Maradams Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MARADAMS book 1 BY AYSHA A BAGUDO.txt
Chapter 16 of 18
Page 23
Ji tayi qasusuwan jikinta suna barazanar kasa riketa , lokaci guda zuciyarta na barazanar tarwatsewa bata san sanda ta kurma ihu da iyakacin karfinta tana d'aura hannuwanta duka bisa kanta mahaifiyarta hajiya salema ta shigo d'akin da sauri tana dubanta cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali, zata iya cewa yanayin data ganta ciki bata ta'ba ganinta cikin irin yanayin ba sai yau wanda shine karo na farko da taga wannan yanayin atare daita , yanayi ne mai cike da firgici da tashin hankali."
Rawar da jikin nuzla yake ya qaru hjy salema ta matso kusa daita ta soma girgiza nuzla wacce ta koma tamkar mutun mutumi a wajen "nuzla nuzla!! lafiya what's wrong with you ?!me ke faruwa dake ? me adam yayi miki kike kuka haka ko ince laifin me kikayi masa dan nasan ruwa baya tsami banza tunda naganshi nasan akwai abinda kikayi masa ? ta jera mata tmbyoyin a rud'e tana riko hannunta cikin nata. nuzla tayi shiru tana wani irin kuka mai d'aga hankali "ki min magana mana ko hankalina zai kwanta ? ta mike a matukar firgice tana duban hjy salema sai dai bata iya amsa mata tmbyoyinta ba dan bata da amsar da zata bata a halin da take ciki ,dan haka ta cigaba da kallonta da rinannun idanunta dake cike da ruwan hawaye kafin daga baya ta fara kuka wiwi tana safa da marwa acikin d'akin hajiya salema na biye daita cikin tsananin damuwa ."
" tabbas idan har hasashe da yarda yaya adam akanta ya tabbata a zuciyarsa to fa tabani ta lalace ta shiga ukunta dan wallahi tasan zai iya aikata fiyye da abinda ya fad'a mata .hankalinta ya sake matukar tashi tabbas tayi niyyar aikata hakan amman daga ita sai Allah'n daya halicceta da zuciyarta da kuma yaya adam ne kawai suka sani ,"ba itace tayi kissan ba to waye yayi ?ta furta hkn a qasan ranta tana furta "wayyo allah na shiga uku ni nuzla ta ina zan fara ? waye yake son jifa rayuwata cikin maseefa ? da wani irin sauri ta nufi kofar fita hjy salema ta biyota tana kiran sunanta amman ina bata tsaya ba tunin ta kai kofar fita daga gidan ta biyo bayan ata ."
ya d'an yi nisa amman bai kurewa ganinta ba dan tana hango bayansa daga inda take ta kira sunansa da karfi cikin tsananin tashin hankali , shi kuwa ata yana jinta amman yaki waiwayowa ya cigaba da tafiya kmr baya son taqa qasa ."ta qara sauri sosai kamar zata hantsila , kallo d'aya zaka wa nuzla ka fahimci bata cikin haiyacinta da natsuwarta ."adaidai bakin kofar shiga side din mami ta iske shi tare da shan gabansa gif haka nuzla ta zube qasa bisa gwiwowinta agabansa idanunta na qoqarin sake kawo ruwa cikin wani irin murya mai gauraye da tashin hankali hade da rudani take furta "yaya ka taimakeni ka tsaya ka fahimceni karka yanke wannan hukuncin wallahi ban san komai akan lamarin nan ba."
ya tsura mata tsumammun idanunshi kafin ahankali ya soma magana cikin izza "taya zan iya yarda da hakan bayan kece da bakinki kika furta hakan kuma kika aikata ? "wallahi wallahi !! idan ka yarda da rantsuwata bani bace sam sam ban aikata abinda kake zargina akai ba hasalima ni yau tsawon kwanaki goma sha biyar kenan kafafuwana basu taka haraban gidan nan ba ina kwance bani da lafiya ."yadda take maganar zaka fahimci tana cikin rud'ani da tashin hankali kamo kafafuuwansa tayi cikin kuka tace "please yaya try to understand me bazan ta'ba aikata hakan ba kawai dai na fad'a maka haka ne dan ka tausaya min ka aureni amman ka yarda dani ban san komai akai ba ."
"Bazan ta'ba yarda dake ba domin nasan zaki iya aikata taadanci makamancinsa koma fiyye dashi a halin yanzu ba wannan magiyar bace ta kamaceki ki fara shirin yadda zaki aiwatar da aikin dana baki idan kuma zaki tonawa kanki asiri né tun yanzu bismillah ." jikinta da muryarta na rawa tace "baxan damu ba koda asiri zai tono dan ban aikata komai ba bare naji tsoron fallasa kuma Allah shine sheidata ban aikata ba amman zaka iya bincike akan wanda ya aikata abinda kake zargina akai amman ni bani bace kuma duk inda zaa kaini zan tsaya ne akan gskyta bazan ta'ba karban laifin da bani na aikata ba ."
a natse ya soma daga kafafunsa dan wucewa ya barta dan ya gaji da jin sautin muryarta da kukanta yana shiga kanshi over ,yaga tana qoqarin jan gwiwowinta domin biyosa ya kalli securities din dake tsaye a wajen "karku sake ku barta ta shigo ciki "okay yallabai an gama ya shege ciki ya barta durkushe tana kallonsa tmkr wani sabuwar halittta a wajenta ."mikewa tayi tare da cure hannayenta waje daya tana bugawa da juna bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin ta yau ba har ga allah bata san haka abun zai rikice ya dawo kanta ba ta dauka idan ta fad'a masa haka zataci bulus ne ashe masefa zai zame mata ashe bazataci bulus ba wahala zata sha ?"me yasa batayi shiru da bakinta ba ?me yasa ta gaza hakuri har sai data fito ta fad'a masa shirinta gashi ta kai kanta ta baro ? kaicona ni nuzla bakina ya janyo min matsefa na tarowa kaina bala'i da kaina ta sauke ajiyar zuciya tare da furzar da zazzafar iska daga bakinta ."
"Ai kam wallahi sai dai yayi mata duk abinda zai mata idan ta kama ma ya mikata ga hukuma amman bazata ta'ba aikata abinda yake bukata ba sannan bazata ta'ba karban laifinta ba sai dai idan kasheta zaayi akasheta ta yarda amman bazata cika masa burinsa ba, shi idan har da gaske yake baya qaunar maryam din ya aikata lahira da kashi ba sai ya had'a daita ba da sauri ta juya ta soma tafiya kamar zata tuntsura kasa sai kace mahaukaciya ta shigo gidansu inda ta iske mahaifiyar tsaye cikin zullumi ."
Tana ganinta ta qaraso gareta tana tmbyrta nuzla ta zauna akan kujera jagwaba tana fidda numfashi duk tmbyr da mahaifiyarta take mata bata kulata ba illa hawaye dake zubar mata "wani laifi kikayi wa adam ?tayi shiru kawai batare da tace uffan ba hjy salema tace "to da alamun laifin mai girma kikayi masa yasa har ya biyoki "kamar ta bayyanawa mahaifiyarta halin da take ciki kafin ya damkata hannun hukuma a kashe mata ita a banza a wofi amman ta kasa dan gaskiya bazata iya ba domin tasan irin qaunar dake tsakaninsu kasancewarta auta a wajenta ,banda kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take furtawa tare da dafe kanta dake mata wani irin sara Kmr zai rabe gida biyu hjy salema ta barta ta koma dakinta dan ta fahimci laifi tayi masa mai girma wanda yasa ta kasa furta wa ."
Nuzla ta rufe idanunta gam tana jin yadda maganarsa ke tashi acikin kunnuwanta da zuciyarta so take ta sakawa gangar jikinta hakuri da jarumta har zuwa waadin daya dibar mata ya cika amman ta kasa bata jin zata iya, a halin yanzu ma ba mgnr aurensa bace a gabanta illa mafuta lallai tana bukatar mafuta ta mike tsaye tana zariya acikin parlour'n "ko na gudu ne na bar gidan ne ?ta tmbyi kanta ,gudunki bashine mafuta ba nuzla hakan ma qara min laifi zai yi idan kuma maganar ta fito shikenan kin tabbata mai laifi a wajen kowa dakinta ta shiga tayi zaman dirshan tana saqa da warwara ni dai wallahi nasan bani na kashe mubina ba haka zalika banyi yunkurin kashe mrym ba ,"shin ta ina zan fara ?ni kaina ina bukatar gano wanda yayi hakan , ta lumshe idanunta tana tunani dan dole tayi bincike dan gani wacce tayi yunkurin kashe mrym kuma ko wacece acikin estate dinsu take km itama tana son adam ne Kmr yadda take son shi jikinta ya dauki zafi sosai ."
Zaune mr ata yake akan kujera kushin dake d'akinsa yayi zurfi cikin duniyar tunani yayinda hankalinsa gabadaya ke sake tashi a duk sanda ya tuna da maganar aurensa da mrym sai ya dinga jin hankalinsa na sake tashi , yayinda a kullum ya daura kwayar idanunshi akan yarinyar sai ya dinga jin tsananin tsanarta ,shi da kansa ya kasa sanin takamaimain dalilin dayasa yake jin tsananin tsanarta haka dan bazai ce dan rashin tsawonta bane da kuma kasancewar ta fara bane ya janyo haka yanayinta dai ya taimaka wajen tsanarta ne ,duk yadda yake qoqarin yakice tsanarta da sanyata ko kadan acikin ransa zuciyarsa taki amince da zamanta a tsakaninsa tafe tafe har tunaninsa ya kawo kan zanen wukar dake ajiye akan bedside dinsa wanda aka kashe mubina daita kuma ake qoqarin kashe mrym dashi shine ya zana ya ajiye a wajensa kafin a mika wukar ga hukuma ."
ahankali ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ya sake gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune tunanin duniya yayi akan wacce tayi karfin halin shigo masa gida da taadanci , baya da tabbacin ko nuzla ce domin kuwa har ya gama kallon mai shi ta camerar d'akinsa bai iya gane ko wacece ba zargin nuzla kawai yake bisa yanayin jikin wacce ta shigo da kuma furucin bakinta amman bashi da tabbas akanta bincike ne kawai zai tabbatar masa daita ce ko kuwa wata ce dabam ta kashe mubina km tayi yunkurin kashe mrym "idan wata ce dabam meye dalilinta ?meye hujjarta ? me yasa take yunkurin aikata hakan ?iya tunaninsa yanzu ya fara gane wasu abubuwa akan me kisan wala akanshi ake yi kisan kmr yadda kwakwaluwarsa take haska masa wala kuma wani laifin suka aikata mata take masu dauki dayday ,cikin sanyi jikin nan nasa tamkar mara laka ya matso ya kunna CCTV camera .
idanunsa kawai ya zubawa camerar yana kallon wacce ta shigo masa gida cikin bakaken kaya wondo da riga gabadaya babu inda ta bari wanda zai kafa hujja akanta amman dai tabbas yanayinta ya nuna macece "to wacece wannan yarinyar ?tunaninsa ma yadda ta iya shigowa securities din bakin kofar shigowa basu ganta ba ? ko da yake ta yuwu wani abun tayi masu amfani dashi domin gusar da hankalinsu dan kuwa duk tashin hankali daaka shiga bacci suke basa ma cikin haiyacinsu har sai da aka taimaka masu ,tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin mai kaifin baseera irin na yarinyar ba Sannan tunda yake bai taba samun kansa cikin damuwa irin na lokacin ba ,sam sam ya qasa kwanciya yayi bacci sai wurin karfe biyu saura bacci barawo yayi awon gaba dashi ."
bangaren nuzla ma yadda taga safiya haka taga dare ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta kafin gari ya waye ta sake yin wata doguwar rama jikinta ya dauki zafi kamar garwashin wuta dan haka dole da gari ya waye aka kira doctor ya dubata nan ya tabbatar masu da damuwa ce dan har jininta ya hau ya wuce kaida yayi ja hankalinta akan yawon tunani sannan ya daura mata drip ya kama gabansa hjy salema ta tsura mata ido kawai tana kallon yadda numfashinta ke fita da kyar ta riko hannunta cikin nata zafin jikinta ya ziyarci tafin hannun hjy salema bata son ganinta cikin damuwa da tashin hankali duk sai taji itama ta shiga damuwa yanzu da tana da dama data cire mata ciwon ta dawo dashi kanta "nuzla !."ta kira sunanta ta bude idanunta dake lumshe ta zubawa mahaifiyarta "meke damunki ko akan hisham ne ?ta gyada mata kai kawai alamun "eh! .
"Halan akan maganar adamu yazo jiya ?ta sake gyada mata kai kawai dan bazata iya magana hjy salema ta numfasa kana ta cigaba da magana "me yasa zaki saka maganar aranki har haka ?tunani shine abu na farko dake fara nukurkusa rayuwar dan adam ,kiyi hakuri ki fallawa allah komai shi keyi a lokacin da yaso haka shi Ke hanawa alokacin daya so fatana Ki barwa allah lamarinki Kiyi addua abinda yafi zama alkhairi atsakaninki dashi Allah ya tabbatar mana, amman ina kyautata zaton zaki ji dadi agidansa zaki samu kwanciyar hankali a hannunsa domin hisham yaron kirki ne amman dai mu cigaba da addua mu barwa allah komai nuzla ta runtse idanunta kawai tana ji da abinda ya dameta ."
tun safe mami da mrym har ma da nana hauwa'u suka shiga kitchen suna had'awa ata breakfast suna hira ,mami ta fito tana amsa wayar hajiya nuriyya wanda adaidai lokacin ata ya sauko hannunwansa duka acikin aljihun wondonsa, sanye da riga brown colour mai hannun long sleeve da dogon wando baki "eh ke dai nuriyya abinda ya faru kenan wallahi acikin estate din nan ne amman yanzu tunda ya dawo in sha allahu bazai wuce a saka sati uku zuwa hudu ba ba ,eh babu damuwa tunda open ticket zakuyi nan ata ya wuce yayi nufi hanyar dakin jim dinsa domin motsa jiki ."
Har yayi taku biyu ya soma jiyo sautin magana kasa kasa kuma abinda yaja hankalinsa shine sunansa da yaji an kira ,ya dan dawo baya kad'an ya tsaya ya kasa kunne yana jin tautaunawarsu "matar yaya adamcy ikon allah miko min kayan ingredient din can na zuba ko ke kadai zaki hadawa mijinki breakfast na cire hannuna na kama gabana?"kai sister kina son kasheni da raina ."
"dan nace matar yaya adamcy ikon allah shine zan kasheki da ranki ?mrym ta gyada mata kai alamun Eh ! ai in sha allahu sai anyi wannan auren ko ana so ko baa so kuma muna bayan ki kamar doro ki zuba mulkinki son ranki a gidansa dan kinci dubu sai ceto babu abinda zai faru "Allah yasa sister dan irin mijin da nake so kenan .
"gashi kuwa kin samu kin yiwa sauran mata zarra ,na yiwa sauran mata zarra ko na fisu shiga matsala ?kina ganin dadi zanji a gidansa ni tun yanzu na fara tunanin yadda tunani da damuwa zai haukatani a gidansa ga rashin sonshi da bana yi ga matsalar taurin kai da wanne zan ji ? ." kina bani mamaki wani lokacin kamar ba mace ba ai ina gaya miki tsab zai sauke komai mrym ta girgiza mata kai kawai tana cewa "taimaka ki zuba min maggie dai dan ni ban san dalili ba duk yadda zan saka maggie a miyya sai yayi yawa ."
"gsky matsalarki kenan sister mman da sannu zaki qara samun gogewa agidan yayana ,wannan yaya dai ana sona dashi shi kuma baya sona,ana son na shiga gidansa shi kuma yace aa wanne zaayi aciki ? "Ke manta dashi wuyarta ayi auren ,ko da yaushe sister haka kike fad'a min wani lokacin sai naji na amince da samu natsuwa ,wani lokacin kuma sai naji hankalina yayi kololuwar tashi ni kaina zan so na ganni a matsayin matarsa dan nasan da sannu zan iya son shi da yana son kenan matsalata a halin yanzu rashin són da ....."
saurin datse harshenta tayi da karfi sakamakon ganin mutun tsaye ta bayan nana hauwa'u daman ta juya da niyyar fuskantar nana hauwa'u ne shirunta yasa nana hauwa'u tace "lafiya sister kikayi shiru ? bata iya bata amsa ba illa numfashi data dauke da karfi tana cigaba da kallon bayanta ."
ya tako a natse ya shiga cikin kitchen din sosai kamshin daddan turare da takun da nana hauwa'u taji yasa ta dan juyo ,ta dan tsorata da ganinsa nan take gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa amman sai ta dake ta bude baki da sauri tana cewa "san ..sannu ya.. "saurin d'aga mata hannu yayi yana qara had'e fuska , nana hauwa'u tayi taku biyu zata bi gefensa ta wuce domin ta tsira da lafiyarta taji yace "munafukar allah Koma ki tsaya wato kina d'aya daga cikin masu bawa wannan guntuwar mummunar yarinyar kwarin gwiwar aurena ? tayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "zan kifa miki mari yanzu idan kika sake girgiza min kai koni saanki ne ? ta sake girgiza masa kai cikin tsananin tsoro ."
"Kika ce da zarar anyi aure shikenan?idanuwanta sukayo waje wani gumi ya soma tsatsafo mata akan hanci ,sannan kika ce ta manta dani wuyarta ayi auren ni zaa manta dani ?yayi maganar a matukar tsawace cikin bacin rai ,dan allah yaya kayi hakuri nifa ba wani abu nake nufi da hakan ba ina qoqarin gyara au...."ai wani mugun kallo da yayi mata batasan sanda tayi shiru ta qara shiga hankalinta ba ,kinga nayi miki kamata da irin mazan da zarar anyi aure shikenan ?ko kinga nayi miki kama da bawan mace ?ta girgiza masa kai alamun a'a ki shiga hankalinki wallahi idan ba haka nayi sadaka dake na bawa duk wanda naga dama aurenki mu huta sha sha banza da wani katon bakinki a wajen ."
ita kam mrym hannuwanta duka tasa ta rufe fuskarta sakamakon hawayen daya cika mata ido idan akwai abinda ta tsana a kalamansa gareta bai wuce munzantata ta hanyar zagin halittar da Allah yayi mata "Ke kuma na dawo kanki nan da wasu kwanaki zaki zama mata agareni ban isa na hana hakan faruwa ba amman kamar yadda kika furta tunani da damuwa ne zai haukataki a gidana tabbas haka ne domin bakinciki da damuwa zaki aura bani adam ba ,daman tunda kika shiga rayuwata kema kinsan bazakiyi farinciki arayuwarki ba, har karshen rayuwarki a wahala zaki qare a gidana gara ma kije kiyi kuka da Kururuwan a fasa auren nan shine kawai mafuta agareki da kwanciyar hankalinki nonsense kawai da bata san me take yi ba ,yanzu ke kina ganin kin dace dani ?common maggie baki iya sakawa acikin abinci ba sai an taimaka an saka miki stupid girl kawai wallahi gara ki taimaki kanki tun wuri yana gama fadar hk ya juya ya fita daga kitchen din yana jan tsaki ."
kuka mrym ta qarasa fashewa dashi ta koma bayan kofar kitchen ta hade kanta da bango tana jin wani irin zafi mai radadi duk da yadda take jin rashin sonshi amman haka ta bawa zuciyarta hakuri ta karbi aurensa amman shi burinsa yaci mutuncinta ya tozarta tasan yadda ya fad'a haka ne zai kasance rayuwar bakinci zatayi a gidansa zai hanata kwanciyar hankali da walwala ,zai hanata sukuni da jin dadi cike da jin haushi nana hauwa'u tace meye kuma abun kuka ? kina jin tsoron yaya fiyye da kaida ,"shiyasa naga kin iya mutsa masa alokacin da yake magana yake ci min mutunci , ko kin iya taka masa burki alokacin da yake cin zarafina ?tayi mgnr cikin bancin rai tana mai juyowa gbdy ta fuskance nana hauwa'u hawaye na zuba akan kuncinta."
"Sarai kijin abinda ya fad'a yanzu ,kuma Kinsan zai iya aikata fiyye da abinda ya fad'a ,shikenan nan ni haka rayuwata zata qare , kisa hannu sister ki saurari zuciyata kullum cikin bugawa take da karfi kin kuwa san abinda nake ji ?"gano yanayin tsoronki yasa yake miki haka wallahi ni ace nice zai aura bazan dauki abubuwansa ba ,"ki daina zugani sister yana fad'a min duk maganar daya ga dama, yana tozartani a duk sanda yaso , lallai ya kamata nayi kuka nayi kururuwan ataimakeni a kawo min dauki fasa auren ."nan tana gama fadar haka ta fice fuuuuuuu ta bar kitchen din ."
kai tsaye dakinsu ta shige ta fad'a saman gado ta kwanta ruf da ciki sai nana hauwa'u ce ta qarasa hada masa breakfast."wuni ranar babu abinda mrym take sai cika take tana batsewa tana jan tsaki tana tunanin mafutar da zatasa a fasa auren ta huta
abinda mami ta kasa ganewa bayan rashin son da yaya adam baya mata har da kasancewarta farar mace sol mara tsawo ne dan tasan yadda bai son farar mace yafi son chocolate colour yar doguwa mara kiba baa siyar da tsawo data siya ,baa siyan baki da ta koma baka Kmr yadda yake só tunda baya sonta kuma babu duk abinda yake bukata daga macen da zai so tô meye amfanin auren ?gara itama ta kawowa kanta mafuta tana kwance ta zabura ta mike tsaye ta fito ta nufi dakin mami lokacin karfe biyar daidai na yammaci"
Mami na zaune a dakinta abakin gado kunneta manne da waya maryam ta shigo duk jikinta a sanyaye kallo daya mami tayi mata ta fahimci akwai damuwa dan haka ta katse wayar da take ta hanyar cewa "khadija zan kiraki zuwa anjima sannan ta ajiye wayar a gefenta tace "lafiya maryam naga kin shigo wani iri? duk da wuni yau na lura bakya cikin walwala , hawaye mrym ta share tace "gsky mami na gaji da abinda ya adam yake min ,ina ganin lokaci yayi da komai zai zo karshe ,numfashi mami ta sauke cikin tsigar rarrashi "haba maryam haba diyata ki daina fad'ar haka ,kece fa karfin gwiwana idan baki auresa ba nasan hk zai qare rayuwarsa bai yi ba kiyi hakuri wata rana sai labari ."
"Amman mami ni haka zan qare rayuwata yaya baya fahimtar nima biyayya kawai zanyi ?nasani mrym amman ina ji ajikina wata rana Adamcy zai sauya zai zo har gabanki neman afuwan abubuwan da yake miki ido mrym ta zaro waje tace "mami ko kin manta halinsa ne ?"ban manta ba maryam amman na yarda da allah kuma Kinsan lamarin ubangiji ya wuce nan karkiyi mamaki wata rana ya zamo bawa agareki barin ma idan kin haihu dashi kuma gani a tsakanimu muddin ina raye bazaki shiga uku a gidansa ba ,ajiyar zuciya maryam ta sauke haka ne mami lamarin ubangiji ya wuce nan nima ikonsa ne yasa har zan zama mata agaresa ."
"Haka mami ta zauna ta dinga tausar maryam tana bata baki har mrym ta saki ranta ta manta da batun wulakanci ata ta cigaba da harkokin gabanta ranta fari kwal washegari aka tsaida ranar dazaa daura auren ata da mrym hisham da nuzla nan da sati hud'u masu zuwa kamar yadda mami ta tsara shima dan alfarma cousing sister dinta nuriyya ne domin tana son yaranta suyi hutu tazo dasu gbdy bugu da qari lokacin zai yi daidai da hutun karshen shekara wanda daman kusan lokacin da yan'uwanta dake kasashen duniya ke zuwa hutu kenan bancin hk ai da kwanaki goma kawai zata saka ayi a wuce wajen shi kam mr ata kam ko ajikinsa dan babu ruwansa da ko sati nawa zaa saka idan ma an ga dama a daura a ranar ba damuwarsa bace ."
A hankali yake saukowa daga saman mattakala jikinsa sanye da complete black suit yayinda kafafunsa ke sanye da brown shoe's agogon rolex ke daure da tsintsiyar hannunsa ,idanunshi na manne da wani hadadden farin glass ,a hankali ya cigaba da takowa cikin isa da izza alamun shi din wani ne a fadin nigeria ,yana saukowa sanyayyen kamshin turarensa REED ya soma tashi ta koina kamshin turarensa ne ya kaiwa hancin maryam ziyara da sauran jamma'a wurin sakon fitowarsa .
Maryam ta dago idanunta a natse ta tsura masa tana kallonsa tun daga sama há qasa tamkar ranar ta soma ganinsa arayuwarta ji tayi gabanta na wani irin mugun bugawa da karfin gaske, hakan nan yau ta tsinci kanta da kasa dauke kwayar idanunta akansa
sister dake zaune a gefenta ta bita da kallo tsab domin dai ta fara fahimtar wani abu akan maryam a din a game da yayanta a tun dawowarsa daga kasar france duk da ita taki yarda da zarginta tana nuna mata alamun bata son danuwanta amman kuma ita kar take kallonta domin kuwa akwai dinbin son shi makale a ranta da kwayar idanunta wanda itama bata san tana yi ba . "
"taya zaka samu miji kmrshi kace wai baka so ai sai dai idan abun yafi karfinka nmj da mata suke nema har suke rububi akansa itam saa taci da kuma darajan mahaifiya if not har abada sai dai ta tsaya akansu abbas da anas shi kuwa kallo ne daga nesa dan fin karfi kam yafi karfin aurenta ."daga inda yake yana iya jiyo sautin muryoyin mutanen dake zaune a bangaren dining area, a natse ya tsaya idanunshi karrrr akan sister dinsa da maryam wacce ta zama tamkar doluwa a wurin rike da cup din tea a hannunta tana kallonsa abinda yafi tsana kenan kallon kurulla daga mace ,kallo daya yayi masu ya dauke kwayar idanunshi akansu yana busar da iska daga bakinsa tare da furta "nonsense "! a fili wanda hakan daya furta yasa maryam tayi saurin dawowa haiyacinta tana sauke naunayen ajiyar zuciya sai dai ta qasa dauke idanunta akanshi ta cigaba da kallonsa"
bai tsaya akoina ba kai tsaye dinning área ya nufa yana shan kamshi , har ya samu wuri ya tsaya tare da soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa ,Still maryam bata dauke kwayar idanunta akanshi ba ,sister ta zungureta da sauri "ke ki dawo hankalinki mana wannan kallon da kike masa kin dai san halinsa , idan yaga dama sai ya sakaki kinyi bayanin wannan kallon dalla dalla ."numfashi maryam ta sake saukewa da karfi tana waskewa ta shafa gefen fuskarta tace "wani irin kallo kikaga nayi masa "? ni gbdy ma hankalina baya cikin gidan nan ."
"yana ina shi hankalin naki ?nana hauwa'u ta tmbyeta tana tsareta da idanunta ,domin dai ita tasan gskyr abinda ta gani kenan kallon yayanta take amman tana kokarin waske mata "ki yarda sister da gaske shi kika ga ina kallo ?maryam ta tmbyeta tana qara shafa gefen fuskarta nana hauwa'u ta gyada mata kai alamun "eh!"zai iya kasancewa haka idanuna na kansa amman kuma hankalina ba akansa yake ba, mai ma zan tsaya kallo ajikin mutumin da ba mutunci garesa ba ?"tayi mgnr a hankali."
"me kika ce sister naji kamar kinyi mgn ?"no no bance komai ba ,kinga sister dauko wayarki ki daukar mana abincin nan kar na manta ban daura breakfast din dana ci a social media ba ,ta fadi haka ne saboda ta shashantar da zargin sister akanta "okay ni nayi laifi kenan ?tô wallahi bada ni ba ,
matsawar bai bar parlour'n nan ba babu hoton wani abinci da zan dauka, idan kin matsu ki dauka da kanki wayarki ce bazan hanaki ba ta janyo wayarta dake ajiye ta mika mata ta tashi ta bar gurin gabadaya karta jaza mata balai da sassafe."
A hankali maryam ta shiga daukar abinci gefe guda kuma tana faman satar kallonsa ta kasan idanunta, ba qaramin kyau yayi mata ba cikin shigar suit ,da alamu ma barin garin zai yi ko kasar gbdy karaf kamar ance ya waigo idanunsu ya tsarke cikin juna da mugun sauri ta dauke idanunta zuwa wani gefe tana sauke numfashi sama sama dogon tsaki yaja tare da furta stupid girl sannan ya samu wuri ya zauna batare da ya kalli inda sauran mutanen da suke zaune akan kujerun dake zagaye da dining table ba hakan kuma ya faru ne sakamakon zattukansu dake shiga kunnuwansa suna yi masa kuwa ."
kallo daya mami tayi masa ta dauke kanta tare da girgiza kai sannan ta tura masa plet din abinci gabansa tare da black coffe wanda ya zame masa jiki a hankali ya dauki cup ya kai bakinsa ya kurbi tea kadan yana lumshe tsumammun idanunshi yana dan motsa kafarsa daya akan tayis magana baba qarami ya cigaba da yi cikin zafin rai sai dai "on expecting suka ji sautin muryar ATA yana cewa "babu abinda zaa bawa kowa sai abinda naga dama shima a siffar albashi ko kyauta zan bayar kamar yadda na saba .""yayi mgnr tmkr ba daga bakinsa ta fito ba hankali kwance ya cigaba da kurban tea yana lumshe ido ."
"mai kake qokarin kace adam ?kana nufin mu babu komai namu acikin dukiyar ko me ? yes of course uncle domin babu shi acikin kundin da dad yake rubuce rubucensa aciki , amman mai yasa tun tuni baka taso da wannan maganar ba sai yanzu ?yanzu né naga ya dace nayi magana tunda naga ita wannan uwartaka batasan abun arziki ba, idan kowa yaja bakinsa yayi shiru saboda jin tsoronta da gudun magana toni bana jin tsoronta kuma bana gudun magana ,zanyi mgn km dole a kasafta abani rabona bazai yuwa kayi mana karfa karfa akan gumin da mahaifinmu yayi wahala ya tara tsawon shekaru ba ."
"babu abinda zan bayar..., ."ya sake maimata mgnr daya fada yana sakin spoon din hannunsa hakan yasa hankalinsu yayi matukar tashi gab gab !! baba qarami yaji gabansa na wani irin faduwa gbdy parlour'n ya dauki shiru tmkr babu wasu hálittu a wurin "koda ma akwai dukiyar babu abinda zan cire na bawa kowa tunda babu shi a rubuce idan kuma kayi trying wani non..."shiiiii mami ta furta tana daura dan yatsanta akan lip's dinsa dan dakatar dashi domin tasan halin kayanta karshe kalmar nonsense ne zata fito daga bakinsa "wai meye haka kake yi adamcy ? baba qaramin sa'anka ne"?
"Karka manta kanin mahaifi ne me yasa ma sai anan zaa yi discution din wannan matsalar dan kawai a daga min hankali ? ta juya inda baba qarami ke zaune "karki fada min hk sannan abu na gaba ki fada wa d'anki yayi bincike mai kyau akan abinda na fada tabbas akwai dukiyarmu acikin dukiyar ubansa wanda byn mutuwar mahaifinmu muka barshi a hannunsa idan kuma ba hk ba komai zai iya faruwa idan wani abu ya faru ki kuka da kanki karki yi kuka da kowa." yana gama fadar haka ya mike cikin tsananin fushi yaransa maza biyu salim da sultan suka mike suna hararar ata kafin daga baya suka marawa mahaifinsu baya .
Hajiya zualai ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali tana binsu da kallo gabanta na faduwa tasan yana son kunno da damuwa ne sbd rashin amincewar auren adamcy da hindu da kuma makudan kudaden da yayansa sukai qoqarin hadamewa adamcy ya hana ,ATA ya kai hannunsa ya riko tsintsiyar hannunta "sweetheart ki zauna "ta zauna cike da sanyin jiki tana duban kyakkyawan tilon dan nata nmj kwaya daya da allah ta mallaka mata "karki damu sweetheart da mgnrsa everything will be fine tunda ni bani da wani business dashi so karki saka wani abu aranki ,ban san meye damuwarsa ba ."?
" ban san me yasa yakewa kudi mugun só haka ba ."? duk ribar dake shigowa ta AGC ina iyakar kokarina ana cirewa kowa hakinsa na bashi kuma sweetheart a qokarina na kar company ya ruguje kullum hannun jari nake qarawa batare dasanin kowa ba kuma su waye ke kokarin karya company ? yaransa né kullum cikin sata suke sannna yanzu yazo da wani batu this time around sweetheart sai dai ki yi hakuri I can take it dan bazan dauka ba wallahi baba qarami na mugun son kudi duk ma yafi sauran karbar kudi a kamfani amman yanzu yazo yace ga zance ga magana agc ne dai yanzu na soma zuwa kula dashi bazan yanke zuwa ba bare su samu damar yin babakeri da dukiyarmu ."
" adamcy ni nasan baba qarami ba kudin yakewa ba, tunda bai taba mgnr wasu kudade ba sai yau na dai lura tunda aka fito da batun mgnr auren da maryam ya canza , amman nasan ba komai yake damunsa ba so yake ka auri diyarsa hindu ."shiru adam yayi yana sauroronta yana tsakurar abincin gabansa batare da ya furta komai ba dan babu ruwansa da mgnr "ko zaka taimaka adam ka had'asu duka biyu ka auresu"?
"What ?"
ya furta da mugun karfi yana sakin spoon din hannunsa "mami ta lumshe masa ido "kayi tunani akai kaji adamcy nah "am done am leaving kiyi min addua fatan alkhairi ya fada yana mikewa da d'an hanzarin ya soma tafiya cike da kuzari hannunsa daya cikin aljihun wondonsa." tabi bayansa da kallo tana kiran sunansa cikin tsananin tashin hankalin "adamcy !adamcy !!! Ka tsaya kaji me zance adamcy ."amman ina bai juyo ba bare ya tsaya yaji mai zatace,itama tasan adaidai wannan yanayin da yake ciki bazai tsaya ya saurareta ba domin maganarta ce tasa zuciyarsa ta yunkuro har ya kasa sauraranta shiru tai tana dafe goshinta cike da takaici da kuma mamakin halin biladam ."mutane sam sam babu tsoron allah aransu "shekara da shekaru baka tashi dauko maseefa ba sai yanzu dakaga yaro zai yi aure kazo da wata magana ."
Tana cikin wannan halin maryam ta qaraso hannunta rike da glass cup da magani ta mika mata "ki cire damuwa aranki mami ki sha magani lokacin shan maganinki yayi mami ta dago kanta ta kalli mrym yana daya daga cikin abinda yasa ta kwadai tawa danta aurenta domin zai samu natsuwa daita muddin tana raye sai ta zama uwar gidansa km uwar yayansa ".na gode maryam da kulawar da kike bani "haba mami kullum sai kinyi min godiya karki manta ni din fa dolenki ce haka kema dolena ce duk abinda nayi miki tmkr nayiwa mahaifiyata ce "haka né maryam amman duk da hk na gode sosai allah yayi albarka kinci abincinki ko kuwa kin tsaya tallatawa duniya "?mrym taà murmushi tace "kai mami naci !"kina ji ko mrym kiyi kokari ki rage son social media din nan idan ba hk ba bazuku shirya da adamcy ba kasancewar shi mutun ne da yake da raayi dan allah ki daina kmr yadda na sha fada miki "in sha allahu mami zan rage tare suka baro parlour'n ."
******
Karfe 11:00 daidai na safiyar laraba nuzla zaune a parlour'nsu ita kad'ai cikin tunani da zullumin abu biyu aurenta da hisham da kuma aikin da ata ya bata wanda ita sam bata jin zata iya aikatawa ita da kyankyaso ma tsoronsa take ji bare akai ga kissan mutun ai tasan duk runtse duk wuya bazata iya ba kullum tana gida bata fita koina duk da tana buqatar fita yin shopping din abubuwan buqatanta amman haka ta hakura ,tun kwanaki uku da suka wuce waadin da ata ya bata suka cika amman shiru babu wani sammacin daga yansanda haka zalika babu wanda yazo mata da magana makamanciyar zarginsa akanta dan haka ta dan samu natsuwar zuciya ta mike tsam ta shiga dakinta ta shirya cikin kananan kaya ta daura abaya a saman kayan tayi roling kanta da mayafin abaya ta dauki turare ta feshe jikinta ta dauki handbag dinta ta rataya ta fito ta shiga dakin hjy salema tana zaune tana lazimi akan dadduma dan ta idar da sallar wallaha kenan ."
"momy zan dan je shooprit na dawo murmushi jin dadi ta sakar mata dan yaushe rabon ta fita kullum tana kunshe a daki cikin damuwa "sai kin dawo nuzla allah ya tsareki ta bata amsa da haka cikin halin farinciki "akwai kudi a hannkin ne ?ta waiwayo tana dubanta "akwai kudin da yaya Ibrahim ya tura min cikin account dina dasu zanyi amfani to shikenan sai kin dawo ta juya ta fita daga dakin tana kiran bolt dan bata jin yin driving ."
a hankali take taka qasa har ta fito bakin get din estate dinsu fuskarta a daure kana ganinta zaka fahimci tana cikin damuwa kadan tayi tafiya tana kiran mai bolt taji a inda yake kawai taga motar yansanda a gabanta nan take taji gabanta yayi wani mummunar bugawa da matsanancin karfin gaske ta sauke wayar kunneta batare data kashe ba ta tabi gefe zata wuce cikin tashin hankali tana adduar allah yasa ba wajenta suka zo ba amman ga mamakinta mutun biyar suka fito suka sha gabanta suka tsaya ta kallesu daya byn daya cikin tashin hankali kafin ta kai ga bude bakinta duk suka fito mata da ID card dinsu daga gaban aljihu suka nuna mata daya daga cikinsu yana cewa "sunana inspector Almustapha hasan umar da fatan kece nuzla ?
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
  MAR'ADAMS
  💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
    Page 24
Qoqarin cire tsoro da fargaban dake tattare da jikinta tayi ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Eh yes nice nuzla fatan dai lafiya kuka tsayar dani ? "Ki adana tambayarki tukunna muna gayatarki zuwa office dinmu yanzu ."akan wani dalili kenan kuke gayyatata ? idan munje zaki ji komai ,kamar tayi musu taurin kai amman sai taga d'aya daga cikin 'yansanda na qoqarin fito da handcuff daga cikin aljihu yana cewa "zaki wuce muje ta girma da arziki ko kuma sai mu saka miki handcuff mu wuce dake ta karfin tsiya ."
ba tayi mutsu ba dan ta rigada tasan da komai dan tun tuni take jiraye dasu saboda dama tasan hakan na zuwa saboda tun rabuwarsu da yaya adam tasan ya zuba tsaro sosai akanta ta yadda duk wani motsinta arayuwarta yana sane dashi ,haka ma yansanda, dan tayi imani anan din ya bada umarnin aka mata dan da suna son kamata cikin tonon silili da har ciki zasu biyota ,ba tayi ma tunanin zata wuce lokacin daya bata batare da ta shiga hannun hukuma ba." sosai zuciyarta ta shiga rudani taji wani gagarumin bakinciki ya rufe mata kahon zuciya kuma tayi imani matukar tayi gardama dasu haka zasu da'ba mata handcuff su wuce daita , ta ma godewa Allah da ba har cikin estate dinsu suka shigo suka tafi daita ba ai da kuwa ta shiga ukunta ."
Ahankali ta soma daga kafafunta domin isa inda motarsu take jikinta na karkarwa a duniyarta idan akwai abinda ke firgitata shine hukuma tana tsanani tsoron shiga hannun yansanda, duk da tasan ba wani laifi tayi ba ,dan abinda har yasa suka gayyace din akanshi bata aikata ba ."tafiya take tana tunani da mamakin wanda ya aiko su "me ta yiwa yaya adam da zafi har haka daya kasa yafe mata ? shin laifi ne dan tace tana son shi?dan dai tasan hukuncin zafin furta masa kalmar só ne ya janyo mata wannan tashin hankali, tayi masa runtsuwa da Allah bata aikata abinda yake zarginta akanshi ba amman ya kasa yarda daita "shin tayi masa kama da wacce zata iya kisan kai ko yunkurin kisa ne ? zuciyarta ta dinga mata zafi tana mai sake tabbatarwa kanta lallai yaya adam baya sonta, bayan soyayya ta aure har da soyayya ta yanuwantaka ma baya mata gashi ita duk duniya babu wanda take so sai shi ."
"anya bazata rushe wannan wahallalliyar soyayyar ba ta dawo qiyayya da tsana mai tsanani ba "? ji tayi jikinta yayi sanyi matuqa dan bata jin zata iya wannan aika aikan ,jikin nuzla a sanyaye yansanda suka sakata a bayan mota tare da wasu jami'an tsaro mutun biyu inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon bakincikin sakata a tsakiyarsu da sukayi tun anan idanuwanta suka canza kala tana kallon tafkeken get din estate dinsu aka wuce daita ,tafiya kadan sukayi suka iso police station."direban motar yayi parking ya kashe motar sannan suka firfito suka shiga ciki suka karbi duka kayanta sannan aka bude wani daki wanda babu kowa aciki suka sakata ciki suka maida kofar suka rufe kukan bakinciki ne ya kufce mata ,ta soma rera kuka tana jin wani irin zafi acikin ranta saboda ta duba hagu da dama babu inda zata zauna duk inda ta kalla qazanta ne da zarnin fitsari uwa uba duhu ."
Aqalla ta kusan awa biyu tsaye tana jiran azo a fara tuhumarta domin a tunaninta da sunzo zasu fara jeho mata tamabayoyi tana basu amsa idan sun gano bata da laifi su saketa ta kama gabanta batare da sanin kowa ba sai taga sun shareta sun ma shiga wata tsabgar dabam har wata awa daya tazo ta wuce basuyi lokacinta ba ,wanda zuwa wannnan lokacin kafafunwanta sun fara sandarewa da tsayuwa ahankali tayi qasa ta tsuguna a cimintig dakin tana hawaye yayinda bakinta ya soma furta adduar neman dauki ."
Shi kuwa ATA lokacin da sakon samun nasarar kamata ya isar masa yana zaune a parlour'n mami tare daita dan bai jima da shigowa ba lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa labbansa da kyar "ina fatan babu wanda yaga lokacin da kuka wuce daita ?okay sai nazo ya fad'a tare da jan boyayyan numfashi ya sauke ,okay zaku iya fara aikinku kafin na shigo amman karku ta'ba lafiyar jikinta ,sun dauki Kmr minti goma suna magana yana gama waya ya ajiye wayar a gefensa yana jijjiga kafarsa daya mami wacce kwayar idanunta Ke kanshi a tun sanda ya fara wayar yace ."
"Yaakayi adamcy nah naga kayi wani iri ko akwai damuwa ne ?cikin kwantar da murya yace "no sweetheart yunwa nake ji ,bari nasa aka ..."haba sweetheart karki saka kowa please ni ban san me yasa kike yawon sako wasu cikin lamarina ba" to sarkin korafi ,kai dai da wannan halin naka Allah yasa ka canza ,kullm kai kenan cikin bakin hali naga ranar da zaka canza bazaka barni naji da tsufana ba tun kana yaro nake hidima da kai har gashi ka tsufa ta qarashe mgnr cikin salon tsokona tana hade rai ."
Ya dago a sukwane ya tsura mata idanuwanshi "yanzu ni ne na tsufa sweetheart?sosai kuwa kai yanzu tunaninka baka tsufa ba ?haba haba !!sweetheart allah idan ba fad'a akayi ba babu mai cewa na wuce 40,dan ni wallahi jina ma nake Kmr .." "kai dan Allah kama mana baki shima gyara ne ,da babu gyara da kasan kai ba yaro bane "wel ko babu gyara zan zama Kmr yaro dan gadon jikin mai kyau nayi "
"A wajen kenan ?
Ya sake tsaita idanunshi akanta sosai yace "wajenki mana! shakiyi kawai ya dai kamata ka rage wadan nan abubuwan dan ka kusan zama baba nan da wani lokaci ,nan da nan ya hade rai Kmr wanda aka fadawa sakon mutuwa duk da tsananin son haihuwa da yake amman kwata kwata baya qaunar haihuwa daga mrym ya gwamaci ya qare rayuwarsa babu haihu akan ya haihu daita ".
Ahankali ya bude bakinsa zaiyi magana mami ta katseshi dan tasan ba alkhairi zai fad'a ba "ina son zuwa yanzu ka bawa mrym matsayi mai girma acikin zuciyarka ,ya sake kallonta cikin rashin fahimtarta "Eh !nasan abinda nake yau idan ka runtse idanunka da zumar bacci ka matso daita kusa da zuciyarka zaka ga abubuwa masu yawa akanta" ya dage girarsa daya yana dubanta dan ya fara gano rikicin tsufa ya fara kama mahaifiyarsa idan ba hk ba ina shi ina wani kusantota da zuciyarsa yaji me ?bai gama mgnr zuci ba ya sake jiyo sautin muryarta ".
"tunda ta zama mahadin rayuwarka dole zuciyarka zata dinga bibiyarta " numfashi ya sauke da karfi dan yasan ba abune mai yuwuwa ba shirunsa ne ya bata amsa mgnrta "ta gyara zama kai dai kayi qoqarin yau kawai ka kusantota da zuciyarka idan Allah ya kaimu gobe zan tmb..."sweetheart yunwa !"Okay bari na tashi sarkin korafi "thank you my sweetheart Kiyi sauri please dan yunwa nake ji sosai har cikina ya fara zafi "dariya ma ya bata a duk sanda taji ya fadi haka sai taganshi tmkr yana yaro ,adamcy kenan ko yaushe zai san ya girma ? kullum idan yana gabanta tmkr qaramin yaro yake dawowa ."
Jallof din kuskus wanda yaji hanta da nama da ugu ta kawo masa ta ajiye agabansa tace "bismillah sarkin korafi kallonta kawai yayi yana girgiza kai sannan ya fara ci a natse ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana kallonsa hatta cin abincinsa dabam ne ,yana ci tana yi masa hirar yadda take son bikinsa ya kasance shi dai bai ce uffan ba ya cigaba da kwasar abinsa bayan ya gama cin ya mike ya haura saman d'akinsa wanka yayi ya canza kaya marasa nauyi ya zauna abakin gadonsa ya kunna system ,ahankali sakonnin abokan kasuwancinsa ke shigowa wasu ya amsa wasu kuma ya wuce ."
Washegari yana zaune akan daya daga cikin kujerun dinning sanye da wondo da riga long sleeve sai dai ya dan nade hanuna rigar kadan ta yadda zaa iya ganin hadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayinda mami ke tsaye a gefensa tana qoqarin saving dinsa ,ta kallesa zaune shiru ya hade hannunwansa waje daya tace "jiya da nace ka rufe idanunka tare da kusanto mrym da zuciyarka , fad'a min daka rufe idanunka me ka gani ."Kai sweetheart "nasan mrym ka gani alokacin daka rufe idanunka ko ba haka ba ?" ni ba wata mrym dana gani sai princes dina na gani ."
" kada kayi min karya dan nasan baka iya karya ba "tunda Kinsan bana karya ya kamata ki yarda dani wallahi ni banganta ba Kinsan wani abu a duk sanda na runtse idanuna princess dina nake gani wata rana cikin farinciki wata rana cikin damuwa nifa jikina yana bani yarinyar nan ba karya bace gsky ce km ba aljana bace tana nan acikin duniyarmu sai dai a ina take? " yaushe ne zan ganta ?shine bansani ba amman nasan zamu hadu shiyasa nake jin Kmr a fasa wannan auren "kai sakarai menene ya kawo batun a fasa aure kuma daga magana ?"
Kamar yayi dariya ganin yadda magaarsa ta d'aga mata hankali "wannan auren fa sai an daurashi babu makawa zaku rayu tare har ma wata rana zaka amince daita tare da furta wa mrym kalmar so na tabbatar maka da haka "tunda ya fara cin abinci bai sake cewa uhm ba bare uhm uhm har ya gama ya goge bakinsa da tissue ya mike tsaye yana qoqarin yi mata sallama suka jiyo sallamar baba babba fuska cike da damuwa mami ta bar ATA ta qaraso wajensa a inda yake tsaye dan ko zama bai samu damar yi ba kallo daya mami tayi masa ta fahimci yana cikin damuwa suka gaisa adaidai lokacin da ATA ya qaraso ya gaishesa cike da girmamawa sukai shiru mami ta dubesa tace "baba babba ka zauna mana bari akawo maka breakfast ."
Yace " zulai ba sai na zauna ba nazo ne na sheidawa adamu tun jiya baa ga halimatu ba daga zuwa siyaya nan da nan hankali mami ya tashi "baa ganta ba to ina taje ?kuma an kira layinta bata d'auka ba ?wallahi kwana mukayi kiran layukanta guda biyu shiru abinda yafi daga min hankali bata saba irin haka ba ,kuma duk runtsi ka kira wayarta zaka sameta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta furta tana cewa "Allah ya cecemu " ATA ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga lokaci ya fara tafiya ya bude bakinsa da kyar yace "baba babba muje daga waje yana gama fadar haka ya nufi kofar fita suka bar mami cikin tsananin damuwa ."
  tare suka jera har haraban estate din baba babba yana sake masa bayanin tashin hankali da suke ciki "ka kwantar da hankalinka baba nasan inda take "wani irin naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana dubansa a tsanake tare da neman qarin bayani ."wani dan bincike zaayi akanta da zarar an kammala zata dawo gida "shiru baba babba yayi yayinda zuciyar tsohon ya shiga bugawa fiyye da kaida domin kai tsaye kwakwaluwarsa ta hasko masa binciken da zaayi akanta muryar tsohon a sanyaye yace "to allah yasa muji alkhairi" ameen !ATA ya furta atakaice anan suka rabu yayi masa sallama ya nufi inda motacinsa Ke jiransa dan tun fitowarsa aka gyara tsayuwar su , tun kafin ya qaraso escort dinsa dake tsaye tmkr mashi suka yo kanshi cike da girmamawa ya shiga mota suka bar gidan ."
Bangaren nuzla kuwa gaba daya duniyar ce ta cakude mata waje daya bata ta'ba sanin haka tashin hankalin irin wanda take ciki yake da ciwo ba"ta dauka zafi da ciwon rashin son da yaya adam ya nuna mata shine damuwa mafi tsayi arayuwarta a she qaramin abu ne damin kwana daya tal da tayi acikin dakin kurkun da take ciki ya ninkashi sau babu adadi ,tana durkushe bisa gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta taji motsin ana bude qaramin kofa ,bata bude idanunta ba bare taga masu shirin budewa ,wata murya taji ta doki dodon kunnenta cikin tsawa tana bata umarnin ta fito sai lokacin ta bude idanunta da suka kumbura tsabar kukan data kwana tanayi ."
Koda ta motsa qafafuwanta dan mikewa sai taji ta kasa yunkurawa dan sun qara sandarewa kamar dotse ,hannunta ta kai ta rike karfen kofar sannan ta kai dayan hannunta ta riko kafarta daya ta yunkura da kyar ta mike tsaye ,ahankali ta fito wani qaramin daki aka nufa daita, babu laifi yafi wanda ta fito tsafta kujeru biyu tagani sai table dake tsakiyarsu ."tun kafin abata umarnin zama ta zauna dan kafafuwanta bazasu iya cigaba da daukarta ba ,mutumin daya shigo daita ya fita byn second biyar wata police mace ta shigo fuskarta a hade
har tafi na farko ban tsoro da razanarwa duk da bata aikata komai ba amman zuciyarta ta cika da tsoro mai tsanani ."
Idanunta na kan nuzla ta ajiye wukake har guda uku akan table din gabanta sannan ta zauna tana fuskantarta ,nan nuzla ta sake tsurewa hankalinta ya sake tashi wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar gangarowa daga kwarnin idanunta ."
Bayan mintuna goma police ta soma da tmbyr sunanta ta dago idanunta dake zubar da hawaye ta bata amsa sannan ta cigaba "yanzu dai sheidar da muka samu daga bakin danuwanki ya kore duk wata hujjar da muke nema akan masu amfani da wannan wukar wajen kisa da fari ko zamu san dakilinki nayi kisan ?
Nuzla tayi shiru dan bata da amsar da zata bata sai dai ta dago ta zuba mata idanunta tana kallonta hawaye na zuba daga kwarnin idanunta ,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen idanunta yasanya hankalin nuzla qara tashi ba shiri ta soma mgn cikin rawar murya "ni ..ni ban kashe kowa da wannan wukar ba, hasalima ni a yanzu na fara ganinta "amman ai kin ta'ba turawa yayanki adam sakon zaki ga bayan matar da zai aura ko me zaki iya cewa akan haka ?babu abinda zan iya cewa akan haka baya ga qaddara , kuma nasan tana iya fadawa akan kowa ,a garin na tsoratar dashi akan tsananin soyayyar da nake masa wannan matsalar ta faru dani ."
"kenan kin tura masa sakon cewar zaki ga bayan matar da zai aura ? ta runtse idanunta wasu ruwan hawaye masu zafi suka zubo mata ta gyada mata kai "Eh! na tura masa amman ban aikata komai ba"karya kike karki wahalar da hukuma domin yin hakan yana qarawa mai laifi laifinsa dan haka ki fad'a mana gsky domin kawowa rayuwarki sauki "
Nuzla ta girgiza mata kai jikinta na rawa "Allah ki yarda dani ban san komai ba "da fari kin kashe mubina wacce ta kasance yar uwa agareki kin kashe sadiya dake aiki tare da yayarki shahida yanzu kuma kinyi yunkurin kashe mrym shiru tayi kawai tana tunani wacece sadiya kuma ?ta dai san mubina da maryam amman sadiya kam bata santa ba ."
"Kin kashe mubina yaruwarki dan ta furta tana son adam haka zalika kun hadu da sadiya a hospital kafin rasuwarta itama ta furta tana son adam kin yunkuro kan mrym ita kuma dan ta amince zata auresa kin kashe mutun biyu din nan adalilin sun furta suna son abinda kike so ko ba haka ba ?
Ji tayi zuciyarta ta tsaya CAk ta daina aiki na wani lokacin kafin daga baya taci gaba da bugawa ji take magaarta ba'a kunneta kadai ya tsaya ba har cikin zuciyar ta take jin komai saboda dacin kalmar ."
 "kuka ta saki mai cin rai meke shirin faruwa dani ?ta furta a fili cikin tashin hankali da firgice ,wai ita ake zargi da laifin da ba taji ba bata gani ba kallonta tayi da idanunta da suka koma kmr an diga jini acikinsu , tace "me zakice akan haka ?daga kalmominsa komai ya sauya mata ta gane ita din ba kowa bace sannan ta soma fahimtar bata isa tace zata ma kaddarata wayo ba ,yau din taxo mata da tashin hankalin da rudani ya zatayi da kaddara da ta fada mata " ?duk yadda yarsanda taso ta amsa laifinta amman taki dan haka ta mike ta fice ta bada umarnin a canza mata daki zuwa wani dakin dabam ."
Ai tana shiga dakin hawaye nadamar furucinta ya kufce mata domin har gara dakin farko daaka sakata dan wannan bashi da maraba da kabari yayinda zarninsa da warinsa da duhunsa ya zarta duk wani wari da mutun ya ta'ba ji tana kuka tana istigifari" Allah na tuba Allah ni bawar ka ce ya Allah kasani ban aikata laifi mai muni hk ba amman na kudurta yinsa ka gafartamin ban isa na maka wayo na hana faruwar kadarata ba " Allah ka kawomin sauki cikin wannna tashin hankali".
kuka tayi sosai ,sai dai duk rintse bazata taba karban laifin da bata aikata ba ."Ahankali kwakwaluwarta ke son tuno mata wacce sadiya dake aiki da aunty shahida da tunanin wanda zai iya aikata wannan taadanci acikin danginsu a daura mata , sai dai duk tunaninta kwakwaluwarta ta kasa gano kowacee sadiya da kuma wanda yayi amfani da damarta yayi mata haka ,hakika bata da makiyi kamar shi kuma ya cutar daita ya zalinceta ba kuma zata ta'ba yafe masa ba ,wajen bazai isheta zama ba dan hk ta gwamaci ta kwana acikin zarni da kazantar waje tana kwance taci kuka ta koshi idonta sunyi lulu dasu ."
Qarfe biyu daidai na rana ya fito daga cikin makeken office dinsa kai tsaye hanyar massalacin dake cikin ma'aikatan ya nufa yayi sallar azahar sannan ya bawa direbansa da masu tsaronsa umarnin tafiya police station babu bata lokaci kowannensu ya zama ready yana qarasa isowa aka bude masa mota ya shiga suka dauki hanyar police station yana shiga kai tsaye da cp Amir suka hadu suka tsaya suna magana akan nuzla suna gama magana cp yayi gaba zai masa iso wajen dpo ."tun kafin ya kai ga shiga dpo ya mike ya fito da kanshi cikin girmamawa yau ga matun kamar adam tariq abdullahi acikin station dinsu dan kasuwan daya fi kowani dan kasuwa kudi ya shiga office din suka zauna cp ya basu waje suka gaisa sannan suka soma tattaunawa akan nuzla ".
"ranka ya dade mai zai hana awuce kotu kawai ?ciza lip's ATA yayi yana girgiza kai muryarsa a matukar raunane yace "a'a nan ma ya isa banason aje ga kotu fatana ma ya zamanto babu hannunta ciki ,amman yanzu abi mataki na karshe ayi amfani da sheidar hannunta "muma shine last option dinmu domin shi zai warware komai ya runtse idanunshi hankalinsa na sake tashi babu wanda yake tausayi Kmr mahaifinta da mahaifiyarta yayyenta da kuma masoyinta hisham ya tuna halin daya gansa yau din gbdy baya cikin natsuwarsa haka ma yan'uwanta ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana cewa "ko zan iya ganinta ?why not ranka shi dade "inspector runke !ya kwallawa yarsandar dake kan kanta kira cikin girmamawa ta shigo sai data sara masa sannan ta kame waje daya "jeki fito da yarinyar nan wacce akawo jiya "Okay sir ta fad'a tana juyawa cikin sauri ."
Tana fita ATA ya kalli dpo "amman babu wanda ya ta'ba lafiyar jikinta kawai gsky nike bukata ?"yallabai babu wanda ya ta'bata yarinyar ma bata da rigima tunda aka kawota take kuka, very gud kar wanda ya ta'ba lfyta in sha allahu yadda kace haka zaayi batayi ma rashin kunyar da zaa ta'ba lafiyarta ba kawai dai taki amsa laifinta ne ya qarasa mgnr adaidai lokacin daaka shigo daita kallonta kawai yayi yana mamakin yadda kamaninta ya canza acikin kwana daya da yinin datayi ga dai shi babu alamun duka ajikinta amman cizon tsoro yayi mata yankan qauna ga dotti ya soma zama ajikinta tana ganinsa ta fashe masa da kuka tana cewa "dan girman allah yaya adam ka ceceni kasa a fitar dani daga nan wallahi idan na cigaba da zama anan mutuwa zanyi wallahi ban aikata komai ba ."
ATA dake kallonta ya sake hade fuska babu wata alamun tausayi bata damu da yanayinsa ba dan tasan halin miskilancinsa da zafin zuciyarsa dpo Karan kanshi ya tausaya mata ya nuna mata wajen zama ta zauna ATA ya tsareta da idanunshi yana kallonta yayinda ita km ta cigaba da sheshekar kuka "har yanzu kenan baki shirya fad'ar gsky ba ?ban aikata komai ba me yasa zan amsa laifin da ban aikata ba wallahi kasa a tsananta bincike ni nasan ko waye acikin estate dinmu yake amman ni ban aikata ba ,wani kallo yayi mata sannan ya mike tsaye zaa yi bincike na karshe akanki kiyi adduar babu hannunki dan muddin ya zamoto kece zaki qarasa rayuwarki a inda yafi nan muni yana gama fadar haka ya bada umarnin a fitar daita tana kuka tana kiran sunansa aka fice daita ya kalli dpo yana sake jadda masa kar ta'ba lafiyar jikinta har sai an gama bincike yayi masa kyauta sannan ya wuce ."
*****
bayan tafiyarsu alhj alqasim ummah suna hira da maryama tace da zarar kin qare bautar kasa kema zanyiwa alqasim magana ya nema miki aiki mai kyau ta yadda zaki samu damar taimakawa aunty ,dan Allah ummah kiyi masa maganar idan ya dawo kinga yace qasar ma zasu bari kinga idan yasan da maganar wata killa zai barwa wani sallahu".
" in sha allahu maryama zanyi masa mgn kuma nasan zai min wannan alfarma bare kuma naga alamun kin kwanta masa arai murmushin jin dadi maryama tayi tace "ai duk saboda ke ne ummah darajanku naci banci haka ai bazan taka matsayin ko daura kwayar idanuna akanshi ba ".
hirar sukayi sosai cike da so da kulawa wata ya qare ummah ta saka ran zuwansu alhji alqasim amman shiru har wani wata ya kai goma dan haka ta fidda rai da ganinsa koda ummah tayi hirar da maryama ta rausayar mata da kwayar idanunta domin ita a ganinta haka masu kudi suke da fad'ar abu su fasa mussaman idan bai shefesu ba "ummah karki wani damu da rashin zuwansu tunda daman su suka saka kansu ba wani ne ya sakasu ba ."
Satin da suke ciki ya qare babu dalilinsu sai da aka sake shiga wani sati sai ga wayarsa yana sanar da yaya sadam yana nan zuwa ranar lahadi ranar suna jumaa dawowarta kenan daga wajen aiki ta samu labarin zuwansu daga bakin ummah ai kuwa dadi kmr ya kasheta da murna ta shiga side dinsu tana sanar da aunty cewar ranar lahadi zasu zo dan daman ta fad'a mata taimakon da ummah zatai mata sosai taga farinciki a fuskar aunty daman ita kadai take tausayawa a rayuwarta tana son ta taimakawa mahaifiyarta amman bata da hali ,dan zanen da take ba wani manya kudi yake kawo mata ba sakasancewar sai kayita bin office office na masu kudi dan ba kowa ya gama saninta ba bare su nemeta dan kansu, gashi tana son fitar da mahaifiyarta cikin wahalar da take ciki amman bata da iko sai dai ta mika lamuranta zuwa ga Allah dan ya kawo masu saukin halin da suke ciki.
ranar lahadi aka sake maimata irin hidimar daakayi masu a wancan ranar sai dai kuma wannan zuwan nasu akwai qarin abubuwa masu yawa daakayi karfe goma da yan mintuna motarsu ta tsaya a sabon titi market street wannan zuwa babu driver da babban dansa yusif da kuma kanwarsa Kausar sai dady da yake zaune a bayan mota ranar kamar wacan ranar yaya sadam ne ya tarbosu zuwa cikin gida sai dai shi Yusif bai shigo ba ya tsaya a haraban gidan yana amsa waya ."sakina aunty salma da aunty hassana da yayanta da baba gali duk suka fito tarbonsu ita kuwa maryama sai ta koma dakin ummah duk da tana bukatar farinciki wa rayuwarta amman sai ta boye kanta ."Kausar tafi yusif surutu dan ita take ta haba haba da su sakina da Islam da kaulat har ma da shukura da bata ta'ba ganinsu ba umma ta fito suka gaisa ta tmbyesu hanya ."
Wannan dalilin yasa ta fito daga dakin umma dan karta kwatanta na kwana baya sai dai ta kasa shiga cikinsu ta rabe can nesa dasu byn ta gaishe da dady ta fito ta zauna a tsakar gidansu hannuwan yusif acikin aljihu ya shigo bakinsa dauke da sallama wacce ta makale a fatar bakinsa ganin maryama ya tsayar masa da sallama ya tsura mata ido jikinta ya bata ana kallonta dan haka ta dago a natse domin ganin mai kallonta nan take ta firgita ta qara gyara zamanta da daidaitawar mayafinta." ya tsura mata ido sosai yana kallonta ahankali yace "sannu !"
sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta amman ta kasa maida masa da sannun da yayi mata sai sunkuyar da kanta tayi dan bata son yawon kallo shine ma dalilin da yasa take yawo da nikaf duk inda zata dan sai mutane suyita kallonta wai tana da kyau da sauri ta mike ta nufi hanyar side dinsu ya dan lekota adaidai lokacin data waiga suka hada ido jin alamun tafiya yasa ya dawo da natsuwarsa sannan ya shiga cikin parlour'n umma da sallama tana ganin shigarsa ta dawo dan bata son tayi nisa ummah tazo tana nemanta ai kuwa tana zama tajiyo sauti muryar ummah tana kiran sunanta jiki a sanyaye ta shiga parlour'n ta durkusa."
Kausar na ganinta ta fadada murmushinta ta riko hannunta "mamana ta bani labarinki ta fad'a hannunta na cikin nata maryama tayi murmushi wanda Ke bayyana kyawunta tace "da fatan tana lafiya? tana lfy tana can tana kewarki tace kin fini kyau da kunya har ma da qoqarin karatu da fari na karyata amman yanzu na gasgata a ganin da nayi miki a karon farko ,alhj alqasim da ummah sukayi murmushi yayinda yusif sai kallon maryama yake bai ce komai ba Islam kam sai wani yatsina fuska take jin yadda kausar ke yabon maryama ,alhj alqasim yace "ku bamu waje kuje kuyi hira "maryama muje wajen mamanki mu gaisheta lumshe idanunta tayi tare da cewa "to !
Hannun kausar na cikin na maryama suka fice Islam na biye dasu a baya maryama ta lura da irin kallon da yusif yake mata dan haka tasha jinin jikinta ,suka shiga side dinsu kausar tabi falon da kallo sannan ta dawo da kallonta kan maryama "tabbas nayi farinciki da ganinki a matsayin wacce mamana ta yaba da halinta har ma naji qaunar yin kawance dake ."maryama tayi murmushi kawai dan ita bata iya doguwar hira ba sai dai acikin ranta taji dadi ,ko bakya sona da Kawa ?ya zaayi naki sonki da qawa ai daman ke qawata ce kuma yaruwata ,ta rike hannuwan maryama da'ace acikin gari kike da yanzu ana nan ana hada gumi akanki maryama bata fahimci maganarta ba sai dai ta fahimci tana yi ne akan kyawunta murmushi tayi tace "akan me zaa hada gumi akaina ."
Ta gyara zama "kyawunki yafi karfin zama acikin geto area bakowane acikin geto area hk zai iya cewa yana sonki ba saboda sanin kinfi karfinsa ko kina da samari ?"Sosai ta bawa maryama dariya ta kuma girgiza mata kai alamun bata da dan ganinta shi ya fiye mata sauki akan tace sun gudu sun barta ne ko kuma an kwace mata ,ai dole samari suji tsoron zuwa irin wannan kyau Masha allah wallahi ba wasa nike ba tun kafin na ganki momy ta fad'a min tayi min kyakkyawar qawa jinta kawai nayi domin ina jin babu wata macen da zan iya qawance daita anan amman ganinki na sha mamaki banda qawa zaki iya zarce komai agareni maryama tayi murmushi kawai tace "na gode ."
"Kinga yayana yusif?
Ta tambayeta tana kallonta "ko da yake ba sai anji a bakina ba maryama ta tsura mata idanu kawai tana kallon kausar cikin rashin fahimta dan ta fuskanci kausar nada yawon magana sosai ita kadai take kidinta take rawarta,dan ko tmbyr manufar abinda ta fad'a batayi ba ta rabu daita suka cigaba da hirar geto area ."acan kuma parlour'n umma alhj alqasim da baba gali da yusif da yaya sadam suna zaune bayan sunci abinda aka kawo masu saà alhj alqasim yace "ka gane wannan ?ya nuna masa yusif da hannu baba gali yace "yusif ne mana ya zaayi na kasa ganesa, a'a to yaron yanzu ne kwana kadan idan baka gansu ba sai kaga sun qara girma yusif yayi murmushi ya basar bai sake cewa komai ba ."
Bayan tashin ummah dady ya dube baba gali yace "Gali wato zuwan da mukayi wancan karon wani ikon allah mai dakina mustafshira tun ganin maryama sai taji qaunar yarinyar har taji tayiwa danta shaawarta a matsayin matar aurensa dalilin da yasa banzo kenan ba tun wancan watan danayi alqawarin ba yusif baya nan yaje canada wannan dalilin yasa na tsaya har sai ya dawo sannan zamu zo tare ,yaron yaso yaki wai tayaya zai zo geto area neman matar aure amman sai na shawarcesa daya daure yazo ya gansu gbdy wacce tayi masa sai ayi maganarta ."
Baba gali yayi murmushi zuciyarsa cike da farinciki yace "gsky abu yayi kyau mutun uku suna nan babu wacce akayi mgnr aurenta Islam da sakina sai maryama wacce take bautar kasa sauran biyu din km tun daga secondary basu cigaba ba amman dai ni ina son sakina ta cigaba alhj alqasim yayi shiru yana kallon Yusif yace kai duk gasu nan wacce ka tarar anan itace Islam din da nafisa ko ?baba gali yace a'a sakina wacce ta shigo karshe itace maryama "to kaji yusif itace sakina sai Islam wacce ta shigo karshe itace wacce mahaifiyarka tayi maka shaawar duk yayana ne babu wacce bazan yi murna idan ka aminta daita ba ,kai ma bazaa takuraka ba idan kaji babu wacce tayi maka sai a hakura ."
Yusif yayi shiru yana tsotsa keya yace " zabin momy shine zabin da yayi min dan haka maryama itace ta shiga raina a kallon farko danayi mata alhj alqasim ya washe baki yana murmushi baba gali ba dan ranshi yaso ba yace to shikenan duk da daman akwai maganar wani dake sonta amman dai babu komai sai abashi hakuri alhj alqasim ya tsayar da idanunshi akan baba gali "da kuma kace babu wanda yake nemanta da aure? ya tmbyesa cikin mamaki shi kuwa yusif ido ya ware sosai dan shi wallahi yayi mata ko sama da kasa zasu hade sai dai ya hakura ya bar masa ."
Baba gali yayi sauri yace "ai kasan samarin yanzu ba wani serious yayi ba amman sharesa kawai dan sama sama yake ma zuwa yusif ya sauke ajiyar zuciya alhji alqasim yace "shikenan ayi mata magana tayi miji shi wannan babu zuwa sama sama yazo kenan ayi mata magana sai muje mu gaisa da mahaifiyarta koda yaya sadam ya fad'awa umma murna har da sujja tayi ita kuwa Islam cikin kunci ta shige bangaren su byn ta gama ji sakina kam ko ajikinta dan ita tana son maryama bata dai san meke sata jin tsanarta ba ,maryama da kausar suka fito suna hira ganinsu yasa shi ya tsayar da hankalinsa akanta tabbas ta hadu yayi mamakin samun mace kamarta gata yarinya qarama just 20 amman ta hada abubuwa masu yawa dan ya darata da kusan shekaru shatakwas a duniya"
Alhj alqasim ya bukaci ganawa da maryama ta shigo a natse ta zauna tare da takwashe kafafunta kanta sunkuye yayinda yusif yake ta kallonta bai ta'ba sanin akwai baki mai kyawun da tafi fari ba sai akanta ko da yake bazaa kirata da baka ba sai dai chocolate colour" maryama ina son nayi miki wata tmby guda daya kuma ina son ki sanar dani tsakani da Allah ki sanar dani gsky ki daukeni tmkr mahaifi ne yake tmyrki ita dai shiru tayi tana tunanin irin tmyr da zai mata domin bata kawo komai aranta ba ko hasashen abinda zai tmbyeta "maryama ya'ya zamanku yake acikin gidan nan "?
Ta tabbatar akwai abinda alhj alqasim ya gani yasa har yayi mata wannan tmyr tabbas bata da tacewa ba zata iya fad'ar irin bambamci da abubuwan da ake mata daga bangaren baba gali da aunty hassna har ma da sauran yanuwansu wadan da suka kasance yanuwa ga mahaifinta tunda daman duk mutumin da bashi ya haifeka ba ,dole sai an gane kuma bai zama lallai ya soka ba ,ya qara mata tmbyr ganin bata da niyyar cewa komai hakan kuwa ya qara sa zuciyar yusif mace wa akanta gbdy ganinta yasa ya manta da husna yarinyar da suka dauki tsawon shekaru daita kawai taimakonsa bai kawota gidansu ba daya san shikenan ya tafka asarar samun maryama ."
Ya sake tmbyrta a karo na uku cikin sanyayyar muryarta tace "ban san ta inda zan fara ba amman dai bani da matsala muna zaune da kowa lafiya tayi mgnr tana sunkuyar da kanta shi kuwa yusif ya kasa dauke idanushi akanta alhj alqasim yayi shiru na dan wani lokaci sannan ya shaki iska yace "har mamanki ?ta sake gyada masa kai duk muna lfy bamu da wata matsala da kowa acikin gidan nan ita kam bata ga dalilin da zai sa ta fitar da sirri gidansu ,su din yanuwanta ne duk da basu dauketa a haka ba ." yayi shiru yana nazarinta shi dai ya fuskanci akwai matsala daga hasana har gali amman gashi ta boye masa yayinda zuciyar maryama ta dinga raya mata ta sanar masa gsky zaman da suke wanda naci ma da taimakon umma suke samu amman ina bazata iya ba ."
Wannan hali nata yasa yaji lallai ta qara shiga ranshi duk nmj daya sameta yayi saa a duniya domin macen dake iya rike sirrinta itace mace da haka ya gama yace ayi masa iso wajen mahaifiyarta a natse Umma tayi masu iso zuwa wajen aunty ta tarbi bakinta yadda ya kamata dan katuwar tabarma ta shimfada masu, alhji alqasim ya jima yana kallon aunty cikin tsananin tausayawa sannan ya dubi Yusif muryarsa sanyaye yace "ga mahaifiyar maryama suka qara gaisawa shima yana satar kallonta da alamun ya gano kyawunta maryama ta dauko duk da bata cikin sukuni amman fatar jikinta ta ya'yan masu kudi tana nan lafiya lau kyakkyawar fata mai sheki babu abinda ta rasa wajen auna kyakkyawa , hanci baki mai kyau idanu kausar kam kusa daita ta koma ta cigaba da zuba mata surutu nan da nan hira ta barke sosai atsakaninsu "
Alhj alqasim ya gano dansa na bukatar kebewa da maryama dan kallon da yake mata babu sauki yace "maryama fitar da wannan matsoracin yaga cikin geto area daga nan akwai abinda zai fahimtar dake ta dan yi murmushi tare da dago idanuta suka hada ido da yusif wanda yayi zuru da idanunshi akanta aranta tace "bashin me naciwa bawan allah nan yaketa bina da kallo? bai yi tsammanin zata iya fad'ar haka ba dan hk yace mata "bashin gaisuwa mana baki gaisheni ba sai lokacin ta fahimci a fili tayi mgnr ai kuwa da sauri ta mike ta fice daga parlour'n jamar dake zaune a wajen sukai dariya yayinda yusif ya mike ya fito tana tsaye a tsakar gidan rungume da hannunwanta ya qaraso inda take tsaye "ina kwana ta fad'a tana sunkuyar da kanta sakamakon idanunshi dake yawo a sansar jikinta "yanzu ne ina kwana ? to ai bashi ka biyo kuma gashi na baka."
Shiru sukai na dan lokaci ta sake sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ko zan iya tmbyarki ?kai kawai ta gyada masa tare da yin shiru tana mai jin tsanani kunya most especially idan ta fahimci sanar daita kalmar só zaayi ko mgnr aure dan ma wayewar karatuta ta rage mata wasu abubuwa ,amman duk da hk a shirye take da irin tmyr da zai mata dan kallon yayanta take masa tunda mahaifinsa yace ta daukesa tmkr mahaifi kunga kuwa dole ta daukesa matsayin yaya agareta muryata a sanyaye tace "nima ina da tmby idan kayi naka ka gama ?ya danyi taku kadan yana shirin barin wajen domin canza waje" muje daga can ta biyosa cike da natsuwa cikin tafiyarta kamar bata son taka qasa ."
Ya tsaya tare da tsura mata idanunshi ya gyara tsayuwa hade da rungume hannunwansa a qirji "Kinsan tambayar da nake son nayi miki ?ta girgiza masa kai tana mai sake dukar da kanta "kina da saurayin da kike so ?ta dan dago idanusu suka tsarke cikin juna tayi saurin dauke nata tana cewa "acikin ranta kar dai abinda nake tunani ne zai tabbata ?kamar tace tana da mlm yahuza dan saukakawa kanta sake shiga wata rayuwa amman sai ta tsinci kanta da ce masa "a'a bani da kowa kin san kuwa kina da kyau sosai ?tace ina dai ji mutane na fad'a amman ni dai nasan bani dashi ,kiji tsoron allah yadda yayi maganar yasa tayi murmushi har fararen hakoranta da wushiryarta suka bayyana ."
"Kina da matukar kyau ,Ke rayuwarki ce kawai a irin wannan area amman siffar ki da halinki suna manyan unguwa ne kinfi dacewa da zaman acan nasha mamakin dana ganki anan ?tayi murmushi "to saboda me zakayi mamaki dan na kasance a irin wannan unguwar ?",su mutane dake rayuwa acikinsa su ba mutane bane ?ya sake tsareta da idanunsa ganin karfin halinta akan maganarta "har wani dagewa kike da tmby okay ai an kusan daukeki tunda baba ya amince ?
Shiru tayi tana nazarin maganarsa ai an kusan daukeki tunda baba ya amince domin kawar da maganar tace "dady yace zaka fahimtar dani wani abu me zaka fahimtar dani ?yayi shiru murmushi akan fuskarsa yace "matsalarki kunya ni kuma tsoro ta dan yi Jim ,a ina na zama matsala ?bai bata amsa ba sai kallon gabansa daya cigaba da yi daga bisani yace "ni baki tmbyeni ko ina da yammata ko bani dashi ba ?ta dan daga kafadanta alamun babu ruwanta da hakan domin wannan babbar maganace tama fi karfinta me ma ya kai ta ga wannan tmbyr ? "kodan saboda baki damu da yayanki ba ?
"A'a?
"Ya a'a da kin damu dani nasan zaki tmby ko yaya abinda ya shafi rayuwata mussaman Kiyi koyi da irin tmbyr danayi miki akan samari " nan da nan taji wani iri da alamun zai yi rigima da jan magana idan ba haka ita ina ruwanta da wasu yammatansa "karkiji da wai sai kin mun irin tmbyr da na miki zaki bar nan idan ba haka sai dai na tasa keyarki na wuce dake " ta zaro ido tana kallonsa da mamaki wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama "to shikenan bari na tmbyeka sai dai ba tmyr ka zanyi akan kana da yammata ko baka dashi ba dan nasan kana dasu aruru wata killa ma kullum sai kayi budurwa sama da hudu "dariya mai dan sauri yayi yana kallonta "lallai sai kace wani na mamajo yadda ya fadi mgnr ya bata dry dan hk daga dryr bata sake cewa komai ba sai shine ya cigaba da cewa "ni nan da kika gani matsoraci ne tsoron mata ne dani ban ta'ba cewa ina son ko mace daya ba ,ba dan kuma bana ganin wadan da nake so ba sai dan kawai dana tunkaresu da maganar só sai naji gabana yana faduwa ."
Murmushi tayi "lallai ka cika matsoraci ta fad'a acikin ranta ya dan kyaleta amman gashi momy ta gaji da zamana haka ta samomin wacce zan aura "gsky kaji kunya kai yanzu mata ma kake jin tsoro a yadda zamani ya samu cigaba,sai kana yiwa mace kallon macen arziki sai kaga ashe ba haka bane ta dan yi jim ,"ina tmbyrka a ina matsalar take kace matsalarka tsoro ni kuma kunya a wani fannin kenan ?shiru ya biyo byn tmyrta har ga allah bata kawo komai ba saboda bata tunanin hadadden saurayi kamarsa zai ji wani abu akanta har ma ta burgesa sam bata kawo akanta ba haka take biyewa zancensa ."
Ya katse mata tunani da cewa "daace zuciyar kowa zata fitar da matsalarta dana tabbatar zamu samu fahimtar juna har ki fahimci dady da kuma kin gane zabin da momy ta tay min "tayi shiru a ganinta mgnrsa bata dace daita ba bata san komai akan rayuwarsa ba ya sake katse mata tunani "kin shirya cire kunyar ki ni kuma na cire tsoro dan ki samu amsar tambayoyinki .?ta dan tabe baki " ni wai waya fad'a maka ina da kunya ya zaro ido "Subhallah Au baki da kunya ?tayi murmushi "to ai kaine wallahi ni ne wallahi me ?"wai na cire kunya sai kace kunyar takalmi ce ya danyi murmushi ya tsaida idanunshi akanta ita ma shi take kallo dan tana tunanin zai fadi matsalarsa ne ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa tayi qasa da idanunta ta fara shan jinin jikinta domin irin kallon da yake mata mai fassara ne ."
"Maryama wacce momy na ta zabar min ita ce daidai da rayuwata kuma tana kusa dani yardarta abbana yake nufin a matsayin na fahimtar daita soyayyata ya dan gyara tsayuwa "kece zabin abbana kece zabin momy sannan kece zabin kanwata ta sauke kanta ta qasa tsayuwar da kafafuwanta wata shuumar kunyarsa ta mamayeta ji take tmkr ta nitse a wajen daman manufarshi kenan agareta amman ta tsayar dashi tana ta dogon zance dashi ya qara fuskantarta "kece kadai naji duk duniya tun a kallon farko soyayyarki ta doki zuciyata da wani shauki ganinki a karon farko kaunarki ta mamaye ni yardarki itace yarda da abba yake nufi ki bani yardar soyayyarki ni kuma zan nuna miki hallacin so zan fayacce miki irin soyayyarki da take cikin raina ."
Kamar ruwa ya cinyeta haka ta koma a wajen tmkr ba itace Ke hira ba ita kanta hirar datayi a awaanin abaya datasanin yinta take ,da kyar ta daga idanunta ta kallesa ganin gbdy idanuwanshi suna kanta yasa ta sake gyara mayafinta "ki daure ki sanar dani abinda zanjewa da momy domin ta samu sukuni momy na tana matukar qaunarki kullum tana kewarki da alfahari da halinki domin tace bata ta'ba ganin diyar talakawa da irin jarumtarki ba fannin hali da tarbiya da ina ganin momy ta dauki abun da zafi amman ganinki ya tabbatar min ni kaina zanyi alfahari dake idan kika kasance mata agareni kin dace da rayuwata ."
Hakikanin gsky sai dai taki yusif saboda gudun rashin tabbacin samunsa ba dan bai cancanta ba har zuciyarta kalamansa sun dan wanke mata mikin dake daskare a zuciyarta na rashin mlm yahuza da abinda akayi mata amman duk da hk bazatai ganganci amsar wata soyayya a yanzu ba ina ma tana da tabbacin samunsa ? kinyi shiru kice min wani abu "batare dasanin ba kawai taji kalmar allah ya tabbatar mana da alkairi,kenan kin amince zaki auri matsoraci ?kai ma ka yarda zaka auri mai kunya tana gama fadar hk ta bar wajen da d'an saurinta ta boye abayan windowsu tana sauke numfashi ita ba wai tana jin sonshi bane aa ta gaji da rayuwar gidansu km tana son ta dauke mahaifiyarta daga cikin gidan suyi rayuwar farinciki kuma taga alamun zata samu a wajen Yusif ,"
Da zasu wuce aka shigo da kayan abinci masu uban yawa umma ta kara masu godiya yayinda maryama bata bari sun qara yin wata hira da Yusif ba duk da shi yaso suyi sallama amman taki duk mutanen gidan suka fito har yammatan gidan a tunaninsu zai ce yana só nan kuwa basu san tuni ya gama amayar da abinda ke ransa ba, suna tsaye a tsakar gidansu daga nan maryama bata qara taku daya ba ta koma side dinsu har bakin mota suka rakasu baba gali bai saba boyewa aunty salma komai ba dan ya kwashe abinda ya faru ya fad'a mata sakina na zaune tana jinsu aunty salma tayi shiru hankalinta a matukar tashe tace kai wani irin mutun ne da bai san ciwon kanshi ba ? ga sakina bazakayi mgnrta ba gsky wannan hadin bazai yuwu ba kenan rasa yahuza ma cigaba ya kawo mata ? "to ai kece da baki ruguza mgnrsa ba ai da dole cikin yayanki zaa aura shiyasa naso ki barta dashi Ke kuma kika matsa ."
"Tô ai sai ka nuna masu akwai wanda take so idan yaso duk abinda akayi akan mlm yahuza sai a kwance kaga dole nasan zai dauki shukura ko sakina tunda iyayensa anan suke son ya zabi matar aure baba gali yayi shiru aikin gama dai Ya gama shiyasa komai nake gaya miki ki dinga bi ahankali gashi nan da kanki kin rusa rabon yayanki dan da tuni yusif rabon yayanki ne aunty salma tayi shiru tare da cewa "yanzu ma bata baci ba nan da dan wani lokaci kadan zai fasa ya kalleta ai nasan zaki iya amman hakan zai sa iyayensa su gane akwai wata sannan mutane ma zasu zagemu ."tsaki taja kai ka damu da wannan in har kana son yayanka da arziki ya zama dole wannan karon ka bani hadin kai baba gali yayi murmushi to ai ki bada himma da haka suka kawo karshen hirarsu tá tashi ta dauki mayafinta ta nufi gidan alfa
Tayi saa bata samu kowa ba duk abinda ya faru ta sanar dashi yayi murmushi yace "kada ki damu Ke ai mutumi yar arziki ce bakya rabuwa damu duk runtsi kuma da yarda allah zan taimaka miki ki tashi kije ko kaffara bazan yi ba wallahi sai yusif ya auri sakina ko shukuran Kike so ,cikin farinciki ta koma gida duk yadda sukai da alfa ta sheidawa baba gali ya kuma yi murna dan shi kanshi da baya son tana zuwa bin malamai dan yasan har dashi takewa amman yaji dadin na wannan karon tunda yar shi guda jininsa zata taimaka ."
duk mutanen gidan suna zaune a tsakar gida Maryama na zaune kusa da umma ganin kamar zaa tautauna akan yusif yasa ta yunkura ta mike nan kuwa taji sun fara tautaunawa akanshi tana tafiya tana tsinkayo maganarsu har tayi nisa ta daina jin komai ."da misalin karfe tara na dare sai ga kira daga baba gali bata kawo komai aranta ba sai mgnr yusif zai mata ,tana isa ta gaishesa ya amsa yana gyara zama yace "wai me ya hadaki da mlm yahuza ne ?tambayar tazo mata a bazata domin irin haka bata ta'ba hadata dashi ba, koda suka rabu bai kirata ya tmbyeta ba sai yanzu data manta dashi tace "babu komai dan ban san abinda nayi masa ba daya canza da shukura" to ai ba soyayya bace a tsakaninsu da shukura ita kanta salma rashin fahimta ne ku dawo Kmr yadda kuke dan dazu da kanshi yazo neman ki"
"Nemana kuma me kuma zai min ai ni na rigada na yafesa har abada ,aa maryama ban sanki da fushi ba Kiyi hakuri idan ya dawo ki samu ku sasanta kanku kinji bai kamata ba dama shi irin wannan sabanin ai dole yana zuwa a mijin da zaka aura ,ido kawai ta zuba masa kafin daga baya ta sunkuyar da kanta kasa ahankali ta furta to "baba ina kuma alqawarin da kayiwa abban kausar ?yayi shiru yana dan nazari "maryama da na zama qaramin mutun ta bangaren mahaifin mlm yahuza ai gara na zama ta bangaren alqasim maude domin shi zai min uzuri kuma idan na hada yusif da yaruwarki sakina ko shukura nasan komai zai wuce ."
Tayi shiru kawai hawayen takaici suka nemi zubo mata daga idanuwanta gbdy ta rasa abun yi kawai ta mike ta koma banger su ta fad'a dakinta ta kwanta ta kudundine kanta ta fara rusa kuka mara sauti dan tasan wannan ma ya zama ba rabonta ba tunda ma baba da kanshi ya furta mata haka yanzu ita hk rayuwarta zata qare cikin kunci da wahala "me ta tsare masu da basa qaunar cin gabanta? duk wani abu da suka san zai zama cigaba arayuwarta basa so ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.