Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt

Chapter 15 of 40

*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)

1⃣5⃣

Ubangiji ya kar6a addu'ar Aysha hajia babba ta amince suje Kano suwuni Dan da driver ma aka had'asu yakaisu, bak'aramin gargad'i Aysha tasha barazana.
Haka sukatafi itada gwaggo bintu da yakubu direba. Kasancewar tafiyar asuba sukayi k'arfe 11:24am acikin birnin Kano tamusu, amotama gwaggo bintu nata kwakwkwafar Aysha.
Ita Aysha ma dariya suke bata wlhy, kokad'anma batadamu da fargabarsuba, damuwarta tafi karkatane da d'okin san ganin mamanta da ummah, saikuma yayunta tunda tasan k'annenta duk basa cikin Kano yanzun.
Motar natsayawa kojiran yakubu yagama parking batayiba tafice da gudunta tana kwala kiran sunan ummah da mama.
Ummah Ce kawai a tsakar gida tana tace kullun awara dasuke sonci yau, mama kuma tana bayi, Aysha tadaka tsale tad'ane ummah tana fad'in wayyo ummanah nayi kewarku wllhy.
Tuni Ummah tasaki abin Tatar tarungume Aysha itama, suduka kukan farinciki sukeyi, mama jin karad'in Aysha yasata fitowa da hanzari.
Aysha tasaki ummah taje tamak'alk'ale mama, adaidai nan gwaggo bintu tashigo, ganin yanda Aysha tad'ane mama yasaka gwaggo bintu ta6e baki.
Da k'yar Aysha ta iya sakin mama, su saima yanzu suka lura da gwaggo bintu daketa wani 'yan yatsine-yatsine, sunsaba da halinta shiyyasa suka watsar da lamarinta suka mata tarbar mutunci su.

Dukda Aysha tana fuskantar wahalhalu agidan Alhaji Abdallah, hakan baihana jikinta murjewaba, tak'ara girma da k'iba, ga hasken fatarta yak'uru sosai Dan Aysha farace tas dama, yanayin canjin abinci darashin yawo arana saiya k'ara hasken NATA, Aysha doguwace gaskiya dukda dai ba irin shantaleliyarnanba, idan zata tsaya kusadasu ya khaleel dogaye sosaima baza'aga tsawontaba, farace tas kuma k'yak'yk'yawa, tana masifar kama da mama, Aysha batada k'iba, amma k'ila zuwa nangaba idan hankalinta yakwanta tak'ara girma zatad'an k'ara k'iba fiye da yanzun, a6angaren k'yawun fuska kam ba'a magana komai yaji masha ALLAH, tanada manyan idanu da dogon hanci, ga zara-zaran gashin ido masu d'aukar hankali, idan Baka saniba saika rantse tak'arane, kuma natane, idan Aysha tak'ara girma zuwa nangaba dolene akirata sarauniyar mata gaskiya.
Mama taji dad'in ganin yanda Aysha tayi k'yau, wannan yasaka hankalinta k'ara kwanciya dazaman Aysha gidan Alhaji Abdallah, tasan yanzu hankalin d'iyar tata akwance yake tunda gashi har za'akaita makaranta k'asar waje itada yarangidan. (Nace hummmm kedai mama abar kaza cikin gashinta kawai, su gwaggo bintu sundai tsarakune).

Sai wani dama-dama gwaggo bintu takeyi da Aysha saboda gudun karta fad'i wani Abu, su mama basu kawo komai aransuba, gwarama Fadeela da Hafsat sukam saisukaga kamar Aysha nacikin damuwa, amma gaba d'aya gwaggo bintu tahana Aysha sakewa barema tafad'a, dak'yar gwaggo bintu tayarda Aysha tashiga makwafta ta gaidasu, Duk ida taje sai sha'awar kyawun data k'ara akeyi, itadai batacewa komai saidai dariya, damacan asali Aysha bamai yawan surutu baceba, idan kaga tafiya magana akan Abu tofa takai makurar cutuwa dashi, bayan sallar azuhur suka ajiye uwar tsaraba da hajia babba tayimusu sukai sallama Aysha nakuka suka taho, jitayi kamar kada tadawo Abuja ma, amma tanason tacigaba da ganin ya khaleel koda daga nesane, tunda tafara ganinsa yake bala'in birgeta. (Hummm Aysha miye sirrin🤔?.)
Sunbiya tagidan kawu bilyamin, suntarar yaran gidan duksun tafi islamiya tahfiz, suma su Aysha sunayi sanda mahaifinsu Nada rai, amma yanzu rashin gata dukya ruguzawa rayuwarta wannan tanajin.
Aysha bataji dad'in rashin ganin su sadiyaba, tayi kewarsu sosai, amma yazatayi.
Tunda suka kamo hanyar Abuja takifa kanta da guywa, ahankali taketa rera kuma maiban tausayi da tsuma zuciya.
5:pm suka iso abuja.

Hummm abinda yabama Aysha mamaki bai wuce ganin sunnufi wata anguwar dabanba sa6anin maitama.
Abinda Aysha bata saniba shine bayan tafiyarsu Kano hajia babba tasanar da 'yan gidan cewar Aysha bazata dawoba, wai k'anin mahaifinta yace makaranta zai sakata.
Lamarin ya Sosa zuciyar aunty Mamie, takumaji haushin gwaggo bintu sosai tunda bata sanar da itama Aysha zataje gidaba, dama tanada k'udirin saka Aysha amakaranta, jiratake hankalin ya khaleel yakwanta tasakashi yasamoma Aysha school mai k'yau, to gakuma abinda yafaru.
Tunda Aysha tagansu a gidan hajia kaltum jikinta yayi sanyi, lallai tasan yau tafaru ta k'are kam, kukadai tashashi awannan daran, tayi mai isarta tahak'urema ranta.

____________________

Ahanzarce yafito daga 6angarensu, kansa ak'asa yana k'ok'arin d'aura agogonsa, sanye yake cikin Uniform d'in aiki, kayan sunmasa matuk'ar k'yau da fito da kwarjini dacikar haibarsa, duk bin kwankwantonka baka Isa banbance turaren da ya khaleel ke amfani dashiba, akowane lokaci dasabon k'amshin turare zakajishi, hakan yana cikin dabarun aikinsa.
A'a babana saurin mikakeyi hakane?.
Wlhy aunty IG ne yamin kiran gaggawa, shinefa nake hanzarin fita, security na jirana awaje.
Amma duk saurinka yakamata ka karya koda kad'anne, yanzu hakama bakasha maganinka ba, wannan ciwon dakake rainawa idan baya samun kulawar magani saiya girmama.
Hular hannunsa ya matse a hammta tareda had'e hannayrnsa biyu alamar rok'on tabarsa yatafi🙏🏻, please Mamie.
Aidama bahanaka tafiyar zanyiba agogo sarkin aiiki, bara nahad'a maka katafi dashi office d'in, katabbatar kuma kacishi.
Kai Anty Mamie, saikace wani d'an Nursery school?.
Dariya aunty tayi batareda tabashi amsaba tafara had'a masa break fast acikin lunch box, shikuma yanufi gaida sauran masu gidan.
Momy ma tafita aiiki, su Anty zuwairah kuma basu tashiba, da Hameedah kawai yagaisa itama tana shirin fita aikine, Umme ma tafita aiki, baidad'eba a 6angaren Ammah, yashiga wajen Baffah.
Yana zaune afalonsa yanajin labarai a redio ya khaleel yashigo, cikin girmamawa suka gaisa.
Baffa yace, "har za'a fitane mu'azzam?.
Eh wlhy baffa yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
To ALLAH ya tsare manaku, nagama wannan karon kadad'e ak'asar?.
Eh wlhy inada ayyukan cikin gida 9ja sosaine, amma dukda haka zanje Indonesia nextweek, daganan nabiyo ta france, zandad'e sosai a Najeria wannan karon.
To masha ALLAH, kaga kenan ad'an lokacinnan saikayi aure tunda zaka dad'e.
Shafa kai ya khaleel yayi, fargaba dukta cika masa zuciya, bai iya cewa komaiba.
OK idan tsoron matan kakeji saina duba maka, dama ance police akwai tsoron mata, Ya hannun naka?.
Hannu da sauk'i baffah, ya amsa maganar k'arshe Dan gusar data farko.
Dariya baffa yayi, tashi kaje kada ka makara, zamuyi maganar a tsanaki....
Kafinma baffa yarufe bakinsa har ya khaleel yamik'e kamar Wanda yake zaune acikin wuta.😂
Baffah madai abin yabashi dariya, amma saiya murmusa yanabin khaleel d'in dakallo harya fice.

Yauwa Anty bara nawuce, asaka yariyarnan tagyarmin d'akina yayi datti sosai, musammanma bathroom d'ina.
Wai Aysha kake nufi?.
Ni banma san sunantaba Anty Mamie, amma farar dai. eh ayshace.
Bata nan, takoma Kano wajen iyayenta, saidai bishirah tagyara kokuma cikinsu Amal.
To Mamie, amma yaushe takoma? yana tafiya.
Jiya-jiya, takoma makarantane wai.
Yaje daidai fita falon yace shikenan su Amal su gyaramin idan basuda school saina dawo.

Motocine guda uku ak'ofar gidan, yana fitowa sauran security suka shiga Sara masa, hannu kawai yad'aga musu yana gyara zaman hularsa akansa, bak'aramar kamala da kwarjini hular tak'ara masaba, aka bud'e masa motar tsakkiya dasauri yashiga ya zauna.
Aguje sukabar anguwar, jiniyarsu dukta karad'e kunnuwan jama'a.

A office d'in IG yak'ame tareda yimasa salutes, IG yakar6a ma ya khaleel shima tareda nuna kujerar gabansa yana fad'in J! bismillah.
Zama ya khaleel yayi, IG yamik'a masa hannu suka kumayin musabaha.🤝🏻, ya hannu?.

Alhmdllh sir.

Yauwa J! Koka tatsi bayanai daga David kuwa? Dan nasan yanada iyayen gida.
Yes sir, nima nayi nazari akan hakan, amma ban binciki komai agareshiba dama sai yau. kamar yanda yaransa yafad'a akwai manyan k'usoshin gwamnati da 'yan kasuwa dake tareda David, amma ya tabbatarmin baisan kowaba acikinsu, Dan aikin sirri sukeyi da David, kuma baya barinsu su yaransa Susan komai akan hakan.
Saidai nad'an samu wani solution, amma kamar yanada rauni.
OK nami kenan? Miyasa kuma Baka yarda da ingacinsaba?.
Saboda ban tabbatarba, dama Akan wani Alhaji ne, Dan ana gobe zamu kama David naje club d'in dashi David yake zuwa inhar yana 9ja..
Dayake Amashin naje wajen, lokacin danake k'ok'arin shiga ciki shikuma motar Alhajin nafita, nakuma ga fuskarsa.
Abinda yasa nazargi Alhajin nacikinsu, nayi hira dawata yarinya a cikin club d'in ta tabbatarmin da cewar club d'in na David ne, duk kuma Wanda nagani awajen yanada alak'a dashi.
Anawa kuma tunani babu yanda za'ayi mutum mai daraja kamar alhajin Dana gani, inhar bashida alak'a da David yace zaizo wajen, tunda yanada kud'in daza'a kaimasa mata har gida ko hotel, babu kuma alama data nuna yasha wani Abu alokacin, balle muce shaye-shaye yakaisa wajen.

Jinjina kai IG yayi, cikin gamsuwa da bayanan ya khaleel yace, "yes kanada tunani maik'yau j!, so yakamata asakama Alhajinnan idanu, nasanka zaka gano inma yana taredashi, Dan nayarda dakai 100%, kasan aikinka.

Thanks you sir! Ya khaleel yafad'a cikin nuna alamun jin dad'i dayabon ogan nasa.
Jin jina kai IG yayi tareda mik'ama ya khaleel wani file, ga wannan file d'in, Case d'in yaron nanne Mansur Lawan, Wanda aka kama da coken a airport d'in Nijer, so inaga zasu bamushi nanda 2weeks k'ila, saikayi k'ok'arin bincike akansa shima, amma zaka samu had'in guywar hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta k'asarnan, ya mik'o masa guntun pepper, ga number shugaban hukumar nan, kayi k'ok'arin Ku had'u, kokuma ka wakilta Wanda kayarda dashi, dannasan aiki yamaka yawa.
OK sir, zanyi k'ok'ari insha ALLAH.
ALLAH ya taimaka Ibraheem Abdallah jigawa, I'am proud of yau akowane lokaci, ina yabawa da aikinka danka cancanta.
Musabaha sukayi sannan ya khaleel yafita zuwa office d'insa..................🖊

*Rashinyin comments nawasu groups zaisa narage yawan typing , nasan kuna karantawa amma babu comment, sai k'alilan acikinku sukeyi, agaskiya bazai yuwu na ajiye ayukana nazauna INA typing wani lokacin har 2times yazama babu wani nuna alamun jin dad'inkuba.*
*sannan inhar buk d'innan yay nisa bazan kuma turama wani ta PC ba, bazan iya had'a typing da posting ba sannan kuma ana bina PC ana rok'on naturo, ina jin kunyarku amatsayin masoyana, amma gsky zuwa nagaba zansaka bak'in Google😎.*

ALLAH yasa mudagyara.

😻😻😻😻😻😻😻😻
[8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.