Ciki Da Gaskiya Littafi Na Daya Complete Hausa Novels
Reading file: Ciki Da Gaskiya Part 1.txt
Chapter 27 of 40
*_part 1_*
(littafi na d'aya📕)
_Sak'on gaisuwar nakune yau 'yan group d'in miss xoxo *HOME OF NOVELS & HAMAGEE AND FAN'S*, gaisuwar ku babbace ina godiya da k'auna._
_inayinku wlhy, irin sosai d'innan😍😍😍😘✌🏻_
2⃣7⃣
Cikin rawar baki data jiki meerah tace, umm...um Anty kubra ina kichin ne, sanyi nakeji shine nadafa shayi nad'ansha a can.
Bata jira cewar Anty kubra ba tafad'a d'aki wuff.
Haka kawai kubra taji bata yarda da meerah ba, dasauri tamik'e tanufi d'akin nasu.
Saidai tana shiga ta iske meerah kwance agado tana hawaye.
Kuka kuma? Waike mike damunkine? Naga wannan karon tunda Nazo duk kinwani canja? Kodai wani yafara tsara miki wani abune?.
Zaune meerah tatashi, a'a Anty zauna kiji abinda yasakani kuka, wlhy Naufal ne ko! Wai mukai fad'a jiya, shinefa yace wai murabu kawai, nikuma wasu kud'i nakeson tatsa ajikinsa, idanma zamu rabunne saimu rabu, tunda dama kinsan mu rayuwarmu babu doguwar soyayya.
Dariya Anty kubra tayi, tace, akan wannan kike 6ata ranki, kwantar min da hankalinki, bayau saura kwana 6 birthday d'in John ba? Kuma yace anan k'asar zaiyi celebration?.
Eh Anty.
To aranar zan koya miki wani salon dazakiyi maganin iskancinsa, ki gayyatoshi kedai.
Cikin murna meerah ta rungume kubra, kekyace murnar gaskiya takeyi, amma a can cikin ranta fad'i takeyi nima aranar zanbaku mamaki aii. Dan nasan dukkan shirin dakukeyi akan Aysha ranar.
Bayan fitar kubra ad'akin meerah tad'aga filo tazaro box d'innan, dama tanajin tafiyar Anty kubra tacusashi awajen.
K'ark'ashin gadomsu tasakashi itama tafad'a wanka cikin farincikin tasamu nasara.
Bayan tafito tad'auki wayarta tayima ya Naufal text message, tana turawa tatshi tahau d'aukar abubuwansu masu muhimmanci tana shiryawa a k'aramar bag.
Saida tagama tsince komai tas sanan tad'aukar musu kayan dabasufi seat 5-5 ba suma tasaka awata bag d'in.
Kafin Aysha tashigo tagama komai tasaka bag d'in cikin wardrobe nasu.
Koda Aysha tashigo bata Sanar mata komaiba, fira sukad'an ta6a Aysha tayi barci, itakuma tatashi tafita fallo kar a d'auka wani abun suke kullawa.
Da daddare meerah tashirya tafita club kamar yanda suka saba, Aysha kam barcima tayi kwanciyarta.
Bayan kowa yagama kwalliyarsa tarashin mutunci yafita, meerah tadawo gidan, dama tunkan tafita saida tad'auki mataki akan CCTV d'in dake falonsu data k'ofar dazaka fita zuwa titi.
Bag's d'inan tad'auka tafita dasu, ya Naufal dake mota takaimawa, yauwa ya Naufal kaje dasu, sauran bayani kuma saimun zauna, insha ALLAH zakaji komai daya angancemu a wannan karon.
ALLAH Sarki Naufal sarkin sauk'in kai, murmushi yamata tareda fad'in karki damu, bara nawuce kada wani yadawo cikin 'yanmatan gidan naku.
OK.
Bayan tafiyar ya Naufal meerah tadawo tad'auki box d'in data d'akko ad'akin Anty glory tamaidashi, danta d'auki abinda takeso aciki.
Kuma ficewa tayi bayan tamaida CCTV cemara d'in gidan yanda suke cikin dabara batareda samun wani kuskureba.
Fitarta babu jimawa Anty glory da anty kubra suka dawo sukam, Dan meerah ma taga sanda aka ajiyesu amma tad'an 6uya dankarsu ganta.
Dukda haka saida Anty glory tace nikam sainaga kamar meerah ta gitta yanzunnan.
Kai a'a gaskiya glory, kodai kinsha abinda yafi k'arfin kankine? Cewar kubra.
ALLAH sainaga tamkar itane.
To ba itabace kuwa, idonkine kemiki gizo kawai.
Shiru Anty glory tayi tunda batada hujja.
Duk firar dasukeyi meerah namak'ale tana jinsu, saida taga sunshiga gidan sanan tafita daga Inda take 6oye.
Kusan atare suka dawo dasauran 'yan gidan, daganan suka Shiga ramuwar barci kuma.
_____________________________
Tafiya yakeyi cikin Nutsuwa da k'asaitarsa, kaida kagansa kasan kaga jarumin ma'aikaci, su Samuel na take masa baya.
Inda Oga David yake rufe suka nufa, yaud'inma d'akin dund'um yake da duhu, saida aka kunna fitulu masu hasken tsiya.
Bak'aramin girgiza nayiba daganin yanda aka maida Oga David, gaba d'aya yafita hayyacinsa, Wanda yasansa ada bazai ta6a shaidashiba ayanzun kam.
Khaleel ya zauna idonsa akan Oga David d'in, fuskarnan d'am-d'am babu alamar sauk'i, iska ya furzar daga bakinsa, yad'age gira sama, tareda crossing kafafunsa, cikin muryarsa mairazana marajin magana yace, "David Obiner! haryanzu kana kan bakanka ne?".
Dak'yar David ya iya d'ago kansa, idanunsa suna lumshewa da bud'ewa cikin matuk'ar nuna wahaltuwa, maganarma bafita takeyi dak'yauba, yace young man kona fad'a maka babu abinda zaka iya musu, munada d'aurin gidin manya-manyan jami'an tsaro takowanne fanni, harma acikinku, karkaga kasamu nasara akaina kacigaba da walar da kanka dason kama sauran friend's nawa, nima kuskure aka samu, kuma zanfita, kasaka aranka nakusa fita anan gurin, daga wannan lokacin kuma zan nuna maka k'arfin ikona.
Murmushi ya khaleel yayi, haryanzu kuma idonsa nakan David, yasauke k'afarsa k'asa yanacigaba da kallonsa, kaikace television yasamu, bindigarsa yaciro a k'ugunsa yana gogata a gemunsa, haryanzu baice komaiba, kallon dai David d'in yakeyi.
Su Samuel da youseef ma suna tsaye suna kallon ikon ALLAH, sunsan shirunnan Na J bakomai bane face hasala da zuciyarsa keyi, kuma tabbas yau sai David ya d'an d'anama aya zak'inta..........
Basuko kai k'arshen tunaninsuba sukaji k'arar bindiga da ihun Oga David alokaci d'aya.
Babu Wanda hantar cikinsa bata motsaba, amma gogan naku tamkaa bashine yayi harbinba, yawani d'age gira sama yanacigaba da wasa da bindigarsa hankali kwance.
Saida David yagama ihunsa da murgina-mirginar azabar shigar bullet ajikinsa yakoma fidda numfashi dak'yar ga uwar zufa daketa kwarara tako ina ajikinsa, kaikace wanka yayo, ga k'afarsa da ya khaleel yaharba sai zubda jini takeyi.
My Sweet Friend! Kashirya fad'ane?.
Ya khaleel yay maganar yana latsa wayarsa.
David da azaba ta Isa yace, "bazan fad'aba, amma tunda kace kai jarumin ma'aikacine mai kwazo akan binciken mai laifi mizai hana naga kwazon naka, kana kiran kanka young tiger amma kakoma kare mai dogara ga uban gidansa, mizaisa ka la6e a bayana wajen nuna jarumtarka, inhar kacika tiger kaje daji domin farauto abincinka, hakan shine zai tabbatarmin kaid'in jarumine, amma cigaba daneman bayanai awajena yanasani kallonka amatsayin kare Wanda kullum sai uban gidansa yanemomasa abincin dazaici".
Saida yama David kallon mintuna 4 sannan yamik'e yana wurwura bindigarsa, baicema kowa k'alaba yabar d'akin.
David kuma yakece da dariyar mugunta, dukda muryar tasa agalabaice take.
Bai waigoba, kuma baice kalaba harya fice, cikin hanzari su youseef suka take masa baya.
Koda yashiga office saiya kulle kansa, baya buk'atar kowa yabiyoshi abaya.
Zama yayi yakifa kansa saman decks, maganganun David ne ke k'ona zuciyarsa, musammam dayace sunada d'aurin gindi wajen jami'an tsaro daban-daban, lallai biri yayi kama da mutum, (kullum aiki sukeyi dare da rana amma babu wani sauk'i Na raguwar 'yan ta'adda) wasuma koda ankamasu daga baya sai kotu ta ku6tar dasu, kenan manyansune kefiddasu?.
Ya furzar da huci abakinsa, tareda mik'ewa yashiga zagayen office d'in, tabbas dolene yacanja taku, domin tsuntsu mai wayo tabaki ake kamasa, baikamata bincikensa yatsaya iya nanba, zai fad'ad'ashi domin samun nasarar burinsa, *CIKI DA GASKIYA....* aii wuk'a bata hudashi, yasan zaitsinci kansa a k'alubale iri-iri, amma tabbas ranar biyan buk'ata aii rai ba'a bakin komai yakeba inji k'uda.
Wani malalacin murmushi yasaki, saboda wata mafita da zuciyarsa takawo masa.
Ya lumshe idanunsa tareda rumtse hannayensa biyu✊🏻.
Yace yeeess!!..
Tundaga nan yafara canja taku, yakoma aikin *Sirri* iya kansa kawai, saikuma amintattunsa youseef, taheer, Joseph, Adams, sukansu bakomai suka saniba.
__________________________
Tunda abinnan yafaru da Ngozi da Aysha ta kalleta saitaji kuka yazo mata, tausayi sosai yarinyar kebata, ga matuk'ar tsorata da abin kebata aduk lokacin data tuno yanda john yayma Ngozi kaca-kaca, gaba d'aya tarasa sukuninta, had mafarkin abin takeyi.
Idankuwa john yazo gidan aii yanzu zakiga tsoro ya bayyana a idonta, duksai ta rikice tarasa kwanciyar hankali.
Wasunsu sukan mata dariya, Damata kallon shirme, ciki kam harda Anty kubra.
Idan john yazo gidan haka zaita binta da kallo saikace tsohon maye, itakam daya zoma take shigewa d'akinsu tasaka key, baya binta, Dan acewarsa takusa zuwa hannu, haka kawai kuma bayason takurama yarinyar, saboda jinta yakeyi ajikinsa.
Yau takama birthday d'in john, tunda safe su Aysha basu hutaba, suyi wannan suyi wannan dukda bama agidan za'ayiba, awani hotel za'ayi..
Mai kwalliya ta musamman aka d'akko Dan yima Aysha ita kad'ai, abin yabama Aysha mamaki, dama tunjiya Anty glory tabata wata arniyar riga mai k'yau da fidda tsiraici wai tasaka, Aysha zatayi magana meerah ta zungureta Tahana.
Yaukuma saiga mai kwalliya tazo, yanzuma Aysha tayi yink'urin yin gaddama amma meerah tahanata, tana kuka ana kwalliyar, harsaida mai kwalliya yagaji yamata magana sannan tadaina kukan, kwalliya tafitar hankali akama Aysha, bama kowane zai iya shaidataba idan yaganta, tayi k'yau saikace aljana, hakama datasaka rigar pink, tayi masifar mata k'yau, saidaifa tafidda mata jiki sosai.
Idonta taf da hawaye ta kalli meerah, Anty meerah yanzunan Dan ALLAH ahaka zan fita saikace kafira?.
To Aysha yazakiyi? Tunda haka suka za6i kije wajen aii dole kiyi hak'uri kije, kinsan dai banida wani k'arfin hanaki fita haka, amma ga rigar sanyi kisaka asama, idan sunyi magana kisanar musu sanyi kikeji. Tunda lalla6aki akeyi zasu barki da ita.
Meerah tak'ara k'asa damurya tace akwai wani Abu mai muhimmanci dazaki d'auka agidannan?.
Aysha tace, "Anty kamarya?".
Kamar yanda kikaji nafad'a, aii Hausa nayi miki.
Shiru Aysha tayi tana kallomta, tarasa wace masifa Anty meerah takoya kwana biyun nan?, amma afili saitace bara naduba.
Aysha tagama bincikenta bataga wani Abu muhimmi dazata d'aukaba, hasalima duk taga ankwashe komai, har takardunta Na makaranta daduk wani Abu nata important.
Sai around 9pm agogon k'asar suka fito, kowa yashiga motar saurayinta, meerah batada saurayi yanzu kam, kuma tace kada ya Naufal yazo wajen saboda gudun zargi, Anty kubra tace meerah tashigo motarsu.
Aysha kam awata had'ad'd'iyar mota aka kaita, Ashe john yana ciki, addu'oi taketa zubawa ga gabanta sai fad'uwa yakeyi.
Yayi k'yau shima cikin Suit bak'ak'e, ainahin suffarsa ta bature cikakke tafito, baice ma Aysha komaiba, saidai yakamo hannunta yarik'e, jitai tamkar anjinginata ajikin wuta, sai addu'a takeyi itadai damik'a lamuranta ga ALLAH.
Aysha tanada jiki mai k'yau, Wanda bakowane zai ganta yace shekarunta 15 ba, musamman data kasance doguwa babu laifi, komai nata cif yake saboda tana ganiyar girmane.
Sun isa had'ad'd'en hotel d'in, wajen daza'ayi komai atsare yake, saida kowa yagama shiga sannan john da Aysha suka shigo, wajen dund'um ankashe fitila, har Aysha tafara tsorata saikuma taga haske ya gauraye wajen tareda ihun mutane, flower's akaita watsa musu masu k'amshi, harsuka isa wajen zamansu, Aysha jitake tamkar tayi kuka.
Duk abinda ke faruwa idon meerah nakan Aysha.
Biki yacigaba da gudana, yayinda aketa shaye-shayen giya damasu shak'ar cocaine da sigari, john saifama da Aysha yakeyi tasha wani Abu tak'i, daya d'auki kofin giya zaika bakin Aysha sai meerah ta dallama Aysha harara, da sauri Aysha take kauda fuskarta tak'i sha, k'yaleta yayi tareda kiran abokinsa gefe.
Su sukasan misuka k'ulla, meerah kuma duktana kallonsu, dama tabama Aysha waya, tatura mata message da hausa.
Aysha naganin haka tagyad'a ma meerah kai, idonta tab da hawaye.
Wajen around 12 waje yakacame anata rawa, wasu duk sungama buguwama, hannun Aysha narik'e Dana john kaikace tare aka haliccesu, itadai Aysha binsa kawai takeyi tamkar rak'umi da akala, duk gift d'in da akabama john saiya mik'ama Aysha ta ajiye, ana haka sai akaga waje yayi dud'um ankashe wuta.
Tsorone Yakama Aysha yayinda taji andamk'i hannunta Na dama, Na haggu kuma john yana rik'e dashi, karki damu nice, kiyi dabarar dazaki kwato hannunki wajen john.
To Anty, Aysha tafad'a jikinta narawa, Aysha tad'an matsa jikin john, murya k'asa-k'asa tace baby bara nacire takalmina nagaji dashi.
OK yafad'a yana sakin hannunta.
Aii yana saki meerah taja Aysha suka fito da hanzari, sai k'utsawa sukeyi cikin jama'a.
John kuma tuni ya damk'e hannun wata yarinya atunaninsa Aysha Ce, (dama shine yasaka akashe wutar, Dan soyake yad'auke Aysha yakaita wani d'aki, bayan ya shak'a mata cocaine).
Da sauri yashak'ama yarinyar cocaine, atunaninsa Aysha Ce, cak yad'auketa yafice.
Su Aysha kam ALLAH ya tsaya musu sunfito daga wajen, saidai kuma security suka taresu, saboda ganin yanayin dasuka fito arikice.
Sai magiya sukeyi ank'i barinsu, ga ya Naufal sai kiran meerah yakeyi akan suyi sauri time yakusa cika.
Hazbinallahu wani imal'wakil, kawai Aysha ke ambata, cikin kuka meerah take rok'onsu akan ayshace takeda wani ciwo zai tashi, shine zasuje asibiti, su taimakesu please.
Ganin Aysha Na kuka, kunsan bature da tausayi, saisuka barsu suka fito.
Motar da ya Naufal yazo suka k'arasa wajen da Sauri, amma cikin ilimi sukayi abin, dankar aganesu, saboda lamarine Na CCTV camera ako ina su'acan turai.
Suna shiga motar suka fara hango mutane ana fitowa, da'alama su ake nema, saboda sunga Anty glory da john sunama Security bayani.
Da sauri Ya Naufal yaja motar yabar wajen.
A can kuwa john nad'aukar yarinya wadda yakema zaton Aysha yafita, sai aka kunna fitila, saida yashiga d'akin daya tanada domin keta haddin Aysha sai yayi tozali dawata tsohuwar budurwarsa, wadda tun zuwansu wajen ya ganta, dama itama tana Neman hanyar dazusu had'une da john, amma yanata shareta, saboda aganinta yasamu Aysha, ganin fitilar wajen tamutu shine tasamu damar matsowa gareshi, shikuma baimasan itad'in baceba.
Jefata yayi saman gado kawai yadawo hall d'in da hanzarinsa, Neman Aysha yafarayi, Anty kubra tagansa ta tambayesa, yasanar mata halin da'ake ciki.
Daga nan suka fara Neman Aysha, saidaga Bayama suka farga babu meerah, Anty glory tace suje waje, dama taga tun d'azun Aysha da meerah namaganar kurame, wannan dalilin ne yasakasu fitowa har wajen security.
Sukuma suka tabbatar musu sunga su Aysha, kuma sunfita yanzunnan za'akai d'aya aciki asibiti batada lfy.
Duk sun d'auka gaskiyane asibitin su meerah suka tafi, Dan basu ta6a tunanin meerah zata iya guduwaba.
Mota suka shiga suka nufi asibitin dasukanga likita idan matsala tafaru da d'ayansu.
Su meerah suna hango motarsu alokacin, saboda ya Naufal yatsaya saya musu wani Abu.
Yana dawowa motar meerah take sanar masa taga su john sun biyosu.
Murmushi yayi yace, 'karki damu bazasu ganemuba, tunda basusan motarba, ammafa gaskiya dolene kamar yanda muka tsara gobe kuwuce Canada, abokinama yagama muku komai, Dan haka gobe dawuri zaku tafi insha ALLAH.
nima nanda 2days zan biyo bayanku.
John yanada kud'i sosai, Dan haka zaibi duk hanyar data dace wajen nemanku, kuma zuwa nanda kwana biyu kacal zasu fahimci kun gudu.
Hakane ya Naufal mungode sosai da taimakonka akanmu.
Sai alokacin Aysha tafahimci halin da'ake ciki.
Kuka kawai ta6arke musu dashi saboda tsabar farincikin wannan taimako Na bayin ALLAH, ta tabbata domin ita suketa wannan k'ok'arin.
Harsukaje gidan ya Naufal tana kuka, sukuma suna aikin lallashi.
Bayan sun huta Naufal yakira dadynsa yamasa bayani akansu Aysha kamar yanda yasani, mahaifinsa mutumin kirki yace babu damuwa, aii d'a nakowane, yadaiyi k'ok'ari subaro k'asar kam gobe idan ALLAH yakaimu saboda gudun matsala
Naufal yace to Dady.
Duk yanda sukayi da dadynsa saida yasanar musu, sunyi murna sosai damasa godiya.
Yace karku damu, ayanzu baikamata kukoma Nigeria ba, Dan acan sunada d'aurin gindin yin duk wani 6arna, abune maisauk'i suganoku.
Kuyi hak'uri kuzauna a Canada zuwa wani d'an lokaci saiku koma gida.
Sun yarda da maganarsa, Dan haka suka masa godiya kuwa.
Aranar daga Naufal har meerah da Aysha kwana sukayi akan sallaya suna mik'ama ALLAH kukansu da godiya agaresa.
Washe gari tunda wuri suka fito zuwa airport, dama kayansu ya Naufal yaturasu tun kwana biyu dasuka wuce, tunda shima yana shirin barin k'asarne.
*_airport_*
A airport bayan kammala komai su Aysha suka samu shiga jirgin farko dazai sauka Canada.
Shigarsu babu dad'ewa Naufal ya hango john, da'alama wani abunne yakawoshi airport d'in.
Cikin sauri ya Naufal ya6uya.
Amma yana kallon duk wani shigi da ficinda john yakeyi a airport d'in.
Hankalinsa yakai k'ololuwar tashi alokacinda ya hango john da Security d'in airport d'in biyu sun nufi cikin jirgin dasu Aysha ke aciki.........✍🏿
😬 *_Nima ya Naufal atsorace muke nida masu karatu._*😰
I love you all😘😘😘😘✌🏻
[8/16, 6:32 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.