Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 20 of 21
Cigaba tayi da ciyar da shi abincin , kafin ta ji ya riƙe hannun ta ,
"na ƙoshi Fatima , buɗe bakin ki na baku ke da Baby ,
Bata musa ba ta buɗe baki ya shiga ciyar da ita , ita ma kaɗan ta ci tace ta ƙoshi ,
"kaɗan kika ci Fatima , ki ƙara saboda Baby ,,
"Na ƙoshi , ai kaima kaɗan ka ci ,
Bai ce kome ba , sai jawo ta da yayi jikinsa ya haɗe ta da ƙirjinsa tsam-tsam ,
Cikin kunnen ta yace
" ina sonki Fatima Zahra ,
Lumshe idanun ta tayi , wasu siraran hawayen da bata san dalilin sauƙar su takamaimai ba suka silmiyo suka sauƙa a fatar ƙirjinsa , runtse ido yayi yana jin tausayin ta mai tarin yawa yana mamayarsa a wajen sa babu abar tausayi sama da ita ,
Sun É—an yi mintoci kaÉ—an a haka kafin ya zare ta daga jikin sa , "Fatima , magarib tayi muyi Sallah ,
****
Bayan sun idar da Sallah sun yi addu'o'i shiru ne ya ratsa tsakani kafin Falmata tace
" ina so na shiga wajen Yakaka ,
Shiru Youssouf ya yi bai ce ƙala ba , saboda har ga Allah bai son su dunga kaɗaicewa saboda bai san da wacce manufa Yakaka take tafe ba , sai dai koma menene yana fatan kar Allah ya bata damar fayyacewa Fatima kome .
Jin yayi shiru ya sa Falmata sake cewa
"zance wajen Yakaka muyi hira kaÉ—an , ga shi Mama ma tana ta bacci ba abun na tayar da ita ba ta je Maman ta ta gan ta ,
"ki rabu da ita , mu je na raki ki kiyi mousu sallama ki dawo nan ki kwanta ki huta , gobe kun yi hira ,
Youssouf yace haka yana kama hannun Falmata cikin zuciyar sa dan babu yadda zai yi ne , da ba zai bari ta fita ba ,
Tare suka shiga har falon , basa nan dan haka Falmata ta ƙarasa ƙofar ɗakin Hajja , shi kuma ya dakata daga tsakiyar Falon ,
Ƙwanƙwasa ƙofar tayi ,
"Yakaka , na dawo .
Zuruf Hajja ta miƙe daga kishingiɗar da tayi tana jaan chasbaha , ta buɗo kofar tare da leƙowa ,
"uwarÉ—akina ai Yayar ki tayi bacci tuni , ki koma kiyi kwanciyar ki ki huta kun haÉ—u gobe da safe ko kuwa ,
Murmushi tayi , "kai Yakaka har tayi bacci ikon Allah ,
ÆŠan jim tayi sai kuma ta sake cewa ," Hajja to ko cikin dare idan ta farka ki faÉ—a mata na zo muyi hira tana bacci , ai ta ci abinci ko ?
"ta ci abinci sosai ta cika cikinta dam ,
"to Hajja sai da safe ,
" yauwa uwarÉ—akina maza a je ayi bauta a huta ,
Har ta juya sai kuma ta sake dawowa ,
"amma , un, un Hajja nace da dai kin taso ta ta koma É—akina , ina da filo mai laushi irin wanda take so , Yakaka bata son filo mai tauri irin naki Hajja ,
Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,
"aifa Lalle , ita Yakaka jaririya ce kenan ? To ai wannan surutun da kike ba kai ba ƙafafu ya isa ya tayar miki da ita daga baccin da na lallaɓata da kyar take yin sa , ni wuce Dan Allah ki tafi Allah ya tashe mu lafiya ,
Ƴar dariya Falmata tayi jin yadda Hajja take yi mata shaguɓe akan Yakaka , juyawa tayi ta kama hanya cikin ranta ba haka ta so ba , so tayi su raba dare suna hira da Yakaka , bata so Yakaka ta ga kamar ta kyale ta ta maƙalewa mijin da bata da tabbacin cigaban zaman su ,
Youssouf da sauri ya taryeta a cikin ransa yana hamdala da rashin ganawar su ,
Hajja tana komawa ɗaki ta dubi Yakaka da take zaune akan sallaya riƙe da Alkur'ani tana karatun ta hankali kwance , duk zantukan Falmata a kunnen ta , tausayi gami da ƙaunar 'yar uwar ta suna bin jinin jikinta da gudu ,
Hajja ta mokaÉ—e baki , lokacin da take komawa ta zauna a wajen da ta tashi ,
"ai a wani ƙaulin irin wannan ƙaryar tana iya zama makaruhi , ko kuwa ba haka ba Babba uwar Mama ?
Yakaka bata kulata ba ta cigaba da karatun ta , can Æ™asan ranta diramar Hajja ta fara bata dariya ,Â
**
Youssouf , Yakaka , da Falmata kusan kowannen su raba dare yayi bai yi bacci ba musamman Youssouf da ƙiran sallan farko na ƙarfe uku da rabi a kunnuwan sa a hankali ya zame Falmata daga jikinsa wacce itama bata jima da samun bacci ba , ya miƙe tare da shiga banɗaki ya ɗora Alwala , jallabiya ya zira yazo ya tada sallah
Nafila yayi tayi har zuwa lokacin da masallatan unguwar suka sa Assalatu , sai ya sallame ya miƙe ya ɗau turare ya fesa tare da ɗaura agogon sa ,
Fita yayi ya nufi masallaci , bayan ya ja ƙofofin gidan gabaɗaya ,
Yana bada baya , mutumin da yake maƙale da jikin katangar , ya siɗaɗa kansa tsaye ya shiga gidan ,
Yakaka wacce ta shiga banÉ—aki domin É—aura Alwala sallah ta ga inuwar mutum ya gifta ,
Tsam tayi tana tunanin waye ?
Haka kawai ta ji zuciyarta ta tsinke , sai ta juya da sauri ta fito , sannu-sannu take tafiya , hasken lantarki ya game ko'ina , gabaɗaya unguwar ƙiran sallah ne ta ko'ina ,
Mutum ta gani a tsaye ya bada baya yana nufar ƙofar falon Youssouf ,
"Waye ne ta ce
Idanunta ƙyar akansa ,
Chak aka tsaya ba tare da an jiyo ba ,
Matsawa tayi ta sake cewa waye ne nace ?
Ba'a amsa ba ,
Taku ta fara yi tana kusantar sa , ta zo kusa da shi bata ankara ba ta ji an kifa mata marin da ya gigitata ,
Tayi taga-taga tana jin wani tsuu a kunnuwanta saboda ƙarfin marin , ta ji takun gudunsa sai dai ta kasa watsakewa daga zafin marin da yayi mata dan haka bata yi wani yunƙuri ba ,
Lokacin da ta watsake babu kowa a wajen ,lokacin an idar da sallah gari har ya É—an yi shaa ,
Yawatawa ta fara yi a wajen tana raba ido ko Allah zai sa ta ga azzalumin da ya mare ta haka ?
Ƙarar buɗe ƙofar gidan ya sa ta juyowa a tsorace , wanda ta hango ya shigo ya sa zuciyarta bugun uku-uku ,
Da sauri ta gyara zaman hijabinta , ta fara tattaro duk wata dauriya da ƙarfin halin da take da shi ta kuma shiga harhaɗa manyan kalmomi masu kaushi da take son yin amfani da su domin su taya ta tunkarar sa ,
Tirus , Youssouf yayi yana hangota , sarai ya gane ta , wani É—an guntun yawu ya haÉ—iye lokacin da tunaninsa ya gama ba shi dalilin tsayuwar ta anan ,
Gyagijewa yayi a matsayin sa na soja bai kamata ya tsorata har haka ba .
Kai tsaye ya nufi ƙofar falonsa yana yin kamar ma bai san tana wajen ba ,
bai ƙarasa ba ya ji tashin muryarta ta ƙira cikakken sunan sa ,
" Youssouf Abdul-Aziz Baskore ,
Sai ya juyo a hankali ya fuskantota da takunsa mai girma , fuskar sa babu alamun É—aukar wargi ,
"Gani
Yace da ita muryar sa a kwance tamkar fuskar sa ba a murtuke take ba ,
Cikin zallar ɓacin ran da yake tunkuɗo kansa daga ƙasan ranta da ta wanzu tana ɗauke da shi tsawon shekaru , ta ƙaraso daf da shi da taimakon hasken Alfijir da ya ƙeto ya dusashe hasken lantarkin wajen suke iya kallon fuskokin juna ,
" Nasan baka san wannan ranar zata zo ba , baka san cewa zan dawo ba , shiyasa har ka samu damar kutsawa cikin rayuwar ƙanwata, ka cuceni ka yaudareni , ka ɓata min rayuwa , ka lalatamin Asalin 'yata , ka sa rayuwata ta shiga garari kuma ka zo kana sake cutar min da ƙanwata , a karo na biyu kana sake gurɓata mata rayuwa , Allah zai saka mana abunda kayi mana , kai wanne irin marar imani ne macuci Azzalumi , Mayaudari kuma fasiƙi mazin ....
" KI MIN SHIRU .
Baisan lokacin da ya daka mata tsawa ba saboda kalamanta da yaji suna tayar masa da hankali , take jijiyoyin kansa suka fito ruÉ—u-ruÉ—u , idanunsa suka sauya launi , jikinsa har tsuma yake yi , irin tashin hankalin da yake ji , da akwai bindiga a hannunsa zai iya kai harbi .
Tsawar da yayi ita ta farkar da Falmata wacce taji tashin muryar sa a tsawace , shafa ɓangaren da yake tayi ta ji baya nan ,
Sassauta murya Youssouf yayi yana kallon Yakaka da take masa kallon sheƙeƙe kallon tsana kallon baka isa ba , , zata yi magana ya sake katse ta ,
"Nace kiyi shiru ,
zuciyar sa ya ji tana kai kawo wajen tuno masa da girman kuskuren sa , girman laifin da ya yiwa Yakaka , sai ya shiga ƙoƙarin sassauta fushin sa tabbas kome Yakaka zata faɗa masa ya cancanta , shi ɗin ai ya cutar da its dayawa kamar yadda tace ,
"ki yiwa Allah kiyi haƙuri , kiyi shiru mu bar kome a tsakanin mu ko dan saboda Albarkacin Fatima da Mama , ki faɗa min duk abunda kike buƙatar nayi miki zan yi ,
Ya furta hakan muryar sa a ƙasa yana satar kallon ƙofar falonsa,
Cikin rashin sanin sa Falmatan tana tsaye daga jikin ƙofar ta bayan labule kalmomin sa na ƙarshe kuma sun cigaba da sauƙa a kunnuwanta tarwai .
"Abunda nake so shine kawai ka sakar min ƙanwata , ka sake ta Youssouf ka kuma bani 'yata , Falmata baza ta taɓa cigaba da zama matarka ba muddin ina raye , ka auri Falmata Alhlin babu sanina ba kuma tare da amincewar wani nata ba , ya zama dole ka saki Falmata , ka sake ta nace .
Ganin yadda ta birkice masa tana ɗaga sauti tamkar bata cikin hayyacin ta yasa Youssouf ruɗewa yana gudun kar Falmata ko Hajja ɗayar su ta ji maganar , dan haka cikin yanayi na lallaɓa yace ,
" to naji naji , zan SAKE TA ,
Wani irin kallon kar ka raina ni Yakaka tayi masa ,
" yanzu nake son ka sake ta anan idan kuma ba haka ba wallahi zan je masarautar maraÉ—i a yau ba gobe ba ,
Da tashin hankali Youssouf yake kallon Yakaka , wacce ta tsattsare sa da ido babu alamun shakku a tare da ita ,
Gani yayi gabaÉ—aya ta rikiÉ—e masa tamkar ba yarinyar nan da ya rainawa wayo , ya kuma yi wasa da rayuwar ta a shekarun baya ba ,
Falmata wacce hawaye suka riga suka wanke mata fuska kamar ruwan fanfo, ta sanya tafukanta duk biyu ta rufe bakinta ta hana sautin kukan da take yi fitowa , a hankali ta silale ƙasa ta durƙusa tana jin yadda marar ta ta wani irin curewa guri guda ..
Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wuni lafiya ?ðŸ˜â¤
Wai-wai , kai-kakai , yau wacce rana ?? 🤓😂
Uhmmm ai idan har baku daina sakar min bama-baman Comments da likes din ku irin na jiyan nan ba ( ko ma fiye da haka )Â Nima kuwa ba zan yi k
Æ™asa guiwa ba wajen cigaba da sasukar rubutu ba, "Ah to meye? Ai tuwon girma miyar sa nama, sannan kuma yaba kyauta tukuici. â¤ðŸ˜
Amma kuyi hakuri da yadda bana samun damar maida muku da martanin sharhin ku, idan nace zan dunga daukar waya ba zan kammala aiyuka na da wuri har na samu damar typing ba , duk da haka nayi alkawarin zan bibiyi comments din ku baki daya na bada amsa inshaallah .
Nagode.
Na manta ko da wacce take buÆ™atar hayar É—an Biri saboda tsaro ?! ðŸ’😂[11/26/2019, 3:24 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
Umm'muaz
42
Wani ɗan kuka ciki-ciki da Mama ta fara daga can cikin ɗakin kwanan su mai haɗe da nishi shi ya sa Falmata miƙewa daga inda ta durƙushe tana rishin kuka ,
A duƙe ta ƙarasa ɗakin saboda mararta da take ji ta riƙe , da taimakon hasken lantarki ta hango Mama a ƙasa ta faɗo daga kan ɗan gadon ta da yake dakin ,
Da sauri ta ƙarasa ta ɗagota tare da rungume ta a jikinta, tana tattaɓa jikin da ta ji yayi zafi rau , muryar ta na karkawa tace ,
" Mama meyasa kika faɗo daga gado ? Ina ne yake yi miki ciwo faɗa min , ? Kai ne ko ƙafar ki ko hannu ? Ko Bayan ki ne ??
Mama wacce take wani irin nishi ta riƙe hannun Falmata tare da ɗorawa akan cikinta ,ƴar muryar ta da kyar take fita tace ,
"ciki na ne ,Mama cikina yana ciwo sosai , ki bani magani zan sha ,ina so nayi bacci Mama ,
Wasu sabbin hawayen ne suka silmiyo daga gurbin idanun Falmata ,
"sannu Mama ,sannu kin ji zan baki magani yanzu ,
Bata amsa ba sai nishi da ta cigaba da yi , a hankali Falmata ta dafa cikin nata ta ji yadda ya kumbura yayi ƙem-ƙem ko numfashi da kyar take fitarwa, wani irin tausayi ne ya kamata tare da tashin hankali a lokaci guda ta nemi ciwon marar da take ji ta rasa ,
Tana dafe da cikin Mama ta fara yin addu'ar samun lafawar ciwo kowanne iri ne ,
Tashin hankalin da zuciyar ta ke ciki a lokacin yana neman kayar da ita , saboda rikicewa da jikin Mama yake neman yi da ƙarin ƙarfin nishinta ta fara ƙiran Baban ta ,
"Papa , Papa ,
Youssouf wanda shigowar sa kenan falon jikin sa a sanyaye ya zauna a kan kujera zuciyar sa cike da tashin hankali kan iƙirarin Yakaka na ya saki Falmata ko kuwa ta je ga iyayensa , sam bai yi zaton abubuwa zasu rinchaɓe masa ya irin haka ba ,
Yasan cewa shi mai lefi ne a wajenta amma ko meyasa baza ta saurara su bi kome a sannu ba ?
Ƙiran sunan sa da Mama take yi ya sa ya miƙe ya nufi ɗakin zuciyar sa ɗauke da sabon zullumi kan tashin ciwon ta ,
A kiɗime ya ƙarasa kan su ya tsugunna ta bayan Falmata yana zagaye su duk biyun da hannuwansa da ya kai ya ɗora a cikin Mama inda ya ga Falmata ta riƙe ,
" Meye ya same ta ? Ciwon ciki take yi ,
"Papa ,
Mama ta ƙira sunan sa tana ƙokarin buɗe ido ,
" na'am princesse ina yake miki ciwo ?
'papa ciki na ka bani magani ina so na kwanta ,
"Mama ai a kwance kike , bari na kawo magani kisha kafin mu tafi hospitalisé,Â
"Fatima yaushe Mama ta fara ciwon ciki ?
Ya tambaye ta yana kallon fuskarta ,
Sunkui da kai tayi tana kaucewa ganin Fuskar sa , muryar ta a É—an dishe tace "Yanzu ne ,
Bayan ya kawo maganin ciwon ciki ya bata ta sha , ya janyeta daga jikin Falmata ya É—ora ta akan gado , " Fatima kin yi sallah kou ?
Girgiza kai tayi tana miƙewa ,
'kiyi sallah mu tai da Mama hospitalisé ,
Bata amsa ba ta ɗau hijabinta ta zura tana barin ɗakin da take jin sa a ƙuntace tunda shigowar sa ,
Ta kama hanyar da zata sada ta da ciki sashinta , sannu-sannu take tafiya tamkar wacce aka zarewa laka ,
damuwa yayi mata yawa bata taɓa zaton zuwan wannan ranar ba , saki a tsakaninta da Baban Mama ?
Da kowanne daƙiƙa guda tunawa take da kalaman Yakaka , da Baban Mama taƙi yarda wani sashin zuciyar ta da yake bijiro mata da rashin kyautawar Yakaka tare da son kai da take ganin ta nuna ƙuru-ƙuru ya rinjayeta ,
Ƙoƙari take ta haɗiye tashin hankalinta ta haƙurƙurtar da ranta ta kuma ƙarbi duk wani hukuncin da su biyun da a yau duniya bata da kamar su zasu kai ga yankewa akanta ,
So take ta rufe ta binne duk wani sirrin dake zuciyar ta a can ƙasan ranta .
Sai dai zuciyarta rawa take tana tantamar anya zata iya ??
Hannu ta sa ta tura ƙofar falonta ta shiga , tamkar baƙuwa haka take sanɗa a falon , aiyanawa take nan da ɗan wani lokaci kaɗan kome na gidan zai tashi daga matsayin mallakinta , to ya koma na wa ??
Taƙi yadda ta hasaso ƙarshen lamarin saboda bata jin zuciyar ta zata iya jurar yadda ƙarshen kome zai zama bata son tuno da makomar Rayuwarta .
Har ta nufi ɗaƙin ta sai kuma ta dawo da baya ta yi ɗakin da Yakaka take ta ɗan ƙwanƙwasa ƙofar ,
Yakaka wacce take zaune akan sallayar da ta idar da sallah tana lazumi ta tashi ta buɗe mata ƙofar ,
" Falmata kin tashi ?
 "un bari nayi sallah , ta amsa mata tana ratsawa ta gefenta ta wuce banɗaki ,
Bayan ta idar da sallah ta É—aga hannuwanta duk biyu tana addu'a ,
Ta kwashe fiye da mintoci sha biyar tana addu'o'i , har zuwa lokacin da zuciyar ta tayi rauni gaba É—aya hawaye ya taho mata , sai ta fashe da kuka mai sauti ,
Yakaka wacce take azkar ta tsahirta , a hankali ta É—ago kai tana kallon ta , sai ta tashi daga inda take ta dawo kusa da ita ,
Dafata tayi fuskar ta na bayyana damuwa tace mata
 'Falmata meyasa kike kuka ? Wani abu aka yi miki ? Ko baki da lafiya ne ? Ki daina kuka Falmata ki faɗa min abunda ke damun ki kin ji ?
Idanunta suna zubar hawaye ta riƙe hannun Yakaka , muryarta ɗauke da sautin kuka tace ,
" Mama bata da lafiya Yakaka , Tunda ta tashi tana da ciwo har turai mun je saboda lafiyar Mama amma ba'a dace ba , yanzu ma bata da lafiya zamu tafi da ita asibiti , ki mata addu'a Yakaka .
Wani irin tashin Hankali Yakaka ta shiga , zuciyarta na tsananta bugu tace ,
"Mama tana da ciwo tunda na haifeta ? Aina ciwon yake ?
" a cikin jinin ta , idan ciwon ya tashi tana shan wahala sosai Mama abun tausayi ce ,
Shiru Yakaka tayi cike da tausayin É—iyar ta ,
A hankali tace" kije ki shirya ku tafi Falmata , Allah ya bata lafiya , Allah ya warkar da ita babu ciwon da bashi da Magani ,
Miƙewa Falmata tayi ta fita zuwa ɗakinta , tana fita kukan ta ya sake dawowa sabo , can cikin ranta neman hanya take da zasu yi magana da Yakaka , so take ta tambayeta meyasa ta ji suna hayaniya da Baban Mama ? Ba tare da ta nuna mata ta san zancen da suka tattauna ba , a sanin ta Yakaka kaifi ɗaya ce wataƙila ta fayyace mata dalilinta ,
Sai dai rashin samun ƙafar maganar da Yakaka ya sa tayi shiru da tarin damuwarta da ciwon Mama ya zo ya ninka mata ,
Bayan fitar ta kukan da Yakaka take dannewa ya taho mata, nadama marar iyaka ta sake rufe ta ,
"Ashe Mama ba ma mai lafiya bace amma ta tsallake ta tafi ta barta ? Haka ta dunga rayuwa da ciwo tun tana jaririyar ta ? Babu tausayi da kulawarta a matsayinta na uwa a gareta ? Ita kuwa anya Mama zata yafe mata idan ta girma labari ya iske mata ? Alƙawartawa kanta take yi tana sake jaddadawa bazata sake yin nesa da ɗiyar ta ba kome runtsi .
Kasa zama a É—akin tayi ta fito falon da babu kowa sai kwarafniyar Hajja daga cikin kitchen ,
Zama tayi akan kujera tayi jugum cikin allhini ,
A sukwane ya turo ƙofar ya shigo yana saɓe da Mama wacce tayi luruf , bai lura da Yakaka ba , ya ɗaga sauti dake bayyana tashin hankalin sa ,
"Fatima ki fito mu tai asibiti jikin Mama ya matsanta kada ta shiga hatsari ,
Miƙewa tsaye Yakaka tayi tashin hankali bayyane bisa fuskarta , jikinta har rawa yake ,
Yi tayi kamar zata taka taje inda suke sai kuma ta jaa ta tsaya , idanunta baki É—aya akan Mama , ba ko dubi fuskar Youssouf ba ,
Muryar sa ya sa Hajja fitowa da take kitchen tana aiki , turus tayi tana raba ganinta tsakanin Yakaka da Youssouf ,
"Babban soja barka da asuba ,
"Barka Hajja yaya hidima ? Mama batta lafiya yanzou zamou tai da itta asibiti ,
Take fuskar Hajja ta sauya daga mamakin da take yi zuwa Alhini ,
"Allah sarki kai wannan yarinya kina shan wahala , sannu Mama Allah ya baki lafiya , Babban soja Allah shi baku ladan jinya da hidima da ita ,
"Amin Hajja ,Amin
Ya furta dai-dai fitowar Falmata cikin hanzari , idanunta hawaye shar-shar suna zuba , da kyar take ganin gabanta ,
"Hajja ina kwana , tace cikin muryar kuka ,
Cike da tausayawa Hajja ta amsa ,
"Sannun Falmata bari kuka haka nan , Allah dai ya bawa Mama lafiya kin ji ? Ai ke kece uwar Mama duniya da lahira .
Tana ƙarasowa Youssouf ya riƙe hannunta suka kama hanyar barin Falon ,
Sai dai taku biyu suka yi , Falmata ta waiga ga Yakaka wacce take tsaye idanunta cike da ƙwallar son sanin halin da Mama take ciki ,
Inda take hango alamar Yakaka ta nufa , tana zuwa ta lalubo hannun ta ,
" zo muje asibitin tare Mamar Mama ,
Babu musu Yakaka ta biyo ta , ganin haka ya sa Youssouf nufar waje bai ce ƙala ba ,
" Hajja mun tafi ,
Yakaka tace ,
bata amsa ba har suka ƙarasa barin falon tana bin Yakaka da kallon mamaki , nisawa tayi bayan wucewar su ,
  "o ni Hauwa'u naga abunda yafi ƙarfina , ji bi dan Allah yadda ta bi su ƙobare-ƙobare babu ko 'yar kara ? Geme-geme da ita ta shiga tsakanin su ,  Da ta san tana son ƴar tayi tafiyarta dandi ta bar ta ?? Tawa ta sameni nikam sai nayi da gaske zan hana yin ɓatatciya a gidan nan ,
***
Dukkanin su biyu a baya suka zauna , yayin da suka shimfiɗar da Mama a tsakanin su , kanta yana a ƙirjin Falmata ta rungume ta , ƙafafuwanta kuma suna kan cinyar Yakaka , Youssouf shi ke jaan motar ,
Hawayen su duka biyun yana ɗiga akan Mama wacce zuwa lokacin bata a haiyyacin ta , kowaccen su tana tofa mata addu'o'in da ya sawwaƙa gareta ,
Da gaugawa Likitocin bada taimakon gaugawa na yara suka amshi Mama wacce ta riga ta suma a lokacin , suka rufu akanta suna ƙoƙarin ceto ranta ,
Bayan kuka da addu'a babu abunda Yakaka da Falmata suke yi , Youssouf kuwa ya kasa tsaye ya kasa zaune , idanunsa sun kaɗa sun yi jaa , bakinsa ya bushe ƙemas , sai kai kawo yake yi yana addu'a Allah ya dawo da lafiyar Mama ,
Suna nan cikin halin juyayi likita guda ya sanar da su an samu nasarar dawo da numfashin Mama da mummunar mura ta tokarewa kirji sakamakon kwayoyin cuta ,
Sai dai ana neman jini saboda ƙarancin na jikinta da shine musabbabin kawo hargitsin ciwon nata ,
duk da cewa ba wannan ne karo na farko na sanya mata jikin ba kamar koyaushe a yau ma sun shaida masa sun fi son wani cikin dangi ya bada jinin fiye da na saye da ake sawa ,
Shi jinin sa bai zo dai-dai da nata ba haka ma na Falmata tuntuni sun san haka ,
Bayan likitan ya bar wajen Falmata wacce ta ji duk abunda likitan ya faÉ—i da faransanci tace ,
" ko za'a nemo wani to wanda ya yarda zai bada jinin a gwada jinin ko Allah zai sa a dace ?
Yakaka wacce ta rafka tagumi kanta a sunkuye , jin haka sai ta É—ago kai ,
" muje a auna jini na ko zai zo É—aya da nata ,
Kallonta Youssouf yayi kamar zai ce wani abu sai ya fasa ,
"tasso muje , yace ,
Da sauri Yakaka ta miƙe , kallon Falmata yayi ,
"Fatima yanzou zamou dawo kinji kou ?
A hankali ta gyaÉ—a kai ba tare da ta waiga sashin da yake ba.
Cikin sa'a da aka auna jinin Yakaka yazo dai-dai da na Mama jinin su B+ ne ,
A take aka yi duk wasu gwaje gwajen da suka dace zuwa lokacin da aka jaa jikin Yakaka leda guda ,
Bayan jiran tsawon awanni fiye da hudu ,zuwa ƙarfe biyu na rana aka ɗaurawa Mama jinin bayan an kaita ɗaki na musamman da suka saba zama muddin aka riƙeta a asibiti ,
Baki ɗayansu gajiya tare da damuwa sun bayyana a siffofinsu , tun safe babu wanda ya ci abin kirki a tsakanin su , duk kuwa da cewa Hajja ta kawo musu abincin kari tare da kayan da zasu iya buƙata anan, kuma ta koma yin abincin dare ,
Ko maganar kirki basa tsawaita yi kowanne yana ji da damuwar sa da ta masa katutu ,
Da lallaɓa Falmata ta iya cin abincin kaɗan wanda Youssouf ne ya bata da kan shi , ba tare da ya lura da Yakaka ba , da ita ma baya ta basu tana zaune akan kujera daga gaban gadon ta riƙe hannun Mama da aka ɗaura mata jini .
Ba da son ranta ba ta ɗan ci dankalin da yake sanya mata a baki tare da ƙwai, sam bata so mu'amalar su ta tsawaita a gaban Yakaka da take iya hango bayanta ,
" Na ƙoshi .
Tace tana ture hannun sa da yake sake kawo mata dankalin ,
Shima bai ce ƙala ba ya janye farantin gefe , sai ta miƙa hannu ta ɗauka , ta cika shi da dankali da soyayyen ƙwai ta yunkura ta ɗauka , gaban gadon ta kai ta ja wata kujera ta ɗora akai ,
"Yakaka biri3 bui3 , ( Ki ci abinci )
Kallon abincin tayi , ko kusa bata jin yunwa , ganin irin yanayin da Mama take ciki ya tsinka mata zuciya , yasa zuciyarta tayi rauni , so da tausayin 'yar ta ya ci ƙarfin zuciyar , tsoron rasa ta kuma ya mamaye ta ,Sama-sama ta ci abincin .
Ƙarfe biyar da rabi Hajja ta kawo abincin dare sai ta ce , "Falmata da Youssouf su tafi gida saboda halin da itama Falmatan take ciki na buÆ™atar kulawa da samun isasshen hutu ,Â
"Ita da Yakaka kuma su zauna tare da Mama a asibitin har zuwa gobe ,
Shawarar ta yiwa Youssouf daÉ—i dan haka basu jinkirta ba yace su tafi gida , ganin jikin Mama da sauki kaÉ—an akan zuwan su,
likitoci sun ta kai kawo a kanta kuma babu laifi zazzaɓin ya sauƙa , cikin ne dai har kawo yanzu a kumbure ,
Falmata wacce da farko ta so tirjewa taƙi tafiya , sai da Yakaka tace mata ta tafi ta huta tunda ita ma Hajja tace bata da lafiya,
Sannan fuskarta babu walwala tayi musu Sallama idanunta na kan Mama ta bi bayan Youssof wanda tun bayan da ya matsa gaban gadon Mama ya yi mata addu'a tare da sumbatar goshinta ya shafa kanta yayi ficewar sa ya tsaya daga waje yana jiran fitowar ta ,
Bai ce kome ba ya riƙe hannunta suka tafi , ita ma har suka shiga mota bata ce masa ƙala ba sai tunanin zuci da take yi ,
Bayan fitar su Yakaka ta kai kallon ta ga Hajja ,
"Hajja meye yake damun Falmatan ita ma ? Naji kin ce bata da lafiya amma ita bata faÉ—a min ba , ?
Sasakai Hajja tayi tana kallon ta ,
"au sai ta faɗa miki tukun zaki gane ? Ji min rashin kan gado , yanzu ke Babba uwar Mama Allah baki Fahimci ƙanwar ki tana da yaron ciki ba ?
Dukkanin wata nutsuwar ta Yakaka ta tattaro ta juyo sosai ta fuskanci Hajja , muryar ta a nutse tace ,
" Menene yaron ciki kuma ? Ki min bayani mai kyau ni Hausa ba yare na bane Hajja ,
Â
Kallon gefen ido Hajja tayi mata , sannan tace ,
" Au haka fa , to abunda nake nufi shine ƙanwar ki tana ɗauke da juna biyu , ciki na haihuwar ɗan mutum , nan da wasu watanni idan Allah ya kaimu zaki sake samun wata ɗa ko 'ya , yanzu kin gane ko Babba uwar Mama ??
Tun da ta ambaci ciki a jikin Falmata , Yakaka ta daina Fahimtar a halin da take ciki dukannin sauran bayanan Hajja bata fahimce su ba ,
" Ciki a jikin Falmata ? Kuma Youssouf ne ya yi mata ? A lokacin mantawa tayi da cewa aure ne ya gifta tsakanin su , tashin hankalin da take ciki ji take tamkar abunda ya faru ga rayuwarta ne ya afku ga Falmata ,
Wani irin Kuka ta fashe da shi ta haɗa kanta da ƙarfen gadon ,
Shin Youssouf wanne irin mutum ne haka Mai cike da zalinci da sharri ?
Bata san lokaci ya ƙure mata ba sai yanzu da tasan kome da take gudu ya faru , ƙanwarta kuma ta afkama tarkon Youssouf a karo na biyu , Youssouf yayi nasara akan ƙanwarta kamar yadda ya ci galaba akan ta ,
Kukan ta ya tsananta da yasa jikin Hajja yin laƙwas , karkata kai tayi tana ƙifta ido
" Ikon Allah Babbar uwar Mama menene abun kuka haka ga abunda yakamata ayi farin-ciki da Samuwar sa ? Ni har jikina yayi sanyi wai kaza ta taka wuƙa ,
Yakaka bata kula Hajja ba , hasalima hankalinta baki ɗaya baya jikinta , ya tafi tunanin neman mafita , ita yanzu yaya zata yi ? Wanne mataki ne yafi dacewa da ta ɗauka ? Anya tana da mafita a yanzu ?
Ganin ta cigaba da kuka yasa Hajja yin shiru , hasashe take akan dalilin kukan Yakaka daga jin labarin cikin Falmata , to ko dai kishi take ??
***
Duk yadda Youssouf ya so ya samu Falmata ta kula shi su yi ko ƴar maganar kirki ne taƙi ,
Tunda suka zo wanka tayi ta shige ɗakinta ta rufe ta kwanta , sai dai duk yadda ta so ya ƙyaleta ta kwana a sashinta ƙi yayi a ƙarshe ma hankalin sa ne ya tashi ya fara tambayar dalilin sauyawar ta ? Cike da fargabar ko dai Yakaka ta mata wani zance ne
Amma tace masa babu kome kawai rashin lafiyar Mama ke damunta , nan ya lallaɓata suka tafi sashin sa ,
A nan ɗin ma zama suka yi babu wata hirar kirki , shima da ƙarin damuwar sa da ƙira yake ta shigowa wayar sa daga Matansa waɗanda suke zuba idon ganin sa tun jiya ,
ya rasa kuma takamai-mai uzurin da zai basu kome ya kufce masa sau biyu yana ɗaga ƙiran su a mabanbantan lokuta yana cewa "yana uzuri ne zai ƙira daga baya ,"
Daga Maimounatu har Siyama sun gaza gane kan mijin nasu tun gabannin tafiyarsa turai , ga shi ya dawo ɗin ma ya zo su gan shi abu ya ta'azzara , ga shi sun gama yin duk wani shiri na tarɓar sa ,
Musamman Siyama da kewar sa ke walagigi da ita , tun tana daurewa har ta kai yanzu kowa ya ganta zai iya fahimtar damuwar da take tare da ita ," duk tsoronta kar wata ce ta É—auke masu hankalin miji ,Â
***
Ƙiran Tafeeda ya sake shigowa karo na biyar a yau ,
Yana kallon wayar ta gama ƙara , kiran na katsewa ya ɗau wayar ya kashe , ya miƙe tare da kashe wutar ɗakin ya zo ya kwanta daga bayanta yayi rigin-gine .
Falmata wacce duk tana jin ƙiransa da ake yana ƙin ɗauka , ta kuma fahimci wata sabuwar damuwar da shima yake ciki ,
sai ta ji tausayin sa ya kamata , ko babu kome a gurinta shi mutumin kirki ne , managarci Mai kyaun hali da kyakkyawar zuciya , sai ta juyo a hankali ta ɗaura kanta akan ƙirjinsa ta rungume shi da hannun ta guda, tana jin lokacin da yayi ajiyar zuciya mai ƙarfi .
Cikin dare bacci ya ƙauracewa idanun Youssouf tunaninnika sun masa yawa , yana son ya san halin da Mama ke ciki yasan kashe wayar da yayi ma a halin yanzu kuskurene tunda yana da marar lafiya a asibiti ,
Dan haka ya miƙe zaune ya ɗau wayarsa tare da kunna ta , kan layin Hajja ya danna ƙira yana kallon agogo wayar da ya gwada masa ƙarfe ɗaya saura mintuna biyar ,
Yasan cewa dare yayi sosai amma ya zama dole ya san halin da É—iyar sa ke ciki tun bayan barin su wajen ta , da kuma yadda zata kwana ,
A can wayar ta ɗau ƙara , yaji alamun shigar ƙiran ,
Muryar da ta doki kunnuwan sa ya sanya shi miƙewa tsaye , yayi taku kaɗan , yana waiwayen Falmata ,
" Mai wayar tana bacci ,
  cewar Yakaka da ita ta ɗau wayar Hajja saboda ƙarar wayar kar ya tayar da Mama da ta samu bacci da kyar bayan kukan ciwo da take yi , tare da rikicin neman Iyayenta .
 " Yaya jikin Mama ?
Yace , yana fitowa daga É—akin zuwa falo domin kada ya tayar da Falmata daga bacci ,
Miƙewa tayi daga kujerar da take kai , tana jin tsanar sa na sake bijiro mata da jin sautin muryar sa ,
" Youssouf
  Ta ƙira shi , bata sauƙe mumfashi ba ta ɗora da cewa , "ina batun mu ? Kar ka manta da abunda na faɗa maka muddin kana son cigaba da ganin farin-cikin iyayen ka sannan....
Katse ta yayi ,
" yaya jikin É—iya ta nake tambayar ki ? Ke baki da tounani ne ? Baki ganin halin da Mama take ciki ? Ba yanzou bane lokacin yin wannan maganar kiyi hakuri don Allah .
" Yanzou ki tada Hajja daga barci ki bata wayar zan tambaye ta kan lafiyar ɗiya ta ,
Ƙit !
Yakaka ta kashe wayar har ita yake ƙira marar tunani ? Akwai marar tunani da ya wuce shi ? Duk sanadin waye suke cikin halin da suke ciki a yanzu ? Da bata haɗu da shi ba zata haifi Mama ne ? Ko kuwa yana nufin shi da ya gudu ya barta da cikin Mama ya fita ƙaunar Mama ɗin ne ? Yana da sani ne ko kaɗan akan irin wahalar da ta shiga na kwana a rumfar kasuwa tare da cikin Mama a jikinta ?
Guntun tsaki tayi tana komawa ta zauna a kujerar da ta tashi ,
 ta shafa kan Mama wacce take baccin zoma tana ɗan nishi kaɗan-kaɗan , duk da cewa an ƙara mata jini leda guda amma har yanzu ƙafa da hannunta fari sol alamun rashin jini
tausayinta yana sake kama ta , ko runtse bata runtsa ba , tun lokacin da Hajja ta faÉ—a mata cikin jikin Falmata damuwarta ta sake ninkuwa ,
Duk dogon nazarin nema mafita da tayi hankalinta yaƙi amincewa da ta ƙyale Youssouf ya cigaba da zama da ƙanwar ta ta gwammace ya saki Falmata su koma Nigeria tayi rainon cikin ta haihu idan yaso su ɗauko abunda aka haifa a kaiwa iyayensa tunda shi da Falmata aure suka yi ,
Dole iyayensa zasu riƙe abunda ta haifa , ita kuwa Mama 'ƴar ta ce da suka haifa ba tare da aure ba ta san iyayensa baza su riƙe Mama ba , Mama zata kasance tare da ita .
**
Youssouf ya ji yadda ta katse ƙiran ba tare da ta bashi amsar da yake son ji ba , sauƙe wayar yayi bai sake ƙira ba ya juya ya koma ɗakin ,
Zama yayi a bakin gado , cikin ransa rikicin da Yakaka ta zo da shi ya kai matakin ƙure shi, ya fara neman mafitar yaya zai yi da Yakaka domin kuwa ko a mafarki ba zai yi mata yadda take so ba , ya saki Matarsa akan wanne dalili ? Aurensa da Falmata aurene da sai mutuwa ce kaɗai zata raba su ,
Yana son matar sa , yana ƙaunar ta ,yana tausayin ta , ya kuma shirya tsaf domin zamar mata bango abun jingina , idan ya rabu da ita taje ina ? Waye zai jiɓanci lamarin ta ? Wa suke da shi a duniya jigo ? Daga ita har Yakaka masu rauni ne domin kuwa mata ne tayaya zai sau aurenta ? Alhalin ga zuri'a a tsakani Allah ya fara basu ,
dangantakar su ba mai yankewa bace har abada ba zai rabu da ita ba ko da kuwa ace ita da karan kanta ta nemi da ya sake ta ba zai aikata hakan ba ,
bare wasu mutane daban da ba sune suke riƙe masa da igiyoyin auren sa ba , Fatima Zara matar sa ce har a lahira baya fatan rabuwar su .
Zai roƙi Yakaka da tayi hakuri ta yafe masa duk wani laifi da take zaton ya yi mata , tare da Alƙawarin kula da hidimar Rayuwar ta muddin zata yadda ta cigaba da rufe asirin tsakanin su daga sauran mutane , ciki har da Falmata da Mama idan ta girma .
sannan tayi haƙuri ta koma Nigeria ta samu miji tayi aure shi zai tsaya mata a wannan gaɓar .
muddin kuwa taƙi yadda da tayin salama , bai iya hasashen yadda ƙarshen lamarin su zai ƙarƙare , bai san ba gurin hukuntata akan yunƙurinta na raba shi da matar sa ko zai iya yi mata sassauci Albarkacin Mama ba?
abunda ya riga ya sani ne tun a ranar farkon ganin sa da ita ba soyayya ce ragamar tarayyar su ba illa musiba tare da sharrin shaiÉ—an da shi ya faÉ—awa a ciki , ita kuma ta gagara tsamo sa a madadin haka ma sai ta zama abokiyar taya shi ,ashe idan haka ne itama da nata laifin ,
Zai yi kome zai kuma jure kome domin ganin ya cigaba da rayuwa da matar sa da 'ya'yan sa ,
A hankali ya hau gadon ya rungume ta tsam a jikinsa , runtse ido tayi hawayen da suka taru mata suka zubo , tun daga tashin sa ta ji shi , ta ji wayar sa da Yakaka ,
Wanne irin sirri ne a tsakanin su da suke ɓoye mata basa so ta ji ? Jikinta yana bata rabuwar su da ita da Youssouf ta zo kusa.
Washegari
Tunda tayi sallar asuba gari yayi haske ta shiga kitchen duk kuwa da Youssouf ya so hana ta amma ta dage ,
"bai kyautu ba kuma Hajja ta dawo daga asibiti tayi mana girki zan iya ba abu mai wahala zan dafa ba kawai pasta ne zan yi , tace da shi .
Ba yadda ya iya saboda gaba ɗaya ta koma mishi kamar farkon auren su , sai janye jiki take da shi ,tana ƙin kallon sa , bata tsawaita zance da shi
Bayan ta gama girkin ta zuba ta rufe , ta zo ta wuce shi a falon yana zaune ba tare da tace masa kome ba ,
Da ta shiga ɗaki wanka tayi ta koma ta kwanta a gadon ta saboda tun ƙarfe ɗayan dare rabon ta da baccin kirki , lokacin da ta ji wayar da suka yi , tana kwanciya bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta
Youssouf da ya gaji da jiranta ta zo suyi karin kumallo , tashi yayi ya leƙa ɗakin nata ,
A gado ya hangota tayi luf tana baccin ta , ransa yayi sanyi da yaga tana bacci sosai haka , a hankali ya taka zuwa cikin É—akin ,
Zama yayi a bakin gadon yana ƙarewa fuskarta kallo , ƙaunar ta na sake fisgar shi , gani yayi ta fi yi masa kyau idan tana bacci ,
Kamar motsi ya ji an taɓa ƙofar falon , dan haka ya miƙe ya fito yana dube-dube , sai dai bai kai ga ganin kome ba , tsayuwa ya cigaba da yi a harabar gidan ya zura hannu a aljihu yana tunanin zuci ,
"yana son zuwa Maraɗi ko domin iyayensa , amma tsoron abunda zai tarar a can ya hana shi samun ƙarfin zuwa ,
Ciki ya koma inda ya tarar wayar sa da ya ajiye akan kujerar da ya tashi tana ƙara ,
Zuciyar sa ta buga da ƙarfi ganin Mai ƙiran nasa da ba kasafai ta cika yin ƙiran waya ba , sai fa da Babban dalili ko kuma idan shi ya ƙira domin gaishe ta ,
"Adda Ammi ce Babbar yayar su baki É—aya da take aure a jahar Damagaram ,
Har wayar ta tsinke bai ɗauka ba saboda fargaba , amma bai jinkirta ba ya bi bayan ƙiran da hanzari ,
**
Daga cikin motar ƙirar Honda Accord da take tafiya da matsakaicin gudu akan titin Boulevard Mali Véro ,
Hamshaƙan matan su biyu masu kamanni ɗaya suke zaune , ɗaya tana daga gaba Babbar tana baya , ta gaban ta ɗan waiga kaɗan , lokacin da direban ya karya kan motar zuwa cikin unguwar da take gefe da su ,
"Adda Ammi kadda kice mini ke ma Youssoufa bai ɗau ƙiran ki ba ?
Zata yi magana wayar ta ta É—au kiÉ—an shigowar kiran sa ,
" ga shi ya biyo sawun ƙiran ,
  Tace ba tare da ta ɗaga ƙiran ba ,
Tafeeda wanda shi yake jaan motar ya juyo kaɗan kafin ya maida hankalin sa ga tuƙin yana cewa "ai ga gidan can ma mun iso Adda Ammi ,
Duk suka zubawa gidan ido ta cikin gilashin motar suna kallo ,bayan ya dai-daita tsayuwar motar , suna shirin fitowa lokacin da suka ga an buɗo ta ƙaramar ƙofar gidan a hankali an fito ,
Su dukkanin su wara ido suka yi suna kallon sa da Mamaki ,
" Mouhammadou ?
Tafeeda ya ƙira sunan sa da mamaki a muryar sa ,
suna ganin yadda yake dube-dube yana sauri , ya miƙa kan titin unguwar da babu kowa shal , sai fa giftawar motoci jifa-jifa , ba tare da shi ya gan su ba saboda gilashin motar da yake da duhu ,
Shiru ne ya gifta tsakanin su , kafin Ubbo ta ce
"Tafeeda ka ce mouna babu wanda ya san da tabbatuwa lamarin nan sai kai ɗai ? Sai kouma mu da yanzou ka taho da mu , to Yaya anka yi mouhammadou ya iso nan ? Ko kouwa shi Youssoufa ya ƙiraye shi ?
Cike da nazari Tafeeda ya nisa ,
"Adda ni bansan kome game da wanzuwat shi ba , wataƙila Youssoufa ya ƙiraye shi , sai dai nafi zaton zuwan kan sa yayi ɗauke da wani ƙudiri nashi na daban ,
Duk suka sake yin shiru a motar , bayyanar Mouhammadou a boyayyen gidan Youssoufa na sirri ya sanya su a ruÉ—ani ,
Bayan iyayen su da suka san maganar zaman Youssouf da mace har ma da É—iya ba ta aure ba a ta bakin wasu mutane ,
Tafeeda shine mutum ɗaya tal da yasan haƙiƙanin gaskiyar lamuran , shine kuma ya yi ta ƙoƙari wajen ganin ya wanke Youssouf , ya dunga neman Youssouf da ya dawo su fuskanci matsalar su maganceta tun kafin duniya ta ɗauka .
Amma daga baya sai Youssouf yaƙi ba shi haɗin kai , wannan dalilin ne ma ya sa shi dole ya samu yayun Youssouf ɗin Adda Ammi , da Ubbo da su ma suke cikin tashin hankali jin cewa ɗan uwansu yana can America tare da karuwa da 'yar su ,
Shi yayi musu bayanai na haƙiƙanin gaskiyar kome cewa ba fa zaman dadiro Youssouf yake yi ba amren yarinyar yake yi daga ƙasar Nigeria wacce kuma ƙanwace ga ainahin uwar yarinyar da ya yiwa ciki ba ta hanyar aure ba ta kuma rasu a wajen haihuwar 'yar .
Ba ƙaramin baƙin-ciki suka shiga ba da jin irin ta'asar da ɗan uwan su ya aikata , har kuma yake da tsaurin idanun cigaba da yin yadda ya ga dama ,
Dan haka suka tsaida shawarar muddin Youssouf ɗin ya dawo su zasu yi takakkiya zuwa gidan da ya ɓuya yake yin rashin gaskiya ,
su kuma sanya dole ya saki amren yarinyar da yake riƙo tare da haɗa ta da ɗiyar su koma da ita can ƙasar su ,
su basa yadda ya gurɓata musu sunan zuri'a da masarautar su , ba kuma zasu amince ya kawo musu baragurbin ɗiyar sa ba , bare wata matar da bata da masauƙi a tsakanin su ,
wacece ita da zata zama sanadin ɓacin ran iyayen su , ta kuma samu damar zama matar ɗan uwan su Yarima sarkin watarana ??
Adda ammi ta ɗau wayar ta tana sake ƙiran layin Youssouf dai-dai lokacin da taxi ɗin da Yakaka tayi shata , ya ajiyeta a ƙofar gidan ta bashi kuɗin sa ,
Ta kama hanyar shiga gidan hannun ta riƙe da kulolin abincin da ta dawo da su daga asibiti , da kyar take taku saboda tsabar gajiya da bacci da ya cika mata ido ,
Adda Ammi tana jin Youssouf ya É—aga wayar bata tsaya amsa gaisuwar sa da yake yi mata ba cikin dakakkiyar muryar ta tace da shi ,
"Youssoufa ga munan ƙofar gidan ka , ka hito ka yi mouna jagora ,
Da 'yar ruɗewa cikin muryar sa lokacin da yake miƙewa yana barin abincin da ya fara ci yace
"Adda ai bani gida maraÉ—i ba kouma na tahoue , ina Niamey ne wajen aikina ,
"Na sani ƙofar gidan ka na niemey ɗin nake magana ko kouwa baka hitowa ka mouna jagora sai mu shiga da kanmu ?
Fitowa yayi hankalin sa a tashe ya nufi ƙofar gidan ko takalma babu a ƙafarsa ,
A harabar gidan ya ci karo da Yakaka wacce take shigowa , kallon juna suka yi kowannen su ransa a ɓace , ya gota ta kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan idanunsa suka sauƙa akansu duk ukun suna fitowa daga motar ,
Yawun bakin sa ya ji ya ƙame , ya rasa halin da yake ciki takamaimai , ,
da murmushin yaƙe ya ƙaraso gaban su , ya ɗan sosa ƙeya bayan ya rage tsawo ya shiga gaishe su ,
Sama-sama suka amsa suna binsa da kallo ganin yadda duk yake a firgice da alamun rashin gaskiya ,
"Bismillah,
yace da su yana yin gaba , ba tare da ko sau ɗaya ya dubi sashin da Tafeeda yake tsaye ba saboda gudun yadda zata kaya a tsaƙanin su da ya riga ya san cewa shine ya haɗo masa wannan gangamin ,
Da shigar su harabar gidan yayi nufin kai su sashin sa , sai dai tsintar maganar Adda Ammi yayi tana tambayar sa ina matar gidan ?
Cikin dakiya ya waigo , "tana ciki , yace a takaice yana kallon ta ,
"to ai wajen ta yakamata mu shiga duk muyi maganar da take tafe da mu ,
ÆŠan jim yayi yana kallon ta , cikin shakku , sai dai yadda tayi maganar cikin lumana ya sa ya wuce gaba zuwa sashin Falmata suna bin bayansa ,
Zuciyarsa cike da fatan samun masalaha akan koma menene , fatan sa Allah yasa zuwan su ya gyara kome ,
Suna shiga falon suka tarar da Yakaka a zaune daga ƙasa tana hutawa tare da jiran shigowar Falmata da take zaton ko tana wajen Youssouf zuciyarta ɗauke da ƙudirin fara sanar mata da kome a yau ,
Shigowar su ya sa ta miƙe , fuskarta kadaran-kadahan ta gaishe su ,
Shi Tafeeda bai amsa ba , Ammi da Ubbo ne suka amsa a taƙaice suna ƙare mata kallo sama da ƙasa , zuciyar su na shaida musu wannan me kama da asbinawan ce ta sa ɗan ouwan su kaucewa hanya ??
Ratsawa tayi zata wuce ta bar su Ubbo ta dakatar da ita ,
"baiwar Allah dawo nan , kou ba ita ce matar gidan ba ?
  ta juya akalar tambayarta ga youssouf
Da sauri Youssouf ya girgiza kai ,
  "Ba itta ce ba ,
To ita wannan wace ?
Adda Ammi ta tambaye shi
a ciki ya amsa ,
"yal ouwatta ce ,
.ubbo tace
"itta ina tai ?
" bacci take , adda domin Allah muyi duk maganar da zamu yi ni da ku ,
"Ke
Adda Ummi ta buɗe murya wajen ƙiran Yakaka wacce har lokacin take rakaɓe daga gefe a tsaye ,
"ki tai ki tado mouna da 'yal ouwakki ku taho tare ,
Yakaka bata san me suke nufi ba hausar tai mata nisa dan haka ta tsaya tsam tana kallon su ta ƙasan ido ,
Youssouf da yanayin Ammi ya fara É—arsa masa tsoro a rai , ya nunawa Yakaka É—akin da Falmata take ciki ,yace
" Fatima tana ciki ki ƙira ta ,
A hankali Yakaka ta tura ƙofar ɗakin Falmata da har kawo yanzu baccin ta take yi ,
Ta ƙarasa bakin gadon a hankali ta dafa ta ,
"Falmata , Falmata , ta ƙira sunan ta tana ɗan jijjigata ,
Buɗe idanunta da suka yi mata nawi tayi , sai kuma ta ware su da sauri ta miƙe zaune tare da riƙe hannun Yakaka da take hango ta dusu-dusu ,
" Yakaka kece ? Ina Mama ? Ya jikin nata ? Ta samu sauƙi ? Tayi bacci ? Bata yi kuka ba ko ?
" jikin Mama da sauƙi na baro ta tana bacci , Yanzu muje falo kina da baƙi ,
" Baƙi ?su waye ? mu babu wanda yake zuwa wajen mu ai ?
"wasu mata ne ina ga Æ´an uwan sa ne ,
Yakaka tace tana miƙewa tsaye ,
A hankali Falmata ta kai hannu ta laluɓi gilashinta ta sanya a fuskar ta , bayan ta ɗora hijabi akan doguwar rigar jikinta ,
Tare suka fito falon yatsunsu cikin na juna ,
Har ƙasa Falmata ta durƙusa ta gaishe da matan da ta tarar da ƙamshin su ya cika falon , sannan ta gaishe da Tafeeda ,
Sai tayi shiru jin yadda suka amsa mata a cike da ginshiri ,
"wannan ce matar taka ? Uwar 'yar taka ? Wannan kuma 'yar uwarta ?
Adda ummi ta tambaya tana nuna Falmata da Yakaka da hannun ta a walaƙance ,
"Eh , ah ah , eh ita ce Matata Fatima ,
Kallon sa su duka biyu suka yi jin yace "eh ya kuma ce "Ah ah ,
Gyara zama tayi ta matso kusa daga kan kujerar ,
" ke yarinya kina jina ?
 Falmata wacce ta fahimci da ita ake , ta gyaɗa kai a hankali bayan ta fuskanci inda take iya ganin Matar da take mata magana sosai ,
" daga ina kike ? Su waye iyayen ki ?
daga Falmata har Yakaka zuciyoyin su suka buga , Sai Falmata ta sake matso Yakaka tana riƙo Hannun ta ,
A hankali Yakaka ta sauƙe ganin ta akan Adda Ammi ,
" Mu 'yan gudun hijira ne a ƙasar Nigeria, kuma iyayen mu duk sun rasu ,
Ƙutawa tayi tana gyaɗa kai cikin buɗaɗɗiyar Muryar tace " kin san Youssouf wanene ?
Girgiza kai Falmata tayi alamun "ah ah ,
  " shekarar ku nawa kuna amre ?
Youssouf wanda ya fara hango tsoro a fuskar Falmata tare da hasasho inda Adda Ammi zata ƙarƙare maganar ta ya yunƙuro da nufin katse ta
" Adda Ammi ....
Da hannu ta dakatar da shi , "Youssoufa ba kai nake tambaya ba ,
"yarinya shekarun ku nawa nace da Amre ?
"shida ,
  Falmata tace cikin siriryar muryar , zuciyar ta cike da son sanin yau wacece agaban ta ko dai mahaifiyar Baban Mama ce ??
Muryar ta ya katse mata tunani,
"kin taba ganin wanni daga cikin dangi nashi ya zou inda kuke ? Ko kouwa ku ya taɓa sada ku da dangin sa ?
Shiru Falmata tayi ,
"kin san dalili ?? Bata jira amsar Falmata ba ta ɗora da cewa ,
"sabadda kama dagga kan iyayensa da mou 'yan ouwansa har zouwa kan dangin da masarautar mu zouwa kan mutanen jahar mou baki É—aya ba mou san da amren kou ba ,
"Youssoufa ɗan Sarki ne , Yarima ne shi , yana da iyayen sa suna raye mu yayyensa ne , yana kouma da ƙanne , sannan yana da matan amre har biyu da ɗiyar sa ,
"duk baki san mou ba , a yadda ɗan'ouwansa kuma abokinsa ya buncika mouna ya amre ki ne tare da ɗiyar yal ouwakki da ta haifa ba tare da sun yi amre da shi ba shigiyar ɗiya, ya zo nan ya ɓoye kou , yana rayuwar sirri da kou , kin raba tsakanin sa da matayensa , kin ɗauke hankalin sa daga aikin sa , bashi da watta hidima sai taku ke da ɗiyar da gurɓatatciya ce shin yarinya baki gudun jefa rayuwarki ga hargitsi maigirma ?
Cikin wata irin murya Falmata ta ɗamƙi hannun Yakaka ta jijjiga ta tare da cewa
" Yakaka kiyi magana mana , kina ji fa an ƙira Mama shegiya ,
shiru Yakaka tayi tana jin yadda wani abu ya zo mata ƙahon zuci ya takore , ko motsa laɓɓanta ta gaza ,
Juyawa tayi wajen da Youssouf yayi suman zaune akan shamtar sa da Adda Ammi tayi ,
"Baban Mama ka ji wai Hajiya yayar ka tace Mama ba 'yar aure bace , ka faÉ—a musu gaskiya yadda ka faÉ—awa Baba prof lokacin auren mu dan Allah,
Hawayen da suka cika gurbin idanunta suka sauƙo , ta matso gaban su ,
" Hajiya dan Allah ko da ni baza ku karɓeni ba kuyi haƙuri ku karɓi Mama kar ku ɓata mata asali , Mama yarinya ce marar lafiya dan Allah kar ku ....
Tsawar da Ubbo ta daka mata ya sanyata yin shiru ,,
"ke yarinya raba mu da ƙazanta ,yadda kuka zou tare hakka zaku kouma tare , mu karɓi ɗiya mu tai da itta ina ? Muyi me da itta ? Mu 'yan nasaba ne , ɗiyan asali ɗiyan halak ba zamou taɓa yadda da zouwanta cikin mou ba ai daman ɗiyan zina na uwattai ne , can zaku koma da itta ,
Da rishin kuka Falmata ta miƙe tsaye ta tsaya akan su ,
"ƙarya kuke yi Yakaka ba ƴar iska bace bata taɓa zina ba , dan haka Mama ba shegiya bace ,
Juyawa tayi ta ɗago Yakaka da ruwan hawaye ya jiƙa mata gaban riga , ko kusa bata san wannan ranar da zasu shiga tozarta ita da "yar uwar ta a sanadin kuskuren da ta aikata zata zo ba ,
Kuma bata so ba wasu suka riga ta sanar da Falmata ta irin hanyar da ta samar da Mama ba ,
jijjigar da Falmata ta yiwa kafaɗunta da ta riƙe duk biyu shi ya tsorata ta ,
"Yakaka kina jina ki je gaban su ki faɗa musu ƙarya suke miki sharri suke muku ke da Baban Mama ba zina kuka yi ba , ki faɗa musu Mama ba shegiya bace , ki ce musu ƙarya suke yi , Mama ƴar halak ce kamar su ,
Ta karasa zancen tana fashewa da kuka ,
Kukan da ya hargitsa duk wata guntuwar nutsuwar da ta ragewa Youssouf , ya miƙe a ɗimauce , lokacin da muryar Yakaka ya ratsa wajen ,
" Gaskiyar su ne Falmata , Mama shegiya ce , ba muyi aure ba ni da Baban Mama muka haife ta ,
tamkar an harbi Æ™waÆ™walar ta haka Falmata ta ji zancen , sai ta wara idanun ta fes akan fuskar yar uwar ta muryar ta babu Æ™arfi irin na É—azu illah tsantsar tashin hankali ta ceÂ
" Yakaka tsoron su kike ji ? Dan kina tsoron su shine kema zaki ƙira Mama shegiya dan kawai bakya son ta ? ,
sai ta tunkuÉ—e ta baya , ta wuce kai tsaye wajen Youssouf da Æ™afafun sa ke karkarwa ta tsaya daf da shi ta É—aga kai tana hangen farar fuskar saÂ
"Baban Mama ka cewa Yayar ka ƙarya take , ka faɗa musu kai mutumin kirki ne bazaka cutar da Yayata ka ɓata asalin Mama ba ? Ka faɗa musu ba zaka yi zina da Yayata kuma ka aureni ba .
hannun sa dake rawa ya miƙa ya rike kafaɗar ta , sai dai hannun sa yana sauƙa a jikinta ta doke hannun da wani irin matsanancin fushi , tace "kaima zaka ce gaskiya ne ? Eh ?
Ubbo wacce abunda Falmata take yi ya fara bata haushi a ganin ta tsaurin idanun Falmata ya wuce iyaka da har take ƙaryata su kai tsaye ,ta kuma tsare Youssouf ɗin a gaban idanun su dan haka sai ta miƙe tsaye ta ƙaraso wajen ,
Ta fuskance shi tana cewa
" Youssoufa menene haka nake kallo ? Macce ke tsare gaban ka Youssoufa ? A gaban ka take ƙaryata Adda Ammi ? Ka sake ta Youssouf a yanzou , ka sau amrenta nace wacece itta da bata wuce bayun mu ba ?
Da dukkanin Fushin sa ya juya gare su  muryar sa da Amo mai ƙarfi laɓɓansa na karkarwa yace.
"Adda Ammi, Adda ubbo , Tafeeda , domin Allah ku tafi abunku , ku fita dagga Rayuwa ta , Rayuwata tawa ce ni ɗaya ba tare da ku ba , duk kome nayi a cikin ta domin kai na ne ,
" ba zan saki Matata ba haka kouma ba zan rabu da ɗiya ta ba , naji ban samar da Mama ta halastatciyar hanya ba , amma ina ƙaunarta fiye da yadda nake kaunar kaina , ni nake da laifi Mama ita wankakkiya ce tsaftatatciya ,
"ba zan danganta Mama da ku ba asalinta ya tsaya ne daga kaina ni kaɗai , ba zan raɓa ta da ku ba , samuwar Mama a wajena wani kaddara ne Maigirma daga ubangijina ,don Allah Adda ku tafi nace ,
"to maras kunya fitsararre , idan kai ka zare mu dagga rayuwar ka mou ba mou fita ba , asalin mu gouda da kai sannan akwai hakkin 'yan ouwantaka da na iyayen mu akan ka ,
Ubbo tace haka ,
Bata saurare shi ba ta juya ga Falmata wacce ta durƙushe a wajen tana wani irin kuka marar sauti ,
"ke yarinya tunda baki da alkunya ku tattara yanzou ku fita zouwa wani wajen cen , ku tafi kuyi nesa da ƙanina shi ba tsaran amren kou bane ɗiyan matsayitta masu gajeren assali ƴaƴan titi....
Kalamanta sun ƙona zuciyar Yakaka , dan haka ta tako gabanta tana jin duk wata shakkar su na ficewa daga ranta tace ,
" Ya isa , Ya isa nace Ya isa kar ki zagi iyayen mu , da basa raye a duniya , ko daman baki faɗa ba Falmata ba zata cigaba da zama da azzalumin ɗan uwanku ba , wanda tushen sa da asalinsa tare da girman da kuke fariya da shi bai katange shi ba daga aikata alfasha , kamar yadda kuka faɗa ya zama dole ya saki ƙanwata ya kuma ba ni ɗiya ta ,
" Nima bazan taɓa yadda ta zauna atare da ku ba , idan kun so a yau ku ɗora shi ya zama sarki , har abada Mama baza ta sake nuna shi a matsayin Uba ba ,
Takawa tayi ta ƙarasa gaban Youssouf , idanunta jazir da ɓacin rai tace
" ka saki auren Falmata na sake maimaita maka , ka kuma fita daga rayuwar mu Youssouf ...
Assalamu Alaikum masu karatu , da fatan duk kuna lafiya ??
Wannan shafin kachokam É—insa tukuici ne ga duk wasu masoyan MHR a duk inda kuke alherin Allah ya iske ku , ina Æ™aunar ku domin Allah ðŸ˜â¤
Nagode
[11/29/2019, 1:17 PM] +234 806 600 1491: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
43
Ƙiran wayar Youssouf da aka yi ƙarar ita ta ratsa shiru mai ɗauke da tashin hankalin da ya biyo bayan martanin Yakaka ,
Baya cikin nutsuwar sa ya dubi fuskar wayar da take riƙe a hannunsa , ganin wacce take ƙiransa ya sa zuciyar sa ta tsinke ,
Hannunsa na rawa ya ɗaga ƙiran wayar da ya zarce da sanya ta a hands-free batare da ya ankara ba ,
Muryar Hajja ciki kuka ta karaÉ—e falon , da take cewa
"Babban soja , ku zo Dan Allah, ku zo wajen Mama ku ga jikin nata , jikin Mama babu daÉ—i...
Rige-rigen ficewa daga falon aka yi tsakanin Youssouf ,Yakaka da Falmata da babu wanda ya saurari kansa bare waninsa burin su kawai su isa wajenta ,
Kuma a tsakanin Falmata da Yakaka babu wacce ta nufi motar Youssouf da ya shiga ya tayar dukkanin su biyu kai tsaye mafitar gidan suka nufa ,
Suna fita ya sha gabansu da Motar ,"ku shigo ,
 Yace da wata irin murya
Dukkanin su a lokacin ganin Mama shine burin su , dan haka suka shiga motar ya jaa da gudun gaske ,
A lokacin hawayen fuskar Yakaka da Falmata sun ƙafe kamar yadda yawun bakin su ya ƙafe ya daƙile fitowar wata kalma daga gare su , bayan addu'o'i babu abunda kowannen su yake yi a zuciya
Suna ficewa daga layin gidan motocin da suka yi jerin gwano su kimanin guda biyar suka shiga layin .
Gudun da yake yi ya wuce ka'idar tuki , kiyayewar Allah kaɗai ta kai su asibitin , ba inda ya kamata ya ajiye motar ya ajiye ba , bai ko lura da securities da suke masa magana ba , ya fito daga motar sauƙar ƙarfar sa akan titin da ya ɗau zafin rana shi ya ankarar da shi cewa fa ko takalma babu a ƙafafunsa ,
da gudu-gudu suka nufi É—akin da suka san Mama tana ciki suna rige-rigen kutsa kansu ,
Turus suka yi ganin babu kowa akan gadon nata , da sauri ya fita suka bi bayansa , ma'aikaciyar jinyar da ya fara cin karo da ita zata wuce ya tambayeta ,"ina É—iya ta ?
Ta san shi sosai a saboda yadda suke yawan zaman asibitin da kuma kasancewar sa babban Mutum , sai ta nuna musu É—akin da aka mayar da Mama wanda yake daga ciki sosai ,
Bai saurari me zata sake faÉ—i ba ya nufi inda ta kwatanta masa da sassarfa ,
Bankaɗa ƙofar ɗakin yayi ya danna kai su Yakaka suna bin sa ba tare da sun bi ta kan Hajja wacce take tsaye daga bakin ƙofar tana sharar hawaye da gefen mayafin ta ba ,
Shigar su ya zo dai-dai da lokacin da likitan yake zare trach tube ɗin da yake fuskar Mama ,
Da gudu Youssouf ya ƙarasa ya ratsa ta tsakankanin Likitocin da suke zagaye da ita , fuskokin su cike da Alhini ,
Ya tarairayo ta bayan ya zauna a bakin gadon ya ɗagota lokacin da take jaan wani irin numfashi mai tafe da gurnani ciki-ciki , idanunta a buɗe akan fuskar sa ,
Hannun sa ya kai yana goge mata tsinkakken yawun da yake zuba a bakin ta , muryar sa tana karkarwa yake kallon likitocin yana cewa,
" Doctora yaya hakka ? Kuyi wani abu mana , Mama tana hakka alhalin kuna tsaye ?
"Mama, kar ki barni ki dubeni Mama ,
ya ƙira ta da wata irin muryar yana jijjigata a jikinsa ganin yadda idanunta suka yi sama , numfashin da take kokawar riƙewa kuma ya ƙarasa barin jikinta , dukkanin wasu jijiyoyin jikinta suka tsayawa aiki , kamar yadda zuciyarta ta tsaya chak daga barin bugawa na har abada .
Da gudu Yakaka ta ratsa tsakanin su ta kai hannu tana riƙo hannun Mama da yayi wani irin sanyi ƙalau ya sake ,
"Mama tashi mana , me ya same ki haka ? Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon .
 Tace da kuka a muryar ta ,
"Mama ,
Falmata ma ta ƙira ta lokacin da ta ƙaraso gurin idanunta basa gani sosai Amma tabbas a yau tana iya hange gefen Fuskar Mama tar-tar , shafa kanta tayi da yake rungume a kirjin Babanta
"Mama meye ya same ki ? Ki tashi Mama , kin ga fa Mamar ki ta asali ta dawo zata rayu da ke , Mama baki ko mata magana ba , bata ji muryar ki ba shine kuma za ki zama haka ? Mama ki tashi ,
Ta ƙarasa maganar tana jijjiga su ita da Youssouf ,
KafaÉ—ar Youssouf Babban likitan ya dafa , yana cewa
" Innalillahi wa inna ilahi raji'oon , kuyi hakuri duk wani ciwo na safiyya ya warke , ta komawa ga Ubangijinta , dukkan wani mai rai mamaci ne kuyi haƙuri , kuyi haƙuri , kuyi addu'a
Baya yayi a hankali yana kaucewa ganin tashin hankalin da yake ƙwarar idanun su su ukun ,da suke kallon sa zuciyar sa cike da tsantsar tausayi , tabbas mutuwar abunda ka haifa akwai ciwo , ciwo kuwa mai raɗaɗin gaske , ɗaya bayan ɗaya likitocin suke ficewa daga ɗakin suka bar guda biyu kawai a tsaye ,
Jikin Youssouf babu inda baya rawa , ya zaro Mama daga ƙirjinsa yana kallon fuskar ta yadda kan ta ya tafi galau ,
Ya sa kukan da yake riƙewa fisge masa , sai ya fashe da kuka mai ƙarfi ya mayar da ita ƙirjin sa da yake wani irin bugu da matsewa tamkar ana daure masa jijiyoyin dake gudanar da jini ta cikin sa ,
amon kukansa ya sa Hajja shigowa É—akin , cikin ranta tana aiyana inda ake gudu nan aka zo aka tsaya , Mama ta rasu ,
Tun-tuni ta ga Alamun mutuwa a tare da yarinyar tunda jikin ya birkice daman ranta yake kai-kawo , Allah sarki mutuwa bata a shekaru , bata barin ƙarami ta ɗau babba domin wai ta jinkirtawa girman sa , ita lokaci kawai take jira , ko ɗan da yake cikin mahaifiyar sa tana ɗauka ,
Falmata wacce hankalinta ya kasa amincewa da mutuwar Mama kamar yadda likita ya faɗa , ƙarasawa tayi ga Yakaka wacce ta zube guiwar ta biyu a ƙasa ta kifa tafukanta biyu akan fuskarta , kuka take marar sauti , illahirin jikinta rawa yake sai ta kai hannu ta dafa ta , a lokacin da Hajja ta nufi wajen Youssouf , da muryar dake bayyana tsoro da tashin hankalin da me ita yake ciki tace ,
"Yakaka , ki tashi , ki tashi ki karɓi Mama mu tafi , mu tafi da ita Yakaka , ko kin manta da Alƙawarin da muka mata tun tana ciki ? Cewa ni da ke zamu kula da ita Yakaka , zamu bata kariya yaya kuma kina gani Mama zata tafi ta bar mu , ?
Alhalin ...Ya.Yakaka ki tashi nace kin san fa mu uku ne kaɗai a duniya Dan Allah kar Mama ta mutu , Mama kar ki barni mana , yaya za ki min haka Mama ? Bayan nayi alƙawarin zaki warke Mama .
Kuka ne ya ci ƙarfin ta har tana shiɗewa numfashinta ya fara yin sama-sama
Da sauri Yakaka ta rungumeta kukan ta yana daɗuwa ta riƙe fuskar ta ,
"Falmata kiyi addu'a , kice innalillahi wa inna ilahi raji'oon , mu da Mama duk Allah ne ya yimu , ya bamu rai da muke rayuwa da shi , kuma shine ya hallicci mutuwa ya sa ta zama mai zare rayukan mu idan lokacin da ya kayyade mana na rabuwar mu da ruhin mu yayi , da ni da ke da Baban ta duk Allah ya fi mu sonta kiyi mata Addu'a Falmata ,
Da ƙarfi Falmata ta rungume Yakaka wacce ƙarfin hali ne kawai take yi domin kadda Falmata tayi rauni dayawa ,ita abunda take ji bata taɓa jin makamancin sa ba wani abu take ji mai ɗaci yana kai kawo a tsakanin zuciya da maƙogoron ta , gaba ɗaya ranta cike yake da duhu da take iya ganin duhun har ga idanunta ,
Hajja tana ƙarasawa ga Youssouf ta shiga bada baki da tunasarwar da ake yiwa wanda aka yiwa mutuwa , itama sharar hawaye take zuciyarta cike da tausayin su , tana kimanta irin zogin da zuciyoyinsu ke ciki kan mutuwar ɗiyar su ,
Sun É—au mintoci kusan goma a haka cikin halin É—imuwar jin zafin mutuwa kafin likitocin biyu su nemi da ya basu Mama zasu zare duk na'urorin su da suka riga suka jona mata ,
Bai dube su ba kamar yadda bai ce kome ba illa bakin sa da tun-tuni yake motsawa da alamun addu'a yake yiwa Æ´ar sa ,
Shi da kan sa ya raba jikinta da duk wasu na'urorin su ba tare da ya ajiye gawar ta ba ya jaa farin mayafin su na asibitin ya rufe fuskarta zuwa jikinta da shi , bayan ya shafe fuskarta da tafin hannun sa .
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.