Complete Hausa Novels

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 21

Cigaba yayi da tafiya har ya cimma babban titi , nan ya hango wani shagon sayar da coffee ,

Bayan ya ƙarba musu coffee me zafi ya zaunar da Mama a kujerar da ke fuskantar ta shi ,

Juya ɗan chokalin hannun sa yake yi ya gagara shan coffee ɗin , damuwa tayi masa ƙawanya duk wata walwalarsa ta kau ,

Ko kusa ba zai iya duban ta ya fayyace mata lamuran da suka auku tsakanin sa da 'yar uwar ta ba , yana jin kunya , yana kuma tsoro .

Meyasa ta kasa fahimtar barin abunda ya riga ya wuce a muhallin shuÉ—aÉ—É—an lamari shi yafi alheri fiye da tone-tone . ?

Duban sa ya kai ga Mama wacce tayi shiru ta lanƙwasa kai fuskar ta bayyane da damuwa ,

Tausayin ta ya ji domin ya san damuwar ta ta samo asali ne ga abunda ya faru tsakanin sa da Falmata , da shima zuwa yanzu nadamar ihun da yayi mata yake yi ,

Bai yi hakan da wata manufa ba illa ruɗanin da ya tsinci kan sa a ciki da ya sa bashi da wata hanyar daƙile yunƙurin ta tare da kawo ƙarshen maganar idan ba ta hakan ba .

Tashi yayi ya zagaya ya É—auki Mama suka fito daga Coffee Home É—in ba tare da ya sha coffee da ya saya ba ,

Sake nusawa yayi bakin titi yana tafe sannu kan hankali har ya tadda ɗan wani killacaccen wajen yin sallah , nan yayi sallar la'asar tare da Mama a gefen sa  ,

Bayan ya idar hankalin sa ya kai kan wani fili gaban wasu gidaje da matasa da yara suka taru suna wasan ƴar zamiya akan dusar ƙanƙara Tobogganing , kama hannun Mama yayi suka ƙarasa wajen ,

Ya zauna daga gefe kan kujerar gefen hanya tare da É—aura Mama a cinyar sa ,

Sosai wasan ya ɗau hankalin Mama ganin yara ƙanana sa'o'in ta nata faɗuwa da tashi cikin dusar ƙanƙara , nan take ta shagala da kallon su har tana taya su dariya idan wasun su sun faɗi ,

Ganin walwalar Mama ya bashi damar zurfafa a tunani , sashi guda na ran sa na shawartar sa akan idan ya koma gida ya faɗa mata gaskiya ksn abunda take son sani , yayin da sashi mafi rinjaye ke ƙwabar sa tare da tsoratar da shi abunda faɗa mata gaskiyar zai iya haifarwa ,

Abunda ya haƙiƙancewa ba zai iya jurar fushin ta da damuwar ta ba domin kusa take sosai da ruhin sa ,

Bai ankara ba har duhun dare ya fara shigowa , dan haka ya sake komawa wajen da yayi sallah , ya sallaci Magarib  , 

Yana idarwa ya kamo hanyar gida bayan ya saɓa Mama a bayan sa da tayi laushi tuɓus ,

Ta gaban manyan shagunan sayar da kayan ƙele-ƙele na mata ya zo wucewa , idanun sa suka kai kan wata 'yar kyakkyawar sarƙa da take ɗaukar ido tare da taimakon hasken lantarki da ya haske cikin gilashin da sarƙar take .

Murmushi yayi lokacin da idanun sa suka hasko masa sarƙar a cikakken wuyan Falmata ,

Da hanzari ya shiga shagon ya sayi  sarƙar da take ta farin zinare ƙirar ƙasar Amurka suka zare kuɗin su ta katin sa tare da zura masa akwatin sarkar cikin 'yar jakar da take ɗauke da tambarin Manns jewelry .

Cike da fargaban halin da zai riske ta ciki ya nufo gidan , zuciyar sa na aiyana masa wataƙila tayi ta kuka ,?wataƙila kuma ran ta ya sake ɓaci da shi, koma menene zai bata haƙuri ys rarrashe ta ta bar maganar nan ,

Da Sallama ya tura ƙofar gidan ya shiga ,

Shiru ya ji bata amsa ba ,

Ya lalubi wutar falon ya kunna ,

Idanun sa akan É—an wajen kunna witar É—umama É—akin da har wutar ta mutu , hakan ya sa É—akin ya É—au sanyi

cikin ran sa babu daɗi  , Ya zaunar da Mama akan kujera , yayi tsaye yana saƙe-saƙe , jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi da barin ta da yayi ita ɗaya ,

Takawa yayi ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ya ɗan ƙwanƙwasa ,

" Fatima , mun dawo

Ya furta haka da sauƙaƙar murya ,

Shiru ya sake ji babu alamun motsi ,

Sai ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ɗakin , cikin 'yan daƙiƙai ya fahimci bata ɗakin , da sauri juyo , kai tsaye ya leƙa cikin ɗaya ɗakin , babu alamarta

Tamkar an safure shi haka ya dunga bin kowanne lungu da saƙo na gidan yana neman ta tare da ƙira sunan ta ,

A ƙarshe ya hiƙanƙancewa kansa tabbas bata gidan , ta fita ne ? Ko an sace ta ? Shikenan shi kam ya shiga ukun sa , ta shi kuma ta same shi .

Da gudu ya sunkuci Mama ya fito , dusar ƙanƙara na sauƙa a kan su yayi tirus a harabar wajen , ina zai fara nufa neman ta ? Wa zai dosa ya tambaya akan ta ?

Gidan da yake maƙwaftan na su ya nufa da sauri ya danna musu ƙararawar neman iznin shiga gidan ,

Zuciyar sa na ayyana masa wataƙila ta shiga gidan ,

Tunanin sa ya katse lokacin da aka buɗo ƙofar wani mutum magidanci yayi tsaye yana kallon sa ,

Da harshen turanci ya gabatar masa da kan sa a gurguje kafin ya É—ora masa tambaya kan ko matar sa ta shigo gidan su ?

Da harshen larabci mutumin ya miƙa tambayar ga matarsa da take daga bayansa a tsaye ,

Nan suka tabbatar masa da babu wacce ta shigo musu ,

Har ya juya sai kuma ya dawo ,

Rokon su yayi akan su taimaka su riƙe masa 'yar sa zai je neman matar sa ,

Basu musa ba suka karɓi Mama da tayi rau-rau da ido tana shirin kuka ganin Babanta zai tafi ya bar ta hannun waɗanda bata kai ga sanin su ba ,

Bai kula ba ya juya da sassarfa mai haɗe da gudu ya kama doguwar hanyar da tayi cikin unguwar sosai yana tafe yana dube-dube da waige-waige , hankalinsa yayi ƙololuwar tashi , maƙogoran sa ya bushe , idanun sa har raɗaɗi suke yi masa ,

"Yaa Allah Fatima ina kike ? Yaya za ki min hakka Fatima , ? Meyasa kika fita ?

Ya furta hakan muryarsa na karkarwa , bayan hannun sa ya sa ya goge fuskar sa da iskar dusar ƙanƙara ta watso masa ,

Ganin har ya kusan ƙure unguwar bai gan ta ba ya sa shi komowa baya , yana cigaba da neman ta , addu'o'i iri-iri yake yi ,

Zai iya cewa tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na tsuƙin lokacin nan ba , bai taɓa sanin ita wata kadara ce mai maɗaukakiyar daraja a wajen sa ba sai a wannan gaɓar da yake gaf da rasa ta ,

bazai yafewa mummunar zuciyar sa ba idan har wani abun cutarwa ya same ta ,

Sakin hanya yayi ya nufi wata doguwar hanyar da tayi gefe a tsakankanin dusar ƙanƙara

Fatima , Fatima , Fatima

Yake ƙwala ƙiran sunan ta ,

Ya ƙure hanyar bai ko ga alamun sawun ta ba sai zunzurutun sanyin a yake ratsa sa ,

Dawowa yayi da baya ya sake kama wata hanyar ta daban nan ma yana tafe yana kiran sunan ta ,

Durƙushewa yayi a gefen hanya yana jin tamkar ya ƙwala ihu ko ya ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki ,

Kamar a sama ya fara jin amon Murya ta daga nesa , tana ƙiran sa

Da gudu ya nufi inda yake jin tashin sautin ta ,

A gefen hanya zaune cikin dusar ƙanƙara ya hango ta ,

Hannuwan sa duk biyu ya sa ya ɗago ta , ya riƙo kumatun ta dama da hagu ,

"Fatima meyasa kika fito ? Ina za ki je ?  Fatima kar ki sake tafiya ki bar mu .

Ta kifta idanun ta da suka bushe ƙemas saboda sanyi tace ,

"Baban Mama ku na fito nema , dan Allah kayi haƙuri kar ka sake tafiya ka bar ni , bazan sake yi ma laifi ba ,

Kamota yayi suka miƙe tsaye , yadda take rawar sanyi ya tashi hankalin sa , "

Juyawa yayi yayi durƙuso

"Fatima kama ni hau bissa bayana mu je gida ,

Duk da wahalar da take ciki , noƙewa tayi , muryar ta na rawar sanyi tace ,

"Baban Mama zan iya tafiya da kaina mu taf....

Bata ƙarasa zancen ba ta ji ya ɗaga ta ciɗak , ya ɗauketa , da sauri ta riƙo rigar sa , ya nufi gida da ita .

Duk da tafiyar akwai tazara amma bai gajiya ba ko dan kasancewar sa ingarman sadaukin soja ne ?

Yana ajiyeta akan kujerar falon su ya shiga haÉ—a wuta ,

Muryar ta can ƙasa tace masa ,

"ina Mama ,

" zan É—auko ta tana gidan daura da mu ,
    yace

Da sauri ya dawo ya zauna a gefenta ya shiga zare mata safar ƙafafunta da suka ɗau sanyi , ya zarce da cire mata hular sanyin kan ta ,

ɗaki ya shiga ya ɗauko ƙaton bargo ya rufa mata har kan ta

Ya kamo ta ya dawo da ita gaban wutar sosai ,

Hannuwan sa biyu ya shiga karawa a gaban wutar su ɗau zafi sosai sai ya cire ya sa mata a ƙafafunta ,

A karo na biyu ta sake cewa ,

"Baban Mama , Mama tana waje ko ? Kar sanyi ya tada hargitsin ciwon ta ,

Da ido yake bin kyakkyawar fuskar ta da kallo , yadda fuskar ta ke da kyau haka ma zuciyar ta , ya aina hakan cikin ran sa , duk laifin da yayi mata , duk wahalar da ta sha a sanadin sa , ita ta lafiyar 'yar sa take ,

"bari na ɗauko ta , ya miƙe

Har ya kai bakin ƙofa , ya waigo

"Fatima kadda ki matsa dagga gaban wuta ,

Bai jira amsar ta ba ya fita da sauri , ya shiga ya É—auko Mama wacce har tayi bacci ,

Godiya sosai ya yiwa maƙotan sa da suke musulman larabawa ,

Kai tsaye ya wuce da Mama Kan shinfiɗar ta ya ƙwantar da ita a ɗaki tare da haɗa wuta a cikin ɗakin ,

Inda ya barta nan ya dawo ya tadda ta kamar yadda ya umarceta bata motsa ba , kamar yadda bata daina rawar sanyi ba

"Zanyi Sallah tace da shi ,

Bayan ta idar da magarib ya ja su isha'i ,

Da suka idar kai tsaye ya nufi shayi me zafi ya haÉ—o mata ,

Da chokali ya ɗan sisita shi ya shiga bata a baki tana kurɓa kadan-kaɗan , yadda take rawar sanyi yana damun sa dan haka ya ajiye kofin hannun sa ,

ya kusanto da ita sosai cikin jikin sa , bayan ya rage kayan jikin sa ya rage 'yar rigar sa ta ciki ya ware bargon da lulluɓa da shi ya rufa musu su biyu ,

Hannun sa ta ji ya buɗe zif ɗin rigar sanyin jikin ta , kafin ta ankara ya zura hannuwan sa ya kewaye ta da su tare da ƙwanto da ita kan kirijn sa sosai ,

Ɗumin jikin sa tare da firgici suka yi tasirin da suka hanata ƙwaƙwararan motsi har zuwa lokacin da ya ƙarasa zare rigar sanyin jikinta da ta ɗau sanyi na ban mamaki yayi cilli da ita gefe ,

Habar sa a tsakiyar kanta ya rungume ta tsam a jikin sa tana iya jin bugun zuciyar sa da yake tashi sannu kan hankali ,

Wani irin yanayi mai cike da daÉ—i da nutsuwar zuci da gangar jiki suka tsinci kan su ,

" Fatima ,

Ya ƙira sunan ta muryar sa ƙasa-ƙasa ,

"na'am

Ta amsa masa a hankali ,

"Kar ki sake tafiya wani waje ke kaÉ—ai ba tare da iznina ba kin ji ko ?

Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaÉ—a a hankali ,

Shafar bayanta yayi da hannuwan sa masu É—umi ,

"Fatima ɗazu kin tsorata ni na shiga tashin hankali , kada ki ɓata a ƙasa irin US ,

" kayi haƙuri Baban Mama neman ku na fita sai kuma na kasa gane gida ,

" kan ta ya ɗago daga kirjin sa ya riƙe fuskarta ba domin yana ganin ta ba saboda duhun da yake cikin bargon ,

A hankali ya sumbaci goshin ta ,

"Na haƙura Fatima, ke ma kiyi haƙuri da faɗan da nayi miki ɗazu , kin haƙura ?

" kan ta ta mayar cikin jikin sa ta sa hannuwanta biyu ta zagaye bayan sa cikin shauƙi tace

"ni baka min laifin kome ba Baban Mama idan ma kayi min na yafe ma ,

Murmushi yayi da sauti , ya sumbaci kafaɗar ta , yana jin tilin ƙaunar ta da yake binne cikin ramsa suna tunɓuƙowa da wani irin shauƙi da yasa ya gagara mallakar kan sa a karon farko ya shiga gwada mata zallar ƙaunar ta da yayi raino tun wasu shekaru a baya da tsiron sonta ya fara ɗarsuwa a ran sa ,

ita ma bata ƙi ba , bata kuma bijire masa ba ta ɓuɗe tafukanta ta tallafi muradin sa , tare da miƙa masa abunda yake halalin sa ..

daga falo ai sai aza room ko kuwa ?? 

Assalamu Alaikum Masoya !

Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya tare da ƙwanciyar hankali ?

Ina mai baku haƙuri bisa ga jinkirin da ake samu wajen cigaba da rubutu , ajizanci ne irin na ɗan Adam.

Nagode .
[11/13, 7:04 PM] +234 706 503 6187: MAFARI..
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

38

Washegari sun tashi cikin farin ciki tare da walwala marar misaltuwa , musamman Biyamuradi Youssouf da yake jin kan sa tamkar yau ya fara angwancewa a tarihin rayuwar sa ,

Zallar ƙauna tare da tattali yake gwada mata da ita kuma take ta zille-zillewa tare da jin tarin nawin sa , gefe guda na zuciyar ta tsiron ƙaunar sa ya fara yaɓanya yana baza rassa .

Da dukkanin daƙiƙa guda yana wucewa ne tare da tunanin sa dake manne cikin ƙwaƙwalwar ta duk kuwa da ga shi zaune zahiri a gaban ta .

Yau ne Alƙawarin su da likita dan haka bayan sun kammala karin-kumallo , suka shirya cikin jibga-jibgan rigunan sanyin su rufaffu tundaga wuya, crew neck sweatshirt.

Biyamuradi ya maƙalo hannuwan Falmata tare da ɗaukar Mama bisa kafaɗar sa ,

Ƴar tafiyar da bata cika yawa ba , mai cike da nishaɗi saboda 'yar hirar da ta gifta tsakanin su da ta ƙara musu shauƙin jin daɗin kasancewa da juna ,

Suka iso asibitin , babu ɓata lokaci suka haɗu da likita , bayan tambayoyin da yayi mata game da sabon cigaban da take samu kan  lafiyar ta ,

Cikin amsoshin da ta bashi da bincike-binciken da ya sake yi , ƙarshe ya shaida musu da cewa dole a kai ga matakin ƙarshe na yin aiki ga idon .

Ba tare da ja ba Biyamuradi Youssouf ya amince , cikin lokaci kaÉ—an aka shigar da bayanai tare da É—aura ta akan wasu magunguna daban da zata sha na tsawon sati biyu da za'a mata aikin idon .

Sun baro asibitin zuwa gida , akan hanya Biyamuradi Youssouf ya cigaba da ƙarfafawa Falmata tare da kwaɗaitar da ita samun lafiyar idon ko da kuwa ace bata warke baki ɗaya ba .

Maƙotan su suka tadda daga ƙofar su suna ƙoƙarin kulle na su gidan ,

Cikin mutunci Biyamuradi Youssouf ya matsa kusa suka yi musabaha da Maigidan duba da irin mutuncin da suka yi masa a jiya na riƙe masa Mama  ,

Balaraben da matar sa suka sake jajanta masa kan ɓacewar Falmata a jiya ,

Cikin jin daÉ—i ya sake matso da Falmata jikin sa , yana shaida musu cewa ita ce wannan ,

Nan ya gabatar musu da kan sa , Matar sa da 'yar sa , ƙasar da ya fito da dalilin zuwan sa nan .

Inda shi ma Balaraben ya gabatar masa da kan sa , sunan sa Musa Adnan , matar sa kuma Ramlat , sai Yaran su mata biyu Hind da Zahira , Aiki ne ya kawo su nan ,  musulmai ne 'yan asalin ƙasar Kuwait .

Da murna tare da ƙauna irin ta musulunci Ramlat ta matsa ga Falmata ta kama hannun ta tare da juya harshe cikin faransanci ta gaishe ta tana tambayar ƙarin lafiyar jikin ta ? ,

Da jin daɗi Falmata ta amsa mata ,tana riƙe hannun Ramlat da ke cikin nata ,

Babu ɓata lokaci Musa Adnan yayi musu tayin ko zasu bi su strong museum? Inda zasu tafi da 'ya'yan su domin shaƙatawa ?

ÆŠan Jim Youssouf yayi , cikin son yin nazari ,shi fa bai cika son tsawaita mu'amala da mutanen da bai wani san su sosai ba

sai dai Musa ya katse masa hanzari ta hanyar bugun kafaÉ—ar sa kaÉ—an , ya juya masa harshe cikin faransanci ,

"Allez, c'est l'un des meilleurs endroits pour emmener des enfants et des familles dans la région de Rochester am sure you'll enjoy the place. ( ka zo mu tafi , yana daga cikin jerin wurare mafiya kyau domin iyali da yara a garin Rochester na tabbatar zaka ji daɗin wajen ) 

Falmata wacce daman zaman waje É—aya tsawon satika ya fara gundurar ta , ta É—an kwanto da kan ta bisa kafaÉ—ar sa ,

"BaBan Mama s'il vous plaît nous devons y aller, ( mu tafi mana ?  )

ta furta hakan tana yin ciki da muryar ta ,,

Ganin sa ya kai kan zagayayyar fuskarta da take ƙyallin da ke bayyana shaidar yanayin wajen ya amshi fatar ta ,

Ya mayar da ganin sa ga Musa dake jiran amincewar sa ,

   "Okay let's go.

Cikin motar da Musa ke jaa da kansa suka kama hanya , akan hanya hira ta sarƙe a tsakanin su , inda Musa yake sanar da Youssouf aikin sa na cruise-ship worker da yake yi ƙarƙashin company jiragen ruwa na ƙasar amurka , ya cigaba da sanar da shi irin tarin ƙasashe da garuruwa gami da tsibiran da ya ziyarta wanda aikin sa ne ya bashi damar haka .

Falmata da Ramlat ma suna Æ´ar hirar da bata cika tsawo ba saboda rashin nunan yaren faransancin a bakunan su duk biyun , yayin da ita kuma Falmata bata jin Turanci bata jin larabci yaruka biyu da Ramlat ta fi iyawa .

Basu yi tafiya mai nisa ba suka iso bakin katafaren Museum É—in , Musa shi ya yanka musu tikitin shiga ciki .

Da sanya kafar su wajen ya ɗau hankalin Youssouf da yau ya taɓa zuwa , ƙwarai tsarin gine-ginen wajen suke da ban sha'awa ,

Mama kuwa tsalle ta fara yi ganin manya-manyan liluna da kayan wasanni irin na yara masu É—aukar hankalin yaro har ma da babba .

Da gudu ta saki hannun Falmata ta bi bayan su Hind da suka riga suka yi gaban kan su zuwa wajen kayan wasanni ,

Falmata tana ƙoƙarin riƙo ta , ta zille mata ,  hankalinta tashe ta shiga ƙiran sunan ta bata so ta gusa daga kusa da ita kar ta ɓata ,

Youssouf ya kamo hannuwanta , yana fuskantar ta , yace mata

'ki rabu da itta Fatima , kayan wassan yara ne dayawa a wajen su ta gani ta tafi wurin tare suke da sauran yara,

"kar ta ɓata ko kuma ta ji ciwo Baban Mama da dai...

"shitt
yace yana É—ora mata yatsa akan bakin ta ,

"baza ta ɓata ba , zo mu tafii inda take ,

Yana riƙe da hannun ta suka nufi ciki , inda da ƙyar suka lalubo yaran da suka nutse cikin kayan wasanni ,

Mama sai ihu take me yasa aka zaƙulo ta daga cikin shirgin da ta shige ?

Musa shi yayi musu jagora zuwa shashi daban-daban na kayan tarihin wasannin yara tun na tala-taini , tare da tsoffin cartoons,

Suna tafe har suka ɓullo gaban gidan sasemet street  ,

ÆŠan murmushi Youssouf yayi yana É—age girar sa , kafin su haÉ—a baki shi da Mama wajen cewa,

"Sasemet street ?

Dariya Musa da Ramlat suke yi ganin yadda Mama take tsallen Murna , tare da ihun ƙiran sunan toys ɗin da take gani na sasemate street a waya ko Laptop ɗin baban ta da koyaushe shine cartoon ɗin kallon ta , Wanda shima kuma favorite children's show ɗin sa ne tun yana yaro hakan ya sa ya koyawa Mama ma kallon sasemate street.

"Elmo , Grover, Abby, cadabby , cookie-monster,  Big bird ..

Ta ƙarasa jera ƙiran sunayen su tana rufe bakin ta da hannuwan ta biyu , da gudu ta taka zuwa wajen ƴar ƙofar gidan Elmo ,

Tana matsa ƙararrawar ding dong ditch , ga zaton ta Elmo zai leƙo ya buɗe mata ƙofa ,

Kara ƙunne tayi a jikin ƙofa cikin 'yar muryar ta take ƙiran " Elmo , Elmo ouvre la porte ( Elmo open the door )

Dariyar da wajen ya É—auka tare da hasken camerorin da suke É—aukar ta hoto shi ya ankarar da Youssouf yawan mutanen da suka tsaya kallon shirmen da Mama ke yi cikin Burgewa ,

Dariya yayi ya taka wajen ta yana ƙiran sunan ta ,

ÆŠaukar ta yayi ,

"Mama Elmo il dort maintenant ne le dérange pas okay ?) , elmo yana bacci kar ki tayar da shi kin ji ko ?

Gyaɗa kai tayi tana waiwayen ƙofar , daga step ɗin suka tsaya Musa ya ɗauke su hoto a camerar sa , Youssouf ya kamo Falmata suka tsaya a wajen Musa ya sake yi musu wasu hotuna ,

Haka suka cigaba da yawatawa a strong museum , tsawon lokaci kafin su yada zango a wajen wasan pinball , nan wasan ya koma na manya tsakanin Youssouf da Musa , an tuno ƙuruciya , cike da nishaɗi da dariya suka dunga buga wasan pinball , kafin daga bisani su koma kan wasan retro arcada .

Sosai suka nishanÉ—antu , basu yi aune ba har lokaci yayi ta tafiya, wajen cin abinci suka yada zango,

Kowa ya nemi a kawo masa abunda zai ci , sanin da Youssouf yayi har yau ba kome Falmata da Mama suke iya ci ba dan haka yayi musu order na abunda zasu iya ci .

Daga can wani babban fili da yake a tsaftace suka samu waje gefe , Musa ya jagorance su suka yi sallah .

Hira suka cigaba da yi nan zaune bisa kan dakalin da aka yi su da kayan wasan yara yayin da yaran suka tashi suna cigaba da wasannin su da hawa kan liluna ,

Cikin hirar su Musa ke basu labarin wani tsibiri daya da ya taɓa zuwa a yankin Africa , cikin ƙasar Tanzania , mai suna BAWE a yankin ZANZIBAR,

"Bawe zanzibar yana ɗaya daga cikin tsibirai masu kyaun yanayi da namun ruwa masu ban sha'awa tare da tsirrai masu kyaun gani da taɓa zuciya da na taɓa gani  ,
     Cewar Musa ,
ya cigaba da cewa ya yawata a ƙasar Tanzania sosai , ya ga manyan namu dawa a cikin dazuzzukan su , wanda duk duniya a yankin ƙasashen Africa kaɗai ake samun irin su ,

Ya ɗora da yi masu bayani kan tsibirin Bawe da ya ƙira da dausayin duniya ,

Har wasu daga cikin hotunan wajen ya nunawa Youssouf daga camerar sa,

Karɓa youssouf yayi yana kallon wuraren da suka yi matuƙar tafiya da hankalinsa , ashe muna da irin waɗannan dausayin masu ban sha'awa a yankin Africa ?

Miƙa masa camerar sa yayi bayan ya gama ganin hotunan ,

ya É—ora ganin sa ga Falmata wacce ba ganin hotunan ta yi ba illa labaran da ta tsinci wasu abubuwan da Musa yake faÉ—a ,

Amma fuskar ta yalwace take da Kyakkyawan murmushin da ya ƙara mata kyau da haiba ,

"hannun ta ya riƙe yana murza yatsun ta ,

Yace,

" Fatima watarana zamu raya daren mu a Bawe Zanzibar island , kina so ?

Murmushi mai bayyana haƙora tayi , a hankali ta gyaɗa kai

  " ina so Baban Mama ,

Shafar kumatun ta yayi ,yana jin yadda ƙaunar ta ke sake mamayar sa , cikin tunanin sa yana hasko yadda zasu yi rayuwa a tsibirin Bawe gefen taku .

Bayan sati biyu

Cikin sati biyun da suka biyo baya Falmata ta cigaba da shan magungunan da aka É—ora ta akai cikin bin ka'idar shan maganin ,

Gefe guda sassanyar ƙauna na gudana sannu kan hankali a tsakanin su mai cike da girmamawa daga ɓangaren Falmata , tausayi da zallar nuna kulawa kuma daga Youssouf ,

Duk wani rashin sakewa da ɗari-ɗarin da take da shi ta rage , ta fara sakewa da shi , har ma tana iya bashi wasu daga cikin labaran da suka shafe ta ,  iyayen ta, 'yan uwanta da garin su ,

Jin ainahin haƙiƙanin labarin su ya ƙarawa Youssouf zallar tausayin ta , tare da tasowar mikin binnennan laifin sa ga Yakaka ,

Ya haƙiƙancewa kan sa a yanzu Falmata bata da wanda ya fi shi , dan haka ya ɗau alƙawarin kome runtsi zai bata kariya cikin kowanne hali iyakar ƙarfin sa , shi zai zama inuwar hutawar ta bayan gwagwarmayar Rayuwar da suka shiga .

Yau tun da suka tashi sallar asuba basu koma ba , zama suka yi yin addu'a sosai game da aikin da za'a yiwa Falmatan a yau da misalin ƙarfe tara na safe  , suna fatan Allah ya sa ayi aikin a sa'a .

Sai da gari yayi haske misalin bakwai , Mama ta farka ta fara neman abin karyawa ,

Kamar koyaushe Youssouf shi ya yi musu abun kari da shi da Falmatan sama-sama suka ci saboda rashin nutsuwa tare da Fargaban da suke ciki .

Takwas da rabi na safe ya yi musu a ofishin likita ,

Bayan gaisuwar da suka yi , likitan ya ƙara musu da kalmomin karfafawa ganin kamar suna tare da damuwa ,

A ƙarshe ya yi musu umarnin da su taso ya musu jagora zuwa ɗakin yin aikin inda sauran likitoci suke jiran su ,

Har bakin ƙofar dakin yin aikin da take iyakar sa ya raka ta ,

"kiyi ta addu'a Fatima , nima zan yi ta yi kin ji kou ? Ki roki Allah ya sa ayi aiki bissa sa'a , ki samu lafiya ,

Kai ta gyaÉ—a ,
  Ba tare da ta furta kalma ba ,

Fuskar ta ya riƙo cikin tafukan sa  ya Sumbaci goshinta ,

" ki shiga Fatima da Ambaton Allah ,  Allah shi baki lafiya ,

"Amin
   Ta amsa idanun ta na kawo ruwa , haka kawai take jin fargaba gani take tamkar zata iya rasa ran ta a garin neman lafiyar ido ,

ÆŠaya daga cikin nurses É—in da suke cikin É—akin ta taho ta kama hannun Falmata zuwa ciki ,

Labulen da yake tsakanin su aka yaye , ya zama Youssouf yana iya hango Falmata ta tsakanin gilashin da yayi ƙawayan ga ɗakin da take ciki ,

A shirye ya hangota tsaf, da taimakon nurses ta kwanta akan gadon da yake tsakiyar wasu fitilu masu matsanancin haske ,

Ba ɓata lokaci Manyan likitocin suka matso gaban gadon suka yi ƙawayan yayin da wasu suka shiga jona mata wasu na'urori a kai , wasun su na shirya kayan aiki ,

Aikin da ya É—auke su tsawon awa guda da mintoci arba'in , da Youssouf ya ji lokacin tamkar tsawon shekara ,

ÆŠaki na musamman aka mayar da Falmata bayan an gama yi mata aikin inda zata zauna tsawon awanni arba'in da huÉ—u kafin a kai ga mataki na gaba ,

Nan suka nemi Youssouf da ya tafi gida zata kasance cikin ƙarƙarshin kulawar su ,

Ya so yayi gardama saboda hankalin sa da yake tashe da son sanin halin da Falmatan ke ciki ,

Sai da Likitan ta ya yi masa bayani mai gamsarwa tare da kwantar masa da hankali ,

Ya sanar da shi allurar da aka mata zata sake ta nan da wasu mintoci , sai dai sun fi son kasancewar ta ita kaÉ—ai , a wannan É—akin da take zasu cigaba da bata duk wata kulawar da ta dace ,

Hankalin sa bai kwanta ba sai da ya yi masa jagora zuwa bakin ɗakin inda ya hango Falmata a kwance kan gado , an naɗe mata idanun nata da farin ƙyalle , da alama bacci take ,

Sanin da ya yi Mama bata cika lafiya ba ya sa dole ya bar asibitin tare da ita ya nufi gida da zummar dawowa zuwa anjima domin ba zai iya yin har tsawon wasu awanni masu yawa ba tare da ya gan ta ba , ya san halin da take ciki ba ,

Ko da suka dawo gida daga shi har Mama gidan bai musu daÉ—i ba ,

Mama kaɗai ya soyawa ƙwai tare da kifin gwangwani , ita ma bata wani ci na kirki ba ta ɗauke kai , Alamun ta ƙoshi ,

"Mama ki ci abinci sossai mana ,

Girgiza kai tayi tana ƙwalan-ƙwalan da ido ,

"Papa mu tafi wajen Mama yanzu ,

"zamu tafi idan kin ida cin abincin ki kin ji kou ?

Shiru tayi tana kallon sa ba tare da ta buɗe baki ta karɓi abincin da yake miƙa mata ba ,

Gajiya yayi da riƙe chokalin , ya ajiye gami da miƙewa yana jin yadda zuciyar sa ke cike da kewar ta , baki ɗayan hankalin sa na kan ta ,

Ya daÉ—e a zaune yana mata addu'a akan sallayar da ya idar da Sallar Azahar ,

Shafa kan Mama yayi wacce tayi bacci a gefen shinfiÉ—ar sallar sa ,

Cikin ran sa yana aiyana irin yawan kewar Mamar ta da tayi wanda ya duƙusar da walwalarta

ÆŠaukar ta yayi ya kaita É—aki ya kwantar tare da rufe ta da bargo , ya zauna daga bakin gadon ,

Wayar sa ya ɗauka ya latsa ƙiran layin  Tafeeda da ya yi ƙiran sa a ɗazu lokacin da ake yiwa Falmata aiki , bai samu damar ɗaukar kiran nasa ba

Bayan sun gaisa , tare da Tambayar lafiyar juna Youssouf ya É—ora da tambayar sa Leila matar sa da É—an su Imran , ?

" duk lafiya suke É—an'ouwa , Yarima kana ji na kou ?

"ina jin ka da kyau É—an'ouwa ,

" Yarima kou kana da labarin mutanen da ka baro shekarun baya a Nigeria ?

Da ace Tafeeda na gaban shi a lokacin da zai iya hango firgicin dake zane ɓaro-ɓaro bisa fuskar sa ,

"waÉ—anne mutane Tafeeda ke magana kan su ?

Tambayar da zuciyar sa ke yi ya bayyana kan harshen sa ,

Jim! Tafeeda ya yi yana nazartar firgicin da yake iya jiyowa daga Muryar Youssouf É—in ,

"wannan É—iya da tsautsayi yassa ta samu a duniya , nace kou ka sake waiwayar ta ? Tafiya ta kama ni zouwa Nigeria shine nake biÉ—ar izni kan na tai na gan ta ko da ba kai tsaye ba ne na....

Cikin sauri Youssouf ya katse sa muryar sa a É—an sama kaÉ—an ,

"Tafeeda ban ma izni ba , batun wannan É—iya ai mun jima da ajje shi ghefe kou , ka kyale kawai wani lokaci idan Allah ya ida nufi ni naje da kaina na duba ta ,

  Ajiyar zuci Tafeeda yayi ,

"tou babu kome 'dan ouwa Allah shi gwada mouna lokacin da lafiya , Allah kouma shi ƙara rufa asiri ,

'Amin Amin 'dan ouwa ,

Shiru ya gifta tsakani sakamakon tunani mai zurfi da kowannen su ya faÉ—a ,

Babu shakka Tafeeda yana da wani dalili da ya sanya shi bijiro masa da zance Mama a dai-dai wannan lokacin da tsawon shekaru wajen shidda bai taɓa tambayar sa game da lamarin ta ba sai fa yau .

a daddafe ya iya kaiwa bayan la'asar a gida , ya sake shirya Mama da ita ma duk ta damu da son su koma wajen Falmata ,

Ko da ya isa asibitin har lau bai samu damar shiga É—akin da Falmatan take ba .

Haƙuri likitar da take da Alhakin kula da ita ta bashi , akan ba zai yiwu ya shiga inda take a yau ba sai ko zuwa gobe da yammaci

Haka suka ƙaraci zama daga gefen ɗakin da take ciki har duhu ya fara shiga, dan dolen sa ya miƙe da Mama ya ƙarasa jikin ƙofar ɗakin da take ,

Ya yi mata addu'a , kafin su bar asibitin zuwa gida ,

Daren ranar bai zo masa da sauƙi ba , baki ɗaya sai juye-juye yake yi ya gaza yin baccin kirki , bai san da haka ƙaunar ta ta rarake masa zuciya ba sai da ya gaza bacci saboda damuwa da son sanin halin da take ci gami da kewar ta mai tarin yawa ,

Abunda bai taɓa jin kwatankwacin sa kan kowacce ɗiya mace ba , ko da kuwa Maimounatu ,

Salon ƙaunar da yake yiwa Fatima daban ne da yake tafe da wani irin yanayi mai tasiri sossai a gare shi ,

Sai gefen asuba bacci ya É—auke shi cike da mafarkai iri-iri , da har ya sanya shi makara wajen yin sallar asubahi .

Tara na safe suka samu isa asibitin , inda kuma cikin sa'a ya samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ƙarƙashin jagorancin likitan ta ,

Da takun ƙafar su ta san da shigowar su ɗakin da take da ita ma ta kwana cikin kewar su duk kuwa da zogi da idon ke yi mata lokaci zuwa lokaci , amma ta fi damuwa da ta san a wanne hali Mama da Baban ta suke ?

"Mama , Maama

Suka haɗa baki wajen ƙiran sunan junan su ita da Mama wacce da shigowar ta ɗakin ta hango Falmata , ta tafi da gudun ta ,

Ɗago ta Falmata tayi ta rungume ta a jikin ta , tana jin yadda sanyin ƙaunar ta ke ratsa zuciyar ta , babu shakka ƙaunar Mama magani ce ga ta ta zuciyar , 

Da murmushin samun nutsuwa ya ƙaraso bakin gadon ,

"Fatima yaya jikin naki ? Babu inda ke miki ciwo kou ? Baki cikin damuwa kouma ?

Waigawa tayi sashin da take jin tashin muryar sa ,

"Baban Mama ina kwana ? Yaya Mama ta kwana ? Bata yi ciwo ba ko ? 

ÆŠan tsayirtawa tayi , kafin ta É—ora da cewa

"bana jin damuwa ko ciwo mai tsanani , amma ina son a warware min idon nawa wannan abunda suka rufe min ido da shi yana damuna ,

"likitan da duk yana jin abunda take faÉ—i tare da taimakon na'urar kunnen sa ,

Ya matsa yana sake rarrashin ta tare da yiwa Youssouf bayani kan cewa kafin su warware mata idon zuwa gobe anfi buƙatar idon ya zauna a rufe haka , har sai bayan awanni arba'in ,

A cikin ɗakin suka wuni tare ,  sau biyu Gimbiya maimounatu na ƙiran wayar sa , ya gaza ɗaukar ƙiran . 

Bai san dalili ba amma can cikin ran sa ya gujewa yin hira da maimounatu ne saboda gudun ɓacin ran Falmata .

Washegari kamar yadda suka sharÉ—anta , awanni arba'in da huÉ—u da 'yan mintoci ,

Misalin ƙarfe goma na safe likitocin suka yi da'ira , a kan ta ,

Babba daga cikin su wanda kuma shine ainahin wanda ya yi mata aikin , shi ya warware mata idon ,

Bayan sassauta haske tare da sauya launin hasken zuwa marar kaifi , cike da fatan nasara likitan ya umarci Falmata da ta buÉ—e idanun ta ,

Babu karsashi ta fara wara idanun da suka mata wani irin nawi , hasken da ta ji kamar ya chaki idon shi yasa ta saurin runtse idanun ta kai tafukan ta biyu ta rufe fuskar ta ,

Cikin sauri likitar da ke gefen ta ta sauke hannunwan nata ,

Rarrashi da kalaman ƙarfafawa suka shiga yi mata cikin kwantar da murya , suna umartar ta da ta buɗe idon ta zata ga duniya ,

Sannu kan hankali ta ware idanun da suke rawa kaɗan-kaɗan , baƙon yanayi ne ya ziyarci ƙwaƙwalwa zuwa gangar jikin ta lokacin da raunanan jijiyoyin idanun ta suka fara ɗaukar jirkitattun hotuna suna aikawa da shi zuwa cikin ƙwaƙwalwarta da sauri ,

Wajen ya ɗauki shiru , likitocin suna ƙure ganin su akan ta da take gwale idon cike da burin son samun ƙarin ƙarfin ganin da tare kuma da son fahimtar abubuwan da take iya ganin hotunan su duru-duru , shin wannan shine hasken duniyar ? Haka kuma suffofin mutanen yake a zahiri ?

A sama ta tsinto muryoyin su lokacin da suka cigaba da yi mata magana , dusu-dusu take iya ganin kusantowar motsin wani abu kafin ta tsinkayi muryar likitan yana tambayar ta ko tana iya ganin alamun motsin sa ??

Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaÉ—a ,

Hannu ya kai yana ɗaukar wani baƙin tabarau mai haɗe da 'yar na'ura na musamman wanda cikin awanni arba'in aka yi shi domin Falmata ,

Ya sanya mata a fuska tare da daidaita mata shi , ya miƙe tsaye da murmushi a fuskar sa cike da burin nasara , ya tambaye ta ko tana iya ganin sa ?

Zuba masa ido tayi tana iya ganin shatin sa fiye da É—azu , suffar sa ta mutum ta bayyana duk da ba tarwai take iya gani sa ba ,

a hankali ta juya ƙwayar idanun ta zuwa kan kome da yake sararin wajen daki-daki take ƙure musu kallo , duk da ba sosai take ganin abubuwa ba ba kuma fahimtar su take yi ba ,

A hankali likitocin suka dare , tare da bada hanya ga Youssouf da Mama da babban likitan ya yi umarnin su shigo ,

Hannun sa yana riƙe da Mama suka shigo ,

Kamar koyaushe takun Mama ya fara isa ga dodon kunnen ta ,

Dan haka take ware ido cike da buri , burin da ada ta ɗauka ta haƙura da shi ,

'yar ƙaramar halittar da ke kusantota ta ɗorawa ido ,

Ko ba'a faɗa mata ba , ko da cewa bata taɓa ganin wata halitta da idanun ta ba , ta san wannan ita ce Mama ,

" Mama ,

Mama ta ƙira sunan ta dai-dai da ƙarasowar ta gaban ta ,

Hannuwanta biyu ta sanya ta É—ago Mama , da wani irin yanayi ta matso da fuskar Mama daf da tata bayan ta É—aura ta a cinyar ta ,

Ƙure mata kallo take yi , cike da son ganin ta fiye da yadda take iya hango ta dusu-dusu a yanzu ,

Runtse ido tayi ta buÉ—e a hankali

'Mama
   Ta ƙira sunan ta, 

Dariya Mama tayi tana É—ora 'yan hannuwanta akan hannun Falmata da take tallafe da kumatun ta ,

Ta ga hasken haƙoran Mama da fuskar ta , a yanzu ta yadda da cewa ta samu waraka , irin ganin da take yi dusu-dusu shine ganin da ta haƙiƙance kowanne ɗan adam yana yi ,

Irin haske marar ƙarfin da take gani shi ta aminta da cewa shine hasken duniya , ita kuwa mai zata yi da ya wuce godiya ga Allah da ya nufe ta da samun waraka ?

rungume Mama tayi tana faɗin kalmar Alhamdulillah , Alhamdulillah babu ƙaƙƙautawa ,

Raf-Raf-Raf likitocin da suke wajen suka É—au tafi , cike da bayyana farin cikin su na samun nasara kan aiki ,

Youssouf wanda farin cikin sa bazai misaltu ba ya tako zuwa gaban gadon Falmata ,

" Fatima
Ya ƙira sunan ta , da amon muryar da take cike da shauƙi da zumuɗi ,

cike da ƙwaɗayin son ganin Fuskar wannan ma'abocin Alheri a gare ta ta ɗago kan ta daga fuskar Mama da take ta son sake gani tamkar mai son haddace kamannin ta a ɗan tsakanin lokacin ,

Dariyar haƙoran sa ta fara cin karo da su , kafin hasken farar fuskar sa irin na Mama da ta fahimci basu kai sauran mutanen wajen haske ba , ta bayyana mata , 

Kafe shi tayi da ido tana burin ganin kamannin sa ko da kuwa ace shine abu na ƙarshe da zata iya samun nasarar gani kafin hasken da ta samu ya koma duhu da har yanzu ta gaza yadda a zahiri ne ba mafarki ba cewa idanun ta suna ganin duniyar da ta rayu tsawon lokaci a cikin ta ,

Irin riƙon da ta yiwa fuskar Mama shi ta masa , ta kai hannun ta kan sajen fuskar sa ta tallafo fuskar tana kallon sa da irin ganin da ya sawwaƙa a gare ta  ,

Dariya Youssouf ɗin ya cigaba da yi da haƙoran sa ganin yadda ta riƙe masa fuska ƙam-ƙam , kamar wanda zai ƙwace ya gudu , ko kuwa ya ɓace mata ,

Da ƴar dariyar mai tafe da amon da  ke bayyana tsantsar farin-cikin ta , ta kai goshin ta ta haɗa da nashi , tsinin hancin su na gugar na juna ,

"Baban Mama nagode , nagode nago...

  "Fatima ki godewa Allah da ya baki lafiya , ni ma shi nake godewa , da ya nufa aka cimma nasarar aiki ,

Zama yayi daga gefen ta a bakin gadon ,

Mama tana tsakiyar su ya sanya hannu sa ya kewaye su da shi ya rungumo su jikin sa , yana jin matsanancin farin-ciki na zagaya ruhin sa ,

Tamkar a ire-iren shuÉ—aÉ—É—un lokutan da suka wuce cikin rayuwar ta da Yakaka , sautin ta ya bijiro cikin tunanin ta tamkar a lokacin take furta mata ,

" Falmata na ina ji a jikina watarana za ki warke , za ki ganni kamar yadda nake ganin ki .

Hawaye masu ɗumi suka silmiyo ta ƙarƙashin gilashin idanun ta , kewa tare da ƙaunar ahalin ta suka bijiro mata , a sarari ta furta

" Allah ya jiƙan ku Baba , Mama , Yakaka,  Bakura da Baana ,

'Amin 

Youssouf ya amsa mata .

*****

Cike da tarin sabbin dokoki da sharaÉ—in ziyartar likita a duk bayan mako guda na tsawon watanni biyu ,

Suka samu sallama daga asibitin , tafiyar ƙafa suka yi zuwa gidan su , inda Falmata ta dunga bin titi da ganin ta marar ƙarfi ,

Murna fal cike da zuciyoyin su ita da Youssouf , kome ta hango shatin sa sai ta tambaye shi wannan abun menene shi ? Meye sunan sa ?

Shi kuma babu gajiyawa cikin jin daÉ—in tambayoyin da take masa yake bata amsa tare da faÉ—a mata sunayen abubuwan .

Ƙofar gidan Musa suka tsaya , farin cikin da zukatan su ke ciki ya tunbatsa so suke su yi ɗaukanin sa da wani , alhalin babu wani nasu makusanci tare da su , dan haka gidan Musa suka yada zango ,

Musa da Ramlat sun taya su murna sosai inda a ƙarshe har 'yar walima suka shirya musu nan cikin falon su,

Yana riƙe da hannunta suka shigo gida ,

Suna shiga tun kafin su zauna ta ce  shi ,

"Baban Mama ka ƙira Hajja a waya na faɗa mata na warke nima yanzu ina gani ,

Yana murmushi ya zaro wayar sa daga Aljihun sa ya shiga lalubar layin Hajja ,

Ya san dole tana neman wani makusanci nata wanda zata raba farin-cikin ta da shi ,

Nigeria

Tsawon satikan da suka biyo bayan Rayuwar Yakaka tayi su ne wajen ganin ta cigaba da ƙokarin wanke laifin ta daga idanun jama'ar gidan Prof ,

Babu inda take zuwa kullum tana gida ita ke yin mafiya yawan aiyukan gidan ,

A hankali Hajja ta fara fahimtar kyawawan É—abi'un Yakaka , na kawaici da gudun tashin hankali , sannan kuma me sakakkiyar fuska ce ma'abociyar murmushi ,uwa uba yawan ibadar da ya zauna mata .

Hakan ya sa ta fara sakar mata fuska har takan É—an ja ta da hira a wasu lokutan ,

A yau ma zaune suke , suna 'yar hira Yakaka tana taya Hajja tsinke ganyen zogalen da zata yiwa Prof girki da shi

Wayar Hajja da take ajiye a gefe ta ɗau ƙara ,

Da sauri Yakaka ta ɗau wayar ta miƙa mata ,

"Ni hauwa'u waye ke ƙirana da wannan sanyin la'asar ɗin ? Allah jishe mu Alheri ,

ɗaga ƙiran tayi dai-dai da ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi , Yakaka ta miƙe da saurin ta tana cewa

" Oyoyo Rahima .

Ta nufi ƙofar ,

"Assalamu Alaikum Hajja ni ce Falmata ,

Muryar Falmata ta karaÉ—e kunnen Hajja ta cikin wayar ta mai maÉ—aukakin sauti ,

Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye ɗingis-ɗingis ta nufi ɗakin ta da yake gefe ,

"Lale Lale Marhabin da uwarÉ—akina Fatima mutan turai ,

Ta furta hakan lokacin da take ƙarasa shigewa ɗaki cike da son kar Yakaka ta san da wacce take waya ,

" UwarÉ—akina ince dai duk kuna lafiya ? Ya Babban soja tare da 'yar rigima Mama , dafatan an samu nasara wajen neman magani ?

"Hajja Alhamdulillahi ki taya ni murna , na warke Hajja na samu lafiyar idona ,

"Da gaske Fatima kai Alhamdulillah nayi murna , nayi murna Allah Abun godiya kin warke Fatima ,? Buwayi gagara misali ,

Murnar Yakaka ta rikiɗe zuwa Fargaba lokacin da idanun ta suka sarƙe cikin na Sofi matar Yaya Dakta ,

Kallon-kallo na daƙiƙoƙi suka yiwa juna kafin ta tsinkayo muryar Doctor Hamza wanda yake tsaye daga bayan sofi ,

  "Malama kauce ki bada guri mutane su wuce kin yi wani sanƙanƙam a tsaye kina zarewa mutane ido ,

Da sauri Yakaka tayi baya tana komawa falon ƙarƙashin rakiyar mummunan tsakin da sofi ta bita da shi .

Ɗan diri-diri tayi a falon rashin ganin Hajja yasa sum-sum ta nemi mafakar ta a can ƙarƙashin kafar benen da yake falon ta samu guri ta zauna ran ta duk a dagule .

"Me ya sake dawo da shi yau kuma ? har ma da matar sa ?

Daga inda take tana iya jiyo tashin Muryar su ,

Da Sallamar da Docto Hamza ya yi ,

Basu ko zauna ba Sofi ta fara faÉ—in

"Wannan kuma wacce jemammiyar 'yar aiki aka samu haka a gidan nan ? Sai tashin ƙarnin man masu bleaching take ,  Doctor ba dai ita take yin wanke-wanke ba , ? Dan bana jin zan iya riƙe ko chokalin da ta wanke ,

A kaikaice Doctor hamza ya dube ta yana samarwa kan sa mazauni akan kujerar falon mai cin mutum guda ,

Motsa laɓɓan sa yayi kamar zai ce wani abu sai kuma yayi biris da ita yana zaro wayar sa daga Aljihu ,

Hannun kujerar da ya zauna ,Sofi tayi matsuguni a É—osane tana cigaba da cewa ,

"Ni kamar ma nasan Fuskar ta a wani waje ?

A hankali ya ɗago kai yana duban ta da ita ma ta karkato gare shi , fuskar ta ɗauke da wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai da bai kai ga sanin dalilin samuwar sa ba ,

" akan wa kike magana ne ?

" wannan yarinyar mai kama da farar kura , "

Ta furta hakan lokacin da tunanin ta ya gama tuno mata da inda ta taɓa ganin Yakaka a gidan Samy baby ,

Dariya ce ta so kama Doctor Hamza jin an kwatanta Yakaka da farar kura ,

     " ko ina sofin sa ta san wannan gantalalliyar yarinyar ?
       Ya tambayi kansa a zuci .

" okay ,

Yace a taƙaice yana mayar da hankalin sa ga fuskar wayar sa ,

"irin karuwan nan ce masu tsayawa a bakin hanya suna ne...

Fitowar Hajja cikin Murna ya katse mata zance da ta É—auko yi ,

" a a' ah Babban likita kaine tafe iwar haka ? Sannu da zuwa sannu da zuwa ka sha hanya tun daga birnin tarayya,

Da 'yar fara'a Doctor Hamza yake amsawa Hajja gaisuwar da take masa ,

Hajja ta ɗora ganin ta kan Sofi wacce ta jirkita sosai kan kafaɗun Doctor Hamza kirjin ta daf da fuskar sa , fiye da rabin cinyar ta na kan jikinsa ,  kan ta a ɗage sai shan ƙamshi take , ko ƙala bata cewa Hajja ba , "ah to wacece ita 'yar aikin zata gaisar ?

Ƙanƙan da ido Hajja tayi ,

" Yau ina ganin taɓara maigida da kukan tsarki , mene haka wata shaɓatartar da ke kin wani ɗaɗɗane ɗan mutane ƙin kalmashe shi ? O ni hauwa'u inda ranka ka sha kallo , ikon Allah 'ya'yan zamani , mu lokacin mu ina muke iya ɗaga ido mu dubi miji a gaban mutane ?

Cike da 'yar kunya doctor Hamza ya miƙe bayan ya ture Sofi daga jikin sa ,  yace ,

" Rahima bata nan ko Hajja ? A É—an sama mana abinda zamu ci please ina tare da yunwa ,

" Rahima bata nan likita , bata ƙaraso ba daga Makaranta , to babu laifi yanzu kuwa za'a samar da abinci ,sannun ku da hanya ,

Wani banzan Kallo Sofi ta jefawa Hajja tana bin bayan mijinta , cikin ranta cike da haushin kalaman Hajja , cikin ran ta tana cewa ,

"ji min tsohuwar nan da kinibibi ? Ko ina ruwanta da ni ," ? Idan har ta ce zata shiga harka ta kafin na bar gidan nan sai na ratsa mata tarbiyya ,'

" Mts
  Hajja ta saki tsaki bayan barin su falon
, "abun haushi Nama na jan kare ,  me ake da mace marar kunya da kamun kai ? Kunya ai ado ce .

Murnar labarin da Falmata ta bata na samun warakar ta ya taso yayi awon gaba da takaicin da sofi ta bata ,

*****

Washegari bayan Doctor Hamza ya shirya kai tsaye ya nufi yin abunda ya kawo shi garin .

Bayan ya je sun gaisa da Prof shi da Sofi , daga bakin mashigar sashin Prof ya dakatar da ita daga binsa ,

" Sofi ki koma ciki , ni fita zan yi sai na   dawo ,

Zunɓur-ɓur ta turo baki ,
   Cikin salon da koyaushe take amfani dashi idan tana gaban shi na ƙoƙarin ta nuna masa ƙuruciyar ta da a zahiri ta riga ta yi mata adabo ,
        A shagwaɓe tace

"Haba mana Doctor please zan bika mu tafi tare naga gari , ka ga fa irin yanayin gidan shiru ba...

"please Sofi kar ki ɓata min lokaci a banza ai kin san yanayin gidan babu abokin hira kika dage sai kin biyo ni , kuma ni wajen aiki zan tafi ba yawo a gari ba ,

  Juyawa yayi ya ƙarasa ga motar sa ya shige ciki bai ko sake waigowa ta kan ta ba ya tada motar yayi tafiyar sa ,

" jagale ! Tayi a tsaye ranta cike da ƙuna ,
    "so take ta san meye Doctor yake ƙullawa a garin da yake ta zirga-zirga a tsakanin Maiduguri da Abuja ,

Cikin wata guda wannan ne zuwan sa na uku , ita fa duk wani abu da zai sha gaban ta , ya mata katanga kome ƙanƙantar sa da Doctor Hamza yaƙi take yi da koma menene ,

Ko aikin sa dan bata da ikon hana shi ne amma da tuni ta shata layi tsakanin su , so take koyaushe ya zama bashi da uzuri sai nata ,

A fusace ta juya ciki ,

****

Kai tsaye gidan Amne ya nufa , ya taddata tana karin kumallo da Fankaso da miyar gandar ƙafar sa ,

Ya gaishe ta cike da ladabi , ta amsa tana mai farin-cikin ganin sa ,

Tambayar sa tayi ya safiyya ?

Ya shaida mata ai tare suka zo garin .

"Shine kuma baka kawo min ita mun gaisa ba ?

Ta furta haka lokacin da take zuba masa miya akan fankason da ta zuba masa ,

"Amnee fita zamu yi tare zuwa wani waje ,

Ya furta haka lokacin da yake kai lomar farko bakin sa.

" ina kuma zamu ? Allah yasa dai Lafiya .

"lafiya lau Amne sai Alheri ,

cikin nutsuwa ya gama cin abincin sa ,

Bayan ya wanke hannu , yace

"Amne zamu iya tafiya yanzu ko kina da wani uzurin da zaki yi ?

"ba abunda zan yi , amma tukun wai ina zaka kai ni ? Kaƙi sanar da ni .

"kiyi haƙuri Amnee mu je ki gani ,

"to bari na yafa mayafi na ,

Tare suka fito shi da ita ya buÉ—e mata gidan baya na mota ta shiga ya rufe , gami da zagayawa ya shiga ya tada motar yana barin unguwar ,

Ya riga ya gama tsara hanyoyin da zai bi domin ganin ya dai-daita lamarin iyayensa , wanda daman burin sa ne tun ma kafin bayyanuwar Khaalty Rahima a gare shi ,

Bayyanar ta ya sauƙaƙa masa lamarin , ya kuma ji daɗi domin yasan dawowar ta a dai-dai lokacin matakin nasarar gyaruwar kome ne wanda hargitsewar kome yake da nasaba da ita ,

Bayan duk lallamin da yayi mata akan  ya mayar da ita gida , amma taƙi amincewa ,

Cikin dogon nazarin da yayi ya yanke shawarar haÉ—a su kitsumun , ba tare da sanin kowaccen su ba .

Dan haka a yanzu da ya É—au Amnee kai tsaye ya nufi gidan da Khalty Rahima take ba tare da ya sanar da kowaccen su game da 'yar uwarta ba .

Suna 'yar hira shi da Amnee har suka iso ƙofar gidan , ya fita a motar ya nemi iznin shiga gidan daga maigadi inda ya amince nan take har ma yake sake jaddada masa , ai kuwa Mamar Bulama tana ,

Tare da Amnee suka shiga wacce take cike da mamakin ina Hamza ya kawo ta ? Gurin wa suka zo ? Allah dai ya sa lafiya ,

Shi ya fara shiga sashin da Khaalty Rahima take , daga bakin ƙofa ya dogare ,  yana fuskantar Cikin gidan

daga inda yake yana hango Khaalty Rahima wacce ta duƙufa yin wanki daga gefe ,

Babu Alamun ta san da tsayuwar sa a wajen ,

"Bissmillah Amnee shigo ,

" Assalamu Alaikum ,

Amne ta ce lokacin da ta shigo filin gidan ,

Dai-dai da É—agowar Khaalty Rahima wacce sautin Hamza ya ankarar da ita tsayuwar shi a wajen ,

Zuciyoyin su suka buga da wani irin yanayi mai girma , daga ƙasa har sama Amnee take kallon ta ,

Kowanne irin jirkituwar halitta ce ta samu Rahima ƙanwar ta , ba zai sa ta gaza gane ta ba ,

"Rahma,  Rahmatullah ,

Ta ƙira ta da wani ɗan guntun sauti ,

"Rahmatullah hal hdha haqiqiun lak 'Yaa ukhtee ? ( shin dagaske ke ce 'Yar uwata ? )

A hankali ta saki rigar hannun ta da take wankewa  ,

Da hannu biyu Amnee ta rufe fuskar ta lokacin da hawayen farin-ciki ya fara zarya akan fuskar ta ,

Bata jira ƙarasowar Rahima ba wacce take tahowa da sassarfa , ta taka da sauri ta tadda ta ,

Rungume juna suka yi hawayen murnar ganin junan su na sauƙa ,

Khaalty Rahima bata san haka take cikin maricin tare da kewar 'yar uwar ta , yayar ta , madadin uwa agare ta ba sai yanzu da ta gan ta tsaye a gaban ta bayan tsawon shekaru fiye da ashirin da suka kwashe basa tare .

Hannu biyu Amnee ta sa ta riƙe fuskar Rahima ,

"ke ce wannan Rahimatullah ? Meyasa kika tafi kika barni ? Kina garin nan Rahimatullah duk tsawon shekarun nan bakya nema na ? Meye na miki mai girma haka Rahimatullah  ?

"Rahimatullah wacce irin Rayuwa kike yi tunda kika barni ? Nan ne gidan ki ? Kin yi aure ne ? Ina maigidanki ? ki min magana mana ƙanwata

Muryar Doctor Hamza ta ratsa tsakani , shi da kansa ƙwalla ta taru masa a ido , irin ƙaunar da yake hangowa a fuskar kowaccen su ga 'yar uwar ta , ta masa yanayi da na yaran nan biyu 'yan gudun hijira .

"Amnee ki kwantar da hankalin ki , Khaalty Rahima ta gamu da larura tana jin magana amma bata iya mayarwa ,

Sabon Kuka Amnee ta fashe da shi ,

"Rahimatullah ce ta kurunce ? Meye haka ya faru da ke Rahimatullah ?

Cikin ruÉ—ani ta waiga ga Hamza

" mu tafi asibiti a duba min ita yanzu Rahimatullah Amana ce a wajena ,

Da sigar rarrashi khaalty Rahima ta jijjiga hannun Amnee da yake cikin nata ,

Waigowa tayi tana kallon ta ,

Murmushi tayi mata , ta kai hannu ta goge mata hawaye tana girgiza mata kai ,

ƙoƙarin taro ta Amnee take lokacin da ta ga tana ƙoƙarin tsugunnawa ,

tare suka durƙusa ,

Khaalty Rahima ta rubuta mata a ƙasa cikin yaren su ,

"ki daina kuka , murna yakamata muyi da sake ganin junan mu Yaa Amina .

Bayan Awanni biyu

Doctor Hamza , tare da Amnee da Khaalty Rahima da Bulama suka kama hanyar komawa gidan Amnee.

Ga mamakin Hamza Khaalty Rahima bata yiwa 'yar uwarta irin tirjiyar da tayi masa kan komawa gida ba ,

Ko daman dan bata ga 'yar uwar tata bane a gaban ta ?

abunda ya ɗan riƙe su a gidan shine batun tafiya da Rahima da ɗan ta da suka yi wanda da farko matar da khaalty Rahimar take yiwa aiki bata Amince ba .

sai da suka bata gamsassun bayanai tare da ƙwararan hujjoji ta kuma ga shaida tare da Amincewar ita kanta Khaalty Rahimar tukun ta yarda ta sallami Rahima tare da yi mata fatan Alheri .

Da shigar su gida Amnee ta shiga hidimar Khaalty Rahima , kama daga shirya mata wajen zama na musamman har zuwa gyara mata shimfiÉ—ar da zasu kwana ita da É—an ta.

Abunda ya sake bawa Hamza tausayi shine duk inda Amnee ta gusa , Khaalty Rahima zata matsa kusa da ita tana yunƙurin karɓe aikin da take yi , Amnee taƙi sakar mata ,

banda murmushi mai cike da tarin ƙauna da tausayi babu abunda suke yiwa junan su .

Sai da Amnee ta gama gyara musu waje tsaf sannan ta dawo ta zauna kusa da Rahima , ta riƙo hannun ta tace ,

"Rahimatullah ina son jin labarin yadda kika yi rayuwa bayan barin ki gida , amma babu dama a yanzu , inshaAllah daga gobe zaki fara ganin likita ,

Gyaran murya Doctor Hamza yayi ,

"Amne

Ya ƙira sunan ta , a hankali ta waigo gare shi ,

"Amnee ina son dan Allah yau ki bani labarin abunda ya faru da rayuwar ku ke da Baba da Khaalty Rahima ? Dan Allah kar ki ƙi , ki ban labarin a matsayin tukuicin dawo miki da Khaalty Rahima da nayi .

Shiru tayi na wani ɗan lokaci , kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ,

***

"Labarin ba wani mai daÉ—i bane da kake naciyar sanin sa ,

"Kamar yadda ka sani ne mu 'Yan asalin ƙasar Chad ne daga Babban birnin N'Djamena , inda aka haife mu , iyaye da dangin mu baki ɗaya. 

"Mahaifin mu sajjan ne ( mai gadin gidan yari )  a babban alsijn na ƙasar mu , albashin sa bai cika yawa ba dan haka mai ƙaramin ƙarfi ne sosai , dangin sa duk talakawa ne ,  haka ma mahaifiyar mu ta fito daga gidan talakawa sosai , sana'ar iyayenta sarrafa gishiri daga bakin teku su kawo cikin gari su sayar ,

ni ce Babbar  'yar su sai ƙanne na maza huɗu "Salihu , Mohammed , Usman da Jamil  sai ƙaramar mu Rahimatullah .

"Rahimatullah tana shekaru biyar ni ina da goma sha shida Mahaifiyar mu ta rasu , inda ba'a ɗau lokaci ba bayan mutuwar ta Maifinmu ya sake yin aure , ya auri wata mata mai 'ya'ya huɗu daga ƙabilar N'gambaye mabiyar Adinnin Christian ƴar ainahin ɗarikar Roman Catholic .

"zuwan "Aichawa rayuwar mu shi yayi sanadiyyar faɗawar mu ƙunci domin Aicha irin mugayen matan nan ce marar imani , babu irin aikin wahalarwa da bata sanya mu , Su salihu sun zame mata masu nemo mata kuɗi , inda ni kuma na zama baiwar ta mai yin duk wasu aikin cikin gida,

hatta Rahimtullah da take ƙanƙanuwa bata tsallakewa izaya daga hannun Aicha ba .

"shi da kansa Mahaifin mu bai tsira ba daga bala'in ta dan a wasu lokutan har duka take yi masa , idan ta nemi kuɗi bai bata ba, hakan ya sa yake masifar tsoron ta ba shi da kataɓus , ya auro jaraba .

"mugun neman kuɗi irin na Aicha ya sa nima ta sama min aikin goge-goge a babban ofishin jakadancin ƙasar mu tun a wancen lokacin da ba'a cika barin 'ya'ya mata fita neman kuɗi ba ,

"karatu ma alokacin iyakata primary ban ci gaba ba . 

"da murna na fara zuwa aikin saboda ganin zan huta daga masifar Aicha da wahalar aikin gida , sai dai kuma tunanin Rahimatullah da zan dunga bari a gida ya rage min karsashi ,

" ganin cewa aikin nawa shara ne da goge-goge sai na nemi iznin na dunga zuwa da Rahimatullah tana zama a gefe ni nayi aikina , saboda nasan idsn na bar ta a gida azaba za'a dunga gana mata , cikin sa'a aka amince min .

"Tafiya ce miƙaƙƙiya a ƙafa daga unguwar mu zuwa wajen aikina , amma haka nake goyon Rahimatullah daga alfijir ya keto mu ɗau hanya , kafin lokacin da muke isa gari ya waye sosai ,

"Haka zan yi aikina Rahimatullah tana ƙiriniyar ta ,

"Rahimatullah irin yaran nan ce masu son wasa , hakan ya sa sai ina aiki ina kaffa-kaffa da ita kar ta yi musu ɓarna dan wani lokacin ma sai na neme ta na rasa ta shige ƙarƙashin tebura ko tayi wani wajen ,

"Amne ta tsagaita tana duban fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi ,

"Ashe Bulama ba a ƙasa ya tsinta ba gado yayi ,

  Doctor Hamza ya kitsima hakan a ransa ,

Amnee ta cigaba da cewa ,

"Na ɗau tsawon watanni shida ina aikin goge-goge a ofisoshin guda biyar kafin a rage min yawan su zuwa kula da ofishi biyu rak , na wata mata Basudaniya ( Sudanese )"Mademe Laura , da kuma na wani jakadan ƙasar Nigeria "Al-Mustafa Dilmari .

"tsakanina da su Gaisuwa msi cike da girmamawa ne idan sun iso ofis sun tarad dani a bakin aikina ,

"wata alaƙa bata taɓa gifta tsakanin mu ba sai Ranar da Rahima tayi wata mummunar ɓarna a ofishin Ambassador Mustapha , inda ta yayyaga wasu takardu masu muhimmanci da ya mance ya tafi ya bar su a ofishin sa ba tare da ya adana su ba ,

"Ranar na shiga tashin hankali domin kuwa faɗa sosai ya dunga yi min , bai tsagaita ba sai da Rahimatulla wacce take goye a bayana , saboda zamu tafi ƙiran sa ya cimmin , ta leƙo da kanta cikin harshen larabci ta ce da shi yayi haƙuri ya daina yi mana faɗa irin yadda Aichatuwa take yi mana kullum ai ita ta yaga takardun tana so ta yiwa ƴar tsanar ta kaya ,

"Ban san dalili ba sai naga ya sassauta fishin sa , a ƙarshe yace mu tafi kawai ,

"tun daga ranar sai naji tsoron sake zuwa da Rahima domin kar tayi wata ɓarna sa zata sa a kore ni daga aikin wanda albashin sa a lokacin da shi nake yi mana hidimar yau da kullum  ni da ita duk kuwa da cewa kaso uku Aichatuwa take raba albashin ta ɗau kashi biyu da rabi ta bani guntun ,

"daɓ dole nake barin ta a gida tana kuka , wani lokacin nima har ta saka ni ƙwalla , nake tafiya na bar ta ,

"ba'a yi sati guda ba wata safiya har na kammala aiki zan tafi , Ambassador Al-mustapha ya ƙira ni , zuciyata cike da tsoro na je na ɗauks batun laifin Rahima ne bai wuce ba ko kuma ni ce na sake yin wani laifin .

" ga mamakina sai naji yana tambayata ina ƙanwa ta take meyasa na daina zuwa da ita ?

" na ce masa tana nan , inajin tsoron kar ta sake ɓarna shiyasa na daina zuwa da ita ,

" sai ya umarceni da mu cigaba da zuwa tare amma na dunga lura da ita kar ta dunga yin ɓarna ,

"shikenan Tun daga ranar na cigaba da zuwa da Rahima ,

"a hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Ambassador Al-mustapha da Rahimatullah saboda 'yan kayan maƙulashe na yara da yake mata hasafin su ,

"kafin wasu watanni shaƙuwar su da Rahima ta shafeni wanda a ƙarshe cikin shekara guda tsakanin mu ya rikiɗe ya zama soyayya ce mai ƙarfi ,

"duk kuwa da tazarar matsayi da yake tsakanin mu hakanan Allah ya kulla auratayya a tsakanin mu , bayan rigin-gimu da suka taso daga dukkan ɓangarorin biyu , daga Aichatuwa , da bangaren iyaye da 'yan uwa Al-mustapha na jini , wanda suks tirje akan ba zai auri 'yar wata ƙasa ba wacce ba ƙabilar su ta kanurai ba , alhalin ga 'yar uwarsu wacce take dakon jiran sa suyi aure ,

"hakanan ɓangaren Aichatuwa wacce ta bi duk wata hanyar da zata iya bi domin ganin auren mu bai yiwu ba da Mahaifin ka , amma dayake shi aure Kaddara ce daga kaddarorin da Allah yake yi ga bayin sa .

"A ƙarshe aka ɗaura Auren mu ni da Mahaifinka tare da Amincewar kakan ku wanda ya taka har ƙasar mu ya nemawa ɗan sa aurena cikin mutuntawa , bai duba ƙasƙancin mu da shi yake babban Attajiri a ƙasar su kuma mai ilmin addini da na boko tun a wancen zamanin .

" Bayan auren mu mun zauna shekara guda a N'Djamena kafin aikin mahaifin ku ya ƙare da ƙasar mu , muka kuma fara shirin komawa ƙasar su ,

"a kuma tsukin wannan lokacin Allah ya yiwa Mahaifin mu Rasuwa sakamakon sukar sa da wuƙa da wasu ga cikin 'yan firsina suka yi a ƙoƙarin su na gudu daga gidan yari .

"Mutuwar Baban mu ta gigita mu ganin cewa duk wani gatan da muke da shi ya ƙare ,

"a ƙarshe dole muka haƙura , riƙon Rahima kachokam ya dawo hannun mu da duk wasu ɗawainiyar ta Al-Mustapha ke yi ,

"Sauran ƙannena maza suka raɓu da gidajen 'yan uwa  , ,

"Ba mu jima ba bayan nan muka koma Nigeria tare da Rahimatullah da   kuma kai a lokacin kana ɗan jariri .

"na fuskanci tsangwama da ƙiyayya iri-iri daga kakar ku , da dangin mahaifin ku da baki ɗayan su basa ƙaunar auren mu , idan aka ɗauke Salman wanda ƙani ne na uku ga mahaifin ku da shi babu ruwan sa da duk wasu lamura da suka shafe ni .

"Haka shekaru suka yi ta tafiya tare da nasarar rayuwa , matsala mafi girma da ta zama sanadin rabuwar auren mu da mahaifin ku ya samo asaline daga lokacin da Soyayya ta shiga tsakanin Salman da Rahimatullah ,

"lokacin Rahima ta gama makarantar gaba da primary , kai kuma ka shiga makarantar kwana ta gaba da primary ,

"rikicin an É—auki lokaci ana yin sa tun bayan bayyanuwar soyayyar su da suka yi shekaru biyu suna boyen ta a tsakanin su ,

"Salman ya doshi mahaifiyar su da sauran 'yan uwan sa da batun auren Rahimatullah , ƙaramin yaki aka yi a tsakanin su saboda lokacin kakan ku ya jima da rasuwa .

"Lamari yayi tsamari da yasa har kakar ku ta ƙira mahaifinku ta masa kashedi kan muddin yana son Albarkar ta , ya zama dole ya raba tsakanin ƙanwar matar sa da ƙanin sa ,

"daga lokacin shima Mahaifinku ya fara nuna adawar sa da soyayyar tsakanin Salman da Rahima domin bin umarnin Mahaifiyar su , da hakan ya kawo saɓanin a tsakanina da shi domin ni ɗari cikin ɗari nake tare da su akan lamarin soyayyar su .

"ana cikin wannan hatsaniyar uwar matar da aka so aurawa Mahaifin ku wacce take ƙanwar kakan ku ce ta zo da wani lamari mai yanayi da tsafi ko kuwa chanfi  , kan cewa muddin ba'a yi gaggawar raba tsakanin Salman da Rahima ba to babu makawa guda a tsakanin su zai mutu , domin Malamin ta yace babu aure a tsakanin su , '

"Maganar bata ɗaga min hankali ba sai da naga kamar Mahaifinku ya yarda da batun inda har ya fara maganar ko dai Rahimatullah zata koma N'Djamena na ɗan wani lokaci , idan kome ya lafa ta dawo ,ranar nayi kukan Maraicin mu da rashin gatan mu  ,

" an yi haka bai fi da wata guda ba , Rahima ta gama shan kukan ta akan wannan batun , Babban Al'amari ya afku,

"Ranar wata juma'a bayan Rahimatullah da Salman sun gama hira da rabin ta neman hanyar warwaruwar matsalar su suke tare da kaiwa ga cikar burin su ,

"ƙarfe biyu da rabi na ranar bayan sallar juma'a labarin Rasuwar Salman Dilmari matashin Saurayi, ya bazu tare da yin tambari a baki ɗayan birnin Maiduguri kasancewar sa matashin ɗan siyasa da ya yi suna a lokacin ,

"ya rasu a sakamakon mummunan haÉ—arin mota da yayi akan hanyar sa ta komawa daga masallacin juma'ah mintoci arba'in da rabuwar su da Rahima ,

" mutuwar data girgiza zukata da dama , ta kuma bar miƙi a zuciyoyin wasu da dama , Salman Mai Alheri ne , Allah ya gafarta masa ,

Shiru ne ya ratsa tsakanin su saboda kuka haiƙan da Rahima take yi , kukan tasowar tsohon miƙin dake zuciyar ta da ya tarad sabon ciwukan dake cin ranta a kullum kwanan duniya ,

Mutuwar  mijinta uban 'ya'yan ta da ta tarar da gawar sa a yashe cikin gona , haka kuma tana ji tana gani ta tsallake shi domin ceton ranta da na 'ya'yan ta ta tafi ta bar gawar sa a daji,  tare da ɓacewar manyan 'ya'yan ta da har yau bata da sanin haƙiƙani kan rayuwar ko mutuwar su ta ma fi haƙaƙewa akan Yakaka da Falmata sun mutu kamar yadda harsashi ya samu Baana yayar Bulama ta mutu akan cinyar ta ,

Bakin lafayyar ta Amne ta sanya ta sharewa Rahima hawaye sannan ta cigaba da cewa ,

"Fasalta irin halin da baki É—ayan zuri'ar Dilmari ta samu kanta a ciki bashi yiwuwa ,

  "ai ka san lokacin kana da wayo sosai kana secondary School ,

gyaÉ—a kai Hamza yayi wanda idanun sa suka yi jaa ,

" Rahima ta shiga ɗimuwa marar misali domin har suma ta dunga yi , sai da Maigadin gidan ku na lokacin ya dunga yi mata rubutu , cikin sati guda da mutuwar sa Rahima ta rame tamkar majiyanciya , ni da kaina ƙarfin hali nake yi , nake hana kaina tunani saboda tsohon cikin Rahima ƙarama da nake ɗauke da shi .

"abu mafi muni da ya biyo bayan mutuwar Salman shine takowa da 'yan uwansa suka yi har gida bayan kwana arba'in da mutuwar sa , suka ci mutuncin mu ni da Rahima , a ƙarshe suka danganta mutuwar Salman da cewa ni da Rahima muka lashe masa kurwa muka kashe shi , to waye ya san salsalar asalin mu ??

"Ni kuka Rahima kuka , sannan abun takaicin mahaifinka yana zaune ya gagara hana su ko ɗaukar wani mataki na ba mu kariya , wanda hakan ni kuma ya tunzuro ni , na yunƙuro domin maida musu martani a karon farko bisa duk abubuwan da suke min marasa daɗi ,

"Ga maɗaukakin mamakina sai mahaifinka ya hayyaƙo min ya takore ni daga yin magana har ma yace muddin nace wani abu kome zai iya faruwa ga igiyoyin auren mu ,

"bisa tilas nayi shiru sai hawaye da muke yi ni da Rahima suka gama zage mu tas har da dungurin Rahima da alama ma duka suke da niyyar yi mata sai É—an uwansu ya rarrashe su ,

'tundaga wannan ranar Rahima ta sake yin sanyi duk ta susuce firgici ya bayyana cikin suffar ta bata da aiki sai tunani   ,

"duk da ceqa ina bin duk wasu hanyoyi domin kwantar mata da hankali duk da cewa nima hankalin nawa a tashe yake domin tsakanina da Mahaifinku babu daɗi , nema yake ƙarfi da yaji ya raba Rahima da gidan sa wanda nasan zugar 'yan uwansa ne da ni kuma ko kusa bazan lamunta ba , idan Rahima ta bar wajena ina zata ??

"har zuwa safiyar wata rana da na wayi gari Rahima kin yi gaban kan ki wajen barin Rayuwata , kin tafi kin barni cikin tashin hankalin da ya tunkuɗo min da naƙuda ,

"kika tafi ba tare da kin yi tunanin me hakan zai haifar ba cikin rayuwata ,

"duk wani wajen da nake tunanin zaki je Rahima naje neman ki har ms da wuraren da baza ki ba naje neman ki ,

" a cikin halin nan na matuƙar tashin hankali na haifi jaririyata da tun lokacin da na haife ta na shaidawa mahaifinku sunan ta Rahimatullah .

" da É—anyen jego na dunga fita kusufa-kusufa neman ki da hakan ya tunzuro Al-Mustapha yace muddin na sake fita neman ki da kaina a bakin auren mu ,

" a wannan ranar nima zuciyata a taurare take da zafin rashin ki dan haka nima na taso masa , a take a wajen na nemi da ya sawwaƙe min auren sa tun a nan domin kuwa fita neman ki yanzu na fara har sai ranar da na ganki ,

"shima da alokacin yake ganin zallar laifin ki na cewar ai ke da kan ki kika ga damar tafiya dan haka zaki dawo ,

"a fusace a wajen ya datse igiyar auren mu ba tare da yayi la'akari da irin raunin dake tare da ni ba ,

"Ban kwana a gidan ba na tafi tare da jaririya Rahima , na bar masa Hafsa da Zainab Hamza kuma yana makaranta,

" nayi neman ki Rahimatullah har N'Djamena naje an tabbatar min da baki zo ba ƙarin tashin hankalina shine duk sauran ƙannena a cikin matsanancin talauci suke ,

" Na tattara musu duk wasu 'yan kuɗaɗen da na tafi da su na basu , na sake dawowa Nigeria , tare da taimakon ƙawayena biyu Hajiya Hadiza da Hajiya yaana , na sayar da tarin sarƙoƙi da ƴan kunnayena zuwa wara-waren zinare da nake da su , na sayi gidannan da muke ciki , na ɗora neman ki daga inda na tsaya saboda na tabbatar kina Nigeria wataƙila gari kika sauya , meyasa kika min haka Rahima ???? 

"aina kika rayu ? Ina mijinki kina da wasu 'ya'ya ne bayan wannan na cinyar ki ? Idan kina da su suna ina ??

Amnee ta ƙarasa bada labarin rayuwarsu da ɗora tambaya ga Khaalty Rahima wacce idanun ta yayi jazir tsabar kuka ,

Tausayin yayarta ya cinye zuciyar ta , ashe haka ta shiga damuwa akan rashin ta ??

ƙasa take son sharewa tayi rubutu ,

Amnee ta miƙe ta kawo mata takarda da biro , ta sanya hannu biyu ta karɓa ,

taƙaitatcen rubutu tayi a jikin takardar ,

" tsoron kar na zama sanadin rabuwar auren ku da Yaya mustapha yasa na tafi daga gareku ukhtee Amina ki yafe min , bansan ba zan zama sanadin tarwatsewar jin daɗin rayuwar ku .

"Mairambiri shine sunan ƙauyen da na rayu tsawon lokaci a cikin sa kafin zuwan yan tawayen boko haram su tarwatsa garin su kashe mijina da manyan yarana biyu mata da suma nake zaton sun mutu , Amina da Fatima shekaru shida yanzu da mutuwar su .bayan su ina da wata 'ya da ita ma harsashi ya same ta ta mutu , a yanzu Bulama shine kaɗai ɗana .

ASSALAMU ALAIKUM

'Yan uwa ina miƙo saƙon gaisuwata tare da fatan Alheri gare ku baki ɗaya , ina kuma mai yabawa bisa ga yadda kuke nuna ƙaunar ku ga littafin nan ,

nagode .
[11/15, 11:03 PM] +234 806 600 1491: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

39

Duk yadda Falmata take tunanin daÉ—in dake ga mallakar idanu ta tadda shi ya wuce haka , jin kanta take tamkar sabuwar halitta ,

Har bata so bacci ya shiga tsakanin ta da ganin hasken duniya , karambani kuwa babu irin wanda bata yi , har girki take karambanin yi Yousssouf kuwa yana taya ta ,

Shima a ɓangarensa baya gajiya da duk wasu tambayoyi da ko karambanin da zata yi , wani irin son ta yake yana riritata ,

Mama da kanta tasan cewa yanzu Mamarta ta samu waraka saboda wata kulawa na musamman da idanun ta sun hango mata wani É—an datti a jikin kayan Mama zata yi maza ta gyara ta ta sauya mata wani ,

A kullum ta Allah sai ta miƙa godiyar ta ga Youssouf kamar yadda cikin duk wasu sallolinta sai ta ƙara godewa Allah akan wannan babbar kyauta da ya yi mata na dawo mata da ganin ta ,

Godiyar da take yiwa Youssouf ba a fatar baki kaɗai ta tsaya ba , har a aikace take gwada masa ta yadda take nuna masa ƙauna tare da ɗaukar buƙatun sa ba tare da gajiyawa ko ƙorafi ba .

Kamar yadda likita yace tana cigaba da zuwa ana dubata , babu wata sabuwar matsalar da ta ɓullo tunda aka yi mata aiki .

Idan tana da wata damuwa to ta lafiyar Mama ce wacce kwana biyu ciwon ta yake ƙoƙarin tasowa suna danne shi da tarin magunguna gami da ƙara ƙaimi wajen kulawa da ita , amma duk da haka kallo ɗaya za'a mata a iya hango tarin raunin dake tare da ita tun daga cikin raunanan idanunta da suka ɗan sauya launi zuwa ruwan ɗorawa har zuwa ƙafafunta da hannayenta da suka ɗashe suke yawan ɗaukar sanyi ,

Gaba É—aya Falmata da shi kansa Biyamuradi Youssouf basa tare da walwala sosai ,

"Baban Mama ko dai za'a sake komawa asibitin nan ne maganar aikin Mama ,

Youssouf wanda yake shafa kan Mama wacce take kwance cikin jikin sa lamo , ya ɗago kan sa yana duban idanun Falmata da suke nuni ƙarara da damuwar da ruhin ta ke ciki ,

"Fatima duk wassu bayanai da zamu sake samu daga Doctora basu wucce batun baya da sunka faÉ—i muna , wanda kouma mun bar Lamari ga Allah zouwa lokacin da za'a samu damar yin aikin ,

Shiru tayi tana cigaba da kallon sa , cike da damuwa , so take yayi wani yunƙuri kome ƙanƙantar sa ,

Ji yayi gangar jikinsa na karban sakon dake fitowa daga cikin ƙwarar idanunta masu kyaun kallo ,

"idanun ki suna da kyau idan kina kallon Mutum da su Fatima , lokacin da basu da Lafiya kyan su bai kai haka bayyana ba , kina da sassanyan kallo Mai cike da nutsuwa ,

Murmushi tayi kaɗan , kafin ta ƙira sunan sa ,

"Baban Mama ,

Sai kuma tayi shiru ,

Kamo hannunta da yake kusa da shi yayi ya riƙe ,

"Ummh ina jinki menene ?

" daman nace ko zamu je ni ɗin a gwada ni  ?

"gwaji Fatima wanne irin gwaji , akwai damuwa ne ga lafiyar jikin ki ?

Sunkui da kan ta ta sake yi tana jin nawin zancen akan harshen ta , sai dai tana jin zata iya yin kome domin ganin Mama ta samu lafiya , muryar ta a ciki tace ,

"ko Allah zai sa a dace un-un ko wai a jikina akwai abunda da za'a iya amfani da shi wajen yiwa Mama maganin ,

Kiris ya rage Biyamuradi Youssouf ya kwashe da dariya , sai dai ya gintse saboda yana son jaan ta ,

" Fatima kin manta likita yace ke baki iya bada jinin ki ?

Cikin sauri ta katse shi ,

" ai ba jini na ba , wai a auna ko akwai cikin ?

" ciki aina ?

Yace da dariya a cikin sautin sa,

Ɗago kanta tayi tana iya hango hasken haƙoransa da yake dariya,

" un-un a jikina ko ?

Dariya ya kwashe da ita , cikin ransa  ƙaunar ta na sake yawaita , kunya da kawaicinta yana burge shi haɗi da salon rashin wayewarta da baya sa ta fidda tsagoron ƙauyencin ta .

"Fatima ciki ai sai ya nuna Alamunsa tukun ake zouwa ayi gwaji , hakanan bai yiwuwa aje ga gwajji sai a mouna dariya ,

Shiru Falmata tayi tana ganin wautar kan ta , to ita ya zata yi ne ? Ta matsu Mama ta warke ta samu lafiya kamar sauran Yara , tsintar kanta tayi da addu'ar Allah ya nufe ta da samun ciki nan kurkusa domin lafiyar Mama ,

Daren ranar basu samu bacci ba saboda jikin Mama da ya tsananta idan banda nishe-nishe da ƙananun kuka babu abunda take yi , hankalinsu baki ɗaya a tashe , Falmata ta rungume ta anjima Youssouf ya ɗauke ta ya ɗora a jikinsa , haka suka yi ta fama .

Asubar farko a cikin tsananin sanyi suka nufi asibiti a take likitocin ta suka shiga bata kulawa ,

Ba'a fi awa guda ba ciwon ya lafa ta samu bacci , tana rungume a jikin Falmata

Ƙarar wayar sa ya sanya shi miƙewa daga kujerar da yake zaune ya ɗan taka zuwa wajen ɗakin yana ɗaga ƙiran da ake masa wanda yake daga Tafeeda ,

" Youssoufa akwai Al'amari maigirma da muni da yake tunkaro ka ,

Sune kalaman da Yaji Tafeeda ya furta masa ba tare da sun ko gaisa ba ,

Ji yayi ya cigaba da cewa ,

"Bayan tsawon shekarun da ka kwashe kana ɓoye kuskuren da ka aikata yanzu kome yana daf da bayyanuwa batare da ka farga ba mutanen da suka ɗau lokaci suna bibiyar sawun duk wani motsi naka ba tare da ka kai ga hankalta ba gaf suke da cimma nasara akan ka ,

"Ya zama dole ku dawo tare da kai da 'yar taka da matar da ka aurawa kan ka kafin kome ya lalace , mafi girman lamarin shine nan da kowanne lokaci Maimartaba tare da Hajiya umma zuwa kan iyalai tare da 'yan uwanka zasu iya sanin Mummunar Fuskar ka ,

" Maƙiya kuma zasu samu damar kassara ka , wanda kafi kowa sanin me hakan ke nufi ??

"Ta-Tafeeda , meke Faruwa ne yi gaugawar sanar min ,

"ni a matsayina na 'dan ouwa a gareka zan yi dukkanin bakin ƙokarina wajen ganin lamura basu munana fiye da ƙima ba , duk kuwa da cewa ni ai ba bakin koume nake gareka ba ,

ÆŠut-É—ut !
Yaji ƙarar Alamun yankewar ƙiran
Tashin hankalin da ya zo masa a lokacin maigirma ne , me Tafeeda duk ya faÉ—a masa ??

"Tayaya ya san cewa tare yake da Fatima da Mama ? 

"Su waye maƙiyansa masu bibiyar rayuwar sa ?

"Fallasuwar Asirinsa a gurin iyayensa hakan na nufin ɗebe ƙaunar sa daga zukatan su ,

"wai shin me yake shirin faruwa ko kuwa ya ma riga ya faru  ??

Ya zama dole ya koma gida ,

Da sauri ya shiga neman layin Tafeeda sai dai har ta gama ƙara bai ɗauka ba , ya sake gwada ƙira a karo na biyu nan ma ba'a ɗauka ba ,

Tashin hankalin sa ya yawaita da har Falmata ma ta kai ga Fahimta , damuwar sa ta ƙara mata damuwa , sau biyu tana tambayar sa ko me yake damunsa ? Yana ce mata ba kome .

Kafin dare Mama ta warware dan haka suka koma gida ,

"Falmata ta haÉ—a ruwa mai zafi ta yiwa Mama wanka ta shirya ta cikin jibga-jibgan kayan sanyi , kasantuwar cikin magunguna da Alluran da aka yi mata akwai masu sa bacci bata jima ba bacci ya sake É—auketa ,

Itama wankan tayi ta shirya cikin wondo wide-leg da Rigar sanyi ribbed sweater ta É—aura hular sanyi akanta ,

Ta fito ta cimma masa yana zaune a ƙasa ya jingina bayan sa da kujera , hannun sa biyu tallafe da ƙeyarsa ,

Babu wadatar haske a falon saboda duhun dare da ya shigo fitilar falon kuma É—aya ce a kunne , kasantuwar idanun nata ba gani suke sosai ba , ya sa bata ma kai ga ganin sa a wajen ba sai duhu-duhu take gani ,

"Fatima ,

Ya ƙira sunan ta lokacin da ya ga ta kashe ƙafa daga ƙofar ɗakin , alamun tana buƙatar ɗan jagora ,

"zo nan ,

Yace da ita

Inda take iya hango duhun sa ta nufa a hankali ,

kallo yake bin ta da shi ganin yadda kayan suka karɓi jikinta musamman ɗan wondon da bai kai ga sauka ƙasa ba , daga ƙungunta ya zauna ɗas saboda ɗaura shi da tayi akan rigar .

Hannun ta ya kama ya ƙarasa zaunar da ita akan jikinsa yana jin yadda ƙamshin daddaɗan turaren da ta fesa yana ratsa hancin sa ,

Lamo tayi a jikin sa tana jin damuwar rashin walwalar sa na damun ta ,

" Alhamdulillah Mama ta samu sauƙi ko ?

Tace da shi da dabarar son jin maƙasudin damuwar sa ,

"Mama ta samu sauƙi Alhamdulillah ,

Ya ce yana ƙanƙameta a jikin sa ,

"Har hankalin mu ya kwanta , bana son ciwon Mama ina tausayinta ,

"Fatima zamou kassance cikin shiri zouwa wassu kwanaki nan gaba zamou koma gida ,

" É—ago kanta tayi da son ganin fuskar ko Allah zai sa ta fahimci damuwar sa ,

"Baban Mama na É—auka sai an samu lafiyar Mama ?

Zai yi Magana wayar sa tayi ƙara ,

Ganin sunan Hajiya Umma a fuskar wayar ya sa zuciyar sa tsinkewa ,

Da sallama ya É—au wayar , sai dai yadda ya ji ta amsa masa ya sa jin hankalinsa ya sake tashi ,

Sama-sama ta amsa gaisuwar sa , bayan nan abunda ta sanar da shi shine kawai duk me yake ya nemi izni ya taho gida cikin kwanakin nan kusa .

Shiru yayi bayan ya ajiye wayar , tabbas akwai abunda ke wakana game da shi a gida .

"Baban Mama...

Ya katse hanzarin ta

"Fatima zamou kouma gida , a gaba zamou dawo neman lafiyar Mama ,

Sai ta mayar da kan ta jikin sa tayi shiru , baki ɗaya walwalar da ta ɗan samu na murnar samun sauƙin Mama ta kau ,

Daren ranar babu wani armashi agare su musamman ma Falmata da damuwar da take ciki ta haifar mata da zazzaɓi da ɗan ciwon kai , dan haka washegari ta tashi haka sukuku ,

Karin kumallo ma sama-sama suka yi ,

Bayan sun gama karin kumallo su dukkanin su biyun sun yi shiru sai mama ce take É—an wasan ta ,

" J'ai réservé notre vol, nous rentrerons à la maison le 18 le mois prochain , ( nayi mana tanadin jirgin komawa , zamu tafi ranar sha takwas ga watan gobe , )

Muryar sa ratso shirun wajen ,

"Allah ya kaimu Baban Mama , ko zaka sanarwar da Hajja itama ta fara shiri ko ?

"Eh zan sanar da ita idan ya ragge kwanaki goma mu tafi sai tayi shiru cikin kwanaki biyar , idan ya rage kwanaki biyar da tafiyar mu sai direba ya É—aukota daga Nigeria ,

"To Allah ya kaimu ,

****

Wasa gaske cikin 'Yan kwanakin Youssouf ya gaza samun kwanciyar hankali tsoro ne cike taf a ransa , duk kuwa da cewa babu wanda ya sake neman sa kan wani batu sai dai yana tsoro ne kar ko tana ƙasa tana dabo .

Falmata har ta gaji da tambayar sa akan yadda ya zama koyaushe cikin tunani babu nutsuwar kirki , 'yar soyayyar da yake gwada mata mai sanyi da shiga zuci duk ya rage a wasu lokutan ma raba dare yake tunani , da juye-juye ,

Kasantuwar daman ita mace ce marar hayaniya mai kammalewa sai bata tsananta shisshige masa ba ta É—an janye jikinta itama ta maida hankalinta baki É—aya kan Mama ,

da kuma fama da kanta da take yi saboda wani ciwon kai marar daɗi da yake addabar ta tare da bugun zuciya fiye da ƙima duk tayi wata 'yar hidima sai ta ji mummunar gajiya da bugun numfashi sun taso mata ,

Mama da kanta ta san cewa Babanta ya rage kula da dararrakin ta sosai saboda duk ta dame shi zai samu ya zameta ya shiga É—aki ya rufe ,

Ya rage sati biyu tafiyar su da ya ke tsawon kwanaki kusan goma da yin wayar sa da Tafeeda , wanda duk yadda ya so ya samu damar da zasu sake yin wata magana , Tafeedan yaƙi ba shi haɗin kai idan ya ƙira wayar sa ba bai ɗauka saƙonnin sa kuwa ya tura su babu adadi ta kan yanar gizo da kai tsaye ta hanyar saƙon karta kwana , nan ma ga shaidar an karanta sako amma babu amsa , dan haka shima ya zuciya ya daina neman sa .

Ya fito wanka da safe ya tarar da miss call É—in Tafeeda , da hanzari ya É—au wayar bai ko tsaya shafa mai ya sanya kaya ba ya É—au wayar ya shiga neman layin sa ,

Sai dai kakarun Amai da ya jiyo daga Falon su ya sanya shi sauƙe wayar daga kunnen sa ba tare da ya kashe wayar ba ya fito falon hankalinsa a tashe ya ƙaraso ga Falmata wacce take durƙushe daga ƙofar kitchen ɗin su tana Amai ,

Da hanzari ya ƙaraso wajen ya riƙo ta zuwa jikin sa bayan ya ajiye wayar sa a ƙasa da aka riga aka ɗaga kiran daga ɗaya ɓangaren ba tare da ya sani ba ,

"qu'est-ce qui ne va pas avec toi chérie, es-tu malade? ( me yake damun ki ? Baki da lafiya ne ? )

Bata amsa ba illa yunƙurin Aman da ta cigaba da yi duk kuwa da babu kome a cikin nata ,

Shafa bayanta ya shiga yi yana É—an bubbugawa tare da jero mata sannu ,

Mama wacce tashin ta kenan daga bacci ta jiyo muryar su ta fito , itama ta tsaya tana kallon su fuskar  ɗauke da alhini da 'yar muryar tace

"Papa qu'est-ce qui ne va pas avec Mamma ?

"Princess Maman ki bata da lafiya ne, dauko min papier mouchoir dagga É—aki na goge mata baki ,

"To ,

Ta juya da É—an gudu zuwa É—akin su ,

"Sannu Fatima ,

Yace cike da tausayawa , 

Daga can ɓangaren Hawaye masu ɗumi suka silmiyo daga idanun Hajiya Umma , ta zare wayar Tafeeda daga kunnen ta tare da miƙa masa wayar ,

Karɓar wayar yayi ya duba wayar yaga ba'a katse ta ba dan haka cike da tashin hankali ya kara a kunnen sa yana fargabar ko wani abu ne ya faru da Youssouf ɗin ,

Sai dai ya ƙarashi Maganar sa bai ji Youssouf ɗin ya amsa ba , sai muryar wata mace yake ji ƙasa-ƙasa , dan haka ya katse wayar waigo ga Hajiya Umma ,

"Umma Lafiya Yarima yake kou ?

"babu shakka lafiya yake ,
ta amsa da wata irin murya ,

Ganin yanayin ta ya sa Tafeeda miƙewa yayi mata sallama zuciyar sa cike da tunanin meye haka Youssouf ya faɗi wanda ya sa Hajiya Umma ƙwalla ?

Shi daman zouwa yayi ya gaishe ta tare da cigaba da kwantar mata da hankali bayan tashin hankalin da ta shiga a kwanaki sakamakon wani Al'amari mai girma da ya taso game da Youssouf É—in ,

wanda shi yayi tsayuwar daka wajen ganin lamarin ya dai-daita da a yanzu yake mataki na ƙarshe na gyara kome wanda kuwa hakan ba zai samu ba sai da haɗin kan Youssouf ɗin ,

tunanin ko zai yadda da lamarin da zai je masa da shi a matsayin shawara ko ba zai yadda ba ya sanya shi yin jinkiri yana nazari dan haka nema yaƙi yarda suyi magana da Youssouf ɗin

Sai fa yau da Hajiya Umma ta sa ya ƙira sa a gabanta ta warware masa labarin mummunan ƙullin da aka so yi masa ,

Sai kuma ya ga Umma ta ƙare wayar ba tare da ta ce kome ba sai ƙwalla , lamarin da ya ƙulle masa kai kenan , koma menene zai ƙira Youssouf ɗin ya ji .

A ɓangaren Su Youssouf bayan Falmata ta gama Amai ya gyara wajen ya ɗau wayarsa bai lura da Shaidar an ɗaga ƙiransa ba saboda hankalinsa da yake kan Falmata wacce sai numfarfashi take saboda ƙaruwar bugun zuciyar ta tare da ciwon kai da ya haɗu mata ,

Ko sannu da Youssouf yake yi mata da kyar take amsawa ,

"Fatima ko mu tahi hospitalisé ne ?

Jikin ta babu kuzari ta gyada kai ,

Cikin hanzari ya shiga ya shirya ya wankewa Mama jiki tare da goge mata baki , ya dawo ya tarar da ita tana baccin zomo ,

"Fatima mu je ki shirya ,

Shi da kansa ya taya ta ta gyara jikinta yana riƙe da hannun ta suka fito

" za ki iya tafiya da kan ki ko kuwa na ƙira taxi ,

"zan iya tafiya ,

Basu sha wata wahala ba kasantuwar daman tana kan ziyartar likita , dan haka suka samu ganin likitan ta inda shi kuma bayan tambayoyin da yayi mata da duk bayanan da ta ba shi , ya miƙa su ga wata likita daban , wacce ta sake yi mata tambayoyi ,

Daga haka ta yi mata gwaji , bayan bayyanar sakamako ,

da fara'a likitar take miƙa musu sakon taya murnar cewa Falmata tana ɗauke da ciki na tsawon sati huɗu ,

Duk da cewa Falmata tana jin yaren faransanci babu laifi , Amma a yau ji tayi sam bata Fahimci me likitar ke nufi ba , tamkar ta manta ma'anar kalmar ,

Sai da ta ga Biyamuradi Youssouf ya rungume ta , yana bayyana farin-cikin sa da lokaci guda Albishirin da likitar tayi masa ya wanke masa zuciya tare da yin awun gaba da duk wata damuwa tasa , "Ya'ya ai arziƙi ne .

"Fatima Tu es enceinte, tu portes mon bébé , Alhamdulillah

Ya É—ago fuskar ta ya sumbanci goshin ta ,

Hannunta ta kai kan nasa hannun da yake tallafe da kumatun ta , kyawawan idanun ta na bayyana farin-cikin dake maƙare da zuciyar da

"Baban Mama da gaske ina da ciki ? Zan haifi jariri daga cikina Mama Zata samu dan uwa , Mama zata wa....

Katse ta yayi ta hanya ɗora laɓɓansa akan nata ya sumbace ta ,

"Mama da Yumna zasu samu É—an ouwa ko Æ´ar ouwa insha Allah nayi Farin-ciki Fatima .

Mama da take tsaye tana kallon su ba tare da ta san me suke yiwa murna ba , sai ita ma ta sa dariya ta taho ta rungumo su ,

Hannuwansa ya sa ya zagaye a jikinsa yana jin waɗannan rayukan guda biyu sun zama wani ɓangare na daga rayuwar sa ,

Da wannan farin-cikin me tarin yawa suka baro asibitin zuwa gida , bayan likita ta basu shawarwari tare da  'yan magungunan da zasu taimaka a matakin farko na zaman ciki .

Falmata Ji take babu wata rana da take kai wannan ranar farin-ciki a wajen ta , minti kaÉ—an zata kai hannu ta shafi cikin ta , farin-cikin ta biyu ne ,

Tana ganin cewa lokacin warkewar Mama yayi tunda gata É—auke da ciki ,

Da shigowarsu gida wayar sa tayi ƙara  Tafeeda ne ya sake ƙiran farin-cikin sa bai ɓuya ba a muryar sa suka gaisa da Tafeeda ,

Kafin Tafeeda ya É—ora da cewa ,

"Yarima magana nake so muyi kou ka bani dama ?

Jin haka sai ya miƙe daga jikin Falmata ya fita zuwa 'yar barandar gaban gidan ,

"É—an ouwa na baka dama faÉ—i ina jin ka ,

Yace masa a taƙaice ,

"Magana ce zamu yi game da lamarin yarinyar nan da kake boyen sa gareni tsawon wannan shekaru , na riga nasan koume kan zaman ka tare da su da amren innan ita yarinyar da kake har gidan da kun ka tare a Niamey na shina Yarima ,

"To munin Al'amarin ba dagga gareni yake ba , sai fa dagga maƙiya waɗanda sunka dunga bin lamarinka , a cikin binciken da nai kai tamkar da sanya hannun su kome da ya faru ya kai ga faruwa  ,

"Lamari ya munana ta inda zance ya taho ga Fada ya iske kunnen Maimartaba da Hajiya Umma bai tsaya nan ba har sai da ya iske mutanen cikin Fada baki É—ai ba'a kouma san waye ya fiddo maganar ba ,

"cewa Yariman MaraÉ—i yana da É—iyar banza bata Amre ba , tare da yin zaman banza da Mahaifiyar ta zaman dadiro , tun dagga Nigeria ,

"Yarima nayi duk bakin ƙoƙarina wajen ganin anbi daddigin masu yaɗa maganar nan an dakile bazuwar ta , kouma anyi nasara ,sannan na ƙaryata batun gaban moutanen cikin fada tare da Maimartaba ,

"Amma nasan wannan yunƙuri nawa ai bai isa ba ya kawo ƙarshen maganar nan tunda kouwa akwai ta da gaskiya , maƙiya ba za su bar lamarin nan ba .

"Menene mafita a yanzou ?

Youssouf ya katse dogon bayanin da Tafeeda ke yi masa ,cikin miƙa wuya

'Mafita gouda ce ,ka rabu da ita wannan yarinyar da kake amre , ka sallame su su tafi tare da É—iyar nan ,

"ka rabou da ita domin tsarkake kan ka dagga zargin al'umma ,tare da aibatawa ,

"ka rabou da ita domin tsira da mutuncin tare da ƙimar ka ,

"ka rabou da ita doumin gujewa russa alaƙar ka da iyaye da 'yan ouwan ka ,

"ka rabou da ita doumin gujewa samar da bakin-ciki a zuciyar Mahaifiyar ka ,

"ka rabou da ita domin gudun samun galabar maƙiya a kan ka ,

"ka rabou da ita domin tsarkake masarautar ku tare da kaiwa ga matakin nasarar zama sarkin maraÉ—i a watarana .

"ka nesanta kan ka daga wannan ɗiya da innarta doumin tsallake ramin maƙiya , muddin ka ƙiya ? Za ka gamou da dariyar maƙiya da baƙin-cikin iyayen ka .

"cigaba da zama da itta yana nufin rassa kowa tare da kai ciki kouwa har da ni kaina .

"Tafeeda ,

Youssouf ya ƙira shi da wata irin murya mai cike da tashin hankali ,

"Yarima shawara ce ni na baka zaɓi yana dagga gare ka , ni na barka lafiya ,

Wani iri yake ji tamkar an zare masa laka , menene yake shirin Faruwa da rayuwarsa ne ?

Kalmar Rabuwa da Fatima tayi masa nawin saurara ko a kunne kawai ,

To amma kuma shi ya zai yi ne? Ji yake kamar an raɓa ƙwaƙwalwarsa da duk wata tunani .

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.