Complete Hausa Novels

Afnan Complete Hausa Novel

Reading file: Afnan_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 16

*Chapter 12*

*KOGI LAKWAJA*

Tun da motar tasu takifa ,mutanen dake kusa da gurin suka karaso domin kawo musu dauki, Nan danan gurin yacika fal da mutane ,Abu kamar Wasa "yan jarida da "yansanda sun iso Nan take akashiga zarosu daya bayan daya dai dai lokacin da motar asbiti ta karaso, cikin sauri likitocin suka shiga dubasu Amma Ina kowanne daga cikinsu Babu Rai, Kamal kuwa dashi da sauran abokanan da tuni sun hallara agurin ,run the Ido Kamal yayi ya hankade kowa tare da tsugunawa a gaban gawar AREEF Yana kuka Yana cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un yanzu wane' Mara imanine ya aykata muku Haka" wane laifi kukai musu, wayyo Allah na munshiga uku yanzu kenan AFNAN ce kadai tarage kuka yake har da majinar munafurci Yana jijigashi, hakuri Aka Shiga bashi ana ta tausar zuciyarsa ,masu hotuna da vidéo kuwa saï faman yi ake ana ta dorawa a Jafar sada zumunta ,wasu kuma gidan redio wasu t.v nan take mutuwar italan alhaji ABDULLAHI da dan sa millions A.R ta zagaya ko Ina.

Doctor na zaune a office dinsa Yana kallon wata Tasha yaga an dauke an Nuno accident din da su AREEF sukayi, Abu kamar bazata mikewa yayi cikin hanzari ya zame glass din sake idonsa ya kurawa gawawwakin Ido tabbas Babu makawa sune ,to Amma Ina AFNAN?" Zaro Ido yayi yace" kardai ace t.v dake dakinta a kunne take an shiga uku"ya kwasa a guje zuwa dakin datake kwance ,dadai lokacin da ta Kai kansa zai Shiga lokacin AFNAN takawo Kai zata fito tana faman rusa ihu, kanta ko dankwali Babu ruwan ma fincikewa tayi ta fito, daga ita sai jallabiyar AREEF dake jikinta ,rukota likitan yayi Yana cewa"lafiya kitsaya AFNAN kada ki fita ,yanzu bakya cikin hayyacikin" kacikani doctor kabarni ,yazakacemin na dakata bayan ga ahalinacan akwance Ina gani, wallahi koka cikani ko ayanzu namaka ihun kwarto" eh naji koma mezakice Amma ki dakata mutafi tare" "Baki tabude zatayi magana numfashin ta yashiga yin sama sama daker ta iya cewa" likita canciiiiiiii".... Dakata AFNAN yayi saurin sakinta ta watsa a guje, duk inda ta huce a asbitin kallonta ake wasu kuma su gudu sun zata mahaukaciya ce, gudu take zubawa akan titi duk motar da tataho sai dai ta kwauce mata badai ita tamatsa ba Dan Takoma bataji Bata gani da alamun tafara zarewa, inda taga mutane jingim da yansanda Nan gurin ta karasa aguje, tana zuwa ta hankade kowa ta huce, an zagaye gurin yadda Babu Wanda zaije Amma ita tusa Kai kawai take, dasauri dansan Dan ya rikota Yana cewa" yarinya lafiya kuwa"? Banza tamasa itadai Babu abin da take cewa sai" nashiga uku na lalace shikkenan narasa duk wani gata ,yau Babu momy Babu Yaya AREEF me kula dani innalillahi wa'inna ilaihirraju un" hannunta ta fincike ta fada kan gawawwakin tana kuka abin tausayi ,daga taje ta jijjiga wannan sai ta jijjiga wancan" AREEF ta kalla tana kuka tana ganin yadda yake kwance kamar me bacci sai dai baya numfashi, kuka take tana cewa" Dan Allah Yaya katashi kada kacemin bazaka tashiba* Dan Allah kace mafarki nake Yaya,Yaya AREEF kada kacemin tafiya Kai kabarni, Dan Allah Yaya katashi Dan Allah katashi sai da nace kada kafito Amma kaki" yanzu shikkenan narasaka wayyo Allah Ni AFNAN Naga rayuwa, nashiga uku Yaya katashi Dan Allah, idan katafi kabarni wanene zai kula dani waye zai nunamin soyayyar dakake bani, waye zai min wanka yabani abinci, waye zai n'a kula dani yaya sankinkayana Kai ne kagogemin kaccanzamin Kaya ka lallasheni har nayi bacci to yanzu duk wazaimin wadannan " Dan Algirman Allah kada kutafi ku barni Ni kadai Babu uwa Babu uba Babu dangi Babu yayana" to mezanzauna nayi aduniyar ,wayyo Allah na meyasa mutuwa zakimin yankan kauna ,natsani wannan duniyar banason rayuwar Nima mutuwa zanyi" ta karasa maganar tare da tashi dasauri ta nufi bakin titi ta tsaya a gaban wata mota ,wai tataketa ay dasauri doctor da ya biyo bayanta ya janyeta zuwa gefe Yana cewa" AFNAN Wai Baki da hankaline bakisan kaddaraba, luuuuuuu ta sulale a kasa sumammiya Bata ko motsi.

Mutanen dake gurin kuwa bakaramin tausaya mata sukai ba domin tun da suke Basu taba jin irin wannan Abu da yarinyar Nan take fada ba tabbas jikinsu yayi sanyi wasu suna kuka wasu Kuma idonsu duk yacicciko da kwalla.

*LONDON*

"AMEER kabi abin da nace maka kana son ubangiji ya kamani da laifi biyu ne, da ace nasan Haka zata faru da tun wuri na daga Kira sa yanzu Ina Zan samesu BAYAN akunnena naji kamar sunyi accident ne" duk yacce za a Yi yau dinan sai na kwana a KOGI kagane Kuma kubi abin da nace a hadamin kayana sanna ashiryamin jirgi yaudinna saina bar London bazan sake kwana anan ba" shiru Ameer da AYAAN sukayi kowanne yayi tsuru tsuru Yana kallon ikon Allah ,sudai sunsan tun da suke da shi Basu taba ganin mutanen dasuka shiga zuciyarsa irin wadannan ba ko meyasa ,to shi Ina ruwansa da koma mené ta samesu saï kace wani su ne sukayi accèdent d'in AYAAN ya fada acikin zuciyarsa, "AYAAN mekake tunani bazakai abin da n'a saka ba ?" Am sorry yaya ni n'a isa Bari yanzu Zan je nayi" wallahi AYAAN idan ka batamin lokaci bansani mutanennan ba akanka Zan huce Dan kasan sauran.

_ 💋 *AFNAN* 💋______
*Chptar 13*

💃💃*TO!! TO!! TO!! Shhhh*😌 *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*💋*AFNAN*💋WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA 💋 *AFNAN* 💋.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
💋_*AFNAN*_💋
*BOOK one*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.