Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 21
Cigaba yayi da yi musu bayani har zuwa lokacin da ya tabbatar sun samu gamsuwa sun kuma fahimci duk bayanan da yayi musu ,
da kan shi ya jaa jinin Falmata ya fita da shi zuwa É—akin gwaji saboda ya auna ya san irin magunguna da alluran da suka dace yayi mata bisa ga mataki na farko .
Basu bar asibitin ba sai da aka mata allurai biyu ta babbar jijiyar hannun ta tare da yi mata É—aya a jijiyar da take daf da idonta na dama ,
Ba ƙaramar juriya ta nuna ba wajen tsayuwa da tayi cikin nutsuwa aka huda mata jikinta babu zilliya bare ihu da hatta shida kansa likitan sai da ta burge shi sanin da yayi allurar gefen idon tana da zafi ,
    Ya dube ta bayan ya Æ™are mata allurar gefen idon ,Â
"Â sorry It'll hurt but just for a few minutes .
  Gyaɗa kai tayi tana jin yadda idanun nata suka yi nawi ga wani irin yanayi marar daɗi da take ji a idon ,
" Baban Mama , ta ƙira sunan sa tana lalubar hannun sa ,
 Da sauri ya riƙo ta
" Na'am Fatima , sannu kina jin ciwou ? comment vous sentez-vous en général ? ( How are you feeling overall ? )
"Â Idona yayi jini ne ?
"bai yi jini ba Fatima , sannu .
 Â
****
Misalin ƙarfe tara na dare suka bar asibitin bayan sun ci abinci sama-sama daga kitchen ɗin cikin asibiti .
Suka yi bankwana da likita omer bisa ga yarjejeniyar sake dawowa asibitin nan da kwanaki huɗu masu zuwa , bayan ya haɗasu da mugunguna ɗore da dokoki da sharuɗɗan da ya gindaya musu .
Baki É—ayan su sun gaji Mama tayi bacci a jikin Babanta , Falmata kuwa tsukun da idanunta ke yi yana damunta wanda yake ta zubar hawaye , gaba É—aya bata jin daÉ—in kome ,
damuwarta ta tayar da Hankalin Youssouf da yake amfani da kalmomin rarrashi iri-iri yana jera mata sannu , har suka dawo gida , kai tsaye ya zarce da mama ɗakin baccin su ya kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo tare da kunna hutar ɗumama daki ya fito falo inda ya tarar da Falmata ta rufe fuskarta da hannu biyu , ta jingina kanta da jikin kujerar da take
A sanyaye ya ƙaraso wajen fuskar sa na nuna damuwa ƙarara ,
Zama yayi a kusa da ita jikin sa na gogar nata , ya kai hannu a hankali ya sauke hannun ta daga fuskar ,
Hawayen da idanun ke yi ya goge da hankicif É—in da ya zaro a aljihunsa ,
"Fatima yaya ne ? Ciwo ne har yanzou ? Kou zamou koma ga doctorat ?
" Baban Mama idanuna ciwo suke kamar zasu fita , idona bai taɓa ciwo haka ba , bazan warke ba kar kayi asarar kuɗi dayawa , lafiyar Mama yafi samun lafiyar idona muhimmanci kuma ..
"Â Shittt , yace yana kai hannun sa kan É—an bakin ta .
 " Fatima baki ji abounda Doctorat ya faɗi ba ? Zaki warke ko ba du ba , waye ya faɗi miki zata zam asara doumun nayi jinyar ki daga jakka ta ?
" kiyi ta addu'a Allah shi sa a cimma nasara bissa ga neman lafiyar ki kin ji kou ?
Shiru tayi , ita ganin zancen likitan take soki-burutsu tayaya idanun ta zasu fara gani ? Bayan a iya sanin ta bata taɓa ganin hasken duniya ba .
Muryar sa ta katse tunaninta "
Kou baki so watarana ki ga fuskar mijinki ? Kou baki so watarana ki ga fuskar É—iyar ki Mama tare da 'É—iyan da zaki haifa nan gaba ?
Jin ya sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi sai ta ɗago kanta , '
" inaso , amma nafi son na samu ɗa domin ya sadauƙar da ɓargon sa ga Mama , ta warke kamar yadda likita ya faɗa ,
 Sai yayi shiru yana kallon ta da taimakon hasken da bai cika yawa ba da ya hasko daga jikin ƙwan fitilan dake ajiye saman teburin gaban su ,
zancen ta ya zo masa a bazata , ya ratsa ƙwaƙwalwar sa a jirkitatcen yanayi da ya kasa tantancewa .
Ita ma shiru tayi cike da fargabar kasassaɓar da tayi , kada dai tayi masa laifi ? Ko dai zantukanta basu dace ba ? Tayi masa tsaurin ido ko ?
Sauƙar hannun sa cikin nata ya katse mata tunanin zucin da take yi ,
"Fatima mu tafi muyi sallar isha'i kiyi kwana (bacci ) dare yayi ,"
A sanyaye ta amsa da "To,
Har suka kwanta bacci babu wanda ya kuma magana kowanne a tsakanin su yana tunani,
Wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira , da azama ya ɗauka ganin wacce ke ƙiransa ya sanya shi miƙewa a hankali ya nufi ƙofar ɗakin , ya zo fita ya juya gami da kai kallon sa kanta da tayi lamo cikin bargo kamar mai bacci ,
ajiyar zuciya ya sauƙe ransa cike da tunaninnika barkatai ya fita gami da jaa musu ƙofar ,
Falmata wacce duk motsinsa a kunnen ta , ta miÆ™e zaune gami da yaye bargon , cikin ranta sam babu daÉ—i gani take kamar ta É“ata masa rai da maganganun ta tunda gashi daga lokacin bai sake cewa da ita kome ba , ko fushi yayi ?Â
Tashin muryar sa da yake magana kamar a gabanta "kasantuwar ta mai buɗaɗɗen kunne " ya sa ta saurarawa zagayayyar fuskarta na bayyana wani yanayi irin na wanda aka shammata lokacin da taji yana cewa ,
"bonjour ma princesse comment allez-vous aujourd'hui mon amour? ( Alo gimbiyata yaya kike yau masoyiya ? )
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.