Complete Hausa Novels

Afnan Complete Hausa Novel

Reading file: Afnan_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 16

*Chapter 8*

_______zuciyar AREEF tukuki take kamar zata fashe Dan bakinciki ,magana yafarayi shika dai kamar wani Mara hankali Yana cewa" why "Ina Zan ganka "shin Kai wanene ?" *BOSS MAN* lion* waye Kai meyasa kake buya Dan Allah ka bayyana min kanka" hannu yakai ta shafa fuskarsa saï ji yayi yatabo danshi a fuska ashe hawaye yake shi bema sani ba. Yana tsaka da wannan tunanin ne yaji shigowar numbobin hakan yasa yayi saurin dubawa ,wadda akasa *boss man* yafara Kira ,abin mamaki itama dai tana shiga Amma ba a dagawa, Dan Haka ta dauki numbar farko da doctor ya bashi ya Kira itama tana shiga, number da alhji ilu ya bashi takasar *America* itama Kira yayi tana shiga ba a daga ba, wannan abun yayi masifar kullemasa Kai "to kenan Aina yeke da zama acikin gaririwannan guda uku sannan Taya ake duk numbobin suke shiga" to idan hakane rainamin hankali kawai ake mutuminnan baya Raye kawai wahalar Dani suke, to idan baya rayé taya akai sunansa yazaga duniyoyi da dama, ni narasa kan abinnan mutanennan so suke su hauka Tani , kwakwalwa ta takasa daukar abin da nake ji ,Amma Bari itama matannan na gwada Kiran ta itama Naga gudun ruwanta" naji abin da zata cemin.

Number hajiya Fateema da aka Tura masa ya shiga Kira bugu daya ta dauka tare da yin sallama, Kai da kaji muryar matar kasan ta Dade a duniya ,yanayin muryarta da yadda take magana Yana nuna alamar tsufanta, Amsa sallamar AREEF yayi tare da yimata bayanin abin da yake nema, cikin zakuwa tsohuwar Tace "waye Kuma *boss man" niban sansaba?" Eh dama ance baya taba amfani da suna daya a garuruwa biyu Ina tsammanin kema da wani sunan kika sanshi ba wannan ba,amma shidai likitan *Dick* ne!!.

"Oh saï kacemin *DOCTOR L .B.M. AY".
"Me wannan wane irin sunane Haka Taya Zan sameshi"? Dagaske Yana Raye"?
"Tabbas *doctor AY* Yana Raye Kuma Ina tunanin duk wani nemansa da kake yasani "
"Yasani Kuma"?
"To Amma meyasa bazai bayyanamin kansa ba, nasha wahalafa ko ince Ina kansha"
"Hmm bakasan wane shi ba shiyasa kake tunanin Haka "
"To wayeshi"
"Bansani ba nidai nasan bataba ganinsa sau uku shima duk karshen shekarane lokacin Ina saudiya "
"Okay yanzu Ina Zan sameshi?"
"London"Yana can Ayanzu inda zaka samesa idan kajene bani da tabbaci"
"To kenan ke ma number Zaki bani nashiga uku nidai Naga takaina wannan ko Aljanna zai bani ay janran ya Isa Haka , agaskiya wannan mutumin Yana da girmankai da takama".
"Ko kadan *AY* ba Haka take ba idan yagama tabbatar da aykin dakakeso amata da gaskene da kansa zai zo har inda kake yasameka"
"Hmm bazaki gane ba madam wannan mutumin nayarda ya huce inda nake tunaninsa yau kusan sati biyu fa kenan kullum cikin Kiran layikansa nake akullum sai na turamasa message ko da Zan samu ya taimakeni Amma Ina kullum shiru ,Yana tunanin ba da gaske bane zanta bawa kaina wahala akan nemansa ko yayi tunanin so nake naganshi kawai Dan naji dadi nifa namijine ba mace ba balle yace ina nemansa ne dan wata bukatata".

"Dagaske har yanzu baka Yi abin da zaisa *AY* ya taimakeka ba ko yayarda da abin da kazo dashi"
"Me yakamata nayi akai kenan" ?
"Sunansa muddum kanemo asalin sunansa ka turamasa message da wannan sunan wallahi summa tallahi ko minti 5 bazaka karaba alokacin saika ga kiransa"
"Sunansa Kuma to kenan wadannan sunayen ba sunansa bane ,to mené amfanin nemo sunan?"
"Sunansa Yana da amfani kafcikin nahiyarna daidaikun mutanene wadan da suka san asalin sunansa Wanda iyayensa suka rada masa, koni kaina bansan asalin sunanshi ba ,
"Aina zansamu sunan nashi?"
Kaje kaduba duk wata kafa ta sadarwa idan Allah ya taimakeka zakasan me asalin *AY* take nufi idan kayi Haka tabbas zai yarda aykin da gaskene tun da har kanemo asalin sunansa Dan bakowane yasan waye shiba"
"Tom shikkenan madam nagode kwarai da gaske yanzu ki turamin number tashi ta kasar *London* din saina jarraba".
Daga Haka sukayi sallama ya katse wayar.

***
Zama yayi ya kalli bangon dake fece din inda yake kome yake tinani oho ,can Kuma sai Naga ya dauki wayarsa ya rubuta *L.B.M.AY* kurawa sunan idon yayi Yana nazarin abin da sunan yake nufi can Kuma sai Naga ya dauki letter (L) ya saka _Lion a Gaba itama Letter(B) din sai yasaka _boss sannan ya dakko itama (M) yasaka nata _man daga Nan kuma sai ya tsaya domin besan me *AY*ke nufiba, TIKTOK yashiga yiyi search din Lion be fito ba, sai ya sake searching din boss man shima be fito ba, haushine ya kamasa Dan Haka ya koma FECBOOK nanma yayi irin yadda yayi a tiktok Amma shiru kakeji ,kansa ya Dora a tsakanin gywoyinsa yatafi duniyar tunani, Can kuma kamar an tsikareshi ya Mike yace" Kay to ay in hakane naje you tube Mana " cikin sauri ya shiga yin searching din likitocin *dick* na duniya Baki daya ,sai gashi an watsomasa mutane da dama', shigarsu ya dingayi Yana duba video din har yazo kan wani vidéo da baka ganin komai sai duhu tsaki yayi ya kashe wayar ya kwanta agurin Yana tunani, sai Kuma yace" kardai wannan video din shine ,mutumin da be yadda asan sunansa bama shi zai yarda aga fuskarsa"? Tabbas ko shine ,Mike wa zaune yayi har gumi yake faman hadawa wajan kunna data hannunsa kuwa harrawa yake wajen danna video, kunnawa yayi yaji anfara magana Amma Bata ganin komai sai duhu " ASSALAMUALAIKUM" INAYIWA YAN,UWANA MAZA DA MATA BARKANKU DA ZUWA WANNAN TARO ME ALBARKA ,WADA ADUK SHEKARA NASABA HALARTARSA AKASA ME TSARKI WATO SAUDIYA, TO DA FARKO DAI SUNANA *AREEYAAN NOOR MUTALLAF* WANDA AKAFI SANI DA BOSS MAN WASU KUMA DAYAWA SUNA KIRANA DA LION KO AY.... Ay tun da AREEF yaji wannan sunan nasa na asali ya tabbatar da shine wan da yake nema yasa ya katse video din tare da ajiye wayar a gefe ya durkusa yayi sujjada Yana Mai yiwa Allah godiya da ya nunamasa wannan Rana. Mikewa yayi ya dauki number da hajiya Fateema ta turamasa yashiga rubuta message kamar Haka.

"ASSALAMUALAIKUM" inamaka barka da wannan lokacin sannan Ina maka fatan alkairi,nine dai AREEF Wanda akullum yake cikin nemanka Kuma bana gajiya da nemanka harsai ka fuskanceni ,doctor AREEYAAN wow suna me dadi inafatan kamar yadda kake da wannan sunan yasa ganinkama yaxamemin me kyau , ok nafatan kataimakeni kataimaki kanwata domin kayi mata ayki nagode ".
Daga Haka AREEF ya tura message din.
Cikin minti 2 yaji Kira ya shigo wayarsa ,Yana dubawa wazai gani doctor...... Bakinsa da jikinsa har rawa suke wajan daukar wayar yace "alhamdulillah Allah nagode maka Ashe dama' zanga wanan ranar "hello doctor AREEYAAN!!!!.

__ 💋 *AFNAN* 💋______
*Chptar 9*

💃💃*TO!! TO!! TO!! Shhhh*😌 *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*💋*AFNAN*💋WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA 💋 *AFNAN* 💋.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
💋_*AFNAN*_💋
*BOOK one*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.