Afnan Complete Hausa Novel
Reading file: Afnan_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 15 of 16
*Chapter 15*
*SAUDIYA*
*MASARAUTAR MANAMI*
_______sarauniya zakiyyace zaune a kishingide a tsakiyar tam kamemen falo na alfarma, falon da yasha ado da kelleli da kayan more rayuwa irin na gidan sarauta, MASARAUTAR MANAMI MASARAUTAR ce wadda Aka ginata kan tafarkin gaskiya da amana ,MASARAUTAR da tayi fice ta fannin taimako da jin kan talakawan ta, MASARAUTAR da Babu kamarta kaf cikin MANAMI.
Tun da yarima AREEYAAN yasako kafarsa bakin falon kamshin turarensa ya daki ancin ZAKIYYA say rin lumshe ido tayi tare da furzar da iska daga bakinta tace" gwarzon MANAMI ya karaso".
Dur kusawa barori da hadimai dama jakadiya saรฏ faman Mika gaysuwa suke wajen AREEYAAN suna kaywa harkasa domin gaysar da uban gidan nasu Kuma sarki mejiran gado, batare da yace komai ba kawai daga musu Kai yake Yana hucewa har ya karaso tsakiyar falon daidai inda sarauniya ZAKIYYA take zaune, batare da ya kalli inda take ba ya nufi wata kofa wadda zata sadashi da bedroom dinsa, zuciyar ZAKIYYA kamar zata fito Dan zafi, afusace Tace" nizaka wulakanta agaban bayi da jakadiya " kawai ta Mike ta bishi har dakin ,motsi yaji ana kokarin shigowa hakan yasa yayi saurin dagowa domin ganin waye" karaf suka hada ido da ita ta sha alkebba ta ruke kugu tana wani jijjige jijjige, bace mata komai ba ya maida kansa kasa yacigaba da abin da yake shine Kiran numbar AREEF , tsaki yaja ya hurgar da wayar a kasa yace "oh God yanzu Ina Zan samu gayenan"? Yafada tare da kwanciya a bed, zakiya kuwa wadda ta daskare a tsaye kwalla duk tacika idonta Tace," Yaya baka ganniba" banza yayi mata bece komai ba, "Yaya maganafa nake maka Amma kamin shiru?" Wata uwar harara ya watsa mata wadda tayi sanadiyyar sa hanjin cikinta kadawa ta fita daga dakin a guje tana kuka, Kay tsaye wani daki tashiga inda ta tarar da wata kekkewar dattijuwa a zaune sanye da glass medical tana karatun Al,qur,Ani me girma, batare da tayi ko sallama ba ta fada cinyar matar ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ta karasa star data ke karantawa ta mai da que,anin Tace" lafiya ZAKIYYA meyafaru?" Ko ke da mutumin nakine?" "Momy Allah Babu abin da ya sauya game da halayyar Yaya AREEYAAN wallahi momy baya sona " tasake fashewa da kuka, "baya sanki kuma shiya fada Miki da bakinsa?" Momy koda ace be fada da bakinsa ba Amma alamu sun nuna ,Yaya AREEYAAN akwai wadda takeso domin agaba na yakira wayarta Taki dagawa shine ya wurgar da wayar ya kwanta Yana tunani, nikuma yashanyani ga banza" wata Kuma tunani fa kikace Kuma nawata, shi son dinne yake wannan abin Kay Anya kuwa" Allah momy dagaske nake bazan Masa sharriba" tom shikkenan kishare hawayenki kirubuta ki ajiye AREEYAAN mijinki ne na har abada'' Koma wacece wadda yakeso be Isa ya kawota gidan Nan ya auraba sai dai ya aureki Dan Haka ki kwantar da hankalinki ke ce sirikata matar son insha Allah" share hawayenta ZAKIYYA tayi Tace " Allah momy da ace zanga yarinyar da yakeso saina sa an saba mata kamanni yadda bazai taba iya gane taba, me tafini idan kyau ne ay nima ina dashi ,idan mulkine mune mulki ,ina tunanin ma yarinyar ba yar kowa bace YAKE faman wahala akanta" uhm kedai nace ki Yi hakuri ki kwantar da hankalin ki yanzu abin da nakeso dake ki jirani yanzu Zan dawo", tom Amma momy Ina Zaki?" Kedai kawai ki jirani kinji" daga Haka momy ta fita ,Kai tsaye sashen AREEYAAN ta nufa wan da yasha ado da kayan alatu Dana more rayuwa, tana shiga kamar yadda ZAKIYYA ta fada mata dawayar AREEYAAN tafara karo akasa yahullar, baki takama tare da karasawa gefan gadon Tace" ah lallai abinda ZAKIYYA ta fadamin ya tabbata gaskiyane ,to idan ma zaka daina tinani kadaina domin Nan MASARAUTA munfitar muka da mata Kuma ita ce ZAKIYYA yakamata kasani domin ka kiyaye"shiru yayi ya zubamata Ido cikin mamaki yace" momy waya ce Miki Haka ita ZAKIYYA ce Tace inasoyayya dawata?" Eh haka tafada min Kuma nasan tsab zaka aykata nasan halinka fiye da yadda baka zato son kayiyayi fishinmu tun da wuri kasauya takunka ZAKIYYA itace mata a gareka nafada maka" murmushin takaici yayi tare da sake kallon ta yace" Ni arayuwa ta banason yarinyar da take Sona ,Kuma bana son yarinyar daza ana tusamin ita idan miji tarasa sai aba data keuta gurin wani Amma ba gurina ba, tun da nake bantaba son ZAKIYYA ba Kuma bazan sota ba Dan Haka Babu Wanda ya Isa yamin Dole anan gidan, Dan ansamu ma nadawo wallahi Kiran mahaifiyata ne kadai yasaka nadawo ban da Haka Babu wan da ya Isa yasaka nadawo daga ita sai maimarta ba karkuyi tunanin nadawo ne domin n'a auri "yarku momy kada ki batamin rai kifita dan Allah " fada tare da Kara tamke fuska, fashewa da kuka momy tayi Tace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un yanzu AREEYAAN ni kake fadawa Haka sabi da ba nice na haifekaba , shikkenan Zan je n'a fadawa ita uwar taka naji in itace Tace kamin rashin kunya..."short up"!!! Ya katseta da sauri tare da daka mata tsawa, yace" kull idan zakiyi maganarki karki sake saka mahaifiyata aciki kiyita iya Ni kurum " daga Haka ya juya tare da furzar da iska ya kwanta be Kara kallon inda takeba.
Ita kuwa momy fita tayi daga dakin azafafe, Kai tsaye Bata Shiga part dinta ba saรฏ ta huce part d'in Dake fece din nata, shiga Tai afusace ko sallama Babu ta tarar da ita azaune tana sallar nafila, batare da tinanin salla takeba ta tsaya akanta tafara surfa bala,I tana cewa" YAYA gurin ki nazo ,sonake naji idan kece kika daurewa AREEYAAN hindi yake abin da yakeso ,harni zaikalla yayi wa rashin kunya kodan bani na haifesa ba "wallahi kijamasa kunne akan lallai lallai yafita daga idon MASARAUTAR Nan ,akanshi akafara yafi kowane dazaice bazai bi umarnina ba shi wane" shiru Yaya babba wadda ke durkushe tana salla tayi ,batare da ta saurareta na taci gaba da yin sallarta har Tai sallama sanan tayi addu,a tukunna ta juyo takalli momy " inajinki " kinajina fa kikace wato duk abin da nake cewa bama kisan Ina yiba kenan?" Lokacin bakiga salla nake ba" to Amma kunnene yakeji ba jikiba ko" walalhi kijawa danki kunne nadai fada Miki" uhm Yaya babba tayi wani kayataccen murmushi n'a bangirma irin nasu n'a manya tace'" ay ina tunanin bana da abin da zan iya cewa akai idan har kin yarda Ni na Isa da AREEYAAN Zan iya Masa magana yaji to Bekamata kizo kaina kinamin rashin kunya ba" muddum kinason AREEYAAN ya girmamaki ya dinga jin maganarki dolene kina bani girmana " Kuma Ni Akan batun aurensa da ZAKIYYA nayi iya nawa kokarin bazan Masa Dole ba kubarshi ya auri wadda yakeso, "llai nayarda kekike goyamasa baya shiyasa yake sharra rashin mutuncin sa a MASARAUTAR Nan ,to wallahi baza a barsa ya auri wadda yakeso dinba ZAKIYYA itace matarsa, "hmm okay gaki gashinan ay kinsan AREEYAAN ba karamin yaro bane sanna koba akan aure ba shi ba a Masa Dole abin da yaga yafi dacewa da shi shiyakeyi bawan da mutane suke soba, Dan Haka idan kuka cigaba da takura Masa ayau dinna kunsan ya dawo ko, to ba karamin aykinsa bane ya Kara tattarawa yatafi wata kasar" tsaki momy tayi kawai tafice domin gani take idan ta tsaya biyewa uwa da danan zasu sakamata ciwan zuciya Dan Haka ta Kuma dakinta.
A bangaren AREEYAAN kuwa runtse idonsa yayi Yana faman tuni yadda za ai ya samu hanyar da zai fara neman AREEF ,Taya kennan gaskiya yakamata duk yadda za ay nafara neman hanyar da Zan Nemo mutanen Nan, to Amma suna Raye ko sun mutu, najifa kamar hatsari accident dukayi, Yana tsaka da wanan tunanin yasaka wancan ya warware wanan saiga Yaya babba ta shigo, da dago Ido yayi ya kalleta tare da mikewa cikin nutsuwa ya sakko kasa ya ce" barka da shigowa ya mahaifiyata dafatan nasameku lafiya" lafiya kalu alhamdulillah ya ahanya tun da dai Naga baka shigo ba shine nace Ni Bari nazo na gaysheka" am sorry Ammi wallahi yanxu nake Shirin shigowa" Yar dariya tayi Tace " harma Kashi go ay ,yaron kirki nace meya hadaka da momyn Kane yau naji kanku"? Uhm yayi kwafa ya sosa Kai azuciyarsa yace "lallai ma wanan matar wato zuwatai ta hadani da mahaifiyata " afili Kuma yace" uhm ammi bakomai kawai akan abin da suke sone nikuma banaso Kuma kinsan kema bayadda za ay kazauna da abin da bakaso" hakane kayi gaskiya Amma ita wadda kakeso Yar gidan wacece agarinan ko Yar wace MASARAUTA ce"? No Ammi ni haryanzu bansamu wadda nakeso ba tukunna dai idan da dama abari nadanyi nazari " oky amma dai kadan baza abarka kaitazama a hakaba ko?" Eh hakane Amma Dan Allah kinema min alfarma gurin memartaba abani Nan da five weeks nagani" uhm shikkenan Zan gwada nagani, amma dan Allah Kari kokari samo matar dazaka aura a wanan lokacin da kadauka daman anacewa dasa hannuna kakeyin komai bayanni Babu ruwana, idan baka samoba lokacin da aka baka yaceka komene aka ce za a maka Babu ruwa na sanan Ni dakaina Zan baka umarnin auren ZAKIYYA " Kai a,a ammi insha Allah ma zansamu kafin wanan lokacin nagode sosai mahaifiyata Ina alfahari dake " yafada tare da komawa kangadon ya kwanta ,ita Kuma Yaya babba ta fita daga dakin.
*KOGI LAKWAJA*
_ ๐ *AFNAN* ๐______
*Chptar 16*
๐๐*TO!! TO!! TO!! Shhhh*๐ *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*๐*AFNAN*๐WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA ๐ *AFNAN* ๐.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *โ๏ธ
๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ฦAN GORO*_
๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ๐ผ
_*JARUMAI๐ช๐ปWRITER'S ASSOCIATION๐*_
_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar ฦasฦanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
๐_*AFNAN*_๐
*BOOK one*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.