Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt
Chapter 35 of 40
*_part 1_*
(littafi na d'ayađ)
3âŁ5âŁ
Kano tadabo tunbin giwa, kofa dami kazo dagaske munfikađ, amma banda tsiyađ€.
Tunda akace sunshigo Kano farincikin Aysha ya bayyana, babu abinda kake gani tareda ita sai farin ciki tsantsa, itakam tsaf tagane gidansu, dukda canje-canje da'aka samu kuwa, gidanma gaba d'aya ya canja mata, danyasha sabon fenti sai d'aukar ido yakeyi, 'yan anguwa kam sai kalon zuk'a-zuk'an motocin sukeyi, hardasu Kansu masu motocin, ko kad'an babu wanda yagane Aysha, to yama za'ayi kad'auka Aysha bahaushiyace, balle tak'ara girma da k'yau, kaikace irin bak'ak'en Amurakawan nanne, itakam dayawansu ta shaidasu, saidai dukta mance sunansu, murmushi taketa zubawa abinta, dakanta tamusu jagora zuwa cikin gidan, tunda sukayi sallama tafara kwala kiran mama da Ummah.
Fadeela daketa faman jijjigar Ummu-hanee tana kuka talek'o Dan mamakin kiran da ake kwalama iyayen nata.
Tsam tatsaya tana tantama akan shin Aysha ce? Kokuma watace mai kama da Aysha?, gadai kamannina na Aysha ajikin matashiyar budurwar, amma ko dawasa ba'a fara kiranta Aysha ba.
Da gudu Aysha tak'arasa wajen Anty fadeelah, ta mamuk'eta tana ihun murnar ganinta, ihunne yatada Ummah dake barci saboda kanta dakeyin ciwo.
Ai Aysha naganin Umma tasaki Fadeelah taje ta d'are Ummah, wayyo ummanah nayi kewarki wlhy.
Ummah tarungume Aysha, hawaye nazuba a kumatunta tace Aysha dagaske kece? Dama zaki dawo garemu? Shikenan babuke babu bintu?.
Meerah mom ifteehal natsaye suna kallonsu cikin burgewa.
Dad da Naufal maheer suna k'ofar gida suna jiran amusu iso.
Fadeelah Ce taimasu mom marhabun, aka shiga dasu falon Ummah, haryanzu Aysha na nane da Ummah, sai tanbayar mama takeyi, babudai Wanda yabata amsa.
Bayan zamansu ne fadeelah takawo musu ruwa, Ummah kuma takira number mijinta da kawu bilyamin, hardasu Qasim yayunta wad'anda aketa shirin bikinsu.
Aysha tak'ara fad'in Umma wai ina mama?.
'Yar dariya Ummah tayi. Tace Aysha mama na Abuja abinta.
Abuja kuma Ummah? to wajen wa?.
Aure takeyi, Ummah tafad'a tak'aice.
Nan take fuskar Aysha ta canja, idonta tab da kwallah tace aurefa Ummah?. Kishin sosai a idanun Aysha tana taya mahaifinsu kishi.
Babu Wanda hace komai saboda shigowar Mijin mama da kawu bilyamin, saisu dad dake binsu abaya.
Gaishe gaishe aka fara, kowa sai d'okin ganin Aysha yakeyi, ita kuma tana jikin Ummah rik'eda Ummu-hanee.
Su dad sunyima su kawu bilya bayani akan Aysha, amma sun 6oye komai kamar yanda Aysha tabuk'ata, Dan so take da kanta tad'au mataki akan su gwaggo bintu.
Sunce Aysha karatu taje, kuma tun farko a hannunsu take, kowa yaji dad'i kuwa, sunsha godiya sosai.
Kafin kacemi anhad'a musu cima mai k'yau da gamsarwa.
Dukda bawani sabawa da cimar sukayiba sunci babu laifi, ita kanta Aysha ta fara manta cimar k'asarta, (kowa yabar gida, aii dolene gida yabarsa)..
Aranar aka kira mama aka sanar da'ita dawowar Aysha, tayi farinciki, jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano, lokacin suna shirin zuwa asibiti duba gwaggo bintu.
Tace zata taho Kano gobe idan ALLAH ya kaimu.
Kawu bilyamin yace a'a tayi hak'uri, insha ALLAH nanda kwana uku za'a kawo mata Aysha har gida.
Wannanne yasakata hak'ura da zuwan.
Aranar su dad suka baro Kano, Aysha harda kuka dazasu taho, sunyi sallama akan saita zo Abuja, suma daga nan Kaduna zasu tsaya, sai zuwa jibi zasu shiga Abuja, daga nan zasuje sokoto ma.
Zuwa yamma saiga Hafsat, su Rufaida da sadiya ma saigasu, gida yagama had'uwa, Aysha tana tsakkiyar danginta, jitake kamar ta shekara dubu basa tare, sukam sai sha'awarta sukeyi, danta canja musu gaba d'aya, saikace wata baturiya, anyi-anyi takira mama tak'i, dukda d'okin ganinta datakeyi wai fushi takeyi da ita akan tayi aure, hakama Ummah duk haushi suke bata ita adole kishin babansu takeyi.
Makwafta sai shugowa akeyi ganin Aysha 'Yar turai, kai kace wani abin kallo aka kawo gidan.
Koda yake Aysharfa ta cancanci azo kallonta, Dan komai nata ya canja, dolene kaganta ta burgeka harka lalace wajen kallonta.
Har washe gari bata canja zaniba, 'yan uwa sai tururuwar zuwa ganin Aysha akeyi, itakam kowa yazo kar6ar mutumci take masa, dama can ba halin Aysha bane wulak'anta jama'a.
_____________________________
Su mama sun isa asibiti itada Anty Mamie domin duba bintu.
Saida doctor d'in dake dubata yafito sannan suka shiga, gwaggo bintu na zaune akan gado, ta jingina da filo, bishirah nabata abinci, sallama dasu mama sukayice tasakata d'ago ido tana kallonsu da amsa sallamar ahankali.
Ganin mama yasaka gwaggo bintu wata zabura, har taune harshe takeyi wajen fad'in fad'ima! Kece?.
Mama ma tace, "bintu! Dama kece mara lafiyar?".
Hawayene suka shiga zarya a kumatun gwaggo bintu alokacin data tsinkayi muryar Anty Mamie na fad'a mata aii itace Baffansu ya aura kwanaki ko, kuma matarsace tunkan ya aureta, jikinta sai rawa yakeyi, tabbas tasan mama tata6a aure kafin ta auri yayansu, kenan Alhaji Abdallah jigawane dama tsohon mijin nata?, nan take zufa tafara ambaliya akowane sashe najikin gwaggo bintu, fad'i take a zuciyarta nashiga uku ni binta, yanzu yazanyi da wannan kulli? Ina zan samoma matarnan 'yarta? Nasan dolene ta tambayi ina Aysha, ni bintu nashiga Tara, nikuma k'arshena yazo kenan, hajia babba kin cuceni keda shaid'anin daya bani k'arfin guywar yarda daku.
Babu Wanda yazargi wani Abu tsakanin Anty Mamie da mama, duk zatonsu ciwon ne yake damunta, dukda mama tana ganin kamar mamaki gwaggo bintu tayi dakasancewarta matar mai gidanta.
Sunkai mintuna 30 a d'akina sannan sukai musu sallama suka fito, amota mama take sanarma Anty Mamie dangan takar dake tsakaninta da gwaggo bintu (wadda suke kira Maman yara), Mamie tayi dariya, tace haba shiyyasa naga ta nuna mamakinta da ganinki, lallai ALLAH kenen mai hikima.
Mama tace aikuwa dai, (bata fad'ama Mamie komaiba dangane da rashin k'aunar da gwaggo bintu take nuna mata, lokacinda tana matar yayanta).
Harda sukazo gida abin na'a zuciyar mama, amma bata damuba, tunda alhamdulillah 'yarta tadawo gareta.
Gobe idan ALLAH ya kaimuma, zatazo Abuja itada fadeelah.
_____________________________
Washe gari Aysha da fadelah sukayi shirin zuwa Abuja, da mortar haya zasu hawo, amma sai kawu bilyamin yabada motarsa akaisu.
Hakan yayma Aysha dad'i, dan dama batason hawa motar hayar.
Kasancewar tafiyar yamma sukayi sai around 6:30 suka iso anguwar ta mai-tama. Gaban Aysha ne yaketa luguden fad'uwa tunda suka shigo anguwar, danta gane anguwar data zaunace kafin barinta k'asar, mamakine ya isheta akan miya kawo mama nan?, batama tsinkeba saida taga mortar tatsaya k'ofar gidan alhaji Abdallah Jigawa tana horn, kallon fadeelah tayi, tace Yaya fadeelah anan mama take aure?.
Eh, nanne Aysha, fadelah tafad'a kanta tsaye.
Shiru Aysha tayi tana had'iyar yawu, aranta tace *Cakwakiya kenan*, lallai nabar *baya da k'ura*, wannanfa shine *Kwai cikin k'aya*.đ€„
Abubuwa dayawa sun canjama Aysha, bakamar zuwanta da gwaggo bintu ba, taga ancanja gate d'in gidan, hakama ansamu wasu sauye-sauye, fentin gidanma bawanda tasani baneba.dukda sun isa ana shirin magriba ne hakan bai hana anguwar kasancewa cikin hasken wutar lantarkiba, ko ina farr da haske.
'Dan gwari mai gadi dai haryanzu shine gateman d'in gidan, amma yad'an kara manyanta, bakamar sanda Aysha ta sanshiba.
Aharabar gidan baba bala yayi fakin, kamar ankwashema Aysha jini haka tafito daga motar, handbags nasu kawai suka d'auka, sauran kayan baba bala yace suje za'a shigo dasu, fadeela sai zumud'in Shiga takeyi dantayi kewar mama, amma ga Aysha Sam abin Bahaka baneba, tafiya takeyi kwakwalwarta na tariyo mata baya, jitakeyi kamar yauma tazo gidanne amatsayin boyi-boyi Mara 'yanci.
Rungumetan da akayine yasakata sakin ajiyar zuciya da d'ago kanta, Ashe harsun shigo falon batama saniba, mamace tarungume Aysha cikin matuk'ar kewar 'Yar d'iyar tata, itama Aysha ganin haka saita k'ank'ame Maman tareda sakin wani irin kuka dabasan dalilinsaba.
Fadeelah dai 'Yar kallo takoma.
Babu kowa a falon, Duk sun shige d'akuna Dan gabatar da sallah, 'yan uku ne kawai ke k'iriniyarsu.
6angaren mama suka yanda zango, saboda tsabar farinciki mama tama kasama Aysha magana, sai kallonta takeyi tana zuba murmushi.
Ayshar Ce tagaji tace Mamana nayi kewarki, ina sonki, amma shine kikayi aure bansaniba ko? Tak'are maganar da turo Baki gaba.
Daga fadeelah har mama abin yabasu dariya, Dan haka suka dara abinsu.
Mama tace to Aysha ayima mama afuwa, nasan kina kishin babankune, amma inaso kiyarda da k'addara, haka ALLAH ya hukunta mana, nima bawai da son raina baneba kinji.
Aysha ta jinjina kanta, saitaji tama daina jin haushin mamar, wanka sukayi sukai salloli, mama tayima umma-hanee itama, 'yan uku na nane zasu Aysha, Aysha sai dad'i takeji suma yanzu mama ta haifesu dayawa, gata da k'anne maza, abinda tadad'e tana sha'awa kenan.
Bayan sunci abincin da mama ta shirya musu suka mik'e danzuwa gaida mutan gidan, harsun fara shirin Fita saiga Anty Mamie tashigo, a'a inakuma zakuje?.
Fadeelah tace zamuzo gaishekune Mamie.
A'a fadeelah kuzauna Ku huta, wanan wahalar tafiya aii tayi yawa, da safe sai'a gaisa aii, nima sallah natsaya yi shiyyasa ban lek'oba tunda kuka shigo, Dan 'yan uku sunkaimin labari.
Mama tayi dariya, aii wad'annan 'ya'yan naki bilkesu sune redio mai jini.
Mamie ma dariya tayi, tace a'a a'a, ai abunda suka gani suke fad'a.
Aysha sai kallon Mamie takeyi tanajin k'aunar matar aranta, amma talura bata ganetaba, taji dad'in hakan, Dan dama bata fata kowa yaganeta agidan, hakanne zai bata damar aiwatar da aikinta akan su hajia babba hankali kwance.
Mamie tace d'iyata 'yan turai, ya turai da karatu?.
Murmuahi Aysha tayi, cikin rissinar dakai tace alhmdllh Mamie, munsameku lafiya?.
Lfy lay muke, yagajiyar hanya?.
Alhmdllh.
To masha ALLAH, mamie tafad'a tanama ummu-hanee dake hannunta wasa.
Mamie ce tahanasu zuwa gaida kowa agidan tace su huta, dama baffah bayama k'asar, Ammah kuma tana Jigawa. Daman takanje tayi dogon Hutu a can idan tajuyo mata..............âđż
*_I love you allđđđđđđđđ_*
[8/26, 8:48 PM] Aisha Galadima: *_TypingđČ_*
đ€°đ»
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{đȘwuk'a bata hudashiđĄ}_
*_Bilyn Abdull ceđ€đ»_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*đ
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
đ€Čđ»đ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.