Complete Hausa Novels

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 21

Cigaba suka yi da kutsawa cikin unguwar suna neman wurin yin alwala har dai suka yanke shawarar tsayawa a dai-dai wata mahaɗar da ta fi kama da tashar tsayuwar motoci saboda yawan ababen hawan da suka gani a wurin ,"sai dai yawan masu saye da sayar a wurin kama tun daga kan masu ɗanyen kaya ,da masu kayan abinci na awu ,"har ma zuwa masu saida dafaffen abinci da kuma masu toye-toye , ga kuma ƴan tebura nan dangin su masu saida biredi da sauran su ya sanya su hasashen ƙila kasuwa ce," tsayawa suka yi a wurin suna rarraba idon neman wurin da zasu samu damar Alwala ,

Daga gefe kaÉ—an da su , suka hango masallaci wanda rumfar kwano ta kare gaban sa mutane suna ta Alwala wasu kuwa sun kammala alwala suna sallolin su a cikin rumfar ,"

Ɗan yawatawa da idanun ta yakaka tayi tana neman ruwan Alwala ,"sai dai yawan idanun da ta gani akan su ya saka ta cikin firgici ,"kusan illahirin mutanen wurin hankulan su da idanuwan su akan su yake ," kuma idan ba idanun ta suke mata ƙarya ba kusan duk mutanen wuri ɗaya suke kallo a jikin su", daga kan kirjin su zuwa cikin su ,'!

A hankali ta sauke idon ta tabi inda suke kallo a jikin su ta gani koh wani abun ne a jikin nasu ,"

Hannu ta kai tare da gyara wuyan rigar ta da ya ɗan saɓule lokaci ɗaya kuma tana kai hannu ta gyarawa falmata ita ma nata wuyar rigar , duban ta 'ta mayar kan yagana wacce ta fahimci ita ma ta lura da irin kallon rashin yaddar da illahirin mutanen wurin ke bin su da shi ,"

Ƙasa tayi da muryar ta "yagana kin lura da irin kallon da mutanen nan ke bin mu da shi ? Koh daman haka mutanen birni ke yin kallon su ?

Ina lure da su nima ,"amma ina ga haka suke kallon su "dan yaakura na tace a lokacin da ta kawo ni asabitin tsatsareni da ido likitan nan yayi a cewar ta saura kaÉ—an ta É—auke ni mu tafi dan tayi zaton ma koh karama ne (maye ) É—an guntun tsaki ta jaa a lokacin da suka haÉ—a ido da wani matashi majiyi karfi yana kallon su tsakar ka, lokaci É—aya kuma yana danna wayar sa tare da kara ta a kunne ","

Jibe shi dan Allah ya wani tsare mutane da ido toh kurwar mu kur ," Falmata kawo kuɗin nan na ƙarasa can na sayo mana ƙosai da doya nan wurin ma jama'a sun yi yawa mun ƙara gaba kawai muyi sallar ,"

Falmata bata ce ƙala ba ta miƙa mata gudar ɗari biyun da take duƙunƙune a hannun ta "sashi guda na zuciyar ta! Yana gaskata mata zancen su yakaka na cewa da suka yi an zuba musu ido domin kuwa ita ta riga su sanin ana kallon su ,dan tun da suka nufo wurin jikin ta ya bata akwai wani abun cutarwa ko kuwa idanun mutane akan ta ,'duba da yadda taji tsikar jikin ta tana ta faman miƙewa,'hakan shine alamun da ita take fahimtar akwai matsala a wuri "baiwar ta kenan" , a gefe ɗaya cikin ranta kuwa cike fal! Da haushin yagana akan yadda take nuna ita fa ala dole ta fi su sanin maiduguri Alhalin kuwa su da ita duk sammakal tilo ," basu da wani bambanci.

Taku biyu yagana ta yi suka fara jiyo tsuwwar wani abu wanda basu san ko meye bane ,"yayin da hankalin su ya kasu biyu É—aya akan mutanen da suka ga sun fara guje guje wasu ma har suna barin kayayyakin sana'o'in su ,gefe guda na hankalin su na ga kan tsuwar nan da suke ji tana sake durfafo inda suke , so suke su fahimta akan wannan tsuwar ne mutanen ke gudu koh kuwa meye dalili ,?

Yakaka ƙarar meye ne wannan ɗin kuma meyasa naji kamar takun gudun mutane ?falmata ta furta hakan a dai-dai lokacin da take lalubar jikin yakaka tana gyara ƙullin da ya haɗa bakin rigunan su 'da alamun shirin gudu take "
Nima ban sani ba Falmta,"
Yunƙurin buɗe baki yagana take cikin cewa wani abu amma sai maganar ta maƙale mata a fatar baki.' sakamakon ganin manyan motocin da suke ɗauke da irin fentin da suka gani a jikin jirgin saman nan da yayi musu ɓarin wuta a daji ," a take suka fahimci ƙarar nan da suke ji daga jikin motocin nan take fitowa .

ÆŠurum dum ,"bugun sautin zuciyoyin yakaka da yagana a lokacin da suka yi idanu huÉ—u da tarin motocin da suke da tabbacin na waÉ—annan mamallakan jirgin saman ne ,"shikenan mun mutu mun lalace yakaka , shikenan wallahi sun biyo mu ne su kashe mu ,"
Su waye suka biyo mu ? Yagana wai meke faruwa ne ,"cewar falmata da maganganun yagana suka yi mugun ruÉ—a ta ,"
Sojojin da suka biyo mu da jirgi a daji sune gasu nan a mota ....
Sauran maganar maƙalewa tayi a fatar bakin yagana a lokacin da ta ga gungun sojojin nan suna durƙowa daga bayan manya manyan motocin su hannayen su duk riƙe da bindigogin su da ya sanya cikin yagana ba da wani sautin ƙululu lokacin da tayi arba da su ,"wannan fa shi ake cewa anyi gudun gara an tadda zago ,"

Jeruwa sojojin suka yi daga nesa kaɗan da inda su yakaka ke tsaye a sandare ko numfashi da ƙyar suke jaa ,"
Da gudu wani soja ya fito daga cikin gaban wata mota hannun sa riƙe da wata jibgegiyar bindiga ," ɗaga ta yayi gami da jaan kunamar bindigar ƙaraƙat ,'ya saita ta akan su yakaka da zuwa yanzu suke ta ɗigar gumi kamar an tsamo su daga rafi ,"

Remove your clothes all, "

Sasarai su dukkanin su suka yi suna wulwulga idanu cikin rashin sanin takamaimai É—in abun yi lokaci guda kuma tsoro ya sake cika zuciyoyin su a sakamakon lura da suka yi cewa duk yawan mutanen wurin nan a yanzu basu ga ko mutum guda ba daga su sai sojojin nan ,"ji suka yi zuciyoyin su na barazanar faso kirjin su .,

Fahimta da sojojin nan suka yi su yakaka basa jin turanci ya sa É—aya daga cikin su É—aga murya ",
Ku cire kayan jikin ku idan ba haka ba zamu harbe ku mu kashe ku ,"
Cikin tsananin firgita yakaka da yagana suka kalli juna lokaci É—aya suka ji falmata ta rushe da kuka ,"
Ji suka yi an sake daka musu tsawa
Zamu harbe ku idan kuka sake minti É—aya ,"

Ba shiri yagana ta fara cire tun daga É—angalallen hijabin ta har zuwa rigar ta da yanzu take kan cirewa ,"

Satar kallon yagana ,"yakaka tayi kafin cikin rawar jiki ta miƙa hannu tana warware kullin da yake tsakanin rigunan su ita da falmata lokaci guda tana me cewa falmata ki cire kayan ki idan ba haka ba zasu kashe mu ,:

Tsaye suke daga su sai siket din ciki hannayen su rumgume da kirjin su ,fuskokin su kuwa shaɓe shaɓe da ruwan hawayen da ya chakuɗa da majina gami da gumi ,"

Magana sojojin suka yi a tsakanin su bayan sun gama ƙare musu kallo Daga wurin da suke ,"

Sir I think they're not Boko Haram girls , there was no bomb in their bodies,"
( shugaba ina tunanin waÉ—an nan. ba Æ´an matan boko haram bane , babu nakiya a jikin su )

Yes they're not ,

(ƙwarai ba su bane )

Daga inda sojan nan ya yake tsaye ya sake É—aga murya tare da basu umarni su sanya suturun su ,"

Koh kafin ya ida rufe bakin sa har sun yi nisa wurin sanya kayan nasu ,"tsayawa suka yi suna jiran su sake jin umarni na gaba ,"idanuwan su kuwa basu bar zubar ruwan hawayen wannan tozarci da tashin hankalin da suke ciki ba ," ba ma dai kamar falmata wacce har karkarwa take tsabar kuka ,"

Gani suka yi ɗai ɗaya da ɗai ɗaya suna komawar su cikin motocin su ,"yayin da suka ga waɗan nan biyu da suke yi musu magana ɗaya da hausa ɗaya cikin yaren da basa fahimtar sa sun nufo inda suke bindigogin su saɓe akan kafaɗun su ,"

Suna ƙarasowa wannan me jin hausan yace musu ", daga ina kuke kuma ina zaku ?
A wannan karon shiru yagana da ta kasance jaa gaba wurin mayar da amsa tayi tana zazzare idanu tare da satar kallon bindigogin hannun su ,"

Jin yagana tayi shiru ya sanya yakaka ta buɗe bakin ta cikin maƙyarƙyatar murya tare da gurbatatciyar hausar ta tace ",
:Umh daman mu Æ´an hijira ne daga garin mu shine-shine muka zo nan neman gwamnati ta taimaka mana da masauki ,"
Inane garin naku ?
Ƙauyen mairambiri

Magana sojojin nan biyu suka yi a tsakanin su cikin harshen turanci ,"

Ku zo mu kai ku camp mu ajiye ku saboda idan kun cigaba da yawo haka a gari mutane baza su yadda da ku ba a karshe ma ana iya yi muku dukan tsiya da tunanin ku irin ƴan matan da boko haram suke ɗaura musu nakiya ne , su shiga cikin kasuwa koh taron jama'a su yi ƙunar baƙin wake ," bayanin da sojojin nan suka yi musu kenan bayan sun gama shawara a tsakanin su

Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin yakaka da yagana ," camp ina ne camp ?koh dai gidan horar da mutane ne sojojin nan zasu tafi da mu ? Wannan ne zancen da yake ta kai kawo cikin zuciyoyin su dukkanin su uku lokaci guda kuma suka ji wata sabuwar nadama baki daya ta kama su ,"daman haka mutanen cikin birni suke azzalumai haka kawai sai su hau jibgar mutum ?

Tsawar da aka daka musu ita ta sanya ba shiri yakaka ta kama hannun falmata suka bi bayan sojojin nan da su har sun yi juyawar su sun kusa isa ga motocin su tun bayan da suka basu umarni ,"

Wani irin mahaukacin gudu motocin sojojin nan suke akan tsakiyar titin na Maiduguri ," duk inda suka gifta motoci da sauran ababen hawa darewa suke suna basu hanya ,"

Tsugunne su yakaka suke a bayan hilux ɗin, sojoji biyu sun sanya su a tsakiya a zaune a kan ɗan tudun da aka tanada domin zama ," ji suka yi iskar shaƙa ta musu yawa a saboda gudun da motar ke yi ,"nan take maƙoshin su ya bushe ƙemas , idan ban da sharar hawaye babu abun da suke yi ,tun da suka hau motar babu me cewa ƙala ,"

Gware yakaka da falmata suka yi ," a sakamakon wani irin birki da motar da suke ciki ta jaa," wani marayan kuka falmata ta fashe da shi a dalilin zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwar ta a dalilin gwaren da suka yi ",

Dira sojojin da su ke tare da su a bayan motar su ka yi kafin su yi musu umarni akan su sauƙo ,

Tsayawa yakaka-da-yagana suka yi suna ƙarewa wurin da aka kawo su kallo ,"wata babbar kofa ce a gaban su me kama da kofar gari a ganin su, sai da ƴaƴan hanjin cikin su yakaka ya kaɗa sakamakon ganin wasu gungun sojoji da suka yi daga cikin wata rumfa a gefen kofar ,"
Yakaka ina aka kawo mu ,? Inji falmata ,"
Nima ban sani ba falmata ,amma dai kamar wani babban gari ne shima gashi dai har da wata babbar kofar sa ," ta furta hakan tana me satar kallon sojojin da koh kula da su basu yi ba,"

Ku zo mu je nan shine camp (sansanin Æ´an gudun hijira ) inda gwamnati ta tanadar ga ire-iren ku ," a cewar wannan sojan da ya wuce gaba ,"

Da sauri su ka bishi ransu yana wani É—an motsin daÉ—i-daÉ—i ! Duk da cewar dai basu gama aminta da zancen sa ba domin basu tabbatar ba ,'

Yakaka da yagana su na sanya kafa cikin wurin suka fahimci ba ƙaramin babban fili bane ta ciki , a yayin da suka fara yawata idanun su zuciyoyin su cike da mamakin ganin mutane birjik fululu iyakar ganin su suna ta harkokin su ,"

Hayaniyar jama'ar da falmata ta fara ji yana tashi cikin yaren su , shi ya sanya ta ji kaso goma na tsoron da yake cike da ranta ya kau ,!

Bayan ƴar gajeruwar tafiyar da suka yi , bakin wani gini sojan nan ya tsayar da su yayin da shi ya taka ya shiga cikin ɗan wurin mai kama da ɗaki ,"(Office)" bai kai minti biyar ba ya fito ba tare da yace da su kome ba yayi wucewar sa cikin rashin kulawa da gaisuwar da wasu mutane maza da suke zaune turmus a cikin ƙasa da suke yi masa ,"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.