Complete Hausa Novels

Afnan Complete Hausa Novel

Reading file: Afnan_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 16

*Chapter 9*

_______ "hello doctor AREEYAAN ,kana jina?" Daga can bangaren wani saurayine kekkewa dauke da tell phone a hannunsa ,ka dakaga wanna saurayin kaga asalin cikkakken balaraben usul ,bakinsa ya fara motawa Yana cewa " ba Yaya AREEYAAN bane AYAAN ne "
"To kenan Ina doctor din?" Yanzu Ina kokarin hadaka dashine abin da yasa nakiraka banason kace an wulakanta ka ko mu barka da jira shiyasa nakiraka don n'a fadamaka yayana Yana amsa wayane ta umarceni da nafada maka kabashi nan da minti 5 zai kiraka da asalin number sa" murmushi AREEF yayi yace" oky Tom Babu damuwa Bari zanjira shi" okay AYAAN ya kashe wayar kitt.

"Nafara yadda da abinda hajiya Fateema ta fadamin akan doctor ,yanzu shi Dan zaiyi wani uzurin sai yasa ankirani an bani hakuri Sabi da Kar ya batamin lokaci " ikon Allah ya saka hannunsa a kumatun da Yana zabga murmushi shikadai, jiyayi kamar muryar AFNAN tana cewa" Yaya murmushi me kake"? Dagowa yayi da sauri Dan ya tabbatar itace tayi maganar ,ayko ita dince Dan Haka ya karasa kusa da ita yace "AFNAN kin tashi ?" Sannu ko yajikin naki meyake damunki, ko kina bukatar wani abune?" Lokaci daya ya gigice Yana jefo Maya tambayoyi, wash Yaya dagani inason na maka magana " tom shikkenan kanwaty" ya karasa maganar tare da dagota zuwa jikinsa, "inajinki AFNAN" aziyar zuciya ta sauke tare da saka idanuwanta anashi Tace" Yaya AREEF kayafemin Dan Allah" nayafe Miki Kuna mekikai min!!? "Yaya nakasa jurewa ne shiyasa har takaini da saka hannu a gabana Dan Allah kada kace zakayi fishi Dani" uhm kanwata kenan ayni bana fishi dake Koda nayi ma bazan iya jurewa ba Dole sai na sakko, yanxu dai ba wanan ba albishirinka"? Goro!! Fari ko jaa?" Fari fat Yaya" to nasamu nasarar samun doctor a waya Kuma ma yamin alkawarin Nan da minti biyar zai kirani" hmm. Yaya Allah natsani doctor dinan "? Meyasa AFNAN shine fa Wanda zai taimakeki kisamu lafiya" Yaya Sabi da Yana wahalar min dakai natsani mutum irinsa Allah Yaya natsanesa" Kuma ay Naga lafiya ubangiji ne ke bayarwa ba shiba allah da ta halicceni da wanan abin shiyasan meyake nufi dani kuma shiyake son ganina a Haka, dan Haka koda ace zai min aykinann Banaso nafison nayi zamana a Haka narayu tare dakai cikin farinciki iya soyayyar dakake nunamin ta isheni yayaemin damuwa ta " ta karasa maganar hawaye na bin kuncinta" a,a AFNAN kada kiyanke hukunci cikin fishi Kuma ba acewa antsani mutum sai dai kice kin tsani halinsa, Kuma mu basanin asalin halinsa mukaiba balls har mumasa kallon mutum me wulakanta Dan Adam, AFNAN indai har kina Sona Kuma kin yarda Ni AREEF na Isa dake ki Bari ayi Miki aykinnan" runtse ido tayi ta bude Sana Tace" Yaya duk abin da kakeso Nima inaso Babu damuwa indai kanaso na amince ayimin aykin indai haka shine yafi alkairi arayuwar mu Baki daya"wow kanwata Daman Haka kika iya magana me dadi " Masha Allah Allah yayi Miki albarka"ameen Yaya na "ta Kara rungumesa tsam a jikinta.

*LONDON*

Babban gidan da yakasance daya daga cikin gidajen doctor na kasashe dadama tsayawa tsara kyau da ado da daula irin nagidan Bata bakine, Kai tsaye wannan saurayin Naga ya nufi wata kofa wadda take daga hannun dama' afalon wadda takasance itace kofa ta goma Sha biyu a gurin, shiga yayi dauke da sallama abakinsa ,saikuma yayi shiru can najiyo wata tausasassiyar murya daga ciki ance" yes" cikin nutsuwa ya tura kofar yashiga ciki, Baki nabude tare da sakin yawu kukukut tsabar haduwar dakin da tsaruwar sa dafarko idan kashiga dakin zaka tarasa yar madaidaiciyar loka a gefe wadda Tasha ado da kayan alatu na duniya, sai Gaba Kuma akwai gado Dan karami Wanda befi kwanciyar mutum daya ba ,Amma saidai kana hawansa saikasan ka hau gado ba muna gadoba ,wannan katifar ta kan gadon Kana hawa zakaji kamar a kan audiga kake tsabar laushi ,gefe guda Kuma covar ce itama karama me dauke da murfi biyu ,gaba kidaya jikinta kelkeline n'a gwaldin color, can gefe Kuma kujerace itace wadda na hango mutumin a zaune akai nai daga bayan sa yadda nagansa Zan iya fasal tamuku yanayinsa ,dogone sosai a Haka sai dai Yana da kauri ta sama ma,ana kirjinsa Yana da Fadi,duk da gashin kansa da na ga ya lullube Gaba daya kafadarsa da fuskarsa bana iya tantance wane irin mutum ne, karasawa AYAAN yayi yace" barka da safiya yaya" Kai kawai ta daga masa batare da ta juyo KO yayi magana ba , magana AYAAN yasake yi yace" yaya Yashirya fa ,yakamata ka taimakesa gaba kidaya angama tantancesa yacancanci a karbi aykinsa" kada kamanta Yana jiran kiranka ayanzu" Kai yakara dagamasa ta cigaba da abin da yake still dai be juyo ba ,Juyawa kaninnasa yayi ya fita tare da danna wani abu sai kofar dakin ta rufe.

Lokacin da yafito falon Ajiyar zuciya yayi yace" hooo yayana kenan "wanan mutumin saรฏ a hankali narasa irinsa" daga Haka ya fice daga falon yashiga daya daga cikin kofofin dake falon.

Kilillllll wayar AREEF tashiga ruri, AFNAN ya rungume a jikinsa ya dakko wayar ya ga bakuwar number ,cikin sauri ya daga tare da karawa a kunnensa yace" assalamualaikum" daga can bangaren naji ance" Amin wa, alaikumussalam warahamatullahi"!! Zumbur AREEF ya Mike daga Dan kishin gidar dayayi atsorace harsai da ya tsorata AFNAN besan dan da bakinsa ta kubuce yace "wowwww wanna murya Haka macece ko namiji"? Yaya lafiya ban fahimce kaba me ya tsorata ka Haka" shiru yayi mata tare da saurin katse wayar yace " AFNAN wata daddadar murya naji wadda Tun da nake ko a mace banta ba jin irinta ba" Allah na tsorata"? Kay Yaya tsoro Kuma kirawo muji" kafin takarasa rufe Baki aka sake Kiran sa, hannunsa Har rawa yake wajen cewa hell.... Katseshi yayi dacewa" kana magana da doctor AREEYAAN" zaro Ido AREEF yayi yace" nashiga uku AFNAN kinajin abin da nakeji kuwa"? Yaya inaji Wallahi muryarsa dadadi Anya kuwa mutumne wanan kodan yaga munneman doctor ne yasa mukayi gamo da aljani" Tsaki AREEYAAN yayi ya katse wayar " tare da kirawo AYAAN, duk da bansan abin da yace masaba Amma Naga dai ya bashi waya ya Yi Kira , dagawa AREEF yayi yace Hello doctor?" AYAAN ne yace" bawan Allah kudaina zuzuta ko da daya daga halittar yayana, bayaso "to yanzu kunji muryarsa ma kun gigice ballantana ma kugansa?" Sorry walalhi mun tsoratane" okay to yanzu zai Kara Kira idan yakirawo kuyi Masa bayani kawai ,kada Wanda ya Kara santin muryarsa" daga Haka AYAAN yakatse wayar.

__ ๐Ÿ’‹ *AFNAN* ๐Ÿ’‹______
*Chptar 10*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*TO!! TO!! TO!! Shhhh*๐Ÿ˜Œ *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*๐Ÿ’‹*AFNAN*๐Ÿ’‹WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA ๐Ÿ’‹ *AFNAN* ๐Ÿ’‹.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *โœ๏ธ
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦŠAN GORO*_
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ

_*JARUMAI๐Ÿ’ช๐ŸปWRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ“š*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦ˜asฦ™anci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
๐Ÿ’‹_*AFNAN*_๐Ÿ’‹
*BOOK one*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.