Maradams Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 1 BY AYSHA A BAGUDO.txt
Chapter 12 of 18
Page 12
Aunty tayi shiru tana duban maryama yanayinta kamar kazar da'aka tsamo cikin ruwa gaba daya alamu sun nuna gajiya a tattare daita amman dan karfin halin irin nata take boye mata damuwarta , hawayen da suka cicciko acikin kwarnin idanunta tayi qoqarin maidawa tana danne damuwarta saboda farinciki diyarta ."
ahankali ta dauke kwayar idanunta aKan tilon diyarta zuwa wani bangare dabam tana tunanin rayuwa da abubuwan da sukai ta faruwa daita ta sha wahala arayuwarta shiyasa batason maryama ta sha wahala irin wanda ta sha ,wannan aikin da aunty salma kesata yana matukar ta'ba zuciyarta domin ko ita da tayi sanadiyyar zuwanta duniya bata sakata aiki haka koda tace zatayi ma bata yarda ta bar mata tayi ita kadai sai dai suyi a tare amman bata da yadda zatayi da rayuwata dan bazata iya hanawa ba "tabbas bata da yadda zatayi kuma bata isa ta hanata ba tunda zaman gidan ya zame mata dole dan bata son rasa yaranta kuma bata son ta koma ga danginta ." tayi maganar a kasan ranta .
maryama ta kalli mahaifiyarta duk da bata san me ya canza yanayinta ba amman tasan meke yawo acikin kwakwaluwarta ta matsota sosai tana jijiga Aunty wacce tayi nisa cikin tunanin rayuwa "meke damunki Aunty ?firgigib ta dawo haiyacinta tana dubanta duba mai tattare da damuwa tana cewa " babu abinda Ke damuna princess " ta fad'a tana mai jin tausayinta domin dai duk halin da suka tsinci kansu aciki itace sila, itace silar janyowa ya'yanta rayuwar wahala wacce bata kamacesu ba duk wani abu daya faru da ya'yanta itace ta janyo masu adalilin zunzurutun Kaunar data nunawa mahaifinsu ya janyo mata rasa komai domin ta zabi
Mahaifinsu ta bar danginta wanda yasa kowa acikin danginta yaji babu dadi akanta."
"me yasa kowa ya tsanemu acikin gidan nan ?" bayan mahaifinmu da granny da umma da abba babu mai qaunarmu acikin gidan nan gashi abba ya rasu ya barmu kamar yadda mahaifinmu ya barmu why Aunty ?me yasa basa qaunarmu ? "Me yasa suka tsanemu ko kin yi masu wani laifi ne ?ina son nasan abinda ya kawo wannan kiyayyar ?shiru kawai Aunty tayi tana dubanta dan bata da abinda zata fad'a mata domin kare kanta maryama yarinya ce da bata wuce shekara ashirin a duniya ba but she's smart in ance smart ana nufin mutun wanda ya kasance mai tsananin hankalin da kwakwaluwa tare da kaifin baseera sannan yarinya ce mai fadar gsky komai d'acinta zata fad'a she's very shap akan komai dan wani lokaci har mamaki take bata idan tayi wani abu kanta naja sosai fiyye da yadda take tunanin tasan muddin taji ta zabi mahaifinta ne akan iyayenta yasa dangita suka juya mata baya tabbas zata fad'a mata gskyr data kasa amsa daga ahlinta "Ina danginki suke Aunty ?ta jeho mata tambayar data nemi bugar mata da zuciya tana mai d'aura kanta a saman cinyarta ."
tsura mata ido tayi tana kallonta kafin daga bisani tace "suna nan ! "suna nan amman me yasa bakya zuwa inda suke kamar yadda Aunty salma keyi ?"babu komai "ta bata amsa atakaice tana jin wani tuttukin bakinciki acikin ranta mai tattare da damuwa "Aunty karki ce babu komai lallai akwai dalili akwai abinda yasa bakya son zuwa inda suke har yasa bamu sansu ba ,mahaifiya mahaifi yan'uwa duk ba abun wasa bane domin suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ."
Naunayen ajiyar zuciya aunty ta sauke tana sake tsura mata ido "dan baki san abinda suka aikata gareni bane maryama shiyasa zaki fadi haka ta fad'a hk a zuciyarta " ahlinki suna da matukar mahimanci sannan suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali ,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?yadda kike iya hakurin rashin zuwa ga iyayenki bazan iya barinki daidai da second daya batare dana daura kwayar idanuna akanki ba saboda qaunar da nake miki ina sonki aunty fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan haka Kiyi qoqarin kije garesu nasan suma zuciyoyinsu na cike da kewarki da qaunarki tunda kika haifeni na girma na kai wannan shekarun ban ta'ba ganin ranar da kika shirya kika ce zakije ga ahlinki ba , kullum muna cikin dangin dady cikin kaskanci da wulakanci ya kamata ko sau daya ne muje domin nima ina son ganinsu ina son ganin danginki zaki je ga ahlinki ? tayi mata tmbyr tana mai tsura mata kyawawan idanunta masu matukar kyau ."
Kusan minti goma aunty bata amsa mata ba har sai data sake maimaita abinda ta fad'a sannan tace "to maryama zanyi qoqarin zuwa." ta fadi hakan ne ba dan zata aikata hakan ba sai dan abar maganar ta wuce "da gaske kike Aunty zaki ga ahlinki ? murmushi tayi mata domin bata son damuwarta dan ta fahimci yau din nan tana cikin damuwa ."
maryama ta rungumeta tsam tsam ajikinta tana mai jin dadi "naji matukar dadi Aunty ina son ganin ahlinki nasan habib ma zai ji dadi yaushe zamu je ? ta fad'a tana zare jikinta daga na Aunty yayinda idanunta Ke kallonta aunty tai shiru tana dubanta hakan nan ta tsinci kanta cikin farinciki wanda tasan maryama ce sila tana matukar son farincikin yaranta murmushinsu murmushinta ne haka zalika damuwarsu damuwarta ce tana matukar qaunarsu fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan sune iyayenta yayyaenta kannenta komai nata daman tasha yin addua ko a can baya Allah ya bata ya'ya masu albarka wadan da zasu maye mata gurbin yan'uwa."
"aunty !
Ta kira sunanta cikin sanyayyar muryarta mai tsananin kashe jiki a duk sanda tayi mata magana da wannan muryar tana tuno mata da mahaifinta ko habib da ya kasance nmj bai dauko sanyin muryar mahaifinsu ba sai ita "na'am my princess ta amsa tana dubanta tana saurararta "a ina danginki suke zaune ?"tayi mata tmbyr fuskarta na nuna farinciki."
"suna zaune acikin garin nan" "cikin garin nan ? maryama ta maimaita abinda mahaifiyarta ta fad'a cike da mamaki Aunty ta gyada mata kai alamun" Eh!wani sabon mamaki ya sake cunkushe zuciyar maryama "suna zaune a gari daya amman duk tsawon wannan shekaru bata taba zuwa dasu inda suke ba bare su sansu gashi ta zauna tana rayuwa cikin kunci da babu tamkar wacce bata da kowa acikin duniyar nan ,numfashi ta janyo da kyar ta fesar a hankali kafin ta bude bakinta da kyar "yaushe zamu je wurinsu ?".
"karki damu sarauniyata in sha allahu zamu " cike da farinciki maryama ta kai hannunta ta dauki remut tana mai kunna tv tare da maida hankalinta Kan program din daake yi a tashar galaxy tv tana mai jin farinciki da natsuwar zuciya "Aunty zan so naji ranar da zamu na soma lissafa kwanaki "canza fuska tayi batare datai auni ba kafin daga bisani ta kawar da kanta gefe dan karta fahimci damuwarta dan gbdy ta soma neman natsuwarta ta rasa bazata iya zuwa garesu ba ,haka zalika ya'yanta ma bazasuje ga danginta ba most especially mahaifiyarta ta barsu har abada kamar yadda suka barta zata karasa rayuwarta a haka cikin kunci ."
a qalla sun dauki mintuna goma zaune suna duban tv babu wanda ya sake yunkurin cewa komai
Kafin ahankali cikin sanyi jiki maryama ta mike daga kwanciyar da tai akan cinyar mahaifiyarta ."Aunty lokacin sallah yayi bari naje nayi sallah gashi ina son na danyi zane kafin na kwanata ga bacci da nake jin yana fixgata tamkar zan fadi ni zan shiga ciki sai da safe dan gabadaya yau ko gurin umma bazan shiga ba idan sakina ta shigo kice mata na shiga bacci dan bazan sake fitowa ba allah ya bamu alkhairi ."tana gama fadar haka ta juya ."
har tayi taku biyu Aunty ta dakatar daita ta hanyar kiran sunanta "princess!
Ta dan tsaya tare da waigowa "abinci fa ? maryama ta dan yatsina face dinta tana ciza gefen lips dinta sannan ta girgiza mata kai alamun "a'a ! "to amman karatun jarabawa ya kamata kiyi ba zane ba ko gobe baku da exam ne ? muna da shi zanyi karatu sannan na d'an yi zanen sai na kwanta " "kiyi karatu da kyau maryama Kinsan a final year kike, ni da son samuna ne da kin bar zanen nan har sai kin gama karatu " karki ji komai Aunty duk zan iya Kiyi min addua da fatan samun nasara ."
Aunty ta sauke numfashi tana cewa "allah ya bada saa yayiwa rayuwarki albarka "Ameen sai da safe "
"okay to shikenan allah ya bamu alkhairi "Ameen ! ta sake juyawa tana rausaya tamkar zata karye dan rashin jikin da Allah ya bata , har sai da Aunty taga ta shiga cikin d'akinta sannan ta dauke idanunta daga kallon bayanta ."
Tana shiga dakin bayi ta shiga tayi wanka hade da dauro alwala ta fito cikin sanyi jiki tana goge gashin kanta da towel tana goge jiki tana mamakin abinda yasa mahaifiyarta bata son zuwa ga danginta alhalin suna gari daya ,"me yasa haka? " zata so tasan dalilin dayasa bata son zuwa garesu da wannan tunanin ta saka doguwar rigar bacci fara sol har kasa ta qarasa inda take ajiye sallaya ta dauka ta shimfida ta kai hannunta ta dauki zumbulelen hijab dinta ta saka ta kalli gabas a natse ta tada sallah ."
byn ta idar ta mike ta cire hijab ta ajiye a gefen gadonta ta zauna akan kujera kwaya daya dake dakin wanda gabansa dan qaramin table ne mai dauke da tarin textbook da fararen takardu na zanenta ta janyo textbok daya daga ciki sannan ta zaro farar takarda kwaya daya ta ajiye a gabanta ta soma karatu tana joting kusan mintuna talatin sannan ta rufe ta maidashi inda yake ta sake zaro wata takarda ta ciro pencil da kayan aikinta ta fara zane wanda ya kasance abinci ruhinta a duk lokacin da zaka ga maryama a natse zaka ganta kuma akan aiki idan bata makaranta boko tana islamiyya idan bata islamiyya tana Kan aikinta na Architect wanda dashi take samu take taimakawa mahaifiyarta batayi karatu akanshi ba kawai baiwa ce daga allah ya bata babu abinda bata iya zanawa tun tana qarama take Zane dashi ta girma ."
cikin kankanin lokaci ta fara zana wasu hadaddun mutane sanye da kaya na maaurata guda biyu macen sanye da wedding gwan yayinda nmj kuma ke sanye da suit sunyi matukar kyau kamar a kirasu su amsa tayi shiru tare da tura pencil cikin bakinta tana taunawa tana kallon zanen ahankali ahankali tana lumshe idanunta alamun bacci "bari na bar aikin nan haka tunda ba urgent bane zuwa gobe na qarasa idan na dawo daga school ta tattara ta bude durowar table dinta ta tura ta mike tsaye ta sake daukar hijab ta sanya ta tada sallah ishai tayi addua ga mahaifinta da alummar muslimai ta mike ta nade dadduma ta maida inda yake ta hau gado ta kwanta ko cikakken minti uku batayi ba bacci ya dauketa ."
A can falo kuwa Aunty zaune kawai take duk hirar da habib da sakina ke zubawa da idanu kawai take binsu hankalinta na wani waje karfe goma daidai sakina tayi masu sallama ta wuce tana fita Aunty ta mike tsaye tana cewa habib "ka rufe koina ni zan shiga ciki allah ya tashemu lfy ta nufi hanyar dakinta har zata shiga ta hango haske a dakin maryama dan haka ta dawo ahankali ta shiga dakin ."
tana kwance ta dungule waje daya a tsakiyar katifa ta cusa kanta cikin jikinta kwanciya mai tattare da damuwa duk wanda kaga yayi irin wannan kwanciya tabbas yana cikin damuwa ko maraici kuma a duk sanda taga tayi irin wannan kwanciyar ba komai take tunawa ba illa kanta take tunawa alokacin baya irin kwanciyarta kenan wanda damuwa ne silar nata kuma tasan damuwar ce ta janyo mata itama ta qarasa shigowa d'akin har inda take kwance ta kai hannu ta gyara mata kwanciya ta janyo abun rufa ta lullube mata jiki ta shafa gefen fuskarta tana sake jin soyayyarta acikin ranta ya'ya sune farinciki iyaye amman ita ta rasa wannan gatan daga nata most especially mahaifiyarta ."
"abinda mahaifiyarta tayi mata abu ne da mutun zai iya yafewa amman bazai ta'ba iya mantawa ba kuma abu ne da bazata ta'ba yiwa ya'yanta ba zata so ya'yanta tamkar rayuwarta bazata iya kuntata masu ba bazata iya azabtar dasu ba sannan bazata iya hanasu cikar burinsu ba zata basu farinciki duk abinda suke so zata basu matukar bai sabawa shari'a ba, fatanta dai allah ya raya matasu cikin aminci "ta mike tsam har lokacin idanunta na Kan maryama dake qoqarin sake dunkulewa waje daya ta kashe mata hasken d'akin sannan ta fito tana mai janyo mata kofar dakin ta shiga dakinta "
Ahankali ta zauna a bakin gado zuciyarta cike da zullumi har kusan shabiyu na dare tana zaune sai dai zuwa wannan lokaci tayi rigingine tana kallon saman dakin daya byn daya maganar maryama Ke dawo mata "me yasa bakya son zuwa inda danginki suke ?" mahaifi mahaifiya yan'uwa suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ahlinki suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?nan take taji wasu hawaye masu zafi ya ganganro gefen idanunta."
"tabbas gaskiy diyar cikinta ta fad'a mata amamn ai sune sukace babu ita babusu har abada me zataje tayi masu a yanzu da take cikin damuwa da bata da komai tasan ko taje garesu wulakanci ne zai biyo baya gara ta cigaba da zamanta hk babu dangi har karshen rayuwarta ,maryama da habib sun isheta komai , sheshekar kuka take sosai wanda batasan tanayi ba maraici sosai take ji alhalin ita din ba marainiya bace ta daura hannunta daya a saman kanta ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata ."
tana cikin wannan halin taji an turo kofar dakinta da sauri ta dago tare dawowa haiyacinta tana mai goge hawayen idanunta da hannuwanta duka habib ne ya shigo wanda sakamakon sheshekan kukanta ya shigo dashi sai daya mata kallon tsanake sannan yace "me ye damuwarki male? dake shi kuma haka yake kiranta dashi ta sake sanyawa jikinta jarumta tana girgiza masa kai " alamun babu komai."
"karki fad'a min haka byn kukanki ne ya shigo dani ya fad'a yana kafeta da fararen idanunshi qara maimaita tmbyrta yayi tayi kasa da kanta sakamakon hawayen daya sake cika mata ido domin kwalkwaluwarta ta toshe ta kasa fad'a masa dalili "ya sake matsota sosai male ki fad'a min damuwarki domin bazan bar dakin nan ba muddin baki fad'a min ba domin dai damuwa Ke saka mutun kuka irin wannna kuma tunda nake ban ta'ba ganin kukanki irin haka ba kuka mai fitowa daga kasan zuciya ."
Ya kai hannu ya dago habarta yana kallon hawayenta dake zuba yabi hawayen da kallon hankalinsa na sake tashi cikin tsananin tashin hankali yace "wanene ya bata miki ranki haka? ta girgiza masa kai kawai "wai meye haka ne male kina son zuciyata ta kasa sukuni ne ko me ?ta sake girgiza masa kai ya juya a fusace zai bar dakin "bari naje na taso heartbeat.."
ta riko hannusa da sauri "karka tashe ta bacci dan baccinta yayi nisa gashi gobe tana da exam's "to ki fad'a min damuwarki kamoshi tayi ta zaunar dashi a gefenta ya zauna yana sauraronta kusan second goma sannan ta zayyane masa komai sai daya numfasa kana ya soma mgn "male duk abinda heartbeat ta fad'a is right and it good dan daman nima ina neman hanyar da zan miki wannan tmbyr domin abu ne daya dade cikin kwakwaluwata har ya Kan hanani kwanciyar hankali Kiyi tunani male
gsky heartbeat ta fad'a miki ya kamata kije ga danginki ko mu ki fad'a mana inda suke muje domin muna bukatarsu "
Jin haka yasa ta barke da wani sabon kuka "baku san me suka min ba baku san irin wahalar dana sha a hannunsu ba ,na sha wahala kuma duk akan mahaifinku ne bana tunanin zasu qaunaceku shiru yayi yana dubanta cike da mamaki "me dady yayi masu haka ?sannan wani irin wahala kika sha a hannunsu ?yayi mata tmbyr a jere cikin tsananin tashin hankali kafin a hankali ya kai hannu yana goge mata hawaye shiru tayi ita kanta tana son ta basu labarinta amman bata san yadda zata dauki abun ba "tana son mahaifiyarta tana tausaya mata tana gudun bacin ranta ,bata son ganinta cikin damuwa amman a karshe itace abar kyama itace abar wulakantawa, itace mara mutunci a idanunta
har tana cewa allah yasa mijinta ya wulakantata Allah ya hanata haihuwa Allah yasa ya saketa mijin da take tsananin so duk akan ta zabeshi a matsayin jikin aurenta ."
Kuka sosai take tmkr ranta zai fita tana furta "na yafesu har abada zan zauna na qarasa rayuwata ni kadai "yayinda habib Ke share mata hawaye yana kuka yana bata hakuri domin yasa duk abinda yasata kuka irin haka mai girma ne muryarsa a sanyaye yace "kiyi hakuri male ki daina kuka kukanki na balain daga min hankali na hakura da son jin komai domin jinsa bazai zame min alkhairi ba amman kema kiyi qoqarin ki manta abinda ya rigada ya
wuce amman iyaye da yanuwa duk abinda sukayi baa yafesu ."yana gama fadar haka ya juya har ya fita ya rufe mata kofar dakin hawaye ne yake fita dga idanunta "yaya suke son tayi da rayuwarta duk abinda suka fad'a mata tasan gsky ne amamn har yanzu zuciyarta ta saka mantuwa akwai wani abu da yake tsaye acikin zuciyarta ta rufe idanunta ta sake jingina jikinta da pillow daya saka mata a bayanta tana jujjuya maganganun yaranta tana yin filla filla dasu tana son kawar da bukatarsu amman tasan gsky suka fad'a mata bata taba daukar ya'yanta zasu girma da son danginta irin haka ba kasancewar suna cikin dangin mahaifinsu."
*****
mrym zaune a d'akin hjy zulaiheart tana shirya mata kayanta da mai gugansu ya kawo tana tsaka da aikin aunty shahida ta shigo bakinta d'auke da sallama ta amsa tana gaisheta fuskarta d'auke da murmushi "aiki kike yi ne haka amaryar ATA tayi mgnr cike da zolaya " sannu da zuwa auntynmu me kika zo mana dashi ta fadi haka dan kawar da maganarta ,cikin dariya aunty shahida ta zauna akan sofa tana cewa "kayan dadi da bazasu fad'u ba maryam tayi murmushi yasu madina kwana biyu shiru kmr anyi ruwa an dauke "ke dai bari madina exam ne ya sakata gaba Amman Ina ganin ma zuwa wani sati zasu kammala ".
"okay to Allah Bada sa'a "Ameen ta amsa tana cewa "wata shawara nazo miki dashi a tsakaninki da ATA jin haka yasa ta dan tsaya ta kasa cigaba da abinda take hankalinta gbdy ta tattara shi kan aunty shahida " Ina sauraron shawara daga bakin aunty nah maganin kukana " Marym please ki sanya kunnen baseera akan abinda zan fada miki "ta sake mika mata hankalinta sosai " kin dai san halin wanda zaki aura yana da kyau ki dan rage wasu abubuwa sannan ki koyi wasu abubuwa nasan kin fahimci abinda nake nufi ki zamo mai kwantar da kai da iya girke girke dan bazance girki ba ,daga ke har nana na fuskanci Kuna da matsala ta wannan bangaren dan haka ki dage ki koyi kowani irin girki da tsafta duk Inda zaki kasance acikin gidanki the next thing shine kamshi domin shi din ma'aboci son dadd'adan girki ne da son kamshi ki zamo mai hakuri da lallabashi domin ta haka zaki yi saurin dakusar da duk wani taurin Kansa abubuwan social media Shima ki rage "dan kinsan bazai yarda dashi ba wasu daukar hoto kullum ana d'aurawa a duniya Shima bazai yarda ba ".
"shikenan naji aunty inshallahu Kuma duk zan d'auki shawararki ki dai tayani da addua biyyaya zanyi a aurena da ya Adam Allah yasa ya zamemin alkhairi "Ameen byn biyyaya har da soyayya sai kunyi aure zaki fahimci hk "Kai aunty babu wata soyayya " ki rubuta ki ajiye a Inda bazai goge ba ko na mutu sai kin fada "Kai aunty shahida bana tunanin yaya zai soni a yadda yake nunawa ni dai zanyi iya yina kawai "karki tsaya iya yinki kiyi kokari ki canzasa gbdy ta yadda zai manta da mafar.."
"wannan Kuma impossible aunty bazata iya ba " suka ji sautin muryarsa acikin dodon kunnensu a tare suka juyo a firgice suka Kalli Inda yake tsaye sanye da farar jallabiyya mai gajeren hannu ajikinsa gashi kan nan nashi sai sheki yake zubawa tamkar balarabe kallon second biyar mrym tayi masa tayi saurin d'auke kanta sakamakon mugun kallo da yake jifanta dashi .matsowa kusa da aunty shahida yayi sosai fuskarsa a hade babu alamun murmushi "babu abinda za'a ta iyayi wanda zai dakusa wannan soyayyar dake dawainiyya da zuciyata da gangar jikina Ina son princess so mai girma sannan gara ki fad'a mata babu iskanci da sakarci a gidana dan bazan dauka ba ."
Take kwakwaluwar mrym ya shiga ceculating abinda mgnrsa take nufi kenan akwai wacce yake so aka takura masa aurenta ?take jikinta ya kama kyarma ya ware hannuwansa duka cikin jin dadi "okay a she fa bata san da wannan zance ba fa ?"gsky ya kama ta san cewar akwai wata acikin zuciyar Adamcy Kuma ko ba dade ko bajima muddin na ganta zata kasance cikin rayuwata bukatata na ganta domin nafi bukatarta fiyye da komai ."
gbdy mrym dake zaune taji babu dadi acikin ranta "tabbas wannan shine dalilin dayasa bai maraba da aurenta wani bakinci ya ziyarci qirjinta ta mike tsam zuciyarta cunkushe ta nufi kofar fita tana fita aunty shahida ta soma magana cikin fushi "wai me yasa kake yin hk ne sam bai dace ba? "me Kuma nayi byn gskyr dake cikin Raina na fada gara tasani ? ''idan kana yiwa mrym hakan bazamu ji dadi ba , rainmu zai dinga baci fiye da bacin ran daka gani yanzu acikin kwayar idanuna ,dan bazamu yarda ka fifita wata banza can akanta ba banzar ma da ba gskiya bace .
"duk son da nake maka zan iya ajjiyeshi gefe na hukuntaka hukunci mai tsanani akan mryam ,kada ka sake makamancin wannan maganar a gabanta wannan ya zamo Karo na karshe ya jiyo sautin mahaifiyarsa wacce ta shigo byn fitar mrym nunfashi ya fesar yana cewa ''relax sweetheart insha Allahu an gama ya fice ya barsu "Allah ka shirya Adamcy na rasa meke damunsa " meke damunsa kuwa ban da iskanci aunty shahida ta katse hjy zulaiheart , nifa wani lokacin sai naji kmr Abar had'in nan kar yazo ya bata zumunci ."babu wani zumunci da zai bata wannan auren Allah ya rigada ya hadashi tunda gashi har ya amince ayi ,da yarda Allah rayuwar gaba zatai dadi "Allah yasa inji cewar aunty shahida.
Da fari baba qarami hjy zulaiheart taso ta kira ta sanarwa hukuncin data yanke kasancewar shi yana bangaren baya inda mallakinsa yake sai dai tayi tunanin ta fara sanarwa baba Babba kasancewarsa babba a tsakaninsu a yanzu saji daga bakinsa
tayi murmushin Jin dadi dan tasan baba qarami zai ji dadi sosai idan labarin auren adamcy dan kusan kullum sai yayi mata maganar ."
*****
a natse ta fara neman layin qanwarta hjy nuriyya wacce ta kasance abokiyar wasanta iyayensu uwa d'aya Uba d'aya Kuma akwai shakuwa sosai a tsakaninsu tana zaune a kasar london tun aurenta har zuwa wannan lokacin acan ta haifi yaranta duka iyakarta da naija ziyara ko wani sha'ani mai mahimmam. suka gaisa cike da farinciki Inda hjy zulaiheart take sanar mata batun hada Adamcy aure da maryam " Kai alhamdulillah masha Allah gsky abu yayi kyau sosai Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokaci ,wannan karon zanyi k'okari na shigo kasar kafin lokacin domin ayi biki dani ".
Hjy zulaiheart tace "gsky kam anyi bukukuwa duk baki samu damar shigowa naija ba "haka ne kam amman inshallahu zan shigo wannan bikin nayi ne no any excuse ta k'arasa maganar tana murmushi suna cikin hirar hjy zulaiheart tace "nuriyya wai kuwa kina jin labarin bilkisu ?dip hjy nuriyya tai tmkr an d'auke wuta nepa tana jin wani irin daci acikin ranta sai data yi kusan minti biyar sannan tace "bana Jin labarinta Kuma bana son na ji labarin Inda take , kuma Ina son ku shareta ku cireta acikin zuciyarku har abada Kmr yadda mukayi yarinyar data nuna mana bamu Isa daita ba ,sannan bata sonmu ta zabi rayuwa ko babu mu me yasa zamu damu daita ?
"ni dai duk wanda zai nemata acikinku yaje amman ni nuriyya bana ciki kuma babu hannuna babu kafa ta ciki "naunayen ajiyar zuciya hjy zulaiheart ta sauke tana cewa " dan Allah nuriyya kiyi hakuri ko babu komai rayuwarta qaddara ce Allah ne ya d'aura mata wannan rayuwar babu yadda zata gujewa qaddararta ,wallahi duk sanda ta fado min sai na zubar da hawayen tausayinta , da nasan Inda zanganta wallahi zan nemota .
"Kune fa kuka damu daita ko nace ke dan duk cikinmu babu me zanceta wallahi sai ke ,bata ga wuya bane shiyasa bata dawo ba, wallahi nafi son rayuwa ta juya mata baya ta dawo tana kuka tana rokonmu kullum mummunar adduar da nake mata kenan sannan Ina adduar duk tsanani karta dawo mana da zuria Kmr yadda hhyrmu take addua ."
"wannan addua ta rashin haihuwa a tsakaninsu batayi ba ku daina mata mummunar addua gskiya "ai babu abinda ya kamaceta da wuce mummanar addua " yanzu dai kiyi hakuri muyita mata addua da fatan alkhairi a duk Inda take lokaci nata tafiya a lisafinsa shekaru ashirin kenan rabonmu daita , kiyi hakuri dan mu barwa Allah komai sannan muyi mata adduar Allah yasa ta waiwayo mu cikin koshin lafiya naunayen ajiyar zuciya hjy nuriyya tayi sannan tace "shikenan big sister ai abinda kikace shi zamuyi cike da qauna yar'uwarta hjy zulaiheart sukayi sallama da yaruwanta suna gama wayar uncle Umar ta kira ta sheida masa tana son ganinsa ."
Ranar asabar da misalin karfe hud'u na yammaci baba bAbba yazo bisa Kiran da hjy zulaiheart tayi masa , byn sun gaisa hjy zulaiheart ta karanto masa hukumcinta akan ATA cike da farinciki uncle Umar yace "masha Allah wannan hukuncin yayi Kuma mun gamsu dari bisa dari dan burin mu bai wuce muga adam ya ajiye iyali ba ,bugu da Qari zaa sake karfafa zumunci a tsakanin inshallahu zan sheidawa sauran yan'uwana sai mu saka ranar da zamu ga alhj saidu dan zamu so a daura auren nan kusa". "wannan maganar tayi Kuma naji dadinta sosai dan haka a fara sheidawa baba qarami dan nasan murnarsa sai tafi ta kowa domin duk yafi mu d'auki son ganin Adamcy yayi aure ta k'arasa maganar tana murmushin jin dadi "ai kuwa daga nan ma bangarensa zan shiga na fara sheida masa Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokaci "Ameen ya Allah,Allah kadai yasan murnar da zaiyi idan yaji ya sha lemu da kayan snaks din da'aka jera masa suka zarce da tautaunawa kafin daga bisani sukayi sallama ."
Baba qarami na zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga baba Babba wanda ya kasance yaya garesa Kuma Kani ga mahaifin ATA yana ganinsa ya saki fuska tare da farincikin ganinsa ya d'an mike tsaye cike da girmamawa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya nuna masa mazauni atare suka zauna "sannu da zuwa yaya ! "ya gida da iyalin fatan suna lfy?"alhamdulillah kowa Lafiya yake ya naka iyalin ?"Suna lfy ya bashi amsa yana murmshi ya mike ya dauko masa abun sha "bazan sha komai ba daga bangaren hjy zulaiheart nake na sha " .
suka yi shiru na second biyu sannan baba babba ya fara magana a tsanake " kamar yadda na fad'a mk daga bangaren hjy zulaiheart nake tayi decide ta had'a Adam aure da diyar kaninta abdulrauf " what ?"when ?ya fada a matukar rude yana Jin wani irin abu ya caki kahon zuciyarsa , yayi saurin runtse idanuwanshi "zulaiheart na bukatar wannan labarin ya zamo Kaine ka fara jinsa bisa kokarinka na son ganin adam ya ajiye iyali dan haka nan da sati me zuwa zamu gana da yayan mahaifin yarinya alhj saidu ."
shiru baba qarami yayi har sanda yayansa ya dasa aya ya mike tsaye"to ni zan wuce duk abinda ake ciki zan kiraka a waya a fusace baba qarami ya mike Shima yana cewa "yaya wannan wace irin maganar banza ce kazo min dashi sannan kana k'okarin sa kai ka wuce ka barni ? yayi mgnr a fusace yana sa hannu ya daki center table din dake tsakiyar falonsa wanda ke d'auki da ruwan lemu kala dabam dabam ,nan take wasu glas cup suka tarwatse yana huci yake kallonsu "yanzu ni dana cin burin ya zabi daya daga cikin ya'yana ya aura shine dan munafurci zata hadashi da diyar kaninta saboda son Kai irin nata ?
"ya'yana yafi dacewa Adam ya aura ba wannan yarinyar ba ya sake dukan table wanda hakan yasa gbdy ahlin da ke numfashi a part din suka bayyana" burina bai wuce ya'yana ko jikokina su had'a iri da dashi ba yayi mgnr yana kallon cikin kwayar Idanu dan uwansa ."me yasa zaka fadi haka idris? "eh na fad'a yayi mgnr yana cakunar wuyan dan'uwansa da iyakacin karfinsa yana maxurai abinda bai taba faruwa ba a tsakankanisu ,hindatu wacce suke kira da hindu ta samu guri ta zauna tana kallonsu zuciyarta na rawa dan ta dade a tafkin qaunar ATA mahaifinta ne ya hana a fito da soyayyar a cewarsa yana jiran lokaci yau ga lokaci ya zo masu a wani iri .
sauran kuwa hankalinsu ne yayi kololuwar tashi ganin yadda mahaifinsu ke rike da wuyan dan'uwansa uwa d'aya Uba d'aya .Wallahi yaya Kai kare ne da bai san ciwon kanshi ba ! "shin ya'yana basu dace dashi bane ka bani answer ?uncle Umar yayi shiru kawai yana kallon hannun uncle idris dake rike da wuyansa batare daya ce uffan ba.
"me yasa kazo min da wannan banzar labarin mara dadin ji ?ya k'arasa maganar yana sakar masa wuya yana dubansa yana huci "saboda mu bamu Isa ta hada jini damu ba shiyasa ta za'ba masa acikin dangi ta ?"to me zai faru idan na hana auren ?"zan hana wannan auren ta karfin tsiya yayi mgnr yana d'aga hannunsa sama sannan ya dungule ya naushi bangon falon sai da gurin ya tsage ya tsaya yana huci da kallon wani bangare ."
Baba babba ya tsaya abayansa hankalinsa a matukar tashe " maganarka gaskiya yayanmu suka fi dacewa da aurensa sai dai kayi hakuri dan'uwana bana tunanin da wata manufa zulaiheart ta had'a wannan auren ,idan baka manta ba shekara nawa ana fama da yaron nan akan ya fitar da mata yayi aure bana tunanin zata ki had'a zuria da daya daga cikinmu sannan da kasan kana da wannan burin me yasa baka fito dashi ba ?
Baba qarami bai ce uffan ba illa numfashi da yake sauke da sauri sauri gumi na karyo masa "dan haka kayi hakuri karka bari wannan matsalar ta zamo Silar da za'a samu matsala ka bar wannan burin bayan anyi wannan auren sai ayi maganar a had'ashi da daya daga cikin yaran".
"Kai kare idan ka sake yin min wannan maganar banzar sai na datseka gbdy Komai naka banga ta yadda nawa burin zai zama daga baya ba muddin d'aya daga cikin yarana basu yi nasarar shiga sawun farko ba babu wacce ta Isa ...."
"kayi hakuri ka yafe min ban fad'i haka dan quntata maka ba ya fadi hk kasancewarsa me saukin Kai sannan marason tashin hankali yafi son yayi rayuwarsa cikin salama duk maganar da baba babba yake sam baba qarami bai juyo ba ",shi wannan Karen zai wuce sai kaji daga garesa sai dai ya kamata ka sakin ranka dan wata rana ....saurin d'aga masa hannu baba qarami yayi still bai juyo ba sai dai qirjinsa sai faman bugawa yake Uncle Umar ya juya cike da matsanacin firgici da yanayin dan'uwan nasa ."
sai lokacin baba qarami ya juyo yabi bayansa da wani irin mugun Kallo Idanunsa a waje har sanda takunsa ya kai uku bai juyo ba haka shima baba qarami bai daina kallonsa ba .a sanyaye fahad dansa yabi bayan baba babba zuciyarsa na rawa dan shi kansa ya koka da abinda mahaifinsa yayi ya raka uncle Umar sai dai bai Kai shi har bakin get ba a tsakiyar hanya ya barshi yana bashi hakuri "karka damu fahad na gode allah yayi maku albarka ya amsa da Ameen ya dawo part dinsu da sauri .
falon ya d'auki shiru na tsawon lokaci yana tsaye yana tunanin bayanin daya samu daga bakin dan'uwansa a yanzu wanda yake jinsa tamkar dalma acikin zuciyarsa , "uhmmmm yanzu dai ta nuna mana cewa itace uwar Adam Kuma ita kadai ke da iko akan shi ?sai mugani idan shi din d'an mace ne Baba qarami yay maganar yana jan tsaki a fili tare da watsa katuwar harara da mugun kallo kamar tana gabansa fahad ya d'auki farin glass cup ya tsiyaya masa tattacen ruwan inibi ya mika masa "kasha baba kaji sanyi a ranka yasa hannu ya Kar'ba ya rike shi gam a hannunsa sai dai bai sha ba haka zalika bai ajiye ba."
"zan iya kasheki akan wannan haukan da kika yi zulaiheart domin Ina da tanadi da buri akan adam ya karasa maganar yana filinging da cup din hannunsa a fusace Wanda yasa take yaransa maza da mata tare da matarsa suka sake shiga rud'ani cike da matsanacin firgici suna kallonsa gabansu na faduwa ban da Hindu data samu guri ta kame akan kujerar da mahaifinta ya tashi zuciyarta tafi ta kowa zafi da tuttukin bakinciki tare da shiga tashin hankali" Fahad ...." !
ya kira sunan dansa Wanda aka kira da hkn ya d'ago ya kallesa a matukar tsorace batare da yace komai ba "abinda na fada Ina nufi har cikin zuciyata gara ta bar duniya ko ita yarinyar ta bar duniya akan rasa burina yayi maganar yana nuna sa da d'an yatsansa "wannan shine Karo na sau babu adadi da take kawo mana tashin hankali tun dan'uwanmu na raye dan haka Ina son kasheta na huta da ganinta a doron duniya muddin ba daya daga cikin ya'yana adam zai aura ba ."
daya bayan daya suka shiga kallon junansu cike da mamakin jin furunci mahaifinsu hatta hindu wannan karon atsorace take kallon mahaifinta ta gigita kwarai da gaske "a kullum kokarina naga na kawar daita a duniya darajan halakar da nake son qullawa adam yasa na barta ya karasa maganar a kausashe .yayi taku daya biyu ya tsaya gaban hindu yana kallonta "kece ya kamata ace kin auri adam ba wannan yarinyar ba kije kiyi rayuwa tamkar sauraniya a gidansa ki taka kowa yadda kike so sannan ki juya duk Wanda kika ga dama wannan hannun nawa babu abinda yasani a halin yanzu kamar ya wahalar da zulaiheart ya gigita ta hanyar azabtuwa mai muni ,ya matso kusa da hindu Sosai suna fuskantar juna "wannan karon fuskarsa da murmushin mugunta akanta "ke hindu ko zakiyi iya karfin halin kashe min zulaiheart?
Wani sanyayyayen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta wanda mahaifinta ne kawai ya fahimci manufarsa ganin yadda ahlinta suke kallonta a tsorace yasa tayi saurin waskewa tace "baba me yasa kake mgn fiyye da kaida ?gsky sam sam hakan bai dace ba tayi maganar tana kawar da idanunta gefe al'amun bata ji dadi ba gumin da ya tsatsafowa sauran yanuwanta suka shiga gogewa suna sauke numfashi da ajiyar zuciya atare Jin abinda tace daman km ita kad'ai ke iya fadawa mahaifisu mgn kai tsaye batare da shayi komai ba , a hankali ya juya yana taku cikin tsananin damuwa da tashin hankali suka juya gbdy suna kallon bayansa har ya shige bedroom dinsa yana shirya yadda zai kawar da hjy zulaiheart ko mrym daga doron duniya .."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 13
"Baba qarami na kwance har kusan tsakiyar dare ya kasa runtsawa dan sam bacci yaki zuwan masa sai faman juyi yake akan makeken katifarsa ,yayinda matarsa hjy aljannatu ke d'akinta kwance tana sharar bacci amman shi kuwa baba qarami sai tufka yake yana warwara ya d'an zabura ya mike zaune daga kwanciyar da yay, ya had'e hannunwansa duka waje d'aya "babu tantama hjy zulai tana da manufar had'a wannan auren yasan tayi haka ne dan kar wani acikinsu yaci arzikin d'anta , kunga idan ta had'asu aure da diyar d'anuwanta dole dai arzikinsa yana tare daita , dan da zarar mrym ta haihu dashi komai na adam zai dawo nata gbdy zuwa yanzu dai bai san abinda ya kamata yayi ba ko hanyar da zai bullo masu a maida auren Kan diyarsa ."
Sosai kwakwaluwarsa tayi zurfi cikin tunani neman mafuta har bai san sanda hindu ta shigo d'akin ba , ta matso kusa dashi ta tsaya tana jijjiga baba qarami wanda yayi nisa cikin duniyar tunani "baba baba !! " ta kira sunansa har sau biyu ajere sannan yayi firgigib ya dawo haiyacinsa " wai meye haka baba?" me yasa zaka damu kanka akan wannan 'yar qanqanuwar matsalar ?" baba qarami bai iya amsa wa ba sai zuba mata rinannun idanunshi da yayi yana dubanta har lokacin yana maimaita abinda ta fad'a " ai a wajensa wannan ya wuce gagarumin matsala ba qanqanuwa ba ko ita kanta tasan da zaman haka ta dai fad'a ne dan kwantar masa da hankali shi kuwa hankalinsa bazai ta'ba kwanciya ba matukar ba ganinta yayi a matsayin matar adamu ba ."
"Dan girman Allah baba ka kwantar da hankalinka mubi komai a hankali idan muka bari suka fahimci wani abu attare damu bazamu iya nasara akansu ba " cikin wani irin murya mai gyaraye da tashin hankali had'e da rud'ani yake furta "bazan iya ba hindatu , bazan iya kwantar da hankalina ba muddin ba ganinki a gidan adamu nayi a matsayin matarsa ba ,maganar aurensa da mrym ta dokeni fiyye da tunaninki ,Allah Allah nake gari ya waye naje ga zulai ayita ta qare domin kece kika fi dacewa da Adam ba wannan yarinyar ba dan wannan tsantsar muguta ne kawai take son nunawa"kai dai baba ka dan boye damuwarka baba" .
D'akin ya d'auki shiru tamkar babu wasu halitta acikinsa sai na qara ac dake aiki da kuma saukar numfashinsu haka zalika baka jin motsin komai daga sai na tsuntsaye dake shawagi kasancewar a gra suke hindu ta sauke numfashi tana mai kamo hannunta mahaifinta cikin nata "idan kaje me zaka cewa mami akaina ? " zan so nasan abinda zakace baba idan ma hali kaje tare dani ayi komai akan idanuna shekaru sha biyar kenan , tun inada shekaru sha shida nake dakon soyayyarsa bazan iya jurar rasashi ba, bazan zuba idanu wata ta mallakesa ba "zan fad'a mata komai akan soyayyarki ni ko ta biyu ce kizo bazan damu ba burina ki kasance matsayin mata acikin gidansa , ki zama tmkr sauraniya, ki yi yadda kike so nima nayi yadda nake só da kamfanunuwansa ."" nan take ta had'e fuska tamkar dariya ba muryarta a kausashe ta cigaba da mgn "muddin a ta biyu zanzo nasan bazai ta'ba aurena ba , ya adam fa yana da tsari acikin rayuwarsa shi din ba mutun bane kamar sauran mutane bashi da raayin tara mata "wa yace miki bashi da raayin haka ? zai yi raayi dan uwarsa Allah dai ya kai mu gobe tare zamu wajen uwarsa kafata kafarki ."
Baba qarami ya mike tsaye ya goya hannunwansa abaya yana girgiza kai yana duban hindu kafin daga bisani ya matso kusa daita sosai ya soma mgn can kasa kasa kusan mintuna goma yana mata mgn murmushin jin dadi né ya bayyana akan fuskarta " idan bata yarda ni na zama matarsa ba I will killed mrym idan ni ban samesa ba to babu wacce zata mallakesa anan gidan duniya yadda take mgnr zaka fahimci da gaske take kuma har cikin ranta abinda take nufi kenan ganin byn maryam ."
Washegari da misalin karfe goma na safiya a kofar shiga bangaren hjy zulaiheart tayi masu kai tsaye a babban falon gidan suka iske mami zaune yayinda d'aya daga cikin masu aikinta ke zaune tana mammatsa mata yatsun kafafunta sallamarsu baba qarami tasa mami dauke idanunta daga Kan tv ta maida kansu tana sakin fuska sai dai kallo d'aya tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ,aranta tayi addua allah yasa ba wata matsalar bace ta taso , ta amsa sallamarsu tana cewa "sannuku da zuwa !" baba qarami ya samu waje ya zauna akan kujerar dake fuskantarta yayinda hindatu ta zauna a kasa kan kafet a gaban mami ta sunkuyar da kanta kasa tmkr mai neman gafara tare da gaishe da mami cike da ladabi ta amsa tana mami ta maida hankalinta ga baba qarami tana nazarin fuskarsa sannan ta kalli yarinyar dake zaune a gabanta tace "salaha tashi kije Ki bamu guri cikin sauri yarinyar ta mike tare da fadin "tô !"
Mami ta sake maida hankalinta sosai garesu sannan ta fara magana a natse "baba qarami fatan dai lafiya dan naga yanayinka ba kamar yadda na saba ganinka ba yace "lafiyar dai da sauki "ta gyara zamanta cikin tsananin damuwa "daman dai na lura da hakan dan ba haka yanayinka yake ba kai din mutun ne mai faram faram duk sanda za'a ga fuskarka cikin murmushi take tô ina jinka fad'a abinda ke tafe da kai ."
Naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana sake gyara zama yace "zulai jiya baba babba yazo min da wata magana akan hukuncinki akan Adam" ta gyada kai tana sauke numfashi "haka ne nasan zaka fi kowa jin dadi "tabbas naji dadi sai dai wani hanzari ba gudu ba nima na dade ina son had'asu aure da hindatu "mami tayi shiru tana dubansa da hindu dake zaune tana nazarinta tana son gano wani abu atattare da hindu domin dai ita din macece mai tsananin baseera tare da saurin karantar mutun sai data numfasa sannan tace "ita hindatu tana son shi ne ?
"tabbas tana tsananin sonshi na tsawon shekaru tunda tashi da soyayyarsa ta tashi ni ne mutun na farko data fara sheidawa da fari na nuna mata illar rayuwar data jefa kanta na afkawa soyayya da qarancin shekarunta alokacin na tmbyeta meye dalilinta na son shi ? me ya dauki hankalinta akanshi ? tace ba dan yana dukiya da kyau ba ,yau da zai wayi gari bashi da komai bashi da hannu bashi da kafa koda akan titi zasu rayu zatai rayuwa dashi kawai son shi ta keyi dan Allah alokacin shekarunta shashida né kawai wanda ni nake ganin bata san ma me take ba bama tasan meye soyayyar ba yasa take fadin haka ahankali baba qarami ya fayyacewa mami komai akan soyayyar da hindu ke ma ATA babu abinda ya rage numfashi mami tayi ta saukewa tana girgiza kai cikin tausayawa tana kallon hindu data sake dukar da kanta kasa sosai ."
"Masha allah naji dadin wannan abu sosai soyayya mai hade da zumunci allah ya bamu ikon sada zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba ". ta sake numfasawa ta cigaba da magana "nima daman tun farko burina kenan adamcy yayi aure biyu" ahankali baba qarami ya kalli inda hindu take wacce mgnr mami yasa ta dan dago kanta mami ta cigaba da magana "zan yi iya kokarina hindu na kawo karshen damuwarki duk da adamcy baya da raayin ajiye mata biyu amman zanyi convincing dinsa domin kawo farinciki arayuwarki da yarda allah ."
da sauri hindu ta kalli mahaifinta shima din ita yake kallo domin dai yasan diyarsa da tsananin kishi zata fi bukatar ganin ita kadai ta mallakesa Kmr yadda ta sheida masa kallon da takewa mahaifinta só take yace a fasa auren da mrym gbdy ya aureta shi kuwa baba qarami a hakan ma maganar tayi masa dadi "fatana mu hadu muyi addua akan lamari sannan mu nemi zabin allah allah kuma yasa gogan naka ya yarda ya amince ya hadasu su biyu din , ku bani lokaci kadan zan yi magana dashi duk abinda mukayi dashi zan nemeka da wannan maganar suka kawo karshen zance sukayi mata sallama ."
Suna shiga dakin baba qarami hindu ta fara zubar da hawaye acikin slow voice tace " baba ina ji ajikina ya adam bazai aureni ba dan dai idan amincewarsa zaa tsaya nema wallahi bazai ta'ba amincewa ba bugu da qari ni banason sharing dinsa da kowa nafi son ni kadai dan sam ban dace da zama da wata aba kishiya ba zan só mu rayu dagani sai shi ta karashe mgnr tana shesheka murmushi baba qarami yayi tare da fadin "hindu kalleni nan " ta tsura masa idanunta Kmr yadda ya bukata "ki kwantar da hankali babu wani abu acikin ya haduku biyu din amincewarsa shine abinda muka fi bukata a yanzu dan zaki iya kawar daita byn auren ki zauna ke kadai keda kike da baiwa iri iri nasan zaki bawa babanki mamaki haka dai baba qarami ya tasa hindu a gaba yana kwantar mata da hankali babu laifi hindu ta saki jikinta tare da karfafa zuciyarta sai dai ta rantse muddin bata samesa babu wata mace da zata mallakesa tana raye ."
****
Sanye ATA yake cikin farin yadin vol mai shegen haske da tsada a hankali yake taku yana gyara zaman hullarsa baki haka zali takalmin dake sanye da kafafunsa black cover shoes ne tsintsiyar hannunsa daure da agogon rolex yana dumfaro falon kamshi turarensa ya mamaye koina Kmr shagon turare yana gama qarasowa yace wa hisham "muje ko ".kai me yasa bakasan ka bawa mutun rai ka bashi hakuri ba duk lokacin dana bata ina zaman jiranka da muje ko zai qare " ina laifin kace hisham Afuwa kayi hakuri muje abokina km danuwana."
Dogon tsaki yaja kawai batare dayace uffan ba .
"matsalata da kai kenan ka gama bata lokaci amman zaka wani jawa mutane tsaki still bai ce komai ba
ya nufi hanyar dakin mami tana zaune ya shigo ta dago a natse tana duban kofar ganin shine cikin shigar da tafi qauna ta saki fuska cikin tsananin farinciki tace "Masha allah adamcy nah kayi kyau sosai allah yayi maka albarka ,sai dai wannan uban wanka da kashi haka kmr yau daurin aurenka, ai ko yau né daurin aurenka sai iyakarka hk kai ni kamar ma har da hoda ka shafa ko? Tsuke bakinsa yayi dan tsokanar sweetheart dinsa na yau yazo da wani salo ana zaman lfy me zai yi da wani hoda shi ba mace ba ."
"sweetheart ni zan fita amman zan dan jima ban dawo ba dan yau zaa bude kamfanin tace mai petir da sinadarin gas "Alhamdulillah masha ,allah allah yasa albarka arayuwarka data kasuwancinka allah ya tsare min kai ,yadda zaka fita lafiya allah ya dawo da kai lafiya sharrin mutun da aljani Allah rabaka dashi yace "Ameen !atakaice ya juya a natse yana taku tmkr wani jinin saurata "sai na dawo sweetheart ." a dawo lafiya adamcy nah ta fad'a tana cigaba da kallon bayansa "yau tsawon kwana uku kenan tana son sheida masa bukatar baba qarami amman ta kasa, ita kanta tana jin tsoron tunkararsa , tayi dukkanin tunaninta ta rasa ta ina zata fara shigo masa da maganar , auren mrym ma da yaya ya amince yanzu kuma ta sake kawo masa mgnr wata tasan tattara wa kawai zai yi ya gudu ya barta dasu ."
har ya kai bakin kofa yana shirin d'aura hannunsa akan handling din kofar ya tsaya cak ya waigo
bayansa adaidai lokacin da mami ta sauke numfashi da girasa ya tambayeta ,ta girgiza masa kai kawai tamkr wata marainiya "ko akwai damuwa ne ?ta sake numfasa wa kana tace " babu komai adamcy nah ina dai kallonka ne kayi min kyau sosai shigar ta amshi jikinka "me yasa bazanyi amfani da wannan damar na fad'a masa bukatar kanin mahaifinsa ba ? tayi mgnr acikin ranta da sauri zuciyarta ta gargadeta "karki soma yace ya fasa auren gbdy gashi goben nan zaa je neman masa auren mrym numfashi ya fesar "saboda Ke nayi shigar dan nasan zaki ji dadi gaahi yau juma'at "ai kuwa naji dadi kwarai da gaske na kuma gode sosai allah ya baka zuria masu albarka yadda kake ji dani kake min biyayya Allah baka masu yi maka bai amsa ba ya sa kai ya fice daga dakin zama ta cigaba da yi tana tunanin mafuta zata jajurce da tsayuwar dare domin neman zabin allah dan shine kawai mafuta agareta."
Aunty abinda na gama jin bayanin ibrahim taji kafafunta suna barazanar kasa daukarta lokaci daya zuciyarta na barazanar tarwatsewa Ibraheem ya matso yana girgiza Aunty abinda wacce ta dawo tmkr mutun mutumi "abida abida!! lafiyarki what's wrong abida?abida tayi shiru kawai tana sauke numfashi batare data amsa ba " baba babba zasuje nemawa ATA auren maryam gobe goben nan idan dai ba karya kunnuwanta suka jiye mata ba haka taji ya fito daga bakinsa " ibrahim me naji kace ? tana bukatar ya sake maimaitawa babu bata lokaci ya sake maimaita mata " wai tukunna wace maryam zai aura ?"maryam dai wacce Ke zaune a gidan mami diyar kaninta ita zai aura "da gaske ka tabbatar mrym zai aura ? ya gyda mata kai kawai yana maida hankalin Kan wayarsa dake qara "
"ina sam sam wannan aure bazai taba yuwa ba ta runtse idanunta da karfi ATA jarumin nmj né uwa uba kyau da natsuwa da Kamala ga tarin dukiya dasanin yakamata ai babu macen data dace dashi sai sultana gani yana mata wani irin kallo tayi saurin dawowa haiyacinta sunanta ya sake kira tare da jawo hannunta ya zaunar daita akan kujerar daya tashi cike da rauni tare da yin kasa da murya yace "abida meke damunki ?babu abinda ke damuna nidai dan Allah kar aje neman auren nan wai ma waye ya hada wannan auren ?shi ATA din da kasan ne ya zabi auren mrym din ?"ta karasa maganar cikin tsananin tashin hankali da bacin rai akan fuskarta ."
"me yasa ?saboda me kar aje neman auren ?"
Meye damuwarki da aurensu ? kanta ta rike da duka hannuwanta ta fuskancesa cikin sanyin murya tace "sbd sultana né bazan só ATA ya auri wata ya bar sultana ba "ita sultana tana son shi ne ?eh ammm daman umma ce ke ...."sai km tayi shiru ta kasa qarasa mgnr. "auren nan fa kamar anyi shi an gama domin babu wani abu ko mahalukin daya isa ya hana wannan auren mami da kanta ta hadata wannan auren ,ATA nason yarinyar ko baya sonta wannan shine bansani ba amman zuwa neman aure wannan dole ne gara ma ki binne duk abinda ke ranki karki shigo da wata magana da zata janyo matsala cikin jin haushi tace "idan kuma rabon sultana né fa ?har ya bude baki zai bata amsar tmbyrta wayarsa ta sake daukar qara ya dauka yana duba screen din wayar sunan ATA yaga yana yawo cikin sauri ya mike ya dauka ya soma mgn yana juyawa zuwa kofar fita tana ganin fitarsa ta mike tsaye ta soma zagaye falon tana maimaita abinda ya fada mata ashe kuwa zaayi wulakanci acikin gidan nan ko ta wani hali koda tsiya koda tsiya tsiya sai tayi duk abinda zatayi sultana ta shiga gidansa koda ata biyu ce ."
*****
"Maryama kyakkyawar budurwa ce mai kyan gaske doguwa ce sambal dan tsawonta bai sa ta rankwafa ba sai dai ita din ba fara bace haka zalika baza'a kirata da baka kirin ba chocolate colour ce tsayinta ya fito sosai domin irin matan nan ne masu shape din cocakola tana da siririn hanci da manya idanuwa masu matukar d'aukar hankali dan duk wanda tsautsayi yasa ya kalli cikin kwayar idanunta sai ya kusan suma saboda wasu sirrika da Allah ya hallita acikinsu masu kallon cikinsu ne kawai zasu iya karar da yanayin da suke tsintar kansu ."
idan tayi murmushi kuwa zaka ga siraran wushiriyarta sama da kasa sun bayyana wanda sune suke qara haskaka kyawunta ,ga gaban goshinta kwance suke da suma luf luf !! duk da kanta a daure yake a koda yaushe da d'ankwali amman kallo daya zaka mata ka gano irin matan nan ne masu yalwan gashi sannan tana da kafa mai kyau haka ma yatsun kafafunta zara zara ne lullube da farata masu matukar haske haka zalika muryarta idan tana magana dan dole ka tsaya ka saurareta kuma dole ka kalleta ."
Maryama ta samu tarbiya mai kyau daga gurin mahaifiyarta tayi karatunta na primary har zuwa matakin jami'an acikin jahar lagos kuma duk akarkashin kulawar gwanaty , haka bangaren karatun alqurni baa barta abaya ba domin tun tana primary ta sauke alqurni km hakan bai sa ta daina zuwa islamiyya ba idan kaga bataje ba sai dai wani aiki ne ya sha kanta ."
kyawun maryama mai tsayawa ne arai sai dai duk da wannan kyawu nata bata da wani tsayayyen saurayi duk wanda yazo neman aurenta dayazo sau d'aya zuwa sau biyu zai daina zuwa batare da wani dalili ba koma karshe taga ya koma gurin kaulat diyar kanwar babanta Aunty hassana gata da kyau sosai na bugawa a jarida amman mutane na mata kallon mai bakin jini abun yana d'an damunta sai dai bata nunawa dan ba samari bane a gabanta karatunta ya fiyye mata komai mahimanci koda yaushe ka kalli fuskar maryama zaka ganta a daure sakamakon rashin farinciki shiyasa mutane suke mata kallon mai tsananin girman kai ."
Sannu ahankali maryama take tafiya tamkar tana jin tausayin qasa ko macijiya dan babu wani karfi a tattare daita cikin shiga ta Kamala riga da sket dinki zamani da kuma dogon hijab mai hannu har qasa fuskarta manne yake da bakin nikaf kalar hijab din jikinta wanda ya zame mata jiki a duk sanda zaka ganta a waje ko a makaranta da wannan nikaf din zaka ganta sam bata yarda ta fita koina batare dashi ba a cikin gidansu ne kawai zaka iya ganinta sadaka yayinda kafad'arta Ke makale da jaka baka mai dogon igiya ,a zahiri kana kallonta kasan a matukar gajiye take dan yanayin tafiyarta ma ya qara yin slow sa'banin na sauran lokuta sakamakon ranar data kwaso gefe da gefenta qawayenta ne subai'a da sumaiya ne suka sakata a tsakiyarsu ."
Tafiya suke a natse suna hirar yadda jarabawar su ta qarshe ta kasance adaidai jeaction din ummahani street suka rabu da kawarta sumaiya tayi hanyar hagu da zai kaita unguwar daji suka cigaba da takawa da subai'a itama dai tafiya kadan sukai tayi dama wato markaz ya saura ita kadai ta cigaba takawa zuwa unguwarsu market street batayi wani doguwar tafiya ba ta qaraso unguwarsu bata tsaya akoina ba sai kofar qaramin get din gidansu wanda kallo daya zaka masa kasan na masu rufin asiri ne dan bazaa kira gidan da gidan mai kudi ba haka zalika bazaa kiran gidan da gidan talaka fútik ba daidai misali gidansu ginin da ne kuma ginin kasa ne filasta ne ya rufawa ginin gidansu asiri da kuma jamar dake rayuwa acikin gidan ."
a natse ta shigo haraban gidan nasu idanunta ya sauka akan kaulat wacce ta sha kwaliya cikin atamfar chiganvy gold black touch of milk ,kallo daya tayi masu ita da wanda ta gani tsaye ta dauke idanuwanta zuwa wani bangaren tana cigaba da tafiya dan wanda suke tsaye da kaulat din ba bako bane a wajenta tasha ganinsu tare ."duk da bilal baya ganin faukarta amman duk sanda ya ganta yana rasa natsuwarsa a kullum burinsa yaga fuskarta yaga yaya take ,kasa cigaba da motsi yayi daga inda yake tsaye yabi tafiyar maryama da wani irin kallo komai nata a natse most especially tafiyarta abun burgewa shi kam ina ma zata yarda ko sau d'aya ta bude nikaf din yaga fuskarta yasan zatai kyau duk da bai ta'ba ganin fuskarta ba."
Kaulat na ganin irin kallon da yake mata taja dogon tsaki yayinda maryama bata sake duban inda suke tsaye ba ta cigaba da tafiya zuciyarta na matukar jin tausayi kaulat dan babu abinda tasa gaba sai aikin tara masu samari marasa inganci a gida maimakon tai concentrate akan karatunta da kullum yake yin baya sai ta maida hankalinta ga tara samari marasa amfani , tare suka shiga jss one ,sukai jss1 tare, sukai jss 2 tare sukai exam na zuwa jss3 ta barta suka wuce ss 1 ita da sakina itama sakina lokacin da zasu shiga ss2 tayi fail ta wuceta sai dataje ss3 sannan kaulat taje ss1 sakina taje ss2 gashi ita yanzu daga rubuta jarabawar karshe ta fito amman ita kuma har kullm cikin repeating take a qalla a tunaninta tayi repeating ya kai sau hudu allah yayi mata jarabawa ta rashin ilimin dan babu abinda tasani daga bokon har islamiyyar zero ce amman ita da mahaifiyarta kullum cikin cin zarafin mutane suke barin ma ita da tarasa dalilin dayasa suka tsaneta suka tsani ganin wani tare daita duk wanda zasu gani tare daita wala mace wala nmj sai sunyi qoqarin rabasu "
"Wai bilal meye haka ne ? ka wani karkace kai kana kallon maryama gbdy ma ka manta ina tare da kai idan kasan ba wajena kazo ba na qara gaba dan na fahimci duk sanda kaga wucewarta sai ka maida attention dinka wajenta ko zuciyarka na kanta ne sai kayi min bayani nasani ba wai ka raba hankalinka gida biyu ba alhalin ina tare da kai "?
"wallahi da tun asali ita na fara gani to da babu abinda zai kawoni wajenki yayi mgnr acikin zuciyarsa amman a zahiri cewa yayi "meye laifi dan kalli halitta mai natsuwa ? ta zaro idanuwata waje tana masa wani irin kallo kafin daga baya cikin d'aga murya cike da maseefa tace "ko zaka koma wajenta ne ko me kake nufi da wannan maganar ?da zan samu haka wallahi da naji dadi sosai "ya sake fad'a acikin ransa "ai daman haka halinku maza yake da zara kunga mata sai kama 'bare 'bare to du ka gama 'bare 'barenka ka hakura dan ita wannnan dai ko ka koma wajenta ma dole ka gudu da kafarka dan idan kasan akanta matsalar duniya ta qare, kana fara soyayya daita komai daka mallaka zai qare idan kayi sa'a ma wani mummunar bala'i bai sameka ba tayi samari day day sun kai guda hud'u kuma duk da aure suke sonta amman da zarar sun fara zuwa zance wani mummunar bala'i Ke samunsu ganin ta inda take shiga ba nan take fita ba yasa ya matsota sosai ya rage murya ya soma magana ."
"Haba kaulat banda sharri fa dan kawai mutun yace yana sonta sai wani mummunar bala'i ya samesa sai kace wata annoba ,wannan ai tafi annoba "to ko zaki hadani daita kawai ina son naga tasirin bala'in dake tattare daita ?tayi shiru kawai tana nazarin maganarsa idan zata kintata daidai son maryama yake cikin karayar da murya kaulat tace "me kake nufi da wannan mgnr ?ya tsura mata idanunshi kawai "kaga bilal banason wannan maganar karka qara min hk da kuka ta qarasa maganar dan duk cikin samarinta tafi qaunar bilal "ya salam !meye kuma abun kuka anan daga wasa ?kuka kaulat take sosai ganin haka hankalinsa ya tashi sosai "kinga wallahi ni wasa nake ya ciro hankacip ya mika mata "wip your tears karki min asarar hawayenki da kyar ya samu ya rarrasheta ta daina kuka ."
Da sallama maryama ta shiga part dinsu inda ta iske habib na zaune akan wata tsohuwar kujera mai zaman mutun uku yana ganinta ya saki fuska yayinda aunty ke zaune akan daddumar sallah , " heartbeat sannu da zuwa "yauwa after dad ta fad'a tana cire nikaf din fuskarta da hijab din jikinta " yau baka fita bane na ganka a gida ?"wallahi na fita ban dai jima bane saboda ranar daake yau tayi zafi da yawa "gsky kam yau an zuba rana ga doguwar tafiyar mun kwaso wallahi a matukar gajiye nake da kyar na qaraso gida , kasan tun daga dopemu da kafa muka shigo agege ya zaro ido yana cewa "halan matsalar mota ?ta gyada masa kai tana rausayar da kwayar idanunta ."
Ya mike tsaye ya qarasa inda d'an qaramin fridge dinsu thermocool yake wanda ya gaji dan murfin ma ya balle idan an bud'e da kyar ake maidashi a rufe ya ciro pure watar mai sanyi ya ajiye akan hannun kujera ya maida murfin fridge din da kyar ya qaraso inda take "heartbeat ga ruwa ki sha "yauwa after dad na gode sosai ya koma Kan kujera daya tashi yana cewa "ya exam din fatan yazo da sauki ?sai data zuke ruwan sannan tace "babu wani sauki amman muna fatan samun nasara daga Allah bata sake cewa komai ba sannan bata zauna ba ta qaraso bayi ta dauro alwala ta fito ta d'auki wani dadduma sallah daga inda suke ajiyewa ta shimfida kusa da mahaifiyarta dake zaune har lokacin tana kaiwa allah kukata akan yaranta most especially maryama wacce ta fita jarabawar karshe ta tada sallah a natse ."
Bayan ta idar da sallah ta mike tsaye tana ninke sallayar ta samu waje ta zauna kusa da habib tana sauke numfashi "kai wallahi ban ta'ba gajiya irin na yau ba wannan hanyar ta yanoba akwai matukar wahala alhamdulillah daga yau dai mun huta bata gama rufe bakinta ba taji an bako kofar shigowa falon nasu da karfi atare suka kallo kofar kaulat ce tare da mahaifiyarta tsaye suna huci Aunty hassana tace "yauwa gara da Allah yasa na sameku gbdy uwa da ya marasa mutunci to wallahi na gaji ki jawa wannan tantariyar yartaki mai suffar manufukai kunne ta shiga hankalinta bata tashi dawowa gidan nan daga yawon karywancinta sai yamma tayi lokacin da manema auren yarana suke zuwa ta dinga wannan yar iskar tafiyar tata simi simi kmr macijiya dan kawai ta dauki hankalin samarin ya'yanmu to wallahi kinyi kadan bake ba hatta uwar data kawoki duniya ga tanan tayi kad'an bare Ke karan kada miya ,ko su sukayi koba dinki?
" ko su sukace maza su dinga gudunki ?ko Kuma su suka sanya mugun balai ajikinki da maza ke gudunki ? babu daya da sukayi aciki dan haka daga yau banason sake ganin gyallinki idan bilal yazo gidan nan aikin banza kawai kyau har kyau amman bashi da amfani , ana fakewa da karatu ana yawon karuwanci "tana kawo nan habib ya zabura ya mike jikinsa na rawa tare da daga hannu zai zabga ma Aunty hassana mari...."
aunty wacce ta mike tsaye tun fara maganr Aunty hasana tayi saurin rike masa hannu tana cewa " qul habib karka fara ko ka manta wacece ita da matsayinta agurinka? "amman male bakiji kalmar da take fad'awa heartbeat ? "an fada Kuma an sake fada dan uwarka da ubanka kayi duk abinda zakayi karya na fada ba yawon karuwanci take ba ?" idan bashi take ba me yasa samarinta suke gudu su barta ?idan baka sani ba kasani daga yau ai raba masu kanta take kmr MTN shiyasa suke gudu suna barinta jairi kawai da wani katon kanka can shegu marasa mutunci jinin marasa mutunci ai da bakayi haka ba bazansa kayi gadon dangin uwarka ba masu arziki amamn matsiyatan mutane ."
Tunda ta fara magana hanakalin maryama yay kolowar tashi sosai ta firgita da kalaman aunty hassana ba idanuwanta suka cika da ruwan hawaye ta kalli inda kaulat take da kyar ta bude baki cikin sanyayyar muryarta mai tsananin kashe jiki "mama Ke kanki sheida ce akaina Kinsan bazan ta'ba aikata wani abu da zai 'bata sunan ahlina ba ,walalhi bana aikata komai karatu kawai nake zuwa sannan mama ko babu komai ni din diyar d'anuwanki ce kuma abar tausayi a irin wannan rayuwar da muke wacce babu wani yanci acikinsa sai tsabar kaskanci kece mutun ta farko da daya kamata ki cetomu amamn sai gashi kece mutun ta farko dake bibiyarmu da mugun alkaba'i ta sake kallon inda kaulat take tsaye tana zabga mata harara."
"ga kaulat nan idan zata fadi gsky babu wani abu danayi hassalima ko magana banyi ba ta gefensu na raba zan .." dakata dan Allah malama banson manufarci bangane atambayeni ba ta fad'a cikin zafi rai kafin daga baya ta dawo gabanta ta tsaya "duk abinda mama ta fad'a gsky ne kisa kunnen baseera ki ji abinda aka fad'a miki ,ki tsaya iya matsayinki ki kiyaye shigowa alokacin da bilal yake zuwa tana magan tana nuna maryama da yatsan hannunta "idan karuwanci zakiyi sai ki san inda zakiyi ba ..." tas tas !! habib ya dauketa da gigitaccen mari "da uban wa kike wannan maganar ?da ubanka nake banza kawai mara kunya ta fad'a tana dafe kuncinta .
"idan kika sake zagina ko zagin yaruwata wallahi sai nayi miki jina jina anan shegiya yar iskar banza kakar ubanki ce karuwa..."ai bai gama rufe baki ba Aunty hassana ta sauke masa nashi mari ji kake tas tas !! sau biyu ajere "dan uwarka a gabana zaka mari yata ?" jakar gidan uwarka ce da zaka mareta ?"
habib ya bude baki zai sake yin magana aunty ta sake dakatar dashi" karka Kara cewa komai wannan idan da sabo tuni princess ta saba dan haka komai hassana zata fada akanta banason ka sake cewa uhm bare uhm uhm dan yarta ce halak malak idan karuwa ce ita tayi silar zuwanta duniya ."
aikuwa ransa yayi massefar bacci ya dinga Jin wani tuttukin bakinciki na taso masa "ke ai da kin kuskura ya sake ta'ba min lafiya 'ya wallahi da yaga aika aika da yau mun kwashi Yan kallo dake dan kece saar yina basu ba habib bai daddara ba yace "allah Aunty ki kama girmanki Kafin na miki abinda bakya tunani koda yake ai ba girma atare dake mahaifiyarmu tafi karfinki sai dai Kiyi damu ba arabi ba boko shiyasa baki san haramcin abinda kikeyi ba "da uwarka da dangin uwarka kake ba dani ba tana gama fadar haka taja hannun kaulat suka nufi kofa tana cewa"dan kutumar uba kawai ."
Kuka maryama take sosai a wajen tamkar ranta zai fita aunty ta qaraso wajen da take tsaye tare da dafa maryama me ye kuma na kuka bayan wannan ba sabon abu bane ? Kuka taci gaba dayi habib ya matso "dan allah heartbeat ki daina kuka idan ba haka ba nima zanyi kuka tana kuka habib na kuka nan da nan aunty ta samu waje ta zauna ta d'aura kanta a hannun kujera itama kukan take da karfi
A hankali suka qaraso suka durkushe kasa kusa da kafafun Aunty tare da daura kansu a saman cinyarta suna cigaba da rera Kuka wanda har umma ta shigo basu saniba" umma ta qarasa shigowa da sauri tare da dafe qirji bilkisu me ya faru Kika tasa yara gaba kuka ? Kuka suka ci gaba dayi ba tare da sun bata amsa ba..."Ke maryama taso muje ki gayamun me yafaru da ke da mamanki da kaninka haka kuke kuka ? ."
hannunta umma ta riqo suka nufi bangarenta Aunty salma dake tsaye taga wucewarsu maryama na goge kwalla tasan ba lafiya ba ta biyo bayansu da sauri umma ta zaunar da ita a Kan kujera ,a lokacin kukan nata ya fara raguwa"me ya sameku haka kuke wannan uban kuka haka maryama ? Jin shirun da tayi ne yasa aunty Salma ta tunzura "wani mahaukacin tsawa ta sakar mata wanda sai da ta burkice "wai ba magana ake miki ba ne?sai lokacin umma tasan da shigowarta ta dago tana kallon tana mamakin hali munafurci irin nata ko wa ya kirata data shigo ? umma ta hade rai tana cewa "a'a salma ba haka akeyi ba ki barni daita kawai karki hargitsa mata lissafi ki barta zatai magna."
"uhm ina jinki maryama fad'a min damuwarki cikin sheshekar kuka ta zayyanewa umma komai da ya faru naunayen ajiyar zuciya ta sauke "gsky bata kyau ba , amman Kiyi hakuri ita rayuwa ta gaji haka komai da kika gani kafin a samu nasara sai anyi hakuri in sha allahu wata rana zai zama labari ,ku ya kamata ku dinga kwantar wa da mahaifiyarku hankali ba wai ku dinga tayata kuka ba yi hakuri kinji maryama Ki bar komai a wajen Allah in sha allahu sai kin zama madubi abar dubawa acikin gidan nan masu takaki wata rana sai sun zama fadawanki "wallahy aunty aseeya har da laifinki wajen iskanci yarinyar nan kawai daga yar wannan mgnr zasu zauna suna kuka Kmr mutuwa akayi ke km sai ki zauna kina bata lokacinki ."
" babu ruwanki dole na rarrashi diyata mikewa tayi ta fice cikin fushi umma tabi bayanta da kallo karki qara damuwa da sharrinsu idan kina kuka suna ganin rauninki to kin shiga matsala dan kullum da abinda zasu dinga miki amman idan kika jajurce kece zaki ga rauninsa ta fad'a hk tana goge mata fuska da gefen zaninta "kin ci abinci ma kuwa ?ta girgiza kai alamun a'a to maza jeki ki rarrashin mahaifiyarki da danuwanki ki dawo ga abinci kizo kici ta mikar daita ta rakata har bakin kofar fita da kyar ta fito zuwa bangarensu wanda lokacin tuni aunty ta daina kuka suna zaune da habib tana gama shigowa taji saurin muryar Aunty "my princess taho kici abinci nasan kina tattare da yunwa."
Babu yadda ta iya ta sakar mata murmushin gefe baki tana dubanta tace "kamar kin sani Aunty gbdy suka qarasa zuwa Kan kujerun roba dake zagaye da qaramin table wanda shima din na roba ne aunty na zaune tare da yaranta suna cin abinci amamn ita tayi shiru tana tunani ta kasa cin abinci "male kici abinci mana ta dago ta kalli habib maryama ta ajiye spoon din hannunta ta soma magana a tsanake kamar ba yanzu ta gama kuka ba."
"kiyi hakuri aunty akan duk abinda Ke faruwa a gidan nan wani lokacin Allah yana gwada mutane ya gwada imanin bawa kinsan al'imanu yazidu wa yankus imani na raguwa yana qaruwa to Ke aunty a mizanin da kike allah yana son ya gwada imaninki ne Kan wasu abubuwa dake faruwa damu duk duniya bani da abar yabo da koyi da hali mai kyau sama danaki sannan kowa yasan ke din mutuniyar kirkice hatta makiyanki suna fadan hk a bayanki to me yasa abubuwanki sukaki daidaita duk wannan hakuri naki da juriyar amman ba komai bane kawai Allah yana son ya gwada imaninki da jin tsoronsa ne dan duk allah yana sane ya tsara haka hk ."
"Mu qara hakuri hakuri ne kawai zai kawo mana sauki kuma Allah yace annan nasara maasabarin duk wani nasara na rayuwa yana tare da hakuri ,
hakuri da kike dashi yana cikin tsani da zai kai mutun zuwa aljanna, hakuri halin manzon allah ne wal hilmi wal sabri duk kina dashi aunty kina da dauriya kina da juriya kina da tawakkali kina da imani kina da ibada so duk wani abu da kike ganin yana samunki mara kyau ko yana shirin faruwa dake to wallahi jarabawa ce km kina ta cinye jarabawar sai kiga allah ya tsara bazakaji dadi anan duniya ba sai a lahira ,wallahi aunty da ace kana da rabo a duniya baka dashi a lahira wallahi gara ace kana dashi a lahira baka dashi a duniya ."
"sai abu daya da nake son ki fad'a mana" ta dago da rinannun idanunta ahankali tana duba kyakkyawar diyarta son kowa kin wanda ya rasa abar tinkaho kuma yar baiwa domin samun irinta sai an tona "aunty idan bazan takuraki ba ina son ki fad'a mana inda danginki suke muna son musani domin na fara tunanin akwai wani mummunar abu daya faru a baya dake ,dan idan babu komai bazai yuwa kana da dangi kuma kuna gari daya amman bakwa ziyar juna"tunda maryama ta fara magana idanun aunty suka sake cika da hawaye basu samu nasarar zuba ba sai data kawo karshen mgnrta "ki fad'a mana mu yaranki ne bazamu taba juya miki baya ba duk runtsi duk wuya muna tare dake koda kuwa kice kika batawa yan'uwanki zamu kasance dake domin kece karfin gwiwarmu ta qarasa mgnr tana riko hannun mahaifiyarta ."
Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.