Complete Hausa Novels

Afnan Complete Hausa Novel

Reading file: Afnan_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 16

*Chapter 10*

_____"hooo Kay AFNAN kinji abin da naji kuwa" eh Yaya naji Dan Allah ko yakirawo kada ka daga ,wadannan daga gani kaga jinsin aljanu" dariya ce ta subucewa AREEF harda rike ciki ,saï da yayi me isarsa sannan yace" baki karya ba AFNAN saï ta iya yuwuwa dan ni ko a film ban taba gani ba ko naji,to Amma mu Ina ruwan mu mudai ba ayimana ayki ba" "hmm tom shikkenan Yaya "lall Yaya ana kira fa! "Au shine wallahi ,Kinga Bari na daga ki nutsu kinji" tom yayana" daga wayar yayi tare da karawa a kunnensa yace" hello!" Inajinka Fadi matsalar?" Yafada a takaice, AREEF ne yafara magana Yana bashi labarin halin da AFNAN take ciki tiryan tiryan har zuwa yanzu da ta jiwa kanta ciwo a asbiti, daga can bangaren Yana kwance cikin bargo baka iya gano fuskarsa ya ce" Okay kadakko hoton gurin Naga " okay Amma an sawa gurin bandeji" eh a cireshi sai a min hoton gurin tukunna" katuramin ta what's app" Yana Gama maganar bejira abin da AREEF zaice ba ya katse wayar.

Kallon kallo suka shigayi wa juna ,AFNAN ce Tace "yanzu Yaya Kuma turamasa zakayi?" A,a gaskiya akanme Zan tura Masa gaban matata haukama kenan, "au to Yaya idanma baka turaba ayshi zaiyi aikin Kuma zaiga komai" hakane fa shikkenan baby yadda zanyi ne Allah dankawai inason kisamu lafiyane yanzu mugani sainayi vidéo kawai saiyafi ganin yadda zaiyi aikin,
Gyra kwanciyar ta tayi ya daga rigar dake jikinta yashiga yiwa gurin video Yana Dan runtse ido kadan kadan, don wani abu yakeji ajikinsa kamar yasaka hannu agurin ya taba,kokuma yayi kissing dinta,gumi yashiga hadawa Yana kallon yadda gaban nata duk taji ciwo Amma duk da Haka ba Hana Kellin gurin bayyana ba " Yaya AREEF gumimme kake" ? Ta tambayesa tare da tsaresa da idanu, shiru yayi mata batare da yace komai ba Dan yakasa magana ,BAYAN ya kammala videon ne ya kalli AFNAN kawai ya dauke Kai tare da mayar mata da rigarta yadda take ,ya kunna data ya hau what's app yayi searching din numbar doctor lion ,ayko saiga ta tafito Nan take ya tura Masa, sanna ya fita daga what'app din ya ce "AFNAN Bari naje n'a Kai su momy gida dan yau doctor yace za a sallamemu "zaro Ido tayi Tace" au Yaya gida fa nashiga uku wallahi anty fadeela zata sake dawowa Ni tsoro take bani" uhm AFNAN kenan. Ki kwantar da hankalinki indai fadeela ce bazata dawo ba har abada'' domin nayi maganin ta " kayi maganinta Kuma?" Eh AFNAN lokaci Yana kurewa Zan je suna jirana a waje" gashi munyi waya da Kamal yace zaizo ya dubaki yau nafadamasa sai dai yazo gida Dan yau za a sallamemu" magana yake mata Amma zuciyarta bugu take kamar gan ga idanunta sun kasa kiftawa daga kallon sa da take ,jitake gabanta Yana faduwa kamar wani abu zai faru , "Yaya AREEF"na,am AFNAN lafiyarki kuwa kinbi kin kuramin Ido" yaya idonka nake kallo kamar ya canza kala" kamarya AFNAN?"yaya idanuwanka fararene amma yanzu saï nake kallonsu amatsayin green" green kuma?" Allah Yaya dagaske nake kashiga bathroom ka kalli mudubi" batare da yace komai ba ya Shiga bathroom din cikin asbitin tare da kurawa mudubin Ido,"Kay to meyake Shirin faruwa danine AFNAN tayi gaskiya Nima gabana ya fara bugawa" ya Dade a tsaye a gurin kafin ya fito inda AFNAN take yace" AFNAN kina da gaskiya Amma bansan meyake faruwa ba "Yaya gabana faduwa yake Dan Allah ku fasa tafiyar nan" a,a zamuje mudan shirya zuwan tarbar doctor Kinga karyazo ba a shiryamasa komai ba" shiru AFNAN tayi batare da Tace komai ba, shiko AREEF durkusawa yayi kanta yamata kiss Nan take tarike hannunsa idonta na zub da hawaye,"Yaya Dan Allah kada katafi kabarni" AFNAN Wai yakike fadar Haka Ina zanje nabarki?" Nidai banason katafi Dan Allah"nanfa ta Kara fashewa da wani sabon kukan me karfi zuciyarta tana rayamata wani abu, zame hannunsa yayi daga nata ya Soma tafiya ,har yaje bakin kopar kirjinsa yayi wani mummunan faduwa, "yaya" AFNAN ta kirawo sunan sa, juyo wa yasakeyi zuwa bakin gadon inda take ayko cikin hanzari ta Mike ta fada jikinsa ta rushe da kuka me ban tausayi"yaya dan Allah kada katafi hankalina yakasa kwanciya" a,a AFNAN tafiya zanyi Babu abin da zai faru Dani ,nidai BURINA ki samu lafiya, AFNAN dan Allah ki kula da kanki ,koda ace BAYAN Raina kada kibari rayuwarki ta lalace "Yaya Wai mekake nufine" kardai kace idan katafi bazaka dawo ba, meyasa kake min zantuka irinna wadan da zasu mutu?" Uhm Zan dawo AFNAN insha Allah bazan mutuba har sai munrayu tare dake kawai dai Ina fadamiki ki kula dakanki duk wuya duk runtsi AFNAN bautar ubangiji kada kiyi Wasa da ita, "allah Yaya nakasa yarda da abin da nake gani a idanuwanka da wan da bakinka ke furtawa" uhm AFNAN duk Wanda ya mutu kwanan sa ne ya kare Kuma bawa baya tsallake kaddarar sa mudum Allah yayi yau Zan mutu to ko Ina zaune a yanzu inda nake muna magana dake saikiji nadaina motsi Allah ya karbi Raina" shikkenan Yaya adawo lafiya Allah ya tsaremin ku "ta Yi maganar tana zame jikinta daga na sa Takoma ta zauna sharaf jiki Babu kwari.

AREEF tafiya yasomayi har ya karasa bakin kofar sannan ya juyo ya sake kallonta, itama shi take kallo, murmushi ya sakarmata yace" Ina sonki AFNAN" kallonsa kawai take ta kasacewa komai domin ita jikinta yariga ya mutu da lamarin AREEF Yama za ayi ace mutum ya canza lokaci guda ,itama kakaro murmushi tayi tasakar Masa, futa yayi inda ita Kuma tasake rushewa dawani kukan.

Yana fita yasamu su momy da dady a tsaye a bakin motar ,karasawa yayi yace momy na nabarku da jira ko?" Murmushi momy tayi Tace Babu komai zai tun ce dai kawai Tace yaya yaki fitowa" "yar dariya yayi yace "ay daman nasan saï ita uwar surutu mutum haryanzu Yana gwaranci amma yace saiyayi shira" Yana magana Yana kama kumatunta, jiyayi Tace "Yaya mutuwa a idonka" dariya su momy sukayi domin sun dauka gwarancin tane na yara, shiko AREEF sai da gabansa ya sake faduwa dajin wannan maganar, Amma sai ya kakaro murmushi yace "ZAITUN mutuwa Kuma ?" Yanzu ita mutuwar tarasa inda zata zauna sai a Ido na" to kema mutuwa a idonki" Gaba kidayansu dariya suka kwashe da ita , AREEF yashiga kokarin bude motar ,babban abin da ya bashi mamaki shine, yadda yaga glass din motar an daukeshi kasa, juyowa yayi ya kallisu momy yace" momy waya sauke glass din motar Nan?" Ah Wai dama' bakai bane to ay mu munyi tinanin kafito kajiramu sai ka bude shi, dakaga bamu fitoba kakoma ciki" shiru AREEF yayi Yana tunani Anya kuwa sutafi kuwa, Kay bakozaibi shawarar AFNAN ya zauna ba"? Ko dai dagaske ne mutuwa zaiyi?" Shahada yayi ya bude yashiga sanna su momy ma suka shiga da Sadiq da umar Kuma suka shuga Gaba sanan suka rufe ,get din asbitin megadi ya bude musu suka fita, AREEF kuwa Yana tuki Yana juyawa ta mudubi Yana kallon get din asbitin.

_ 💋 *AFNAN* 💋______
*Chptar 11*

💃💃*TO!! TO!! TO!! Shhhh*😌 *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*💋*AFNAN*💋WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA 💋 *AFNAN* 💋.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
💋_*AFNAN*_💋
*BOOK one*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.