafe jikin ta da shi .

Yanayin ta na sanyi da nutsuwa shine yanayin da yafi so da ita komen ta sannu kan hankali take yi babu kwarafniya , irin ta irin matan da yake mafarkin samu kenan .

Da É—an murmushin da yake cikon halittar ta tace "Yaya Dakta nagama .

Shiru ya ɗan yi yana kallon ta bai ƙi ba ace tayi tsaye haka nan gaban shi yayi ta kallon ta zuciyar sa na daɗa ƙawata masa kyaun halittar ta.

Yamutsa fuska ta ɗanyi saboda ta fara siƙewa da yunwar da take ji ,

"Yunwa nake ji..

Kafin ta ƙarasa magana ya miƙe ya tako a hankali ya kama hannun ta suka fita tare "muje ki ci abinci Wafaa .

Basu tarar da Sofi a falon ba , dan haka Doctor Hamza ya zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun falon yace "bari na ƙira Sofi kafin nan zuba mana abincin .

Da ɗan saurin sa ya nufi sama , Sofi wacce daman tana laɓe daga sama jin tahowar sa yasa tayi sauri ta fito daga maɓoyar ta ,

Tayi wanka ta sake sabon shiri cikin wata evening gown backless, launin sararin samaniya da ta bi tsarin jikin ta irin na matan da suka É—au duniyar su da faÉ—i suke bin dare da rana wajen ganin zubin jikin su ya koma haka watau (Wisdom tooth body).

Rigar ta bi jikin ta ta lafe sassan jikin ta da suke da É—aukar hankali sun bayyana a sarari.

Jikin ta ta haɗa da nashi ta fara masa salo , da sauri ya riƙe hannun ta da ta ɗaura akan ƙirjin sa yana dawo da nutsuwar sa dai-dai yace "Sofia wannan kayan bai yi ba ki je ki sauya kin san dai ba mu kaɗai bane a gidan nan ? Bai dace ba ki fito a haka .

Kaɗa ido tayi cike da shanye ruɗanin da ta shiga ganin yadda yau yake kawar da ido daga kan abubuwan da a da baya motsin kirki idan tana masa juyi a gaban sa tace "Doctor dan ka ƙaro aure ne zan kasa sakewa a gidannan ko meye ? It....

"Sofia pls ki fahimceni ko da a gaban mace 'yar uwar ki bai dace ki fita haka ba jikin ki duk a bayyane , kuma .

Ɗan tsahirtawa yayi yana kallon yadda koɗaɗɗiyar fuskar ta ta fara yin jaa da bayyanar ɓacin rai , gudun rigamar ta yake yi sosai dan ya san mahaukacin kishin ta baya so yayi wani abu da zai sa ta ƙullaci Yakaka dan haka ya riƙo hannun ta yana sake tausasa murya yace "kuma ai kin san dai ina kishin ki sosai unh my pump truck ?

ÆŠan murmushi tayi tana jin zuciyar ta na farfaÉ—owa , haÉ—a jikin su ta sake yi tana kwantar da kan ta a kafadar sa a hankali tace "Doctor your Love is my strength and hope in this life always remember this.

Ajiyar zuciya yayi baki ɗaya hankalin sa yana ga Yakaka ya ɗan ɗagata daga ƙafaɗar sa "Sofi kiyi sauri ki sauya kayan ki sauƙo mu ci abinci Wafaa tana jiran mu .

Zamewa yake ƙoƙarin yi yaji ta riƙe hannun sa , cike da gajiya ya ɗaga idanun sa zuwa fuskar ta , hawaye ya gani sun ciccika gurbin matsakaitan idanun ta suna daf da fara sauƙa ,

"Sofia menene kuma ? Ya furta hakan cike da gundura .

"Ka raka ni na chanja kayan sai ka zaɓar min wanda ya maka .

Tausayin raunin da ya hango a tattare da ita da ya san son shi da tsananin kishin sa da take ya sa haka , sai ya gaza musa mata a ƙoƙarin sa na son kyautata mata ya rage mata raɗaɗin da take ji ya bi ta hannun su haɗe cikin na juna suka shiga ɗakin Sofi ta rufo ƙofar ta murɗa key .

Yakaka baki ɗaya tayi laushi a zaune kan kujera tun kan ta na sunkuye tana jiran ta ji takun sauƙowar su har ta kai ta fara ɗaga kai tana kallon ƙafar benen .

Ganin ko alamar su babu ita kuma yunwa na neman halaka ta yasa ta sauƙo.ƙasa gaban abincin ta zuba kaɗan a Plate ta cinye daɗin ɗanɗanon miyar Amnee da ta wadatu da kaji kamar zata tsinke mata kunne har wani lumshe ido take .

Kafin ta farga ta cinye cikin zaƙuwa ta daɗa wani , a cikin nutsuwa take cin abincin ta bata ankara ba sai da ta cinye kusan rabin abincin ta ɗaura da ruwa taji cikin ta dam .

Ta dawo nutsuwar ta sai lokacin ta fara farga da daɗewar da suka yi basu zo ba , ƙaton agogon falon da yake aiki ta duba ta ga har ƙarfe goma na dare saura 'yan mintoci .

Shirun da duniyar baki ɗaya ta ɗauka a kunnen ta ya tafi ya tado da maƙallalen tsoron da yunwa ta binne shi ,

Ɗas!Ɗas! Ƙirjin ta ya buga da tuno ƙaton karen da ta tabbata yana nan a cikin gidan yana shawagi .

Sauƙa tayi daga kan kujerar ta takure a ƙasa tana jin yadda baki ɗayan tsikar jikin ta ke miƙewa '

Tsoron ta yana sake hauhawa da ƙaruwar kowacce daƙiƙa ɗaya , bata san lokacin da ta miƙe ba a hankali ta nufi ƙafar benen ,sai kuma ta jaa ta tsaya tana jin shakkun hawa sanin da tayi ɗakin Sofi ne a saman , ita tsoro take ji sun bar ta ita kaɗai ko da ba zasu yi hira ba su sauƙo ta dunga ganin su .

Muryar ta tana É—an rawa tace "Yaya Dacta , Yaya Dacta '

Ko alamar motsi bata ji ba

Ɗan sake ɗaga sautin tayi tana sake ƙiran sunan sa wannan karon har da "Auntie Sofi .Amma kamar basa gidan '

Wani irin tsinkewar zuciya ta ji da ya sa ta kusan faÉ—uwa saboda gurnanin kare da taji a daf da ita .

A daskare ta waiga bata ga karen ba sai fa gurnanin da take cigaba da ji , addu'o'i ta fara yi da duk ayar da tazo bakin ta bata saki sai ta kai ƙarshen ayar .

A hankali ta fara yin baya-baya har ta koma kan kujera, haushin da karen yayi da ɗan ƙarfi da yake bata tabbacin yana cikin falon yasa bata san lokacin da ta shige tsakankanin kujera kudundune ta cure guri ɗaya duk kuwa da rashin sararin wajen .

Bata san tsawon lokacin da ta ɗauka a haka ba sai ji tayi hannu na ƙoƙarin zaƙulo ta a wajen da bata kai ga fahimtar hannun mutum ne ko kuwa na karen da zuwa yanzu ta fara tunanin aljani ne ba.

Wani irin ihu ta sa tana runtse idanun ta gam cikin fitar hayyaci .

Riƙo ta Doctor Hamza yake yi tana kufcewa ba tare da ta daina ihun da take yi ba ,

Jijjigata yayi da ƙarfi yace "Ke Amina ki nutsu ki dawo hayyacin ki me yake damun ki ne haka ? Tsoron ki yayi yawa .

Jikin sa ta shige tana wani irin kuka cikin muryar kukan tace "Yaya Dakta dan Allah ka mayar da ni gida wallahi idan ba haka ba karen nan zai kashe ni ..

"Wafaa ki nutsu babu kare a gidan nan ba mu da kare tsoron ki ne ya cika yawa ki daina saka tsoron abu haka a ran ki da har zai dunga yi mi ki gizo .

"Akwai wallahi ba gizo bane akwai kare yanzu ma yana nan anan ina jin kukan sa .

"Wai me ya faru ne wannan take yiwa mutane ihu da daren nan ? Kamar wata sabon kamu ...

"Sofia ki yiwa mutane shiru please .

Hamza yace haka a harzuƙe da jin haushin ta .

Yana shafa kan Yakaka wacce take ta ajiyar zuciya a ƙirjin sa .

Ƙyeɓe baki Sofia tayi kafin ta tausa murya tace "Doctor ni yanzu ka zo muje muyi wankan mu ka san dai kullum kaina kake hana ni zama da janaba.

Kamar wacce wuta ta jaa ta Yakaka ta raba jikin ta daga na shi , kallon wasu 'yan daƙiƙoƙi ta yiwa ƙwarar idanun sa da suke cike taf da so da tausayin ta , ta sauƙe nata idon ƙasa tana jin wani irin abu mai nawi yana danne mata zuciya .

Da sauri Doctor Hamza ya taka yana son sake riƙo ta , sai ta sake gocewa cikin muryar ta da kuka ya duƙusar tace "kar ka taɓa ni Yaya Dacta kaje kayi wanka .

Bata tsaya ba sai ta juya da sauri dai-dai da sauƙar wata ƙwalla da bata san takaimai ta mece ce ba daga cikin idanun ta nufi 'yar hanyar da zata kai ta ɗakin sa tana jin tsoron da ya cika mata rai na raguwa sakamakon wani baƙon yanayi da zuciyar ta bata gama tantancewa da shi ba da yake mata ciwo a zuci fiye da tsoron.

Wata 'yar ƙaramar dariya Sofia tayi da yasa Doctor Hamza da duk ya jikin shi yayi sanyi kamar wani mai laifi ya mayar da ganin sa kan ta tana tsaye daga ita sai ɗan wani guntun towel da iyakar sa cinya .

Ƙaramin tsaki yayi yana hararar ta yace " Sofia ki dunga sanin abun da kike yi please .

Za ta yi magana ya É—aga mata hannu tare da kewaye ta ya wuce É—akin sa .

Da shigar sa ɗakin ya ɗora idanun sa akan ta tana kwance akan Sofa ta bada baya da alama tayi shirin bacci domin ta rufu da dogon hijabin ta daga wuya har ƙafar ta .

Wani irin tausayin sa ne ya tsirga masa baki ɗaya ya rasa me yake damun ta take irin wannan tsoron shi dai tunda ya san ta ya san ta da tsoron kare amma bai san abun nata yayi ƙamari haka ba .

Bai ce ƙala ba kamar yadda ita ma bata nuna alamun ta san da shigowar sa ɗakin ba ta ya wuce Banɗaki .

Yakaka da idanun ta suke rufe tunda ya shigo ɗakin ta buɗe idanun ta a hankali tana jin yadda damuwa take ƙara mata yawa har ta rasa da wanne zata ji ? Da tsoron Sofi wacce ta mata barazanar da take da tabbacin zata iya aikata mata abunda ta ce ko kuwa da tsoron karen da yake gidan yake rayuwar sa da take da tabbacin Sofi ta san da zaman sa tunda tare ta fara ganin su .

Gefe guda kuma ga ciwon da take ji kan yadda zuciyar ta ke ƙenƙesa mata rashin so da shi kan sa Doctor Hamza ya fara gwada mata banda haka ita ta wuni da yunwa ƙarƙashin horon Matar sa , shi kuma tunda ya dawo banda nan-nan da matar tasa da yake yi suna naniƙar juna baya ta tata da take baƙuwa a tsakanin su dan saboda tsabar cin zarafi ma daga zuwa ya ƙira ta shine.'...

Ai ita ba yarinya ƙarama bace ta san abunda ya tsaya yi da matar sa , duk da tasan yana son Matar sa amma bata san son da yake yi mata ya kai ya mayar da ita wofi ba a dararen su na farko a rayuwar aure , tun yanzu ma kenan Sofi ta fara janye shi lokacin da yakamata ace da ita yake tare ina kuma a gaba ?

Kalaman Sofia suka fara dawo mata da take gargaÉ—in ta kan haÉ—a shimfiÉ—a da mijinta "to a yadda ta ishe shi É—in nan ma ita yaushe zai wani kula ta ?

Ita dai ai kawai zata zauna ne ta ga yadda rayuwa zata mata amma bata tunanin wani farin-ciki irin wanda ake samu a rayuwar aure .

Ko da ya fito tsayuwa yayi a kan ta bayan ya sanya riga da wondo na kwanciya bacci , a hankali cikin tausasa murya ya ƙira sunan ta "Wafaa , shiru tayi kamar bata ji shi ba .

Jikin sa ya ba shi idanun ta biyu tana jin sa dan haka ya taka a hankali ya matsa tare da zama a bayan ta jikin sa na gugar nata .

"Wafaa nasan kina jina ta shi muje na baki abincin nima yunwa nake ji .

Shiru ta sake yi , ganin haka ya sa hannu ya juyo da ita bayan ya janye hijabin da ta rufu , idanun ta da suke ƙasa-ƙasa yake son kallo amma taƙi da kyar ta iya cewa "yaya dacta nifa naci abinci na ƙoshi .

"Meyasa kika ci kika barni ? Daga yau idan ba bana gida ba kar ki sake cin abinci ke kaÉ—ai ba tare da ni na baki ba kin ji ?

Shiru tayi masa .

Sake sassauta murya yayi saboda ya fara fahimtar kamar fushi take yi da shi abunda kuma ba halinta bane ita mace ce ma'abociyar fara'a da yawan murmushi.

"To yanzu muje ki zuba min ni na É—an ci ko kaÉ—an ne kin ga yunwa nake ji sosai .

ÆŠan jim tayi kafin tace "to .

Tsayawa yayi yana kallon fuskar ta da ta É—an kumbura kumatun sai ya ga kamar daÉ—a kyau tayi "Wafaa kome kika yi sai kiyi kyau da kike fushi kamar kar kiyi dariya idan kina murmushi kuma bana so ki daina saboda fara'ar ki haÉ—e take da farin-ciki na

ÆŠago kai tayi ta É—an kalle shi tana jin tasirin kalaman sa har a cikin ran ta , a hankali tace "mu tafi ka ci abincin .

Da suka koma falon ta zuba masa abincin dai-dai cikin sa yana ci yana É—an kallon ta da tayi shiru tamkar mai tunani kafin ya fahimci gyangyaÉ—i take yi .

Bata san lokacin da ya gama cin abincin har ya Sha shayin sa ba saboda kwantar da kai tayi a jikin kujera sosai take bacci .

A hankali ta ji ya taɓa ta da yasa ta firgit ta buɗe idanun ta da suke cike da bacci ta kalle shi ,

"Mu je ki kwanta Wafaa dare yayi sosai .

Kama hannun ta yayi suka shiga É—aki bayan ya kashe wutacen falon da duk wasu na'ura .

Sofia wacce duk abunda suke tana falon a laɓe daga lungun kitchen da yake da ɗan duhu ta saɗaɗo ta fito ,

Wani ƙaramin ɗaki da yake matsayin na 'yan aiki nan ta buɗe ta shiga bayan ta ɗau kwanon miyar da sauran miya da nama yake ciki ,

Tana buÉ—e É—akin Sam da yake kwance ya taso da gudun sa yana É—an gurnani , shafa kan sa tayi kafin ta ajiye masa kwanon a gaban sa .

Wani irin ɓacin rai take ji bata ƙi ba ta ɓace ta ɓulla cikin ɗakin Doctor Hamza ta ga me suke yi shi da Yakaka ? Duk da dai tasan ba shi da buƙata amma ita fa ko kallon Yakaka bata so ya dunga yi

"Ya zama dole nayi wani abu akai ba zan iya zuba ido haka ina kallon su ba kissa kaÉ—ai ba zata gamsar da ni ba kar na tsaya galala shegiyar yarinyar nan ta min shigar basaja .

Ta furta hakan a sarari lokacin da take barin ɗakin ta jaa ƙofar ta kulle tana nufar ɗakin ta .

Duk yadda Yakaka ta so Doctor Hamza ya ƙyale ta ta kwanta kan kujera ƙi yayi dan dolen ta da kuma baccin da ya riga ya ci ƙarfin ta ta dawo kan katifar daga can ƙarshe ta kwanta .

Tana kwanciya kuwa bacci ya É—auke ta , fahimta da yayi baccin ya mata nawi ya sa shi jaan jiki a hankali ya matsa ya haÉ—a ta jikin sa , yana jin wani irin nutsuwa ta musamman tana bin jijiyoyin jikin sa yayi musu addu'a yana rufe ido bacci mai daÉ—in gaske ya É—auke shi .

Da asuba shi ya riga ta tashi , motsin da yayi da kuma fitsari da ya matse ta yasa ta buÉ—e ido a hankali .

Cikin nutsuwa ta fara fahimtar a inda take kwance kan ƙirjin Doctor Hamza .

Wani irin bugu nata ƙirjin yayi abu na farko da ya fara safkowa kwakwalwarta gargaɗin Sofi .

Kamar an soke ta ta miƙe daga jikin sa ta fara ƙoƙarin matsawa ta sauƙa daga gadon .

Idanun sa ya mayar ya rufe yana sake riƙo ta da ɗan tsauri ya jawo ta ta dawo kan sa "gudun me kike yi bayan kin kwana kin hantse kina bacci mai daɗin da baki taɓa yin irin sa ba .

Ya furta hakan muryar sa a ƙasa sosai .

Yakaka cikin yanayi na tsoro tace "Yaya Dacta dan Allah ka kyale ni kar Auntie Sofi ta shigo ta gan ni .

Da sauri ya buÉ—e idanun sa jin abunda tace .

"Sofi kuma ? Me zai kawo Sofi É—akin nan war haka ?

Shiru Yakaka tayi tana kwantar da kai

, "kin cika shirme Wafaa ke Matata ce ko Sofi ta gan mu ba abunda zai faru .

"Yaya Dacta kar a shiga Sallah .

Ta tunasar da shi cike da son ya kyale ta .

Yana rungume da ita ya miƙe zaune yana zaunar da ita a cinyar sa yace "zan tafi Masallaci na dawo kar kiji tsoron kome kin ji ko ?

"To tace tana miƙewa daga kan shi .

Shima miƙewa yayi ya shiga banɗaki yayi alwala ya fita masallaci .

Yana fita ita ma ta shiga banÉ—akin dan ta kintsa jikin ta .

Lokacin da ta fito kan ta yana ƙasa tana gyara jikin ta bata ankara akwai mutum a ɗakin ba sai da ta zo tsakiyar ɗakin ta ɗago kai .

Idanun ta suka faÉ—a cikin na Sofi wacce take mata wani irin kallon da ya firgita ta.

Assalam Alaikum Masu karatu tare da fatan alkhairi .

Kuyi haƙuri da wannan bai kai yawan yadda aka saba ba , jimawar ne nima bata min daɗi shi yasa na baku wanda ya sauwaƙa .

Idan dama ta samu zaku iya sake ganin cigaba nan da kwanaki uku insha Allah .

Nagode .
[3/19, 5:14 PM] +234 706 503 6187: Mafari.

. ( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

53

Tsayuwar minti ɗaya zuwa biyu tayi tana kallon ta kafin ta ƙaraso gaban gadon ta zauna ba tare da tace mata ƙala ba .

Hakan da tayi ya sake ƙular da Sofia dan haka a fusace tace " zaɓi na zo baki ko dai yini tare da Sam ko kuwa ki fice daga gidan nan ki tafi can inda kika saba zuwa yawon ki a garin nan idan shi da ya ajiye ki ya dawo kin dawo dan yinin ki da ni a gidannan bana jin zan iya jurewa .

Yakaka wacce kan ta ke ƙasa har Sofia ta gama bayanin ta bata ce mata kome ba tamkar dai bata jin yaren da Sofia take yi ta miƙa hannu a hankali ta ɗau wayar ta ta fara dannawa ba tare da tasan me take yi ba '

Hakan da tayi ba ƙaramin tunzura Sofi tayi ba a fusace tace "Dan Ubanki watau ga mahaukaciya tana magana kin wani yi banza dan....'

Kamar an safure ta Yakaka ta miƙe daf da Sofi ta zo ta tsaya idanun ta ƙyar akan ta cikin muryar ta da bata cika ƙarfi ba tace "Duk wani cin mutumci da zage-zagen ki ya tsaya a iyakar kaina , kar domin kin ga ina yin shiru kiyi zaton za ki iya zagin iyayena na ƙyale ki .

" ban ajiye iyayena kurkusa ba idan ke kin raina naki iyayen na.....

Turo ƙofar da aka yi yasa su duk biyun waigawa .

Doctor Hamza turus yayi yana kallon su kafin ya ƙaraso fuskar sa cike da mamaki ya tattara ganin sa kan Sofi wacce har kawo lokacin bata farfaɗo ba daga ruɗanin da ta shiga kan ji da tayi Yakaka ta mayar mata da Martani har ma tana ƙoƙarin rama zagin da ta mata.

"Sofia me ya faru ? Me kika zo ...

Sai yaƙi ƙarasawa ya ɗan riƙo hannun ta ganin wani irin huci da take yi ,so yake ya jaa ta waje .

Amma sai ta ƙi da ƙarfi ta warce hannun ta kafin ta fashe da wani irin kukan baƙin-ciki .

"Na shiga ukuna Yakaka ni kike zagi ? Iyayena kike zagi Ni-ni kika zaga ? Yakaka uwata da ubana kike zagi ? Daga kawai na shigo na tayar da ku Sallah ?

Yakaka wacce ta cika da mamaki da tsoro ta É—ago kan ta fuskar ta É—auke da mamakin makircin Sofi da bata saba da irin sa ba tayi rau-rau da ido tana kallon Doctor Hamza wanda shi ma ita yake kallon fuskar sa a É—aure , ta juya ga Sofia tace "ki ji tsoron Allah ni na zage ki ? Ba ke kika zage ni ba ? Ina ke ce kika shigo kawai kika fara zagi na har da Babana ?

Sofia ta zaburo zata yi magana Doctor Hamza ya dakatar da ita da cewa "saurara Sofia wai me yake damun ki ne ? Ya za ki shigowa mutane É—aki haka da sassafe ?

Zata yi magana ya sake katse ta wannan karon muryar sa a kaurare yace "Sofia bana son tashin hankali da fitina , ran ki zai yi mummunan ɓaci muddin kika ce ...

Sofia wacce take jin zuciyar ta kamar zata fashe ganin Doctor Hamza yana shirin birkice mata kuma a gaban Yakaka .

Nan take ta haÉ—iye kukan kissar ta ta murje ido cikin salon ta na goggagun matan da suka raina mazajen su kunya kuma ta mata nawin É—auka ta gatsina fuska da buÉ—aÉ—É—iyar murya tace

"Wannan wane irin rashin adalci ne kake fara rabawa a tsakanin mu tun yanzu ? Kenan dan tana É—akin bani da ikon shigowa É—akin ka a duk lokacin da na so ?

"Sofia ki wuce ki koma ɗakin ki kar ki ɓata min rai ki ɓata min lokaci .

Buɗe baki tayi kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa tana mayar da ganin ta kan Yakaka wacce ita ma ita take kallo , da haƙoran ta ta cije leɓen ta na ƙasa tana yiwa Yakaka wani irin mugun kallo tayi ƙwafa kafin ta juya a fusace ta fita a ɗakin tana wani irin bugo ƙofar da har sai da Yakaka ta firgita .

Tsoron Sofi da ya ɗan yi ƙaura saboda zuciya da tayi da ta zagi Baban ta taji yana dawowa sabo fil ,ta tuno da zaɓin da tace ta bata kan ta zauna ta yini da kare a ɗaki irin na jiya ko kuma ta fita ta bar gidan to ta tafi ina ?? Yaya dacta ma ai ba zai bari ta fita ko da ƙofar gida bane kuma a can ma an mata nasiha kan fita ba mutumcin matar aure bane a dunga ganin ta a titi haka siƙau muddin ba lamarin zumunci mai ƙarfi ko aiki ko kasuwanci zata fita yi ba .

Hannun sa da ta ji a ƙugun ta shi yasa ta sauƙe ajiyar zuciya , tana jin lokacin da ya sako fuskar sa ta gefen wuyan ta ƙamshin turaren sa na game mata hanci , muryar sa kamar ba shi ya gama kurara Sofi yanzu ba yace "tunanin me kike yi Wafaa ? Bana son kina yawan tunani na faɗa miki .

A hankali ta juyo ba tare da ta fita a tsakanin hannuwan sa da ya kewaye ta da su ba tana yin ƙasa da murya tace "Yaya Dacta wallahi ban zage ta ba ku....

"Shitt yace yana ɗaura hannun sa akan laɓɓan ta da yasa ta ɗago kan ta tana kallon ƙwarar idanun sa da suke cike da tausayin ta

"Ba sai kin min bayani ba Wafaa na san halin Sofia , kiyi haƙuri zan ɗauki mataki ba zan bari ta ci zarafin ki ba da ke da ita duk matan Aure na ne kiyi haƙuri kin ji ko ?

Wata sassanyar ajiyar zuciya tayi jin daɗin bai yarda da sharrin da ta so ƙulla mata ba " Nagode Yaya Dacta .

Murmushi ya yi mata kafin ya sake matso da ita jikin sa kamar mai raÉ—a yace "mu je mu kwanta kafin lokacin tafiya ta aiki .

Da sauri ta girgiza kai kafin tace "Yaya Dacta kitchen zan tafi na yi girkin abin karyawa kafin ka tashi bacci.

Zama yayi a bakin gado yana zaunar da ita a cinyar sa yace "No Amarya ce ke Wafaa bai ma kamata kina shiga kitchen ba har sai mun gama amarcin mu ko ?
Ya ƙarasa da sigar tsokana yana ɗaga mata gira .

Ɗan murmushi tayi tana miƙewa tsaye "zan tafi kitchen Yaya Dacta bana so ka tafi office baka yi breakfast ba .

Da gama faÉ—in haka ta taka tana barin É—akin , fuskar sa É—auke tattausan murmushi ya bi ta da kallo salon kulawar da ta gwada masa ya burge shi daban da na Sofi wacce bata iya kula da duk wasu lamuran nasa ba sai fa gwada haukar So a sarari .

Bai kwanta ba sai ya jawo littatanfan sa na addini ya shiga karatu.

A kitchen cike da azama irin na matan da suka gogu da aiki Yakaka ta ɗora ruwa kafin ya tafasa ta kwaɓa fulawa da baking powder sai 'yar zuma da ta sa a madadin sugar .

Lokacin da ruwan ya tafasa ta wanke shinkafa fara ƙal ta tuwo ta zuba tare da Sugar sannan ta zuba spices da ake amfani da su wajen haɗa shayi .

Kafin shinkafar ta nuna , ta É—ora mai ta fara soya pancake da har ya fara tashi saboda É—umin wajen '

kafin ta gama shinkafar ta tayi ligib dan haka ta dama madarar gari mai yawa ta juye akan shinkafar ta da tayi ligib tana juyawa yayi kauri kamar talge shinkafar kuwa tabi cikin madarar, É—an manshanu kaÉ—an ta zuba aiki ta kashe Sugar ta bari.

Da ta gama soya pancake bata bar kitchen É—in ba sai da wanke kwanukan ta goge ko'ina tsaf .

Sannan ta buɗe fridge ta ɗauko Strawberry ta wanke shi tsaf ta yanka shi a tsai-tsaye bowl ta ɗauko mai kyau tazuba basisen da yayi nar-nar da shi ya kwanta fari ƙal , sai ƙamshin man shanu da kayan ƙamshi yake yana ɗaukar Ido .

Bayan ta zuba iya adadin yadda ta ke ganin yayi sai ta jera Strawberry É—in a kai , ta rufe , ta É—au wani bowl daban kuma ta zuba pancake .

Bata juya ba amma jikin ta ya bata da tsayuwar mutum a bayan ta dan haka ta juya da sauri ,

Ajiyar zuciya tayi ganin Doctor Hamza ne shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa wajen aiki a hankali ya tako har inda take yana bin fuskar ta da kallo da ita ma shi take ta kallo cike da burge ta da yayi kamar wani bature ya tsuke cikin lounge suit launin shuÉ—i Mai duhu .

Yana mata murmushi ya shafa kumatun ta , "Wafaa wannan kallon fa ? Yace da sautin da yake tsakanin maƙoron sa .

Sunkuyar da kai tayi a dan kunyace da 'yar ƙaramar murya tace "ba kome har ka shirya ? Nima na gama girkin .

"Naso na makara ma wafaa , me kika girka mana ? Ya furta hakan yana zarcewa da hannun sa ya buÉ—e abincin da ta haÉ—a , da kallo ta bi fuskar sa cike da son ganin yanayin da zai nuna .

BuÉ—e baki yayi cike da jin daÉ—i sai kuma yayi murmushi "Basisee ? Wow Wafaa ashe kin iya girki ? Kamar kin san na daÉ—e rabo na da na ci Basisee .

Murmushin jin daÉ—i tayi tana É—aukar farantin da abincin ke kai tace "Yaya Dacta to muje ka ci tunda ka ga har ka makara .

Bayan ya zauna a kujera ta Zuba masa basise a Plate ta É—eba masa pancake É—in ta zuba a gefe.

Duk abunda take yana bin ta da kallo cike da so da sha'awa komen ta a tsaftace dai-dai da yadda yake so .

Bayan ta zuba masa yayi bismillah ya É—au pankcake ya dangwali Basisen ya kai bakin sa ya gutsura

Daɗi da ƙamshin girkin ya ratsa shi , a karo na biyu Yakaka bata tsammata ba ta ga ya nufo bakin ta da Pancake ,

Noƙewa tayi tana kallon shi tace "idan ka gama nima zan ci ,

"Buɗe bakin ki Wafaa, yace muryar sa da sanyi amma ƙwarar idanun sa na mata umarni .

A hankali ta buɗe baki ya saka mata yana bin ɗan ƙaramin bakin ta da kallo yadda take cin abincin a kunyace ya so ba shi dariya "yarinya za ma ki sauƙe wannan kunyar ta ki ne a hankali "

sannu kan hankali ya ciyar da su iya cin su da su duk biyun sun yi mamaki domin kusan duk suka cinye sai fa kaÉ—an suka bari da bai wuce cin É—an yaro ba .

Sauƙowar Sofia ya ɗau hankalin Yakaka da ta hango ta sai ta ji wani abu ya ɗan taɓa ran ta da bata san mene ne ba , ta sai ji kamar ta muzanta ganin irin kwalliyar da Sofia tayi cikin wani yadi da aka yiwa kyakkyawan ɗinkin Riga da Siket da suka kama ta ɗam.

Tayi ɗaurin ɗankwalin zamani ƙamshi turaren ta ya riga ta isowa .

A hankali Yakaka ta saci kallon Doctor Hamza ta ga yadda yake bin Sofia da kallo da alamun kwalliyar ta ta ɗau hankalin sa , ganin ta ta mayar kan ta , ta ga tun atamfar jiya da daren nan ce a jikin ta sannan ba wata kwalliya a tare da ita , duk sai ta fara ganin laifin kan ta "Amnee cewa tayi kullum ki dunga ƙwalliyar Safe daban ta rana daban ta dare daban ta kwanciyar bacci daban . Zuciyar ta ta tunasar da ita .

Hakan yasa tayi saurin miƙewa kunnen ta na toshewa daga jin zantukan Doctor Hamza da Sofia da suka fara sabuwar gaisuwa ba'a ce sune ɗazu suke hayaniya ba .

Sofia ta shafe fushin ta kamar kome bai faru ba .

Taku biyu tayi ta ji hannu Doctor Hamza cikin nata ɗayan hannun sa kuwa riƙe da briefcase .

"Wafaa ni zan tafi ba za ki min rakiya ba ?

Murmushin yaƙe tayi tana ɗan kallon Sofia tace "zan tafi nayi wanka ne .

Wata 'yar dariya Sofia tayi kafin tace "anya kya yi wanka yanzu ? Ko da ...

Da sauri Doctor Hamza ya katse ta lokacin da yake sakin hannun Yakaka yace "Sofia na jima ban ji daddaɗan girki irin wannan ba ba domin Amnee kar ta hukunta ni ba zan ce ma ban taɓa cin basise mai daɗin wannan ba Sofi ki koyi girki ke ma zan ji iri..

Taɓe baki Sofia tayi tana hararar bayan Yakaka wacce ta riga ta juya tana barin wajen zuwa ɗaki kafin ta dawo da ganin ta kan Doctor Hamza .

Fuskar sa a É—aure yace "na faÉ—a miki ki daina neman fitina hakan ba kome zai jawo miki ba illa raini yarinyar nan dai a haife ma kin kusa haihuwar ta.

Kamar an soke ta da tsinin mashi haka Sofia ta ji , "ita zai ce ta haifi Yakaka ?

ƙanƙance ido tayi zata fara jaraba yayi wucewar sa cikin ɗaga taku yana barin falon ran sa cike taf da jin haushin korar masa Wafaa da tayi bata bari sun yi sallama ta masa rakiya ba .

Ta jima a tsaye a wajen tana rarrashin zuciyar ta da take ingizata akan ta je ta yiwa Yakaka dukan tsiya idan ya dawo ya ga banbancin shekarun a zahirance '

Sai dai ɗaya ɓarin zuciyar ta da yake cike da tsoron abun da hakan zai jawo ya hana ta aikatawa.

Sai da ta furzar da wata iska mai zafi sannan ta juya ta nufi É—akin da take É—aure Sam .

Yana kwance magashiyan kamar gawa , ƙafar ta tasa ta haure shi amma bai motsa ba " Dan ubanka kai ma ka tashi haka kaje kayi aikin da na kawo ka domin yi , ni inaga wannan maganin ma kamar ya maka ƙarfi yau ba zan baka shi ba .

Yakaka wacce har ta shiga wanka ta tuno da abincin ta na rana da ta ɓoye a kitchen cikin dabarar da take son yi , dan haka ta ɗaura towel ta zura hijabin ta ta murɗa ƙofar ta fito sai da tayi dube-dube ta samu tabbacin Sofia bata nan sannan da sassarfa ta tafi kitchen ta ɗauko sauran Basise da pancake da ta juye a warmer ta rufe ta nufo ɗaki.

zuwan ta tsakiyar falon yazo dai-dai da fitowar Sofia jaye da karen ta da yake ta turjewa yana wani É—an kuka .

Kallon-kallo suka yi a tsorace Yakaka ta jaa baya tana neman hanyar gudu cikin daƙiƙu kaɗan Sofia ta fahimci abunda Yakaka take shirin yi .

Dan haka ta zaburo bayan ta saki karen, da ganin haka Yakaka ta zuba a guje ta faɗa ɗaki da bata nesa da shi sosai tana shiga ta dire warmer ta danna ƙofar ta murza key bayan ta kulle ta zare shi daga jikin ƙofar dai-dai da ƙarasowar Sofia .

Wani irin duka Sofia ta kaiwa ƙofar kamar wacce ta sha giya ta shiga ƙundume-ƙundumen zagi tana cewa sai ta ga bayan Yakaka .

Yakaka wacce take jingine da jikin ƙofar daga ƙasa da ta zame ta zauna ji tayi hawaye na sauƙa a idanun ta wacce irin masifa ce wannan ?

"Ai kin kulle ƙofa a banza ki jira zan nuna miki iyakar ki zan nuna miki cewa nan gidana ne da baki isa min shamaƙi da wani ɓangare a cikin sa ba.

Tana jin lokacin da ta juya ta bar wajen bayan ta gama faɗin haka , ajiyar zuciya tayi ta miƙe tana ɗauke warmer ɗin daga wajen ta ajiye a gefen gado ,

Duk da ran ta na mata ciwo da irin yadda take rayuwar rashin Æ´anci amma ta ji daÉ—i da yau Sofia ba zata samu nasarar turo mata kare kamar yadda ta É—au alwashi ba ita daman ko babu kare a gidan ma yinin falo ba nata bane muddin Sofi na shawagi a gidan .

Wanka ta shiga ta ƙarasa ta kusa fitowa ta ji kamar an buɗe ƙofar an shigo ta ɗan kasa kunne bata ji motsi ba sai dai ƙarar rufe ƙofar da ta sake ji yasa a tsorace ta ɗauraye jikin ta ta fito .

Abun da ta gani yasa numfashin ta yin gargada 'Sam ne Sofia ta sake kawo mata shi kenan tana da makullin É—akin ? Yau ma so take tayi yini makamancin na jiya ?

Wani irin daskarewa take ji zuciyar ta na yi tsanar Sofi na ratsa kowanne lungu da saƙo na ran ta "sofia wace irin Azzaluma ce haka ? Da gaske idan bata bar gidan ba watarana Sofi zata kashe ta .

Kallon karen take yi tana jin yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa tamkar jinin jikinta ya tsinke .

Laɓɓan ta na karkarwa ta fara jaan ayoyi tana yin baya-baya ta koma cikin banɗakin ta rufo ƙofar , sai kawai ta fashe da kuka ,ita tun da ta san kan ta a matsayin mutum babu wani abun da take jin tsoro sama da kare ,

Bata son kare ta yadda ko da takun ƙafar sa ta gani a cikin ƙasa sai ta ji bugun zuciyar ta ya sauya Allah ya ratayawa ruhin ta tsoron kare .

Ta jima a zaune cikin banÉ—akin tana tunanin mafita "shin haka zata zauna kullum Sofi na azabtar da ita ta hanyar turo mata kare ? Ba zata iya ba domin watarana zuciyar ta zata gaza jurewa tsoron da take shiga sanadin haka sai ta mutu .

"To kuma idan ta faɗa me zai biyo baya watakila Sofi ta kashe ta da wuƙa da kuma ta san ba wanda zai san ita ta kashe ta domin daga jiya zuwa yau ta hango wani lamari tattare da Sofi da ya zarce mugunta sai dai a ƙira shi rashin imani.

" Wai kuma da gaske Yaya Dacta bai san da kare ba a gidan ? Anya gaskiya ne ?

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji karen na wani irin kuka ciki-ciki kamar gurnani , can kuma ta ji yayi shiru sai ta ɗan matsa kaɗan ta leƙa ta ƙafar makulli inda ta bar shi a kwance a can ta hango shi ya yada kai gefe .

Ta koma ta zauna tana tunanin yau kuma baya tsalle-tsallen ?

Har azahar tana cikin banɗaki har gyangyaɗi tayi ta farka lokacin ma ana ta sallah , ta sake leƙawa ga mamakin ta har yanzu fa Sam a inda yake anan yake kwance .

Shiru tayi tana nazarin sa da ta ƙura ido sosai sai ta ga kamar ma bacci yake .

yunwar da take ƙwaƙwular ta ita ta tunasar da ita cewa fa lokacin cin abincin ta na rana yana ƙoƙarin wucewa .

Tunanin da ya ɗarsu mata a rai a dai-dai lokacin ya sa tayi wani ɗan zullo tana dafe ƙirji a fili tace "wallahi bazan iya fita ba watakila idon sa biyu .

Can bayan kamar mintoci talatin da ta gama nazarin Sam ta haƙaƙe bacci yake yi sai ta buɗe ƙofar a hankali ta fito saɗaf-saɗaf ta nufi inda ta ajiye abincin ta kafin ta ɗauka sai da ta buɗe ƙaramin fridge da yake ɗakin ta ɗau ruwan roba mai sanyi guda ɗaya .

Tana juyawa kamar ance masa ya miƙe kawai sai ganin sa tayi akan ƙafafun sa huɗu yana kallon ta .

Wani irin ihu ta sa tana sakin ruwan hannun ta da warmer ɗin ta tarwatse a ƙasa da hakan yasa Sam ya dako tsalle yana zuwa a yunwace yasa bakin sa akan Basisen ya fara lasa yana haɗawa da pancake yana cinyewa bai ko bi ta kan Yakaka ba wacce tayi suman tsaye tana jira ta ji shi a kan ta yana kachal-chala mata tsoƙar jiki da faratan sa .

Wani irin riƙe jikin ta tayi har yatsun ta na shiga cikin carfet ɗin da yake shimfiɗe a ƙasa ji da tayi yana lasar rumfar ƙafar ta da basisen ya zuba akai a lokaci ɗaya wani irin tsoro mai haɗe da raɗaɗi ya ratsa tun daga ƙafar ta har ƙwaƙwalwar ta ta saki wani irin ihu da ya ratsa baki ɗayan gidan .

Numfashin ta kuma ya shiga ƙoƙarin barin jikin ta .

Ba zata iya sanin iyakar daɗewar da tayi ba kawai dai ta ji wani irin sanyi yana ratsa rumfar ƙafar ta da yasa ta buɗe ido a hankali .

Abunda ta gani ya matuƙar bata mamaki lokaci ɗaya da shiga sabon ruɗani .

Sam ne ta yake ta faman jido robar ruwan sanyi daga cikin fridge a bakin sa yana zuwa yana É—ora mata a jiki tamkar wanda aka sa shi yana yi yana kaÉ—a jela.

Tsam tayi tana kallon sa da idanun ta da suka rine jazur , sai da ya jido ruwan cikin fridge É—in kaf sannan ya dawo gaban ta ya tsugunna yana kallon ta tamkar mai jiran ta masa wani umarnin Sai zaro harshe yake yana lallago .

Kallon sa Yakaka tayi ta kawar da idanun ta zuwa lokacin har ta kai maƙura a tsoro alhalin babu mai ceton ta ba kuma wajen tsira dan haka ta fara dawowa cikin hankalin ta .

Tun tana tunanin zai bazamo kan ta har dai ta fahimci baya wani yunkuri na cutar da ita da ya wuce banga-banga da yayi a gaban ta dan haka a hankali ta kai hannu ta ɗau ɗaya daga cikin ruwan da ya jera mata bayan ta gama jujjuya robar ruwan a hannu ta ta ɓalle murfin ta sha ruwan da ɗan yawa kafin ta sauƙe gorar .

Mamakin ta ya ƙaru lokacin da ya sake kai fuskar sa ya daɗa turo mata wata gorar ruwan kusa da ƙafar ta .

Tana kallon sa ta kai hannu ta É—auka , sai ta ga yayi baya ya kwanta shirim! daga nesa kaÉ—an da ita .

Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tayi tana jin 'yar guntuwar nutsuwa na shigar ta sai ta gyara zaman ta da bata san yaushe ma ta zaunan ba ta miƙe kafafun ta da suka mata tsami saboda daɗewa da tayi a durkushe .

Cikin siririyar muryar ta ta fara yin karatun Alqur'ani bayan ta jingina kan ta da jikin gado.

Wata irin nutsuwa ce mai girma ta mamaye ta da ta lura hatta Sam shi ma ya samu kwatankwacin nutsuwar domin kwance yayi shiru ya kwantar da kunnuwan sa lanbar lokaci-lokaci yana kaÉ—a jelar sa .

Lokacin da ta fahimci rana ta kusa faɗuwa a hankali ta miƙe abun da ya bata tsoro a lokacin bai wuce ganin yadda shi ma Sam ya miƙe ba tsam ya tsaya '

da sassarfa ta nufi banɗaki tana waigen sa ganin yadda yake bin ta , yasa ta ɗan ƙara da gudu ta shige banɗaki bayan ta shiga ta rufo ƙofar kafin ta fara wanka sai da ta leƙa shi ta ga ya tsugunna a bakin ƙofar .

Cikin nutsuwa tayi wankan ta , kan ta tsaye ta murɗo ƙofar ta fito , yana ganin ta ya matsa mata a hanya ta wuce kafin ya bi bayan ta zuwa gaban madubi.

ÆŠan kallo shi tayi tana mamakin sa cikin ran ta ta aiyana "ashe ma ba zai min kome ba ?

Lokacin da ta gama shiryawa tsaf sai ta É—auko sabbin kayan ta wani lallausan yadi da aka yiwa adon manyan furanni launin ruwan dorawa da fari , É—inkin rigar iyakar guiwa irin ta matan N'djamena da aka mata tattara da roba daga kugun ta da É—an guntun hannu .

Ta ƙasa ɗan dogon wondo ne mahadin rigar da bai ƙarasa idon sawun ta ba , a fuskar ta bata wani cika kwalliya ba powder kawai ta shafa sai ta zizara kwalli a ƙasan idanun ta ɗaurin ɗankwalin da tayi sassauƙa ne ta nannaɗe gashin ta da shi ta baya yayi ɗan tum-tum ta ɗau turaren ta na humra ta shafa sai kuma ta fesa wani kaɗan da ta gani a gaban madubin ɗakin.

Cikin nutsuwa duk kuwa da bibikon da Sam yake mata amma ta dake zuciyar ta tayi ƙam-ƙam ta hana tsoron da take ji har yana mata wani yam-yam a cikin jini ya yi tasirin da zai haukata ta ,ta fara tattara ɗakin duk inda Sam ya ɓata ta tattare ta goge da Moper ta gyara ko'ina tsaf har gado , tana yi tana kallon Sam da yake mayar da ta shi ƙafar a duk inda ta cire ta ta .

Bayan ta gama gefen gado ta samu ta zauna ta É—au wayar ta da bata san lokacin da aka wargaza mata ita ba batirin daban wayar daban a take sofi ta faÉ—o mata a rai tana zaton ita ta mata haka da wayar .

Girgiza kai kawai tayi ta fara neman layin Hajja sai dai tayi ta ƙara daga can ba'a ɗaga ba.

Ɗan saurarawa tayi lokacin da ta ji ana ƙoƙarin buɗo ƙofar ta mayar da hankalin ta ga ƙofar ,

Kamar wacce aka tunkuɗo ta Sofia ta buɗe ƙofar ta shigo , turus ! Ta jaa ta tsaya tana rarraba ido a ɗakin da yake tashin ƙamshin humrar Yakaka ba kamar yadda take zato ba ko'ina tsaf yana ɗaukar ido kafin ta tsayar da ganin ta kan Yakaka wacce tun shigowar ta kallo ɗaya kawai tayi mata ta mayar da ganin ta kan Waya duk kuwa da cewar ta tsorata amma taƙi yarda tsoron ya fito fili .

"Sam .

Sofia ta ƙira shi a tsawace da wata irin muryar da ba Yakaka kaɗai ba har Sam da yake kwance daga ƙasa kusa da ƙafafun Yakaka sai da ya tsorata ya miƙe a safure ya shiga haushi ba ƙaƙƙautawa.

Sofia wacce a dai-dai lokacin duk wata dabarar ta tayi ƙaurar wucin gadi sai ta taho kawai fangam-fangam bayan ta zare takalmin da yake ƙafar ta ta takarkare iyakar ƙarfin ta ta kwaɗawa Sam tsinin takalmin a kan sa har sai da ya durƙushe.

,"ÆŠan iska cewa nayi ka zo kuyi soyayya da ita ? ba cewa nayi ka cije ta ka kashe min ita ba?

Wani irin kuwwa yayi da yasa Yakaka daka tsalle ta hau kan gadon tsoron ta yana dawowa sabo fil .

Sofi bata ankara ba ta ji ya kawo mata wafta da sai da ta kusa tuntsurawa tana ɗaga Ido ta hango takalmin ta a bakin sa ganin yadda yake gurnani yana nufo ta yasa ta fara jaa baya mamakance , laɓɓan ta na ɗan rawa ta fara ƙiran sunan sa

"Sam.Sam.Don't....

Ganin yadda yayi kan ta gadan-gadan ya san kasa ƙarasa kalmomin da take nufin furtawa sai juya ta ruga a guje Sam ya rufa mata baya da gudu da haushin sa da ya karaɗe gidan .

Yakaka wacce jikinta har rawa yake tsabar tsoro da gudu ta duro daga gadon ƙafafun ta babu takalmi ta fito daga ɗakin kai tsaye hanyar fita a gidan tayi a ruɗe "har a ran ta ta zaɓi barin gidan akan ta zauna Sam ya gama da Sofia da take uwarɗakin sa ya dawo kan ta .

Bata san da tahowar sa ba kamar yadda shima bai yi zaton fitowar ta ba a wannan lokacin suka ci karo.

Gaba É—aya ta faÉ—a masa a jiki ta chakume shi..

"Yaya Dakta wallahi kare nan zai cinye Anty Sofi ga su can ya bita da gudu zai kashe ta ya dawo kaina....

Da sauri ya ɗago ta tana sake ƙwaƙwume shi yanayin sa da galabaita sosai da tarin damuwa ya ɗago ta da kyar daga jikin sa bayan ya saki jakar hannun sa ta faɗi ƙasa ya riƙe fuskar ta a tsakanin tafukan sa .

"Me yake damun ki ne Wafaa ? Waye yake tsorata ki da kare ? FaÉ—a min aina kike ganin kare ? Yaushe haka ya fara faruwa da ke ?

Ya furta hakan idanun sa na tara ƙwalla saboda can daga cikin kan sa ya fara hasashen wani abu da baya fatan tabbatuwar sa a gare ta.

Laɓɓan ta na rawa tace "wallahi akwai kare a gidan nan kullum da shi nake wuni a ɗaki , Sofi ,Sofi ita take kai min shi kum....

"Safiya ?

Ya tambaya da wani irin yanayi a muryar sa bayan yanayin fuskar sa ya jirkitu da tsantsar ɓacin rai .

"Eh , Ah' ah ba ita ba amma akwai kare yanzu ma ya bi ta zai cinye ta dan Allah dan Allah yaya dakta ka mayar da ni gida , zan koma Maiduguri ko kum..

"Shit yace yana rufe mata baki "wafaa ki nutsu ni duk bana fahimtar inda maganganun ki ke dosa kika ce Sofia take kai miki kare É—aki ? Sofia ce take kawo kare gidan nan ?

A hankali ta sunkuyar da kan ta tana jin zuciyar ta na rabuwa biyu sashi É—aya tsoron Sofia yayi rinjaye É—ayan kuwa tsoron karen tare da son a fitar mata da shi daga rayuwar ta yana tunzura ta kan ta faÉ—i abunda ke faruwa.

"Sofia ta ke tura miki kare a ɗaki ? Ya sake tambayar ta da taushin muryar da ta ratsa duk wani firgicin da ya cika mata zuci ya mata lulluɓi da nutsuwar da yasa ta dawo hayyacin ta dan haka ta ɗago kan ta a hankali ta motsa laɓɓan ta "Yaya Dacta aun....

"Amarya da ango kenan watau shigar sauri kika min Yakaka shi ne har kika riga ni fitowa taren Miji ? To ai shikenan na ci girma na bar miki .

Sofia wacce take ƙarasowa ta furta hakan tana bin Yakaka da wani kallon da yasa Dactor Hamza kafe ta da ido yana nazarin ƙwarar idanun ta kafin ya bi jikin ta da kallo .

"Sofia me ya same ki haka ? Ya rigar ki a yage ?

Ya furta hakan yana mata nuni da jikin ta ba tare da ya saki hannun Yakaka ba .

"Ƙusa ce ta yaga min .

Ta furta hakan da yanayi na ko'in kula

"Ƙusa ya tambaya muryar sa cike da shakku .

"Eh

Ta amsa masa a daƙile kafin ta matsa kusa da Yakaka ta zira hannun ta a cikin nata tana karyar da murya tace "muje na taya ki girkin kin ga tun ɗazu nake ta cewa ki tashi muje ki fara ina taya ki kika ƙi kika jibge a gaban Tv kina kallo .

Yakaka wacce take kallon Sofia a tsorace É—imbin mamaki na tasowa yana rufe ta ta É—an kifta ido .

"Sofia muje ciki .

Doctor Hamza ya furta haka yana wucewa jaye da hannun Yakaka da ta bi shi da sauri bayan ta zare hannun ta daga cikin na Sofia da take jin sa kamar garwashi .

A falon ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun Yakaka kuma ta zauna a ƙasa.

Sofia da ta shigo daga bayan su ta zauna a kujerar da take kusa da wacce yake zaune bisa.

Sai da ya É—an nisa sannan ya tattara ganin sa akan Sofia fuskar sa ba alamar wasa yace "Sofia akwai kare a gidan nan ne ?

Mui-mui tayi da baki kafin ta dafe ƙirji tace "kare dai Doctor ? Ta ina ya shigo mana ? Ko d...

"Tambayar ki nayi kina sake tambaya ta Sofia ki bani amsa kawai .

Hararar sa tayi ta ƙasan ido kafin ta taɓe baki "babu kare a gidan nan idan akwai kuma ni bana ganin sa .

Yakaka wacce kan ta ke ƙasa ta ɗago da kan ta ta dubi Sofi da bata yi ƙasa a guiwa ba ta jefa mata wani kallon da yake ɗauke da saƙon gargaɗi .

"Ok

Yace yana miƙewa kai tsaye Sama ya dosa inda ɗakin Sofia yake da sauri ta miƙe ta bi shi a baya muryar ta tana ɗan shaƙewa tace "Doctor ko na zo ne akwai magana ? Ko wani abun kake nema ?

Bai kula ta ba ya cigaba da tafiyar sa zuciyar sa tana sake ba shi tabbacin rashin gaskiyar Sofi da duk yadda aka yi tana da hannu wajen tsorata Yakaka , a É—an tsukin ya fara gano wasu É—abi'un Sofia da a da bai san tana da su ba .

Sai dai duk inda yake zaton zai iya dubawa ya ga wani abu makamanci da kare da ake tsorata Yakaka da shi a gidan ya duba bai ga kome ba hatta cikin banÉ—aki da kitchen sai da ya duba .

A gajiye ya dawo falon inda ya bar Yakaka a nan ya dawo ya same ta ya zauna akan kujera lokaci ɗaya ya dafe kan sa da ke ɗan masa ciwo bayan tarin gajiyar da take kassara masa gabɓan jiki .

Shiru yayi har lokacin da Sofia ta ƙaraso wajen ta zauna fuskar ta wasai kamar an mata bishara .

"Wafaa ya ƙira Yakaka da tsauri a muryar sa .

A hankali ta É—ago kan ta.

"Babu kare a gidan nan .

Hawayen da bata san yaushe suka taru ba su ne suka silalo mata .

"A karo na ƙarshe ina faɗa miki ba kare a gidan nan ya kamata ki kwantar da hankalin ki ki daina wannan firgice-firgicen da kike yi ko kina son ƙwaƙwalwar ki ta samu matsala ne ?

"Docto wai daman akan haukar .....

"Sofia idan ina magana ki daina saka min baki please behave yourself.

Yace yana mata wani mummunan kallo gaba ɗaya daga ƙasan ran sa yana zargin Sofia da bai san dalilin hakan ba shi dai zuciyar sa bata aminta da ita ba akan wannan matsalar da tayi sammakon shigowa rayuwar auren sa da Yakaka da ko kaɗan abun bai masa daɗi ganin ta koyaushe a firgice tana guje-guje da safure-safure yana ƙona masa rai tare da sauƙar masa da gajiya .

"Wafaa ya ƙira ta a tausashe , ta ɗago kan ta da idanun ta da suke narke take kallon sa .

"Zan yi shirin Masallaci idan na dawo daga Sallah zamu je mu ci abincin kar ki shiga kitchen yanzu dare yayi .

Langaɓe kan ta tayi kawai bata amsa ba ko kaɗan bata son ya matsa ya bar wani sarari tsakanin ta da Sofi .

Mayar da kallon sa kan sofia yayi wacce take ta faman hura hanci tana kokawa da zuciyar ta da take jin har wani toroƙo take kamar za ta fashe

"Sofi anjima ina so nayi magana da ku baki É—aya .

Bai jira amsar ta ba ya miƙe , Yakaka ma cikam! Ta miƙe tana riga shi wucewa ta yi hanyar ɗakin su .

Da kallo ya bi bayan ta kayan da ta sa a jikin ta ya masa kyau matuƙa sai ya gan ta kamar irin kyawawan matan nan da ake tallan sutura da su .( model's ) a hankali ya taka ya bi bayan ta

Sofia wacce take zaune É—im!akan kujera ta kaiwa kujerar wani irin duka da hannu kafin ta toshe bakin ta da hannu wani irin kuka take yi ciki-ciki , irin kishin da take ji a ran ta akan Yakaka muddin bata É—au mataki ba za ta iya haÉ—iyar zuciya ta mutu.

Lokacin da Doctor Hamza ya idar da sallar Magarib yayi niyyar komawa gida amma yunwar da yake ji da kuma sanin da yayi a gidan ma shi suke jira tunda ya hana ayi girkin sai kawai da ya shigo gidan ya É—au motar sa ya sake fita ba tare da ya shiga cikin gidan ba .

Sofia da ta ji ƙugin tashin motar sa da sauri ta leƙa ta window ta ga fitar sa , tana ganin ya bar gidan a guje ta sauƙa ƙasa kai tsaye ɗakin Yakaka ta tasamma .

Tana murɗa ƙofar ta ji a kulle , ɗan kwankwasawa tayi cikin salon da Doctor Hamza yake yi .

Yakaka wacce take zaune ta miƙe a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar .

Haka kawai ta ji zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan haka ta dakata ta fasa bude kofar cikin siririyar murya tace "Waye ?

Shiru Sofi tayi tana fatan ta buɗe su gamu , sake dukan ƙofar tayi da karfi da hakan ya sa nan take Yakaka ta fahimci wace ce a wajen dan haka a sarari ta furta "Auzu Billah minash Shaytanir Rajeem, baya ta koma ta zauna a inda ta ta shi.

"Ya kamata na samarwa kaina da mafita ni Yakaka lamarin Matar nan ya fara wuce iyakata ta musulunci , ta furta hakan a sarari kawo yanzu ta haƙaƙe da gasken gaske sofi ta ɗaura ɗamarar yaƙar ta dalili kawai;sun hada Miji daya.

"Ina Mafita?

Haka Sofia ta gaji da bugun ƙofar tana surutai , jin shigowar motar Doctor Hamza ya sa tayi saurin barin wajen ta koma ɗakin ta kai tsaye banɗaki ta shiga ta sakarwa kan ta ruwan sanyi .

Kusan mintuna goma sha biyar suka kwashe suna jiran sofia ta zo su ci abinci amma shiru ba alamun ta sau uku yana ƙiran layin ta wayar tana ƙara bata ɗauka ,

Ran sa ya fara ɓaci da salon rainin da yake hango take-taken sa daga Sofia wanda kuma ba zai ɗauka ba .

"Wafaa hau sama ki ƙira Sofia .

Kamar bata fahimci abunda yake cewa ba haka Yakaka take jahiltar sa da ido .

Ganin yadda tayi da fuska ya sa shi miƙewa da kan sa ya nufi saman .

Yakaka wacce ta bi shi da kallo da tuno da abunda ya faru jiya daga zuwa ƙiran Sofi ya sa ta miƙewa tsaye da sauri .

"yaya Dakta .

Ta ƙira sunan sa ,

a hankali ya waigo.

"zan bika .

tace tana yin narai-narai da ido .

Bai amsa ba sai hannun sa da ya miƙo mata alamar ta taho da sauri ta isa gare shi tana jefa hannun ta cikin na shi , ya riƙe ta suka hau saman tare .

Sofia wacce take tsaye a maɓoyar ta tana ganin duk abunda ya faru kafin su ƙaraso ta fito da sauri kamar daga ɗaki ta fito ,

Wani irin kallo ta watsa musu kafin ta gyara fuskar ta tana cewa " Yaks manya ke dai ko ina kina liƙe da Miji ɗa Namiji daɗi ko ai kin saba .

"Sofi sau nawa zan faÉ—a miki ki daina min yawo a gida tsirara-tsirara ?

Doctor Hamza ya katse ta ba tare da ya bari zancen da tayi yayi tasirin da zai hana shi sukuni ba duk da cewa kalmomin ta sun taɓa ran sa .

Buɗe baki Sofi tayi cike da mamaki kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce ta sunkuyar da kan ta a tun kallon farko da tayiwa Sofi da take sanye da wasu bodycon sleeve rigar duk bata karasa kugun ta ba wandon kuwa iyakar shi ƙourin ta rashin kaurin da kayan ke da Su ya ya taimaka wajen fiddo da halittun jikin ta .

Narke murya tayi cike da kissa tana ƙoƙarin haɗiye fushin ta tace "Doctor kai ne fa kake cewa kafi son kana gani na a haka Kana jin daɗi tare da samun gamsuwar ido sobada ganin ko ina nawa a ciccike ko ka manta ne ? Kai ne fa kake cewa siririyar mace ramammiya haushi take ba....

A hankali Yakaka ta zame hannun ta tayi baya tana barin wajen saboda fahimta da tayi gaba kaÉ—an Sofi zata ce wani abu da zai fi haka ji mata ciwo .

"Duk ban tambaye ki wannan zancen ba dan na lura bakya jin kunyar ƙarya Sofi da girman ki amma ina so ki sani a yanzu ba mu kaɗai ne a gidan dan haka bana so na sake ganin ki haka kina min yawo a gida .

"Riga da wondo ne fa Doctor na ? Ta furta hakan a shagwaɓe zuciyar ta sol ganin Yakaka ta ɓace a wajen .

"Eh amma na 'yan iska ba ? Ko Wafaa ma ai riga da wondo ta saka amma na mutunci da zata iya fitowa a gaban ki kuma sun mata kyau sun burge ni .

"Ki koma ki sauya kaya ni ba zan iya cigaba da jiran ki cin abinci ba zamu fara ci dan yunwa nake ji .

Daga haka ya juya yana barin wajen , Sofi ta bi jikin ta da kallo kalmomin sa na dawo mata a kai "Doctor yana daf da kufce min na shiga uku ni Safiya ni ce yau yake cewa na dunga rufe masa jikin da a baya yafi kaunar ganin sa fiye da television?

Bayan sun gama cin abincin da Yakaka take jin sa ba wani daÉ—i sosai hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda duk suka haÉ—a ido da Sofi sai ta galla mata harara .

Dan haka tana gama ci ta miƙe zata yi tafiyar ta Doctor Hamza da duk yake kallon motsin su ya dakatar da ita ta dawo ta zauna har ya gama cin abincin sa .

Sannan ya fara yi musu nasiha cikin nutsuwa da fiye da rabin ta yafi karkata akan tunasar da su kan gujewa ɗaukar hakkin juna/cutar da juna sannan ya kwaɗaitar da su daɗin da za su ji su kuma jiyar da shi muddin suka zauna lafiya da juna a matsayin 'yan uwa ba abokan hamayya ba sannan ya tunasar da su shi aure bangare ne na ibada da ake samun ɗimbin lada a gurin Ubangiji Allah ta dalilin sa , dan haka yake jaan hankalin su da suyi ƙoƙari wajen ganin sun yi bautar su yadda ya dace. sai ya rufe da cewa

"Muddin kuka haÉ—a kai ku ka min rumfa ku ka bani kariya , ku ka bani kulawar da ta dace da ta samar min da nutsuwa ai ba za ku bar wata damar da wata za ta sake ratso tsakanin mu ba ku biyun nan kun isheni rayuwa ta duniya Safiya da Amina bayan ku duk sauran mata ba zan gan su har su burge ni ba

Da murmushi Yakaka take kallon sa kalmomin sa sun mata daÉ—i sosai kafin a hankali tace "Yaya Dakta da yardar Allah ba zamu zama sanadin tashin hankalin ka ba kai ma ka dunga mana addu'a Allah ya haÉ—a kan mu ya kori shaiÉ—an a tsakanin mu .

"Ameen Wafaa tun kafin yanzu ina muku addu'a zan kuma cigaba da yi muku insha Allah .

"Sofi baki ce kome ba ?

Ya furta hakan yana É—ora ganin sa akan ta wacce ta tattara hankalin ta duk akan fuskar wayat ta kamar bata wajen '

Sake yi tayi kamar bata jin sa duk kuwa da cewa sarai tana jin nasa shi ma kuma ya san tana ji dan haka ya É—auke ganin sa daga kan ta ya mayar ga Yakaka yana cigaba da cewa

"Sai batun kwanakin girkin ku bayan kin gama kwanakin ki bakwai na amarci kamar yadda addini ya tanadar da yau kike da kwanaki biyu a gidan nan dan haka yau mun samu kwana biyu ko Wafaa ?

Murmushi Yakaka tayi tana gyaɗa kai , a hankali ya miƙa hannu ya riƙo hannun ta da yake ajiye akan teburin gaban su kafin yace "to kwanaki nawa za ku dunga yi na girki kwana ɗaya ko biyu ?

Kallon Sofi tayi ta ga yadda ta zuba mata ido É—auke kan ta tayi murmushin ta bai É—auke ba tace "yadda duk kake so Yaya Dacta amma ana yin raba kwana É—ayan ne ya zama awanni 12-12 ?

Da mamaki tare da zumuÉ—in son jin manufar ta yace "idan ana yi me zai faru ?

A shagwaɓe Yakaka tace

" Sai ka dunga yini a sama 12 hours kana saukowa ni kuma mu kwana tare tunda ka ga ni fa ƙarama ce kuma 'yar siririya idan dodo ya zo min da dare ya zan yi ? .

Wata 'yar sassauƙar dariyar da take tafe da amon nishaɗi Doctor Hamza yayi kafin ya lakace tsinin hancin Yakaka yace " Wafaa lalle kam ke yarinya ce amma ba'a haka sai dai kwana ɗai-ɗaya ake yi dan haka zan dunga kwana ɗaya a sama ɗaya a ƙasa tare da ke kin ji..

" What the hell ? Dole mana ki ce haka tsohuwar kilaki uwar jarababbu , idan karuwancin kike ji da shi ai da sai ki cigaba da tsayawa a bakin titi kamar yadda kika saba a can ba za ki rasa wanda za ki dunga kwana da shi ba kullum amma tun da kika auri Mijina wal.'

"Sofi bana son hauka da rashin tarbiyya a gabana kike zagin ta daga wasa ? ..

Doctor Hamza ya katse ta a tsawace .

Bata dube shi bare ta yi ko gizau ta cigaba da cewa

"Kuma wallahi ban yarda da kwana bakwai ba wannan bazaurar za'a yiwa kwanaki bakwai da ake yiwa budurwa gal a leda ? Daga gobe kwanan ta uku ya ƙare kuma kwana biyu nake son a dunga yi na girkin aikin banza tsohuwar 'yar iska kawai za ki zo kina wani yen-yen-yen wai ke ga 'yar barki to na bi barikin da gudu .

"Sofi zan matukar saɓa miki idan kika sake maimaita makamantan kalmomin da kika furta , Wafaa Matata ce ni ne nake auren ta ba ke ba , budurwa ce ita ko ba budurwa ba ce ba hurumin ki bane , A sanina bata taɓa aure ba dan haka a matsayin budurwa na aure ta ko da kuwa ba budurwar bace tsautsayi ya gifta a rayuwar ta kamar yadda na aure ki a matsayin budurwa duk kuwa da ban samu tabbaci kan tsautsayin da ....

Wani irin ihu Sofi tayi tana miƙewa tsaye tayi kukan kura ta jawo Yakaka ta cukui-kuye ta bata cikin hayyacin ta take jijjigata "sai kin faɗa min irin asirin da kika yiwa Mijina da tun ranar da ya fara ganin ki ya susuce akan ki tun kina kuchakar ki ƙazama fiye da shekaru shida na zauna a ƙarƙashin mulkin da kike yi a zuci..

"Sofiya ki sake ta , ki sake ta nace kafin na saɓa miki .

Doctor Hamza yake furta hakan yana ƙoƙarin shiga tsakanin su ko kusa shi ba mutum bane mai son tashin hankali da hayaniya ga Sofi tana neman dagula masa lissafi ta ko'ina .

Ƙarar marin da ya karaɗe wajen ya taho da wani ɗan takaitatcen shiru a bayan sa 'tsit' kamar an kashe radio sai numfashin Sofi da ke sassarfa yana kai kawo lokaci ɗaya idanun ta ke tsartuwar wasu zafafan hawaye da take jin ɗacin su har a maƙoron ta hannun ta ɗaya dafe da ƙuncin ta ta ɗaga ɗayan hannun tana ɗorawa a kirjin ta da wata shaƙaƙƙiyar murya tace "Doctor Ni Ni Ni ka mara ?

Jaan numfashi tayi kafin ta juyar da ɗan allin ta kan Yakaka da take laɓe a bayan Doctor Hamza tana leƙen ta tace "akan wannan ka mare ni ? Akan ta ?

Ba sabon sa bane dukan mace shi ko hararar Matar auren sa bai cikin tsarin rayuwar sa sai fa da Allah ya haɗa shi da 'yar gagara irin Sofi yasa dole a wasu lokutan yake ɗaga mata muryar sai dai duk da haka a duk zaman su bai taɓa ɗora hannu akan ta ba sai fa yau da ta kai shi maƙura ta gajiyar masa da ruhi da gangar jikin sa sannan kuma tsananin So da yake yiwa Yakaka ya ingiza shi ganin tana neman ji mata ciwo bayan irin kalamai na ɓatanci da take furzo mata da suke tafasa masa rai '

Nadama na son kawo masa farmaƙi ya ɗaga hannun sa yana mai matsawa kusa da ita yace "Mu ga gurin baki ji zafi ba ko ? Ai ke ce kika jawo Sofi .

Da sauri ta kauce idanun ta har wani jirkituwa suke yi saboda tsabar tashin hankali da ruÉ—anin da take ciki.

Ta buÉ—e baki amma ta gagara cewa kome ko'ina na jikin ta tsuma yake kawai sai ta juya da maÉ—aukakin taku ta bar wajen kamar ana ingiza ta .

Da hannun sa É—aya ya dafe kan sa bayan barin ta wajen gaba É—aya nadamar É—ora hannu akan ta yake yi ,"Nagartatcen Namiji ba ya dukan Mace , zuciyar sa ke tunasar da shi hakan.

waje ya samu ya zauna ya yi tagumi da hannu biyu, Yakaka wacce ita ma jikin ta yayi sanyi akan abunda ya faru duk tana ganin kamar har da laifin ta ita ta tunzura Sofi a ƙoƙarin ta na ganin ta rama wasu kalmomin cin fuska da ta san da gangan Sofia ke furta Su a gaban ta dan ta bata haushi.

Durƙuso tayi a gaban sa tana jin tausayin sa na kawo mata "duk ke kika jawo ɓangaren zuciyar ta ya ƙalubanci ɗaya ɓangaren.'

"Yaya Dakta kayi haƙuri d..

Shit yace mata yana sauƙe hannun sa ya ɗago ta daga durkuson da tayi ya mata wajen zama akan ƙafar sa idanun sa da suka yi ciki saboda gajiya da damuwa su ya ɗaga yana bin ta da kallo rigar jikin ta duk ta yamutse har ta yage ta wuya saboda cukumar ta da Sofi tayi , idanun sa ya sauƙe a ƙasan wuyan ta kaɗan da duk yayi birɗi-birɗi kamar borin jini .

Da sauri ya wara idanun sa kafin ya kai hannu yana janye rigar da hakan ya bashi damar ganin jikin ta sosai, da Sauri a kuma tsorace yake duba sashin jikin ta da gaba daya yayi burÉ—i-burÉ—i.

"Wafaa wannan anxiety rashes É—in me ya kawo miki su ? Tsoro ? Tsoron me kike haka ? Wafaa ki rage tsoro ba abunda zai same ki a duk lokacin da kika tsorata da wani abu kiyi addu'a Wafaa .

"Kin ga yadda duk jikin ki ya tashi , kin ga duba .

Yace yana nuna mata hannun ta da shi ma duk yayi ruÉ—u-ruÉ—u .

Fuskar ta ya riƙe da hannun sa kafin yace "faɗa min me kike tsoro ?

Sauƙe idanun ta tayi kafin a hankali tace "Babu .

"Babu ? Ya tambaye ta cike da shakku

"Eh .

Ta amsa tana miƙewa daga kan shi "yaya Dakta zan tafi na kwanta dare ya fara yi.

Taku ɗaya tayi ya riƙo hannun ta kafin ta ankara ya dawo da ita inda ta tashi ya kewaye ta da hannun sa kafin ya kwantar da kan shi a ƙirjin ta yana shaƙar ƙamshin jikin ta yace "meyasa za ki gudu ki bar ni bayan kin san ina da damuwa ? Ba zan ji daɗi ba idan aka ce zaman ku ya zama haka , ba zan samu farin-cikin da Magidanta ke samu a gidajen su ba muddin kuna faɗa . ina tsoron gaba na samu rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yana .

Shiru yayi kafin ya ɗago kan sa daga jikin ta da taimakon hasken da yake wajen tar ta iya hango yadda idanun sa suka yi jawur da har sai da tsigar jikin ta ta miƙe .

"A gare ki ina zaton zan samu kwanciyar hankali Dan Allah kar ki min bazata kin ji ?

GyaÉ—a kai tayi duk da bata gama fahimtar kalmomin sa ba ya É—ora da cigaba da cewa
"Duk abinda Sofia za ta miki kiyi haƙuri kar ki dunga biye mata kuna tashin hankali fitina ba halin ki bane Wafaa kar ta ɓata min ke .
"ke saliha ce managarciya salihar mace irin ki bata tashin hankali duk abinda zata faÉ—a kar ya tunzura ki har ki biye mata kuyi rigima kin ji ko ?

Ya furta hakan yana ƙurewa fuskar ta kallo, ɗago kan ta tayi su ka haɗa ido

Kalaman sa sun mata tasirin da yasa ta lumshe idanun ta da wani boyayyan murmushin da ya ɓullo daga can ƙasan ran ta har wani danshi take ji daga saƙon zuciyar ta yana ratsa mata sassan jiki samun yabo a wajen wanda kake neman yarda da amincin sa abu ne mai daɗi da haifar da nishaɗi.

ba tare da gangar jikin ta tayi shawara da ita ba sai ta tafi a hankali ta kwanta a jikin sa tana kewaye shi da nata hannun da hakan ya sa shi rufe Idanun sa ya matso da ita sosai jikin sa ya rungume ta .

Daɗewa da yayi yana fama da son ta daɗi da yadda yake kan gabar neman mai tallafin sa a dai-dai lokacin da ƙwaƙwalwar sa ke buƙatar hutu sai gangar jikin sa ta mata tarɓa na musamman da ahankali ya fara bin jikin ta da hannun sa ya shiga gwadama mata zallar ƙaunar da yake mata tun a mafarin farko.

Tana jikin sa ya miƙe tare da ita cike da gudun abun da zai gifta tsakanin su ya daƙile masa daddaɗar nutsuwar da yake samu a tare da ita da ba zai ce ya taɓa samun makamanciyar ta ba .

Washegari a tare suka tashi cike da nishaÉ—i suna hirar su suka shiga kitchen tare tana girkin ta yana mata hira da tsokanar ta lokaci-lokaci yana É—an kasa kunne ko zai ji motsin fitowar Sofia amma ko alamar ta babu har lokacin da ya koma É—aki yayi shirin tafiya aiki ya fito suna shirin fara cin abinci Yakaka ta danne zuciyar ta a hankali tace "Yaya Dakta har yanzu bata fito ba ko za ka kira ta muyi breakfast ?

Kallon ta ya yi da yanayi na ko'in kula a muryar sa yace "ita da kan ta za ta fito kyale ta .

"Zuba mana abincin mu ci ina sauri Wafaa.

Cikin nutsuwa ta zuba musu soyayyan dankalin da ƙwai hadi da soyayyar ayaba , sai kuma farfesun marara zallah da tayi masa dafuwa irin na mutan Ndjamena (shurban) a ƙasa ta ajiye musu abincin a tsakanin su .

Suna ci Doctor Hamza yana ta santi , jin sa yake kamar ya dawwama a haka yana kallon fuskar ta da take cike da annuri .

Bayan sun gama cin abincin ya goge bakin sa da tissue "Wafaa ya ƙira sunan ta.

"Unmh
Ta amsa tana ɗago kan ta hannun sa da yake miƙa mata wani kwali mai kyau ta bi da kallo ba tare da ta karɓa ba ta daga idanun ta ta mayar kan sa da sigar tambaya?

" karɓi mana , sabuwar waya na saya miki ta hannun ki bata da wani amfani koyaushe na ƙira ba kya ɗauka kamar jiya kam ma a kashe ta wuni , bana jin daɗin haka na fi son na dunga jin ya kike ? Ko da bana gida .

Da yalwatatcen murmushi tare da ɗan boyayyen zumuɗi ta karɓi kwalin kafin ta fara kici-kicin buɗewa bai dakatar da ita ba har sai da ta buɗe ta zaro sabuwar waya sumfurin iPhone8+ da take ta daukar ido .

"Masha Allah .
ta furta a sarari lokacin da take kallon sa with her light brown eyes that were deeply creased with smile line at the coners.

"Yaya Dakta Wannan wayar ta 'yan gayu tawa ce?

Ta furta hakan da zallar farin-ciki kafin ta É—ora da cigaba da cewa " Kai wallahi nagode sosai , ina nufin nagode dayawa Ya Dakta Allah ya daÉ—a ma buÉ—i da arziki mai Albarka...

"Wafaaa

ya ƙira sunan ta ƙasa-ƙasa yana jin yadda farin-cikin da ya hango tare da ita ya ke ba shi wani shauƙi na musamman

Kumatun ta ya ɗan shafa yana miƙewa tsaye bayan ya ɗauki briefcase din sa da murmushi yace " Wafaa I can bring the whole world to you if I have it.

A hankali ta dago kan ta rana ta farko da ta ji kamar tana son mayar masa da martanin tsadaddun kalaman sa tana so tace wani abu ko da kadan ne akan tarin alkhairin sa marasa adadi da ya wanzu yana hidimta mata, "to me zan ce ne? Ta tambayi kan ta, daga can ƙasan ran ta kalmomin suka haɗo kan su suka fito ta tsakanin laɓɓan ta ba tare da ta janye ƙwarar idanun ta da ke cikin na shi ba ta ce "I always cherish your company Yaya dakta for that I'll forever serve you and do anything for you here in Duniya insha Allah. Thank you for everything! I mean everything Yaya Dakta.

Ɗage girar sa yayi yana jin sa kamar mai yawo a sama kalmomin nata taƙaitattu ne amma masu faɗi ne a wajen sa da zai yi zama na musamman domin yi musu fashin baƙi ,

" I appreciate that and I cherish yours even more, integrity you're worth-valuing, worth-treasuring and worth-cherishing. Your value is such unfathomable Wafaa.

zamewa ƙafar Sofia tayi da ƙiris ya rage ta gangaro daga ƙafar bene, bata taɓa sanin ƙeyar mutum na da ido ba sai da ta ji tana taka matakalar bene ta baya , kalaman na mata amsa kuwwa suna mata rakiya har ɗakin baccin ta da ta na shiga ta zube a ƙasa kan ta na juya mata tana ganin kome na dakin yana tafiya da kafafun sa.

A narke Yakaka take kallon sa lokacin da yake furta mata kalmomin da suka mata zurfi wajen fassara har ya sunkuyo ya sumbanci goshin ta, " ni zan tafi Wafaa .

Ya furta haka yana ɗaga taku ya nufi hanyar ficewa daga falon har ya kai ƙofa ya waigo ta , kallon sa take da murmushin da yafi so a tare da ita a hankali ya ƙarasa ficewa a falon ran sa cike taf da ƙaunar ta fuskar ta tana zanuwar masa a cikin rai yana jin zata ishe shi farin-cikin yau har ya je ya dawo .

Ya tada motar sa a hankali yana ficewa a gidan zuciyar sa na daÉ—a hasko masa yanayin da ya bar ta a ciki " she's smiley, she is smile just like the sunflower. Ya furta hakan a sarari.

Cike da zumuɗi Yakaka ta kunna wayar da cikin sa'a ta tarar da sabon Sim a ciki , duk da bata taɓa riƙe babbar waya ta kan ta ba amma bata gagara sarrafa wannan ɗin ba saboda Lubna tana riƙe irin su a wasu lokutan tana karɓa tayi 'yan taɓe-taɓen ta saboda sosai manyan wayoyi suke burge ta dan dai kawai bata da damar mallakar su ne .

Ta kwashe tsawon lokaci tana wasa da wayar cikin taka tsan-tsan ta shiga nan ta fita can kafin ta miƙe tana riƙe da wayar duk hankalin ta na kai ta tafi ɗaki ta ɗauko tsohuwar wayar ta ta kunna ta cike da zumuɗi ta kwafi number Hajja akan sabuwar wayar ta ta fara ƙira da ɗokin son ta yiwa Falmata albishir .

Bugu ɗaya Hajja ta ɗaga tana ɗauka da ta ji muryar Yakaka sai ta sa dariya "Ah ka ga manya a baku naku daban Babba Uwar Mama uwargida kuma Amarya a gidan Babban likita , ai yau kwana uku kenan uwarɗakina tana nacin ƙiran wayar ta ki bata samu tun ranar da muka samu labarin kin tare da fatan ana Amarci yadda ya dace ?

'Yar dariya Yakaka tayi ta fara sabo da halin Hajja na jaan zaren magana tayi ta tsawo , "Hajja kenan muna lafiya ya ya wajen ku ?

"Mu ma lafiya ras muke bari na miƙawa gimbiyar wayar ku yi magana tana ɗaki .

"To Hajja nagode .

"Ince da kuÉ—i a wayar ta ki ? Kar ki katse yanzu zan ba ta

A zaune ta tarar da Falmata ta tasa cikin ta a gaba da cikin kwanakin nan yake wani irin girma na ban mamaki daga gefen ta faranti ne a cike da warmers ɗin da aka shaƙe cikin su da kayan cimaka .

Miƙa mata wayar Hajja tayi tana cewa "Uwar biyu ma za riƙe waya Babba Uwar Mama ce ke kai .

Zunbura baki Falmata tayi kafin ta karɓi wayar tana cewa "Hajja ina faɗa miki bana son sunan nan wai Uwar biyu dan Allah Hajja ki daina .

Ta ƙarasa zancen tana kara wayar a kunnen ta dariyar da Yakaka take yi ita ta fara sauƙa a kunnuwan ta da yasa ita ma ta saki 'yar sassauƙar dariyar jin daɗin sauraron tashin muryar 'yar uwar ta da cikin kwanakin nan take jin kewar ta matsananciya .

"Yakaka na .

Ta ƙira ta da dariya , bata jira ta amsa ba ta ɗora da cewa "wallahi nayi fushi Ya yanyi3 ki ka koma Abuja ba muyi Sallama ba kuma bakya ko nema na yaya Dakta ya mantar da ke ni ko.?

Dariya Yakaka tayi tana rufe bakin ta da hannu ta ce "Falmata sharrin da za ki min kenan ? Haba Falmata na tayaya zan mata da ke 'yar uwa rabin jiki , kiyi haƙuri tunda na zo bana cikin kwanciyar Hankali ne Falmata na ....

Da sauri Falmata ta katse ta "Yakaka bakya cikin kwanciyar hankali ? Me yake damun ki ? Sofi ce ko ? Me take miki ?

"Falmata , abunda Sofi take min ba kyau ta takura min ta hana ni sakewa har fa kare take kawo min cikin É—aki'....''

"Me ...? Kare ?

Falmata ta katse ta hankalin ta a tashe har tana wani É—an yin zillo da hakan ya jaa hankalin Hajja da take shirin barin É—akin dan ta basu dama suyi hirar su ta 'yan uwa ta É—an dawo da baya tana cewa "UwarÉ—akina ince dai lafiya ?

"Wallahi Falmata kare Sofi ta kawo gidan nan take kulle'....

Chak ta tsaya da bayanin da take sakamakon bugo ƙofar da Sofi tayi ta shigo a haukacen ta daga yadda take gama hanya na nuni da alamun ta shawu .

Cikin Yakaka yayi wani ƙugi ƙululu , ba tare da ta katse wayar ba ta sauƙe ta daga kunnen ta ta riƙe ƙam a hannu lokacin da take miƙewa ta tsaya akan ƙafafun ta .

Daga can Falmata ta ji shiru Yakaka ta katse zancen da ta faro yi mata zare wayar tayi a kunnen ta ta duba ta ga cewa Yakaka bata ajiye wayar ba , sanya wayar tayi a handsfree da zaton ko network ne da ɗan ƙarfi tace "Hello Yakaka kina jina ? Ki min magana..

Sautin da ta ji ya fara fitowa daga cikin wayar ya sa tayi saƙare tana kallon wayar .

"Yakakaakaa ko ? Ko Wafaaaa in Doctor voice ? Ko Aminaa Aminaa , whatever dan ubanki me na faɗa miki akan rayuwa ta da kika shigo kin manta alƙawarin da na miki dan me koyawa tsohuwar ki darasi ? Da har ki ka iya yin tsaurin idon yi min rashin kunyar da ta sa aka mare ni akan ki Kin yi kuskuren da ba zan bari ki maimaita makamancin sa ba .

Girgiza kai Sofi tayi kamar lokacin aka mare ta ta riƙe ƙuncin ta "Mari ni Sofi aka mara akan ki.?

Taku ta fara yi tana kusantar Yakaka wacce ko ba'a faÉ—a mata ba ta fahimci manufar Sofi , kuma tuni ta fara neman hanyar tsira .

Laɓɓan ta na rawa ta fara jaa baya tana cewa "Anty Sofi Dan Allah kiyi haƙuri walla.'..

Wata waftar da Sofi ta kawo mata ya sa ta daka tsalle ta tsallaka kan gadon ta hau ta tsaya..

"Zan kashe ki Yakaka na ga abunda zai faru ba dai kin gwada min naci ba ? Kin nuna a dole Mijina naki ne ko ? To sai na kashe ki kamar yadda na sha alwashi.

Daga can kuka Falmata ta sa ta yunƙura da ƙyar ta miƙe jikin ta na rawa ta miƙawa Hajja wayar da duk abunda Sofi take cewa a kunnuwan su muryar ta na rawa tace "Hajja , Hajja kin ji wai Sofi za ta kashe min Yakaka wallahi kuma za ta iya dan Allah ki bata hakuri Hajja.

Karɓar wayar Hajja tayi ta shiga cewa "alo 'Alo babba uwar Mama ba wa mahaukaciyar kishiyar ta ki wayar dan ƙunduƙurin ubata yau ji min tsinannana? Kishi hauka ne?

Jin shiru yasa Falmata ta sake rikicewa da muryar da take gaf da fara kuka tace ,

"Yakaka , Yakaka Dan Allah kiyi magana , Yakaka ki gudu dan Allah kar ta kashe ki..

"Ke jaa can ar kishiyar za ta guduwa ? Zancen banza ma kenan ,mugun nufi ai baya kashe ɗan barewa Babba uwar Mama zage ki taushe bakin akuyar wofi ki ɗaga ta sama ki doka ta da ƙasa kika yadda kika gudu ni da ke ne , nace ki zage ƙwanji 'yar nan ki kwaci 'yancin ki ta isa ne ma ta kashe ki ? Naushe ta a ƙahon zuci nace.

Hajja ta furta hakan har tana kaiwa iska duka tana cije baki cike da jin wani irin takaici na rufe ta .

Daga can kokawa tuƙuru ta sarƙe tsakanin Yakaka da Sofi da take neman shaƙe Yakaka amma ta kasa samun galaba abun mamaki wani irin ƙarfi ta tarar Yakakan na da shi da ko kusa ba ta yi zaton sa ba dan haka bata ankara ba ta tunkuɗa ta baya bata yi aune ba tayi baya ba shiri daɓas ta zauna da manyan mazauna ta akan wata ƙwalbar turaren da ta faɗo sanadin kokuwar da suke nan take kwalbar tace fusss! Ta fashe a take ta soki ɗuwawun ta.

Lokaci ɗaya wani irin raɗaɗi ya ratsa mata ƙwaƙwalwa da yasa ta saki ihu kafin ta dawo hayyacin ta Yakaka da daman matsera take nema ta tsallaƙe ta da gudu ta fice daga ɗakin bata tsaya ba ta buɗe ƙofar falon ta fita daga ita sai kayan jikin ta ƙafar ta ko takalmi babu sai fa wayar ta da take riƙe ƙam a hannun ta .

Sofi wacce bata saurari azabar da mazaunan ta ke mata ba ta fito gaba gaɗi tana ganin ƙofar falon a buɗe ta fahimci Yakaka ta fice a gidan abunda daman take so kenan .

Dan haka ta tura ƙofar falon da ƙarfi ba tare da ta kulle ba ta juya ta hau sama saboda raɗaɗin da take ji a mazaunan ta tana son ta duba irin raunin da ta ji.

Yakaka wacce take tsaye daga harabar gidan ta hango rufo ƙofar da Sofi tayi dan haka a galabaice ta samu waje daga gefe ta zauna baki ɗaya bugun zuciyar ta ba dai-dai yake ba .

Sofi ta kulle mata ƙofa ta bar ta a waje da tazarar tsakain ta da titi bai wani cika nisa ba sauran mutanen da suke makwaftaka duk za su iya ganin ta haka babu mayafin kirki wannan wane irin rayuwa ce take yi ?

Kiran wayar ta da aka yi yasa ta duba fuskar wayar sunan Hajja ta gani dan haka ta É—auka tana É—agawa daga can Falmata da ta kasa zaune ta kasa tsaye ta ce "Yakaka ke ce ? Bata mi ki kome ba ko.? D''

"Falmata ni ce eh na samu na gudo ki....'

"Kika gudu ? Gudu fa kika ce ?

Hajja take tambayar ta daga can kafin Yakaka ta ce wani abu Hajja ta karɓe wayar daga hannun Falmata tana cigaba da cewa

"Ke wacce irin Solobiya ce ? Kishiyar ke bin ki kina rugawa da gudu dan ragwanta da mutuwar zuciya kenan ko me ? Bakya tsayawa ki nuna mata banbancin ƙwarin jikin tsohuwa da na yarinya ? Wai ko ba wannan fantekar matar ta babban likita me jemammiyar fuskar nan ba ce ? Yanzu ita kike gudu ? Ita kike tsayawa tana cashe miki haka ba ki rama ba ? to wallahi kin rako mata 'yar nan ah lalle fa kina ina yanzu ?

A sanyaye Yakaka tace "ina waje harabar gidan Hajja ta koro ni wallahi tsoro nake ta ɗau wuƙa ta soka min dan haka ta ce min wai wallahi za ta kashe ni kuma ni wallahi bana son tashin hankali Hajja ni fa ko musu na fatar baki ciwon kai yake saka ni bare danbe hajja....

"A ah ai fa lalle abun nayi ne wai an biyawa bazaura Hajji , na gani na kuma shaida haka waliyya to kina jina ko ?

"Ba dai ita ta ce 'yar iska bace? Zata hana ki rawar gaban hantsi ke da gidan Mijin ki da ke kuma ta same ki solobiya kike biye mata ?

"Hajja .....

"Yi min shiru 'yar nan barni da ita ke dai bin umarni ne na ki , ince dai can layi ta koro ki ?

"Eh Hajja .

"Da mutane a wajen ko kuwa ?

"Eh da mutane dai kaÉ—an .

"A yaya kika fito titin ?

Yakaka ta É—an yi jim ita fa bata cika son biyewa subaÉ—aÉ—in Hajja ba muryar Hajjan ta katse ta da ta ji tana sake cewa

"Nace da kayan arziki a jikin ki ko kuwa É—an diras ne a jikin naki ?

"Hajja da kaya a jikina .

"To yaga su

"Eh Hajja?

"Nace ki yage kayan ki musu mummunan yagu .

"Haba Hajja ya kuma za ki ce ta yaga kayan ta a waje fa take ?
Falmata ta furta hakan tana zaro ido da mamaki

" kar ki katse ni ki min shiru '.

"Babba uwar Mama kina jina?

"Ina jin ki Hajja ki saurareni da kyau 'yanci nake son taya miki ki kwato , shi maganin biri karen maguzawa dan haka duk abinda nace miki kiyi , kiyi kawai ina mai tabbatar miki daga yau bata sake chakumar ki da dambe bare har ta kora ki layi .

"Ince kina da layin wayar shi Hamzan ?

"Ina da shi Hajja

" You katse ƙiran nan ki ƙira shi ki tabbatar kina gunjin kuka za ki ƙira shi kice ya taho yanzu ga matar sa za ta kashe ki kina faɗin hakan idan kin tabbatar ya ji sai ki kashe wayar daga nan ki sake ƙira na.

Doctor Hamza ya gama round kenan misalin sha biyu saura ya ga ƙiran Yakaka , fuskar sa cike da annuri ya ɗaga ƙiran yana jin 'yar guntuwar gajiyar na barin jikin sa .

Sai dai me ? Muryar ta da ya ji cikin kuka ya sa zuciyar sa yin tsalle hankalin sa a tashe yake tambayar ta me ya faru ? Tana kuka ta fara masa bayani bai gama saurara ba ma ya katse wayar hankali tashe ya fara ƙoƙarin barin asibitin .

Yakaka tana sauƙe wayar ta ƙira Hajja da daman tsumayar ta take dan haka nan take ta ɗaga "na ƙira shi Hajja . Ta ce a sanyaye .

"Yauwa ta farka rigar ta ki ta waje-wajen wuyan sannan ta ƙasa ma ki yiwa zanin naki ko siket mummunan yagu ta wajejen cinyar kina jina ?

"Hajja dame zan ya ga ? ba zai ji daÉ—i ba idan ya gan ni haka jiki a buÉ—e a waje .

"Kin ci gidan ku ana son ƙwatar miki ƴanci kina gardama cewa nake fitinannar matar sa ta koro ki ? Yi maza ki yage kayan nan dan a kori gaba .

Ba yadda Yakaka ta iya haka ta ɗan yiwa kayan jikin ta rauni da ƙyar saboda ƙarfin su .

Hajja tana iya jin ƙarar ɓarkewar kayan tace "Yauwa to sai abu na gaba da kin dai-daici ya kusa zuwa ki cisge ɗankwalin kan ki ki yasar , kuka kuwa kar ki ƙaƙƙauta har sai kin ga nata hawayen ita ma ba dan kome nasa kiyi haka ba sai dan a kori gaba kin fahimta ko.?

"Naji Hajja .

"Madallah.

Ba'a rufa mintuna goma ba sai ga Doctor Hamza a guje da motar sa da Yakaka tana hango shi ta fara kukan da daman yana cin ran ta kan irin tozarcin da Sofi ke mata.

Ƙafafun sa kamar ba za su iya ɗaukar sa ba ya fito a motar idanun sa da suke bayyana tashin hankali akan ta yana bin duk saassan jikin ta da kallo .

Yana ƙarasowa Yakaka ta faɗa jikin sa shi ma ya riƙe ta gam da wani irin yanayi a muryar sa yace "wa ya mi ki haka ?

Tana shiƙar kuka tace "auntie Sofi .

Hannun ta kawai ya kama suka nufi ƙofar shiga gidan yana murɗawa ya ji ta a ɓude '

"Sofi Wacce take baje akan kujera tana zuƙar shisha daga ita sai 'yar doguwar rigar shan iska gefen ta Sam ne a kwance daga ƙasa ta tasa masa abincin sa a gaba yana ci .( irin ita Bosslady )

Lokacin da ta ɗago kan ta tayi zaton Yakaka ce sai kawai tayi ido huɗu da Doctor Hamza da yake tsaye yana mata wani irin kallo na tsana daga bayan sa kuwa Yakaka ce take rakuɓe .

Assalam Alaykum masu karatu da fatan alkhairi.

Ina dai neman afuwar ku yau da gobe ta fi ƙarfin wasa jiki kuma da jini .

Ina kaunar ku domin Allah.'

Nagode
[4/15, 8:07 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
......... HARGITSIN RAYUWA

UMM' MUAZ

54

MAI RABON SHAN DUKA

Ganin irin mummunan kallon da Doctor Hamza yake yi mata bai karya guiwar Sofi ba da zai sa har ta gaza yin wani yunkuri kare kanta ba .

Dan kuwa zuruf ta miƙe bayan ɗan taƙaitatatcen tunanin da ya gifta mata da bata yi ƙasa a guiwa ba ta fara ƙoƙarin tattaro nata makaman yaƙin "ai ba zata bari Yakaka ta ci ta da yaƙi ba haka nan take .ta aiyana hakan a zuciyar ta

"Doctor ka ga'.....

Wata irin tsawa Doctor Hamza yayi da ba ita Sofi kaɗai ba ,hatta Sam sai da yayi zillo yana ɗan kuka ya koma bayan kujera ya laɓe.

"Kar ki ce min kome Sofi , bana buƙatar jin ƙaryar ki ta banza abunda nake so kawai shine ...

Ɗan jim yayi yana kallon ta yadda ta wani irin saƙare cikin rashin madafa matsanancin tashin hankali gami da wani nisassashen yanayi shimfiɗe akan fuskar ta inda take bata motsa ba , ba domin tazarar dake tsakanin su na da ɗan yawa ba da babu abunda zai hana ya iya jin sautin bugun zuciyar ta..

"Ki tafi gida Sofi .

Ya ce da wata irin kakkaurar murya yana É—auke ganin sa daga kan ta ya zagayo da Yakaka daga bayan sa yana sake bin jikin ta da kallo kamar dai yana yiwa Sofi nuni da mummunan laifin da ta aikat ,yana kallon fuskar Yakaka tamkar ita yake yiwa maganar ya É—ora da cewa.

"Ki je gida akwai buƙatar ki sake samun ƙarin tarbiyya irin ta masu hankali da cikakkiyar koyarwar Islama ko ɗaya ba zan iya sake jimirin ɗaukar salon haukar da kike yi ba .

"Ki tafi gidan ku Sofi.

Ya furta hakan da buɗaɗɗiyar muryar da yasa kuka tahowa Yakaka da sauri ta shige cikin jikin sa tana zagaye shi da hannunwan ta , matsanancin tsoro na ɗarsuwa a ran ta ganin ɓacin ran sa Mai tsanani irin wanda ta daɗe bata gani ba.

"Ga Sofi kenan  matar son sa da ita ce ta kora ta layin.

ina ga ita kuma ? Da ta yaga kayan ta da kan ta ? Watakila idan ya gama da Sofi  ya dawo kan ta "shikenan Hajja ta jawo mata .

Hannun sa da ya sauke a bayan ta yana É—an buubbuga ta alamun rarrashi yasa ta ji nutsuwa ta fara dawo.mata da sauri ta É—ago kan ta tana kallon fuskar sa da shi ma ita yake kallo.

Zata yi magana ya hana ta ta hanyar jaan hannun ta zuwa hanyar ɗakin sa ba tare da yace  ƙala ba

A ɗan tsorace ta dubi sashin Sofi har lokacin tana nan a tsaye inda take tamkar an dasa ta kallo ɗaya ta yiwa fuskar ta tayi saurin janye idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ta doka da ƙarfi babu shakka ta hango wani lamari mai kaifi daga cikin idanun Sofi da suka tara ruwan hawayen da basu kai ga zuba ba '

"Ki tafi tare da dabban da kika kawo min gida bana so na fito na ga É—ayan ku .

Doctor Hamza ya furta hakan kafin su kai ga shiga É—aki.

Wani irin tsuma jikin Sofi yake so take Allah ya kawo wani ya wanka mata marin da zai farkar da ita daga mummunan mafarkin da take yi "Doctor Hamza ne da kan sa yau yace ta fita ta bar gidan sa ? Razanar da ta tsinka mata gudun jikin jikin bai wuce dalilin korar ta ta ba " akan wannan kuchakar 'yar gudun hijirar  'Yar talakawa 'yar ƙauyen ne Hamzan ta ya kore ta?

Kai ina ƙarya ne lokaci yayi da zata farka daga gyangyaɗin da take yi da har yasa tayi saken da wankin hula ke shirin kai ta tsakar dare akan Yakaka.

Ihu take son kurmawa amma tana ganin a halin da take ciki babu lokacin ihu , da gudu ta taka ta hau sama É—akin ta mukullin motar ta kawai ta É—auka sai fa wani siririn mayafi da ta rufa akai ta fita daga gidan .

Wani irin gudu take yi a kan titi da ya zarce ka'ida tana yi tana dukan kan ta da hannun ta É—aya .

Lokacin da ta shiga gidan su kai tsaye falon Momy kori ta zarce wacce bata san da shigowar ta ba sai da ta ji ana mata rotse a falo ta yunƙura daga kwanciyar hutun da take yi akan gado ta fito tana cewa "meye haka ? Meke...'

Sauran kalmomin sun maƙale ganin 'yar ta Sofiya ce take mata wannan aika aikar duk ta farfasa mata show-glass

Da gudu ta ƙarasa tana riƙo ta Amma sofi sai sake fisgewa take da alamun fitar hayyaci a tare da ita .

Hankali tashe take kiran sunan ta

"Sofi , Safiya ke Safiya meye hakan ? Kin yi hauka ne dan ubanki.?  Nace hauka kike ?

Ganin taƙi saurararta yasa Momy Kori ta cire hannu ta wanke ta da marin da yasa Sofi wani irin juyowa a fusace ta tunkuɗa Momy kori tayi zaman dirshan a kujerar gefen ta .

"Momy ki rabu da ni wallahi sai na tarwatsa rayuwar Yarinyar nan yadda nake tarwatsa wannan show-glass din naki.

"Wallahi sai na kashe ta , kafin ta kashe min aure ta raba ni da Hamza a ƙarshe tasa baƙin-ciki ya kashe ni .

Wani irin kallo Momy kori take bin ta da shi da yake nuni da zunzurutun takaicin da take ciki da kyar ta buÉ—i baki ta ce .

"Yanzun nan ke dan Ubanki akan kishiya kike wannan haukar ? Akan kishiya kika min wannan ɗanyen aiki ? Kika min wannan ɓarnar Sofi ? To billahil azim sai kin biya kuɗin abubuwan duk da kika rotsa dan buhun ubanki.

Miƙewa tayi tana jin gara ta bar gurin kafin zuciya ta ciwo ta ta jawo ta ta fara kirɓa .

Tana barin wajen Sofi da take tsaye ta silale jaɓar ta zauna a ƙasa kafin ta saki wani irin ihun da farkon sa kururuwa kafin ya miƙa da wani irin Kukan da yake siƙewa ta maƙollotan ta .

...[4/15, 8:07 PM] +234 706 503 6187: MAFARI

.......HARGITSIN RAYUWA

Umm'muaz

54b

Ta É—au tsawon lokaci a haka kafin ta ji hannun ya dafa ta da sauri ta É—ago kai cike da zumuÉ—in son ganin Doctor Hamza ne ya zo rarrashin ta .

wacce ta gani yasa ta saurin kawar da kan ta tana turo baki gaba .

Momy kori ta ƙarasa zama akan kujerar dake daf da ita tana jin tausayin 'yar ta na daɗa mamaye ta shi so jarabbata ne sannan muddin idan Sofi ta gado ta wajen matsanancin kishi to fa tana iya hasashen irin ciwon da take ji a rai wanda ita ma da a ba ita aka yiwa kishiyar ba amma tunda aka yiwa Sofi take cikin jin takaici a duk lokacin da ta tuno .

"Sofi kukan nan ya isa haka ki nutsu ki faɗa min me ya faru ?  Ki min bayani dan na cire ki daga wannan halin sanin kan ki ne ba zan juri ganin ki haka ba .

Ganin Momy kori ta ɗan sauko yasa Sofi gyara zama ta shiga rattaba labaran da suke cike da ƙarairayi kan irin tozarcin da Yakaka take sa wa Doctor Hamza na yi ma ta tana yi tana sharar ƙwalla a ƙarshe kuma ta juya baya ta kwaye rigar ta ta nunawa Momy kori inda kwalba ta yanke ta tana cigaba da cewa .

"Wallahi Momy kin ga inda ta sa wuƙa ta soki bayana kawai dan ta ga yana ɗaukar hankalin Doctor , da kokuwa fa ta kama ni tuƙuru Momy  ....

"Dan Ubanki ni rufe min baki ke kina me har wannan afiruwar yarinyar me kama da kazar mayu zata kama ki da kokuwa bakya shaƙe shegiya ki mata ƙamshin mutuwa ?

"Amma kuwa albasa bata yi halin ruwa ba cewa nake da wayon ki sarai a gidannan kin san dai kishiyoyi uku na kora idan aka haɗa da wanɗan da zamanin ku na ƙanana kuwa su rai takwas ne ras ai ni bana barin kishiya ta rufa kwana arba'in nake saita mata hanya ko tafi kuturwa naci kuwa.

"Amma shine ke dan sakarci za ki sakarwa kishiya baki har ta raina ki tana rarumar ki da kokawa kamar wata sa'ar ta ? Gaba-gaba kuma ai sai dai ta zane ki da bulala, dan ubanta da za ta ce ba za kiyi kiwon kare ba gidan na uban ta ne ko na uwar ta ?

"Shi kuma Hamzan da yake ya zama shanyayye sallamamme shine har zai koro min ke yace ki fita ki bar masa gidan ? To bai isa ba ,  Ai auren ku ke da shi mutu ka raba tunda ya zama sanadin da kika je kika huh-hura jikin ki haka kika yiwa kan ki illa ai kuwa bai isa sakin ki ba muddin ina raye ubansa ma na raye .

Langaɓe kai Sofi tayi tana kif-kifta ido irin ta wanda gaskiya ta yiwa yawa yake kuma buƙatar a bi masa kadu .

Kwafa momy kori tayi kafin ta buÉ—e murya tana kwala kiran mai aikin ta

"Lami ke Lami wai bakya ji ne ? miƙo min wayata ki kuma zo ki tattara gurin nan ki gyara mayyar TV ke da bakya gajiya da kallo sai ki tashi daga gaban Tv haka ya isa .

Da gudu wacce aka ƙira da Iyami ta miƙo wayar ta kuma dauƙo tsintsiya ta fara aikin gyaran gurin .

Layin Doctor Hamza Momy Kori ta shiga nema amma har ta tsinke bai ɗaga ba , a ƙufule ta sake ƙira wannan karan ma sai da ta kusa tsinkewa Yakaka wacce take gyaran ɗakin inda su ka sha kokuwa ita da Sofi ta ɗaga wayar ganin mai ƙiran "Momy ne kawai a rubuce dan haka tayi zaton Amnee ce .

"Hello tace da 'yar muryar ta mai sanyi .

"Tsam Momy Kori tayi tana sake samun tabbaci kan duk abinda Sofi ta faɗa mata jin Yakaka ce ma ta ɗau wayar Hamzan lalle Yakaka ta riƙa .

"Dan Ubanki ina mai wayar yake ? Ko nima iskanci za ki min ? To bari ki ji ko karuwar uwarki Mayya bata Isa bare ke Dallah ni ba shi wayar nace .

Ta ƙarasa tana sakarwa Yakaka wata tsawar da ta razana ta ba shiri ta sauƙe wayar ta ajiye dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya sha artabu da Sam kafin ya fitar da shi daga gidan .

Yana shigowa wayar ta sake ɗaukar kiɗa ya ƙarasa ya ɗauka ganin mai ƙiran na sa ya sa shi yin tsaki a sarari , har wayar ta tsinke bai ɗaga ba .

Nan take wata ta kuma shigowa.

"Yaya Doctor ka É—auka Dan Allah .

Ta furta hakan tana ƙoƙarin barin ɗakin hannun ta riƙe da sharar da ta tattara na fasasshiyar kwalbar .

"Salamu Alaikum Momy kori .

Muryar sa babu walwala ya furta hakan bayan ya É—aga kiran .

Momy kori bata amsa sallamar ba illa tambaya da ta É—ora masa .

"Hamza me yake faruwa Sofi ta zo gida haka tana kuka jikin ta jina-jina .

ÆŠan jimm yayi lokacin da wani É—an guntun tunani ya gifta masa "jikin ta jina-jina to hatsarin mota tayi ? .

"Lafiya ta bar nan kuma ni nace ta tafi gida , Momy kori Sofi ta zauna a gida zuwa wani lokaci ayi amfani da lokacin wajen ƙara mata tarbiyya da tunasar da ita darajar aure da ni kaina idan lokaci yayi zan zo .

Jin yana ƙoƙarin ajiye wayar yasa Momy Sofi da take ƙoƙarin danne ɓacin ran ta ta tunzuro dan haka a fusace ta ce

"Kai Hamza bana son rashin kunya za ka faÉ—a min abinda tayi da yasa ka koro ta gida ko kuwa ban Isa ba?

"Abubuwan da Sofi take yiwa Amina dayawa har fa kama ta take da kokuwa tana yaga mata kaya sannan ta kora ta layi yanzu wannan dai-dai ne ?

"Kana nufin akan matar ka ka koro ta ? To a dalili da me ? Ba ita ta tarar da ita a gidan ba ? Ai ita ya dace ta fita ta bar gidan tunda zaman nasu ba zai yi daÉ—i ba bafa na son ka fara da rashin adalci .

"Momy kori ni kaina Sofi tana min rashin kunya sannan fa har kare Sofi ta É—auko ba da izinina ba ta kawo min shi cikin gida..

"To shine me ? Ina cewa dai tunda ka san Sofi ka san ta da ƙaunar pets ? ..

"Amina tana da Cynophobia ba zai yiwu su rayu gida É—aya ita da kare ba hakan hatsari ne ga lafiyar ta dan haka Sofi ta cigaba da zama a gida har sai na samu damar raba musu wajen zama .

"Rufe min baki sakare idan ita 'yar gwal É—in taka Cynophobia ne da ita ita kuma Sofi Nostophobia ne da ita haÉ—i da Zelophobia dan haka tun wuri ka zo ka É—auke ta ku koma ...

Bai ƙarasa jin bayanin ta ba ya katse wayar sa gami da latse ta ya kashe gaba ɗaya .

"Ba zan dawo da Sofi ba har sai ta gane kuskuren ta .

Ya furta hakan a sarari yana fita falon inda ya tarar da Yakaka a zaune kan kujera ta rafka tagumi duk jin ta take wata mai gagarumin laifi gani take ita ta jaa aka kori Sofi.

Zama yayi a daf da ita kafin ya sa hannun sa ya É—auke hannuwanta da tayi tagumi da su , ya runtse su cikin nasa hannuwan yana É—an murza mata kan yatsun ta '

A hankali ta ɗago tana kallon sa da ya zuba mata nasa idanun da ke aika mata saƙon zallar ƙaunar ta .

"Bana so na ga kina damuwa Wafaa idan ina nan babu mai iya cutar da ke ba tare da na baki kariya ba .

Haɓar ta ya ɗan ɗago da hannun sa guda cikin taushin murya ya cigaba da cewa "babu kare yanzu a gidan nan dan haka babu sauran wani tsoro ki saki jikin ki , nan gidan ki ne kin ji ko Wafaa ?

Gyaɗa kai tayi kafin a hankali ta motsa laɓɓan ta "Yaya dakta dan Allah Sofi ta daw..''

"Shitt

yace yana ɗora yatsan sa ɗaya a kan laɓɓan ta ,

Shiru tayi tana ɗaga kallon ta zuwa cikin nasa idanuwan da suka ɗan yi ciki kaɗan lokaci guda gangar jikin ta na sauyawa kan irin salon da yake yi da ɗan yatsan sa akan laɓɓan ta.

Kasa jura tayi , babu zato ta faɗa jikin sa tana kwantar da kan ta a ƙirjin sa wani irin yanayi na bin jikin ta lokaci ɗaya da wata matsananciyar kunyar sa da bata san ma daga ina ta taso ba mene ne kuma takamaimai dalilin ta.

Murmushi yayi mai sauti fahimta da yayi tarkon da ya ɗana mata ya kama ta "ashe ma raguwa ce " ya furta hakan daga can ƙasan ran sa .

Ya ɗan ɗauki lokaci da ita a jikin sa alhalin bai mata kome da ya wuce shaƙar ƙamshin humarar ta Mai sanyin ƙamshi har lokacin da ta dawo dai-dai dan kan ta ta ɗaga shi tana sunne kai .

Yadda take yi ya ba shi dariya dan haka ya ɗan saki sassauƙar dariya lokacin da yake miƙewa tsaye yana duban agogon hannun sa yace

"Wafaa ni zan koma office sai bayan magarib zan dawo ki rufe ƙofar please kowa ya buga kada ki buɗe har sai idan ni ne , kuma ki bar wayar ki a kunne zan dunga kiran ki kin ji ko ?

"To Yaya Dacta .

ta ce haka tana miƙewa ganin ya fara tafiya , har bakin ƙofa ta raka shi tayi tsaye kan ta a sunkuye tana jiran ya wuce ta rufe ƙofar jin shiru ya sa ta ɗago kan ta bata ankara ba ta ji ya haɗe fuskokin su waje ɗaya tsawon minti ɗaya da 'yan wasu daƙiƙoƙi kafin ya jaa baya yana mata murmushi .

Yana wucewa ta rufe ƙofar da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya ta jingina bayan ta da ƙofar tana ƙoƙarin daidaita numfashin ta .

Har lokacin da ta ji tashin motar sa sannan ta bar wajen ta dawo falo .

wani irin nishaɗi take ji yana bin sassan jikin ta da yasa ta yin ɗan wani juyi kafin ta faɗa kan kujera wayar ta dake ajiye a gefe ta ɗauka kai tsaye ta danna ƙiran layin Falmata

***

Daga can Falmata ta ɗauka da daman har kawo lokacin hankalin ta bai gama kwanciya ba dan ma dai Biyamuradi ya zo gefen ta da salon kulawar sa gami da ƙaunar sa mai samar mata da nutsuwa .

"Hello Yakaka na ta furta hakan cike da zumuɗi a hankali Biyamuradi da yake matsa mata 'yan yatsu ya ɗago kan sa yana kallon fuskar ta da tayi ɓul-ɓul daman bata cika tsawo ba sai ta sake yin round .

Baya jin abunda Yakaka take faɗa mata amma daga yadda take ƙyalƙyala dariya ya fahimci labarin da take bata na ban dariya ne wanda irin sa daman aka fi so ta dunga samu a irin halin da take ciki .

Dan haka ya ji daÉ—i a cikin ran sa

Murmushi yayi yana miƙewa kafin yayi taku ɗaya ta riƙo hannun sa ɗan tara kumatu tayi alamun bata so ya tafi duk da cewa bata yanke wayar ba .

Komawa yayi ya zauna yana rungumo ta ta kwantar da kan ta a ƙirjin sa tana juya harshe cikin yaren su suka cigaba da hirar su ita da Yakaka .

Bai katse ta ba har sai da ta gama a hankali ta dago daga jikin sa "Mon bonheur ina za ka tafi ka bar ni?

Murmushi yayi yana kallon ƴar fuskar ta yadda ta shagwaɓe fuskar ta masa kyau kamar wata 'yar baby .

Kumatun ta ya ɗan shafa kafin yace "Mon bébé kin sani ai bani iya barin ki ko na matsa sai dan watta larura mai girma kouwa .

"Kamar wacce irin larura ?

ta ce tana É—aura hannun ta akan nasa .

"Kamar ta aiki na Mon bébé.

Nan take ta kwaɓe fuska walwalar ta kuma duk tayi ƙaura ita kam bata ƙaunar wannan aikin na Youssouf aikin da zai raba tsakanin su a dai-dai wannan lokacin da take tsakiya da buƙatar sa ya kuma riga ya shagwaɓa ta da zallar ƙaunar sa mai sanya ta jin kamar tafi kowacce mace sa'ar samun Miji a duniya.

Sai ga shi lokaci ɗaya zai tafi ya yi mata nisa zuwa wata jahar guda da ta san kome son ta da ganin sa dole ta haƙura da ganin sa kullum kamar yadda yace mata dai idan sun tafi a gobe duk sati zai dunga zuwa ganin ta har lokacin da zata haihu ta gama wanka .

Bata san hawayen ta na sauƙa ba sai da ta ji hannun sa mai ɗumi yana shafe mata fuskar ta ,

Kukan da bata shirya masa ba shi ya taho a lokacin , cikin 'yar muryar ta ta shiga rera kukan da yake sukar zuciyar Youssoufa nan take ya ruÉ—e ya shiga rarrashin ta ba ita tayi shiru ba sai da ya rufe bakin kukan nata .

"Fatima kamar gobbe ne idan na tai sati guda za tai na zo na diba ku kedda É—iyana kukan ki tada min da hankali yake ko kouwa kina so na bar aikina ?

A hankali ta girgiza kai tana ƙoƙarin danne damuwar ta ta ɗago kan ta muryar ta a shagwaɓe tace "amma ka min alƙawarin kullum zan dunga ganin ka a Appel vidéo ko ?

"Na miki wannan alƙawarin Bébé duk na samu lokaci zan ƙira ki Appel vidéo ina ganin huskar ki mai haske .

Ya furta hakan tare da sumbatar goshin ta .

Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi yasa suka gyara zaman su sannan shi yayi iznin da a shigo .

Ɗaya daga cikin bayun sashin ta ne take neman iznin shigowa da saƙo daga Hajiya Umma nan take Biyamuradi yayi mata izni

Bayan fitar ta suka dawo tare da bayu mata biyu da suke riƙe da wasu manyan farantai da suka sha lulluɓi da wani kyakkyawan tuma-ƙasa da bai ɓoye kyaun kwanukan da suke jere bisa farantan ba .

Bayan sun ajiye suka yi gaisuwa sannan suka ɗora da cewa "Saƙo ne daga jagorar cikin gida cewa a kawo wa Gimbiya Fatima .

Kamar kullum bayan fitar su Youssoufa da kan sa ya taso ya bubbuɗe kwanukan da suke maƙare da cimaka na alfarma da yafi ƙarfin cin ƙatti goma ma bare fa Falmata da Hajja kaɗai .

Yana murmushin da yake bayyana farin-cikin da yake ciki ya dubi Falmata wacce itan ma shi take kallo tana jiran ya zubo mata abincin da jin ƙamshin sa kaɗai duk ya bi yasa yawun ta ya tsinke wata bijirarrar yunwa kuma ta fara sasuƙar ta da yasa ta tuno da rabon ta da abinci tun tattaciyar madarar da ta sha da safe bata ci wani abin kirki ba ga shi yanzu gefen azahar .

"Fatima kin zama 'yar gatan Umma kullum cikin kwasar gara kike bayan saƙonni gaisuwa da girmamawa da suke isko ki a kullum anya kouwa baki haye min ƙaraga ta ga wajjen ta ba ?

Dariya tayi har gajerun haƙoran ta na bayyana kafin ta ce " ai kada kayi kokonto Biyamuradi yanzu ni ce ke da Umma .

Yunƙurawa tayi zata miƙe da sauri ya taso ya kama ta suka tako tare zuwa gaban abincin bayan ta zauna ya jingina mata pillow daga bayan ta tana ɗan sake bajewa .

Da hannu take gwada masa waɗanda take so yana zuba mata , lokacin da ya gama wani cokalin daban ya ɗauka zai bata a baki fahimtar hakan da tayi yasa ta karɓe plate ɗin daga hannun sa da sauri '

ba zata iya jurar yunwar da take ji ba , bare har ta iya jira a ciyar da ita bayan tayi Bismillah cikin nutsuwa ta sanya hannu ta ta fara ci .

Daɗin abincin na ratsa ta yana dasa mata ƙaunar uwar Mijin ta da ta fahimci tunda abun nan ya faru ya wuce baki ɗaya ta sauya duk wata rashin kulawa da rashin ƙaunar da take gwada mata sun juye sun rikiɗe sun koma tsantsar kulawa da nuna ƙauna a fili .

Tun faruwar lamarin da rashin lafiyar da tayi har ta samu sauƙi cikin sati guda kuma ta tare a sabon sashin ta da ta zo ta tarar da shi a shirye tsaf cike da kayan alatu irin na saraki da Biyamuradi ya tabbatar mata da cewa Maimartaba ne ya mata kome har sai da tayi hawaye cikin ran ta kuwa ta dunga miƙa godiyar ta ga Allah da idan ba shi ba babu mai ɗora misuƙa miskiniya irin ta a matsayin da take a yau babu shakka Allah shine abun godiya .

Bayan Hajja da take taya ta zama an haɗa ta da bayu mata biyar masu hidima kaɗai a sashin ta duk da cewa ba girki suke mata ba sai fa aiyukan shara da goge-goge ,wanke-wanke da sauran ƙananun aiyuka .

Abincin ta daga Sashin Hajiya Umma yake tahowa ita ta hana ta cin kowanne abinci sai fa na sashin ta har zuwa lokacin da zata haihu sannan ta sauwaƙe mata zuwa gaida ta kullum ta ce ta dunga sanya kwana ɗaya a tsakani saboda tayi nawi kuma da 'yar tazara a tsakanin su Hajja ita ke zuwa kai gaisuwa kullum.

Tana tunanin zuci bata san ta cinye abincin ba sai da ta laluba ta ji ba kome sai 'yan tsirarun shinkafa.

Ta ɗago kan ta a hankali ta dubi Fuskar Youssouf wanda ya rafka tagumi da hannu biyu yana mata kallo mai ruwa biyu , zallar ƙaunar ta da kuma tausayin halin da take ciki .

A kunyace ta ɗan yi murmushi kafin tayi magana ya riga ta da cewa "kin ƙoshi ? Bai  jira amsar ta ba ya kai hannun sa ya goge mata gefen bakin ta da miya ta ɗan sauƙa.

"Mon Bébé kin ƙoshi ?
Ya sake tambayar ta

" Na ƙoshi Baban Mama ta furta tana ƙoƙarin tashi shi ya taimaka mata ta wanke hannun ta .

Tare suka zauna yana maƙale da ita ko yaya ta motsa yana mata sannu tare da gwada mata So.

ƙiran Sallah da akayi shi yasa shi sallama da ita bayan ya fita kai tsaye sai da ya shiga sashin Siyama da tun asuba rabon shi da ita saboda girkin Falmata ne

A zaune ya same ta an yi mata zanen ƙunshi a fararen ƙafafun ta tana jiran ya bushe ta wanke .

Daga inda yake yana iya hangen jelar ƙananun kitson da aka mata da suka kwanta har a kafaɗun ta 'yar doguwar fuskar ta ta sake fitowa sai ƙyallin gyaran jikin da ta samu take yi .

Ba tare da ya zauna ba yake amsa gaisuwar da Siyamar ke yi masa bayan sun gama gaisawar ya ɗan yi murmushi kafin ya ce "wannan ƙwalliyar du ta tafiyar ce ? Ko kouwa tawa ce ?

Ɗan wara idanun ta tayi sai kuma tayi dariya cike da jin daɗi da ɗoki ta ce "ƙwalliya taka ce Baban Yumna kamar yadda tafiyar ma take taka domin kai .

Ɗaga mata gira yayi yana juyawa akan ƙafafun sa yace "idan hakka ne ayi shiri da kyau a kouma gama bisa kan lokaci doumin kamar yadda na faɗi gobbe kafin hantsi ya ɗagga zamu tai da yardar Allah .

"To Insha Allah ba zan makara ba.

Ta furta hakan tana bin bayan sa da kallo wani irin farin-ciki na ratsa ta sanin da tayi gobe iwar haka daga ita sai shi a wani yanki .

Daren ranar kusan raba shi suka yi Youssoufa yana aikin rarrashin Falmata da shima kawai daurewa yake yi amma har cikin ran sa yake jin rabuwar da zasu yi.

Dan dai babu yadda zai yi ne a cikin halin da take ciki ba zai yiwu ya ɗauke ta su tafi bariki ba can wata jahar da babu kowa nasu ko shi da kansa ba zai so hakan ba bare ma kuma Hajiya Umma da Maimartaba sun riga sun gama magana akan ya bar ta anan gida har ta haihu abunda ta haifa yayi ƙwari kafin ta fara bin sa jahar da yake aiki .

****

Washegari.

Duk yadda Falmata ta so ta ɓoyewa Siyama damuwar ta lokacin da ta shiga sashin ta domin yi mata Sallama kasawa tayi .

Idanun ta suka tara ruwan hawayen muryar ta na ɗan rawa tace "Maman Yumna zan yi kewar ku ke da Yumna sosai dan Allah ki dunga ƙirana Appel vidéo .

Riƙe hannun ta Siyama tayi cikin ran ta tana yabawa ƙwarai da juriyar da ta gwada na ɓoye mata ainahin dalilin damuwar ta , cike da rarrashi tace "ma petite soeur mu ma za muyi kewar ki amma kar ki damu kullum za mu dunga yin waya dan Allah kar kisa damuwa a ran kin san ba'a so ki zauna cikin damuwa a halin da kike ciki ko ?

"A hankali ta gyaÉ—a kai tana jin yadda zuciyar ta ke matsewa kamar zata fashe .

Murmushi Siyama tayi mata tana É—an jaan hannun ta tace " to tashi ki zo ki mana rakiya le chauffeur ya zo za mu tai yanzu .

ÆŠan jimm tayi tana jin wani yanayi marar daÉ—i na ratsa ta tayi zaton Youssoufa zai sake shigowa suyi wata Sallamar bayan Sallama bayan da Sallamomin da suka dunga yi tun daga jiya har wayewar garin yau da safe kafin ya shirya ya fita daga Sashin nata inda ya kwana .

"Maman yumna bari na É—auko Mayafi na.

Tace tana zame hannun ta daga nata ta nufi É—aya daga cikin É—akunan ta '

Bayan shigar ta ɗakin bata jima ba ta fito hannun ta riƙe da wata Paper-bag.

Bayan ta ƙaraso sai ta miƙawa Siyama ,muryar ta da rauni ta ce "Maman Yumna ga tsaraba ta nan kiyi amfani da kayan ciki.

Murmushi Siyama tayi kafin ta sanya hannu ta karɓa tana ɗan leƙen cikin jakar ta ce "ma petite soeur kyauta ce hakka anka min ? Na kouwa gode miki ƙamna ta Allah shi bar ƙauna a tsakani.

"Amin .
Falmata ta amsa tana Murmushin yaƙe .

A bakin mota suka tarar da Biyamuradi Youssouf yana riƙe da hannun Yumna yayi shirin sa tsaf cikin kakin sa na soji da yake matuƙar amsar jikin sa .

Tun da Falmata ta samu lafiyar idanun ta yau ce rana ta farko da ta gan shi sanye da kakin soji sai ta shagala wajen kallon sa yadda yayi mata kyau ji take kamar ta ruga da gudu ta rungume shi a ƙarshe kuma ta hana shi tafiya ya zauna a gaban ta tayi ta kallon sa haka tana miƙa godiyar ta ga Ubangiji Youssoufa Namiji ne da kowacce mace zata so ta mallaki irin sa a fagen kyaun suffa da cikar zati irin na cikakken ɗa Namiji yayi zarra .

Shi ɗin ma ita ya zubawa ido a tun fitowar su yana nazarin damuwar da take danƙare a fuskar ta wanda a take ya ji tana kassara masa gaɓɓai da a zahiri ma dan haka ne ya ƙi shiga sashin nata yayi mata bankwana saboda yana tsoron abunda ka iya biyo bayan hakan wataƙila ma ya fasa tafiyar .

Gyaran muryar da Siyama tayi yasa Falmata tayi saurin ɗauke ganin ta daga kan sa tana yin ɗan baya kaɗan ta riƙo hannun Yumna wacce ta baro Baban ta ta dawo wajen Mamar ta .

"Yumna zan yi kewar ki sosai , ta furta hakan tana shafa kan ta .

Mayar da ganin ta tayi sashin da Siyama take tsaye "to Maman Yumna Allah ya kiyaye muku hanya dan Allah idan kun isa ki sanar min .

"Nima zan yi ƙewar ki ƙamnata Amin nagode sosai dan Allah ki kula muna da kan ki da bébé mu .

Gyaɗa kai Falmata tayi tana mayar da ƙwallar da take ji tana cika mata ido taƙi yarda ta sake kallon Sashin da Biyamuradi yake tsaye duk da cewa tana jin idanun sa na yawo a kan ta.

chauffeur ya buɗe ƙofar motar Siyama da Yumna suka shiga ganin haka yasa a hankali ta juya tana ɗaga takun ta dan barin wajen.

" Fatima .
ya ƙira sunan ta .

Chak ta tsaya ba tare da ta jiyo ba , ɗan taku yayi ya matso kusa da ƙofar motar cikin amon sa mai ƙarfi yace "je t'aime tellement Et tu me manqueras.

Har cikin ran ta ta ji kalmomin sa a hankali ta runtse idanun ta hawayen da suka cika gurbin idon suka gangaro kan ƙuncin ta .

Muryar ta na rawa ta furta "Allah ya kiyaye mu ku hanya ya kai ku lafiya Amin .

Da sauri kamar ba ita ce ke ɗauke da wannan tirtsetsen cikin ba ta ƙarasa barin wajen idanun ta a rufe da ruwan hawaye .

Youssouf da yake tsaye ji yake kamar ya bita ya riƙe ta ya hana ta tafiya amma ya san idan yayi hakan zai ɓata goma ne ɗaya bata gyaru ba .

Lokacin da ta ɓacewa ganin sa dan kansa ya shiga motar direba ya jaa suka ɗau hanyar barin-gidan suka kama hanya ɗoɗar zuwa Birnin Tahoua inda yake aiki .

Lokacin da Falmata ta koma sashin ta abu na farko da ta fara yi bayan ta ci kuka har ta bawa aku lada ta ji idanun ta sun fara raurawa suna mata alamun ciwo '

Lallaɓawa tayi ta ɗau wayar ta wacce take ji tana ta ɗaukar kiɗa da ko bata duba ba ta san Biyamuradi Youssouf ne ke kira

A hankali ta shafa wayar ta kashe tana zunɓuro baki kamar yana ganin ta tace "Na fasa yin Appel vidéo ɗin da kai .

****

Duk da cewa tafiyar bata yiwa Siyama armashin da ta so ba amma hakan bai guntule mata jin daɗi da ɗokin ta ba sai hira take yi masa wani ya amsa wani kuwa yayi shiru yana shafe-shafen waya da sarai ta lura da wacce yake faman ƙira Fatima ce .

Ko da suka isa jahar Tahoua da gefen Azahar a share a tsaftace suka tarar da gidan dan haka aikin da tayi ba mai yawa bane ba illa kayayyakin su da tayi musu ma'ajiya a muhallin da ya dace ta sake yin wasu 'yan gyararraki da ba'a rasa ba.

Kafin ta gama wani Soja da yake hidima da gidan ya zo da cefene dan haka kai tsaye ta shiga kitchen duk da cewa ba sabon ta bane yin girki amma bata gagara iyawa ba dai-dai gwargwado ta zage-damtse dan farantawa Mijin ta tayi girki mai kyau da daɗi Yumna na taya ta da ɓarna .

Youssouf kuwa tunda suka zo da aka sauƙe su shi wucewa direba yayi da shi can babban ofishin su inda zasu yi wata ganawa shi da abokan aikin sa .

Ba shi ya samu damar komawa gidan ba sai bayan isha'i lokacin da ya shiga gidan tsit babu motsin kome sai na na'urori.

bai tarar da Siyama a falon ba sai fa wani daddaɗan ƙamshi da ya shaƙa wanda take ya tado masa da tunanin Fatiman sa domin kuwa ƙamshin irin nata ne a duk inda tayi bigire nan yake jin irin ƙamshin kewar ta mai yawa ya ji tana bin jikin sa , tunda suka taho yake son ya ji lafiyar ta amma taƙi ɗaukar wayar a ƙarshe ma ta kashe ta baki ɗaya kuma tunda ta kashe bata kunna ba .

Zama yayi akan kujerar falon yana sunce igiyoyin takalman sa , bai ji tahowar ta ba sai sauƙar kyakkyawan hannun ta da yasha adon ƙunshi ya gani ta ajiye akan hannun sa ta karɓe kunce takalmin da ya fara .

Sakar mata yayi yana bin jikin ta da kallo da ta sha ado da wata bugaggiyar shadda Boo ɗinkin bubu tayi ɗaurin ɗankwali mai ban sha'awa jelunan kitson ta da ta haɗa ta tufke ta haɗe cikin ƙaton ribbon ya taimaka wajen ɗago da ɗaurin daga ƙasa sai ya zauna ɗas a kan ta kamar hula .

"Siyama ma'abociyar kwalliya ce , daga can ƙasan ran sa ya aiyana haka .

Yana kallon ta har ta gama ta É—ago fuskar ta da bata cika fente-fente ba tana masa murmushi ta ce "Bienvenue mon amour et comment va le travail? Sannu.

Fuskar sa a sake da taƙaitatcen murmushi yace "ke za'a wa Sannu Maman Yumna da hidmar gida da kaɗaici , ɗakin taro mun ka hige sai yanzou munka kai ga hittowa.

bata amsa ba ta miƙe da ɗan murmushi a fuskar ta ta wuce ɗaki daga can ta haɗa masa ruwan wanka .

Ya shiga yayi bayan ya gama ya sako ƙananun kaya da basu cika nawi ba a jikin sa ya fito

Daga nan abinci ta kawo suka ci tare bayan sun gama ta tattara wajen ta dawo ta zauna daga gefen sa suna kallon TV tare duk da dai ita ba wani jin daÉ—in kallon take ba saboda tashar labarai ne shi yake ganin kayan sa .

Lokacin da ta ga ya ɗau waya sa sai da zuciyar ta ta doka tana satar kallon sa ta ga ya fara ƙira bugu ɗaya biyu , daga can ta ji computer na sanar da shi wayar a kashe take chajin wayar sa ya duba ya ga saura kadan ta mutu dan haka kawai sai ya kashe wayar ya sa a chaji

yana jin duk babu daÉ—i "meyasa Fatima za ta masa wannan horon ?

"Biyamuradi

Ta ƙira sunan shi

Da ido ya amsa mata yana kallon ta .

Murmushin yaƙe tayi kafin ta ce "tunda muka zo nayi ta neman wayar ƙamnata a kashe wayar....

Kafin ta ƙarasa Youssouf ya amsa mata fuskar sa na bayyana damuwa "nima itta nake ta ƙira amma ta kar wayar ko mai yassa tayi hakan ?

"Watakila batta so ta tsare ma aiki ne , Siyama ta amsa masa tana É—an nazarin sa ta É—ora da cewa

"Amma ko za ka gouda kiran Hajja ne saboda a san halin da ta yini ciki.

"Hakka ya kamata, Amma itta telephoné na babu wutta cikin ta.

"Bari na ƙira ta da telephoné na sai ta sada  mu da itta

Bugu É—aya Hajja ta É—au wayar ta tana É—an gigin bacci tace "hallo waye anan ?

Daga can Siyama ta amsa mata tana jin muryar ta ta watsake suka gaisa faran-faran ta ɗora da faɗa mata dalilin ƙiran nan take Hajja ta yunƙura ta fita daga ɗakin ta ta nufi ɗakin Falmata cewa take "kada ma ki katse ƙiran ai yanzu zan kai mata idon ta biyu dan ban jima ba ma da barin ɗakin nata bayan mun gama hira .

"Hello Maman Yumna da fatan kun isa lafiya ? daga can Falmata da ta karbi wayar ta furta

Shiru ta ji anyi "Hello ta sake cewa.

Daga can ɓangaren da tunda ta ɗaga wayar Siyama ta miƙawa Youssoufa

"Fatima .

Sautin sa ya doki dodon kunnen ta da yasa ta runtse Ido tana jin yadda gangar jikin ta ke sauyawa daga jin amon sa .

"Fatima me yassa kin ka kashe min waya unn ?

Shiru ta sake yi tana jin sa ya cigaba da cewa "kin sa na shigga damouwa , kar ki sake min ya hakka kin ji kou ?

"Fatima

"Mon bébé kina ji na ?

Sautin kukan ta ya ba shi tabbacin tana jin sa runtse ido yayi yana jin ciwon kukan nata ya fahimci Fatima tana da zafin kishi sosai da sosai da shi a ganin sa ba kome ya kawo hakan ba illa tsananin son da take masa.

Ajiyar zuciya yayi daga ƙasan ran sa ya fara harhaɗo kalaman da zai rarrashe zuciyar ta take cike da ƙaunar sa.

****

Bayan Awa ÆŠaya da Rabi:

Rarrashi ya rikiɗe ya koma hira mai cike da raha da ƙaunar juna daga ƙarshe ma suka koma video call kamar ba sa rabu ba kafin daga ƙarshe ya sake wani rarrashin kafin su yi Sallama da alƙawarin gobe za ta gan shi a vidieo call a dai-dai wannan lokacin

Zuciyoyin Su cike da nishaÉ—i da begen juna suka yi Sallama bayan sun aikawa da juna Sumba ta iska .

Sai bayan da ya sauƙe wayar ya lura da yadda dare ya shiga wajen shaɗaya da rabi na dare.

Yawo yayi da idanun sa a falon sai dai ko alamun wacce yake dubawa bai gani ba , haka kawai ya ji wani irin yanayi na bin jikin sa yana ganin rashin kyautawa kan abunda yayi musamman da ya tuno da cewa da fa wayar ta su ka sha hira shi da Fatima , "anya kana adalci ? Zuciyar sa ta ƙwanƙwashe shi.

Cikin rashin kuzari ya miƙe bayan ya kashe kayan kallon ya rufe ko'ina ya nufi ɗakin baccin su '

A hankali ya turo ƙofar cike da son kiyayewa kada ya tada su a baccin da yake hasashen suna tsaka da yin sa .

Da shigar sa yayi turus kafin ya ɗan yi duru-duru saboda ido huɗu da suka yi shi da Siyama wacce take zaune daga ƙasa ta tasa laptop a gaba da alama karatu take yi .

Murmushin da ta jefe shi da shi lokacin da take zare gilashin idanun ta bai taimaka ba ko kaÉ—an wajen rage masa yanayin da yake ji a dai-dai lokacin da shi kan sa ya gaza fahimtar ainashin wanne irin yanayi ne ? .

"Ya Fatima da Bébé ? Duk suna lahia kou.?

"Suna lafiya , ya amsa mata kafin ya zauna daga kan kujera ɗaya tal da take ɗakin yana ɗan sosa ƙeya .

"Siyama .

Ya ƙira sunan ta yana kallon ta .

Cikin nutsuwa ta É—ago kan ta ba tare da ta amsa ba

Da taimakon hasken ɗakin ya iya hango yadda launin idanun ta suka sauya su ka yi jaa kaɗan  .

"Ba kiyi bacci ba har yanzou ?

Ya tambaye ta .

Wani irin murmushi mai ciwo tayi tana kawar da kan ta , muryar ta babu ƙarfi sosai ta ce " Ban yi bacci ba Biyamuradi ina jiran ka shiggo muyi Sallama.

"Siyama

Ya sake ƙiran sunan ta bai jira amsawar ta ba yace .
"Duk lokacin da kin ka ji bacci kiyi ko da ina gidan ko bana nan ba sai kin jira mun yi sallama ba...''

"Saboda me ? Ta katse shi da wata irin muryar da take tsakanin harshe da wuyan ta

Kallon sa tayi ta ga yadda ya ke duban ta da rauni a cikin idanun sa , kafin ta É—ora da cewa .

"Saboda baka sona ? Baka ƙamna ta ? Baka amre ni domin so ba ? Ni matar cushe ce gare ka ?

"Siya...

Da sauri ta katse shi lokacin da ruwan hawayen ta ke sauƙa yana ɗiga ta cigaba da cewa

"Laifi zuciya ta tayi a doumin ta so ka ? Ko kouwa ni nayi laifi da na kassa jumriya akan ƙamnar ka har dai nayi kafiya kan Amren ka ? Da ka ke gwadan rashin ƙamna a fili kake watsi da sha'anin da duk ya shafe ni ?

Tasowa yayi ya dawo gaban ta ya zauna yana jin girman laifin sa na masa lulluɓi tunda ya kai girman da har ta kai yau Siyama ta ɗaga Muryar ta .

Hannuwan ta da suka ɗau sanyi ya riƙe yana lalubo kalmomin da ya musu ajiya mai nisa da basa taso da kan su sai fa akan wacce aka yi ajiyar su a domin ta yau so yake ya ƙalato su ya yiwa Siyama kyautar su wataƙila sa wanke mata zuciya su samar mata da nutsuwa a cikin hakan babu laifi domin ita ma ta cancanta.

"viens chérie yaya ki ke faɗin hakka ? Me yassa za ki ce bani ƙamnar ki ? Bani ƙamnar ki na amre ki har mun ka haihu ? Ina son ki mana Siyama...

Zame hannun ta tayi tana girgiza kai lokaci guda tayi wani murmushi mai ciwo muryar ta da 'yar dariyar baƙin-ciki tace .

"Kar ka jefe ni da kalmomin aro domin shi kayan aro ai basshi rufe katarar mai su , wannan kalmar ta so ba tawa ce ba ban taɓa samun ta ba ga gurin ka kai tsaye sai ko dan alfarma bani son jin ta domin ba'a halicce ta a zuciyar ka a domin ni ba .

Saƙare yayi yana kallon ta wata irin kunyar ta ya ji a lokacin tana tasowa tana danne shi har yana jin kamar bai iya numfashi mai kyau .

Ganin yayi shiru ya sa ta miƙewa bayan ta kashe laptop ɗin ta ta tura gefe , wani irin ciwo zuciyar ta ke yi so take ta samu waje tayi kuka yadda ya kamata .

Sai dai kafin ta ɗaga ƙafa ta bar gurin ya jawo hannun ta da ƙarfi ta taho gaba ɗaya ta faɗa masa yayi mata kyakkyawar runguma a ƙirjin sa .

Kukan da yake cin ta a rai shi ta samu damar yi ta shiga rairawa har jikin ta na tsuma .

Biyamuradi Youssoufa ya kasa cewa kome illa rungume ta da yayi tsam yana jin yadda kukan ta ke ratsa jijiyoyin jikin sa suna tsinka masa gudun jini tare da É—arsa masa wani irin yanayi mai kama da tsoro-tsoro a cikin ran sa "tsoro yake ji na É—aukar hakkin ta , tsoro yake kar Allah ya kama shi da laifin rashin adalci a tsakanin Matayen sa .

Sai da tayi kukan ya ishe ta har ta fara lafawa dan kan ta sannan ya kai hannu a hankali ya riƙo hannun ta ya ɗora shi a saitin ƙirjin sa muryar sa can a ƙasan maƙoshi yace .

"Kin ga nan , kin ji yadda zuciyata ke tsanan ta bugu a halin yanzu ? Akan ki ne Siyama tuhuma ta take yi meyasa na ɓata miki Siyama ? Zuciyata na ganin GIRMAN ki ke ABAR GIRMAMAWA kike a gareni , ina jin Kunya idan na ga na ɓata miki Siyama a nan duniya cikin 'ya'ya mata wace ta samu ƙima da girman matsayi kwatankwacin naki a gurina Siyama ? Amsar ita ce babu.'

" Yakanar ki ta sayo miki mafi É—aukakuwar daraja a gurina shin ba za kiyi alfahari da hakan ba ?

A hankali ta ɗago kan ta daga cikin ƙirjin sa tana jin yadda ruwan hawayen ta ke ƙafewa zuciyar ta ke tsantsamewa kunnuwan ta ke buɗewa .

Kallon da take masa kallo ne na irin " sake faÉ—a na ji ? Da gaske kake ?

Da hannunwan sa biyu ya riƙo fuskar ta yana jin yanayin da yake ji a game da ita na sake ninkuwa har yana neman fin ƙarfin sa so yake kawai ta yarda da abunda yake faɗa mata .

"Siyama zuciya ta na girmamaki gangar jikina kuma na buƙatar ki ke ɗaya ce ke da wannan matsayin a guri na da alƙawari na miki watta ba zata samu gurbi ya irin na ki ba , watta ba zata ɗau wannan matsayin ba ki yarda da ni .

Ɗan bakin ta da ya faɗaɗa da murmushi yake motsawa da son cewa wani abu shi ya rufe domin a lokacin baya buƙatar tace wani abu .

"So , ƙauna , haƙuri , Yakana da kawaicin da ta kwashi shekaru tana gwada masa sun riga sun masa gamsarwar da bai buƙatar ta sake furta kowacce kalma a gare shi a domin wai ta maida masa martanin kalmomin sa lokaci ne yanzu yayi da ita ma zai kyautata mata gwargawdon girman da zuciyar sa ke bata .

"Ta gaza tantance a halin da take ciki tsawon lokaci ji take kamar mafarki take za ta farka , kalmar girma ta mata nawi wajen ɗauka kamar yadda zuciyar ta ta gaza wajen jurar irin farin-cikin da take ciki wanda da ɗai a rayuwa bata taɓa samun makamancin sa ba dan haka ta dunga maida masa martanin Soyayyar da yake gwada mata cikin nishaɗi da basu taɓa samun makamancin sa ba a duk zaman auren su .

"Shin me ya kai hakan martaba a ce Mijin ka wanda Allah ya umarta da ka girmama shi , da bakin sa yace shi ke girmama ka ?

"Ashe ba soyayya ce kaÉ—ai abun nema a wajen Miji ba akwai abunda yafi soyayyar girma da martaba .

"Babu shakka daga yau za ta iya tutiya da matsayin da Mijinta ya ɗora ta akai matsayin da bata taɓa tarayya da wata akan sa ba nata ne mallakin ta ita kaɗai .

"Ina ma da mata zasu fahimci hakan a duk lokacin da hagu ta ƙi su a gurin Miji suyi amfani da Dama su samarwa da kan su ramin kan su ba tare da sun nace da suyi kafaɗa da kishiya ta fanni ɗaya ba.? Da kuwa gidaje da yawa an zauna lafiya a tsakanin kishiyoyi .

Siyama ke ayyana hakan a cikin ran ta bayan bacci ya É—auke Biyamuradi Youssouf da ita kuma zallar farin cikin da take ciki a yau shi ya hana ta bacci .

A karo na biyu ta É—aga kan ta duk da cewa da duhu a É—akin so take ta sake ganin hasken fuskar sa ko da sau É—aya ne kafin bacci ya É—auke ta .

A daren yau son da take masa ya sake ninkuwa ne akan na daa har tana jin kamar ba zata iya É—auka ba .

Cikin bacci ya mayar da kan ta jikin sa ya kwantar tare da sumbatar goshin ta kafin ya cigaba da baccin sa cikin nutsuwa .

Ɗan murmushi tayi ta sumbanci ƙirjin sa kafin ta rufe ido baccin da yafi daɗi da kan sa daɗi ya ɗauke ta.

****

Abuja

Cikin satika ukun da suka biyo bayan barin Sofi Gidan Doctor Hamza wata irin Soyayya mai daɗi da shaƙuwa mai girma ne ya ƙullu tsakanin ma'auratan biyu Doctor Hamza da Yakaka .

Musamman da ya kasance daman 'yan uwan juna ne dan haka sai aka yi dace wasu daga cikin halayen su suka zo ɗaya kamar yanayin buƙatuwar halittar su da matsananciyar tsaftar su , yawan ibadar su , da rashin son hayaniyar su dan a wasu lokutan ma shiru gidan yake ɗauka suna gudanar da soyayyar su a aikace ko kaɗan basa gajiya da junan su kusan koyaushe cikin ƙoƙarin farantawa juna suke muddin dai suna tare .

A satika ukun har wata 'yar sirantatciyar ƙiba Yakaka tayi ta sake fari tayi fes da ita  , yawan gyaran da take yiwa fatar ta kamar yadda Amnee ta koya mata bayan ta haɗo ta da kayan gyaran yasa kullum jikin ta kamar bayan ƙwai luwai-luwai .

Ga ƙamshi na musamman da ya zauna mata saboda turara da take yi gaba ɗayan jikin ta da hakan shi yafi kome sa Doctor Hamza ya liƙe mata kasantuwar sa ma'abocin son kamshi.

Ga girki da kullum take yi musu masu gamsarwa da ƙara lafiyar jiki saboda har ajin koyan girki ta shiga a whtsapp na musamman da shahararriyar ƙwararriyar mai koyar da girke-girken nan kuma Marubuciya Maryam Talba ta bude take kuma jagorar azuzuwan musamman domin koyar da mata girke-girke masu gamsar da Maigida,

Tare da goyon bayan Doctor Hamza da shi ma yake jin daɗin girkin ta dan haka ya amince ta faɗa ajin Koyan girki Na chef  Maryam Talba

(wacce duk take da ra'ayin shiga ajin girkin Chef Maryam Talba duba da cewa Azumi ya gabato Uwargida kina bukatar sabbin darasi kan girke-girke domin gamsar da Maigida da iyalan ki , to kar ki ji kome yi maza ki min direct message insha Allah zan sada ki da Chef din da na san sai kin min godiya a gaba sannan babban abun farin-cikin da za ki tadda shine a kudi mai rahusa za ki fada ajin 👌sai kun zo👍)

*****

Yau ta wayi gari cike da burin gwada wani daddaɗan girkin da a jiya Chef Maryam ta gwada musu da yayi matuƙar burge ta .

Kamar yadda Chef Maryam ta kware a girke-girken mu na nan gida Nigeria har da na ƙetere ma ba'a bar ta a baya ba ta ƙware a girkin larabawa dan haka yau Yakaka tayi aniyar gwada dafuwar Maqluba wadda dafuwar shinkafa ce da kaza, dankali, ganyayyaki haɗi da sauran sinadaran girki .

Maqluba girki ne na mutanan gabas ta tsakiya wanda yake da matuƙar daɗi .

Cike da nishaɗi take aikin ta tana yi tana bin ƙira'ar Alkur'ani da ta sa a wayar ta.

Kafin ya bayyana ƙamshin sa ya sanar mata da wanzuwar sa a gurin zuwa lokacin da ya shigo kitchen ɗin ta ɗago kan ta a hankali tana jifan sa da wani tsadaddan murmushi .

"Habibi barka da tashi , gaskiya ka sha bacci.

Ta furta hakan ba tare da ta janye murmushin ta ba

Ƙarasowa yayi ya rungume ta ta baya yana ɗora kan sa a kafaɗar ta yace .

"Wafaa kin saɓa doka ta meyasa ?

Wara ido tayi tana ƙoƙarin juyowa ya hana ta a hankali ta ce

"Kayi haƙuri cikin rashin sani ne.

"Ba laifi kika yi ba Wafaa , amma ban ji daÉ—i ba da kika manta cewa na hana ki kiyi aiki ke kaÉ—ai idan har ina gida ko da bacci nake ki dunga tashina muna yi tare .

Murmushi mai bayyana haƙora tayi ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya lokacin da ta kashe gas saboda girkin ta ya kammala .

Tana ƙoƙarin juyowa ya sassauta riƙon da ya mata ta juyo tana fuskantar sa.

"Hannun ta ɗaya ta ɗora a ƙirjin sa tana ɗan bubbugawa a shagwaɓe tace "wallahi har hankali na ya tashi ko wani laifin na yi ban sani ba.

Dariya yayi yana riƙe hannun ta yace "laifi kika yi mana meyasa za ki wahalar min da ruhina da kika san koyaushe yana nan ne a  tare da ke , meyasa baki tada gangar jikin ba ? Anyi aikin tare da shi ?

Murmushi tayi tana kallon sa irin waɗannan kalaman nasa su suka ta dilmiye a cikin ƙaunar sa ba tare da ta ankara ba ko kaɗan baya mata ƙouron kalaman sa na soyayya kamar yadda baya ƙasa a guiwa wajen gwada mata ƙauna a zahiri bai kuma jinkirtawa wajen yaba mata a duk lokacin da tayi wani abun a yaba kome ƙanƙantar sa kuwa '

Maza irin sa sukan sauya akalar zuciyar kowacce mace cikin sauƙi .

Sauƙe idanun ta tayi ƙasa tana murmushi saboda wani irin narkakken kallo da yake mata , ita irin salon Soyayyar sa nawi take mata kunya take sa ta har ta dunga jin wani yarrr a jikin ta.

Ko kaɗan bata iya masa martanin kalaman sa , kuma bata jin daɗin hakan so take ita ma ta koya su dunga musayar ƙauna kamar abun zai fi armashi .

Sautin dariyar sa ta ji da yasa ta É—ago kanta da sauri tana kallon sa sai ta ga idanun sa bayan ta yake kallo .

Juya ta yayi yana mata nuni da wasu tattabaru Mata da Miji (aure ) , da suka sauƙa ta gaban tagar kitchen ɗin suna soyayyar su .

"Wow look at them Wafaa so lovely.

Ya furta hakan muryar sa kasa-kasa yana rungumeta ta baya.

Zuba musu ido tayi tana kallon yadda suke sumbatar junan su kamar sa cinye bakin juna, sun matukar birgeta tsuntsaye kenan ma suke wannan soyayyar ? Ba shakka soyayya aba ce mai daÉ—i.

Daga shi har ita shagala suka yi da kallon soyayyar tattabarun mai ban mamaki da Sanya sha'awa tare da nishadi a zuciyar ma'abota soyayya.

Basu Ankara ba Matar ta gayyaci Mijin dan Su cimma maƙurar soyayyar Su ganin haka yasa da sauri Yakaka ta ɗaga tafukan ta biyu tana rufe fuskar ta .

"Habibi mu bar su hakan nan zasu yi sirrin Su.

Ta furta hakan tana ƙoƙarin janye jiki daga wajen .

'Yar dariya Doctor Hamza yayi yana sauƙe mata hannun ta da ta rufe fuskarta da shi

Cike da zolaya a muryar sa yace "ki buÉ—e ido ki kalle su darasi za mu É—auka mu ma anjima sai mu gwada.

tana buÉ—e idanun ta ta gan su a halin da ita bata so da sauri ta sake rufe ido ta juya tana shigar da kan ta kirjin sa har a cikin ranta kunya ta ji .

Rungume ta yayi yana dariya ƙasa-ƙasa kunyar ta na ɗaya daga cikin abunda yasa yake ƙara son ta ,kunya alamun imani ce bayan haka tamkar ado take ga ma'abota ita.

Ƙiran wayar sa da aka yi shi ya katse shirun nasu ya sassauta riƙon da yayi mata kafin ya zaro wayar sa daga aljihu. 

Cikin ransa cike da addu'ar Allah yasa ba É—aya daga cikin waÉ—an da yake zato bane .

Addu'ar sa kuwa bata karɓu ba domin kamar yadda ya zata dai Baba Prof ne da kan sa yake ƙiran sa.

Cike da ladabi ya É—aga kiran suka gaisa kafin ya tsinkayi Baa yana masa maganar da yake gujewa tsawon sati guda .

"Hamza ka kuwa je kun taho da iyalin taka ?

Shiru yayi saboda ya san kawai ya tambaye shi ne ba wai dan bai san cewa bai je ba sai dan ya ba shi damar shigar da uzurin sa.

"Ban tafi ba Baa amma yau dai nake son na je Insha Allah .

"To ka daure dai ka je saboda kullum sai Mahaifiyar ta ta ƙirani bana son kayi wani abunda zai taɓa mana zumuncin mu na dai faɗa maka ina kuma sake maimaita ma shi aure daman haƙuri ke jagorantar sa sannan ba zaka gina gidan ka ba sai ka zama jajirtatcen Namiji tsayayye sannan gidan ka zai zama yadda ake so .

"Ina umartar ka da kaje anjima ka dawo da Matar ka ka kuma cigaba da haƙuri da su su duka biyun aure ibada ne .

"To Baa insha Allah zan je Allah ya ƙara girma.

"Madallah Allah ya muku Albarka baki É—aya.

"Amin

Ya amsa yana sauƙe wayar ya kashe.

Ba sai ya faɗa mata ba daga cikin maganganun sa ta fahimci akan me ake zance da lokacin da ta fahimta ba ƙaramar juriya tayi ba wajen ɓoye razanar ta ta juya tana ƙoƙarin zuba musu abincin a farantin da ta ɗauko .

"Wafaa ya ƙira sunan .

"Na'am ta amsa tana ƙin kallon sa .

Ɗan jimm yayi yana juya zancen da yasan dole ya taɓa mata rai kafin ya tattaro juriyar sa yace .

"Baa da Amnee sun ce Sofi ta dawo , dan haka anjima zan je mu dawo tare.

Wata 'yar fara'ar da take tsakanin laɓɓa ta sakar masa da 'yar dariya tace "Yeehh Anty Sofi Oyo-yo gaskiya naji daɗi Yaya Dacta .

Matso ta yayi yana mata rumfa fuskar sa babu walwala yace "me kika ce ?

"Cewa nayi naji daÉ—i .

Ta sake faÉ—in hakan da siririyar murya ganin yadda ya haÉ—e fuska .

"Ba wannan ba da wanne suna na ji kin ƙirani yanzu ?

Dariya tayi tana tura shi baya ta ce "Anty zata dawo sunan ka na baya ma zai dawo..

Abincin da ta fara zubawa shi ya hana ya sake riƙe ta amma muryar sa bata ɓoye halin da zuciyar sa take ciki na rashin jin daɗi ba yace "Wafaa kar ki rage ko ɗigo na daga yadda muka saba al'amuran mu dan wai Sofi za ta dawo idan kika yi hakan za mu ɓata ni da ke , umarni ne wannan nake ba ki .

Bai sake cewa da ita ƙala ba ya fita daga kitchen. zuciyar ta taji ta ƙuntata "to ita meye laifin ta dan ta ce zata janye sunan da take ƙiran sa da shi a gaban matar sa ? Ita a ganin ta kiyayewa take son yi sanin da tayi Sofi tayi nisa a fagen kishi.

Hawayen da suka cika gurbin idanun ta ne suka zubo , wani irin tsoro take ji kan dawowar Sofi ko yaya zaman su zai sake kasancewa ?

Jikin ta duk a sanyaye ta gama zuba abincin ta ɗauko ta nufi falon , a kan kujera ta hango shi kafin ta ƙaraso ya taryo ta ya karɓe farantin hannun ta , sai ta koma kitchen ta ɗauko masu kayan sha da ta haɗa .

Ɗan shiru ya ratsa tsakani kafin lokacin da ta fara zuba musu haɗaɗɗiyar Maqluba da ƙamshin ta ya ɗau wajen ya tado wa da Doctor Hamza muguwar yunwar da yake ji .

"Wow what a delicious ? a complete meal containing, carbs, protein, fats, fibre, essential vitamins and minerals.

Da murmushi take kallon sa lokacin da ya kai loma ta farko ya haɗiye ya sake ɗiban wata yana lumshe ido ya cigaba da cewa  .

"Wafaa do you know Basmati rice has higher fibre content and is a great option for various meal plans, prevents against Cancer cell formation and prevents constipation against heart health risk.? 

Tana ɓoye dariyar ta ta ɗan girgiza masa kai alamun bata sani ba.

Kazar da ya É—auka ya gutsira ita ya nufo bakin ta da sauran .

Noƙewa tayi tana dariya tace " ni fa ba kaza zan ci ba kawai shinkafar raina ke so.

Wara ido yayi yana mata kallon mamaki kafin yace "Come on ki ci kaza Wafaa chicken is a great source of lean protein and has abundance of selenium, phosphorus, niacin.

Haka ba dan ta so ba ta gutsiri kazar ta ci kafin ya cigaba da bata abincin Suna cikin ci tace "Habibi kai baka cin tumatir Sosai ni kuma shi nafi so ka dunga bani sosai.

Bayan ya haÉ—iye abincin bakin sa yace "eh kuma kina da gaskiya domin shi tomato is a great source of vitamin C, potassium, vitamin k1, folate which are great for normal tissue growth and cell function.

Dariyar da take ta riƙewa tuntuni ita ce ta kufce mata ta shiga ƙyalƙyalawa har tana kwanciya a jikin kujera , shiru yayi yana kallon ta da murmushi a laɓɓan sa daman burin sa kenan ya ga fara'ar ta farin-cikin sa yana tare da walwalar ta.

****

Kamar yadda Doctor Hamza ya alƙawarta A daren ranar bayan Sallar isha'i ya tafi gidan su Sofi domin su dawo tare lokacin da ya ɗora idanun akan ta sai da ya razana saboda ramar da yaga tayi cikin 'yan satika.

Yadda yake zaton za ta masa hauka sai ya ga akasin haka sai nan-nan take yi da shi daga ita har Mahaifiyar ta da hakan yasa dole shi ma ya sau jiki suka ɗan taɓa hira da Momy kori kamar kome bai faru ba.

Inda ya É—an ga alamun sauyi daga wurin su bai wuce lokacin da suka kawo masa girke-girken da aka shirya musamman domin shi sannan su ka matsa kan sai ya ci.

Shi kuwa ya riga ya É—ebi girkin Yakaka ya É—ora da lafiyayyen kunun aya da ta musu dan haka cikin sa a cike yake ha'in babu masaka tsinke , dan haka ya kafe kan cewa shi babu abunda zai iya sake sanyawa a cikin sa sai kuma gobe.

Nan ya ga yadda Sofi tayi kicin-kicin bai bi ta kan ta ba yace tayi sauri ta shirya ta zo su tafi.

Ga tunanin sa Momy Kori zata ajiye Sofi a gaban sa ta mata ko da 'yar nasiha ce tunda Baban su baya ƙasar yayi tafiya amma ga mamakin sa ko addu'a Momy Kori bata musu ba .

Mamakin sa bai ƙaru ba sai ma lokacin da suka ta shi tafiya yaga Momy Kori ta sa an kinkimi Manyan kulolin abincin nan ta ce wai a kai masu mota su tafi da abincin idan ya so gobe da safe sai Sofi ta ɗumama masa yayi breakfast .

Mamakin sa bai ɓuya ba yace "Momy ɗumamen abinci kuma.? Da Allah a mayar da abincin nan a bayar ga masu aiki .

Momy Kori za tayi magana Sofi tayi saurin katse ta "eh Momy a mayar da abincin nan Doctor fa baya cin abincin da ya kwana .

Wani kallon yatsutsu Momy Kori tayi mata kafin ta kaɗa kai ta ce "to ai shikenan kowa rai ya yiwa daɗi bayan mai shi kai kuma My Son ka bar daɗi tunda baka cin ɗumame sannu ka ji baƙin bature .

Daga haka tayi juyawar ta cikin gida su kuma suka shige mota .

A hanyar su ta komawa gida Sofi sai shisshige masa take tare da bayyana masa zallar ƙewar sa da tayi .

A can-can yake amsa mata saboda ba wai ya huce bane gaba É—aya.

Bai ankara ba ya ji ta faɗo mai jiki gaba ɗaya ƙiris ya rage kan motar ta kufce masa yayi saurin gangarawa gefen titi.

Ransa a matuƙar ɓace ya waiga yana kallon ta "Sofi wanne irin shirme ne wannan ki...

Bata ba bar shi ya ƙarasa abunda yake son cewa ba sakamakon haɗe fuskar ta da tayi da ta shi.

Sun ɗau lokaci a haka kafin ya zame fuskar sa bai ce ma ta kome ba ya fara ƙoƙarin tada motar yana dai-daita nutsuwar sa '

Ba sabon abu bane a wajen sa Sofi ta  nema shi da kan ta amma yau sai ya ji sam bata wani burge shi ba kamar baya , har ji yayi tana ɗan ba shi haushi-haushi , ya fara sabo da yadda ake ɗan jaa masa aji yana nema ana ɗan nan-noƙewa ana zille masa hakan yana ba shi nishaɗi tare da sa shi ya ji cewa lalle fa shi Namiji ne .

"Sofi ki bari nayi driving please kar ki sake taɓa ni.

Bata amsa masa ba illa wani shaiÉ—anin murmushi da take jifan sa da shi tana wani kashe masa ido É—aya .

Lokacin da suka ƙarasa gida Sofi ta riga Doctor Hamza sauƙa a motar dan haka ita ta riga shi takawa zuwa wajen ƙofar kai tsaye ta miƙa hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi

Yakaka wacce take zaune zaman jiran su zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan sanin bugun ƙofar ko na waye .

A hankali ta miƙe ta ƙarasa gaban ƙofar kafin ta buɗe sai da tayi addu'a sannan ta miƙa hannu a hankali ta buɗe ƙofar  .

Kallon-kallo aka yi a tsakanin su kafin Yakaka ta ƙalato murmushi ta ɗora akan fuskar ta dai-dai da ƙarasowar Doctor Hamza ta ce "Anty Sofi sannu da zuwa .

Sofi wacce fuskar take ɓoye yanayin halin da zuciyar ta take ciki ta miƙa hannunwan ta duk biyu ta rungumo Yakaka.

"I miss you so much Lil how are you?

Ta furta hakan kafin kuma ta sake ta  tana mai tura ta baya ta samarwa da kan ta hanyar shiga gidan ta wuce kai tsaye ba tare da ta sake kallon Yakaka ba.

Yakaka bata dawo nutsuwar ta ba sai da ta ji sanyin hannun Doctor Hamza ya riƙe nata hannuwan "Wafaa mu shiga ciki .

Cikin wani irin yanayi Sofi take bin gidan da kallo kamar an sauya mata shi ta ko'ina ƙamshi ne ke ta shi shiru falon sai ƙira'ar kur'ani da ke fitowa ta sifuku .

Akan kujerar da ta saba zama nan ta zauna tana harɗe ƙafafu ta miƙa hannu ta ɗau Remote tana ƙoƙarin sauya tasha .

A ɗarare Yakaka ta zauna a kujerar da take kusa da ƙofa shi kuma Doctor Hamza kai tsaye ya wuce ɗakin sa .

"Anty Sofi ina wuni.? Ya Su Momy ?

Yakaka ta furta hakan tana kallon Sofi .

Wani irin ɗago kai Sofi tayi ta tsattsare ta da ido tsawon daƙiƙai fiye da hamsin irin kallon da take mata ya kaɗa mata ciki har yasa ta nemi diriricewa .

Wani mummunan tsaki Sofi ta jaa da Yakaka ta ji shi har tsakiyar kan ta .

Lokaci É—aya ta É—auke kan ta a fusace tana kaÉ—a kai.

Nan take ta tunanin kama kan ta ya faɗo mata dan haka bata sake cewa ƙala ba sai ta ɗau wayar ta .

Zaman shirun da yake cike da ƙosawa daga ɓangaren su duk biyun ne ya miƙa suna jiran fitowar Doctor Hamza wanda sai da ya shafe fiye da mintoci talatin dan kuwa bayan wanka da yayi sai da yayi sallolin sa na shaf'i da watir .

Sannan ya fito falon ya same su kamar wasu gumaka , ita Yakaka kan ta yana ƙasa tana amfani da wayar ta ita kuwa Sofi sai sauya tasha take , bayan ya musu Sallama bai ɗau lokaci ba ya musu 'yar gajeruwar nasiha da ƙare ta da gargaɗi tare da hannuka mai-sanda ga Sofi kan cewa babu shakka shi ba zai sake ɗaukar raini ko rashin kunya tare da neman fitina ba dole ne kowaccen su ta zauna da 'yar uwar ta lafiya a ƙarshe ya sake musu batun rabon kwana inda ya tabbatar da yin ƙwana ɗai-ɗaya a matsayin ranakun girkin kowaccen su '

Bayan gama nasihar sa da dukkanin su suka nuna Amincewar su tare da ɗaukar gargaɗin sa ita Yakaka miƙewa tayi bayan ta musu Sallama.

Taku ɗaya tayi shi ma Doctor Hamza ya miƙe , yana yin taku ɗaya ya riƙo hannun ta da yazo dai-dai da jin sauƙar hannun Sofi da yayi a cikin ɗaya hannun nasa.

Yakaka tana juyowa idanun ta suka sauƙa akan hannun sa da Sofi ta riƙe wani abu ta ji ya soki zuciyar ta da yasa da sauri ta zame hannun ta daga cikin na shi .

Ba tare da ta sake juyowa ba ta nufi É—aki tana shiga ta murÉ—a É—an makulli ta rufe .

Jikin ta kamar babu lakka ta samu wajen zama a bakin gado .

Bata ankara ba kuka ya taho mata ta kai hannun ta biyu ta toshe bakin ta .

Ta kasa sanin dalilin da yasa zuciyar ta ke ƙonewa bayan kuma ba yau ne ba rana ta farko da Sofi ta fara riƙe Doctor Hamza a gaban ta amma a baya bata taɓa jin irin yadda take ji yanzu ba ko me yasa ?

Kukan ta chak ya tsaya lokacin da ta ji ya taɓa ƙofar cikin kwantatciyar muryar sa yake ƙiran sunan ta .

Shiru tayi ba tare da ta amsa ba "Yau lokacin Sofiya ne Yakaka kar ki aikata abunda idan aka aikata miki ba za ki so ba.

Zuciyar ta ta mata gargaɗi mai kama da tunasarwa , dan haka taƙi yarda tayi ko da ƙwaƙƙwaran motsi haka tana jin sa ya ɗan yi mintoci biyu zuwa uku yana taɓa ƙofar kafin ta ji takun sa yana barin wajen .

Silalewa tayi ta kwanta ruwan hawayen idanun ta na hagu na shiga cikin na dama .

****

Washegari da safe lokacin da Doctor Hamza ya sauƙo daga ɗakin Sofi a kitchen ya tarar da ita tana aikin ta hankali kwance  duk yadda ya so ya hango wani sauyi a tare da ita bai ga ko alama ba daga yadda take masa bata sauya ba .

Sai ya ji ta saƙe ƙima a idanun sa ƙaunar ta kuma ta sake ninkuwa a zuciyar sa babu shakka managarciya ce tana kuma da dattaku.

Shi ya taya ta suka ƙarasa aikin kafin a gurguje ya shirya kafin ya gama shiri ta haɗa musu abin karyawa .

Yana gaf da kammala Breakfast Sofi ta sauƙo yau dai da alama ta ji faɗan Doctor domin doguwar riga ce a jikin ta mai faɗi wacce bata ƙarasa ƙasa ba ta tsaya gaba kadan da guiwar ta sai hula da ta sa ta rufe kan ta .

Kadaran-kadahan ta amsa gaisuwar Yakaka kafin tace mata "zuba min abincin na ga ko zan iya ci .

Da sauri Yakaka ta É—au faranti ta zuba mata abincin butter chicken ne tare da khubsa.

Tun Sofi tana ci tana wani gatsine-gatsine har dai ta sau jiki daÉ—in girki ya kwashe ta ta buÉ—e baki tana wurga loma bayan loma .

"Doctor wannan Butter Chicken ɗin kamar daga HH Continental aka yi order ko? Dan naji irin dandanon girkin su ne. 

Ta gefen ido ya dube ta dai-dai lokacin da yake miƙewa ya ce "Ni da nake da Mata kamar Wafaa yaushe zan tafi yawon gidan sayar da abinci ai wannan ya zama tarihi sofiya .

Hannun Yakaka ya kama "Wafaa mu je ki min rakiya ni zan tafi .

Sofi tana son miƙewa amma daɗin abinci ya danne ta dole tana ji tana gani Yakaka ta tafi raka Doctor Hamza ita tana kai lomar girkin Yakaka.

Bayan ta dawo daga rakiyar sa ta tarar Sofi ta gama cin abincin ta bar kome a wajen ta koma kan kujera ta hakimce .

Bata gaji ba ta tattara kwanukan ta kai kitchen ta wanke .

A É—arare ta dawo falon ta zauna akwai wani series ne da take son kallo da bata samu damar gani ba jiya ta san suna maimaitawa da safe .

Tana zama ta ji Sofi ta jaa wani ƙaton tsaki.

A hankali ta miƙa ɗaga idanun tana kallon ta irin mummunan kallon jiya shi ta hango a idanun Sofi .

Har ga Allah tsoron yanayin kallon take domin kallo ne irin na hatsabiban mutane mugaye , kallo ne da yake ɗauke da saƙonni  masu zafi tare da ƙaƙƙarfan gargaɗi .

Ciɗak¡ ta miƙe bata tsaya ba sai ta wuce ɗaki tana jin lokacin da Sofi tayi wata ƙwafa mai ƙarfi .

Tana shiga wayar ta ta ɗauka ta ƙira Amnee suka gaisa wacce ta dunga mata nasiha tana kwantar mata da hankali kan dawowar Sofi a ƙarshe ta miƙawa Mamar su wayar .

Suka gaisa kafin su yi 'yar hira da rabin ta labarin diramar Bulama ne wanda aka kai shi makarantar kwana ta firamari amma ya gudo da kukan sa da kome a cewar sa ba zai iya barin Mamar Bulama ba .

Yakaka ta yi ta dariya tana jin ƙauna tare da tausayin ƙanin ta wanda ba su wani shaƙu da juna ba.

A ƙarshe suka yi Sallama tana sauƙe wayar ta ƙira Falmata nan ma hirar suka sha sai dai a cikin muryar Falmatan ta iya jin tana da damuwa da nan take hankalin ta ya tashi dan haka ta matsa mata kan sai faɗa mata me yake damun ta ? Ko haihuwar ce ta zo ?

Falmata bata ɓoyewa Yakaka kome nan ta faɗa mata irin matsananciyar damuwar da take ciki kan barin ta da Youssouf yayi ya tafi wajen aiki ta ɗora da cewa "kuma fa Yakaka sau uku kawai muke waya a rana kuma sau biyu kawai muke Appel vidéo a rana kafin ya tafi kuma ba haka ya min alƙawari ba cewa yayi kawai koyaushe yana tare da ni .

Shiru Yakaka tayi tana jinjina rikicin Falmata a zuciyar ta kafin ta ce "Falmata waya har sau uku a rana ? Ga kuma vidieo call ? Sau biyar fa kenan kike jin sa bai yi yawa ba Falmata ?

Kin san fa tare da matar sa yake a can , sannan ita ma tana da hakki a kan sa bakya ganin za ki shiga hakkin ta dayawa idan ya zama koyaushe kuna tare a waya ? Ni dai fatana Allah yasa bakwa doguwar wayar dare Falmata abunda duk ba za ka so ayi ma ba kar fa ka yiwa wanin ka '

Tsit Falmata tayi daga can tana É—an turo baki kamar Yakaka na ganin ta sai cewa tayi "to ai nima ina da hakkin ni ba barina yayi ba ma gaba É—aya ya tafi da ita ba ? ina cewa kullum tare suke kwana ? Meye dan kawai mun yi waya ?

Yakaka tana danne dariyar ta ta ce "a ah wallahi da kome muddin aka ce za ki dunga ratsa tsakanin lokutan da ya kamata ace yana tare da ita to ba shakka kina shiga hakkin ta haba mana Falmata ban fa san ki da zalunci ba , dan Miji yafi son ki kar ki yadda ki biye masa ya dunga ƙuntatawa matar sa .

Ni yanzu da Yaya dakta yafi son Sofi akaina za ki so ya dunga min abunda babu daÉ—i akan ta ?

Girgiza kai Falmata tayi tana jin duk jikinta yayi sanyi ta ce "ki daina cewa haka Yakaka Yaya dakta yana son ki ba zai taɓa walakanta ki akan Sofi ba.

"Kuma nima ba wai so nake ya dunga walakanta matar sa akaina ba kawai dai.

ÆŠan shiru tayi tana numfasawa kafin ta ce "Yakaka ina son shi ne dayawa zuciyata tana min ciwo idan har na tuno yana can tare da ita ni kuma ga ni nan da ciki himm ina fama.

"Ki rage kishi Falmata kowacce mace tana son Mijinta amma domin a zauna lafiya babu cutarwa sai a dunga sassautawa ana tausar zuciya kin jin ko Gimbiya Falmata., ke ce fa Uwargidan Sarki watarana uwayen gida da kawaici aka san su domin suke jagorar Gida .

Sassauƙar dariya Falmata tayi tana jin ranta na yin sanyi ƙaunar 'yar uwar ta na kawo mata

****

Kafin cikar sati ƙarfi da yaji Yakaka ta koma zaman ɗaki saboda yadda Sofi ta kasa ta tsare alhalin ta san Yakaka tana matuƙar shakkun ta .

Muddin ta fito falo to aiki za tayi ta bar wajen ko kuma idan Doctor Hamza yana nan wanda shi bai san yadda yinin su yake kasancewa ba idan baya gidan .

Babu abinda yafi daÉ—a tayarwa da Yakaka hankali irin ji da tayi Doctor Hamza a jiya da dare yace cikin kwanaki biyu masu zuwa zai yi tafiya zuwa jahar Kano za shi asibitin koyarwa na Kano yin wani aiki na kwanaki uku "kenan zai bar su daga ita sai Sofi a gidan 'yar sakewar ma da take samu tayi a cikin awowi ishirin da huÉ—un idan yana nan zasu zama babu .

Hakan ya daɗa sanyayar mata da jiki har wani ɗan zazaaɓi take ji yana kama ta bayan bugun zuciyar ta da take ji yana sauyawa a bayan kowacce sa'a ɗaya ga kasala da ta dirar mata .

Bayan fitar sa aiki da ƙyar ta iya lallaɓawa ta fito yin girkin rana da ta san Sofi za ta iya buƙata ba wai dan cikin ta ba saboda ita gaba ɗaya ma yau tunda ta tashi bata sha'awar kome dan ko da suka zauna karin kumallo bata iya cin kome ba sai ruwan shai da ta zubawa cikin ta.

Ba irin rarrashin da Doctor Hamza bai mata ba kan ta ci abinci amma ta gagara dan kan shi yayi shiru ya bar ta bayan ya gama nazarin ta.

Fitowar ta daga ɗakin ya zo lokaci guda da ƙwanƙwasa ƙofar gidan da aka yi dan haka ta ɗan saurara jin ana sake ƙwanƙwasawa yasa ta taho ta buɗe ƙofar .

Musayar kallo suka yi ita da wacce take  tsaye a dokin ƙofar tana jifan ta da siririn murmushi mai tarin ma'anoni .

An-anty Samy .

Ta ambata a harÉ—e ,

"Yaks Amarya a gidan Doctor , matsa min hanya mana na wuce ko kuwa na koma ne ba'a maraba da ni ?

Da sauri ta matsa tana girgiza kai da 'yar fara'a tace "a ah ina maraba da ke mana Anty Samy sannu da zuwa .

Tayi gaba Samy baby ta bi bayan ta tana ƙare mata kallo .

Suna ƙarasawa tsakiyar Falon Sofi na sauƙowa daga sama wata 'yar shewa suka yi ita da Samy Baby kafin su taho su rungume juna suna 'yan ƙananun maganganun su na shaiɗana .

Samy baby za ta zauna Sofi tayi maza ta hana ta "friend me za ki zauna yi anan ? Ta shi mu tafi sama akwai muhimman maganganun da kin san nan ba muhallin yin su bane ba .

"Ok friend

Samy baby ta furta haka tana miƙewa tsaye ta ɗau jakar ta kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce take rakuɓe a gefe wata 'yar iskar dariya tayi mai kama da shewa

"Hehehe Yaks kenan ka ga manyan amare masu harin miƙamin uwargida an gaishe ki  Yaks da tsaurin ido .

Shiru Yakaka tayi bata ce ƙala ba gaisuwar da ta yi niyyar yi ma ta fasa jin yadda Samy Baby take mata ba'a sarai ta fahimta .

Kitchen ta koma su kuma su ka hau sama suna shiga É—aki Samy Baby ta lailayo wata ashariya ta kwatsawa Sofi .

"Kina me Sofi ? Nace kina me har kika bari yarinyar nan ta samu sakewar da zata fara haramar ajiye ƙwai a gidan nan ? Na shiga uku Sofi ina mai tabbatar miki taki ta kusan ƙarewa a gidan nan .....

Sofi da lokaci ɗaya ta diririce idanun ta suka sake shigewa ciki da in'ina a muryar ta tace "me..me ..kika ce ban..ban fahimta ba wanne irin ƙwai kuma kamar wata kaza'

"Yo ai ga ki nan babbar kaza Sofi tunda har kika kasa gane Yarinyar nan Yaks tana da shigar ciki kike zaune baki sake baki É—au kowanne irin mataki ba...

Bata ankara ba ta ji Sofi ta sakar mata Mari da yasa shiru ya gifta wajen .

Kafin ta tsinkayo muryar Sofi tana cewa "kar ki sake min wannan mummunan Fatan mummunan zancen ,

"kin yi hauka ne Sofi za ki mare ni ?

"A turu nake Samira ya za ki zo kina barazanar fasa min zuciya da mugun fata ki sa na faɗi na mutu tun kwanana bai ƙare ba .

Gyara fuska Samy Baby tana ƙoƙarin shanye fushin ta saboda tarkon da take son ɗanawa kar ya lalace ta sassauta muryar tace

"Wallahi tallahi I swear Sofi Yarinyar nan ciki ne da ita ki nutsu ki dawo hankalin ki tun wuri mu yiwa tufka hanci kafi....

Wani razanannan ihu da Sofi tayi da ya amsa gidan gaba ɗaya sai da yasa Yakaka wacce take kitchen ta zabura tana dafe ƙirji a take taji zuciyar ta ta hautsina da daman tunda tafara girkin warin Albasa ke ɗaga mata hankali.

Ba shiri ta bar baro kitchen ta wuce É—aki tana mayar da numfashi "anya Sofi kan ta É—aya ?

"Samira da gaske kike ? da gaske kike da gaske ?

Kamar an safure ta ta miƙe tayi hanyar fita daga ɗakin da gudu Samy baby ta bita ta riƙo ta .

Kufcewa tayi tana watsa mata wani mugun kallo kafin cikin muryar da ta buÉ—u kamar ba ta ta ba tace "ki bar ni naje na kashe ta na farka mata ciki na zo miki da É—an tayin cikin na ta wallahi sai na kashe ta.

Kallon baki da hankali Samy baby ta jefa mata kafin ta ce .

"Dallah Sofi ki nutsu ya kike abu kamar wacce ba tayi karatu ba ? Kina abu kamar wata jahila kina tunanin yanzu idan kika je kika kashe 'yar mutane ke ma za ki rayu da Hamzan ne ba tare da an miki É—aurin rai da rai ba ko kuwa ke ma a kashe ki.

"Na yarda a kashe ni idan na kashe ta akan dai mu rayu ni da ita alhalin ta raba ni da farin-ciki na ina ji ina gani bakin-ciki zai kashe ni na mutu na bar mata duniyar su rayu ita da Mijina .

"Na yarda za ta mutu amma ba ta irin wannan hanyar da kike son bi ba ko da kashe ta kike son yi ki bari sai an kauda-bara ta yadda za ki kashe ba tare da an samu mai iya É—aga ido ya dube ki ba ko kuwa ma kawai a mata abunda zai kashe ta ba tare da an zarge ki ba .

"Ta yaya faÉ—a min hanyar ?

Sofi ta furta hakan jikin ta har wani mazari yake , a kaikaice Samy baby ta dube ta cikin ran ta kuwa dariya take kwasa "Yau Sofi uwar bin Bokaye har wata nahiyar ita ke tambayar ta yaya za'a yi ? Lalle notikan cikin kan Sofi sun kwance baki É—aya .

Gyara zama tayi tana jin Allah ne ya kawo mata hanyar warwarewar tata matsalar da kome ya kwaɓe mata bariki tana ƙoƙarin kwashe kayan ta daga kanta ta juya mata baya ta bar ta a cikin rana dan kuwa ko Alhaji Gali a halin yanzu fiye da watanni uku kenan ta daina ganin ƙeyar sa alhalin lokacin biyan kuɗin gidan haya yayi haka tana ji tana gani bayan ƙara mata sati biyu da masu gidan suka yi suka zo a ƙarshe suka kore ta sai gidan ɗaya daga cikin abokan shaiɗanan ta ta koma da ko kaɗan ba jin daɗin zaman gidan take ba saboda ba shi da wani hali sosai irin mazan nan ne da Zina ta aure su wanda ko basu da sisi sai sun yi ta.

Fahimtar hakan da tayi yasa ta fara ƙulla wacce za ta fissheta idan zaman Abujan ya gagara ne tana iya komawa ko Damaturi ne ta karkaɗe kwalin ta ta shiga neman aikin da za tayi ta riƙe kan ta dan kuwa ko a mafarki ta san bata doshi Maiduguri gidan Ubanta ba bata ma da matsugunni a gidan sannan ita a karan kanta bata jin za ta iya rayuwa ƙarƙashin iyayen ta.

Sai dai me ? Kuɗaɗen da suke account  ɗin ta ba zasu ishe ta yin irin rayuwar jin daɗin da take tsarawa kan ta ba ko da ta koma Damaturu domin so take ta shiga gari sosai ta wataya a ƙarshe ta samu wani ɗan Matashin kyakkyawan Saurayi haka ta chaka masa su yi aure .

Dan haka ido rufe take neman kuÉ—i tunda kuwa yanzu dama ta samu da zata iya samun su daga Sofi to me za ta jira ?

Muryar Sofi ta katse mata tunani ta da take cewa " Ni kin hana ni naje na aiwatar da manufata ke kuma kin yi zaune shiru baki kawo wata hanyar ba ki faÉ—a min ya zan yi ?.

"Sofi ki buɗe bakin Aljihu kiyi ɓarin kuɗin na san dai kin Fahimceni ni kuma na miki alƙawarin ko nan da birnin Sin ne zan je miki wurin Boka ba sai kin ma tafi da kan ki ba bare har a iya zargin ki .

Da wata irin Murya Sofi ta ce " ki koma min karnataka Samira gurin Bokan da ya min aiki akan zuciyar Doctor zan baki adireshin sa da kome sannan zan bayar da kuɗin da zai ishe ki har kije ki dawo da kuma kuɗin aikin sa , bana so na motsa ma daga tsakanin su domin ko kallo bana so ya sake shiga tsakanin su ....

Samy Baby wacce tafi zaƙuwa da zancen kuɗin jin tarkon ta yayi kamuwa tace "amma fa kin san kuɗaɗen dayawa Friend..

"Ko miliyan ishirin ne zan sayar da gwalagwalai na na baki kuɗin bana so a ɗau lokaci nasan kin san manyan mutane a ƙasan nan dan haka samun visa ba zai miki wahala ba idan son samu ne cikin satin nan ki tafi kai ni idan zai yiwu ma cikin kwanaki biyu masu zuwa saboda bana so bana kuma fatan yarinyar nan da ita da abunda ke cikin ta su sake yin sati ɗaya a duniya .

Nisawa tayi tana gatsa gefen bakin ta da haƙori tace " Sannan so nake na kashe ta da hannun na Samira da hannu na nake son kashe ta shine kaɗai abunda zan iya mata da zai sa zuciyata ta wanku daga baƙin-cikin da ta samu a ta sanadin ta dan haka daga kin isa can an yi aikin kawai ki ƙirani ki sanar min ina mai tabbatar miki da sai dai ki dawo ki tarar ana zaman makokin mutuwar ta .

Shiru Samy Baby tayi tana kallon Sofi cikin ran ta tana girmama rashin Imani irin na Sofi yau ta zama rana ta farko da ta fara jin shakkun samuwar cikakken hankali ga Sofi to kodai tana da rauhanai ne ????? Ko kuwa Mai rabon shan duka ne da baya jin Bari

Assalam Alaikum masu karatu.

Albishirin ku ?

Na san kun ce goro goriya goro .

Yau Maman 'yan biyu tagwayen shafuka ta muku.

Ina nufin kar ku motsa shafin nan tare yake da É—an uwan sa da yakasance kuma murfi na baki É—ayan littafin Mafari insha Allah .

A sha karatu lafiya .
[4/15, 8:17 PM] +234 706 503 6187: MAFARI

           ( HARGITSIN RAYUWA)

UMM'MUAZ

KARSHE

(A)

A daren ranar Doctor Hamza bai dawo daga aiki ya tarar da Sofi a gida ba saboda tunda rana suka fice ita da Samy ko Yakaka bata san fitar su ba .

Hakan ba ƙaramin ɓatawa Doctor Hamza rai ya yi ba saboda ai tsagoron raini ne matar auren ka ta fita unguwa ta kai har dare ba tare da ta nemi iznin ka ba .

Sai dai halin rashin lafiyan da ya zo ya tarar da Yakaka a ciki ya É—auke masa hankali daga kula haukar Sofi .

Nan take ya shiga bata duk wata kulawar da ta dace domin samun tabbacin abinda yake zato .

Maƙurar farin-cikin da zai iya cewa bai taɓa jin yanayin sa ba ya tabbata a zuciya da kewayen jinin jikin sa baki ɗaya lokacin da gwajin fitsarin da ya yiwa Yakaka ya bayyana masa da tabbatuwar zaton sa

Yakaka tana É—auke da gudan jinin sa a Mahaifar ta nan da wasu watanni zai zama uba bayan shekaru bakwai da ya kwashe da yin auren sa na farko wanda hakan ya sadar da shi cikar shekarun sa arba'in cif ba tare da ya samu É—an kan sa ba .

Sai fa yanzu da Allah yayi tsiron halittar gudan jinin sa a tare da Yakaka shi kuwa da wacce irin kalma zai miƙawa Ubangiji godiyar sa ?

Ganin sa ya mayar kan Yakaka wacce take bacci hankalin ta kwance da ba domin larurar saurin bacci na mata masu ƙaramin ciki ba a ɗan zaman su da yanzu-yanzu tayi fitsari ta ba shi yayi awu bai ci ace kafin ya gama gwajin har tayi bacci ba .

Fuskar ta ya tsirawa idanu yana jin wani ƙaunar ta mai ƙarfi tana sake fisgar sa har yana jin kamar babu wani sarari da yayi saura a zuciyar sa da ƙaunar ta bata riga ta cika ba .

A hankali ya ɗaga hannu yana shafar kumatun ta da suka sake yin suɓulɓul suna ƙyalli na musamman .

Zazzaɓin da ya dawo ya tarar da shi ya rufe ta sosai a yanzu ya sauƙa saboda ya bata maganin sauƙe zafin jiki ta sha .

"Wafaa .

Ya ƙira sunan ta a hankali yana ɗan hura mata iska a fuskar ta '

BuÉ—e idanun ta da suka yi nawi tayi tana kallon sa a raunace .

"Wafaa yaya kike jin jikin yanzu ? Za ki iya tashi muyi sallah ?

"Habibi nayi sallar isha ina jin bacci sosai ni.

"Na san kin yi wannan Sallar miƙa godiyar mu ga Ubangiji za muyi da yayi mana kyautar sa mafi girma .

Hannun sa ya kai ya É—ora akan cikin ta kafin cikin taushin murya yana kallon idanun ta ya cigaba da cewa

"Allah ya arzuta mu da samun rabo , Wafaa we are going to have a baby, zan zama Baba Wafaa za ki Haifa min Baby .

"Da gaske ?

tace da shi tana ƙoƙarin miƙewa zaune ya taimaka mata ta zauna.'

Yana murmushi ya amsa mata "Da gaske Wafaa na baki Baby i am gonna be a Daddy.

Wani irin yanayi ta ji mai sanyi tundaga ƙasan ran ta da ya chakuɗu da kunyar ta ta halitta dan haka ta tafi da sauri ta shige jikin sa tana ɓoye fuskar ta a ƙirjin sa .

Dariyar da bata da sauti yayi yana riƙe da ita ya miƙe kafin ya sake cewa " Alhamdulillah for blessing us in the most special way as a Mum and Dad.

Ya É—ago ta a hankali ya sumbanci goshin ta sannan ya sake cewa "muyi Sallah Wafaa domin mu nunawa Ubangiji godiyar mu.

GyaÉ—a kai tayi ba tare da ta amsa ba .

Tsananin farin-cikin da yake ciki a daren ya mantar da shi takaicin Sofi dan ko da ta dawo tana wani kame-kamen ta lokacin da ta shigo falon ta tarar da shi yana aikin sa a laptop Yakaka kuma tana bacci a jikin sa .

Wajen ƙarfe goma saura na dare za ta fara masa ƙwarƙwasa ya ɗora hannun sa akan laɓɓan sa yace "shittt please Sofi kar kiyi hayaniya ki tayar da ita a bacci tana buƙatar hutu Sosai bana son abinda zai dame ta .

Wani sakototo Sofi tayi baki sake tana kallon sa .

"yau ga sabon salo kuma , kullum abun daÉ—a lalacewa yake , ta aiyana hakan daga cikin ran ta .

kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce ta juya baya tana kwance akan kujera tayi matashin kai da cinyar sa fuskar ta na fuskantar jikin sa'

Hayaƙi-hayaƙi ta ji yana safko mata yana sanya ta gani dusu-dusu .

"Bata da lafiya ne ?

Ta furta hakan a shaƙe tana tattaro duk wata sauran juriya da ta rage mata .

Murmushi Doctor Hamza yayi da har take Iya hango ƙyallin haƙoran sa da muryar sa mai cike da nutsuwar da bata ɓoye halin farin-cikin da yake ciki ba yace "Sofi we are pregnant insha Allah in nine months we will welcome a new bundle of joy into our family.

Kamar wacce aka dokawa guduma a ka haka Sofi ta ji, kunnuwan ta suka rabu da ji na ɗan wani lokaci duk kuwa da cewa a ɗazu Samira ta faɗa mata batun cikin Yakaka amma bata ji dukan zancen irin yanzu ba dan kuwa a ɗazu tana da ƙarfin jikin iya yin zabure-zabure a yanzu kuwa da  zancen ya tabbata cewa dai Doctor Hamzan tane ya yiwa Yakaka ciki ji tayi duk wata jijiyar jikin ta tayi tsayuwa daga barin yin aiki na wucin gadi .

A yau taurin zuciyar ta gaza yin tasiri yayi domin kuwa ruwan hawaye ne ya ɓalle mata kamar an buɗa famfo .

Sai shiƙar kukan ta Doctor Hamza ya ji wanda ya mayar da kan sa ga aikin sa .

Tsam yayi yana jin ɗan guntun tausayin ta na kawo masa , daga can ƙasan ran sa sai ya ji kamar fa bai kyauta ba yadda ya sanar mata da batun cikin Yakaka dole za ta iya jin babu daɗi tunda ita Allah bai bata ba musamman da yakasance Sofi tana da bala'in kishi.

A hankali ya ɗago kan sa yana kallon ta sai dai kafin yayi wani yunƙuri ta miƙe kamar ana tunkuɗa ta ta bar wajen .

Girgiza kai yayi yana mai mayar da kan sa ga aikin sa da yake so ya kammala kafin gobe saboda a gobe da yamma yake so ya bar garin zuwa Kano .

Washegari

D

octor Hamza da kansa ya shiga kitchen domin samarwa Yakaka da abunda za ta ci saboda kusan kwana tayi da zazzaɓi asubar farko kuma ta fara Amai .

Dan haka ya kama ta zuwa falo ya kunna mata tv yace tayi kallo kafin ya gama haÉ—a mata abun karyawa.

Ba dan ta so ba ta haƙura ta bar shi ya shiga kitchen sai dan ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin ta wata irin kasala ce take bin gaɓɓan jikin ta jikin ta babu ƙarfi gefe guda kuma bata son warin Albasa da tasan muddin ta shiga kitchen to kuwa sai ta shaƙa .

Lokacin da ya gama ya kawo mata bata wani ci dankalin da ya kawo mata tare da ƙwai na kirki ba tace ta ƙoshi .

Yana tsakiya da rarrashin ta kan ta daure ta sake ci kaɗan Sofi ta sauƙo bata dubi inda suke ba ta zauna akan kujera ta ɗau remote.

Lokacin da ya dubi fuskar ta sai da zuciyar sa ta doka da karfi ganin yadda fuskar tata ta kumbura suntum idanun ta kuwa har kamar kwanciyar jini.

Da sauri ya baro Yakaka ya juyo gare ta "Subhananlah Sofi me ya same ki haka ? cikin dare ɓarayi sun shigo gidannan ne ?

Ba tare da ta dube shi ba tace "Da aljanu muka yi dambe ko ka manta?

Yadda tayi maganar a cushe ya so ba shi dariya amma sai ya gintse fahimta da yayi so take ta zo da rainin na ta da tayi alƙawarin ta daina '

"Oh i see .

Yace yana barin kusa da ita ya koma ga Yakaka wacce ita ma ta tsorata da ganin yadda Fuskar Sofi ta kumbura tayi jawur kamar wacce ta shiga filin dambe da wanda ya fi ƙarfin ta .

Bayan ya shirya ya fito gargaÉ—i ya yiwa Sofi kan kada ta yarda ta fita ko'ina ta zauna ta kula masa da Wafaa .

Kafin azahar zai dawo su yi Sallama saboda bayan Azahar zai tafi .

Bai yi zaton samun amsa mai daɗi daga gurin ta ba amma ga mamakin sa sai ya ji ta amsa har tana masa fatan alheri hakan sai ya faranta masa tare da ƙara masa kuzari ya bar gidan cike da nishaɗi farin-ciki goma da ashirin .

Sai dai yana fita Sofi ma ta fice kai tsaye inda suka yi za su haɗu sa Samy baby domin ta bata cikon kuɗin da za'a yi harkokin aiki kama daga kuɗin jirgi da Samy Baby ta bata tabbacin ta samu wanda zai mata hanya muddin ta saki kuɗi cikin kwanaki uku ma za ta ɗaga India, da yake kan Sofi ya kunce ilmin zamanin ta tare da wayewar ta sai suka gaza yi mata amfani saboda taƙi basu dama shaiɗan da muƙarraban sa kaɗai ta sau wa ragamar rayuwar ta cikin tsakanin jiya da yau ko ibada ta daina yi kwata-kwata da daman dai ba sosai take tsayar da Sallah ba amma daga jiya zuwa yau ko Sallah ɗaya bata yi ba,  cikar mummunan burin ta kawai take mafarki a bacci ko a farke ita dai burin ta ta ga bayan Yakaka "kaicho Sofi .

Haka ta É—au kuÉ—i zunzurutu naira Miliyan biyar da dubu dari shida ta bawa aminiyar ta Samy Baby bayan naira Miliyan huÉ—u da rabi da su kenan kuÉ—in da ke account É—in ta da tun a jiya tayi transfer su zuwa account na Samira.

Wannan farin kudin kuwa kudin duk wasu gwala-gwalan ta ne tare da wani daya na Momy kori da ta amsa Aro bata mayar mata ba duk ta hada su ta sayar ta dankawa Samira kudin. 

"Samira dan Allah ki tabbatar kome ya tafi yadda ya dace kin ga Doctor tafiya zai yi to so nake kafin ya Dawo kome ya kammala sai dai ya dawo ya tarar da gawa kawai .

"Kar ki damu ƙawata to meye amfanin ƙawancen mu idan ban miki ba ? Ke ce fa Sofiya ? kar ki damu jibi-jibin nan zan bar ƙasar nan ke dai ki kwantar da hankalin ki bana son yadda duk kika bi kika tada hankalin ki kin ga yadda kika koma kuwa? Kamar wata bazaurar Jaɓa .

Ɗauke kai Sofi tayi tana jin zagin walaƙancin da Sofi tayi mata a fakaice .

Cikin wayencewa Sami baby ta miƙa hannu ta ɗau wayar Sofi da take ajiye a tsakanin su ba tare da Sofin ta hana ta ba tayi wasu 'yan taɓe-taɓen ta a wayar ta ajiye mata daga nan Sallama suka yi saboda Sofi ta ce bata so Doctor Hamza ya dawo bata gida .

Haka kowaccen su ta nufi motar ta Sofi ita ce ta fara barin harabar wajen kafin Samy Baby ma ta tada tata motar ta jaa ta cike da nishaÉ—i ta kama hanya '

Kome ya tafi mata dai-dai yadda ta tsara yanzu abunda ya rage mata kawai shine ta tattara duk wasu abubuwan da ta mallaka a garin Abuja ta cika motar ta ta bar garin zuwa garin Damaturu inda ta zaɓa domin gina sabuwar rayuwar ta .

Ita da Sofi kuma daga ta ƙarasa rufta ta a rami kamar yadda ta shirya a jibi kafin ta bar jahar Abuja sun rabu kenan haihatan ah to aina Sofi ta san za ta kama ta ? Sannan ma cikin shirin ta na ƙarshe da zata yi ta san za ta ingiza Sofi ta aikata abunda zai sa ta iya ƙarasa rayuwar ta a gidan Yari da ba zata samu damar neman ta ba ma dan haka ita ta sha kenan ta kuma rufe shafin Sofiya a rayuwar ta "kayya Samira .

Lokacin da Doctor Hamza ya dawo gida ya tarar da Sofi a kitchen tana girki ba ƙaramin daɗi ya ji ba dan haka ya saki jiki da ita ya tsaya a kitchen ɗin suka yi 'yar hira yana ta jaan ta da wasa .

Ƙarfe biyu dai-dai ya musu Sallama ita da Yakaka bayan ya haɗa su ya musu 'yar nasihar kan su zauna lafiya kafin dawowar su sannan ya ɗau kuɗi masu kauri ya danƙawa Sofi ko za su buƙaci wani abu sai suyi amfani da shi duk da ya san a store da kitchen akwai kome na daga kayan abinci

Dauriya Sosai Yakaka ta nuna lokacin da suka masa rakiya bata yi kuka ba sai Sofi ce ma ke zuba masa shagwaɓa wai za tayi  kewar sa shi kuma gaba ɗaya hankalin sa yana kan Yakaka

Ko kaɗan ba son ransa bane yayi nisa da ita a dai-dai wannan lokacin sai dai dan ba yadda zai yi aikin sa aikin ceton rai ne dan haka bashi da zaɓi na lokacin da zai yi tafiya a bakin aiki inda za shi ma ceton rai zai tafi dan haka tilas ne tafiyar sa.

Haka suka yi Sallama cike da alhini ya jaa motar sa da zai tafi da ita zuwa gidan Doctor Suleiman wanda shi ne zai kai shi airport ya koma da motar tasa gidan shi .

Yakaka ita ta bada hanya Sofi ta fara wucewa cikin gidan suna shiga Sofi ta rufe ƙofar ta murɗa ɗan makulli ,  ta ƙasan ido Yakaka ta dube ta Kallon nan da take tsoro shi ta hango a idanun Sofi idan ba gizo idanun ta ke mata ba ma ta ga kamar tana mata wani guntun murmushi.

Zuciyar ta ta doka da ƙarfi sum-sum ta wuce ɗakin ta ta bar Sofi a wajen .

Kitchen ta shiga a gur-guje tayi girki ta zuba a kula ta bar sauran a tukunya sannan ta jidi ruwan gora da juice É—in da take É—an sha ta kai fridge na É—akin ta ta sa ta dawo ta É—au abincin tazo fitowa daga kitchen É—in ta ga Sofi ta tare hanya har yanzu dai wannan kallon ne a idanun ta sannan bata janye murmushin mugunta da take mata ba .

Muƙut Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .

"Mai ciki girki aka yi ne ?
Sofi ta tambaye ta fuskar ta a yanayin da bai yi dai-dai da kalmomin da ta furta ba.

"Eh nayi girki ne Anty Sofi , naki ma yana tukunya daman yanzu zan zuba miki '

"Bari na kai nawa É—aki .

Sai da Sofi ta mula sannan ta É—an matsa da kyar Yakaka ta wuce tana shiga É—aki ta murza É—an makulli tana jin nutsuwa na safko mata daga nan bata sake fita daga É—akin ba har dare komen ta a ciki take yi tsakanin banÉ—aki da tsakar É—akin

Sai wayar ta take yi da Falmata da kuma Lubna da su duka biyun suke cikin watan haihuwar su .

Washegari

Kamar yadda tayi a jiya haka yau ma tayi girkin ta ta kai É—aki ta rufe tsawon yinin bata bari sun haÉ—u da Sofi ba duk kuwa da cewa ta ji motsin ta daga falo .

Sau biyu ta samu damar yin waya da Doctor hamza wanda ya shaida mata cewa a gobe zai dawo idan Allah ya yarda dan haka ta ƙarasa yinin ranar cikin nishaɗi da jin daɗin dawowar sa duk da cewa tsakanin jiyan da yau laulayi sosai ya taso ta gaba gadan-gadan kawai dauriya take yi .

A washegari da safe Bayan tayi wanka taso fita ta haɗa abin karyawa amma jin yadda Sofi ta ƙure muryar tv tana jin kiɗa ya bata tabbacin tana falon ita kuma cikin kwanakin nan kamar Allah ya ƙara mata tsoron Sofi ne wani irin matsanancin tsoron ta take ji ta yadda ko haɗuwa bata so su yi dan haka ta fasa fita tayi zaman ta kawai a ɗakin da daman ba jin cin abincin sosai take ba yau ta tashi da matsanancin ciwon kai ne .

Can kamar hantsi haka tana ɗan taɓa bacci ta ji wayar ta ta ɗau kiɗa , da kyar ta miƙa hannu ta ɗau wayar ganin ƙiran daga masoyin ta ne yasa tayi azamar ɗagawa .

Cike da ƙauna da kulawa suka gaisa kafin Doctor Hamza ya shiga rarrashin ta a ƙarshe ya shaida mata cewa dawowar sa a yau ba zata yiwu ba sai nan da kwanaki biyu watau ranar juma'a

Wannan karon bata ɗaure ba sai da ta sanya masa kuka da kyar ya iya shawo kan ta tayi shiru da alƙawarin zai dunga ƙiran ta akai-akai duk dai idan ya samu dama .

Ba dan sun so ba suka yi sallama saboda  jiran sa da ake yi., duk da cewa ya so yayi magana da Sofi ma domin ya sanar da ita ɗaga dawowar ta shi amma sau uku yana gwada ƙiran ta yana nuna masa cewa tana  amfani/waya da layin nata dan haka ya haƙura ya tura mata saƙo kafin ya kashe wayar sa .

Sofi da take baccin asara ƙiran waya ne ya tada ta lokacin da ta ɗau wayar wasu numbers ta gani haka irin na ƙasar waje idan idanun ta sun gani dai-dai ma numbers ɗin na ƙasar india ne dan haka cike da ɗoki ta ɗaga kiran

Kamar yadda ta zata ne Samira ce take ƙiran ta daga ƙasar india kamar yadda numbers ɗin suka shaida mata kafin ma ta ji daga bakin Samy Baby .

Bata jira sun gaisa ba a ƙagauce ta fara tambayar "Samira kada dai har kin isa india ?

Nan Samy Baby tace mata ai ma tana karnataka har kuma ta gana da Boka yanzu haka ma da take jin hayaniya a cikin jirgin ƙasa take kan hanyar ta na komawa masauƙin ta ta kasa haƙura dai dole ta ƙira ta fara mata albishir Boka yace nan da awa biyu zai kammala aikin ta .

Wani irin ihun jin daÉ—i Sofi tayi tana jin kamar an mata bishara da gidan Aljanna.

za ta sake yin magana É—if Samy Baby ta kashe wayar ta .

Tana wani murmushin mugunta ta buɗe gidan sim ta zare sim card ɗin ta gutsittsira shi da haƙorin ta ta watsar a gefen hanya ajiye wayar tayi a gefe kafin ta ɗaura seatbelt a hankali ta daga glass na motar kafin ta tayar da motar da bala'in gudu ta cilla ta a titi .

Yadda take gudu a titi ba'a ce Mace ce ke jaan motar ba har dai tayi nisa da ainashin garin Abuja tana tuƙi tana bin waƙar da take tashi ta sifukun motar ran ta fes a dai-dai lokacin ji take duniya ta mata daɗin da bata taɓa jin makamancin sa ba ta samu duniya abunda ya rage kawai sai ta miƙe ƙafa domin cin ta .

Kafin kamar walƙiya ta ga ɓullowar wasu motoci biyu da gudu da suka yanko daga cikin daji suka yi banga-banga akan titi da yasa ta cikin matsanancin tashin hankalin da ya maye gurbin nishaɗin da take ji ta taka birki ƙuuuuuuu da ba domin Allah ya kiyaye ba da babu abunda zai hana motar tayi ƙundumbala da ita .

Samy Baby bata tabbatar yau ita ce rana mafi muni a tarihi rayuwar ta ba sai lokacin da ta fahimci hannun ko su waye ta faÉ—a'

Masu yin garkuwa da mutane ne kidnappers  da take jin labarin su wai-wai sune yau take ganin su a gaban ta kamar a mafarki .

Kwakwalwar ta taƙi samun kwanciyar hankalin yin tunani ɗaya kamar yadda idanun ta suka ƙafe ƙaf daga samun damar zubar hawaye duk wasu kalmomi kuma suka ɓace suka shafe daga bakin ta har zuwa lokacin da suka ɗora mata bakin bindiga suka tasa ƙeyarta bayan sun kwashe kome da yake cikin motar suka nausa da ita cikin daji .

***

Sofi ji tayi farin-cikin da take ciki ya mata yawan da bata jin za ta iya jurar sa bata ɗan wataya ba dan haka ta ɗau wayar ta da sai lokacin ta lura da saƙon Doctor Hamza .

Wani tsallen jin daɗi ta sake yi jin cewa ba zai dawo ba ma a yau sai nan da wasu ƙarin kwanaki wanda hakan duk alamun nasara ne a gurin ta domin kuwa dama ce ta sake samuwa a gare ta .

KiÉ—a ta kunna a wayar kafin ta buÉ—e wata 'yar karamar loka da take jikin gadon ta ta fara zaro kwalabe da sauran kayan mayen ta '

Sai da ta tara su jibgi a gaban ta sannan ta shiga É—aga su É—aya bayan É—aya tana tuttulawa a cikin ta tayi ha'in tana jin ta tamkar tafi kowa farin-ciki a duniya tana tangaÉ—i ta shiga juya jikin ta tana rawa .

Daga can ɗakin Yakaka da ta ji shiru babu alamun motsin sofi a falon sai ta lallaɓa ta fito kai tsaye ta tafi kitchen saboda yunwa da ta fara sasuƙar ta har jiri-jiri take ji .

Cikin awa guda ta gama irin girkin da take jin sha'awar ci ta kwashe ta kai ɗakin ta ba tare da ta rufe ƙofar ba sai kawai ta faɗa banɗaki tayi wanka ta ɗauro alwala saboda azahar ta gabato.

Tun tana wanka take jin ana ta ƙiran wayar ta har sau uku dai-dai da fitowar ta wayar ta sake ɗaukar kiɗa da sauri ta ƙarasa ta ɗaga ta lokacin da ta ga sunan mai ƙiran Falmata ce .

"Hello Falmata na kina lafiya ko ? Ko haihuwar ce ? Ko kin haihun ne ?

Ta jero mata tambayoyin ba tare da ta ajiye numfashi ba saboda koyaushe cikin bin haihuwar Falmatan take a rai musamman da yake ita ta taɓa haihuwa ta ɗana ta ji yadda haihuwar ke da zafi duk sai take jin tausayin ƙanwar ta kullum cikin addu'ar sauƙa lafiya take mata musamman da cikin na Falmata ya kusan shige kwanakin haihuwar sa da hakan sabon abu ne a haihuwar fari .

"Hello Falmata kina jina kuwa ? Ta sake furta hakan cikin damuwa

Dariyar da Falmata ta cika mata kunne da ita yasa ita ma ta murmusa tana sauƙe ajiyar zuciya ta ce "meye abun dariyar kina jina ina miki magana wallahi duk kin ɗaga min hankali ganin yadda kike ta ƙirana ina wanka na zo kuma na ɗaga kin yi shiru.

"Yakaka bani nake ta ƙiran ki ba wallahi ni yanzu nan na ƙira ina ƙira kuma kika ɗauka .

Ɗan jimm Yakaka tayi "to waye yake ƙirana ? Ta tambayi kan ta , sai bata wani damu ba kawai ta zauna a bakin gado suka shiga hirar su ita da Falmata .

Sun ɗau tsawon lokaci suna hirar da take sanya su duka biyun a farin-ciki tare da sake ƙaunar juna '

Kafin kamar daga sama Yakaka ta ji an damƙi kafaɗar ta da yasa ta matuƙar tsorata ta saki wayar ta ta faɗi .

Jikin ta yana rawa ta miƙe tsaye tana kallon Sofi wacce take tsaye kiƙam hannun ta ɗaya a ɓoye a bayan ta.

An-anty Sofi in-ina wuni.

Wata irin shashashar dariya Sofi ta saki da hatta Falmata da bata kai ga katse wayar ba ta ji ta .

Zuciyar ta ta fara sauya bugu daga lokacin da ta fara saurarar duk wasu zantukan da Sofi take yi cikin maye murya sama-sama .

"Kin yi zaton na kyale ki ko ? A tunanin kin shaa da ni kenan ? Ƙaramar kwakwalwar ki ta baki tunanin kin yi nasara ?  Ni Safiya na bari ki rayu da Mijina ki haihu ?

"Wacce irin cusashiyar ƙwakwalwa ce da ke ? Ta kifi ? Kin taɓa ganin an yi haka ? Ba zai yiwu ba , ba zai faru ba ba zai taɓa faruwa ba ki zo ki gina rayuwar ki a kan tawa Hamza nawa ne ni Kadai.

"Dole na rusa rayuwar ki a duk lokacin da na so , dole ki mutu Yakaka tunda kin ƙi fita a rayuwa ta to zaki Mutu zaku mutu tare da ke da abunda ke maƙale a cikin ki .

Wuƙar da take ɓoye a ɗaya hannun ta ita ta zaro wata kakkaifar wuƙa ce sabuwa fil da alama ita ce mafi girma a cikin jerun set ɗin wuƙaƙen ta .

Lokacin da Yakaka ta ɗora idanun ta akan wuƙar ta kuma ji abunda Sofi take cewa jikin ta gaba ɗaya sai ya saki kamar an zare mata lakka wani yanayin da ta kasa tantancewa da shi ya shiga bin gaɓɓan jikin ta idanun ta kuma suka kafe akan wuƙar a hankali ta ji kunnuwan ta na toshewa .

"Amma kafin na kashe ki zan so na miki ƙarin bayani kan dalilin mutuwar ki zan faɗa miki irin faɗi tashin da na dunga yi dan na auri Mijina da irin son da nake masa , da nasan ke kan ki za ki iya min uzuri akan kashe ki da zan yi .

"Tun ranar farko da na gan shi na kamu da son sa , haka na dunga faÉ—i tashi alhalin ina korar masoyana har nayi nasarar da aka min tsafin da yasa ya fara kulani a matsayin budurwar sa .

"Kar kiyi zaton ke ce rai ta farko da na kashe a kan Hamza ke ce ta uku na farkon jariri ne lokacin da aka bani tabbacin idan har ba'a yi mummunan aikin da aka raba tsakanin jaririya da uwar ta ba to babu shakka uwar jaririyar ita ce matar da Hamza zai aura ba ni ba idan kuwa har aka raba tsakanin su za'a kaÉ—a uwar wani waje mai nisan gaske ni kuma cikin shekarar Hamza zai aureni hakan ne kuma ya kasance .

"Na sha wahala kafin na samu wani ɓangare na daga zuciyar Hamza wanda a ƙarshe sai da aka min aikin da aka kashe wani Mijin da zuciyar sa ta mutu a ƙauna matar sa a can ƙasar india bayan duk na sha wannan wahalar ina zaman daɗi da Mijina za ki ratso rayuwar mu ?

"Ya kike tunanin ba za ki zama ta uku ba a cikin jerin Mutanen da za su mutu ba ? Dole ki Mutu dole ki zama mutum ta farko da zan kashe da hannu na akan Hamza .

Wasu kauraran hawaye ne suka zubo mata kafin ta cigaba da cewa "kin ga laifi na ne ? Ki duba yadda na lalata jikina saboda kawai na burge Hamza na lalata Mahaifata saboda kawai muyi rayuwar hutu da Hamza bana son ko 'ya'yan cikina su ratsa tsakanin mu .

Juyowa tayi ta wani irin fisgo Yakaka da daman tuni alhinin Mutuwa ya safko mata bata da wani sauran ƙarfi .

Ta gwara kan ta da bango kafin tayi majaujawa da ita a tsakiyar ɗakin ta yasar da ita da wani azabar ciwo ya sarƙe Yakaka yasa ta saki ihun da ya daki dodon kunne Falmata wacce duk take jin abunda Sofi ke cewa..

Ita ma ihun ta saka da ya amsa sashin ta gaba ɗaya da ƙarfi ta miƙe tsaye lokacin da take sakin wayar hannun ta ta faɗi ƙasa tunanin ta yana tabbatar mata da cewa Sofi ta kashe mata Yakaka a yau .

Da gudu Hajja da wasu bayun ta biyu suka shigo waɗan da ihun ta ya je har kunnen su Hajja tana shigowa ta gan ta a durƙushe tana murƙususun ciwo tare da ihun ƙiran sunan Allah da na Yakaka cewa take "Yakaka na ta mutu Sofi ta kashe Yakaka dan Allah ku kaini Nigeria .

Hajja wacce kallo ɗaya ta yiwa Falmata ta ga alamun haihuwa a tare da ita ita kuma cewa take "To Alhamdulillah abun yau yazo kenan fatan mu Allah ya raba lafiya sannu Uwarɗakina sannu kin ji daure kowacce Mace da haka ta zama uwa daina iface-ifacen nan ikon Allah ke kuma taki naƙudar da ƙiran sunan 'yar uwar ki ta zo miki o wannan ƙauna ta ku ta girmama .

Kafin mintoci goma sha biyar labari ya je wa Hajiya Umma kan cewa Falmata na naƙuda nan take ita da kan ta ta taso zuwa sashin .

Ƙarƙashin Umarnin Sarki aka fita da ita zuwa asibiti da kawo lokacin Falmata ta daina surutai saboda ganin idon Hajiya Umma sai dai ruwan hawaye da suka ƙi daina zuba mata a zahiri ciwon da take ji a cikin ranta na rashin 'yar uwar ta yafi ciwon da take ji a sassan jikin ta na buɗuwar ƙasusuwan ta sakamakon abunda yake cikin ta da ya shiryawa fitowa duniya a yau .

***

Ciwon da ya turnuƙe Yakaka daga ƙasa ya riƙe mata mara shi yasa ta kasa yin wani yunƙuri na kwatar kanta har lokacin da Sofi ta ƙaraso inda ta jefar da ita tana mata wannan kallon da salon murmushin da zuwa yanzu ta san manufar ta ta kuma gane dalilin da yasa take jin matsanancin tsoron Sofi ashe dan ta ita ce ajalin ta

Ɗaga wukar Sofi tayi da iyakar ƙarfin ta ganin  haka ya sa Yakaka kare fuskar ta da tafukan ta biyu tana maimaita kalmar shahada a cikin ran ta kamar yadda take jin kome da ya shafi duniya yana shafewa daga ƙwaƙwalwar ta lahira na maye gurbin sa .

duhun da yake da alaƙa da tsanantar gudun jinin jikin ta da aikin da ya wuce misali da zuciyar ta ke yi ya safko yana mamaye ganin ta ya koma dusu-dusu take iya hango abunda yake faruwa ta tsakanin yatsun hannunta

Ba zata iya tantance mafarki ne ko ido biyu ba lokacin da ta ga kamar an É—aga Sofi anyi cilli da ita gefe .

Doctor Hamza take Iya gani ya gifta ya É—ago Sofi da ta faÉ—i a gefe.

Mari ya shiga ba ta a fuskar ta dama da hagu kafin ya ji cewa marin bai gamsar da shi ba ya shiga ƙoƙarin zare belt ɗin dake kunkumin sa da muryar da ba tayi kama da ta shi ba yake cewa "Sofiya ashe haka kike ? Haka kika min Sofiya ? Haka za ki min ?  Kisa kike ?  daman Sofiya kisa kike yi ? .

Ta ko'ina yake zuba mata belt É—in a jikin ta kafin ya fisge ta su ka fice daga É—akin ya tunkuÉ—a ta ta bugu da bango jikin ta gaba É—aya ya farfashe yayi shatin belt .

Ragwab ya zauna akan kujera kamar kuma ya zauna akan ƙaya sai ya sake miƙewa gaban ta ya dawo ya tsaya yana kama goshin sa da hannun sa ɗaya muryar sa na karkarwa yace "Sofiya duk abunda na ji kina faɗa da bakin ki gaskiya ne ? Gaskiya ne ? Kin yi kisan kai kina kuma yunƙurin sake yin wani a cikin gidana duk kuma a dalilina ?

Fisgota ya sake yi a inda take yashe tana wani wuri-wuri da ido ko ɗigon ƙwalla babu a idanun ta illa wani irin ƙuna da ran ta ke yi ganin kome take kamar a mafarki .

Fisge jikin ta tayi muryar ta a hargitse tana sarƙewa bata cikin hayyacin ta tace " Duk abunda ka ji nace na aikata a ta dalilin ka nayi kuma a shirye nake da nayi abunda yafi haka Wallahi ni Sofiya a shirye nake da na kashe kowa akan ka , idan kuma aka nemi raba ni da kai ta ƙarfi zamu Mutu tare ni da kai zan kashe ka na kashe kaina .....'

Wani marin ya daÉ—a bata kafin ya fisgota Yana tunkuÉ—a ta hanyar barin gidan yake cewa ,

"Na sake ki Sofiya Ni Hamza na sake ki saki Uku ki fita daga gidana kar ki sake nuna min fuskar ki har abada na tsane ki .

Chak! Sofi ta tsaya ta tirje taƙi tafiya lokacin da kalmomin sa ke mata amsa kuwwa a kunnuwan ta suna zama kamar ɗigon ruwan narkakkiyar dalma a kogon kunnen ta .

Zata silale ƙasa ya ɗago ta da ƙarfi ya ƙarasa tunkuɗa ta waje ya rufo ƙofa a fuskar ta da har sai da ƙofar ta bugi bakin ta ya fashe .

Wani ihu tayi ta shiga buga ƙofar kamar zata ɓalla da yasa makofta fara leƙowa wasu ma daga sama suke buɗe windows suna leƙen ta .

Lokacin da ta fahimci ta zama mahaukaciya sai ta tashi da gudu ta nufi bakin titi ta tare taxi .

Tana zama ta faɗi inda zai kai ta kafin ta cigaba da Sambatu cewa take " wallahi ban saku ba Hamza ƙarya kake ni da kai mutu ka raba ahaf ai daga aikin karnataka ya fara ci nan da gobe ma zan dawo gidana Kashe Yakaka kuma ban fasa ba wallahi sai na kashe ta wallahi sai ta mutu..

Ƙiiii mai taxi ya ci birki abinda kawai ya iya cewa shine "Hajiya Dan Allah sauƙa na fasa yin Area da kika faɗa .

Haka ta sauƙa bayan ta cusa masa zagin rashin tarbiya da turanci shi kuwa ya jaa motar sa da ƙarfi ya buɗa mata ƙura '

Haka ta taka da ƙafa tana tafe tana surutai a dai-dai lokacin ba wanda zai gan ta ba tare da ya mata ganin mashahuriyar Mahaukaciya ba .

***

Lokacin da Doctor Hamza ya koma É—aki inda ya bar Yakaka anan ya tarar da ita yana share guntun hawayen idanun sa ya É—ago ta ya rungume ta tsam a jikin sa yana jin yadda bugun zuciyar ta ke sassarfa da yasan hakan hatsari ne ga lafiyar abinda ke cikin ta .

Nan take ya fara ƙoƙarin bata agajin gaugawa sai dai bisa tilas ya shirya ta suka nufi asibiti saboda fahimta da yayi cewa dole abinda ke cikin ta da bai yi ƙwari ba sai ya fita saboda bakin mahaifar ya riga ya buɗe jini ya fara sauƙa.

A can babban asibiti na ƙasa da yake aiki suka mata abinda duk ya dace kafin a mata allurar bacci na ɗan wani gajeran lokaci da ana sa ran idan ta farka firgicin da take ciki ya bar ta .

Zama yayi akan kujera yana riƙe da hannun ta ya zubawa fuskar ta ido a can cikin ransa kuwa lamarin Sofi ke daɗa sanya shi a ruɗani a bayan kowacce daƙiƙa yadda yake jin kome kamar a mafarki

Wai Sofi ta aikata duk abubuwan da ta lissafa da bakin ta.? Ga kuma ƙwaƙƙwarar shaida nan tana yunƙurin kashe masa Mata da ba domin Allah ya kawo shi ba da babu shakka Wafaa bata raye yanzu a duniya .

Sake runtse hannun ta yayi a cikin nasa yana jin ciwon rashin gudan jinin sa da yayi wanda har ƙaunar sa ta fara yaɗo a cikin ransa "Safiya Annoba ce da ya dace ɗan Adam ya nemi tsari da mata ire-iren ta .

Maradi

Duk yadda likitoci suka yi kokari tare da son ganin Falmata ta haihu da kanta abu yaci tura gaba ɗaya ta gaza yin yunƙuri yadda ya kamata saboda firgicin da ta kasance a ciki ya tafi da duk wani ƙarfi nata .

Mafi munin abun shine jinin ta da yake daÉ—a hauhawa a bayan kowacce minti talatin .

Ba hajiya Umma kadai ba har Maimartaba ma ya shiga zullumi da yasa yake ƙiran waya bayan duk ƙaramin lokaci .

Dole tasa ya sanar da Biyamuradi Youssouf da bai kai ga sanin Matar sa na asibiti ba saboda a da so suka yi sai ta haihu kawai sai a sanar masa amma a yanzu da lamari ya yi gardama dole aka sanar masa sannan kuma aka shiga addu'a fiye da wacce ake a baya sannan aka ɗaura tukwane domin yin abinci a bayar sadaƙha duk dan Allah ya sauƙi Gimbiya Falmata Matar Yarima Youssouf lafiya .

Ganin lokaci zai tafi tare da shiga hatsarin rasa Baby ko uwar yasa likitoci suka nemi da wani makusanci ya sa hannu a shiga da Falmata É—akin fiÉ—a .

Maimartaba sarki Abdoul-azizou shine da kansa ya zo har asibitin ya sa hannu aka shiga da Falmata É—akin fiÉ—a.

Anyi aiki cikin nasara an fitar da ƙatuwar jaririyar da ba'a ce ɗiyar fari bace saboda girma zabgegiya da ita jajir mai tarin suma akai kamar an kifa mata hular gashi dan har sai da likitan da ya ciro ta ya sanya almakashi ya yanke mata gashin ta gaban kan ta sannan ta iya buɗe ido .

Babu wanda yasan da tahowar Youssoufa kawai sai ganin sa aka yi a asibitin lokacin har an gama aikin an tura Falmata recovery room.

Duk suna tsaye suna jiran a fito da ita zuwa É—akin da zasu Iya shiga su gan ta É—aya daga cikin manyan malaman jinyan ya fito ya nemi son yayi magana da Youssoufa .

Nan yake shaida masa Falmata ta farka amma kuma sai surutai take tana kuka tana ƙiran sunan wata .

Ana buƙatar idan zai yiwu waccan ɗin ta zo ko kuma a ƙira ta a waya a haɗa ta da Falmata suyi magana dan kar kuma wata matsalar ta ɓullo .

Tare suka koma cikin É—akin da take abunda ya bashi Mamaki bai wuce nunawa da Falmata tayi ita ba shi take son gani ba Yakaka yayar ta take nema .

Shi ba shi da layin wayar Yakaka amma yana da ta Baba Prof , Amnee da Mamar su da yake ƙira akai-akai yana gaishe su da baya zaton ma kawo yanzu sun san Falmatan ta haihu 

Dan haka kawai sai ya ƙira Amne Bayan sun gaisa a gurguje ya sanar da su halin da ake ciki na haihuwar Falmata bayan an mata fiɗa da kuma halin da take ciki a yanzu na neman Yakaka .

Yanayi biyu ne ya chakuÉ—uwa Amnee na farko farin-cikin haihuwar Falmata tare kuma da fargabar halin da aka ce Falmatan na ciki bayan fiÉ—a da aka mata aka cire mata 'yar .

Nan take ta tura masa number Yakaka da bai jinkirta ba ya fara ƙiran layin sai dai sau biyar yana ƙira ba'a ɗauka hankalin sa duk ya daɗa tashi ganin yadda har lokacin Falmata bata bar kuka ba .

Dan haka ya sake ƙiran Amne lokacin da ta ɗauka ma suna tsakiya da tattauna da khaalty Rahima kan haihuwar da kuma halin da aka ce tana ciki hankalin su duk bai wani kwanta ba. dan haka sai ta haɗa su da khaalty Rahima tayi masa barka ta kuma sake tambayar jikin Falmatan ?

Nan yace har yanzu tana kuka kuma Yakaka take nema sannan ita kuma bata É—aukar wayar .

Jin yadda hankalin sa ke tashe sannan ita ma tana iya jiyo kukan Falmatan da take surutai sai ta ce to bari ta tura masa layin Mijin Yakaka ya ƙira shi wataƙila suna tare amma bari a fara sanar da shi

Lokacin da ta ƙira Doctor Hamza dawowar su kenan daga Asibitin da yaga ƙiran Amnee ya ɗauka har labarin abunda ya faru ne ya je musu dan haka yayi hanzarin ɗaukar wayar sai dai bayan sun gama gaisawa sai ya ji Amnee ta ɗaura masa da wani batu kan Falmata da ta haihu da kuma halin da take ciki na kuka da neman Yakaka.'

Yana jin haka ya fahimci cewa Falmata tana da sani kan abunda ya faru da hakan ne yasa ta firgicin da take ciki a halin yanzu .

Amnee ta cigaba da faɗa masa cewa " idan har yana tare da Yakaka to Mijin Falmatan zai ƙira yanzu sai ya haɗa su suyi magana .

"To
Ya amsa kafin yayi wani yunƙuri Amnee ta katse wayar ta.'

Bai rufa mintoci biyu ba sai ga ƙira daga ƙasar Niger.

Ɗan jimm yayi kafin ya ɗaga ƙiran saboda sanin da yayi ƙiran daga Biyamuradi Youssouf ne Baban Mama .

Lokacin da ya É—aga ga mamakin sa ba kamar yadda yayi zato ba sai ya ji muryar Youssouf É—in faran-faran kamar ya san shi haka ya gaisa da shi dan haka shi ma sai ya daure zuciyar sa suka gaisa har ya masa barka .

Daga nan sai Youssouf ya nemi da ya haÉ—a shi da Yakaka , Falmata ce ke son magana da ita.

Cikin nutsuwa Doctor Hamza yace "ka kai mata wayar idan ka bata sai na haɗa su  .

"D'accord .

Youssouf ya amsa yana mai takawa ya matsa gaban gadon da Falmata ke kwance a hankali ya kara mata wayar a kunne cikin taushin murya yana shafa kan ta yace "Mon Bébé ga Yayar ki nan kuyi magana kiji sai hankalin ki ya kwanta ta ki daina kuka .

"Hello Yakaka na tace tana shiƙar kuka..

Jin muryar ta yasa Doctor Hamza karawa Yakaka wayar a kunnen ta wacce duk abunda yake faÉ—a tana jin sa amma bata san da wa yake maganar ba .

Jin sautin Falmata tana kuka yasa ita ma kukan ya zo mata sai suka dunga yi tare cikin kukan Falmata ke tambayar ta "Yakaka baki mutu ba ko ? Sofi bata kashe ki ba ? Ashe Sofi haka take muguwa azzaluma  ? Yakaka ki koma gidan Baa kawai idan Sofi ba zata bari ki rayu a gidan ba kin ji Yakaka Dan Allah ki koma Maiduguri kar watarana Sofi ta kashe min ke Yakaka idan ta kashe ki ni kuma ya zan yi.?

Doctor Hamza shi ya fara ƙoƙarin hana kukan Yakaka muryar sa a ƙasa yace " Wafaa ki daina mata kuka ta haihu ana so jinin ta ne ya dai-daita a halin da take ciki kwantar da hankali take buƙata ki rarrashe ta .

Kallon sa take yi kafin a hankali ta buÉ—i baki tace "Falmata kin haihu da gaske.? Me kika haifa muna ?

Falmata tana goge hawayen ta da bayan hannu Youssouf na taya ta tace "eh Na haihu Yakaka amma ni ban san ma me na haifa ba ban gani ba ma Ya..

Da sauri Yakaka ta katse ta tana cewa "ina abunda kika haifa ? Ki sa a kawo miki ki ɗauki abinki ki riƙe a hannun ki ki rungume ki shayar da shi arziƙi ne babba yau Allah ya miki Falmata kin zama uwa a yau Dan Allah kar ki bari abunda ki ka haifa yayi kuka a domin rashin ki a kusa da shi sa a kawo shi Alhamdulillah Alhamdulillah .

Wata irin nutsuwa kalaman Yakaka suka zo mata da shi cikin sanyi murya ta ce "To Yakaka zan sa a bani abunda na haifa yanzu amma Yakaka kina lafiya ko ? Sofi bata yi miki ciwo ba .

"Lafiya ta ƙalau Falmata , ki sa a kawo Baby nan ki sa min naji sautin numfashin abunda kika haifa Falmata .

"Ina Baby na ?
Falmata ta cewa Youssouf haka , É—an murmushi yayi yana jin daÉ—in yadda ta fara dawowa hankalin ta.

"Riƙe telephoné na amsa miki ɗiyar mu ki ganta Fatima '

Fita yayi sai ga shi ya dawo rungume da jaririyar a hannun sa da shi ma sai yanzu ya ɗauke ta a shirye take tsaf ta sha kayan  sanyi irin na alfarma tayi kyau matuƙar gaya .

ÆŠora mata ita yayi a jikin ta bayan ya É—an É—ago mata gadon sai ya zauna tana jingina da jikin sa daga shi har ita tsurawa jaririyar ido su kayi suna ganin tsananin kamannin ta da Mama kamar lokacin da aka haife ta , marabar su kawai wannan tana da girma kuma tafi Mama gashi bayan hakan za'a ce Mama ce kawai Allah ya dawo musu da ita .

A hankali ta É—ago ta sumbanci kumatun ta dama da hagu da yasa ta motsawa a hankali tana É—an yamutsa fuska irin na jarirai.

"Yakaka na É—auke ta ,Yarinya ce mace Mai tsananin kama da Mama , Allah ya dawo mana da Mama Yakaka.

Daga can murmushi mai sauti Yakaka tayi tana jin ƙaunar 'yar da bata kai ga ɗora idanu akan ta ba na samun wajen zama na musamman a cikin ran ta a lokacin ji take kamar tayi tsuntsu ta je ta gan ta ta ɗauke ta ta riƙe a hannun ta ta rungume ta a ƙirjin ta ta gwada mata ƙauna a matsayin ta na uwa a gare ta ba wai Yayar uwa ba kawai ɗiyar Falmata ɗiyar ta ce halak malaƙ .

"Allah ya raya ta Falmata , Allah ya mata Albarka , Yaa Allah yasa ta amfanar da Al'ummar musulmai ajiye wayar ki ɗaga ta ki shayar da ita anjima zan sake ƙiran ki .

"Amin Yakaka .

Daga haka Doctor Hamza ya zare wayar daga kunnen ta ya kashe kafin ya jaa ta cikin jikin sa ya rungume ta tsam suna musayar jin ciwon rashin nasu gudan jinin da suka yi .

Sumbatar goshin ta da Youssouf yayi bai sa ta janye idanun ta daga kallon fuskar 'yar ta ba da take jin wani abun da ya zarce a ƙira shi da So sannan kuma ya wuce ƙauna tasiri yana bin duk wani sarari na ran ta yana dasa wani al'amari mai girma ji take kamar ta tsaga ƙirjin ta ta sa ta .

Wai yau ita Falmata ce take riƙe da 'yar ta ta cikin ta babu shakka Allah shine mafi girman Abun Godiya "Alhamdulillahi Yaa Allah .

Ta furta hakan a sarari tana jin wata ƙwallar farin-ciki na cika mata gurbin ido .

A hankali Youssoufa ya kai hannu yana ɗauke 'yar daga jikin ta bata yi wani yunƙuri ba illa bin su da tayi da ido cikin ran ta bata mamakin yadda ya iya ɗaukar jariri saboda tun akan Mama ta san ya ƙware .

Addu'o'i ya shiga yiwa 'yar sa tsawon mintoci fiye da talatin dan tun Falmata tana kallon su har ta É—an fara gyangyaÉ—i .

Hannun sa da ya shafa mata kumatu shi yasa ta buɗe ido da kyakkyawar fuskar sa tayi arba yana mata murmushi kafin sautin  sa ya sauƙa a kunnen ta "Mon Bébé kina ji na ?

A hankali ta gyaÉ—a masa kai idanun ta cike da baccin gajiya suke lumshewa sai dai kalmar da ya faÉ—a ya sa ta wara idanun ta da sauri ta dube shi tana son sake jin me ya ce ?

"Wanne Suna kin ka zaɓarwa ɗiyar mu na bar miki zaɓi dan saboda kawai na gwada miki kaɗan dagga farin-cikin da nake ciki.

"Da gaske kake ?
Ta tambaye shi tana narkar da idanun ta cikin nasa .

"Da gaskiya Fatima na bar miki zaɓin sunan ɗiyar mu mai darajja '

" a sa mata Yakaka .

Sautin da ya taso daga ƙasan ran ta ya subto akan laɓɓan ta .

Shiru yayi yana kallon ta kafin yayi magana ta katse shi ta hanyar cigaba da cewa "indai dai har ka bani zaɓi to a sa mata sunan Yakaka Yayata .

"Babu shakka ta cancanta domin kuwa ita ce Mafarin silar haɗuwar sa da Fatima-zahra ba domin ita ba da bai samu Fatima ba bare har ta haifa masa 'yar da yake riƙe da ita yanzu a hannun sa a ƙarshe kuma ita ɗin uwa ce ga 'ya mafi soyuwa a gare shi da har abada baya zaton za'a samu mafiyin ta wajen matsayi a cikin 'ya'ya .....

Tunanin sa bai yanke ba ya juyo yana fuskantar Falmata riƙe da Babyn a hannu yace "Meye Sunan ta na ainashi..?

Cike da zumuÉ—i Falmata tace "sunan ta Amina.

Bai ce ƙala ba sai ya sake mayar da kai ga yiwa 'yar sa addu'a kafin bayan ɗan gajeren lokaci ya ɗago kan sa yana mai ɗora mata 'yar a jikin ta yace

" Sunan 'yar mu Amina riƙe ta da kyau 'ya ce a gurin ki sannan kuma 'yar uwa.

Da hannuwanta biyu ta rungume ta tana jin yanayin da yafi na ɗazu yana danne ta ta kasa tsayar da hawayen farin-cikin da yake sauƙa fuskar ta kamar yadda ta kasa ɗauke ido daga fuskar Amina .

Haka ma Biyamuradi Youssouf da yake tsaye akan ƙafafun sa hannuwansa duk biyu a zube cikin aljihun sa yana murmushin da yake bayyana haƙoran sa ya kasa janye ganin sa daga kan su kamar yadda yake jin ƙaunar su biyun tana fisgar sa tamkar wanda guguwa ta riska a tsakiyar rairayin hamada .

***

Daga nan É—akin da Falmata zata cigaba da zama kafin a sallame ta aka kai ta bayan nan Hajiya Umma da har yanzu bata tafi gida ba ta shiga inda suke ta mata sannu sannan ta sake mata addu'a ita da Amina kafin ta bar asibitin .

Sai kuma ta fara amsar waya daga Iyaye da dangin ta na Nigeria har dai zuwa lokacin da likitoci suka buƙaci da a bar ta ta samu hutu mai yawa kar a takura ta.

***

Daga lokacin da Doctor Hamza ya ga har dare yayi bai ji wani labari ba daga iyayen sa sai ya fahimci Sofi ta rufe zancen duk abunda ya faru bata faÉ—a ba .

Dan haka shi sai ya yanke shawarar sanar da iyayen su da kansa dan haka a daren ranar bayan sallar isha'i ya hada conference call da Baba Prof da Amne da Khaalty Rahima da Momy Kori da shi kan sa Baban Sofi.

Bayan duk ya gaishe su sai ya nemi da su bashi dama zai musu bayani.

Nan ya shiga basu labarin duk yadda kome ya wakana a tsakanin sa da Sofi tun daga farko har ƙarshe .

Kafin ya gama Sallallami da kukan Momy kori tare da Amne ya cika wayar .

Sai da kyar Baba Prof ya sa suka yi shiru domin shi da kansa Baban Sofi ya gaza cewa kome kawai kamar ruwa ya cinye shi saboda tsabar shiga razana da muzanta shi da Sofi tayi.

Ɗan taƙaitatcen Bayani Baa yayi akan lamarin da ɗari-cikin-ɗari ya goyi bayan hukuncin da Hamza ya ɗauka ya ɗora da cewa "tunda har dai abu ya zama da neman aikata kisan kai to babu shakka ba amfanin zaman rabuwar ita tafi dacewa.

Matsanancin kuka Momy Kori ta sa cikin rishin kuka take sanar da su cewa ita har kawo yanzu ma da ake wannan maganar bata ga Sofi da idanun ta ba Sofiya bata zo gida ba to ina ta tafi ?

"Ta tafi ko'ina ma Kori , ina mai tabbatar miki da cewa Safiya ba za ta zo ta zauna min a gida ba domin nima ba zan zauna da mashayiya kuma makashiya ba tunda irin rayuwar da ta zaɓarwa kan ta kenan to tafi duk inda za ta tafi tayi rayuwar ta amma ni dai ban amince ta zo gidana Alhaji ka shaida ni na cire Safiya daga cikin 'ya'yana' ku kuma ina mai baku haƙuri kan abunda ya faru ita yarinyar ma dan Allah a bata haƙuri ita da iyayen ta .

Daga haka Baban Sofi ya yanke ƙiran daga ɓangaren sa .

Duk son kai irin na Momy Kori yau sai ta gaza kare 'yar ta haka tana ji tana gani saki Uku ya tabbata tsakanin Sofi da Hamza sannan kuma dole ta bada haƙuri ga su Amnee da shi kansa Doctor Hamzan da ya rasa gudan jinin sa sannan ta ajiye wayar .

Daga nan suka cigaba da jimantawa tsakanin sa da iyayen sa inda Amnee ta nuna son Yakaka ta zo gida a kula da ita amma tun ma kafin ta gama magana Baba Prof ya nuna rashin amincewar sa hujja da cewa ai shi Hamzan likita ne dan haka zai fi kowa lura da ita dole Amnee ta haƙura ita kuwa Khaalty Rahima daman bata cewa kome sai addu'a kawai tayi ta danne duk wata damuwar ta saboda kara .

Daga nan aka yanke shawarar cewa jibi Amnee da Zainab za su tafi Abujan daga nan su haÉ—u da hafsa idan sun duba Yakaka da jiki daga nan sai su dawo Kano su wuce Niger gurin Falmata .

Su Hafsa zasu dawo bayan suna Amnee kuma za ta É—an yi ko da sati biyu ne tana kula da Falmatan .

Kafin kwanaki biyu zance ya gama baza dangi kan abunda Sofi ta aikata na yunƙurin kashe kishiyar ta kuma ta gudu ba'a san inda take ba.

Amnee sun je Abuja tare da direban su a babbar motar da Amnee ta cika kusan rabin ta da kaya .

Sun kwana a gidan Doctor Hamza ta sake rarrashin takwarar ta Yakaka sannan ta bata kayan gyara da tarin wasu turarurruka sannan ta sanar da ita sakon Prof da yace cikin satin nan za'a zo a shirya mata kayan ta a gidan .

daga nan kuma sai suka wuce Maradin Niger da tarin kayan ƙamshi da gyaran jiki tare da kayan jarirai masu kyau da tsada  da Amnee tayi tanadin su musamman domin Falmata da zata haihu kayan gyaran tafiyayyu ne daga Chad .

Can a Maradi suka ga tarba irin ta saraki sai nan-nan ake da su ana sauƙe musu kabbakin arziki.

Daga Zainab har Hafsa sai da suka yi santin kyaun sashin Falmata da irin gatan da ake mata babu abunda yafi burge su irin tarin hadiman da take da su da ko yaya ta motsa sai sun mata sannu girma irin ta sarauta sai gidan sarauta .

Lokacin da Yakaka ta samu labarin cewa jaririya Sunan ta ta ci har sai da tayi kuka dan farin-ciki .

Doctor Hamza ma ya ji daɗi ya kuma musu fatan Allah ya ƙara musu zumunci a ƙarshe yayi alƙawarin daga ya ɗau hutun sa nan da wasu watanni cikin shekara mai zuwa zai kai Yakaka har Niger ta gano takwarar ta .

Ranar suna kuwa Al'umma da suka taru ba'a ce Falmata bata da dangi a Niger ba.

A gurin taron suna dangin suka dunga tsurkun tururuwar zuwa duba Hajiya Mama wacce jinya ta sarƙe ta sakamakon wasu munanan ƙuraje da suke feso mata duk a ƙafafun ta bayan hawan jini da ciwon zuciya da suka mata rubdugu bata ko iya tafiya gaba ɗaya rayuwa ta mata juyin waina a tanda .

Kowa ya fito daga sashin sai yayi gulmar sakayya ce take gani tun daga nan duniya .

Wacce irin ta Maimounatou ɗiyar sarkin Agades ma ta samu sakamakon mutuwa da Mahaifin ta yayi a tun jinyar da ya afkama sanadin mummunan abun kunyan da ta aikata kan yunƙurin kashe Mijinta a halin yanzu kuwa rayuwa ta mata atishawar tsaki batta ga tsuntsu batta ga tarko .

'Yayan Hajiya Mama kansu gaba É—aya basu da sakewa a cikin taron sunan duk kuwa da cewa sun zo sun kuma kawo kayan jaririya da na uwa irin na alfarma .

Da kaya sai da Falmata ta rasa gurin zuba su tsakanin wanda Mijin ta tayi mata da wanda iyayen sa suka mata da wanda Iyayen ta suka kawo mata da kuma na 'yan uwan sa ga kuma na dangi da abokan arziƙa .

***

Bayan suna da Zainab da Hafsa da zasu koma kayan niƙi-niƙi aka haɗa Su da shi .

Ita kuma Amnee ta zauna kula da Falmata da ta dage tana lura da ita saboda haihuwar da tayi wani ɗam rami na musamman na turara jiki ta sa aka mata a cikin uwarɗakin Falmata kamar yadda al'adar su take su basu cika shan magungunan na mata ba sai gyaran jiki tsaftar sa da ƙyalƙyale fata suka fi bawa muhimmanci .

Gefe guda kuma ita ma Hajja ta dage da nata gyaran irin na matan ƙasar Hausa da su kuma suka fi bawa shan kayan ɗa'a muhimmanci .

Kafin sati biyu Fatar Falmata ta zama kamar bayan tarwaɗa yayin da wani fitinannan ƙamshi ya zauna mata a jiki 'yar kiɓar shayarwa da tayi ta amshi jikin ta sai ta koma kamar irin hamshaƙan matan nan da suke kan ganiyar ƙuciyar su duniya kuma ta juya hasken ta akan su tana haska su .

Bayan cikar sati biyu da kwanaki biyu Amnee ta koma Nigeria inda ta je ta tarar da labari mafi daɗi da Prof ya tare ta da shi kan ya samarwa da ƙanwar sa Rahima Miji .

***

Sheikh Mukhtar ɗaya ne daga cikin jerin ƙannen abokansa da bai yasar da zumunci ba ko bayan mutuwar wansa yake ziyartar sa lokaci zuwa lokaci muddin ya shigo garin Maiduguri daga can ƙasar Saudi-Arabia da yake aiki da zama tare da iyalin sa sama da shekaru ashirin da yayi aure.

Wannan zuwan nasa lokacin da Prof yake tambayar sa iyalin sa yake shaida masa ita matar tasa ta rasu shekarar da wuce .

Prof ya masa ta'aziyya bayan nan ya shawarce shi da kar yayi jinkirin yin wani auren saboda shi aure ibada ne sannan kuma kariya ne .

A lokacin Sheikh Mukhtar ya nuna masa cewa har kawo yanzu dai bai samu matar da ta kwanta masa ba wacce ya yarda da hankalin ta da zai iya danƙa mata amanar tarbiyyar 'ya'yan sa da matar sa ta mutu ta bar masa su huɗu .

Sannu kan hankali cikin dabara irin ta manya Prof ya gabatar masa da Khaalty Rahima cikin sa'a da ganin girman sa Sheikh Mukhtar ya nuna amincewar sa É—ari bisa É—ari muddin dai ita ma ta amince da shi .

Lokacin da aka sanarwa da Khaalty Rahima batun Sheikh Mukhtar bata ƙi ba tunda dai iyayen-goyon ta sun amince ita kuwa me zai ta tayi gardama idan tana da damuwa ɗaya ce ji da tayi ƙasar za ta bari gaba ɗaya ta bar Bulama dan ta sauran 'ya'yan ta mata ta san Allah ya riga ya sanya mata su a hannun nagartattun Mazaje '

Damuwar ta Bulama ne da ya shaƙu da ita fiye da misali sannan babu wani dangin sa na uba da aka samu ɓullowar su har kawo yau duk kuwa da neman da aka ta yi saboda har kawo yau da ake ɗiban shekaru fiye da bakwai da tarwatsa musu gari da 'Yan tawayen Boko Haram suka yi alƙaryar su bata sake kafuwa ba an riga an shafe ta mafi yawan mutanen su kuma sun mutu da take hasashen ciki har da mafiya-yawan dangin Uban su Yakaka da daman ba wani yawa suka cika ba ƙaramar zuri'a ce da su masu gajeran baya .

Duk da ba wai shakkun Bulama zai wahala bane idan har ta bar shi a hannun Amnee sai dai tasirin tsakanin uwa da ɗa ne musamman waɗan da suka shaƙu ya haka raba tsakanin su ba ƙaramin abu bane sai ko Mutuwa .

Ga jin daɗin ta kuma lokacin da suka yi ganawar farko da Sheikh Mukhtar shi da kansa ma ya mata batun riƙon Bulama zai dawo hannun sa daga zarar sun yi aure .

Da yake lamarin ba wai na yara bane cikin satika uku har magana tayi ƙarfi inda nan da satika huɗu mai zuwa za'a ɗaura auren idan ya tashi tafiya nan da watanni biyu ya tafi da Matar sa da ɗan su .

Bayan watanni shida.

Maradi Niger

Siyama tare da Falmata ne tsaye suna Sallama a jikin motar da Biyamuradi Youssoufa yake lafe a ciki yana riƙe da Amina wacce Falmata ta mata laƙabi da ( Ukhtee ) take ƙiran ta haka da kuma sunan ya bi bakin jama'a kowa ma hakan ke ƙiran ta.

Jin Sallamar tasu taƙi yankewa yasa Youssoufa leƙo kan sa yana cewa "Siyama kin ka ce yau aikin rana kin ka tahi yanzou kouwa ga hantsi ta ɗagga ko kouwa kin fara wassa ne da aikin naki ko kouma kin gajiya ne za ki bari dagga farawar ki.?

Da sauri Siyama ta saki hannun Falmata da ta riƙe jin cewa Biyamuradi Youssouf ya  sako maganar aikin da da kyar yarda ta nema ta fara zuwa har sai da Maimartaba ya sa baki yace aikin ta na ceton rai ne sannan tun tasowar ta burin ta ne ta zama likitar haƙora ƙaƙa zai hana ta bayan shi ya san daɗin samun cikar buri a rayuwa tunda shi ma babu wanda ya katse masa nasa burin na zama Babban Soja mai yiwa ƙasar sa hidima .

Ba yadda ya iya haka ya haƙura aka samar mata da aiki a babban asibitin jaha tare da sharaɗin ba ita babu bin sa jaharTahoua sai dai shi zai dunga zuwa kamar yadda suke yi a tun can baya .

Babu jaa Siyama ta amince saboda ranta ya afu ga son taimakon Al'ummar ta itama  lokaci yayi da za ta bayar daga ilmin da Allah ya hore mata falalar sa .

Baya tayi tana jaan mayafin ta ta rufe cikin ta da ya fara girma da yake nuni da nan ba da jimawa ba Ukhtee za ta samu ƙani ko ƙanwa .

"Ƙamnata Allah shi kiyaye mukku hanya hirar mu ba mai yankewa ce ba ina dai sake faɗa miki dan Allah dagga kin koma ecole ki dagewa karatu kiyi zarra ga abokan karatun ki hakan zai zama abun alfahari ne a gare mu.

Falmata tana murmushi ta amsa da "Insha Allah ba zan baki kunya ba Docteur Siyama nan da wassu 'yan shekaru ƙamnar ki zata zama diplômée.

"Allah shi badda sa'a ƙamna ta.

"Amin .

ta amsa tana shigewa Mota direba ya jaa suna barin gidan , Falmata ta waigo tana miƙa hannu domin ɗaukar Ukhtee da take ta tsalle a jikin Baban ta tana wasa girman jikin ta da wayon ta sun wuce na watannin ta shidda sai dai a kai ta watanni goma .

Noƙewa tayi tana ƙin zuwa ta faɗa jikin Baban ta da sauri tana ƙyaƙƙyala dariya irin ta yaran da lafiya da jin daɗi ya wadace su .

A lokaci ɗaya iyayen nata su ma suka sa dariya suna bin ta da kallon dake cike da ƙauna Falmata ta ɗan jaa kumatun ta "Ukhtee yau ni kike yiwa ƙyauya ? Ai anjima kaɗan za ki zo ne .

Shafa kan ta Youssoufa yayi wanda ya sha adon ribbons irin na yaran gata da ya dace da lallausar sumar kan ta mai tarin yawa da yake sake fiddo kyaun ta da ido bai gajiyawa wajen kallon ta.

"Ki rabbu da ita Fatima kin iya shigga tsakanin É—iya da Mahaifin ta ?

Girgiza kai Falmata tayi tana mai matsowa jikin sa ta kwantar da kan ta ta ɓarin jikin sa na dama ita da ukhtee fuskokin su na kallon juna akan ƙirjin sa .

Haɗa su yayi ya rungume bayan ya sumbanci kan Falmata da yake ƙirjin sa. "Fatima-zahra ina son ku irin son da ba shi da iyaka.

"Biyamuradi Youssoufa mu ma haka muna ƙaunar ka irin ƙaunar da bata da iyaka.

Direban da yake iya jiyo sautin su sai ya ƙara volume ɗin radio da waƙar matashiyar mawaƙiyar nan camelia jordana mai taken mens moi take tashi cikin baitukan ta inda take cewa  :

"Je rougis je rougis je rougis
Quand tu me souris
Ô tes yeux menthols
Me mentent et m'affolent

"Oh mens-moi si tu m'aimes
Mais me manque pas
Me manque pas
Me manque pas

"Je défaille à tes mots fous
Mots doux vaudous
Quand je suis dans tes bras
Hé dis, tu penses à quoi ?

Abuja

Sofi lokacin da ta bar gida bayan ta ci uwar wahala kafin ta samu É—an tasi É—in da zai yadda ya É—auke ta taje ta sayar da É—ankunnen gwal É—in da ya rage mata tal a kunnen ta ta biya shi kuÉ—in sa .

Daga nan wani ɗan ƙaramin hotel mai sauƙin kuɗi ya kai ta ta kama ɗaki ta shiga ta zauna a cikin dabarar ta da tayi niyyar ƙullawa na rufewa kowa maganar saki ukun da Hamza ya yi mata har sai zuwa lokacin da aikin boka ya ɗau wuta akan Hamza shi da kansa ta san zai fara neman ta daga nan idan ta gama wana shi ta rama duk irin cin mutumcin da ya mata sai ta nemi da su rufe zancen sakin a tsakanin su kada kowa ya ji su koma su cigaba da zaman su..

Tasha alwashin sai ta walakanta rayuwar Yakaka dan ta ma fasa kashe ta da wuri sai ta mata gashin ƙuma sannan za ta ƙarar da numfashin ta a doron ƙasa..

Kashe wayar ta tayi ta kwanta amma ta gagara bacci saboda tsamin da jikin ta yayi yana mata ciwo na fitar hankali .

Dole ta sa ta tafi asibiti aka bata magunguna ta zo ta sha .

Daren ranar haka ya ƙare mata tana surutan iska .

Washegari kuwa da farar Safiya ta dasa zaman ƙiran Samy Baby sai dai layi ya ƙi shiga wasa-wasa sai da ta shafe tsawon yinin ranar da waya a hannun ta tana ƙiran layin da Samy Baby ta ƙira ta da shi har wayar chaji ya ƙare ta mutu bata samu ta shiga ba

Ta lallaɓa ta sayo kan chaja ta zo tasa bata jira wayar ta cika ba ta dasa daga inda ta tsaya wajen ƙiran layin Samy Baby .

Kafin cikar kwanaki uku Sofi tayi ƙaramar hauka a ɗakin otel saboda dai babu wani saƙo daga Samy baby babu alamar sa kuma ita ta gagara samun ta sannan kuma ko alama bata ga ƙira daga wani nata ba da da har kashe wayar take dan kar a ƙira ta.

Doctor Hamzan da take hasashen aiki ya fara cin sa kuwa duk lokacin da taga alamun Kamfanin Sadarwa sun tura mata saƙo zato take shine .

Haka zata yini sambatun ƙiran sunan sa.

Kafin cikar Sati kuɗin hannun ta ya ƙare da daman fiye da rabi zama take da yunwa tana biyan kuɗin ɗakin da take kwana .

Ala tilas ta fita daga Otel ɗin kawo yanzu kwakwalwar ta ta ƙara birkicewa ta kasa yarda da abun da ya faru da ita yake kuma sake faruwa da ita .

Ciwon mazaunan ta da suka É—uri ruwa tun ranar da ta yanke shi yafi kome É—aga mata hankali saboda azabar da take sha kullum dare bata iya bacci .

Ba arziƙi ta kama hanyar gidan su a birkice kamar sabuwar mahaukaciya .

Da zuwa zata sake dasa sabuwar ƙarya ta tarar da ashe tuni kome ya jima da kwaɓe mata asirin ta ya daɗe da tonuwa kowa kuma yasan abunda ya faru abunda ta aikata da irin hukuncin da Hamza ya yanke mata .

Babban tashin hankalin ta yadda tana ji tana gani Baban su da ya dawo ƙasar kwanaki biyu da suka wuce ya kore ta a gidan bayan ya ƙare mata tanadi .

Gidan wata dangin dangau ɗin Hajiya Kori da take mata kore a can irin unguwannin kusa da ƙyaukan Abuja nan Hajiya Kori ta sa direba ya kai Sofi ba tare da sanin Mahaifin ta ba domin idan ta shi ne kawai Sofi tayi tafiyar ta Momy kori ta ce ta zauna a can kafin Baban ta ya huce ya saurare ta .

Bata haƙƙaƙe da babu wata sa'a da ta rage mata a rayuwa ba sai da aka shafe fiye da kwanaki arba'in tana ƙirgawa babu Samy Baby ba labarin ta .

Zuwa lokacin ta haƙiƙance cikin biyu ɗaya ne ko dai Samira ta yaudare ta ta mata damfara ta gudu a duniya ko kuwa ta gamu da mummunan hatsarin da ya rutsa da rayuwar ta a can india ba tare da an mata aikin da ta aiketa yi ba .

Ƙurunƙus sai gaba ɗaya mummunar zuciyar ta da shaiɗan da bai riga ya gama cika aikin sa akan ta ba suka cigaba da mata raɗa cewar ai babu wani amfanin da rayuwa za ta iya sake mata nan gaba .

Dan haka sai kawai ta afkama shaye-shayen miyagun ƙwayoyin da basu cika tsada ba sai mugun aiki dan da haka kaɗai take iya samu ta hasko kan ta a irin rayuwar da ta kwashi shekaru tana tsarawa a kan ta ita da Doctor Hamza.

Kafin wasu watanni ta yiwa rayuwar ta illa ga kuma ciwon da yake daɗa cin jikin ta gaba ɗaya ta sururuce ta koma irin mutanen da ƙwaya ta gama musu illa a rayuwa suka zama marasa amfanin da ba zasu iya yiwa kan su ba ma bare su yiwa wani .

To ai daman a rayuwa muddin ShaiÉ—an ya zama jagorar ka ba zai kauce ba har sai ya kai ka tsakiyar kogin nadama da ba kuma za ka iya fiddo da kan ka ba.

***

Yakaka da Doctor Hamza kamar kullum suna kitchen da safe suna aikin su tare da dai mafi yawan aikin Doctor Hamza ne ke yi saboda kome Yakaka ta É—auka za tayi sai ya hana yace kar ta wahalar da kan ta da Babyn sa .

Suna gaf da kammala haɗa abun Breakfast ɗin su tattabarun rannan suka sauƙo sai dai a yau su uku ne tare da su da 'yar wata matashiyar tattabara da duk alamu ba'a jima da fara fita da ita kiwo ba.

Da sauri Yakaka ta nuna masa su tana cewa "Laa Habibi ka ga tattabarun mu na rannan har sun samu baby ko ba su bane .?

Da sauri Doctor Hamza ya mayar da ganin su kan sa yama dariya yace "ai kuwa sune wai har sun haihu ? Gaskiya sun yi ƙoƙari .

"Ba dan nima dai ga nawa Babyn yana hanya ba ai da sai nace sun cinye mu a wasan .

Dariya Yakaka tayi tana É—iban 'yar shinkafa ta watsa musu kafin ta taya shi su kwashe abincin karyarwar su kai falo .

Bayan sun gama brakfast suka yi wanka Yakaka ta taya shi ya shirya suna yi suna 'yar soyayyar su da ba'a cika magana a cikin ta sai da suka fito za ta masa rakiya yana riƙe da kunkumin ta sannan yace "Wafaa  kin ga na manta har zan fita ban sanar da ke ba ƙanwar abokin aikina da yake nan unguwar ai kin san shi ko Doctor Abdallah ?

GyaÉ—a kai Yakaka tayi tana jin zuciyar ta na sauya bugu da ba ma zata iya bada amsa da baki ba.

Murmushi Doctor Hamza yayi yana mayar da ƙofa ya rufe ya jawo ta jikin sa ya matso da ita Sosai cikin ta ne kawai ya tokare ya hana haɗuwar ƙirjin su .

Muryar sa a ƙasa-ƙasa yace faɗa min meye a zuciyar ki na ji ta sauya bugu me kike tunani ?

Girgiza kai ta sake yi cike da ƙagautuwa ta ji ƙarshen zance tace "ba kome , habibi me ya faru da ƙanwar Doctor Abdallah ?

'Yar sassauƙar dariya yayi ya jaa karan hancin ta kafin yace " sunan ta Madina ma'aikaciya ce a ƙungiya mai zaman kanta da take bada tallafi ga kasashen da annoba ta fadawa a sakamkon yaki ko na ɓullar cutuka watau NGOs babbar ma'aikaciya ce a kungiyar da bata dade da da dawowa daga...

Cike da gundura Yakaka ta Katse shi "Habibi mana to ni meye alakata da ita?

Wannan karon dariyar da yake gintsewa ita ce ta bayyana ya shiga kyakyatawa ganin haka yasa idanun Yakaka cika da ƙwalla ta fara ƙoƙarin zamewa ta bar gurin .

Da sauri ya riƙo ta gaba ɗaya ya rungume ta a jikin sa yana dai-daita nutsuwar sa daga barin yin dariyar da yake yace "Wafaa aina kika koyi kishi haka un ?? Haka kike sona ashe ? Ki kwantar da hankalin ki Wafaa ni naki ne ke kaɗai da yardar Allah babu wacce zata sake ratsa tsakanin mu ke kaɗai kin isheni rayuwar duniya kin ji ko ?

A tare suka yi ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa "Abdallah shine ya bani labarin ƙanwar sa da shirin da take yi na tafiya Maiduguri domin yin aiki dalilin da yasa ya min zancen domin ya ji yaya lafiyar garin yake ? To bayan na ba shi amsar da ta dace shine har ma na ɗan ba shi bayani akan labarin rayuwar ku yadda kuka kasance a matsayin 'yan gudun Hijira har ma ya sake jimantawa to ashe ya faɗawa ita ƙanwar ta shi sai jiya yake shaida min cewar wai na nemawar Madina izni idan har kin amince tana so ta zo yau ta ɗan tattauna da ke kan yadda rayuwa ta kasance muku a Sanadin Boko Haram .

Ya ɗan tsahirta kafin ya ɗora da cigaba da cewa "Wafaa da fatan ban saɓa miki ba da na bada wani ɓangare na labarin ku ba tare da amin....

Da sauri Yakaka ta rufe masa baki da lallausan hannun ta tana girgiza masa kai  tace "Habibi kar kace haka ni wallahi baka min laifin kome ba ina maraba da Madina kace ta zo insha Allah za ta iya samun duk wasu bayanai daga bakina daidai gwargawdon yadda rayuwar mu ta kasance .

Sumbatar ta yayi a goshi kafin ya sake ta yana jin yadda take ƙara shiga ransa saboda sanyin halin ta .

Daga nan rakiya ta masa ya tafi cike da kewar juna da suke ji a koyaushe idan zasu yi rabo da juna ko da na awa guda ne .

Bayan ta dawo cikin gidan da ƙwazo irin nata ta gyara gidan tsaf tana yi tana hanzari tana duba waya dan kar lokacin ƙiran ta kula da Ukhtee yayi .

Ta gama ƙarfe tara cif tana zama kuma Falmata ta ƙira ta a skype bayan sun gaisa Falmata tana tsokanar ta Maman biyu sai ta haɗa Su da Ukhtee ita ta shiga lectures.

Da kamar kullum idan za ta shiga lectures da take yi a sati sau uku Ukhtee bata yarda da mai rainon ta ta riƙe ta har Falmata ta gama ihu za tayi ta yi tana kuka .

Sai fa idan an ƙira Yakaka a Skype an haɗa su nan ne kuma babu ruwan ta da Falmata bare wata mai raino za tayi ta damuƙar wayar tana gwalatu da dariya Yakaka na biye mata tana mata wasa har tayi bacci idan ta farka kafin Falmata ta fito Yakaka za'a sake ƙira ta kula da ita ta waya .

Wata irin ƙauna da shaƙuwa ce ta ban mamaki a tsakanin Su biyu yadda Ukhtee ta gane da Falmata da Baban ta haka ta gane da Yakaka haka kuma take son ta .

Sai da ta gama mata wasa ta samu tayi bacci sannan suka yi sallama da mai rainon ta ajiye wayar fuskarta ɗauke da murmushi tana jin ƙarin ƙaunar Ukhtee na bin jikin ta "daga an yaye ki zan je na ɗauko ki takwara koda kuwa Baban ki baya so sai dai yayi haƙuri sa samu wasu bayan ke amma ke kam tawa ce 'yata 'yar gidana.

Ta furta hakan a sarari dai-dai lokacin da aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan.

A hankali ta miƙe tana ɗan tura cikin ta gaba da duk cikin watannin sa biyar amma yayi girma sosai "Matar likita ko 'yan tagwaye zata haifa ?

Lokacin da ta buɗe ƙofar sai ta ci karo da wata kyakkyawar mace da zata girme mata da kaɗan a shekaru wacce kallo ɗaya tal za'a mata a hango tarin ilmin Boko da wayewar da suka samun wajen zama na dindin a tare da ita bayan hutu da yake numfasawa a jikin ta .

Daga kan takalman ƙafafun ta marasa tudu har kan ɗan farin gilashin da yake saƙale akan doron siririn karan hancin suna nuni ne da irin tsadaddiyar rayuwar da take yi ta 'ya'yan gata 'ya'yan manya.

"Madina ce .

Yakaka ta aiyana hakan a cikin ran ta kafin ta ɗan sake faɗaɗa fuskar ta da murmushi  cikin muryar ta mai sanyin ta ce "sannu da zuwa ki shigo mana .

Da taƙaitatciyar Sallama ta shiga gidan kamar yadda fuskar ta ma ke ɗauke da taƙaitatcen murmushi.

Bayan sun gaisa Yakaka ta kawo mata zoɓo mai sanyi da yake tashin ƙamshin kayan shai irin na mutan Ndjamena da take ƙamshin ya ɗau hankalin Madina '

Bayan sun ɗan taɓa hira lokacin da Madina take shan Zoɓon da daɗin sa yake ratsa ta "bata taɓa zaton irin wannan local juice ɗin yana da daɗi haka ba , ta aiyana hakan a cikin ranta.

Da ta gama sha sai ta fuskanci Yakaka sosai ta sake gabatar da kan ta tare da yi mata godiya da amincewar da tayi ta bata damar tattaunawa da ita .

Cikin jin daÉ—i Yakaka ta ce ita ma tana godiya daga haka shiru suka É—an yi Yakaka tana É—an satar kallon Madina wacce take shafa fuskar haÉ—aÉ—É—iyar ipad É—in ta har dai ta kai inda take son zuwa ta É—ago kanta.

Fuskar ta a sake tace "Amina zan so ki bani labarin yadda rayuwa ta kasance muku bayan da 'yan tawayen Boko-haram suka tarwatsa garin ku wanne irin tallafi kuka samu daga ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa ? shin kun samu taimako ?  sannan a wane hali kuka kasance kafin taimako ya zo muku da kuma bayan taimakon ya riske ku.?

Shiru Yakaka ta É—an yi sannan ta mayar da ganin ta kan kyakkyawan agogon hannun Madina tamkar mai nazarin lokaci kafin ta buÉ—e bakin ta a hankali cikin sanyi muryar ta tace .

"Mafarin Hargitsin Rayuwar mu ya fara ne ni da ƙanwata Falmata sanadin 'yan tawayen Boko haram da suka sa muka tsinci kan mu a matsayin 'yan gudun Hijira.

Tammat Alhamdulillah .

Alhamdulillahi.Alhamdulillah. Alhamdulillah Godiya ta tabbata Ga Allah Maɗaukakin Sarkin wanda ya bani ikon Farawa da gama litaffin nan da na ɗau tsawon watanni Ashirin da kwanaki shidda  ina rubutun sa tsakanin faɗi-tashi na rayuwar yau da kullum tare da juyin yanayi tsakanin zafi da sanyi da ruwa da iska babu shakka Allah shine abun godiya .

Ina roƙon Allah ya yafe min daga abunda ya kasance kuskure na rubutu kasantuwa ta 'yar Adam mai cike da rauni da tarin laifuka ( Allah na tuba ) sannan abunda yake na lada Allah Ubangiji ya karɓa ya ɗora shi bisa mizanin kyawawan aiyukana ( Amin )

Sannan godiya ta marar yankewa ta tafi ne gare ku masoyan rubutu na da baki ba zai iya lissafa adadin ku ba Wattpidians wanda da kuka yi jimirin bibiyar rubutuna tsakanin lokaci mai tsawo da yake cike da tsaiko mai tarin yawa daga gareni , babu shakka ƙauna ce sila kaunar da ku ka nuna ita ta ban ƙwarin guiwar da har ta kai a yau muka kawo ƙarshen littafin tare da ku ,  hakika kalmar nagode tayi kaɗan wajen bayyana muku godiya ta sai dai nace Allah ya saka muku da alkhairi nima Ina ƙaunar ku saboda Allah .

Godiya ta musamman ga ƙawa kuma 'yar uwa Fatima Salim aka Batul Mamma da ba domin ita da tarin gudumawa da alkhairin ta a bisa rubutun littafin nan ba da fa tafiyar bata miƙa ba nagode ƙwarai ƙwarai Sister Fatima Allah ya bar ƙauna.

Yabo tare da Fatan Alherin ya tafi ne baki ɗaya ga Yayana kuma Malamina Sheikh Muktar Yaa Allah ya saka da alkhairi Yaa Mukhtar kalmar nagode tayi tsororo a tsakanin mu sai fatan Allah ya bar ƙauna .

Sannan akwai tarin masoya masu daraja da littafin Mafari ya zama sanadin haɗuwar mu amma ƙaunar mu sai tayi ƙarƙon da ta zarce dalilin haɗuwar Littafi daga cikin su Akwai baki ɗayan jama'ar group ɗina na Mafari fans .

Sannan  'Yar uwa kuma jagorata a harkar rubutu Sumayyah Abdulkhadir Takori , tare da ke da dukkanin jama'ar ki na Takorities ina godiya a gare ku tare da ƙaunar ku Allah ya bar zumunci .

Jama'ar Batul Mamman na KDM ina godiya da yawan ƙaunar ku .

Nafeesa Tafeeda tare da jama'ar ta na Maman Mama novels.

Sister Amina Mafari fans Group admin Jameela aka Meela ,Raliya Garba Zulaihat rano , Zahra aka donutfairy ,Maryam Talba ,Auntie Aisha , Fadeela Khabeer godiyar ku ta musamman ce Allah ya bar Kauna.

da da da da Masoya haƙiƙa kuna da yawan da ya wuce fa na ƙirga ku musamman dai da yake ai kun san ƙyuiya irin tawa ah to da ya muka sha a rubutun ma ? Lol.

Masoya ga dama ta samu na tattaunawa akan duk wani abunda na rubuta daga farko har ƙarshen littafin Mafari .

Ga masu min gyara ko domin gaba ina maraba .

Ga masu ƙorafi domin gaba ina maraba .

Ga masu neman ƙarin bayani/tambayoyi kowanne iri muddin b

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.