Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt

Chapter 31 of 40

*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)

_bara namik'o gaisuwar ban girma my kakus, (maimuna) & Maman Khaleed & Dan mom, ALLAH yabar zuminci._
_bilyn Abdull namik'o gaisuwar ban girma agareku_
😍😍😘✌🏻

3⃣1⃣

Tab lallai yarinyar nan tantiriyace J, kallafa kaga shigar dake jikinta?.
In banda abinka youseef ba 'yar gata baceba, kowafa yasamu rana yay shanya, aii duk Wanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa.
Mafi yawancin yaranmu idan anturosu karatu k'asashen k'etare abinda sukeyi kenan, kadubafa ko agida Nigeria yanda jami'oin mu suke, saikayi babbar sa'a zakasamu Na kirki acikinsu, haka zakaga weekend anata kwasar 'yan matan jami'a zuwa d'akunan maza, kaikace gidan karuwaine, iyaye kuma sunacan sun saki baki 'ya'yansu Na karatu a jami'a, wani har k'afafa zakaga yanayi.
Inhar ak'asarka ana irin wannan 6arnar kuwa, yakake gani lokacin da 'ya'yanmu suka gama samun damar zuwa karatu k'asashen k'etare?.
Shiyyasa Baffah baita6a yarda yakai d'ansa karatu wata k'asaba, kaf d'inmu agida Nigeria mukayi karatu, saidai wani coast yafiddaka amma bashi yakaikaba.
Ai wlhy haka yanada k'yau, nifa tsoronma aure nakeyi, aje a haifamaka d'anda zai kaika lahira baka shiryaba.
Youseef kenan, zakaima ALLAH wayone?, aii ka tabbata yanda kata6a 'ya'yan wasu sai anta6a naka, dama masu iya magana nacewa (wanzami baya son jarfa).
Youseef zaiyi magana saikuma yayi shiru. Saboda isowar Taheer wajen.
Ya zauna yana sauke numfashi. Suduka idanunsu akansa, wai miya farune kaketa wani hura hanci kamar kayi noma?.
Mtsoww kabari kawai j, ALLAH yarinyar can bala'ice, inaga kawai muyi amfani da hanya tabiyu, ita ayanda nalurama bata harka saida turawa.
Murmushin k'asaita ya khaleel yayi, yagyara tsayuwarsa tareda cin serious, ganin haka ya tabbatarma su Taheer amatsayin ogansu zaiyi magana ba abokiba.
Mik'ewa sukayi tsaye suma, suka k'ame dama salutes.
Cikin sanin darajar kai shima yamayar musu murtani, ya kalli agogon dake manne a tsintsiyar hannunsa, sannan yamaida kallonsa ga Taheer, inason magana da headquarter d'inmu nan America.
OK sir.
Taheer yafad'a da girmamawa.
A cikin mintuna dabaifi 5 ba Taheer yagama komai, daga nan kai tsaye babban Office d'in shugaban Interpol Na America suka nufa.
Sungama dukkan shigi da ficinsu, tareda samun had'in guywar 'yan uwansu police interpol na k'asar, insha ALLAH a Daren ranar suka had'a tarkon kama Alhaji Alasan Atiku kwangila..

___________________________
Baffa ya kalli matan nasa, ransa duk a6ace yake, yace ina Laurah?.
Kowa tayi shiru batareda sun bashi amsaba, Dan basusan mizasuce dashiba.
Shima baidamu dajin amsar tasuba, yaciro wayarsa daga aljihu yakira hajia babba, harta yanke bata d'agaba, Yakuma kiranta a karo Na biyu, nanma saida takusan tsinkewa tad'aga tana Jan tsaki.
Kina INA? Baffah yayi maganar cikin serious.
Nafita, itama tafad'a adake.
OK, yamiki k'yau sosai, kuma INA mai tabbatar miki inhar Baki dawoba wlhy saikinyi Dana Sanin fitarki, idan kinji wasa kuma kada kidawo d'in, ya yanke wayarsa kawai.
Ran hajia babba ya6aci, amma tasan sarai wanene Baffah, baya d'aukar raini koda wasa, duk iskancinta tasan kalar datake masa, amma tanajin shakkarsa sosai.
Tsawa tadakama driver, wadda tasakashi taka birki cikin hanzari, balbaleshi tayi damasifa akan Yakoma gida.
Su Kansu su hasnah Lamarin yabasu tsoro.

Afusace tashigo 6angaren baffa, babu Wanda yace da ita k'ala acikinsu umme amarya, baffa kam dama tun d'azu yashige bedroom d'insa.
Sai surutai hajia babba takeyi, wai anyi munafurcinta, babu Wanda yakulata har baffa yadawo falon.
Cikin tsare gida yafara musu fad'a, yace, ''kukam wai sai ayaushene? zakusan kun girma, gida cikeda 'ya'yanku da surikai amma bakubar raba abin kunyaba, wlhy inamai gargad'inku akan wannan yazama shine first and last dazaku k'aramin haniya agida, nagaji da iskancinnan hakanan, da girmana kuringa zubarmin da mutunci wajen Matan 'ya'yana da 'yan aikin gida, awannan karon gargad'i namuku, next time idan aka sake mataki zan d'auka akai.
Daga nan kuma saiya kwantar da murya cikin hikima da dattako irin Na dattijan kwarai yafara musu nasiha, duk kuma sai jikinsu yayi sanyi, har ita hajia babba d'in, suduka hak'uri suka bashi da alk'awarin insha ALLAH baza'a sakeba.
Yayi farinciki, da fahimtarsa dasukayi, sund'an ta6a hira daga nan ya sallamesu.
Fitarda hajia babba batayiba kenan aranar.
Suna fitowa daga ang6aren baffa suka Tatar Zunnurain yadawo da Ammah daga asibiti, dama yakaita taga likitane saboda ciwon k'afarta.
Duk rissinawa sukayi suka gaisheta, tareda mata sannu.

______________________________
A Canada kam su Aysha sunata shirin bikin ya Naufal da Anty meerah, shirin biki akeyi Na 'yan gata, dukda bawasu dangine a can d'inba saidai 'yan uwan momy, kuma duk Christen ne, saikuma abokan arzik'i Na dady da ya Naufal, Maheer ma danasa gayyar, hakama Aysha da Ifteehal.

Amarya meerah tasha k'yau, dukda takan ke6e tasha kukan bak'incikin halin rayuwa data Shiva abaya, wai yanzu amatsayin budurwa zatayi aure ko bazawara? Shikenan bazata kai abinnan mafi daraja ga kowacce 'ya macen kwarai ke zuwa gidan mijinta dashiba?.
Sauk'in tama ya Naufal yasan komai dangane da rayuwar datayi abaya shida iyayensa, amma ya amince zai aureta ahaka, Dan acewarsa aii ita yakeso ba jikintaba.
Takanji a zuciyarta kamar ta cutar da Naufal d'in, Dan bai dace da Auren mace irintaba, dukda yasanar da ita gaskiya yana Neman mata, amma insha ALLAH ya bari, Dan tundaga lokacin dayaje Islands UK bai k'ara tarayya dawata maceba.
Amma dukda haka tad'aukama kanta alk'awarin ko a nangaba Naufal yace zaiyi aure bazata ta6a hanashiba, wannan shine tukuycin dazatama Naufal saboda sadaukarwar dayayi akansu a rayuwa, bakomai yasakata amincewa da aurensaba sai k'yautatawar da yayi musu shida iyayensa, amma dukda haka saida akasha gumurzu da ita kafin tayarda da soyayyarsa, Dan tadad'e dacire kanta alayin wad'anda zasuyi aure aduniya.
Amma shi ubangiji gafurunne kuma rahimun, saiya shiryeta alokacinda batayi zatoba, yakar6i tubanta batareda dubi da munanan ayyukan data aikataba, harma yadarajata ya k'addara yin aure acikin kundun tarihin rayuwarta, itakam mizatace wa Ubangiji? Banda tayita bautamasa da godiya agaresa, tak'ara tsoronsa da taka tsantsan wajen gujewa sa6a masa. Hawaye suka cigaba da zirara a kumatunta.
Ahankali taji ana share mata, tasan Aysha ce, danhaka tarik'e hannunta tareda jawota jikinta suka kuma fashewa da kuka.
Anty meerah ki godema ALLAH, yakamata kidaina kukannan, komai yayi farko zaiyi k'arshe, ALLAH yamana sutura irin wadda ba kowa yake baiwaba, banta6a tunani rayuwa zatayi mana k'yawun ganiba, amma dayake bamuda hak'in kowa akanmu sai ALLAH ya katangemu saboda adalcinsa.
Bamuda abinda zamu sakama ya Naufal da iyayensa dashi, saidai muyita rok'a musu gafarar ubangiji har randa zamu amsa kiransa.
Dan ALLAH kibar kukannan haka, kinga karkije gidan ya Naufal arame.
Murmushi meerah tayi, tasharema Aysha hawaye, itama ta share mata.
Ya Naufal dake tsaye a bayansu shida mom suma duk sai tausayinsu yakamasu, harga ALLAH suna k'aunar Aysha da meerah, saboda yaran komai nasu abin koyine, kawaidai k'addarace tayi haijiya da rayuwarsu, gashi kuma sun kar6eta da hannu biyu, basu zama masu butulci ga ALLAH ba.

Ahaka aka shiga shagalin biki, dukda bawani armashi yayiba kamar anan gida Nigeria daza'ayi cikin dangi, amma komai yatafi cikin tsari, meerah tazama amaryar Naufal babu uwa babu uba alamarin aurenta, wannan shinefa maraicin dole, amma tagodema ALLAH, kobabu komai mahaifiyarta ta turota tayi karuwanci saboda kwad'ayi abin duniya, gashi zata koma gareta da aure, wannan kad'ai ayace ga mahaifiyar tata, hardama masu hali irin NATA nason zuciya.

(To halimatus-sa'adiyya & Naufal, ALLAH ya sanya alkairi, yasa musha suna kafin aje Nigeria😂).

_____________________________
Cikin nasara su ya khaleel sun sami damar cafke Alhaji Alasan kwangila.
Dan danan gidajen TV da redio suka d'auka, k'asashen waje dana gida Nigeria, kasancewarsa babban mutum a k'asar ta Nigeria.
Hankalin mutanensa yatashi sosai, ciki harda manyan k'asarnan, Dan sunsan tunda aka fara dashi wataranafa Kansu za'a zo.
Aciki harda manyan ma'aikata na jami'an tsaro a fannoni da dama, cikin ma'aikatar su Ya khaleel ma akwai.
Washe gari suka iso dashi Nigeria, duk k'ok'arin 'yan jarida nasonjin ba'asi akan kamashin ya khaleel yak'i basu had'in kai, daga bayama kashe wayoyinsa yayi yatafiyarsa gida.

Kasancewar weekend ne kuma safiyace yashigo gidan babu kowa afalo, duk yawancinsu sunata barci, sai 'yan aiki kawai dake had'a abinci a kichin, Dan yau aikin hajia babba ne.
d'akin NASA fes yake, Dan kullum sai Anty Mamie tasaka an gyarashi dukda baya k'asar.
Wanka yashiga first, bayan yafito yazura kaya marasa nauyi yay kwanciyarsa.
Har around 12 yanata barci bai tashiba, zuwa sannan mutanem gidan sun tashi, ganin motocinsa da Securitys nasa ya tabbatarma da mutan gidan yadawo, amma babu Wanda yayi yunk'urin zuwa d'akinsa.
Sai d'aya saura yatashi, yakuma yin wanka yay shiri cikin k'ananun kaya yafito, Baffah yafara zuwa ya gaida, sukad'an ta6a hira har zuwa kan aikinsa da kama alhaji Alasan dasukayi, anan yay break fast, daga nan yaje suka gaisa da Ammah, wadda tatasashi gaba da fad'a akan rashinyin aure, hak'uri yabata da tabbatar mata insha ALLAH yakusa auren.
Amma ta ta6e baki tana fad'in ALLAH yasa, kullum ma bahaka kake fad'iba, Iro aurofa shine cikar kamalar kowanne d'a namiji, harma da macen, bakasan yanda rashin aurennan naka ke damunaba, amma nakula ita mahaifiyarka abin ko damunta bayayima.
Kiyi hak'uri to Ammah, insha ALLAH saikin goya yarona.
To ALLAH yasa, yakuma tabbatar dahakan.
Yashiga yagaida mama da Anty Mamie, harda umme amarya, fitowarsa falo k'annensa duk suka gaidashi damasa sannu da zuwa, daga nan yatafi gun tsohuwarsa, kusanma a can ya wuni.

___________________________________
Akwana atashi babu wuya wajen ALLAH, su Aysha an kammala karatu, zuwa yanzu kam tazama cikakkiyar 'Yar jarida, tasamu result mai k'yau, itada ifteehal, kowa yayi farinciki agidan, Dan har party aka shirya musu.
Sunata shan hutunsu agida, alokacin kuma dady yace, sufara shiri zasuje Nigeria, jira kawai akeyi Anty meerah ta haihu, Dan cikinta yatsufa sosai, haihuwa ko yau ko gobe.
Murna dai anar Aysha harta rasa wace iri zatayi, wai itace zata koma k'asarta ta haihuwa, k'asar da'aka rabota da it'a tak'arfin tsiya, k'asarda zalincin wasu mutane yasakata nisa da ita, k'asar datafi k'auna fiyeda kowace k'asa a duniyarnan, k'asar data share tsawon shekaru hud'u bata cikinta, zataje taga mama da Umma, su Anty fadeelah, hafsat, ya Qaseem dasu Rufaida, wayyo dad'i zataje Nigeria.
Dariya su ifteehal suketa mata, itakam ko'a jikinta, murnarta taketa zubawa.
Ana cikin wannan haline sukaji doorbell Na k'ara.
Safwan ne yaje yabud'e, matashin yaro dabazai wuce sa'an Safwan d'inba yamik'ama safwan bag🛍 mai k'yau, wai abama sholy.
Safwan yakar6a cikin mamaki tareda maida k'ofar yarufe.
Aysha yamik'ama sak'on ta amsa tana tafad'in namiye Safwan?.
Bayani yayi mata.
Harzata bud'e mom tahanata, tace, ''taje d'aki tabud'e".
Batayi musuba tatshi itada Ifteehal sukaje d'aki.
🎁bud'ewa sukayi, flower🌹ce tanata k'amshi, saikuma kwalba mai k'yau wadda ruwa ke'a ciki da tsuntsaye biyu,🕊 d'aya da fire a bakinsa yana mik'ama d'aya, sai zobuna biyu a can k'an tsuntsayen d'aya kan d'aya💍, k'ananun kifaye nata yawo aruwan.
Aysha tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka ta6a bata a UK 2years dasuka shud'e, hartayi tunanin Ariana Ce takawo mata.
Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta, kwalbar ruwa maid'aukeda kifaye da'aka kawo mata awancan karon tad'ako, iri d'ayace data yau, banbancinsu kawai tayau akwai tsuntsaye da zobuna acikin ruwan bayan kifaye, ifteehal ma kallonta takeyi cikin mamaki, da sauri ta y kwalaben takoma kan sak'on, yauma akwai k'aramar takarda, tazarota da sauri tabud'e.

*_Ranar aurena yazama gaske mafarkina, nacika burina innasameki miradina!._*

Wannan shine kawai arubuce, Aysha ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?, abinda ya d'aure mata kai shine wak'ar Hausa, to, wanene? Kodai ya Naufal ne? Kai anya kuwa?.
To amma idan bashi baneba itakam wanene, hartayi rayuwar islands tabarota bata ta6a had'uwa da kowaba bahaushe sai ya Naufal.
Kuma tabbas mai wannan sak'on yasantane, yanakuma tareda ita tun'a UK d'in.
Tadafe kanta datakejin yana Sara mata, wani k'aramin akwati takuma fiddawa ja, yayi k'yau sasai, tabud'eshi, had'ad'd'en zobene Na diamond💎.
Yahad'u sai d'aukar ido yakeyi, acikinsa anyi wani rubutu da salo.
Su Aysha sungaza gane me aka rubuta acikin zoben.
Saikuma turare mai masifar k'amshi, Aysha ta shinshina turaren talumshr idonta.
Jitake tabbas tata6ajin wannan k'amshin, amma a ina?.
Shine abin tambayar.

Koda takaima Anty meerah kayan tagani tayi matuk'ar mamaki itama, sunyi hasashensu harsun gaji amma sungaza gane wanene mai sak'on.
Ita kanta meerah tafara zargin kodai Naufal ne?.
Dan shekara 2½ dasuka wuce lokacin da'aka kawoma Aysha sak'on farko basu dad'e da had'uwa da Naufal ba.
Anya kuwa bashine mai basajar nanba??.
Zata gwadashi danta tabbatar.........✍🏿

Nidai bilyn ku nace, "ALLAH kad'ai yasan karatun kurma🤣".

*_kumuje zuwa fan's, anzofa wajen😍😍😍😍😍😘_*

*nima nabaku diamond💎💎💎💎💎🤣*
[8/23, 9:23 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*

🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜

*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.