Trending Hausa Novels

Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels

Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt

Chapter 2 of 40

*_part 1_*
(littafi na d'aya)

0⃣2⃣

Bak'aramin kuka Aysha tasha ba, hakama mamanta tayi kukan a 6oye, fadeelama tasha kuka Dan za'a rabata da 'yan k'annenta masu d'ebe kewarta, amma babu yanda zatayi, Dan dolene kowa yabi umarnin k'anin mahaifin nasu, Wanda ayanzu ya maye musu gurbin mahaifi agaresu, tunda basuda kamarsa.

Tunda safe gwaggo Asma'u tawuce da Abba katsina, (a can take aure).
Hakama uncle Ahmad yawuce da Ummulkhairi Jigawa wajen aikinsa (shima iyalinsa nacan).
Itakam Aysha sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu da safe zasu wuce da gwaggo bintu zuwa Abuja.

_______________________
*Washe gari*

*(Sabuwar rayuwa)*

Haka Ai'sha tatashi sukuku kasancewar kuka datasha itada fadeelah yayarta a daren jiya, haka sukaita kuka har saida mama ta tsawatar musu, daga baya kuma tayi musu nasiha da nuna musu muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara, tak'arashe dayima Aysha nasiha akan takare mutuncinta a bak'on muhallin dazata tsinci kanta.
Kada ta kasance mai kwad'ayi da shiga sabgar da babu ruwanta, banda rashin kunya ganagaba da ita, takuma ringa yima gwaggo bintu biyayya amatsayinta na k'anwar mahaifinta, kada tasake wani yarud'eta ya lalata mata tarbiyyar dasuka gina tsawon shekara 13, koda kuwa a yaran gidanne, tarik'e addininta kada tazama mai sakaci dashi, takula sosai.
Nasihar mama tashigi Aysha, kuma ta kar6a cikin kuka da alhinin rabuwa da mahaifiyar tasu, wadda tunda tayi wayau basu ta6a rabuwaba koda na kwana d'aya, Dan marigayi baya barinsu zuwa ko ina Hutu, indai ziyara tawuce ta wuni d'aya basa zuwanta.

Haka suka kwana Aysha na kwakume da mama har asubahi, bayan sunyi sallar Asuba gwaggo bintu tashigo tace Aysha tashirya dan sotake su Isa da wuri.
Itadai mama batace uffanba, tana zaune tana lazimi, Aysha tamik'e tana shiri tana kuka, gwaggo bintu kam tafita tanamai ta6e bakinta.

*6:30am*
Aysha tashiga d'akin Umma (abokiyar zaman mama), Umma nazaune afalo tana waya Aysha tashigo ta zauna ak'asa tana sharar kwallah.
Ganin haka Umma takatse wayar tata, takamo hannun Aysha tamik'e, kusada ita ta zaunar da'ita tareda rungumeta, ALLAH Sarki shatu d'iyar albarka, kiyi hak'uri kinji, yazamuyi, haka ALLAH ya tsaramana rabuwa daku badan mun shiryaba, inamiki fatan Alkhairi kinji, kibar kuka tunda kinga nanda wata 1 ma zaku zo bikinsu Hafsat, insha ALLAH zamu kasance masu muku Addu'a aduk inda kuka tsinci kanku, amma kirik'e addininki, kada kiyarda kiyi sakaci dashi, banda biyema shed'anun mutane, kitsare mutuncinki kikula da kanki kinji, ALLAH yabamu hak'urin rashin juna, ALLAH yajik'an Malam.
Sosai Aysha taji dad'in nasihar Umma, Dan tana kallontane tamkar mama, tanajin dad'in yanda Umma da mama ke zaman lfy, tunda take bata ta6ajin sunyi fad'aba, ko kuma habaici irinna kishiyoyi.
Gwaggo bintu ce shigo tana fad'in yaya barirah barta mutafi hakanan, nikam ina mamakin son 'ya'ya irin naku, yakamata dai kusama zukatanku salama.
Umma batace komaiba, Dan tasan bak'ar magana gwaggo bintu tafad'a mata, kuma idan dasabo sun sabaji, Dan kokad'an gwaggo bintu batada kirki, (irin dangin mijinnanne masu d'aukar matan 'yan uwansu da zafi).
Sudukansu ba k'aunarsu takeba, saidai tafi nuna k'iyayyarta ga Maman Aysha, kasancewar Maman Aysha tanada zafi, bata barin saita kwana, Dan bata ragama gwaggo bintu kokad'an.
sunaji suna gani gwaggo bintu tad'auke Aysha suka tafi.
Kukakam sunshashi, barema sa'adiyya da Rufaida, wad'anda suka kasance kusan sa'anni, amma yazasuyi an rabasu da 'yar uwarsu.
Mama kam k'in fitowama tayi daga d'akinta harsu Aysha suka tafi.

*_ABUJA_*

K'arfe 12:30 a garin Abuja tayi musu, tunda sukataho Aysha tanata barcinta, bayan tagama shan uban kuka, kokad'an gwaggo bintu batace mata uffanba barema ta lalasheta, sun tsaya awata tasha wadda Aysha batasan inaneba, daganan suka shiga wata taxi wadda tatsinkayi maganar gwaggo bintu tana fad'in akaisu mai-tama.

Tafiyar dabata wuce 47mnts ba takawosu wata katafariyar anguwa, mai k'yawun gaske, wadda aka k'awata da manyan gidaje na alfarma, tun ahanya Aysha taketa yaba k'yawun birnin na Abuja, aganintama yanda ake fad'arsa yaci uban haka k'yau, Dan wlhy kamar ba 9ja ba.
Tunanin Aysha baikuma tainkewaba saida suka kutsa kai cikin gida mai k'aton bak'in gate, Wanda ba'a bud'e musuba saida mai gadi yatabbatar dasu waye, ganin gwaggo bintu yasashi washe baki tareda bud'e musu k'ofar.
Mai gadi yace, "Maman yara kece yanzu da rana tsaka?.
Wlhy kuwa d'an gwari nice, nasameku lfy?.
Lfy lau, yak'arin hak'urinku?.
To sai godiyar ALLAH, d'an gwari, bara muk'arasa ciki, namaji gidan tsit ko lfy?.
A lfy lau, kinsan yara suna makaranta, samarin gidanma duk sunfice wajen aiki, wasu kuma makaranta. Hajiya babba ma tana wajen aiki.
Sanin shegen surutun d'an gwari yasa Gwaggo bintu katseshi dafad'in to ALLAH yadawo dasu lfy bara muk'arasa muhuta.
Har sun fara tafiya d'an gwari yace, "Maman yara! Ina kuma kika samo mana wannan mai k'yau d'in haka?.
Cikin k'osawa da surutunsa tace, " d'iya tace. Batajira amsarsaba tacigaba da tafiya, ganin haka yasa Aysha tacigaba da binta abaya.
Masha ALLAH!, Aysha tafirta ahankali Dan ganin wani katafaren falo mai kamada gari guda, iya had'uwa falon yahad'u, ank'awatashi da kujeru sets uku akowace kusurwa, set d'aya jajaye, d'anyan farare, d'ayan bak'ak'e, kowanne 6angare kuma akwai kayan kallo, sai can gefe ankafa dogon tebir mai d'aukeda kujeru rututu, aranta tace kaji wani dinning saikace tebirin taro.
Babu kowa afalon, sai sassanyan k'amshi dake tashi acikinsa, Dan ko'ina tsaf yake, kuma k'al-k'al, babu wutar lantarki, wannan yasa akad'an d'aga wasu daga cikin labulolin falon hasken rana yashigo, dukda kuwa a gefen danning akwai wani dogon gilas fari tas da'aka k'awata wajen dashi, hakanne yak'arama falon k'awataccen haske mai cika idanu.....
Jin an mangareta yasata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin, gwaggo bintu ce ta watsa mata harara amma batace komaiba, sai yanzu Aysha tafarga da matar dake tsaye cikin shiga ta alfarma, bazata wuce shekaru 53 ba aduniya, saidai yanayin jikin k'iba datake dashi yak'ara mata yawan shekaru da girma, durk'ushewa Aysha tayi awajen tana gaisheta.
A d'an yatsine ta amsa, saidai bata d'aure musu fuskaba, amma dukda haka Aysha taji babu dad'i.
Maganar gwaggo bintu taja hankalin Aysha, cikin muryar ladabi gwaggo bintu ke fad'in hajiya ga d'iyatanan nazo da ita danta d'an ringa taimakona dawasu ayyukan saboda girma dake k'ara saukamin.
Yayi.
kaiwai hajiya tafad'a, sannan tagyara zaman Jakarta tana fad'in nawuce aiki saina dawo.
Kai gwaggo bintu ta jinjina tana mata addu'ar dawowa lfy.
Jikin Aysha yayi sanyi sosai, Dan yau taga wulak'anci irinna masu kud'i da'ake fad'a, ko kad'an batason dizgi arayuwarta, saima abinda yafi firgitata shine furicin gwaggo bintu datace wai tataho daita danta tayata aiki. Kenan aikatau aka taho da'ita tayi?, gabantane yayi mummunar fad'uwa, da sauri tace kai ALLAH ya kiyaye, nida gatana nazama 'yar aiki? Ina bahaka baneba, banji zance daidaibane.
Jan hannunta gwaggo bintu tayi suka nufi wajen dining table, wata k'ofa daked'an gefe ta Gila's suka nufa, gwaggo bintu ta danna wani green d'in Abu k'ofar tabud'e, wani k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'a yadoki hancinansu, mutanene ak'alla sunkai hud'u a kichin d'in.
Kusan atare sukace lale marhabin da Maman yara, baki sosai gwaggo bintu ta washe tareda musu sannu da aiki, tak'arasa gaban wata k'yak'yk'yawar mace, fara tas da'ita, itama tanada d'an jiki, amma matar d'azu tafita k'iba, ita kuma wannan kamar zatafi ta d'azun shekaru, Dan zatakai ak'alla 48year's aduniya, saidai k'yawunta da kwarjininta sun 6oye yawan shekarunta, (aganina harda jin dad'ima) tana sanye da doguwar riga bak'a wadda tak'awatu da adon fararen duwatsu, tayi rolling d'ankwalin rigar a kanta, bak'aramin k'yau tayiba kuwa, kaikace tafito daga jinsin larabawane.
Durk'usawa gwaggo bintu tayi yanzuma, cikin nuna girmamawa tace hajiya ina yini? Munsameku lfy?.
Fuskarta d'aukeda murmushi tace lfy lau Alhmdllh Maman yara, yak'arin hak'uri kuma? ALLAH yagafarta masa.
Ameen yarabbi hajiya, ya yaran?.
Duk suna lfy. Kowa yana makaranta.
Aysha dake durk'ushe itama tace inayini?.
Kallonta sosai hajiya tayi, haka kawai taji girarta tadama ta harba, hakama k'irjinta saida yad'an buga, ahankali tafirta "innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un". Sannan ta amsama Aysha gaisuwarta, har yanzu idonta nakan Ayshar, tace Maman yara wannanfa?.
d'iya tace Aunty Amarya, tawajen mai rasuwarce nataho da ita.
ALLAH sarki 'yanmata ya sunanki?.
Kan Aysha ak'asa tace, "A'ISHA!".
Masha ALLAH Ayshatu humairah, yahak'urin rashin mahaifi?.
Idon Aysha taf da kwallah tace, " Alhamdllh mama.
Aunty Amarya taji dad'in sunan da Aysha takirata dashi, tace ALLAH yagafarta masa, yabaku hak'urin rashinsa kinji.
Kowa a kichin d'in ya amsa da amin.
Bayan gwaggo bintu tagama gaisawa da sauran mutanen sukaimata gaisuwa, Aysha dai kuka yahanata gaidasu.
Kulada kukan datakeyi hajiya tace, "Maman yara kushiga cikin Ku huta kafin muk'arasa girki, yau mun makarane wlhy.
Da girmamawa gwaggo bintu ta amsa tareda Jan hannun Aysha suka fita.
Binsu da kallo hajiya tayi, wani tausayin Aysha da k'aunarta suka tsarga zuciyarta lokaci d'aya, haka kawai yarinyar tashiga ranta, (amma saita alak'anta hakan da tausayinta na maraici).

Nace humm anya kuwa Hajiya?.🤔

Daga nana fita suka kumayi daga falon gaba d'aya zuwa wani gini madaidaici dake can baya, shima yanada k'yansa, amma k'aramine sosai, suntadda matsakaicin falo mai d'aukeda kujeru set 1, sai d'akuna ak'allah hud'u, gwaggo bintu tabud'e d'aya da makulli suka Shiga, d'akine madaidaici mai k'atuwar katifa, sai wardrop d'in bango da abinda ba'a rasaba.
Kaya kawai suka ajiye gwaggo bintu tashige wata k'ofa, inaga band'akine awajen.
Wannan yatabbatarma Aysha shine 6angaren dazasu zauna kenan.
Ba'a wani d'au lokaciba gwaggo bintu tafito, da'alama alwala tayi, tace Aysha taje itama tayi.
Bayan sun gabatar da sallah cikin wad'anda suka Tarar a kicin takawo musu abinci, zama tayi suka k'ara gaisawa da gwaggo bintu.
Daganan surutu ya 6alle a tsakaninsu Wanda yawanci duk gulmar 'yan gidance da labarin abinda yafaru bayan tafiyar gwaggo bintu wajen rasuwar abbasu Aysha.
Itadai Aysha taci abincinta, tana kuma saurarensu daki-daki.
Zuwa can iya Hama ta mik'e, tana fad'in bara naje Na huta kafin uwar saka aikincan takiramu, kinsan duk ranar aikin Hajiya Bilkeesu babu mai Hutu agidannan, itabata hutaba batabar wani yahutaba, barema yau Alhaji Na gari.
Ha6a gwaggo bintu tarik'e tana fad'in ke Dan ALLAH?.
wlhy kuwa yana nan, yau kwanansa uku da zuwa, jiya hajiya babba ta ajiye aiki, yau hajiya Bilkeesu takar6a.
Cikin magana irinta gulma gwaggo bintu tace, haba nifa ko ince, nayi mamakin tadda hajiya Saudah agida irin lokacinnan.
Ina hama ta ta6e baki tana fad'in hummm, kemadai k'yafad'a aii. Daganan tafice abinta.
Aysha tace, "ALLAH ya k'yauta azuciyarta, dankuwa su gwaggo bintu sun bata mamaki sosai, suna k'ark'ashin arzik'in mutane amma suna gulmarsu da saka musu ido alamarin gidamsu...............🖊

*I love you all my fan's*😍
[8/7, 7:36 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*📲

🤰
*_CIKI DA GASKIYA.......!!_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_

*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜

*Sadaukarwa*
_My sweet dady_
(ALLAH ya gafarta maka)🤲🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.