Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt
Chapter 34 of 40
*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)
_Kuna raina *HAUSA NOVEL FARIN CIKI* kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._
_ina yinku aradu_😍😍😘
3⃣4⃣
To masu iya magana nacewa d'a da mahaifa sai ALLAH, hakance tafaru da meerah, dukkan wani 6acin ranta da tsanar mahaifiyar tata datayi, hakan bai hanata kwace hannuntaba dagana ya Naufal tanufi mama da gudu tana kuka, kanta tafad'a tana rubzar kuka mai matuk'ar tada hankalin mai saurarenta.
Ya Naufal dasu Aysha duk sunyi tsaye suna kallonsu, wasunsuma kuka sukeyi suma.
Kusan mintuna 4 meerah da mama nata kuka, kuma suna'a rik'e da junansu.
Ganin kukan zaiyi yawane yasaka mom matsawa ta janye meerah daga jikin mamar saboda ganin halin ciwo da mama take aciki.
Rasa inda mama zata ajiye wad'annan 'yan gayu tayi, sukam su mom babu ruwansu, tabarmar dake a falon suka zazzauna, Raudat cedai keta kuka saboda zafi bata sababa, gashi dama yaud'in da akwai rana.
Maheer daketa faman jijjigata akan tayi shiru yace waimike damun Raudat ne? Dukta rud'e wlhy.
Mom tamik'a hannu ta kar6eta, cikin hausarta dabatama iyaba sosai tace maybi zafine, tafara k'ok'arin cirema yarinyar Riga, mafici mama tamik'o Dan ama Raudat fifita.
Dad yakar6a yana fifita Raudat data fara rage kukan tana sauke ajiyar zuciya ajikin mom, kai kace wata babbace.
Saida ta tsagaita da kukan sannan mom tamik'ama ya Naufal dake kusada ita, Naufal mik'ama Meerah tabata abincinta.
Kar6arta yayi tareda sumbatar goshinta, my dear mah-mah sorry kinji, zafine kawai yamiki yawa nasani, yamik'ata wajen Meerah da gaba d'aya hankalinta na'akan mamanta.
Saidama ya zungureta sannan tajuyo tana kallonsu shida d'iyar tasa, da ido yamata nuni yunwa.
Batace komaiba takar6eta tad'ora a cinya, mama dai tana kallon ikon ALLAH, da al'ajabin abinda ke shirin faruwa, wai Meerah da d'iya.
Bata k'ara gaskatawaba saida taga tafara shayar da yarinyar sannan.
Dad datun d'azun yake kallon mama a sace, yadai daure yace nikam baiwar ALLAH Na tambayeki mana?.
Mama tace ina saurarenka Alhaji.
Dad yagyara zamansa, yayinda duk idon yaran ke'a kansa Dan mamakin furucinsa ga maman meerah.
Yanisa sannan yace, kama kikemin dawata a sokoto mai suna Zainabu 'yar Dije.
Mama da idonta yacika da hawaye, tace tabbas itace, kuma tunda kashigo nake maka kallon Sani, saidai banida tabbas akan ko yahaya ne k'anin malam Abdul'majedu?.
'Yar zabura dad yayi, bakinsa har rawa yakeyi yace tabbas shine, Abu kina nufin da gske kece?, ina d'an uwana Abu? Kardai kice Ameerah jini nace? Karki cemin haryanzu baki canjaba Zainabu?.
Inna lillahiwa'inna ilairraji'un, dad yashiga ambata yana hawaye.
Tofa falo yayi tsit ana kallon ikon ALLAH, mama da dad duk kuka sukeyi, Wanda babu Wanda yasan ma'anarsa cikinsu ya Naufal..
____________________________
Tunda suka zo gidan gwaggo bintu batada lfy, wannan yasaka matan gidan babu Wanda yasan da zuwanta gidan.
Sun sandai zuwairah tazo, itakam dama babu matar datake gaidawa agidan, saima tazo tagama zamanta baifi tahad'u dasu Anty Mamie sau uku ba, shima sai idan tata ta fiddota daga 6angarensu, amma bada nufin gaida matan gidanba, to yanzuma girma yak'aru ga daraja, saboda dawowar mama tayi alk'awarin tadaina shiga 6angaren ko waccensu.
Iya hama ce takaima mama gulmar dawowar Gwaggo bintu gidan, harda halin datake ciki.
Anty Mamie akwai tausayi. Wannan yasaka hankalinta tashi tanufi gefin masu aikin taduba gwaggo bintu, ganin halin datake ciki yasakata kiran Hafiz yayi driving nasu zuwa asibiti itama tana nan tahowa zata gama wani aiki.
Hafiz yad'auki iya hama da gwaggo bintu dake kashir6an cikin halin rashin lfy yatafi.
Komai shiyayita k'ok'ari aka mata, har aka basu gado, sai a sannan Anty Mamie ta k'araso itada ya Zunnurain daya kawota.
Da taimakonsu aka kammala komai, gwaggo bintu tafara samun kulawa.
___________________________
Saida sukayi kuka mai isarsu sannan falon yay tsit, dad yace Abu miya dawo daku Kaduna? Nidai nasan harna bar k'asarnan kuna sokoto?.
Hawaye mama tashare, cikin nadamar abinda ta aikata tace yahaya ka gafarceni, tabbas ni azzalumace, kuma na cutar dakai kaida d'an uwanka.
Tabi su ya Naufal da kallo tana hawaye, tace bara nabaku labarin wacece zainabu 'Yar dije.
*Tuna baya*
Kamar yanda kuka sani mu 'yan asalin sokoto ne, amma a k'aramar hukumar Gwadabawa, Ni bama cikin gwadabawa nakeba, ina awani k'auyene Bamana, tallar kayan koli ke kawoni cikin gwadabawa, a k'auyenmu na Bamana babu Wanda baisan Zainabu 'Yar dije ba, tun ina k'aramata banajin magana, Dan ko'a gidanmu babu Wanda ya isa yasani nayi, babata dije bata yarda ko hararata ayiba agidan, kasancewar nikad'ai tahaifa aduniya.
Tallan kayan koli danake zagawa k'auyika da cikin gwadabawa yasaka idanuna suka k'ara bud'ewa, kokad'an bansan bariba.
Ayawon tallata nahad'u da Abdul'majedu, soyayya kuma tak'ullu a tsakaninmu, har akayi aurena da Abdul'majidu danginsa basason auren, musammanma yahaya, Dan yasanni sosai, idan nakawo talla har majalissarsu nake zuwa.
Wannan k'iyayya da yahaya ya nunamin yasakani tsanarsa, kokad'an bana raga masa bayan na auri yayansa, kullum babu abinda nakeyi sai had'asu fad'a, saidai abdul'majidu baya kulawa.
Hakan yana k'onamin rai, dan aganina Abdul'majidu yafison k'aninsa dani.
Saida mukayi shekaru goma bansami haihuwaba, zuwa sannan yahaya yayi aure. Harma matarsa tayi 6ari, 6arin datayi yatada hankalina, gashi tafini samun jin dad'i ajaken mijinta, hasalima arzik'insu mikeci.
Wata ranar talata muka tashi da alhinin rasuwar mahaifiyarsu yahaya, sosai yahaya yayi rawar gani akan hidimar rasuwarnan ta mahaifiyarsu, yabon da akaitama yahaya awajen rasuwar ya6ata raina Dan haka na kullaceshi a zuciyata.
Shiryawa nayi naje k'auyenmu, na fad'ama tsohuwata komai, ita tabani shawarar abinda yakamata nayi yahaya yabar gidan, shawararta kam tayi tasiri, Dan ina dawowa washe gari nakira yahaya d'akina akan zamuyi magana, lokacin Abdul'majidu baya gida.
Saida yashigo d'akina da sallama, ina la6e abayan labule nikam, yayta sallama nak'i na amsa mishi, saiya nemi guri ya zauna Dan azatonsa ina band'akine.
Ina nan ala6e ban fitoba saida naji motsin dawowar Abdul'majid, wuf nafito natsala ihu ina kiran kwarti-kwarto.
Kankace mi gida yacika da jama'a, yahaya dukya rud'e, mutane kuma sai tsinarsa sukeyi, babansu harda kuka da matarsa, awannan karonkam Abdul'majidu ya yarda yahaya yazo kwartanci d'akina.
Sannan ya haddasa fad'a sosai a tsakaninsu, ko kad'an Abdul'majidu yak'i sauraren yahaya, gashi ina k'ara kunna musu wuta daga gefe.
Matar yahaya kuwa takoma gida, tace bazata iya kallon wannan abin kunyaba, daga Bayama sai iyayenta suka nemi yasaketa.
Gwadabawa tayima yahaya zafi, babansu da yayansu suna fishi dashi, ga matarsa anrabasu, wannan yasa yashirya batareda sanin kowaba yabar Gwadabawa.
Wayyo hakan yamin dad'i, daga nan duniya tazama sabuwa agareni.
Shekarun yahaya kusan uku dabarin gida mukaji labarin wai wani Alhaji yatafi dashi k'asar waje, sai da naji babu dad'i, Dan banason naga yahaya yacigaba arayuwarsa.
Alokacin kuma gaskiya tafito. Mahaifinsu yahaya yasan gaskiyar magana akan tuggu nashiryama yahayan, abin ya6ata ransa, harya kwanta ciwon dayazama ajalinsa.
Tundaga rasuwar baba muka fara fuskantar matsaloli a k'auyenmu, sai zagina akeyi, shima kansa Abdul'majidu bai tsiraba, ahaka ALLAH yabamu ciki alokacin, munyi murna sosai kuwa, nahaihu da kwanaki 9 babata dije tarasu, nashiga tashin hanakali sosai, dama itace me k'arfafamu, aikam rasuwarta garin gwadabawa yagagaremu zama, dole muka d'akko d'iyarmu Suwaiba muka gudo sainan Kaduna...........
Kaf takwashe labarin zamansu na Kaduna tabamasu dad labari, harda barin Ameerah k'asar.
Da bala'in data shiga bayan tafiyar Ameerah, yanzuma basusan inda Suwaiba takeba, 'Daheera kuwa tazama 'Yar shaye-shaye, k'annen Ameerah biyu kam tuni suka koma sokoto, itakuma taita ciwo, dak'yar tasamu makwafcinsu ya taimaka mata zuwa asibiti, shine akace tanada ciwon sugar (diabetes), anasakamin dokoki akan abinda zan ringaci, amma nak'i bin doka, saboda lokacin duniya nakaimin, akwai kud'i a hannuna, shekara ta 2 kenan wani maruru yafitomin, yayi ruwa anmatse, amma saiya k'ara wani ruwan aka matse, yak'arayi, hakadai yayta girma harya zamemin gyanbo ak'afa, ganin k'afata zata ru6e nahad'a dukkan kaddarar dana siya dakud'in tafiyar amirah nasaida, shine makwafcin nan nawa mutumin kirki yasake kaini asibiti aka guntule k'afar, Dan since zata harbi dukkan jikina...
Tak'arshe maganar da rushewa da kuka.
Labarin ya girgiza su Naufal, mom kanta dabawani jin hausar takeba sosai saida tayi kuka, da mamakin wannan murd'ad'd'ar rayuwa.
Shima dad yabata labarin cigaban daya samu tundaga barinsa gida, har zuwansa turai, da karatu dayayi, yanuna mata matarsa daduk 'ya'yansa, harda had'uwar Naufal da Meerah a islands UK, Dama auren dake tskaninsu, harda k'yautar Raudat da ALLAH yabasu.
Mama tak'ara fashewa da kuka, da jinjina Girman mulkin ALLAH, tana Neman gafarar ameerah tana kuka, da nadamar abinda ta aikatama gudan jininta da kanta.
Ya Naufal yace nifa nayi mamakin irin wannan k'auna dake tsakaninmu da meerah, ashedai jininace ban saniba, ALLAH mai alkairi kenan, maji6incin al'amuran dake 6oye.
Mama kamar zata cinye Raudat danso, itace jikarta data fara gani aduniya, to cikin 'ya'yan natama wakeda niyyar aure, suwaiba ma Takai shekaru uku rabonta da gidan, 'Daheera kan saidai addu'a.
Hotel suka koma suka kwana, akabar meerah nan susha hirar yaushe gamo da mahaifiyarta.
Amma ina Raudat kuka takwanayi, zafi ya isheta, ga sauro, abinda bata Sababah.
Dole washe gari ya Naufal yanemo Generator da AC aka sakamusu, a daddafe sukayi kwana uku, washe gari kuma suka rankaya Kano da nufin idan sun dawo daga Raka Aysha Susan yanda zasuyi da mama, Dan baikamata abarta ananba.
*kano*
.................✍
Kumuje zuwa Guy's😄, Sholyn Ku a kn😉.
😍😍😍😍😍😍😘
[8/25, 9:58 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.