Maradams Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 1 BY AYSHA A BAGUDO.txt
Chapter 15 of 18
Page 21
Duk da ba wani son mlm yahuza take ba amman tunanin rabuwa dashi Kullum yana bibiyar zuciyarta dan duk yadda take qoqarin ta yakicesa daga tunaninta abun ya cutura ba dan komai ba sai dan tsananin kirkinsa da tausayinsa gareta komai na duniya ya fitar mata a rai hatta zaman gidansu ya fita ranta saboda Harare hararen da take sha daga kowace fuskar ta mutan gidan wanda hakan yasa ta kasa samun sukunu ta rasa da me zataji da kwace mata saurayi da suka yi ko kuwa da nemanta da fitina da suke yi ?."
Tana kwance shiru akan katifa kamar mai barci alhalin ba baccin take ba. aunty ta leko d'akin tana kiran sunanta "princes baki ta shi bane ? tasan dole ta kasan tashi saboda abinda ya faru dole zai hana zuciyarta sukuni ."ahankali maryama ta yunkura ta mike daga kwanciyar da tayi ta ari murmushi da sukuni ta dasa a ranta tana cewa "aunty na tashi , tayi haka ne dan kada aunty ta gano har yanzu abinda ya faru yana ranta har yasa ta qara mata zancen addu'ar ma data kwana yi cikin dare ya d'an sanyayyar mata da zuciya, kuma har ranta taji ta samun sauki dan har yanzu data mike tana maimaita adduar Allahuma ajirni fi musibatihi wa aklifini khairan minha yafi sau babu adadi dan bata san iyaka adadin data yi ba , aunty ta riko hannunta cikin nata suka fito zuwa parlour ta zaunar da maryama ta lumshe idanunta cikin sanyayyar muryarta tace "aunty ina after dad ?"
"Tun safe ya fita zuwa filin kwallo amman nasan yana kan hanya dawowa yanzu numfashi ta sauke da karfi sakamakon tunawa datai yau asabar ce daman kuma ranar asabar da lahadi sune ranakun daya ware domin zuwa filin kwallo , ta mike tsaye a natse ta nufi hanyar kitchen domin had'a kan kayan wanke wanke ta jiyo sautin muryar aunty tana cewa "ina zaki ?" .
"zan shiga kitchen na had'a kayan wanke wanke na wanke ne ." tayi maganar cike da raunin zuciya Kmr zatayi kuka , shiru aunty tayi tana kallonta cike da tausayawa kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankali tayi wata muguwar rama " ga abinci akan table ki d'auko kizo ki karya kafin ki fara aiki ."
ta sauke numfashi sannan ta rausayar da kwayar idanunta bata jin cin komai amman kuma bazata iya cewa aunty bazata ci ba dan tasan bazata ji dadi ba dan damuwarta damuwar aunty ce , idan ta runtsa aunty ta runtsa ,idan ta kwana Jin motsinta to haka itama bazata runtsa ba ,ta dinga kai kawo kenan a tsakanin d'akinta da nata ."
Jikinta a matukar sanyaye ta qarasa inda kular abincin yake ta bud'e ,shiru tayi tana kallon abincin , sai data d'auki second goma tana kallon abincin sannan ta kalli aunty fuskarta d'auke da tambaya "ummah ce ta aiko mana dashi , sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta d'auko Kula tazo ta zauna kusa da aunty ta fara ci a natse , ba wani abincin kirki taci ba ta rufe kular tana qoqarin mikewa tsaye aunty tace "har kin yi me kenan princess ? " ki koma ki qara cin abinci duk fa kwanakin nan ina lura dake ba wani abinci kirki kike ci ba ,ki taimakeni ki manta da abinda ya faru ga gobe can tana d'aga muna hannu kullum cikin miki addua nake , nayi imani allah bazai barki haka ba zai kawo miki wani mafi alkhairi."
"Wallahi aunty na koshi ne sannan idan ban hakura ba ya zanyi aunty ? nasan haka Allah yaga dama dani kuma na kar'bi qaddarata ni kawai mlm yahuza nake tausayawa domin duk ranar da zai dawo haiyacinsa sai yayi kukan bakinciki abinda ya faru , tana gama fadar' haka ta shige kitchen ta ajiye kular abincin da taci ta rage ta fara da had'a kan kayan wanke wanke ta wanke sannan ta share d'akunansu ta fito da sharar har tsakar gidansu domin kasancewar weekend ce kuma daman ta saba hakan a duk ranar weekend ."
Lokacin data fito duk mutanen gidan suna zaune suna hira ganinta suka hau fad'a
fad'ensu da suka saba akanta musamman aunty salma da aunty hassana da yaranta kaulat da Islam dan ita sakina shiru tayi tana sauraronsu haka ma shukura sai dai duk lokacin da suka had'a ido da shukura sai ta zabga mata harara ,sai dai allah da ikonshi sam bata ji komai game da abinda tai mata ba illah iyaka tausayin mlm yahuza dana mahaifiyarta dake ranta ,adadin soyayyar aunty gareshi mai yawa ce, domin shine saurayi na farko da aunty taji ta gamsu dashi ,shine mutumin da rabuwarsu ta ta'ba zuciyarta ,shine wanda har ta tsaya tayi mgn akan ba'a mata adalci ba duk sanda yazo kuwa sakon gaisuwarta zuwa gareshi kad'ai ta kai ashirin, banda yabo da qara mata kwarin gwaiwa da take mata akanshi."
Bayan ta gama aikinta taje tayi wanka ta shirya kanta cikin Jallabiya maron touch of white ta d'aure gashin kanta da rebbon kasancewar tana da yalwan gashi mai tsoho sannan tasa mayafin jallabiyar ta daure kanta ,tana zaune kusa da aunty yayinda hanuta Ke rike da reza ta d'aura kafarta d'aya akan cinyarta tana yanke kunbunan kafafunta suna hira da aunty inda take fad'awa mahaifiyarta tana son zata 1829 super market siyan abubuwan bukatanta ,aunty ta amince tace "sai da yamma kenan zaki ?"a'a idan after dad ya dawo yanzu zamu je tare dashi "princess me yasa bakya iya zuwa koina sai tare da habib ne ?" wallahi aunty bana jin dadi tafiya ni kadai ne sai naji Kmr zaa saceni bare irin wurare nan da jama'a suke cika Kinsan ni fa yawon mutane na matukar tsoratani."
"ai na sani princess amman dai ya dace ki saba da yin wasu abubuwa Ke kad'ai saboda kinsan wata rana zakiyi aure gashi kinsa habib aranki dayawa karki manta habib nmj ne shi din d'anuwan wasu ne tunda nan gaba aure zaiyi "
" babu wacce ta isa ta shiga tsakanina da 'yaruwata , babu wannan matar a nan gidan duniya wannan shine sallama da habib yayi sannan ya shigo parlour'n sosai ya furta sallama ."
atare maryama da aunty suka amsa masa maryama ta d'ago kwayar idanunta daga abinda take ta zuba masa tana sakar masa murmushin farinciki yana tsaye sanye da wondo da riga na yan kwallo na kamfanin arsenal kayan sun amshi jikinsa sosai ,suna matukar kama da habib sosai abu d'aya ne ya bambamtasu shine launin fata shi fari ne sol yayinda ita kuma ta kasance chocolate colour ."
Aunty tayi murmushi tana dubansa tana sake maimaita maganarta "to ai gsky ne kai d'anuwan wasu ne mana ,dan girma Allah aunty ki daina furta cewa ni din d'anuwan wasu ne , wasu suwa kenan ? "yan'uwan matar da zaka aura mana ta bashi amsa da haka tana kunshe dariyarta "dan girman allah ki daina fad'ar wannan mgnr nifa babu matar data isa ta juyani ,haka zata ganmu ta barmu mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka faro babu wacce ta isa ta raba mu ko shiga tsakaninmu bakiji sunan da nake kiranta dashi ba bugun zuciyata ? bani da kowa sai ke daita , uwa d'aya uba d'aya , jini d'aya ina jinta araina fiyye da komai dake cikin duniyar nan "dan allah kama mana baki zaka cika mutane da dadin baki har ka girma kayi auren muga yanayinka ,amman a yanzu babu abinda zaka fad'a na yarda da kai nawa nawa suka cika baki irin naka a karshe ..."
"A'a aunty akwai shakuwa mai karfi atsakanina da habib ai duk wacce tace zata shiga tsakanin mu allah ma bazai barta ba bare bana tunaninta hakan ,shi kansa ma bazai d'auko mana matar da zata rabamu ba , matar da ma ni da kaina zan zaba masa inji cewar maryama ta fad'a tana murmushi "yauwa heartbeat fad'awa male taji da kyau, nima koda wasa bazan kawo irin wannan matar ba ,sai ma wacce heartbeat ta za'ba min Kmr yadda zan za'ba mata miji anan gaba yana fad'ar haka yasa kai zai shiga bayi maryama tace "karka dade zaka rakani 1829 "okay ki shirya kafin na fito ya qarasa shigewa ciki ta mike tsam tana cewa aunty "bari naje na sake shirya na fito ."
ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa yellow touch of black atamfar ba wata sabuwa bace dan ta dan kode sai dai fés take agoge sai takalmi flat kasancewar maryama mayar saka flat ce cikin kankanin lokacin habib ya fito yana kiranta yana d'aura agogo a tsintsiyar hannunsa na gama ke nake jira fa "ganin nan fitowa nima na gama hijab kawai zan saka da nikaf ,byn second biyar ta fito suka yiwa aunty sallama "sai mun dawo aunty ."
" to sai kun dawo Allah ya tsare min ku habib ka kular min da yarinya na baka amanarta yayi murmushi yana cewa "to ni kuma wa zai kular miki dani ? ."kai wannan yaro wannan yaro akwai manyamce ku dai je Allah ya tsare karku dade suka fice suna fitowa suka hango yaya sadam a haraban gidan hannusa daya rungume a qirjinsa yana waya da murmushi akan fuskarshi suka gaishesa hannu kawai ya d'aga masu suka wucesa ."
Basu suka dawo gidan ba sai daf da magariba habib ya wuce massalaci maryama ta cire nikaf dinta tare da hijab ta fad'a bayi domin yin alwala bayan ta idar da sallah suna zaune sai ga dan sako daga umma cewar tazo babu ' bata lokaci ta mike ta nufi side dinta bakinta d'auke sallama ta shiga a natse kamar koda yaushe umma tana zaune a parlour'n gefenta yaya sadam ne zaune ya d'aura kafafuwansa duka a saman table yayi crossing leg's dinsa suka amsa mata sallamar ,cike da girmamawa ta gaishesu sannan
ta samu waje ta zauna tana fuskantar ummah " .
"yauwa maryama gobe idan Allah ya kaimu zamuyi baki daga cikin gari zasu zo Ina son dan allah gobe da safe kizo ki tayani aikin kaji dazu na aika kizo aka ce kin fita tare da habib har na aka Islam ta siyo min kayan miya ina ganin gobe ma tare daita da sakina zaku tayani aiki ."
"To shikenan ummah Allah ya kaimu zuwa karfe goma yayi ko karfe nawa kike bukatar nazo"? tayi mgnr cikin jin kunya ,"eh to zuwa tara ma yayi ,maryama ta d'an jima suna hira da umma yayinda sadam Ke waya."ahankali ta mike tai mata sallama ta dawo side dinsu tana sheidawa mahaifiyarta bukatar ummah dan haka bata tsaya yin wata doguwar hira ba dan lokaci ma ya fara tafiya kai tsaye taje tayi sallah isha'i ta kwanta bacci dan ta samu ta tashi da wuri ."
washegari tun bakwai na safe ta tashi ta fara da gyara d'akunan su karfe takwas da rabi ta kammala da aikinta na yau da kullum sannan ta nufi side din ummah ta fara kama mata aiki sakina da Islam na zaune basu da ma alamun saka hannu har sai da yaya sadam ya buga masu tsawa sannan Islam da sakina suka kama mata aikin kajin, saboda ganin aikin da maryama take yayi mata yawa , wanda ita ko ajikinta dan ko ita kad'ai aka bari da aikin zata kammala komai ta tashi ."
d'aya bayan d'aya mutanen gidan ke shigowa hatta baba gali sai daya shigo cikin tsananin murna da zuwa bakin da zasuyi wanda ita maryama aranta take raya irin bakin da umma zatayi hakika ko su waye lallai masu matsayine a gun kowa dake cikin gidan tunda take a gidan bata ta'ba ganin hakan daga garesu ba, baya farincikin da suke ciki har da hidmar wanda ke nuna wani mai matsayi ne zai zo ."
Sosai ta kasa kunnuwanta tana son ko kad'an taji irin bakin da zasu zo amman bataji komai ba sai dai ummah da aunty hasana da aunty salma suna ta hira akan bakon da alamun sun san wanda zai zo alhji alqasim maude kenan yaushe rabon shi da kasar nan?".
"Ke ai kudi sunyi wallahi dan baki ta'ba zuwa gidansa ba wannan yar wayewar da kike ganin kina dashi sai kin nemeta kin rasa inji cewar ummah ,aunty hassana tayi murmushi cike da jin dadi "haka naji abakin babansu sakina ya ta'ba zuwa tare da abban sadam allah ya jikinsa da rahma yace aljannar duniya ne gidansa kamar ba qasan nan yake ba su kansu mutanen unguwar da yayi ginin kallon gidan suke ."aunty salma ta fad'a tana tafa hannuwanta ."
Sai yanzu maryama ta gane waye zai zo abokin abban sadam ne wanda sukayi karatu tare tun daga primary har zuwa diploma har suka girma sukayi aure dake shi alhji alqasim maude yayan mahaifiyarsa yana siyasa shi ya samammarsa shcolaship zuwa qasar india ya wuce tare da matarsa wannan ya dan yanke zumuncin abban sadam dashi sannan mutuwa ta qarasa gabadaya sai dai jin rasuwarsa ya mugun d'aga masa hankali sosai ."
mutuwarsa ya dawo da zumuncinsu ya d'aure sosai shine ma ya d'auki nauyin karatun yaya sadam har ya qare karatu kuma shine mutumin daya samammar masa aikin da yake yi ahalin yanzu a awaf ,alhj alqasim maude mutun ne mai kirkin gaske da sanin darajan mutune da taimakawa talakawa a yadda ta samu labari duk ya kwashe ya'yan yan'uwa zuwa kasashen duniya wasu na karatu wasu na kasuwanci shine ma ya bud'ewa abban sadam gidan buredi kuma yana taimaka masa a duk sanda yazo qasar "
Umma ta mike tsaye rike da wayarta sakamakon qarar data d'auka ta nufi hanyar shiga side dinta dake a tsakar gida suke aiki aunty salma na gani ta tashi tace "sakina Islam ku cire hannunku haka nan ku huta ku barwa yar wahala ta cigaba da aiki tunda dama ita ta saba aikin neman suna da neman gindin zama ,wallahi ba ai kin kyauta salma daman tun dazu nake son dakatar dasu
su bar shegiya yar wahala ta cigaba a haka rayuwarta zata ware bauta ,maryama ta kallesu batare data ji zafin maganarsu ba, dan aiki kam matukar na umma ne zatayi shi sai inda karfinta ya qare ,tayi nasu ma da basu da aiki sai nacin zarafinta bare na umma ,ta cigaba da aikinta ta dauki wata roba ta qarasa inda korfot yake ta wanke shikafar dake ciki ta bud'e tukunyar dake kai ta zuba shimkafar cikin ruwan zafi tana cikin aiki shukura ta fito daga side dinsu ta zauna adaidai lokacin umma ta fito ."
Aunty hassana da aunty salma har ma da ya'yansu suna hira ummah ta kalli sakina da shukura da islam zaune suna tayasu hira ta kalli maryama dake faman dikar aiki "a'a ya zaku bar maryama da aiki ita kadai Ke shukura sakina islam kusa hannu kuyi tare mana na gayyatoku ne dan kutayani aiki ba dan ku zauna kuyi hira ba ,maryama ta fahimci maganar ba dasu shukura kadai ummah tayi ba har dasu aunt hassana tayi cikin rashin son aiki suka qaraso inda take gyara kaji shukura na kunkuni wanda bazai kai ga kunne ummah ba , maryama tace "kinga shukura idan baza kiyi ba ki koma ki cigaba da zamanki idan ma gbdy bazakuyi ba ku barshi duk zanyi dan kawai an sakaki aiki zaki dinga wa ummah kunkuni
ta watso mata harara tare da kallon banza "ke ki kama kanki dan na lura tunda mlm yahuza ya dawo da neman aurensa kaina kike min kallon gani gani nake miki kallon gani gani ko kike min ?"
maryama ta fad'a a dan hassale tana hura hanci .
"Ban sani ba banza kawai mai bakin jini sai wani 'bare 'bare kike dan kinga mai kudi zai
zo , abinda kome zaayi na banza né tunda babu abinda zai haifar sai cigaba da zaman gida da yawon ta zubar wai ana zuwa bautar kasa "Ke ni kike gawa magana "? an gaya miki me zakiyi ?"ai maryama cikin fushi ta zabga mata mari wani qara ta saki tana dafe kuncinta wanda yasa aunty salma da duk wanda suke wajen suka juyo zuwa inda suke ita kanta irin qarar da shukura ta saki sai da gabanta ya fadi ta tabbatar yau ta dibowa kanta ruwan dafa kanta "kutumar uban can me tayi miki kika zabga mata mari haka ?"aunty salma ce akan maryama take neman ba'asi cike da maseefa."
Maryama tayi shiru tana datasanin Marin datai mata hakan shi ya fusata aunty salma bata tsaya wata wata ba ta zabgawa maryama nata mari har biyu a kowani kunci "idan dadi né kema kiji ina dalili daga tazo ta tayaki aikin wahala sai mari jakar gidan ubanki ce ? taja hannunta zuwa kofar dakinsu tana share mata ruwan figar kajin data goga mata ."
Ummah tace "maryama me ya hadaku har daya kaiki ga marinta ? tayi shiru tana shayen zafin marin dan bazata iya fad'a mata bakaken maganganun data fad'a mata ba kawai ta rufe fuskarta saboda tuttukin bakinciki da zuciyarta Ke mata nan da nan kuka ya kwace mata umma ta qaraso kusa daita "kinsan kema uwarta bazata barki ba me yasa kikasa hannunki ajikin shukura ?sakina kanta ta tausaya mata tana son tayi mgn dan kare maryama da sheidawa ummah cewar ba laifin maryama bane laifin shukura né amman ta kasa ."
"kinsan halinta ya kamata ki dinga kiyayye duk abinda zai hadaku daita da yaranta ni wallahi nayi danasani ma sakasu cikin aikina kinga sakina tashi ki bisu kuje kema Islam jeki na gode kema hassana wuce idan bakin sun qaraso kwazo ku gaisa " kukanta ya fiyye mata maganar ummah , bata cewa ummah komai ba tana tsaye akanta ita kuma tana cigaba da kukanta ta share mata hawaye "kiyi hakuri kinji Allah zai saka miki maryama bata ce mata komai ba ta cigaba da aiki datasata domin tana ganin hakan shine zai fiyye mata akan kukan da take ."
Karfe tara da minti arba'in da daya daidai bakin suka shigo cikin unguwarsu cikin wata qatotuwa Jeep mutun uku ne a cikin matarshi da kuma shi kanshi alhj alqasim maude sai mai tuka su inda baba gali da yaya sadam suka fito tuni tsayuwar jiransu da sauri baba gali ya qarasa ya bude kofar da alhj alqasim maude yake da murmushi cike da kulawa suka gaisa sosai."
Alhj alqasim maude ya rike hannun baba gali yana cewa "Kai amma an jima ba hadu ba, ya jama'a ya iyali.?"baba ya ce,"duk lafiyarsu qalau barkanka da zuwa ya hanya? da irin wannan gaisuwa matarsa Hajiya mustafshir ta fito daga motar suka gaisa da baba gali cikin kulawa, sannan alhji alqasim ya rungume yaya sadam ajikinsa cike da farinciki dan duk sanda ya gansa yana jin farinciki sakamakon kamaninsa da mahaifinsa "sannu dana fatan kana lafiya ya fad'a yana shafa bayan yaya sadam ya dan zame kadan ya gaishesa "barkanku da zuwa dady da fatan baku sha wahala ba ?"babu wata wahala sadam sukai masu jagora zuwa cikin gida ."
kai tsaye babban falon ummah wanda aka qawatashi babu laifi anan abban sadam yake saukar bakinshi kujeru set guda zagaye a dakin sai dan teble a tsakiya na glass , parlour ya sha gyara har da turaran wuta kala hudu maryama ta saka a kowace kusarwa na falon ,suka zauna ana qara gaisawa da tambayar mutanen gidan hajiya mustafshira tana dan duba wajen tana murmushi itama tana dan ta'ba hira umma ta fito daga dakinta maryama na zaune gefe daya kuma aunty salma ce da sakina har ma da shukura da islam duk komai an gama shiryashi daidai ta yadda duk wanda ya gani bazai raina ba "maryama ki kawo wa baki abinda muka yi ta yunkura zata tashi islam tayi sauri ta dauka batare da an bata izini ba ta wuce dakin da farantin dake da kayan ."
Hakan yasa ta koma ta zauna batace komai ba sai dai ummah tace taje wajen baban yara mai Shgo zai bata sako dan haka ta fasa zaman ta gyara zaman hijab dinta ta fice daga falon roban ruwan faro ne guda shida wanda suka dauki sanyi da kwalbar multina shima guda shida ya saka mata acikin leda baka ta nufo ummah bata shiga dakin da bakin suke ba tana zaune suna hira da aunty data iske zaune kusa daita da jamar gidan tace "yauwa diyar albarka ki kai masu amman kawo mugani islam je dauko wadan can kofunan na glass acikin dakina cikin sauri taje ta dauko ta hada da bakar ledar da maryama ta shigo dashi taje ta kai hakan kuwa yayiwa aunty hassana dadi dan tafi son ace islam ce Ke kai kawo a masaukin bakin."
ita kuwa maryama ta rasa me yasa take son shiga dakin har da zalamarta aunty hassana da yayanta biyu kaulat da islam suka shiga suka gaisa sun dan jima aciki sannan suka fito sannnan ummah da aunty suka shiga bayan wasu mintuna aunty ta fito ita kadai zata wuce har maryam ta mike zata bita su koma side dinsu tare , aunty ta dakatar daita " ki tsaya idan ummah ta fito bata ganki ba zata damu ko bama haka ba dole Kinsan zata nemeki ."
"to ! kawai ta furta ta koma ta zauna bata shiga dakin ba dan ita a ganinta babu abinda zai kai ta ciki zama gurin bai mata ba dan harare hararen da take samu daga yammanta ta mike ta shiga dakin ummah tayi kwanciyarta duk da tana son ganin bakin amman haka ta hakura tana jin su sakina suna santin bakin fad'ar haduwar hjy mustafshira da irin kayan alfarmar da take sanye dashi ita dai shiru tayi bata damu ba domin ko sun tafi basu ga juna ba ita ba damuwa zatayi ba dan ganinta haduwarsu bazai wani qareta da komai ba ."
Kusan karfe uku saura suna hira dasu ummah da baba gali har ma da yaya sadam suka fito domin niyyar tafiya suka tsaya a falo inda jamar gidan suke zaune aunty salma da ya'yanta haka ma aunty hassana domin suyi sallama dasu "amman gsky yaranku basu da hayaniya amman dai duk sun yi karatu ko "? Murmushi baba gali yayi "Kai kasani dole suyi karatu domin sanin amfaninshi ita wannan tuni ta gama secondary kuma ina son rai zata cigaba ya nuna sakina ."
alhj alqasim yace "Allah sarki gsky karatu kam yana da matukar mahimanci kayi qoqarin da ka bar yaranka sukayi karatu dan da sun biyoka da rashin son karatu da abun bai yi kyau ba dan wannsn zamanin sai da karatu sukai dariya gbdy sakamakon jin abinda alhj alqasim ya fad'a "ai gsky ne yayanshi yafi sa son karatu sosai allah dai bai yi zai yi karatu mai zurfi bane Allah ya jikansa "Ameen hjy mustafshira ta amsa tare da jamar wajen ."
Alhaji alqasim ya nuna shukura "wannan yarinyar ussein ce ko ?"uhm uhm bata ita bace wannan diyata ce ta uku ita ina ganin tana bangarensu baba gali ya bashi amsa da haka ,allah sarki allah ya jikinsa shima yasa suna aljanna Ameen ai kasan ita maryama bata fiyye son shiga cikin mutane ba mussaman idan bakin fuska ne allah ya zuba mata kunya gashi ita har ta qare karatunta na digree yanzu haka ta fara bautar qasa ta kuma yi saukar alquranin mai girma tana da hadda uzu arbain da wani abu akanta ."
"kai masha allah a she dai kuna da zakakura acikin dangi ?"sukayi dariya kawai suna yiwa ussein addau "gsky ussein yayi saa arayuwarsa duk wannan rashin jin maganar daya ta'ba amman allah ya albarkacesa da samun yarinya mai kokari haka "? wallahi abun na allah ne yaransa ma duk masu natsuwa sai ma ka gansu, yabon ummah sam bai yi kowannensu dadi ba amman babu yadda zasu yi tunda umma ce
kuma sun san adalilin ta suka zo gidan"ai ina qaunar ussein domin shi din mutun ne mai barkwanci da son mutane ai naso na dawo qasar nan na iske shi a raye maryama tana cikin dakin ummah duk tana jin maganar Alhaji alqasim da ummah tana jin matukar qaunar mahaifinta alokacin da bataji tahirinsu da mahaifiyarta ba amman daga baya dataji komai sai ta daina kewar babanta duk da ba wani saninsa tayi ba dan duk lokacin data tunashi sai damuwarta ta ninku acikin zuciyarta ganinta shine ya raba aunty da yanuwata ,bugu da qari yadda kowa yasan mahaifinta baya jin magana."
kuka taji ya kwace mata "Ke shukura je ki kira min maryama taí Jim dan tasan tana dakin ummah amman dan bakinciki karta gaisa da bakin yasa ta fice Jim kadan ta dawo tace "aunty tace bata nan ,bata nan kuma ?ummah ta furta a fili tana qoqarin neman layin aunty can bayan Kmr second goma maryama tajiyo muryar ummah na kiran sunanta "maryama maryama !! hakan yasa tai saurin mikewa ta share idanunta da gefen hijab dinta ta fito ko hada idanu ta kasa da bakin saboda tsura mata idanun da matarshi da shi kanshi Alhaji alqasim sukayi ."
"Haka diyar ussein ta girma lallai dan mutun sai allah ussein din guda nawa yake har da 'ya haka ?ita dai maryama gaisuwa ce kawai nata domin bata da abun cewa hjy mustafshira ta shafa kanta sannunki kinji ya aiki da fatan yana tafiyar miki yadda ya kamata kyakkyawa dake tubarkalla masha allah shine kika fitowa kizo mu gaisa ko ?
Ta dan yi murmushi ta dago kanta tana kallonta amamn still ta kasa cewa komai "me ya sameki kamar kuka naga kinyi bata san hawaye na makale da idanunta ba da sauri tasa gefen hijab dinta tana sharewa hjy mustafshira ta qaraso ta dagata daga tsugunno datayi ta dan rungumeta ajikinta "babu mamakin maganr da mukayi ta mahaifinta ce tasa ta kuka ita kanta ummah ta shiga damuwar ganin hawayenta ,ki daina kuka kinji allah zai kai rahama kabarinsa Kiyi hakuri ki cigaba da yi masa addaua shi kanshi yana can yana alfahari da samu diya kamarki mai riko da addini kai kawai ta daga mata tana qara goge kwallar data taru a idanunta aunty salma da aunty hassana da yaransu kuwa babu abinda suke aikin yi sai harare harare iri iri da bakinciki ."
"Ai mahaifiyar ce ta shigo dazu muka gaisa ko ? alhj alqasim ya tambaya yana duban baba gali "Eh itace baba gali yayi saurin fad'ar haka ai tunda ussein ya mutu taki koma wajen danginta bare tayi wani auren ta cigaba da zama anan ai kasan yadda akayi aure danginta saboda rashin son useein din suka sall.."
"Eh nasan komai abban sadam duk ya fad'a min alokacin amman dai nayi tunanin komai ya wuce zuwa yanzu Alhj alqasim ya katse maganar ya zura hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi bandir daya na yan dubu dubu ya damka ma maryama taki amsa tare da cewa ya barshi sai ummah ce ta karba ."
Gabadaya sai daya bisu da kudi yana cewa" in sha allahu zan sake dawowa nan kusa tare da yarana gbdy asan juna kafin mu tattara mu bar qasar yayi gaba yaya sadam ya bishi da baba gali hajiya mustafshira bata saki hannun maryama har bakin mota ita dai bata ce komai ba binta kawai take da alamun tausayinta ne ya game jikinta sai faman hakuri take bata sukai sallama tayi mata godiya sosai suka shiga mota suka tafi ."
Ita da yaya sadam da baba gali suka koma gida kai tsaye dakinsu ta nufa da yamma ummah ta shigo ta mika wa aunty kyautar kudin data samu aunty tace "a'a bazan karba ba ummah saboda me balkisu ? Ki rike kawai domin kece mai yin hidima acikin gidan nan bare ma akanmu wannan ai ba wani abu bane amana ce rike a hannuna, ni dai kawai ki rike ."
"to ki cire wani abu aciki aunty tasa hannu ta zari dubu daya ummah ta girgiza kai tana cewa allah baki isa ba kin kuwa san ko nawa ne dubu dari ne fa shine zaki cire dubu daya ta raba kudin biyu ta mika mata rabi allah sunyi yawa ummah bazan karba ba nifa ba butulu bace nasan ya kamata ta cire naira dubu biyar tana cewa wallahi iya su sun isa allah yasa albarka rantsuwar datayi yasa ummah bata qara cewa komai ba ta mike ta koma wajenta ."
Da yammacin ranar maryama ta shirya zata wuce makaranta islamiyya "aunty ni na wuce makaranta sai kin dawo princess idan kinga malam yahuza ki gaishe min dashi maryama tayi shiru tana kallonta
"Eh haka na fad'a har yanzu zuciyata tana qaunarsa dan haka kice masa ina gaishesa "to ! kawai maryam ta fad'a tasa kai ta wuce zuciyarta cunkushe da damuwar abinda baba gali yayi shi kansa alhj alqasim din yasan maganar bata dace ba shiyasa ya katsesa ".
ta kusan kai bakin get din Ardus salam ta hango mlm yahuza yana tahowa ta hanya mai fitar da mutun afanla ta cigaba da tafiya a natse adaidai lokaci daya suka iso bakin get ta gaishesa ya amsa fuskarshi babu annuri sosai bata damu ba domin sakon aunty kawai take son isarwa "aunty tace tana gaisheka "na gode kawai yace yayi gaba ya barta tsaye abun yaso ya bata haushi amman tunawa datai baya cikin haiyacinsa yasa bata ji komai ba sai dai ta kasa cigaba da daga kafafuwanta tayi shiru kawai bata san a tsaye take ba ashe ta kasa tafiya ne sai da wata kawarta lauratu tazo wucewa .
"Ke kuwa tsayuwar me kike anan kamar mai jiran wani nan ta diririce "Ke na hango ai kin kusan qarasowa shi yasa na tsaya ta dai jita ne kawai amman alamunta basu nuna hakan ba suka shiga makaranta tare koda mlm yahuza ya shigo ajinsu domin kara masu karatu ko inda take baya kallo sabanin da in har yana cikin ajin murmushinsa kadai ya isheta bayan an tashi ta dan tsaya hira da kawayenta koda suka rabu ta nufi hanyar inda suke tsayawa dashi anan ta ganshi shi da shukura ko kunya babu tasan kuma duk sharrin shukura ne dan ta gansu sosai ne hakan bai dameta ba tunda idan kayi da kyau zaka ga da kyau idan ma akasin haka kayi zaka girbi abinda ka shuka ta wucesu cikin fushin zuciya har ta isa gida abun na cinta arai wai yanzu duk abinda mlm yahuza yake fad'a mata akan soyayyarsa ya tashi abanza ya koma kan shukura hakika basu yi mata adalci ba amman ta barwa allah komai ."
*******
Zaune mr ata yake acikin masaukinsa yana jiran abokinsa bashir sosai yayi kyau sai dai ace masha allah dan yanayin gyara tattare da kulawar da jikinsa yake samu ya hana shekarunsa bayyyana dan idan ba kaji shekarunsa ba bazaka ta'ba cewa ya kai 40 wani abu ba , zaka dauka shekarunsa basu wuce talatin a duniya ba fatar jikinsa kawai ka kalla kasan kudi suna aiki ba karya haka ma kayan jikinsa tun daga kan wondo rigarsa takalminsa har zuwa agogon dake makale a hannunsa dukansu tsadaddun gaske né ,shine ma ya zana da kansa kaf duniya su uku kawai ke da irinsa shi mb sai bashir abokinsa rolex ne mai shegn kyau ."
ya hade rai sosai kana kallonsa kasan yana cikin damuwa mai tsanani maganganun sweetheart dinsa yake tunowa a wayar da sukai daita a wannin data gabata. inda take sake jadda masa alqawarin da yayi mata kafin ya bar qasar , koda yayi qoqarin sake lallabata cewa tayi "kada kace min komai bana son jin wani kalaman yaudararka gareni ,kasani a wata biyu din da kace zakayi yau sauran sati daya ka dawo ."amman idan bazaka dawo ba ,ka cigaba da zama adamcy kayi son ranka kayi abinda kaga dama kayi abinda kaga yafi maka arayuwa ,amman kuma idan ka san zaka dawo ka dawo kamar yadda mukayi alkwari da kai ,karka dawo da wani abu a zuciyarka ka bar duk wani mugun nufinka a inda kake ,karka dawo gareni da mugun nufi ka barni na cigaba da rayuwa babu kai domin dawowarka da wani sabon salon yaudara ko mugun nufi zai sa nayi maka abinda har ka mutu bazaka daina mamakina ba abun bazai mana kyua ba adamcy ta fad'a tana kashe wayarta."
zuciyarsa ta sake cika da tashin hankali "ina zai ma
iya karya alqawarin da yayi sweetheart dinsa ?
ya shiru kawai yana ciza gefen lips dinsa ,ina bazai iya ba bazai iya karyar mata da zuciya ba ita din jigon rayuwarsa ce zai iya yin komai domin yaga ya faranta mata kamar yadda yasan zata iya sadaukar masa da faricinta haka shima a yanzu ma da yaji muryarta tausayinta ya cika zuciyarsa "
ahankali ya daga tsumammun idanunshi ya sauke su akan agogon dake daure a hannunsa 11:44 am tsaki yaja "what a heck sannan ya gyara zamansa "kada kace min komai bana son jin wani kalaman yaudarar ka gareni ,kasani a wata biyu din da kace zakayi yau sauran sati daya ka dawo ."amman idan bazaka dawo ba ,ka cigaba da zama adamcy kayi son ranka kayi abinda kaga dama kayi abinda kaga yafi maka arayuwa ,amman kuma idan ka san zaka dawo ka dawo kamar yadda mukayi alkwari da kai ,karka dawo da wani abu a zuciyarka ka bar duk wani mugun nufinka a inda kake ,karka dawo gareni da mugun nufi ka barni na cigaba da rayuwa babu kai domin dawowarka da wani sabon salon yaudara ko mugun nufi zai sa nayi maka abinda har ka mutu bazaka daina mamakina ba abun bazai mana kyua ba adamcy ."
"shine kawai abinda yake ta yawo acikin kwa kwaluwarsa "why sweetheart ?me yasa kika kasa fahimtata instead ki barni tunda na nuna bana son auren nan ya allah ka kawo dalilin da zai sa a fasa auren nan na huta tsaki yayi inda fuskar princess keta masa yawo a cikin idanunsa da sauri ya runtse idanunshi dan a halin yanzu baya son ko tunawa daita ahankali akayi knocking din kofar parlour'n yana daga kwance yayi nisa cikin tunani shiru bashiri yana jiran a bashi izinin shiga amman shiru daya daga cikin masu tsaronsa ya dan leko dakin yana ringine amman bai bawa mai yin knocking din izinin shiga ba ."
Dan haka ya dawo ya bawa bashir izinin ya shiga dan ya rigada yasan ko waye bashir din a wajensa kuma tun safe ya sheida masu zuwansa,bash ya shigo parlour'n bakinsa dauke da sallama shiru mr ata bai amsa ba ."bashir ya zauna yana fuskantarshi sai dai kusan mintuna goma mr ata bai bude kwayar idanunshi akan bashir ba haka zalika bai ma san da shigowarsa ba ya yunkura ya tashi ya isa inda mr ata yake ya dafa shi a matukar zuciye ya bude idanunshi da niyyar saukewa wanda ya dafa shi maseefa ganin amininsa yasa ya sauke naunayen ajiyar zuciya "kai mutumina meke damunka ne haka duk kayi wani irin ina lura da kai tunda ka sauka a qasar nan kake yawon tunani ?bashir ya fad'a tare da zama a gefensa kallonsa yayi zuciyarsa na zafi "yaushe ka shigo kuma me yasa ka shigo baka nemi izinina ba ?"
Ajiyar zuciya bashir ya sauke sannan yace "kai dai anyi dan iska ina tmbyarka kana tmbyta yanzu dai fara bani amsar tmbyata tukun sai na baka taka numfashi ya sauke mai zafi ,kai dai bari kawai ina cikin rudani auren dole zaa min , bashir ya zaro idanuwa "Ata din dana sani zaawa auren dole ? no no it can be possible ya qarasa mgnr yana dan murmushi,kai ma dai ka fadi haka wai kamata zaayiwa auren dole kamar muna in does day nan ya kwashe komai ya fad'a ma bashir har da alqawarin da yayi wa mami , wallahi bana son yarinyar nan kiyayyarta bazata misaltu a zuciyata ba gbdy zuciyata bata bugawa idan na ganta, kaga mutuwa kusa kenan dariya sosai bashir yayi tuni mr ata ya kule kallonsa yayi rai a bace ,kaji min dan iska ina fad'a maka damuwa kana mun dariya to wallahi maza tashi ka bar nan yanzu ."
"Sorry my friend hukunci mami ne ya bani dry kai da yanzu bata zatar da wannan hukunci akanka ba haka zaka qare rayuwarka kana yaudarar kanka shin zaka tuna kafin mu rabu da kai last na fad'a maka wannan yarinyar mafarkinka ba mutun bace sannan ka guji ranar da mahaifiyarka zata gaji tayi maka irin wannan auren kace bazatayi ba ?kaso wannan yarinyar marym karkazo hannu kazo kana sonta ta samu dama akanka."
" dan Allah bash ka bar wannan maganar ka bar kawo min maganar zan sota ya zaayi na sota ma ?"mr ata ya fad'a cikin tsananin damuwa zan cigaba da rayuwata haka zan bar zuciyata babu kowa cikinta yadda zan cire soyayyar princess a zuciyata bazan bawa kowace mace damar shiga ba sai dai na qare rayuwata haka ,haka dai suka cigaba da tautaunawa bashir na bashi kwarin gwiwar yayiwa mahaifiyarsu biyayya ."
Ana sauran kwana hud'u mr ata ya dawo ya kira mami ya sheida mata ai kuwa taji dadi har ta kasa boye murnar ta , ta tattara kan masu aikinta domin su gyara gida da kuma sauya wasu abubuwa dake gidan sakamakon dawowar dan lelenta jirgin karfe hudu daidai na yammaci ranar lahadi zai sauke su tare da babban yaronsa da masu tsaronsa da sukayi tafiyar tare dan haka mami ta hana kowa sakat acikin gidan daga masu aiki har maryama babu wanda ya zauna suna tsaye bisa kafafunsu duk da tun jiya sun yi redy wasu abubuwa da suka san yafi bukata maryam tana wanke hannunta tana qoqarin fitowa daga kitchen sai ga mami abakin kofar kitchen din suka hadu mami ta kalleta da murmushi kwance a fuskarta ."
"tun daga parlour nah na biyu nake ji kamshin girki fatan kice kikayi komai da kanki ?Allah mami ki tambayi tabawa duk ni nayi su kawai wanke wanke sukeyi gsky idan duk wannan kamshi daga hannunki ne naji dadi Kwarai da gaske dan tun banga abincin ba miyona ya tsinke muje kawai na fara da jin dandanon girkin kafin adamcy ya qaraso ,ai mami idan kikaci sai kunnenki yayi rawa ,haka né hajiya duk ita tayi gsky babu abinda muka tayata sai wanke kwanuka ,hakika tayi qaqari sosai ."
"ai kam yau zan bada maki mai yawa dan tun daga parlour'na nake jiyo kamshi muje suka koma cikin kitchen din tare mami na bude manya kuloli kula farko alkubus da miyar naman rago kula ta biyu shimkafa bastimatic ce da teaw wanda yaji naman kaza sai kula ta uku wanda sakwara ce da miyar egusi wanda yaji ganye ugu da nama da busashen kifi "masha allah mami ta furta a fili "lallai adamcy nah zai ci dadi ,yau kam nasan har da santi zai yi murmushi mrym tayi tana cewa" allah yasa mami allah yasa ya yaba da girkin tayi maganar cikin sanyin murya ,karkiji komai diyata zai yaba ta fada tare da daukar qaramin spoon ta dibi miyar farko ta kai bakinta ".
"Woww miyar nan tayi dadi sosai daya bayan daya ta dinga d'an dana miyar tana lumshe idanunta tana santi da yabawa maryam din ,da gaske mami tayi dadi?sosai tayi kawai abu daya ne zan gyara miki shima idan mutun ya kasance mai son cin maggie dayawa a abinci ne bazai ta'ba miki gyara ba "meye shi mami ?ta tmbyeta cikin tsanani damuwa jikinta har rawa yake ,ki natsu ki kwantar da hankalinki ba wani abu bane maggie zaki rage zubawa miya dayawa ,tun daga tafashe kinsa maggie kuma kinga zakiyi amfani da ruwan miya wajen hada miya dan haka baki bukatar zuba maggie dayawa acikin miyarki yanzu kenan maggie yayi yawa ta fada cikin tashin hankali?bawani yawa bane kawai na gyara miki ne dan gaba idan hannunki yana zarcewa a maggie matsala ne."
" wannan ne kawai maggie yayi yawa ko duka miyar né ?Ki kwantar da hankalinki kusan duka ne amman karki damu aa mami dole na damu dan wallahi idan yasan ni nayi na shiga uku gara kawai na sake wani ."What ? "mami ta furta tana dubanta babu abinda zaki sake anan haka zai ci har yayi santi
ta sauke numfashi tana cewa "amman mami karki ce ni nayi kice kece kikayi dan allah idan yasan ni nayi wallahi karshenta bazai ci ba ,mami ta kalli agogon dake hannunta kinga karki damu muje ki shirya dan jirgin adamcy ya kusan sauka nima bari nayi sauri na shirya kafin a dauko shi yazo yana yiwa mutane naci dan tun jiya yace bazai ci komai ba sai ya dawo ."
Mami ta bawa masu aikinta dake tsaye umarnin su fito da kulolin zuwa dinning suna shirya dinning suna hira suka jiyo sallamar hindu gabdaya suka amsa mata kallo daya mami tayi mata ta dauke kanta tana sanye cikin wani irin ado tasha tamkar wacce zata turakar miji cikin ratsatsen lace maron colour touch of green dinki yaji stone ta koina dan hasken fatarta ya sake haskawa sam bataji dadin ganinta ba bata qaunar abinda zai kawowa adamcynta matsala arayuwarsa ta fada mata tayi hakuri dashi ta nuna a fuska duk wata hanya da zata nuna mata ta hakura dashi tayi amman sam kamar bata fahimta ."
"Mami fatan kin shirya muje tarbo ya adamcy ,dawa kenan zakuje?hindu tayi shiru tana dubanta ,ai wannan sai dai matarsa ni kam na yafe ,tô shikenan ni bari naje AirPort tarbosa "allah ya tsare sai kin dawo tace ameen mami ta fada haka né dan tasan halin kayanta bata són taje ya disgata cikin mutane amman hindu ba irin mutunen nan masu fahimta bane ."Mami tana kallonta ta juya tana rausaya cike da farinciki kamar wacce akayiwa albishiri da zata mallakinsa taso ta tsaidaita amman ta barta sai da hindu ta fice daga falon sannan mami ta dawo da kallonta ga maryam zan shiga dakina na shirya kema idan kin gama kije ki shirya mrym tace "tô!
Sai data tabbatar da komai yayi daidai sannan ta wuce dakinsu inda ta iske nana hauwa'u kwance tana karanta wani hausa novel acikin wayarta mai suna cutar da kai ,har yanzu kina kan karatun nan sister?ina kai ko akwai abinda zan miki né ?bazakiyi shirin tarban ya adam ba gashi har ya kusan sauka koma mace ya sauka ?ta qarasa mgnr tana duba makeken agogon dake manne da bangon dakin ,wannan kuma kece zan tmby dan ni tsakanina dashi sannu da zuwa né ke dai kije yi maryam bata sake cewa komai ta shige bayi
Wanka tayi ta fito ta goge jikinta ta zauna akan kujerar mirrow ta d'auko mai ta fara shafawa ahankali haka nan take jin faduwar gaba mai tsanani ,kinyi shiru bazaki shirya ba sai ya shigo mami tazo tana daga miki hankali ta tsaida hannunta akan damtsen hannunta tana kallon nana hauwa'u ta cikin mirrow sai data numfasa sannan ta mike wallahi sister haka nan nake jin mummunar faduwar gaba jikina har rawa yake gabadaya bana cikin natsuwata tunda mami tace zai dawo yau na tsinci kaina cikin damuwa bare gashi na kwabsa kadan a girki mami tace Maggie ya dan só yayi yawa tsorona kar ya tambayi wanda yayi tace nice ta qarasa magana tamkar zata zubar da hawaye ."
"gsky kina tare da aiki marsi wai shi yaya dodo ne da Kike jin tsoronsa haka ?numfashi ta fitar da karfi ta mike tana cewa "ban san me yasa wani lokacin kike manta kiyayyarsa gareni ba ,ki daina cewa kiyayya yaya baya kinki halinsa né km kowa yakewa amman kema zuwa yanzu ya kamata ki saba dan da nice dana maidashi man shafawana ,uhm baki san halin wannan yayan naki ba idan yana kin mutun halinsa dabam kiyayyarsa dabam ta fada tana taku har ta qarasa in da Kwabar kayanta yake ta ciro doguwar rigar lace mai shege kyau da tsada sabuwa ce bata taba sakawa ba sai a lokacin bata tsaya yin wata doguwar kwaliya ba ta zauna zaman jiran kiran mami ."
Tana zaune ta jiyo hayaniyar shigowar motoci haraban estate din ahankali cikin sanyin jiki ta mike ta isa jikin window dakin ta dage labule ahankali idanunta ya sauka akan motocinsa da motocin ss guda shida inda masu kula da lafiyarsa mutun uku suka fito da sauri mutun daya ya bude masa murfin mota ya fito ya tsaya bisa kafafunsa ."
A natse ya soma taku mutane suka sakashi a tsakiya wanda dayawan su yan tarbosa ne yayi matukar kyau sanye cikin riga da wondo na black suit mai tsaida da sheki yayinda sumar kansa Ke kwance luf yana zuba sheki alamun yana samun kulawa haka zalika farinsa ya qara fitowa alamun yana cikin koshin lafiya sai wani ipod dake manne da kunnensa na jin mgn gaba daya mutanen dake tare dashi ya zartasu a komai hasken fata da tsawo cike da Kamala tana tsaye suka gama wuce wa ta lumshe idanunta na second biyar sannan ta bude idanunta ahankali suka sauka akan hindu tsaye fuskarta murtuke cikin bacin rai aranta tace ko me ya bata mata rai ita da tayi kamkamba da shishigin zuwa tarbosa?."
"Uhm yanzu haka halin nasa yayi mata nan wani murmushi ya bayyana akan lip's dinta haka nan ta tsinci kanta da jin dadin yanayin dataga hindu ai kin iya shishigi kuma karshen masu irin halinki kenan ajiyar zuciya ta sauke tana sakin labule ta juyo idanunta cikin na nana hauwa'u,"kin gama kallonsa ."
"Shi wa ?"
"Ya adam !ta bata amsa atakaice,kai haba sister kai haba sister ko gsky Ke na gama karantarki fa kema kin fad'a sawun masu son ya adam kar muyi haka dake sister ."allah ba wasa nake ba kina son shi son ..."
nan da nan idanun maryam ya cika da hawaye nana hauwa'u ta zaro ido ke fa matsalata dake kenan saurin kuka kamar wata qaramar yarinya daga na fadi gsky ."
"Aa sister wannan ba gsky bace taya zaki fada min haka ?me yasa zan so mutumin da bai sona?
nana hauwa'u ta sauko daga saman gado ta dafa kafadanta zaku so juna wuyarta ayi aure muamular miji da mata ya sha bambam da rayuwar waje fatanmu allah yasa ya sauko da wuri ."
" sister bazai sauko ba kema Kinsan halinsa yana son mutun ma ya ya qare bare ni da yake jin Kmr ya kasheni ,ni ban san ya zanyi da rayuwata ba gashi kowa son shi yake kalli hindu fa har airport taje tarbosa " kinga matsalata dake kishin maseefa ."
"allah ba maganar kishi bane sister da me zan ji da rashin son da bai me ko kuma da yammatan dake sonshi "kyale wannan mahaukaciyar kema Kinsan bazai sota ba dan hk ki saki ranki kisawa ranki kece sauraniya a gidansa in sha allahu kece glashin idanunsa naunayen ajiyar zuciya mrym ta sauke sai lokacin taji natsuwa ajikinta tana damke hannun nana hauwa'u cikin nata "na gode da addua Sister Allah yasa hakan ya kasance ."
Gyada kai nana hauwa'u tayi ta zare hannunta ta nufi kofar fita "ni na tafi tarban babban yaya sai kin fito mami na tsaye a tsakiyar parlour'n fuskata dauke da murmushin farincikin dawowar tilon danta yana gama shigowa tsumammun idanunshi ya sauka akanta cikin shiga na alfarma fuskarsa kamar koda yaushe babu annuri amman duk da haka yayi farincikin ganin sweetheart dinsa cikin koshin lafiya atare suka soma daga kafafuwansu domin isowa ga juna suna gama qarasowa yana qoqarin durkusawa mami tayi saurin rike kafafunsa ta rungumeshi ajikinta tana shafa bayansa "sweetheart mun samuku lafiya ?lafiya lau adamcy nah da fatan ka dawo lafiya ? ajiyar zuciya kawai ya sauke ta zaresa ajikinta ta qarasa dashi kan kujera mai zaman mutun uku ta zauna a kusa dashi tana rike da hannunsa rayuwarta né adamcy tana matukar qaunarsa shiyasa yake mata abinda yaga dama ."
nana hauwa'u tai masa sannu da zuwa ya amsa da kyar yana zaune mutanen gidan suka dinga shigowa daya byn daya suna masa sannu da zuwa ita kam maryam bata fito ba tana daki ta kwanta rigingine jiran mami ta nemeta mami bata nemita ba har akayi sallah magrib da ishai sai data ga babu alamun mutanensa a falo dashi kansa ata ta fito ta zauna tare da nana hauwa'u da mami aka cigaba da hira daita "
Karfe tara daidai mr ata ya sauko cikin blak long sleve da farin wando na shan iska sai kamshi turarensa na Reed ke tashi akoina ajikinsa ya samu waje ya zauna a daya daga cikin kujerun falon yana duban mami dake zaune tana waya nana hauwa'u ta sake gaishesa ya amsa aciki, ganin haka yasa maryam ta bud'e bakinta da kyar cikin in ina "ya..ya sannu da zuwa da fatan ka dawo lafiya ?"banza yayi mata tamkr bai ji abinda ta fada ba nan kuwa yajita sarai sai ma ya dauke idanunshi akan mami ya maida kan wayarsa numfashi ta sauke da karfi ta kama bakinta ."
Bayan Kmr mintuna shabiyar ya motsa lip's dinsa da kyar" sweetheart yunwa nake ji cikina har zafi yake murmushi mami tayi allah shiryeka adamcy kullum girma kakeyi amman sai ka dinga abubuwa kamar yaro ya yatsina fuska a gaban uwata nama fi yaron goye ,allah ya shiryeka me zakaci akwai alkubus akwai rice and stew akwai sakwara "rice kawai ya isa okay maryam maza zuba masa ki daura a tray ki kawo masa nan "bana bukatar daga gareta kisa wani yayi min "
"Bangane haka ba ? yayi shiru kawai yaki cewa komai duk bakinsa mgnr yake son yi "zaka fara ko daga dawowarka?yaruwarka kuma matar da zaka aura ce kakewa haka ? Allah adamcy ka fita cikin idanuna daga zuwanka zaka fara da bata min rai kuma ya mukayi da kai ?bance ka bar duk wani mugun nufinka a inda ka baro ba ?"yi ...ha ..kuri sweetheart ya fad'a tare da dago kanshi nan take kwayar idanunshi ya shiga cikin na mrym wani mummunar faduwar gaba ya risketa saurin cire nata tayi ilahirin jikinta na daukar rawa "maryam jeki yi abinda na sakaki a tsorace muryarta na rawa tace "to! ta juya ta shige kitchen domin dauko trya
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 22
Saurin mikewa tsaye mr ata yayi ya haura samansa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ransa a dagule yake taka step dan idan akwai yarinyar daya tsana anan duniya to wannan maryam din ce, ji yake kamar ya kasheta ya huta da muguwar tsanar da yayi mata ,mami tabi bayansa da kallo har ya qarasa sauka akan step tana jin zallar bacin rai da bugun zuciya yana shiga d'akin ya cire rigar jikinsa da singlet ya cila kan kujera ya shige bedroom dinsa ."
koda maryam ta fito daga kitchen taga wayam babu shi babu alamunsa a inda ta barshi ta kalli nana hauwa'u ta kalli mami fuskarta da alamun tambaya "zuba masa abincin daya buqata ki bishi d'akinsa dashi maryam tai saurin zaro ido waje ,cike da matsanancin tsoro ta shiga girgiza ma mami kai yayinda yanayin bugun da zuciyarta yake ya qaru, yanayin tsoratanta kuwa sai ya baka mamaki idanuwanta ta runtse jin tashin hankalin daya kusantota ."
nana hauwa'u ta mike daga inda take zaune ta qaraso inda mrym take tsaye rike da tray mrym bata ankara ba sai jin mutun tayi tsaye kusa daita ta dafa kafad'anta ta bud'e idanuwanta da kyar akan nana hauwa'u "common sister ki sanyawa jikinki natsuwa ki rage wannan tsoron please ".ta fad'a tana riko hannunta ta fara tafiya daita."
"Sister bazaki gane bane wallahi ina matukar jin tsoronsa, na sani yanzu dai kiyi abinda mami tace babu abinda zai iya miki keda kike da mami a hannunki ai sai yadda kikayi dashi, da taimakon nana hauwa'u ta had'a komai a tray ta rakata har samansa adaidai bakin kofar shiga parlour'nsa taja ta tsaya tana cewa "ki shiga da kafar dama sannan ki sanyawa jikinki jarumta daga nan ni zan koma "haba sister mu shiga tare mana Kinsan fa bani da wannan jarumtar "rufa min asiri sister kar ya sauke fushinsa akaina gara ke idan yayi anything stupidty zai had'u da mami ni kuwa fa ? komai yayi min yaci lafiya ,kafin mrym tayi wani yunkuri yin magana har nan hauwa'u ta juya ta soma tafiya tana waiwayenta tana karfafa mata gwiwa "
Cikin natsuwa ta tura kofar parlour ta shiga bakinta d'auke da sallama taga baya parlour ta had'iye wani yawu daya tsaya mata a makoshi tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ,ahankali ta ajiye tray hannunta akan center table din dake ajiye ta nufi kofar bedroom tayi knocking ahankali saboda tasan baya són hayaniya jin shiru yasa ta sake knocking amman still shiru ".
ganin kar abincin yay sanyi ta sake qarawa kanta laifi a wajensa yasa ta murd'a kofar cike da tsananin tsoro da tashin hankali ta shiga idanunta a runtse tare da rufe kofar ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya balbaleta da ruwan maseefa amman taji shiru .jin shiru yasa ta d'agowa taga baya cikin d'akin wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke , kai tsaye kwakwaluwarta ta bata yana cikin d'ayan d'akinsa ."
Ahankali ta juya ta fito daga cikin d'akin har tayi taku uku domin isa bakin kofar d'ayan d'akin sai kofar d'akin ya bud'e ya fito daga shi sai gajeren wondon dake sanye ajikinsa a matukar tsorace take kallonsa da kallon murd'add'en jikinsa dake sheki tsabar kulawar da yake samu ."wani wulakantaccen kallo yayi mata mai had'e da harara yasa a tsorace ta d'auke kwayar idanunta akan shi tayi saurin juya masa baya tana neman afuwarsa "am really sorry mami tace na kawo maka abinci .."
Tsaki yaja a fili yana kallon bayanta daga inda yake tsaye yana iya hango tashin hankalin da take ciki ya rasa me yasa sweetheart take masa hk ?ya guji cin abinci daga hannun yarinyar amman sai da tasa aka biyosa d'akin dashi kmr dole sai yaci abincin hannu ?"yayiwa kanshi tmby yana mai sake jan wani tsakin ."
ta gefenta ya raba ya wuceta ya shige d'ayan bedroom dinsa dan ganinsa tsayawa ma inda take asara né ,kusan mintuna shabiyar ya sake fitowa a tunaninsa ta fita amman abun mamaki tana nan tsaye Kmr wata tsohuwar soja , ya ja tsaki ya zauna akan kujera ya kunna computer dinsa ya shiga yanar gizo fannin kasuwancinsa . ta cigaba da tsayuwa sai dai ta rasa yadda zatayi masa magana yaci abinci sai ta motsa labbanta zata masa magana amman tsoronsa ya hanata ."
tana tsaye aka fara kiran wayoyinsa yana amsa kira ,duk abinda yake ko ajikinsa dan babu ruwansa da tsayuwarta ya cigaba da abinda yake tana kallonsa ta kasan idanunta ya kashe computer ya kwashe wayoyinsa ya d'auki rigarsa ya rataya a kafad'ansa ya fito ya barta tsaye ya sauko kasa har lokacin mami na zaune ita kad'ai ."
Ya zauna batare da yace komai ba , mrym ba tayi fushi ba dan daman ita ba mai saurin fushi bace , kafin kaga fushinta da wahala sai dai akwai zuciya ,zuciyar ma yana dadewa bai motsa ba amman idan ya motsa babu kyau ,ta d'auki tray data shigo dashi ta fito, a parlour ta iskeshi zaune yana shan kamshi inda kasan wani jinin sarauta yana daddana waya ,har gabansa ta qaraso ta ajiye tray din akan table din dake gabansa ta bud'e masa kular abinci cike da tsoro dan kar tayi laifi ta d'auki ruwan dake kan tray ta juya a natse ta shiga kitchen ta bud'e fridge ta canza masa da wani ruwa mai dan sanyi kad'an tazo ta ajiye masa "ga abincin !
Biyayyarta na matukar burgesa domin shi din mutun ne mai tsananin son ya juya duk wanda yake karkashinsa most especially mace , yanayin tsoronsa da biyayyarta yayi ,matsalar dai baya sonta , mami dake zaune kuwa kallonta kawai take yadda take komai a natse cike da kulawa da tsoro da gudun kartayi laifi amman sam adamcy bai damu da duk abinda take ba hasalima hankalinsa da natsuwarsa basa gareta ."
duk yadda mami take són mrym din ta kasance a yanzu tayi babu wani abu d'aya saura ga dukkanin alamun zata kular mata da adamcy yadda ya kamata , daman kuma irin macen data kamacesa kenan mai tsananin biyayya da hakuri da gudun 'bacin ransa saboda yanayinsa ,maryam bata tsaya ba ta nufi d'akinsu inda ta iske nana hauwa'u kwance tana chart, ita kam zama tayi shiru cike da damuwa ita kadai tasan halin damuwar da take ciki duk yadda take son waya a wannan lokacin ya d'an fara fita kanta , dan ko ta d'auki wayarta dan shiga what's app bata 'barkata komai ,hakan friend's dinta zasu yita mata mgn har su gaji su hakura ."
Mami ta tashi daga mazauninta ta dawo kusa dashi ta zauna ta riko hannunsa d'aya cikin nata tana dubansa cike da kulawa dan bazata iya fushi dashi ba , kuma tasan muddin ba itace ta tursasa masa ba haka zai kwana da yunwa, kuma ta rigada tasan bai ci komai ba dan muddin yana qasar baya ta'ba cin abincin kowa sai nata"."look at me adamcy ,ya bar abinda yake yi ya kalleta Kmr yadda ta bukata ,look at the time adamcy ta nuna masa makeken agogon dake manne a bangon parlour'n "lokaci na tafiya tunda ka shigo gidan nan ruwa kawai ka sayanwa cikinka "bai kalli agogon data nuna masa ba bare yasan lokacin daya d'auka bai sayanwa cikinsa komai ba sai ma d'auke idanunshi da yayi akanta yana hura hanci ."
"Tsawon wata biyu bamu had'u ba sai kuma tayi murmushi ganin yadda ya qara had'e girar sama data qasa kamar wani qaramin yaro , ta d'aura d'ayan hannunta akan hannunsa dake cikin nata "me yasa baza kayi abinda zai faranta ran sweetheart dinka ba ? Ta numfasa irin nasu na manya kana ta cigaba da magana "koda yake ina son wannan fushin naka ban sani ba ko dan yana qara maka kyau ne ?"
lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya juyo ya kalli mami ba yace "nima ina son fushina ina son yadda Allah ya halliceni " murmushi mami ta sake yi "to ai shikenan daman ai mai hali baya gudun halinsa yanzu dai kaci abinci shine abinda nafi buqata "na koshi ".ya fad'a atakaice yana fesar da numfashi .
mami ta juyo da fuskasa gareta ta dungure masa kai tana cewa "allah baka isa ba ,duk yadda aka sha wahala akayi girkin nan kace ka koshi ,allah sai kaci idan ba haka zanyi fushi mai tsanani da kai sai da mami ta had'a da marairaicewa sannan ya fara cin abinci daga hannunta " a ranta tace hukuma sai da rarrashi ."mami girkin nan kamar ke kikayi Kmr kuma bake kikayi ba?".
"me yasa ka fad'a haka ?yayi shiru yana nazari sannan yace "yayi dadi Kmr naki but ya dan yi maggie kad'an ba kamar abincinki ba dan sam girkinki maggie baya yawa , kamar ta fad'a masa gskyr wacce tayi amman tasan halin yan kayanta sai ya birkice mata yanzu ta rasa gane kanshi dan haka tace" ni nayi kasan yau da gobe sai allah, ni kaina naji maggie ya d'an so yayi yawa amman ai yawan da yayi bazai hana a kasa ci ba ,shiru yayi ya tsura mata tsumammun idanunshi yana dubanta a tsanake bai san me yasa ba sai yake jin Kmr ba gsky sweetheart ta fad'a masa ba ,dan dai yasan wacece sweet heart dinsa a fannin girki babu karya tana da matukar kwarewa tun yana yaro ya sani suna zaune ma take had'a girkinta ta tashi ."
bayan ya gama cin abinci mami ta kallesa a natse kafin daga bisani ta kira sunansa "adamcy nah? ya tsura mata tsumammun idanunshi kawai yana kallonta da sauraronta "ya ake ciki da maganarku dasu sultan naji ko a waya baka sake ce min komai akai ba ?ya lumshe tsumammun idanunshi na second biyar sannan ya motsa labbansa yace "magana ta wuce tunda sun dawo da makudan kadaden da suka sace "ikon allah ! account dinka suka saka kud'ad'en ko kuwa account din agc ?" no Ibrahim suka kai wa cheek amman ya fad'a min fahad ne ya kai masa bayan sultan da salim sun qare masa zagi .
"Zagi kuma ?!
Ya lumshe mata ido kawai alamun "eh !
"Wannan abu gsky bai yi dadi ba Allah
sarki ibrahim bawan Allah to shi meye nashi
da zasu zagesa ? a cewarsu yayi masu munafurci alhalin ni bashi ya fad'a min ba hasalima bai sani ba a bakina yaji ,"allah sarki bawan allah ,allah dai ya kyauta kawai , Allah km ya shirye su shiri na addinin muslinci , bancin company agc ya tsaya da kyau nasan da zuwa yanzu an rufeshi kullum daga anemi kud'ad'e a rasa sai a nemi kaya arasa kuma duk masu yi suna gindinmu ."
"sosai kuwa shiyasa yanzu gbdy zan tattara hankalina zuwa agc kusan ma nan zan fi karfi a sati sau uku zan dinga shiga sauran ranakun kuma zan dinga leka wanda suka samu acikin companies dina , hakan yayi daidai allah yasa mu dace yace "ameen ! ya fad'a tare da d'aukar remut ya canza channel zuwa aljazera.
Mami tayi shiru tana kallon tv can ta waigo inda yake zaune idanunshi na kallon tv , kallonta yayi ta gefen ido kafin ya maida idanunshi sosai kanta ya dage mata girasa daya alamun tambaya ,numfasawa tayi sannan ta soma magana "nace bakaga ya kamata ka dinga d'an jan yarinyar nan mrym ajiki ba ?
"Janta ajiki kuma kamar wata yarinya qarama ? ya fad'a cike da jin mamaki " ba maganar kamar wata qaramar yarinya bane yana da kyau ka jata ajiki ta yadda zata sake da kai idan ma ta kama ka dinga kiranta hira domin ku samu fahimtar juna ?"Wani fahimtar juna kuma ya saura sweetheart ? yarinyar nan tasan halina tasan abinda nake so da wanda bana só ."
"duk da haka dai ya dace ku dinga zan tawa "gsky sweetheart bana jin zan iya, akan na kirata zance gara a fasa auren kawai dan nasan bazan ta'ba iyawa ba ,taya ma zan fara ?"mami tayi murmushi irin nasu na manya tace ,idan baka san ta inda zaka fara ba ai sai ka tmbyi abokanka masu aure sa koya maka ta inda suka fara , idan kuma kana jin kunyarsu ne sai ni na koya maka ko ba shikenan ba tunda dai ni nasan baka jin kunyata ".
tunda mami ta fara magana ata ya sanya hannunsa a tsakanin hancinsa da bakinsa kawai yana kallonta "ko na kira maka ita yanzu ?"mrym ! mami ta kwalla ma mrym kira "oh my godness god , haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?kai ma me yasa bakasan kayi abinda ya dace ba ?"allah sweetheart bazan iya kira kowace mace da sunan zance ba " Allah ko ?! ya dage mata girasa d'aya alamun "Eh! ai kam dole ka kasa iyawa tunda ka zama tuxuru fuskarsa a had'e yace "sweetheart ai itama yarinyar taki tsohuwa ce wallahi , baki ga duk kashin tsufa ya bayyana ajikinta ba ? mami ta dan ware idanunta sosai "akwai wani kashin tsufa ajikin mutun ne ?ta tmbyesa dry na kufce mata ."
Wani sanyi dadi yaji aransa yace "sosai ma kuwa akwai ,to kai taya akayi ka gani ? kodai adamcy ya kamu ne yana so yana kaiwa kasuwa ?bai ce mata uffan ba sai dai a zuciyarsa yace " allah ya tsareni ,ata ya kamo hannun mami cikin nashi yana marairaice murya "sweetheart ! ya kirata sunanta tana dariya tace "ina jinka adamcy nah "dan girman allah laifin me nayi miki da kika zabi ki hadani da yarinyar nan aure ?".
"taurin kanka ne ya jawo had'a zumunci "amman sweetheart baki ga rashin dacewarmu ba ni dogo ita duwaf ? ban son wulakanci adamcy yarinyar tawa ce duwaf ?ta fad'a tana had'e rai ."ai yar daidai kusa da kafad'ata kamar zata fi dacewa dani akan mace guntuwa ?," idan ta kai maka daidai kafadanka cin tsawon zakayi ?ta fad'a tana kunshe dryata yayi shiru kawai yana zare hannunsa cikin nata."abinda bakasani ba dogo nmj da mace mara tsawo sunfi dacewa , karka damu da rashin tsawon maryam nagartata zaka duba ,Kmr yadda na sha gaya maka mrym ce daidai da halinka sannan zata haifa maka ya'ya na gari zuqa zuqa ."
"Sweetheart sai da safe yayi ma mami sallama ya mike tsaye da rigarsa akafad'a dan yasan bazata barsa ya huta da maganar yarinyar ba , kai tsaye ya wuce saman d'akinsa wanka ya fad'a zuciyarsa cike da tsananin mamakin maganar mami "wai ya kiranta zance idan ya kirata yace mata me ?yaja dogon tsaki ,aikuwa muddin sai ya kirata zance sai dai a hakura da auren ,byn wasu mintuna ya fito yana goge sansar jikinsa , byn ya gama ya qarasa inda turarukansa suke ya dauki bodyspare ya feshe ilahirin jikinsa sannan ya saka gajeren wondo iya cinyarsa da riga fara sol ya kwanta yana mai jin tausayin kansa ."
"ya rasa me ya tsarewa mahaifiyarsa da take son ta had'ashi aure da wannan guntuwar yarinyar mai siffar wada yarinya sam babu fasali , yasan muddin ya auri maryam rayuwarsa da farincikinsa zasu yi kasa ,kai gbdy komai nashi zai canza kuma yasan har da walwalansa ,ya gyara kwanciyarsa tare da janyo pillow ya d'aura asaman ruwan cikinsa ya rungume tsam tsam yana jin kamar princess ce duk da yana son mantata amman duk sanda zai yi bacci sai yayi tunaninta sannan bacci mai dadi yake d'aukarsa "
a yadda yake jin felling din yarinyar yayi imani zai had'u daita sai dai yaushe ne ? a ina ne ? bai sani ba , ahankali ya dinga juyi akan katifar yana jin felling dinta mai tsanani yana sauka a sansar jikinsa ,ji yayi kamar anyi kissing din lip's dinsa ya d'an bude idanunshi yaga wayam babu kowa sai shi kad'ai a d'akin, ya sake maida idanunshi ya runtse sai dai a haka yake jinta kusa dashi kuma yake imaginetion din komai ."
sake janyo pillow yayi ya rungume tsam yana jin tamkr itace ajikinsa , ahankali bacci ya d'aukeshi cike da mafarkinta wai gata ta hau saman qirjinsa ta kwanta tana shafa qirjinsa zuwa kan nipples dinsa wani irin d'auke numfashi yayi da karfi dan alokacin da'ace akwai wani a d'akin dan dole ya fahimci yana cikin wani hali .wani irin juyi tayi har rigar dake sanye a jikinta ya zame wanda daman dashi da babu duk daya ganin abinda yafi so ajikinta wato dukiyar fulaninta ya tashi zaune acikin mafarkinsa ya rike hannunta gam cikin nashi yana murzawa "my princess ina kika shiga two day's baki zo min ba ? banje koina ba ina tare da kai ,tayi masa mgn tana kai harshenta qirjinsa ta fara lasa wani irin abubuwa yake ji suna yi masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa ."
tsigar jikinsa gbdy suka mike yayinda jijiyarsa ta dinga harbawa da sauri sauri rungumota yayi sosai ya sakata a tsakiyar qirjinsa hancinsa ya cusa cikin suman kanta daya zubo har gadon bayanta ahankali ya dinga shakar kamshin jikinta tare da lumshe ido yana jin wani sanyayyen abu a zuciyarsa".
"kina sona ?ta gyada masa kai alamun "eh !,to ki taimaka ki bayyana min kanki tun kafin ayi min auren dole ,wani bayyana maka kaina zanyi byn gashi muna tare ?ni da kai muna tsananin son juna ko ka manta tsawon lokacin da muka kulla soyayya a tsakaninmu ?ya gyada mata kai ," alaka soyayyarmu mai karfi ce domin kai din nawa ne na har abada ,sake matsota yayi sosai ya kai hannunsa kan karan hancinta yayi kasa da hannunsa har zuwa kasan marata , yana jin lokacin data sauke numfashi zuciyarta na bugawa da karfi hakan yasa ta shige masa tun daga wuyanta ya fara shafata itama tana shafashi ,kamkameta yayi ajikinsa ya had'e bakinsu waje daya yana wa bakin wani irin tsotsa na fitar hankali ."
Bangaren marym itama kwance take tana faman juyi akan katifa dan ta kasa runtsawa tana saka da warwara kwalkwaluwarta na sake nitso cikin kogin tunani ta yadda zatai rayuwar aure da mutun irin mr ata ,mutumin da baza tace ga ranar data ga murmushinsa ba ,hasalima fuskarsa koda yaushe a had'e take tmkr hadari juyi kawai take tana tunanin abubuwa dayawa akan aurenta dashi bai sonta ,gashi tunda akace ita zai aura bata sake samun isashen bacci ba kullum da abubuwan da take facing ,sai ta dinga jin kamar ana farautarta, wani lokacin idan ta runtsa idanunta sai taga mutun akanta ana qoqarin caka mata wuka da zarar ta bud'e idanunta ta kunna wuta sai taga wayam babu ko alamun mutun dan wani lokacin tashi take tayi alwala ta gabatar da sallar nafila.
yayinda take nan kwance cikin tsananin tunani da fargaba shi kuma mr ata yana can duniyar mafarkinsa ."ajiyar zuciya ta sauke ta kalli nana hauwa'u dake sharar baccinta hankalinta kwance "allah sarki sister kin huta, kina rayuwarki hankali kwance baki da wata damuwa ,ya allah kasa auren yaya adam arayuwata alkhairi ne ta furta
hakan a fili ,ganin har kusan karfe biyu da wasu yan mintuna na dare bata runtsa ba ga gari ya dauki shiru sosai baka jin motsin komai ,taji kamar ta tashi taje tayi alwala ta roki Allah alkhairi daga cikin alkhairun dake cikin dare amman sai taji ta kasa tashi domin alokacin idanunta sun fara mata yaji alamun bacci ahankali bacci barawo ya d'auketa ."
cikin bacci mrym taji numfashinta baya sauka yadda ya kamata kamar an danneta ta kai hannunta tana qoqarin cire abinda taji ya danne mata fuska wanda take tunani pillow ne akayi amfani dashi amman sai taji an sake danneta da iyakacin karfi ta yadda ko sautin muryar ta bazaa iya ji ba nan fa ta fara mutsu mutsu da kafafunta tana kokarin kwatar kanta cikin ikon allah ta samu nasarar rike hannun mai shi nan fa suka fara kokuwa mrym na qaqarin ta amshi pillow amman ana sake danne fuskarta ita km sai qoqarin ceton ranta take ."
inda tayi wata irin zabura ta fixge pillow ta kwalla wata razananniyar qara wanda yasa gidan gbdy ya dauki sauti kuwar qararta ,nan da nan nana hauwa'u ta farka daga naunayen baccinta tana kiran sunan da take kiranta dashi " sister lafiya tare da qoqarin kunna wutan dakin ? mrym bata amsa mata ba sakamakon inuwar mutun data ga yana qoqarin ficewa daga dakin tayi wata irin sufa sai gata ta rike gefen rigar mai shi adaidai lokacin da nana hauwa'u ta samu nasarar kunna wutar d'akin adaidai lokacin mai shi tasa hannuwanta duka ta ingiza mrym da iyakacin karfinta tayi baya luuuuu sai dai ido cikin ido suke kallon kwayar idanun juna sanye take cikin bakaken kaya tun daga samanta har kasanta babu abinda zaka iya gani ajikinta sai kwayar idanunta ."
a kallon da mrym take ma yanayinta ya nuna mata mace ce hannunta daya rike da wuka duk da suna kallon lokacin da tayi fillinging da wukar a tsakiyar daki ta fice da sauri tana haki nana hauwa'u ta sauko a rude ta tare bayan mrym tana rungumeta ajikinta "sister ki bita karki bari ta fice wallahi kasheni take qoqarin yi duk suka rude sai zufa suke fitarwa mrym tace "wallahi kasheni zata yi ta sake fad'a tana qoqarin mikewa domin tabi bayanta ."
Mrym na qoqarin mikewa tsaye alokacin mami tare da masu aikin gidan suka shigo cikin dakin cikin tsananin tashin hankali a matukar firgice maryam ke matsu bayanin komai mami tace "Inna lillahi !a garin yaya ? ta yaya ma hakan ta faru ?wallahi mami da gaske yau kwanana ne kawai Ke gaba dana bakunci lahira daman kullum ina jin ana yunkurin kasheni ,wallahi mami nafi tsawon wata biyar ina jin ana farautar rayuwata cikin dare maryam ta fad'a cikin matsanancin tashin hankali "to akan wani dalili kenan ?"wallahi bani sani ba ta fad'a cikin muryar kuka har da shesheka nan da nan nana hauwa'u ta fashe da kuka ta kamkame mrym magana take son yi amman muryarta ta kasa fita tana kallon wukar dake yashe kasa ,sabuwa fil da alamun baa ta'ba amfani daita ba ."
"Mami kalli wukar datazo daita nasan wallahi kwana ne kawai agaba yasa ta fara amfani da pillow bancin haka tana daba min wukar nan cikin bacci sai dai na farka najini a lahira, mami ta qarasa inda wukar take ta tsura mata ido muryarta a sanyaye tace auta miko min wukar data yar , ta dauki wukar ta mika wa mami " wannan kamar irin wukar daa aka kashe mubina ko ?gbdy suka sake shiga rudani nana hauwa'u ta matso kusa da mami sosai tana cewa "tabbas mami irin tace nima kallon da nake ma wukar kenan dan lokacin rasuwar mubina nima na ga wukar " .
"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun daman acikin estate din nan makashin mubina take ? domin babu tantama acikin estate din nan ne domin babu wanda zai tsallake masu tsaro sama da goma sha biyar banda securities ya shigo esatate din nan lallai acikin estate din nan ake qoqarin kashe mrym nana hauwa'u ta gyada mata kai alamun haka maganarta take .""auta taso min adamcy da mugun sauri ta fice daga dakin zuwa nashi bata tsaya neman izini ko sallama ba ta banka dakin baccinsa yana kwance rungume da pillow "yaya !yaya! cikin bacci yaji ana tabashi hade da kiran sunansa ya bude idanunshi cikin tashin hankali yana cewa "Lafiya ?wai kazo inji mami da sauri ya kalli qaramin agogon dake ajiye akan bedside dinsa karfe uku yanzu ta wuce saukowa yayi da sauri dan yasan koma meye ba lafiya ba da wannan tsohon dare tace a kirasa ."
Jallabiyarsa ya dauka ya zira ya fito rike da gefen Jallabiyar dan ya samu damar daga kafafunsa da kyau biyu biyu ya dinga taka step yana gama saukowa ya karya zai shiga parlour'nta na biyu nana hauwa'u tace "tana dakin mu kai tsaye ya wuce bai tsaya jin dalilin ba atare suka shiga dakin cikin tashin hankali mami take masa bayanin abinda ya faru ."
shiru kawai yayi yana duban mrym dake wani irin kuka bai yi mamaki jin abinda mami ta fad'a ba sannan babu wacce tazo cikin tunaninsa sai nuzla domin ta tura masa da sakon lallai idan bai amincewa aurenta ba zata ga byn mrym sai dai itama idan ta kasheta a kasheta lokacin daya ga sakon shi ko ajikinsa dan kuwa da allah yasa tayi nasara kasheta data taimaka wa rayuwarsa ita taje da Allah shi kuma ya huta da qaya."
kiran mutanen estate din mami tasa nana hauwa'u ta dinga yi suna nan tsaye a daren sai ga jama'ar gidan duk suka rude iyayen mubina sunfi kowa shiga tashin hankali yayinda mrym Ke kuka har lokacin mahaifiyar mubina kam ta yarda domin kuwa me wukar tazo yi dakin maryam kuma exactly irin wukar ce babu tantama ,mami ta qaraso ga mrym dake zubar da hawaye "me yasa zasu kashe min mrym ?ince duk esatate din nan yanuwan juna ne babu bare acikinmu ?
"me yasa zaa dauki ran wani ?dan girman allah ku taimaka ku fad'a min cewar duk wannan abun dake faruwa a mafarki ne domin bana tunanin haka daga cikin ahlin nan, bana tunanin wani zai iya aikata min haka kuce min wasa ne ba niyyar kashe min mrym akayi ba ?"mrym ta sake fashewa da sabon kuka tana rungume mami ajikinta gbdy ta tsure ta nemi natsuwarta ta rasa itama mami rungumeta tayi tana shafa bayanta ."
"Sweetheart kukan ya isa ki bar kuka ki kwantar da hankali kowaye acikin estate din nan zan fito dashi Ke kuma malama kin cikawa mutane kunne da hayani just keep queit I don't want to hear any sound please ya juya ya kalli wadan da suka hallara a dakin dan ba kowa ya shigo ba, dan wasu na can na bacci bama su san meke faruwa ba na kusa kusa ne suka samu damar shigowa yace "kowa ya tafi ya kwanta zai dauki mataki , ya dauki wukar ya fice .
daya byn daya suka dinga fita daga dakin cike da jima min , mrym da nana suka bi mami dakinta kowace ta haye gado sai dai ba da niyyar bacci ba dan mrym kam kuka take sosai babu abinda take gani sai mubina cikin jini shikenan da yanzu wani labarin ake ba wannan ba ,da yanzu tana cikin jini tana wannan imagenation din tana kuka nana hauwa'u kuwa zaman dirshan tayi da mami suna tautaunawa dan bacci kam ya kaurace masu ."
Washgari baba babba ya tara manya gidan tun daga kan kannensa har zuwa kan yayyansa na sama dasu dana kasa dasu dake esatate din acikin dakin na musamman da suke ganawa a duk sanda abu makamancin hk ya faru ,ya dade yana bayanin abinda ya faru a daren jiya tare da jan kunne da nasiha mai ratsa zuciya a karshe yace zaa yi bincike duk wanda aka samu da sa hannusa zaa mikasa hannun hukuma dan maganar da nake daku yanzu haka nayi report wajen police har na mika masu wukar domin a fara bincike duk hankulansu a tashe mrym kuwa har wanna lokacin kuka take aunty shahida da khadija kaf yayan mami tun safe suka yiwa gidan diran makiya jama'a kuwa sai zuwa jaje suke yi wa mami haka ma iyayen maryam sun kira yafi sau babu adadi wuni ranar haka mrym tayi shi cikin dakin mami cikin tsananin tashin hankali ."
Bayan kwana biyu da faruwar lamarin da misalin Karfe hud'u sauran wasu mintuna mr ata ya shigo estate dinsu drivenshi na tsayawa batare da bata lokaci ba masu kula da lafiyarsa ta hukumar dss suka fito da sauri kafin ma su bude masa ya bude ya fito yana gyara zaman rigar jikinsa kai tsaye masalacin dake cikin esatate din ya nufa domin gabatar da sallah bayan ya idar da sallah ya nufo gidansu nana hauwa'u da da maryama na zaune idar da sallar su kenan sai ga diyana ta shiga hira suke kadan kadan mrym na bawa diyana labarin abinda ya faru daita "amman Kinsan wani abu diyana duk yadda muke da nuzla bangata ba kuma nasan taji abinda ya faru dani har cikin daki aka biyoni zaa kasheni amman ta kasa zuwa tayi min jaje tunanina ni kuwa laifin me nayi mata? wallahi har da kwalla nayi na rashin zuwanta saboda banyi tunanin hk daga gareta ba ."
"gsky da mamaki kuma kinga ai ba haka take ba tana da kulawa da mutane most especially idan abu ya sameka na farinciki ko akasinsa amman Kiyi mata uzuri wata killa tana nan hanyar zuwa tunda duka yau kwana biyu ne da faruwar abun ,wannan gsky ne nuzla bata da haka amman baku lura a tsakankanin lokacin nan ta dan canza ba ?inji cewar nana hauwa'u"eh ta canza kam sosai ko Kinsan damuwarta ?ko daya ban sani ba wallahi na dai kula ta canza ko a yanayin jikinta zaki fahimci akwai abinda ke damunta mrym tace " to koma meye allah yafi mu sani Allah ya yayewa kowa damuwarsa Suna zaune mr ata ya shigo gbdy suka masa sannu da dawowa ya amsa Kmr yadda ya saba aciki sannan ya kalli auta yana tmbyr mami "ke auta ina sweetheart. ? "tana ciki ta shiga tayi sallah yana gama ji ya haye sama suka cigaba da hirarsu ."
Bai sauko ba sai bayan awa daya sanye da shirt ajikinsa da wondo ficewa yayi bai tsaya akoina ba sai gidansu nuzla ya tmbyi mahaifiyarta ta sheida masa tana dakinta bata jin dadi a natse ya nufi kofar dakinta ya tura kofar ya shiga tare da sallama akan lip's dinsa tana ganinsa ta mike zaune tana ware fararen idanunta akanshi tayi qoqarin ta sakashi cikin nashi idon sanda yake takowa zuwa inda take tana masa duban mamaki dan bata ta'ba expecting zata ganshi har cikin bedroom dinta ba ."
sosai ya dauki hankalinta yayi wani fresh yayi qara kyau kaman zane ta koina ya hadu matsalar dai shi din mugun miskili ne sai dai hakan ma qara masa kyau yake ahankali ya janye idanunshi acikin nata ya maida dakin yana qarewa koina kallo "Lafiya
yaya adam da wannan zuwan naka na bazata ?"
Shiru yayi yana cizan lips dinsa na kasa kafin daga bisani yace "bai kamata kiyi min wannan tmbyr ba domin kuwa Kinsan dalilin zuwana "ya fad'a alokacin daya jingina jikinsa da mirrow dinta yayi crossing leg's dinsa ya rungume hannuwansa duka a saman faffadan qirjinsa yayi da idanunshi ke kallon zara zaran yatsun kafafunsa."
da kyar ta mike daga zaunen da take tana cewa "ni ban san abinda ya kawoka ba idan dai ba kazo da niyyar karbar soyayyata bane amman kafin nan me zan kawo maka ?"yayi mata banza zuciyarsa na zafi jin yayi shiru km ta rigada tasan halinsa tayi tunanin ta kawo masa ko ruwa ne har tayi taku biyu taji ya fixgota da karfi yana watsa mata wani kallo da idanunshi dake cike taf da bacin rai gbdy taji ta fara muzanta daga kallon da yake mata taji gwiwarta tayi sanyi ."Idanushi ya tsareta dashi yana kallonta yayinda gabanta ya fara faduwa tana adduar allah yasa ba wani laifi tayi masa ba ."
Sai daya gama kallonta sannan ya watsata akan katifa ta sauka da karfi sai da hantar cikinta ya kada still bai dauke idanunshi akanta ba ,nan take ta soma sheshekan kuka sannan ta fara mgn "yaya idan wani laifi nayi maka ya dace ka fad'a min amman wannan kallon naka na hargitsa min lissafi .kallonta ya cigaba da yi bai ce uffan ba har sai data gama ,cikin izza ya motsa labbansa "nasan kin san abinda kikayi sannan kuma kinsa shine dalilin zuwana " cikin mamaki da tsoro take kallonsa ya tsareta fes da idanunshi yana mata kallon banza ."
ranshi a bace ya daidaita tsayuwarsa yana cigaba da kallonta kallon dake qara kashe mata jiki da tsoratarwa "hakika kin tabbatar min da abinda kika turo min a kwanaki uku da suka gabata na zakiga byn mrym , kinyi yunkurin kasheta Kmr yadda kika kashe mubina dan tace tana sona ko?"Idanuwa ta zaro gabanta na faduwa a fili tace" na shiga uku tana dafe qirjinta tare da nuna kanta "ni din na kashe mubina sannan nayi yunkurin kashe mrym ?wani kallon banza yake mata yana jin Kmr ta raina masa wayo ne babu abinda yafi tsana sama da karya yafi son duk abinda ya tmbyeka ka fad'a masa gsky ta haka zaka samu sausauci daga garesa "ban kashe mubina ba me yasa zan kasheta ?"wallahi ban aikata komai ba sannan banyi yunkurin kashe mrym ba tabbas na tura maka sakon zanga bayanta amman wallahi ban aikata hakan ba ,amman ina da niyya to waye yasan da wannan shiri nawa da har ya rigani aiwatarwa?
"Lafiyayyen mari ya zuba mata yana cewa "ni kike wa wannan tmby ?nan take ta rude ta dafe kuncinta inda marin ya sauka abinda yafi damuna kashe mubina da kikayi me tayi miki nuzla ?kuka ta saka mashi tare da durkushewa kasa "wallahi sharri ake son min dan ban san komai akai ba .wani kallo ya watsa mata sannan ya juya mata baya "nasan tabbas kece kika kashe mubina dan hatta wukar da kika kasheta kinyi kuskuren barinta a yunkurin kashe mrym ."
"Da mrym kika kashe wallahi bazai ta'ba damuna ba saboda neman kai nake daita ,ni da zaki kashe min ita amatsayinki na yartaada kafin ta zama mallakina lallai ni kuma da nayi akawarin aureki .nuzla ta sake rudewa ta gigice ta soma jan gwiwowinta ta qaraso inda yake tana kuka "na baki kwanaki goma masu zuwa ki kashe min mrym kafin ta zama mallakina batare da an samu wata hujjar cewar kece kika aikata hakan ba , sannan kada asirinki ya tono ni kuma zan aureki idan kuma kika gagara kasheta har lokacin dana baki ya cika ni kuma nayi miki alkwarin zan damkaki a hannun hukuma a kwatarwa mubina hakinta kin dai sani idan hukuma ta tabbatar da kece kika kasheta karshenki biyu ne, kisa ta hanyar rataya ko kuma zaman gidan yari na har abada muddin rai kenan yana gama fadar haka ya soma qoqarin ficewa daga dakin .."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.